" dan rashin mutunci shine ina kiranka, kamin bansa saboda hula 'kanci."
Cikin ban ha'kuri affan yace. " wallahi banjiba saboda tv a kunne take, amma dan Allah kiyi ha'kuri."
Cikin isa uwani tace. " maza cire kayanka kamin tausa har inyi barci, kuma saura in kaga nayi barci ka fice yawon banzar ka."
Cikin sauri affan yacire kayansa daga shi sai singileti, da gajeran wando, kallonsa uwani tayi ta kwashe da dariya.
" haba affan kamar kai kanada kudi amma ace gajeran wandonka, robar tasaki jibi sai wani jansa sama kake, Allah ya shiryeka inka futa aganka fes da kai nankwa basu saniba cikin, ba magana, nizo kamin tausa ta." Cikin dariya uwani ke wannan maganar.
Tausa yake yimata hartayi barci, baidenaba saida yaga tayi nisa tukun yakoma falo, alwala yayi domin anfara kiran sallar magariba.
Saida akayi sallar isha tukun uwani ta tashi, ba magariba balle isha, falo tafuto inda ta tarar da najwa na jere abinci.
" kinyiwa kanki 'kiyamillaili da wallahi sai kin gane baki dawayo." Uwanice mai wannan maganar cikin nuna isah.
Itadai najwa bata ce mata cikankiba, tana gamawa tayi d'akinta.
Teburin uwani taje ta zauna,tacika filat, da dambun shinkafa yaji albasa sa zogale gefe kuma ga farfesun kaza, sai lemon kwakwa yaji madara sa ayaba.π
Saida tayi nak tukun. " shegiya ashe ta iya girki haka, amma takesani inyiwa mijinta nad'auka bata iyaba wallahi." Uwanice mai fad'in haka.
Affan ma dayadawo daga masallaci, yabaje tunbi yaci ya koshi.
Falo yadawo yakunna labarai, a tv yana gani uwani kuma ana d'aka ana waya da hafsat ana bata labari, saida karfe 10:00 tayi tukun yakashe kayan kallon ya shige d'aki.
" tsaya mezakayi, naga kana 'ko'karin hawa gado, to wallahi saidai kaje falo ka kwanta, haka kawai yau kaci dammu kadameni da tusa, ka kumburamin ciki, baze yuhuba ungo fulo katafi kan kujera ka kwanta." Uwani ce maiwannan gadarar.
Cikin sanyin jiki affan ya amshi fulon yafuta falo, doguwar kujera ya samu ya kwanta, yana tunanin wannan wane irin bala inee...
*kuyi hakuri da wannan banji dadi wallahi yanzuma daga asibiti nake*
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*wannan shafin nakine 'yar mutan arkilla Allah yakara basira*
*following us as:*
------
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
------
*Check us blogger*
Zamaniwriters.blogspot.com
--------
*Email us your comment and reports*
Zamaniwritersassociaton@email.com
*✍π»shaxeee*
*page 8*
Najwa tana gamawa ta jere atebir din cin abinci, takoma d'akinta,tashi sukayi sukaje sukaci suka 'koshi.
Uwanice tafara magana. " affan inaso kaje gidan hafsa,zaka amso min sa'ko."
Tuni affan yami'ke yayi hanyar waje. " to bara naje saina dawo." Motarsa yashiga yatafi gidan hafsa, akofar gida yaganta zata futa ita dawani dan duniya.
" uwanice tace inzo zaki bani sa'konta in kai mata." Affan ne mai wannan maganar.
Cikin duniyanci hafsat take magana. " ok bara ina dakko maka, dama yanzu nake cewa bara in kai mata, in bata turoba." Gidan takoma, ta dakko 'karamar akwati, ta futo ta bashi amsa yayi, yashige mota ya yo gida.
Uwani ana kan kujera ana cin apple,( abinka da farin shiga saiwani murmushi take kamar king yaga queen d'in saπ)sallama affan yayi yashigo falon, ko amsawa batayiba.
Cikin kulawa affan yace. " gashi tace agaisheki kuma tace zatazo,( to yaushe akayi hakaπ€)."
Wani ta bud'e akwatin, kananun kayane aciki, gaba d'aya ba na kirki duk afige suke, wani dan karamin siket ta dakko ko cinya bai rufeba, kuma rigarsa bireziyyace kawai mai mad'aurin a huya, sun had'u (dan koni sun ban sha awa kamar in kwaceπ)
" ungo affan jeka sako muga yadda zasuyi yimaka kyau." Inji uwani.
" haba uwani taya zan saka wad'annan kayan, kuma na mata." Cikin nuna damuwa affan yake wannan maganar.
Cikin masifa uwani take magana. " in bazaka sakaba saika gayamin, zaka wani tsaya yimin musu, kasaka kagani mana, base ka saka tsumma ba a bireziyyar, maza jeka saka kazo inga ni."
Mi'kamasa tayi ya amsa, yaje yasa kamar yadda tace,kwalla yake yana gogewa abin kunyar har ina, haka yafuto falon.
" woww kaga yadda kayi kyau kuwa, dakai macene daka more, yauwa tsaya in kunna maka wa'ka kad'an taka, dan na dad'e banga ana rawaba." Uwanice mai wannan maganar.
Wakar kujerar tsakar gida tasaka, ta 'kure vol din tibin, rawa yafara badan ya iyaba.
" yabaka girgiza maza kadinga mur gud'a duwawu mana, bakaji taken wa'kar bane." Cikin dariya uwani take wannan maganar.
Haka yadage yanata girgiza( ππwayaga maza da girgiza) juyi jawai yake, yana jijjuyawa, in yafaki idonta kuma ya share hawaye.
Najwa duk tana jinsu dan tana le'kensu ta kofarta, kuka kawai take duk itace sular shigarsu wannan halin, dabata takura masa ba saiya nemomusu yar aiki, datuni suna zamansu lafiya.
Saida yagaji tukun tace ya tsaya haka.
" jeka cire kayan tukun, kawanke min ban d'aki, sannan zakaga kayan barcin dana cire acikin band'akin, kawanke su sufuta." Cikin izza uwani ke wannan maganar.
Tashi yayi ya shiga d'akin,saida ya canza kaya tukun yafara aikin data sakashi.
****************
"Nifa alhj hankalina ya kasa kwanciya, dawannan auren affan din, ga mugayen mafarke - mafarken danake akansa masu muni." Inji umman affan kenan.
Cikin damuwa abban affan yace. " nima haka wallahi shiyasa naketa yimasa addu'a sosai domin abin ba dad'in ji, nayi binkice sosai shiyasa nagayamiki kema."
*asalinsu*
Alhji kabir d'an kasuwane mai tashe, yana zaman lafiya da iyalinsa yabasu tarbiya dai-dai gwar gwado, 'ya'yansa biyu affan sai aisha affan dakansa yace yanason najwa domin yar aminin babansa ce wato alhj abubakar, saita yi wata biyu agidansu, iyayensu sunji dad'i dasuka had'a kansu, anyi bikinsu nagani na fad'a, bayan sun tare da wata bitu najwa ta takurawa affan saiya kawo musu yar aiki saboda zuwa office, dakyar ya yarda, yakawo mata wata tafara aiki, da kwanaki tace bata yimataba,aka canza wata tace itama bata yimataba, saida aka kawo mata yan aiki guda shida tana canzawa, sai akan uwani ta ce tayi mata, iyayenta dana sa basusan abinda yake faruwaba, tunda aisha agidan su najwa take tana karatu saboda gidan yafi kusa da makarantarsu, shiyasa ta koma can, da zama.
*wannan kenan*
*************
Uwani ana zaune a gefan gado affan kuma yana falo.
" affan!! Affan!!! " uwanice take wannan har gagin.
Yana rawar jiki ya shigo.
" kai dan.....
π³π³π³π³π³π³π³π³
*to komai uwani zatayiwa affan Allah yasa karta mareshi*π
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*nasadaukar da page dinnan wa ALJANAR FATIMA aikinki yana kyau*
*following us as:*
Fb.me/ZAMANIWRITERASSOCIATION
---------
*check us blongger*
Zamaniwriters.com
----------
*email us your comment and reports*
Zamaniwritersassociation
*✍π»shazeee..*
*page 10*
"Ace kaida gidanka amma yafi karfinka,dazan iya ai dana tattakata amma ko dogon kallo bana iya yimata." Duk azuciya affan yake wannan maganar.
Itakwa uwani barci harda minshari.
Najwa kuma adaidai lokacin takira ummanta tamata bayanin komai. " najwa duk laifinki ne nabaki tar biya daidai gwargwado,amma kikaje kawayenki suka zigaki,yanzu wa gari yawa duk kanku kunga tashin hankali, abinda nakeso dake kidinga sallar dare kina addu a sosai, sannan kidinga yawan karanta alkur,ani banda wasa da salla,kiri'ke tsafta da girki dannasan kin iya girki saidai 'kiwa ta hanakiyi, kidinga kula da mijinki koda baze kulakiba, wataran da kansa zai dinga kulaki, inkikayi haka zakiga cigaba." Duk wannan bayanan umman najwa ce kemata awaya.
" to umma insha allah zan yi yadda kikace." Najwace mai wannan maganar.
Sallama sukayi ta kashe wayar, tashi tayi tayo alwala ta gabatar da sallah, tadad'e tana kai kukanta gun allah( wai mutane sai anji huya aketunawa da allah sanda kake shanawa mantawa kake dashi.).
Tafi awa biyu, tana addu,oi sannan tashafa takwanta, tuni 'barawon dayafi kowa iya sata aduniya yasaceta, wato barci.
Da asiba kowa yatashi yayi sallah amma banda uwani.
Misalin karfe 7:00 najwa tafuto, zata d'ora girki affan tagani akan kujera yana kallon labarai, zuwa tayi kusa da shi ta tsugunna, sunkwiy da kai tayi,cikin rawar murya tace. " ina kwana antashi lafiya."
Cikin jargagi yace. " waimeyasa zakizo kidameni ne nafuto falo dan in kalli labaran nan,saboda shifa natashi dahuri, nabaro matata tana barci,amma zaki hanani sakat,dan allah 'bace min daga gani."
'Dago kai najwa tayi, ganin fulo tayi akusa dashi ga wayarsa ma ga agogo da zobe duk azube,alamun anan yakwana,murmushi kawai tayi ta shige kichin.
Shayi ta dora doya ta feraye, tawanke ta tas tasami abin goga ku'bewa ta gogata tajuyeta aroba, tazuba su maggi da kayan kamshi, ta jajjaga attaruhu tazuba tafasa kwai wanda ze isheta tasaka ludayi ta juyashi sannan ta dinga bugashi kamar 'kullin kosai saida yabugu tukun ta sami leda ta 'ku'k'kullashi tazuba ruwa atukunya tazubashi ta rufe, saida ta tabbatar yadahu sannan ta sauke ta kunce shi a filet, tabasa kwai aroba ta yayyaka doyarnan kamar yankan awara ta dora mai ahuta tadinga tsomashi a ruwan kwai tana soyawa saida tagama tukun ta juye a kula takai falo tajere shi, shayinma ta kaishi tadawo tafara gyara cikin din,tana gamawa tadawo falo yanzu affan baya nan.
Gyarashi ta fara yi sallama taji anayi, juyawa tayi wata mata tagani yar 'kauye da ita ga 'kullin kaya akanta duk tayi kura da ita, sai washe jajayen hakora take.
Saiga uwani ta futo ita da affan sunyi wanka da kwalliya. " inna kece da sanyin safiyar nan haka
" uwanice mai wannan maganar.
Tuni inna ta 'karasa shigowa falon tazauna akan kujera, tafara magana cikin farin ciki. " wallahi nice 'yannan cewa nayi bara inzo inga yakike, kuma in dan kwan biyu."
Cikin jin kunya uwani tace. " to shi abban fa da yaya yusha,u waze dinga yimusu abinci."
Muskutawa inna tayi tace. " rabu da wad'annan basu damu daniba, kekad'aice kike sona, shi yusha,u yatafi yawon sace sacen sa,kuma inya sami kudi sai yatafi ya kashewa karuwansa, ko ficika baya bani, shikuma babanku kinsan ba..."
" to duk naji mekike so adafa miki." Uwanice tayi saurin katseta haka domin tasan zata iya 'balle mata ruwa, yanzuma duk kunya ta isheta, agaban najwa da affan taketa zuba.
Najwa duk rana jinsu tana aikinta, ko 'kala bata ceba.
Inna ce tafara magana. " adafamin shayi mai kauri sai aban biredi d'an dari biyu sai Asoyan kwai guda shida yaji albasa sai akawomin wannan abunda isa mai shayin garinmu yake shafawa a tsakiyar biredi, shikenan sun isheni, kinsan bawani cin abinci nakeba danaci 'kadan saikiga na koshi, ko ran..."
" ina kwana inna." Affan ne ya katseta dan yaga bayaninta baya 'karewa saidai atsaida ita.
" lafiya kalau yaro, ya hada hada, danna sanka da aiki, da bikinnan naku naga kata hada hada, kayinan kayican ka d'au wannan ka kai wannan, dama haka akeson mutun mai kuzari, kuma kasan wani abu wallahi ingaya ma w..."
" inna ya isa haka kiyi shiru, akawo miki abin karin mana." Uwanice ta taka mata birki.
Uwani ta kalli najwa. " kinji abinda inna takeso ko, base na maimai ta mikiba, maza a kawo mata da sauri.
Najwa batace komaiba domin umman ta tace kome akamata tayi shiru, kicin taje dama ta dafa shayi kwai kawai tasoya tanayi tana dariyar hirar inna. " kai zamusha dirama agidannan kan wannan matar ta tafi."
Tana gamawa ta dakko biredi ta kawo musu falon, harsun fara karyawa ajiye musu tayi ta 'karasa aikinta ta huce dakinta domin takai nata can dan ra karya.
Suna gamawa affan yafuce, uwani bata hanashi ba sanin cewa in ya zauna, inna saita sakata taji kunya, kokuma yafara rainata.
" innah ga d'akina can nada sanda nake musu aiki kije can akwai 'ban d'aki kiyi wanka ki kwanta kiyi barci, kima ajiye kayan ki ad'akin." Inji uwani kenan.
Dakin ta rakata tanuna mata komai, tafuce saida inna tayi wanka sanna ta kwanta sai barci.
Misalin karfe 12:30 uwani tana falo azaune ita da inna, inna sai zuba take uwa kanya.
Najwa ce tafuto tazo gun uwani. " zan d'ora girki maiza a dafa."
" innah mekikeso kici." Inji uwani kenan.
Gyara zama inna tayi tafara lisafi. " adafan shinkafa yar gwamnati domin yar hausa tacika tsakuwa, sai ayimin miyar dage dage tasha kaza, tasoyu sai lemon roba mai sanyi."
Tuni najwa tashige kicin tana bude firig ta dakko miyarta dama yanzu dayawa takeyi ta ajiye, tana amfani da ita ahan kali, shinkafa ta dora, tana dahuwa ta tace ta juye a kula, ta dora taliya, itama tana dahuwa tajuye ta ta dumama miyar tazuba a kula tamaida ragowar, ta dakko salak da kabeji ta yanka tawanke ta dafa kwai ta yayyanka akan salak tasaka kokwamba bayan ta yayyankata kanana, tazuba waken gwangwani da bama tajuyasu, ta saka afirij domin yadanyi sanyi, ta dakko abarba ta markada ta ta zuba zuma kadan aciki, tasaka abin kwamshin lemo, tasaka 'kan'kara, taje tajere komai takai nata d'aki, duk tanayin wannan abunne saboda affan tasan da beciba yanzu takeso yaci, yasan ta iya itama, shiyasa ko ajikinta.
Su inna harda kunce zani saboda ci, lodi kawai take, tana kora lemo. " dama haka 'yan bunni suke cin dad'i haka amma mu muna 'kauye abushe wallahi bazan komaba ainazo jenan, harnima insami Miji mai kudi, inje malan yasakeni inzo in aureshi." Azuciyar ta take wannan maganar.
*naga sakwanninku sosai nagode allah yabar zumunci, nagode nagode nagode.*
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*wannan page din nakine quee tawa allah yabar zumunci, allah ya kata zakin hannu, acigana da suburbudo mana ILLAR BASHI*
*follawing us as:*
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
________
*Check us blongger*
Zamaniwriters.com
----------
*Email us your comment anda Reports*
Zamaniwritersassociation@Email.com
*✍π»shaxeee..*
*page 11*
" innah Wai tunanin mwkike ne haka." Uwanice ta katse mata tunaninta.
Cikin inda inda inna tace. " a a wallahi bakomai kawaidai ina tunanin jin dad'in dakike cikine abin sha awa, jibi yadda kika mirje abinki, kuma ki.."
" innah ya isa haka kici abincinki kar ki kware." Uwanice ta katseta.
***********
" dazu abban najwa yamin waya, yake gayamin halinda gidan affan yake ciki, yace najwa ce tayiwa umman su waya ta gayamata komai." Abban affan ne yake wannan maganar.
" nima tabugon waya tagayan saidai muyi tamusu addu,a allah ya dawo da al amarin daidai." Inji umma affan.
" zanje gun malan nuhu yadinga yimusu addu a da sadaka,in sha allah komai zezo da sauki." Abban affan ne yake wannan maganar.
************
Dare yanayi affan yakasa
shiga dakin, yana tunanin kar uwani taci mutun cinsa.
Inna ce tafulo daga dakinta, ganin affan tayi akwance akan kujera, matsawa tayi kusa dashi tace. " d'annan mekake akwance anan yanzufa karfe 11:31 kai aiyanzi ba a yayin gudun amarya, ko a kwauye ma anddena, kuma da d'inma ai mata ne suke guduwa ba maza ba, tashi muje in rakaka."
Ko 'kala baice mataba, yatashi yabita itace agaba, suna shiga d'akin, sukaga uwani a kwance tasaka kayan barci, innah ce tafara magana. " yar albarka ga mijin naki a falo naganshi akwance, shine nace masa ai yanzu andena yayin gudun amarya ko a kwauye ma bar birni, shine narakoshi nidai na tafi saida safenku."
Fucewa tayi Tarufo musu 'kofa, shidai affan yana tsaye beyi gaba ba beyi bayaba.
Dago Kai uwani tayi ta kalle shi, tace masa." Kaje kayi wanka kashirya kazo mukwanta."
Dasau ri yashige banda ki wanka yayi yafuto yashirya, yazo ya kwanta.asiba ta gari.
Gari yana wayewa bayan sun karya affan ya futa najwa tana d'akinta, uwani kuma tana shirin futa unguwa.
" kar kije ko ina kizauna agida inkika futa zaki iya bata,ko 'yan yankan kai sukamaki." Uwanice mai wannan maganar.
" karki damu ba inda zanje ina gida, kuma ai kince ba dadewa zajiyiba, sai kindawo kitawomin da abarba da lemo." Inji innah kenan.
Futa uwani tayi tashiga mota direba yajata suka tafi.
Innah tanata kallo harta gaji tarasa mai zatayi. " bara inshiga d'akin 'yannan ingani koda kayan dad'i kuma insami kud'i." Innah ce mai wannan zancan.
Tashi tayi tashiga d'akin uwani tanata bunkice, tabude kwabar affan taga kudi, aikwa saida ta 'kirga taga dubu saba inne. " bara indau ki dubu talatin, na yi siyayya dama su masu kud'innan basa ganewa in an d'auka." Azanin ta taboye su, kwabar uwani ta bude babu ko fucika, sai wani kwaran gwal data gani, an soke zuciyarsa dawani 'karamin karfe. " uwani da kwashe kwashe,komai zatayi dawan d'an aljanin."
Juyashi takuma yi ahannunta, kawai jitayi tana sha war karya masa kafa, kafar dama takarya ta sai kuma ta karya ta hagu, har ta ajiye saita kuma dauka. " bara inkarya hannayan ma aljani dakai harda wata kafa akayima, ko ina ruwan aljani da kafafu shida tashi yake sama." Hannayen ta karya duka ta mayar ta ajiye, futowa tayi takoma d'akinta, zuwa tayi ta 'boye kudin, sannan ta kwanta akan kago. " gobe sai kasuwa insiyo kayan kwalliya na yan birni indinga irin shigar su, konima nasamu miji mai kudi." Afili innah take wannan maganar.
**********
Affan yana office yaji gaba daya jikinsa yana ciwo, waje yasamu ya kwanta, yafi minti goma a kwance tukun yadawo daidai jin sa yake sakayau amma zuciyar sa kamar ansa dutse andanneta, kayan sa ya had'a ya futo dan komawa gida.
*************
" haba hafsa yaza kice in kula wani bayan kinsan yanzu inada aure." Uwani ce mai wannan maganar.
Cikin lallashi hafsa tace. " kinga wannan irinku yakeso kuma kud'i zai saki, shiyasa ma nakiraki amma tunda ba kya so shikenan."
Cikin hazari uwani tace. " to shikenan tunda zai saki kudi, nayarda."
Dakin hafsat uwani ta shige, domin yana ciki yana jiranta.
Murmushin mugunta, hafsat tayi. " da ga yau zaki gane ramin kura bagun wasan akuya bane, nizaki ciwa amana...
0 comments:
Post a Comment