Hafsat tana zaune afalo tana kallo yayin dasukuma su uwani ana d'aki.
" kinga uwani indai zakiyi harka dani, to yazama dole kidena kula mijinki, inba hakaba to saidai inne mo wata."
Wani tunani uwani tayi, dama dan kudi ta auri affan, kuma gawani shima zai sakar mata kudi, to maizaisa ka ta 'ki amincewa.
" kaga ciko na amince kawai, mushana nima bason mijin nawa nakeba, kawaidai ina zaunene."
Daga nan suka shiga aika aikarsu( allah ka tsaremu da tsarewar ka ameen kasa mufi karfin zuciyarmu.)
**************
Najwa ta gama kimai har girki tagama, jerawa kawai take a tebur affan yashigo.
Tsugunnawa najwa tace. " sannu da zuwa ya hanya."
" lafiya kalau ya gidan." Yabata amsa.
Ba 'karamin mamaki tayiba, dan bata d'auka zai amsaba.
'kara sawa gunsa tayi ta amshi jakarsa tayi hanyar d'akinta, binta yayi abaya.
Tana jin takunsa yana binta, murna kamar tayi rawa ta juya.
Suna shiga d'akin ya zauna abakin gado, tacire masa takalmi, ta rage masa kayan jikinsa, ruwa ta dakko mai sanyi a 'karamin firij dinta,irin na gefen gado.
Zuba masa tayi yasha tashiga ban d'aki saida tayi rawa ta juya, sannan ta had'a masa ruwan wanka ta futo.
" dear na had'amaka ruwan wanka, kaje kayi."
" ok baza ki taya niba ne yau." Ta girgiza sosai kodai affan yadawo daidai ne, inkwa hakane saita fi kowa murna.
" mai zai hana muje bama taya ka zan yiba yimaka zanyi." Tare suka shige 'ban d'akin suna dariya abin sha awa.
*************
Innah saida ta sha barcinta tukun, sannan ta tashi ruwa ta watsa ajinta, sannan ta canza kaya cikin kwana biyunnan harta fara haske, tayi shar da ita.
Futowa tayi falo, ta haye kan kujera ta 'kurawa tv ido, bata gane komai amma ita alallai dole saita kalla.
Su affan suna gama wanka suka futo cikin farin ciki, suka shirya junan su.
" byba kawomin abincina nan, bansan mai yasaba bana son futa." Affan ne mai wannan maganar.
" yadda kace haka za ayi ranka ya dade." Murmushi sukayi gaba d'ayansu, wayarta najwa ta d'auka ta futo.
Zuwa tayi ta huce inna tana kallo, kicin ta shiga takira umman ta a waya.
" hello umma kitayani godewa allah affan ya dawo hankalinsa." Gaya mata tayi yadda affan yanzu yadawo.
A 'ban garan umman najwa kuma cemata tayi. " dama inaso inbugo miki waya, d'azu naje gun malam hassan 'kanin abban ki yayi istahara, yace duk wani asiri najikin affan ya karye, amma banda guda d'aya, d'ayan kuwa shine baze iya sakin uwaniba, amma komai zai iya yimata banda saki, dan haka yanzu fagen naduk wadda ta iya kwace mijine." Nan umma tabawa najwa shawar wari, da yadda zata kwace affan cikin sauki, da kissa kala kala( haka akeson iyaye mata mukasance mucire kunya mubasu shawara mai kyau.).
Najwa ta nutsu ta ji komai, kuma ta d'auke su.
Umma ce tacigaba da cewa." Ina fatan kinsha magun gunannan, domin basu da illah dan agun *maman khalifa* na siyesu, kayanta sunada kyau, kuma zata cemaka idai bemaka aikiba kadawo ta baka 'kudunka, shiyasa banaso kiyi wasa dasu."
" e umma duk nasha har kazar ma nacinye, tsiminne kinsan dayawan sa shine ban shanye ba."
"To yimaza ki koma gunsa, kikula da duk abinda nace miki, sai anjima." Wayar suka kashe.
'diban duk abinda zatayi amfani dashi, tayi tafuce takai d'aki ta dawo ta kwashe abincin kan tebur duka, takai d'aki tajere agaban affan.
Futowa tayi ta dibi lemo a firij, inna ta gani tafara hamma, murmushi tayi. " nima yanzu likacina yafara, zaku gane bakuda wayo, wallahi sai kunyi nadama ada nayi saka ci amma ayanzu zan nuna muku nima yar ri'ka'k'kiyar karuwace amma ta gidan aure." Duk azuciya najwa ta take wannan maganar.
Huce ta tayi yakoma gun affan, sukaci abinci cikin farin ciki da raha, suna gamawa najwa ta kwashe ragowar abincin ta kaiwa masu gadi, suka juye ta koma ta maida su kicin, tana sane ta 'ki wankewa.
'daki takoma ta keyiwa affan tausa.( mata kuna sakaci dayiwa maza jenku tausa, tanada mihimmanci so sai, misammamma in miji yadawo daga kasuwa.)
Innah kuwa har yunwa tafara tumur musar ta, gashi taje kicin ba abinci, gashi bata iya kunna gas ba, bare ta dafa tarasa yadda zatayi, ragowar biredi tasamu taci da ruwa, tana zaune afalo sai ga uwani.
" yauwa 'yata tun d'azu nake jiranki, baki dawoba ga hunwa ta addabeni." Innace mai wannan bayanin.
Waje uwani ta samu ta zauna." Ina waccan sakaryar take, bata dafa bane, nima hunwar nakeji sosai, kuma naga motar affan koshi mai yasa baki gaya masa, yasaka ya ta dafa miki."
" hmm inafa kallonta harta dora a wancan tebur d'in, saikuma ta kwashe ta kai d'akinta, data futo dashi tayi waje tabayar, ta dawo da kwanukan, kuma shi affan d'in bansan inda yakeba, kuma baya d'akinki."
" taf ta tsokalo sama da kara ni zata hula 'kantawa uwa, kiyi ha'kuri inna bara in kira affan d'in awaya, yazo ya d'au hukunci akanta."
Huci kawai uwani take, ita kanta bata san irin hukuncin dazata d'auka akan najwa ba, ga shi tanajin hunwa ga shi wancan ya gurjeta son ransa, kuma ta kira affan bed'agaba.
Itakwa najwa duk ta jisu, neman abinda zata nuna musu yanzu fa va da bane, dabara ce ta fad'o mata.
Cakulkulu tafara yiwa affan, yana dariya, shima yana yimata, mintsilinsa tayi acinya, aikwa yatashi ya biyota 'kofa ta bud'e ta futa falo sai zagaye kujeru suke.
Baki innah da uwani suka bud'e, ko kula da su affan beyiba, bin najwa kawai yake, saida ya kamata suka fad'a kan kujera.
" wana kama kingama gudunko." Cikin haki affan yake magana.
Saiyanzu yaga su innah. " au sannun ku ashe kuna falon, wallahi ban kulaba, ashe kin dawo." Affan ne yake wannan maganar.
Uwani rasa abin fad'a tayi mai yake shirin faruwa.
Najwa kuwa tana kan cinyar sa. Bata sauka ba, inna sai raba ido take.
Cikin kissa najwa tace, dear kacewa uwani tamin wanke wanke wallahi na gaji dayawa, shiyasa ban hiba..
*muje zuwa*
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*
*bazan gaji da baki kyautar page ba ALJANAR FATIMA Allah ya ja zamaninki*
*Masoyan yar aikin gidana ina ganin sakonninku Allah yasa da alheri*
*following us as:*
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----------
*check us blongger*
Zamaniwriters.com
-------------
*email us your commernt and report*
Zamaniwritersassociation@email.com
*✍π»shaxeee..*
*page 13*
Kallon najwa affan yayi, duk ta yi kalar tausayi, ta marairaice.
Juyowa yayi ya kalli uwani, ta ziba masa ido tana harare harare.
" mai zai hana tayi himiki, ai naga duk aikin gidan kekikayi, uwani maza jeki hi mata wanke wanke."
Cikin masifa da uwani take magana." Bazan yiba kehar kin isa kija dani, kewacece to wallahi kome kika bawa affan ni zan dawo dashi yadda nakeso, kuma Bari kiji ba a ja da ni wallahi, dan ahaka kikiyayeni zan iya 'batar dake adoron duniya."
Innah ce itama ta tashi tafara nata guntun bala in." Tabb wallahi baku isa kumayar min da 'ya *'yar aikin gida* ba Wallahi,kekuma kifita daga idona in...."tassss kakeji affan ya mari uwani, bashiri inna tayi shiru.
" ke har kin isa kidinga zagin matata, agabana keda uwar ki wallahi kushiga hankalin ku inna ba hakaba zaku gane kurenku, kuma ki gaggauta zuwa kiyi wanke wanken, inkika 'ki hi wallahi saina zaneki shashasha kawai." Cikin fada affan yake wannan maganar.
Abin hada d'a bawa uwani mamaki, kodai ba affan din data sani bane.
Tuni tashige d'aki domin duba halin da kwaran gwal yake.
Tana bude kwaba ta d'ad'd'aga kaya, ta d'akko shi, tashin hankali wanda ba a saka masa rana.
Ganin kafafu da hannayen kwaran gwal akarye suna reto. " wayyo Allah na waya min wannan ta asar, nashiga uku, dolene inkira hafsat dan ta koma gun boka, sake sabon shiri ayau d'innan." Waya ta d'aukko takira hafsa, tana d'agawa tahimata bayanin komai.
" karki damu 'kawata yanzu zanko ma gun boka, in amso miki magani." Cikin murmushin mugunta hafsat take wannan maganar.
Kashe wayar uwani tayi, tafuce falo bakowa sai inna tayi ta gumi." Innah kije kiyi wanke wanken, kinzauna kinyi tagumi danni bayi zanyiba, gwara kije kiyi inba hakaba kuma inyafuto ya koreki kyauye." Jin za maida ita kyauye yasa ta tashi tashige kicin, tafara wanke wanken.
Tana gamawa uwani tazo ta d'ora musu indomesukaci.
****************
Hafsa agaban boka mai 'kwaran gwal.
" sonake kayi wanda zai tsaneta ita da uwarta yadinga gana musu azaba, kuma ya saketa saki uku." Hafsa ce mai wannan jawabin.
Hhhhhhhhhhh boka ya yi dariya." Za ayi wanda zai tsaneta tsana mai tsanani,harda uwarta amma baze iya sakinta ba har sai, an zare wannan kibiyar ta zuciyar kwaran gwal din ana cirewa kominti biyar baza ayiba, zai saketa."
" hakanma yayi, gwara saita jigata tukun da kanta zata cire."
Wata laya yabata yace " kijefa arijiya tana fadawa to zaiji yayi mugun tsanarta uwa ya kashe ta ita uwar." Amsa tayi tabiya shi ta futo.
A hanya ta sami rijiya ta cilla ta tafi.
****************
Affan yana zaune a kan gado yana danna loptop, najwa kuma tana kicin tana girkin dare.
Jiyayi kansa ya sara, yaji duk duniya bawanda yatsana kamar innah da uwani.
Tashi yayi yafuto falo bakowa, dakin uwani yashiga, tana kan gado akwance ana barci.
Futa yayi bakin get gurin mai gadi. " baba dan Allah ban aron bulalar ka babbar mai baki biyu dinnan, ta korar awaki."
" to shikenan mai gida." Dakinsa ya shiga yad'akko masa wata shar'bebiyar bulala yabashi.
Gidan yadawo d'akin uwani, betsaya wata wataba yafara lafta mata, wani ihu tasaki tatashi afurgice, dukanta kawai yake ba 'ka'k'kautawa.
Najwa tagama komai tana goge guri, taji ana ihu bashiri tafuto, innah ma taji ihu uwani bashiri tafuto, har zaninta yana nema ya fad'i.
Yana ganin inna yajawota ya hada da ita yana lafta, duka bana wasaba itakanta najwa abin yabata tsoro gudin kar ahada da ita yasa ta ruga da gudu tashige dakinta.
Saida yaga basa motsi tukun ya kyalesu, gun mai gadi yakoma.
" baba daga yau inba niba sai najwa kar wanda ka bari yafuta ko yashigo, gidannan indai bani nace abar shi ya futa koya shiga, kuma wannan bulalar narike ta zan dinga amfani da ita."
" angama ranka ya dade."
Ciki yakoma yashige dakinsa, ganin najwa yayi tayi tsuru tsuro, aikwa abin yabashi dariya.
Dariya yake harda rike ciki, kamota yayi yarungumeta." Haba byba na me na tsoron kinsan keta dabance, suma kawai jinayi na tsanesu wallahi barima in koma dan abinda nayimusu be isheniba."
*kuyi hakuri da wannan nadan futane naje asibiti dubiya*
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN*
*yau zaga yowar ranar rasuwar mahaifina ta shekara 4 nasadaukar da wannan page din washi duk wanda yakaranta yayi masa Addu,a allah yajikansa*
*following us AS:*
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITION
---------
*check us blongger*
ZAMANIWRITERSASSOCAITION.com
-----------
*email us your commenrt and reports*
Zamaniwritersassociation@email.com
*✍π»shaxeee..*
*page 15*
Saida innah tayi kuka harta gaji ga rana tana dukanta, bashiri ta tashi takoma ciki.
" innah yanaga kin dawo mai ya faru kuma." Uwani ce mai wannan maganar.
Cikin ta'kyaici inna tace." Badole indawo ba ja irin yaronnan ashe yace kar abar kowa yafuta, shikuma mai gadin kwata kwata bashi da mutuncu, gidanma yakulle yakoma d'aki yakwanta."
Haka suka zauna suka jimami taya zasu futa, agidan suje gidan boka.
*************
Falone anhadu sai hira ake abin sha awa, affan najwa da umma sai abba da eesha, dan tazo gida hutu.
" to ni bara in huce Office, lokaci yayi inna dawo sai inbiyo mutafi." Affan ne yake wannan maganar.
" to allah yabada sa a " inji abba da umma.
Tashi najwa tayi taraka shi mota saida yatafi tadawo.
Tabasu labarin yadda affan yadawo daidai.
" Allah zamuyiwa godiya, kekuma aiki kiyaye gaba, kunga dai halin dakuka shiga." Abba ne yake wannan maganar.
Fada sosai sukayiwa najwa, kuma ta sauraresu sosai, ta dauki abinda sukacemata, abba ma futa yayi kasuwa najwa kuma suka cigaba da hirarsu.
*****************
Hunwa ta addabi su inna, sunrasa yazasuyi da rayuwar su kuka kawai inna take yi, tana zaman zamanta takwaso 'kananun 'kafafunta ta tawo inda za a kasheta da hunwa.
Inna tunawa dakud'in data sata tayi, dubu ta dakko. " ungo jeki bawa mai gadi yasiyo mana abinci muci." Innah ce mai wannan maganar.
" dama inna kinada kudi amma kika barmu cikin yunwa." Cikin tsiwa uwani take wannan maganar.
Amsa tayi ta je gun mai gadi tabashi tace dan allah yasiyo musu abinda zasu ci, amsa yayi yaleka yabawa yaron makocinsu yasiyo musu.
Mintuna kadan tsakani yakawo musu harda lemo, duniya sabuwa agun su inna sukaci suka koshi, suka 'boye ragowar a daki.
Sai karfe goma na dare su affan suka dawo, kota kan su uwani basu biba suka shirya suka kwanta abinsu.
*****************
Gari yana wayewa su innah suka tashi suka fara aikinsu.
Najwa kuma tana kicin, affan yana falo yana waya.
" karka damu kawai ina gida yanzu kayi sauri kazo ka kawomin, in baka kudin kawai." Banji mai akace adaya bangaranba.
" ok muhadu a Office din, badamuwa." Wayar yakashe. Ya ajiyeta.
Tashi yayi yabude dakin uwani na da, yana shiga yabude kwabarsa don d'aukar kudinsa dan har ya manta dasu, saiyanzu yatuna, yana dakko kudi yaga ankwashe kudi.
" tab dijan dama ai yau ban disfula suba, dan in basuba babu wanda zai taba min kudi, wallahi saikunyi nadamar daukar min kudi. Cikin murmushin mugunta affan yake wannan maganar.
Futowa yayi falo lokacin har najwa ta gama komai." Byba zomuje kitayani wani aiki." Tashi tayi tabishi.
Farfajiyar gidan suka futo lokacin su inna ana zaune ana hutawa.
Hade fuska affan yayi uwa *ALJANAR FATIMA* " ku kuzo nan nace." Tuni suka tawo domin bawasa afuskarsa.
Mai gadi yakira, yana zuwa yace." Dakkomin farar kujerarcan guda biyu." Tuni mai gadi yaje ya d'akko yakawo, zama yayi shida najwa, sukwa su inna ana tsugunne agabansa.
" kowane Cin mutunci kuma yau zai mana oho." Duk azuciya innah take wannan maganar.
Cikin isa affan yace. " na ajiye kud'i adakinki nada, amma yau naje dauka naga andibi kudin, dan haka kufuto min da kudina ko kugane baku dawayo."
Kallon kallo sukewa juna dan uwani tasan innah ce ta dauka dan tagaya mata.
" wallahi bamu muka dauka ba." Harsuna hada baki.
" wato dai bazaku futo dashiba ko." Rantsuwa suketa yi basu dauka ba.
" tunda kundage shikenan amma ni zan amsa tadda bazaku ji dadiba, mai gadi dama kai kayi harkar daba ko to gayamin kalolin mugunta."
Washe baki mai gadi yayi yace." Ai mai gida nasansu sunada yawa. Akwai wanda za a sami barkono addadakashi ahada da fasassun kwalabe aturawa mutun ta baya, akwai wanda za a sami ruwa adanna kan mutun aciki, akwai wanda za a sami 'katuwar roba wadda mutun zai iya shiga azuba ruwa aciki asaka mutun sai asa wayar shokin aciki. A kwai..."
" wadannanma sun isa maza jeka samo kayan daza ayi amfani dasu."
Jin wannan kalolin azaban daza ayi musu tuni innah tafara fitsari harda guntun kashi, tuni inna tace." Basai anyi hakaba wallahi ni nadauka, bara indakko maka kudinka."
Tuni inna ta tafi tana rawar jiki, taje ta dakko tabashi, 'kirgawa yayi yaga ba dubu d'aya.
" naga babu dubu d'aya ina taje." Cikin rawar baki uwani tace." Wallahi abinci muka siya jiya muka ci saboda ba abinci agidan."
" ina ruwana yanzudai kun kashe min kudi ko to zanmuku hukunci daidai da kudin da kukaci." Komawa gida yayi yad'akko bulalarsa, yadawo gunsu duk abinda ake najwa tana kallo.
Cikin fada affan yace. " maza tashi kufara tsallan kwado kuma duk wanda ya tsaya zan tsula masa bulalarnan." Tuni suka fara yi saisun kai 'karshen farfajiyar sai su dawo, inna kuwa tagaji, shiyasa ta dan tsaya ta huta, aikwa affan yasaita duwawunta ya tsulamata, wata kara tasaki tacigaba uwanima ya tsula mata, sunfi awa biyu sunayi, najwa ce taga abin yaki 'karewa shiyasa tace.
" dear dan allah kabarsu haka ai sun daku kaji nawan."
Cikin murmushi affan yace. " maza kutashi kuje ku tsugunna agabanta kuyi mata godiya kuma kuhuce daki saura inga kunfuto."
Da rarrafe suka karasa gunta suka yi godiya, da rarrafe suka shiga gidan suka koma d'akinsu.
Suma komawa gidan sukayi sukaci abinci, ruwan shayi da biredi yaje d'akin yakai musu, yafuto saida sukayi wajen awa awa hudu sannan suka tashi suka sha shayin duk da yayi sanyi.
Wanka sukayi suka zauna suna tunanin wannan irin azaba.
" innah gyara d'akin duk kin zubar da kaya bara ni inje inmata wanke wanke nasan tagama girki yanzu. Uwanice mai wannan maganar.
Fucewa uwani tayi zuwa kicin.
Innah ce tafara gyara musu kaya, tagama hada nata tazo hada na uwani aikwa tayi karo da wannan 'kwaran gwal din." Shegen aljaninnan komai uwani take dashi, ni wallahi nagaji da ganinsa a cikin kayanta." Cikin fada innah take wannan maganar.
Bata tsaya wata wataba tazare kibiyar jikin zuciyar sa, ta kakkaryashi 'kanana 'kanana tazubar adakin, daidai lokacin uwani tashigo tana ganin abinda inna tayi ta daskare agun....
0 comments:
Post a Comment