Yana futowa yagansu akwance inda yabar su, duk jikinsu afarfashe, murmushin mugunta yayi yahuce kicin.
Ruwan dimi yasamu azuba uban gishiri, yajuya sosai yafuto.
Bai tsaya wata wata ba yadinga yayyafa musu, ihu kawai suke suna neman temako, saida ruwan yakare yamayar da kwanon kicin, dakin uwani yashiga ya katse hutar dakin gaba d'aya.
Bandaki ma yashiga ya yanke hanyar daruwa zezo bandakin yafuto yakoma daki gun najwa.
Da'kyar suka tashi awalce suka koma daki, wahalce inna tace. " uwani maikika yiwa yaron nan haka kotausayi babu yamana wannan azabar, harda ni koganin cewa ni babar matarsa ce beyiba."
Cikin 'kunar rai uwani tace. " nima bansaniba haka kawai ina barci yazo yana dukana, dole inkoma gun boka yanzu basai gobe ba wallahi, amma affan yayi babban kuskure daya dakeni har najwan saina musu abinda zasu yi nadama mai girma."
" yauwa uwani maza hanzarta kije konima bayafewa zanyiba."
Dakyar uwani ta sake shiryawa, tadau kudi da jaka tafuto, tana zuwa bakin get maigadi yahanata futa, yace. "mai gida yace karwan da yafuta saida izininsa."
Haka ta hakura tadawo cikin bacin rai, waya ta dakko takira hafsat, amma tanata ringin amma ba a d'agaba, harta gaji ta hakura, tagumi tayi "maiyake kokarin faruwane wayamin wannan ta asar karyamin asiri."
Abinci najwa takowo musu saki sukaci suka koshi ragowar affan yace takaywa mai gadi, haka kuwa tayi dakansa yazo ya kulle kicin din yakoma daki, sukayi shirin barci suka kwanta.
Waje karfe 1:39 hunwa ta addabi su innah da uwani gashi kicin arufe, uwanice ta duba d'akinta ta samomusu ragowar cake, sukaci daruwa suka kwanta gazafi ga duhu dakin sun rasa yazasuyi ahakadai sukayi barci.
***************
*DA A SIBA*
Affan yana dawowa daga masallaci dakin su uwani yaje, sunata barci harda minshari.
Komawa yayi yaje ya dakko bulalarsa yashigo dakin.
Tsula musu yayi afur gice suka tashi.
" kunyi sallane kuketa barci haryanzu sai kace kafurai." Cikin fada affan yake wannan maganar.
Saida ya yimusu uku uku tukun yace sufuce waje suje farfajiyar gidan gun famfo suyi alwala.
Suna futa yakarewa dakin kallo, dakinsa ne fa nada amma wadannan masu kama da a gwagin suke zama aciki.
Bude kwabar yayi yasami jaka yazuba wa uwani duka kayanta aciki harda mayuka.
Yafuto dasu falo komawa yayi yabude akwatinanta na lefe, ba abinda aka taba aciki, gani kayan yayi ko lokacin bikinsa da najwa, baimata kaya masu yawan haka da tsadaba.
Duka ya kwashe yakai dakin najwa, yadawo ya kulle dakin.
Zama yayi a falon kan kujera, yana kallo duk wannan diramar da ake najwa tana kicin bata saniba tana kokarin hada abin kari.
Su uwani anyi sallar da ba asan ya akeyintaba, sun tawo domin komawa akwanta suna shigowa falon affan yakirasu.
" ku kuzonan " bamusu suka zo.
" kinga kayanki daga yau kin koma wancan d'akin naki nada kuhadu keda uwarki kukwanta aciki, sannan daga yau duk aikin gidannan kuzaku dinga yi harda bawa shika ruwa da share farfajiya, da wankin mota, harda wankin mu insun yi datti nadena asarar kudina tunda ga 'yan aiki agidana, kuma duk ranar dakuka 'ki yi ko kukayi ba dai daiba ko kuka yiwa najwa rashin mutunci, wallahi saikin ji badadi agidannan maza kuje kufara aiki."
Kayan uwani tafara kaiwa dakin innah, ta ajiye ta futo shara suka fara hi har falon suka goge komai sukaje kicin sukayi wa najwa wanke wanke, suka futa farfajiyar gidan duk busassun ganyayyaki suncika wajen, haka suka share da kyar suka bawa shuka ruwa, sannan suka fara wanke motoci guda ukun.
Sukwa su najwa ana ciki ana karyawa ana raha abinsha awa,
Adaddafe suka karasa suka koma ciki lokacin su affan ana kallo najwa kuma tana kan cinyar sa ana shagwaba.
Awahalce sukace. " mungama aikin duka komai da komai."
Biredi da ruwan shayi ko siga baijiba yamika musu. " allah yasoku da rahma da bakuyiba wallahi saina azabar tar daku, banzaye masu kama da a gwagi, nibansanma jarabar data sani na kwasokuba, ku ungo kuje kusha kuma da ranama haka zakuyi kullun sau biyu."
Najwa kuwa sai gwalo take musu suna gani bayadda zasuyi,amsa sukayi suka shiga dakinsu, ci sukafara kamar wanda suka ashekara basu ciba( dama hausawa sunce jiki magayi).
" dear inshirya muje gaishe dasu umma daganan miyi siyayya mudawo gida." Najwa ce maiwannan maganar.
" byba yaudai yawo kikeji, to muje mushirya sai in ajiyeki intafi Office inna dawo sai in biyo mutafi ko." Tsallan murna tayi, suka shiga ciki suka shirya suka fice, kan affan yafuta saida yajadda dawa mai gadi karwanda yafuta ko yashigo.
Su uwani ansha huya suna kwance suna hutawa, innace ta tashi zaune." Wallahi bazai yuhuba ace nida natawo inhuta a Birni ko agidana ba a dukana, ga horon hunwa ga aiki kamar bayi, wallahi gida zan koma bazan mutu abanza ba in nakoma zan sami wani bokana yamiki aiki akansa, yadawo mijin tace kiyi yadda kike so agidannan, amma bazan iya zamaba wallahi."
" yauwa innah kitemaka min in mallaki affan insami kudi sai inbar gidan, amma ko nabar gidan yanzu yazama ban amfana da komaiba."
Innah kuwa tuni ta hada kayanta tayiwa uwani sallama ta futo tana zuwa bakin get.
" mai gadi budemin zan koma garinmu, dama cewa nayi bara inmusu kwana biyu kuma nayi yau zan koma."
Mai gadi kuwa yahade rai yace. " hajiya mai gidan yace kar kowa yafuta kuma karwanda yashiga dan haka kiyi hakuri, dan wallahi bazaki futaba." Kulle kofar yayi da kwado yakoma dakinsa yarufo kofa.
Zaman da'baro inna tayi tadora hannu aka." Nashiga uku ina nakawo kaina, shegen kwadayina ne yajamin, gaji na 'bige da aikatau wayyo allah na..
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*'YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*FOLLOWING US ON THIS DETAILS:*
-------
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
ππ»
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITON*
---------
*CHECK OUR BLOG'S*
ππ» *zamaniwriters.blogspot.com*
------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
ππ»
*Zamaniwritersassociation@email.com*
*✍π»shaxeee..*
*page 16*
Cikin tashin hankali uwani tace." Inna kinkwa san mai kikayi, asirinefa akamin, yanzu kuwa affan zai sakeni nashiga uku, gashi ban tara komai ba zan futa abanza."
" yo ni danasan ana cirewa zai sakeki ai da na dade da cirewa, wannan irin bala i haka, jibi yadda nayi ba'ki na rame ni ai farin ciki ma zanyi dan zan bar gidannan."
" nama gama ganoki innah kekika fara karya min asiri, kika karya wa gwaran gwal dinnan hannu da kafa ko." Cikin bacin rai uwani take wannan maganar.
Tsuru tsuru innah tayi dan tasan itace ta karya bawani ba.
*********
Affan yana office yaji zuciyar sa kamar ana kunna mata huta, can kuma sai yaji tayi sanyi yaji uwa bashiba.
Kamar an tsikareshi haka yaji, tuni yatashi ya futo, ko kulle office din bai tsaya yiba.
Motar sa yashiga yakunna, hanyar gida yanufa, gudu kawai yake kamar wanda zai je maka.
Yana zuwa gida ya yiwa mai gadi wani ham mai 'karfi, mai gadi shi kanshi yarikice tuni yabude get din, saura kadan ayi ciki da mai gadi Allah yasa yamatsa.
Futowa yayi daga motar ya shiga gidan. " UWANI!! UWANI!!." Cikin d'aga murya yake kiranta.
Saida cikin uwani ya kad'a shikenan yanzu zata koma kwauye, cikin hanzari ta futo ita da innah.
Najwa ma saida ta futo cikin furgici tadauka wani abinne yafaru.
Affan yana ganin ta yace." Kije nasakeki saki uku, kuma Allah ya isah tsakanina dake dan bazan taba yafe mikiba, kuma na baku minti uku kubar min gidana." Yana gama fada ya shige dakin najwa.
Najwa ce ta yi buda tace." Sai akoma kyauye acigaba da cin bakin tuwo da koriyar miya, ansami miji anyi yadda akeso ko, dama ance in zaka gina ramin mugunta ka ginashi daidai dakai dan wata rana kai zaka fada ciki."tana gama fada tayi hucewarta Daki.
A sanyaye suka shige daki suka hada kayansu gaba daya, suka futo suna zuwa bakin get mai gadi yahana su futa saida yakira affan yace yabarsu sufuta tukun yabarsu.
Cikin jimami innah tace. " uwani yanzu a ina zamu sami kudin mota, mukoma kyauye."
" karki damu inna akwai wayata kuma tanada tsada ita zan siyar, saimu koma amma saina fara biyawa ta gidan hafsat tukun, inga ko lafiya bata nemeniba kwata kwata."
Haka kuwa akayi sukaje wani shagon waya, yabasu fubu hamsin dukda cewa wayar tafi haka, mai adaidai ta ta tsayar tace ya kaita gidan hafsa.
Suna zuwa ita kuma zata shiga mota.
" yauwa hafat dama nace lafiya naga baki neme ni ba ko awaya nakira baki d'auka ba." Uwani ce mai wannan maga nar.
Wani irin kallo tayi mata sannan tace. " ke atunaninki zan nemeki to bari kiji cin amanar da kikamin ba yafewa nayiba, shiyasa nabiki asannu narama abinda kikamin, nafarko nasa boka ya yimiki asirin da affan ya tsaneki, na biyu kuma wannan ciko din dana kawoki gunsa, dama nina turoshi saboda yanada kanjamau, kuma nasan kema yanzu kin dauka, dan haka maza kibar min gidana konasa ayi muku hulakanci."
" abinda zakiyim kenan hafsa am ma kin cuceni wallahi kuma bazan taba yafe mikiba, kuma gida yanzu zamubar miki." Cikin kuka uwani take wannan maganar.
Kama hannun innah tayi suka tafi, adai daita suka kuma hawa zuwa tasha.
Suna zuwa suka hau motar garinsu basu dadeba mota ta tashi inbanda kuka ba abinda uwani take, ga nadama data shigeta, data tabi duniya asannu da bahaka ba.
Awa daya ce takai su garin su, dama banisane da shiba.
Suna zuwa gidan su sukaga abban uwani awaje a zaune yana ganinsu yashige cikin gidan.
Suma binsa sukayi ciki, suna shiga suka ganshi da wata tsohuwar akwatin karfe.
" dama ke nake jira kidawo in gaya miki abinda zan gaya miki intafi gun yan uwana, dafarko dai kin cuceni kin rabani da kowa nawa, saida Allah yasa wani bako damukayi a garinnan malami yatemaka min asirin da kikamin ya karye ni nayafe miki, duniya da lahira kije nasakeki saki uku, kuma ki nemi baban su uwani kibashi 'ya 'yansa, ni narafi tunda dama gida nakine, Allah ya hada kowa da rabonsa." Fucewa yayi suna kallo yarafi, kuka kawai innah take.
Cikin fur gici uwani tace. " inna dama mu ba 'ya 'yan sa bane ina baban mu yake...
[12/6, 10:15 AM] First LadyπΉ: ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
ππ»ππ»
ππ»
*"YAR AIKIN GIDANA*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*FOLLOWING US AN THIS DETAILS*
--------
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
ππ»
*fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITION*
------------
*CHECK OUR BLOG'S*
ππ»
*zamaniwriters.com*
--------
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME*
ππ»
*Zamaniwritersassociation@email.com*
*✍π»shaxeee..*
ππ
*page 17*
Cikin kuka inna take magana. " gaskiya ne bashi ya haifekuba, ubanku daban amma yanxu xan baki labarin komai."
Zama sukayi sannan innah tafara bata labari.
" iyayena duk sun mutu, ahannun kishiyar mama na natashi ita take turani gun wata *DIJE MAI TUWON YAN GAYU*( littafi na mai zuwa) ina hiwa matar aiki anan nafara bin maza, duk da innar tawa tasani amma bata hananiba saidai ma ta kara dorani akan hanya, ana haka ciki yabayya na ajikin, data fuskanta saita kaini aka zubar dashi, bayan wasu kwanaki tafara rashin lafiya har ta mutu, yan uwana sukace bazasu dauke niba saboda kowa yasan halina, suka siyar da gidanmu suka bani dubu biyar waishine rabona nikuma nabar garin nadawo garinnan, gun wata mai abinci atasha ina taya ta girki har nazama babba agunta komai ninake bada umarni, ana haka na hadu da babanku tasi,u yana kashemin kudi sosai, ahaka nasami cikin wanki, yace inzubar damukaje asibiti akace zan iya mutuwa nikuma naki yarda ahaka harna haifi wanki, bayan na yayeshi, sai tasi,u yakuma dawomin, nayarda dashi bayan wasu watanni nakuma samin ciki, yana ganin haka yagudu haryau ban kara ganinsaba, ahaka har na haifeki, inata rainonku harnima nazama wata atasha nasai gidannan, ana haka naga malam shikuma daga wani gari yake yana zuwa nan kasu wanci, tunda naganshi nace ina sonsa yaki amincewa tunda yasanni, saina kaishi gun boka ya asirceshi harya aureni namallakeshi, tundaga sannan bai kara zuwa garinsuba, to kinji yadda abin yakasance."
Inbanda kuka ba abinda uwani take, tana nadama datasan asalin labarinta toda bata yadda ta 'bata rayuwar taba.
*********
Rayuwa mai dadi su najwa ake abin sha awa har ta sami ciki suna tattalinsa kamar d'anyan kwai a kan dutse.
**********
Haka su wani suke rayuwa cikin 'kunci yara har gidan suke lekowa ganin su.
Ga ciki ya bayyana ajikin uwani, wanda tasan na osi ne kuma ance yanada hiv.
Tarasa yadda zatayi darayuwar ta.
Kuma yayan ta shima yadawo gida ashe fashi yake aka harfeshi a hannu.
Yana gida yana jinya harya d'an sami sauki.
Shawara sukayi susaida gidan su bar garin.
Haka kuwa akayi suna tawo kano ta dabo.
Suna zuwa garin barayi suka sace kudinsu, uwani kuma tayi tuntube ta fadi, jini ya balle mata haka suka sami wani dan kango suka zauna.
Yusha,u yayan uwani shine yatemaka yasamo musu ruwa ta gyara jikinta .
Haka suka cigaba darayuwa awannan kangon, yusha,u yafuta dako sukuma bara suke.
Yauma sun tawo bara sukaga wata mota, dagudu sukazo gunta, suna lekawa danyin bara wazasu gani.
Su affan ne da bybe su namiji, sun tsaya siyan lemo sa ayaba, zubewa uwani tayi agaban affan tana neman yafiyarsa.
" tashi uwani ba komai nayafe miki tunda dadewa." Affanne mai wannan maganar.
Yafiyar najwa tanema itama ta yafe mata.
Gayamusu halin dasuke ciki sukayi, sun tausaya musu, inda affan yanemin kwatancan inda suke gobe zaizo.
Gaya masa sukayi yabasu kudi sukayi masa godiya.
*********
Washe gari affan yazo kangon dasuke, yadaukesu duka.
Wani gidan mai daki biyu sai karamin tsakar gida yabasu kyauta, godiya suke mai harda kukansu kudi yabasu yace suyi sa na a.
Yashe gari uwani taje asibiti akayi mata gwaji, allah yatemaketa bata da HIV murna harda kuka.
Abincin siyarwa suka fara dalemo kuma suna ciniki shikuma yusha u akofar gida yayi tireda yana saida kayayyaki.
Isilamiya suka samu dukansu suka koma har yusha u, din.
ALHAMDULILLA ANAN NAKAWO KARSHEN WANNAN GAJERAN LABARIN ALLAH YASA
MU AMFANA DA AKON CIKI AMEEN.
0 comments:
Post a Comment