_kamar yadda nayi alk'awari gareku masoyana masoya_ _littafaina bayan_ *IZZA TA* _zanzo muku da sabon labari a kyauta to Alhamdulillahi alk'awari_ _ya cika👌🏼_ *SLIMZY CE* ✍🏻
*1*
Fararen kujeru da d'an karamin centre table me kmr stool shine a gabansu a harabar gidan da laptop Me dan girma akan centre table din me kama da stool,gabaki daya fuskarsa babu walwala ko kadan babu alamar faraa,hira take zuba masa amma sam hankalinsa baya kanta be ma san tanayi ba hannuwansa kawai ke motsi wajen danna keys din laptop dinsa da alama,aiki yakeyi mai muhimmanci,...."sweet kasan ko ummah da naje gida cewa tayi wai nayi kyau abuna saidai nad'an rame kodai ciki gareni..."ta karasa maganar cike da nishadi ko kallonta beyi ba ya cigaba da abinda yakeyi,zuwa yanzun zuciyarta ta soma harzuka ta soma tafarfasa,wani kululun bakin ciki ne ya taso ya tokare mata wuya,kallon jikinta tayi suturar dake jikinta da yadda take zuba kamshi amma sammm beko bin ta kanta,har yaushene zata soma burgesa?har yaushene zata iya jan hankalin mijinta?..tsaki tayi cikin zuciyarta,nan da nan idonta ya canja kala ta hadiyi wani miyau da ya bushe a bakinta saboda bacin rai,niyyar mikewa tayi tabar wajen ta koma parlor tayi kallo amma bazata taba barin wajen ba saita amayar masa da abinda ke cikinta dikda indai irin wadanan maganganun ne sun saba....
"Sweetttttt....wai nikam bakaji ina magana ina baka labari ba?ka shareni sai zuba nakeyi kamar an kwance kura?"a fusace tayi maganar.
Bece komi ba ya cigaba da typing dinsa,kara fusata tayi zatayi magana a karo na biyu,ganin bakinsa na motsi yasa ta dakata Tana dubansa cike da bacin rai,dakyar ya motsa labbabsa "inace magana kikeyi?...kuma kunne keji?umm?ai ina jinki"ya maida kai cikin ko in kula ya cigaba da typing dinsa.
"Ehh magana nakeyi,amma nikadai nakeyi ai sunan mijina yana gefe na ne amma sammm hankalinsa baya wajena yana can wani waje daban"ta d'an hararesa cike da kosawa,
Murmushin gefen fuska yayi "jiddah kenan....tou aidai kina ganin aiki nakeyi ko?kuma bazan bar aikina in tsaya sauraren shirmen labarinki ba,kuma dai ai kunne na yana sauraronki ko?inace dama kunne keji?"
Kara k'uluwa jiddah tayi ta mike tsaye ta rike kwankwaso cike da takaici,wai miji kakewa hira yana cewa kunne keji kamar wata sauna haka ya maidata,"nasan aiki kakeyi ai , Amma naga nan ba office bane kuma yau ai sunday ne ba ranar aiki ba ,ta yaya ina bukatar lokacinka kai baka da nawa?yai da ya zama sunday zamu kasance tare da juna kana manne da computer kamar wani bature?"dariya ma ta basa jiddah ta saba irin wadanan rigingimun ta kasa gane cewar bazai iya ajiye aikinsa ya tsaya shirmen banza ba,dole ne ya nemi abinda zai gina rayuwarsa da ta yaransa,sanan da aikinsa ta gansa amma kullum saita yab'a masa maganganu marasa dadi akan aikinsa ya kamata ace ta saba tunda dai tasan ai Yana sonta bawai baya sonta bane.....saida ya kwashi minti biyu tana tsaye tana jira ko zai ruko hannunta ya zaunar da ita alamar ban hakuri,amma shiru ta cire rai hakan yasa kwalla ta cicciko a idonta,dago kyawawan idanuwansa yayi ya saukesu akanta memakon yayi magana girgiza kai yayi hade da dan murmushi ya maida kansa ya cigaba da abinda yake.....juyawa tayi ta ruga sashensu hawaye na bin fuskarta a yuje tahau matakalar da zata sada ta da babbar kofar patlorn su ta bude kofar da karfi ta rufo ta....yana hangenta ya girgiza kai yana murmushi,jiddah rikici itadai a zauna ayi soyayya ayi hira shine muradinta.....ya kai hannu ya dauki lemo ya kurba ya ajiye cup din sanan ya maida kansa ya cigaba da abinda yakeyi.....
Zama tayi a parlor ta rike kanta hawaye na gudu a fuskarta,har yaushe ne zaisan muhimmancinta?har yaushene zai dauketa da muhimmanci kamar yadda ya dauki aikinsa?mijinta fari cikinta wanda dik lokacin da take tare dashi tana tsintar kanta cikin farin ciki da nishadi mara misaltuwa amma basa cikakken minti biyar batare da farin cikin nan ya juye zuwa bakin ciki ba,hakan na faruwa ne saboda yanayin da kullum suke ciki na aiki da dare da rana yana kan aikin nasa kamar wani bature....cije lebe tayi tana jin wata kaunarsa a zucuyarta saidai haushin da takeji a yanzun haka yasa tana kallonsa bakim kirin.....wayarta dake jikin carji ta ciro ta dawo ta zauna,share hawayenta tayi dikda wasu ne ke kara zubowa ta daddana numbobi ta kara a kunnenta....
Bugu daya akan dauka "hello"daga can bangaren ta fashe da kuka jiddah kasa magana tayi "yadai jiddah meyake faruwa?meke damunki ne?"
Daga can babgaren ake magana cike da damuwa,ta dau mintuna tana kuka kafin daga bisani ta tsagaita da kukan kadan sanan tace "kamar dai koda yaushe matsalar daya ce wadda na saba kiranki in sanar miki ki kwantar min da hankali yau ma itace ramla"
Murmushi ramla tayi domin tasan dama zancen gizo baya wuce na k'oki zancen be wuce na Abdallah bayi da lokacinta,"ina saurarenki kawata yanzun meyafaru?"
Cikin shasshekar kuka jiddah ta kwashe abinda ya faru ta zayyanawa ramlah ta cigaba da kuka,....girgiza kai ramla tayi daga inda take kwance waya makale da kumnenta ta lumshe ido,take kamannin Abdallah ya bayyana cikin kwayar idonta ...jiddah wawuya ce harabada bazatayi hankali tasan yadda ake hakuri da halin miji ba,tasan cewa ga yadda zata dauki hankalin mijinta koda beda lokacinta amma sammm saidai complain kullum da yawan fushi...hmmmm Allah ya kai damo ga harawa ramla ta furta a zuciyarta kafin daga bisani ta nisa ta furzar da wata iska a bakinta "jiddah ki kwantar da hankalinki ki bar wanan koke koken da kikeyi ki natsu,nasha fada miki ki kyalesa kawai ki sa masa ido kiyi harkokin ki tunda dai ai yana sonki lokacinki ne kawai beda shi ko?"tayi maganar fuskarta cike da murmushi...
Kwantar da kai jidda tayi jikin kujera tana cigaba da hawaye tace"hmmm ramlah bakisan zafin zama da miji da beda lokacinka ba shiyasa kike wadanan maganganun,ramlah kinsani ni macece mai son soyayya da kulawa amma sam abdallah baya bani"tayi maganar cike da takaici.
Aiko bazai baki ramla ta furta a zucuyarta kafin daga bisani ta nisa "nikam jiddah yanzun me kikeyi kina ina shi kuma yana ina?"
"Ina patlor ,na barosa a harabar gida yana abinda ya saba"...
Zabura ramlah tayi ta zauna zuciyarta na harabawa,tabbas dama ta samu da zata je gidan tayi tozali dashi koda bazai kulata ba don tasamu sukuni a zuciyarta..."ammm...kinsan me...kiyi shiru gani nan zuwa gidan"...dadi ne ya lullube jiddah ta gyada mata kai tamkar tana ganinta sanan ta kashe wayar ta maida kanta jikin kujera tana sauke numfashi.....
********
Cikin minti arbain
Ramla ce ta fito daga cikin keke napep fuskarta ta sha hoda da tayi dau,ga kawalli da tasa wanda ke kara fito mata da ainihin kyawu irin nata ,sallamar me napep din tayi ta karaso gate din ta shiga bugawa,...a guje mai gadi ya taso ya zo ya bude gate din,ganin ramlah ce ya washe baki "barka da zuwa hajiya ramla"
"Barka dai baba garba ya aikin"tana maganar ne tana kokarin shirgowa,suka gaisa amma gaba daya hankalinta na kansa,tun daga nesa ta hangosa ya dora ido akan computer gashin kansa yasha gyara,yana sanye da polo shirt fara sai daukar ido yakeyi...wani numfashi taja saboda yadda tasamu shock a zuciyarta,lumshe ido tayi tana takowa batare da sanin inda takesa kafarta ba,wani yarrrrr takeji a jikinta so da kaunarsa suka hadu suka lullube jinin jikinta da tsokarta,...tsaye tayi dan nesa dashi tana kallonsa pink lips mata aka sani dashi amma Abdallah ko wata macen bazata nuna masa kyawun labba ba masu daukar hankali....yanzun nasamu wanan mijin?hmmm ai nagama samun aljannar duniya,kome zaiyimun zan hakura zan kuma bi dik hanyar da zanbi wajen samun hankalin mijina amma banda waccen saunar da tana gabbbb da yin wauwtarda zatayi danasani mara amfani....sauke ajiyar zuciya Ramla tayi ta d'anyi taku gab dashi ta gyara muryarta sanan tace "barka da yammaci Abdallah....anata aiki ne?"jin murya ba irinta jiddah ba ya dago kai Yana ganinta yayi murnushi "hajiya Ramla kece a gidan namu da yamma haka?"
Washe baki tayi ta gyada masa kai tana murmushi ya maida kansa "yanzun mutuniyar taki ta shiga ciki"
"Hmmm anata aiki ne?toh Allah ya bada saa ayi aiki lafiya da kyau"tana fadin haka ta juya ta nufi sashen nasu...dago ido yayi ya bi bayanta da kallo ya tabe baki "jiddah ta kasa fahimtar aikin nan don ita da yaranta nakeyi mai makon taimun addua irin haka saidai raimun rigima... yanzun nasan Tana ciki tana abinda ta saba kuka,dole ne ma inbata hakuri don ta barni inyi schedule dina na dare"...ya cigaba da aikinsa ..
********
Gefenta ta zauna tana lallashin jiddah cike da damuwa "ni banaso kinasawa zuciyarki damuwa har kizo kisamu wata matsala a ta dalilin Abdallah,nasha fad'a miki masu hali irin na Abdallah basu canjawa dik macen da ta samu miji me hali irin na Abdallah to tabbas tanada aiki idan tace sai yayi mata abinda takeso tana da aiki tanada wahala,kinki ganewa ke kuwa kullum cikin kuka sai hawayenki ya kare"
Dago rinannun idanuwanta jiddah tayi tana kallon ramla,sosai tayi kyau tasha make up dikda simple make up ne hakan be hana fitowa da ainihin kyawu irin na Ramla ba,saidai fa dik kyawu irin nata bata kama kafar ita kanra jiddan ba,amma zuciyarta batayi mata dadiba,haka kawai taji kishi domin abinda ta tsana ne ganin mace tayi makeup mai kyau kuma mijinta ya ganta,dikda tasan halin Abdallah sam beda lokacin kallonta ma balle wata mace amma tanajin matukar kishi idan wata mace tayi kwalliya ya ganta balle har su gaisa,kuma ta tabbatar sun gaisa din....ganin jiddah taki magana sai kallonta take yasa ramlah dan kai mata duka "dik takaicin Abdallah din ne?yasa kikemun wanan kallon?...na gansa ai min gaisa hankalinsa na kan computer"
Kishi ne kuma ya lullube zuciyar jiddah amma saita danne saidai ramla ta kafeta da ido tana karantar yanayin nata wanda ta kasa fahimtar komi...."jiddah...inada shawara da zan baki akan abinda Abdallah yakeyi miki"..da sauri jiddah ta ruko hannunta "ina sauraronki kawata...ina matukar jin dadin fada miki damuwata a koda yaushe saboda nasan kina kawomin mafita,dan allah menene mafita akan lamarina da mijina?ina bukatar soyayyarsa,ina bukatar samun kulawarsa,ina bukatar lokacinsa....me zanyi insamu wad'anan"...kallom jiddah kawai ramla keyi..a tunaninki zan kawo mafita?saidai in nemi mafitar da ni zan shigo in samu hankalinsa da dik abinda ke kike bukata,...murmushi tayi mai ciwo "irinsu Abdallah sammm baa samun abinda akeso a wajensu jiddah.... dik abin nan da kika lissafo bazaki samesu ba saidai inbaki mafita kawai ,ki rinka samun relief cikin ranki"...gyadawa ramlah kai jiddah tayi cike da kosawa tace "ina sauraronki kawata"....
Kauda kai Ramla tayi,zuciyarta na raya mata...damar farko ta samu...wadda zatai leading dinki zuwa ga cikar burinki Ramla.....
Muje zuwa masoya ..bayan cakwakiyar KAMAL da BILLY....ga wata sabuwa😂
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:01 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN FA'RI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY MENTOR....BILLY GALADANCI... ILYSM*🎂❤💋
*2*
Shiru Ramlah tayi tana kallon jiddah cike da tausayawa,hawaye ne suka soma zubowa a fuskarta shaffff shaffff hakan yasa jiddah ta kara narkewa da kaunar kawartata aminiyarta....zuciyarta a karaye tace "banida kamarki kibar kukan nan ramlah ki fadamun mafita kawai abinda zai fusheni nake bukata,ina bukatar taimako banida wanda zai bani shawara kaf duniyar nan daya wuceki domin na yarda dake"tasa hannu ta goge hawayenta,runtse ido ramla tayi bugun zuciyarta ya tsananta tabbas kukan farin ciki takeyi a zahiri amma a bad'ini kuwa tanayi ne don jiddah ta kara gasgata irin yadda ta damu da ita, katse mata tunani jiddah tayi "come on ina saurarenki kawata"
"Hakika kina bukatar taimako da shawara,saidai ke kin kasance bame son social life bace,kawai dai kinada ilimin ne amma rayuwa irinta wayayyu baki fiye sonsu ba jiddah,kuma rayuwar nan matukar kanason farin ciki to dole ka cire duhun Kai ka waye kamar yadda sauran mata sukeyi wadanda mazajensu basu fiye basu lokacinsu ba"gaban jiddah ne ya fadi me ramlah ke nufi wato tabi maza da aurenta ko yaya?...kallon da ramlah keyi ma jiddah take ta karanci inda jiddah ke hasasowa,hmmmm bazan doraki a hanya yanzun ba bazan taba fito miki a mutum ba saidai a hankali zaki hau hanyar da kanki,dukkansu shiru sukayi,kafin daga bisani ramlah ta nisa"nasan inda tunaninki yaje,sammm bana miki fatan wanan kazantacciyar rayuwar da sauran matan aure sukeyi na huld'a da wasu mazajen da ba nasu ba dikda mazan keda laifi 70%wasu kuma matan ne masu son abun duniya da kwadayi"ajiyar zuciya jiddah ta sauke"har naji Dadi kawata wallahi har gabana ya fadi da naji kin ambaci wayewa da social life,yanzun fito dani haske don kinsani a duhu kin kuma bani a dukunkune"...murmushin nasara ramla tayi "kinada babbar waya ta kece raini ai kin wuce bacin rai,kawata daurewa zakiyi kisa kanki rayuwar chat kina fira da kawayenki da abokan arziki suna debe miki kewa,akwai abubuwan da waya ke debe maka kewa dasu a wanan hanyar kake gogewa ka waye ka koyi abubuwa da dama,sanan koda yaushe kina kunshe kanki a daki kamar wata kura,kuma sunan kin iya mota amma ko nan da can baki fita balle kiga gari ki hadu da sababbin mutane kiyi rayuwa kamar ko wace mace me yanci, Abdallah bazai taba hanaki dan zuwa supermarket shan ice cream ba saboda bashida lokacin da zai kaiki balle kuyi soyayya sai kikai kanki ki zauna kisha iska kiyi hotuna kema kiga gari haba kawata kina matukar bani mamaki"...ajiyar zuciya jiddah ta sauke,tayi shiru tana tunani tabbas maganganun da ramlah ta fada gaskiya ne amma idan taje shan ice cream bazata had'u da maza ba kuwa?....tou idan kin hadu dasu ai sai kinbasu fuska ke kawai kinje kiyi nishadi ne"wata zuciyar ta bata amsa,take tasamu natsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata...
Ruko hannun ramlah tayi "hakika banida kamarki kawata kinkawo shawara sosai hakan zanyi da yawan kallace kallacen nan da nakeyi na films kala kala ai gara in rinka shiga duniyar gizo ance har koyon rayuwar aure akeyi"
"Kwarai dagaske kawata"ramlah tayi maganar cike da gamsuwa.....
********
Gab da kiran magriba ramlah ta fito rike da hannun jiddah wadda ta fito raka ta,hangosa yasa bugun zucuyar ramlah ya tsananta adduarta Allah yasa ko allah ya kiyaye hanya yayi mata taji muryarsa kafin ta tafi amma da alama waya yakeyi har suka karaso dabbb dashi zasu wuce...jiddah ta ruke hannunta alamar su tsaya,"naga sweet na waya bari kuyi sallama ko?"
"Kikasan lokacin da zai gama wayar?kibari kawai ma hadu next time"...
Shi kuwa waya ya cigaba da yi "haba man kaiko abun kunya ace tunda nayi aure shekara daya har yanzun baka zo gidana ba yanzun kacemun zakazo amma kana fad'amun kila wa kala meye haka zanyi fushi kuma itama zatayi fushi zan zugata dik ranar da kazo taki baka ko ruwa"....kallon side din dasu jiddah suke yayi ya sakar mata wani murmushi da wani irin kallo mai narkar da zuciya, tsuke fuska jiddah tayi dikda yadda kallon ya saukar mata da kasala amma haushinsa tajeji,ita kuwa ramlah tamkar ta saki fitsari taji saboda yadda kallon ya tafi da tunaninta jijiyoyin jikinta dik suka saki.....washe baki yayi hakoransa suka bayyana kafin daga bisani ya kashe wayar "dama yana dariya?"ramlah ke tambayar kanta,maganar jiddah ta katse ta "sweet ramlah tazo har zata tafi ko gaisawa bakuyi ba balle kace mata wani abu to zata wuce"...
Amshe zancen Ramlah tayi "ke kuwa kawata aiki yakeyi ai nagani,kuma mungaisa dama ba donshi nazo ba danke nazo ai"ta karashe mgnr cike da zolaya....maimakon yayi magana murmushi yayi ya dago hannu "ki gaida gida ramlah"ya dauki laptop dinsa ya nufi cikin gida....kallo jiddah tabishi dashi cike da takaici.....kafin suka nufi gate ta raka ramlah saida taga tafiyarta sanan ta juyo cike da haushinsa ta nufi gidan....
Tura kofar tayi ranta babu dadi ta rufe kofar ta juya da nufin shiga dakinta taji an janyota jikinsa ta fada ya ruko kugunta yana kallon kwayar idonta batare da yace komi ba kallon da yake mata ne ya kashe mata jiki ta kasa ko motsi mai makon yayi magana hade bakinsu yayi guri guda yayi mata light kisss ya dage mata gira tasan abinda yake nufi sarai....hakuri kenan amma bazai iya bude baki ya bata ba,haushinsa ya turnuketa ga soyayyarsa da ke azalzalar zuciyarta....cike da mulki ya soma magana "abokina zai zo bayan sallar isha'i a shirya masa wani abu mai sauki,aminina da nake fada miki bezo bikin mu ba amma dai yanada hotunan mu na biki yau nayi masa gori yacemun zaizo insha allahu yaganki"... tabe baki tayi ya kashe mata ido ya saki kwankwasonta "zan watsa ruwa in cigaba da aiki kafin a kira magriba"be jira cewarta ba ya shige dakinsa ya barta nan tsaye kamar an dasata ga rukon da yayi mata ya haifar mata da kasala....
******""
Tana idar da sallah ta janyo wayarta ramla ta mike tsaye ko hijab bata cire ba ta shiga trying wata number....
Daga can bangaren kyakkyawan saurayi ne ajin farko Wanda kallo daya zakayi masa kasan ya hadu naira da hutu sun zauna yana kwance babu Riga jikinsa gashin kirjinsa sun kwanta lufff luffff tunda ya gama waya da Abdallah ya kife wayar a gefensa,yana jin kiran sallah ya kasa tashi domin yana tunanin yadda zaai yaje gidan Abdallah ya hadu da kyakkyawar matar nan tasa mai mugun kyau wadda tinda yayi tozali da hotonta soyayyarta ta mamaye zuciyarsa....kiran waya ne ya katse sa....dago wayar yayi ido a lumshe ganin me kiran kamar bazai dauka ba ya dauka "hello"cike da kasaita yayi maganar.
Ajiyar zuciya ramlah ta sauke "Ran manya ya dade mai sarauta...tun daxun nake trying numberka bata shiga yaayah bilal"tayi maganar cike da ladabi..."ramlah kanwata ya akayi? fadi maganarki don sauri nakeyi zan fita"
"Dama nayi maka massage ne a WhatsApp,akwai wata kawata kyakkyawar gaske nasan zaku dace dikda kace ka daina soyayya,amma kusan matsalarku daya don heart break tasamu zakaji recording dinta yadda take bukatar soyayya da kulawa nasan zaka taimaketa yaayah bilal"...shiru yayi yana saurarenta,bayajin akwai yarinyar da zaiso yanzun don zuciyarsa cunkushe take da abubuwa "owk zan bude massage dinki bari inyi wanka"yana gama maganar ya datse be jira cewarta ba tayi jifa da wayar a kujera yana tangadi ya fito sashensa sukai karo da momynsa... "Kayi sallah kuwa?"
Shafa kai yayi "sallar zanyi dai inaso indauko abune can dakin na ajiye takalmina"ya wuceta tabisa da kallo.....
Wani dadi ne ya rufe ramla....ta soma magana ita kadai "nasan cewa zansha jan aji wajenka ya bilal amma nasan zakaso jiddah...don kyawunta ya zarce dik wani tunanin me tunani,dikda nasan kai din ba mutumin banza bane saidai kuyi soyayya...kuma zata soka saboda ka iya kulawa....baxan taba sanar dakai cewar matar aure bace,kuma itama nasan a hankali zaku saba"....wani dadi ne ya lullubeta ta lalubo wayarta ta hau WhatsApp ga mamakinta saboda gb WhatsApp gareta taga besty online...sunan da taiwa jiddah saving dashi,number bilal ta shiga har yanzun be bude massage dinta ba balle yaga hoton data tura masa da recording din jiddah lokacin da take hawaye tana fadin "kinsan ni mai bukatar kulawa da soyayya ce amma sam bana samu wajensa,zuciyata bataimun dadi da wanan halin na ko in kula da yake nunamin"...tana rungume da wayar tana murmushi ramlah ta kishingida....
Tsaye tayi akanta tana kallonta cike da kulawa yar dattijuwar matar tayi magana "ah ah ramlah yaushe kika shigo ne?sai murnushi kukeyi rungume da waya?ko kinyi wani babban kamu ne"tai maganar tana gyara zama gefen da ramlah ke kwance,
"Ummah na kenan bazaki gane bane"tayi maganar tana fara'a sosai tana kokarin duba waya....
Kwatsammm taga bilal ya bude sakonta...
********
Yana gefenta yana aiki yana kallom sashenta minti minti tana rike da waya batace masa komi ba,tabe baki yayi yau jiddah ce rike da waya?hmmmm ai gara ko ta kyaleni inyi aikina "jiddah...."ya kirata cikin wata irin murya,dago ido tayi ta dubesa batare da tayi magana ba ,be damuba yace "kin kammala abinda nace kiyi?man zaizo gidan nan inaso yaci wani abu"..gyada masa kai tayi a sanyaye tace "ehh nayi masa miyar kwai da hanta na dafa masa couscous,tunda dama inada pepe soup a fridge na kayan ciki sainayi warming a microwave kawai na hada da samosar da nayi da safe"...tana mgnr idonta akansa wani irin sonsa ke fuzgarta,cije lebe yayi "thanks "yace ya maida kai ya cigaba da aiki ta janyo wayarta....
*******
Kafafuwansa kasa daukarsa sukayi bilal ganin tsalelen hoton jiddah da ramlah ta turo masa,zooming yayi yana kallo idonsa ko kiftawa bayayi zuciyarsa ce kawai ke harabawa,tabbass jiddah ce wanan matar Abdallah abokinsa,amma ta yaya ramlah tasanta?saidai bashi da amsar tambayar daya wuce ai tace kawarta ce....ya kunna VN din....yana saurare,cikin kuka tayi VN din shiru yayi yana nazarin kalamanta ko shakka babu Abdallah beda lokacin matarsa don yasan waye Abdallah,ya kuma san halinsa na nuna halin ko in kula akan kowa indai game da aikinsa ne....wani irin abu yaji na yawo a jikinsa da ya haifar masa da kasala...hoton yake kallo ko kifta ido bayayi,tabbas itace soyayyarta ke dawainiya dashi....taya tarayyarsa zata kasance da matar amininsa?....anya kuwa?...saidai tausayinta yakeji jin furucinta...idan haka ne kuwa zai bada kai zai bada hadin kai wajen sama mata farin ciki,zai boye kansa gareta....zai karbi numberta bazai taba bayyana gareta ba saita saba dashi....gumi ne ya barko masa duka jikinsa,ga fanka amma yadda jikinsa ke saukar da zufa yasa shaddarsa ta jike ta gaba...saidai fa Abdallah amininsa ne toya kenan?"...anya ma zaije gidan kuwa?idan yaje gidan shikenan bazai samu damar fiddata cikin wanan halin ba,yana jin tausayinta sosai kuma dama yana sonta...to kodai ramlah tasan yana sonta ne?..da sauri ya girgiza kai batasani ba saboda basu haduba tadaisan yanada aboki Abdallah....mikewa yayi ya zare rigar jikinsa ya fada kujera ya ruke kansa....
Tana kwance tana zabga murmushi ganin ya bude massage din kamar daga sama taga ya rubuto send me her number... jikinta ya kama rawa farin ciki ya lullubeta,a zuciyarta ta furta yanzun zan tura maka number matar abokinka da bakasani ba...nasan bakasanta ba bata sanka ba.... Allah yasa ka kamu da sonka itama haka...idan hakan ta kasance na hau hanyar farko na cikar burina...first step kenan na plans dina.....ta tura masa number...
*******
Karfe tara bezo ba kamar zatayi magana ta fasa,gashi tana son hira da mijinta amma bashida lokacinta tana ruke da wayar tana magana da ramlah ta WhatsApp tana sanar mata da gata gashi amma be kulata,...hankakinta na kansa baya ga wayar ko kadan tana kallonsa minti minti yakan dubi agogo...wayarsa ya janyo yayi dialing number dik tana kallonsa minti kadan taji ya soma magana "man...najika shiru ga dare yayi ko ka fasa zuwa ne?"... bataji me akace ba taji yayi shiru can yace "owk allah ya tsare"ya kashe wayar ya dubeta,
"Man bazai samu zuwa ba wai abbahn sa jikinsa ya tashi sunje asibiti tun tuni tunanin fita dashi waje ma suke sai ya dawo komi ya natsa zaizo"ya maida kans.
Tabe baki tayi ta hararesa batare da ya ganta ba ta cigaba da latsa waya....horn din mota yasa ta dakata da danna wayar tana kallon kofa dik tunanin ta ma abokin nasa ne yayi masa surprise,wasu yan mata guda biyu ne suka soma shigowa dukkansu sanye da jallabiyoyi kafin ta motsa dattijuwar data biyo bayansu fara kyakkyawa mai matukar kama da abdallah ta shigo sanye da medicated glass ...kallon fuskarta tayi gabanta ya fadi jikinta ya kama rawa "barka da zuwa ummah....sannu da zuwa ku zauna"wani kallo ummah tai mata "hamshakiya ko bakice inzauna ba tunda gidan dana ne ai dole in zauna..."wani miyau ta hadiya jikinta na rawa tana kallon ummah da take watsa mata wani kallo cike da kiyayya....
Abdallah kuwa ture table yayi "barka da zuwa ummah"
"Barka dai Abdallah,...kana zaune hamshakiya na gefenka tana danne danne a waya da tsohon daren nan kana kallonta,chating din takeyi itama na tsiya"..kallon jiddah yayi da idonta yayi jajir ya girgiza kai "ba chat takeyi ba"...wani kallo ummah tayi mata tasan abinda take nufi yasa ta mike jiki babu kwari ta nufi daki "dangin tsiya"taji ummah tace hawaye ya sulalo mata inda sabo ta saba da wanan zagin na ummah a cewarta dik kudin mahaifinta be kaisu ba... gyara zama ummah tayi "najika shiru yau bakazo gaishemu ba...na biyo inga halin da kake ciki sanan in sanar maka da an soma biyan kudin aikin hajji...ya dace a biyawa su rumaisa ko"dadi ne ya kama daya daga cikin yan matan....cike da ladabi abdallah ya sunkuyar da kai "insha allahu gobe zaaje a biya zan hada da jiddah ma..."wani kallo da ummah ta watsa masa yasa ya gimtse abinda yayi niyyar cewa "to bada yawu na ba...dangin tsiya ita dik ta gama zaman gidan ubanta be biya Mata ba?mai kudin lukudi da kayan daki na kirki beyi mata ba to ban yarda ba"sunkuyar da kai Abdallah yayi sammm beji dadin yadda ummah ke fada tana daga murya ba yasan jiddah na jiyota....
Hawaye takeyi akan gado,dik abinda ummah ke fada a kunnenta...itadai ta shiga uku uwar mijinta bazata taba sonta ba,ga miji beda lokacinta...ya zatayi ina zatasa rayuwarta? Abdallah yana sonta amma beda lokacin kulawa da ita...beda lokacin ta ko kadan...kifa kanta tayi a pillow tana hawaye...hasken wayarta yasa ta janyo massage gareta a WhatsApp...kamar bazata duba ba ta bude...wata number ce aka rubuta Assalamu alaikum .....
Shiru tayi tana nazarin number waye wanan keyi mata massage?share hawaye tayi tana kokarin amsa sallamar...
Ganin tana typing bugun zucuyar Bilal ya tsananta...ta bude massage dinsa...toya kenan?ta ina zaifara?shafa kansa yayi ya furzar da iska mai zafin gaske....runtse idonsa yayi tunani ya shigayi...bazai taba sanar mata da shi waye ba hk ramlah bazai taba nuna mata yasanta dama yana sonta ba....
Bangaren ramlah kuwa mikewa tsaye tayi ta shiga zagaye dakin rungume da hannuwanta yadda zatayi wa plans dinta.......
MUJE ZUWA
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:04 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*3*
Hawaye ke gudu a fuskar jiddah kamar an bude famfo hannu tasa ta share hawayenta tayi replying massage din bilal daya shigo a take kmr haka
Inaso insan da waye nake magana please...
Daga inda bilal ke rike da wayarsa ya daga idonsa sama ya sauke hade da furzar da iska mai zafi...
_Mai satan mutanene shine nakeso insaceki ta cikin waya in gudu dake in maidake yar wanke wanke da shara..._
Murmushi ne ya subucewa jiddah ta karasa goge hawayenta,mai satan mutane? yake bayyana kansa kuma ta chat?hmmmm wanan wasa ne kawai...samun kanta tayi da yi masa reply... banason Wasa,nasan babu yadda zaai mai satan mutane ya zamana yazo social network yana bayyana kansa....am not in d mood please raina bayamun dadi ko wanene yayi gaggawar bayyanamun kansa...
Ya dade yana kallon massage dinta kafin ya lumshe ido yayi mata reply kamar haka,ni dama aikina insamawa mutane farin ciki a lokacin da suka rasa,idan haka ne kinga shikenan kinsamu mai saki farin ciki jiddah....
Zaro ido tayi rike da wayar tana mamakin yadda ya kira sunanta....tun shigowar Abdallah dakin yake kallonta batama san ya shigo ba cike yake da bakin ciki yana matukar jin tausayin jiddah....ta jikin gado taga alamar inuwar mutum ta juyo da dubanta gareshi tana masa wani kallo....gyada mata kai yayi "ki fito kuyi sallama da ummah zasu tafi yanzun ma batasan zan fada miki ba sako zanbasu na shigo nan nasan kina nan"yana gama fadin haka ya fice...kallo ta bisa dashi ta runtse ido...
Da sauri ta mike ta kalli jakar dake gefen madubinta ta dauka ta bude yadda suke haka suke turarruka da abdallah ya kawo mata masu tsadar gaske ta dauka ta share hawayenta ta fito
Abdallah ya mika mata bandir din kudi yan dubi dari guda daya jiddah ta fito dauke da faraa a fuskarta ta mikawa daya daga cikin yan matan jakar ledar "amshi wanan rumaisa ki rikewa ummah turaruka ne"
A wulakance rumaisa ta amshi ledar tana yatsina fuska hade da leka cikin ledar itada dayar matashiyar,tsaye jiddah tayi tana kallonsu hakan yasa ummah ta fusata "dalla tunda kin kawo kayan munafuncin naki ba saiki juya ki tafi ba?kinaso sai kinji sakon da yake bani ko?"...da sauri jiddah ta juya ta shige dakinta....
Kayan jikinta ta shiga cirewa a hankali ta janyo towel a jikin wardrobe dinta ta daura ta shiga wanka.... tana wankan tana hawaye haka cikin minti ashirin ta fito sai zuba kamshi takeyi tamkar tayi wankan turare....kallon jikinta yakeyi yadda take sheki tamkar tarwad'a mikewa yayi ya karasa ya rungumota ta fada jikinsa ya hade bakinsu waje daya ya shiga tsotsan lips dinta,hannunsa yasa ya shiga yamutsa gashin kanta zuwa wuyanta....wani abu takeji yana mata yawo a jiki tamkar tana nan da nan hawaye suka shiga zubowa a idonta...ya iya soyayya yana azabtar da zuciyarta da soyayyarsa amma beda lokacinta ko kadan...ja da baya yayi a kasalance itama kallonsa take idonta sun kankance tana kokarin Kara narkewa a jikinsa yaja da baya "sha mai kisa nighty dinki ko?...ammm soo sorry da abinda ummah tayi miki hope ya wuce?"umm?gyada masa kai tayi idonta cike da kwalla a zahiri wani irin shaawarsa takeyi amma bazata iya sanar masa da hakan ba waigawa da tayi ta hangi laptop dinsa akan gado zuciyarta ta harzuka tayi bakin kirin...batace komi ba ta karasa gaban mirror tana kallon kyawu na halitta irin nata amma samm mijinta beda lokacinta...jiki babu kwari ta shafa mai sama sama ta saka riga da wando na bacci da suka kamata hips dinta suka bayyana,tana tafe suna motsawa ta karaso ta hayo saman gadon ta zauna gefensa.... vibration din wayarta ya nunar mata da a bude tabar data dinta....
Gefensa ta matso ta ruko hannunsa tana murzawa cike da wani irin salo mai tada hankali tana yawo da yatsanta a tafin hannunsa ta dora kai a kafadarsa "i need you badly sweet..."wani kallo yayi mata da taja da baya sai kuma ya maida kai"kina sane da gobe monday inada yawan ayyuka a office hakan yasa na dauko laptop dina nake ragewa ki sauraramun please kekam baki gajiya da soyayya ne ina yanzun nayi miki kiss?"
Haushi ne ya turnuketa ta sakar masa hannu cike da takaici "ai nasan haka zakacemun mammadi kyalkyal wanda ya halitto computer bature?toko bature yanada lokacin matarka.....wallahi banga anfanin wanan auren da baa bawa hakkinsa ba"idonta a rufe tayi maganar
Wani irin kallo yakeyi mata mai cike da mamakim furucinta bece komiba yanada niyyar juyawa ya cigaba ta datseshi "baka da lokacina saina aikinka,safe dare rana kana kan computer kamar kaine ka halittota toni nagaji bazan iyaba ina da bukatar mijina da hankakinsa gareni inada bukatar kulawa da biyamun hakkina,wallahi kana tauyemun hakkina Abdallah sai Allah ya sakamun"hawaye ke zuba a fuskarta take maganar,bakin cikin furucinta yasa ya dauki laptop dinsa ya fice bakin cikin haka yasa ta daga murya "sai Allah ya sakamun"....be gama fita ba call ya shigo wayarta....
Tsaye ramlah take tana kallom agogo tayi dialing number jiddah...kallon agogo tayi sha daya da minti goma na dare,kardai suna can tasamu kansa suna rungume da juna?anya bazai yuwu ba Abdallah bazai taba samun lokacin jiddah ba....ta kara dialing number...
Share hawaye jidda tayi ta dauki wayar ta lumshe ido Allah sarki Ramlah kamar tasan tana cikin bakim ciki....ta kara wayar a kunnenta cikin shassheka tace "hello ramly baki bacci ba"
Gyaran murya ramla tayi "lafiya dai ko me kikeyi?naji kamar kuka kikeyi inace ma kuna can kuna soyewa da Abdallah,ashe kina kuka"kuka jiddah ta fashe dashi cike da takaici allah sarki aminiyarta..."ba soyayya mukeyi ba ramly ya tadamum da hankali ya gusar mun da kuzari n...."ta kwashe dik yadda ya shigo yayi mata bayan fitowarta wanka ta sanar mata...
Kishi ne ya dirarwa Ramlah a zucuya ta runtse ido tana imagining Abdallah na kissing dinta ita kanta...bude ido tayi "yanzun kuka kikeyi? mtswww har yaushe zan sanar miki da abdallah ba irin maxan da mata ke iya canjawa bane?meye amfanin wayarki?kidau wayarki ki kauda wani tunanin Abdallah kiyi hira da mutane nima ina online din muje muyi magana"
Share hawaye jiddah tayi "owk ramly"ta dire wayar ta cire ta a key ta bude massages...
Yana kwance rike da wayar yana zooming din hotonta yana kallon dan karamin bakinta da zaiyi dadi da tsotso yaga alamar ta hau online jikinsa har rawa yake ya kurawa contact dinta ido ganin yayi indicating tana typing.....
"Sorry please who are you,meya kawoka cikin rayuwata?"
Murnushi yayi "nazo ne insaki farin ciki kmr yadda kikacemun dazun baki ciki...ni banason inga kanenna cikin bakim ciki...jiddah kanwata na daukeki domin inada kanne mata kuma mata abun lallabawa ne....
Lumshe idonta tayi, bugun zuciyarta ya tsananta,kalmar mata abun lallabawa ne shine ya tsaya mata a rai ta shiga maimaitawa...kwalla ce ta ciko a idonta tunawa da abinda mijinta yayi mata...maizai hana bazata maidasa yayanta ba?tunda har ya iya wanan furucin...kinyi shiru....ya turo mata...
Lumshe ido tayi ta gyara kwanciya tanajin wani abu cikin jikinta...muguwar shaawah ce tattare da itam.."naji dadi dana samu yaya mai kaunar farin cikina...dama a gidan mu banida yaya namiji....
Wani dadi ne ya kama bilal ganin reply dinta...yasamu damar da zai amsheta a hannun Abdallah...domin ba irinsu Abdallah kesamun ramla ba...kwanciya ya gyara ya dauki hoton fuskarsa da pink lips dinsa ya fito da harshensa ya tura mata....
Ganin ya turo mata hoto tsoro ya kamata kardai hoton iskanci ya tura mata...dakyar ta bude hoton...kallon harshensa da lebensa lips dinsa takeyi...lumshe ido tayi zuciyarya na bugawa,wani abu taji ya tsarga mata tai saurin kifar da wayar ta kwantar da kai lamo akan pillow.....massage din ramla ya shigo ta karamar wayarta..."kawata...gobe ki tambayi Abdallah muje musha ice cream kodan in gusar miki da wanan damuwar da kike ciki wallahi nakasa bacci a dalilin jinki kina hawaye...hope dai kindaina kukan....murmushi jiddah tayi tai mata reply da...
Nabar kuka nadansamu nishadi kasantuwar ina online.....tana mata reply ta kashe wayar ta maida kai a pillow ta lumshe idonta...ba bacci takeyi ba kewar mijinta takeyi da sauri ta mike ta dan daga labule hasken computer take hange a parlor ta kalli agogo daya saura na dare...dawowa tayi ta fada kan gado ta fashe da kuka mai ciwo....
********
Misalin karfe bakwai da rabi na safe tana rike da waya a kishingide da pillow tana taba chat sama sama...tana jiyo motsinsa zuciyarta da ruhinta na wajensa amma zafinsa da takeji yasa ta kasa motsawa,kallom agogo tayi taga lokaci tasan shirin fita aiki yakeyi gashi ko nemanta beyi ba,anya ta kyauta kuwa?ajiye wayar tayi gefen pillow ta fito
Kayan baccin jiya nw jikinta gashinta kwance a kafadarta ta fito kallo daya tai masa taji wani yarrrr a jikinta yana sanye da suits bakake ya gyara gashin kansa sosai da ID card dinsa makale a jikin gaban rigarsa yayi kyau sosai yana rike da jajarsa hannunsa daya cup ne na tea daya hada ya kurba ya dire akan centre table ya ajiye jakar a kujera yana kokarin gyara necktie tayi saurin ruko hannunsa yana kallonta bece komi ba ta kama ta shiga gyara masa idonta nakansa shima kallonta yakeyi...tausayi ta dan basa ya ruko kwankwasonta da niyyar hadata da jikinsa tayi saurin janyewa tana ja da baya tana girgiza masa kai daga mata gira yayi ta sunkuyar da kai "sai ka dawo allah ya tsare"...makale kafada yayi ya rataya jaka ya daga Mata hannu har ya Kai kofa ta tsaidashi "ammmm sweetttt..."cak ya tsaya yana kallonta "dama inaso in fita zan siyi cosmetics zan biya insai ice cream"... murmushin gefeb fuska yayi "kwad'ayin ya motsa kenan....to a dawo lafiya..amm ki biya gidan ummah kijirani har indawo"gyada masa kai tayi tana daga masa hannu ya fice...ja da baya tayi ta zauna a kujera ta sauke numfashi ina sonka mijina....hawaye suka zubo mata...
*******
Sanye take da bak'ar jallabiya musamman dama shigar data saba ce ramlah tanason bakaken kaya dikda bita din ba fara bace chocolate coulor ce mai shegen kyau yasa jallabiya ke amsarta yau da wani gyale tayi nadi maroon fuskarta sai sheki take ta fito parlor rataye da maroon din jaka
"Ah ah ramlah sai Ina da sassafe haka? nadaisan bakida inda zaki da ya wuce gidan jiddah amma yanxun safiya tayi dayawa gashi kinsha kwalliya kamar me zuwa gasar fidda gwani"...dariya ramlah tayi ta kalli agogo ummah nason bata mata lokaci tanason bata mata plan dinta na yau,tasan Abdallah na gab da wucewa ta kofar unguwarsu kuma bazai ganta gefen titi batare da ya dauketa ya rage mata hanya ba....kamshin turarensa takeson shaka...
"Ummah sauri nakeyi sako zan bada wallahi....yaya bilal ne ke jirana"
Wani kallo ummah tayi mata kafin tace wani abu ramlah ko dubanta batayi ba tai gaba abinta...itama mikewa tayi ta nufi dakin kannen ramlah ta tasosu suyi shirin makaranta....
Tuki yakeyi cike da natsuwa a hankali a slow motarsa ke tahowa tundaga nesa yake hangenta,sai ya rage gudu waccen kamar ramlah kawar jiddah anya to ina zata da safen nan da alama abun hawa take jira...
Ita kuwa bugun zucuyarta ne ya tsananta ganin yadda yake slow alamar zaiyi parking a daidai gefenta yayi parking, fuskarsa as usual babu faraa ko kadan ya nisa "ramlah ina zakije ne da safen nan?kike tsaye a titi ga sanyi"
"Ina kwana Abdallah"ta gaishesa tana murmushi.
"Lafiya....idan babu damuwa inda zakije hanyata ce ki shiga in direki mana?"
Girgiza masa kai tayi tana kallon kwayar idonsa...zuciyarta na cigaba da harbawa,bece komi ba sai jiranta da yake...bata da zabi daya wuce ta shiga ta shaki kamshin turarensa...bude motar tayi ta shiga ta zauna ta daidaita yaja motar beko kalli inda take ba babu kuma fara'a. Ko kadan a fuskarsa....kallon faffadan kirjinsa tayi ji takeyi tamkar ta kwanta ya rungumeta taji duminsa...sun danyi tafiya kafin ta nisa "dik inda zaka nemi aiki a kasar nan baka samu,kuma aiki a yanzun shine babban abu me muhimmanci ga wanan rayuwar da ake ciki...shiyasa bana ganin laifin masu aiki da suke maida hankali su wajen bawa aikinsu muhimmanci gani nan sai wahala nake da takardu"...tayi maganar tana satar kallonsa,drivin yakeyi beko ce komi ba sai can har ta fidda rai zaiyi magana "kina neman aiki ne?...a ina"ya kalli agogo yayi tsaki ganin ya kusa latti...
"Kusa da maaikatar ku ne nan gidan wani radio dake jikin maaikatar ku"
"Meye qualifications dinki?kamar daga sama yayi tambayar...
"Mass communication"ta bashi amsa a takaice daidai sun karyo kwanar kofar maaikatar da take fada masa ,gefen hanya yayi parking...."bani photocopy akwai wani Dana sani ciki,idan na shiga office zan nemesa inbasa takaddunki...idan mundace to"...wani farin ciki ne ya lullubeta tana kallon lips dinsa da dogon hancinsa...saidai fa ya tsare gida amma ajiyar zucuya tayi ta bude jakar ta kawai ta ciro takaddun da dama tana tawo dasu ta mika masa...be jira me zatace ba ya bude mata motar da key "bye"...jiki babu kwari ta fito tarufe motar ta d'aga masa hannu yaja ya karya kwana ya nufi office... Tsaye tayi tana bin motar da kallo....wani farin ciki ne ya lullubeta...burinta na dabbb da cika matukar tasamu aikin nan... Allah yasa dai tasamu....idan tasamu kuma sai babban aikin dake gabanta wato shawo kan Abdallah... domin da alama bata ko burgesa....zata kuma sha wahala...amma tasawa ranta jurewa mafarkinta shine ta kwanta a faffadan kirjinsa.....
*******
"Oyoyo Anty Ramlah oyoyo natashi banganki ba ina kikaje da safe ne"
Ajiyar zuciya ta sauke cike da gajiya ta zauna gefen ummah dake kallonta tana jiran karin bayani domin mika sako wajen awa daya?..."ummm kinsan me wallahi takadduna na bada zaa nemamin aiki Allah dai ya taimakeni domin ina jiyo mana kamshin sabuwar rayuwa"...shewa kannenta suka dauka ummah ta washe baki "kinga kisamu aiki... Allah ya baki saa kisamu miji kamar mijin kawarki jiddah"
Karaf kanwar ramlah ta amshe "aiko mijin jiddah ne yace zai aureta ummah ajiye kawancen nan zaai domin miji ne na kerewa saa"... dariya ummah tayi batare da tace komiba ta mike "kwaji da shirmen nan naku Allah ya kawo na gari"...
Mikewa ramlah tayi rike da jakarta "bari inshiga indan huta dan zamu fita nida jiddah anjima"...ta nufi dakin ta tana shiga ta rufe kofa ta bude WhatsApp...ga mamakinta jiddah online...tun safe take online...hmmmm tarkon da ta d'ana ya kamu kenan,ta kara dubawa ya bilal online...hmmmm tace ta kwantar da kai pillow ta zame dankwalinta bakin gashinta ya zuba a pillow dinta ta lumshe ido...na tabbatar yanzun kinsaki jiki..nasan yadda zan bullo ku hadu anjima wajen shan ice cream komi inayinsa cikin tsari da kwarewa....jiddah kinyi kuskuren auren miji kamar Abdallah....
*******
Rike jiddah take da waya tana karanta labaran da bilal ya turo mata wata irin dariya take kyalkyalawa tamkar mahaukaciya ita kadai a d'aki ta furta...yaayahhh na Allah nagode maka daka hadani da yayana dole inbawa ramly labarinsa anjima...nasan zata bani shawara saboda aurena...kar inzo insamu matsala tunda namiji ne...kallon agogo tayi kusan sha biyu da mintuna ko breakfast batayi ba yunwa yasa ta jefar da wayar...bari inyi breakfast inyi wanka kafin mu hadu da ramly rigima nasan bata african time.... gabanta ya fadi data tuna zataje gidan ummah gaidata...nan da nan farin cikinta ya gushe... Allah sarki umminta koya suke oho...jiki a sanyaye ra nufi kitchen dan nemawa kanta abinda zatasa a cikinta.....
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:05 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*4*
Zaune take a parlor tana cin dankali soyayye da kwai gefenta cup din tea ne da take kurba minti minti..hannunta rike da wayarta,murmushi ne makale a fuskarta tana karanta sakon bilal....
Yaye labulen shigowa tayi bakinta dauke da sallama suna hada ido ramlah tayi mata hararar Wasa,"wato baki ma ko shirya ba ko?inata sauri don nasan halinki bakida hakuri ko kadan jiddah amma sainazo na tarar dake zaune kina breakfast"
Murnushi jiddah tayi "kaina bisa wuya....rigima.com karaso mana kin tsaya daga nan kin soma zazzagawa haba tawan"
Karasowa tayi tana bin jiddah da kallo,kayan baccin dake jikinta yasa wani kishi ya yunkuro mata,tabe baki tayi tana kokarin zama tace "wato tun tuni kinata soyayya da Abdallah ko kayan baccin ma baa cireba,gashi ansa riga yar jan raayi"kallon kanta jiddah tayi sanan ta tuntsire da dariya "meye kuma riga yar jan raayi?sabon sunan riga kenan"
Murmushin k'eta ramlah tayi "ehh gashi kinja raayin Abdallah,wayasani ma ko aiki ya kasa zuwa?"
Zaro ido jiddah tayi "hmmm ashe zaa maimaita yakin biyafara,matukar Abdallah beje aiki ba...tou bari kiji ban tari numfashinki ba jiya saida ya gama tsotsemun baki ya kunnamin network ya sakeni ya haye gado na da sunan yim aiki,niko kinsan halin nawa nan da nan na hau na soma masifa karshe ya fice Niko na janyo wayata na cigaba da chat dina,hmmm bari kiji jiya kadai shawararki taimun amfani don nasha hirata nakai har daya na dare ina abuna yana can yana tsiyarsa....amma kinsan wani abu wallahi hankalina na wajen mijina ina son Abdallah bansan wani irinso nake masa ba"tayi maganar a slow cike da damuwa hawaye ya gangaro mata...
Wani dadi ne ya lullube ramlah bakinta ya kasa rufuwa,abinda takeson ji kenan burinta kawai kada jiddah ta rabi Abdallah da sunan jan raayinsa..."kawata ai nafada miki wallahi zakiji dadin chat zakuma ki hadu da mutane da dama da zasu debe miki kewa"...
Mikewa jiddah tayi tana fadin "naga amfanin hakan kawata bari in wanke hannu in watsa ruwa ba wani makeup zanyi ba kawai mu kama hanya"...tayi gaba ramlah tabi ta da wani irin kallo da murmushin keta....ta dawo ta wuceta tayi hanyar bedroom
Ramlah kamar jira taketi ta ciro wayarta a jaka nan da nan tayi dialing number bilal....
Shirin breakfast yakeyi ganin bega jiddah online ba ya ajiye wayar yaci abinci...sai kiran ramlah ya shigo hannu ya kai ya dauki wayar...murmushi yayi Ramlah manya a tunaninta bansan jiddah ba ..hmmm jiddah ni ya kamata insameta ba Abdallah ba, recieving ya danna ya kara wayar a kunnensa cike da katsaita yace "umm hmmm ina jinki"
Bata damu da yadda yayi maganar ba "nace yayah bilal ko zakasamemu wajen shan icecream na cikin gari?,inaso kayiwa kawata surprise ta ganka amma banaso tasan nina fada maka ka samemu kaga zaka kara ganinta....ko?wallahi cikin damuwa take ka taimakawa kawata ina matukar sonta".... tunda ta soma maganar ya dire spoon din hannunsa,jimmm yayi yana tunani jin shiru yasa ta daga wayar daga hannunta ta kalla taga tana tafiya ta kara a kunneta "hello ya bilal"
"Ina jinki ramly,bari mugani idan kun isa just tex me"
Wani farin ciki ne ya lullubeta,tamkar ta taka rawa takeji....
Shiko yana dire wayar tagumi ya rafka, tunanin yadda zai fuskanceta yakeyi,gashi awwanni da basu wuce ashirin da hudu ba kadai ya saba da ita,ya lura tanada shagwaba tanada son attention....uwa uba tanason hira yadda take replying massage dinsa jiya daddare kadai ke daure masa kai tambayar kansa ya shigayi "ina Abdallah a wanan daren matarsa ke chat"?
********
Takaddun da ramlah ta bashi ya ke nunawa wani abokinsa dake kusa da maaikatarsu "bashir wanan kace bazata samu aiki ba?"
"Ehh sir Abdallah,ai ta kawo takaddun nata ma kafin ta kama kafa da kai,matsalar bamu da vacant yanzun a kasa da badan haka ba ko saboda kai ma zamu sama mata ai kafi karfin hakan,yanzun haka ma mun tura mata massage akan bazaa samu dinba,gashi tasha wahala kusan kullum saitazo wallahi"...karbar takaddun Abdallah yayi hankalinsa na kan abinda yake kokarin turawa ta system din sa "ok no problem"..ya karba ya ajiye takaddun gefensa kofin tea dake table dinsa yadan kurba ya maida kai ya cigaba da abinda yakeyi,shiru babu meyiwa wani magana office din bakajin karar komi sai aikin fanka da AC da ta ratsa ko ina a office din hankalinsa na kan aikinsa ko motsa idonsa bayayi ga wani kyau da yayi sosai bilal ne ya fado masa arai ya kamata idan an tashi aiki ya biya ya gaida momynsa ya gansa ya dakkosa yakai gidansa tunda beda niyyar hakan,yanaso bilal yazo gidansa kodan yaci abincin jiddah....
*******
Facing din juna suke ko wacce da robar ice cream a gabanta...tun daga nesa ramlah ta hango bilal cikin wata arniyar shaddah blue da hula yayi mugun kyau dik kyaun Abdallah wani lokaci idan taga bilal rudewa takeyi,saidai bilal be kai zatin kakkarfan namiji mai ji da fadi da isa irin Abdallah ba... Sarai ya hangosu bazai taba nunawa ramlah yasan jiddah ba kuma dama yana sonta ba,sabida bayaso ramlah tasan yanada alaka da abdallah...
Kuriiiii Ramlah tayi da ido tana kallonsa yana tahowa farar fatarsa har sheki take da bakin sajensa dake kwance a fuskarsa...hmmmm jiddah zaki fada tarkon soyayya da abokin mijinki amininsa,dik ranan da Abdallah yasani kashinki ya bushe...dik wata hanya da zatasa yasani zan dod'eta har sai nasamu cikar buri na...
Hannu jiddah tayiwa Ramlah tafi a fuska "wai waye kike kallo haka?"tayi maganar tana wauwayawa... harshenta ne ya makale ganinsa a wanan lokacin,take hoton bakinsa da rabin fuskarsa daya turo mata ya hasko mata a fuska,da hotonsa dake dp dinsa,zuciyarta ce ta shiga rawa wani irin shock taji....tsaye yayi a setin su,"ah ah en mata ya kuke?ya garin tun daga nesa na hango wata kamar kanwata jiddah"
Zaro ido ramlah tayi "au dama kunsan juna?a ina kika sansa jiddah?hmmm lallai kin hadu da d'ansa nishadi don yaya bilal akwai labari da mantar da damuwa"
Murmushi jiddah tayi gabanta ya fadi ta dake "wallahi a WhatsApp na tsinci numbersa yanamun sallama harda cemun shi satan mutane yakeyi"
Dariya Ramlah ta kyalkyale dashi"indai ya bilal ne zakiji abinda yafi haka, bismillah ya bilal zauna"...murmushin gefen fuska yayi ya zauna,kallon jiddah yakeyi wani abu na ziyartar sa tun daga tafin kafarsa zuwa tsakiyar kansa...ashe hoto yana rage mata kyawu, kyawunta ya zarce dik tunaninsa....dan karamin bakinta shi yafi tafiya da tunaninsa...wani kallo yakeyi mata da baisan yana mata irinsa ba,itama kallonsa takeyi mamakin irin kallon da yake mata yasa taji jikinta yayi sanyi, gabanta ya fadi take wata zuciyar ke kwabarta da ke matar aure ce...amma irin kallon da bilal keyi mata kadai ya saukar mata da kasala...wani abu taji yanajin jikinta tamkar tayi fitsari...
Wani kallo ramlah keyi musu hmmmm tarkonta ya d'anu aminin Abdallah Bilal tare da matar Abdallah jiddah batare da yasani ba,wayarta ce tayi kara kamar jira take ta duba text ne amma saita mike da niyyar barinsu a wajen....abinda ta gani ne yayi mummunan tada mata da hankali...gumi ne ke karyo mata ta ko ina massage daga maaikatar da take neman aiki cewar basu da vacant?kenan aikin banza tayi bawa Abdallah takardunta da tayi ... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun... shikenan babu hanyar da burinta zai cika...kwalla ce ta ciko mata a ido ya zaai burinta ya cika?ta wace hanya zatabi da zata sadata da haduwa da Abdallah cikin sauki da har zata mallakesa batare da boka ko malam ba?yatsanta tasa a baki ta ciza...kaiwa da komowa ta shigayi...tanayi tana waigen inda su bilal ke zaune..hangosu tayi suna murmushi bakin jiddah na motsi alamar magana sukeyi...ga koshi ga kwanan yunwa yanzun ya zatayi?....
Dawowa tayi ta zauna jiki babu kwari kallonsu tayi ta washe baki "iyyeeee wanan yaya da kanwar kodai kodai?"..dagewa Ramlah gira jiddah tayi da wani sirri,sarai ramlah ta gane jiddah na tuna mata da ita matar aurece ya kenan?...sai ta kashe mata ido daya alamar zasuyi magana....sun kwashi lokaci suna hira minti minti ramlah na basu waje itako jiddah gaba daya bilal yadda yake mata shu'umin kallonsa ke haifar mata da kasala da wata tsantsar shaawah....wajen yamma sukai sallama da bilal suka barsa wajen sun nufi inda jiddah tayi parking amma zuciyarta bata bar harbawa ba,waige take tana kallonsa haka kawai tasamu kanta da hakan....
*******
Tafe suke a mota Ramlah taki magana gabaki daya hankalinta baya jikinta..kallon side dinta jiddah tayi"yadai ramly naga dik yanayinki ya canja kodai akwai wani abu ne?naga kina cikin damuwa"
"Ina cikin damuwa jiddah...aiki kullum saina fita nema babu inda bana kai takadduna da sunan neman aiki amma bansanuba,inda nake da hope ma yau sunyimun massage babu vacant,ina cikin damuwa gashi nayi karatu inaso insamu aiki saboda mahaifiyata da marayun kannena"..wasu hawayen bakin ciki suka zubowa Ramlah na babu yadda zatayi...shiru jidda tayi tana tunanin yadda zata taimaki kawarta ta faranta mata...ramly tausayi take bata mutum ce meson neman na kanta gashi ba wasu yan uwa garesu a garin ba,wata hanya ce ta fado mata ta sauke ajiyar zucuya ta furta "alhamdulillahi...nasamo mafita ramly"...daidai nan traffic ta tsaidasu dake alkali road...da sauri Ramlah ta dubi jiddah cike da kosawa taji me zatace "ina jinki jiddah Allah yasa mafitar ta fiddamu"
Murmushi jiddah tayi "ki kwantar da hankalinki....zanyiwa Abdallah magana ya sama miki a wajen aikinsu,domin akwai wata da tabar aiki sakamakon tayi aure baa garin zata zauna ba kawai a cike gurbinta da ke"...wani ihun Ramlah tayi "wayyo Allah kawata....wayyooo Allah dadi inama hakan ta kasance?da nafi kowa farin ciki da bazan taba mantawa dake da halarcinki ba kawata"..itama cike da murna take dariya suka karya kwanar unguwarsu dayake unguwarsu daya da umman Abdallah "inaso kiyi farin ciki kema burinki ya cika da albashin nan zaki samu abinda zaki tara idan lokacin aure yayi kinga babu me daga miki hankali a dangin abbanki"...farin ciki Ramlah takeyi bakinta yaki rufuwa bata taba kawo wanan dabarar ba cikin ranta,hmmm harta hango kanta burinta ya cika,bata gama tunani ba sukayi parking a kofar gate din gidan su abdallah hankalin jiddah ba karamin tashi yayi ba neman dik wani farin ciki tayi ta rasa a zucuyarta, Ramlah na lura da hakan tasan matsalarta da dangin mijinta...anya bazata soma kamun kafa ba kuwa?hmmm bazata fito sakkk a mutum tana son Abdallah ba amma wanan aikin da jiddah zata mata hanya ta wajen mijinta shima zaiyi linking da jonuwarta da dangin mijinta....tasan ta inda zata kamasu
Fitowa sukayi sukai cikin gidan...rumaisa na tsaye da blue jeans da polo shirt rike da kwallo suna bugawa da kannenta sauran ai tana ganin jiddah ta shigo,ta sa kwallo a kasa ta bugo d karfi is a goal sai kwallo tai sama saitin jiddah tayi suka bi kwallon da kallo....
******"
Karfe shida da rabi ya shiga hada hadar tashi aiki yanason ya ziyarci bilal yayi masa ba zata dole koyaki koyaso sai ya kaisa gidansa yau sai ya hadasa da jiddah ya ga amarya....ciro waya yayi yana kokarin rataya jakarsa ya dau makullansa yana kokarin kiran bilal,sai ya fasa gara yayi masa ba zato....
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:23 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*5*
Kallon jikinta tayi ta daga kai tana kallonsu rike da kwallon,sauran ukun yaran kanwar ummah ne dik jikinsu yayi sanyi kallon rumaisa tayi wacce annuri ya bayyana a fuskarta da gangan tayi hakan,sosai kwallon ta batawa jidda jiki sakamakon dattin dake jikinta....kallon juna sukayi da Ramlah wacce ke kallon ikon allah,cije lebe tayi kawai "muje ciki ramlah"tayi gaba ramlah na biye da ita sunyi taku zuwa goma rumaisa ta sheke da dariya ta juya ga yaran dake tsaye "ya naga dik jikinku yayi sanyi?oya mu cigaba da gashi"suka dau ihu suka cigaba da ball dinsu,
Sosai zuciyar jiddah keyi mata zafi dangane da abinda rumaisa tayi Mata a gaban bakuwa dikda ramlah tasan halin su dama,a parlor sukayi sallama suka shiga ummah na zaune gefenta wata matashiyar budurwa ce hannunta rike da plate din abinci tanaci ta bude baki zata amsa ta gimtse maganarta "au ashe dangin Allah wadai ne"ta yunkura ta mike hannunta rike da plate tazo giftasu ta ja tsaki ta watsawa jiddah wata harara....daga bayanta taji an rugumota "oyoyo anty jiddah"lumshe ido jiddah tayi ko baa fada mata ba afee ce masoyiyarta ita kadai ke sonta "oyoyo afeen anty jiddah ashe kina ciki"
Da faraar ta "ehh ina ciki keda Anty ramly ne sannunku da zuwa ku karasa mana"ta dan saketa suka karasa parlorn,ko kallonsu ummah batayi ba saida suka zauna cikin faduwar gaba jiddah ta hadiyi wani miyau "barka da war Haka ummah ina yini?"ta dan zamo daga kujerar,bata ko kalleta ba "barka dai...sai yanzun kika gadamar zuwa?ina tun tuni yace kizo ki jirashi anan kika biya yawonki tukunna?"ta kalli gefen ramlah...sunkuyar da kai ramlah tayi ta hadiyi wani miyau mai kauri ganin kallon da ummah tayi mata sai ta dan washe baki "ina yini ummah?an wuni lafiya?"
Jimm kadan ummah tayi "lafiya"ta mike tana kokarin dauke plate din dake gabanta da sauri ramlah ta tare ta "ummah bari a kai miki kawo"...saida Ramlah taga ummah ta juyo cike da kissa ta take kafar jiddah ta dago jajayen idonta ta kashe Mata ido alamar ta karbi plate din jiki babu kwari jiddah takai hannu zata amsa,da sauri ummah ta dakatar da ita "au ai ba irin tarbiyyar taki daya da kawarki ba,ita tasan ya kamata tunda saida ta miki nuni da ki amshi plate a hannu na ki kai zaki amsa,koda yake ba laifinki bane haka kikaga uwarki nayi"
Tsaki taja tayi gaba ta barta nan tsaye tana mika hannu,sosai ranta keyi mata suya,sunkuyar da kai Ramlah tayi tana jinjina yadda zata zauna da wanan a matsayin uwar miji idan ta mallaki Abdallah...komawa tayi ta zauna cike da bacin rai...
*******
Yana kokarin fitowa da mota ,zai sake fita Abdallah yayi parking a kofar gidan, Yana hango Abdallah ya fad'ada murmushinsa sai yayi parking ya fito Yana dariya,fitowa Abdallah yayi fuskarsa a dan daure ya harde hannu "common man ya ka hardemun hannu haka ko gaisawa bazamuyi ba?dik fushin banje gidanka naga amarya bane?"
"Ehh...ace dik yadda nake dakai inyi aure har yau bakasan gida na ba bakasan matana ba?haba bilal wallahi banji dadi ba ranan har abincu aka shirya maka bakazo ba"...jimmm kadan Bilal yayi yana sosa kai gaskiya bayajin yadda yaga jiddah sukai ido da ido ya tabbatar da ta aminta dashi a matsayin yaya zaije a matsayin abokin mijinta,idan yaje ai komi ya lalace shikenan ya zaiyi da sonta da yakeyi?...tabosa Abdallah yayi "malam kabar wanan tunanin da kakeyi ka taho muje gidana dan yau din nan nakeso muje dakai ka maida motarka ga motana nan muje kawai"...kallonsa bilal yayi ya sauke ajiyar zuciya bashida option da ya wuce ya bisa amma ta yaya zaije gidan ya fito basu hadu da jiddah ba..."owk bari in maida motana ciki yau dai inje in ga amarya inci girkinta kona huta da gorinka".. murmushi Abdallah yayi alamar yaji dadi haka bilal ya juya da motarsa cikin gida yayi parking sauri sauri ya shiga ya shaidawa momynsa zaije gidan Abdallah tayi masa Allah ya kiyaye ya fito har Abdallah ya tada mota ya shiga suka kama hanya....
********
Kasa zama jiddah tayi saboda yadda take a parlorn a takure kamar mujiya babu kecewa wani uffan dukkansu sai hirarsu suke suna nan zaune afee ta fito da tray da flask da plate ta dire a gabansu "Anty jiddah da Anty ramly bismillah ga abincina...nice na dafashi da kaina don yau hannatu mai aikin mu batazo ba"
Murmushi jiddah tayi "Anya kin iya girki kuwa?kardai kim cika gishiri da maggi"dariya afee ta kwashe dashi ta zauna gefen jiddan a kasan carpet "bari ma kigani ni zanyi serving dinku"ta bude kular lafiyayyar jealouf ce da kayan lambu an yanka nama da hanta kanana kanana ciki sai kamshin curry da tyme takeyi tayi serving dinsu a plate,ta bude dayar kular ta zuba musu pepe meat din da tayi a gefen abincin tasa cokali "kuci abincin sai kuyi sallah ko?"gyadawa afee kai jiddah tayi tana son yarinyar sosai saboda ita kadaice take sonta ita kadai ce jininsu ya hadu,kallon agogo jiddah tayi har bakwai da rabi Abdallah be shigo ba gashi yace ta jirashi kila ma ya wuce gida ya mance da ita a nan,dan tsaki tayi afee ta dubeta "halan yaya Abdallah kike tsumayin zuwansa ko?"
Gyada mata kai tayi "kamar kinsani wallahi shi yace inzo nan injirasa idan ya tashi aiki zai biyo ya daukeni mutafi ,gashi Ramlah na kwasota muntaho yana bata mana lokaci"
Karaf ummah ta amshe zancen "zaman gida na ne bata lokaci?au dama in bece kizo ba bazakizo ba to saiki tattara ki tafi kisamesa a gidan naki yar matsiyata a gabana kike fadin haka saboda kin raina ni"
Kasa tauna abincun dake bakinta tayi jiddah saboda yadda takejin furucin ummah tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta,afee ce ta zumburo baki "haba ummah yanzun fisabilillahi me Anty jiddah tace,bata fahimceki ba badake take ba...da"
"Da ubanki take?yimun shiru shashashar banza da batasan meke mata ciwo ba munafuka tashi a wajen kafin in kwabdeki"tashi afee tayi ta nufi daki tana waigen jiddah da hawaye suka ciko fal a idonta...tsaye afee tayi a jikin labule da suka hada ido take girgiza mata kai tana daga mata hannu ta shige daki...
Bakin ciki ya gama rufe idon jiddah domin dik abinda akeyi a gaban ramlah akeyi hakan yasa ta dubi ramlah "muje ramly bazai biyo ba"kamar jira ramlah take ta mike,dakyar jiddah tace "ummah saida safe"tayi gaba don tasan ba amsawa zatayi ba,cike da ladabi ramlah ta durkusa "ummah saida safe sai anjima"itama tabi bayanta Tana jiyo ummah na fadin "Allah ya raka taki gona,kuma bari Abdallah yazo gidan nan wallahi koni ko shi a gidan nan zai fada min idan shi ya aikoki kimun rashin kunya"...
Tafe suke a mota ga hadari ya hadu bakin kirin hawaye ke sauka a fuskarta dakyar take ganin gabanta ga go slow ta inda ta yanko don ta biya ta sauke ramla "ke ko jiddah ni banga abun damuwa ba,idan halin wanan bakar dagar matar ne kinsaba,banga abun tashin hankali ba,kamata yayi kiciresu a rai ki cigaba da rayuwarki dangin miji dangin banza dangin wando, Don ma taga kina zuwa gidan su ne mtswww"tayi maganar cike da nuna takaici akan abinda akaiwa jiddan,tana satar kallon jiddah,zucuyarta cike da zumudin kada jiddah ta mance da zancen yiwa Abdallah maganar neman aiki..."akwai haushi ramlah ashr uwar mijina bata sona shi kuma mijina baida lokacina?Auren fari fa?a budurwa na auresa ba bazawara ba balle ace shi be samu yadda yakeso ba a jikina ga mahaifiyarsa na tsinemun... Taja mota aguje...
*******
Tunda suka shigo bilal yaji sanyi rashin samun jiddah a gida,"ai ni man na mance fa nace jiddah ta jirani gidan hajiya zan biya in daukota zumudin tahowa wajenka intaho dakai ku hadu gashi kai kazo bata nan,gashi inata trying number ta bata shiga ince ta taho gida"
Murmushin farin ciki bilal yayi "karka damu next time ai zamu hadu,yanzun haka hadari ne garin yayi bakin kirin ruwa baxai sameni a nan ba in kwana kai ka kwana rungume da amarya don nasan komi dare zaka dauko abarka...aure akwai dadi abokina kaga yadda ka kara canjawa"
Yar dariya Abdallah yayi wadda ta kara masa kyau domin shi baya wuce yayi murmushi "shegen gora nasan manufarka amma banji dadi ba wallahi mukara 5 minute ko zata shigo"mikewa Bilal yayi hade da kwasan wayoyinsa "gashi kasa na taho babu mota ya zamuyi kenan?"
"Tou muje in saukeka"
Girgiza kai bilal yayi "bani key kawai ai akwai motar da zaka fita aiki gobe ko?"
"Ehh ba matsala,"ya mika masa key suka fito tare...gari yayi bakin kirin ruwa kawai ya rage ya kece....
********
Tunda ta karyo kwanar gidan idonta a rufe yake saboda ruwa da ya soma sauka sam bata lura da gidtawar motar Abdallah da bilal ke ciki ba,shiko kasa yayi da glass kadan yana kallonta,fuskarta babu walwala yana iya hango manyan idanuwanta yanda sukayi jajir....meya sameta haka?gabansa ya fadi ko baa fada masa ba yasan bata cikin farin ciki...nan da nan hankakinsa ya tashi zucuyarsa ta dugunzuma yaji babu abinda keyi masa dadi,tuki yake hankalinsa na wajenta yanada bukatar ya kara ganinta inama yanada ikon kebewa da ita ya lallasheta?huro iska yayi daga bakinsa ruwa ke sauka kamar da bakin kwarya titi babu motoci sosai lumshe idonsa yayi ya kai hannunsa ya shafi sajensa,i cant believe na kamu da soyayyar matar abokina...sanan nasoma muamala da ita ta hanyar aminiyarta...anya babu wani kulli da Ramlah tasani da har ta hadamu?koda yake ramly batasan nasan jiddah matar aure bace ...ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da driving
Wucesa tayi ruwa har ya soma jikata kafin ta karasa side dinsu bayan tayi parking...tura kofar tayi ta gansa zaune gaban laptop tv na aiki ana ball,wani bakin ciki ne ya lullubeta kallo daya yayi mata ya maida kai ya cigaba da aiki hakan yasa zucuyarta kara yin zafi ta tube takalmanta ta shigo....tsaye tayi ko zaice wani abu beko kalleta ba yace "sorry na barki gidan hajiya ko?wallahi na mance dake can na tafi wajen Bilal muka taho nan dashi kuma sai muka tarar baki nan kuma donke yazo shine kuma ya tafi...naga kin jike jeki cire kayan ko?"wani kallo tayi masa ta girgiza kai ta nufi dakinta ko ta kansa bata bi ba .
Toilet ta fada tasa ruwa mai zafi tayi wanka ta dauro alwala ta fito ta zura jallabiya ta tada sallah,magriba da ishai ta hada sanan ta mike ta cire jallabiyar jikinta ta feshe jikinta da turare,ta ciro wata yar riga iyakarta gwiwa tasa light blue sharashara ana ganin jikinta ta fito parlorn, zuciyarta babu dadi ta zauna gefensa amma sai ta danne "Sweet"ta kira sunansa cikin wata irin siga,...be ko kalleta ba ya amsa "naam"bata damu da hakan ba don bata da lokacinsa mgnr aikin ramlah takeson masa sanan ta koma daki ta kunna datar ta,"dama nace zan rokeka wata alfarma ce nasan inada alfarma wajen mijina"
"Fad'i alfarmar da kikeso jiddah"yana cigaba da aikinsa,jimmm kadan tayi ta nisa "akan ramly ne kawata,dama tasha wuya tana neman aiki bata samuba kusan shekara daya kenan Abdallah dik inda takai takaddu bata samu shine nakeso ka taimake ta kasama mata gurbin wadda tabar aikin nan ta maaikatarku"...da sauri ya d'ago kai yana kallonta...shiru yayi yana kallon kwayar idonta yadda tayi suffar tausayi ...sai kawai ya cigaba da aikinsa kamar bazaice wani abu ba can ya nisa"owk kice ta kawo takaddun nata gobe"...wani farin ciki ne ya lullube jiddah ta rungumesa ta baya ta zura harshenta cikin kunnensa tana goga masa kirjinta a baya...shi kansa saida yaji wani yarrrr ya saki jiki sanan ta sakesa tana murmushi "i love you sweetheart"ta mike kawai ta nufi daki yabi hips dinta da kallo...jiddah macece dirarra mai kira ga nono da take dashi tana tafe komi nata na motsawa...shafa kansa yayi ya cigaba da aikinsa...
*******
Karfe daya na dare takai online suna chat da bilal wani irin nishadi takejin kanta...umarni yayi mata da yanason ganin fuskar kanwarsa kafin ya kwanta yanason kiranta video call... jimmm kadan tayi ta jingina tana tunanin yadda zatayi video call da namiji...massage tayiwa ramly " _kinsan me wai yayah yanason video call dani fa ni ya zan masa kuma har yau ban nuna masa ni matar aure bace_
Ai ramlah na ganin massage din jiddah cikin sauri tayi mata voice note..." _karki kuskura ki nuna masa kinada aure tunda be sani ba ai yayanki ne kuma na lura yana son farin cikinki wallahi ya burgeni yadda yake kulawa dake ina ma_ _Abdallah ne haka kuyi mana tinda yana can kan aikinsa?_
Da sauri ta koma chat din bilal da kanta tayi dialing numberta sa video call ta sa earphones a kunne....daukar wayar yayi yana kallon ta...murmushi take masa ta turo baki "yaya gani to"...lumshe ido yayi hade da jifanta da wani kallo ya kishingida...babu riga a jikinsa gashin jikinsa kwance a kirjinsa....ya gyara kwanciya...kallonsa takeyi gabanta na faduwa ta gyara kwanciya itama "ya bilal...kayi shiru"batasan yadda tayi maganar ba salon maganar ya saukar masa da kasala ya hango kirjinta da suka cicciko kasa dauke idonsa yayi akan nipples dinta da suka bayyana a rigar....
Motsin bude kofa yasa jiddah kife wayar a kan gado..kallonta yayi ya dauke kai ya nufi toilet ta bisa da harara ta tabe baki...
******
Murmushi kawai Ramlah takeyi lokacin da ta fiddo kaya daga akwatinta karfe biyu na dare ta kasa bacci saboda farin ciki gobe rana ce da bazata manta da itaba a rayuwarta...ranar da zata dira a maaikatarsu Abdallah takai masa takaddunta a matsayin maaikaciya a karkashinsa...tana daga cikin ranakun da zatayi marking unforgettable...lumshe ido tayi...yanzun ne zata daura dammarar samun farin cikinta..... Abdallah ba zata taba yarda tasan saina sha fama kafin ta samu kansa..amma dik runtsi saita mallakesa a matsayin miji zata soma fadawa ummahnta tasan bazata kware mata baya ba...amma bazata taba nunawa ummanta ita keson mijin aminiyar tata ba...
*****
Tana tashi da safe bayan ta idar da sallahr asuba ta hau online...massage dinsa ta tarar "shine kika kife wayarki naga duhu daga baya naji shiru ko my sis?...
My sis plsss come back inada magana dake...
Irin wadanan maganganun tagani ta lumshe ido gashi online sai kawai tayi masa massage "good morning big brooo miss ur bandariya"
"I cant lie i miss u too my sis...plsss ya zaai inganki?"
Shiru tayi tana tunani sai kawai ta yanke shawarar yazo gida kawai mana tinda Abdallah bayanan idan ma yazo ya tarar dashi ai zatace yayanta ne....
Bata tsaya jiran wani abu ba batare da wani tunani ba tayi masa massage da address din gidan ta tura masa ta kashe data ta nufu Kitchen don ta hadawa Abdallah breakfast...
A parlor ta tarar dashi da jallabiya yana ganinta ya lumshe ido yana makale da waya ya mika mata hannu ta taho ya rike hannun ganin yana waya tanada niyyar gaidasa ta dakata "ummah dan allah kiyi hakuri..."yadda yayi maganar cike da damuwa ta dubesa tana jiyo tashin muryar ummah tana fada a waya....da asubar nan...hmmm sai kawai ta saki hannunsa ta nufi kitchen....
*******
Bilal kuwa yana ganin massage dinta da address din data tura masa ya zauna zaune yana sauke numfashi gumi ke karyo masa....tabbas ko baa fada ba jiddah ta fara sabawa dashi cikin kwana biyu...me hakan ke nufi?tana son sa kenan?......
**Toh fa yanzun zaa soma wasa...ga ramly ga Abdallah...ga bilal ga jiddah...*
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:23 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*6*
Tsaye take a gaban gas a kitchen tana kwashe dankali da take soyawa ya tsaya a jikin kofar kitchen din ya harde hannuwansa,kallom jiddah yakeyi cike da so da kauna,ina son matata amma ta kasa gane hakan banida lokacin tsayawa kulawa da wata mace da sunan soyayya a yanzun banida abinda yafi aikina muhimmanci...kare mata kallo yakeyi yana bin rigar jikinta da kallo tsigar jikinsa ke tashi amma ya kauda wani abu a ransa yayi gyaran murya,sarai ta gansa tsaye a bayanta bata juya ba saida yayi gyaran murya sanan tayi farrr da manyan idonta ta zuba masa su tana murmushi ta juyar da kai tana kokarin zuba plantain a mai "ya dai sweet....ya akayi har kayi shirin aikin ne?ina kokarin in soya maka mutuniyarka ne plantain"ta juyo ta dubesa fuskarsa kamar koda yaushe dan d'age gira yayi "owk kiyi sauri ina so in shiga office da wuri don ina son ganin director akan maganar aikin Ramlah da kikayi requesting"....murmushin jin dadi tayi ta juyo tana kallonsa "yanzun zaa karasa kaga ya ma soyu muje parlorn gani nan zuwa"...shiru yayi yana kallom yadda take kwasar plantain din sai can ya juya tamkar Wanda ya tuna wani abu...
Wata flask ta dakko daban ta zuba cheeps din da plantain ta rufe ta dora a kan friedge sanan ta ciro dinner set ta zuba masa nasa ta gyara plate din da kyau ta dauko flask dinta tayo parlor...yana zaune ya tasa jakarsa a gaba da suit dinsa a hannun kujera ta dire plate din abincun ta koma ta dawo da suger da madara da bounvita ta dire...har ta kusa daki ta juyo "what next?"ta tambayesa tana daga gira,tabe baki yayi wato bazata zauna kenan ba oho may be hakan takeso ya kada kai "nothing"ta shige daki abinta saida ta bace sanan ya janyo plate din ya soma breakfast yaba cin abinci....
Toilet ta fada tayo wanka ta fito da karamin towel a hannunta tana goge kanta da ta wanke,shigowa dakin yayi ya tsaya gaban madubin da take tsaye ya tsaya ta bayanta Yana kallonta ta cikin madubi,itama shi take kallo,ba karamin kyau yayi mata ba Abdallahn ta akwai kyau da kwarjini lips dinsa ta kalla sirara kamar na mace ta lumshe ido,ganin tana kallonsa yasa ya dage mata gira...tsaye yayi da necktie dinsa da be gyara ba yana jiran ta gyara masa don jiya yaji dadin yadda ta gyara masa ita ko kallon sa takeyi tanajin wani irin zafi cikin ranta kanada miji ka tsaya gabansa babu Riga. Sai towel amma ko yar soyayyar nan ya kasa Mata,yaushe rabon da ya kusance ta?kusan sati biyu kenan rabon daya kusance ta saidai kullum yana kan computer yana aiki tamkar shiya kero ta,idonta ne suka cicciko,shiko dire jakar yayi ya shiga gyara tie din nasa ganin haka yasa ta juyo da niyyar gyara masa ta ruko rigarsa sai towel dinta ya zame kirjinta ya bayyana....kure nononta yayi da ido tamkar meson gano wani abu amma sai kawai ya juyar da kai "zan tafi baby sai na dawo"tsaidashi tayi da sauri tace "sweet....i need u"
"What"yayi maganar yana kallonta,batare da ya fahimci me take nufi ba,...sunkuyar da kai tayi "ina jin shaawar mijina inason kasancewa dashi inada bukatar d'umin mijina"...hawaye ya zubo mata,mamaki ne ya kashesa don tana shaawarsa saitayi kuka?mtswww yaja dan tsaki "idan na dawo,yanzun ina sauri zani aiki kinsani"gyada masa kai tayi tasa hannu tana share hawaye "Allah ya tsare ya kiyaye hanya"
"Ameeen"yace yana kokarin fita daga bedroom din rataye da jakarsa....
Zama tayi akan kujera tana kallon kanta a madubi hawaye ne suka shiga zubowa a idanuwanta....wace irin masifa ce wanan miji be damu dakai ba amma Yana sonka?soyayya gabaki dayanta tana tafiya da kulawa ne...amma shi samm be kulawa da ita balle ya mata wata soyayya,hawayenta suka karu tunawa da tayi yanzun saboda abinda yake mata yasa ta kulla alaka da namiji batare da ta sanar masa ita matar aure bace a matsayin yaya da kanwa...sosai yake bata attention wani lokacu idan baya online saitaji tamkar ta kirasa a waya....tana cikin wanan tunanin wayarta kirar iphonex ta soma ringing akan jikin madubi tayi saurin daukar wayar tana kallon mai kiran nata... Mahaifiyarta ce da sauri ta gyara fuskarta ta dauki wayar hade da sallama....
********
Tun karfe bakwai da rabi Ramlah take zaune a reception ta wajen office din Abdallah,fanka da Ac kadai ke aiki sai tv dake makale a sama a jikin bango...atamfa ce a jikinta wadda suka dinka iri daya ita da jiddah mai ruwan ganye,ita skrt da riga tayi ta sha daurin dankwali tayi kyau matuka gyalenma a saman kai tasa fuskarta sai sheki takeyi....tun shigowarta maaikata ke kaiwa da komowa suna mamakin wacece wanan kuma gata kyakkyawar gaske ajin farko...
Wani cleaner ne yana mopping wani guy da yake sanye da suit ya shigo ya taba sa"waccen fa?kai amma ta hadu fa tanada kyau"..."kai nima naga hakan amma kasan dik haduwarta batakai matar oga Abdallah ba da mukaje wajen partyn bikinsu?hmmm "
Karar takun Abdallah yasa suka bar maganar kowa yayi ta kansa....tana zaune ta jingina ta lumshe ido jin takun shigowa reception din yasa ta shiga bude idonta a hankali ta saukesu akansa....fuskarsa murtuk babu annuri...lumshe ido tayi ta shaki kamshin turarwnsa,gyara zama tayi tana dan murmushi ta sunkuyar da kanta....ga mamakinta bude office yayi ya shige masinjansa ya bisa yi yayi tamkar besanta ba...sosai taji wani iri amma ta danne ta sunkuyar da kai tana wasa da gyalenta....
Bayan Abdallah ya zauna yana kokarin kunna computer masinjansa yadan rusuna "ranka ya dade sir akwai wadda ke zaune a reception tana jiranka"...jimmm Abdallah yayi wacece kuma ke jirana?...kamar yasan me yake tunani ya Kara risinawa "tun safe tazo sunanta Ramlah tace mun"
Ajiyar zuciya ya sauke au ashe yazo "owk shigo da ita"yajuya ya fice...
Alamar ta taho yayi mata suka shiga office din farko da ta tarar ta hangi wata kofa ciki wanan computers ne da abubuwa da files a wajen sai suka karasa inda ta hangi kofa ya bude mata kofar ta shiga shima ya shiga "ranka ya dade gata nan"
Beko kalli inda yake ba yace "owk you can go"masinjan ya juya ya rufo kofar...tana nan tsaye tayi poster tana kallonsa sai aikinsa take alamar akwai abinda yake shigarwa...kallonsa takeyi zucuyarta na sak'a mata abubuwa da dama cikin zuciyarta...wutar sonsa ke ruruwa a zuciyarta,numfashinta da bugun zuciyarta da soyayyar Abdallah suke tafiya...kusan minti goma sanan ta nuna mata seat "ki zauna"yayi mata umarni...ba tace komi ba ta zauna ..idonta sun kankance saboda yadda takejin wani sauyin yanayi a tattare da ita bugun zuciyarta kansa ya sauya salo...lumshe ido tayi taja numfashi,katseta yayi da "already inada takaddunki,shigowata din nan nasamu director ne gaba daya akan maganarki nafada masa matata tayi requesting a daukeki aiki ta rokeni na amince mata,tou...dik ba wanan ba last last ya amince"wani dadi ne ya lullube ramlah kamar ta rungumesa tayi masa kiss..ya cigaba "d first office da kuka wuto bayan reception,akwai computers ciki da kayan printing da sauransu da files office din former secretary ce to tabar aiki nan zaki zauna....tou kome zakiyi u should ask kafin kiyi idan akwai ayyuka zan turo miki kiyi su sanan idan nayi baki ke zaki musu iso"dik maganar da yakeyi ko dago idonsa ya kalleta beyi ba sai daddana computer yake cike da kwarewa fuskarsa babu fara'a...bata damu ba sunkuyar da kai tayi ta sauke ajiyar zuciya "Insha allahu dik abinda akasani shi zanyi your wish is my command"tayi maganar cikin siririyar murya,gyada kai yayi "good"ya janyo drawer ya ciro wata yar jaka ya ciro flash ya mika mata "take dis yanzun zanyi miki sending abu kiyi printing kiyi filing dinsu"ya maida kai....a sanyaye ta mike tankar kada tabar office din ta rataya jaka ta nufi kofa,ta bude kofar ta tsaya tana kallonsa ganin zai dago kai yasa ta fice ta rufo kofar....
Telephone ya janyo ya shiga danna numbobi ya kara a kunnensa....
*******
Tun shigowar tex dinsa na gashinan zuwa gabanta ke faduwa kaiwa da komowa ta shigayi cikin dakin gabaki daya batada sukuni hankalinta a tashe yake,ramlah ce ta fado mata da sauri ta cire pin din wayar tayi dialing numberta...
Dago wayar ramlah tayi tana kallo,lumshe ido tayi ta danna recieve ta kara a kunne...cikin rawar murya jiddah ta soma magana "ramly...ina cikin tsananin damuwa"
Gyara zama tayi"menene meyake faruwa dake jiddah?"tana maganar tana kallon kofar office din Abdallah..."hmmm yaayah ne yakeso tazo inda nake ya gaida ni kuma na rigada nayi masa kwatancen gida na,nashiga uku ramly gidan aurena ne"
"Sai me jiddah idan gidan aurenki ne?mijinki ya damu dake ne?hmmmm ai kibari kawai yazo kuyi hirarku ko kya samu sassauci cikin zuciyarki kuma akwai labarai da yawa don yanzun Haka an amsheni har anbani office nice sakatariyar mijinki ma"
Haka kawai gaban jiddah ya fadi, sakatariyar mijina?ta maimaita a zuciyarta haka kawai taji wani abu cakk ya caki kirjinta...akwai yarda sosai a tsakaninta da ramly amma tanajin kishin wata mace ta kusanci mijinta koda rabiah ce teemah ce kanwarta kuwa,...kallon wayar ramly tayi jin shirun jiddah "hello besty ina aiki bari zan kira back"kawai ta kashe wayar ganin Abdallah ya shigo daga kofar baya yana kallonta..murmyshi tayi masa ya daga mata hannu yayi ciki tabi bayansa da kallo ta jingina...saida taga shigarsa sanan ta shiga sake saken yadda zata soma mission dinta....
********
A kofar gate yayi parking bilal yana sanye da shirt da wando ya gyara gashinsa sosai yayi kyau sai kamshi yakeyi... nocking gate yayi mai gadi ya taho da sauri ya bude gate din...juya baya bilal yayi yana kokarin kiran wayarta....tana ganin call dinsa ta goge kwallar dake makale a idonta, zuciyarta babu dadi sammmm batajin dadin muamalar da takeyi dashi amma bata da wani sukuni da farin ciki daya wuce kasancewa dashi...slipas tasako ta fito sanye da rigar atamfa doguwa dinkin play gown tadan yafa dankwalin..mai gadi na ganinta ya dan rusuna "barka da fitowa"
Hannu ta daga masa ta leko "ya bilal..."ta kira sunansa yana juyowa ya aika mata da wani kallo,wani yarree taji a jikinta ta juya kawai yabi bayanta hannunsa rike da waya yana daddanawa...kallo mai gadi yabi su dashi,tabbas wanan abokin Abdallah ne da sukazo jiya Allah sarki koda yake besamu me dakin ba jiya...komawa yayi dakinsa ya rufe kofa bayan ya rufe gate din...
Waje ta nuna masa "bismillah"tace Tana yake gabanta na cigaba da faduwa ,kashe mata ido yayi ya tsaya yana karantar yanayin nata "ya naganki haka kanwis sam bakida walwala,menene ko baki murna da zuwa na ba?"... girgiza kai tayi idonta sukayi kwalkwal cike da shagwaba tace "umm umm nidai babu"lumshe ido yayi ya zauna kodai abokin nasa ya mata wani abu ne?tausayinta ya kamashi da ta nufi kitchen yabi bayanta da kallo...
*******
Tura kofar tayi ta tsaya batare da ta rufe ba ta langabar da kai tana kallonsa ,yana jin shigowarta ya dago kai ganin itace ya juya ya dauko wata takadda yana dubawa zuwa gidan ummah ya fado masa,saida yaji faduwar gaba ya dake "yadai meyafaru kika shigo?".. girgiza kai tayi beko kalleta ba "umm umm bakomi dama na gama wancen aikin ne yasa nazo idan akwai wani ka kawo in tayaka mana... banason zama hkn batare da yin wani abuba ko a gida"cike da kissa tayi maganar..."babu aiki zaki iya tafiya"
Shiru tayi tana kallonsa batare da ta motsa ba,dagowa yayi suka hada ido ta lumshe masa ido ta juya ta rufo kofar.....
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:24 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*7*
Bilal ko parlon ya shiga bi da kallo zuciyarsa nayi masa d'ar d'ar...tabbas nan gidan amininsa ne da yazo jiya kuma ya tabbata jiddah matar Abdallah amininsa ce suke tarayya, yanayin ta ya nunar masa akwai wani abu dayake damunta,yarinya ce tausayi take bashi sosai kamar jiddah kamata yayi ace tasamu miji meji da ita da soyayya da kulawa,samun mace zukekiya a wanan zamanin kamar jiddah sai an tona sanan a kamalarta ya nuna cewar zatayi hakuri... gashi cikin yan kwanaki ya saba da ita yana matukar sonta soyayyarta a jinin jikinsa take yawo matar amininsa tun suna yara,....tunani yakeyi har ta iso da flask ta ajiye a gabansa da plate da lemo ta dire masa a gaba ta zauna ta zuba tagumi tana kallonsa ko kifta ido batayi,..ayyanawa take ina ma Abdallah irin halin bilal garesa?da bata fada son wani ba alhalin tana da miji dikda bata gama gasgata soyayyar da takeji tana neman kamuwa da ita ba ta yaya bilal...a jikinsa yaji tamkar ana kallonsa hkn yasa ya dago manyan idonsa ya dora akanta amma bata sani ba,shiru yayi na dan wani lokaci kafin ya nisa "my lil princess meyake damunki naganki tamkar kina cikin damuwa menene akwai wani abu da kike bukata ne?...ina su ummahnki?naga gidan kamar ke kadai"...ya jero mata wadanan tambayoyin a tare kafin ya tsareta da ido yana so yasan amsar da zata basa,girgiza kai tayi ta sunkuyar da kai tana kokarin boye kwallar dake shirin kubuce mata "ummah na basa nan sunyi tafiya sun tafi dubai sai wani lokaci zasu dawo"ta sharo masa karya...yadda tayi maganar muryarta na rawa yasa ya danyi murmushin gefen fuska yasan karya ta sharo masa,dago ido tayi ta kallesa ko ya gano karya tayi masa sarai ya lura da hakan sai kawai ya kauda zarginta da bude flask din dake gabansa,tururin dankali da kamshin plantain ya gauraye parlorn,jan numfashi yayi ya sauke yana kallonta yana murmushi "waya sanar dake cewar banyi breakfast ba na fito?"ya kashe mata ido,girgiza kai tayi tanajin wani shock a jikinta....wani irin yammmm takeji saboda matsananciyar shaawar dake addabarta a wanan lokacin..."ko baa fadamun ba nasan yaayah na dan gayu ne ai nasan baya breakfast da wuri"...ido ya zura mata yadda bakinta ke rawa tamkar mai zazzabi,hannu yasa ya dauki dankalin guda daya ya kai bakinta...ido ta sa masa batare da ta amsa ba bugun zuciyarta ya tsananta nan da nan fuskarsa ta juye mata zuwa fuskar mijinta Abdallah...lumshe ido tayi ta bude sai taga bilal ne gabanta wasu zafafan hawaye suka zubo mata...kafeta yayi da ido yanajin tausayinta na ratsa zuciyarsa..ya tabbatar Abdallah ne ya bata mata rai in haka ne meyasa shi bazai lallasheta ba yadda zata soshi ta shaku da soyayyarsa har bazata iya rabuwa dashi ba?. hannunsa yasa ya dangwalo hawayenta yakai bakinsa ya lashe,idanuwanta sunyi jajir take kallonsa ya mika mata dankalin "oya let's eat together"yayi maganar da tsare gida ..ga mamakinsa yaga ta buda baki yasa mata ta shiga taunawa a hankali ...shima ya dako yasa a bakinsa a haka yake bata yana ci har suka cinye a tare dik cikin damuwa jiddah take,dik motsinta a idonsa takeyi,remote ta dauka ta canja tashar zuwa zee world ana wani film na soyayya...flask din ta dauka ta mike cikin tafiyarta mai daukan hankali tafiya take mazaunanta suna motsawa...hannu yasa ya shafa kansa ya hura iska...idanuwansa sunyi jajir saboda yadda yakejin kaunarta na fuzgarsa...
Tana tsaye gaban sink tana kokarin wanke kwanuka hawaye kawai ke zuba a idanuwanta....sammm zuciyarta batayi mata dadi na kawo namiji da tayi gidan aurenta amma batada option,she needs to be happy always,babu farin ciki a gidan Abdallah ina ma bashi ta aura ba?da bata nemawa kanta zunubi ba gashi kiri kiri zuciyarta ta kasa mata adalci ta kamu da soyayyar wanin mijinta... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun....hawaye ke gudu a fuskarta...tsaye yayi jinta shiru yasa ya biyo ta...har ya karaso dab da ita batasani ba saida yakai hannunsa fuskarta yana share mata hawaye "kina boyemun damuwarki my lil princess...na tabbatar kinada damuwa yasa na shigo rayuwarki don in zame miki haske me haska duhun da kike ciki,meyasa kike kuka?digar hawayenki tamkar digar dalma nakeji a cikin zuciyata...inajin radadi da zugi idan har naganki cikin wanan halin...haba jiddah"yayi maganar a sanyaye ..gabanta kw faduwa cikin kitchen ya biyota?kallonsa takeyi idonta jajir ta girgiza kai "muje parlorn kaji?"cikin dasasshiyar murya tayi maganar jikinta na karkarwa...mika hannu yayi ya ruko hannunta ha fuzgota ta fada jikinsa ya kankameta....rawa jikinta ya somayi wani irin abu ke fuzgarta idan ta kara minti biyar a kirjinsa zata iya suma,saidai rukon da yayi mata bazata iya fuzgewa ba...kallon yadda take hawaye yake nan da nan idonsa suka cicciko da hawaye "kinaso inyi hawaye ko?bazan iya jure ganin kyakkyawa kamarki cikin wanan halin ba"fashe masa tayi da kuka saboda yadda takeji a jikinta shaawarta na kara karuwa musamman tsintar kanta da tayi a kirjin wani namiji ba mijinta ba....ta yaya zata cigaba da aikata hakan da aurenta?kukanta ya karo....pink lips dinta yake kallo da suke attracting dinsa ji yake tamkar ya hadesu ya tsotse su,soyayyar matar abokinsa kullim karuwa take cikin zuciyarsa...ina ma ace shine ya mallaketa?da taga soyayya...ganin tana kici kicin kwacewa yasa ya hura mata iska a fuska "is ok zan sakeki amma sai kinyimun alkawari hawayen nan zasu k'afe kuma bazasu sake zuba ba"...kallonsa take yadda yaka mata magana cikin sigar lallashi ina ma ace mijinta ne yake mata wanan tarairayar? runtse ido tayi ta budesu ta kwantar da kai a kafadarsa....mamaki ne ya lullubesa yasa hannunsa ta baya yana shafa bayanta a hankali wani irin abu takeji kamar tafiyar tsutsa da tayi saurin janye jikinta tana murmushi,shima murmushin yakeyi ya dage mata gira..."muyi wanke wanken a tare ko?"daga masa kai tayi alamar eh sai kawai ya nannade hannun shirt dinsa ya karaso tabisa da kallo sosan wanke wanken ya dauka yana yi ta tsaya gefensa "kawo inyi banaso kasha wahala"
"Nafiki rashin son ki wahala...da zan bude miki zuciyata kiga yadda kike ciki?da ko kuda bazaki yarda zan bari ya tabaki ba my lilly"...idonta sukayi kwalkwal tana kallonsa ya gama wake kwanukan ya dubeta "sai me?har gyaran gado zanyi miki"...batasan lokacin da ta fashe da dariya ba tayi gaba yana biye da ita yana kallom hips dinta yadda suke motsawa.... mazaunin sa ya zauna yana fuskantar ta suna kallon juna...wani irin shauki ne ke lullube dasu biyun addua kawai jiddah takeyi akan ta rinjayi zuciyarta idan ba haka ba zatayi abun kunya.....
Hira ya dauko mata ta daban ta mance da wani Abdallah,tare sukayi lunch da rana ta dumama samosa da meatpie dake fridge suka sha da lemo...dik inda tayi yana biye da ita har laasar...kallom lokaci yayi any time Abdallah zai iya shigowa ya kamata in bar gidan nan dikda zanyi kewarta ya furta cikin zuciyarsa,itama kallonsa take fargabar halin da zata shiga takeyi matukar ya tafi to tunani zata komayi...katse mata tunani yayi "my lill..."ta dago kai da sauri "zan tafi inaso zan kai momy dubiya asibiti karfe biyar gashi yanzun karfe hudu"jinjina masa kai tayi ta sunkuyar da kai,mikewa tsaye yayi a gabanta kanta a kasa tana kokarin hawaye "am going stand up and give me last hug please dont say no"yayi maganar a sanyaye yana duban yanayinta...kusan second arbain sanan ta mike a slow ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai...kallonta yakeyi tausayinta na kara shigarsa "come close ..."bata tsaya wani tunani ba ta fada kirjinsa ya rungumeta,wani irin yakeji saukar breast dinta a kirjinsa,ya kankameta yana furzar da iska...jikinta ne ya mutu bazata iya tabuka komiba ya dago kanta "am gonna miss you lill"yayi maganat murya a dashe cikin wani yanayi...wani abu ne ya tsaya masa a zuciya ya sakar mata light kiss a lips sanan ya saketa beko kalleta ba yayi hanyar fita...ko waigenta beyi ba ya fice....hawaye suke gudu a fuskarta ta fada kan kujera ta fashe da kuka Abdallah ya cuceni haka akeji a soyayya idan ana tare da wani?ya hayyu ya kayyum...ya rabbbb zuciyarta ke harbawa...inama mijinta nayi mata irin hakan?da be jefata cikin wanan halin ba banason kasancewa da kowa saikai mijina...ta furta a hankali tana hawaye...
********
Hannunsa rataye da jakarsa ya fito a office din suit dinsa na kafadarsa fuskarsa a daure ya fito,sakin baki tayi tana kallonsa har ya karaso table dinta "zaki iya tafiya lokacin tashi yayi"yana fadin haka ta kalli agogo karfe shida saura minti biyar...yayi gaba abinsa,wata kasala ce ta saukar mata ta sakar masa murmushi daga baya,nan da nan ta mike ta zari jakarta ta ciro hoda ta shafa da man baki,kallon gefenta tayi wani dan box ne a jikin bango da numbobin waya jiki tana dubawa a sama taga number Abdallah ta mtn an rubuta sir Abdallah MD...murmushin jin Dadi tayi ta dauka...wasu takaddu da take ciccikewa ta diba da bata gama ba tasa a yar jakar kwali mai tambarin tutar Nigeria ta fito tana tafe kwass kwass cike da daukar hankali take taku dik inda ta gifta kallo komawa kanta yake...
Har ya shiga motarsa ya hangeta ta jikin madubin motarsa tana tahowa ..ya furta banason daukan yarinyar nan amma da kunya ace ta sameni ban dauketa ba koba komi aminiyar matata abar sona ce...take motar yayi yana kallon yadda take taku,mtsww yaja tsaki kamar me tausayin kasa ya furta a fili.....ta lura da jiranta yake amma saboda kirsa irinta Ramlah canja hanya tayi da nufin zuwa gate yayi horn ko waige batayi ba ..da karfi mai gadi ya furta "ranki ya dade,oga dake yake fa"
Dan farr tayi da ido "au dani yake?ai bansani ba"tayi maganar tana juyawa da nufin zuwa wajensa,tsaye tayi a jikin motar "ranka ya dade ance kana magana ko kayi mantuwa ne?"tayi maganar da langabar da kai,ko kallonta beyi ba ya maida kansa gefe sanan yace "shigo insaukeki koda a hanya ne saiki karasa don zan biya gidan ummah"
Bude motar tayi ta shiga ta zauna,yabi jakar data zuba takaddu da kallo bece komiba ya tada motar,murmushi tayi "nasan zakace na fiye zaqewa ka ganni da takaddun office zani gida yau daya da fara zuwana...hmmm inaso in zama busy a gida inyi aikin office abinda zai fussheni kenan"tayi maganar tana satar kallonsa,murmushi yayi "ohhh ba laifi"ya karya kwanar fita gate ya hau titi sanan ya mika hannu ya janyo wayarsa yayi dialing number jiddah yasa a speaker...jin yayi dialing call ta juya ta dubi screen din wayar PUREHEART taga an rubuta da manyan baki...hmmm kawai tayi a ranta tanajin wani kishi sam bataji dadi ba wato kiranta zaiyi a gabanta?ikon Allah jiddah taki picking call har dau biyu,a fili Ramlah taja ajiyar zuciya ya dubeta ya maida kai titi be kawo komi ba,...har suka iso kan kwanar da zai karya ya nufi unguwarsu ummah..parking yayi gefen titi "inaga ki sauka a nan saiki karasa gida ko?"yace babu walwala...kallonsa tayi "kamar wani abu na damunka ko?menene na ganka cikin wanan yanayin ranka ya dade ko gajiyar office ne?koda yake kasha aiki...hope idan kaje gida zaka huta nasan kawata zata tarairayeka"tayi maganar tana bude motar,wani haushinta ne ya lullubesa ko ina ruwanta oho...hmmm kawarki meta iya banda fitina?ya furta a ransa ta rufo masa kofar kobi ta kanta beyi ba yaja motar ya barta tsaye...bin motar tayi da kallo daidai nan me napep ya tsaya gabanta "tafiya ne hajiya?"batace komi ba ta shiga yaja ta saida sukayi tafiya mai nisa sanan ya tambayeta inda zasuje ya nufi gida da ita.... Allah allah take ta isa gida don taji wainar da jiddah suka Toya da bilal Allah yasa dai burinta ya cika...
*******
Kannensa ne cike da parlorn suna kallo ya shigo nan da nan kowa ya shiga taitayinsa "sannu da zuwa ya Abdallah"rumaisa ta gaishesa ya daga mata hannu be lura da attachment din da ta kara a kanta ba afee tace "barka da zuwa ya Abdallah a kawo ruwa ko lemo?"ta tsaya gabansa tana murmushi,murmushin ya sakar mata Afee akwai hankali"kawo ruwa afeen ummah"Yana kokarin zama rumaisa ta mike ya kai idonsa gashinta da sauri ya daka mata tsawa "ke rumaisa meye wanan akanki?sai kace wata ashawo?"turo baki tayi tana kallon ummah,da tayi magana mana "yayah bakomi fa kitso ne"
"Uban kitson,karin gashi kikaje akayi miki?abinda annabi ya fada a hadisi Allah ya tsinewa me karin gashi da Wanda aka karawa da mai karin kanshi shine kikaje kikayi tsinuwar Allah ta tabbata akanki kenan ko?"tura baki tayi tabar parlorn tana Harare harare "wato ubaidu yana kallonki kikayi ko?"...afee ce ta shigo parlorn hannunta dauke da dan tray da ta doro gorar swan da lemo ta dire gabansa,ya bi ta da kallo tasha kwalliya abinta ko kadan ba irinsu daya da rumaisa ba wallahi fatansa Allah yasa kada ta canja,zuba masa tayi ta mika masa ya amsa ya kurba,sanan ya dan rusuna "ummah ina yini"wani kallo tayi masa "na dauka ai bazaka gaisheni bane sarkin sani wanda yafi kowa sanin daidai?...koda yake matarka ma saida kawarta ta ankarar da ita ta gaisheni sanan ta gaisheni"..shiru yayi ya sunkuyar da kai batare da yace komiba,lura yayi da ummah fada takeji "nasan abinda ya kawoka kiranka da nace inayi....to ba wani abu bane yasa na kiraka illa kaimun iyaka da matarka don ni ba saarta bace ba saar uwarta bace bare ubanta dangin tsiya masu kudin lukudi"
"Ummah...mai jiddah kuma tayi?"
"Waini jiddah zatazo gida na ta ke cewa kawarta da sukazo tare da tasan bata lokaci zatayi a nan da batazoba gashi bakazo ka sameta ba,yarinyar nan kawarta ce ke nusar da ita ta amshi plate a hannuna sanan tazo zata amsa saboda tsabar raini da rashin tarbiyya to ta kiyayeni kada ta kuma zuwa gida na tunda banida mutunci a idanunta niban haifeta ba inda uwarta ce bazatayi mata haka ba ai,koda yake kaine ka bada fuska ai"shiru tayi tana kallonsa cike da masifa,
"Kiyi hakuri ummah...insha Allahu zatazo ta baki hakuri bazata kuma ba kiyi hakuri ummah"
Kauda maganar tayi da "ya maganar zuwan su rumaisa saudiyya?"tayi maganar tana kallom isonsa,sunkuyar da kai yayi "tana nan"
"Tou yawwa dama yar hajiya talatu ta haihu jibi suna ya dace kayi wani abu talatu kanwata yarta halima"...
*******
Ta fito daga kitchen hannunta dauke babban tray ta jera kulolin abinci da jug ta hado juice din mangwaro ta dire jiyo rurin wayar ta a bedroom da sauri ta karasa ta dauki wayar ganin mai kiran "manya ramly ansamu office an mance dani daga cewa zankiraki baki kuma kirana ba ai nayi fushi"ta turo baki kamar ramlah na ganinta,
Ramlah kuwa yatsina baki tayi "sorry kawalli ya ake ciki?ya mutumin naki?"cike da zumudi jiddah tace "ya tafi ya barni da kewarsa ramly...nikadai nasan me nakeji...ashe haka sabo da kulawa yake da dadi?hmmm yau na dandana abinda ban tabajinsa ba,konaji ma ba irin wanan tarairayar ba"...
Mikewa ramlah tayi ta zauna cike da kosawa,meya faru haka jiddah ke wanan furucin me sukayi da bilal?ta tambayi kanta sanan ta hadiye miyau cike da murna "meya faru labarta mun kawalli"
"Hmmm... kedai bari"nan jiddah ta kwashe abinda ya faru tsakaninsu ta shiga labartawa Ramlah da take ta faman murmushi...motsin shigowar Abdallah yasa ta ce"bari zan kiraki Abdallah ya shigo"cikin rada tayi maganar ta dire wayar ta jefa kan gado ta fito....
Kicibis sukayi "barka da shigowa sweetttt ka dawo?"kallonta yayi ya danyi murmushi"nadawo"ya wuceta ya nufi dakinsa...tabe baki tayi tabi bayansa tana bin sa da kallo cikin dakinsa juyowa yayi zuciyarsa batayi masa dadi ba da abinda ummah ta sheda masa jiddah tayi....dikda yasan ummah ta tsaneta amma yasan jiddah tanada wani irin hali na wawtar magana "inaso ki shirya kije kibawa ummah hakurin abinda kikayi mata don naje naji"yayi maganar babu yabo ba fallasa yana kokarin cire safar kafarsa,takaici ne ya lullubeta wato an hadota dashi shi kuma ya amince ko?harda cewa taje ta bata hakuri ranta ya kara baci,ficewa tayi a dakin ta bugo kofa yabi ta da kallo tana fadawa dakinta ta fada kan gado ta fashe da kuka...lallai ma Abdallah wato yarda yayi da maganar mahaifiyarsa bayan yasan komi shine zai shigo yana mata fuzga haka ko?yama gama raina mata wayau lallai goro nasa zawo,au yazo yaci mata ne akan mahaifiyarsa?tou wallahi be isa ba gobe wajen ummahnta zataje itama saita fada musu abinda yakeyi mata a raba auren ita tagaji....ta fashe da kuka....
******
"Ya bilal wai tunda ka dawo na ganka a haka kana murmushi kai kadai halan budurwa kayi kuka daidaita"
Harara ya watsawa me maganar "ni saan wasanki ne wai?mtswwww fitar mun a daki kinzo zakimun iyayi"tura bakinta tayi yabi bayanta da harara...massage ne ya shigo wayarsa yayi saurin dubawa jiddah ce.... *please zamu iya haduwa a wani waje?i need to be happy gobe zan fita inason kasancewa dakai yayaah....* Ya karanta massage din yafi sau goma..murmushi yayi ya mata reply "why not"...
******"
Idanuwanta sun kumbura ta fito ta tarar dashi parlor,bata karasa shigowa ba wayarsa tayi kara...kallon wayar yayi yaga bakuwar number saida ta kusa tsinkewa sanan ya dauka amma idonsa na kan jiddah ,sam bayason kukanta da tasan yadda yakeji idan tana kuka da ta rinka shanye kuka sam bayason damuwarta amma ita aikinta kenan fitina,kallon table din tayi abincu yakeci amma takaddu ne da stamp agabansa alamar aiki yake..."hello ya furta"
Ramlah ta lumshe ido "hello ranka ya dade...na kira ne inyi maka godiya a bisa kokarin da kaimu. Mahaifiyata tace in gode maka yasu ummah?hope kasamesu lafiya ya gajiyar dawainiya dani? Allah ya saka maka da alheri"...tunda ta soma maganar yake kallon jiddah da ta kafesa da ido jiyo sautin muryar mace ke kiransa..."ki godewa matata....nagode nima"ya datse wayar...
Tambayar kanta ta shigayi wacece ta kirasa har yake cewa ta godewa matarsa?wani azababben kishi ne ya lullube jiddah ta zabura ta karaso gabansa"wacece ta kiraka daddaren nan?au mata ka koma nema yasa baka da lokacina?"ta fashe da kuka...jan numfashi yayi "kawarki ce Ramlah...take godiya"
Maimaita sunan tayi Ramlah?ta tambayi kanta ya akai Ramlah har ta amshi numbersa daga soma aiki take kiransa daddare?hmmmm wani it shi ya taso mata wallahi ko kannensa kishinsu take balle kawarta...tanason Ramlah zata taka mata burki da kiran mijinta daddare...kai koma da yaushe bazai yuwu ba.......
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:25 AM] Mis Slimzy😍🥰: 💥 *💥AUREN F'ARI....* 💥💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MU'AZU AMIR RUMA...*
*8*
Wani irin kallo take masa mai cike da ma'anoni kala kala,nan da nan cikin mintuna da basu wuce uku ba idanuwanta suka kankance sukai jajir yana hango yadda bugun zuciyarta keyi a kirjinta...shima wani irin kallo yakeyi mata tamkar zai hadiyeta yana son matarsa anma samm batasan yadda zata zauna dashi ba batasan yadda zata koya masa abinda takeso ba shi be saba da hakan ba amma ta kasa ganewa fitinar jiddah tayi yawa...ji yake tamkar ya rungumeta ya samu sassaucin soyayyarta dake ruruwa a zuciyarsa amma bashida yadda zaiyi....kallon da yake mata yasa ranta ya kara baci kallon agogo tayi ta maida kai ta dauki wayarta ta mike cikin fushi ta nufi dakinta fuuuuuuu....gurgiza kai yayi yaja nunfashi ya sauke....
Gado ta haye ta kwanta,sauke numfashi take a hankali a hankali ta soma samun sassaucin rad'adin da takeji a ranta,ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta batai mata adalci ba da take raya mata kishi akan kawarta ramlah bayan tasan yadda suke ramlah bazata taba kallon Abdallah da wata manufa ba koda yake haka Allah ya halicceta da son mijinta....runtse idonta tayi bilal ne ya fado mata a rai lokacin da yake rungumarta a jikin kofar koshin da lokacin da yakai mata sumba a gefen wuyanta ..murmushi ne ya subuce mata har batasan takai hannunta ta shafo gefen wuyanta ba....nan da nan taji wani sabon shauki akan bilal wanda bata ji sa ba lokacin da yake gidan..."yayana yana son harkar turawa"tayi dariya inba bature ba waye zai rungumi kanwarsa harda kiss...mantawa tayi da wani bacin rai cikin sauri ta kunna data ta shiga laluben contact dinsa tana dubawa ta gansa online..dafe kirji tayi ta sauke ajiyar zuciya....
*******
Tana shirin kwanciya ta saka kayan bacci tana feshe jikinta da turare aka turo kofa,cikin sauri ta juya ummahta ce,fad'ada murmushinta tayi ta zauna gefen gado tana kokarin kwanciya...ummah ta karaso ta tsaya "har zaa kwanta ramlatu?"
"Ehh ummah...inaso in kwanta saboda gobe in tashi inyi shiri da wuri banaso ma oga ya rigani zuwa wajen aiki sanan inaso in dan soya samosa a kitchen kafin in fita shiyasa ma nayi komi daddaren nan kafin in kwanta"
"Toh... Allah ya bada saa ramlah a dai kula a kama kai sai Allah ya fito miki da mijin aure da kikeso shima yake sonki"
Kallom ummah tayi tai murnushi "ummah...kenan kedai kiyimun addua insamu cikar burina don yanzun haka akwai?"sai kuma ta rufe fuska tana dariya...itama dariyar ummah tayi tana kokarin juyawa "Allah yasa Ramlah ya cika miki burinki"
"Saida safe ummah"ta gyara kwanciya ta kwanta kunna data tayi ta duba jiddah na online...massage din jiddah ta gani kamar haka "kawata...shine kika kira mijina daddare?kikeso kisa zuciyata ta buga?kinfi kowa sanin yadda nake kishin Abdallah har yan uwansa"...wata yar dariya ramlah tayi lallai kina gab da mutuwa don saina tabbatar da na samu kan mijinki na shigo gidanki na goga dake a matsayin matarsa ta sunnah ba dadiro ba don Abdallah ba kalan namijin da zaa bi a waje bane kuma banida raayin binsa...badai bakisan yadda zaki hakuri ki koyi jan hankalin mijinki ba?ki canja sa da kanki?hmmm zan canja Abdallah dik runtsi.....
Kin mata reply ramlah tayi kawai ta kashe datar ta ma ta kwanta ta rufe idonta tana hararo kanta kwance a kirjin Abdallah...
Karfe biyu na dare suna manne a waya itada Bilal sun gagara chat din hira kawai take masa ta mance da wani mijinta "ya bila...."ta kira sunansa cikin wata irin murya.
Cikin murya mai kama da rad'a "my lilly....am serious missing u wallahi...kefa kyakkyawa ce wani ya taba fada miki hakan?"
Farrrr tayi da ido cikin duhu "babu wanda ya taba fadamun haka saikai my yaayah"tayi maganar cikin sanyin jiki...kallom kofa takeyi ko zai shigo ya lallasheta amma shiru muryar bilal ce ta bugi kunnenta "gobe kinaso mu hadu ko?tou kiyo kwalliya sosai inaso inganki cikin make up kishafa komi na adon mata kinji my baby sis?"
Gyada masa kai tayi tana murmushi kamar yana ganinta"ina jin bacci my yaayah"..kallom agogo yayi daga inda yake kwance... Bayajin zai jure rashin jin muryarta amma bashi da yadda zaiyi dan yasan kila Abdallah zai shigo dakin ta yanzun...ajiyar zuciya ya sauke "good night"ya datse wayar be jira cewarta ba saboda masifar kishin ta da yakeji da wutar kaunarta dake ruruwa a zuciyarsa... Anya zai iya rayuwa ba tare da ita ba?wata zuciyar ta ayyano masa matar amininka Abdallah ta yaya zaka mallaketa?saidai in mutuwa Abdallah yayi kayi ganganci da ka bari soyayyarta tayi galaba a zuciyarka....
Itako trying kiransa back takeyi wato fushi yayi kenan?da ta sani ta barsa sunyi waya Allah sarki yanzun ta gagara samun wayarsa ya zatayi ta sameshi ta fada masa gaskiya?kwalla ce ta cicciko a idonta...ita kanta Bata gaji dashi ba gudun kar kaddara ta gifta Abdallah yaji tana waya da wani cikin dare...kwanciya tayi tana juyi hawaye na bin gefen fuskarta...ya dace ace tana kwance a kirjin Abdallah yana lallabata tunda shi yayi mata laifi amma shi sam besan damuwarta ba besan yadda take sonsa ba gashi zuciyarta nayi mata barazana da kamuwa da son wani Wanda ba mijinta ba wanda bazata taba mallakarsa ba....hawaye ke gudu a fuskarta wani irin feelings ke yawo da ita ta kasa mance sanyin lips din bilal a wuyanta....ta kasa mance yadda zuciyoyinsu ke bugawa tana kwance a kirjinsa....
*******
Kwalliya sosai Ramlah keyi a gaban madubi,ummah na tsaye jikin kofa tana kallon tsabar kyau wanda ramlah tayi ita kanta ta kasa daina kallonta Tana kallon yadda take nad'a daurin dankwali na atanfa akanta cikin kwarewa tanayi tanasa pin..har taa gama tana hangen ummah a jikin kofa ta juyo ta sakarwa ummah murmushi "masha allahu ramlatu kinga yadda kikayi kyau kamar me zuwa gasar sarauniyar kyau?"
Cike da nishadi tayi dariya "ummm ummah kenan bari kiga seven sauri nakeyi inaso in riga kowa zuwa aiki shiyasa tunda nayi sallah ban koma ba na fiddo samosa a fridge na soya gashi can a basket sanan nayi wanka"tana maganar dakyar take taku saboda fitted gown ce jikinta tabi jikinta ta karasa ta dauki gyalenta medium medan girma baki ta yafa ta sakesa ta rataya jaka ta zuba wayoyinta cikin jaka..."ummah saina dawo zan tafi"
"Allah. Ya tsare ramlatu a kula"tare suka fito da ummah tana rike da basket da ta zuzzuba abubuwa ciki harda flask na ruwan zafi da cups ciki.
Tsaye yayi a kofar dakin ta yana kokarin shiga ta fito daga kitchen idanuwanta sun kumbura sunyi jajir kallo daya yayi mata yaji gabansa ya fadi fuskarta ta fada idanuwanta sunyi jajir sun dan kumbura,kwana tayi kuka kome yasa idonta yayi ja haka?...kallonsa tayi ta dan sunkiyar da kai ta dire tray din "ina kwana sweet"
"Lafiya kalau...ya kika kwana?hope babu wani abu dake damunki, wallahi jiya na gaji kina barin parlorn na wuce dakina na kwanta naso zuwa gareki amma nasha aiki bacci yaci karfina"
Takaici ne ya kara lullubeta,kaida mijinka besan yadda ka kwana ba saboda aiki da gajiya..."lafiya lau,ga breakfast nan nakawo idan akwai abinda kake bukata u let me know zan dan kishingida a daki bacci nakeji"
Kallonta yakeyi cikin wani irin yanayi,to meya hanata bacci kuka kome?to menayi mata da zata damu kanta haka...tallabo fuskarta yayi yana kallonta ido cikin ido ya kashe mata ido tai maza ta kauda kanta....jiddah kenan rigimammiya ce sam batasan yadda zata zauna dashi ba....jan jikinta tayi ya ruko ta ya hadata da kirjinsa yana kallonta tausayinta ya lullubesa...da ace zai iya daya hakura ya bar zuwa aiki yau ya lallabi matarsa yasan fushinta...amma ya kudura a ransa yau idan ya dawo zai shayar da ita soyayya da zai mantar da ita damuwarta dikda yasan halinta saita samu hanya kuma amma yasan ta inda zai bullo mata...kallonsa take tanajin bugun zuciyarta na karuwa hmmm Allah yasa ya bani hakuri ya rungumeni ina son mijina...ta furta a zuciyarta kuka ke neman kwace Mata yasa ta gwada janye jikinta ko zai ruko ta sai taga ya kalli agogo ya mufi inda ta dire breakfast....girgiza kai tayi kwalla na bin fuskarta batare da ya gani ba ta shige daki...
*******
A gaban table dinsa ta dire masa wasu kyawawan kuloli kanana masu shegen kyau pink da flask silver da cup ta jera sunyi kyau sosai cleaner yana ta mopping yana satar kallonta...wanan sakatariyar kyakkyawa ce ta hadu ba laifi tanada fuska kallonsa tayi "musa sannu da aiki"
Washe baki yayi "yawwa ranki ya dade"ta fice yabi bayanta da kallo...kicibis sukayi dashi yau ash colour din suit yasa ta mugun karbarsa yayi kyau kamar wani bature kamshin turarensa da nata suka kauraye wajen,dan rusunawa tayi "barka da zuwa ranka ya dade"..mamaki ne ya kashesa harta shigo kenan,ya kalli agogon dake makale jikin bango as usual beyi latti ba karfe bakwai da rabi yake shigowa yanzun ma karfe bakwai da rabi ne,amma ita karfe nawa tazo haka?"sannunki"yace mata hade da murmushi ya wuce ta tabi sa da kallo....har ya shige tana kallonsa bata daina ba ta juya ta nufi wajen zamanta....
Tunda ya soma aiki a laptop kusan minti goma sha biyar sai yanzun ya dago kai idonsa suka sauka akan flask da kuloli dake gefen table,yatsina fuska yayi waye haka ya ajiye masa wadanan kayayyakin gaba table?..da sauri ya danna kararrawar kiran ramlah ko ita ko musa....
Ci gaba da aiki yayi ta turo kofar hade da sallama ta rufe ta karaso ta zauna a kujera "kana bukatar wani abu ne?"ta labgabar da kai cike da ladabi...kallonta yayi jimmm shi kansa saida ya tsinci kansa cikin faduwar gaba wani irin kyau tayi haka?meta shafa a fuskarta da ya canja mata kamanni?...tana lura da kallon da yayi mata me kama da kallon wulakanci "waye ya ajiyemun wadanan abubuwan?"
Gabanta ya fadi yadda yayi maganar fuska daure cike da isa...dakyar ta saita kanta "nic..e dama nazo da mana dashi naga harka wuni a office bakacin komi"..wani irin kallo yake mata mai cike da wulakanci yasa ta sunkuyar da kanta nan da nan jikinta yayi sanyi..shiru yayi sanan yace "bana bukatar cin komi yasa banaci ke daga zuwanki har kin lura da banacin wani abu?meya shafeki?ina ke kawar matata ce?"...sosai zuciyarta ta muzanta...wani irin kunya ne ya lullubeta kamar kasa ta bude ta shiga takaici ya lullubeta haka nan ta cije ta dago manyan idanuwanta da suka soma yin ja ta langabar da kai cike da kanskantar da kai cikin sigar lallashi tace "am sorry... banyi hakan don ranka ya baci ba,nayi ne don kyautatawa kuma naga kamar inada damar hakan,amma tunda banida damar hakan kayi hakuri bazaa sake ba ranka ya dade".. idanuwanta suka kawo ruwa cike da lallashi take maganar,sosai yake kallon yadda take motsa bakinta amma hakan besa yaji wani abu ba saidai yaga rashin kyautawarsa na tsawar da yayi mata...furzar da iska yayi ya juya ya ciro takadda yana kokarin signing jiki "is ok... shikenan thanks for your care zanci"..da sauri ta dubesa...dik yadda ya wulakantata hakan besata jin wani farin ciki ya lullubeta ba... fuskarsa a daure yake sa hannun babu fuskar da zatace wani abu,muka mata takaddar yayi"ki kaiwa director yasa hannu a nan ki dawo mim da ita"..gyada masa kai tayi "owk sir"ta mike cike da kwarkwasa tayi hanyar fita...
Ture laptop din yayi ya janyo cup da flask din ya zuba ruwan zafin kamshin citta da kanunfari da dauran kayan kamshi ya bugi hancinsa...tururi kawai yake yasa hannu gefen table dinsa ya ciro cubes din shuga a kwali da yake ajiyewa yasa guda biyu ya soma juyawa ...
Bilal ne ya fado masa lallai be kyauta ba ya dace ya kirasa yaji yadda ya koma gida shekaran jiya,koda yake Bari idan anyi break ya samesa a inda yasan zasu hadu...
********
Cikin sauri jiddah ta feshe jikinta da turare kallon kanta take a madubi samm tun bayan bikinta da akayi mata makeup na aure da kyawunta ya razana duniyar Instagram da hotonsu ke yawo bata Kara yin kwalliyar da tayi masifar kyau irinta yau ba har tsorata tayi ta dafe kirji yellow din material ne jikinta da hula yellow irin wadda ake yayi masu design kala kala...kiran wayarsa ce yasa tayi saurin juyawa taga shine,ya iso kenan "hello my yaayah... tun jiya da kaimun fushi baka sake kirana ba yanzun ma na shirya ne kawai saboda nasa ran zaka kirani bawai inada tabbacin hakan ba"
Lumshe ido yayi ya kwantar da kai jikin kujera "am waiting...ina kofar gate zaki fito da mota ne?ko su ummah sun dawo?"Yana sane yayi mata tambayar..jim kadan tayi "ah ah ba yanzun ba,bazan fita da mota ba zan bika idan munyi magana sai ka saukeni gidan kanwar ummah na"ta sharara masa karya...gidan su kenan jinjina kai yayi hmmm jiddah kenan shi tausayi take basa yana sonta inama abokinsa yayi gigin sakin ta...hmmm
Kullo kofofin tayi ta fito ta yane kanta da bakin gyale har daukar ido takeyi me gadi na zaune ya na kokarin yin alwala "ranki ya dade zaa fita ne?"
"Ehh zani gidan ummah na ne saina dawo"da sauri ya bude mata gate motar da yayi tozali ce yasa ya dan leka Yana iya hangosa...abokin Abdallah ne zai sauketa kenan bece komi ba ya rufe gate din....
Tunda ta Doso bugun zuciyarsa ya Karu hailala ya shigayi a bakinsa ya kasa dauke idonsa daga gareta bin ta da kallo kawai yakeyi har ta bude motar ta shiga da faraarta "yaayah na barka ko?ina mukayi?"tayi masa tambayar idonsa na kanta...."am talking"ta furta ya sauke numfashi "my baby sis.. u look so gorgeous...lets hug umm?"ya kashe mata ido...kallonsa take bata motsa ba sai kauda kai da tayi "common lets hug...nifa bature ne na saba hakan da sisters dina i dont take it personal ni ai yayanki ne"....bata fuska yayi ya hade girar sama da ta kasa ,batason ransa ya baci saboda yadda takejin sa a zuciyarta kawai ta fada jikinsa ya rungumeta tsammmmm... runtse ido tayi yanajin yadda kirjinta ke harbawa turaren jikinta ya bugi hancinsa humra mai kamshin gaske nan da nan yaji network dinsa na neman daukewa matseta yayi a jikinsa..."my lilly...."ya kira ta cikin wata irin murya...ita kanta muryarsa saida ta sagar mata da jiki dakyar tace "naam"...yana rungume da ita yana goga sajensa a fuskarta taji yar...yawo yake da bakinsa a fuskarta ya d'ago fuskarta yana kallonta idonta a lumshe...ya dora lips dinsa akan lips dinta bedai hade ba amma hura mata iska yakeyi harshensa na dangwalo lip balm dinta mai zaki yana kadawa ya cire fuskarsa..."kinsa lipgloss mai zaki"ya ja numfashi tamkar mejin sanyi tana rike a jikinsa ta kauda kanta .nan da nan taji wani abu na sauka a jikinta..."lets go ina mukayi?..inaso mu kebe in kalli kwalliyar nan inada labarai da zan baki"
Jinjina masa kai tayi tana saike numfashi idanuwanta sun canja kala...batace komiba yasa ya kalleta dik ta sauya har yar rama tayi ko me yayi mata oho...jan motar yayi suka bar wajen karar tafiyarsu yasa mai gadi cewa "ikon Allah sai yanzun suka wuce kenan"...
*MASU BUKATAR SIYAN IZZA TA COMPLETE DOCUMENTS YA* *KAMMALU AKAN NAIRA DARI BIYU KACAL...DASHI DA* *ZAINUL ABIDEEN* *ZAFAFAN LABARAI WAD'ANDA SUKA SIYA KADAI ZASU BAKU LABARI MESON DUKA YA BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN 2255398727* *ZENITH BANK AMINA JIBRIL GA WHATSAPP NUMBER TA 08166177830 .....*
Wayarsa ya kwasa gara yaje ya nemi afuwarsa don yasan tunda yaki kiransa bayan sun rabu fushi yayi bilal baya daukar lokaci be nemeni ba bamayin kwana biyu,yanzun ma ba lallai yana gida ba amma yasan yana crystal garden hanyar unguwar rimi wajen zuwansa ne na nishadi,fitowa yayi ya rufo office dinsa karar rufe office din yasa ta juyawa sashen office dinsa shine ya fito cikin kasaita yake takunsa ta saki baki tana kallonsa saida yazo zai wuce yace "am going out amma dai zan dawo nan da awa daya"be ji metace ba ya wuce abinsa,yaji dadin ruwan zafin nan sosai cikinsa ya koshi ba laifi yanason irin wadanan abubuwan yana zuwa office dasu tunda shi bameson cin abinci a waje bane....
Har ya tada motarsa ya rike wayarsa yana son kiran jiddah yaji yadda take ya tabbatar tana can tana kuka koda yake zataje wajen su umman ta amma dai sam be yarda da yadda yaga idanuwanta ba dole idan ya koma ya lallasheta yana son matarsa ita gani take tamkar besonta shiko kokarin nema mata abinda zata rayu ta ginu yakeyi...i miss you jiddah ya furta a fili kife wayar yayi bari kawai idan yaje gida ya sameta su sasanta kansu tada motar yayi ya fice....
Tunda suka hau hanya take tunanin Abdallah ya bata mamaki ya nunar mata da samm batada muhimmanci a wajenta dole ma tasan nayi zatayi magana da ramlah anya bazata bar masa gidan sa ba kuwa?tayi tunanin dazun zai lallasheta su shirya amma sai ya nunar mata da be damu da itaba bedamu da damuwarta ba ga halin da ya jefata nan...kallon bilal tayi Yana tuki yana kallonta ta gefen ido yadda take kallonsa yasa ya mika hannunsa daya ya ruko hannunta yana murzawa"yadai baby sis da satar kallo na nayi miki kyau ne?"...ya na murza hannunta kunya ce ta lullubeta ta sunne kanta gefe tana jin dadin rukon da yayi mata "muje crystal garden ko?inaso mu kebe in kalleki dakyau mu tattauna in baki kulawa ko?"..jinjina masa kai tayi tana jin wata kasala a jikinta can kasan zuciyarta kuwa tamkar an watsa mata rushin wuta....
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:25 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
*Inawa daukacin masoyana makaranta littafaina da na haske writers gabaki daya Barka da sallah Allah ya maimaita mana...SLIMZY✍🏻*
*9*
Tafe suna yana kallon sashen ta yana jin kansa cikin wani irin nishadi da bai taba jinsa ba,kallon mirror din motarsa yayi da sauri ya sake kallo abinda idonsa yake gane masa ne yakeso ya tabbatar shin wanan Abdallah ne yake biye dasu ko yaya?kara kallon mirror din yayi wanan karon waya yake latsawa daga bayansu sakamakon wutar traffic da ta tsaida motoci a junction sin ministry of education kaduna....wayarsa ce tayi kara tana ajiye yayi saurin dauka ganin tana kallon inda wayar ke vibration Abdallah ne ke kiransa, shin kodai ya gansu ne?wani irin bugu zuciyarsa tayi yana kallon call din kafin ya furzar da iskar bakinsa cike da kwarin gwiwa "hello man ya ne?"
"Lafiya lau,na biyoka inason ganinka muyi magana but na hangi kamar kanatare da budurwarka dikda ban kalli fuskarta ba dai na juya please ka sameni a gida kawai muyi magana"
Wani gumi ne ya karyowa bilal ya sauke ajiyar zuciya"owk"ya datse wayar ya kalli jiddah da ta kafesa da ido,sosai take kallonsa gabanta ke faduwa domin tana jiyo sautin murya kamar ta mijinta Abdallah,shin Abdallah yasan bilal ne?...da sauri zuciyarta ta kaudar mata da tunanin Abdallah bazai taba sanin bilal ba,ajiyar zuciya ta sauke ya dubeta ya Kai hannunsa ya shafi gefen fuskarta ta lumshe masa ido sosai take shagala da kallonsa bata gajiya da kallon nasa,
Lallai yau sunyi narrow escape yau da abdallah ya gansa da matarsa jiddah a matsayinsa na amininsa to yace masa mene? akwai kunya sosai saidai babu wani abu da zaiji face damar samun mallakar auren jiddah...shin meyasa ma be gansu ba ayita ta kare?....
Ko wannensu tunani suke har suka iso crystal garden inda kasantuwar ranar aiki ce babu mutane dayawa tsurarun mutanene yawancin su ma masu aure ne.....parking motarsa yayi ya ruko hannunta "let's go"
"Amma dai bazamu dade ba ko?"tayi maganar muryarta na rawa tana kallon kwayar idonsa,gyada mata kai yayi yadan matse hannunta kafin ya sake ta suka fito a tare....
********
Kamshin turarensa ne ya sanar mata da dawowarsa da sauri ta kalli hanyar shigowa bata gama gyara zamanta ba ya shigo,shagala tayi da kallonsa yana tafe yana latsa waya "barka da zuwa sir Abdallah....har ka dawo?sannu ka gaji ko?"
Kallonta yayi,ji wanan waye yace mata shi ya gaji?mtsww yadan ja tsaki "na dawo"ya amsa a takaice yayi gaba ta bi sa da kallo,jakarta ta janyo ta bude turaruka guda uku ne ciki ta ciro tayi murmushi for rumaisa,afee da meenah nasan zasu so shi amma ta yaya zataje gidan mahaifiyar Abdallah domin kamun kafa?...murmushi tayi dabarar da ta fado masa...
Lumshe ido Abdallah yayi kyakkyawar fuskar jiddah ce ta hasko masa a daren jiya lokacin da take tambayarsa me kiran nasa, Yana missing din matarsa yanason kasancewa da ita amma samm aikinsa baya basa wanan damar,shiba mutum bane meson yawan nanikewa mace salom ta rainasa amma tabbas yau ya tanadar mata tarairaya ta musamman....
*******
Dan zukan lemo yayi ya dire cup din yana facing dinta...gabaki daya yanayinta ya canja sammm yana lura da akwai abinda take bukata saidai besan ko meye shi dinba "yadai my lilly?"ya dage mata gira, sunkuyar da kai tayi tana girgiza kai bugun zuciyarta na karuwa,
"My lilly....."ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya "hakika na shiga wani yanayi a ta dalilinki....na tsunduma kaina cikin wani harkalla da bazan iya fita ba sai ke"da sauri ta dago kai tana kallonsa idonta cike da tsoro,kada kai yayi "nasan kina mamakin meye ne wanan harkallar,...harkallar bata wuce soyayyarki ba da taimun dirar mikiya batare da ta shawarci zuciyata ba,hakika soyayya bataimun adalci ba... kanwa ta na daukeki amma at the end na kamu da matsananciyar kaunarki"cikin wata iriyar murya mai kama da rada yake maganar,.... innahlillahi wa innah ilaihi... ta furta a zuciyarta cike da tsoro tabbas na yaudareka da na kasa fada maka nidin matar aurece ga waninka,saidai dagani har kai zuciyoyin mu basuyi mana adalci ba....inajin sonka a can kasan zuciyata,saidai soyayyar mijina itace ke yawo a jijiyoyin jikina....kulawarka da nuna tausayawa da nake gani a kwayar idona sune suka shagaltar dani na mance da igiyar aure uku da suke daure a kaina....ta shagala cikin kogin tubani tabo lallausan hannunta yayi ya langabar da kai kamar zaiyi kuka yanajin zuciyarsa na kara azalzalarsa "kinyi shiru jiddah... kiyi magana kimun alkawari bazaki taba iya rabuwa dani ba...kimun alkawari komi runtsi dik wuya a nan gaba bazaki barni ba koda wani mummunan lamari ya faru a rayuwarmu zaki amince da aurena idan nazo miki dashi?"..kallonsa take maganganunsa na barazanar tarwatsa mata kwakwalwar kai,to kodai yasan cewar tana da aurene yakeso tayi masa alkawari koda mummuna lamari ya faru bazasu rabu ba?wani mummunan lamari ne ya wuce wanda mijinta yasan tana mu'amala da wani da har zasu shiga wani hali?...me kalaman bilal ke nufi ne?gumi ne ke karyo mata jikinta yayi sanyi kasa motsi tayi saidai bazata mance da halarci da bilal yayi mata ba na gayyato farin ciki cikin rayuwarta, tsintar kanta tayi tana magana "nayi maka alkawari bilal....komi runtsi bazan taba rabuwa da kai ba saboba ina matukar...."sai kuma tayi shiru muryarta ta kama rawa "ki karasa mana jiddah ki fadamun kina matukar mene?please mana love ki fadamin kinji hakan zaisa in kwana cikin farin ciki da murna"girgiza kai tayi tana murmushi ta dubi agogon dake makale a hannunta laasar ta kusa..."inaso in koma please nace zaka saukeni a wani gida"gyada mata kai yayi yana kallon dan bakinta...i cant wait na amsheki a hannun wacen wawan ya furta a ransa mikewa yayi ya mika mata hannu babu musu ta dora hannunta akan nasa ya dagota suna dariya...sosai mutanen wajen ke kallonsu wani mutumi nesa dasu kadan ya kashe musu hoto a waya....
*******
A kofar gidan ummahn ta sukayi parking ta dauki jakarta kamar kada su rabu take ji shima kallonta yakeyi "zaki fita bamuyi sallama ba?"
Yar dariya tayi ta sunkuyar da kai ya fuzgota da sauri ta fice tana dariya yadan daga mata murya "kinci bashi"daga masa hannu tayi ta nufi gate din gidansu har ta shige Yana murmushi....kafin ya tada mota ya fice...
Sallama tayi tundaga harabar gidan takejin kanta cikin wani farin ciki a guje ta shige cikin gidan bata tsaya ko ina ba sai a parlorn gidan su tana fadawa ta daga murya "ummah..... oyoyo"dik suka juya ganinta yasa ummah ta washe baki cike da murnar ganin jiddah ..."oyoyo oyoyo oyoyo jiddah yar abbah"..rungume ummah tayi ta baya kannenta yan mata biyu dake parlorn suka hada baki "oyoyo yayah jiddah"
"Oyoyo yan biyun ummah Koda yake nayi fushi tunda baku zomin ba"
Kujera ta nema ta zauna tana fuskantar ummah "ummah na ina abbah ne baya gida ne?"
"Dama ai yau ranar aiki ce ko kin mance yau talata ne?keda ganin abbah sai dare nasan ma bazai tarar daku ba keda Abdallah ne?"..
Take yanayin jiddah ya sauya tayi shiru kafin ta nisa "Abdallah yana wajen aiki nikadai ce"
"Ohh da motarki kike tafe kenan"
Girgiza kai jiddah tayi "ah ah abokin Abdallah ne ya kawoni"tai saurin zukawa ummah karya "fatan dai kuna lafiya babu wata matsala"
Saida tayi shiru kafin ta ansa da babukomi.... kanwarta na nan ta kafeta da ido tana lura da yadda jiddah ke amsa magana idan anyi mata maganar mijin nata...."yayah jiddah nikam gani nake kamar akwai matsala keda Abdallah ina kallon yadda fuskarki takeyi idan aka tambayeki shi"ta tsare jiddah da ido "ke Ashmah kin iya sa ido ni babu komi"
Kiran bilal ne ya shigo wayarta tana ganin shine ta mike ta nufi dakin kwanan kannenta dukkansu suka bita da ido "sabon salo ya jiddah ya Abdallah ya kira harda barin parlor bayan kafin aurensu ma gaban ummah sai tayi wayarta ko bayan aure ma haka sai yau"ta tabe baki ta juyar da kai
"Banson iskanci Abeedah,itada mijinta bakusan me sukeso suce ba tabar parlorn,a Shiga ciki a zubo mata mutumin nata dambun couscous idan ta gama sai taci ko"
Tare suka mike kyawawan yan biyu masu matukar kama da juna inba ka san abidah da Aisha ba bazaka banbance su ba "ummah tou a ragewa yaya Ib ne?"
Daga mata kai ummah tayi ta juya suka shige tare....
Cikin murya mai kama da rada jiddah ke magana idonta a lumshe "yanzun yanzun fa muka rabu har kaji kanason kara ganina?...kai my yayah kabari gobe sai mu wuni tare kazo gida"
Kwantar da kai yayi yanajin wani abu mai kama da shocking na jansa "bakisan menakeji ba game dake ko?hmmmmm ina son kasancewa dake jiddah...fatana ki rikemun alkawari"
Call ne ya shigo wayar jiddah tadan daga wayar ta duba besty...ramlah ke kiranta,lumshe ido tayi besty na kiraki daga baya...ta cigaba da magana "all right yanzun ka taho ka daukeni sai ka ganni saika maidani gidan"
Zabura yayi daga kwancen cike da zumudi "kin amince?"
Gyada masa kai tayi kamar tana tare dashi "ehh nima inason kasancewa dakai"dago kai tayi sukai ido hudu da abidah tabe baki abidah tayi ta dire mata plate "idan angama soyayyar da ya Abdallah sai aci abinci saikace bazaku hadu a gida ba"...ta fice girgiza kai jiddah tayi "bari in shirya kataho kawai"ta datse wayar,dafe kirji tayi tanajin yadda zuciyarta ke harbawa...me takeji ne game da bilal dagaske sonsa takeyi?anya kuwa ba huce haushi bane?bazataso wani da namiji kamar Abdallah ba,yunkurawa tayi ta fito "ummah zan tafi Abdallah ya turo a daukeni"
"Ehh ai naji kunata zuba soyayya"cewar abida "daga zuwanki zaki tafi ko dambun couscous din ma bakici ba"
Yatsina fuska tayi daidai kiran bilal ya shigo "idan nakara zuwa naci,a gaidamun ya ib da abbah,bari inje kada yayita jirana ummah"
"Allah yayi albarka,a gaida Abdallah"...sauri sauri ta fice suka bita da kallo...
Motar ta shiga ya tada ta sakar masa murmushi, rivers yayi sukayi kwana suka miki hanyar fita...motar ibrahim yayanta sukayi clashin...kallonsu yayi da daurarriyar fuskarsa yayi gaba ko waye wancen da jiddah oho...koda yake daga gida take dole ya tambayi ummah yaji....
Tafe suke a mota kiran ramlah ya shigo "besty sorry kinyimun call ina gidan ummah..."
Gyara zama ramlah tayi Tana harhada jakarta Tana kallon time "ok dama zance miki gobe zan sato hanya inzo kice bilal dinki yazo mana?"..kallon sashen bilal dun tayi yana jiyo wa ya mika hannu ya amshe wayar "ramlah....ai ko bakice ba zanje gidan rabin raina zanso mu hadu"
Zaro ido ramlah tayi wato suna na tare kenan?hmmm lallai abu ya kankama...target na gaba ya kamata ta hada ,yake tayi "insha Allahu yaya zanzo sai mu hadu asha hira"
"Tou ga sweet din tawa"ya mikawa jiddah wayar yana kallon yanayinta dik ta kosa ya bata tana amsa "keda kike wajen aiki ya zaai kizo?"
Kallon gefe tayi "zanzo zance banida lafiya sai inzo inganki besty i miss u soo much mundade kwana biyu banganki ba naji daga gareki"tayi maganar cike da kissa...
Kaunar Ramlah ta kara ratsa jiddah "Allah sarki yar uwata i cant wait to see you"sukai sallama ta kashe wayar....murmushi ramlah tayi ta ja kujera ta jingina tana kada kai....
*******
Rukota yayi yana murza hannunta sanda yayi parking a kofar gate din "nidai banason wanan murza hannun wani iri nakeji"
Kasa da murya yayi "sure?....tou ki shirya gobe zan murza sosai"makale kafada tayi ta bude motar "hope zamuyi video call yau"
"Ehh zamuyi"
"Tou sai munyi i miss you"yayi kissing hannunta ta fice....tana waigensa ta buga gate din shima ita yake kallo yana murmushi ya shafa sumar kansa...ta shige yaja motar....
*******
Kafin Abdallah ya fito Ramlah ta shirya kayanta tsaff har yar hoda ta shafa tana ganinsa ta sunkuyar da kai "idan kin shirya muje in saukeki a hanya don zan biya gidan ummah na"farin ciki ne ya lullubeta "ok sir Abdallah am done"
"Let's go"yace yayi gaba da sauri ta biyo bayansa da basket din flask sukayi wajen motarsa inda yake parking ya bude ya shiga itama ta shiga da sauri yaja motar... fuskarsa babu faraa "meyasa jiya kika kirani a waya daddare ina gida?"yadda yayi maganar yasa gabanta ya fadi wani miyau ta hadiya mai kaurin gaske "kada kisake kirana ina gida"
"Amma idan kiran akan wani aiki ne fa?"ta tsinci kanta da yi masa wanan tambayar....
"Zaki iya"yace yana kokarin fita daga gate din maaikatar mai gadi na daga masa hannu suka fice...
Babban titi suka biyo tun daga nesa yake hangen me kilishi...slow yayi alamar son tsayawa wajen me kilishin,da sauri ramlah ta kallesa wato kilishi zai siyawa jiddah? wanan kilishin bashi zaici ba don jiddah ta taba sanar mata da bayacin kilishi bema taba ba itace masoyiyar kilishi... parking yayi ya fita ya amso,wani bakin ciki ne ya lullubeta ta janyo wayarta ta rubutawa jiddah massage...." *kawata fatan kina lafiya....nasan Abdallah na nan Yana muzguna miki inata tunaninki wallahi...ya kamata ki share lamarinsa ki nemawa kanki yanci....daga baya zaizo Yana neman shiri kada ki basa fuska domin aikinsa ya fiki zai lallabaki ne* *kawai daga baya ya yasar dake...yanzun ma naga alamar so yake ya lallasheki idan ya dawo gida don naga ya fita ya siyo kilishi zaizo miki dashi...yanzun haka sex yake bukata karki amince sauran maganganu da shawarwari sai mun hadu* *don akwai labarai....*
Tana gama tura mata ta kife wayar ya shigo ya tada motar suka bar wajen....
Ta fito daga kitchen kenan tana goge hannu da kitchen napping taga massage ya shigo wayarta jikinta har rawa yake don tasan babu mesonta sai bilal ganin ramlah ce yasa ta shiga kitchen tana karanta massage din tana juya nama da take soyawa....
Runtse ido tayi hmmm Abdallah bazai taba tarairaya ta bama ramly...saidai aikinsa da ya fini koda ya sai kilishi ya siyane don ya kawomin kawai...hmmm wani bakim ciki ne ya lullubeta taji kuka na neman kwace mata...
*******
Suna karyo kwanar da zai sauketa ta yatsina fuska tana kada hannu,kallonta yayi "yadai bakida lafiya ne"
Girgiza kai tayi "fitsari nakeji sir Abdallah ko zaka taimakamun muje gidan ummah sai inyi daga can sai in wuce?"
"Owk"kawai yace ya canja hanya zuwa gidan ummansa....murmushin nasara ramlah tayi batare da ya ganta ba,suna isowa kofar gidan afee na fita da driver...
"Kash shuaibu kaga yayanmu da anty jiddah sunzo ni mukoma please inaso inganta inbita gida"
"Ba anty jiddah bace waccen,amma tayimun kama da wadda sukazo tare ranan kawar nan tata"
Zaro ido afee tayi"shuaibu Anya idonka na gane maka daidai?"
"Itace wallahi afnan".. bata fuska afee tayi"to me sukazo yi itada Yaya gidan mu?...bari mudawo zanji komi bakinsu meenah idan be gamsheni ba zan fadawa anty jiddah ta hanata bin mijinta"ntswww afee taja tsaki....
Tafe yake Abdallah tana biye dashi har cikin gidan..
*******
Abinci ib yakeci a parlor ya dire plate din "ummah dazun waye ya kawo jiddah gidan nan?na ganta da wani namiji sun fice daga layin nan?"
"Ehh tace abokin mijinta ne Abdallah ya kawota kuma kaga da sanin Abdallah din kenan ya kawota tunda ai yasan gidan iyayenta ne yasa aka kawota kuma"
Ruwa ya kora "tou bedai dace ba gaskiya sam sharia batace hakan ba muke janyowa kanmu abinda daga baya zai zama matsala"
"Allah ma ya rabamu da matsala ibrahim,kai dai kullum baka fadan alheri sai sharri banson kara jin hakan"girgiza kai ibrahim yayi sam ummah batasan yanzun andaina kiwon mutum sai dabba ba tsaf zaa musu sharri kuma ta zauna tunda tare aka gansu ai..mikewa yayi yabar parlorn ummah tabi sa da harara....
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:30 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
*10*
"Barka da zuwa yayah Abdallah...ina yini"rumaisa ke gaida Abdallah a d'arare ta mike meenah kuwa hankalinta na kan waya bata ko dubi inda suke ba rumaisa na satar kallon ramlah tana kokarin ficewa daga parlorn ya dakatar da ita "rumaisa "
"Naam yaya"ta juyo ta sunkuyar da kai,"Dan Allah kai ramlah toilet tayi fitsari shi ya biyo da ita nan"
Kokarin zama yakeyi,ummah ce ta fito sanye da Atanfa dinkin bubu tayi mata kyau da farin glass a idonta "nakejin murya kamar ta Abdallah..."ta karaso
Da sauri Ramlah ta tsugunna ta zube "ina yini ummah...barka da yamma"
Sosai ummah ke kallonta Tana kokarin gano inda tasan fuskarta "barka dai lafiya lau, kamar kawar jiddah ko? wadda ta amshi plate a hannuna ko?"..jinjinawa ummah kai ramlah tayi cike da ladabi "nice ummah"ta mike tabi rumaisa dake biye da ita.
"Abdallah daga ina Haka kaida kawar matarka,kai yarinyar nan akwai ladabi wallahi naji Dadin nunamin mutunci da tayi ranan da sukazo sabanin waccen matsiyaciyar"
Cije lebe Abdallah yayi yana jin zafin zagin da ummah tayiwa jiddah "umm a wajen aikinmu tasamu aiki yanzun ma zan sauketa in biyo nan tacemun tana jin fitsari shine muka biyo"
Shigowar su Ramlah yasa ya mike "sai muje koh?"
Jakarta ta bude kanta a kasa ta ciro wata farar jaka,mai kyaun gaske turarruka uku ta fiddo "gashi rumaisa,keda meenah da afee"
"Laaaa harda hidima haka anty ramlah mungode sosai"rumaisa tasa hannu ta karba,meenah ta yunkura daga kwancen ta danyi murmushi "mungode Anty"jinjina kai tayi batare da tace komi ba Tana kokarin fita ummah tace "ki gaida ummanki"
Dan durkusawa tayi ta amsa da "zataji"... Abdallah kuwa tuni yayi gaba abinsa tabi bayansa....
"Ummah kinga turaren nan fa tsada ne dashi ta bamu,daga biyowa fitsari?"
"Kila nata ne dai ta siya ta bamu kyauta"rumaisa tayi maganar Tana kallon ummah....jinjina musu kai tayi ummah ta zauna tana fuskantar Tv.
Minti minti yakan ja numfashi yana driving samm bayason yadda ummansa ta tsani jiddah bashida yadda zaiyi gashi kaf kannensa sun hade kai da mahaifiyarsa,afnan ce kadai keson jiddah gashi jiddar ba wani abu tayi musu ba tsabar tsana ce.... mamaki ne ya lullube Abdallah yadda ramlah ta ciro turare ta bawa kannensa,me hakan ke nufi?ko tayi hakan ne don ta samawa jiddah muhalli a zukatan kannensa da ummahn sa tunda kawarta ce?..tunani yake kala kala har sukazo junction dinsu ramlah yayi parking "su rumaisa sun gode da turare fa"yayi maganar kansa na kallon titi ko inda take be kalla ba,
Ajiyar zuciya tayi "kannena ne,ummah kuma uwace a gareni sanan jiddah Aminiya ta ce"jinjina mata kai yayi ya kunna motar yaja abunsa...
Ita jiddah meyasa batayi tunanin yi musu da kanta ba,saidai ta saka kawarta ta nema Mata muhalli a zukatan zuriar sa?da alama ummah taji dadin kyautar da ramlah tayi musu harda su rumaisan ma...kada kai yayi ya cije lebe,ya sauke ajiyar zuciya... Ramlah tanada son kyautatawa mutane gashi bata fushi,inama haka jiddarsa take?kullum sai son soyayya amma batasan yadda zata ja raayinsa ba,ko batasan cewar mace tana canja mijinta bane?....tunanin da yakeyi kenan har ya shigo cikin street dinsu shiru babu kowa haka ya iso gate din gidan ya shiga horn...da sauri mai gadi ya bude masa ya shige....
*******
Cikin sauri afee ta shigo parlorn har tana tuntube Allah Allah take ta cire hijabin dake jikinta,kallonsu takeyi kafin ta dubi meenah "ya meenah wacece naga sunzo gidan nan itada Yaya Abdallah kamar Anty ramlah kawar Anty jiddah?metazo yi kuma harda biyo yaya su biyu sukazo babu Anty jiddah"tai maganar cike da son karin bayani,
Rumaisa ta karbe zancen tana kokarin miko mata turare "ehh fitsari ta biyo yi tare suke aiki da yayan mu kingani har turare mai kamshin gaske ta kawo mana kowa daya daya nidake da meenah"
Shiru afee tayi ta mika hannu ta anshi turaren Tana jujjuya wa "meye huruminta na zuwa gidan harda kawo mana turare?munada wata dangantaka da ita ne?wanan munafunci ne da neman gindin zama"tayi maganar da murguda baki,
Wata harara ummah ta watsa mata "tou dangin miji da bakusan abin arziki ba?daga abun arziki?ita matar yayan naku me ta taba anfana muku inace ranan da mukaje ne daddare ganin idon mijinta ta kawo ta baku?"tura baki afee tayi ta dire turaren ta mike tana kunkuni "yaseen gobe gidan Anty jiddah zani infada mata ta takawa kawarta burki da bin mijinta kafin ta aure mata shi,munafukar banza munafukar wofi"
"Kece dai babbar munafuka da batasan abun arziki ba shashasha kije kiyi abinda zakiyi wawuya"...afee ko kallonsu batayi ba ta fada daki,
Tsaye tayi a gaban madubi tana cizan yatsa,me hakan ke nufi?lallai ma wanan matar uwar iyayi mtsww to in ma son yayan mu take bazamu so ta ba ta fada toilet don tayi alwala....
*********
Goge flask din data jera a centre table takeyi,ya shigo da sallamarsa hannunsa rike da jakarsa da ledar kilishi,kamshin turarensa ya haifar mata da faduwar gaba,
Shiko tsaye yayi ya harde hannuwansa ya watsa mata ido,cakkk ta tsaya Tana dagowa a slow har suka hada idanuwa,wata irin faduwar gaba ta tsinci kanta...murmushi yakeyi mata sai ta sadda kanta ta karasa tana kokarin karbar jakarsa "sweet sannu da zuwa...ya aikin"Tana maganar ne fuskarta babu yabo ba fallasa,cije lebe yayi fushi take masa saboda baya bata lokacinsa,ta kasa gane halinsa ta kasa fahintar komi yakeyi don farin cikinta yakeyi?rukota yayi ta fada jikinsa ya runguneta sosai Yana shafa bayanta zuwa kanta,a hankali ya zame dankwalin dake kanta,ya tura hannunsa cikin gashinta....laluben bakinta yakeyi ya hadesu ya shiga tsotsar lips dinta cike da kwarewa.....wani hawaye ne ke zuba a idonta...mijinta gwani ne wajen soyayya amma baya mata hakan sai lokacin da ya gadama...kasa rike kanta tayi ta saki jakar dake hannunta a kasa,jikinta ya saki don haka motsin kirki bata iyawa sai bugun zuciyarta da tasa da suke tafiya a tare sakamakon kankameta da yayi har yanzun harshensa ne cikin bakinta,a hankali yake zuge rigarta yana shafo gadon bayanta har ya kaiga hannunsa maballin bra dinta,
Ballewa yayi ya kai hannunsa breast dinta nan da nan jiddah taja numfashi jin yadda yake wasa da kirjinta,zuciyarta ke harbawa sama sama, kokarin kwace bakinta take amma ya rike sosai yake murzar nipples dinta...wani irin nunfashi taja ta sauke ya dan zare bakinsa daga nata yana kallon kwayar idonta...hawaye ya gama wanke mata fuska yayinda idanuwansa suka kankance...shi kansa yakai stage din da matarsa yake bukata,
Cak ya dauketa kamar baby ya nufi bedroom dinsa da ita,kamshin turaren kamshi ya shaka yaja numfashi ya sauke kafin ya dorata akan makeken gadonsa,
Zare suit din jikinsa yayi da rigarsa daga shi sai singlet ya zare wando sa sai boxer ya hayo gadon ya haye Saman jikinta kansa yakai wuyanta yana yawo da harshensa yana busa mata numfashinsa dake rikitata ...wani irin kaunar mijinta ke ratsa ta,lokaci daya taji wani ciwo da bakin ciki tunawa da tayi bilal yayi mata hakan da ta rudata... runtse ido tayi tana karbar sakwanninsa,tana jin haushinsa amma sam takasa hanasa,sucking breast dinta yake tana jan numfashi tana sauke wani wahalallen nishi da yake kara rikitasa ..nan da nan Abdallah ya soma nuna mata soyayya,kusan mintu arbain suna abu daya kafin ko wannensu ya gamsu...kwantar da ita yayi a kirjinsa yana shafa kanta tana sauke wahalallen numfashi...kissing goshinta yayi ya rad'a mata a kunne "i'm sorry my wife....dik abinda nakeyi inayi ne saboda ke ina kokarin gina mana feature inaso in canja but i cant"
Haushinsa ne ya lullubeta ta kauda kai gefe wata kwalla me zafi nabin gefen fuskarta,yana jiyo saukar abu kamar ruwa a jikinsa nan da nan ya dago fuskarta yaganta shab'e shab'e da hawaye....tausayinta ya kamasa yana son matarsa matsalarsa shine bashida juriyar lallashin mace beda lokacin wata soyayya yau ma yayi ne don kawai ya faranta mata...share mata hawaye yayi ya girgiza Mata kai alamar ta bari,
Yunkurawa tayi ta mike yanabin manyan breast dinta da kallo haka ta sauka ta daura towel ta fada toilet ta rufo kofar...kallon sama yakeyi yana sauke numfashi....
Ruwa mai zafi ta tara ta shige ciki tayi luffff ta runtse idonta hawaye kawai ke gudu a fuskarta,wani yanayi ta tsinci kanta me cike da tashin hankali tunawa da tayi tana muamala da bilal wanda ba mijin aurenta ba,samm batason muamalarsu kullum tanajin zafi a kasan zuciyarta saidai batada zabi ko menene tayi mijinta shine sila...ita mutum ce mai son soyayya da kula sanan mabukaciya ce amma sam batasamun hakan wajen Abdallah,aikinsa ya fiye masa komi a rayuwarsa gashi yau ya faranta mata rai amma kasan zuciyarta wata wuta ce takeci wani radadi takeji a cikin zuciyarta...hawaye ke gudu a fuskarta ta dauki lokaci tana kuka kafin tayi wankan tsarki ta dauro alwala ta fito....daga kai tayi ta dubi agogo takwas saura minti goma ko magriba basuyi ba,sashen gadon ta duba ya fice dakinta ya tafi kenan bata bawa kanta amsa ba ya shigo daure da towel dinta a kwankwason sa gashin kirjinsa dana kansa sun kwanta lufff shagala tayi da kallonsa fuskarsa a daure kamar koda yaushe yana kokarin ciro jallabiya a wardrobe dinsa ta wucesa harta kai kofa ta tsunkayi muryarsa "ki fito parlor muyi sallah baby".waigowa tayi suka hada ido ta gyada masa kai ta fice....
Tsaye yake yana jiranta ta fito da hijab jikinta ya tada sallah,shine yaja musu sallar sukayi magriba da isha'i sun dade zaune suna azkar sanan Abdallah ya shafa ya mike ya nufi kujera "come and feed your husband"
Batace komi ba ta karaso ta zuba masa jealouf din couscous da yaji kayan lambu da nama ta tsiyaya masa lemo ta dire ta wucesa tayi dakinta....
Kaiwa da komowa Ramlah takeyi tun dazun take kiran wayar jiddah batayi picking ba kome takeyi oho,
Shigowa jiddah tayi taga wayarta gaban madubi inda ta direta shigowarta sa kaya tayi saurin dubawa Ramlah ke kira,murmushi tayi"besty sorry kinyita Kira ko?"
Ajiyar zuciya Ramlah tayi ta sauke numfashi "yar uwata ina kika shiga nake kiran wayarki haka ko anata soyewa ne?"
Lunshe ido jiddah tayi "ehh to...yau mutuminki soyayya yakeji don yaudai munkashe arna"
Wani abu ramlah taji kamar mashi ya soki kirjinta nan da nan ta sarke ta Soma tari sai kawai ta kashe wayar fadawa kan gadonta tayi ta fashe da kukan bakin ciki.... innahlillahi yau Abdallah ya kwanta da jiddah over sati biyu ko kusantar ta bayayi?mutumin da ko sex be damesa ba bemasan soyayya ya akai jiddah ta shawo kansa yau yake gwada mata soyayyar da take mafarkin samu?matse idonta tayi kwallar bakin ciki ke gangaro mata a fuska...ta yaya zan mallaki Abdallah?tayaya zan soma sharbar romon soyayyarsa?inaaaa bazai yuwu ba wallahi saina auresa ko ta wani hali...jiddah kinyi kuskuren auren namijin da nake mafarki koda yaushe wallahi bazai yuwu ba ta fashe da kukan bakin ciki....kallon call din jiddah tayi daya shigo ta kife wayar wani abu me dacin gaske ke taso mata a kirji...ummahn ta ce ta shigo tana tozali da Ramlah cikin tashin hankali tace "ramlatu lafiya?meke damunki kike hawaye haka?"ta karaso gadon tana kokarin tallabo ta,
Ciwon son Abdallah da kishinsa,ta furta a zuciyarta amma a zahiri yatsina fuska tayi "wanan ciwon kan nawa ne ya tashi ummah ji nake kamar zai rabe gida biyu"
"Akwai magani a dakina bari in dubo miki"ummah ta sauko daga gadon ta nufi fita Ramlah tabi ta da kallo tana kara runtse ido wasu hawayen na sauka ...
Kiran waya jiddah keyi Ramlah taki picking,dafe kirji jiddah tayi "wayyo my ramly allah yasa ba kwarewar nan da kikeyi kikayi ba"ta rike wayar jiki a sanyaye tayi shiru tunanin kawar tata kawai takeyi....
Fitowa tayi ta zauna a kujera tana kallonsa ya kusa gama cin abincin "ke bazakici bane?"
Girgiza kai tayi "bana jin ci zanci anjima"
"Akwai yougourt da kilishi a waccen ledar your favorite"..kada masa kai tayi tai masa murmushi....
Kwashe plate tayi ta nufi kitchen shiko mikewa yayi ya dauko jakarsa a tare suka shigo parlorn...dire laptop dinsa yayi ta zauna nesa dashi kadan saida ya kunna ya dubeta "come close yau tare zamuyi aikin zo insaki a cinyata"Yana kallonta,
Kauda kai tayi "umm umm just do your work"tace a takaice haushi ne ya lullubeta,hmmm inzo muyi aiki kayo aiki a office ka dawo kuma yau din danasamu aka kawar mun da kishi maimakon insamu soyayya sai akasin haka..hmmm,data ta kunna ta shiga WhatsApp scrolling tayi taje massage dinsa30 massages ta dan zaro ido ta bude sai kawai ta mike ta nufi daki ganin dik misscall na video call ne hmmm tunda bashida time din hira bari muyi hira da kai yaayah B yayita aikinsa abun haushi taja tsaki....
Gyara kwanciya tayi ta latsa kiransa....da sauri yayi picking.... kallonta yakeyi ta cikin waya tamkar meson gano wani abu gashin kanta dake kwance gaban goshinta yake kallo kamar tasa ruwa akai,
Kashe mata ido yayi ta sa dariya "am sorry ina kitchen kuma data na kashe yake"
"Dont worry i will always have time for you my happiness"yayi maganar yana kallonta....kallonsa takeyi tana murmushi...
"Kinyi kyau sosai saidai bana ganinki da kyau"kada kai tayi Tana dariya "dont worry zaka ganni gobe"
"Me kika tanadar mun?"
Rufe ido tayi da dayan hannunta sai kawai tace "komi kakeso"
"Kinyi alkawari?"
Ta gyada masa kai ya bugi gefen gadonsa "sai kin cika"....
********
Juyi Afee takeyi akan gado tun abinda ya faru da yamma ke Mata yawo akai,meyasa yayansu zaiyi yawo da kawar antynsu a mota,shin antyn tasani?..kallonsu rumaisa tayi ko wacce da waya hannunta,ta daga kai ta kalli agogo sha biyu na dare suna ta chat....
"Meenah kinsan ko anty jiddah na online har yanzun?hmmm kome takeyi oho a wanan lokacin kuma yayan mu na kallonta,jiyafa har biyu na dare ina ganinta online WhatsApp Dina gb ne yana nunamin ita"
Mikewa afee tayi ta shiga toilet,"rumaisa ke jiya kika soma gani,ai daga ganin wanan idon nata sai a hankali"
"Hahaha kai meenah"suna hirar ne suna latsa wayoyinsu afee ta haye gado ta kwanta tayi luffff tanada waya amma sam social media bedameta ba tanayin wata bata hau online ba,to yaushe Anty jiddah ta Soma son chat haka?....gobe da Rana zani gidan Anty jiddah inji dalilin da yasa take kokarin sharin mijinta da kawarta,meyasa zata bar mijinta da kawarta?tsaki afee tayi da karfi,cikin hada baki rumaisa da meenah sukace "ke kuma lafiya?"
"Wallahi tunanin Anty jiddah nakeyi wai tabar ya Abdallah da kawarta suna yawo tare ko kishi batayi bata gudun snatching"
Tabe baki rumaisa tayi "ni dama zai aureta da munji dadi ai"
"Wallahi kuwa... don gaskiya ta hadu"meenah ta amshe zancen,
Kwantar da kai afee tayi cike da bakin ciki....
*******
*Washe gari*
Tun zuwansu office hankalin Ramlah ke wajen jiddah so takeyi ta samesu da bilal don ta kara dana tarkonta ya zatayi taje gidan take tunani, daga gani Abdallah a hargitse yau kila jiddah bata kula dashi ba don taga hakan a kwayar idonsa, zuciyarta ke bata karfin gwiwar taje wajensa....
Shiru yayi ya kasa fara aiki mamakin yadda jiddah takai dare jiya tana chat yakeyi gashi yau da safe bata ko samu damar masa breakfast ba,haka ya shiga dakinta ya sameta tana sharar bacci da waya a hannunta kare a kunnenta alamun a haka tayi bacci, to dawa take wayar ko dawa take chat dun?kila da Ramlah takeyi aminiyarta don zancen gizo baya wuce na koki amma zaiji daga bakin ramlah din,yaso ya ganta kafin ya fito amma tanata bacci...
Turo kofar da akayi ne yasa farka daga tunanin da yakeyi...tsaye tayi jikin kofar ta langabar da kai hannunta rike da flask..."yadai"yace yana kokarin kunna laptop
Rufe kofar tayi ta karasa ciki taja kujera ta zauna tana kallonsa,shiru sukayi yana kallonta ta gefen ido shi ta zubawa ido kawai,ji yadda take kallonsa kamar wata mayya..."lafiya?"
Girgiza kai tayi cikin shagwaba tace "haba sir Abdallah tunda na soma aiki kakemun wadanan halayen da kyara tamkar baka sanni ba, dik da kasan nidin kawar matarka jiddah ce meyasa kakemun haka?koni ba yar uwarka bace?bakason ina shiga huruminka ne?"ta karyar da murya kamar zatayi kuka,..
Jikinsa ne yayi sanyi yadda take magana cikin sigar lallashi da shagwaba,sosai ta burgesa a wanan lokacin inama Haka jiddah takeyi idan yana tare da ita taga changes ta tambayesa cikin lallashi da jan hankali da tarairaya Amma sam bata iyaba, gashi kawarta ta san yadda zatai masa magana cikin kwanciyar hankali itako sai fushi?gashi jikinsa yayi sanyi ta kashe masa jijiyiyin jikinsa?dikda ba dabi'arsa bace son magana ko yaushe amma da tana masa hakan wata kila ya sauya ya canja raayi..."kayi shiru sir Abdallah....kayi hakuri idan ina maka shisshigi amma ina ganin nidin kasanni kasan wacece ni niko inaso in rinka magana dakai koda time to time ne"
Jinjina mata kai yayi yace "am sorry...zangani yadda zaai,naga bakida hurumin hakan tunda kedin ba matata bace"yana sane yace hakan ya kalli fuskarta da sauri yanason gano yanayin da zata shiga.. ganin hakan yasa tayi saurin murmushi don tasan ya fadi haka ne yaga yanayinta,cije harshenta tayi ta langabar da kai "aini ban kai matsayin matarka ba amma da matsayina yakai hakan ma da koda ina gida na dameka da tarairaya da lallashi domin abinda na lura kaiba mutum bane meson ayi maka Dole kayi saika gadama...ya Abdallah angon jiddah..nidai a barmun wanan halin dik ina shiga damuwa kaji?"tayi maganar cike da shagwaba,dage kai yayi ya kalleta yana mamakin yadda take kokarin jan raayinsa da kalamai masu hikima...inama ace jiddah ta iya hakan?kila da yanzun ya sauya.... Yana sonta yanaso ya sauya amma ta kasa sashi a hanyar da zai sauya din..."ga pepe soup nan nasan bakaci komi ba kila madam ta makara don jiya na farka cikin dare na ganta online nayi mata massage ta bude batamun reply ba"...shiru yayi yana saurarenta...har takai kofa ta rike ciki washhhh
"Menene "da sauri yayi tambayar...
"Wallahi sir dakyar nayi bacci jiya saboda ciwon ciki yanzun ma nazo aiki ne kawai da zaabani dama inje gida gobe idan na warke sai inzo da naji dadi"tana maganar kwallar kissa cike da idonta...tausayi ta bashi ya jinjina Mata kai"you can go ai bamu da aiki sosai"
Dan durkusawa tayi "nagode sir"ta cije lebenta alamar ciwo "sorry"yace ya janyo drawer Yana duba abu....tsuru tai masa na seconds talatin sanan ta fuce....
Tun da ta tashi bata gansa ba tasan ya tafi...karfe sha biyu yanzun ya dade a office bature ana can gaban computer ta tabe baki...kwankwasa kofa yasa tayi saurin kallon kofar,shiru tayi tana sanye da kayan bacci ta juyo cike da yanga gashinta kwance a bayanta ta karasa ta murda kofar ta bude....suna hada ido dashi taja da baya ta dafe kirji hade da zaro ido...yayi kyau sosai farar shirt ce me layi layin baki jiki,murmushi ya saki ya wuceta ya shige ta rufe kofar mamaki ne ya kasheta ya tsaya cakkk "ya..yah da safen nan?aina dauka sai rana zakazo".
"Bazan iya hakuri ba babyna ...yanzun kika tashi kenan...kayan baccin nan sunyi Miki kyau sosai"kallom kanta tayi ta rufe fuska da hannuwanta ta juya ya ruko kwankwasonta ya rungumeta ta baya...wani zirrrrrr taji yadda yake yawo da hannuwansa a wuyanta....yana kokarin shafo kirjinta....
*******
"Wai afee yau tun safe kike aiki kina sauri sauri ina zakije haka ne?ko zaki wani wajene baa fada mun ba?"ummah tai mata tambayar tana tsaye kofar kitchen afee na ciki itada me aiki suna girki "ummah gidan ya Abdallah nakeson zuwa wajen Anty jiddah inaso inganta nayi missing dinta"
Tabe baki ummah tayi "tou iyayen tsegumi,zaaje ai tsegumi da iyayi ko?allah yasa inji wata magana ta fito ta muna funci ubanki zanci "tayi gaba afee ta cigaba da wanke wanken kayan da suka bata,
Suna parlor ta fito ta suce daki nan da nan ta shiga toilet don tayi wanka ta shirya....
A napep ramlah take adduarta Allah yasa ya bilal na gidan...tanason ta dana tarkon da shi zai zama silar wargajewar komi....idan har haka ta kasance to tabbas kota shigo gidan Abdallah babu wata barazana da jiddah zatayi mata don tanada makamin fidda ta a gidan cikin sauki... Abdallah bazai taba sanin sirrin komi ba sai ta auresa...fatanta ta samu kansa kawai...da alamu tanada nasara.....
******
Sosai Abdallah yasha farfesun ya masa dadi da lipton dinta me kayan kamshi yana mamakin yadda take da azancin magana sabanin jiddah da batasan yadda zatai masa magana ba,ya dace yabar wulakantata haka tunda bakomi bane tsakaninsu sai mutunci....harga Allah kalamanta sun sanyaya masa jiki bedace yake hakan ba ...zaiyi kokarin rinka goda gaisawa ne da ita....
0 comments:
Post a Comment