D'ago kai tayi tana kallon bilal da narkakkun manyan idanuwanta da suka wadatu da zara zaran eyelashes da suke karawa fuskarta kyau,shiko cigaba yayi da yawo da hannunsa a wuyanta yana mata tafiyar tsutsa yayinda hannunsa daya ke ruke da kwankwasonta...yadda take kallonsa yasa ya daga mata gira "menene my baby sis"..girgiza kai tayi ta sunkuyar da kai yasa hannunsa ya kwantar da kanta a kirjinsa...a hakan ya karasa parlorn da ita yana kokarin dorata a cinya ta zame jikinta ta dan juya baya "barka da zuwa"tayi maganar muryarta na sarkewa saboda yadda dik ya kashe mata jiki da salonsa...gashi bata gama farfadowa da soyayyar da Abdallah ya nuna mata ba mai tsayawa a zuciya...mijinta salonsa daban ne amma sam bashida lokacinta ko hirar kirki bayayi da ita balle yasan damuwanta...gaba ki daya ita kadai tasan yanayin da take ciki...juyawa tayi da niyyar ta shiga daki ta dau zani ta daura akan kayan baccinta ya ruko hannunta...cakk ta tsaya bugun zuciyarta na karuwa...
Shiko Bilal be taba tsintar kansa cikin wanan yanayi ba,wani irin abu ke yi masa yawo a zuciya,be taba ganin surar mace mai kyau irinta jiddah ba Allah ya bata shape da zati da diri uwa uba kyau da kwalliya...be gaji da jin duminta ba,wani abu ne ya tokare masa zuciya mai kama da kishi daya tuna matar wani ce fa ya kamu da azabtaccen sonta matar ma ta amininsa da seat dinsu daya tun daga nursery classs...janyota yayi ta juyo da sauri suna hada ido taga yadda idonsa suka sauya gabanta ya yanke ya fadi,shima ta bangarensa hakan ne domin yana hango soyayyarsa karara a kwayar idonta....
D'orata yayi a cinyarsa, Yana lura da yadda jikinta ke rawa hakan yasa ya rada mata a kunne "feel free i will marry you my jiddah,trust me i love you soo much"a karaye yake maganar, kwantar da kanta tayi a kirjinsa yana shafa bayanta,bugun zuciyarsa da nata suka hade waje daya wata zafaffar kaunaraa ke ratsata amma zuciyarta a karaye take hawaye masu zafin gaske suka soma sauka mata babu wanda ya fado mata a wanan lokacin irin Abdallah....d'ago fuskarta yayi ganin tana hawaye yasa ya kafeta da ido.... tabbas yasan hawayen nan tana yinsa ne saboda tasan tanada aure babu wanda take tunawa sai Abdallah ya rigada ya fahimci irin damuwar da take ciki sanan ya gama karantar dik lokacin da zasu kasance tare sai yaga tana hawaye,inama Abdallah zaiyi gigin sakinta?karamar yarinya batasan dadin soyayya da kulawa ba a *AUREN FARI*...
yana rike da kanta hannunsa na jikin wuyanta ya sa harshensa yana lashe hawayen ta a hankali yana cigaba da shafar wuyanta har harshensa yazo bakinta...jikinsa na rawa ya zura harshensa cikin bakinta ya soma sucking cikin wani irin salo da ya kusa gigita jiddah nan da nan jikinta ya soma shocking... hannunsa yake kokarin kaiwa breast dinta da suka cicciko a cikin kayan baccinta....
A kofar gidan napep din Ramlah yayi parking,a tsanake ta sako kafarta waje ta fito ta dubi me napep "nawa ne kudinka malam"
"Dari hudu zaki bada hajiya"
Zuge zip din jakarta tayi ta ciro 500 ta mika masa ya bata canji ta juya ta karasa kofar shiga gidan,.knocking tayi Tana tsaye kusan minti daya sanan mai gadi ya leko ta jikin wani gate din ganin ramlah yasa yayi jimmm ah ah meke faruwa kodai hajiyar gidan ce batada lafiya,katse masa tunani tayi ta hanyar kara knocking ya bude mata "barka da rana baba ina yini"
"Barkadai ramlatu kwana biyu"
Yar dariya tayi batare da tace komi ba ta nufi cikin gidan...
Tsaye tayi a jikin kofar dakin tana iya jiyo yadda suke sauke numfashi,zare ido tayi badai sex ya bilal sukeyi da jidda ba,kallon kofar tayi baa bame kofar yadda idan ta bude zasuji kara ba sai kawai tadan tura kofa...ita kanta saida gabanta ya fadi basu san ta tura ba bakin bilal dana jiddah a hade yake hannunsa na kirjinta yana shafawa....da sauri ta zaro wayarta jikinta na rawa bazanyi wasa da wanan opportunity din ba...ta furta a ranta nan da nan ta seta camera saboda hasken fitilar dakin batasa flash ba tayi musu hotuna akalla biyar sanan ta dauki video for 30 seconds na duka parlorn yadda zai zama bawai hada video din akayi ko hoton bam...ja da baya tayi ta koma sanan tayi knocking...
A furgice jiddah ta zare bakinta daga nasa jikinta na rawa ta kalli kanta ganin yadda ya zane rigarta nipples dinta a waje yasa ta runtse ido ji tayi tamkar an watsa mata rushi a jikinta...kafin ta karasa kofar kiran ramlah ya shigo wayarta,
Ganin kiran yasa tasan itace,ajiyar zuciya ta sauke hade da hamdala da ba wani bane yazo daga gidansu Abdallah ko kuma Abdallah mistakely ya dawo dikda tasan be taba hakan ba,
Dire wayar tayi ta karasa kofar ta bude....taja da baya hade da sauke lallausan murmushi kafin ta watsa mata harara "ni nayi fushi ma yar uwata ta mance dani ko kizo ki dubani ko?aiki ya soma dauke miki hankali"
Shigowa Ramlah tayi tana bin jiddah da wani irin kallo daga sama har kasa,hakan yasa jiddah taji d'ar jikinta yayi sanyi "ah ah besty ashe ya bilal yazo da safen nan"tana maganar tana murmushin mugunta...
"Ehh wallahi ban ma san da zuwan nasa ba bude kofa kawai nayi na gansa wai ya kasa bacci yazo ya ganni"
Neman kujera tayi ramlah ta zauna tana wa bilal wani kallo kafin tace "kauna...ashe kai kana nan idonka ya rufe da soyayya ka mance da ni ko ya bilal?"ta dan tura baki...
Shafar sajensa yayi kafin ya nisa cike da izzarsa "Ramlah...ya kike ya gidan?kwana biyu"
"Lafiya kalau my yaayah yanzun ma da ban biyo na ganka wajen masoyiyarka ba da shikenan bazaka nemeni ba"
Sai lokacin jiddah tayi dariya ta yunkura ta nufi bedroom "ina zuwa"tace tana cigaba da tafiya,kallon da Bilal yabi jiddah dashi yasa Ramlah girgiza kai ..hmmmm mutanen nan basu san nasan halin da suke ciki ba,saura kiris hakata ra cimma ruwa...juyo da dubansa yayi suka hada ido da ramlah ta kashe masa ido yayi murmushinsa dake fiddo masa da asalin haibarsa da kamalarsa...
Doguwar riga tasa baka ta fito ta samesu "ina zuwa bari inshiga kitchen insama mana abinda zamuci koh?bari inyi mana faten dankali da alayyaho sharp sharp"tana maganar tana kallon kwayar idonsa ,shima ita yakewa wani kallo yana shafa gemunsa "bangane da wanan kallon soyayyar da kukeyi ba kodai na katse muku hanzari ne na hanaku soyewa?niba zama zanyi ba ma da kinbar abincin kuci soyayya ko?"cike da zolaya ramlah ke maganar tana dariya dukkansu dariya sukeyi...
Zaiyi magana Bilal watarsa ta katse masa hanzari ya zarota a aljihun gaban rigarsa Abdallah ke kiran nasa da sauri ya danna recieve ya kara a kunne,yana kallon fuskokinsu Ramlah da su ma shi suke kallo "ya ake ciki friend ya kake?"
Daga can bangaren Abdallah ya kwantar da kai ya sauke numfashi "am fine but akwai wata yar matsala da nakeso kazo mu tattauna akai"
Jimm kadan bilal yayi "yaushe kakeso me kuma yake faruwa?"
"Inadai bukatar ganinka ina office yanzun haka zamuyi break kazo mana "
"Owk"yace ya kashe wayar yayi jimm kadan Abdallah ya wuce ya nemesa yazo akan wata damuwa yaki zuwa amma bayaso yayi nisa da jiddah yana son kasancewa da ita yana son farin cikinta bayason ganin damuwa a tare da ita,yunkurawa yayi ya mike ya dau makullin motarsa "Kiran gaggawa ya sameni wani aminina yake son ganina i have no option dan inje inda yake don bansan matsalar tasa ba"
Dan bata fuska jiddah tayi nan da nan taji zuciyarta batayi mata dadi ba haka kawai bataso yayi nisa da ita zai tafi ya barta da tunaninsa,kallonta yakeyi yana karantar yanayinta "am sorry princess xamuyi chat kinji za kuma muyi magana ok?"jinjina masa kai tayi ranta beso ba nan da nan idonta yayi kwal kwal kamar zatayi kuka,ji yayi tamkar ya rungumeta ya lallasheta,kallon sashen ramlah yayi nan da nan ta kauda idonta daga kallonsu tana kad'a kafa tamkar bata san dasu ba,jan nunfashi yayi "sai munyi magana"gyada masa kai tayi Tana binsa da kallo ya fice,
Jabar ta zauna a kujera jikinta babu kwari ta kalli sashen da Ramlah ke zaune "ko baa fadamun ba jiddah nasan kina cikin farin ciki kinsoma samun walwala samun me debe miki kewa a tare dake hakika bilal yana taka wata rawa ta musamman a rayuwarki"
Idonta ne ya cicciko da hawaye "amma ramlah aurena fa?ko kin tuna inada aure?ko kin manta nidin matar wani ce matar Abdallah ce ni? hakika Abdallah ya cutar dani shine sanadiyyar da na kamu da soyayyar wani daban hakika yanzun yadda nakeji banajin zan iya minti goma batare da bilal ko naji muryarsa ba,inajin wani bangare na zuciyata ya dade da kamuwa da soyayyarsa"...kada kafa ramlah tayi tai wani murmushi....
A kofar gidan driver yayi parking da ita daidai gilmawar bilal daga cikin gidan tana iya hango gefen fuskarsa,tambayar kanta afee tayi kamar yaya bilal...bude mota tayi ta fito tana kokarin tai sauri ta cin masa,saidai ta tada motarsa yayi gaba memakon yayi kwana ya biyo ta inda suka shigo sai taga yabi ta saman layin,ajiyar zuciya ta sauke ta koma tana kokarin yiwa driver magana "kazo bayan magriba ka daukeni "
"Owk afnan"driver yace yana jinjina mata kai yarinya karama mai halin dattako irin na manya,kaf Yan uwanta Babu Wanda ya kaita hankali...karasawa tayi kofar ta tura sai taga ta bude ta shige kawai me gadin yana can cikin dakinsa ma....
Hawaye ke sauka a idon jiddah lokacin da afee ta turo kofar da sallamarta cike da faraa ta bude baki "Anty..jid...."turus tayi tana kallon jiddah da hawaye ya wankewa fuska ta juya ta kalli ramlah dake gefenta,ta kalli jiddah ta kalli Ramlah Tana tsaye gabanta na faduwa kallom tuhuma takewa Ramlah mai hade da tsana,haka kawai taji jikinta be bata ba nan da nan fuskar Ramlah tayi bakinkirin a idonta... cikin sauri jiddah ta goge hawayenta ta fad'ad'a faraarta "iyyeeee yan matan anty jiddah ce a gidan?afee tawa zuwa babu notice Babu sanarwa yanzun da kinzo bana nan fa?"
Karasowa tayi tana faraa mai kama da yake ta bude hannuwanta "oyoyo Antyna i miss u"cikin farin ciki jiddah ta rungume afee suna dariya,wani bakin ciki ne ya lullube Ramlah hade da kishi kenan tana shiri da afee tunda gashi tazo gidan harda wani oyoyo cikin farin ciki, hakan na nufin sauran ne basu damu da lamatin jiddar ba,kwafa tayi karaf a kunnen afnan ta kalleta ta kafeta da ido kafin jiddah ta katse mata hanzari "afee babu gaisuwa bakiga anty ramlahki ba?"
Dan yake afee tayi ta jefar da jajarta da gyalenta wata maroon doguwar rigace jikinta me stones ta yane kanta da gyale "naganta anty jiddah...ai itama batai murna da ganina ba"tana sane tayi maganar ta nemi kujerata fada ta kwanta,
"Nayi murna da ganinki afnan banajin dadin jikina ne,na biyo inga besty na kwana biyu banganta ba kinsan jini da hanta"tai maganar tana ruko hannun jiddah dake faman musu dariya,
Tabe baki afee tayi,wai besty bestynki jininki kike yawo da mijinta cikin mota saboda rashin hankali da salon cin amana ni banma yarda dake ba,a zahiri ko dariya tayi "tou na huce Anty ramlah ina yini"
Mikewa ramlah tayi "nima bazan amsa ba kizo gida ki gaisheni sai in amsa bana cin mike"tayi maganar tana kokarin rataya jaka "ya naga kina rataya jaka ramly ina zuwa?"
Yatsina fuska tayi "gida...kinsan nace miki fa banida lafiya,yanzun ma a office wajen oganki na nemi permission dakyar ya bani saida nasha lallashi da lallaba sanan ya amince mun"kallon kwayar idon jiddah tayi tana maganar,take ta hango wani yanayi nan da nan jiddah ta nuna a fuska,murmushin keta ramlah tayi "kinga ko bayazo gida ya sameni ba gidansa bayan nayi karyar ciwo,kinga bazai sake yarda dani ba don ban saniba ko zai zagayo soyayya"cike da zolaya da iskanci take maganar,tabe baki jiddah tayi zuciyarta batai mata dadi ba furucin da ramly tayi wani miyau ta hadiya nan da nan taji kishi "haka ne ramly ok tou muje in rakaki"
"Ba saikin rakani ba ko kin manta kinada bakuwa gata nan kwance?kiyi mata abincin kawai kuci tunda mu muntafi"tayi maganar tana tafiya...daga mata hannu ramlah tayi "sai munyi magana tawan akwai labarai"
Dan zaro ido jiddah tayi cike da yarda "sure?ok till we chat"ta gyada mata kai ta fice...
Cikin zafin nama afee ta mike daga kwancen da tayi tai lamo zuciyarta na mata suya na abinda Ramlah tace "ke ko Anty jiddah kina ina kawarki zata kwace miki miji?"
Gaban jiddah ya yanke ya fadi"ban ganeba waye zai kwacemun miji wacece kawata"cikin sarkewa tayi maganar,
Murmushi mai ciwo afee tayi "tou nidai ban yarda da wanan kawar taki ba ramlah don tana yawo da mijinki a gaban mota"
Ajiyar zuciya jiddah ta sauke tayi murmushi "ehh yana dakkota ya ajiyeta a hanyar gidansu kinsan wajen aikinsu daya da yayanku"
Harara afee ta watsawa jiddah har saida taji bataji dadin kallon da tai mata ba koba komi antynta ce matar yayansu "tou tare sukazo gidan mu jiya da yaya Abdallah wai tazo fitsari har ta kawowa su meenah turare dani kaina ta kawo mana,kinga kenan tasan da zuwan gidan tunda tayo guzurin turare ba fitsarin ya kawota ba"
Bugun zuciyar jiddah ne ya tsananta nan da nan gumi ya Shiga karyo mata ta ko ina...maganar afee ke mata yawo a kunne kina ina zaa kwace miki miji,wani irin kwace miji ta yaya ramly zata kwace mata miji bayan mijinta nata ne ita kadai?na tabbatar Abdallah bazai taba bawa Ramlah fuskar da zaisa ma yaji yana sonta ba babu wanan a tsakaninsu,...tou meye nata na bawa su afee turare?kuma fitsari taje gidan...shiru tayi tana tunani,yayinda afee ta tsareta da ido tana kokarin gano wani abu a fuskarta....
********
Kwantar da kai Abdallah yayi ya rasa abinda ke damuns zuciyarsa cunkushe take da tunani kala kala,babu wanda zai basa shawara face Bilal amininsa dikda bakomi bane yake fadawa bilal din daya shafesa,amma harga Allah jiddah ta bata masa rai yau, tunda yake be taba fitowa gida zuwa office a burkice ba sai yau data kwanta tana barci,saboda kwana da takeyi daddana waya har yakai ta barsa da yunwa ya fito beci komi ba sai Ramlah ce ta damu dashi take tsan masa abincinta,yarinyar da yake wulakantata baya bata fuska dik saboda kada wani abu ya shiga tsakaninsa da ita har ya zama na cin amana,amma dik yadda yake kokarin kare mutuncinta yake neman mata abinda zai ginata a rayuwa dik bata gani take masa wadanan kananan iskancin...runtse idonsa yayi yana matuwar son matarsa amma wadanan canjin da ta tsiro dasu da wasu halaye suna jefasa cikin garari,jiya yana lura da ita koda yake biya mata bukatarta sam hankalinta baya wajensa,yana wani waje daban sai wani cika take tana batsewa kamar dole,...kullum Ramlah neman hanyar da zata kusanta kanta dashi take amma ita tana neman hanyar da zata nisanta kanta da shi, Allah sarki ramlah da tana nan da yanzun ta shigo office dinsa yafi sau biyar koda bazai mata magana ba koya jikinta oho....turo kofar da akayi ne yasa ya bude idanuwansa a hankali kamshn turaren bilal ya bugi hancinsa,a hankali ya dago kansa da jajayen idanuwansa da suka kankance...
"Welcome my man"yace a dusashe,
Shigowa bilal yayi ya nemi kujera ya zauna ya mika masa hannu suka tafa suka gaisa "ya na ganka haka ranka ya dade,meyake faruwa dakaine hakan?"
Ajiyar zuciya Abdallah yayi,shiru yayi yai jimmmm yana tunani "babukomi halin mata ne ya motsa wallahi,sam jiddah bata kyautamun horo takemun akan rashin bata lokacina sam takasa gane muhimmancin aikina wallahi, saita rinka ganin kamar aikin ya fita muhimmanci kuma wallahi ina sonta ina son in canja itace batasan yadda zata canja nin ba"yayi maganar a kausashe cike da damuwa da sanyin jiki....
Tsura masa ido Bilal yayi kafin daga bisani ya girgiza kai "kayi hakuri Abdallah amma kaima baka kyauta ba kuma kayi kuskure babba"
Cikin rashin fahimta yake kallon bilal din batare da yace wani abuba,da alama karin bayani yakeso"ehh kayi kuskure domin kuwa ko wace mace tana son kulawa da soyayya kai kuma aikinka yafi komi muhimmanci a wajenka"
Tabe baki Abdallah yayi "inda bana sonta bazan aure ta ba,wace soyayya kuma zan nuna mata bayan wacce nakeyi mata tunda har na aureta?koka manta cewar akwai yan matan da sukesona na kisu na aureta?sanan kacemun wai bana nuna mata kulawa da soyayya,inayi mata badai ta da godiyar Allah ne kuma batasan yadda zata zauna daniba,fine....ita ta jiyo ni yadda zan rayu cikin farin ciki nake planing she shoul keep on doing what shes doing nibanida matsala...ina cida ita ina mata sutura ina mata komo den what again"zuwa wanan lokacin Abdallah ya tunzura cikin daga murya yake magabar,girgiza kai bilal yayi lallai akwai matsala dole jiddah ta nemi me sata farin ciki a hakan yana hango soyayyar jiddah a idon Abdallah yana sonta tunda abubuwan da takeyi ya damesa amma yana yaudarar kansa zuciyarsa na gab da bugawa don tabbas yayi kuskuren rasa ta shi zai aureta ya nuna mata soyayyar da ta rasa kuma ko zai mutu kuwa saidai hakan ya kawo sanadiyyar rabuwarsu...
"Ka gayyatoni nazo wajenka ne ka daga mun murya kaimun masifa kamar danka?koko jiddar ce anan wajen da kake wanan zaburar?inace maslaha da shawara kake bukata yasa ka kirani?baka bani damar baka ba kake cika kana batsewa kana dagamun murya?ko ka manta waye bilal?ni banason hakan"
"Baka d niyyar bani shawara ai tunda kana neman hanyar goyon bayanta bayan har yau baka santa ba baku hadu ba,ni karka fadamin abinda zai karamin bacin rai cikin Wanda nake ciki"
Zuwa wanan lokacin bilal ya zucuya ya mike don babu abinda ya tsana irin a rinka gasa mai magana ana daga masa murya,"tunda haka ne kada kasake nemana akan matsalarka da matarka idan wani abu ne da be shafi matarka ba zaka iya kirana amma bazan dauki ka rinka daga mun murya ba ka gane ko?"shi kansa ya zuciya,
Ficewa yayi ya rufo kofar office din,jikin Abdallah yayi sanyi meyasa yayiwa aminin nasa haka?bayan shi ya nemesa saidai baxai iya ajiye aikinsa da activities dinsa ya tsaya lallashin mace ba kamar itace zata nema masa kudin da zai gina feature dinsa, indai akan jiddah ne bazai kara nemansa ba zai share maganar zai barta da halinta,sanan zaiyi kokarin rinka sakewa ramlah ko yayane tunda itama tanada tarbiyya kamar jiddah....dafe kansa yayi zuciyarsa na tafarfasa kamar zata fasa kirjinsa ta fito.....
Gudu yake a titi cike da bakin ciki bilal minti minti yakan ja tsaki,lallai Abdallah shine musababin jefa jiddah cikin wanan halin da suka tsinci kansu kuma da alama tana sonsa yana gane tana shiga damuwa da tunanin mijinta dik sanda suke tare.... Abdallah zai sha mamaki idan haka ne yanzun ya soma son jiddah kuma zai cigaba da faranta mata har zuwa lokacin da zai kwaceta ya mallaketa be cire rai ba....
Abdallah kuwa takaddu ya soma tattarawa bayajin zai iya cigaba da aikin idan yaje gida ya cigaba zaiyi aikin komi dare amma yanzun zucuyarsa batai masa dadi,cire laptop yayi jikin carji yasa a jakar laptop din ya rataya,kallon basket din ramlah yayi yaja tsaki ya tafi dashi gida ne ko ya barsa idan tazo gobe ta tafi dashi?amma kuma kwanikan zasu bushe dauka yayi bari inje gidan hajiya daganan in biya gidansu inbata abinta....
******
Parking yayi a parking lot ya fito, zuciyarsa bata masa dadi haka suka gaisa da shuaibu driver ya wuce cikin gida...da meenah yayi karo tana sanye da wando ya matseta iya gwiwa kanta babu dankwali da waya a kunne "ke meye haka uban me kike a nan a haka?"cikin tsawa yayi maganar da meenah ta razana jikinta na rawa ta datse wayar ta kwasa da gudu tayi cikin gida yana biye da ita a guje ta shiga parlorn idonta furi furi "meye haka ke kika kwaso a guje?"hajiya na zaune da wata mata suna dan kama d ita daga gani kanwarta ce,
Da sallamarsa ya shigo "ohh kingani hajiya bintu Ashe yayansu ne ya wartako ta shine ta shigo a haka a guje"ya dariya hajiya bintu tayi,
Tsugunnawa Abdallah yayi "ina yini momy bintu"
"Lafiya lau Abdallah an taso aikin?"
"Ehh"
"Ummah Ina wuni?barka da yamma"
"Lafiya lau,barkanka,antaso?"
"Ehh"yace ya mike yana kokarin zama kujera "ina abokiyar aikin naka ramlah yau batazo ba bata biyoka ba?"
Gabansa ya fadi kardai halin kirki da ramlah tayiwa ummah yasa har take tambayarta abinda tunda yake bata taba tambayar jiddah ba "ehh bamu tare,tazo ta tafi gida saboda bata jin dadi"
"Ayya allah sarki yar kirki Allah ya sauwake,ai saikaje ka gaidata ko bakomi abokiyar aikinka ce"
Jimmmm Abdallah yayi bece komiba ya sunkuyar da kai,yanzun gashi har hajiyarsa tana damuwa d Ramlah saboda halinta na damuwa d mutane da rashin fushi,itako kullum complain batayin abinda ummah zata sota....kusan minti goma sanan ya mike "zan wuce momy da ummah"
"Tou saida safe a gaida gida"
Hajiya bintu tana faraa tace "a gaida jiddah nayi fushi batazo ba"
Jinjina kai yayi yana cigaba da tafiya....
"Hajiya wacece abokiyar aikin Abdallah kuma?"hajiya bintu tai tambayar,
"Wata yar kirki ce har nan sunzo da jiddar,kawarta ce kuma tare suke aiki da Abdallah,yarinyar akwai hankali da tarbiyya nida aurenta zaiyi ma har sadaka sai nayi"
"Haba hajiya keko har yanzun kiyayyar yarnan tana ranki?ita wanan din kinsan halinta na boye?ban bada goyon baya ba"
"Bazan taba son jiddah ba,tunda tun farko ba son auren nake ba,wanan din ma bawai zance ya aureta bane idan har yace zai aureta ne zan amince"
"Tou allah ya kyauta,yamma tayi bari in koma ni nabaro yara"
Tare suka mike suka nufi hanyar fita ....
*******
Kwance take a kujera ta shiga Instagram tana duba posts ta shiga na Abdallah tana kallon posts dinsa,shiga tayi followers dinsa tayi tozali da sunan bilal...zaro ido ramlah tayi tou kodai Abdallah yasan bilal ne?kodai yasan kwarton matarsa ne?..murmushi ne ya subuce mata call din Abdallah taga ya shigo gabanta ya yanke ya fadi ta zaro ido mamaki ne ya kasheta Abdallah ke kiranta a waya da kansa?kallon call din tayi bugun zuciyarta ya tsananta rufe idanuwanta tayi wani dadi ne ko farin ciki da sauri ta bude ta danna recieve cikin siririyar murya tace "assalamu alaikum"
"Waalaikumussalam...ina kofar gidan ku dan fito"yana fadin haka ya datse wayar ji tayi kamar an soka mata mashi mutuwar zaune tayi Abdallah a gidan mu?ta kwalla wata kara da mahaifiyarta ta fado dakin a guje "lafiya dai ramlah?"
"Wayyoo Allah dadi"ta fada cike da farin ciki....
Jiddah kuwa kallon afee takeyi yadda take magana cike da hikima amma bata gasgata cewar Ramlah zata iya auren mata miji ko ta rabata da mijinta ba.......
*SLIMZY*....meson izzata complete ko zainul abideen 08166177830
[11/5, 7:31 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
_Sakon gaisuwa da fatan alheri gareku:_
*SLIMZY FANS GROUP*
*SLIMZY NOVELLAS GROUP*
*SLIMZY HOUSE OF NOVELS*
*MRS OMAR HOUSA NOVELS*
*AUREN FARI FANS GROUP*
*JIDDAH HOUSA NOVELS*
*RUBUTACCIYAR KADDARA FANS*
*ZAUREN HASKE* *WRITERS*
*da sauran groups din da ban kira sunansu ba da wadanda suke aikomin da sako na jinjina da yabo slimzy na godiya....ina kaunarku fisabilillahi😫❤😍*
*12*
Cikin sauri ramlah ta karasa gaban madubi tana kallon kanta,babu makeup a fuskarta amma yadda fuskarta tayi ita kanta tayiwa kanta kyau nan da nan ta warware gashinta ta gyara parking kananan kalaba dake kanta tabar guda ta gefen fuskarta,powder ta shafa da lipgloss,ta gyara girarta cikin mintuna da basu wuce biyar ba,can gefen gado ta hango bakin gyalenta ta dauka ta yane kanta har zata fita tadawo ta feshe jikinta da turare,
Karar bude kofarta yasa duka suka juya da dubansu gareta har ummahnta kallon yar tata takeyi "ina zuwa kuma ramlatu da yamman nan?"
Farrr tayi da manyan fararen idanuwanta "ummah bako nayi a waje ina zuwa,idan na dawo zanyi miki bayanin komi"bata jira cewar ummah ba ta fice suka bi ta da kallo....
Key yayiwa motarsa yana son tafiya kusan minti goma bata fito ba to me takeyi mtsww yaja tsaki,hangota yasa ya dakata,fuskarta sai sheki takeyi ga wani annuri dake fita kallonta yayo sau daya ya kauda kansa har ta karaso, gefensa ta tsaya mazunin driver daga waje "ina yini sir Abdallah...fatan kana lafiya"..jinjina kai yayi ya ja numfashi ya furzar yana shakan kamshin turaren ta,"lafiya lau...ya jikin?"a takaice yayi tambayar hade da kallonta cikin wani yanayi,
Take Ramlah ta fahimci yana cikin wani yanayi me kama da damuwa don haka ta nisa cike da kissa "lafiya lau saidai inata kewar aikina yau kawai banji dadi ba baroka da nayi da ayyuka fatan dai kasamu gamawa batare da wata matsala ba"
Jinjina mata kai yayi "ehh na gama"...hannunsa yakai kujerar dake gefensa inda ya ajiye basket ya dauko "ga basket dinki thank you soo much"
Hannu tasa ta karba harda dan durkusawa tana karewa fuskarsa kallo wata soyayyarsa kw fuzgarta "ammm...sir nace ba"
"Umhmmm ina sauraronki ya dai"muryarsa a dasashe yayi maganar "nace na lura kamar kana cikin wani yanayi na damuwa na gano hakan ne a fuskarka da kwayan idonka,ina iya hango bacin rai karara a fuskarka"
Da sauri ya juyo ya zuba mata narkakkun idanuwansa da sukayi jajir,itama shi take kallo cikin wani salo da daukar hankali take kallon nasa,shiko mamakin yadda ta gano yana cikin damuwa da bacin rai yasa yake kallonta,har yaushe suka kebe ko sukai dadewar da zatasan bacin ransa da damuwarsa? sabanin matarsa da kullum suna cikin gida tare batasan damuwarsa ba bata duba yanayin da ya shigo gida dashi saidai ta hau complain...hmmmm yau zai gwadata ya gani tunda har kawarta tasan damuwarsa,
Cije lebe yayi ya girgiza kai "babu komi ramlah, Allah ya sauwake,idan baki samu damar zuwa ba goben ki huta sai monday"
Gabanta ne ya fadi jin ya ambaci monday anya zata iya hakuri da rashin ganinsa har zuwa monday kuwa?ina hakan bazai ma yuwu ba "ai nasha magani anyimun allura insha allahu zanyi kokarim zuwa kodan in tallafa maka goben"
"Owk,babu laifi take care"ya tada motarsa ta dan ja baya tana kallonsa "nagode sir Abdallah Allah ya kara girma"
Jinjina mata kai yayi yaja motarsa yayi ribas yana kokarin barin unguwar tana tsaye tana binsa da kallo...murmushi ne ya subuce mata "akwai kamshin nasara,nakai mataki na farko na mallakar Abdallah"ta furta a fili ta juya rike da basket din take takun ta daidai mai kama da yanga.....
Labulen parlorn ta yaye ta shigo bakinta dauke da sallama,ganinta cike da annuri yasa kanwarta fadin "Anty Ramla kinganki kuwa daga ganinki kina cikin farin ciki kinsamo mana yaya ne?cant wait...nida ummah mamakin yadda mukaga anzo wajenki mukeyi tun fitarki muke magana"ta kara tsalle ta zauna cike da murna dan harararta ramlah tayi "tou azarbabi harda you cant wait ko you cant wait for what?"ta harareta,
Ummah ta amshe zancen"nidai nakosa aimun bayani don na kagara,yau ramlah ta wani yazo yayi sallama a waje ta fita?batare da ta koresa ba?na dauka ma mus'ab ne yazo ai kun daidaita kin amince yasa kika fita"
Turo baki kadan tayi "ba mus'ab bane ummah Abdallah ne mijin jiddah fa yazo...wai kinsan me hmmm jiddah fa ta dage sai Abdallah ya aureni shine harda turosa yazo duba jikina"
Zaro ido ummah tayi "ke ramlatu jiddah kanta daya kuwa?shine zatace ki auri mijinta?tou ita ai baa haka sai tayi miki adduar kema allah ya fito miki da naki nidai inaga da kamar uwa hada miji da kawa"
Mikewa ramlah tayi "ummah to akan hakan har fushi tayi dani shine kikaga da yazo na fita munyi magana nidai idan nasamu mijina aurena zanyi bazan auri mijinta ba"tana gama maganar ta nufi kitchen da basket din a hannunta....
Gyara zama sosai kanwar ramlah tayi "ummah dik yanayinki ya canja,meyasa?don yaayah ramlah ta fada miki abinda anty jiddah tace"ta tabe baki,
"Abun da kamar wuya ne nana"
Fitowa ramlah tayi daga kitchen da plate din abinci ta nemi waje ta zauna "wai ina sauran yaran gidan ne ummah"
"Sunje lesson suna hanyar shigowa"bata rufe baki ba ta jiyo hayaniya"gasunan ma"
********
Girgiza kai kawai afee tayi don tasan jiddah bazata taba yadda da maganarta ba sai kawai ta kauda maganar cike da bakin ciki "anty jiddah mijinki na gab da dawowa tashi mu shiga kitchen...ko kuma me zan dafa muku me sauki ki shiga kiyi wanka kafin nan na dora girkin"
Ajiyar zuciya jiddah ta sauke "kome ma ki dafa afee bari in shiga inyi wanka tun safe a hankan nake"
Mikewarta keda wuya Abdallah ya bude kofar dakin "Assalamu alaikum"ciki ciki yayi sallamar,afee da faraarta ta amsa sabanin jiddah da tabisa da kallo har ya tube takalminsa,"barka da zuwa"tace murya a shake,kallonta yayi ya kauda kai sai kuma suka hada ido da afee hakan yasa ya dan saki fuskarsa "Afnan ashe kina nan shiyasa banganki a gidan ummah ba ko?"
"Laaa ka biya gidan ummah ne,aiko ina nan tun rana nan na wuni yaya"
Neman waje yayi ya zauna itako jiddah kallo take binsa dashi kamar mutum mutumi....kujerar da Bilal ya zauna dazun nan Abdallah ya zauna,kamshin turaren Bilal ya bugi hancinsa,dan yatsina fuska yayi yana waige waige..."yadai yaya"cewar afee,
Girgiza kai yayi "kawomin ruwa afnan"yace yana cire suit din sa,
Wani sabom salo Abdallah ya dawo dashi tana masa sannu da zuwa ma kamar tana takurasa,ji yadda yake daura fuska kamar anyi masa wani abu,hmmm dik take takensa na kada ta bukaci lokacinsa ne idan haka ne ya makara don ta dade da watsi da wanan bukatar dik yadda takai ga sonsa kuwa,..batace komiba ta wuce ciki,
Bin bayanta yayi da kallo ya girgiza kai,ji yadda ta tsaya masa kamar gunki babu ko ya aiki balle ta lura da yanayin nasa, shin meke damun jiddah ne?ajiyar zuciya ya sauke ya furzar da iska daga bakinsa,yana son matarsa amma sababbin halaye data bullo dashi ne be gane musu ba,sanan ita batasan yadda zatayi masa magana cikin kwanciyar hankali ba saidai daga yayi magana taji haushi,ko baa fada masa ba yasan wucewar nan da tayi haushi taji mtswww yaja tsaki,
Tray afee ta dire masa na cup da gorar ruwa faro mai sanyi "bari in shiga kitchen yau girki na zakuci kaida Anty jiddah"
"Allah yasa dai kin iya"yace cikin sigar tsokana amma fuskarsa a murtuke,..sabo da hali irin nasa tasan tsokanarta yake yasa tayi dariya"kadam ba nafi Anty jiddah iyawa ba"ta wuce tana dariya shima murmushi yayi yana tsiyaya ruwa a cup.....
Sosai yasha ruwan sanan ya mike ya nufi bedroom dinsa,
Cakkk ya tsaya mamaki ne ya lullubesa,ganin yadda ya fita ya bari haka ya tarar,meya samu jiddah ne haka?abinda batayi shine ta tsuro dashi yanzun...be gama tunani ba ta shigo dakin da sallama daure da towel,
Wucesa tayi ta ajiye kaskon turaren wuta mai kamshin gaske akan madubi sanan ta shiga gyara gaban madubin ta dawo kan gadon yana satar kallonta,ko kallonsa batayi ba aikinta kawai takeyi....
Dagashi sai boxer ya fito toilet lokacin ta gama gyaran gadon tana shirin fita ya kira sunanta "jiddah"...tsayawa tayi ta juyar da kai nan da nan idonta yayi kwal kwal kamar zatayi kuka "amma kinsan kinyimun laifi ko?"
Gabanta ne ya fadi, batace komi ba sai kara juyar da kai da tayi har ya karaso gabanta,"baki tambayeni laifin da kikaimun ba"
Dakyar ta tattaro natsuwarta ta hadiyi wani miyau me daci cike da takaici "laifin me nayi maka"muryarta na rawa ta tambayesa,
"Yau haka na fita babu breakfast,..sanan yanzun na shigo gida dubi irin karbar da kikaimun kamar ba mijinki ba ne ya dawo"
"Ohhh...sorry...na dauka baka bukatar tarba ta ai, saboda ai bakada lokacina baka da lokacin soyayyata shiyasa na janye jikina na kama mutuncina daga gareka lokacin da kake bukatata hanya a bude take zaka iya nema..."tayi maganar kwalla na zubo mata ta share,yana tsaye a gabanta ta ratsa ta gefensa ta wuce,
Wani kululum bakin ciki ne ya tokare masa wuya,lallai jiddah ta tabbata batasan darajar miji ba batasan me ake kira aure ba,wai shin goyata takeson ya rinkayi?...harda cewa wai ta kama mutuncinta?tasan me wanan kalmar ke nufi?kamar wadda ba zaman aure sukeyi ba?mata nawa ne suke mallakar zuciyoyin mazajensu ta hanyar mika kansu da nuna musu soyayya da tarairaya?da haka har su samu abinda sukeso ita bata iyaba sai jiran tasamu soyayya daga gareshi daga sama...lallai wanan tace wani abu,kawarki tana nan tana neman shiga a wajena amma ke kina haukar banza aiko zan shayar dake mamaki jiddah....idan haka ne ramlah itace macen data dace dani me irin halinta na hakuri da juriya ba ke ba.....bude drawer yayi ya ciro jallabiyarsa ya zura ya fito ya nufi masallaci....
Fadawa tayi kan gano ta fashe da kuka mai ciwo,inama ace Bilal shine mijina ba kaiba?gashi sanadiyyar wanan halin ko in kula da kake nunamin yasa ka jefani cikin soyayyar da ban shirya ba ka jefa rayuwata cikin bata da halaka....hawaye kawai ke ambaliya a fuskarta cikin kunar rai ta ke neman wayarta ta kira bilal taji muryarsa ko zata samu sassauci.....
********
Tun shigowarsa ya kwanta a doguwar kujera a parlorn mahaifiyarsa,ya dora pillow a fuskarsa,ba bacci yake ba saidai yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da wutar kaunar jiddah,ta wani bangaren kuma mugun takaicin Abdallah ne cunkushe cikin zuciyarsa,ta yaya Abdallah zai rinka cutar da yarinya kuma ana kokarin fada masa gaskiya ya rinka masa tsawa, Abdallah yasani babu abinda ya tsana sama da hakan,amma zai nuna masa kuskurensa,
Ta dade tsaye akansa tana kallonsa,sam ta rasa Gane kan bilal kwana biyun na gashi yadda ya yawaita muamala da waya, Allah yasa dai matar aure yasamo mata itama tasamu suruka amma yau kuma sai taga tankar yana cikin damuwa,
Takowa tayi ta karaso kusa da kujerar ta sunkuya ta bubbuga gefen kujerar "bilal bakajin kiran sallah ne?tun dazun ake kira kana kwance kuma kasan babu kyau baccin goshin magriba,a tashi ayi sallah azo aci abinci sai a kwanta kafin sallahr isha'i idan baccin kakeso"..dik maganar da takeyi be motsa ba saida ta sake kiran sunansa a karo na biyu"bilal"...ture pillow din yayi idonsa a rufe,a hankali ya bude idonsa da sukai jajir kamar gauta,
"Subhanallahi...bilal lafiya?"sai kawai ya dafe kansa da yaji wani abu kamar an sara masa gatari..."kai na momy"
"Subhanallahi...ciwon kan naka ne ya motsa?..bilal menene yake faruwa ne?naga tun shigowarka ka kwanta a nan kuma da alama bakada lafiya"
Jinjina mata kai yayi "raina ne ya baci momy,samm zuciyata tafarfasa takeyi gashi ciwona na kokarin tashi"dakyar yake maganar harshensa ya masa nauyi,zuciyarsa kanta tayi masa nauyi...ga soyayyar jiddah data mamaye masa zuciya...
"Innalillahi wa innah ilaihi rajiun...abinda nafi gudu kenan Bilal,gashi tunda mahaifinka ya bi mahaifin amininka Abdallah London ka daina zuwa company saidai kullum ka shirya ka fita ka dawo baka zuwa ka duba abinda ke faruwa can zai gamu dakai kasani bilal...gashi dazun hajiyar Abdallah ta kirani take shedamun zasu dawo gobe,amma basu fadaba suprise sukeson muku"...dik maganar da takeyi hannunsa na dafe da kansa
Abdallah kuwa daga masallaci gidansu bilal yayo da dan acaba, beko dauko motarsa ba,yasan bazai iya hakuri ya kwana suna fushi da juna ba,...wayarsa ya zaro a aljihu ya danna kiran bilal din...
Wayarsa ce tayi kara yana dagowa yaga Abdallah ne ya kife wayar,momy na gefensa"ka dauki wayar mana kayi kokari kaje kayi sallah,kafin nan zuhura sun karasa abinci"...jijina mata kai yayi,
Kusan a tare jiddah ke kiran bilal...number busy tun tuni ta kasa samunsa,to dawa yake waya haka?tayi mamakin da wayarsa taki shiga call waiting sai number busy....kife wayar tayi ta kwantar da kai...afee ta turo kofa "Anty....meke faruwa?har yanzun baki shirya ba gashi ya Abdallah daga zuwa masallaci shiru"...boye fuskarta jiddah tayi gudun kada afee ta hango hawaye a fuskarta...
"Nasan halin zuciya irin ta bilal,nasan yana ganin call Dina yaki picking"mtsww yaja tsaki kawai ya kwankwasa gate din gidan me gadi ya bude masa suka gaisa cike da girmamawa ya shige...
Mikewa bilal yayi jiri na neman daukarsa kenan Abdallah yayi sallama,.."yauwa Abdallah sannu da zuwa"
"Sannu momy ina yini"Abdallah ya durkusa cike da girmamawa kansa a kasa yake gaida momy,
Wucesu bilal yayi ya nufi toilet din dake makale a parlorn, Abdallah ya bisa da kallo yana girgiza kai,take momy ta fahimci sunyi fada...murmushi tayi tasan zaa rina dama inhar bilal da Abdallah sukai fada tun suna yara to basu da sukuni sarkim zuciya bilal har ciwo yakeyi,tasan zasu shirya yasa tace "Abdallah zauna bari zuhra ta kawo lemo ko?"tayi gaba,
A parlor ya shimfida dadduma ya tada sallah Abdallah na zaune har ya idar,suna hada ido bilal ya watsa masa harara "kazo ne nan din ma ka dagamun murya kaimun tsawa kamar yadda kayi dazun?aida baka nemeni ba kagani idan ni zan nemeka"
Rike kunnuwa Abdallah yayi alamar ban hakuri batare da yace komi ba hakan yasa bilal yaja ajiyar zucuya "is ok ya wuce"..nan da nan kuma suka hau hira suna magana nan bilal ke shedawa Abdallah iyayensu zasu dawo zasu sauka a nigeria da yamma....sun dan dau lokaci kafin suka fito a tare dikda haka dishi dishi bilal ke gani kansa ciwo yake masa jiddah kawai yakeson gani yakeson jin muryarta amma babu damar hakan tunda Abdallah yana gida....makullin mota bilal yabawa Abdallah "kaje da motana kawai"
"Har yau kaki zuwa kaga jiddah ko?kaki zuwa kaga amaryata bilal ai fushi takeyi dakai"..lumshe ido bilal yayi "zanzo in wanke laifina"
"Idan bakazo bama gobe dai su Abbah zasu dawo don haka zamu hadu a airport wajen taryarsu shikenan sai ka ganta anan kaga kaji kunya"girgiza kai bilal yayi "what time"
"Ni inaga gida zataje wajensu ummah su dunguma saimu hadu dasu a can airport din zan taho daga aiki nasan six zasu sauka"...tada motar yayi ya daga masa hannu....
******
Afee ta shirya tsaf shuaibu driver ma yazo a kofar gida,yayan nata take jira tana zaune jiddah na gefe sanye da kananan kaya sun amsheta sosai rigace pink da blue jeans da ya kamata da kwalliya gabansa kanta babu dankwali..."yauwa Anty ga yayah nan niba sai ya shigo ba zan fita tunda shuaibu na waje,saiki shirya gobe zamuje airport tarar su abbah zasu dawo harda dadynsu zuhra kanwar aminin ya Abdallah kimsan saboda amintar su yayan mu yasa iyaye suma suke aminta"jinjina mata kai tayi "tou afee a gaida ummah dasu rumaisa nagode sai nazo goben".. Abdallah ne ya shigo yaji jiddah na wanan maganar yasan to afee taji dawowar abbah,..."yaya saida safe"
"Ku shirya da wuri zakuje ai muku passport na tafiya saudiyya,sanan da yamma zaa taryar su abbah"
"Ok saida safe"ta dagawa jiddah hannu, itama daga mata tayi... ranta babu dadi sambatason tafiyar nan zuwa airport dasu ummah inba saa akaiba sai ummah ta wulakanta ta,saidai zataje ne don tasan in bataje ba Abbah zaiyi fushi da ita,kuma bazaiji dadi ba yadda yake sonta yake ji da ita....
Beko karasa shigowa parlorn ba wayarsa ta shiga kara yana dubawa ramlah ce, saida ya kalli sashen jiddah sanan ya kara wayar a kunne yana kokarin zama.."yadai...ya jikin naki?hope kinsamu sauki"
Lumshe ido ramlah tayi "ehh da sauki...ya kaje gida?hope ka isa lafiya ..ya jiddah'
"Lafiya lau,na iso lafiya...sorry allah ya kara lafiya"yace a takaice,
"Ameen...hope ka daina bacin ran da naganka ciki dazun,inata tunani gashi banida hurumin da zan kwantar maka da hankali sai matarka"...hmmm yace cikin zuciyarsa,bata iyaba sai batamun rai da rashin godiyar Allah...a zahiri kuma lumshe ido yayi yadda take masa magana yasa yadanji relief "alhamdulillahi ya wuce...nagode da kulawarki..kije allura and make sure u take ur drugs,good night"..dippp ya kashe wayar....
Kissing wayar ramlah tayi ta dora wayar a kirjinta tana sauke numfashi a hankali cikin wani irin yanayi mai cike da annuri....
Wayar ramlah ce tayi karar shigowar massage a WhatsApp da sauri ta bude ta shiga hoto ne aka turo tana budewa ta ja numfashi "yauwa secons evidence."hoton jiddah ne da bilal a wajen da suka fita kwana biyu daya wuce.... zooming din hoton tayi...ba karamin kyau sukayi ba sosai,hakan yasa ta furta "yesssss...yanzun zan bude sabon Instagram account in posting hoton nan sanan inyi following Abdallah"....wata zucuyarta haneta kada kiyi gaggawa Ramlah...kibari ki shiga gidan Abdallah sanan lokaci daya ki tarwatsa su...wani tunani ne ya fado mata tayi murmushi bari tabi wanan plan din da yasa tayi murnushi.....
Kuka jiddah ta fashe dashi,dama Abdallah neman mata yakeyi shiyasa yake kasa biya mata bukatarta da nuna mata soyayya yanada karuwa a waje?...da gudu ta nufi dakinta...
Wayarta tayi dialing wayar ramlah kuka ya kwace mata koda ramlah ta dauki wayar taji kukan jiddah wani farin ciki ne ya lullubeta tasan kukan na menene,nan da nan ta wasa wukarta da kalaman da zatayi amfani dasu wajen hargitsa komi....
"Ya akayi besty kukan me kikeyi dan allah kiyi shiru kin tadamun da hankali kifadamun damuwarki bakida wadda ta fini"
Kara rushewa da kuka jiddah tayi kishi ya turnuke ta ko gani batayi "besty... Abdallah ashe neman mata yakeyi watace yanzun ta kirasa"....murmushi ramlah tayi jiddah dakikiya ce ko ta mance ta sanar mata da tayi karyar ciwo ne tazo gidanta dazun?amma yanzun ta kasa gane itace ta kira...hmmmm
"Hmmm...tou banso fada miki bane,amma nasan komi,tausayi kike bani jiddah nasan komi tunda na soma aiki naganewa idona"..cikin rawar murya ramlah ke maganar kamar zatayi kuka,....hakan yasa jiddah kara haukacewa "ki fadamun komi besty karkiji komi ke yar uwatace ki fadamun wlhy yau bazan kwana gidan nan ba yaji zanyi gidan mu zani"
Kashe wayar ramlah tayi cikin kuka, hakan ya kara tadawa jiddah hankali,ta zabura kamar mahaukaciya ta nufi parlorn wajen Abdallah......
*SLIMZY✍🏻*
[11/5, 7:31 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(home of expert and perfect writers)*💡
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
*13*
Fuskarta sharkaf da hawaye ta fito daga bedroom idanuwanta sun kankance saboda tsananin kishin dake taso mata ji takeyi kamar ta shake masa wuya,tsaye tayi akansa hawaye na sauka a idonta kamar ruwa,shiko Abdallah abinda ke gabansa ya cigaba dayi ko kallonta beyi ba,"Abdallah,ashe cin amanata kakeyi a waje bansani ba?kana can waje kaida matan banza"
Da sauri ya dago kai ya watsa mata wata harara ,a haukace jiddah ta cigaba da magana "Allah ya isa tsakanina dakai tunda gani gaka a cikin gida amma babu abinda nake tsinana maka babu abinda kakemun saidai munzauna kamar hoto ashe akwai wadda take gamsar dakai karuwarka"....
Wani irin kallo ya watsa mata zuciyarsa na tafarfasa bayason abinda zaisa ya aikata abinda zaizo yana danasani daga baya,so far dik wanan maganganun da takeyi kishi ne,amma ai kishi ba hauka bane "kada kisake hadani da kalmar karuwa"
"Karya akaayi?ba karuwar bace?inba karuwa bace meyasa zata kiraka a waya kana tare da iyalinka?ko abinda kukeyi a waje be isheta bane take kiranka tayi kewarka?"
Zuwa wanan lokacin jikin Abdallah ya soma rawa zuciya kawai ke taso masa kalaman jiddah da take jifansa dashi tamkar Tana watsa masa rushin wuta,mikewa yayi tsaye yana nunata da dan yatsa "Ina gargadinki da ki iya bakinki idan ba haka ba"
"Idan ba haka ba me?mezakayimun ?ai nasan komi dik abinda kakeyi a tafin hannuna kakeyinsa Abdallah kuma Allah ya isa tsakanina dakai sai allah yasaka mun mugu azzalumi,saidai ka barni da shaawarka kamar zata kasheni bakada lokacina sai na matan banza"
A zuciye Abdallah ya shararawa jiddah mari biyu masu kyau gefe da gefen fuskarta wadanda saida taga giftawar taurari a idanuwanta,lokaci daya kunnuwanta sukayi dummmmm tamkar an zuba mata ruwa cikinsu....cakkkk tunaninta ya tsaya tana kallonsa ruwan hawaye kuwa sai ambaliya sukeyi daga idannuwanta hannuwanta biyu na dafe a kumatunta..."ka..mar.."bata karasa ba cikin kakkasar murya ya soma magana "an mareki jiddah...ke wacece da bazan mareki ba matukar bazaki fasa hadani da kalmar karuwa ba da matan banza ba a waje bazan fasa marinki ba saboda ni ba mazinaci bane,wawuya jahila wadda kishi ke kokarin jefata a halaka,kishinki na banza da bakisan yadda zakiyi ki janyo hankalin mijinki ba?ita wadda kike jifana da kalmar karuwa da ita a yanzun kokarin kusanta kanta dani take yayinda ke kike kokarin nisanta kanki dani,bakida hakuri kullum complain ke kenan kece akewa laifi ke baki laifi,idan bani da lokacinki ko bana kulawa dake ke bakisan kissar da zaki kusanta kanki danib"..cikin daga murya yake maganar muryarsa na amsawa a parlorn,jiddah kuwa ta kafesa da ido bugun zuciyarta na karuwa ji take kamar zata hadiyi zuciya ta mutu,
Taku daya biyu yayi ya juyo ya cigaba da magana "bakisan,kiganni cikin damuwa ko bacin rai kiyi kokarin faranta mun ba,bakisan ki jure kiyi hakuri da halayyat mijinki ba kiyi kokari wajen janyo hankalinsa gareki,mahaukaciya dabba ...tou kisani wanan abun da kikayi kin taka mataki na farko da zan auro mace in kawota cikin gidan nan koda banida niyyar hakan,domin a yanzun zuciyata tafara mun kokwanto akan tsantsar biyayyar da karuwar waje take nuna mun ke kuwa kina nan kina girman kai....kin kasa tarairayar mijinki,inaji a jikina a wanan tafiyar tabbas zan kusanto da ita gareni saboda ta cancanta,tasan farin cikina,tasan bacin raina tasan damuwata,dik wani mood nawa tasani jiddah....uwa uba tana hakuri da halayyata kullum burinta be wuce ta samu abinda zataja hankalina dashi ba dik yadda na kaiga rashin sakar mata fuska kuwa....mace mafi kusanci dake tasan mijinki fiye da ke"....ya watsa mata wani kallo mai cike da takaici sanan ya juya ya sunkuci laptop dinsa da wayoyinsa ya nufi bedroom dinsa kansa na sara masa saboda takaici,
Fadawa jiddah tayi kan kujera....maganganun Abdallah suna barazanar tarwatsa mata zuciya shikenan maganar Ramla ta tabbata Abdallah yanada budurwa...ta tabbata tana gini ne wata na warwarewa.... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...haka Abdallah zai mata, wani radadi ne a fuskarta tamkar ta kone takeji saboda zafin marin da yayi mata,
Yau Abdallah ya tabbatar mata da zai kawo mace cikin gidansa a matsayin mata ta biyu? Abdallah nata mai sonta yau shine ya kirata da mafi munin kalma a duniya?dik Wanda aka kira da dabba to tabbas hakan na nufin yaje last bus stop a ragshin hankali,dik wanda aka kira da dabba to ba karamin zagi akai masa ba, Abdallah nata?menayiwa Abdallah haka yayimun wanan hukuncin mai tsanani?soyayya da kauna sune sakamakonsu yazo da hakan?... toshe kunnuwanta tayi ta saki wata kara a parlorn ta sake fashewa da kuka....
K'arar da jiddah tayi ba karamin razana Abdallah tayi ba daga daki inda yake zaune a tsakiyar gado yasa hannu ya toshe kunnuwansa,cikin tsananin faduwar gaba yake sauraren kukanta a parlorn ji yakeyi kukanta tamkar tana watsa masa wuta a zuciya, Allah yasani yana son jiddah so mai tsanani amma zuciyarsa tafara karkata zuwa inda ake kyautata masa inda ake hakuri dashi,koba komi ramlah yarinya ce mai tarbiyya kuma marainiya idan har ya aureta yayi jihadi...amma ta yaya zai auro aminiyar jiddah ya kawo gidan sa?ba cin amana bane kuwa?...da sauri wata zucuyar tace saboda jiddah ita tabaka damar hakan, Kuma alamu sun gama bayyana da ramlah ta kamu da soyayyarka,kullum ramlah kokari take tasamu farin ciki sabanin jiddah da ta tsuro da wasu iskanci wanda besansu ba jiddah sai ta kai biyu na dare online,some times har muryarta yake jiyowa daga parlor....
Rufe laptop din yayi gabaki daya bashida kuzarin da zai cigaba da aikin da yakeyi,kan drawer ta gefen gado ya dora laptop din ya janyo pillow yasa a bayansa ya jingina, Haka kawai yakejin gumi na barko masa ta ko ina ,dora kansa yayi jikin bord din gado zuciyarsa na harbawa tamkar ta fasa kirjinsa ta fito.....shiru yayi yana tunani kala kala,har bacci ya daukesa,
Jiddah kuwa zazzabi ne mai zafin gaske ya lullubeta a parlorn nan da nan ta hau rawar sanyi ga sanyin Ac da fanka data mike da niyyar zuwa kashe AC da fanka sai taga duhu jiri na neman kada ita saita kwanta,haka ta kwanta a doguwar kujera 3 seater ta dunkule waje daya Tana sauke ajiyar zucuya har yanzun zafafan hawaye ne ke sauka a idanuwanta.... Allah sarki rayuwa yau Abdallah ne yayi mata haka?.... runtse ido tayi wani tukukin bakin ciki na taso mata a kirjinta ...
Juyi na farko Ramlah tayi idonta biyu, Haka kawai takeson sanin halin da jiddah ke ciki,kallon agogo tayi karfe biyu na dare,wayarta ta janyo ta kunna data ta shiga WhatsApp ,lalubo numberta tayi last seen dinta tun karfe takwas na dare,gabanta ya fadi kodai suna can tare da Abdallah suna soyayya?nan da nan bakim ciki ya lullubeta,umm umm Abdallah bazai taba soyayya da jiddah ba,nasan yanzun haka jiddah tana can tana kuka hmmmm jiddah kenan yanzun kika soma kuka tunda kika auri miji na kerewa saa irin mijin da nake mafarkin samu,burina bazai taba cika akanki ba saina shigo gidanki....kuma na tabbatar burina na gab da cika zanyi kwanan farin ciki tunda na shaki kamshin turaren Abdallah da yamman nan da yazo gareni.... bincike kuwa yanzun na soma yi tunda na soma gano bilal Abubakar maska aminin mijinki ne tabbas wanan video na kiss da taba nono sai yaje ga Abdallah bayan na shigo gidanki matukar kika nuna min wani iskanci to saina fiddake....kai jiddah baxan iya sharing Abdallah dake ba idan na shigo gidanki dole ki fita ki bani wuri domin Abdallah ba saan aurenki bane....murmushi ramlah tayi rai scrolling number bilal tana dubawa ta gansa online...tayi murmushi ta kashe data tasa hannu ta kashe wutar gefen gadonta ta kwanta....
3am
Bilal bacci ya kauracewa idanuwansa,babu abinda kukkensa keda muradi sama da jin daddadan muryar jiddah,ya saba da ita yana matukar sonta yanajin babu abinda zai rabasa da jiddah burinsa be wuce ya auri jiddah ba koda relationship din family's din su zai ruguje,tun yamma kansa ke masa ciwo damuwa tasa kansa ya tsananta ciwo idanuwansa sun soma rufewa ga wani zazzabi da yakeji tana taso masa yana kokarin rufesa,kaiwa da komowa yake a bedroom dinsa amma baya ganin gabansa haka ya nufi gaban madubi magungunan dake zube gaban madubinsa ya dauka ya ciro biyu ya bude fridge ya ciro gorar faro mai sanyi ya watsa maganin ya hadiya sanan ya fada kan gadon ya kifa ciki ya kwantar da kansa yanajin yadda bugun zuciyarsa ya sauya....
********
Da asuba ya tashi Abdallah,zucuyarsa batayi masa dadi sam be kyautawa jiddah ba marin da yayi mata amma ita taja hakan,jiki babu kwari ya sauko daga gado ya shiga toilet da niyyar alwala, sai kawai ya bude ruwan zafi ya sakarwa kansa ruwa mai zafin gaske yayi wanka ya gargasa jikinsa ya fito ya samu karfi,jallabiya ya zura yana jiyo kiran sallah a masallacin unguwarsu ya fito....da sauri yaja da baya ganin da yayi mata kwance a kujera ta dungule waje daya sai rawar sanyi takeyi,idanuwanta a rufe suke ya kalli kumatunta sun kumbura sosai ga shacin yatsusa a kumatunta,gabansa ya kara faduwa innahlillahi wa innah ilaihi rajiun meyasa yayi haka?da sauri ya karasa inda take,ya dade tsaye yana kallonta hawaye bushe a idanuwanta....hannunsa yasa ya taba gefen wuyanta da sauri ya dauke hannunsa kamar wanda shocking ya kamasa,jikinta yayi zafi sosai jin ana kokarin tada sallah a masallaci yasa ya kama hanya,ya fice,tana jiyo karar bude kofarsa, dik abinda yakeyi a kunnenta yakeyi wani haushinsa ne ya turnuketa dakyar ta mike ta zauna,wasu sababbin hawaye suka zuraro mata tasa hannu ta goge a hankali ta mike ta nufi bedroom dinta,tana shiga toilets ta fada ta fashe da kuka.
Koda ya dawo sallah be ganta ba a parlor sai kawai ya wuce bedroom dinta yana jiyo karar ruwa yasa yaja ajiyar zuciya ya fita kawai....
Wajen 7:39 ya gama shiri sa tsaf ya dade kamar zai shiga dakin sai kuma ya dau waya yayi mata massage "idan kinsamu dama ki shirya kije gidansu ummah zuwa yamma sai mu hadu a airport daga wajen aiki zan wuce can din....yana gamawa ya fice,
Shigowar massage yasa da sauri ta duba wayar dik tunaninta bilal ne sai taga massage dinsa,shiru tayi bayan tagama karantawa,tsaki taja cikin zafin rai yau da badan abbah bane zai dawo da wallahi bazataje ba ita da ya kira dabba mezataje tayi a gidansu bakin ciki ya kara rufeta tasa kuka.....
Dakyar ya fito daga dakinsa yana hada hanya,tundaga parlor yake jin kamshi kala kala yasan suna kitchen tunda abbah zai dawo ana masa shirye shirye,shirin zuwa kitchen din yayi yar matashiyar budurwa fara tass ce ta fito hannunta dauke da tray "la yaya ka fito yanzun momy kecewa ko yaya jikin naka oho"jinjina mata kai kawai yayi ya koma ya zauna a kujera ya dafe kai,
Momy ce ta fito tana goge hannu da towel "yadai bilal kan ne?anya zaka samu zuwa dauko abban naka a airport kuwa?"
"Ehh zan iya....ke kinsan abbah baxaiji dadi ba ace banje taryarsa ba kinsan fushi zaiyi momy insha allahu zanji sauki zuwa lokacin"
"Rufaida kawo masa breakfast yaci sai yasha magani"...girgiza kai yayi "momy bazanci komiba bari inje asibiti indawo"yace yana cije lebe bayajin zai iya kurbar koda ruwan tea ne besa jiddah a idanuwansa ba,tunanin yaje ya ganta kawai yakeyi,daga kansa yayi ya dubi agogo karfe tara saura yasan Abdallah baya gida zaije ya ganta Sharp sharp ya dawo...hakan yasa yadanji karfi ya mike,
Gaba daya yanayinsa ya tabbatar mata da yana cikin damuwa yau din nan tun zuwansa office ta lura da hakan mikewa tayi tanajin fargabar shiga inda yake saboda wani irin kwarjini da yayi mata,
Abdallah kuwa tunanin jiddah ya hanasa ko taba breakfast din da Ramlah ta kawo masa Haka kawai yakeji be kyauta mata ba,dole ya kira bilal ya sheda masa abinda ya faru sanan ya sanar masa zuwa airport ko zaije gida ya dauketa ya kaita,wayarsa dake hannunsa yayi dialing kiran bilal,
Yana kokarin zura riga wayarsa tayi ringing,ganin Abdallah yasa gabansa ya fadi kodai Abdallah na gida ne yake kiransa?yau idan be yi tozali da jiddah ba tabbas mutuwa zaiyi saboda yadda wutar soyayyarta ke azalzalarsa,wani miyau ya hadiya ya dauki wayar cikin dasasshiyar murya "man...."
"Hello man ya kake yane"cewar bilal a takaice
Shiru Abdallah yayi ya kasa magana haka kawai yakejin babu dadi ya sanarwa da bilal abinda yayi sai kawai yace "ammm nace ba man,ko zakaje ka dauki jiddah kuje airport mu hadu a can?"
Wani irin faduwar gaba Bilal yaji kamar ya soka masa mashi a kirji "amm...banajij dadi banida lafiya"
"Itama bata da lafiyan..don jiya bamuyi kwanan dadi ba rigima taitayi... shine"sai kuma yayi shiru daidai nan ramlah ta shigo,wani abu taji zirrrr cikin jikinta ya shiga wani dadi ne ya lullubeta amma sai ta dake dikda ji takeyi kamar ta taka rawa,yadda take taku cikin natsuwa Abdallah ke kallo harta zauna sanan ya kauda kansa,
Shiko Bilal shiru yayi wani iri yakeji haka kawai zucuyarsa ke sanar masa da babu lafiya Allah Allah yakeyi suyi sallama hakan yasa yace "tou ka kira driver mana ya daukota yakai gidan ummah"
"Yauwa man dadina dakai dabara bari kawai inkirasa zanyi mata massage sai driver ya dauketa ya kai gidan ummah ni kuma daga nan zan tafi airport din taryar abbah tunda kowa na can... shikenan sai anjima"ya datse wayar,
"Barka dai sir Abdallah"
Kallonta yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa"barkanki ya jikin kinji sauki ko?"
"Ehh...ummah na tace a gaisheka angode da zuwa dubiya allah ya saka da alheri yasa afi haka allah ya kara girma"yaji dadin adduarta,
"Ameen"
Kallon kulolin tayi "amma kamar bakai breakfast ba ka fito da ka hakura da aikin idan kaci abinci sai a cigaba ko?"ta langabar da kai cike da kissa,
Janyo flask din yayi yana kokarin budewa tace "sir Abdallah ya dace aje tarbar nan Dani tasu abbah saboda mugaisa dashi nasan idan na gansa zai koremun radadin rashin abbah na da nayi ina matukar so inga abban wasu sai inji kmr abbah na"tayi maganar idonta na kwalkwal....shiru yayi yana kallonta tausayinta ya kamashi yana kokarin dibar soyayyen dankali yace "ba laifi ai kema abbanki ne idan antashi aiki we can go dik zamu hadu dasu jiddah dasu ummah a can"..wani dadi ne ya lullubeta domin tarkonta ya danu lokaci yayi da zata fara fayyacewa jiddah muradinta...lokaci yayi da zatayi amfani da salonta wajen samun cikar burinta...lokacin ciwon zuciyar jiddah yayi..."nagode da ka bani wanan matsayin na zama daya daga cikim danginka"jinjina mata kai yayi yana cin dankalin ..
******
Tana daki kwance taji alamar shigowa shiko kokari yake ya kirata amma wayarta be shiga motsi yasa ta fito ta manta da hawayen da takeyi,ganinsa ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba,kallonta yake musamman kumatunta da suka kumbura yana hango yatsu rad'a rad'a a fuskarta....yadda yake kallonta yasa taji sabon kuka ya taso mata ta barke da kuka ta karasa ta fada jikinsa ya rungumeta tsammmm kuka takeyi sosai shiko wani bakim ciki ne ya darsu. A zucuyarsa haushin Abdallah ne yasa ya kasa magana ga jikinta yayi zafi sosai...bubbuga bayanta yakeyi "is ok my baby sorry...."kokarin janyeta yakeyi a jikinsa tana shigewa ganin yana yakiceta yasa ta fashe da kuka "tureni kakeyi a jikinka bayan kaika koyar dani hakan?bakin cikin da nake ciki samun kaina a kirjinka kadai zai sa insamu sassauci"
Girgiza mata kai yayi a sanyaye "jiddah... lokaci ne kinji zai wuce inaso in nisanci rungumarki gudun shedan,amma kisani nafiki bukatar jin dumin jikinki,inaso in aureki inaso in kasance dake yasa nakeso mu nisanci hakan domin komi daren dadewa zan aureki zaki dawo gareni"
Gabanta ne ya fadi kalamansa bakaramin tada mata hankali sukaiba kodai yasan cewar ita matar aurece yasa yace komi daren dadewa zata dawo hannunsa?ah ah bilal bazai taba sanin nidin matar aure bace....katse mata tunani yayi "ko bazaki aureni ba idan ummanki da abbanki suka dawo?"ya kaudar mata da tunani hade da kafeta da ido "zo mu zauna kifadamun wani mara imanin ne da besan darajarki ba yayi miki wanan marin?ina ganin yatsu a fuskarki tabbas wanda yayi miki marin nan besan tsadarki ba a zucuyata besan muhimmanci ki ba besan kedin special bace"...kalaman bilal na kokarin tarwatsa mata tunani jiki a sanyaye ta karasa parlor suka zauna "baki amsamun ba idan ummah da abbah suka dawo ko?ai zamuyi aure"
Cije lebe yayi yana kallom yanayinta,sai kawai t gyada masa kai hawaye na gangaro mata,sosai tabasa tausayi "amm yanzun nasan baki breakfast ba kiyi sai in wuce nazo inganki ne akwai inda zani"
Nan da nan tayi narainarai da ido tana kallonsa tana bukatar ya rike mata ko hannune taji Dadi amma sam kwarjininsa da furucinsa yasa bazata iya nuna masa ba be side ita matar aurece amma mijinta ne yasata cikin wanan halin kuma gashican da mace ...tsura mata ido yayi yasa ta sunkuyar da kai...kiran Abdallah ya shigo wayarta,
Kallon wayar take tana kallon bilal sai kawai ya kauda kai cikin sanyin jiki kmr bazata dauka ba ta dauka..nan yake sanar mata da zuwan shuaibu driver akan ta shirya da azahar yana Gama fada mata batace komi ba ta kashe,...maida dubanta tayi ga bilal "idan katafi yaushe zan ganka?"
"Gobe my baby"ta jinjina kai...shiko tunanin dabarar da zaiyi idan yaje airport yake dan dolene yaje kuma beso su hadu,ba yanzun bane yakeso tasan koshi waye sai nan gaba kadan.....
******
Afee kuwa tun safe suke shirin zuwan abbansu tare suke a kitchen da maaikatan gidan yau hardasu rumaisa,
"Ya rumaisa yau fa zamu hadu dasu rufaida dasu zuhura fa,hmmm harda ya bilal"
Murmushi rumaisa tayi..."inaso ingansa kuwa don nadade bangnsa ba dikda jin kansa yayi yawa be ko kallon mu idan mun hadu kamar yaga kashi...inaga dai india zai auro"
Kyalkyalewa da dariya meena da afee sukayi atare sukace "kodai kishi ne...mundade da sanin kinason ya bilal fa kina wani bonewa...idan kinasonshi kawai ki bayyana idan Allah yaci dake kisamu"
Tabe baki rumaisa tayi.. cikin zuciyarta ta furta shine mafarki na amma nasan bazai taba sona ba saboda niba kalarsa bace...amma da ciwon sonsa zan mutu....
SLIMZY
[11/5, 7:31 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKARWA:*
*HAUWA'U MUA'ZU AMIR RUMA...*
*ASSALAMU ALAIKUM*
ina matukar godiya da adduoi da dumbin masoyana sukaimun na rashi da nayi,nagode sosai Allah ya saka da alheri allah ubangiji ya bar zumunci nagode nagode sosai banida bakin da zanyi amfani dashi wajen godiya.....
*TUKWICI GAREKU* daukacin members na *HASKE WRITERS ASSOCIATION* ...ina matukar alfahari da wanan kungiya nagode sosai da dumbin kauna bazan mance da ku ba harabada slimzy nayi muku son so fisabilillahi.....👏🏼❤️
*14*
Ajiyar zuciya bilal ya sauke ya ja numfashi ya dora mata kyawawan idanuwansa da tun shigowarsa suke rikida daga fari zuwa ja "zan tafi jiddah...ki kula da kanki kinji?kidaina damuwa idan kinayi nima zanyi damuwar"..jinjina masa kai tayi cikin karayar zuciya idonta na fidda hawaye tasa hannu ta goge "tou nadaina,amma dan allah ina bukatar ka a kusa dani"
"Insha allahu"ya kama hanyar fita,har ya kai kofa ya juyo yana kallonta itama shi take kallo hawaye na sauka a fuskarta idonta akansa,hakanan bilal ya fice zucuyarsa nayi masa zafi ji yake tamkar ya dawo ya zauna da ita,hakika Abdallah kuskure daya zaiyi a rayuwarsa shine ya saki jiddah idan har ya saki jiddah to tabbas shine zai aureta koda zumuncinsu zai kare,haka yakesa kafa batare da sanin inda yake takawa ba idanuwansa a rufe ya fice gidan,kallo mai gadi ya bisa dashi "anya lafiya kuwa cikin gidan nan?"me gadi ya tambayi kansa kafin ya leka ta karamar kofar gate din yana kallo bilal ya tada mota ya wuce...ba gida ya nufa ba phermacy ya nufa don nemawa kansa maganin wanan ciwon kan.....
Dakyar jiddah tasamu tayi wanka saboda yadda zazzabi ke neman yaci karfinta,haka ta fito jiki babu kwari,tsaye tayi gaban madubi tana kallon fuskarta ba laifi kumburin yadan rage amma jan da fuskarta tayi yana nan saima karuwa da yayi,sama sama ta shafa mai ta fesa turare ta bude drawer ta ciro wata jar atamfa doguwar riga super Holland da gyale ja mai stones,ta sa rigar tayi dauri sanan ta yafa gyalen,tana kokarin daukar wayarta taji horn din mota tasam shuaibu ne ya iso don haka bata tsaya bata lokaci ba ta fito daga daki a parlor ta karkashe globes sanan ta rufe kofa ta fito,
Bayan mota ta zauna ta jikin madubi shuaibu ke kallon jiddah,shi kansa gabansa saida ya fadi ganin jan da fuskar jiddah tayi kamar wadda taji a jikinta ta dago manyan idonta suka hada ido sai ya wayance "ina yini hajiya"yana maganar ya tada mota,
"Lafiya lau alhamdulillahi"tace a takaice ta kwantar da kanta jikin seat ta lumshe idanuwanta,wata irin ajiyar zuciya taja babu wanda ya fado mata a rai sai bilal....
******
Dogayen riguna sukayi anko afee da rumaisa da meenah,ta afee baka ta rumaisa milk colour sanan ta meenah red,suna parlor suna kashe hotuna ko ina ya dauki kamshi ummah na gefe zaune ta nade jikinta da lafaya mai shegen tsada jiddah ta iso,
"Assalamu alaikum"tace a sanyaye cikin sarkewar murya,wani kallo ummah tayi mata ta kauda kai tamkar taga kashi,suko yan matan a tare suka juyo,rumaisa da meenah ganin jiddah yasa suka hada rai suka juyar da kai banda afee da ta daka tsalle ta rungumeta "oyoyo oyoyo oyoyo antyna,yanzun nake zancenki a zuciyata ince ko zakizo aje tarbar su abbah dake?"tana maganar tana kokarin kallom fuskar jidda wadda ta sadda kanta kasa "ehh afee ai dole ne inzo yanzun ma yayanku yasa aka kawoni driver gidan nan ne ya daukoni"
Karasowa cikin parlorn tayi ta zauna can nesa da ummah,ta sunkuyar da kai gabanta na tsananin faduwa a d'arare tace "ummah...ina yini barka da yamma"
"Barkanki"ummah tace ta kauda kai tamkar taga kashi,wani takaici ne ya lullube jiddah "an wuni lafiya ya aiki?"
Wata uwar harara ummah ta watsa mata daidai ta dago kanta suka hada ido,da sauri ta sadda kanta tana wasa da gyalenta.."lafiya....aiki kuma ba shi kikaga inayi ba uwar iyayi da yaushema kikasan kicemun ya aiki,mtswwww kinzo daga zuwa zakisa infara tada jijiyoyin wuya"
Kwalla ce ta cicciko ma jiddah amma ta boye fuskarta,afee kuwa ji tayi kamar kasa ta tsage ta shiga dikda dama inda sabo haka ummah ke hantararta,sai kawai afee ta matse "antu jiddah bari in kawo miki test na samosa da meat pie da mukaiwa abbah dazun,nasanki da son samosa ko bazakici ba?"
D'ago ido tayi cike da hawaye "zanci afee ki hado min da ruwa mai sanyi kinji?"tayi maganar tana murmushi,..jikin afee ne ya kama rawa hango shacin wani abu kamar yatsu a fuskar jiddah ga wani jajir da wajen yayi kamar an watsa mata ruwan zafi,tsaye tayi tana karewa jiddah kallo cikin tashin hankali da damuwa,,kallom sashen da ummah take afee tayi kafin tayi gyaran murya da sauri jiddah ta dago kai,afee ta kyafta mata ido alamar su Shiga dakinsu,tana mata haka tai gaba babu musu jiddah ta mike ta nufi dakinsu afee atare ummah dasu rumaisa sukaja tsaki,meenah ce tadan daga murya "keman afee iyayine zai kasheki da shisshigin tsiya munafuka"
A kufule afee tace "niba munafuka bace"ta shige rumaisa ta watsa musu harara...
"Anty jiddah meyasamu fuskarki kamar mari kinga yadda yatsu suka fito baro baro a fuskarki kuwa?"
Girgiza kai jiddah tayi "ba mari bane afee,share kawai zan miki bayani wani lokaci,jeki dauko min samosa yunwa nakeji sosai kuma kinga mun kusa tafiya airport"
A sanyaye ta juya Tana tafe tana waigen jiddah ta fice a dakin....
*******
Fararen yakaddu ramlah ta shigo dashi office din ta karasa har gabansa cikin ladabi ta mika masa "Ramla....yadai an kammala"yana maganar kansa na kan computer,
Lumshe ido tayi ta bude "na karasa sir Abdallah....amma ya dace katashi kayi sallar laasar mukama hanya ko?kasan daga nan zuwa kaduna international airport akwai nisa kuma wajajen mando akwai hold off "cike da natsuwa tayi maganar,
"Owk"yace yana kokarin janye laptop din gefe "kinyi sallah ne?"ya tambayeta yana nade hannuwan rigarsa,
Rufe ido tayi da hannuwanta a fuskarta...ganin haka ya fahimceta ya mike ya fice,kallo tabi kofar dashi sanan ta dawo ta saita natsuwarta ta sauke sassanyar ajiyar zuciya,"nafara samun kansa"ta furta hade da sauke murmushi,mikewa tayi ta shiga harhada kayanta cikin basket,da kanta ta tattara masa takardu gefe daya ta ajiye ta gyara table din ta rufe laptop din tasa masa cikin jakarsa ta ajiye kan table din sanan ta mike ta fice,
********
"Zuhura nikam tun dazun ina yayanku ya shige?daga cewa zaije asibiti ya amso magani gashi yamma tayi dik mun shirya? menene haka ne?yadace mukama hanya"
Ajiye wayar da take latsawa tayi,kanwar bilal ce sanye da lace mai shegen kyau light blue, zatayi magana rufaida ta shigo da nata lace din kalar na zuhura "momy yayah fa tun dazun ya shigo gidan nan cemun yayi bari yayi wanka tun dazun"
Fitowa yayi sanye da darar shadda kansa babu hula fuskarsa tadan rame kadan kwayar idon bilal kawai momy ta kalla ta hango damuwa kwance"yanzun nake cigiyarka ai bilal ya kamata mu kama hanya ko?"
"Owk...motoci nawa zamu dauka?"yayi tambayar yana gyara links din sa,
"Biyu mana driver ya tuka mu kaida abban ku a mota daya ko?ko beyi ba?"
"Is ok,muje to"...ya fice duka suka bisa da kallo,mamakin yayan nasu zuhura keyi tasan yadda ya bilal ke mararin dawowar abbah amma yau gabaki daya bashida walwala,dukkansu cikin damuwa suke da halin da yayan nasu ke ciki har momy daurewa tayi kawai tadauki jakarta,saidai ta alakanta hakan da ciwon kan dake damunsa saidai zatayi kokarin gano ainihin matsalar tasa,
Tafe suke a mota shida ramlah minti minti sukan kalli juna,haka kawai yake jin kansa wani iri meyasa zai dauki ramlah ya tafi da ita taryar abbansa?anya yayiwa jiddah adalci kuwa?koda yake ai aminiyarta ce bawani abu bane kuma ai itama yar uwarsu ce,
"Sir Abdallah"...ta kira sunansa cikin wani irin yanayi hade da zuba masa ido,driving yakeyi beko kalleta ba kusan seconds arbain sanan yadan juyo "umhmmm... menene?"
Girgiza kai tayi"kawai i feel uncomfortable ne shine kawai...yanzun idan naje wajen taryar abbah a matsayin wa naje?a matsayin kawar matarka ko sakatariyarka?ko kanwarka?"lokaci daya ta jero masa tambayar,
Furzar da iska yayi "a matsayin kanwata...kuma matar da nakeso in aura a karo na biyu"yayi maganar fuskarsa tamke ya hade girar sama da ta kasa,yayi hakan ne kawai don kada ta musa masa kada tace masa komi,
Zaro ido tayi ta dafe kirji tsintar kanta tayi cikin tsananin bugun zuciya,dakyar ta hadiyi wani miyau,kawai unexpected Abdallah yayi mata wanan furucin,ta yaya?yaushe harta samu kansa haka?koko dama can shima sonta yakeyi?katse mata tunani yayi "ga motarsu bilal kuwa a gabanmu inaga su ummah sunyi nisa"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai "kunyar ummah nakeji"
Murmushi yayi yadan kalleta,sosai yake son halayyarta komi na rayuwa tafi jiddah,meyasa jiddah bata koyi da halin kawarta?tun baya kulata har tasamu galaba akansa?......
Kusan a tare motocin suka isa airport daidai saukar jirginsu abbah....su afee suna waje dik sun fito daga mota harsu ummah dake gefe ita da momynsu bilal,yan matan duk su biyar suna tsaye waje daya dukkansu fuskokinsu dauke da farin ciki tsayuwar motar Abdallah yajawo hankalin yan matan,afee ce karama itace ta daka tsalle "laaaa ga ya Abdallah ya iso,amma yayi kokari kila ya baro wajen aiki da wuri yasa besamu holdoff a hanya ba"...jiddah dake gefensu tana daddana waya jin an ambaci sunan Abdallah gabanta ya fadi ta kasa daurewa ta dago kyawawan idanuwanta ta dorasu akansa yana kokarin rufe mota,kafe motar da ido tayi ganin an bude dayan side din gaban motar,ramlah ce ta fito....da sauri jiddah ta zaro ido tana kallonsu,rufe motar sukayi a tare suka jero....wani kallo meenah da rumaisa sukayiwa jiddah sai kuma suka saki murmushi,a tare suka tako zuwa garesu "Anty ramlah sannu da zuwa dake ya Abdallah yazo?"a tare suke mata tambayar
Jinjina musu kai tayi ta rungumesu cike da farin ciki "ehh cewa yayi zaizo taryar su abbah shine nace bari in zo nima in samu ladansu abbah ingaishesu...inaso ummah?"
"Gasu can da momynsu zuhrah tsaye jikin mota"rumaisa ta nunasu da yatsa,
Sunkuyar da kai jiddah tayi wani irin faduwar gaba ne ya ziyarceta babu kakkautawa....idanuwanta duhu duhu suke gani... Ramlah da mijinta?a filin jirgi?meye hadinta da biyosa taryar iyayensa a filin jirgi?...dafe kirji tayi wani irin kishi ne ke kokarin jefar da ita a tsayen da take kodai ramlah itace matar da Abdallah ke cewa zai aura kuma idon sani?..... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun.... Ramlah ce ...me ramlah keyi da mijina?tambayar kanta takeyi a fili take maganar muryarta na rawa,ji tayi an dafata da sauri ta juya afee ce sukai ido hudu "anty yau kin tabbatar da maganata?gashi kina tambayar kanki me ramlah keyi da mijinki?.. tou bari inbaki amsa...soyayya domin alamu sun gama nunawa"....hawaye ne suka subucewa jiddah suka shiga gudu a fuskarta,waigawa tayi ta hangi Ramlah tsugunne gaban su ummah tana gaidasu Abdallah na tsaye a gefe....
Bilal kuwa ya jingina da jikin seat din mota idonsa a bude yana hangen dramer da akeyi....tabbas waccen ramlah ce ramla kawar jiddah tare da Abdallah sukazo...tou me ya kawota?dama tasan alakar sa da Abdallah ne koko dama ramlah ta sanarwa da jiddah waye shi?...kansa ne ya daure nan da nan jijiyoyin kansa suka fito rudu rudu a gefen goshinsa.... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun kawai yake furtawa ya dafe kansa,meyasa jiddah take kuka?ganin Abdallah da Ramlah?tou me hakan ke nufi?,
Hango su zuhra yayi sunyi wajen da afee da jiddah kw tsaye,...dukkansu ganin jiddah na kuka sukai jigum jigum....dago ido jiddah tayi ta kalli zuhra,gabanta ya sake faduwa ganin kamannin bilal sakkk a fuskar zuhura kallonta takeyi ko kifta ido batayi hakan yasa a sanyaye zuhura ta gaidata "ina yini anty jiddah"
Afee ce taja numfashi "yaran aminin abbah ne kuma yayansu aminin ya Abdallah ne nasan baki san su ba...ya b...."katsewa afee magana rumaisa tayi "afee gasu abbah"
A tare suka kwasa a guje duka yan matan suka nufi dattawan dake takowa dukkansu sunsha shadda iri daya fuskokinsu cike da annuri....har Abdallah da sauri ya nufi su abbah dake tahowa,
Momyn bilal kuwa waige waige ta shigayi tana neman bilal bata gansa ba,zura hannu tayi a jaka ta ciro waya tayi dialing numbersa is not reachable,... "Ohhh meke damun yaron nan ne wai?yanzun ga mahaifinsa ko Ina ya shige oho?"
"Halan yarona...wai ina bilal bangansa ba tun zuwan mu hajiya"
"Beda lafiya ne,nasan ya kwanta a mota"...su abbah suka karaso inda su ummah ke tsaye gefe ramlah ce ta sunkuyar da kai,ganinsu abbah yasa ta zube a kasa "ina wuni abbah....kun iso lafiya"
Dukkansu suna faraa suka amsa abban Abdallah yace "ah ah wacece wanan kuma?ko munsamu ya ne?"
Ummah tayi dariya "kusan hakan ne don yar ka ce itama"
"Masha Allah"
Abdallah ya rungume dadyn bilal suna gaisawa,abbahn Abdallah kuwa cewa yayi "banga zuwanku ba tunda banga yarona ba ina bilal ne?"
"Abbah bashida lafiya kamar yana mota"inji rufaida.
"Ina sirika ta?"
Waige waige dukkansu suke sun san jiddah yake nufi, Abdallah sai lokacin ya tuno da tana wajen,wato ita bazata fasa mugun halin ta ba yanzun dik yadda abbansa ke mugun sonta a filin jirgi ma saida ta nuna hali saita nunawa duniya suna fada?
"Gata can zuwa abbah"
"Afeen abbah...kinyi missing din abbah ko?...ina zuhura ne?"
"Gani nan abbah...aida nayi fushi ka tambayi kowa banda ni"cike da shagwaba tayi maganar, dik sukasa dariya...
Tsugunnawa jiddah tayi "barkanku da zuwa abbah...kun iso lafiya?"cike da girmamawa ta sunkuyar da kai,
Yar dariya abban bilal yayi "lafiya lau,yanzun muke tambayarki ashe kina nan kin boye"
Murmushi tayi batare da tace komi ba....
Dukkansu rankayawa sukayi suka nufi motocinsu,tun da bilal ya hango abbansa ya sauke murmushi daga cikin motar sai lokacin yadanji farin ciki a zuciyarsa Yana son abbansa sosai...yasan motarsa abbansa zai shigo suma wadancen motocinsu suka nufa,
Jiddah kuwa anata shigan mota daga baya ta tsaya tana kallonsu har suka shige,ummah ta ruko hannun ramlah suka shiga motarsu yayinda abbah da abdallah suka shiga mota daya,
Mamaki ne ya lullube jiddah... Abdallah yama mance da ita a wajen ko kallon inda take beyi ba?me hakan ke nufi?wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tana gani suka tada mota suka wuce....
Bilal kuwa gabansa ne ya shiga faduwa yana hangen jiddah tsaye bata shiga mota ba kuma sunyi tafiyarsu sun barta nan....gumi ne ke karyo masa, dabara ce ta zo masa da sauri ya ciro wayarsa yayiwa wani dan taxi massage akan yazo waje kaza ya dauketa ga hadari....suka wuce,mamakin Abdallah ne ya kashe bilal dakyar yake driving wani irin mugun hali ne wanan? Abdallah ya kama hanya ya mance da matarsa?yana lura da cewar tunda yazo bebi ko ta kanta ba hakan ya tabbatar masa da makirci ramlah dama ta hada....idan haka ne kuwa zaije har gida ya sameta ya mata tambayoyi....
Tsayuwar taxi gaban jiddah yasata sauke ajiyar zuciya tunanin yadda zata bar filin jirgin nan take dama,tana shiga ta masa kwatancen gidan iyayenta....jikinta sai rawa yakeyi Abdallah idonsa ya rufe ya mance da ita tasani sarai ummah nasane da ita tsabar kiyayya ce....
**********
Ramlah kuwa kin fitowa tayi daga mota koda suka iso dik yadda ummah tayi ta fito ki tayi "memakon ki shigo kici abinci?"
Girgiza kai ramlah tayi hade da sunkuyar da kai Tana wasa da gyalenta,
"Shuaibu to ka kaita gida tunda nasan Abdallah dai ba zai kaita ba ga abbansu ya dawo,ki gaida ummanki"
Gyada mata kai tayi ummah tayi cikin gida,afee kuwa tana rike da hannun abbah ta waiga,gefe da gefe da sauri ta dafe kirji "abbah Ina anty jiddah?ina tayi?ko tare kuka taho?"
"Ah ah ai motar mu nida Abdallah ne kawai"
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun... shikenan an baro anty jiddah can mun shiga uku"
Ummah dake bayansu ta karbe zancen "dallah uwar iyayi kin shigowa motar tayi ai ni wanan yarinyar bansan menayi mata ba takemun wanan kiyayyar kamar ba dana take aure ba"...wani abune ya tokarewa Abdallah makogwaro ya tsaya shi be shiga ba shi be wuce ba wato jiddah wawancin da tayi kenan? yanzun ina ta tsaya?kota bi su bilal ne? Anya kuwa?"
"Abdallah sai ka koma airport ka dauko jiddah dan alamu sun nuna anbarota a can"cewar abbah yayi gaba hannunsa rike dana afee wadda jikinta yayi sanyi tausayin jiddah ya kamata...
Motarsa ya koma ya ja aguje yabar gidan zuciyarsa na tafarfasa ga kiraye kirayen sallar magriba anayi ta ina zaifara neman jiddah?meyasa jiddah ke wadanan halayen me kama dana dabbobi?sam jiddah batada hankali batasan meke mata ciwo ba,wani irin kauyanci ne wanan?ana shiga mota ita taki Shiga to ta gidan ubanwa zata dawo? hmmmm kishi ne na ganinsa da kawarta yasa taki Shiga motar,yasan halin kayansa amma don meyasa take wanan halin me kama da na jahilai?ko ance mata an haliccesa dan ita kadai ne?mtswwww yaja tsaki gudu kawai yakeyi a mota kamar zai tashi sama,
Wayarsa ya lalubi number bilal,dik kiran da yakewa bilal yaki picking yana kallon wayar gefensa tana yankewa bakin ciki yasa tun isowarsa gida ko magana yakiyi,
Zuhura dake kokarin zubawa dadynsu abincu ta saci kallom inda wayar ke ringing ta saci kallonsa fuskarsa babu annuri Babu walwala haka nan ta daure"ya....ya naga ana kiranka baka picking lafiya?"
Girgiza kai yayi ya dau wayar ya kashe gaba daya....
Mamakine ya cika Abdallah ganin bilal ya kashe wayar,me hakan ke nufi?sai yanzun ya tuna da ance bashi da lafiya yasa ko fitowa beyi ba a mota,...dafe kai Abdallah yayi nasan ma bata gidansu ya furta a fili.... kafin ya isa airport ruwa kawai ke sauka na sama kamar da bakin kwarya gashi gari yayi duhu,tsoro da fargaba suka kama Abdallah,nan da nan yaji jikinsa yayi sanyi Allah sarki jiddah...kece kikesa nake fushi dake sam banason halayenki,halayenki suke sa in karajin son auren kawarki kodan ya zame miki lesson,kamar zautacce yake magana...
******
Kuka sosai jiddah keyi a parlor tana durkushe jikin mahaifiyarta "ummah dan allah ku raba aurena da Abdallah saboda baya sona, Abdallah ya tsaneni"
Yayanta ne yayi shiru yana saurarenta,zuciyarsa sai tafarfasa yakeyi wato wulakanta jiddah yakeyi kenan,babu mamaki a lamarin Abdallah tunda dama tantagaryar dan wulakanci ne shi din gashi ya nuna tunda ya soma wulakanta kanwarsa,aiko zai gamu dasu dan koya zo jiddah bazata bishi ba.....
"Kiyi shiru yaya jiddah dan allah kidaina kuka kinji?"murya na rawa abeedah ke mata magana dik ji suke kamar suyi kuka,
Sai lokacin mahaifiyarsu ta nisa "shikenan yanzun bari mugani zaizo nan nemanta?tunda yasar da ita yayi a airport din idan yazo nemanta sai a sasanta ta koma"
"Bazata koma ba ummah,bazata koma gidan wanan dan iskan yanzun ba sai ta huta ummah haba dubi yarinyar nan ji fuskarta,uwarsa bata sonta shima yana mata wulakanci kasheta zasuyi indai nine yayanta kuma mazaunin ubanta bazata koma ba"
Lamo jiddah tayi tana sauke ajiyar zuciya,mamaki da al'ajabi har yanzun yana zuciyarta Ramlah ce suka taho tare da mijinta wajen taryar sirikinta?...me hakan ke nufi?wani irin kusanci ne da har Abdallah zai dauko ramlah zuwa filin jirgi?"runtse ido tayi hawaye na sauka a fuskarta....ko shiyasa Abdallah yayi mata wadanan maganganun jiya?....meyasa Ramlah ke neman kusantar mijinta bayan aminiyarta ce?"tambayar kanta takeyi...kanta sarawa yake kamar zai rabe biyu.....
******
Rashin ganin jiddah ba karamin tadawa Abdallah hankali yayi ba,ina zai nufa nemanta?....wayarsa dake gefe tayikara dubawa yayi Ramla ce ke kiransa,...kallon wayar yakeyi sunanta na yawo amma ya kasa dauka saboda dacin da miyaun bakinsa yayi,wani irin takaici ne ya lullubesa tunda be ganta ba a wajen yasan wani waje tayi to ina tayi?kodai gida ta wuce?ajiyar zuciya ya sauke yasan gida ta wuce kawai...can gidan su inda suke zaune amma ai saita fada masa,
Ramlah ta kara kira sai a lokacin ya danna recieve ya kara a kunne "hello'"
"Hello...sir Abdallah...ya gajiyarku yasu Abbah?"
"Lafiya lau,ya kikaje gida nagode fa"...lumshe ido tayi "yiwa kaine...kana ina haka ga ruwa anayi naji kamar kana driving"
"Ehh.... Bari zamuyi call"ya datse wayar be jira cewarta ba....
*******
Bilal kuwa zaune yake parlorn amma kurwarsa na can wani waje,tunani ne suka cunkushe masa kwakwalwa, yanaso yaji halin da jiddah ke ciki,sanan yanada dumbin tambayoyin da komi dare zai nemi Ramlah dasu.....
*BA KULLUM ZAKU RINKA SAMUN POST BA,ABUBUWA SUNMUN YAWA ZAN RINKA TSALLAKEN KWANA DAYA....*
*SLIMZY🥰*
[11/5, 7:31 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*IDAN K'AYA TA SOKI ZAKI,ZAIYI D'INGISHI NA D'AN KWANAKI...BAYAN NAN KUMA ZAI DAWO* *DAIDAI😁*
6
*RANAR *HAUSA3#2020*
*16*
Abidah ce ta turo kofar da sallama afee na biye da ita itama sallamar tayi a sanyaye ta shigo,idanuwanta suka sauka akan fuskar jiddah sukai kurriiii suna kallon juna,dakyar afee ke daga kafa ta karaso gefen jiddah ta zauna jiki babu kwari murya na rawa tace "Anty..jiddah..ina kwana..anty jiddah..ku"kasa magana tayi ta fashe da kuka ta fada jikin jiddah ta rungumeta tana bubbuga bayanta idonta cike da hawaye"is ok,afee ya isa kiyi shiru ba gani kinsameni da lafiya ba?ummm nasan kukan me kikeyi koh?yayanku baya sona yanzun afee rabuwa dashi shine yafi alher"tana maganar hawaye na zuba a idonta tana rungume da afee,kasa jurewa Ashma tayi ta mike ta fice a dakin,dagowa afee tayi "Anty jiddah...kina nufin zaki rabu da ya Abdallah?kina nufin aurenku zai kare ta dalilin hakan... Anty jiddah kiyi hakuri abbanmu yana sonki har fushi yayi da ya Abdallah akanki"
Shiru jiddah tayi hawaye be daina zuba a idanuwanta ba,zafin abinda Abdallah yayi mata ya kara taso mata,ta yaya mijinta zaije waje da wata?kuma don ta nuna kishi ya zama matsala,"afee kiyi hakuri zamu cigaba da zumunci amma banajin zamu cigaba da zama da yayanki cikin wanan yanayin da yake gab da jefani cikin halaka,ina son mijina amma Abdallah baya sona ya fifita aikinsa akaina banida wata kima,afee ke yarinya ce amma Abdallah baya sauke hakkin aurena akansa"kasa cigaba da magana jiddah tayi,kuka yaci karfinta,sosai afee ta kankameta tana kuka "don allah kada kirabu da ya Abdallah dan allah Anty jiddah bazai taba samun mace kamarki ba kiyi hakuri ki koma kinji ni zandawo zama dake anty jiddah"hada hannuwa tayi tana rokon jiddah tana kuka,
Sosai afee tabawa jiddah tausayi amma batada option akan abinda iyayenta suka yanke matukar iyayenta sun zabi kashe aure dik yadda takeson Abdallah zata hakura dashi ta auri masoyinta bilal,wanda tasan yadda yake sonta tasan yadda yadamu da ita bashida burin daya wuce faranta mata rai,babban abinda ya kara masa martaba a idonta shine yadda ya yanke alakar hada jiki da ita dikda irin muguwar shaawarsa da take ciki dik lokacin da zasu kadaice,wani abu ke fuzgarta tamkar shocking daurewa kawai takeyi....kara rike afee jiddah tayi tana sauke ajiyar zuciya,
Sallamar Ashma tasa abida sauke numfashi "aysha yadai,"
"Ya jiddah kizo parlor inji abbah ga ya Abdallah yazo"
Gaban jiddah ya yanke ya fadi da sauri ta kalli afee "dama tare kuke ko?shine ya turoki kizo ki nemi yarda ta kika boyemun ko?"
Girgiza kai afee tayi "ko kadan Anty jiddah,karya nayi zani lesson nataho nan baasan ma nan nazo ba don haka har ya tafi ma bazaisan ina gidan nan ba kada ki fada masa"
Jikin jiddah ya karayin sanyi,son yarinyar ya Kara shigarta dakyar taja jiki ta sauko,toilet ta shiga ta wanko fuskarta ta fito ta goge fuskarta da towel sanan ta zura hijab ya fice.....
**********
Tana kitchen tana kwashe abincin ranan kanwarta ta biyota da waya,
"Ya ramlah ana kiranki tun dazun"
Wanke hannu tayi sanan ta goge da kitchen napping ta karbi wayar tana kokarin duba misscall kira ya sake shigowa,bilal ne tayi murmushi ta dan jima sanan ta dauki wayar,
"Barka da rana...mai sarauta yaya bilal..da me kazo yanzun"
Murmushin keta bilal yayi "ina kofar gidanku"
Farrrr tayi da ido "owk 10 minute please"...bata jira cewarsa ba ta datse wayar,
Karasa kwashe abincinta tayi,ta gyara wajen sanan ta fito parlor ta wuce dakinta,..gyalenta dake kan gado ta dauka ta fito "ummah,ina zuwa nayi bako a waje"
"A dawo lafiya".....
Kishingide yake a jikin seat din motarsa yana fuskantar kofar gidansu,motarsa ta dauki sanyin Ac yana lumshe ido yana budewa ya hangi fitowarta,
Tsaye tayi tana kallon sabuwar dalleliyar motar dake kofar gidansu,saida gabanta ya fadi dikda jikinta ya bata bilal ne a ciki amma fa motar ta hadu dom daga gani taja miliyoyin kudi....taku take daidai yana kare mata kallo har ta iso,
Mamaki ne ya kashe ramlah ganin anbude mata motar,sai bata shiga ba ta leka,idonsa da nata suka hadu,
"Ya kika tsaya daga waje?...haba jarumar mata ki shigo mana"..haka kawai muryarsa da furucinsa ya haifar mata da faduwar gaba,amma dayake jarumar ce kamar yadda yace murmushi ta sauke me kayatarwa ta gyara ta shiga motar ta rufe,
Gyara zama Bilal yayi ya zura mata ido ko kiftawa bayayi,kallon da yake mata yasa tasha jinin jikinta,ga wani kwarjini da yayi mata saidai a kwayar idonsa tana hango tsantsar mugunta kwance ciki,yau ya rikide mata zuwa wani kamanni da batasanshi dashi ba,
"Yada... wanan kalon yaya bilal"...murmushi yayi "ummm . Ramlah kenan gaskiya jarumtarki da kwarewarki ba karamin burgeni sukayi ba domin tsaf zaki iya film,irin wanan basira haka?hmmmm amma fa burgeni kikayi"
Ya gyara zamansa ya kwantar da kansa jikin kujera yana fuskantarta,
Kauda kai gefe tayi "me kake tafe dashi me kazo dashi domin wadanan furucin naka sun tabbatar mun akwai wani babban lamari"
Hmmmm"ramlah kenan lamari babba ya wuce irin yadda kike acting film wajen kawarki,da mijinta?aike abun tsoro ce koda yake alamu sun nuna kina hakan ne don cikar burinki"
"Kuma burina yana gab da cika ba?"tayi murmushi,
"Me kika taka?me kike dashi?hmmm nasan kinada makaman yaki da yasa kike kokarin tarwatsa rayuwarmu duka amma kisani,tabbas zaki nasara domin ni zan baki hadin kai don samun jiddah a matsayin matar aure....kema kuma ki zama matar Abdallah a auren sa na biyu kinga kinsamu farin ciki nima kinsamamun don banida farin cikin daya wuce samun jiddah a wanan duniyar....igiyar aurenta na girgidi kuma a hannunki take amma me kika taka?"
Kalaman bilal tamkar zubawa ramlah garwashin wata yayi cikim zuciyarta,hakika tana hango gaskiya a zancensa,meyasa jiddah zata cigaba da farin ciki?tabbad burinta a rayuwa be wuce jiddah ta kasance cikin bakin ciki da kunci ba,batason jiddah tafita kuma matukar jiddah ta auri bilal ta kara kerewa saa,...dik tunaninta bilal bazaiso jiddah soyayyar gaskiya ba domin da haduwa da komi Bilal yafi Abdallah da wayewa uwa uba naira....
"Kinyi shiru ina tambayarki abinda kika taka da kika hada aminiyarki da aminin mijinta suke soyayya kuma da auren aminin saurayinta na waje akanta"....zuwa wanan lokacin bilal yakai kololuwa wajen batawa ramlah rai,ta yaya zaixo kofar gidansu yana challenging dinta?tamkar wata munafuka ko wata annoba,
Fusata tayi ta ciro wayarta ta shiga jikinta har rawa yake,karawa bilal video dinsa tayi yana kissing jiddah...hannunsa akan nipples dinta yana wasa dasu... clearly video din tana sanye da kayan bacci,
Jijiyoyin kan bilal suka fito sukai rud'u rud'u a goshinsa....nan da nan idonsa sukayi jajir yana cigaba da kallon wayar,
Dariyar keta ramlah tayi "yanzun ka tabbatar da inada babban makami da zanyi wanan yakin ko? lokaci kankani wuta zata tashi cikin family din ku duka lokaci kankani soyayyar abokantaka da yan uwan taka zata koma kiyayya lokaci kalilan duniya zata san kaci amanar amininka ka nemi matarsa har gidansa na sunnah,hmmmm ya bilal kabini a hankali...kuma jiddah zamanta a gidan Abdallah temporary ne"ta karasa maganar tana kashe wayar hade da murmushi tana kada kai cike da mugunta....
"Tabbas na tabbatar da ke cikakkiyar shedaniya ce ramlah... naci amanar aminina tabbas amma amanar jiddah da kikaci ta nunka tawa ninkin ba ninkin,amma kin tafka babban kuskure guda daya"
Da sauri ta dubesa cikin wata iriyar fuska "wani irin kuskure?babu kuskuren dana tafka"
Murmushin keta yayi har wushiryarsa ta bayyana "kin tafka kuskuren nunamin video da kikayi...domin tsaf zan shiryawa yakin don nasan abinda kika taka,kedin kuma bakidan ni mezan taka ba,saidai ina miki albishir da soyayya tsakanina da jiddah yanzun aka soma..."
Yar dariya tayi ta karfin hali dikda zuciyarta nayi mata d'ar d'ar da bilal "zaka shiryawa farautar rayuwata kenan saboda wanan video din"
Gyara zama yayi yana kokarin sawa motarsa key"ko kadan ai idan na farauci rayuwarki nayi give up kenan,aini bazan farauci rayuwarki ba saidai ina me tabbatar miki yanzun aka soma wasan....ga hanya zaki iya tafiya"ya nuna mata kofar fita,
Ba musu ta bude motar,ta fice ta rufo kofar hade da harde hannuwanta a kirji tana kallon motar,..
Yana kallonta ta cikin glasss ya kada kai ya cije lebe, yaja motarsa ya bada mata kura....
Tsaye Ramlah tayi kamar an dasata,tana jin zafin yadda bilal ya kasa bayyana tsoronsa da furgicinsa na ganin video din nan,tasani bilal jarumi ne na gaske koda ya furgita bazai taba nuna mata ba saidai tasan waye shi,tun ba yauba tasan waye bilal....tasan kwakwalwarsa sarai zai iya wasa da hankalinta zai iya tarwatsa mata farin ciki,
Meye mafita?mafita daya ce ta tarwatsa masa farinciki kafin ya bullo mata ta bayan gida....saidai zata jira zuwan jiddah taga dame zataje mata....
*********
Shiru parlorn yayi ya ibrahim wani kallo kawai yakewa Abdallah cike da takaici,dubesa ko alamar nadamar abinda ya aikata beyi ba fuskarsa babu ko faraa bare annuri,
"Yanzun munji abinda kace Abdallah,kace jiddah bata ganin girmanka da mahaifiyarka bata darajasu,kai kanka bata girmamaka kalmar data fito bakinta take fada maka ko?"abbah yace cike da hikima,
Gyada kai Abdallah yayi kansa a kasa yace "sanan, dik ba wani abubane yasa jiddah takemun wadanan abubuwan face kara aure da nace zanyi, hakan yasa ta rainani kishi ya rufe mata ido ta kirani mazinaci"
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun "abbah da ummansu jiddah suka hada baki,
"Wanan kalma tayi muni, banji dadin jinta ba Abdallah,ka tabbata abinda jiddah tace maka kenan?"
Hawaye ya gama wankewa jiddah fuska,ta kasa magana,bakin ciki ya cunkushe mata zuciya,lallai Abdallah ya cika butulu a gaban idonta dana iyayenta yake fadin zai kara aure?ok dama dalilin da yasa baya biya mata hakkinta na aure kenan?ok ita kenan ta sanarwa da iyayenta cewar baya biya mata bukata?baya sunnah da ita?yana tunanin idan ta fito da wanan issue din zata kara zaman aure dashi?ko kotu akaje ta fadi cewat ita mahaukaciya ce be kwanciya da ita raba auren zaayi....kenan Ramla kawarta zai aura?gabanta ya yanke ya fadi i can't believe this ramlah zata auremun miji?...bata gama tambayar kanta ba abbah ya katse mata tunani ya daka mata tsawa "ke....mekike nufi tunda ake magana bakice komiba kin tsaya kina mana kukan banza kukan munafurci?ashe haka kike jiddah?"
Kada kai jiddah tayi hawaye na gudu a fuskarta,kallon ya ibrahim tayi,kauda kansa yayi gefe haushi da takaici ya lullubesa,ya tabbatar karfe daya baya Amo shima akwai abinda yakewa jiddar na cutarwa ai mutum daya baya laifi,
Hada rai ibrahim yayi "ke kibar kallona ki kalli abbah kifada masa dalilin da yasa kika zagi mijinki da mazinaci,idan kuma wani abu yake miki na cutarwa yasa kika fadi hakan ki fada don nan dai kotu ce kowa zaa fitar masa da hakkinsa"...cikin shasshekar kuka ta soma magana,
*******
Driving yakeyi amma gaba daya hankakinsa a tashe yake,lallai zai nunawa Ramlah shi din shedani ne kamarta,zai bullo mata ta bayan gida...yasan target dinta amma yasan maganinta....
Ramlah kuwa kifa ciki tayi kan gado tana tunani idan har ta tsaya sanya bilal zai biyo mata ta bayan gida....mezai hana ta fasa komi cikin awa uku kafin bilal ya yunkuro?
Wata zuciyar tace,kiyi ma Abdallah massage kawai ku hadu akan kinason ganinsa kisa mata kuka ki bayyana video din nan....hannu tasa ta ciji yatsa,
Ba Abdallah ya dace yaga video din nan ba ummansa ce don itace bomb din zai tashi daga wajenta...nan ne kadai zansamu biyan bukata....
Drivin yake amma wayarsa ke hannunsa yana laluben wata number,"Mansoor....shine kadai zaisa muci uban yarinyar nan don mayen computer da waya ne"kokarin kiran numbersa yayi,a kashe,
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"ya shafa kansa ya bugi sitiyarin motarsa,
Gidanku zani,ya furta a fili ya karkata kan motarsa ya canja hanya ya miki sabon titin dake raba road.....
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:31 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*15*
Cikin kankanin lokaci jikin jiddah yayi zafi rau Tana kwance jikin ummah Tana rawar sanyi,"jiddah naji jikinki yayi zafi zazzabi ne ke damunki?meyafaru?"..cike da damuwa ummanta ke tambayarta,
Bakin ciki da takaici yasa abeedah jan tsaki ta mike ta fuce daga parlorn,wani kululun bakin ciki ya tokarewa yaya ib wuya ganin yadda jiddah ke rawar sanyi cikin bacin rai a fuskarsa yace "tashi ki shiga ciki ki sauya kayan jikinki kiyi sallah"
"Tou yaayah ib"ta mike jikinta sai rawa yakeyi,ummah kuwa kallo tabi jiddah dashi ta girgiza kai "wanan yaro to meyake damunsa haka?".
A kufule ib yace "wulakanci ne ai tantagaryar dan iska ne shiyasa ni tun farko bemun ba saboda dan girman kai ne"
"Yanzun dai bari muga zuwansa tukunna muji ta bakinsa tunda munji nata ai ko? Dole aji bangarori biyu ibrahim shine adalci"
Kada kai kawai yaya ibrahim yayi ya mike ya dubi ashmah dake zaune tana kallon film din labarina a tashar arewa 24 "ke kawomin abinci bangarena"be ce komiba ya fice,...itama ashmah ta mike ta nufi kitchen....
*******
A kofar gida Abdallah yayi parking motarsa ya kashe ya fito yayyafi ake ruwan ya tsagaita sai sanyi da garin yayi ya kwankwasa gate din gidan,mai gadi yaleko ta wata yar kafa ganin me knocking din yasa ya bude "barka da zuwa ranka ya dade"
"Barka dai baba,...nace jiddah ta dawo gidan nan kuwa?"ya tsare me gadi da ido cikin tashin hankali,
Irin kallon da Abdallah keyiwa baba yasa ya tabbatar akwai matsala yana hango tsabtsar bacin rai da tashin hankali a tare dashi , jimmm jadan baba yayi "ehh bata dawoba tun fitarta da shuaibu driver yazo ya dauketa bata dawo ba"
"Bata dawo ba?kace bata dawo ba?"muryarsa a dashe yake maganar cikin tashin hankali,
"Ehh ...bata...daw...o ba"
Da sauri Abdallah ya juya ya fice ko rufe kofar gidan beyi ba ya fada motarsa ya tada motar ya nufi gidan su ummah....
*******
Zazzaune suke suna cin abinci banda afee da juya cokalo kawai takeyi,hankalinta gabaki daya baya tattare da ita Allah yasa dai bawani abu bane ya sami Anty jiddah....bana fatan Anty jiddah taje gida da kumbyrarriyar fuskar nan domin ummansu bazataji dadi ba,
Cokalin fried rice ummah takai baki idonta ya sauka akan afee dake juya abinci tun dazun,"ke afnan meye Haka wani irin cin abinci kikeyi tun dazun?dubi yan uwanki kowa ya gama ke sai juya abinci kikeyi"
Kwalkwal afee tayi da ido nan da nan idonta ya kawo ruwa,ta kalli sashen da abbansu ke zaune yana cin abincu kamar hadin baki suka hada ido "yadai auta...menene bakison abincin ne?"
Yatsina fuska meenah tayi "babu wani rashin so abbah,iyayi ne don ta ganka ai ita ce suka dafa abincin tare da mai aiki ta taimaka mata..kawai dai taganka ne zata soma sanaben data saba"
Wani kallo abbah yayiwa meenah nan da nan ta natsu tati gummm da bakinta "ke afee meke faruwa kika kasa cin abince ne?"
Dire cokalin afee tayi kwallar da take boyewa ta gangaro mata,abbah ne kadai zai saurari maganarta saboda shi yasan hakkin dan adam don haka dole ta sanar dashi ta ankarar dashi shacin hannu data gani a fuskar jiddah,"ina jinki afee"...shiru parlorn yayi suna kallonta,wata uwar harara rumaisa ta watsawa afee da jan dan tsaki Wanda ita kadai tajishi..."abbah...dama ina jin tsoron kada wani abu ya samu anty jiddah ne naga har yanzun yaya Abdallah be shigo ba,kuma be kira yace yaga anty jiddah ba...dama ina zargin...naga..."..bata karasaba Abdallah ya bankado labule ya shigo ya tsaya cikin tsananin bacin rai da tashin hankali ...duka suka juya fuskokinsu akansa suna kallonsa,cikin kosawa ummah tace "kai kuma lafiya na ganka Haka?meke faruwa abdallah zaka shigo mana parlor babu ko sallama,me akayi ina jiddar?"ta jero masa tambayar tana karewa fuskarsa kallo, idanuwansa sunyi jajir,
"Ita tasan inda taje ummah...naje inda muka baro ta bansameta ba,na kuma je gidan mu bata nan bata dawoba me gadi ya shedar mun da Haka"
Mikewa afee tayi cikin tashin hankali ta dafe kirji "ya Abdallah bakaga anty jiddah ba?ka nemeta cikin airport gabaki daya?"
Kallon da Abdallah ya ma afee yasa taji hantar cikinta ta kada wanan karon fuskarsa ta bayyanar da haushi da bacin rai,"ina kikeso inje nemanta?haka ta daukarwa kanta ai afnan....abbah nagaji da halayen jiddah gaskiya shiyasa nake shirin kara aure don banason pressure"cikin daga murya yayi maganar,
Murmushi ummah tayi suka hada ido da rumaisa da mamaki ne karara a fuskokinsu duka yau Abdallah da kansa yake cewa zai kara aure?...
"Maganar banza maganar wofi"abbah ya karbe zancen yana nuna Abdallah da yatsa "don zakayi aure sai ka samu damar da zaka wulakanta matarka?kai Abdallah ka fita ka nemo yar mutane tun ban ci maka mutunci ba,da kake cewa zakayi aure har yaushe ka auri jiddah da zakai mata kishiya?wacece kake shirin aurowa?kanada tabbacin ita nata halin me kyau ne?to bari in fada maka mata duka halayensu daya don haka ka Shiga taitayinka kuma ka Nemo jiddah tun ban ci maka mutunci ba"
Ran Abdallah ya kara baci,yau mahaifinsa kecewa zaici masa mutunci saboda jiddah?koda yake abbah baya ganin laifi indai na jiddah ne "abbah banine nasa jiddah taki Shiga mota ta biyomu ba,tayi haka ne don ta ganni da Ramlah kuma ko zata mutu saina auri Ramlah don yar mutunci ce yar gidan tarbiyya"
Sai lokacin ummah ta ja numfashi ta karbe maganar gudun kada kalaman Abdallah su tunzura abbah ya hana auren "kai Abdallah kada insakejin kana fada mahaifinka Yana fada kaji na fada maka ko?kaje ka cika umarninsa tun ban saba maka ba"
Mikewa abbah yayi ya ratsa ta gefen Abdallah ya juyo ya kallesa ya kada kai ya wuce abinsa ko kallonsu beyi ba,
Afee kuwa hawaye ya gama wanke mata fuska tsananin tausayin anty jiddah ya hanata kwakkwaran motsi sai numfashi da take saukewa....fuhhhh Abdallah yayi hanyar fita ummah ta dakatar dashi "dakata Abdallah"...tsayawa yayi batare da ya juyo ba "idan ka fita idan baka ganta ba kaje gida ka kwanta na tabbatar tana gidan iyayenta da kanta zata kawo kanta idan abincin gidan tsoho ya gudureta don haka ka kwantar da hankalinka kaje mota ga rumaisa nan zata kawo maka abinci"...
Sa kai yayi ya fice,"rumaisa dau flask din can ki kai masa mota kada ya kwana da yunwa"
"Tou ummah"...
*******
Washe gari da safe,ya kasance saturday babu aiki,yana zaune gaban laptop dinsa yana bincika wani aiki amma gaba daya hankalinsa na wajen jiddah...sosai yakejin ciwon abinda tayi masa jiya wanan ai hauka ne wato tayi haka don ta wulakanta sa ko?zai bata mamaki don sai ta gane kurenta dikda irin son da yake mata ya lura dik iskancin da takeyi tana yinsa ne don taga yana sonta,
Tsaki yaja ya janyo wayarsa misscals yagani Ramlah ce tayi masa misscall wajen biyar be daga ba,sai yanzun ya tuna da yace zai kirata jiya don haka dialing wayarta yayi,
Tana zaune ta tasa cup din tea a gabanta ta kasa sha dik hankalinta na wajen Abdallah feedback kawai takeso taji burinta be wuce Abdallah ya aikawa da jiddah ta takaddar saki ba kawai a huta...kiran wayarsa ne ya fargar da ita daga tunanin da takeyi , murmushi tayi ta sauke sassanyar ajiyar zuciya ta danna recieve ta kara wayar a kunnenta tana lumshe ido "Assalamu alaikum"... muryarta ce ta daki dodon kunnensa a karo na farko a rayuwarsa dayaji faduwar gaba dangane da hakan....cikin wata iriyar murya yace "sorry i just saw your missed call ya kike"
"Fatan ka tashi lafiya,fatan ban tasheka a bacci ba kaida yar uwata...ina fatan jiya lafiya najika haka?"
Shiru yayi bayaso ya sanar da ita halin da yake ciki da jiddah don yasan bazataji dadiba ita keson jiddah amma jidda batasonta kishi take da ita,
Jin yayi shiru "umm sir Abdallah yadai"
"Umm umm..nothing babukomi ya wuce kawai just hope you are fine"
Jinjina kai tayi kamar yana ganinta cike da nishadi cikin zuciyarta tace sai kewarka sai son ganin kyakkyawar fuskarka da faffadan kirjinka da nake mafarkin kwanciya a kai koda yaushe...a zahiri ko saitace"yes sir...am fine ya ummah...fatan abbah ya huce gajiya"
"Ehh banje gidan ba yanzun nakeson zuwa in duba su"...
"Owk.... Ina gaida kawata"...
"Zataji"ya dire wayar yaja tsaki ya rufe laptop din ya ture table din ya nufi bedroom dinsa...
Jingina tayi da jikin kujera ramlah ta kurbi tea ta kumshe ido tana cin soyayyen dankali da kwai kanta babu dankwali sai gashinta da tayi parking dinsa a tsakiyar kai ,a karo na biyu kiran waya ya shigo wayarta,cikin natsuwa ta dire cup din tea din ta gyara zama dik tunaninta jiddah ke mata call...ganin number bilal da sunansa na yawo akan wayar yasa gabanta ya fadi,don tasan tabbas Bilal jiya yana cikin bakar motar nan kuma sai ya tuhumeta... tabe baki tayi saida call din ya kusa tsinkewa ta dauka ta makala wayar a kunnenta tana cigaba da cin dankwalinta...
Murmushi Bilal yayi sannin tabbad Ramlah tasan abinda ta hada yasa saida wayar ta kusa tsinkewa ta dauka,"ranki ya dade hajiya Ramla...ya kike"a takaice yayi maganar cike da izza,
Jan numfashi tayi tana tauna dankali dakyar ta amsa "lafiya...ya bilal how far?"
"Fine....nakira ne inyi miki bangajiya na ganinki da nayi a filin jirgi jiya na tarbar iyayenmu da kikazo...hope kin koma gida lafiya"
Murmushin mugunta tayi bilal kenan ta furta cikin zuciyarta,"lafiya lau...amma ina mamakin da ka kasa fitowa daga mota ka tarbi mahaifinka...sainaji ance rashin lafiya ne kakeyi hope badai ciwon soyayya kakeyi ba"...tayi maganar tana sauke murmushi da kada ido,
"Hmmmm Ramlah kenan...na fahimceki na fahimci inda kika dosa...tabbas kina buga wasa yadda ya dace domin film dinki Yana zafi sosai kuma zaki kasuwa sosai amma ribar da zakici nake jiye miki don kada garin neman tsagwaron riba ki nemo faduwa"
"Faduwa kam babu alamarta saidai...ina mai zargin kaki fitowa ne gudun jada jiddah tasan kai waye...amma kasan cewa matar abokinka ce jiddah ka fada soyayya da ita"ta tuntsire da dariya,
Mikewa Bilal yayi ya zauna daga kwancen da yake a makeken gadonsa..."bansan da hakan ba sai jiya"
Murmushi ramlah tayi ta juya bayanta kamar me duba wani abu "wayyooo nikam banajin tsoro don jiddah aminiyata ta ganni da mijinta saboda ni hak'ata tana gab da cimma ruwa...saidai hardluck nasan ciwon zuciya zai kamaka na soyayyar matar abokinka da ka fada batare da kasani ba"
Cije lebe bilal yayi zuciyarsa na tafarfasa ya lura ramlah tana gasa masa magana ne cike da gadara kamar wadda ta taki wani abu,to me ta taka da take masa haka?...datse wayar yayi ya jefar gefe ta furzar da iska....ya Kai wa hannunsa naushi jikinsa ya jike da gumi..tabbas Ramlah ta gwada shedanci ta yaya zai sanarwa da jiddah shi aminin mijinta ne?kuma dan uwansa da suka zama family friends?...wata zucuyar ta kwabesa...kada ka kuskura kayi wanan gangancin domin jiddah zata tsaneka....gara kayi yakin da zaka ceto ta ka mallaketa,
Zan mallakeki jiddah koda alakar dake tsakanina da Abdallah zata lalace harabada tunda Abdallah be dace dakeba da rayuwarki,
********
Shiru jiddah tayi tana zaune tsakiyar gado ta rafka tagumi,ashma da abidah suna zaune kasan carpet gefensu plate ne da sukayi breakfast saidai kallo daya zakai musu kasan suna cikin tashin hankali..."keko anty jiddah... Ramlah anya ba amanarki takeci ba da mijinki?ramlah ta cuceki anty jiddah"cewar abidah cike da takaici,
Hawayene suka gangarowa jiddah "banida tabbacin hakan...amma inada tabbacin namiji ba dan goyo bane tunda har Abdallah ya iya kwana batare da yazo gidan nan ya nemeni ba,batare da ya kira wayata yaji inda nake ba,hakan ya tabbatar mun da cewar ya tsaneni babu sauran zama a tsakanina dashi".. ta share hawayenta,
"Ramlah kuma anjima da yamma zan ziyarci gidansu zansameta,zanji dalilin da yasa take yawo da mijina a motarsa menene dalilinta na biyosa taryar sirikina?batada wata alaka da hakan...inaso insan alakarsu i will text her yanzun"...ta janyo wayarta,
Ashma cikin fusata take magana "amma wallahi wanan ramlar itace silar lalacewar zamantakewar aurenki don bakisan metake fadawa mijinki ba idan taje aiki tunda wajen aikinsu daya"
Girgiza kai jiddah tayi hawaye na kara wanke mata fuska,tabbas tanaji a jikinta kamar ramlah amanarta take shirinyi amma bataso ta gasgata hakan don zata iya hadiyar zuciya ta mutu....
Ummah ce ta turo kofar ta shigo da sallama "ke jiddah ga afnan kanwar mijinki tazo"...share hawaye jiddah tayi tayi murmushi "abidah jeki shigo da ita"
Abidah ta mike ta fice....
*******
Dakyar abbah ya amsa gaisuwar Abdallah "ina fatan kaje gidan matarka bikon ta don inada tabbacin,gidansu taje"
Shiru Abdallah yayi ya sunkuyar da kansa kasa,...ummah ta yatsina fuska "tou alhaji ai"
"Ai me...kada kicemun komi badake nake magana ba"
"Banason jin komi ka tashi yanzun ka ficemun daga nan,ka je kayo bikom matarka kuzo nan inada magana daku....sanan bazan amince da aurenka ba sainayi magana da jiddah"..dago Kai Abdallah yayi,ya bude baki zaiyi magana abbah ya daga masa hannu "dakata... banason jin komi...kaje kayi umarnina"..mikewa yayi jiki a sanyaye cike da damuwa ya kalli ummah ta kada masa kai yaje,
"Ina Afee ne?"abbah ya dubi rumaisa,
"Taje waec lesson"ta amsa masa...ya gyada kai ya maida kansa tv yana kallon labarai....
*******
Murmushi ramlah tayi bayan ta karanta massage din jiddah ta mike tsaye tana kaiwa da komowa cikin dakinta....wayarta dake hannunta ta lalubo video din tana kallo tana murmushi...."jiddah kinyi sake...inada makamai na yakarki"...ta furta tana cigaba da kallom video din
*SLIMZY✍🏼*[11/5, 7:39 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
WANAN SHAFIN NAKI NE *HASSYN MAMA WATTPAD* TARE DA DIK WATA MEMBER DAKE *SLIMZY FANS GROUP* INA MATUKAR ALFAHARI DAKU....NA GAIAHEKU KYAUTA *MOM SAEED*
*UMMY SUHANA*
*MAMAN ARFAT* JINJINA GAREKI *MOM* *AHLAN* (MARUBUCIYAR SAMIMA MACIJI YA CE)
*17*
Shiru jiddah tayi ta kasa magana hawaye ne kawai yake sauka a idonta,cikin shasshekar kuka ta soma magana "Abdallah baya sona ummah da Abbah ku rabani dashi kawai"ta cigaba da shasshekar kuka,
Kallon juna abbah da ummah sukayi,ya Ibrahim dake gefe ya gyada kansa,
"Kika ce baya sonki?meyasa baya sonki?"
Dago manyan idanuwanta tayi ta kallesa,ya tsareta da ido ko kiftawa bayayi tana iya hango tashin hankali da furgicin abinda zata fada a kwayar idonsa,tsanarsa tayi wani irin haushinsa takeji meye amfanin zama da mutum irin Abdallah dake kokarin jefata cikin halaka,
"Kiyi magana mana ke muke saurare kina bata mana lokaci"abbah ya daka mata tsawa,
"Bashida lokacina Abbah,sai lokacin aikinsa baya bani cikakkiyar kulawa a matsayina na matarsa koda hira kuwa,koda yaushe yana kan computer koda a gida ne....idan akazo magana ta auratayya kuwa?....."saita fashe da kuka,
.shiru parlorn yayi bakajin komi sao shasshekar kukan jiddah sai kuma karar gudun fanka ciki,shidai abbah shiru yayi don ya fahimci inda jiddah ta nufa itama ummah haka,shi kansa ibrahim yasan metake nufi hakan yasa abbah be zafafa sai tayi bayani ba ya dora da "kai Abdallah kaji abinda jiddah tace,ko kanada ja akan dik abinda ta lissafo?"
Muryarsa na rawa ya girgiza kai,hade da sunkuyar da kansa kasa "babu abbah...amma a gafarceni"yadda yayi maganar ya karawa yaya ib takaici,
"A gafarceka ka koma da ita ka cigaba da cutar da ita?bakasan cewar wanan abun zai iya jefata cikin halaka ba?ohhhh kasan da wanan cutarwar yasa kai ka fake da tana maka mugun halaye da rashin biyayya?to Abdallah kaine babban mai laifi ai, don in kotu akaje raba aurenku zaayi tunda baka musa ba"
Cikin kuka jiddah tace "Dan Allah kurabani dashi wallahi na tsanesa,bazan iya zama dashi ba ko kadan"
Zaro ido Abdallah yakeyi,mamakin jiddah ne ya lullubesa, jiddah ce ke cewa su rabu? jiddah me cewa rabuwa ita dashi sai mutuwa?kenan dama ba sonsa takeyi ba ta shiryawa hakan,
Gyaran murya abbah yayi "gaskiya wanan zama naku lamarine na a duba ayi tunani kafin a zartar da hukunci"
A fusace ibrahim yace "babu abinda zaa duba abbah daya wuce ya aikowa da kanwata takardar saki,baya sonta tunda idonsa ya rufe ya iya barota a dajin Allah batare da yabi sahunta ba sanan ga cutarwa"
"Ya isa ibrahim,inaga yaje kawai ya dawo nan da kwana biyu idan mun zauna munyi shawara da mahaifiyarta da yan uwana"
Shiru Abdallah yayi ya kasa ko motsi bare yayi magana, Ibrahim ya mike ya fice a parlorn,abbah da ummah tare suka tashi suka fita,
Dago jajayen idonta tayi suka kalli juna,ta sunkuyar da kai ta share hawayenta, zaune tayi babu me cewa kowa komi,dakatawa tayi ko zai bata hakuri ya mata alkawarin bazai sakeba bazai mata kishiya ba zasu zauna lafiya,
Shiko tunanin yadda jiddah ta shiryawa rabuwa dashi yakeyi,lallai mata abun mamaki ne koda yake beyi mamaki ba mace zata aikata abinda yafi hakan,
Mikewa yayi ya taka a hankali yayi hanyar fita,dago fuskarta tayi tabi bayansa da kallo wasu sababbin hawaye ke zuba a idonta..... Allah sarki Abdallanta baya Sonta yanzu,ya dace ta nemi mafita.....gyada kai tayi,yau awanni nawa basuyi magana da ya bilal ba Allah yasa dai beje gidan ba,gabanta ya fadi...ya dace ta kirasa,
A daki ta samu afee tayi tagumi takicin abincin dasu abidah suka kawo mata,tana ganin ta shigo ta zabura ta mike da sauri ta karasa wajenta ta ruko hannunta "Anty jiddah kin hakura zamu tafi tare ko?kun daidaita da ya Abdallah ko?"
Girgiza kai jiddah tayi "bamu shirya ba afee,kiyi hakuri zamana cikinku ya kare kinji?yayanku baya sona tunda har ya gagara bude baki ya bawa iyayena hakuri ya bani hakuri kinga ya gaji da zama dani,kiyi hakuri afee kizo kije gida kada ummah tayi miki fada"
Kuka afnan ta fashe dashi ta rungume jiddah....
********
Kallo daya zakaiwa guy din ka tabbatar da cikakken dan duniya ne,gashi ya tara gashi akansa yayi wani irin aski,karasowa wajen motar bilal yayi yana tsaye ya harde hannu a kirjinsa...hannu ya mika masa cike da faraa "barka da zuwa mai gida"bilal ya kada kai cike da kasaita,
"Barkanka black....aikine na dubu dari biyar cikin awa daya nakeso kayimun shi"jinjina kai black yayi ya shafi dan gemunsa,
"Wani aiki ne haka ranka ya dade"...
Shiru bilal yayi yasan waye black sosai yarone mai hankali da rike sirri abokanai suka maidaisa sai a hankali"sakatariyar aminina sunanta Ramla tana zama a nan badarawa kigo road..akwai video a wayarta... idan videon nan ya fita mutuncin mahaifina zai zube...banajin ta tawa sai mahaifina da kuma martabar karamar yarinya don bayin kanta bane"
Jinjina kai black yayi "kanason video din ya dawo gareka ne koko kanaso ayi hacking wayar da video din ke ciki harabada"
Gyada kai bilal yayi "ayi hacking wayar yanzun nakeso don na shiga kwakwalwarta...na tabbatar da zata fidda video din nan yau"
"Oga,idan akwai memory card cikin wayar ko anyi hacking bazaiyi ba amma zaka iya sanarmun da product na wayar kawai ninasan yadda zanyi wayar kacokan zata dawo hannun mu"...
Murnushi yayi bilal "ta yaya"....
"Ka bar komi a hannuna oga....kawai dai kasan product na wayar"
"I guest povour3xair ce tecno wayar"....
"Kana ganin karfe nawa zata bar unguwarsu?"
"Hudu zuwa biyar na yamma"...
"Kabar komi a hannuna"
"Kada a duketa ko a ji Mata ciwo kada kuma ai mata kwace"
"Bazanyi kwaceba oga wanan aiki mutuncinka,ne don haka bazatasan komi ya wakana ba"....
Hannu bilal ya dagawa black "i trust you"
*********
Dafe Kai Abdallah yayi a bedroom na ummah..."dik wanan damuwar Abdallah saboda waccen karfen kafar kakeyi?ka kwantar da hankalinka ka yada kwallon mangwaro ka huta da kuda...dama kanada shirin aure tou inaga yarinyar nan ramlah ita ta dace da kai itace zabina"...da sauri Abdallah ya kalli ummah,
Gyada masa kai tayi "kwarai itace zabina Abdallah...na tabbatar kaimun biyayya bazaka tabe ba,kuma Ramlah yarinya ce mai hankali da kai kanka kasan tafi jiddah"
Jan nunfashi yayi idonsa sunyi jajir,"ummah...ta yaya zanyi rayuwa babu jiddah a gurbin zuciyata"cike da damuwa yayi maganar,
Tsaki ummah taja "gurbin da jiddah ta fice ka cike da Ramlah don ita dama tafi dacewa da wajen don haka,ka bar musu yarsu su jika susha tunda kwana biyu suka bada to kafin kwana biyun ka aika da takaddar sakinta....ita da kanta zatai danasani kai mata saki daya mai ban haushi"
Idonsa na juyawa ya mike yanajin hakan a jikinsa,don yayan jiddah beda mutunci ya lura gadara yake masa shine ya zuga jiddah tai wanan maganar,idan ya saketa idan ana auren uwa daya uba daya sai yayi...kuma zai auri ramlah kodan ya zamewa jiddah jarabawa tunda ita bata iya tarairayar miji da jan hankalin miji ba..."ummah zanyi shawara zuwa goben"
"Shawarar dai itace ka rubuta takadda ka ajiye zuwa safiya"...
Kiran ramlah ne ya shigo wayarsa ya zaro wayar a aljihu yana ganin itace ya kalli ummah dake gefen gado"ramlar ce ke kirana"
Washe baki ummah tayi "Allah sarki yata yar halak me biyayya...dauka mana"
Karawa yayi a kunnensa,
Tana daure da towel da man shafawa hannunta jin ya dauka,ta lumshe ido "ina yini sir Abdallah"
"Lafiya lau...ya gajiya"yace a takaice,
Farrr tayi da ido "gajiya tabi lafiya...ya gajiyar abbah dasu ummah"
"Dik suna lafiya"
"Zuwa karfe hudu zanje in gaida ummah in gaida abbah ma,nayi missing su rumaisa"
"Tou ba laifi"yace ya dire wayar....
"Ya naga ka dire wayar ji yadda kake magana kamar basarake"cikin jin haushi ummah tai maganar,
Ajiyar zuciya yayi ya kama hanyar fita....har yakai kofa ya juyo "tace zatazo muku bangajiya...zatazo wajensu rumaisa"
Ummah ta fadada faraarta "saitazo... Allah ya kawota lafiya"ya fice...ummah ta watsa mai harara "komi abunka sai ka rabu da wanan bakar dagar yarinyar me ido kamar na aljanu".. taja tsaki ta shiga kwalawa rumaisa kira,
Da gudu ta shigo "rumaisa ku gyara antynku Ramlah ce wai zatazo"wani tsalle rumaisa tayi daidai shigowar afee,
Jiki babu kwari dakyar tace "ummah sannu da gida"wani kallo ummah taiwa afee,
"Ke kuma fa,ya naganki haka dik lesson din ne kika yamushe kamar wata albasa"
Girgiza kai tayi kanta na sarawa "bakomi kaina ke ciwo"
"Tou aje aci abinci"
Batare da tace komi ba ta gyadawa ummah kai ta fice ta nufi dakinsu....
********
Yana zaune yana cin lunch wajen karfe uku da wani abu jiddah ta fado masa a rai,"Allah sarki baiwar allah...nayi missing dinki inaso inganki"yace a fili,
Massage ya rubuta mata kamar haka.. *I miss you* *pure heart*
Tana kwance shiru massage ya shigo wayarta,kamar bazata bude ba ta bude....ta karanta ta girgiza kai Allah sarki ya bilal ta lumshe ido ....kyawawan idanuwansa sune ta hasko da kallonsa mai tsada hade da kyakkyawam sajensa da zara zaran eyelashes dinsa...I love you ta rubuta da manyan baki,
Jin massage dinta yasa zai kai abinci baki ya dire cokalin ya karanta...wani dadi ne ya lullubesa,
Lumshe ido yayi,yasani idan har jiddah tasan shine aminin Abdallah zasuyi daru da wuya ta yarda dashi amma zai shawo kanta...yasan tana gidansu don yanada labarin hakan daga mai gadinsu....idan har Ramlah batai nasarar fiddah video ba yasan zatai nasarar tona musu asiri idan har video din be fita ba bashida matsala...ya cigaba da cin abincinsa
******
Tsaye yake da farar shadda da hula kamar ba black ba, yana kallon hoton da bilal ya turo masa a waya ya hangita d bakar jallabiya da kwalliyar pink ta yane kanta....girgiza kai black yayi "amma kyakkyawace....saidai shedaniya ce"
Yana nan tsaye tazo daidaishi....keke napep tasawa hannu a tare sukasa don haka....sai ya tsaya gaban black....
Cike da yanga ta tako "nina fara sa maka hannu fa"
Murmushi black yayi "zamu iya shiga mu biyu ai ko indai hanya daya zamubi saiya saukeki ko yar kyakkyawa?"
Murmushin jin dadi tayi,kallonta black yayi tabbas ya yarda bilal yasan ramlah tunda ya sanar masa tanaso ace ita kyakkyawa ce dikda ita din kyakkyawar ce....
"Ina zakaje? legislative quarters zanje fa?"
"Can zani wajen zabib collage secondary"
"Waje daya ne nikuma wajen primary"..yana rataye da yar jaka ya shiga itama ta shiga....
Kallon drivern yayi ta madubi ya kifta masa ido....a guje yajasu wani irin gudu yakeyi sosai...jakarta ta zamo tana rike da gyalenta saboda iska...
Hannu yasa cikin hikima ya dau wayar sunata gudu,cikin kankanin lokaci black ya zura wayar jakarsa hannunsa na ciki yana mata magana suna yar hira a haka ya zare sim dinta ya maida cikin irin wayarta exactly yasa mata cover din komi da komi ya maida wayar inda ta zamo...taka burki me napep yayi wayar ta fado kasan cikin napep da sauri black ya dau wayar "kinga wayarki ta fado gashi"
"Ba doleba wanan jijjigar dama jakar karama ce"ta amsa tasa jaka "nagode"
A kofar zabib collage primary suka sauketa me napep yayi kwana black ya daga mata hannu yana murmushi....
Waya yasa ya kira bilal "wayar ramlah tana hannuna yanzun haka"
Murmushi bilal yayi "aikinka yayi kyau...turomin account number ka"
"Sai oga"bilal yace cikin ihu....
********
Gumi ne yake karyowa ramlah tun zamanta a parlorn...rumaisa da meenah sun cika mata table da kayan ciye ciye sai rawar kai sukeyi....
Afee na gefe rike da wayarta hankalinta na wajensu amma sam ko kallon inda suke batayi ba....idan ba gizo idonta keyi ba tabbas wanan wayar dake hannunta ba tata bace saidai wayar ce sakkkk babu banbanci har cover din,abinda yafi daurewa ramlah kai shine ya akai sim card nata ya iso wanan wayar?sanan ina videos da hotunan cikin wayarta?....ummah ta katse mata tunani "kici abincin mana ramlah nan gidanku ne ki saki jikinki"
Murmushi ramlah tayi ta sunkuyar da kai nan da nan wani kululun bakin ciki yasa hawaye ya soma sauka a idonta...bilal ya cuceta....zubawa ramlah ido ummah tayi itadasu rumaisa ganin tana kuka,
Cikin kidimewa rumaisa tace "lafiya kike kuka?me akai miki anty ramly"..girgiza kai tayi,
"Nasan cewar jiddah aminiyata ce tana gidansu a yanzun haka"..daure fuska ummah tayi tana gudun kada ramlah tace tazo bada hakuri a maida jiddah,saita katse ta,
"Ehh tana can ai iyayenta sunce raba auren zasuyi,sun goyi bayan yarsu tunda da kanta ta bude baki tace ta tsani Abdallah"...a furgice ramlah ta dubi ummah,
Ummah ta gyada mata kai "ehh haka tace kinga ko zama babu amfani tunda ta iya fadan ta tsanesa baya biya mata bukatun aure beda lokacinta"
Wanan furucin yabawa Ramlah hint na fasa maganarta....tunanin yadda zata tona asiri take taji wanan furucin hakan yasa ta kara samun kwarin gwiwa...."kayya jiddah tayi wawta tayi rashin hankali.kururuwar shedan ce ke yawo da ita nafada mata koda tasamu wanda takeso yafi Abdallah kada ta rabu da Abdallah domin shi miji ne mai nagarta....amma idon jiddah ya rufe,meyasa jiddah zatai hakan sanan na sanar mata da shi wanda takeso din jinin Abdallah ne tunda amininsa ne"tana kuka take maganar,
Sandarewa ummah tayi a zaune... Sallamar Abdallah yasa suka juya a tare......
0 comments:
Post a Comment