Kwankwasa kofar rumaisa tayi ummah tana tsaye gefenta,sau biyu rumaisa ta kwankwasa ramlah bata ko ce musu komi ba sai gyara zama da tayi saida suka sake kwankwasawa sanan kamar bazatayi magana ba tace "a bude ne a Murda a shigo mana wai waye ne yake kwankwasa kofar?"ta karasa tambayar tana yatsina fuska hade da watsawa kofar wata uwar harara,.
Cikin faraa rumaisa ta bude ta shiga ta budewa ummah kofar "shigo ummah"...ummah ta shigo "assalamu alaikum"tace cike da faraa tana kallon ko ina a parlorn kamshin turaren daki ne ya daki hancinta tadan gyada kai tace "masha allahu....komi acan acan iyyeeee Alhamdulillahi"tana rataye da jakarta,
Ramlah bata motsa daga zaunen da take ba saidai fuskarta babu yabo babu fallasa ummah ta karasa cikin parlorn ta nemi kujera ta zauna "y'ata amarya masha allahu"
"Barka da zuwa ummah,ashe kune ai bansani ba ma"tayi maganar a dakile daga zaunen da take,
Ummah kallonta tayi kamar ba ramlar da ta sani ba ganin yadda ta gaisheta babu wani girmamawa tana zaune kafa daya kan daya"yadai Ramlah...bakida lafiya ne naga yanayin naki hakan ko Abdallah ne ya tabamun yar tawa?"
Dan zaro ido ramlah tayi "me kikagani?kinga wani canji ne ummah...umhmmm ummah kenan babu fa karki wani d'an damu"
Girgiza kai ummah tayi ta dubi rumaisa,rumaisa ta juyar da kanta gefe kamar Bata fahimci me ummah ke nufi ba dan tasan kallon da biyu tai mata shi,shiru na dan wani lokaci sanan Ramlah ta katse shirun "ina afnan ne?...naga kowa yazo ganina ita kadai ce bata zo ba"
Yar dariya ummah tayi "afee tana gida batajin dadi zazzabi take fama dashi kwana biyu jikin babu dadi"
"Wayyo"....ramlah tace hade da kauda kai.....
Shiru ummah tayi kusan minti ashirin da shigowarsu ko ruwa ramlah bata basu ba,gyada kai tayi to kodai ita batasan ya kamata bane sai an sanar da ita?koda yake sabon aure ce batasan kan abun ba,abinda ta tuna shine da ta shigo jiddah ke fadawa kitchen ta cika mata gabanta da kayan ciye ciye kafin tayi abinci....gimtse wanan tunanin tayi "ammm y'ata a kawomun ruwa mai sanyi"
Abu na farko kenan daya fara batawa rumaisa rai,lallai ma anty ramlah wato saida ummah ta roki ruwan sanyi....katsewa rumaisa tunani ramlah tayi "amm rumaisa,dan shiga kitchen ki kawowa ummah ruwa da lemo mana akwai chichin da diblan ki dibo muku"tana kai karshe ta mike "ni bari in shiga ciki inyi sallah dan banyi azahar ba"
Ta mike tana kada kwankwaso wata tafiya ramlah takeyi tamkar da gayya take kugunta ne ke motsi a cikin doguwar rigar dake jikinta kanta ko dankwali babu,
Kasa hakuri ummah tayi ta dakatar da rumaisa data mike cike da kunci da bacin rai,ummah tace "ummm tabdijan ga wata sabuwar yar iskar.... Anya kuwa ramlah ce yata dana sani?dika yaushe akayi auren?"
Murmushin takaici rumaisa tayi bata cewa ummah komiba ta nufi kitchen ta dibo chin chin ya jero a tray ta dauko musu lemo fanta ta fito saiga ramlah da hijab a hannu ta fito "ammm rumaisa nasan fanta zaki dauko dan maida ki dauko muku sprite ko coke mana don fantar nan ta Abdallah ce naga yana so"
Kasa hakuri ummah tayi ta watsawa ramlah wani kallo "tou tunda na d'ana ne idan ya dawo ace nice nasha fanta dan dai nasan ko carton goma nakeso Abdallah zai siyamun'ummah tasa hannu ta bude fantar zuciyarta na tsananin tafarfasa,
Tabe baki ramlah tayi ta shige ciki abunta...
Rumaisa da ummah drink din kawai suka sha suka maida hankali akan tv.....sallamar kannen ramlah ce tasa su ummah maida dubansu a wadanda suka turo kofa cike da hayaniya,yar budurwa ce da yara maza biyu sai wata ma wadda zasuyi kai da me kama da ramlaj....rike hab'a budurwar tayi cikin ihu da daga murya "wooooowwwwww......masha allahu anty ramlah....haka gidanki ya hadu"tayi wani juyi dukkansu sukasa ihu cikin parlorn ko rufe kofar basuyi ba,
Ramlah ce ta fito sanye da hijabi jin hayaniya yasa ta fito ganin kannenta yasa itama ta saka kara suka hada baki "oyoyo antyn mu oyoyo anty Ramly munyi missing dinki"
Cikin faraa tace "nayi missing dinku nima sadik da yusufa...Antyn rashin kunya nayi kewarki kadan"suka kyalkyle da dariya,suka nemi kujera suka zauna kaff kannen ramlah babu Wanda ya gaida ummah sai kawar kanwar ramlah da sukazo tare ne suka hada ido da ummah dake faman kada kafa "ina yini hajiya"
"Lafiya...ke kadai ce kikaga mutane kenan "ummah tace a kufule,
Samm murnar ganin kannenta yasa ta mance wasu ummah...."fareedah tashi ki shiga kitchen ki dibo muku drinks da chichin kafin ayi abinci ko"
Zame dankwalinta tayi farida kitson da tayi ya kwanta a kanta itama gashi gareta kamar ramlah taja skirt dinta sama daya kamata ta shige kitchen....
*******
Bilal kuwa cikin gida ya koma ya nemi kujera ya zauna yana fuskantar kofar shigowa,turo kofar da akayi ne ya zabura ya mike tsaye yana kallom kofar,
Yana hango jiddah ko kallo cikin gidan batayi ba tana murmushi ta dagowa zee hannu "zee a gaida Ammiey kinji sosai fa?"
Gyada mata kai zee tayi "ok....ki gaida gwaggo saina shigo dikda nasan bazaki kara shigowa gidan mu ba dan kinada dalili"
Murmushi jiddah tasakeyi tana shirin bata amsa zee ta katseta "bye"ta datse kofar ....shafa sumar kansa bilal yayi ya furzar da iska,kallom tuhuma zee keyi masa dan wani takaici ne ke taso mata a cikin kasan zuciyarta kamar an hura mata wuta,fad'ada faraarsa yayi "my lill"...tura baki tayi idonta sukai kwal kwal kawai ta wuceshi bata ko bi ta kansa ba,kallo ya bita dashi tayi tunanin baya ganinta ta waigo suka hada ido ta sadda kanta kasa tayi cikin gida....
Dage kafadarsa yayi alamar ko a jikinsa ya koma ya zauna yana shafa sajen fuskar sa,tausayin zee yake don ya gama fahimtar dik inda ta dosa,
******"
Ana kiraye kirayen magriba ummah ce mamaki da al'ajabin abinda ramlah tayi musu yake mata yawo a tsakiyar kai,tunanin dama Haka halinta yakene ko zugata akayi?shine 'oyoyo ya Abdallah barka da zuwa"afee tace tana yar faraa hannu ya mika mata suka gaisa yana murmushi "auta ya jiki ance bakida lafiya"
"Ehh yaya zazzabi ne kawai amma naji sauki"tace tana kokarin barin parlorn,
Gaban Abdallah ne ya fadi tunda suka hada ido da ummah yaga tana ciccin magani yasan akwai wani abu, tsugunnawa yayi"ummah ina yini"
"Lafiya....ka dawo?"
"Ehh ummah nadawo, har kundawo daga can gidan namun ne?"
Ummah kamar jira take ta inda take shiga ba tanan take fita ba "Abdallah....bana abinda ka kwaso kenan?"
Cikin rashin fahimta Abdallah yace "bangane ba ummah mena kwaso meya faru?"
"Babu abinda ma bai faru ba Abdallah don naga abinda ya isheni yau ya ishi dakin duniya,wai Abdallah matarka daka auro yarinyar nan ramlah canja hali tayi koko zugata akayi koko dama haka take?"
Shiru Abdallah yayi,don tuni ya harbo jirgin ummah hmmm lallai ummah metakeso yanzun tace so takeyi tace Ramlah ma batada mutunci kamar yadda take cewa jiddah a baya "ina magana Abdallah kayi banza dani'ta daka masa tsawar da saida yadan furgita,
"Tou ai ummah ban fahimcu abinda kike nufi bane"
"Tou ina nufin bana ma ka auro mara mutunci dan wallahi wanan tantiriyar yar tasha ce ko ince karuwa tunda bakaga yadda ramlah ke kadamun gidan kashi ba,ni zata mike tana kadawa kugu kamar na bazawarin kare?ina kwankwason yake?ina abun yake wai maye yaci jariri?...har ruwa saida na roka a gidanka Abdallah?da aka dauko mun drinks matsiyaciyar sai cewa tayi fantar taka ce saboda kanaso?"
Da sauri ya dago ido yana kallon ummah,gabaki daya be fahimtar abinda take nufi dan duka duka yaushe akayi auren da har zata soma complain?wanan ma din batada tarbiyya ne?meyasa ummah ita kowa matsiyaci ne a wajenta?haka zaiyi rayuwa da ita kenan tana korar masa mata?
"Ammm ummah kiyi hakuri amma ina ganin be dace ace tun yanzun kinfara complain akan ramlah ba duka duka yaushe akayi auren?"
Rike baki ummah tayi "iyyeeee Abdallah? goro nasa zawo....hannun ruwa nasa atini ni zaka kalla ka fadawa wadanan maganganun?kana nufin karya nayi mata kenan?hmmm ta wanke wajen ta baka ka shanye ko kuma kai kasha wajen da bakin ka tunda idonka ya soma rufewa"
Innahlillahi.... Abdallah ya furta a fili yana zufa"meya kawo wadanan maganganun ummah?dik be kawo haka ba....kiyi hakuri ummah zanyi hukuncu kiyi hakuri"yace a sanyaye dikda zuciyarsa batai masa dadi da hakan ba....wanan shi ake cewa Allah kada ya kawo ranar yabo...dikda jiddah taci amanar aurensa amma shi kansa yana missing din ta sosai jiddah ce kadai take gamsar dashi a kwanciyar aure dik lokacin daya bukace ta,
Mikewa yayi babu kuzari jikinsa "saida safe"
Kwafa ummah tayi"allah ya tashemu lafiya....
********
Bayan ishai Ammiey ta shigo wajen gwaggo suna bedroom din gwaggo suna tattauna magana....sun dade suna wata magana da Ammie da gwaggo kafin daga bisani ammie da gwaggo suka jero a tare,
Jiddah na zaune tana kallon tv amma samm hankalinta baya wajen tv tunanin bilal takeyi jiya kwana uku daya wuce da suka hada ido taga idonsa yayi jajir....fuskarsa tamkar bashida lafiya ko meyasa hakan oho,
Tsaye ammiey tayi jikin kujera tana kallon jiddah sanan ta dubi gwaggo ta girgiza kai "Allah sarki baiwar allah"
Gwaggo tayi yar dariya,jin alamar motsi a patlorn yasa ta juyo idonta dana ammiey ya hadu...ta sunkuyar da kai ta zamo a kujera ta durkusa "Ammiy in..a yini"tace tana in ina...
"Lafiya lau amma kadan...don nayi fushi baazo gidana ba koh angaisheni"
"Zanzo in gaisheki ammiy"
"Nayafe yarinyata.... kibari ki karasa ibadarki kinji ki karasa iddarki ko?karki kara zuwa sai kingama iddah...ina kuma so kiyimun alkawarin ranar da kika gama iddah zakiyo wanka kizo gaisheni"
Dagawa ammiy kai tayi gabanta na faduwa tsananin tsoro ne ya kamata...."tou ammiy"ta amsa mata bataso tayi mata musu....
******
Koda Abdallah ya dawo yayi mamakin yadda ramlah ke fada masa ummah tazo sun sha hira,abun daure masa kai yayi....lallai lamarin ummah akwai duba....
Shirinsa tsaf yayi ya shige dakinsa .. Yana kwance yaga inuwar ramlah....tsaki yaja batare da taji ba hayowa tayi gadon ta kwanta a samansa ta kankamesa tana shafa kirjinsa... murginawa yayi "Abdallah....i need u"tace jikinta na rawa tana kokarin rarumo shi "dan allah ki saurara mun yau....nagaji babu abinda zan iya inace dazun da asuba saida na sauke miki nauyi?meye hakan wace irin jaraba ce wanan?mtswee yaja tsaki ya juya mata baya.....takaici ne yasa hawaye fara zuba a idanuwanta wani nabin wani tana zaune tayi poster tana kallonsa....
Shiko lumshe idonsa yayi take fuskar jiddah ta fado masa ya kara runtse idonsa bugun xuciyarsa ya tsananta.....meyasa ya kasa mance jiddah dikda cin amanar da tayi masa?.... fuskarta ya kara haskowa tana hawaye wani nabin wani lokacin da yaje gidansu....take jikinsa yayi sanyi yana sauke numfashi sama sama...meyasa dik bugawar da zuciyarsa zatayi sai ya tuna da jiddah?....kodan son da yake mata a jininsa yake?....takaici ne ya lullubesa da ya tuna da ta rungumi amininsa amma ta yaya?ya tambayi kansa....
*******"
A kwana a tashi babu wuya....watan ramlah biyu da aure inda yayi daidai da fitar iddar jiddah....ya saki jiddah da wata daya akayi biki inda ya kama jiddah watanta uku ciff.....
Bilal ya fito daga wanka yana goge kansa da karamin towel ammiey ta shigo...."ah ah ammiy ina kwana?"
"D'an ammiy.... antashi lafiya?"
Murmushi yayi ya saddan kansa kasa....zama ammiy tayi a jikin gado "to d'an ammiey....allah ya bada saa ya dace yau kaje neman soyayyar hasken rayuwarka...don yau gwaggo tacemun take fita idda"
Da sauri bilal ya yadda towel dinsa kasa be sani ba jikinsa ya kama rawa....annurin fuskarsa ya kasa boyuwa...mikewa ammiy tayi tana dariya ta fice ta rufo masa kofa....
Fadawa yayi kan gado ya zauna ya dafe kansa....fargabarsa daya ta yadda zai fuskanci jiddah....amma yau ba sai an kwana ba sai ta fuskanceta yanaso yaji muryarta.....yanaso yayi tozali da fararen idanuwan nan nata....lumshe ido yayi lokacin daya rungumeta a motarsa ya tuna.....da lokacin data mike zuwa kitchen tana tafiyarta mai daukar hankali ta juyo ta kallesa da kayan bacci jikinta ...shafa kansa yayi ya kaiwa katifa nushi....
*******
"Abdallah....wallahi baka isa ba,ta yaya zaai mutum samm beda lokacin matarsa haba Abdallah kasan menake ji kuwa?"tace hawaye na zuba a idonta jikinta na rawa,..w
Wata harara ya watsa mata "me kikeso inyi miki ramlah?waike shin harija ce?so nawa kikeso muyi abu daya nidake ke kisani gaskiya bazan dauki hakan ba,ashe jiddah tayi hakuri da batamun wanan maitar da kikemun kina like dani kamar tare aka haifemu"
Takaici ne ya kular da ramlah wato da jiddah yake kwatance "ehh ai bazata like maka ba tunda tana tare da kwartonta da yake rage mata zafi nima inaga so kake in nemi mw ragemun zafin"bata rufe baki ba Abdallah ya gaura mata mari,
"Ke ni kike cewa zaki nemi me rage miki zafi?wato kema kwarton zaki kawomin gida kenan,koda yake sai hali yaxo daya ake abota"
"Ehh ai idan nakawo kwarton kaine kaja....tunda baka da lokacin mace kai sai kace tsohom gunki...dan haka idan nakawo namiji banida laifi Abdallah....alhakin akanka yake...ka dandanawa mutum zuma a baki ka lashe"tana kuka take maganar,
Take Abdallah yaji kalmar ta na idan ta kawo kwarto ba laifi bane ya daki zuciyarsa.....kenan jiddah ba laifi tayi ba kenan tinda shi yaja batada laifi?....
********
Tunda ummah ta soma kai karar Abdallah wajen kanwar babansa , kanwar baban ta dubi ummah ta tabe baki "habiba kenan....hmmm wallahi alhakin jiddah bazai barku ku zauna lafiyaba...dik abinda kukayi ina sane dashi habeebah ya dawo kunnena wanan ranar nake jira,
Bakiji kunya ba?mijinki kin bijire masa kin xuga danki ya fandarewa ubansa gashi ubansa ya haye ya bar kasar?yanzun kina ganin Abdallah zakice masa matarsa batada kirki ne ya yarda bayan kece kikace ya aureta yar gidan tarbiyya ce?...hmmmm habiba Allah ya kyauta"
"Wallahi bazan taba bari a juyamin kan danaba wallahi bazai yuwu ba bazan taba yarda ba"
"Me kika isa kiyi yanzun?ai tun ranar gini tun ranar Zane habiba,bazakizo gidana kiyimun hauka ki daga murya makota su cikamun gida ba kin kawo karar Abdallah ne in kirasa to bazan taba kiransa ba akan maganarki ba dan babu ruwana"tana dire aya a zancenta wayarta tayi kara,
"Kinga dan halak yana kirana"...ta dau wayar "assalamu alaikum"
"Waalaikumussalam.... gwaggo kina gida?ina cikim damuwar wata magana'
"Wace magana kuma?"hajiya gwaggo tace tana kallom gefen da ummah ke zaune ta tsareta da ido,
Ajiyar zuciya ya sauke "fada muke da ramlah....ta jefeni da wata kalma nake wani hasashe nakeso inzo ki warwaremum"
"Tou sai kazo"ta katse wayar tana jinjina kai,
Mikewa ummah tayi a fusace "nina tafi sai anjima",
"Tou a gaida gida"...
****
Gudu Abdallah ke shararawa kamar zai tashi sama tsabar bakin ciki ko ganin gabansa bayayi ga faduwar gaba da ta tsananta a garesa.....tunanin furucin ramlah takeyi anya kuwa ba hakan yasa jiddah tayi abunda tayi ba amma ramlah yau tana fada masa zatayi ba laifi bane? ohhhh tazo ta sanar masa dana jiddah a matsayin laifi?kenan shine silar da jiddah ta koma huldar banza da abokinsa?....gumi ne ya karyowa Abdallah yana karya kwanar shiga street din...
LITTAFIN ZAINUL ABIDEEN DA IZZATA
2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL 07042277401 ..... COMPLETE DOCUMENTS MASOYA......
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:42 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*26*
A kofar gidan Abdallah yayi parking motarsa ko ciki be Shiga da itaba,fitowa yayi cikin sauri ya nufi makeken gate din gidan ya shiga kwankwasawa,
Mai gadi ne ya bude karamar kofar gidan don ganin me kwankwasawa suka hada ido da Abdallah nan da nan yaja da baya ya tsugunna "barka da zuwa ranka ya dade"
"Barka dai"Abdallah yace beko tsaya gaisuwar da suka saba ba ya shige cikin sauri a bayansa mai gadi ke tafiya cike da gulma yake tambayarsa "yau ko meke faruwa oho uwar tazo ga dan ya shigo a fusace,hmmmm kila dai wani gagarumin lamarin ne yake faruwa"juyowa yayi cikin sauri ya nufi gate wajen zamansa,
Da sallamarsa ya shiga parlorn idanuwansa sunyi jajir kamar gauta,tana inda take zaune ta fad'ad'a faraarta "oyoyo Abdallah na dikda nayi fushi ai Abdallah ka shareni ka mance da mamanka ko?"
Karasawa yayi ya tsugunna gabanta yana shafa kai "kiyi hakuri hajiya gwaggo....wallahi abubuwa ne suka sha kaina shiyasa banzo na gaisheki ba"
"Abubuwa ne sukasa ka mance dani uwarka Abdallah?kokuwa kanajin tsoron zuwa gaisheni saboda ka saki matarka ka auro aminiyarta?.... Abdallah kenan yanzun dik ba wanan ba mu gaisa Bari in kawo maka ruwan sanyi da lemo"tana karasa magana ta mike ta nufi kitchen dinta,
Bin parlorn yayi da kallo babu abinda ya canja hajiya gwaggo akwai tsafta gashi bata taba haihuwa ba itace kanwar mahaifinsa da ke mugun sonsa,kamshin turare ne ko ina a parlorn,shigowarta ne yasa ya daidaita natsuwarsa ta dire masa tray na lemo da ruwa da cup,da kansa ya dauka ya zuba ruwan exotic mai sanyi yasha sosai sanan ya ajiye ya sunkuyar da kansa,..
Shiru hajiya gwaggo tayi tana karantar yanayin nasa kafin tayi gyaran murya cike da lallashi tace "yadai Abdallah na?naga yau dan gwaggo kamar yana cikin damuwa,meya faru meke tafe da kai?"
Shiru yayi kafin daga bisani ya soma magana "hajiya....ina cikin damuwa mai yawa kai na ya kulle munkai matsayin da matar dana auro yau take cemun tunda bana bata kulawa banida lokacinta saina aikina itama zata kawo kwarto gidana kamar yadda jiddah ta kawo me debe mata kewa",
Tafa hannu hajiya gwaggo ta shigayi "Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...me kake fada haka Abdallah?ita amaryar taka take fadin hakan?kai dan kwal ubanka ban ganeba me kake nufi?"
Gumi ne ya karyowa Abdallah "irin matsalar da muka samu da jiddah kenan,gwaggo kaf mata na basu rasa ci ba basu rasa sha ba ballantana sutura amma basuda wani aiki daya wuce complain banida lokacinsu bana basu hakkinsu bana musu soyayya....gwaggo irin yanayin aikina wallahi banida lokacin kaina kuma dik abubuwan da nakeyi da kudin da nake nema inayi ne don in sama mana abinda zamu rufawa juna asiri....gwaggo am the kind of person that am not that romantic,ni banason nacewa mace inyita hira ina bibiyar mace kamar bindi wai soyayya Sam ba haka nake ba irin haka ne ya faru tsakanina da jiddah....ashe amanata suke ci itada aminina bilal shine na saketa na auri ramlah itama ga abinda take fadamun yanzun, yanzun abinda ke damuna be wuce tunanin jiddah da yake hanani sukuni dare da rana, babbar matsalar ummah na,basu jitu da jiddah ba tace batada tarbiyya yanzun ga Ramlah ma ta fara kawo complain dinta"
Tausayin Abdallah da haushinsa ne ya lullube hajiya gwaggo "masha allahu....haka nakeson ji Abdallah bakaga komi ba,ai dik abinda yake faruwa nasani inbaka saniba har gidan su jiddah naje mahaifinka ya turani da niyyar dawo da ita suka sanarmun da rashin mutuncun da kayi Abdallah haka na dawo babu gwiwa,sanan dik abinda kayiwa jiddah anfadamun"
Kallom gwaggo yayi cikin tashin hankali ya sunkuyar da kai cikim tsananin tashin hankali, gwaggo ta nisa "Abdallah,dik kudin namiji dik wadatarsa dik talaucinsa babu abinda mace take bukata a gareshi sama da soyayyarsa da kulawarsa,amma kai bakayi wa matanka hakan,babban damuwar ma ancemun har a cikin gida ma wuni kakeyi kan computer kamar bature,shin tayaya mace bazata bukaci me kulawa da ita ba?ko kasan babu balain daya wuce ace mace tasan dadin namiji a matsayin mijinta yazo be bata kulawa be kwanciyar aure da ita saidai ka jagwalgwala mace ka rabu da ita ka tayar mata shaawa batada yadda zatayi?gumi ne ya karyowa Abdallah yasa hannu ya share,
"Abdallah sai kace jahili?hakkim mace shine wanan abun da bakada lokacinsa idan ci da sha ne da sutura ta zauna gidan ubanta mana ayi mata?tunda ubanta yanayi mata daidai gwargwado?....mace tanaso idan ka dawo gida ka maida kanka gareta ka bata kulawa kuyi hirar soyayya kuyi hirar rayuwa ta nan ne idan wani abu na damunta zata iya sanar maka Abdallah,amma baka bata damar hakan ba ta yaya ko tana cikin damuwa zaka sani balle ka share mata hawaye?kayi kuskure babba a rayuwarka Abdallah gashi wajen yarintarka ka rasa mace mai nagarta kima mutuncu uwa uba tarbiyya kamar jiddah ga kunya"
"Gwaggo.... jiddah fa amanata taci itada aminina bilal"
Cikin tsawa gwaggo ta katse shi "uban waye yaja taci amanar?ka kama su turmi da tabarya?ko kaga lokacin da yacu amanar taka?...wai tsaya ka tambayi shi bilal din dalilin sa nayin haka?...bari kaji Abdallah kayi arziki da ba wani kato na titi jiddah ke muamala dashi ba,sanan wallahi bilal nasan taimakonka yayi amma idanuwanka suka rufe ka jefa kanka cikin danasani ga hakkinta da yake bibiyarka"
Sunkuyar da kai Abdallah yayi kalaman gwaggo suna yawo a kwakwalwarsa suna sauka cikin zuciyarsa kamar saukar aradu....ga tsananin faduwar gaba da fargaba da yake ciki wanda be san ta ko menene ba,kallom yadda yake gumi yasa gwaggo ta dauki remote na AC ta kara ta ajiye sanan ta cigaba da magana "kaine ka kama jiddah da bilal din da kanka?"
. girgiza kai Abdallah yayi batare da ya dago kai ba "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun... Abdallah to waye ya kawo maka wanan mugun labarin ka amince da hakan?"
Tsoro ne ya cika zuciyar Abdallah don yasan gwaggo zata iya marinsa,amma haka nan muryarsa na rawa ya soma bayani..."ammm...gwaggo ram...lah ce ta sanarmun da hakan,amma nasamu tabbacin hakan ne wajen mai gadin gidana don na tambayesa ko bilal din na zuwa gidan nawa?ya sanar mun da ehh....amma kuma daga baya...naji jiddah batasan cewa bilal aminina bane"
Dafe kai gwaggo tayi "Abdallah ka kashe ni,wallahi wallahi tun wuri ko bazaka dawo da jiddah ba kaje ka nemi gafarar ta dana mahaifinka don hakki ne ya fara yawo da kai tun baaje ko ina ba,sanan matarka dake gida tun kafin itama ka halakata ka bata lokacinta ka cire wanan son aikin dakasa cikin zuciyarka kamar wani bature hakan ne zaisa ka tseratar da ita daga fadawa halaka....sanan wallahi ramlah munafuka ce inada tabbacin tanada hannu wajen lalacewar auren jiddah kayi bincike,ka kuma yi tunani Abdallah"
Hawaye ne suka wankewa Abdallah fuska "gwaggo ki taimakeni ki fiddani daga cikin duhun da nake ciki,ina cikin tashin hankali narasa gane kaina musamman akan tunanin jiddah"
Shiru gwaggo tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya "duhun da kake ciki bani zan cireka a ciki ba saboda kaine ka jefa kanka cikin duhun ka rabu da hasken rayuwarka....gashi ita jiddah saboda me kunya ce bata fito ta fada maka zata kawo kwarto gida ba,wanan kadai ya isheka tunani Abdallah kasan cewar ka auro tsagera,....sanan mahaifiyarka kuma ka daina biye mata akan matanka dan wallahi in ka biyewa habiba sai kayi aure d'ari"
Jikin Abdallah ba karamin sanyi yayi ba hakika tabbas maganar gwaggonsa hakane amma meyasa idanuwansa ya rufe?....ta yaya zai nemi jiddah ya roki gafararta?...abbansa ya dace ya fara rokarsa gafara amma jiddah sai ya gudanar da wani bincike tukunna"
Shiru sukayi duka su biyun a parlor,wata uwar harara gwaggo take watsawa Abdallah cike da takaici , Abdallah mikewa yayi "gwaggo zan tafi.....zan dawo gwaggo"
",Bazaka tsaya kaci alkubus ba? shi zanyi fa?"
"Ah ah wajen aikinmu zanje akwai abinda zanyi submitting"
"Tou...Allah ya tsare kadaiji abinda na fada maka ko?"
"Naji gwaggo"
"A gaida mai dakin naka sai na jika"ta yunkura ta dauki tray din da yasha lemo ta nufi kitchen shima ya fice.....
********
Zaune yake a office dinsa ya dafe kansa....gumi ne kawai yake karyo masa furucin gwaggo ne ke yawo a kwakwalwarsa....dik abinda zakayiwa mace babu abinda take bukata face kukawarka da soyayyarka....idan tufatarwa da ci da sha ne ta zauna a gidan ubanta mana ayi Mata?...kansa ya sara....nan da nan kansa ya dauki carji....tabbas ya tafka babban kuskure na rashin bawa mace kulawa a rayuwarsa....wanan kuskure ya dauka amma meyasa jiddah zatayi masa haka?....wata zucuyar ta kwabesa kulllll Abdallah karka fara wanan tunanin,gyara ya dace kayi a rayuwar ka,ta yaya?....
Runtse idonsa yayi wani tururun bakin ciki ke tasowa daga kirjinsa yana fitowa ta bakinsa....duhu ya soma gani hakan yasa ya kife kansa a table dinsa kusan minti talatin yana tunanin yadda zai samu mafita.....
Mikewa yayi ya kalli agogon hannunsa wajen azahar nw yanzun amma sammm bazai iya aikin nan ba gida ya dace ya koma rufe office dinsa yayi ya fito ya samu sabon receptionist dinsa Ahmadi "Ahmadi"
"Ranka ya dade barka da fitowa"
"Barkanka....amm banajin dadin jikina zan je gida aai zuwa gobe idan Allah ya kaimu"
"Ok sir ... Allah ya kara lafiya"
Gaba Abdallah yayi be ko saurari me zai kara cewa ba.....
********
Tunda ya fito parlor yana zuba kamshi ammiey ke kallonsa tana murmushi,yayinda idon zeee yake kansu tana mamakin menene dalilin da yasa ammiy ke kallon bilal tana murmushi?
Tasowa yayi daga inda yake zaune yazo gefen zee ya zauna ya zuba mata ido,sadda kanta kasa tayi saboda yadda yayi mata kwarjini....yana kallon kaunarsa da soyayyarta a kwayar idonsa,amma ta yaya zai Saba mata da ta cire sonsa a zuciyarta?....."zee babyn Ammiey"cikin wani irin yanayi ya kira sunanta Wanda ya haifar mata da kasala....cikin jikinta taji wani yarrrrr da har saida ta kasa amsawa sai kallonsa da tayi
"Inaso ki tashi ki rakani zance kinji?...."ya kafe ta da ido yanason yaga yanayin nata...
Zaro ido tayi waje "zance yaya bilal?wajen wa?har budurwa gareka kenan"....mikewa ammiey tayi tana girgiza kai cike da tausayin yartata tabar parlorn....
Gyada mata kai yayi "ehh ...ko bakiso in sama miki anty?Antyn ma wadda kikasani ta zama matar yayanki?"
Take abinda walidah ta fada mata kwanakin baya ya dawo mata a zucuya cewar bilal jiddah yakeso....hawaye ne ya kawo a idonta da har ta kasa jurewa suka zubo....kafeta yayi da ido yasa hannu ya dangwalo hawayen "menene wanan zee?hawaye fa?kukan me kikeyi?ko bakiso yayanki yasamu farin ciki a rayuwarsa?"..
Girgiza kai tayi tana hawaye "inaso....inason farin cikinka koda ni zai zamemun bakin ciki"
Mikewa yayi ya basar da kukan da takeyi don bayason zuciyarsa ta karaya da tausayinta,a halin yanzun babu wadda zuciyarsa ke mararin gani kamar jiddah "goge hawayenki"
Ba musu tasa hannu ta share hawayenta, cikin in ina tace..."na share"
"Tou tashi ki rakani makota wajen jiddah"yana fadin haka yayi gaba....
Daskarewa tayi a zaune zuciyarta nayi mata lugude,shiko can kusa da gate ya tsaya yana jiranta ....yasa hannuwansa a aljihunsa....ya fidda ran zata fito kafin ta fito ya kauda kai bayason hada idonsa da nata....
Zaune jiddah take a parlorn tana makale da waya tana kyalkyala dariya Tana waya dasu abidah tana sheda musu zata dawo nan da sati biyu zee tayi sallama,..
Gwaggo ce ta amsa kasantuwar jiddah tana waya,hannu jiddah ta mikawa zee alamar ta taho gareta....gintse murmushinta tayi lokacin da Bilal yayi sallama cikin dakin kamshin turarensa suka gauraye parlorn.... mikewa gwaggo tayi don tasan da zuwan na bilal "sannu da zuwa yaro"..
Durkusawa yayi "ina yini gwaggo"cikin muryarsa mai sanyi,
"Lafiya lau mike ka zauna kaji d'ana kaima nan gidanku ne"
Datse wayar jiddah tayi ta wurgar a kujera cikin sauri ta mike tana fadin "muje ciki zee"..
Gwaggo ta dakatar da jiddah cikin tsawa "ke jiddah ina zaki?dakata"..cakkk jiddah ta tsaya batare da ta motsa ba "dawo ki zauna....kina ganin kinyi bako ne zaki tafi?tou wallahi kikabar parlorn nan sai nasa buhari yaci mutuncin ki idan yazo"
Cikin fada gwaggo tayi maganar sanan ta cewa zainab"muje ciki ko?"a sanyaye zee ta mike kishi ya turnuke ta tabi bayan gwaggo suka fice gaba daya....
Hawaye ne ya shiga zuba a idon jiddah kamar ruwa... mikewa bilal yayi ya karasa gabanta ya tsaya dafff da ita suna iya shakar numfashin juna....hawayen da takeyi ne yake ji kamar ruwan dalma mai zafi ke sauka a kirjinsa ...nan da nan yaji jikinsa ya kidime da tashin hankaki da damuwa... Tsugunnawa yayi gabanta ya tara hannunsa kamar mai addua hawayenta na duga a hannunsa hade da sunkuyar da kai kasa shima nasa hawayen na zuba.....
*******
Abdallah ne zaune da mai gadinsa Yana masa tambayoyi...."kace bilal yana zuwa gidan nan idan bana nan?"
"Ehh ranka ya dade yana zuwa...amma mafi yawancin zuwan da yakeyi mai dakinka ta yanzun itama tana zuwa a lokacin"gaban Abdallah ya yanke ya fadi,
"Kenan kana nufin Ramla tasan Bilal?"
"Bandai saniba ranka ya dade amma tabbas tana zuwa dan akwai ranar da ya rigata zuwa ma sai naga ta dawo da baya ta ciro wayarta a jaka ta danna wani abu naga ta daga wayar ta shiga kamar me daukar video,amma dai bansan metakeyi ba gaskiya....kuma ranar ma tare suka fito itada bilal din"
Gumi ne ya jika Abdallah cikin tashin hankali ya dafe kansa dake barazanar rabewa biyu.....me hakan ke nufi?kenan ramlah tasan alakar dake tsakanin jiddah da Bilal?zata iya sani wata zucuyar tabawa Abdallah amsa, saidai kada ka kuskura kayi bimciken da zai kashe aurenka a take...kasawa zuciyarka ruwan sanyi kabi komi a hankali karka sanarwa da ramlah binciken da kake Abdallah,wata zuciyar ta kwabi Abdallah,
Zaune yake akan bencin me gadi dan tun dawowarsa be shigar da motarsa ba ya ajiyeta a waje ya zauna wajen me gadi,
"Ranka ya dade badai wani abu bane ya faru ko?"me gadi ya datse masa tunani...
Girgiza kai Abdallah yayi "umm umm bakomi...ammm yaushe ne karshen zuwan bilal gidan nan zaka iya tunawa?"
Jimmm kadan mai gadi yayi "gaskiya an dade....don ranar da yazo da shigarsa da fitowarsa baai minti biyar ba kuma ya fito nagansa cikin wani irin yanayi mai kama da nadama"
Dafe kai Abdallah yayi tsoro da furgici ya cika Abdallah...to kodai bilal ya kwanta da jiddah ne yasa ya fito cikin nadama Saida suka gama yayi danasani?runtse idonsa yayi gabansa na cigaba da faduwa.... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun yake ambatawa cikin zuciyarsa
Mikewa yayi yana hada hanya ya nufi motarsa yayi mata key yayi horn mai gadi ya bude masa gate ya shiga......
Tana zaune a parlor ta harde kafa ta jiyo horn din motar Abdallah kallom agogo tayi "yau agogo sarkin aiki andawo gida da wuri haka?hmmmm ko anyi tunanin na kawo kwarton ne?"ta kyalkyale da dariya tayi farrr da ido "ashe yana sona yana kishina...hmmmm Abdallah kenan ka shigo hannu ashe"ta mike tana wata tafiya ta karasa jikin kofa,yana shigowa ta rungumesa shima rungumeta yayi wanan karon....mamaki ne ya cika Ramla...shiko wani abu me daci ne ya taso masa daga kirji...inama jiddah ce ya rungume haka?meyasa be nuna mata soyayya ba har taci amanarsa?...meyasa zuciyarsa ta kasa son ramlah?tambayar kansa yake....take binciken da yayi ya dawo zucuyarsa yadan janye jikinsa yayi mata light kiss a lips dinta....ji tayi tamkar ta suma don dadi sai ta kallesa taga idanuwansa sunyi jajir "yadai dear...meke damunka akwai wani abu ne?"
Batare da wani tunani ba yace "bakomi jiddah"zaro ido tayi cikin tsananin kishi tace "au yau nice na koma jiddah kuma Abdallah?...ai nasan dama zuciyarka tana tare da matarka to wallahi bazan yarda ba"cikin fushi ta fashe da kuka ta nufi dakinta....girgiza kai yayi cikin damuwa yabi bayanta.....
********
Kusan minti arbain yayi a hakan jiddah batada niyyar magana sai hawaye da takeyi....mikewa yayi ya tsaya dafff da ita yana mata wani kallo wanda yasa tsigar jikinta tashi nan da nan taji wani yarrrrr wani abu nayi mata yawo a cikin jikinta "am sorry love of my life.....jiddah nayi miki laifi nasani fushi kikeyi dani amma nasan kina sona don ina ganin soyayyata a wadanan kyawawan idanuwan naki farare tass masu haskaka mun zuciyata da rayuwata gaba daya"a karaye yayi maganar,
Wani kallo ta watsa masa,..murmushi yayi yasan dalilin ta na yi masa wanan kallon,zuba hannuwansa yayi a aljihu yana fuskantar ta yasa hannunsa ya dago fuskarta yana kallo "ki kalli kwayar idona kice baki sona....kice yanzun babu sona a cikin zuciyarki soyayyar mijinki ce cikin zuciyarki ni kuma nayi miki alkawarin fita a rayuwarki amma kafin in fita saina sadaki da mijinki tukunna amma cikin awanni ashirin da bakwai zaa sanar miki da sakon mutuwata"
Runtse idonta tayi "ki bude idonki kice baki sona jiddah....ki fadamun?wallahi kina sona jiddah nasan kina sona nima kuma soyayyarki ce fitilar dake haskamun rayuwata....soyayyarki itace tayi bishiya mai inuwar da ta zamemun garkuwa a yanzun haka,soyayyarki ce tayi rassa nabjijiyoyin dake cikin jikina ta zama jinin dake yawo a jikina zuwa zuciyata...."
Kwace fuskarta tayi ta kauda gefe guda.....murmushin nasara yayi a karo na farko......
MASOYA SLIMZY MASOYA LITTAFAI NA LITTAFIN ZAINUL ABIDEEN COMPLETE TARE DA IZZA TA AKAN FARASHIN MAI SAUKI ZAKI SAMU 300 DUKA BIYUN YI PAYMENT KI SAMU COMPLETE DOCUMENTS NA WADANAN ZAFAFAN LITTAFAI MASU DAUKE DA DARRUSA 2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL 07042277401
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:43 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
WANAN SHAFIN KACOKAN NAKI NE ANTYNA,
*AYUSHER* *MUH'D....* KAINUWA DASHEN ALLAH BA NA MUTUM BA...MAMAN *HUSNAH* DA *HANAN* ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'A.....👏🏼❤️SON SO FISABILILLAHI
*27*
D'aki ramlah ta shige ta fada kan gado ta fashe da kuka,tsaye yayi a bakin kofa yana kallon yadda take kuka gabaki daya ya kasa ko motsi irin wanan kukan jiddah take yawan yi dik lokacin da suka samu matsala....shasshekar kukan jiddah ce ta fado masa lokacin da ya mareta a daren da ta kwana a parlor.... runtse idonsa yayi yana jin wani abu na sauka a kansa tamkat tsawa,dafe kirjinsa yayi dakyar ya taka ya haye gadon ya janyota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta,cije bakin sa yayi yanajin wani abu mai kama da tuhuma a cikin zuciyarsa,anya zai iya jure zuciyarsa batare daya tuhumi ramlah ba?....lamo tayi a jikinsa ta dago fuskarsa tanayi masa wani kallo "kana son matarka ko?kana son ka dawo da ita ne?"tayi tambayar hade da tsaresa da ido,
Shima tsareta yayi da ido hannunsa na bubbuga bayanta ya daga mata gira daya cikin sanyin jiki yace "Ramly...ina son jiddah har gobe,kuma ban taba jin tsanarta ba tun abinda tayimun abun na bani mamaki sosai saboda nafara tunanin tafini gaskiya"..
Wata zabura Ramlah tayi ta shiga ja da baya akan gadon tana kada kai cikin tashin hankali "kana sonta? kace baka taba jin tsanarta ba?kuma kana ganin tafika gaskiya?"
Gyada mata kai yayi "tafini gaskiya ramlah...nine silar lalacewar rayuwar jiddah har ta fada aikata zunubi itada aminina nasamu wanan cikakken bayanin ne wajen kanwar mahaifina hajiya gwaggo,tabbas dik namijin daya kasance da irin halayena to tabbas yanada babban kaso wajen lalacewar macen aure da zataje bin wani namijin a waje,a halin yanzun ina yawan tsintar kaina cikin faduwar gaba dik lokacin da sunan jiddah ya fado min,a yanzun kema zan rinka baki hakkin aure da kulawa"
Hawaye ne ya wanke fuskar ramlah wani irin kishi ne ya taso mata a wuya wanda yasa takai hannunta wuyanta ta shake tana kakari cikin zafin nama Abdallah ya fuzge hannunta ya rungumeta ya hade bakinsu waje daya tana kuka tana kici kicin kwacewa yayi nasarar cafkar harshenta yana tsotso hannuwansa biyu kan breast dinta yana matsawa a hankali,lifffffff ramly tayi tana sauke numfashi a hankali ya cire bakinsa ya sauko wuyanta yasa harshensa yana lasar wuyanta da makogwaronta. Hannu tasa tana shafa sumar kansa tana bankaro masa kirjinta....har ya sauko kan boobs dinta ya dora bakinta nan ramly ta soma sauke numfashi tana shafashi cikin kasan zuciyarta bakin kirin kamar hadari....
*****
Wani kallo jiddah tayiwa bilal da ya hada hannuwansa "bana son inji komi bilal....kasan cewar zuciyata tanada rauni akanka ko?kasan yadda nakeji a dik lokacin daka kusanceni maana inda nake? banida kuzari banida karfin da zan iyayi maka hukunci bilal saboda zuciyata bazata iya jure hakan ba,nagano hakan ne lokacin da muka nisanci juna na wata shida....nayi kokarin in kofar da zuciyata hakura da kai amma sammm bugun zuciyata da numfashina kullum kici kicin fada sukeyi da juna akan soyayyarka.....soyayyarka itace numfashina itace bugun xucuyata dikda kasan zuciyata inajin radadin amanata da kaci ka kasa sanarmun da kai din waye, meyasa kaki sanar mun da kaidin aminin mijina ne saida ka shayar dani soyayyarka ta hanyar bani kulawa da kusanci bilal"hawaye ke zuba a idanuwanta,
Jikin bilal yayi sanyi "banci amanarki ba nayi hakan ne in ceto ki daga fadawa halaka da tarkon kawarki don na dade da fahimtar ramlah tsundumaki takeson yi a halaka jiddah".. dago manyan idonta tayi ta dora masa ko kiftawa batayi maana tana son karin bayani,
Gyada kai yayi "ehh jiddah, abinda yasa na kusanceki a lokacin zuciyata da ruhina da idanuwana sun rufe akan kaunarki domin nadade da sanin hotonki a instagram da Abdallah yayi posting....naso inyi yaki da shedan a lokacin amma kururuwar shedan data iblishiyar kawarki yasa idona ya rufe na fada soyayya da matar aure, tabbas nayi laifi na shiga hurumin aure amma kuma nayi hakan ne gudun karta hadaki da wani bayan ni matukar kikasan ni aminin mijinki ne bazaki saki jiki dani ba,a halin da kike ciki na bukatar namiji da soyayya da wanine ba nidin ba tabbas zaiyi nasara akanki zai iya kaiku da aikata masha'a wa iyazubillah....don haka nayi kokarin ni in ginaki akan soyayyata yadda zan kautar miki da hankali akan kula wani bayan ni jiddah..... sanan ina miki albishir da ko kinsan ramlah video tayi mana lokacinda..."nan ya kwashe komi ya fada mata da yadda sukayi da jiddah da wayaun da yayi mata a wajen black....
Ja da baya jiddah tayi ta fada kan kujera ta dafe kanta saboda jirin dake dibarta, rufe idonta tayi gabaki daya saboda damuwa da tashin hankali data shiga ciki tabbas bilal yayi mata laifi amma yanada kwararan hujjojin da ya dace ta yafe masa,hakika Bilal shine me sonta tsakani da allah ba Abdallah da yayi kokarin jefata cikin halaka ba,tabbas da bilal ne hakan ta faru bazaiyi saurin yanke hukunci batare da bincike ba, Abdallah ba masoyi bane Abdallah ba mutumin da zata zauna dashi bane,a halin yanzun taji Abdallah ya kara fita daga rayuwarta saboda baya sonta shine silar komi dikda tanada nata laifin.....
"Habeebty....."cikin wata siga bilal ya kira sunan jiddah ta shiga bude ido a hankali ta dorasu kansa....murmushi yakeyi mata wanda yasa taji kasala ta lullubeta kyau yayi mata wanda bata taba ganin hakan daga garesa ba,shima ita yake kallo sun dau tsawon lokaci a hakan kafin ya hura Mata isks idonta ya lumshe ta bude....."ina neman yafiyarki da afuwarki habeebty....sanan ina naiman soyayyarki a karo na farko mai cike da tsafta inaso ki zamo abokiyar rayuwata,sirrin rayuwata hasken rayuwata,farin cikina kece.... inaso ki zamo matar aurena mai juya akalar rayuwata"ya lumshe ido,
Mikewa tsaye tayi ta juyar da kai tayi taku daya biyu ta tsaya,shime mikewa yayi daga durkushen da yake ya taka ya tsaya a bayanta "ina sauraren amsarki wadda ita kadaice zata zamemun fitila a cikin duhun dajin soyayyar danake ciki"
Ajiyar zuciya taja sanan tace cikin tsanaki cikin siririyar muryarta "a halin yanzun bani da kowa sai kai bilal.....har yanzun zuciyata na cike da soyayyarka tana cike da d'okin kasan cewa da kai a karo na biyu sanan tana mararin kaunarka....da zaka kasance tare da ruhina da numfashina da sun daidaitu sun koma yadda suke watannin baya da suka shude"
Wani dadi ne ya lullube bilal murmushi kawai yakeyi kalamanta suna ratsa masa zuciya ji yakeyi tamkat ana watsa masa ruwan kankara a cikin kirjinsa....jin yayi shiru jiddah ta juyo suna hada ido kunya ce ta lullubeta ta rufe idonta a hakan ta kwashi sauri tayi kwanar dining area ta shiga dakinta taci karo da mutum da sauri ta bude idonta suka hada ido da zee wadda ta gifta ta gefenta ta fice "zeeeee"jiddah ta kira sunanta ko kallonta batayi ba ta fice tsananin kishi ko gabanta bata gani,
Itako jiddah murmushi tayi tasan zee fushi tayi na barin ta da tayi ita kadai.....bilal kallo yabi zee dashi har ta kai kofar fita ta juyo ta kallesa idonta cike da hawaye ta fice,....da sauri yabi bayanta
Karar rufe kofa yasa gwaggo fitowa daga dakinta sukai karo da jiddah a parlorn "ah ah jiddah...ina bakin sun tafi ne?"..
Sosa keya jiddah tayi dan batasan me zata cewa gwaggo ba sai kawai tace cikin in ina "eh...umm sun tafi kenan"
"Kaji shashasha wato tafiya kikai daki kikabar su bakisan tafiyar su ba? tou ai sai ki shiga daki idan kinyi laasar kije gidan nasu"
Kallon gwaggo jiddah tayi cike da fargaba,dan wallahi kunyar ammiy takeyi "ehh zuwa zaki kuma daddare inada magana mai muhimmanci dake kinji ko?"jinjina kai jiddah tayi alamar to ta sunkuyar da kai cike da fargabar me gwaggo zata fada haka ta juya jiki babu kwari ta shige daki ta rufe kofa ta danne kofar da bayanta ta runtse idanuwa tanajin wata natsuwa ta musamman tana shiga jikinta.....
*****
Saida Abdallah ya gamsar da Ramlah sanan ya murgina gefe yana sauke numfashi,ga idanuwansa da sukai jajir saboda tsananin shaawar da yake ciki hakika jiddah aljannar duniya ce don be tabajin gamsuwa tare da ramlah ba hasali kamas yake jinta babu wani armashi sabanin jiddah da ko tabata kadai yayi zata soma tsiyaya,ga wata niimah ta musamman da Allah yayi mata baya taba gamsuwa da jiddah saidai ya gaji da ita saboda yadda yake samun nishadi da ita,
Hannunsa ya dora ya tallabe kansa yayi pillow dashi,rarrafowa ramlah tayi ta haye jikinsa ta kwantar da kanta a kirjinsa tana shafa gashin kirjinsa ..."Abdallah...zuciyata ta karaya"shafo bayanta yayi cikin wani irin yanayi cikin wata irin murya yace "meyasa zuciyarki ta karaya meya faru?"
"Saboda kana son matarka alamu sun nuna kanaso ka dawo da ita kuma tabbas ko zaka dawo da ita sai an daura muku aure don ta fita idda"...dagowa yayi ya dan rungumeta ta gefe gabansa na faduwa dik tunaninsa jiddah bata fita iddah ba,ya manta da wata idda...gumi ne ya shiga karyo masa,
Sallamarsu ummah ce tasa ramlah sauya fuska tallabota yayi "kamar ana sallama naji ko?"bataso yaji ana sallama ba so tayi tai banza su gaji su tafi haka ta rarrafo ta sauko daga gadon ta zura doguwar riga ta fita,
Kamar jira yake ramlah ta fita ya dora hannu akai cikin tsananin tashin hankali ya furta jiddah ki gafarceni a fili....
Kofar ta bude tana ganin su ne tayi musu kallon sama da kasa sanan ta juya suka shigo su kuma,ummah da meenah da rumaisa ne suka nemi waje suka zauna,
"Kira mun d'ana tunda baki iya gaisuwa ba"
Murmushi ramlah tayi ta gyara tsayuwa tana kwantar da gashin ta daya hargitse"ayya mai d'a xan kira miki shi amma kibari yadan samu natsuwa don yanzun ya sauko a motar maji dadi"ta kashe mata ido "kin dai gane ko?"tayi gaba ummah ta bi ta da baki sake sanan ta furta "kutumar ubancan"...ta daga labule zata shiga tayi wa ummah gwalo,
Meenah sarkim zuciya "ummah anya bazamuci uwar yarinyar nan ba kafin mubar gidan nan?"tabota ummah tayi cikim takaici "kwantar da hankalinki yana gidan Naga motarsa"
"Ummah ce tazo, gasu can a parlor",
Tace masa lokacin ya watso ruwa ya fito,tsaye yayi a gaban madubi yana goge kansa da towel sosai ya tabbatar ya tsane sanan ya shafawa kan mai ya zura jallabiya ya fito,
"Barka da zuwa ummah,"
Wani kallo ta watsa masa "tabarka ka fito kenan"
Jimm kadan yayi sanan yace "ina yini ummah"
"Lafiya kalau, nace ban ganka kazo gidan ba shine nace bari inzo inga lafiyarka ni in gaisheka"yasani sarai gatse tayi masa tana binsa da kallo ya sunkuyar da kai,
"Ehh naje aiki ban dade ba nadawo gida ummah saboda bana dan jin dadi"
"Ya maganar zuwansu rumaisa umara ne? Naga an shiga watan koh?"
Fitowa ramlah tayi ta jika gashi tans gogewa "ah ah meenah ina drinks din da nace ki kawowa ummah kafin in fito in zuba muku abinci?'kallom juna ummah tayi da yaran saboda makircin da sukaji ramlah tayi matar da tabita da rashin kunya mamaki ne da tsoron allah ya lullube ummah,bata gama mamaki ba taji ramlah na fadin,
"Aiko dai dear su meenah da sun hakura da maganar umarar nan ummah"
A zabure ummah tace "ke saboda me?"
"Ummah ko last da muka hadu dake kinyi maganar nace miki umara tayi tsada saboda corona da akeyi baa shiga garin ma yanxun ne aka bude saudiyyar kuma tsada zuwan zaiyi gara ayi wani abu da kudin ko kin mance ne ummah?har kikace zakice ya siyamun mota da kudin?"galala ummah tayi da baki tana kallon ramlah "ummah kin fara rikicewa ne"ramlah tace cikin xolaya tana dariya,
Kafin ummah tayi magana Abdallah ya tareta "tou shikenan kinga ko hakan yafi inyaso shekara me zuwa nakara samun kudi dukkanku sai kuje aikin hajji akwai wata motar abokina da zai siyar zan siya in ajiyewa kaina ma kafin a koya miki mota in sai miki taki"
Wayar Abdallah ce tayi ringing ya ciro a aljihu md ne na wajen aikinsu da sauri ya daga "hello sir ranka ya dade barka da yamma"...shiru yayi ana masa magana sanan ya dora da "ok on my way sir ganinan zuwa"mikewa yayi "ramlah miko min makullin motana da sauri md na jiran wasu takaddu zai tafi dasu Abuja,
"Owk"tace cikim seconds ta miko masa "ummah ku jirani indawo"be jira cewar ummah ba ya fice cikin sauri,
Murmushi ramlah tayi bayan taji fitar motarsa "sarkin som kai da son yara?wato kinzo wa yaranki fighting su keta hazo ni matarsa ina zaune ko to babu inda zamuje duka"
"Karyarki tasha karya yar gidan talakaww?baki isaba wallahi nida yarona kice zakizo kifini iko dashi kece kika haifarmin shi naga d'ana ne"
Cije lebe ramlah tayi tana tunanin amsar da zata bata karaf tace "naga mijina ne ko?idan danki ne ai haihuwarsa kikayi kika Haifa mun shi baki isa kimun mulkin mallaka irin na jiddah ba,don haka ki zauna a matsayinki na uwa don ina bashi abinda baki isa ki bashi ba wallahi....kinga nan?"ta nuna gabanta "tou nan nake bashi kinga koda kike uwarsa baki isa ba"
Mari meenah ta shararawa ramlah bata ajiye hannuba ramlah ta kai mata tana nunata da hannu "harke kin isa ki mareni?kin isa dan kina kanwar mijina?kinyi kadan wallahi dik kika ka kara kai hannunki jikina saina mari wanan tsohuwar banzar mara godiyar Allah"ta nuna ummah,
Idanuwan ummah sunyi jajir saboda tsananin bakin cikin kalaman ramlah,rumaisa zatayi magana ta dakatar da ita "da kata rumaisa,rabu da ita zan nuna mata iyakarta wallahi,kuma na rantse da Allah sai kin rabumin da dana"
Dariya ramlah ta kyalkyale dashi ta nuna musu kofa "Dan Allah ku ficemun a gida zaizo gida ya sameku"
"Muje ummah,dan idan muka cigaba da zama zan iya shake matar nan wallahi ummah"cikin fushi meenah ke maganat jikinta har rawa yakeyi tayi gaba,ba haka ummah taso ba amma haka ta mike ta bi bayan meenah rumaisa ta take mata baya,
Suna fita ramlah ta nemi kujera ta zauna ta rafka tagumi "nashiga uku matukar hasashen da Abdallah yakeyi na dawo da jiddah ya tabbata,bazan taba bari jiddah ta dawo gidan nan ba tabar gidan nan kenan harabada"cikin damuwa ta dau wayarta ta kira Abdallah bugu daya ya dauka,
"Dearie...ammm su ummah sun tafi babu yadda banyi dasu ba kada su tafi suka tafi wai ka sameta a gida"
"Owk...gani nan a hanya ma"
"Ammm ankirani yanzun ummah na babu lafiya nace ko intafi ne?"
"Ehh kije daga gidan ummah zan biyo in daukeki"
Lumshe ido tayi "ok take care"ta datse wayar,
Sauri suke tayi ashmah da abidah yamma tayi ga gari na ruwa kannen jiddah ne,har Abdallah ya wucesu a mota gabansa ya fadi ya taka burki ya dawo da baya har yazo inda suke sauri sun wuce motar yayi shiru yadanyo kusa dasu cikin in ina ya tuna sunan abidah "ke abida"ya kira sunanta cikin wata irin murya,
Cakk suka tsaya suna bin motar da kallo daga sama har kasa sanan suka kare masa kallo ashmah uwar tsiwa ta janyo hannun abidah "dalla munje abinmu"
"Ke aysha ina wasa dake ne?ku shigo in rage muku hanya mana?"
Takaici ne yasa abidah kasa magana sanan abidah tanada sanyin hali irin na jiddah"mungode yaya Abdallah,bazamu iya Shiga motarka ba"
"Saboda me"yace fuskarsa Adan daure,
Aysha ta tabe baki "abinda ya hada ya raba,baxamu shiga motarkaba kayi hakuri koda da kake tare da anty jiddah balle daka rabu da ita take wata uwa duniya"aysha ta fuzgo abidah sukayi gaba,
Mutuwar zaune yayi a motar yabi bayansu da kallo yau shine aysha kewa rashin kunya? yaran da suke matukar ganin girmansa....take wata zuciyar tace idonka ya rufe lokacin da kayi naka rashin mutuncin a gidan......ajiyar zuciya yayi ina jiddah taje da yaji aysha tace Tana wata uwa duniya?gabansa ne ya fadi kodai aure tayi? girgiza kai yayi jiddah bazatayi aure ba,
Cikin rashin kuzari yake driving har ya iso gidansu ummah yayi horn mai gadi ya bude masa gate....
*******
Kuka sosai zee takeyi a gaban ammiy a durkushe Tana kan dadduma "ammy.....bazan iya jurewa ba dole in sanar dake inason yaya bilal....ki taimakeni kada in rasashi wallahi ina sonsa"ta ruko hannun ammiey...tausayin zainab ya Gama lullube ammy kallonta kawai takeyi,
Walidah tayi sallama dakin "yaya zee kizo yaya jiddah na parlor tazo wajenki"..jajayen idonta ta dago da niyyar tace ma walida tacewa jiddah batanan ammy ta karbe "jekice gata nan zuwa"
Walida ta fice,
Jiddah na zaune tana wasa da yatsunta zee ta fito idanuwanta sun danyi ja daidai nan bilal ya shigo hannunsa rike da carbi ya dawo massallaci kamshin turarensa ne ya sanarwa da jiddah isowarsa,cikin wani salo wanda batasan ta iya hakan ba ta dago fuskarta suka hada ido ta kada masa ido....lashe pink lips dinsa yayi ya kanne mata ido daya ya wucesu,
"Ke kuma sai kika tafi meya faru ne?meke damunki?kinga idonki yayi ja kawata"kamar zatai kuka jiddah ta tambayi zainab,..
Hmmmm bazaki taba sanin damuwata ba jiddah zainab ta furta a ranta sanan tayi murmushi "ciwon kai sosai kedamuna kuma naga kinyi nisa a shaukin son yayana"ta tsare jiddah da ido,
Farrrr jiddah tayi "kinsan ita soyayya wata abace da har in tana tare dakai to tabbas baka iya sukuni,hmmm ina rasa natsuwata dik lokacin da ya bilal yake gabana banida wani kuzarin daya wuce inyita kallonsa shi kadai ma yana kosar dani idan inajin yunwa"
Kishi ne ya lullube zee take ta kauda maganar ta sako wata hirar...bilal kuwa shigowa ya sakeyi da kwanon abinci a hannunsa jiddah kasa controlling kanta tayi saboda shagala da kallonsa jallabiyar daya sako ta amshesa,
******
"Ummah ashe kinki zama ramlah ta kirani tace tayi tayi ki tsaya kinki tsayawa"
Kawai ummah ta fashe da kuka saboda takaicin makircin ramlah "wanan yarinya tsinanniya ce bazataga annabi ba yanzun abinda ta fada maka kenan?to korar mu ma tayi fa"
Cikinwani yanayi Abdallah ke kallom ummah kamar wata zararriya zaiyi magana abbah ya shigo daga masallaci da alama ma yau ya daeo daga tafiya,
"Barka da zuwa abbah"Abdallah yace yana sunkuyar da kai, abbah ko kallonsa beyiba ya nufi sashensa,
Mikewa Abdallah yayi cikin wani yanayi ya dubi ummah "ina zuwa ummah, inaso im kashe wutar dake tsakanina da abban na"be jira cewarta ba yabi bayan abbah
Yana shiga Abdallah ya Shiga da sallamarsa "abbah"
"Dakata meka biyoni kaimun Abdallah?ka biyoni ka nunamin iyakata ne yau ma?ko ka biyoni kasanarmun da matarka ta fara ramawa tsohuwar matarka abinda akai mata?"
Tsugunnawa Abdallah yayi gaban abbah nan da nan ya soma hawaye"hakika nayi kuskure Abba,ban kyauta ba kayafemun inada niyyar zuwa rokonka gafara kasani ni din dan adam ne kuma ajizi sanan bazan taba ganin haske a rayuwata ba matukar mahaifina yana fushi dani...hajiya gwaggo ta nunamin kuskurena kuma na dauka....abbah ka yafemun sharrin shedan ne wallahi ina son matata ko yanzun haka da soyayyarta nake kwana nake tashi"
"Da kuka soma gane kurenku kaida mahaifiyarka ko?abu daya ya rage tayi mata dukan tsiya"
"Dan allah kayi hakuri kayafemun abbah"
"Nayafe maka Abdallah amma da sharadi"
Cikin sauri Abdallah ya kalli abbah hawaye na zarya a idonsa "sharadin shine kaje ka nemi soyayyar matarka kadawo da ita gidanka a matsayin matarka,sanan kuma baxan taba sa baki akan ta hakuraba yan uwanta su hakura saidai kai kayi aikin"
Share hawaye Abdallah yayi cikin wani yanayi yace "na amince abbah....ina son matata kuma zanyi wanan yakin zan jure"
"Tashi kaje Allah yayi albarka"....
*****""
Momyn bilal kuwa tunda ta soma kwararowa abban bilal bayanin da bilal yayi mata a waya irin wanda yayiwa jiddah yasa jikinsa yayi sanyi "yanzun me kikeso ayi momyn zuhura"
"Dadyn Bilal ka yafewa danka ya dawo garemu Kuma ka mara masa baya wajen auren wanan yarinyar da yakeso"
Jinjina kai yayi yaja numfashi "anything for you momyn zuhra...ki kirasa ya dawo gida sati mai zuwa nima ina bukatarsa akwai company dina ankusa karasawa penti ake yazo ya rike manager"
Wani dadi ne ya lullube momyn bilal ta daga hannu sama "alhamdulillahi"...zuhra kuwa da rufaida murna ce ta kashesu a wajen suka mike sukayi daki a guje suna dariya,
Dady ya mike"jeki hadamun ruwan zafi"
"Ok sir"momyn bilal tace tana sarawa mijinta cike da shauki da farin ciki.....
*******
Tagumi Abdallah yayi a parlor tun shigowarsu da ramlah... tayi shirin bacci ta fito da wasu kananan kayan bacci jajaye riga da wando tazo ta zauna gefensa tana kallon agogo "dear meke damunka ne?"
Kallonta yayi da jajayen idonsa da suka sauya kala,gaba days fuskarsa tadan fada "bakomi jeki kwanta"
"Ta yaya zan iya bacci inbar mijina a parlor cikin wanan halin?dan girman allah ka sanarmun meke faruwa"cike da fargaba tayi masa tambayar,
Kallom da yake mata ne yasa ta sha jinin jikinta ta tsananta faduwar gaba,
"Tou....tunda kin matsa abbah ne ya bani umarnin dawowa da jiddah gidan nan"...wani irin zabura jiddah tayi sai gata a tsakiyar parlorn tana ja da baya tana nunasa....take ta tuna da abinda ta fita tayi kafin ya sameta gidan ummanta....faduwar gabanta ta tsananta.... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun wani irin tsoho ne wanan dake neman tarwatsa mata farin ciki?
Shiko Abdallah mamakin reaction ne ramlah yakeyi meyasa take tsorata dik lokacin daya ambaci jiddah yana lura da yanayinta jiya zuwa yau....alamu sun nuna tamkar ramlah amanar jiddah taci ta auresa...me hakan ke nufi?kallom tuhuma yakewa ramlah tana kallonsa hakan yasa ta kara kidimewa.....take zuciyarta ta kwabeta kidimewarki zata rusa plan dinki ramlah....hakan na barazana da tonuwar asirinki.....nan da nan ta shiga neman natsuwarta tana kokarin saita kanta....cikin rashin kuzari ta dawo gefensa ta zauna gumi na karyo mata a fuska yana diga......
LITTAFAI ZAINUL ABIDEEN COMPLETE TARE DA IZZA TA GA MAI BUKATAR BIYUN YA BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN 2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL ME SIYAN DAYA 200 KACAL SIYAN NAGARI MAIDA KUDI GIDA 07042277401
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:43 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*29*
Wani irin tari sosai jiddah keyi ta dafe kirjinta,dakawa abidah tsawa ummah tayi "yanzun waye yace ki kawo wanan labarin yanzun tana cin abinci?gashinan ta kware ai sai ki dibo ruwa ki kawo mata kuma kada in sake jin kinyi wata magana kinji na fada miki ko?"
Zumburo baki abidah tayi tana kunkuni ta shiga kitchen sai gata da ruwa ta mikawa jiddah ta karba tanasha,
"Ke kuma daga maganar Abdallah sai ki kware?ina ruwanki dashi da har gabanki zaiyi faduwar da zaki kware?kada in karaji,kuci gaba da cin abincinku"umma ta juya tasa kai tayi dakinta,
Idanuwan jiddah sunyi jajir ba karamin kwarewa tayi ba don jin maganar tayi kamar saukar aradu,hakan yasa ta ture kwanon abincin ta kwantar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi sama sama,tsuru tsuru aysha dasu nafeesa sukayi dakyar nafisa ta hadiyi yawu tace "Abla...bamuci abincuba fa tun tasowar mu sai drink da muka sha a hanya ki daure mu karasa cin abincin"
Wani d'aci ne ya tasowa jiddah ta girgiza kai hade da murmushi "maza kici autar gwaggo ni na koshi anjima zan kara kafin in kwanta bacci yanzun bari inyi sallah kinga anyi magriba gashi bamuyi laasar ba ko"jiddah ta kike ta dau wayarta tabar side bag dinta tayi gaba,
Jinjina kai ashmah tayi cikin sigar gulma ta waiga ta ga jiddah ta shige sanan ta juyo tana kokarin yiwa abidah magana "ke abida karki kuma wa abla maganar Abdallah tunda gashi ta kware gaba bamu saniba ko mutuwa zatayi"
Cikin sanyin jiki abida ta amsa da kai ta mike tabar nafeesah da aysha a parlor ta shige ciki....
********
Zuhra da rufaida da momy bakinsu yaki rufuwa sun zagaye bilal a kujerar da yake zaune sai zuba masa hira sukeyi table din dake gabansa kuwa shake da kayan abinci kala kala,
Momy ce tayi magriba ta fito inda ta barsu nan ta samesu,rike baki tayi tana kokarin karasowa "ikon Allah yanzun bilal tun tafiyata bakaci abincin ba yaran nan sunata zuba maka surutu kamar an kwance radio?"tare suka kwashe da dariya,wani irin nishadi bilal yake jin kansa ciki yau gashi a gidan su yaga kowa saura abbansa,"momy sun dade basu ganni ba suna kewar yayansu ne shiyasa nima nayi kewarsu kuma nadawo da labarai masu dadi"
Tsalle zuhura ta daka ta koma gefensa "dagaske yaya?wani labarin ne hmmmm ai momy ta fada mana kun jone kaida anty jiddah a kt anata zuba soyewa"
Girgiza kai bilal yayi sanan ya nunata da yatsa "ke ina wasa dake ko?wato inata zuba soyayya nine nace miki hakan?"ya Kai mata harar wasa ta sunkuyar da kai ta toshe baki tana dariya kasa kasa,momy kuwa dariyar takeyi musu ta zauna nesa dasu,
"Assalamu alaikum"dady yayi sallama Tare suka hada baki "oyoyo dady sannu da zuwa"
"Ashe mutanen katsina ne suka dawo ai tun shigowata daga gate nake jiyo hira da dararraku kala kala"
Zamowa bilal yayi ya sunkuyar da kai cike da ladabi "barka da zuwa daddy ka iso lafiya?....kada kai daddy yayi cike da farin cikin ganin dansa daya tilo namiji "barka da zuwa big man"ya shafo kansa ya d'ago bilal ya rungumesa a kirjinsa yana bubbuga bayansa....kwallar farin ciki ce ta fitowa momy dake zaune tana kallonsu,....rike hannun bilal yayi "muje sashena muci abincun tare?"
"Kai daddy?ya bilal ya dawo zaka fara ko idan ba muma bin ku zamuyi ba?"cikim shagwaba rufaida tayi maganar hade da mikewa zuhura ma ta mike suka bi banyasu,
Momy ta daga hannunta sama ta furta "Alhamdulillahi"...sanan ta take musu baya suka watse a parlorn...
********
Tagumi ummah tayi tai shiru fuskarta dauke da damuwa tun bayan ta idar da sallar magriba ta kasa motsawa daga inda take zaune,tunanin yadda Abdallah ya iya kwanaki bezo gidan ta ya ganta takeyi ba wato saboda yayi auro ya auro jaraba? Abdallah danta ne ya juya mata baya yau? misscall nawa tai masa be dauka ba be Kuma biyo call din ba,
Afee ce tayi sallama dakin ta nemi gefen ummah ta zauna tana kallonta,tausayin umman ne ya kamata don tasan kaf yaranta babu wanda takeso kamar Abdallah,ruko hannun ummah afee tayi ummah tadanyi furgita tana kallon afee "ummah...ya naga kinyi tagumi? akwai damuwa ko?"
Girgiza kai ummah tayi kwallar da take boyewa ta zubo mata,sosai afee ta furgita da ganin yanayin na ummah tunda ta taso iya shekarunta bata taba ganin mahaifiyarta cikim wanan yanayin ba,yau ummah ce da kanta take hawaye?"ummah...nasan kina cikin damuwa kasantuwar ya Abdallah ya watsar dake beko zuwa gaisheki balle yaga halin da muke ciki ko?tun abinda ya faru rannan"
"Afee ina cikin nadama,tunda nake da d'ana be taba bijiremun ya gujeni ba gashi akan wanan almurar ya gujeni nasan wallahi idan jiddah ce bazatayi hakanba tabbas dik wanda ya tuna bara baiji dadin bana ba,ina so inga Abdallah ganinsa ya gagareni ko gaisuwa yana fushi saboda matarsa,hmmmm mata tafi uwa anya Abdallah zai.."da sauri afee ta toshewa ummah baki tana girgiza kai"kayya ummah kada kiyiwa ya Abdallah baki ya fada wani halin fiye da Wanda yake ciki domin yanzun haka yana cikin jarabawa ta mata,idan kikai masa abun zaiyi masa yawa don haka kiyi masa addua kawai ummah insha allahu zai dawo garemu kinji?.... alhamdulillahi nagode Allah da kike tunawa da anty jiddah da alherinta...kiyi addua kibarsaka damuwa cikin ramki kinji ummah?"afee ta langabar da kai,
Jinjinawa afee kai ummah tayi"Allah yayi miki albarka,tashi ki kawomin abinci"
"Tou ummah"ta mike cike da natsuwa ta fice....
*******
Karfe tara bilal ya shigo daki cikin sauri ya fito da wayarsa,domin hankalinsa yana wajenta tun daxun yanaso taji muryarta amma shiru,dialing numberta yayi ya kwanta rigingine kan gado yana kallom ceiling....
Gabaki daya yanayin jiddah ya sauya zuwa damuwa da tashin hankali tun labarin da abidah ta kawo mata sammm yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani Abdallah sunansa kadai yana iya sa ta kamu da ciwon da baxata iya warkewa ba,...kwance take tayi matashin kai da hannunta nafeesa na zaune a tsakiyar carpet tana famar chat sai aysha dake ma jiddah hira minti minti,
Ringing din wayarta da taji ta tabbatar shine don ringing dinsa daban,dago wayarta tayi ta duba sunansa ke yawo cikin manyan baki a fuskar wayar IQBAL...ajiyar zuciyar da tayi ne yasa dukkan su maida hankali akanta,....cikim yanga da kasaita ta dauki wayar ta kara a kunnenta cike da sanyin murya mai dadin sauraro tace "hello Iqbal"ta lumshe ido ta bude kyawawan idanuwanta masu kama da tanajin bacci,
Murginawa yayi ya fadada faraarsa "habeebty....ya kike?"
A kasalance cikin wata irin murya mai kama da damuwa ta amsada "lafiya lau...iqbal kaci abinci?"
Yadda tayi maganar yasa yadan gyara kwanciyarsa "habeebty yadai naji muryarki hakan?dik gajiyar ce?ko kinfara kewata ne intaho yanzun?"
Lumshe ido tayi "babu komi dake damuna sai tarin soyayyarka da taimun yawa take neman zautar dani wanda dana rufe idona na bude hancina yakan sunsino mun kanshin turarenka mai kamada miski"...tayi murmushin karfin hali,
Mikewa aysha da nafeesa sukayi suka fice suna yar dariya ta watsa musu harara ta gefen ido,
Haka kawai bilal be yarda da yadda jiddah ke magana ba, numfashi yaja ya sauke "look habeebty inaji a jikina kina cikin damuwa bakiso ki fadamun ne don haka gani nan zauwa kifadamun damuwarki don bakida wanda ya fini me zantaho miki dashi?"
"Hollandia iqbal"
"Saina zo"yace hade da kashe wayar ya mike ya zare singlet dake jikinsa ya dubi agogo tara ta wuce ya fada toilet dinsa nan da nan ya sakarwa kansa ruwan zafi ya fito ya bude wardrobe dinsa ya ciro milk colour din jallabiyarsa ya zura ya dauki makullin mota....
A parlor momy da daddy ne zaune suna kallom aljazeera ya fito,sosa kai yayi "daddy da momy barka da dare"
"Ah ah dan momy ina zuwa daddaren nan?"
Sosa kai yayi "inaso inci taraba ne shine zanje siyowa da hollandia"
"Tou a dawo lafiya kada a dade kadaiga tara ta wuce"
"Tou momy"
*******
Abdallah kuwa abincin da Ramlah ta zuba masa ya tasa a gaba ya kasa ci yayi nisa cikin tunani tana tsaye akansa,wani takaici ne ya lullubeta taja numfashi ta kauda kai gefe sanan ta juyo da dubanta gareshi "Abdallah ban gane maka ba fa?ko kaje neman auren ne an kasa ka?don naga alamar matarka ce a cikin kokom zuciyarka samm bakasan da zamana ba ma cikin gidan nan yanzun idonka ya rufe"
Wani kallo ya watsa mata wanda yasa tai masa wata harara cike da tsiwa ta juyar da kai,shiru yayi yana kallonta mamaki ne ya lullubesa,wato tau yau shine mace take wa haka?nunata yayi da yatsa "ke ina wasa dakene?ninayi kama da saan wasanki?ni zakizo ki rikewa kwankwaso kina fadamun magana kina harare harare kamar saanki?tou wallahi ki shiga taitayinki kinji na fada miki idan ba haka ba wallahi zan warware miki abinda bakiyi tunani ba"
Cije lebe tayi taja da baya tana kada kugu "wato tunanin wata da damuwarta ce tasa kazo zaka saukemun kwandon hauka a kaina nice nace ka saketa"bata rufe bakiba ya mike ya sharara mata mari ta dafe gefen fuskarta tana kallonsa idanuwansa jajir yake nunata "ni kike kira mahaukaci saboda rashin tarbiyya da dabbanci? Dan uwarki ni saanki ne?ohhh bake kikasa in saketa ba to ubanwa ya kawomun labarin tana kawo kwarto gidana ?"
Jikinta ne ya kama rawa tana ja da baya hawaye ya wanke mata fuska kad'a kai kawai takeyi tana ja da baya fuskarta ta jike da hawaye"ni ka Mara Abdallah?saboda matarka? lallai ma to wallahi baka isaba baka isa ka wulakantani dan xaka dawo da itaba ka watsar da soyayyata saboda ita kake marari yanzun"ta karashe maganar tana rusa kuka batare da ta matsa wajenba hannunta tana dafe da kumatunta,
A zucuya ya kara nunata da yatsa "waye yace miki ina miki cikakkiyar soyayyar da nakeyi yiwa jiddah?ai ita taci soyayya ta rage miki domin sud'in kwanonta kikeyi yanzun haka kuma wanan haukar da kikeyi ihu kike bayan hari don ina gab da warware wani al'amari wanda idan abinda nake tunani ta kasance?to wallahi kashinki ya bushe a gidan nan kuma wallahi bazan sakeki ba sai na dawo da matata gidan nan kin tabbatar da cewar soyayyar da nakeyi mata banayi miki kwatanta dubeki dorin dosano kunun bayan ludayi kawai...."hanyar dakinta ya nuna mata "wuce ki bani waje tun ban zucuya na sumar dake a wajen nan ba mara tarbiyya"
Cikim sauri ramlah tayi hanyar dakinta tana fadin "Allah ya isa tsakanina dakai mari na da kayi kuma sai na baku mamaki wallahi baka isa ka dawo da ita ba"tayi daki ya zabura ta kwasa a kuje ta fada daki ta rufo kofa,
"Da kin tsaya da kinga yadda zanyi wasan kura dake a wajen nan in maidaki gonar masara jahila"ya dawo a fusace ya zauna,
Tagumi yayi jiddah ce ta fado masa,lokacin data fito daga motar bilal ta shiga gida dawowarsu dazu,tsaye tayi jikin motarsa tana kallonsa fuskarta dauke da faraa fararen hakoranta ke walkiya da fararen idanuwan ta masu kama da madara saboda tsabar farinsu,hannu take daga masa lokacin da ya ke kokarin tafiya ta shige gida....ajiyar zuciya Abdallah ya sauke take yaji wani abu ya soki zucuyarsa sanan bugun zuciyarsa ya tsananta, hannu yasa ya kaiwa iska nushi ya mike gumi kawai yake zuciyarsa na tsananin tafarfasa,anya zai iya jure rara gefen nan?da zafi zafi akan bugi karfe wata zucuyar ta bashi amsa,kaiwa da komowa yakeyi cikin parlorn....tambayar kansa yake yaushe ne na saki matata jiddah?wani irin ganganci ne yasa na saki tauraruwar dake haska duniyar rayuwata?....tsaye yayi ya dafa bangon parlorn ya hada kansa da bangon ya fashe da kuka wanda besan dalilinsa na wanan kukan ba...kuka yakeyi wiwi kamar karamin yaro kuka yakeyi don yasan cewar da wuya jiddah ta sauraresa amma da zatai adalci data duba halarcin da yayi mata a rayuwar baya wanda shine silar samun farin ciki lokacin da take dafff da rasa mahaifinta....dafe gefen kirjinsa yayi tsohon ciwonsa daya dade be tasar masa ba yakeson tasar masa,
Abu yaji yana bin hancinsa kamar majina,yasa hannu ya lakuto...jini ne ke fitowa ta hancinsa saboda damuwa da tunanin da yake ciki wanda be taba tsintar kansa ciki ba,jiddah tasani yana sonta amma ta aikata abinda yasa suka nisanci junansu?an halarci jiddah ne donshi haka shima haka don haka babu wanda ya isa ya mallaketa a halin yanzu,bakin rai bakin fama saiya mallaketa.....takowa yayi a hankali ya karasa wajen tv stand ya dauki tissue ya warwara ya sa a hancinsa yana sharewa...gefen kodarsa suka takeyi masa kamar ana tsira masa allura,hakan yasa ya shiga share jinin dake fita a hancinsa yana yar da tissue din ya karasa three seater ya zauna ya sa hannu biyu yayi tagumi....
******
Misalin karfe sha daya na rana ya fito yana driving a hankali yana tafe zuciyarsa na wajenta ya dace ya saje ya tunkareta ko zatai masa adalci a soyayya,
A kwanar layinsu ya tsaya ya siyi exotic mai sanyi ya bude ya kwalkwala ya shanye saboda yunwar da yakeji dan koda yaje office ya kasa aiki a kwanakin nan samm baya iya zama a office gashi yana kewar kannensa,
A kofar gidansu yayi parking motarsa ya tsare gate din gidansu da ido,kusan minti talatin babu Wanda ya fito daga ciki ya ciro wayarsa nan da nan ya shiga latsa numbobinta da yake dasu akansa,yayi kamar ya kira sai ya fasa,
Text ya rubuta kamar haka....
*ASSALAMU ALAIKUM..yake zuciya maabociyar adalci da hakuri....zucuyata da taki bazasu iya rayuwa ba face da soyayyar juna,gani nazo gareki kiyimun hukunci koda kisa ne,zanfi farin ciki idan ya kasance kece silar rasa rayuwata don na mutu ne akan soyayyar yar halak maabociyar juriya da hakuri da yafiya..... sweetie kwana nayi da tunaninki wanda hakan* *yasa na kwana jini na zuba a hancina kodata daya tilo data rage tana sukarmun kamar ana tsuramun allura tamkar ajalina ne zai sauka....kifito insaki a idona in roki yafiyarki...ina jiranki...*
Ya dade yana karanta text din numfashinsa da natsuwarsa na kokawa da juna hade da tsananin tsoro da faduwar gaban abinda zai biyo baya....kallom text din yakeyi yana tunawa da shin Abdallah ne ya iya wadanan kalaman soyayyar?...meyasa ya kasa fada mata wadanan kalaman har ya bari ya rasa ta?shafa kansa yayi yayi sending text din ya runtse idonsa....
Kwalliya sosai jiddah tayi suna hotuna da su nafeesa sun shirya tsaff abida tace "Abla har yanzun ya bilal bezo ba gashi kince da wuri zamuje mu dawo kuma bezo ba'
Text ne ya shigo wayar jiddah ta dubeta "to uwar azarbabi kila shine ga text nan a wayata,ma ya shigo kila be samu wayata bane ya kirani kinsan sharrin network din gidan nan"fita tayi daga wajen camera ta shiga text massage ta duba inbox....tun daga ganin farkon number saman hannunta ya soma rawa ta kasa bude kundin massage din gabanta na tsananin faduwa kamar ansa mata mazari,dakyar ta bude kundin massage din taga dogon massage ta soma karantawa bi da bi....kafin ta gama karantawa ta jike da gomi powder data shafa ta soma d'iga idanuwanta sun kankace cike da tashin hankali...karanta massage din tayi sau uku jikinta na kyarma taja da baya ta fada kan gado tayi zaman yan bori,
"Lafiya Abla?meke faruwa?wani abu ya samu yaya Bilal din ne?"
Girgiza kai tayi tana shirin basu amsa maganarta ta makale special ringing din da tasawa iqbal ya soma, abidah ta dubi nafisa cike da d'oki "gashinan yazo dikda bansaniba amma na fahinci ringing dinsa kenan yau zaki zaga gari yarinya zakisan kaduna tafi katsina wurare"tabe baki nafeesa tayi ",naji wanan a labaran safe"suka kyalkyale da dariya....
A sanyaye jiddah ta dau wayar bilal "hello Iqbal kazo ne?"
"Ehh Ina kofar gida...ko kece cikin wata dalleliyar mota?ko har nasamu rival ne?"yayi maganar cike da tsokana da fargaba,
Dauke wuta tayi dan tasan tabbas motar Abdallah ce,datse wayar tayi ta dafe Kai ta furta "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun.... Abdallah kaxo ka tar watsamun farin ciki ka koremun nishadi na ka hanani rayuwa mai dadi? wallahi baka isa ba"ta zabura ta mike cikin rashin fahimta nafeesa tace ",Abla lafiya kike magana ke kadai?"
"Umm umm,muje yana waje kunga gashi nan yana kirana"ta daga wayar "gamu nan fitowa"
A parlor sukaiwa ummah sallama tana zaune da bakuwa "karku dade a dawo da wuri kunsan fadan yayanku dai"
"Tou ummah,saimun dawo"suka tafi,kallo ummah tabi jiddah dashi don tana hango damuwa a fuskarta,har sun kai kofa ummah ta kira jiddah ta juyo ta taho sumi sumi "gani ummah"
"Akwai damuwa ne?"tayi tambayar da tsare jiddah da ido,..
Girgiza kai jiddah tayi"babu komi ummah"
"Tou a dawo lafiya ki kula da kanki da kannenki kuma a dawo da wuri ina jaddada muku dan kar yayanku yayi fada"
Kada kai jiddah tayi ta fice...
Bakuwar dake zaune ta amshe maganar "yarinya tayi kyau tayi kiba abinta amma bakiga yadda mijin ya lalace ba,ni ji nayi ance ma basu shiri da uwar da amaryar da yayi a gidan kanwar mahaifin yaron najiyo wallahi naje gidan na tarar tanata mitar magana shine nakeji"
"Hmmm"ummah kawai tace ta kauda maganar da wata magana ta daban...
A waje tun daga nesa Bilal ke kallon jiddah ta cikin mota wani irin kallo yake mata wanda besan yanayi ba har ta karaso ta bude motar ta shiga ta shaki kamshin turarensa da sassanyar Ac data gauraye motar...
Su abidah ma suka shigo duka suka hada baki suna gaida bilal"ina yini yaya bilal"beko jisu ba idonsa na kan jiddah,
Nafeesa ta tabo aysha suka kwashe da dariya,yadan furgita ya shafa kansa yana murmushi ya tada mota..."barka dai iqbal"tace tana kallonsa idonta fallll da kwalla wani irin sonsa ne ke yawo a jikinta ga damuwa karara a idonta...kashe mata ido yayi hade da daga gira "barkanki my princess"ya sakar mata murmushi....
Abdallah kuwa jikinsa na sassarfa tashin motarsu ya hanga yayiwa motarsa key ya bi bayansu saidai sun danyi masa nisa amma tabbas su yake bi yana tafe yana tunanin inda zasu shin shi meye nasu na binsu? Dole ka bisu saboda haskenka tana tare dasu zucuyarsa ta basa amsa,
Ta madubin mota jiddah ta ga motar dake binsu, tsoro ya cikata ta kalli bilal "yadai?"ya tambayeta yana karantar ta,
Girgiza kai tayi "babu komi"ya maida kai akan titi,ta kara kallon madubin motar taga binsu yake sau da kafa, innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ta furta a zuciyarta sammm batason bacin ran bilal da damuwarsa shine tashin hankalinta,babbar damuwarta yadda zaiji mutumim da ko sunan Abdallah aka ambata sai yaji kishi...kara kallon bilal tayi tai narai narai da ido "fadamun habeeby"ya rada mata yana kare mata kallo,wata kasala takeji kamar ta rungumesa ta fada kirjinsa takeji...
Parking sukayi a wani katon super market da boutique dake marafa,suka fito,
Fitowa Abdallah yayi cike da kasaita dikda rashin karsashi amma hakan be hanasa tsare gida da hada girar sama data kasa ba, Yan matan dake harabar wajen kallo suka bi Abdallah dashi yana cikin suit,wasu Kuma bilal ne ya tafi da imaninsu saboda haduwarsa musamman yadda suka jero da jiddah....mutane dayawa fadi sukeyi sun dace....
Abdallah wajen receptionist yaje ya tambayi yadda ake payment na kudi aka turasa inda akeyi yaje wajen take ya nuna musu su jiddah da yatsa "kannena ne sukazo siyayya da matana da dan uwana zanyi muku transfer na 500k koda abinda suka siya bekai hakan ba kusha ruwa da canjin"
"Owk ranka ya dade"
Take Abdallah ya bukaci account number suka bashi yayi transfer ya juya ya fice....kallo suka kara binsa dashi matan dake wajen,
Wani bakin ciki ne ya tokare masa wuya numfashinsa ya soma kaiwa da komowa,saida ya saita natsuwarsa sanan yayiwa motarsa key ya nufi gidansu jiddah don ya jirasu...yana tuki ko gabansa baya gani hakan ya iso gidan yayi parking motarsa ya hade kansa da sitiyarin motar....
Siyayya sosai sukayi sukazo wajen biya bilal ya mika musu hannu suka gaisa "kayi total nawa muka kashe sai mu biya ko?"
"Ranka ya dade ai ya biya"
Kallom juna jiddah da Bilal sukayi suka hada baki "waye ya biya?"
"Ya biya yace shi mijinta ne kai kuma kaninsa ne si tare kuke shi ya wuce kafin ku gama inaga bari in duba sunan da akayi transfer din kudi 500k"
Wani wahaltaccen miyau jiddah ta hadiye cike da tashin hankali da bakim ciki,katse ta yayi "Abdallah mai kudi sunansa"
Nan da nan Bilal ya bugi table "uban waye yace ka amshi kudinsa?wayace maka tare muke?ce maka yayi matarsa ce?tou karya yakeyi ba matarsa bace matata ce"ciki daga murya Bilal ke maganar cikin fushi,
"Malam baa mana hayaniya anan dan allah kada ka nemi ka zagemu kuje can ku karata kada ku korarmun costumers"idanuwan bilal sunyi jajir ya dubi jiddah da hawaye ke zuba a idonta..."kinsan zaizo kenan"ya tambayeta a karaye,
Girgiza masa kai tayi "bansaniba iqbal ka yarda dani banason ganinka cikin wanan yanayin hakan zaisa in shiga mummunan hali iqbal kaine farin cikina"kuka take tana maganar,
Ruko hannunta yayi ya dubi mutanen dake kallonsu kamar masu wasan kwaikwayo yayi gaba da ita su abidah suka take musu baya zuwa mota,
Boot ya bude suka zuba abinda suka siyo duka "kada kisa abinda kika saiwa su zuhura matukar da kudin Abdallah ne"
"Tou tabbas muma zamu dire abinda muka dauka idan haka ne dan babu anfanin hakan"...lumshe ido yayi ya daga mata ido tasa,..tasaka ta zagaya ta shiga mota,
Tafe suke tana satar kallon bilal gabaki daya cikin fushi yake minti minti yana furzar da iska mai zafin gaske a bakinsa har suka iso....
Ta jikin glass Abdallah ya hango isowarsu,gyara zama yayi ya kashe AC ya fito motar ya harde hannunwansa a kirjinsa .....
MASU BUKATAR COMPLETE DOCUMENTS NA ZAINUL ABIDEEN DA IZZA TA AKAN 300 YA TURA CIKIN WANAN ACCOUNT DIN 2255398727 IDAN DAYA KAKESO 200 KACAL 07042277401......
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:43 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*28*
Mamakin yadda ramlah ke gumi Abdallah yakeyi kawai yana kokarin karantar yanayin nata tai saurin wayancewa Tana sosa kai "amm...tou shikenan tunda kana ganin zata dawo gareka"..
Maganar da tayi yayi saurin tambayarta "meyasa bazata dawo ba?...akwai wata kulalliya ko wani kulli a kasa kenan wanda kece kika sanshi?"ya karashe maganar hade da tsareta da ido cike da mamaki,
Inda inda Ramlah ta somayi tana sosa kai "ammm...ummm naga yanayin yadda tabar gidan ne shiyasa umm sweeet muje to mu kwanta mana ni inajin bacci"ta kauda maganar ta hanyar marairaicewa cike da shagwaba,..
Wani irin kallo Abdallah ke jifan ramlah dashi wanda yasa tasha jinin jikinta ta kauda kanta gefe zuciyarta ta tsananta bugawa,yana kallon yadda kirjin ramlah ke safa da marwa,meyasa ramlah keyin abubuwa kamar na marasa gaskiya?....meyasa tace kana tunanin zata dawo gareka ne?...kodai akwai wani kulli da ramlah tasani wanda shi be saniba?meye dalilinta na daburcewa bayan itace take kukan kada ya rabu da jiddah a lokacin?itace wadda kejin tausayinsa lokacin da take sharbar kuka a parlorn momy?
Ruko hannun Abdallah tayi cikin sigar shagwaba murya kasa kasa "umhmm umhmmm....dear ya naga dik yanayinka ya canja meyake faruwa?"ta sargafo hannunsa cikin nata tana murza hannunsa,
Kauda kai yayi cikin yanayi na damuwa sanan ya juyo da sauri ya tsura mata ido lokaci daya ya jefa mata tambaya"amm meyasa yanayinki yake canjawa dik lokacin da nayi maganar jiddah?....meyasa kikayi kuka don nafada miki abinda abbah yace bayan kece bakiso in rabu da ita a baya kike kuka?amma yanzun bakison indawo da ita meye dalili?....sanan furucinki yanada maana da kikace kana ganin zata dawo gareka ne?what do u mean?"....kallom da yake mata ne yasa gumi ya karyo mata lokaci daya ta tsinci kanta cikin tashin hankali don tana iya hango tuhuma karara a kwayar idon Abdallah....hakan yasa tai saurin saita natsuwarta ta zare hannunta daga nashi ta juyar da kanta gefe guda cikin minti biyu hawaye ya wanke fuskarta sanan cikin rawar murya tace,
"Kana tuhumata ko?nasan yanzun kana tuhumata da rabaka da matarka dikda nayi hakan ne don in ceto ka daga kangin da kake gabb da shiga....sanan maganar da nayi niba da wata manufa nayita ba,dama nasan hakan zata kasance saboda kana son matarka kuma bakayimun kwatankwacin son da kakeyi mata....zuciyata ta karaya nafara jin tsoro"
Ajiyar zuciya ya sauke ya janyota jikinsa ya rungumeta sosai yana kallon kwayar idonta yasa hannu ta share mata hawaye "its ok....i cant deny of course inason jiddah and ko bayan rabuwar mu still nakasa cireta cikin zuciyata and yanzun hk xuciyata ta sanarmun da nine silar komi and i am ready in gyara laifina kema kiyi hakuri rashin hakkinki da kulawar da bana baki....and sorry to say kibar wanan tunanin kowa da matsayinta cikin zuciyata don haka lets go and sleep"kafin tayi wani yunkuri Abdallah ya kinkimeta a hannunsa,kallonsa takeyi amma fuskarsa tayi mata bakin kirin furucinsa agareta kamar ya watsa mata rushin wuta,tabdijan wallahi akwai matsala sai nayi maganin jiddah wanan karon don tabbas nabari ta dawo gidan nan ina gidan nan naci baya kuma ba sunana ramlah ba sanan niba yar halak bace jinin buzaye.....
********
Makale jiddah take da waya suna hira da mutanen gidansu abidah daga gefen aysha ta fuzge wayar a kunnen aysha,
"Albishirinki Abla wai kinsan munga wanan kidahumin mutumin?"
Cikin rashin fahimta jiddaj ta yatsina fuska "wa ke nan abidah?waye kuma kida humi ni hauwau"
"Hmmm to Abdallah tsohon mijinki"jiddah ji tayi kamar abidah ta soka mata mashi a kirji "kuma in fada miki dan beda kunya harda cewa wai mu shiga mota ya rage mana hanya ya kawomu gida abla,nikam bamu shiga ba nan muka barshi ko sallama bamuyi mushi ba mukai tafiyar mu,hmmmm bakiga yadda ya susuce ya koma ba jin munce wadda zaiyi don ita bata gari ya razana nan da nan yanayinsa ya sauya"gaban jiddah ne ya fadi taja ajiyar zuciya ta tabe baki,
"Bani ummah inyi magana da ita abidah kin cika ni da surutu da wani labarin Abdallah can sai kace na tambayeki ko ina ruwana dashi oho"
Shigowar bilal parlorn yasa ta tsaresa da ido wayar na makale a kunnenta ta kashe masa ido daya,shiko tsaff yaji ta kama sunan Abdallah lokacin da yake kokarin shigowa hakan yasa ya tsinci kansa cikin tsananin kishi da tsoro don beji statement na jiddar ba,
Karasowa yayi parlorn nafeesa ta fito dakin gwaggo sukai karo "ya bilal barka da zuwa ina yini?"
"Lafiya lau nafee ina gwaggo"yayi maganar cikin wani yanayi muryarsa a shake,idanuwansa sunyi jajir yana kuma kallon gefen jiddah da itama wayar takeyi amma hankalinta yana kansa,
"Gwaggo ta dan fita nan baya gaisuwa"
"Owk"yace ya zagayo ya zauna a kujerar da take zaune...wucewa nafeesa tayi tana waigen bilal da yanayin nasa,
Wayarta takeyi da ummah "ummah insha allahu zan dawo bada dadewa ba inaga cikin satin da zaa shiga zanzo haka kukayi missing dina?besan me ummah tace ba yaga jiddah ta turo baki gaba ta soma shagwaba,
Shagalta yayi da kallonta dikda zafin da kirjinsa keyi masa ita ko Allah Allah takeyi ummah ta katse wayar beko san ta gama wayar ba saida ta hura masa iska a idanuwansa,
Juyar da kai yayi gefe, Bata fuska tayi cikin yanayin nata na shagwaba "Iqbal....what umm?menayi kuma don allah"ta turo baki,
Wani kallo yayi mata dikda yaji dadin sunan data kirashi dashi amma ya kauda kansa gefe daya ta mike da sauri ta dawo gefen daya juyar da kai ta kai fuskarta kusa da tashi ya kara juyowa da ita gefe daban ta mike da sauri ta koma gefen ta kira shi "pure heart....what did I do"ta tabe baki "haba Iqbal kayimun magana mana"nan da nan idonta ya kawo ruwa,
Kallonta yakeyi yadda idonta ya cika da kwalla yaja numfashi ya sauke..."habeebty am scared"yayi maganar a raunane kamar zaiyi kuka,
"Why are you scared iqbal? scared of what?me kake nufi da cewar kanajin tsoro iqbal?"
Girgiza kai yayi yaja numfashi ya sauke idanuwansa sunyi jajir yana kallonta,yadda ya sauya yasa tadan tsorata cikin kidimewa da tashin hankali karara a fuskarta take kara tambayarsa "Iqbal what ka sanar dani wani abu ya faru ne?haba masoyina?kanaso in fada duniyar da numfashi ma zai gagareni ne?ta yaya zanganka cikin wanan yanayin ina tambayar ka kakasa sanarmun?"
"Inajin tsoron kiran sunan mijinki a bakinki watarana yayi barazana da in rasaki don nasan cewar Abdallah baxai taba barinki ba kuma wanan karon bazai samekiba jiddah inhar ina numfashi,idanko yayi kokarin kwatarki ta karfin tsiya dani dashi dik zamu rasaki don zamu bakunci lahira"cikin rawar murya da huci yake maganar,
Dafe kirji jiddah tayi "subhanallahi iqbal me kake fada hakan?....ohhh shigowar da kayi kaji na ambaci sunan Abdallah yasa hankalinka ya tashi?"
Daga mata hannu yayi wani sabon kishi ne ya turnuke bilal jin ta kara kiran sunan Abdallah a karo na biyu"kiran sunansa da kikeyi wallahi zan iya rasa raina jiddah kinji na rantse wai kinsan meye so kuwa?'
A razane tadanja da baya ganin yadda ya sauya kamar mahaukaci "haba Iqbal kiran sunansa a bakina tamkar kuskurene wanda a rayuwa baxan taba kara yinsa ba,banida makiyin daya wucesa da kasan yadda nakejin tsanarsa a cikin zuciyata da baka tsaya tada jijiyoyin wuya don na kira wanda dashi da wanda yake a mace dik daya suke a wajena....look iqbal...meyasa zaka raunana ko kasan maanar iqbal?some body that is strong and i know u are strong the ion man....na tabbatar i am blessed with pure husband with pure heart shiyasa nake kiranka iqbal maana mutum me karfin xuciya albarka meyasa zaka karaya don kaji na kira sunan wanda nake gani kamar bakin maciji Wanda ko a mafarki bana fatan kara ganinsa?"yadda take magana yasa bilal ya kara karaya,..
Komawa yayi ya zauna yayi mata nuni da ta zauna da hannu,
Zama tayi babu musu ta kafesa da manyan idanuwanta dake kara susutar dashi "habeebty....ina sonki wallahi kedin rayuwata ce inhar narasaki to babuni babu sauran numfashi cikin wanan duniyar,koda ina a raye zan kasance tamkat ina cikin duniya mai cike da duhu mai tsanani wanda hasken farin wata bazai taba iya haskaka duniyata ba saboda tsananin duhunta....ina sonki don Allah kada kibari mu rabu bazan iya jure rashinki ba"please ya hada hannuwansa,
Lumshe ido tayi sanan ta kada ido "i love you Iqbal"ta sunkuyar da kai cike da kunya,
Dafe kai yayi yana murmushi "kinga nazo miki da albishir amma idona ya rufe"
Da sauri ta dubesa "wani albishir iqbal?"
"Munyi waya da momy yau ina cikin farin ciki daddy yabar fushi dani har muryarsa naji....sanan tambayata yakeyi yaushe zandawo kaduna?"
Zaro ido tayi cike da murna "kai dagaske iqbal amma naji dadi sosai wallahi.... alhamdulillahi"ta daga hannu sama,
Shima ya kasa daurewa sai murmushi yakeyi "tou ai banajin zan iya barinki a nan din"
Jimmm kadan tayi "its ok nima ummah na tana tambayar yaushe zan koma gida nace sai gwaggo ta dawo munyi magana tukunna"
Gyada mata kai yayi "tou know i cant live you here"
"I know"tace ta kashe masa ido "lets me get u something to take"ta mike cike da kwarkwasa as usual tafiyar nan tata mai daukar hankali itace ta kusa sumar da bilal dake zaune....
******
"Waini shin ramlah tun shigowarki gidan nan naga kamar kina cikin damuwa gudu gudu sauri sauri kikeyi inji dai ko lafiya?"umman Ramla ke tambayarta cike da tuhuma,
Kada kai Ramlah tayi "babukomi ummah...sauri nakeyi zanje gidan umman Abdallah dama yace inje can da zai wuce aiki idan ya dawo zai daukeni"
"Wanikam Ramlah tun da akayi aurenki baki taba zuwa gidan nan da jiddah abokiyar zamanki ba"gaban ramlah ya yanke ya fadi zatayi magana kaninta mus'ab ya amshe "ummah ai anty jiddah bata gidan koda muke zuwa gidan yaya ramlah ne ita kadai"
Dakawa mus'ab tsawa ramlah tayi "fad'i baa tambayeka ba sarkin magana aku?wayace maka bata gidan tana nan ko ranar da kuka fara zuwa"
Kanwar ramlah ya budurwa dake kishingide tayiwa ramlah wani kallo ta tab'e baki "kai yaya ramla adai rinka jin tsoron allah ni karyarki ce ke hadani dake ki sanarwa ummah cewar jiddah bata gidan kike kwana kwana?...kinga ummah wallahi jiddah bata gidan ninaji ance ma tana katsina"
"Ke ni kike cewa makaryaciya?kambu aiko sainaci..."
"Ya isheni haka meye haka kukeyi?ke ramlah meye gadkiyar lamari?ban fahimci abinda kannenki suke fada ba magana kamar almara"
Dik gumi ya gama jike ramlah kamar wadda ake watsawa ruwa "am...ummah jiddah tana katsina bata nan taje anyi musu rasuwa....ammm dama Abdallah zaije daukota jibi"ta sunkuyar da kai,
Wani kallo ummah keyiwa ramlah wanda tasha jinin jikinta ta sunkuyar da kai ta janyo jakarta ta rataya "amm ummah bari in wuce"gaba daya ramlah tamkar wata zautacciya haka take abubuwa gashi fuskarta tayi muguwar rama,
"Tou shikenan idan kinsamu lokaci kizo ina son magana dake"ummah tace Mata lokacin ramlah na kokarin fita,
Cikin wani yanayi ta amsa da "tou ummah sai anjima"..sauri sauri ta fice....
*********
Tun shigowar ramlah parlorn babu wanda ya kalli inda take,bata ko gaida ummah ba ta nemi waje ta zauna,
Kallon sapne suhane sukeyi wani india da akeyi a arewa 24da alama suna jin dadin kallom "ke afee dibomun ruwa mana tun shigowata babu wanda ya bani ko ruwan sanyi?"
"Ok anty"afee tace tana kokarin mikewa don zuwa aikem ramlah,sai kada kafa ramlah take har afee ta kai kofar kitchen ummah ta dakatar da ita ta fito daga daki "ina zakije naji kamar anbaki izinin kiyi abu?"
"Anty ce tace in dibo mata ruwa mai sanyi tun shigowarta bataci wani abu ba",
"Dawo nan aiba ita ta haifar mun keba,da zata aikeki kuma ba uban wani bane ya kawo mun ruwan tabari in taje gidanta tasha dawo ku cigaba da kallonku"sumi sumi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki afee ta dawo,
Abbah ne ya fito daga bangarensa dik yanajin abinda sukeyi ya tsaida afee "ke afee jeki dibo Mata ruwa",..murmushi ramlah tayi take taji wani sanyi a zucuyarta,zamowa tayi daga kujera ta sunkuyar da kai ta soma gaida abbah "abban ina wuni"ta gaushesa murya kasa kasa cike da ladabi,
Cikin wani yanayi abbah ya ansa "lafiya"ya wuceta ya karaso "keko habiba ya zakiyi haka?matar yayanta ce ta aiketa kuma ki tsayar da ita ki hanata zuwa keda surukarki?aibe dace ki rinka wadanan abubuwan ba saikace mage da kare? mtswwww kar insakeji"abbah yayi gaba afee ta shigo da tray din lemo da ruwan sanyi ta dire a gaban ramlah,
Wani kallo ramlah tayiwa ummah hade da murnushi,a kufule ummah ta fuzge cup din da ramlah ta dauko ya fashe kasa "gara kofin nan ya fashe da ke ki Sha wanan don bana ubanki bane ba kuma gidan mijinki bane mara kunyar banza kawai juya wadda tunda aka auroki ko batan wata bakiyi ba"
Yar shewa ramlah tayi cike da takaici "ki fadawa mahaliccinki wanan amma ina tunanin rashin haihuwar daga danki ne tunda tun metarsa ta farko bata haihu ba"
Kauda kai ummah tayi kamar bazatace wani abu ba "to fitsararriya gara jiddah tayi barin ciki farkon aurensu wata biyun farko cikin na uku ke kuwa fa? har yau shiru kakeji wai malam yaci shirwa dik abinda aka fada sai kinyi magana kinsa baki saboda babu tarbiyya"
"Dan naki be dade da samun lafiya ba don ita kanta macen ba damunsa tayi ba balle yayi mata cikin kinga daga danki ne rashin kuzari gashi dai cikakken namiji"da rumaisa da meenah suka zabura sukayo kan ramlah suka shaketa "a hir dinki gidanmu kikazo ubanki zamuci dan uwarki"
Ummah daga gefe ta ke fadin "sai ma kun tsaya wata magana?aiku yan halak ne ba shegu ba don haka ku fitarmun da hakki na yanzun yanzun"
Ko gezau ramlah batayi ba saima cike da kwarin gwiwa take magana "wallahi zakuyi kuskuren da bazaku taba yin irinsa ba a rayuwarku bismillah idan kun haifu cikin habiba"aiko rumaisa ta kifawa ramlah mari nan meenah tayi kukan kura ta shake ramlah,
Cikin tashin hankali afee ta dauki wayarta tayi waje cikin kidimewa ta soma kiran wayar Abdallah....
Abdallah kuwa ya taso aiki tuni yana gidan hajiya gwaggo tana bashi shawarwari wayar afee ta shigo wayarsa cikin sauri ya dauka,
Tana haki take maganar "ya Abdallah kayi sauri kazo gidan mu ana rigima da ummah dasu rumaisa da Anty ramlah kayi sauri"
A furgice yace "ganinan zuwa"
"Meyafaru ne Abdallah"gwaggo ke tambayarsa ganin yadda ya tashi a furgice,
"Hajiya gwaggo wai fada akeyi da su rumaisa da ramlah wai harda ummah"
"Kai subhanallahi...wallahi habiba batada girma saina jikinta Allah ya kyauta, kayi sauri kuma ina mai Kara tuna maka da kwarin gwiwar da nake baka"
Beko samu ansa gwaggo ba ya kama hanyar fita ko ganin gabansa bayayi.....
********
Karar takunsa da Ramlah taji ne ta baje a kasa ta soma kururuwa "wayyooo Abdallah kataho gareni ka ceci rayuwata kada ummah da kannenka su kasheni, ummah kamar nidin ba yarki bace kike kallo kannen mijina na wulakanta ni?"
"Niba uwarki bace sheg..."Abdallah ya shigo a fusace beko ganin gabansa ya sabgawa rumaisa mari,
"Ke rumaisa matata kike mari? ohhhhh lallai yau na yarda cewar kune kukayi sanadiyyar aurena da jiddah dik abinda kukeyi Mata tana hakuri bata ramawa gashi yanzun na auro wata ma kun tsanar mun Mata to wallahi baku isaba"
Cikin tsawa ummah ta dakawa Abdallah tsawa "kai Abdallah kake fadin wadanan maganganun?tou yarana yan halak ne don sunyi hakan ne don su sharemun hawaye"
"Ummah kenan kece kikasasu suci zarafin matata ummah kenan ummah dik abinda zanyi don farin cikinki shikenan sai kinsamo wani sanadi da nima zaa muzgunamun?to gaskiya bazan amince da hakan ba bazaa wulakanta mun mata ba dan yanzun haka jibi zan je gidansu jiddah don indawo da ita,tashi mutafi ramlah"ya fuzgo ramlah tabisa,
Ummah ta rangada guda "ayiriri alhamdulillahi tunda ba ni kadai bace naji zafin nadauka wulakantani kakeyi a gaban matarka sai gashi itama ka kuntuka mata tunda zaka dawo da jiddah alhamdulillahi....wallahi ina murna don nayi danasanin abinda mukaiwa yarinyar nan don hakkinta ke bibiyarmu"sai kuma ummah ta fashe da kuka ta fada kujera da rumaisa da meenah suka zagayeta suna lallashinta....
*******
Misalin karfe tara na dare jiddah ce gaban gwaggo "amm jiddah,naasan kinaso ki fadamun zakije gida ko?kin kasa?"
Jiddah ta sunkuyar da kai "tou jibi sai ki shirya kije can kadunan ko amma da sharadi zaki rinka zuwa ganina akai akai"murmushi jiddah tayi "insha allahu gwaggo"
"Allah yayi albarka yanzun ya zaai da Bilal ko shima zai tafin ne?"
Wasa da yatsu takeyi sanan ta rufe ido "gwaggo tare fa zasu tafi don tuni sunyi shirin su"nafeesa tasa Baki,
"Tunda kuns hutu nafeesa ki shirya kuje can ki gaida innar taki zainabu"
Murna da nafeesa da jiddah suka hau yi suka shige dakin kwanansu,
Cikim zumudi jiddah ta kira bila,
Yana zaune gefen gado zee ce gabansa ta tsaresa sai kuka takeyi kiran jiddah ya shigo"habeebty"
"Iqbal....albishirinka"tayi maganar cike da zumudi
"Ina jinki ruhi na?"yayi maganar yana lumshe ido...
"Iqbal gwaggo tace intafi kaduna jibi...don haka kafata kafar mujina"
Yar dariya yayi cike da nishadi "alhamdulillahi...tou sai ayi shiri ko?yanzun dai muyi magana ajima ko ina dan wani abu ne"ta gyada kai kamar yana ganinta ta dire wayar ta lumshe ido....
Bilak tsare zee yayi da ido yadda take kuka "ki fadamun me kikeso kukan na menene?umm?"
"Ina sonka"zaro ido yayi waje Yana kallonta dikda yasan da hakan amma sai ya wayance cikin sigar mamaki yake nuna kansa "ni ?"
"Kai....ya bilal babu macen da zatayi tozali da kai batare da taji ta kamu da matsananciyar soyayyarka ba babu macen da bazatayi kukarin ta mallaki zuciyarka ba kota galin k'ak'a saidai kash.... nidin na makara tunda zuciyarka ka dade da mallakawa wata ita...banida yadda zanyi amma kasani soyayyarka ce ajalina inhar baka taimakeni ka auremu mu biyu ba to tabbas idan na mutu kaine sanadi"ta zabura ta fice daga dakin tana rusa kuka....
********
Yau ta kama ranar tafiyarsu jiddah...tun safe suka shirya da wuri anty fatima ma tana gidan tazo da tsaraba mai yawa da kayayyaki wanda abban hanan ya siya yace a bawa jiddah ta tafi dashi....
Walida kanwar zee ce ta shigo gidan "ina kwana gwaggo"
"Lafiya lau walida"
"Ya bilal yace ku fito"... mikewa jiddah tayi ta rungume gwaggo ta fashe da kuka,ta shiga bubbuga bayan jiddah "gwaggo nagode da kulawarku a gareni....banida kamarku don kune sanadin dana mance da dik wani bakin ciki"murmushin manya gwaggo tayi "Allah yayi miki albarka...sanan zan kira mahaifinki akan maganar ki da bilal"jiddah ta gyada mata kai,
Harta zauna a mota jiddah ta fito ta fada gidan ammiey...a parlor ta tarar da zee tana lekensu ta saman bene hawaye ya wanke mata fuska... Daga bayanta taji an tabota ta juyo da sauri "kukan me kikeyi zee....kina fushi dani ko? menayi miki da ko sallama kika kasa zuwa mun?"wani zafi ne ya tasowa zee a zuciyarta...zaki tafimin da masoyi Kuma kike tambayata?a zahiri kuma share hawaye tayi "nafara missing dinki ne sanan banaso in hada ido dake don zanyi kuka"rungume juna sukayi...dikda jiddah jikinta na bata wani abu haka sukayi sallama da zee ta fito tana sharar hawaye....
*******
Tunda Abdallah yayi parking motarsa a kwanar layinsu jiddah yakejin faduwar gaba,anya zai iya tun kararta kuwa?da wace kalma zai fuskanci jiddah?bashida wanan kalmar saidai tabbas jiddah itace bugun zuciyar Abdallah.....wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri a fuskar Abdallah....amma an sanar masa da cewar bata nan tana katsina gidan gwaggo...kodai yaje katsinan can ne zasu fi samun daidaituwa dan tabbas yasan babu wanda zai kallesa a gidansu jiddah gashi cikin kwanakin nan dik kwanan duniya soyayyarta karuwa takeyi cikin zuciyarsa...yanaso ya gana da ita,yana so ya ganta ya durkusa a gabanta don samun yardarta a matsayin matarsa a aure na biyu....zai sanar mata da yadda ya gyara halayensa ba kamar AUREN FARI da sukayi ba....
Tafe suke a mota cikin garin kaduna...kallon waje takeyi tana lumshe ido gashi garin yayi sanyi sakamakom ruwan sama da aka danyi da yamma wanda yasa hadarin daya hadu ya saki sanyi....kaduna garin gwamna...ta ja ajiyar zuciya sanan ta juyo kamar hadin baki suka hada ido da bilal "iqbal.....gamu a garin mu"
Gyada mata kai yayi "saura gwagwarmayar da zamu tarar dan inajin hakan a jikina"
"Babu wata gwagwarmaya Iqbal...wanan karon jiddah taka ce"
Take mota yayi lokacin daya shigo unguwarsu jiddah.....fiyyyyyy motarsu ta wuce Abdallah da yayi parking a kofar layinsu jiddah.....
Kifa kai yayi yanajin tsananin faduwar gaba sanan haka kawai yake jin kamshin jikin jiddah dago kansa yayi yana hangen wata bakar dalleliyar mota da tayi parking a kofar gidan su jiddah.....rashin kwarin gwiwa yasa yayiwa motarsa key ya karya akalar motar sa ya fice daga unguwar......sauke numfashi yayi inajinki a jikina jiddah...inajin tamkar kindawo gareni....saidai nasan ba lallai insamu soyayyarki ba wanan karon....tuki yakeyi yana jan numfashi kece mace ta farko da na fara so...ya lumshe ido...har yayi nisa yayo kwana yayo hanyar gidan su jiddah again yana shigowa motar bilal na ficewa,yabi bakar motar da kallo,
Gaban mai shagon dake nesa da kofar gidansu kadan yayi parking ya fito...tun daga nesa mai shagon ke kallon Abdallah don ya ganesa,
Sallama yayi masa cikin wani irin yanayi,"waalaikumussalam"mai shagon ya karaso kofar shagon ya mikawa Abdallah hannu
"Kamar mijin hauwau ko?"da sauri Abdallah ya amsa "ehh nine"
"Allah sarki...kace kunsha hanya ko?naga yanzun ma kuka iso garin daga katsina ko?"cikin rashin fahimta Abdallah ke kallonsa,
Gane hakan me shagon yace "ah ah...yanzun fa naga jiddah sun dawo katsina...tadau lokaci bana ganinta dana tambayi yan uwanta sai sukace ta koma katsina ne da mijinta yanzun kuma naganta kuma tare da kai"...gaban Abdallah ya fadi,jiddah ta dawo kenan?tare da wani namiji?waye hakan?take wata zuciyar ta bashi amsa da bilal.....murmushi ya kakalo "eh eh...amm bani coke mai sanyi mana"ya wayance ya ciro dari biyar ya bawa mai shagon ya miko masa,ya mika masa canjin yace ya barshi nan yayi masa godiya ya tafi,no need yayi masa tambayar da yajeyi tunda tun kafin yace wani abu yasamu information din daya kamata sai kawai ya shiga motarsa,kiran ummansa ne yake ta shigowa yaki dagawa don yayi fushi....
Abidah ce ta fito gida bayan tafiyarsa cike da farin ciki ta karasa gun me shago "malam ado abani fanta masu sanyi guda shida"
"Tou abidah...masu tafiya sun dawo lafiya?"
Hararsa tayi "tou dan gulma...ta dawo lafiya"
Yana kokarin sa mata fanta a leda yake fadin ai yanzun Mijin nata "Abdallah yake ko ya bar nan ai naga isowarsu"
Bata fuska abida tayi yana kokarin mika mata "Abdallah kuma?kodai Wanda sukazo tare daga katsina?to yayan mu ne"
"Ah ah Abdallah mijinta ...nafa sanshi abidah ko kin manta tun kafin aurensu nake a unguwar nan?"jikin abidah har rawa yakeyi ta nufi gida a razane da dan mamaki sukai kicibis da yaya ibrahim ta bugesa garin tunani da sambatu "ke abidah meye haka kamar wata zautacciya"
"Yaya ib kaji wai Abdallah yazo kofar gidan nan yanzun ya bari inji Ado"
Murmushi yayi yaya ibrahim"nagansa....ai naji labarin komi da yake faruwa ya kasa zuwa ne don ance kunya marin d'a amma wanan yakin badani zaai ba shida matarsa ne".abida bata gane nufinsa ba tayi cikin gidah tana kwalawa jiddah kira don ta labarta mata,
Aiko jiddah da nafeesa suna cikin cin abinci abidah ta shigo tun daga kofar shigowa parlorn take fadin "wata sabuwa....waye ya fadawa Abdallah cewar kin dawo garin nan Abla?tou yanzun Abdallah yabar nan dan har yaya ibrahim ya ganshi"ai abidah batakai karshe ba jiddah ta kware da shinkafa ta soma tari....
TO.....GA JIDDAH A KADUNA....
0 comments:
Post a Comment