A tare suka fito da sauran yan matan dake cikin motar,zagayawa yayi ya bude musu boot gabaki daya fuskarsa babu walwala,satar kallonsa jiddah takeyi tana marairaice fuska kamar zatayi kuka,har abidah ta juya da leda sukai hada ido da Abdallah cikin sauri ta juyo da dubanta ga su jiddah dake tsaye gefe kallon da abidah tayi wa jiddah ta kada mata ido side din Abdallah yasa jiddah juyawa cikin rashin saa idonta da nashi suka hade waje daya wani irin shock tayi taja da baya cikin sauri ta juyar da kai tana haki,wani kallo bilal yayiwa Abdallah sanan ya cije lebensa gumi na karyo masa jikinsa ya kama rawa "wato biyo mu yayi kenan?meyasa kika kallesa waya baki izinin kallonsa?"cikin tsawa yake mata maganar wanda hakan ya kara razana jiddah ta shiga girgiza kai idanuwanta cike da kwalla "bansan dashiba na kalli wajen ba kallonsa nayi ba iqbal meyasa kake haka ne?"kwalla ta zuraro a idonta tasa hannu ta share,
Takowa Abdallah yakeyi a hankali cike da karfin gwiwa da natsuwa tamkar babu wata damuwa a tattare dashi wani irin murmushi ne wanda daka kallesa kasan na dole ne tunda ya soma takowa sauran yan matan suka furgice ko wanne ya zaro ido, Bilal tura hannuwansa yayi cikin aljihun wandonsa yana kallon Abdallah har ya karaso ya tsaya daff da jiddah,ja da baya jiddah tayi ta koma bayan bilal kadan ta tsaya tana kallon Abdallah,cikin kwayar idonsa take kallo takasa gano wani abu zuciyarta cike da fargaba take,
Murmushin nan nasa yayi yadan bugi kafadar bilal "how far man?ya zaka hana mace kallon mijinta?kai ka isa ka hana jiddah kallona?kayi kadan matukar ina waje jiddah sai taji a jikinta saboda nidin rabin rayuwarta ne gata nan ka tambayeta"
Juyawa Bilal yayi ya kalli jiddah ta kauda kai,cikin kuka ta soma magana "Abdallah ka bace a kofar gidan mu tun kafin in tara maka mutane,ta yaya zaka soma bibiyata daga dawowa na gaban iyayena?meye yayi saura a tsakanin mu?aurene bakayi ka sakeni bazaka kara zama da mazinaciya ba kace to meye namun bita da kulli dukan kabarin kishiya?"cikin daga murya take maganar tana kuka,
"Me yayi saura kike tambaya?akwai abinda yayi saura don wanan karon nazo ne in karbi matata daga barawon matan mutane"...cikin sauri jiddah ta zagayo ta shararawa Abdallah mari tana kuka "kada ka sake kiran bilal barawo donshi ba barawo bane saidai in kaine barawon da ka lallabo kake neman tarwatsa mana farin ciki"
Shafa fuskarsa yayi inda ta maresa yayi kissing hannunsa sanan ya kalli bilal "i expect more than this from her,matukar tana tare da kai,amma congratulations bilal lallai ka iya soyayya tunda soyayyarka tayi tasirin da har mata ta iya marin miji a gaban abokin miji kuma amininsa"
Takaici ne ya lullube bilal "ya isheni haka Abdallah,ashe kaiba dan halak bane,ka farka daga baccin da kayi na watanni shida ne da wuri haka?ashe zaka iya tuna jiddah ka dawo gareta?to bari kaji wallahi idan kazo ne ka tarwatsa mana zama baka isa ba saboda yanzun jiddah bata sonka ni takeso kuma nine zan mallaketa a matsayin mijiiii"bilal ya daga masa murya,
Harde hannuwa Abdallah yayi yana kallonsu kamar film zuciyarsa nayi masa zafi "jiddah ce tace bata sona kai takeso?jiddah bazata taba daina sona ba bilal koda kayi nasarar auranta gata nan ka tambayeta shin idan ta ganni ko taji muryata bata tsintar kanta cikin faduwar gaba"
Bilal ya juya da niyyar tambayar jiddah kafin yayi magana cikin fushi da tsana take nuna Abdallah"bana sonka Abdallah wallahi bana sonka na tsaneka,sunanka ma bana son ji bare Kai kanka,sanan faduwar gaba dole inyita don an kira sunan makiyina ko naga makiyina dole inyi faduwar gaba amma badan soyayyarka ba"
"Karya kikeyi jiddah....ni kikeso wallahi kina sona bacin rai ne yasa kike wanan kumfar bakin da kike amma da zaki kadaice dani wallahi sai kin soni kinsan ni waye a zuciyarki haka kema kinsan ke wacece a zuciyata don Haka babu wanda ya isa yazo ya shiga tsakanin auren da aka daurashi a sararin samaniya"....muryarsa na rawa yake maganar cike da rauni da takaicin furucin da jiddah tayi akansa,
Yadda jikin bilal ke rawa yasa aysha rugawa da gudu tayi cikin gida,....ummah ta fito kitchen da kwandon tsane shinkafa tana kokarin hada abincin rana aysha ta shigo "ummah kiyi sauri kizo kiji wallahi ga Abdallah da bilal da abla nan a kofar gida sai musayar maganganu suke Abdallah ya dawo wai son ablah yakeyi"
Dafe kirji ummah tayi "kan uba? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"tayi jifa da kwandon ta karaso jikin kujera inda ta rataye hijabinta ta zura tayo waje aysha ta biyo bayanta,
A kofar gidan ya ibrahim yayi parking,hayaniya tasa mutane masu wucewa soma tsayawa,ko cire key beyi ba ya fito da sauri yana bin ko wanne da wani irin kallo fuskarsa a daure kamar hadari ya dubi Abdallah yayi murmushi "nasan zaka dawo a karo na biyu....sanan kunzo kuna neman tara mana mutane dan allah ku kama hanya ku wuce gida dukkanku "kuka sosai jiddah takeyi ya ibrahim ya watsa mata harara "tou baure sarkin kuka,kukan me kike mutuwa akayi miki"ya daka mata tsawa yana nuna mata hanyar gida "ku wuce gida dukkanku"
Ummah ta karaso ta ruko ibrahim "ya isa haka sarkin zafin rai ku shiga gida harda kai kaima banason fada da tashin hankali"bilal kuwa yana ganin ummah yayi sauri ya shiga motarsa ya tada ya fice unguwar aguje hade da tada kura,
Ummah ta juya cikin sauri har tana hardewa tayi gida,...yaya ibrahim motarsa yaje rufewa ya shiga gida....tsaye Abdallah yayi kamar an dasashi wani irin bacin rai ke taso masa cikin kirjinsa yana tokare masa makoshinsa,cikin jikinsa kamar ana zuba masa garwashin wuta,
Baya ganin gabansa haka ya tako har inda motar yaya ibrahim yake yazo ya tsaya,ibrahim ya fito daga mota yaga mutum tsaye kamar an dasashi,wani irin takaici ne ya lullube ibrahim kamar ya shake Abdallah "malam gafara zan rufe motata ya akayi ne?"
Kwalla ce ta cicciko a idonsa kawai ya zube a kan gwiwarsa a gaban ibrahim ya rike masa wandon rigar shaddarsa jikinsa na tsananin rawa kamar ana zuba masa ruwan kankara,"banida kalmar da zanyi amfani da ita a gareku wadda zan nemi gafararku da afuwarku a bisa rashin mutunci da rashin tunani da nayi da hauka da dabbanci wanda ya kasancemun kaddara...."ya fashe da kuka,
"Malam ka sakeni bani zakaiwa wanan karatun ba domin nasan komi dadewa zakazo Abdallah lokacin da idonka ya rufe kazo gidan mu kayi rashin mutunci baka tuna da cewar gaba tafi baya yawa ba saida ka aikata....wallahi ni babu ruwana babu abinda zance maka Abdallah...dan allah ka tashi anan don kasa mun zama abun kallo a unguwa"...shiru Abdallah yayi sanan yaja da baya idanuwansa sunyi jajir yaja numfashi "kaimun alfarma guda daya tak"
Rufe mota ya ibrahim yayi sanan ya dubesa ya kauda kai samm haushinsa yakeji dan dole yake magana dashi ya maci saa yau yan fushinsa basa kusa "ina sauraronka me kakeso kace?sauri nakeyi banyi azahar ba"
"Dama inaso ince ne dan allah kada ka hanani zuwa gidanku, zan cigaba da zuwa koda jiddah bazata saurareni ba ganinta ne kadai zai karama numfashina karfi domin nafara yin weak"
"Ka rike wanan karatun naka ka fada mata,babu ruwana da zuwanku nidai tashin hankali ne idan wani ya karamun shi a gidan nan hukuma zata rabamu....masha allahu yanzun tunda kafara sanin darajar dan adam...nabarka lafiya"ko waigensa beyi ba cikin sauri yayi cikin gida....shiru Abdallah yayi dakyar yake jan numfashinsa ya nufi cikin motarsa ya zauna,kasa yi ma motar key yayi don bashida karfi ko ganin gabansa bayayi.....
Tsuru tsuru jiddah sukayi a parlor ummah kuwa ta kasa magana ma sai sauke numfashi takeyi cike da mamaki tace "tabdijan...yanzun shi Abdallah dan...."
Ya ibrahim ne ya shigo ya katse mata maganar,nuna jiddah yakeyi da yatsa "ke abinda kika tara kenan daga dawowarki?tou kisani bazan lamunci wanan iskancin ba dan ke ba karuwa bace da zasuzo suna fada akanki haka kawai,idan fada zasuyi ba a nan ba sanan ban hanaki ba idan sunzo ki fita harshi Abdallah ki fita kije ku karata"ya wuceta yayi cikin toilet din dake jikin parlorn,
Kallom ummah tayi idonta cike da hawaye,"dama kindaina kallona dan babu abinda zance hukuncin da yayanki ya yanke gaskiya ne don haka sai kiyi kokari kiyi aiki dashi,idan mahaifinki ya dawo Zaria ma zan sanar dashi yasan halin da ake ciki"yunkurawa ummah ta mike tayi kitchen "ke abidah zo muje ki kamamun yanka salad"
Yaya ibrahim ya fito ya dauro alwala ya wucesu a parlorn hade da watsawa jiddah wata uwar harara,
Zame dankwalin kanta tayi ta nufi daki tana shasshekar kuka,fadawa kan gado tayi ta fashe da kuka cike da haushin Abdallah,shin me Abdallah ke nufi da hakan da yayi mata?ya dawo rayuwarta ya tarwatsa mata ya rabata da bilal ne?yanzun ne yasan da zamanta kenan tunda ramlah ta fara gasa musu aya a hannu to wallahi bazata sabu ba wankan kuturu da sabulu,
Share hawayenta tayi ta dauko wayarta tana kokarin kiran bilal....
Dakyar Abdallah yayi wa motarsa key ya take yayi Rivas ya bar unguwar cike da zullumi da tsananin bakin ciki idanuwansa sunyi jajir hawaye ya kasa zuba a idonsa,da hannu daya yake driving dayan hannunsa dafe da kirjinsa dake harbawa kamar zuciyarsa zata fasa kirjinsa ta fito....tuki yake kunnuwansa na amsa masa furucun jiddH...bana sonka Abdallah na tsaneka banason koda jin sunanka,bugun zuciyata kuwa inayi ne saboda fargabar jin sunanka da irin tsanar da nayi maka"....cije lebensa yayi sai lokacin idonsa yayi kwalla,
Tuki yakeyi batare da sanin inda zashi ba hakan yasa ya juya akalar motarsa zuwa crystal garden yasamu ya zauna can ko zaiji dadi... Da wanan shawarar yake tuki zucuyarsa cunkushe da tashin hankali
*********
Kuka bilal yakeyi cikin fargaba yana rike da hannun ummansa sai gumi yake jijiyoyin kansa gabaki daya sunfirfito masa a goshi "momy.... Dan Allah karki bari in rasa jiddah idan narasa jiddah tamkat rasa rayuwata ne wallahi matukar kuka sa ido bansameta ba kuma zaku rasa ni"
Jijjigasa momy tayi "kai bilal ka Shiga taitayinka naga alamar soyayya ta rufe maka ido kana nema ka zama sauna ba jarumi da nasanina da ba,meyasa zakazo kana kuka kamar wani ragon maza?kaine zaka jajirce wajen mallakawa zuciyarka abinda takeso bamu iyayenka ba,kasanu bakomi bane mutum yake samu a bagas sai ya jajirce yasawa kansa karfin xuciya,dubi yadda kake gumi kana hawaye saboda rudewa wayace maka dama Abdallah zai barku ku zauna? saboda haka ka dawo hankalinka tun ban bata maka rai ba maza tashi kaje kayi alwala kayi sallah kazo muci abinci mayi maganar anjima"jikin bilal ba karamin sanyi yayi ba tabbas akwai aiki a gabansa,dan tunda yake be taba neman abu ya rasaba a wanan duniyar,cikin sauki yake samun abu batare da yasha wahala ba wanan karon kuwa gagarumin yaki ne a gabansa,matsalarsa daya ce yadda yakejin zafin kishi cikin zuciyarsa dik budurwar da zaiyi kishi ke rabasu wanan karon dole yayi hakuri...dakyar ya tashi kansa na sara masa ya nufi bangarensa,
Alwala yayi ya shimfuda dadduma ya tada sallah,
Kiran wayar jiddah ne ya shigo wayar ta soma ringing har ta tsinke be daukaba wanan shine karo na biyar da ta kira wayar baya dauka,..
Kuka jiddah takeyi kamar zata mutu saboda tashin hankalin bilal yaki daukar wayarta,me hakan ke nufu?ko yana nufin ya hakura da ita ne ya barwa Abdallah ita?tou wallahi bazata iya jure rashinsa ba,kifa kai tayi a pillow ta toshe bakinta Tana rera kuka....
Bayan ya sallame ya mika hannunsa gefen gado inda ya ajiye wayar ya duba, misscall takwas ne duka mutum daya ne jiddah ce,lumshe ido yayi ya bude sanan ya jingina ya kira wayarta....
Cikin kuka ta dauki wayar "haba iqbal ina kiran wayarka kana kin daukar wayata?yanzun dana mutu fa?bakaji yadda numfashina yake kaiwa d komowa ba saboda baka dauki wayata ba...nadauka kayi fushi ka cireni a zuciyarka ne"ta karasa maganar a raunane,
Gyara zama yayi,shiru yayi yana sauraren shasshekar kukanta cikin waya yanajin kunar zucuya cikin ransa,dakyar ya iya saita kansa da harshensa da yayi masa nauyi "kina tunanin cire soyayyarki a zuciyata abu ne mai sauki?....cire soyayyarki ko rabani dake tamkar rasa rayuwata ne habeebty...ina miki soyayyar da ke kanki bakiyi wa kanki saidai bazan iya jure ganinki tare da Abdallah ba matukar Abdallah zai cigaba da ziyartarki to watarana nidashi zasi gawa biyu"
"Ka daina fadin haka iqbal,idan rashin son ganinsa ne zan taka masa burki sanan zan umarci yan unguwa da su jefe motarsa da zarar yazo amma banason in rasaka banason bacin ranka kaga fa...ice cream din da ka siya mana ko sha banyi ba banci cakes dinba ko abincin ummah na kasaci iqbal kanaso kaima ka rasa ni ne?"hawaye ya ciko a idonta cike da rauni takr maganar,
Tausayinta ne ya kamasa ji yakeyi ina ma yana kusa da ita ya rungumeta ya lallasheta,wata irin soyayyarta ce ke shiga jinin jikinsa....cikin sigar lallashi ya soma magana"its ok....habeebty nabar fushi kema ki kwantar da hankalinki kicu abincin ummah kinji umm?"
A shagwabe tace "yaushe zakazo?"kwalla na zubo mata,
Yar dariya yayi "ranki ya dade gobe zanzo kinji?yau momy bazata barni in kara fitowa ba tunda taga yanayin da na shigo gida"yayi maganar hade da dafe kansa dake sara masa ya rufe ido a hankali yana jiyo sautin shasshekar kukanta,
Zuhura kanwarsa ce ta turo kofa cike da natsuwa "assalamu alaikum ya bee"tai mgnr cikin maganarta mai sanyi....yanajiyo muryar yasan zuhura ce ya bude idanuwansa ya kafeta da ido yana makale da waya,
"Yaya bee momy tace ka fito parlor kai muke jira muci abinci"..jinjina mata kai yayi alamar gashi nan zuwa,
Bugun zucuyarsa ne ya tsananta jin kansa yake ina ma yaji jiddah rungume a kirjinsa ya shanye hawayenta ya lallasheta,
Dakyar yasamu kanta sukai sallama da alkawarin yana gama lunch zai kirata.....ya ajiye wayar ya fita parlor,duk sun hallara yana fitowa momy tabisa da kallo gaba daya dakyar yake taka kafarsa ga jijiyoyin sa dik sun firfito a goshinsa alamar ciwon kansa na neman tasar masa,
"Zo kaci abinci idan ka gama kasha magani ka kwanta"..jinjina mata kai yayi ya zauna...
*******
Fitowa ramlah tayi daga daki ta watsa ma ummah harara wadda take faman rawar jiki alamar sanyi na kad'ata tun shigowarsu wajen awa daya kenan ramlah batako fito ta gansu ba balle su gaisa,
"Wai lafiya kukazo mun gida tin sassafe kunyi jugum jugum kamar wasu korarru?"ta murguda baki,
Kallonta kawai rumaisa da meenah sukayi suka kauda kai,afee ce kawai tayi karfin hali dikda itama bataji dadin maganar da ramlah tayi ba "amm ummah batada lafiya sosai tana son ganin ya Abdallah yau kwana da kwanaki beko zo gidan mu ba shine mukazo da wuri dan mu samesa amma bamu samesa ba"muryar afee na rawa tai maganar tana kallon ramlah,
Tabe baki ramlah tayi "au ashe be zuwa gidanku?koda yake yanzun jikinsa rawa yake kamar mazari baya cikim hayyacinsa saboda mararin tsohuwar zuma da yakeyi,na matarsa dama kun tattara kunbarmun gida dan ba yanzun zai dawo ba infada muku"ta watsawa ummah wani kallo,
Dakyar ummah ta mike ta zauna idanuwanta sunyi jajir kamar ta fashe da kuka tabbas tana tsananin son danta Abdallah "ke ko ramlah bakida imani,kinyi nasarar rabani da yarona ko gashi nazo ma ingansa kin hanani ganinsa?kiji tsoron allah wallahi idan babu duniya akwai lahira"
Wata shewa ramlah tayi "hajiya habi ashe kin iya waazi haka?har kinsan in babu duniya akwai lahira?ni kike wa waazi dama kin adana kalamanki kin kaisu inda zasuyi amfani amma ba nan wajena ba kina ji na ko?"girgiza kai ummah tayi ta maida kanta tanajin radadin zafin kalaman ramlah,
Rike kwankwaso tayi "nifa baku isa kusani inyi girki ba don bana girki da rana mijina baya gida"bata hadiye maganar ba taji kuwwar motar Abdallah....da sauri ta kalli agogo karfe uku da minti ashirin da biyar?meya faru?
Da sauri ta ruga da gudu ta lekasa ta window,hangosa tayi ya bude motar yana kokarin rufewa rike da wayarsa yana kokarin yo hanyar balcony....da sauri ta karasa ta zube gaban ummah dai dai lokacin daya bude kofa
"Sannu ummah.... Allah ya sauwake inata kokarin kiran wayarsa bansamu ba....la kinga gashi ma yazo",ta kalli sashen da Abdallah ke tsaye yana kokarin cire takalmansa,
Yadda Abdallah ya koma idanuwansa da yadda ya rike kirjinsa yasa ummah mikewa a furgice dikda al'ajabin Ramlah da takeyi na makircin da tayi,
"Abdallah na? Abdallah kaine? Abdallah kayi fushi da mahaifiya ko? Abdallah waye yace maka yaro yana fushi da iyayensa musamman uwarsa?"kwalla ce ta cicciko a idon ummah tana mika masa hannu alamar ya taho,
Afee da meenah saida sukayi kwallar takaici,afee takasa daina kallom yayan nasu meya samesa yan kwanakin da baizo ba?
Takowa yayi ya karasa shigowa "sannu da zuwa Abdallah dama tun dazun nake kiranka bansamu ba"
"Karya kikeyi munafuka shedaniya iblishiya tunda muka shigo baki ko kalli inda muke ba sai yanzun kika fito kina mana kora da hali sai ga mai gidan yadawo zaki fara munafuncin kissar taki"rumaisa ta karasa maganar tana watsa mata harara,
Abdallah bece komiba don bayason magana ko kadan,kallom Abdallah Ramlah take tanaso taga action din da zai dauka akan abinda rumaisa tayi mata amma sai taga ko kallon rumaisa beyi ba ya karasa gaban mahaifiyarsa ya tsugunna ya dora kansa akaj cinyar ummah....
Kwafa ramlah tayi a daidai setin rumaisa cikin kasa da murya tace "sainayi maganinki wallahi bama ke kadai ba dukkanku"ta wuce ta nufi kitchen, fridge ta bude ta ciro lemuka da cups tasa a tray ta fito ta dire a gaban ummah "gashi ummah tunda kindan samu relief kingansa ko?wallahi mun yafe abinda yafaru kece kawai kika kasa cire damuwa"..wani kallon tsana ummah kewa ramlah yayinda Ramlah ta sakar mata murmushi ta kashe mata ido ta shige daki,
"Abdallah meke faruwa ne meyake damunka haka?"girgiza kai yeyi ya tsiyayi lemo yasha sanan ya dire cup din "ummah ina cikin matsala domin son jiddah zai aikani lahira ..jiddah ta dawo amma ta kasa saurarata yau jiddah hannunta tasa ta mareni"
Dafe kirji ummah tayi cikin tashin hankali da damuwa "ta mareka?meyayi zafi Abdallah mekayi mata hakan?"
"Don nace ina sonta ummah...dom naje rokon ta gafara,amma ina hango soyayyata a kwayar idonta nasan tanasona na kuma fada Mata amma ta kasa gasgata tana sona umman"muryarsa na rawa yake maganar,
Shiru ummah tayi tana danasanin abinda ya faru tabbas dik Halim da Abdallah ya shiga hadda sa hannunta,domin ita keda laifi arbain cikin dari...da bata bada goyom baya ba lokacin da wanan mai kama da aljanun tazo da wanan maganar da baxai saki jiddah ba....sosai ummah ta shiga dimuwa da tashin hankali...kallom yadda Abdallah ya koma tayi saita fashe da kuka.....
Ramlah na makale a jikin labule tana sauraronsu, dawowa tayi da baya ta tsaya a tsakiyar dakin "hmmmm yanzun kuka fara Kuka kuma bazan taba bari jiddah ta dawo gidan nan ba don idan jiddah ta dawo kashina ya bushe sanan banyi nasara akanta ba nasara daya ce in zauna da mijinta zama na harabada kuma ya soni.....tunda haka ne nasan ta inda zan bullo in jagula komi"ta rike goshinta ta xauna kujerar madubi tana tunani murnushi tayi tunawa da yaya ibrahim nada zafi kuma tasan sai ya amince jiddah zata dawo gidan to ta yaya zata bullo yadda zatai nasara?shine batasani ba...kwafa tayi tabbas dole in nemi mafita batare da kowa yasan nice na hada ba...amma yadda na tsani mutuwata haka na tsani jiddah banaso ta dawo gidan nan don nayi baya ya zama banyi nasara ba.....
Jin sun cigaba da magana yasa ta zabura ta dawo jikin labulen ta kasa kunne...
"Ka kwantar da hankalinka jiddah zata dawo hannunka,wanan karon dani zaai yakin Abdallah Kuma zanbaka goyon baya da karfin gwiwa da juriya dari bisa dari...sainayi sanadiyyar dawowar matarka gidan nan insha allahu"tayi maganar tana bubbuga masa bayaz
Kwalla ce ta subucewa afee tausayin Abdallah ne ya kamata dikda ummah furucinta yasa ta kara karyar musu da zuciya dukkansu ji sukai kamar suyi hawaye
Zabura ramlah tayi tai baya jin abinda ummah tace lallai ma wanan matar zan shayar daku mamaki saina nuna muku ibilisancina...
*******
Washe gari...
Misalin karfe takwas na safe Abdallah ya shiga maaikatarsu dik ta inda ya bulla kallonsa akeyi kamar sunga bakuwar halitta wadda basu taba gani ba,
A reception sukai kicibis da cleaner dinsa yadan rusuna "barka da zuwa yallabai,"
"Barka dai"Abdallah ya ansa a takaice yayi hanyar office dinsa cleaner din yabi sa da kallo ya girgiza kai yayi tsaye yana kallon Abdallah har ya shige...
A kan table dinsa yayi karo da farar takadda ya dauka ya soma karanrawa ...gumi ne ya karyowa Abdallah da jiri dake neman kadashi,
Zaune jiddah take a gaban madubi ta gama kwalliya tana makale da waya da alama da bilal take waya "iqbal...jiya fa kaimun alkawari da sassafe zakazo kai zan fara gani gashi har yanzun banganka ba"
"Gani nan zuwa habeebty ki shirya nanda minti talatin zaki ganni"
Ajiyar zuciya ta ja ta sauke "sai ka zo iqbal"tayi farr da ido ta datse wayar,
Dakyar Abdallah yaja jiki ya fito daga office din a inda yabar cleaner din a nan yasamesa "garzali...ashe an dakatar dani daga aiki shine babu Wanda ya kirani ya sanarmun?"..sosa kai garzali yayi cike da kunya da tausayin yanayin oga Abdallah "wallahi oga dukkanmu muna cikin damuwa ne,and ai ba korarka akaiba kwata kwata an dakatar da kai ne da yi maka albashi sai wani lokaci"
Murmushin takaici Abdallah yayi "garzali kenan...ai itama kora ce, shikenan zan tafi dik Wanda yakeson ganina yazo ka sanar masa da ina gida ya sameni"
Wani maaikaci ne yazo wajen Abdallah idonsa jajir yana kallom Abdallah kamar zaiyi kuka "ku kwantar da hankalinku kuyimun fatan alheri da samun inda yafi nan din"suka rungume juna yana bubbuga musu baya, wadanda suka shigo da wuri ne yasamu yin sallama dasu ya fice be tsaya ba motarsa ya shiga yayi mata key ya fice a guje....
Driving yake idonsa yarkaf da hawaye....aikin da sanadiyyarsa ya rabu da matarsa ya jefata cikin halin ko in kula,sanadiyyar aikin nan bashida lokacin kansa ko kadan bare na iyalinsa gashi rana daya an koresa an dakatar dashi daga aikin....wanda sanadin aikin ya rabu da matarsa farin cikin rayuwarsa hasken zuciyarsa.....tuki yake ko ganin gabansa bayayi haka ya iso unguwarsu jiddah yayi parking,
Rike da takaddar ya fito daga motar ya juyawa kofar gidan baya yayi dialing wayarta,
Tana jin vibration na wayarta batabi ta kan wayar ba don tasan bilal ne tunda sunyi maganar gashinan zuwa ta zari gyakenta ta yane kanta ko dankwali babu ga gashinta ya kwanta a goshinta yasha gyara sai kamshi take zubawa ta wuce su nafeesa a parlor suna breakfast...
Samm bata kula da ba motar bilal bace tana hangensa ya juya baya tayi murmushi,yana jiyo karar rufe kofar gidansu yasan itace wato bazata dauka ba saidai ta fito kenan? bugun xuciyarsa ya tsananta dan besan dame ta fito ba wanan karon
Tunda ta tunkaro shi gabanta ya tsananta faduwa kamshin turarensa ya tabbatar mata da ko waye,nan da nan ta nemi farin cikinta ta rasa ta kudiri aniyar karta masa rashin mutunci,
Tana karasawa gabansa ta watsa masa wani kallo daga sama har kasa, shima kallonta yakeyi da jajayen idanuwansa ya d'ago hannunsa ya mika mata wata farar takadda,
Wani kallo take masa daga sama har kasa lokacin da Bilal yayi horn ta juya da dubanta ga motarsa,
Bilal na ganinta tsaye gaban Abdallah yaji gabansa ya fadi sai kawai ya murza sitiyarin motarsa ya juya a guje yabar layin kamar zai tashi sama,
Zaro ido jiddah tayi tana kallon bayan motar bilal har ya bace cikin tashin hankali kamar ta dora hannu a kai ta fashe da ihun......
LITTAFIN ZAINUL ABIDEEN COMPLETE TARE DA IZZA TA AKAN 300 KACAL MAI BUKATAR GUDA DAYA 200 YA TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DIN 2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL 07042277401....HMMM SIYEN NA GARI MAIDA KUDI GIDA WADANAN LITTAFAN BA IRIN SAURAN BANE KU GWADA KU BIYA KU KWASHI DUMBIN DARRUSA.....
*SLIMZY✍🏼*[11/5, 7:46 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*Wanan shafin sadaukarwa ne a gareku HASSAN Da HUSSAINI....gaisuwa ta musamman gareka d'an* *uwa HASSAN ATK😍❤️*
*31*
Tsaye tayi a wajen kamar an dasa ta kafin ta juyo a fusace ta karaso gaban Abdallah cike da tashin hankali wani irin kallon tsana take jifarsa dashi kafin cike da masifa idanuwanta har dishi dishi take gani "Abdallah me kake nema dani wanan karon wace irin masifa ce wanan?ya zakazo ka korar mun masoyi har gida?wai a tunaninka a mafarkinka ni jiddah zan koma gareka ne?ta girgiza kai ta cigaba da magana "idan mafarki kakeyi ka farka domin wanan karon nasha gabanka sanan tsanar da nayi maka tasha gaban inda kake tunani dama mistake ne yasa na aureka ba kai ya dace in aura ba ka fadi cikin rayuwata ka zamemun kaddara don haka nake shawartarka da idan kanason mutuncinka to ka kiyayi zuwa kofar gidan nan idan ba haka ba saikaga abinda zansa ayi maka.....waishin dole ne?"ta rike kugu tana tambayarsa ido cikin ido,
Shiko Abdallah tunda ta soma magana yayi nisa cikin wani tunani daban kallon ta yakeyi daga sama har kasa wutar soyayyarta ke ruruwa a cikin zuciyarsa....ji yake kamar ya fuzgota yasa ta a mota ya tafi da ita,
"Wai shin bada kai nake magana ba?kabar mana kofar gida idan kai ba maye bane mara zuciya"
Sai a lokacin ya gyara tsayuwa cikin wata irin murya mai kama da kasala yace "ni mayenki ne jiddah ko kin manta?....akanki tabbas ni mara zuciya ne dan tuni kare ya dade da cinye zuciyata gangan jikina ne kawai yake tare dani indai akan soyayyarki ne jiddah...wanan kumfar bakin da kikeyi da wanan barazana da kikeyi nasan kasan zuciyarki kina sona tsanata a kwayar idonki take kinaji haushi ne saboda abinda nayi miki amma inada tabbacin nine a cikin jinin jikinki"
Juya masa baya tayi zucuyarta na tsananin tafarfasa ji take kamar ta dora hannu akai ta fashe da kuka kamar ta shake Abdallah takeji ta huta, girgiza kai kawai tayi ta juyo"banida lokacin ka Abdallah don dik me hankali bazai tsaya sa insa da wanda zucuyarsa ta dade da cinyewa daga bakin kare ba....a karshe dai ina kara sanar maka bazan sake zama da wanda besan darajata ba sai aikinsa,wanda baisan hakkin mace ba aikinsa yafini muhimmanci"da sauri ya katseta "da kim bude takaddar nan dana miko miki da kinga sakamakon hakkinki jiddah,tabbas na zalunceki na wulakanta ki ada ina ganin babu abinda yafi aikina muhimmanci amma gashi yau na rasa aikin shi kansa zaman gida zan koma yi narasa aiki na rasa matata da nakeso matar dans fifita aikin akanta ga abinda ya kasancemun....jiddah ki bani dama a karo na biyu zan shayar dake soyayya da kulawa zan maidake yar gatan gidan miji wallahi tallahi sai kin dauki kanki fiye da ko wace macen aure da take samun tarairaya.....
"Dalla malam ya isa kanajinko wai ni meye ma ya zaunar dani ka ke wanan tatsuniyar ina tsaye?... mtswwww"taja tsaki ta kara gaba,
Bin bayanta yayi "jiddah....jiddah karki tafi ki barni tafiyarki sai tafimun mutuwata zafi"...wata harara da ta watsa masa mai cike da tsana yasa ya sunkuyar da kai ya tsuke bakinsa,karar rufe kofar gidansu yasa ya dago jajayen idanuwansa yana kallon kofar gidan ko kifta ido baya yi gani yakeyi tamkar zata kara fitowa,
A sanyaye ya juyo jiri na dibarsa yana rike da takardar a wahale yake taku ya karasa jikin motarsa ya dora kai a jikin motar yana girgiza kai,wani irin radadi ne ke taso masa a kirjinsa cire rigarsa yayi ta sama yabar farar shirt dinsa ya shige mota ya rufe ya kwantar da seat yayi kwanciyarsa hade da rike kansa...yau bayajin akwai abinda zaisa ya bar kofar gidan nan...ya lumshe idonsa hade da dafe kirjinsa da hannunsa daya,
A parlor ta wuce ummah ko ganin gabanta batayi har ta kai bakin kofa ummah ta kira sunanta "mai jiddah yadai naganki cikin wanan yanayin meye ya faru?..."juyo idonta tayi tana kallonsu duka suna parlorn yaya ibrahim yayi shirin fita aiki kwalla ta cicciko idonta "babukomi ummah"tasa kai ta shige daki ummah ta kalli sauran dake zaune kowa jikinsa babu kwari Babu wanda yayi magana ya ibrahim ne yace "kila yau ma sunzo sunyi tashin hankalin ne,da bazata iya taka musu burki ba ni wallahi ina gab da korarsu duka"
"Ai abun mamakin ibrahim. Wai harda Abdallah"ummah tace cike da al'ajabi,ta rike baki cike da mamaki,
"Hmmm ai beda kunya tou ita tasani idan ta rufawa kanta asiri ta zabi daya daga cikin su tayi aure ta huta,abbah na dawowa yau zan sanar masa da abinda ke faruwa bazasu zubar mana da mutunciba a unguwa"ya mike ya dau wayarsa "saina dawo ni natafi aiki"
Ajiyar zuciya ummah ta sauke "Allah ya bada saa"
Jiddah kuwa ganin misscals din bilal a wayarta ba karamin tada mata da hankali yayi ba ashe da ya tafi cigaba yayi da kiranta? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...ta shiga uku gumi ne ya karyo mata ta hadiyi wani mugun miyau tayi dialing wayarsa ta kara wayar a kunnenta tana cigaba da safa da marwa a dakin,...
Yana kishingide call dinta ya shigo idanuwansa sunyi jajir takaici yasa ya daga wayar yaga itace ya kife wayar,kansa na cigaba da sara masa...kiran wayarta ne ya sake shigowa ya dauki wayar a hannunsa yana kallon kiran nata cikin wayarsa saida wayar ta kusa katsewa sanan ya danna recieve ya kara a kunnensa,..
Cikin rawar murya jiddah ke magana "sorry Iqbal wallahi nabar wayar a daki kuma wayar tana ..."
"Ya isheni...kin bar wayar a daki ko kina wajen tsohon mijinki kuna sasantawa ko?...hmmm jiddah idan kina son mijinki ki fada mun tun wuri insan inda dare yayimun infara shirin barin duniya dan soyayyarki zatayi silar da zan rasa raina"
Kwalla ce ta zubowa jiddah a ido"Iqbal....be dace ka fadamun wanan maganar ba ka tsaya ka saurareni kaji mezance maka kaji iqbal kasan me"a sanyaye take maganar ya kara katseta "ba sai kinyimun bayanin kina wajensa kina tare dashi ba ai banbar cikin unguwarku ba nasoma kiran wayarki kikaki recieving call dina tun daga nan nasan komenene kinsan dashi"
Girgiza kai jiddah takeyi cikin kuka "ka saurareni iqbal"dibbb bilal ya kashe wayar gabaki daya ya jefar da wayar ya rufe idanuwansa,..
Kamar an dasata tayi jin ya kashe wayar ta zaro wayar daga kunnuwanta jikinta na rawa tayi dialing wayarsa saidai me a kashe....no no ta shiga karkada kai nashiga uku Bilal abinda kake tunani ba haka bane bazan taba cin amanarka ba,ina sonka kai kadai na mallakawa ruhina da zuciyata da gangan jikina...komawa tayi ta fada kan gado ta fashe da kuka wutar tsanar jiddah ce ta kara ruruwa cikin zuciyarta don shine silar komi meye yake kawo shi gidansu?meye ma yasa ta tsaya sauraronsa harta tsaya kulashi? mtswwww ya kamata tayi masa gagarumin rashin mutuncin da bazai sake gigin dawowa kofar gidansu ba ya dace ta shayar dashi ruwan rashin mutuncin da ko sunanta aka kira sai yaji tsanar sunan,
Kuka sosai jiddah takeyi tana rike da wayarta tana cigaba da kiran wayar bilal bata shiga... Gajiya tayi ta cillar da wayar gefen katifa ta kife kanta tana sauke numfashi sama sama,
Tsaye nafeesa tayi akanta tana kallon yanayin nata...."Abla"ta kira sunanta,tanajin nafeesa amma ta kasa amsa mata saboda halin da take ciki harshenta nauyi yakeyi mata,
"Abla...nasan kina jina ummah tace ki fito kiyi breakfast kada ya huce da zafinsa yanzun".
Dagawa nafeesa hannu tayi alamar tayi shiru ,daga kwancen da take ko motsawa batayi ba sai magana da dakyar tasamu ta sarrafa harshenta"kije kice nakoshi bazan iyacin komi ba nafeesa,and ina rokonki bana son magana kada kicemun komi ki ficemun daga gani"...jin Haka yasa nafeesa bata kara cewa komi ba ta fice,
Tana fitowa ummah ta tarbeta "tace bazataci ba ko?taki fitowa?"nafisa ta ansa da kai alamar ehh cikin rashin jin dadin yadda jiddah tayi mata sai kawai ta zauna a kujera tayi joining kallon da su aysha keyi....
******
Karfe uku da wani abu rana tasamu inda motar Abdallah take a kofar gidan su jiddah yana kwance cikin motarsa yaga tsayuwar motar yaya ibrahim,cikin sauri ya fito ya tunkari motar daidai yaya ibrahim ya fito yana kokarin rufe mota yana ganin Abdallah ya daure fuska kayan jikinsa a yamutse alamar kwanciya yayi a motar,kallon sama da kasa yakewa Abdallah cikin zuciyarsa yace ikon allah.... Yana kokarin sa gwiwarsa a kasa ya ibrahim ya tsaidashi "kai malam lafiya haka kamar Wanda ya samu tabun hankali? Abdallah ka ganka kuwa kamar wani susutaccen mara hankali?ka bani kunya wallahi kada ka bari wanda ya sanka ya ganka a haka zai dauka tabin hankali kasamu"
Kuka Abdallah ya fashewa yaya ibrahim dashi harda shassheka "ka taimakeni wallahi zan mutu idan ban sameta ba ta kirani marw zuciya tace kada in sake zuwa gidansu wallahi tun safe nake kofar gidan nan inaso ta fito inganta sannan intafi gida amma ko inuwarta ban ganiba balle ita"
Galala yaya Ibrahim yayi yana kallon Abdallah kamar karamin yaro tabbas akwai nadama a kwayar idon Abdallah amma sanin halin mutum sai allah baka isa ka gasgata hakan ba sanan shi kansa bazai mance da rashin mutuncin da Abdallah yazo har gida yayi musu ba,... Abdallah kuwa ganin ibrahim yayi kuri yana kallonsa yasa ya soma kokarin sa gwiwoyinsa a kasa "no no tashi da allah banason wanan rusunawar da kakemun da allah...ni banida abinda zanyi maka amma ina baka shawarar kaje gida abunka kaji gobe sai ka dawo idan ta saurareka to"....abida ce ta ruko lemo daga shago data siyo kallom Abdallah take kamar sabon mahaukaci har tana cin tuntube wajen kallonsa kafin ta shige gida a kuje,
"Nace kaje gida gobe ka dawo ko?"
Kamar karamin yaro Abdallah ya shiga gyada kai "intafi?...intafi ko yaya Ibrahim?idan nadawo gobe zata saurareni?dan allah kace ta taimakeni...zan tafi zandawo gobe yaya ibrahim"sakin baki yaya ibrahim kawai yayi dik maganar da Abdallah yakeyi kamar zautacce daga masa kai kawai yakeyi har ya gama ya juya tafe yake kamar dan giya yana tangadi saboda tsananin yunwar da yakeji,
Girgiza kai ibrahim yayi yana tambayar kansa,anya Abdallah baya shan wani abu kuwa?sanan yaja tsaki ya shige gida....
********
Zee ce wadda bilal yasan da zuwanta itada walida ta turo kofar ta shigo yanajiyo motsinta da muryarta lokacin da take kokarin shigowa ya juya baya da sauri ya rufe idanuwansa wanda ta rigada ta ganshi,
Rufe kofar tayi ta karasa shigowa dakin tana bin dakin da kallo ko ina tsaf tsaf kamar dakin mace,
Kallonsa takeyi kafin tayi murmushi "yaya bilal...nasan kana jina kaji shigowata yasa ka juya baya, yanzun tsanar da kaimun yaya bilal ta kai haka?...tun isowarmu kaji zuwanmu amma ka sharemu ko fitowa ba kayi ba yanzun nakasa hakuri nazo muyi hira mu gaisa ka juya bayanka alamar baka son ganina ko?"
Haushi ne da takaici ya kara lullubesa yadan ja tsaki ya d'ago idonsa kamar me bacci "dan allah banason yawan surutu banajin dadi kaina na ciwo ki fita idan naji sauki zan sameki a parlor please"ya juya bayansa be jira cewarta ba,
Saroro tayi a tsaye idonta cike da hawaye "owk tou zan fita amma kayimun alkawari zaka kaini wajen masoyiyarka da kakeso inganta inyi mata zuwan bazata domin inasonta dikda tayimun karfa karfa ta hanani rawar gaban hantsi"
"Dalla ki ficemun a daki nafada miki banida lafiya kin cikani da surutu ko?ki fita mana sai kace dole ai nasan da zuwanku ummah ta sanarmun tun daren jiya kuma nasan ba kinzo dan kiyi hutu bane kinzo ne saboda ni amma kada ki kuskura kiyi gigin da daddyna zaisan kina sona dan wallahi bana miki son soyayya son Yan uwan taka nake miki nafada miki"yaja tsaki ya dora pillow akansa,
Hawaye ne ya wankewa zee fuska,ta juya jiki ba kwari gudun kada momy ta fahimci wani abu yasa tasa hannu ta share hawaye ta gyara fuskarta sanan ta bude kofa ta fice,
Jan tsaki yayi ya gyara kwanciyarsa ya janyo wayarsa ya kunna....yana gama kunnawa massages din jiddah ke shigowa daidai har goma...shiga wayar yayi don ya karanta dikda kishinta dake azalzalarsa,amma ji yakeyi bazai iya hakuri ba ya shiga karanta texs dinta....tausayinta ne ya kamasa jikinsa yayi sanyi ya mike ya zauna ya jingina da jikin gado yayi mata reply... *I love you soo much helmiy ina nan zuwa gareki banajin dadi* *ne kaina na tsananin ciwo...* Ya tura mata ya maida kai ya kwanta,
Lamo tayi akan gado tayi kurriiii tana kallom gefe daya akan gado tex ya shigo wayarta,dakyar ta motsa ta lalubi wayar a kasan pillow ta ciro tana ganin tex dinsa ta zabura ta zauna tana karantawa,...dikda samun relief da tayi amma hakan be hanata kwalla ba,ta koma ta kwanta,
Kiran wayar zainab ne ya katseta taga itace saida taji kunya ta lullubeta dan tun dawowarsu basuyi magana ba,
"Ranki ya dade kaina bisa wuya na tuba"jiddah tace a sanyaye,
Murmushi zainab tayi mai sauti "nakasa hakuri na biyoki kaduna yanzun haka ina garinku shine nakiraki kafin inzo inganki"tana kishingide a kujera a parlor take maganar,.
Shiko bilal kasa komawa kwanciyar yayi ya mike ya fito parkorn yadda yake taku kadai zakasan babu karsashi a tare dashi tana makale da waya tana magana da jiddah ya fito amma gaba daya hankalinta ya koma garesa wanda hakan yasa momy ta kada kai dan dik wanda yaga kallon da zainab kewa bilal yasan akwai magana,
Shiko walida ya soma wa wasa "walilim ammiey...kece a garin namu nayi murnar ganinku"ya nemi gefenta ya zauna,
Turo baki walida tayi "ai munyi fushi tun isowarmu kanaji baka ko fito ka tarbemu ba"...dariyar karfin hali yayi idanuwansa jajir ya hade hannuwansa "am sorry lilly bana dan jin dadi ne yau ina daki a kwance"
Kasa hakuri tayi zainab koda ta dire wayar batai niyyar kulasa ba amma ta cije "Yaya Bilal ka fito?ya jikin kaji sauki"
Saida yaji kunya yadda tayi masa magana batare da fushin abinda yayi mata dazun ba yasa yayi murmushi"baby zee shagwabar ammy yadai umm meye labari?"ya tsareta da ido,
Kwarjini yayi mata yasa ta sunkuyar da kai ta girgiza kai....momy ce ta katsesu "meke damunka haka idanuwanka suka kumbura sukai jajir?"
"Momy wallahi kaina ne kemun ciwo sosai"yayi maganar cikin sigar shagwaba da duka saida suka kwashe da dariya,
"Kaidai kayi girman banza yanzun Kato dakai kake shagwaba mtsww zuhura zubo masa abincu ki kawo bari in kawo masa magani"momy ta tashi ta nufi daki zuhra ta shiga kitchen idonsa nakan tv yana juyowa suka hada ido da zee tana satar kallonsa tayi saurin sunkuyar da kai,
Girhiza kansa yayi ya cije lebe....
******
Kiraye kirayen sallahr magriba ake lokacin da ramlah ta tsaya akan Abdallah ta rike kwankwaso da hannu daya tana kallonsa kamar wani mahaukaci,... tabe baki tayi,
"Nifa ban gane maka ba Abdallah wanan susucewar da kayi kamar wani sauna ko sabon kamun hauka?...tun shigowarka kake kwance a nan baka ko bi ta kaina ba balle kaci abincina"
Dakyar ya tashi ya zauna yana kare mata kallo "ki tashi daga kaina kin tsayamun kerere kamar tabarya kawai mtswww"
"Ba dole in tsaya maka ba naga tun shigowarka gidan nan baka kulani ba ka kyaleni,sanan naganka cikin wani yanayi wanda bansaba ganin hakan ba dikda a kwanakin nan kusan kullum haka kake dawowa dole in tambayeka Abdallah tunda ina sonka ina son ganin mijina cikin walwala"a karaye ta karasa maganar tana langabar da kai,
Wani haushi ne ya lullubesa kamar ya kwasa mata mari,wata uwar harara ya wurga mata sanan yace "ke nace kidamu dani ne?ai bance kidamu dani ba ko....mtswww da kinsan yadda nakejin haushinki da baki tsayamun akai kerere kamar wata bishiya ba.. dalla malama tashi kibani wuri kafin in kwada miki mari",...ba karamin tsorata ramlah tayi ba cikin sauri tabar wajen ta nufi dakinta tana kunkuni,
Kwafa yayi hade da tsaki ya mike ya shige dakinsa,jimmm kadan ya tube kaya ya zuro jallabiyarsa ya fito ya dau makulli motarsa ya nufi masallaci dagacan yana jin sai yaje wajen jiddah tukunna zai dawo gida koda bazai samu ganinta ba kuwa...
*******
Tun safe suke shirye shiryen dawowar abbansu jiddah daga zaria,jidda batada karfi tun jiya dikda tayi waya da iqbal amma baccin kirki bata samu tayi ba gashi har laasar yanzun ake gab da kira,
Kamar wadda aka tsungula ta nufi dakinsu da sauri tana shiga taji wayarta na ringing,kuma kiran na bilal ne murmushi tayi haba dole taji a jikinta ashe rabin rayuwarta ke kiranta a waya,batai wata wata ba ta dauka..."hello iqbal"
"Guest what?"yace mata....lumshe ido tayi ta bude "what?"ta tambayesa cikin wata irin murya,
"Ina kofar gida...and yadda kike nakeso ki fito don inason inganki a haka kada kiyi minti biyar ki fito idanuwana suna mararin ganinki,kunnuwana suna kewar jin zazzakar muryarki mai dadin sauraro ina fatan kinyimun tanadin dik wata tarairaya"
Daga masa kai tayi kamar yana ganinta ta kashe wayar kamar tayi tsalle dan murna dan tayi missing dinsa ta tanadar masa dukkanin tarairaya don zucuyarsa ta kasance cikin farin ciki....kallon kanta tayi riga polo shirt da zani ne a jikinta cikin sauri ta sauya tasa bakar jallabiya ta yane kanta da yellow din gyale ta fito bata ko yiwa kowa magana ba ta fice,
Tun fitowarta yake kallom ta ya kasa dauke kansa daga gareta har ta iso ta bude gaban motar ta shigo ta rufe.....sanyin AC ya gauraya da kamshin turaren sa as usual wanda ya kama motar ga wata waka da yake sauraro...ta umar m sharrif zuciya sirrin maishi take....lumshe ido tayi ta kafesa da ido daidai baitin haka na fada ke kamar raina kike in har babu ke bazanai numfashi ba....ya kifta mata ido hade da dage mata gira "ehh maganar da umar yayi gaskiyace tabbas inhar babu ke bazanai numfashi ba....kuma ai nidake kamar Laila majnun muke koda mutuwa tazo bazata dau daya tabar daya ba ko?baxan iya mutuwa in barki a cikin wanan duniyar ba habebty"
Murmushi tayi ta gyada masa kai "to dama meye anfanina a cikin duniyar da babu kai iqbal...da kasan yadda nakejin kaunarka a cikin jijiyoyin jikina da jinina bazakai tunanin cewar ka mutu ka barni ba dan zansha wahala sosai ina tsananin sonka"tai maganar tana kallon kwayar idonsa ko motsa idonta batayi,
Shima ita yake kallo ganin taki ko kifta idanuwa yasa ya hura mata ido take kunya ta lullubeta tasa hannu ta rufe idonta,
Call ne ya shigo wayarsa, tana jikin motar yasa hannu ya duba zainab ce ya kalleta "kinga fitinanjiyar nan zee ce kuma cewa nayi fa zan kawota amma na zaro jikin nataho wajen helmiy"...
"Iqbal...menene meaning dun helmiy kada kace nayi kauyanci kalmar kamar larabci,"
Gyada mata kai yayi"ehh larabci ne it means my dream"...ya kashe mata ido yana kokarin daukar wayar yasa a speaker...
"Hello...yaya bee shine ka zare jiki ka tafi ko?bakaso inje kuyi soyayya a gabana?gani kakeyi zanji haushi inyi kishi ko?"tayi maganar cikim sigar shagwaba kamar zatai kuka,
. furucin zainab yasa gaban jiddah faduwa....shima kallonta yakeyi yanaso ya karanci yanayin nata amma tana gani yana kallonta sai ta dake ta saki murmushi tana kallonsa,kallonta yakeyi bece komiba saida zee tace "hello hello...yaya bee"..gyaran murya jiddah tayi "sorry kawalli zaizo ya taho dake yanzun ya kasa sukuni ne sai yazo ya ganni tukunna nima i canr wait to see you"...shiru zee tayi kamar ta kashe wayar batare da tace komiba sai ta dire wayar sunata hello hello sanan can aka katse call din gaba daya...
Kallom bilal tayi zucuyarta cike da tambayoyi amma bazatai masa ba da kanta zatayi finding komi wato tagansu suna soyayya taji haushi?...kenan sonsa takeyi?...kishine yadan tasowa jiddah take ta danne kiran ta da yayi "helmiy...."cikin wata siga,
Ajiyar zucuya taja "naam iqbal....gani a tare dakai me kake bukata Wanda yafi haka?..."
"Hmmm samunki a matsayin matar aurena shine cikar burina...yau zan gabatarwa da daddyna soyayyarki yazo da wuri ya tambayamun aurenki"
Dadine ya rufeta ta cika da murmushi tana kokarin bashi amsa ta hango motar abbanta ya dawo...dadi ne ya cikata tun isowarta bataga abbah ba ta tsare inda ya doso da motarsa da ido kallom wajen yayi sanan ya kalleta "wa kike kallo haka ina tare da ke?"
"Abbah ne gashi can ya dawo tun safe muke shirin dawowarsa... kaga ya dawo a daidai"
*******
Dakyar ummahn Abdallah ta roki abbah ya yafe mata laifin da tayi masa saboda halin nadama da take ciki duka suna cikin parlorn suna yar hira ummah tace "abbah dama ina bukatar izininka inaso idan bazakaje gidan su jiddah ba toni kaimun izini inje dikda bansan yadda zasu karbeni ba"
Kada kai abbah yayi "Abdallah yayi kuskuren da ya dace ya gane kurensa dan haka baxanje rokom matarsa ta dawo ba dikda inada alfarmar da mahaifin yarinyar zai amincemun amma gaskiya bazan iya zuwa ba idan ke zaki murje idonki kije to amma sai kinyi hakuri da abinda zaa fada miki dan tabbas zakisha maganganu don kema kin tafka kuskure"
. shiru ummah tayi cike da nadama da takaici "zan dauki afee muje dan yanzun haka a shirye nake jiran izininka nakeyi insha allahu zanyi kokari wajen samowa Abdallah farin ciki"
Murmushin jin dadi abbah yayi "sanan kada ya saki matarsa ta gida dan zai dawo da jiddah idan har ta kasance rabonsa a karo na biyu"
"Insha allahu"
"Afee tashi ki dauko gyalenki muje ko?"...dadi ne ya cika afee tayi kewar anty jiddan ta sosai da sauri ta shiga daki ta dauko gyalenta.
Suna kokarin fita da mota motar Abdallah ta kunno kai dan haka ya fito ya zo wajen motarsu ya leka ummah da afee ce ciki "umah ina zakuje ne?"yayi tambayar yana kallonsu,
"Gidan anty jidd ...."da sauri ummah ta buge mata baki "tou fadi baa tambayeki ba yar unguwa zamu shiga ka jiramu"
"To allah ya tsare"ya juya yaso ummah tabar afee yaji kamar tace jiddah...beso ba shi yazo ya gaishesu ne yaje wajen jiddarsa dan dik yau be ganta ba haka,yabi motarsu da kallo suka fice ya ja motarsa yayi ciki da ita zuciyarsa cunkushe da tunanin ina ummah zasuje data hana afee fada masa.....
MASOYA LITTAFAINA NA ZAINUL ABIDEEN COMPLETE TARE DA IZZA TA AKAN FARASHI ME SAUKI 300 KACAL BIYA KISHA ROMON DA YAFI NA AUREN FARI ...2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL 07042277401 DON SIYAN DAYA 200 KACAL....
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:47 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
KAUNAR MU A JINI TAKE YAR UWATA JININ JIKINA INA KAUNARKI FISABILILLAHI *ANTYNA SARATU* ❤️😭KARAMCIN KI A GARENI DABAN NE ALLAH YA RAYA MIKI ZURIAH YA NUNAMIN AUREN *AMIRA* YA BAWA *ABDUL* LAFIYA......WANAN SHAFIN SADAUKARWA NE A GAREKI MEENAH NAYI MIKI SON SO KAUNA FISABILILLAHI...❤️
*32*
A parlor ta tarar da mutanen gidan dik sun hallara kewaye da Abba sai murnar ganinsa akeyi cike da d'oki ta shigo "oyoyo abbah"tace kamar ta taka rawa don murna,
Fad'ad'a faraarsa abbah yayi cike da farin ciki yake kallon yadda jiddah ta sauya tadanyi jiki babu alamar wata damuwa a tattare da ita "oyoyo uwata.. mutanen katsina ta dikko dakin kara kunya gareku badai tsoro ba,koda yake ana dan taba tsoron ma kadan dan ke farar kura ce"cike da zolaya yayi maganar suka kwashe da dariya har ummah "alhaji wanan dai dani kake ba jiddah ba dan garin mu ne"ummah tai maganar tana dariya,
Tsugunnawa jiddah tayi a gaban mahaifinta ta Soma gaisheshi "barka da zuwa abbah,andawo lafiya ya hanya?"
"Lafiya lau jiddahn abbah nasameku lafiya?"
"Lafiya lau abbah ya hanya ya gwaggon kan fage?(yayar abbah)
"Lafiya lau daga ina kike haka kinata faraa sai kyalli kike ko har an mance da Abdallah ansamu wani?waye wanan mai saar?"
Sunkuyar da kai jiddah tayi Tana wasa da gyalen hannunta,..ummah ta karbe zancen "ehh bilal ne yake zuwa wajenta acen ma suka hadu a katsinan shima yaje wajen yar uwar babansa,.. yaron nan abokin Abdallah"
Nan da nan abbah ya sauya yanayinsa cikin wani irin yanayi yaja numfashi "Bilal?yaron da ta dalilin sa aurenta ya mutu kikeso kicemun ya fito neman aurenta?kodan haka ya kashe mata auren?"....tsitttt parlorn yayi,
Gaban jiddah ne ya yanke ya fadi ta dago kai ta kure abbah da ido,yanayinsa ya sauya amma hakan ba yana nufin fushi yake ba to me kalaman abbah suke nufi? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...ta dafe kirjinta dake tsananin dokawa....maganar ummah ce ta dawo da ita daga tunanin da takeyi "Alhaji ba yanzun zakai wanan maganar ba,bata ma kamace ka ba ka roki zabin Allah tunda kaga yarka Tana sonshi"
Yanayin na abbah ya kara sauyawa still jiddah shi take kallo,shiru yayi yana tunani sanan yaja numfashi"allah ya zabi abinda yafi zama alheri....kawomi. Ruwan sanyi sosai wanan ba sanyi"
Ummah ta mike da niyyat shiga kitchen sukaji sallama,...dakatawa tayi ta amsa da "Ameen waalaikumussalam...a shigo mana"
Ummah ce ta shigo taci lafaya gyale,ta fadada faraarta hakoran makkanta biyu sama da kasa suka bayyana dikda yar ramar da tayi "assalamu alaikum...bakin tsakiyar rana ko ince laasar"afee na biye da ita suka shigo,
Gaba daya parlorn kallon kallo sukeyi suna kallon juna cike da mamaki da al'ajabi....aysha kasa daurewa tayi saida tasa hannu ta murza idonta taga ummahn Abdallah ce?....tsaye sukayi babu Wanda ya iya bude baki ya basu mazauni,
Abbah ne yayi gyaran murya "barka da zuwa hajiya habiba,ya kuka tsaya daganan shigo mana"
Kallon yaran abbah yayi "kai ku tashi ku basu wuri mana kunyi wuri wuri da ido,... Abbah ya dubi umman jiddah "hajiya zainab ya kika tsaya bakiga baki bane?"
Sai lokacin ummah ta iya saita natsuwarta ta fadada murmushin ta tace "sannunku da zuwa hajiya kune da rana tsaka?"
Ita kanta ummah yadda mutanen gidan sukayi tsananin mamakin ganinsu yasa jikinta yayi sanyi babban abinda yasa kunya ta lullubeta kamar ta haka rami ta shiga shine yadda mahaifiyar jiddah da mahaifin jiddah suka amsheta hannu biyu kamar babu abinda ya faru,lallai mutanen nan sun gaji arziki sunsan mutunci,tun shogowarta take faduwar gaban tarbar da zasu samu sai gashi sun samu tarba daga mai gidan kansa,
Ummah ce ta shigo da tray na ruwan sanyi da cup ta dire "bismillah hajiya ga ruwa kusha kun kwaso rana"...
Sunkuyar da kai ummah tayi "unhmmm...mungode"....afee ta mike ta bi sahunsu jiddah da suka shige daki dan ta kagu taga antynta....
A daki kuwa tagumi jiddah ta rafka a gefen gado zuciyarta cunkushe da tunani da fargaba hadi da tsananin tsoro na abinda abbanta yace,shin meye furucinsa ke nufi?....kardai abbah bazai goyi bayan aurenta da bilal ba data shiga uku da wallahi mutuwa zatayi....insha allahu abbanta yana sonta zaiso abinda takeso,tasan halin abbanta akwashi da adalci,shin wanan matar meya kawota gidansu?metazo yi?tabdijan idan ma tazo da niyyar bikonta ne to ta kwashi yan matan kafafuwanta ta tafi dan ko ganinta bata sonyi....sallamar afee ce ta farkar da ita daga duniyar tunanin da jiddah ta tsunduma..."assalamu alaikum" tace ta tsaya daga baki bakin kofar jiki a sanyaye irin kallon da su abidah sukai mata yasa ta sunkuyar da kai,.... jiddah kallon yarinyar take babu abinda ya fado mata sai lokacin da tazo Tana share Mata hawaye hakika batada masoyiyar da ta kai afnan a duniyar gidan Abdallah...dan haka sai tayi kokarin saita natsuwarta cikin farin ciki ta budewa afee hannu alamar oyoyo ta taho "oyoyo afeena oyoyo ummulkhairi uwar alheri...."cikin murna jiddah ke maganar hakan ya sawa afee kwarin gwiwar karisawa cikin sauri ta rungumeta kuka ya kwace na afnan ta fashe da kuka,shafa kan afnan jiddah tayi ta dago fuskarta ta sumbaceta a goshi ta girgiza kai alamar tabar kuka,.
Da nafeesah da abidah da aysha suka hada ido suka tabe baki aysha kuwa bakin ciki da haushin da suka bata kauda kai tayi gefe ta mike ta fice a dakin dan batason abun haushi gaba daya haushi ne ya lullubeta....
"Afeen anty jiddah,dama zakizo gareni kece?ai na dauka kin mance dani kin daina sona kece masoyiyata a duniyar gidan Abdallah"
Dago fuskarta tayi da ta jike da hawaye "a da nice masoyiyarki a duniyar gidan yaya Abdallah amma yanzun dukkan mu ne masoyanki har ummah dasu rumaisa"tsare afee tayi da ido jiddah tanajin kunar rai wato saida tabar gidan sukasan amfaninta kenan koko sun kwashi kashinsu a hannune dalili?
Abida ta kada baki tace "A da ba?ai kowa ya tuba dan wuya ba lada tashi muje can harabar gida nafee raina ya soma baci"ta mike itada nafeesa abidah ta watsawa afnan wani kallo cike da takaici haushin dan uwanta ya shafeta suka fice,
Jiddah ta girgiza kai cike da takaici da ciwo zuciyarta nayi mata tsananin kuna tace "afee ke kadaice kikasoni tsakani da allah kika nunamin kauna ta gaskiya sai Abbah da shima idan har nace ya taba canjamun fuska daidai da second daya na rayuwar danayi dashi a matsayina ta surukarsa nayi masa karya afee, wallahi ummah bata sona bazata taba sona ba haka yan uwanki don haka kima bar fadin abinda kike fada"
Share hawaye afee tayi wasu sababbi na kara fita daga kwayar idonta "kibar wanan hawayen afee banason ganin kukanki wallahi idan kina kuka ina ganin tankar na Gaza miki ne ummulkhairi"a raunane jiddah tayi maganar kamar zatayi kuka tana ruko hannun afnan,
"Anty jiddah idan har baki yarda ummah na sonki ba dasu yaya meenah to kinyarda da soyayyar da yaya Abdallah yakeyi miki"
Girgiza kai jiddah ta sakeyi wani irin zafi takeji a zuciyarta ko ambatar sunan Abdallah bakayi saitaji tamkar ana watsa mata garwashin wuta a jikinta "afnan karki sake cewa yayanki yana sona dan wallahi Abdallah baya sona, Abdallah ya tafka kuskuren da harabada banaji xan iya dawowa hannunsa a matsayin matar aure idan har hakan ta kasance kuwa saina gwammaci mutuwata da hakan,bazan yaba komawa Abdallah ba a halin yanzun babu namijin da natsana sama da Abdallah"cikin daga murya take maganar cike da tsananin fushi jikinta har rawa yakeyi ta mike tsaye,afee kuwa sakin baki tayi tana kallon jiddah yadda take kumfar baki bata taba tunanin tsanar da jiddah keyiwa Abdallah ta kai hakanba saidai abu guda daya ne dikda kankantarta tana hango tsantsar jin haushin Abdallah a kwayar idon jiddah amma ba tsanarsa ba saboda ta wani fannin jiddah tanada raunin zuciya....
Daga parlor sukai shiru suna jiyo sautin kalaman jiddah dake amsa kuwwa a parlor,jikin ummah ya Kara yin sanyi bayan ta gama kwaranyo roko da neman afuwa wajen iyayen jiddah da saka kokon bararta na nemawa Abdallah auren jiddah a karo ns biyu,
Ajiyar zuciya ummah ta sauke "kina jiyo furucin da jiddah keyi akan Abdallah ko?kayya banso kikaji wanan kalamai Marasa dadi da jiddah keyi ba don babu uwar da zataji dadin cewar an tsani yarta,a halin yanzun abinda jiddah takeso gaskiya shi zaayi saboda wahalar da tasha a baya hajiya kiyi hakuri",
Kwalla ce ta ciccikowa ummah cike da nadama da tsananin danasani tabbas sun tafka kuskure saidai daga ganin Abdallah bashida lafiya ciwonsa na kokarin tasar masa wanda har yanzun basusan dalilinsa na bada kodarsa da yayi ba batare da shawara ba shin sun san cewar Abdallah koda daya gareshi koko ta sanar musu ko zasuji tausayinsa?,...gumi ne ke karyo meta ba lallai su yarda yarsu ta auri mai koda daya a karo na biyu ba idan AUREN FARI basu saniba bazasu yarda a karo na biyu ba,
Mikewa ummahn jiddah tayi ta bude laluben dakin da jiddah ke zaune ta yafito ta da hannu,ta nuna kanta "inzo ummah?"
"Ehh kizo ku gaisa da hajiya habiba"tana fadin haka ta saki labule batare da jiran cewarta ba,....sosai gaban jiddah ke tsananin faduwa cike da fargaba ta mike,afee ta ruko hannunta suka hada ido taga yadda kwalla ta cicciko a idon afee sai kawai ta kauda kai bataso afnan ta karya mata zuciya ta tarwatsa zucuya mai cike da karamci da halarci irin zuciyat iqbal....taku take kamat kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shigo parlorn ta nemi nesa kadan ta tsugunna ta sunkuyar da kai,
Shiko Abbah banda gumi babu abinda yakeyi kamar an watsa masa ruwa idanuwansa sunyi jajir yana wani tunani can daban....."hajiya habiba ga jiddah ku gaisa"ummah tsce,
"Ina yini ummah anzo lafiya?"jiddah ta gaida ummah muryarta na tsananin rawa,
Cije lebe ummah tayi "lafiya lau hauwau ya gida ya iyayenki da yan uwanki ya bayan saduwa?"
"Lafiya lau ummah,yasu rumaisa"
"Alhamdulillahi....jiddah...dan allah ki gafarceni kiyafemun laifukan da nayi miki a rayuwa da irin zaluntarki da nayi,sanan ina rokon alfarmar ki dawo garemu a karo na biyu dani da yarana mun tanadar miki ingantacciyar rayuwa ba irin rayuwar da kikayi a baya ba kigafarceni ki ceci maridin d'ana don yana cikin hali na rashin lafiya Wanda bazai fadu ba"
Kwalla ce ta digowa jiddah tasa gefen gyalenta ta goge,dakin yayi shiru sai bugun zuciyoyi ta ko wani fanni "ummah na yafe miki dake da ahalinki gaba daya har Abdallah,amma ina mai baki hakuri Akan bukatarki ta dawowa inyi rayuwa da Abdallah a karo na biyu ba.....kiyi hakuri ummah inada wanda nakeso zan aura bilal"...ta mike ta shige daki a guje ta rufo kofa,
Sandarewa ummah tayi a zaune, innahlillahi wa innah ilaihi rajiun gumi ya karyo mata jin sunan da jiddah ta kira zata aura bilal?aminin Abdallah?tabbas kodar Abdallah zatayi failing dan bazai iya jure wanan damuwar ba,
Gyaran murya abban jiddah yayi "hajiya habiba ina mai baki hakuri,saidai abinda zance shine allah kadai yasan abinda yake boye,amma inaso kisa a ranki aure nufi ne na allah don haka Abdallah ya shiga cikin manema aure babu yadda Allah baya lamarinsa idam da rabon daidaitawa zasu daidaita kinji hajiya?"
Umman jiddah ta kada "allah ya zabi abinda yafi zama alheri ...ya jikin shi Abdallah?meke damunsa?"
"Ammm...ummm da sauki alhamdulillahi amm babu komi"
Afee ta amshe zancen kamar an tsikareta "abbah ya Abdallah kodarsa daya ce....sanan amfanin koda biyu a jikin mutum tasa guda daya ce take daukar nauyin komi,koda biyu a jikin mutum daya ce take amfani da dik wata wahala ,idan tayi failing sai daya ta dauka...to tasa guda daya ce idan daya tayi failing saidai mu rasashi abbah"afee ta fashe da kuka ta toshe bakinta ta mike ta fice tana kuka,
Ummah saida tayi kwalla furucin da afee tayi yasa ta share hawayenta ta yunkura ta mike ta dauki jakarta"tou zamu koma mu,mungode da karamci allah ya saka da alheri ya kara zumunci allah ya tabbatar da alheri"
"Ameen hajiya habiba"ummahn jiddah ta taka musu har wajen gate ta dawo...abbah ya mike ya nufi dakinsa,
Ummah dakinsu jiddah ta daga labule tana kwance ta kifa kai tana shasshekar kuka ummah ta karasa"ke akoke gwamnan kuka?kukan na menene?bakince baki sonshi ba to meye kuma?"
Mikewa tayi tana hawaye jikinta a rawa "ummah furucin abbah ke tadamun da hankali nidai allah yasa kada ya rabani da Iqbal "ta fashe da kuka,
Zama ummah tayi gefen gadon ta tallabo jiddah tana goge Mata hawaye "ya isa haka,zanyi magana dashi bayan ishai"
Bude labulen dakin akayi,abban ne yayi alwala "zainab kyaleta zamu tattauna yau daddare nidake da ita da ibrahim bayan tattaunawar zansan mezanyi don bazata Kara sati biyu a gidan nan ba zoki nemomin dadduma inda kika ajiye a dakina"ya saki labulen yayi gaba,
Ummah ta bubbuga bayanta "ya isa ki kwantar da hankalinki abinda kikeso shi zaai kinji?"... ummah ta mike tabi bayan abbah....
********
Tun da ummah suka shigo cikin wanan yanayin hankalin Abdallah ya tashi abbahn Abdallah kuwa mikewa yayi ya dau wayoyinsa da makullin mota yace yanada ganawa da abban bilal,dansu har yanzun suna zumuncin su,ya fice,
Ummah batada yadda zatayi saboda Abdallah ya tsareta da tambayoyi she have no option than ta fada masa aihinin inda sukaje da abinda ya faru,saidai basu fada masa irin furucin da jiddah tayi ns rashin kaunarsa ba,
Jan nunfashi yayi "da kun sanar mun inda zakuje tun da wuri da ban baku goyon baya wajen zuwa ba dan bazakuyi nasara ba idon jiddah ya rufe laifina kawai take gani bata ganin laifin da ni tayimun ummah...tace muku bata sona ko?"yayi tambayar yana kallom ummah idonsa fal hawaye cije bakinsa yayi ya hadiye kukan cikim zafin zucuya,
"Ku barni inyi yakim neman yardar ta ni kadai, inama ace zaa samu wanda zai fahimtar da jiddah irin soyayyar da nakeyi mata da nadamar da nake ciki a yanzun? gashin yanzun ko aikin yi banidashi"
"Ka auro mai farar kafa Abdallah,kashinka dana ramlah ba daya bane sam batada kashin arziki ko kadan gashi tun baaje ko inaba an dakatar dakai daga aiki ni naga alamar sai komi naka ya kare sanadiyyar wanan bakar dagar"....shigowar ramlah ne yasa parlorn yayi shiru kowa ya bi ta da kallon mamaki meya kawota? Abdallah tunda ya daga kai ya kalleta ya maida kansaz
Wani kallo takewa ummah kallom zamu hadu sai kawai ta zube kasa "ina yini ummah?"
"Lafiya".. ummah ta amsa ta kauda kai,
Abdallah dakyar ya saita kansa yayi karfin halin mata wani kallon daga ina kike?bakinsa yayi masa nauyi be iya motsa harshebsa da yayi masa daci ,kafin ya tambayeta ta amsa tambayar da zai mata"daga gida nake nasam nan kayo na gaji da zama nikadai kuma su meenah bason zuwa suke ba shine na biyoka sai mu koma gida baki daya"..jinjina mata kai yayi ya mike a hankali kirjinsa kamar an dora masa dutse "ummah Bari inje inga jiddah yau banganta ba,",
"Bazaka tsaya kaci abinci ba Abdallah sai ka fadi a hanya?"...ko waigenta beyi ba sai girgiza kai da yayi ya fice,ta girgiza kai tace "allah sarki"ta ja ajiyar zuciya sanan suka hada ido da ramlah ta watsa mata harara,
Kyalkyalewa da dariya ramlah tayi"aini dik wanda yaci tuwo dani miya yasha,sanan ni kuturwar uwace zama dani dole wallahi hajiya habiba kina tunanin zakiyi nasarar dawowa da danki tsohuwar matarsa saboda kin fara gasuwa a hannuna?uhmmm baai komiba"...
Su rumaisa zasuyi magana ummah ta dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu "kina tunanin ke kinkai matsayin da zaki gasa hajiya habiba?baki Kai wanan matsayin ba baki taka wanan mukamin ba komi lalacewar masa tafi karfin kashin shanu yariya.....dik wanan fuffukar da kikeyi cikinki ya duri ruwa kina cike da fargabar dawowar jiddah rayuwar Abdallah saboda ina kyautata zaton akwai kulli wanda bazai warware ba sai jiddah ta dawo..... abun zaiyi miki ciwo da zarar kim bude idonki kinyi tozali da wadda kika kora ta dawo kuma matsayinta da martabarta harta kere taki"
Ummah ta mike ta dubi yaranta "ku tashi mu shiga daga ciki dan bazan tsaya tana fada ina fadaba dan niba farar kafa gareni ko kashin mundiriki ba kuzo muje cik"tayi gaba da afnan da rumaisa da meenah suka takewa ummah baya suna waigen ramlah....
Cije lebe yatsa ramlah tayi lallai matar nan saina sakar mata maciji a ciyawa,zanyi maganin ku dukkanku tabbas idan jiddah ta dawo rayuwar Abdallah Babu riba abinda nayi abu daya ne kawai shine in nemo wanan yaron black dikda nasa ana bincikamun shi nasan yadda zanyi in hada kullim da jiddah zata tsani Abdallah fiye da yanzun kuma saina warware dawowarta gidan nan....ta kushingida da jikin kujera tanajin zafin maganganun ummah....
******"
Sosai jiddah ke nishadi tun kiranta da iqbal yayi yana Kara jadadda mata kalaman soyayya da yadda yake kaunarta tana karajin kanta cikim wata daular soyayya wadda bata taba tsintar kanta ba,
Yaya ibrahim ne ya shigo gidan yana kwalawa jiddah kira "ki fito kije ki sallami wancen bawan allahn mai kamada sabon kamun hauka tun dazun yake aike taki fita ya kira wayarta call waiting"abbah ya tsagaita da tauna abinci "wa kenan kuma ba ibrahim"
"Waye Banda tsohom mijinta Abdallah? yanzun biyoni yayi ya kama rigata kamar zaimun sujada,ta fita ta sallameshi ni abbah kasa wanda takeso ya fito ayi aure"
Rike kai abbah yayi yana juyayin kalaman ibrahim "kira jiddar taje wajensa yanzun ta dawo ta sameni"
Kira ibrahim ya kwala mata cikim sauri ta kife wayar a gado batare da ta kashe ba ta fito "gani yaya,"
"Kije Abdallah na kofar gida yana jiranki"...batace komiba ta juya ta shiga daki ta dau wayarta ta makala ta cikin dankwali tana cigaba da wayarta da bilal ta fice,
Aysha da abida da nafisa abbah yace su shige daki sanan yayi gyaran murya "banji dadin furucin da kayi akam Abdallah ba wanda kodarda daya ce ke aiki a jikina a yanzun haka"
Tsittttt sukayi da ummah da Ibrahim suna kallom abbah ido waje "tabbas kodar Abdallah ce jikina wanda ya bani kyautarta batare da shawarar iyayensa ba a lokacin da jiddah ta dora hannu a kai take kukan shirin maraici"
"Tou abbah dan ya baka koda sai me?sai a biyashi kodarsa yarinya ta auri Wanda takeso",
Nunasa da yatsa abbah yayi "kai ibrahim ka shiga taitayinka ina magana kana fadamun maganar banza?....bazan goyi bayan karya ba ko kadan dan ni inada hankalina dikda bazanwa jiddah dole ba amma ku Shiga taitayinku ku saurari abinda zance da kunnen basira da hankali"
"A tunaninku dukka Abdallah ne yayiwa jiddah laifi da har zai bibiyeta tanayi masa wulakanci?ko kuna tunanin idan akaje kotu bazaa zanesu itada wanda ta kawo gidan aurenta ba?kuna tunanin bazaa kamasu duka su biyun da taka martabar aure ba?.....tou bari kuji jiddah tayiwa Abdallah laifi nacin amanar aurensa koda kuwa Abdallah baya biya mata hakkim aure be dace ta take hurumin aure ta kawo wani kato cikin gidansa ba saboda jahilci da rashin sanin martabar aure.....sanan bilal yake kowa shine babban kasurgumim mai laifi wanda dole allah ya tambayeshi hakkin take martabar aure matukar Abdallah bai yafe masa ba,wallahi idan Abdallah be yafe musuba ko aure sukayi bazasu zauna lafiya ba bawai baki nayi musu kodan ina kokarin kare Abdallah ba ko kadan ina kare mutuncin aure da hakkokin allah ai nasata islamiyya tasan hukuncin laifin da tayi,sanan ko wani irin laifi Abdallah zaiyi mata alheri yana goge Sharrin mutum domin Abdallah ne ya ceto rayuwata kodarsa daya ce ke aiki a jikina wanda da badan taimakonsa da taimakom Allah ba da yanzun dukkanku kun zama marayu"...sunkuyar da kai ibrahim yayi gumi na karyo masa,
Ummah ce tayi karfin halin cewa "yanzun kenan Abdallah beda laifi wulakanci da yayi mata da cin zarafin da yazo yayi mana har gida ko shima ba laifi bane?ita ba ya bace kenan baban jiddah"
Girgiza kai abbah yayi "ko kadan jiddah yace kamar kowa kuma bance Abdallah beyi laifi ba amma inaso ta horasa ko ayi masa hukunci daidai da laifin da yayi.....da babban kuskuren da yayi na rashin bincike da gaggawar yanke hukunci, saidai zainab ina tuna miki ko nine aka sanar dani kinyi hakan da aminina na tambayesa ya amsa yayi to kishi ne zai rufemun ido inyi miki saki uku ma gwara Abdallah saki daya yayi....dan haka ku shiga taitayinku a rinka sara ana duban bakin gatari...bazanyiwa jiddah dole ba amma idan ta dawo gida zanyi magana da ita idan ta amince ta auri kwartonta wanda yayi mata sanadiyyar aurenta na fari aminin mijinta Abdallah fine zan aura mata shi din kamar yadda takeso"
Cikin rashin jin dadin furucin abbah ummah ta kauda kai "bedace kace kwatonta ba kamar ka yarda da cewar sunyi kwartanci ko yayi amfani da ita kenan"
Yar dariya abbah yayi ya girgiza kai "ko beyi anfani da itaba tunda ya taba jikinta yaje gidanta na sunnah kwarto ne amma zanbar kiran sa da kwarto tunda yana shirin zama sirikina"....tsitttt parlorn yayi,
*******
Tunda jiddah ta fito Abdallah ya tsareta da ido ko kiftawa batayi waya take tana zabgawa iqbal shagwaba yana tarairayar ta a hands free tasa wayar, Abdallah ji yake kamar zucuyarsa ta faso kirjinsa ta fito saboda tsabar takaici da kishi,
"Iqbal hold on bari inyiwa wanan mutumim warning da yake kokarin shiga gonar da bashi yayi shuka ba,ya dade da girbe shukar da yayi dikda baici ribar shukarba sai faduwa,iyaka Girman gona da iri da akabasa da taki ya kasa shuka abun arziki ina zuwa sweet"... ajiyar zucuya bilal ya sauke daga cikim wayar ya lumshe ido,
Nunasa take da yatsa "Abdallah....wai Kai ka yarda zuciyarka ne kare ya cinye?wai bana fada maka bana sonka ba na tsaneka bazan koma gidan kaba?kana tinamim har zucuyata ta warke da irin azabtuwar da tayi akam tsananin sonka a baya?...ko kadam har yanzun zuciyata ciwon dake cikinta danye ne sharaf wanda baxai warkeba sai ranar dana auri muradin raina amininka waninka Wanda yasan tattalim mace,yasan kulawa yasan tausayi sanan yasan adalci da halarci don haka ka tattara tsummar kafafuwanka kabarmun kofar gidan mu kafin in farfasa maka glass"ta galla mishi harara,
Tabbas bazaiyi zuciya da itaba amma hakanan zaije ya bata space na kwanaki ko zatayi tunani ta dawo gareshi,zai kwanta rashin lafiyar da ba lallai ya tashi ba,
"Shikenan zanbar kofar gidanki,xan baki space kiyi tunani kema naki laifin da kikaimun jiddah....sanan ina mai rokonki idan na mutu ki yafemun dan koda ta tasoma failing"hawaye suka gangaro masa,
Tabe baki tayi tana masa kallo wato nice ma nayi masa laifi lallai Abdallah kaci uwar rainin wayau tace a ranta sanan ta watsa masa harara "Allah ya jikan musulmi"tayi gaba abinta tana fadin ",hello Iqbal...am back to u i luv u helmiy"tayi cikin gida,
Tana bude labulen parlorn taga sunyi shiru kowa da abinda ke yake sakawa a zuciyarsa tsoro ya cikata take taji wani fitsari na neman kubuce Mata ta daure ta hadiyi wani miyau me kauri ta shige tana kokarin shiga daki abbah ya kirata "jiddah....zo ki zauna nan taron naki ne dama jiran shigowarki nake"gabanta ya yanke ya fadi tsoro ya cika zuciyata ta nemi waje zama ta zauna ta sunkuyar da kai jikinta na tsananin tsuma......
0 comments:
Post a Comment