Cike da tsoro da tsananin kaduwa jiddah ta motsa bakinta kanta a kasa tace "gani Abbah"
"Jiddah....dama jira nakeyi indawo garin inji ko kinada manema aurenki?...yanzun dai su waye ke sonki kuma su waye ke zuwa neman aurenki? inajinki fadamun"
Cikin jiddah saida ya kad'a,ta kara sunkuyar da kai muryarta na rawa cike da kunya cikin sanyin murya tace "Abbah, Bilal ne yake sona sai Abdallah da ya dawo da niyyar aurena a karo na biyu amma ni bilal nakeso shine nakeso in aura"ta karasa maganar muryarta na rawa jikinta na cigaba da tsuma cike da tsoro,
"Jiddah waye bilal?wani irin so yake miki haka da kika zabesa a matsayin mijin aurenki?sanan wace irin halayya garesa da kikai saurin amincewa dashi koko dama can kedashi kundade kuna son juna ne?"abbah ya kafeta da ido,
Tambayar abbah yasa gumi ke karyowa jiddah ta sunkuyar da kai ba tare da ta bashi ansa ba tsawon minti daya batace komiba batada niyyar magana,ummah ce tayi mata magana cikin kosawa da son jiddah ta amsa tambayar ta abbah "ya zakiyi shiru?abbanki ke miki tambaya kinyi shiru ko bakida amsar tambayar tasa ne?"ummah ta tambayeta cikin wani yanayi,
Girgiza kai jiddah tayi "inada amsa ummah"
"Tou muna saurarenki"
Dago ido tayi ta kalli yaya ibrahim taga yayi tagumi ya tsareta da ido ta sunkuyar da kai"abbah bamu dade dashi ba,nasanshi lokacin ina gidan Abdallah ne abbah,bilal ya bani gudunmawa a rayuwata ta hanyar samamun farin ciki lokacin da nake cikin kunci a gidan Abdallah,bilal shine yake bani lokacinsa wajen kawar mun da damuwa gudu gada in fada cikin wani hali"sai hawaye ya subucewa jiddah ya soma zuba a idonta sharrr sharr...
Gyaran murya abbah yayi sanan yace"ba kuka nasaki kiyimun ba inaso insamu kwararan hujjoji ne wanda zasusa kiso bilal aminin mijinki kiji kinada interest na aurensa bayan kinsan alaka mai girma dake tsakaninsa da tsohon mijinki,...jiddah bilal be baki gudun mawa ba a rayuwarki sai gudunmawar bata miki suna da yasoyi a zahirin gaskiya"
Da sauri jiddah ta dago manyan idanuwanta da suke cike da hawaye tana kallon abbah ta kasa magana,..
Jinjina mata kai abbah yayi "kwarai dagaske,don jamaa tuni sun dade da jin abinda ya fito dake daga gidan miji kinga kenan ya tabbata cewar da saninki kikai alaka da aminin mijinki da aurenki meye makomarku duka ku biyu?kun taka sharia sanan kunbi son zuciya kun Shiga hakkin aure wanda akan hakan kadai Allah sai ya muku hisabi da tsohon mijinki koda kuwa shine yake shiga hakkinki sai kema kika dauki hakkinsa wajen tarayya da waninsa,wanin ma amininsa ....jiddah bari kiji infada miki kema kinada laifi babba kuma kin dau hakkin Abdallah koda yanada laifi laifinki ya take nasa"
"Abbah....abbah... Bilal fa"
"Bilal mene?shi bilal din ya taba samun Abdallah ya yi masa nasiha akan abubuwan da yakeyi miki?meyasa be sanar dake cewar shi aminin mijinki ne ba idan har dagaske kaunarki yakeyi bazai taba yin soyayya dake da auren wani akanki ba dan haka ki shiga hankalinki ke roki allah gafara sanan ki roki yafiyar mijinki kuma wallahi ko auren bilal kikayi abinda kukai bazai bari ku zauna lafiya ba hakkinsa ne zai bibiyeki....kuma ina kara tuna miki ni din nan da kike ganina kinajin dadi kina ganina da lafiya mijinki shine ya ceto rayuwata ya bani kodarsa amma idanuwanki ya rufe neman kasheshi kikeyi da bakin ciki"..
Cikin Kuka jiddah tace "Abbah dik naji amma ni wallahi banason Abdallah ni bilal nakeso idan ban auri bilal ba mutuwa zaiyi banyi masa adalci ba abba,ka taimakeni kada kace in koma gidan Abdallah bazan koma inyi rayuwa da Ramlah aminiyata ba..."
Wata harara abbah ya watsawa jiddah ta sunkuyar da kai,ummah kuwa cike da tausayin jiddah tace "ai ba cewa yayi zai aura miki Abdallah ba,abinda kikeso shi zaiyi miki kinji kiyi shiru ki daina wanan kukan"
Girgiza kai abbah yayi ya dubi ummah "Zainab kece kike daure mata gindi kenan?kema kin take gaskiya kin hau tubalin toka karya?tou ramin karya kurarrene kuma ni banyi mata alkawarin aura mata wani bilal ba saidai in son ranta zanyi mata zanyi abinda ranta yakeso amma babu ruwana"
Cike da bacin rai abbah yake maganar gabaki daya takaici ya hanasa kara magana,mikewa yayi ya bar parlorn ya nufi dakinsa,
Kiran yaya ibrahim akayi a waya ya dau wayar yasa a kunne ya mike yabar parlorn shima.....
Fitarsa keda wuya aysha ta shigo wadda dik tattaunawar da akeyi suna daki duka suna jinsu...wuri ta nema ta zauna tana kallon yadda jiddah ta kwantar da kai a cinyar ummah tana shasshekar kuka,abidah da nafeesa a tare suka fito suma suka zauna,
Nafeesa ta nemi gefen jiddah ta tallabo ta "kiyi shiru ablah ki nemi zabin allah kukan ba shi bane abinyi,idan akabi ta maganar abbah tabbas hakan gaskiya ne,don ni zanso ki koma gidan ya Abdallah kodan waccen bakardagar ta mutu tasan baki bar mata mijin ba, inaso ki koma ayi gugar jigida dake da ita a gidan Abdallah...inaso inga da wani ido zata kalleki,"
Abidah ta amshe zancen "da wani ido ko zata kalleta banda idon data kalleta dashi?nadade da tsanar wanan ramlahr wallahi tunda dadewa ablah ta maidata kamar uwarta komi ita take fadawa gashi ta gama sanin sirrinki da mijinki ta aure miki shi tabarki da zawarci da zubar da hawaye ni gaba dayanku ma haushi kuke bani mtswww"abidah ta mike tanata masifa ta nufi kitchen,
Ajiyar zuciya ummah ta ja ta sauke "ni tausayi yaron nan bilal yake bani wallahi"
Abbah ne ya fito zashi masallaci Yana gyara agogon hannunsa "tunda tausayi yake baki saiki aura masa ita,koda yake ban isa da jiddah ba amma dai ina tunasar muku da cewar da sabon gini gwanda yab'e"...ya fice ummah tabisa da kallo taja dogon numfashi ta sauke"Allah ya zabi abinda yafi zama alheri"
"Ku tashi ayi sallah gashi can ana kiran laasar abbanku ma sallah ya tafi masallaci"
Jiddah dakyar ta iya mikewa kafafuwanta sunyi tsami dakyar take takasu ta nufi daki idanuwanta sun kumbura sunyi jajir,tana shiga daki ta ajiye wayarta gefen gado ta cire gyalen kanta ta jefa kan gado ta nufi toilet don tayi alwala,
Cikin toilet din kuka tasa kuka sosai takeyi tana alwala haka ta fito tasa hijabi ta tada sallah....
******""
Ramlah kuwa Tana kwankwasa gate din gidan ta shigo "barka da zuwa hajiya"
Wani kallo tayiwa mai gadi a wulakance wanda yayi saan ubanta har zata wuce ta dawo "mai gidan ya dawo ne?"ta tambayesa cike da isa tana daga kai sama ita ga mai gida,
"Ehh ya dawo bai dade da dawowa ba yana ciki"
Yana bata amsa tayi gaba tana kada kai,girgiza kai baba mai gadi yayi yace "ikon Allah...wanan yarinya fitsararriya ce bana shiga sabgarta kafin ta wulakanta ni,dan ko me gidan bayamun magana haka hatsa gatsa"a fili yake maganar sanan ya zauna a bencinsa dake jikin gate ya kara kada kai yace "Allah sarki yar albarka jiddah.... Allah ya dawo da ita gidan nan inga karshen cin amana Allah ka daidata tsakaninta da mijinta"baba ya daga hannu ya shafa sanan ya dau radiyonsa ya kunna ya cigaba da saurare,
A parlor yake kan daddumar sallar ya sallame ta shigo cike da masifa da takaicin ya barota a gidansu hajiya,wato daga balaguron nasa sai yayo gida "Abdallah wato da badan nagaji da cin kashin da akemun ba nataho da can zan kwana kenan bazaka biya ka daukeni ba?ka baroni a can gidan su hajiya ko?"
Wani kallo yake mata sama da kasa yana azkar dinsa,saida ya shafa sanan yayi gyaran murya yace "can din ba gida bane daji ne kenan?"
Kauda kai tayi sanan ta juyo cike da masifa "aiko gida ne baxaka baroni ka dawo gida ni ka barni ina zaman jiranka ba bayan wulakantani da hajiya da kannenka keyi kamar mujiya"
Gyara zama yayi kan dadduma yana watsa mata harara cike da takaici yace "idan kuma na manta dake a can gidan fa?"
"Abdallah ka manta dani kake cewa?kasan me kake fada kuwa?mantawa dani a wani waje?"
Cikin kakkausar murya yace "ni waliyyi ne da bana mantuwa kenan?kuma ai kece kika maida kanki mujiyar a wajensu,mara hakuri kawai allah ya bawa jiddah hakuri,ita da ake mata wanda yafi naki tayi hakuri"
Wata girgiza ramlah tayi cike da masifa ta tube dankwalin kanta ta jefa kan kujera ta gyara tsayuwa "jiddah daban ramlah daban bazanyi tolerating iskanci da bura uba ba wallahi,dan haka gwara ma kasani kaima wanan take taken naka dik na fahimceka saboda zaka dawo da matarka tsohuwar kwartuwa"
Yatsa ya daga yana nunata sanan ya yunkura ya mike "kada ki kuskura kice zaki zagi jiddah...idan kina tunanin saboda ita nake wulakantaki kiyi abinda zakiti,mara mutinci kuma bari kiji bakoga komi ba wallahi indai akan jiddah ne sai ma ta dawo gidan nan kunyi zaman kishi ki sa ido kiga tsantsar biyayya a wajen matar aure ta gari,idan ta dawo gidan nan ke ba wata ba sai kin kwashi kashinki a hannu mara tarbiyya kawai"ya kafeta da ido,saiga haware sharrr a idon Ramlah...kallonsa take cikin wani irin yanayi, kwafa yayi ya shige daki ya barta nan tsaye ta bishi da kallo sanan ta ja da baya ta zauna a kujera jabar,..
Dafe kai ramlah tayi cike da bakin ciki ta furta "na Shiga uku..."tun yanzun kenan Abdallah ya soma min cin kashi inaga matarsa ta dawo?insha allahu jiddah bazata dawo gidan nan ba dan dawowarta cikin rayuwar Abdallah tamkar masifa ce a gareta,tayaya zaai ma jiddah ta dawo gidan nan?ai idan nabari jiddah ta dawo naci baya,
Shiru tayi tasa hannu ta share hawaye dole ma insan mafita,makirci zan hada miki jiddah sai kin gwammace kida da karatu matukar kika shigo gidan nan sai kinyi kukan da yafi na da, tunda kikasa na zubar da hawaye akanki akacimun mutunci,
Ta zabura kamar wata zautacciya tayi cikin daki ta fada kan gadonta ta kifa kai,soyayyarsa kw hura mata wuta a zucuya ji take tamkar ta tashi ta shiga dakin ta rungumesa ta basa hakuri,amma kasan zucuyarta kishi ne mai tsanani ke azalzalarta....
Tunda Abdallah ya shigo daki ya rufe kansa da makulli ya cire jallabiyarsa yake kuka kamar karamin yaro,hada kansa yayi da bango yana kuka yana rokon allah yasa kada jiddah ta kubuce masa,
*******
Bilal ne ya shigo gida daga wajen mahaifinsa yake can company dinsu,murmushi ne falala a fuskarsa kallo daya zakai masa kasan yana cikin farin ciki,cike da kosawa zainab tayi murmushi "yaya bee sai faraa kakeyi,kamar anyi maka albishir da gidan aljannah ko ance anbaka auren jiddah kutafi"
Dariya suka kwashe dashi su zuhura,wani kallo yayi mata yasan da gayya tayi maganar hakan yasa ya shafa kansa "well kusan hakan ne don daddy ya mallakamun office yau sanan yayimun alkawarin zuwa nemamun auren jiddah gobe insha allahu dan haka ya umarceni da inje ingana da mahaifinta in tambaya masa izinin zuwa"
Tsalle zuhura da rufaida sukayi "zamusha bikii....woooow bikin da baa tabayin irinsa a dangi ba hooo yaya ango"
"Kai shashashu marasa hankali shine abun ihu ni kun cikamun kunne ma,basabanba zaai biki a gidanku ko?"momy ce tayi maganar cikin sigar tsokana,
Nan da nan idon zainab ya cicciko da kwalla tana kallon bilal ya sakar mata murmushi ya dawo gefenta yaja kumatunta cikin sigar tsokana "kumatu kamar kinsha yease?"
Harara ta watsa masa cikin wani irin yanayi tana kokarin danne damuwarta "wayasani ko yease din nasha na hada da baking powder"
Momy tace "ah to ki rinka ramawa kibar bari yana tsokanarki haka babban kwabo dik ya zubar da girmansa",
Rufaida ta kyalkyale da dariya "yaya sai zumudi kake baka kojin kunyar momy zakai aure"
Hararta bilal yayi "munafuka kawai,kinjawa kanki yanzun dama zan kai zainab wajen jiddah bazamuje dake ba ki zauna kici munafumcinki"
Kallon momy rufaida tayi "momy kinji wai bazaije Dani ba kuma nasan zasu biya suci dadi ni sai a barni a gida kenan?"
Girgiza kai momy tayi "waya isa autar momy da daddy kafarsu kafarki idan kuma baxaaje dake ba saidai a fasa zuwan"
Tabe baki Bilal yayi ya dage kafadarsa yana kokarin kiran jiddah yayi hanyar fita parlorn zuwa sashensa,
Wani kallo zee tabi bilal dashi ko kifta ido batayi idonta sun cicciko da hawaye,...rufaida ce ta zunguri momy ta nuna mata zee wadda tayi nisa a kallon bilal har ya bace bata sani ba,
Girgiza kai momy tayi ta furta a kasan zuciyarta "ikon Allah....."
Zuhura da rufaida cike da gulma sukaiwa juna wani kallo sukai murmushi, sanan suka hada baki sukayi gyaran murya,a furgice ta juyo suka hada ido da momy rufaida da zuhura suka kwashe da dariya,
Momy mikewa tayi tabarsu nan ganin zainab ta sunkuyar da kanta kasa....momy na barin parlorn tacewa zuhura cikin wani yanayi "sis....inaji jibi zan wuce katsina"muryarta na rawa,
"Jibi kuma?kuda kukazo mana hutu?ai ammy tace itace zatazo ta daukeku Dan Allah yaya zee kada kiyi mana haka kinji"
Girgiza kai tayi tana kokarin boye kwallar idonta ta mike ta ruga da gudu dakinsu, zuhura da rufaida suma mikewa sukayi sukabi bayanta ...
*******
Rigingine ya kwanta yana makale da wayar idanuwansa a lumshe yake magana "meyasa nakejinki cikin wanan yanayin habeebty?me akayi miki?bayan lafiya lau nidake mukayi waya dazun ko wani ya bata miki rai ne?"
Kada kai jiddah tayi daga inda take zaune ta idar da sallar ishai,kan dadduma hawaye ya sulalo mata tace "me kaji ne iqbal?meyasa kake tunanin anyimun wani abu?tou ko anyimun wani abu ai Dole in mance da koma meye akaimun in ajiye dik wata damuwa gefe inyi magana da farin cikina hasken rayuwata"tasa hannu ta share hawaye...
Runtse idonsa yayi ya budesu cikim hasken lantarkin dake dakinsa suka kashe masa ido yayi saurin rufewa "inajin sautin muryarki kamar hawaye ke diga daga kyawawan fararen idanuwanki,....tou idan ma sune ke zuba inaso su kafe yanzun ta hanyar samun daddadan labarin aurena dake...ina me miki albishir da zanzo yanzun zanyi wanka kiyimun iso wajen Abbah zanzo daddyna yace in tambaya masa zuwa nemamun aure da zaiyi gobe ko jibi insha allahu"bilal ya karasa maganar yana yar dariya,
Cakkkk ta tsaya tana kallon wani sashi na cikin dakim hawaye na ambaliya a kwayar idonta,tsoro ne ya cikata hakika batada labarin da yafi wanan dadi a rayuwarta amma ya abbanta zai dauki maganar?koda yace bazai mata auren dole ba amma tanajin nauyin tunkararsa da zancen turowar mahaifin bilal zaiga kamar maganar da yayi mata ne dazun,
"Hello...habeebty naji kinyi shiru kamar wadda aka daukewa wutar nepa,ko dik farin cikin burin mu yana gab da cika ne?"
Cije lebe jiddah tayi ta saita kanta sanan tace "hakika babu wani labari da yafi wanan labarin dadi a rayuwata a halim yanzun, farin cikin da na tsinci kaina ciki ya wuce tunaninka Iqbal....tabbas idan burin mu ya cika nasameka a matsayin mijin aure?nafi ko wace mace saa a duniya.....
Murmushin jin dadi bilal yayi ya shafi sajensa "tashi ki shirya ki fadawa abbah babu dadewa zan zo gidan,zan taho da zainab tanaso ta ganki sanan yau kannena su zuhura zasuzo suga antynsu,idan yaso kema nan da kwana hudu zanzo in daukeki in kaiwa momyna ke ki gaisheta ko"
Murmushin jin dadi tayi "Insha allahu"sukai sallama ta kashe wayar,
Bin wayar tayi da kallo tana jin kanta cikin wani yanayi na farim ciki na burinsu xai cika tabbas ta kosa tabar Abdallah ta huta kafin ya hura mata wutar da zata kasa kashewa,saidai kasan zuciyarta tsoro ne cike da zuciyarta,ta yadda zata sanarwa da abbanta zuwan bilal da bukatarsu....abbah karbar da zaiyiwa bilal shine babbar damuwarta...
******
Cikin minti ashirin bilal ya tsula wanka yasha farar shadda ya murza hularsa yayi matukar kyau kamar wani balarabe da kayan hausa,fitowa yayi patlor yana zabga kamshi Yana gyara hannun links dinsa momy ce kadai xaune "momy barka da dare"
"Barka dai ango sai kace yau ne ake daura auren?kaganka kuwa dan momy tubarkalla masha allahu"
Murmushi yayi wanda ya kara masa kyau "momy baki rabo da tsokana,nace ina yaran nan ne su zuhura na shirya idan basu fito ba zan tafi inbarsu gaskiya"
Be rufe baki ba suka fito ko wacce ta dau ado sunyi matukar kyau "gaskiya yaya kayi kyau kaganka kuwa kamar wani ango?"rufaida tace taana dariya,
Hararta yayi sanan yayi gaba"munafukai ku biyoni mutafi dare nayi,naji kamar muryar daddy ma"
Daddy ne ya daga labule ya shigo yana tozali dasu yasoma murmushi "kaga yaya da kannensa uban yan mata kenan bilal,kayi kyau sosai hala can gidan zaa ko"cikin wasa daddy yayi magabar,bilal ya sunkuyar da kai cike da kunya yace "daddy barka da dawowa",
"Sannu da zuwa daddy"suka hada baki yan matan...cikin sakin fuska daddy ya amsa yace "kardai ayi dare",ya karasa parlorn bilal yayi gaba suka hada baki "saimun dawo momy"
"A dawo lafiya"tace cike da kulawa ...
Tafe suke a mota minti minti zee takan kalli bilal taja ajiyar zuciya haka kawai shima ya saci kallonsa sai ta bashi tausayi hannunsa ya mika mata "my kanwis....ya da satar kallo"yana driving yake maganar,
Kauda kai gefe tayi cikin shagwaba muryarta na rawa tace 'niban kalleka ba,idan ma na kalleka kai da wani ido ka kalleni"...
Jiddah ce ta fito daki sai kamshin turare taje powder kawai ta shafa fuskar nan tayi fayau ta dubi su ummah suma ita suke kallo,kallon da sukeyi mata yasa tadan tsargu...."ummah barka da dare"tace tana kokarin yin hanyar dakin abbah,
"Barka dai...ke ina zakije haka?"cakkk ta tsaya "zanga abbah ne zan isar masa da sako"
"Tou yana tare da bako ciki saki jirasa koh?"....jimm kadan jiddah tayi tace "ummah bako kuma?yaushe yayi bako?"
"Yanzun ba dadewa,kuma babban mutum ne ciki dan haka sai ki jira su gama saiki Shiga"
Dakyar ta ja numfashi ta juya "dama bilal ne yace zaizo inyi masa iso wajen abbah,"
Jinjina mata kai ummah kawai tayi cike da damuwa a fuskarta....kallom ummah tayi tanaso ta karanci yanayin nata amma takasa abu daya ne tana hango yanayi kamar na damuwa a tare da ummah bawani abu bane kuma tausayin halim da take ciki ne tasan son da ummanta keyi mata harshi abban,
"Ba wayarki bace ke ringing a daki?...kije ki dauka kila Bilal dim ne ya iso,kije idan bakom ya fito zan samu abban naki"
Cikim wani irin yanayi na rashin kwarin jiki ta nufi dakinta......
ALBISHIRINKU MAKARANTA LITTAFAN HAUSA MASOYA LITTAFAI NADANA KUNGIYAR HASKE WRITERS....SLIMZY NAYI MUKU ALBISHIR DA SABABBIN LITTAFAI WANDA SUKAIWA LAKABI DA TAGWAYE BIYU .....KUSAN WASU LITTAFAI NE KUWA?LITTAFAN SUNE RAMIN MUGUNTA.....HADE DA RAMUWAR GAYYA WADANDA HAZIKAN MARUBUTAN ZASU ZO MUKU DASHI DA NI KAINA SLIMZY DA HAZIKAR MARUBUCIYAR LITTAFAN HAUSA WADDA KUKASANTA TAURARUWARTA KE HASKAWA YANZUN HAKA A DUNIYAR LITTAFAI...KADA IM CIKAKU DA SURUTU ITACE FEEDHOM MARUBUCIYAR MATAR ABDALLAH DA RUGUNTSUMI DA WANAN LITTAFIN WANDA DUNIYAR WHATSAPP DA KEWAYE TAKE ALFAHARI DASHI KWADAYI...
WADANAN TAGWAYEN LITTAFAN BIYU ZASUZO MUKU AKAN FARASHI MAI RAHUSA 300 KACAL ZAKI MALLAKI LITTAFAN BIYU IDAN DAYA KIKESO AKAN 200 KACAL MAZA AMFARA BIYAN KUDI DAGA YAU 9/10/2020 KADA A BARKI A BAYA KI TUNTUBI WADANAN LAMBOBI BIYUN DAN KARIN BAYANI NA MARUBUTAN BIYU....SLIMZY CE DA FEEDHOM KUNDADE DA SANIN DADADAN LITTAFAN MARUBUTAN SIYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA...TAGWAYE BIYU 2020
07042277401
08036953516
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:47 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*34*
Bilal ne ke kiran nata a waya cikin sauri ta dau wayar ta dauka cikin wani irin yanayi murya a sanyaye,"hello Iqbal"
"Hello habeebty,gani a kofar gida mun iso"ya datse wayar,tabi wayar da kallo haka kawai ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba, ta dade tsaye sanan ta juya ta tsaya gaban dressing mirror tana kallon kanta,yau kadai tadan rame ta fada hoda ta dauka ta kara shafawa ta gyara fuskarta sosai ta dauki sirrin kwalliyarta, wato kwalli ta zizara a kyawawan idanuwanta wadanda suka kara kyau ita kanta kallon yadda idanuwanta sukai kyau takeyi,tabbas maman afee takwararta tayi gaskiya da tace sirrin kwalliyar mace shine kwalli ko baki kwalliya ba kika shafa kwalli a idonki zaki fito ras kamar yadda ake cewa idan babu gishiri a miya babu miya to haka kwalliya take tafiya da kwalli,babu mamaki abbahn afee kullim yake kara sonta....juyawa tayi ta bude drawer ta zari gyalenta baki ta rufe jikinta ta feshe jikinta da turare ta fito,yadda take tafiyar kadai zakasan jiddah batada karsashi,
"Saina dawo ummah,bilal ne yazo, Dan Allah idan bakon abbah ya fito ki sanarwa da abbah bukatar bilal nason ganin nasa inyaso inya bukaci shigowa sai inzo inji ko kunyi maganar"
Jinjina Mata kai ummah tayi Tana kallom jiddah cike da tausayawa "insha allahu zan sanar masa sai ki shigo da bilal din"
"Tou ummah sai na dawo"ta juya ta fice
Ummah ta kada kai "Allah sarki,jiddah tana bani tausayi Allah yayi miki zabin alheri ya cika miki burinki"ummah tace a fili,
Su abidah suka hada baki"Ameen"
A waje kuwa jiddah tun kafin ta karaso su zuhura suka taryeta dikda yaune rana ta farko da suka soma ganinta,cike da faraa ta rungumesu kamar tasan su "Antyn mu barka da fitowa tun tuni muke waje mun kosa ki fito muganki yaya bee kullum cikin kodaki yake"
Fadada faraarta tayi ta juya ga bilak cikin wasa tai masa wata yar harara mai cike da kissa da soyayya wadda saida yaji numfashinsa kamar zai dauke don ba karamin kyau tayi ba "wato zama kakeyi kana tsara kannena ko?gashi sunzo basuga hakan ba dan ni ban wani hadu ba"
"Injiwa anty?wallahi kin hadu kamar balarabiya,da ace da rana mukazo ma bazamu tafi ba sai munyi hoto dake"zuhur da rufaida suka hada baki,
Itadai jiddah kada kai kawai tayi cike da farin ciki sai lokacin ta dubi sashen da zainab ke tsaye gefen bilal na hagu ta kafeta da ido,zaro ido zainab tayi "ahhhhh mutuniyas afuwan ashe tare dake ake wayyooo my sweet aminiya zo muyi oyoyo mana"tana kokarin karasawa wajenta,
Juya baya zainab tayi cikin sigar wasa take daga hannu "ni kyaleni bayan kin mance dani kin shareni ni ai nayi fushi"
Murmushi jiddah tayi ta hade hannayenta "am soo sorry my dearest sister nayi laifi na tuba bari insa gwiwata a kasa"jiddah ta Shiga kokarin gurfanawa da sauri bilal ya dakatar da ita "ah ah ta hakura ai kanwata ce na ari bakinta naci mata albasa zo muje habeebty akwai maganar da zamuyi"
Kiftawa zee ido bilal yayi tai dariyar karfin hali "wato nasa masoyiyarka wahala ka maza kace ka amshi laifin hmmm laila majnun aje ayi soyayya "
Can gefe suka tsaya da Bilal ya tsareta da ido cikin wani yanayi mai cike da shaukin soyayya yake jifanta da wanan kallon,hakan yasa tadan zumburo baki cike da shagwaba kamar wata baby "iqbal...ni ka dainamun wanan kallon idan kanamun inajin wani abu fa?"
Kashe mata ido yayi "sure?kina loosing control ne?soyayya ce habeebty,...well amma yanayin naki gaba daya is not normal ba yadda kike kamar koda yaushe ba akwai wani abu ne?"
Girgiza masa kai tayi cike da sanyin jiki ta sakar masa murmushi"babu wani yanayi a tare dani sai yanayi na shaukin soyayya da kauna Iqbal....sai kuma zuciyata dake cike da mararin kewarka"
Dan zaro ido yayi "kewata ?kullum muna tare habeebty yau ne banzo da wuri ba sai yau,na sanar miki ina tare da abbah a company kuma shine muka tattauna akan maganar auren namu,shin kin sanarwa da abbah sakon zuwana yanzun?"
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da gyalenta "ehh tou bansamu ganin abbah ba yanzun haka yanada bako amma muna tsaye kamar naga wucewarsa ta kofar gidan mu ta baya nadai sanarwa ummah idn bakom ya fito ta fadawa abbah idan ka shirya sai in Shiga yanzun infada masa sai ayi maka iso"
"Owk...badamuwa is ok yanzun ki shiga tare dasu zuhura su gaida su ummah kafin mugama da abban ko?"
Jinjina masa kai tayi suka hada ido ya sakar mata murmushi,itama murmushin ta maida masa cike da soyayya saidai kasan zuciyarta cikin tsananin faduwar gaba take....
A cikin gida su zuhura suka gaida ummah cike da girmamawa ummah ta amsa tai musu maraba,abidah ta wuce dasu dakinsu,
Jiddah ce tsaye gaban mahaifiyarta tana kallonta cikin sanyin jiki "ummah kin sanarwa da abbah maganar zuwan bilal?yanaso ya shigo ne".
Idon ummah jajir kamar ta fashe da kuka tace "na sanar masa kije ki shigo dashi kinji Allah ya bada saa"
Cikin sanyin jiki jiddah ta amsa da "ameen ummah....ammm ummah ina ganin yanayinki ba kamar yadda ma fita na barki ba kodai dakwai wani abu ne?"
"Babukomi kada kidamu yi maza jeki shigo dashi kinbarosa tsaye bari in sanarwa da abban naki"ummah ta mike tana kokarin boye kwallar dake makale cikin idonta,
Batare da jiddah ta yadda ba ta juya gabanta na dukan uku uku hantar cikinta a kade take,to meke faruwa ummah ke cikin wanan yanayin?da alama akwai wani abu wanda ummah bataso jiddah tasani,...dakyar take daga kafarta ta fice,....
Bilal zaune kan dadduma a dakin abbah,tunda ya shiga ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa daga kai saboda tsananin kunya sai gumi ke karyo masa,bayan sun gaisa cikin mutuntawa da sakin fuska abbah ya tambayesa abinda aka fada masa ko hakan ne? na bukatar neman izini,
Cikin ladabi ya amsa da "ehh Abbah,dama daddy yace inzo in gaisheka sai in tambaya masa lokacin da zaizo kuyi magana shida yan uwansa"
"Masha Allah madalla,amm bilal ko?"
"Ehh abbah"bilal ya amsa kansa a kasa,
"Tou insha allahu zan sanarwa da jiddah lokacin da shi daddyn naka zaizo,dan yanada kyau kafin yazo nima inyi bincike akan ta bangaren naku tunda muba yara bane sanan ba budurwa bace da zaa tsaya bata lokaci"
"Ehh abbah"
"Tou madalla,babu wata matsala, Allah ya shige mana gaba ya tabbatar da alheri,insha allahu zakaji daga gareni Allah yayi albarka"
"Ameen abbah.. nagode sosai Allah ya kara girma"....bilal ya durkusa sosai yayiwa abbah godiya sanan ya fito,
A parlor yayiwa ummah sallama ya kwashi takalmansa a hannu kansa a kasa ya fice,....jiddah na zaune gefen ummah ta sunkuyar da kai "tashi ki bishi mana jiddah kin zauna"
Murmushin karfin hali kawai jiddah tayi zuciyarta keyi mata lugude kamar ana kada ganga,gumi ne ya karyo mata a goshi cikin jikinta kuwa kamar an hura mata wuta,zucuyarta cike da tsoro haka take biye dashi tana daga kafa da kyar har suka fice,
"Ya naganki cikin wanan yanayin habeebty kinga yadda kike gumi kamar kece kika gana da abbah?bake ya dace aga kina gumi ba nine ya dace"
"Umhmm... Iqbal kenan ai dole inyi fargaba bakasan yadda zuciyata take a cikin rudani ba"
Bata fuska bilal yayi yana kallonta,shiru itama shiru tayi cannn ya nisa "meyasa zuciyarki ke cikin rudani habeebty ki fadamun ko akwai wani abu ne da bakiso insani?"
"Ah ah...ko kadan kasan shi aure yadda yake hankalina bazai taba kwanciya ba sai mun mallaki juna a matsayin mata da miji"ta sakar masa murmushin karfin hali,
"Tou ki kwantar da hankalinki akwai alamun nasara"cikin furgici ta dago kyawawan idanuwanta da ta fiddosu waje tace "dagaske abbah ya amince zaka aureni?"cikin subutar baki tayi maganar,
Gabansa yadan fadi "ah ah habeebty ya kike wanan maganar da be amince ki aureni bane?kifadamun ko kina boyemun wani abu ne"
Take ta saita natsuwarta ta shiga girgiza kai "ah ah Iqbal ina cikin farim ciki ne yasa kaji nace hakan amma abbah na beda matsala"
Ajiyar zuciya bilal yayi yana kallon kwayar idonta har yanzun gabansa bedaina faduwa ba sai yaja numfashi ya furzar da isa,sanan ya nisa yayi mata bayananin yadda sukai,
Lumshe ido jiddah tayi,cikin rashin kwarin jiki can kasan zuciyarta,a zahiri kuwa bayyana tsantsar farin cikinta tayi tana kokarin mantar da bilal subutar bakin da taso tayi tana lura da canjin yanayinsa,
Take ta shiga zabga masa shagwabar da bata taba sanin ta iyata ba"iqbal.... nidai nidai ka sanar dani irin tanadin soyayya da kulawar da kai mun a gidan aure na"ta turo baki,
Dariya ta bashi yakai hannu zai buge bakin cikin sigar wasa da sauri ta kauce tana dariya,shima dariyar yake.....
Daga nesa yake kallonsu,idanuwansa suka cicciko da hawaye,ga wani zazzabi dayake ji da ciwon kai,inama ace dashi ne jiddah take wasa take raha,yau matarsa da amininsa suke soyayya a gabansa matarsa da yakeso fiye da komi a rayuwa,itama tasoshi amma yanzun ta juya masa baya gabaki daya,
Hasken motarsa ne ya haske musu ido dan basusan da zuwansa ba shigarsu gida ya iso yayi parkinga,da sauri jiddah tasa hannu ta rufe idonta yadda ya haske mata ido yaja motarsa yayi kwana yayi gaba,
Tsaki jiddah taja tabi motar da harara cike da takaici,bilal kuwa cije lebensa yayi ya dubeta "sorry my luv....am kira mun su zuhura mu wuce dare yayi gashi sunce saina biya dasu sunsha ice cream inaga gida zamuje kawai"
Dan bata fuska tayi "ah ah banyarda ba gaskiya ka kaisu ka siya musu kodan bakuwa gata nan itama zataji dadin zaga garin koh nidai ka kaisu kaji"ta marairaice tana Tura baki,
"Your wish is my command my baby jeki kiramun su zankaisu"
Farrr tayi da ido "nagode Iqbal"ta juya ta tafi kiransu,tare suka fito har wajen mota ta rakosu sun dade tsaye da bilal suna zuba soyayya kamar bazasu rabu ba suka wuce ...
*******
Daddyn Bilal da momy ne zaune suna kallon labaran karfe tara "am nace kinga yaran nan har yanzun basu dawo ba"
",Dik inda suke nasan suna hanya ai yanzun zakaga sun dawo,yau yayansu yana cike da dokin maganar turawa gidansu jiddah ai"
Murmushi daddy yayi "aini ina jinjina wanan lamari na auren bilal da wanan yarinyar saboda kinsan mutane yanzun zaace yayi auren cin amana,banida yadda zanyi ne ma yasa zan nema masa auren nan saboda yanason yarinyar amma bansan da wani ido zan kalli abban Abdallah ba wallahi"
Ajiyar zucuya momy taja "tou ai shi ya saketa ko?kuma ai yanzun bilal nafadamun wai ya dawo da nufin dawo da ita yarinyar taki sai bilal din, bamuda yadda zamuyi da kaddara sai hakuri gashi dalilin hakan zumuncin ya rushe ai"
Shiru daddy yayi yana tunani kafin yaja numfashi yace "amm wancen company din dana bawa bilal MD a ciki,akwai gurbin Abdallah a wanan wajen saboda yanzun haka Abdallah bashida aikinyi kuma tin ana ginin wajen inada niyyar hadasu wajen aiki daya,inaso Abdallah ya rike mukamin director a wajen hajiya"daddy ya karasa maganar yana kallon momy ta cikin farin gilashinsa,
Tana kokarin bashi amsa zuhura ta fado parlorn da sallama "assalamu alaikum...momy daddy mundawo nagaji munsha yawo yau da yaayah bee wallahi"
Dadi ne ya kama momy "kai masha allahu ina autata"
"Kai momy wato ta autarki kike nida nafara shigowa ma bakibi ta kaina ko momy...ainima ga daddyna nan"
"Oyoyo momy"
rufaida ta shigo hannunta rike da ledoji bilal da zainab suna biye da ita a baya,
"Oyoyo auta...andawo?to a wuce daki ayi sallar ishai ayi wanka ayi shirin kwanciya"
"Tou momy"yan matan suka shige ciki....
Bilal kuwa gurfanawa yayi gaban daddynsa ya sanar masa da yadda sukai da abban jiddah,
"Babu laifi hakan yanada kyau nima nasa ayi binciken ai",bilal ya jinjina kai ya mike yana kokarin tafiya,
"Kai bilal....a company din A&B ventures din nan akwai office din Abdallah shine a matsayin director a wajen gobe idan Allah ya kaimu mun hadu da mahaifinsa zanbasa takadda ya kaiwa Abdallah sanan ya turomim shi daga baya"
Momy kallom yanayin na bilal takeyi tanaso ta gano wani abu amma takasa sanin waye dan nata yasa ta amshi zancen "Allah yayi muku albarka bilal....sanan babu gaba kowa da wajen aikinsa inaso a zauna lafiya maida alheri ga sharri ba illaneba"
Kada kai bilal kawai yayi be ko ce komi ba yayi gaba abinsa...momy d daddy suka hada ido sukai murmushi....
*******
Dakyar Abdallah ya iya bude ido da asuba saboda yadda idanuwansa sukayi masa nauyi sosai,jikinsa ya zuge da zafi tun cikin dare yake cikin tsananin zazzabi da ciwon kai,
Dakyar ya sakko yayi alwala ya shimfida dadduma,a zaune yayi sallar saboda yadda kansa yake tsananin sara masa anan ya kwanta hannunsa rike da kansa hawaye na gangarowa ta gefen idonsa da sukayi jajir....
Wayarsa yake lalube a gefensa inda yayi sallah cikin yanayi na ciwo yake laluben number abbansa,
"Abbah barka da asuba"yayi maganar cikin wata iriyar murya,
Da abbah ya furgita daga inda yake zaune kan dadduma ummah a gefensa sun idar da sallah "lafiya kuwa Abdallah?"..
Zaro ido ummah tayi tana kallon abban Abdallah fuskarta dauke da damuwa da tambaya,
"Abbah...banida lafiya..kayi kokari kazo gida kaida ummah ina gab da komawa ga mahalicci na"yayi maganar cikin yanayi na ciwo da sarkewar harshe,
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...meyake damunka ne?...kai Abdallah ka kwantar da hankalinka ganinan zuwa da family doctor insha allahu yanzun "
Kasa magana Abdallah yayi sai kashe wayar da yayi ya murgina a kasa,
Daga labulen dakin tayi tana sanye da kayan bacci idanuwanta sun kankance daga gani Kuka tacu,ganin yanayinsa yasa Ramlah rudewa ta karaso ta tallabosa "dear...meyake damunka?kafadamun dan allah wallahi ina tsananin sonka,nasan damuwar jiddah ce kayi hakuri ka zauna dani na isheka rayuwa"tana hawaye take maganar,
Dakyar ya iya bude idonsa yayi mata wani kallo kawai ya rufe idonsa batare da yace mata komi ba,
Tana tallabe dashi cikin minti talatin taji karar bubbuga kofa da sauri ta dubesa "jeki budewa abbah na da ummah kofa"
Da sauri ta mike ta nifi daki ta sako hijab ta fito taje ta bude kofar,
Abbah ne sanye da jallabiya da makullin mota a hannunsa shida ummah,zubewa Ramlah tayi a kasa ta shiga gaida abbah cike da ladabi,dakyar ya amsa mata cikin halin ko in kula yayi ciki yana fadin "ina Abdallah din yake?"
"Yana dakinsa abbah"beko kalli ramlah ba ya bude labulen dakin Abdallah ya rukosa,
"Ga doctor nan zuwa yanzun insha allahu zaizo ya duba ka"
Kuka ummah ta fashe dashi tasa hannu ta tabo gefen wuyansa zafin da taji ne ya furgita ta ta fashe da kuka tana goge hawaye,
"Wallahi alhaji damuwar jiddah ce ta haifar masa da rashin lafiya kuma kasan condition dinsa dan allah kayi wani abu Alhaji kada mu rasa yaron nan wallahi ya horu yana cikin wani hali"
Daura fuska abbah yayi "habiba ki kiyayeni babu abinda zanyi yanzun ni ta lafiyarsa nakeyi idan ya warke sai ya cigaba da neman auren yanzun bazan iya ba gaskiya"
Ummah yadda taga abbah ya fututtuke yanata fada yasa ta tsuke bakinta, kiran doctor ne ya shigo wayar abbah yana dubawa yace "yauwa inaga ga likitan nan yazo bari inshigo dashi"ya mike yayi waje yana kokarin daukar waya,
A parlor yaga Ramlah tsaye tabi abbah da kallo da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,tana ganin abbah gabanta yake faduwa sosai yake mata kwarjini....hmmmm tagode Allah ma da abbah yaki amincewa da yaje bikon jiddah,dan dik ranar da jiddah ta shigo gidan nan kashinta ya bushe tanaga kishi zai iya halakata,
Tana nan tana tunani abbah suka shigo da likita tabi bayansu cikin sanda kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,daga bakin kofa ta tsaya suna hada ido da ummah tai mata wani mugun kallo a ran ummah tace lallai wanan yarinyar batada kunya,
Duddubasa likita yayi cikin mintuna yayi masa allurar zazzabi nan da nan bacci ya daukesa ya daura masa drip sanan ya gwada masa BP sosai jininsa ya hau ya kuma dibi jininsa da niyyar zuwa yin test....
******
Da yamma abban Abdallah ya fito office motar alhaji maska ta tsaya mahaifin bilal,abban na ganin motar ya fadada faraatsa shima daddyn bilal faraar yake ya mika masa hannu abbah yace "kasan dama dazun nake cewa ya kamata mu hadu dan wallahi mun kwana biyu"..
"Ehh wallahi,ya iyalin ya hajiya habiba"daddy ya tambaya,
"Lafiya lau danka ne Abdallah yake gida babu lafiya amma jikin nasa da sauki ya warware"
"Kai?aiko banji ba"
"Muma yau mukaji amma zazzabi ne yaji sauki yasu zuhura"
"Lafiya lau....kuma kasan musabbabin zuwan nawa nan akan Abdallah din ne?"
"Tohhj meyake faruwa kuma?wani abu ya sake faruwa ko?"
Kada kai daddy yayi "ko kadan...kasan munada niyyar hadasu shida bilal wajen aiki daya wancen company din nawa,to ya kammalu sai kuma naji labarin ashe an damatar da Abdallah a aiki to ga takardar aikinsa na office already komi an kammala masa a matsayin director na A&B ventures"
Shiru abbah yayi yana nazari,bazai iyawa alhaji maska musu ba amma dai zai amsa masa kafin ya hadu da Abdallah "tou allah ya saka da alheri yanzun idan yaji sauki zanbashi takardar zan kuma turosa wajenka"
Jinjina kai daddy yayi cike da farin ciki kamar ya sanarwa da abbah labarin auren bilal sai kuma ya dakata tunda mahaifin yarinyar yace zaiyi bincike...nan suka rabu kowa ya shiga motarsa...
*****
Tun isowar gwaggo gidan su jiddah,jikin jiddah yake a sanyaye wani irin yanayi take jin kanta mai kama da mutuwar jiki,
Shigowa abban jiddah yayi dakin da suke zazzaune ya dubi gwaggo "hajajju amma bazaki tafi mana da nafeesa ba ko?"
"Ai ba tare mukazo ba dan haka tafiyata daban tata daban"
"Tou ba laifi"
"Amm gwaggon yara zaki iya tahowa da jiddah dakina keda ummanta inada magana daku dan sirikinta yazo tafiya da ita yanzun haka"
Kauda kai ummah tayi gefe,bata bari sun hada ido da jiddah ba,
Tambayar kanta jiddah ta shigayi"sirikinta?yazo?waye sirikin nata?"nan da nan ta rude kwakwalwar kanta ta hargitse faduwar gabanta ta tsananta...to kodai abban bilal ne yazo da mutanensa neman aure yasa gwaggo dama tazo?"
Katse mata tunani yayi abbah "taso muje dakina tunanin me kikeyi haka?"
Dakyat ta mike tsaye jikinta na tsuma kamar an zuba mata ruwan sanyi....kauda kai ummah tayi tai gaba ita da gwaggo jiddah tabi bayansu....
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:48 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
*35*
Zama sukayi duka a dakin abbah suna jiran shigowar jiddah,sai gata ta shigo dakyar ta tsaya daga kofar dakin tana bin ko wannensu da kallo cike da tsoro da fargaba,gefe abbah ya nuna mata "zauna uwata"
Ba musu ta zauna dakyar takr sauke numfashi gabanta na cigaba da bugawa dik jikinta rawa yakeyi "uwata"abbah ya kira sunan jiddah,
A sanyaye tace "naam Abbah na"
"Ga gwaggonki tazo,jiya daddare nayi mata Kiran gaggawa shine dalilin zuwan nata nasan dukkanku bakusan da zuwanta ba sai ummanku,da kuka ganta ma bakusan dalilin zuwanta ba, tou nakirata ne tayi miki rakiya zuwa dakin mijinki"
Da sauri jiddah ta kalli abbah tana zaro ido cike da tashin hankali ,ta kasa magana hakan yasa ya cigaba da magana"bawani abu bane yasa na daura miki aure batare da saninki ba sai dan nasan nina haifeki kuma inada hurumim da zan zaba miki mijin aure kuma ki zauna kiyi biyayya,sakamakon biyayyar da zakiyi allah kema zai share miki hawaye"
Koda abbah ke maganar nan jiddah jiri ke dibarta tamkat a wata duniya haka take jinta,tuni kuma hawaye ya wanke mata fuska batare da tace komi ba,
"Batare da bata lokaci ba uwata,abinda zance miki shine dik gidan da kika tsinci kanki a matsayin matar aure to ki tsaida hankalinki kiyi biyayya darajar ni mahaifinki da na yanke hukunci batare da shawararki ba jiddah nayi hakan ne dan rufin asirinki duniya da lahira,kuma insha allahu bazaki tabe ba,...."
Abbah ya dubi ummah da tausayin jiddah yasa take kuka tana share hawaye "zainab ga yarki nan kiyi mata nasiha keda gwaggo mai daukansu yana waje sirikin nata banaso a bata masa lokaci"
Cikin kuka ummah tacewa jiddah "kiyi hakuri kinji jiddah?dik abinda zance mahaifinki ya rigani cewa kuma ina sane da wanan hukunci daya yanke dan haka kiyi biyayya allah yayi miki albarka"ummah na gama fadin haka ta mike ta fice a dakin,
Ita kanta gwaggo saida jikinta yayi sanyi taji tamkar ta zubar da hawaye,dauriya kawai tayi abbah ne yayi gyaran murya "tashi kuje gwaggonsu gobe zaa kawo mata kayanta inaso yau ta kwana a dakin mijinta"
Mikewa gwaggo tayi ta mikawa jiddah hannu ta dagota dakyar kamar mutum mutumi tana sanye da hijab ta tura kanta ciki tana hawaye har sun fito abbah yace "bani wayarki"
Ba musu ta mika masa wayar suka tsaya,bude wayar yayi ya cire sim dinta ya musanya da wani ya mika mata,kasa karba tayi sai gwaggo ce kawai ta amsa suka fito....
Wata mota ce a tsaye suka bude baya suka shiga,jiddah ko kallon wanda ke cikin motar batayi ba ta fada jikin gwaggo ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.....
********
Abdallah yadan samu karfi a jikinsa yana jingine da kujera a parlor drip din da akasa masa ya kare faten dankalin turawa su rumaisa suka kawo masa suna gefensa an zuba masa a faranti ya tasa faratin yayi shiru.... Abdallah tunanin yadda zaiga jiddah yakeyi idosa yayi kwalkwal da hawaye ya dubi ummah kamar karamin yaro "ummah...ummah dan allah aje a fadawa jiddah zan mutu dan allah ta amince dani ta dawo gareni in mutu a hannunta,ummah kinga yau banje naganta ba banga lafiyarta ba"
Cike da damuwa ummah ke kallon Abdallah ga tausayinsa da take tsananin ji "kayi hakuri Abdallah zani gidan gobe idan Allah ya kaimu inkara gwada saata ko allah zaisa mu dace"
Ramlah dake gefe zuciyarta tukuki take ji take kamar ta shake ummah, Abdallah na zaune babu damar yiwa ummah rashin kunya,cike da kosawa da takaici ramlah tace "dear kaci abincin mana dubi yadda yayi sanyi ya fara bushewa ko bazaka iyaci bane inyi maka farfesu?akwai saurar hanta a fridge"
Harara ummah ta watsa mata,itama ta fakaici idon Abdallah ta rama,kwafa ummah tayi "Abdallah na ci abincin mana kaji?dubi yadda ka rame ka lalace umm?kaga yadda fuskarka ta fada kuwa?"
Abbah ne ya turo kofar hade da sallama ya shigo
Da sauri ramlah cike da iyayi tace "barka da zuwa abbah,sannu da zuwa bari akawo ruwa da lemo"bata jira cewarsa ba ta mike tayi kitchen,
"Abdallah jikin ne har yanzun?gashi abincin anzuba maka ma bakaci ba ka rike kayi shiru Abdallah"cewar abbah yana kokarin shigowa ciki sosai,
Turo kofar akayi aka shigo gwaggo ce a gaba rike da hannun jiddah suka shigo "assalamu alaikum"gwaggo tace suna kokarin shigowa,
Mikewa afee tayi ta zaro ido hade da rufe Baki cike da mamaki ta kwalla kara"Anty jiddah.... Dan Allah anty jiddah ce?"
Shiko Abdallah kallon gwaggo kawai yakeyi ya kasa ganeta yana kokarin recalling fuskar take....da ta fado masa tabbas wanan matar bazai mantata ba itace ta kawo masa jiddah gidansa Tana rike da hannunta,
Ummah cikin mamaki dai dakyar tace "barkanku dai barkanku sannunku da zuwa"tana bin gwaggo da kallon rashin sani,
Murmushi abbah yayi "basu ganeki bane baiwar allah"
"Allah sarki"
Bugun zuciyar jiddah ne ya tsananta lokacin da gwaggo ta gyara mata hijabi ta fito da fuskarta.....fuskar jiddah tayi jajir idanuwanta sun kumbura,
Ramlah ta fito kitchen da tray da lemo da cups abinda tagani yasa faratin hannunta faduwa,da sauri tasa hannu ta murza idanuwanta ta kara budesu tabbas ko shakka babu jiddah ce ta dawo gidan Abdallah....jiri ne ya dibi ramlah ta soma ganin biyu biyu da sauri ta dafe kujera kirjinta na sauka sama da kasa,
Abdallah ko kifta idonsa bayayi kallon jiddah yakeyi tamkar matacce kwayar idanuwansa sun tsaya waje daya,ummah tasa hannu wajen idonsa tayi waving amma Abdallah ko kifta ido bayayi,
Faraa ce ta cika ummah ta mike ta daga hannunta sama"Alhamdulillahi.... alhamdulillahi"
"Barkanku da zuwa ku shiga daga ciki"
Yar dariya gwaggo tayi "tou ai bamusan wanne dakin zaa shiga da ita ba don dai da nasan ga dakinta nan"ta nuna dakin jiddah nada wanda ya kasance dakin ramlah yanzun
Abbah ne ya katsesu "inaga ga dakin da zaki shigar da ita nan,dan nan ne zai zama dakinta dakin Abdallah gashi nan"gwaggo bata tsaya wata magana ba ta nufu dakin Abdallah da ita,
Murmushin manya abbah yayi ya dubi Abdallah "tou patient sai a warke dan ga doctor ta iso ko?"
Meenah cikin dariya tace "original doctor kuwa abbah"
Cikin tsananin farin ciki ummah ta zamo daga kujera a gaban abbah"mungode Allah ya kara girma lallai ka cika uba na gari"
Dakyar ramlah tayi sumi sumi ta shige dakinta jiri na dibarta tana shiga ta fada kan gado ta dafe kanta hade da rufe idanuwanta "Allah ka farkar dani daga wanan mummunan mafarki.... Allah kada ka tozartani cikin wanan gida nashiga uku"ta furta muryarta na rawa gabanta na cigaba da faduwa....
Abdallah kuwa ganin yabar kallon jiddah yasa ya lumshe ido "ummah kingani saboda banganta ba yasa takemun gizo yanzun haka nagama ganinta a gabana,da alama kuka tayi"kamar wani zautacce haka Abdallah ke magana,
Ummah ta gyara zama "Abdallah jiddah ce ta dawo gidanka....Abbanka ne yaje ya amso maka aurenta ka gode masa "
Gwaggo ce ta fito "tou nidai zan koma tunda alhaji kace ga driver nan waje yana jirana banaso ayi isha'i ina gidan nan... Allah ya bada zaman lafiya"
Ummah da abbah tare suka mike suka fita rakiyar gwaggo,
Lumshe ido Abdallah yayi saiga hawaye na bin idanuwansa, tabbas bashida masoyin daya wuce mahaifinsa a wanan duniyar....take yaji haushin kansa tunawa da bijire masa da yayi na sakin jiddah, gashi kuma da kansa yaje ya dawo masa da ita lallai wanda ya rasa uba yayi kuka,
Shasshekar kukan jiddah kawai sukeji a parlorn,hakan yasa Abdallah ya kwantar da kai yana sauraren sautin kukanta zucuyarsa nayi masa zafi,saidai yana cikin tsananin faduwar gaba dan yasan yanada aiki babba a gabansa akan shawo kan jiddah.....wata zuciyar ta fada masa samun jiddah shine mai wahala,shawo kanta abu ne mai saukin gaske....jiyo sautin muryoyin su ummah yasa ya bude idanuwansa sunyi jajir gumi ne kawai yake karyo masa,
"Tou Abdallah ga jiddah nan nayi ceto na karbo maka ita,dikda nasan mahaifinta yana tsananin kunyata yasa ya amince ya daura aurenka da yarsa batare da saninta ba,a sallar magriba aka daura aurenku,nasan kukan da jiddah takeyi,aikin gabanka shine ka shawo kan matarka sanan kayi kokarin yin adalci a tsakaninsu"jinjina ma abbah Kai yayi yana kallonsa cike da kauna tsananin al'ajabi da mamaki yasa Abdallah kasa cewa abbah komi,
"Kai afnan ku tashi mutafi gida"
Cike da d'oki suka mike "abbah gobe zamu dawo amma ko?"
Karkada kai abbah yayi cike da zolaya "me zaku dawo yi?ai ba abinda zakuzo kuyi mutafi"
"Kai abbah zamuzo duba jikin yaya"
Yar dariya ummah tayi "muje wasa abbah yake zaku dawo"
"Abdallah Allah ya sauwake ka kula da kanka"daga kai yayi dakyar ya daga musu hannu suka tafi,
Ramlah ce ta fito daga daki tanajin karar rufe kofarsu ta tsaya tsaye ta gefensa ,hawaye ne ya shiga zarya a idonta...daga ido yayi yana kallonta kawai batare da yace komiba,
Cikin kuka tace "yanzun Abdallah meye na rageka dashi da kadawo da matarka?kadawo da itane aimun cin zarafi?dama nasan ai baka sona"
Bece mata komi ba ya mike yana ganin jiri ya nufi dakin sa gabansa na cigaba da faduwa,
Cije yatsa Ramlah tayi"wato dakin da take ya shiga?ohhh daga zuwanta ta amshi girki ne koko zai shiga ne ya lallatseta su tauye mata hakki?"...itada take tsananin bukatarsa yanzun haka?.... zuciyarta ke hura mata wuta da tabi bayansa zuwa dakin...amma ta shiga tayi me ta hada ido da jiddah?lallai ta gaza tunda jiddah ta iya dawowa gidan Abdallah suka hada miji lallai nasamu failure,....wani abu ne ya taso mata ya tokare mata makogwaro,
Gefen gado Abdallah ya zauna tana kwance ta dukunkune da hijabi,kamshin turarensa ne ya sanar mata da shigowarsa,
Cikin wata irin murya mai cuke da tsiwa da takaici tace "ka fice mun daga dakin nan idam baka fita ba ni zan fita bana bukatarka a kusa dani....bana bukatar shakar kamshin jikinka"
Murmushi yayi mai sauti,cikin rashin karfin jiki ya gyara zama yace cikin sarkewar murya "ni kuma ina bukatarki a kusa dani ina bukatar in shaki kamshin jikinki ina bukatar dumin jikinki dan sanyi nakeji ki rungumeni"yayi maganar cike da tsokana saidai be nuna hakan a fuskarsa ba,
Cikin tsiwa da masifa ta mike zaune tana kallon sa cike da tsana take jifansa da wani irin kallo,wanda shi kansa saida tsoro ya kamasa fargabar furucin da zai fito daga bakinta yakeyi...yana binta da wani marayan kallo,jikinta har rawa yake bakinta na karkarwa....
*********
Jigum jigum sukayi a daki da aysha da abidah,nafeesa na can gefen gado tana rike da wayarta,
Abida ta kasa hakuri kamar zatai kuka ta dubi gwaggo "yanzun gwaggo shikenan Ablah ta tafi ta koma gidan yaya Abdallah?shine baa kiramu mun raka ta ba?"
Aysha ta karbe zancen "Ablah ta bani tausayi,nasan tana can tana kuka yanzun haka wallahi wani iri nakeji meyasa akatafi da ita batare da mu ba"
Gwaggo ta girgiza kai tausayinsu ya kamata "kuyi hakuri yan biyu gobe idan Allah ya kaimu sai kuje kuganta ko?"
Hawaye ne ya sulalo a idon abidah...take bilal ya fado mata gabanta ya yanke ya fadi,allahu akhbar yaya bilal...meye kenan zai faru dashi?gashi lokacin zuwansa ya kusa,hmmmm banajin zan iya fita in fada masa wanan mugun labarin.....
Nafeesa daga gefe tace cikin sanyin jiki "lokacin zuwan yaya bilal ya kusa yanzun ya kenan?waye zai sanar masa da halin da ake ciki?"
Aysha tace "tabdijan...ai saidai ku dan ni inada imani dan mara imani ne kawai zai iya sanar masa da wanan mugun labarin....
********
T shirt ce fara a jikin bilal da bakin wando ya shigo rike da wayarsa da tun idar da sallarsa yake kiran wayar ta a kashe,tambayar kansa yakeyi ko menene yasamu wayarta oho?
Momy ce ta shigo daga kitchen rike da flask zainab na biye da ita "an fito sai ina kuma baaci abinci ba?"
"Momy bazan iyacin abincin nan ba sai nadawo wajen surukarki dan wallahi na matsu inganta,nakira wayarta a kashe da yamman nan amma da safe dai munyi magana a waya ina wajen aiki"
Ajiye kular momy tayi akan table tana murmushi "tou rasa kunya beran tanka?ohh ni yasu yaron nan soyayya ta rufe masa ido ko kunyata bayayi to a dawo lafiya abincin ka na nan yana jiranka dan dambun couscous akayi"
Jinjina kai yayi yana yar dariya "momy kice mutumina akai ai yau zanci in koshi in rage da safe a dumamamun,yau ba abinda zai hanani cin abincin nan"
Momy ta karasa maganar da "saidai ikon allah"
Yana kokarin tafiya zainab tace "yaya bee zan rakaka inaso muyi sallama da jiddah saboda gobe nakeso intafi katsina ankoma makaranta"
"Gobe kuma?baxaki tafi gobe ba sai jibi....jeki dauko gyale kisameni a mota"yayi gaba "momy saina dawo"
"Tou a dawo lafiya"
"Ameen momy"
*****
"Amma abban Abdallah kasan cewa wai yaron nan bilal dama takarar aure sukeyi da Abdallah?koda ta gama iddah ai cewa yayi zai aureta"
Shiru abbahn Abdallah yayi yana sauraren ummah "tou amma ni ai bansaniba,...koda yake alhaji maska jiya yake cemun akwai aure da zamuje nemawa bilal ashe auren jiddah ne?"
Dafe kai abbah yayi "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun... wallahi da nasan jiddah ce da dole Abdallah ya sadaukarwa bilal da ita"
"Haba Alhaji ya zakace haka?mutum da matarsa kuma ace an amshe anbawa wani can daban ah ah ai bilal din Allah zai bashi wata"
Cike da damuwa abbah ya dubi ummah "aiko habiba zan samu alhaji maska,zanyiwa bilal huce haushi cikin daya daga cikin yaran nan matukar yanaso kodan indawo da zumuncin dake tsakanin mu kamar yadda yake kokarin tallafawa Abdallah da aikinyi"
Zaro ido ummah tayi "alhaji kada kayi wanan gangancin dan memakon ka gyara zumunci batawa zakayi"
Daga mata hannu abbah yayi ya shiga kaiwa da komowa cikin dakin.......
RAMIN MUGUNTA...SLIMZY✍🏼
RAMUWAR GAYYA..FEEDHOM 💥
TAGWAYEN LITTAFAI BIYU AKAN 300 KACAL ...NEMI SLIMZY TA WANAN NUMBER 07042277401
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:48 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MAI NEMAN AFUWA NA JINA SHIRU KWANA BIYU HAKAN YA FARU NE SANADIN CIWON IDO DANAKE FAMA DASHI KWANA BIYU AMMA INSHA ALLAHU ZAKUJINI KUYI HAKURI DANI KUBAR KORAFI......👏🏼
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
*37*
Komawa jiddah tayi ta kwanta ganin ramlah ta fita da alamar akwai abinda take boyewa,tunani ne cunkushe zuciyar jiddah....lallai ma Ramlah duniya kenan babu gaskiya kishi takeyi da ita ko me?idan kishi takeyi da ita tabbas ta wahala,ashe babu dadi ita ta aure mata miji a matsayinta na aminiyarta yanzun har zataji zafin dawowarta gidan kenan?idan haka ne kuwa dik yadda takejin zafin abinda Abdallah yayi mata da tsanarsa da takeji zata danne kodan tayi *RAMUWAR GAYYA*(sabon littafin feedhom)....tunda ai *RAMIN MUGUNTA*(littafin mai cike da sarkakiya na slimzy)ta d'ana mata dan tabar gidan.....lamo jiddah tayi cike da tunani kala kala taji horn din Abdallah,ta dubi agogo karfe bakwai da rabi na safe tayi murmushin mugunta...
*******
Kwance bilal yake ya tsurawa ceiling din dakin ido tamkar mutumin daya samu ciwon barin jiki cikin kwana daya kacal fuskarsa ta rame sosai ya kara fari....lumshe ido yayi ya bude jiddah ce ta fado masa sai hawaye masu zafi suka shiga zarya a idanuwansa gefe da gefe suke gangarowa....a tare momy da daddy suka shigo dakin ko wanne fuskarsa ba walwala haka suka karaso suka tsaitsaya a gefen gadon,
Daddy ne yayi gyaran murya "yadai bilal....katashi lafiya?ya jikin how are you feeling now?"
Kallon daddy yayi ya girgiza kai"am ok"kawai yace a takaice ya rufe idanuwansa rufffff,kallon juna sukai shida momyn "my boy ka bude idonka ka kallemu mana mune fa iyayenka"
Girgiza kai ya sakeyi"bana son ganin kowa a kusa dani ina bukatar kad'aici momy zuciyata cike take da ciwuwwuka kala kala wanda inajin hakan a jikina tamkar bazan rayu ba"dakyar yake fidda maganar,take tari ya sargafe shi nan da nan momy ta karasa ta tallabosa "sannu my boy....kayi hakuri kadaina wadanan maganganun kaji?dama allah be kaddari cewar jiddah zata kasance matarka ba kaji?"....bude idanuwansa yayi yana kallon momy wasu hawaye ne suke kara bulbulowa a idanuwansa,
"Tabbas nayiwa Allah laifi dolene ya hukuntani ta wanan hanyar, ta hanyar hanani auren jiddah....amma ina mai tabbatar muku bazan taba daina sonta ba saboda da soyayyarta na rayu da ita na ginu kuma d soyayyarta zan mutu momy da daddy"
Kada kai daddy yayi "wace irin magana kakeyi haka bilal kamar wadda baiyi imani da kaddara ba?kasan cikar imanin mutum shine yayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau"
Murmushi bilal ya sakeyi mai ciwo"tabbas tawa kaddarar itace soyayyar matar aminina a da"
Ajiyar zucuya daddy ya sauke"har yanzun Abdallah amininka ne kuma kana kaunarsa kuma harabada bazaa taba daina kiranku da aminan juna ba dan haka dukkanku allah ne ya jeho kaddara da shedan a cikinku kuma Dole kuyi hakuri ku rungumi kaddara kudawo ku kasance waje daya"
Momy ranta ne ya baci da kalaman daddy "kai alhaji kasan abinda kake fada kuwa?mutanen da basusan halarci ba?"
"Sunsan halarci tunda har yanzun ina tarayya da mahaifim yaron kuma shi yanada yakinin cewar yaronshi ba haka kawai ya aikata hakan ba,tafaru ne ta sanadin shedancin mace wadda yarinyar har yanzun tana gidan a matsayin matar Abdallah,yafiso Abdallah ya gano abinda Ramlah tayi da kansa yayi mata hukunci baa zaunar dashi a fada masa ba"
Shiru momy tayi batare da ta kara cewa komiba,bilal kuwa faduwar gabans ce ta tsananta....
*******
Tunda ya shigo dakinta tare da gwaggo tasan zuwa yayi ya dauko gwaggonsa kanwar abbansa da sassafen nan ,
Tsugunnawa jiddah tayi gaban gwaggo ta sadda kanta kasa tana sauraren nasihar da takeyi musu itada Abdallah "jiddah keba yarinya bace karama sanan na tabbatar dik abubuwan nan da kikeyi ba kinayinsu bane don baki son Abdallah ba kinayi ne dan ki kwatarwa kanki yanci a wajensa a karo na biyu sanan kinayi ne don zafi da radadin abubuwan da yayi miki, tabbas Abdallah yanada laifi amma cikin kashi dari kinada arbain da biyar"kallon gwaggo tayi ta sadda kanta kasa,
Jimm gwaggo tayi sanan ta dubi abdallah "bamu waje inada magana da yata ita kadai"..
"Tou"ya mike yana satar kallom jiddah dake gurfane a gaban gwaggo... murmushi gwaggo tayi ganin irin kallon da Abdallah keyiwa jiddah,tausayi ma Abdallah ke bata dan dik ya fita hayyacinsa ya susuce...
Turo musu kofar yayi ya fice,
A daki ya samu ramlah ta fito wanka Tana daure da milk colour na towel,tana goge jikinta,
"Barkanki da tashi, ya kika kwana?"yace muryarsa a darsashe ya zuba Mata ido yanayi mata wani irin kallo wanda yasa tadan tsargu,cikin in ina tace "barkanka.. ya ka tashi?ya kwanan amarci da soyayya"
Murmushin gefen fuska yayi ya juya kamar zai fita ya juyo"amarci alhamdulillahi...soyayya kuwa ana kanyinta ma"
Jinjina kai tayi "ai Naga amaryar nan da zafinta ta dawo"
"Amaryata kuma uwargida na at the same time har yanzun uwar gida ce,wani dan sabani ne ya fiddata wanda nine silar hakan....ammm dik ba wanan ba,ki soya mana dankali da kwai ki hada mana ruwan zafi bata dan jin dadi ne"
Ficewa yayi beko jira amsar da zata bashi ba,bin bayansa tayi da kallo lallai ma wanan Abdallah yaci uwar rainin wayau wato matarsa ta dawo yanzun nice zan zama boyi boyi mai girkin abinci?...
Kofar dakin ya tura ya tsaya yana kallon yadda jidda ke sharbar kuka tana sauraren gwaggo....gwaggo ce ta juyo"meye ya shigo da kai bangama ba?"
"Yi hakuri gwaggo bari in fita"
"Dakata"gwaggo ta tsaidashi,jimmm kadan tace "ya dace bayan kwana uku ka raba musu kwana saboda a cigaba da rayuwa,sanan Abdallah ina mai gargadinka da kaji tsoron Allah shikadai zance maka Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya ...koba ka shigo ba dama zan kiraka dan nagama inaso kazo ka maidani gida nima"
"Tou gwaggo nagode Allah ya Kara lafiya da nisan kwana"Abdallah yace tana murmushi,jinjina masa kai tayi sanan tace "maganar da nayi a hanya da kai kayi kokarin aikata abinda nace"
"Insha allahu gwaggo"....mikewa gwaggo tayi "jiddah zan tafi idan ankwana biyu zanzo inga yadda zaman naku yake"
"Tou gwaggo ina nan zuwa nima"....tabisu d kallo shida gwaggo suka fita,
Tabbas maganar gwaggo gaskiya ce dole ta mike ta dawowa da kanta martaba,amma tayaya hakan zai faru har yanzun tanajin zafin abinda Abdallah yayi mata?....tabbas bankad'a sirrin gidan aure ga kawa babbar masifa take jawowa idan har bakai dace da kawar kwarai ba,
Wani irin kishin ruwa jiddah ya taso mata,cire hijabin jikinta tayi akaj gado ta fito parlorn ba kowa ta nufi kitchen ko zata samu ruwa mai sanyi tana shiga ramlah na rike da wukar firar dankaki suna hada ido da jiddah taga tayi mata wani kwarjini saida gabanta ya fadi nan da nan jikinta ya kama rawa ta sunkuyar da kanta kasa,
Tsaye jiddah tayi don tanason ta bata waje amma ta kasa,ai jiddah na bude baki da niyyar yin magana ramlah taji faduwar gabar datafi ta dazu nan da nan jikinta ya kama rawa "ranki ya dade mai kitchen.... Ramlah matar Abdallah kishiyar jiddah wadda ta kasance aminiyarki a da kidan bani waje zan dauki ruwan sanyi insha dan inada bukatar shan ruwan sanyi a gidan Abdallah....wayar gari da nayi naganni a gidan da akai zaton na barsa har abada"
Bakin ramlah ne ta shiga karkarwa tadan matsa Mata tana bin jiddah da kallo doguwar rigar jikinta ta amsheta musamman yanzun da tadanyi kiba tafi da sai mazaunanta suka sake bayyana cikin doguwar rigar gashin kanta kuwa yasha gyara....take Ramlah ta raina kanta tana kallon jiddah tsaye tana shan ruwa, tanaso ta bata amsar abinda ta fada amma batada bakin bata amsa haka jiddah tasha ruwa ta dago manyan idanuwanta ta watsawa Ramlah wani kallo wanda yasa ta shiga taitayinta,saita juya ta cigaba sa firar dankali...
A kofar fita kitchen sukai kicibis da Abdallah ya dawo hannu yasa ya tare kofar yana karewa jiddah kallo da wani irin mayen kallo da idanuwansa shanyayyu...hannunsa ya sa a wuyanta "jikin yanzun babu zafi ko?babu zazzabin?"
Itama shi take kallo tanajin zafi da radadi cikin zucuyarta amma ta danne tana jifansa da wani irin kallo "babu zazzabi...ya warke alhamdulillahi takurarka ce ta haifar da zazzabin"...tabbas da biyu jiddah tayi maganar amma me maana biyu,fahimtar da Abdallah yayi shine yadda ya takurata da ruko yajanyo ....itako ramlah wani irin daram taji zuciyarta tayi sun kwana suna raya sunnah kenan?....ta gefensa ta ratsasa tanayi masa wani kallo ta fice yabi mazaunanta da kallo yadda take tafiya suna juyawa yasa yaji wata kasala da shaawarta na ratsashi,
"Dear....nace ammm wallahi inada bukatar ka jiya banyi bacci ba saboda ciwon ciki "ramlah tayi maganar unexpected,
"Ba kwanaki bane,kibari inyi mata kwana ukunta tukunna idan naraba muku kwana nadawo dakinki zan biya miki bukatarki in fidda hakkinki"ya gyada mata kai "understand?"...kada masa kai tayi alamar "ehh"
Tana shiga daki ta fada kan gado ta kifa ciki ta fashe da kuka,tabbas tanason sanin halin da bilal yake ciki saidai bazata iya sanarwa da Abdallah hakan ba idan tayi tankar batai amfani da maganar gwaggo bs,
Tsaye yayi jikin kofar dakin yana kallon yadda take shasshekar kuka,ji yake tamkar ana watsa masa rushin wuta cikin zuciya,babu abinda ya tsana dik duniya sama da kukan jiddan....a sanyaye ya hayo saman gadon ya janyota jikinsa tana kokarin kwacewa ya hade bakinsa da nata yana jifanta da wani irin salo.....hawaye takeyi amma tabbas tana karbar sakwannin da Abdallah yake aika mata dan shi din gwarzo ne wajen sarrafa mace ta hanyar soyayya,saida ya tabbatar ya kashe mata jiki sanan cikin wata iriyar murya yace "i need u soo much my wife,dan allah kada kice ah ah jiddah ina tsananin bukatar kebewa dake idan har kikacemun ah ah bazan tilastaki ba zan hakura saidai ina tunatar dake tsinuwar mala'iku akan macen da taki yarda da bukatar mijinta"yana maganar ne yana sunsuna wuyanta yanayi mata wasu irin wasanni hawaye takeyi batace masa komiba ya cigaba da abinsa,....tunda Abdallah ya shigi jiddah yakejin kansa kamar sabon ango kamar yau ya soma kusantarta wata irin niimah ce ta musamman allah ya horewa jiddah ita kankameta yayi yana sambatu shike kidansa shi yake rawarsa....
*******
Suna zaune sungama breakfast abban Abdallah yayi shirin fita aiki ya dubi ummah da farar envelope hannunsa"wanan takardar aikin Abdallah ce"
Take ummah ta washe baki "masha allahu alhamdulillahi.... Abdallah ya samu aiki lallai jiddah itace abokiyar arzikinsa gashi daga dawo da ita ya kara samun aiki"
"Ehh tou ranar dai da nayi niyyar zuwa bikonta aka bani takardar, alhaji maska ne ya bashi aikin a sabon kamfaninsa na A&B ventures a matsayin director dama tun kafin a samu matsalar nan ya fadamun idan ya gama gina company dinsa bilal matsayin manager Abdallah director gashi ya cika alkawari"..
Take jikin ummah yayi sanyi tayi shiru ta kasa magana,
"Ammm kuma dama yau nakeso inje can gidan maska in duba jikin na bilal saboda bashida lafiya zan kuma sanar dasu hukuncin dana yanke na aura masa daya daga cikin yarana wato afnan....
Take afnan ta yarda kofin tea dake hannunta tana kallon abbah, cikin tashin hankali da danuwa,tayaya hakan zai kasance bayan tun farko yaya rumaisa keson yaya bilal tana boyewa....idonta ne ya cicciko da hawaye tana kallon ummah,shiko abbah beko saurari me zasuce ba yasa kai ya fice a parlorn yana kokarin kiran layin Abdallah....
********
Yaya ibrahim kuwa kunya ce ta kamasa koda ya shigo gidan kasa gabatar da kansa yayi sai zainab ce ke shaidawa su momy shine yayan jiddah,
Babu yabo ba fallasa momy ta ansa gaisuwarsa sanan ya bukaci ganin bilal din akai masa iso har dakin da yake kwance,..
Rufaida ke bashi tea lokacin da suka shigo shida zainab da fuskarta tadan fada ta dubi bilal "yaya bee ya jikin?hope kana samun sauki?"
"Ehh ina samun sauki nagode ko?"yace mata batare da ya kalleta ba, jikinta a sanyaye ta fice dakin cike da damuwa
"Ammm dama nazo duba yanayin na jikin naka ne tun jiya naso biyoku to dare yayi shine nace bari inbari da safe inzo inga yadda ka kwana ya jikin?"
Hawaye na sauka gefen idonsa,ya dan motsa jikinsa cikin alamun jin ciwo yana yatsina fuska yace "da sauki alhamdulillahi yaya Ibrahim yasu ummah?"
Tausayin bilal ne ya kama ya Ibrahim ya sunkuyar da kai cike da kunya "ummah sunce a gaisheka ayi maka ya jiki,sun kuma ce in roki gafararka"
Cije baki yayi "Allah sarki ummah,ba laifinsu bane laifina ne da ya kasance na taka dokar allah dolene Allah ya jarabceni ta wanan hanyar,amma nasan da son jiddah zan mutu cikin zuciyata....har yanzun ina sonta inajinta cikin jikina ina sonta fiye da yadda nakeson kaina,am ready to sacrifice my happiness for her to be happy"hawaye ya gangaro masa ya cigaba da magana "ina fatan hakan ya kasance izina ga masu hali irin nawa,ina kuma yi mata fatan zaman lafiya a gidan mijinta"...hawayene ke gangarowa gefen pillown dinsa fuskarsa tayi jajir jikinsa babu riga gashin kirjinsa kwance lufff kana kallon yadda yake sauke numfashi,
Rike kai yaya ibrahim yayi yana girgiza kai tausayin bilal yasa kwalla ta cicciko a idonsa,tabbas soyayya gaskiya ce kuma ciwon so masifa ne....
Turo kofar akayi da sallama momy ce da likita suka shigo tanayimasa bayani "ka gansa nan har yanzun beci komi ba beci abinci ba yakici wallahi narasa yadda zanyi dashi"
Likita da momy suka tsaitsaya gefen gadon suna kallon yadda idanuwansa ke rufe amma wadanan hawayen suna gudu a gefen fuskarsa,
*******
Rungume jiddah Abdallah yayi yana hawaye...."Allah yayi miki albarka jiddah....muyi wanka ki shirya zan fita dake zamuje wani waje kinji?"...batareda ta kallesa ba tace "kaje kawai banaso ka fita dani ko ina inada bukatar kadaicewa nikadai"
"Bazan barki ke kadai ba jiddah...tare zamu fita saboda fitar taki ce"
Bata kara tanka masa ba sai zamowa da tayi ta shife toilet ta rufo kofar Shima saukowa yayi daga gadon ya bi bayanta toilet din yana shiga ya rufe kofar ya cire makullin yasa a sama...
Jinsu shiru yasa ramlah yanke shawarar biyosu daki ta sheda musu suzo suyi breakfast....mamaki ne ya kasheta ganin babukowa a dakin,ta kalli shinfidar su yadda tagani a hargitse yasa kirjinta ya shiga harbawa,mamaki ne ya kamata jiyo sautin karar ruwa da karar jiddah a toilet ya sheda mata da suna wanka tare a toilet....cakkkk network dinta ya tsaya kamar wata gunki ta shiga maimaita abun a kwakwalwarta,wanka su biyu a toilet sukeyi?jiya kadai da dawowar jiddah Abdallah ya sauya hatta ciwon da yakeyi ya warke?
Kwallar bakin ciki ce ta cicciko mata a ido,dik yadda take sonsa take kokarin janyo raayinsa be taba shiga yayi wanka tare da ita a toilet ba,hawaye ya sulalo mata a kumatu a fili ta furta "nashiga uku.....meya dawo da makirar nan rayuwar Abdallah gashi ta fara sauyasa tin kafin aje ko ina?..jin alamar zaa bude kofa yasa ta juya cikin sauri har tanacin tuntube ji kake kummmmm ta bude kanta jikin kofa wanda yasasu zaro ido a tare suna kokarin fitowa,
Basuga kowa ba hakan yasa sukai tunanin a wajene ko kitchen abun ya faru,...kayan dake kan gado jidda ta kwashe ta kakkabe ra gyaggyara,dik inda jiddah tayi Abdallah yana bin ta da wani irin mayen kallo dik ya susuce,
Kwanciya Ramlah tayi rigingine tana kallon fankar dakinta dake juyawa idanuwanta kuwa sunyi jajir saboda radadin da takeji a gefen kanta inda ta bige,ga hawaye da ta kasa tsaidawa,wani irin soyayyar Abdallah takeji cikin zuciyarta dake addabarta amma samm hankalinsa baya kanta..... kamshin turaren sa ya sanar mata da zuwansa da sauri ta mike tana goge hawaye tana kallonsa,farar T shirt ce jikinsa mai rubutu da blue tayi masa kyau sosai da blue jeans jikinsa gashin kansa sai sheki yakeyi yasha gyara sosai,
Saida ya kare mata kallo sanan yace "kuka kikayi ne?koko ince kuka kikeyi ne?"...girgiza masa kai tayi wani sabon kukan ke kokarin turnuketa wato tambayarta ma yakeyi ko kuka tayi?..."ba kuka nakeyi ba, nibanyi kuka ba"tayi maganar cikim sigar shagwaba tana kallonsa,
Kauda kansa yayi cikin halin ko in kula yace "munfito tun dazun munyi breakfast da baby,zamu fita zamuje wani waje saimun dawo ko?,kiyi abincin rana"
Lallai wato ma na zama kuku,tace a zuciyarta....shirun da tayi bata amsa ba yasa yace "ko bakiji menace bane?"
"Me zaa dafa?ko saika tambayi gimbiyar?"tace tana kallon yanayinsa,
"Noo noo bazataci ba nace kiyi ne koda zamuyi baki ,yanzun ma bataci ba zata dafa da kanta idan mundawo...ki kula da gida bye bye"ya fice yana duba agogo kofar ta kurawa ido hade da sandarewa a zaune....zasu yawon shakatawa ni ina gida,ta fada kan pillow cikin tashin hankali....
Tafiya suke yana satar kallonta,itako kanta na gefe ko kallonsa batayi tana duba hanya idanuwanta sun kumbura,hannunsa yasa masu taushi ya shafi gefen fuskarta ta juyo ta watsa masa harara,"babyna nasan haushin me kikeyi am sooo sorry kinsamu lada,wallahi da zaki karamun dana kama hotel mun tsaya yanzun haka"wani kallo da take masa yasa ya tsuke bakinsa ta gimtse dariya,
Tunda sukayo kwanar gidan , Abdallah kansa gabansa saida ya fadi,mamaki ne ya kama jiddah ganin gilmawar mota kamar ta yaya Ibrahim....tabbas shine amma meyazoyo nan unguwar kuma ina ne?
Kallonsa tayi cikin hada rai tace "ina ne nan ka kawoni?wace unguwa ce wanan?"
Batare da ya kalleta ba yace "unguwar su bilal ce bakiga sunan street din ba sunan daddy bane ,maska road?su suka fara zama"
Wani miyau me kauri gaske jiddah ta hadiye sanan cikin sarkewar murya tace "meya kawomu nan?me mukazo yi?"
Murmushi Abdallah yayi da ya fiddo masa da ainihin kyawunsa fararen hakorinsa suka bayyana "munzo mu duba jikinsa ne,saboda beda lafiya"
Kwalkwal tayi da ido "munzo mu kara masa ciwo dai kawai....da nasan nan zamuzo da ban biyoka ba wanan kamar cin fuska ne"
Girgiza kai yayi ,daidai wani tankamemen gate sukai parking,tissue ya zara a gaban motarsa ya ruko fuskarta yana share mata hawaye "calm down....komi zaiyi normal kinji?kibar kukan banaso"
Gabanta ne ya tsananta faduwa me Abdallah ke shirinyi meyazo dasu suyi a gidansu Bilal?....ya dubeta bayan ya kashe motar "muje ko?"....wani irin tsoro ne da fargaba ya shigeta,to kodai bilal din ya mutu ne take tambayar kanta lokacin data fito daga motar tana bim ko ina da kallo.......
KUYI HAKURI READERS BANIDA LAFIYA NE INA FAMA DA MATSANANCIN CIWON IDO KWANA BIYU AMMA NASAMU LAFIYA INSHA ALLAHU ZAKUJINI KUYI HAKURI DANI KUBAR KORAFI......
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:48 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
*36*
A kofar gidan bilal yayi parking ya dubi zainab dake faman satar kallonsa yace "muje ko?"
Karkada kai tayi alamar bazata fito daga motar ba ta kauda kanta gefe batare da tayi magana ba,gwauron numfashi ya ja "ki fito daga motar nace ko?kince zakiyi sallama da ita ko?"
"Ehh idan ta fito kun gama sai infito mugaisa"...daura fuska yayi yana mata wani kallo "kina batamun lokaci ki fito nace"ya juya ya bude motar ,tura baki tayi ta bude motar ta fito ta rufe ta jingina hade da harde hannuwanta biyu tana jifnsa da wani kallo yana rike da wayarsa,
Tsaki yaja "ina neman wayarta ma Bata shiga,ko batada carji ne?...gashi kuma unguwar ko ina da wuta"ya karasa maganar a slow,
Kallon zainab yayi a fakaice ya dan daura fuska kadan "ko zaki shiga kiyi mata magana munzo?"
Kafin ta bashi amsa Yaya ibrahim ya karyo kwana yana waya da alama daga wani waje yake amma baa mota ba,...yana hada ido da bilal yaji tsammm wani iri cikin jikinsa gashi Bilal din ya rigada ya gansa,hakan yasa ya dakata ganin bilal din ya tahi,mikawa ya ibrahim hannu yayi cike da ladabi "assalamu alaikum...yaya ibrahim barka da warhaka ina yini"
"Barka dai,lafiya lau alhamdulillahi ,ya mutanen gidan?"
"Lafiya lau"ya amsa yana sosa keya ganin ya ibrahim ya tsaya yana kallonsa "amm yaya tun dazun nazo bana samun wayar jiddah inata kiranta"
Shiru yaya ibrahim yayi yana kallon bilal kusan second ashirin,bilak dago Kai yayi yana kara duban yaya ibrahim,ganin kallon da yakeyi masa yasa gabansa ya fadi cike da rudani bakinsa na rawa yace "yayah...lafiya dai ko?kowani abu ya samu jiddar ne?"ya jehowa yaya ibrahim tambaya a jere,
Gyaran murya yayi "ammm...bilal gaskiya dai tsakani da allah zan fada maka banso sanar da kai ba amma zan sanar da kai yanzun Allah yasa ka fahimceni,ka fahimcemu Baki daya"
Wata irin faduwar gaba da tsoro ne suka cikasa suka bayyana karara a fuskarsa, Allah yasa jiddah ba mutuwa tayi ba,adduar da ta fado masa kenan be kawo komiba ya daure yace "yaya meya faru ne?ka sanar dani kada ka boyemun"
Jimm kadan ya Ibrahim yayi yana jinjina kalmar abakinsa kafim yace ",tou....jiddah da mahaifin mu ya daura mata aure batare da shawara da ita ba,maana dai ta koma gidan mijinta",
Wata irin walkiya ce ta gifta a idon bilal take yaga duhu ya kewayesa jiri ne ke dibarsa yana neman faduwa kasa ya ibrahim ya rukosa yana kiran sunan sa "bilal... Bilal ka dawo hayyacinka kada ka fadi wani mummunan abu ya sameka a wajen nan"rukon da yayi masa yasa ya tsaya amma dikda haka kafafuwansa rawa sukeyi masa karrr karrr karrr yakai hannunsa ya dafe kansa da yaji kamar ansara masa adda a tsakiyar kai...da kyar ya motsa bakimsa batare da kaji abinda yace ba ya furta "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun allahumma ajjirni fi musibati waklufni khairan minha"....dakyar yake hada kalmomin a harshensa da yayi masa nauyi,zuciyarsa kuwa bugun da takeyi kadai zai baka tsoro da tashin hakali shi kansa yaya ibrahim saida ya tsorata cikin rawar jiki ya kira zainab daje tsaye tana hangosu ta taho cikim sauri,
Kallom bilal take tana zaro ido "yaya bee....yaya meya sameka meyafaru?mekayi masa"ta kalli ibrahim tanayi masa tambaya,
Ya ibrahim kasa amsa mata yayi sai cewa yayi "kin iya mota?"ya tambayeta jikinsa na rawa,
Gyada masa kai tayi "na ita mota amma ban wani kware ba saidai zan iya kaimu gida"...yadda yake fidda numfashi yasa dukkansu suka furgice gaba daya numfashinsa ya kawo wuya,
Da taimakon ya ibrahim ya bude gidan gaba ya kwantar da seat ya kwantar da bilal,sanan ya dubeta "bani number wayarki zankiraki inji yadda kuka isa gida zan biyoku"
Ba bata lokaci ta karanto masa ta shiga ta tada motar ta bata wuta,a guje ta figi motar hawaye na gudu a fuskarta addua kawai takeyi allah ya kaisu gida lafiya dan ba tukin hankali takeyi ba tafe suke tana karawa motoci mota kamar tababbita, tanayi tana waigensa,
Cikin minti ashirin ta iso gida ta shiga zabga mahaukacin horn wanda ya furgita mai gadin ya ruga ya bude gate ganin motar bilal ce garin parking ta gogi motar abbah ta haska wutar motar...gumi ne ke karyo masa amma babu alamar numfashi sai hawaye ido daya da yake gangarowa ta gefen idonsa,....gabanta ya tsananta faduwa ta kai hannunta kirjinsa ta dafa batajin numfashi aiko tana fitowa harabar gidan ta saki mahaukaciyar kara tace "momy......daddy ku fito yaya bee ya mutu"
Zabura momy tayi tana kallom daddy kaji abinda nakeji?zuhura ta fyallo aguje daga daki "muryar zainab ce"
Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun daddy ke furtawa suka fito a tare duka mutanen gidan ta shiga pointing motar tana kada kai hawaye ko ke bulbula "wallahi ya mutu daddy....ya mutu ina sonsa ya mutu daddy"
Basubi ta kanta ba sukai motar daddy ya tallabo bilal ya bude idonsa yaga idanuwansa a kafe a guje ya sunkuto shi yayi cikin gida yana fadin "hajiya kiramun family doctor"kuka su rufaida suka rushe da shi....
*********
Hawayen da ya gani suna bulbula a idon jiddah ba karamin tadawa da Abdallah hankali yayi ba ji yakeyi kamar ya rungumeta ya lallasheta amma inaaaa"Abdallah kayi kuskure wanda yasa gabaki daya nakejin tsananin tsanarka cikin zucuyata,me akeyi da namijin da besan darajar mace ba?me akeyi da namijin da baisan yayi bincike ba yake yanke hukunci cikin fushi?....kaiba namijin aure bane Abdallah saidai banida yadda zanyi ina ganin darajar mahaifi na ni,kaiko bakasan darajar mahaifinka ba dan babu yadda beyi da kaiba kada ka sakeni ka sakeni Abdallah,dik lokacin dana tuna tozarci da kaimun a rayuwa inaji dik duniya banida makiyin da yafika.....bana sonka Abdallah na tsaneka"tana kallonsa ido cikin ido take maganar,
Jikinsa ne ya kama rawa gumi kawai ke karyo masa kalaman da take jifarsa dashi sunyi tsauri amma saidai yasan hakan zata faru "jiddah kina tunanin kin tsaneni ne?kin yaudari kanki wallahi bazaki taba tsanata ba saboda jinin jikina ke yawo a jikinka"
Ido cikin ido ta kallesa"karya kakeyi Abdallah na tsaneka idan zuciyarka na yaudararka akwai sauran kaunarka cikin zuciyata ka yaudari kanka kuma bazan taba sonka ba ka rabani da masoyina....masoyina da baya son kukana yasan darajata yasan mutuncina.... Allah sarki bilal ko cikin wani hali yake oho?mutumin daya sadaukar da farin cikinsa dan inyi farin ciki mutumin da yasan mutuncin mace yasan darajar dan adam ba na aikinsa ba"
Daga mata hannu yayi cike da tsananin kishi jikinsa har rawa yake cikin zafin nama ya fuzgota ya rike hannuwanta ya bankarota jikinsa ya kankameta cikin wani irin riko da saida tayi yar Kara"kada ki kuskura ki kara kuskuren kiran sunan bilal a gabana,dan yanzun ni mijinki ne kuma ke matar aure ce ya kamata kisan darajar aure?"yana mata magana yana karo fuskarsa dai dai da tata tana jiyo zafin numfashinsa alamar zazzabi a jikinsa yana kallonta ido cikin ido....wani irin kallo take yi masa mai cike da tsana saidai rukon da yayi mata bazata taba iya kwacewa ba a wahale ta ce "ka sakeni kada ka karyamun hannu daga dawowa ta"
Girgiza mata kai Abdallah yayi a karaye kawai ya fashe da kuka yana rike da ita,kallon yadda yake kuka takeyi,kuka yake kamar mace kamar wanda akaiwa mutuwa gumi duka ya jikesu dikda sanyin AC da yake a dakin....yana kokarin kai bakinsa bakinta ta kauda kanta gefe tana girgiza kai tana kokarin kwacewa amma karfin daya gwada mata yasa ko motsi ta kasa "kada ka kuskura ka hada bakinka da nawa wallahi zanyi maka allah ya isa"
Da jajayen idonsa yake kallonta yana cigaba da hawaye "jiddah...ina sonki ina kuma son abokina bilal....kaunarsa a cikin jinin jikina take wallahi ban taba tsanar sa ba,ina son bilal....nasan yadda yake sonki inajin pains din da yakeji na rashin masoyi kwatankwacin irin wanda nayi saidai nidin nafishi jin zafin rashin ki dan nasan wacece ke a gareni"cikin rada yake maganar yana shakar numfashinta hawayensa na diga akan fuskarta data rufe ido.....
"Bansan halin da yake ciki ba,bansan yanayin da zai Shiga ba amma na tabbatar yanzun yana cikin mawuyacin hali dan na tabbatar ya je gidanku an sanar masa da kindawo gareni"....
Wanan furucin yasa jiddah kara fashewa da kuka mai ban tausayi,take tausayin kansu ya kamata kuka takeyi ko bude ido bata iyawa tabbas Bilal yanzun yana cikin wani hali ina ma tanada damar da zata sakeyi masa magana?inama ace Abdallah zai mata izinin fada masa kalma daya?da ta umarcesa da ya auri afnan kanwar Abdallah kodan dawo da amintar su....take zainab ta fado mata a rai,ta fashe da kuka,
Cikin rada yake lallashinta "kiyi shiru jiddah kukanki yana sakani cikin wani hali da kinsan yadda nakeji idan hawayenki ya diga da bakiyi ba jiddah....ina sonki ina kaunarki nayi miki tanadin tarairaya wadda baki sameta a *AUREN FARI* ba zan shayar dake zumar kauna da kulawa sai kin mance da dik wani abu daya faru a baya,nasan alhakinki ne yasa na rasa aikina aikin da sanadinsa ne nasa matata cikin halakar dana sata"tallabo fuskarta yayi yana kallonta bude idonta tayi ta dorasu akansa take ta lumshe hawaye na cigaba da gangarowa.....jin jikinta yayi ya saki yasa yayi saurin furgita ya sassauta rukon daya yi mata ya girgiza ta amma inaaaa luuuuuuu ta tafi alamar ta suma.....
"Jiddah jiddah....jiddah ki tashi...dan allah kada ki mutu idan kika mutu wallahi mutuwa zanyi"kwantar da ita yayi ya zare rigar jikinsa yayi hanyar toilet din dakin ya dawo kamar mahaukaci ya fito,
Karo sukai da ramlah wadda ke tsaye ta labe tana saurarensu,wata furgita da tayi taja da baya yasa Abdallah bin ta da wani irin kallo mai cike da tuhuma,giftawa yayi gefenta ya wuce kitchen sai gashi da gorar ruwan suwan mai sanyi yayi dakin dashi,..
Cije lebe ramlah tayi wata kwallar bakin ciki ce ta sulalo mata,irin wadanan kalaman da Abdallah yake fadawa jiddah irin yadda yake jaddada mata soyayya ba karamin tadawa ramlah yayi da hankali ba kishi ne ya lullube ramlah ta kasa motsawa daga wajen da take,meye na fitowa ya dauki gorar ruwa?me sukeyi?haka daya fito daukar ruwa?"
Shafa mata ruwa yayi a fuska tayi ajiyar zuciya yayi saurin tallabota jikinsa idanuwanta sai shanyewa suke saboda jirin da ke dibarta da yadda zuciyarta ke tsananta bugawa rungumota yayi ya fuzge tana kokarin kwacewa jikinta babu karfi ya kara riketa yadda bazata kwace ba...."is ok my dear wife i am sorry nayi miki laifi kiyafe mun,ina cikin wani hali na inaji ina gani matata ta kamu da soyayyar aminina....yanzun jiddah kinason Bilal?kifadamun kina sonsa dik abinda kikeso zanyi miki shi zan nuna miki irin kaunar da nakeyi miki a yanzun zanyi miki sadaukarwa"a karaye yake maganar jikinsa na rawa gumi kawai ke karyo masa cikin lallashi yake fadin "tell me.... tell me my wife..umm?kina son aminin mijinki ko?idan kina sonsa shikenan zan hakura dake in bar masa koda zan mutu"yana kallon kwayar idonta yana jiran amsa,kawai saita fashe da kuka,hakan yasa ya rungumeta sosai ya runtse idonsa...yasani jiddah tana sonsa zafin sa takeji sanan yanzun babu soyayyar bilal a tare da ita sai tausayinsa.... lalubo bakinta yayi ya zura harshensa ciki yana sucking lips dinta cikin wani irin salo yana rike da ita yana sauke numfashi sama sama kamar mai asthma,
Daga labulen ramlah tayi a hankali ta hango yadda Abdallah ya tallabi jiddah yana kissing dinta ...dafe kirji tayi juwa na neman dibarta haka ta miki hanyar dakinta ta fada kan gado ta saki kuka,...wallahi bata isa tazo gidan yau kadai ta kwace Abdallah daga gareta ba... niko slimzy nace karfin hali barawo da sallama mutum da mijinsa.😂😂
*******
Dik treatment din da doctor keyiwa bilal besan inda kansa takeba abu daya ne doctor ya sanar musu da yanada rai be mutu ba yana cikin dimuwa ne kawai..."doctor kayimun kokari ka taimakeni kada in rasa d'ana ina sonsa doctor"momy ke maganar cikin kuka,
"Ki kwantar da hankalinki hajiya,insha allahu zai tashi gwaje gwajen da nayi masa yana mun nunida cewar abu aka fada masa wanda ya jefasa cikin wanan mummunan halin"
Kaiwa da komowa daddy keyi cikim dakin,karar fanka kawai kakeji sai shassheka kukan zainab wadda ta kifa kai a cinyarta tana kuka "wallahi wallahi matukar yarona ya mutu saina kama wanda ya jefasa cikin wanan halin,"kallom sashen zainab dady yayi ya kira sunanta cikin wata iriyar murya "zainab"
Da sauri ta dago fuskarta ta jike da hawaye "kikace kinsan wanda yayi magana da Bilal karshe?hakan ya faru?"
Gyada masa kai zainab tayi "ehh yayan jiddah ne daddy,dan nasansa ranar da mukaje"
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun....tou kodai sun fasa bashi auren jiddah ne yasa hakan ya faru da d'ana"cewar momy cike da tashin hankali "idan haka ne to gobe zani gidan in sanar musu da halin da yake jiki in roki iyayenta su aura mishi ita kada mu rasashi"kuka take,
Likita ne yayi gyaran murya "yana bukatar hutu baya son damuwa,dan allah kubar koke koken nan da kukeyi haka kuyi masa addua,nayi masa allurar da bazai farka ba saida safe dikda ina kokwanton hakan don bilal yanada karfin jini,ina shirin tafiya gida ne gashi wajen karfe sha daya yanzun ya kamata in wuce"
Doctor ya mike yana harhada kayansa "doctor ka tabbatar koya tashi babu wani abu?bazai shiga cikin wani hali ba?"
"Insha allahu ba abinda zai faru koya tashi bazai samu karfin da zaiyi wani yunkuri ba saidai ya kara komawa bacci.... Allah ya bashi lafiya zanzo da safe"doctor yayi musu sallama ya fice,
Minti talatin fa fitar likita bilal cikin idonsa da kwakwalwarsa yaji kamar cikin mafarki ibrahim ke sanar masa da auren jiddah da Abdallah...motsa kafafuwansa ya shigayi kirjinsa yayi masa nauyi.....sai wasu hawaye ke gangarowa a idanuwansa da gudu suke fita amma idanuwansa a rufe....kallom juna momy da daddy sukayi da sauri momy ta karasa tana leka fuskarsa
"Alhaji,wace irin magana ce haka aka fadawa bilal data jefasa cikin wanan halin...duba kaga yadda idonsa ke rufe amma hawaye na gangarowa kamar am bude famfo ga idanuwansa a rufe?...kalma daya ce nake kokwanto ko sunce bazasu bashi aurenta ba to baxai karaya ba,saidai in aurar da ita sukai"wanan kalmar ce ta bugi dodon kunnen bilal "saidai in aurar da ita sukai"
Motsa bakinsa yake kokarin yi dan yayi magana hakan yasa zuhura takai kunnenta setin bakinsa,a hankali ya furta "narasa jiddah....jiddah ta koma gidan Abdallah,"tari ya sargafeshi ya shiga tari idanuwansa a rufe,
Yadda zuhura ta d'ago daga saurarensa tana kada kai yasa hankalin daddy da momy ya tashi har rigerigen magana suke hakan yasa suka hada baki wajen fadin "meyace...meyake cewa zuhura"
"Tabbas naji abinda yake cewa momy....momy jiddah ta koma gidan ya Abdallah shi aka aura mata"
Tafa hannu momy ta shigayi tana salati innahlillahi wa innah ilaihi rajiun....."tabbas nasan hakan zata faru dan babu abinda zai jefa bilal cikin wanan halin wanda ya wuce haka"kallom daddy momy tayi tana hawaye,
Kasa magana daddy yayi jikinsa yayi sanyi yana kallonsu tabbas sunyi kuskuren goyawa bilal baya ya auri jiddah dan hakan cin amana ne,bashida niyyar son bilal ya auri jiddah saboda hujjoji da dama amma idonsa ya rufe yabar dansa ya zurfafa gashi yana gab da rasashi....gumi ke karyowa daddy ya fice a dakin...
*****
Har zuwa wanan lokacin su abidah na zagaye da ya ibrahim wanda yaketa trying wayar zainab bata shiga,sosai ummah ta tausayawa bilal dan har kuka saida tayi gajiya tayi ta nufi daki ta kwanta
Ya ibrahim dafe fuskarsa yayi kawai yana cike da damuwa dik motsi idan yayi fuskarta ce ke dawo masa a idonsa,tabbas tun ranar daya sata a ido yaji yana kaunarta amma betaba sanin kanwar bilal bace ranar da sukazo gidan....anya zai iya bacci beji halin da suke ciki ba?...yadda take kuka kadai ke fado masa a ido,meyasa be karbi motar ya kaisu gida ba? yadda ta figi motar kadai yasa ya shiga tsananin fargabar isarsu gida lafiya gashi tace bata iya mota sosai ba,
Kallom su abidah yayi ya nisa "kuntashi kuje ku kwanta"babu alamar wasa a idonsa yasa suka mike duka sukai daki shiko ya zauna nan ya cigaba da trying number zainab da akece masa a kashe....
*****"
Da zazzabi jiddah ta kwana jikinta sai karkarwa yakeyi haka suka wayi gari,shiko Abdallah gaba daya ya gama karaya dakyar ta tashi tayi sallar asuba ta koma ta kwanta can karshen gado...
Lallabowa yayi yana leka fuskarta,ba bacci takeyi ba "baby.... baby"cikin rada yake Mata magana bata amsa ba "bari in fita inje in kira likita ya dubaki ko? inaso kiji sauki babyna zanyi dik abinda kikeso idan bilal kikeso yau zani gareshi"bata ansa ba sai kwalla dake bin gefen idonta,
A hankali ya sauko daga gadon ya dauki makulli ya fice,
Ta window ramlah taji alamar fita amma batasan ko waye ba,saukowa tayi daga kan gado ta bude drawer ta dauko wani abu ta fito zuciyarta na harbawa sauri da sauri...
Turo kofar tayi yasa jiddah dan bude idanuwanta ta kalleta tsaye da kayan bacci ta rike kwankwaso,
Bude ido sosai jiddah tayi ta cikin duhun dakin tayi gyaran murya cikin isa da izza tanajin faduwar gaba ta daure tace "hajiya ramlah kin lallabo kin shigo ne kiga yadda mata da miji suka kwanta koko kinzo ne kiga yadda muka tashi?...umhmmmm lafiya kalau muka tashi nida mijin da kika kwace, saidai bansan me kikazo ba da wani sharrin kuma kikazo?"jiddah ta yunkura ta tashi ta zauna,ta kai hannu gefen gadon ta kunna fitila take haske ya gauraye dakin.....kallo jiddah kebin ramlah dashi wadda ke kokarin boye wani abu a hannunta....jiddah tana iya hangen wani abu mai kamada hoda a hannunta saidai bazata tantance ba,
Dik yadda jikin ramlah ke rawa be hanata samun kwarin gwiwar watsawa jiddah harara ba hade da kwafa,taja tsaki ta fice....jiddah ta bi ta da wani irin kallo....
MASOYA AUREN FARI DIK ME KAUNATA TO YA DUNGUMO MUYI TAFIYAR TAGWAYEN LITTAFAI BIYU TARE
RAMIN MUGUNTA SLIMZY
RAMUWAR GAYYA FEEDHOM
AKAN 300 kacal....07042277401... slimzy
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:50 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
*38*
Ruko hannun jiddah yayi tana biye dashi suka shiga ciki,bin ko ina da kallo takeyi gabanta na cigaba da faduwa ji takeyi kamar ana buga mata guduma a kirji haka suka kutsa kai babban parlorn gidan a tare,
Suna zaune parlor kamar anyi mutuwa suna breakfast suka shigo da sallama,kallon kallo akeyi momy ce kebin su da kallo cike da mamaki kwayar idanuwanta k'arara ya bayyana tsantsar mamaki kallon Abdallah takeyi tayi shiru,shi kansa kunya da nauyin momy yasa ya tsugunna "momy ina kwana,barka da safiya antashi lafiya?"
Kallo zuhura kebin su dashi ta mike ta nufi dakin da bilal yake momy ta tsaidata "daka ta dawo ki zauna"
Dakyar jiddah ta hadiyi wani miyau mai kaurin gaske sanan tace cikin sarkewar murya "momy ina kwana"
"Lafiya lau surukata ku shigo nan mana Abdallah ya ka tsaya a nan kana d'ari d'ari kamar ba gidanku ba"mikewa yayi ya karasa ya nemi waje ya zauna jiddah ta zauna,
"Ga dakin da yake ciki can bema ko ci abincu ba muma saboda bamu samu bacci jiya ba yasa muka dan natsu muke breakfast"
Kallon jiddah Abdallah yayi "tashi muje ciki"da sauri ta kallesa ya gyada mata kai babu karsashi ta mike haka kawai gabanta ya tsananta faduwa....
Kwance yake yana kallon kofa a zahiri amma a bad'ini ba kofar yake kallo ba yayi nisa cikin duniyar tunani suka turo kofa a tare suka shigo,
Kallom kallo suke tsaye sukayi batare da sun karaso inda yake ba,kafin kace me jiddah ta saka kuka tana kallon bilal ta juya da nufin fita Abdallah ya ruko hannunta yana takowa har gaban gadonsu,
Dakyar bilal ya motsa baki yace cikin jin ciwo "ina ganin mutane biyu a gabana a zahiri amma nasan ba gaskiya bane mafarki ne"
Kuka Abdallah ya fashe dashi"ba mafarki kakeyi ba man,nine Abdallah ne nine nida jiddah mukazo bilal.....haba man ka tashi kadaina ciwo kaji ka warke ka taimakeni matukar kanaso in sakar maka jiddah zanyi maka sadaukarwa"ya karasa ya dago Bilal cikin zafin nama ya rungumesa duka su biyun hawaye sukeyi,
Momy ce ta turo kofar ganinsu cikin wanan yanayin yasa ta tsaya daga kofa tana kallonsu tana murmushi...hawaye na sauka a kwayar idanuwanta..."babu wanda ya isa ya raba hanta da jini,bilal kaida Abdallah sai allah...."tasa gefen rigarta ta share kwallar sake zubowa a idonta,
Abdallah d'ago fuskar bilal yayi tayi jajir bakinsa yayi jajir dik ya fashe"am soo sorry friend nine nasaka ka cikin wanan halin ba kowa ba sanadiyyata kuka fada halin da kuka fada man...kayafe mun ina kaunarka a matsayin d'an uwana kaidin jinin jikina ne"yana maganar jikinsa yana rawa,
Dakyar bilal ya motsa ya d'ago hannunsa da babu alamar karfi ya shiga sharewa Abdallah kwallar dake zubowa a idanuwansa "is ok...i will be fine man"ya gyada masa kai suka kara rungume juna....
Tafa hannu jiddah takeyi a tsaye kuka take tausayinsu ne ya kamata jikinta har rawa yakeyi wani iri takeji a jikinta... tsigar jikinta ke tashi saboda yanayin data gansu ciki,
"Jiddah...miko mun plate din abinci in ciyar da bilal nasan bayacin abinci ko kece zaki ciyar da kanin mijinki?"
Runtse ido Bilal yayi yana girgiza kai hawaye ke gangarowa a idonsa wani irin ajiyar zuciya yake saukewa yana kallon Abdallah yana kallon jiddah sanan yace "kun dace da juna.... Allah yasa muku albarka ya kawo zuriah dayyiba"yace yanayiwa jiddah murmushi,
Itama murmushin takeyi masa tana binsa da wani irin kallo cike da tausayawa,..
Zama Abdallah yayi a tsakiyar gado yana dibo abinci soyayyen dankali ne yana kaiwa bakin bilal...a hankali yake karba yana taunawa kamar wanda yake cin kusa haka yake hadiyar abinci....sosai yaci abincin cikin ikon Allah bacci ya daukesa,
Zainab na tsaye jikin kofar shigowa tana kallonsu,shaawarsu ce ta kamata tabbas wadanan masoya ne guda uku kuma suna kaunar juna tunda basusha wahala wajen yafewa juna ba bazan taba Shiga cikin rayuwarsu ba zan nemi masoyina in aura kawai...zuhura ce ta shigo da waya a hannu "yaya zee gashi ana kiranki a waya naga kinsa ya ibrahim".
"Owk"tace ta karbi wayar ta fice,kallo jiddah tabi ta dashi tana kissima abubuwa cikin ranta kodai yayanta keson zainab?idan haka ne tayi matukar farin ciki amma bazata ji dadi ba idan zainab bata mallaki bilal na,saidai kuma afnan fa da aka baiwa bilal din?saidai inmata biyu zai aura...
********
Tun shigowarsu suke zaune a parlor ramlah bata bi ta kansu ba sai kaiwa da komowa take daga daki zuwa kitchen tana dafa abinci,
Rumaisa ce tace "nikam idan har basu shigo yanzun ba tafiya ta zanyi nagaji da jiransu"
Su abidah ma dariya sukayi "muko tun safe muke nan bamumasan inda sukaje ba ga matar gidan kamar kurma"
Tuntsirewa sukai da dariya,dirin motar su Abdallah ce tasa sukai tsit suna kallon kallo "kodai sune suka dawo"aysha da nafeesah suka hada baki,
"Bari in dubo ko su din ne"meenah ta mike tare da gyara skirt dinta taje window ta daga labule"hmmm ango da amarya ne suka dawo gasu nan sai shekin amarci sukeyi"suka kyalkyale da dariya a tare,
Shogowar su jiddah ba karamin mamaki tayi ganin su zazzaune a parlor suna faman raha ba "ah ah yan mata ne cike da gidan yaushe kukazo?"tayi tambayar cike da mamaki,
"Tun dazun mukazo,ina yini ya Abdallah"suka gaisheshi a tare suna satar kallon da yakeyi wa jiddah cikin wata irin siga,
Harara ta watsa masa ta gefe,tare suka kwashe da dariya tana kallonsu ko wanne ya tsuke bakinsa,..
Waige waige jiddah keyi can ta hangi afnan zaune a kujera tayi shiru fuskarta tadan fada idonta yayi zuru zuru "baby na afee yar kanwis nasan badake akemun shegantaka ba zo nan inji"
Afee tayi kwalkwal da ido cike da kwalla dakyar ta daure tace "barka da zuwa anty jiddah"kallonta sosai jiddah tayi ta girgiza kai "tashi muje kitchen muyi aiki ko?"gyada kai tayi tabi bayan jiddah,
Shiko Abdallah kalle kalle yake bega ramlah ba sai kawai ya nufi dakinta,
Tana zaune gefen gado da waya a hannu ya shigo dakin,kamshin d'ddadan turarensa ya sanar mata da isowarsa,fararen idanuwanta da sujai jajir ta dagosu tana kallonsa cike da damuwa "barka da dawo wa"tace ta dauke kai,
Gefen gadon ya zauna yana kallon ta da yanayinta tadan rame damuwa ta bayyana k'arara a tare da ita hannu yakai ta rike hannunta "yadai....ya gidan kina lafiya?meke damunki na ganki cikin wanan yanayin?"...dago ido tayi ta kallesa ta sunkuyar da kai batare da tace komi ba,wani irin son Abdallah takeyi amma samm halin ko in kula yake nuna mata kwalla ce ke diga akan hannunta yasa ya fahimci kuka takeyi......
Fitowa jiddah tayi daga kitchen ta nufi dakin Abdallah inda yanzun ya zama dakinta,bata gansa ba saida taji wani d'arrr sanan ta fito parlorn tana dube dube kamar me neman waniabu,
"Ina Abdallah ya shiga?"ta tambayi yan matan da suka natsu suna kallon maimaicin shirin labarina...."yana can dakin nakega kamar nan ya shiga"
Gabanta ne ya yanke ya fad'i wato dakin ramlah ya Shiga kenan hmmmm ya zagaya soyayya kenan tace a ranta nan da nan taji kishi ya taso mata fuuhhhhh ta wuce ta nufi kitchen,....
Yana rungume da ramlah yana shafa kainta ya share mata hawaye "bazaki fadamun kukan me kikeyi ba?umm?"
"Ina bukatar kulawarka da soyayyarka"
"Tou naji is ok zaki samu amma kidaina kukan kinga banason kuka ko?"ya bubbuga mata baya sun dau minti goma sha biyar tare sanan ya janyeta ta zuba masa ido "jiddah tana hadawa bilal pepesoup nasan yanzun ta gama bari inje zankaiwa man",
Gaban ramlah ya yanke ya fadi wato sun shirya kenan shida bilal?tabdijam ta hadiyi wani miyau makwattt nan da nan hankalinta ya tashi dan tasan tabbas bilal zai tona mata asiri don ainihin wayarta tana hannunsa.... fitarsa ta gani yasa ta zabura ta shiga Kai komo cikin dakin,
Afee na yanka albasa ta juya baya bilal ya shigo jiddah na cikin store tanata buruntu tana baro da kaya,
Wuceta yayi ya shige store din ta tsugunna tana binciken abu yayi mata cakulkuli ta zabura ta mike,wani kallo data watsa masa yasa yasha jinin jikinsa,ya kai mata runguma ta turesa "kada ka kuskura kaje ka rungumi matarka sanan kazo ka rungumeni"....ya kawo mata runguma ya cafko ta zata zille ramlah ta shigo sukai ido hudu ganin haka yasa jiddah fadawa jikin Abdallah tana tura baki tana masa dukan wasa yana juyi da ita yana kyalkyala dariya,cikin sauri Ramlah ta fice cike da kunar rai wato ya taho wajen matarsa ne yazo wajenta ne na wucin gadi?....
****""
Hannu bilal yasa jikin side drawer ya ciro wata yar jaka,yana sanye da bakar jallabiya sallah ya idar a zaune ya bude jakar ya ciro waya yana jujjuyawa yayi murmushi,
"Yaya bee wayar waye wanan?ka bani man?"
Kada kai bilal yayi "wanan wayar soon amfaninta zaizo zuhura zan kuma maidawa mai ita"yace ya dora wayar gefen jikin gado...
****""
Jiddah na ganin Ramlah ra fita a fusace ta hankade shi tana sunsuna rigar jikinta tana watsawa Abdallah harara dariya yayi ya dage kafadarsa yayi gaba yana fadin "idan kingama ki sameni a daki"...tabi bayansa da harara....
ALLAH YA BANI LAFIYA DA IZININ UBANGIJI YANZUN KOMI ZAI TAFI CIKIN IKON ALLAH LITTAFI YAZO GANGARA......
SLIMZY✍🏼
[11/5, 7:50 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
*39*
Tsaye jiddah tayi a kusa da gadon da Abdallah yake kwance,ya sakalo hannunsa ya rukota yana murza hannunta,wata harara ta watsa masa cike da fushi tace "au kiran da kayimun kenan?kaje can dakin be isheka ba kenan yanzun kazo nan nika tabani to sakanni"ta fuzge hannunta tana murmuguda masa baki, murmushin kasaita yayi ya lashe lebensa, wani kallo yake bin ta dashi cike da so da kauna "kishi ko?baby nasan kinada kishi nima kaddara ce tasa nayi auren amma ai kin isheni"
Idonta ne yayi kwalkwal kishi ya taso mata ta dubesa kamar zatace wani abu ta kauda kai cikin sauri ya fuzgota ta fada jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa kanta,hawaye ne ya gangaro a idonta "ki daina kuka baby kinji?me kikeso?ni kikeso kike kishi na?'bata tankasa ba ta maida kanta gefe juyo da fuskarta yayi suna fuskantar juna yayi mata light kiss a lips dinta "am sorry sweetheart kaddara ce ta riga fata dani dake inda badan hakan ba babu abinda zaisa wani ya shigo rayuwarmu"
"Nika kyaleni nasaka abinci a kitchen kuma kaga munada baki"tayi maganar tana turo baki cike da shagwaba,
Riketa yayi sosai yana kallon dan karamin bakinta "meye amfanin yan matan dake cikin gidan nan?su duba miki abincin mana"yana gama magana ya hade bakinsu waje daya ya kankameta yana kissing....
Ramlah parlor ta fito ta nemi waje ta zauna gabaki daya hankalinta na can wani waje kallo daya zakai mata ka hango tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin idanuwanta...
Hira yan matan sukeyi a parlor dukkansu cikin hirar suke lallashin afee akan maganar auren yaya bilal wadda dakyar ta kwantar da hankalinta...
"Nikam wai anty jiddah tafiya tayi ta barmu ta tafi wajen mijinta?"abida tace tana kallon su,da sauri Ramla ta kalli sashen dakin jiddah ta juyo ta bata fuska,
Tabe baki ayshah tayi ta watsawa ramlah harara sanan ta juyo tayi wata shewa "aikam suna can itada mijinta suna soyewa,dan nikam tun shigarsu daki itada ya Abdallah har yanzun bata fito ba"
Kallon juna sukayi sanan suka kyalkyale da dariya...
A tare suka fito jiddah tana murtsike ido Abdallah yakai mata cakulkuli ta goce tana kyalkyala dariya,haka kawai ya tsinci kansa cike da nishadi....
Yar dariya rumaisa tayi a fakaice tace "love birds"ta gimtse baki gani wani kallo da Abdallah yayi mata "ke ina wasa dake ne?".. girgiza kai rumaisa tayi tana gimtse baki dukkansu dariya suke son yi,
Kallon ramlah Abdallah yayi "ki shirya muje dake gaida bilal zamu kai masa abinci"yace yayi gaba yabi bayan jiddah zuwa kitchen.
Kallo tabisu dashi daga ita har shi dukkansu rigunansu a yamutse suke,wani mugun takaici ne ya taso ya tokare mata wuya kamar zatayi kuka ta mike fuuuu ta nufi daki cike da bakim ciki ,bama zanje ba me zanjeyi gidan su bilal kuma?tabdijan ai idan naje gaida bilal nakai kaina wato ma su shirya kenan?nashiga uku....
Tana kwashe abinci a flask yana tsaye bayanta ya harde hannuwansa yana kallonta cike da shaawa da soyayya dirin ya da kyawun sura irin tata yake bi da kallo,ji tayi kamar ana kallonta yasa ta juyo suna hada ido ya kashe mata ido ta zumburo baki gaba tana hararsa..."kaje ka tube kayan jikinka ka shirya kafin muci abinci dasu abidah nima in shirya muje"
Gyada mata kai yayi "zan daije in shirya in kuma jira matana tazo muci abincin tare"yana fadin haka ya juya ya fice....wani kallo ta bishi dashi ta lumshe ido ta girgiza kai....
Koda suka shirya suka fito ramlah na kwance ta kifa kai a katifa tana shasshekar kuka ya shiga daga kofar daki ya tsaya "kin shirya ko mu wuce ne?"
Dago jajayen idanuwanta tayi "Abdallah idan bazaka iya sauke hakkina ba nima ka sakeni,na lura tunda matarka ta dawo shikenan ka mance da ina existing a ciki gidan nan "
Shiru yayi yana sauraronta harta gama sanan yayi gyaran murya "is ok, yanzun dai kinsam girkinta ne ko?da ta gama zaku koma normal kwana bibbiyu ki jira kigani idan nadawo girkinki idan ban kula dake ba,yanzun ki tashi ki wanke fuskarki sauri mukeyi suna mota"....ya kare maganar da kafeta da ido,kife kai tayi a pillow memakon ta mike saita kwanta tana shasshekar kuka"idan baxakije ba ne ki sanar dani mana"
"Kuje kawai ni kaina na ciwo sosai bazan iya zuwa ba ni"
"Ok", yace yayi gaba abinsa wani takaici ne ya kara lullubeta meyasa bata tashi ta Bata musu lokaci ba ta tsaya kukan banza?...kifa kai tayi tana kuka....
*******
Black na gefen gado zaune Abdallah da jiddah dasu rumaisa suka shigo....kallon black yayi "banaso a samu matsala da abinda nasaka dikda nasan cewar ban taba saka aiki ansamu matsala ba"
Kallom wayar hannun black jiddah tayi kamar tasan me irin wayar nan,...bin hannunsa tayi da kallo tabbas wanan wayar ta Ramlah ce tayi irinta,kamar kuma ba itaba dan in zata tina jiya daddare itace hannunta take chat a parlor....ah ah to ya akai akasamu irin wayar Ramlah?
Gaisawa sukayi da bilal ko wannensu duka sukai masa ya jiki,su zuhura na zaune suma dakin cike da jamaa,bilal murmushi kawai yakeyi yana kallon yan matan yadda suka cika daki,ya maida dubansa ga jiddah da Abdallah yayi murmushi cikin sigar tsokana yace "amarya da ango...kunyi kyau sosai ina abokiyar zamanku?meyasa kuke fita ba tare da ita ba"yayi maganar cikin murmushi yana kallon Abdallah,
Shima Abdallah kallon bilal yakeyi babu laifi yadan samu sauki saidai yayi fari sosai ya rame "tana gida,nayi magana da ita ta nuna bata bukatar zuwan"
Girgiza kai bilal yayi ya cije lebe,....kallomsu yakeyi sosai sukai masa kyau,kallo daya yayiwa jiddah ya dauke kai sosai tayi kyau take yayi addua a zuciyarsa shedan ya kau,ya dace ace masoyan nan guda biyu shedaniyar dake tsakaninsu ta kau saboda suji dadin soyayya saidai wanan aikin nasa ne,..shiru dakin yayi sai kus kus da yan matan keyi suna dariyaz
Bilal ya dubi afee wadda tunda suka shigo ta sunkuyar da kai tana kallon gefe daya,kureta yayi da ido afee kyakkyawar gaske ce kamar Abdallah babu inda kamanninta suka bar nasa saidai ita macece,gata da natsuwa....saidai tayi masa kankanta amma babu yadda ya iya da umarnin daddy"afee baki gaidani ba ko kinaso ki gaisheni idan kowa ya fita ne?"
Girgiza kai tayi tana wasa da yatsunta murmushi take kirjinta ya hau dukan uku uku...."umm umm amm nagaisheka"yadda tayi maganar su meenah suka kwashe da dariya,nafeesah da aysha suka hada baki cike da tsaigumi "ina yaya zainab ne?"
Sai lokacin jiddah ta dago kyawawan fararen idanuwanta tace "laaa wallahi ita nakeson tambaya tun shigowata"
Murmushi bilal yayi yace cikin weak voice "tana waje tare da ya ibrahim.....abun nasu gwanin shaawah"
Zaro ido nafeesa da abidah da aysha sukai "wani yaya ibrahim din?"
Jiddah ta baza kunne taji feedback sai bilal yayi yar dariya yana kokarin gyara kwanciya yace "yaya ibrahim dai naku,ai abu yayi dadi"
Murmushi jiddah tayi fararen hakoranta suka bayyana ta dubi abdallah suka hada ido ya kashe mata ido ta tura baki tana hararsa dik a idon bilal wanda yake kallonsu cike da kulawa...tabbas yasan ya shigo rayuwar masoyan nan amma suna tsananin son junan su...
Zainab ce ra turo kofar ta shigo dukkansu kallo ya koma kanta,itama kallonsu takeyi tana kallon kanta cike da tsarguwa zatai magana momyn bilal da ummahn Abdallah suka shigo a tare suna faraa "daki yayi albarka lallai dana dan gata ne haka"cewar ummahn Abdallah,..
Mamakin ganin ummah yasa Abdallah ya kasa rufe baki, saidai farin cikinsa na ganin iyayensu suma sun daidaita ya kasa boyuwa a fuskarsa,zamowa jiddah tayi kasa "ina wuni momy da ummah"
"Lafiya lau surukata kun dawo?"cewar momy tana yar dariya,
Lumshe ido bilal yayi cike da farin ciki yake kallon iyayen nasa ya mike a hankali ya zauna ya sadda kansa kasa yana gaida ummah.....
******
Cikin sati uku zuwa hudu komi ya daidaita bilal ya warke sosai shida Abdallah ne tare sun fito sanye da suit iri daya bakake sun matukar yin kyau kamar larabawa...bilal ke rike da jaka "amma kasan shirin bikin nan ba wani abu zaai ba na program"
Dan bata fuska Abdallah yayi "meyasa?"
"Kawai inaso a kawomin yar karamar kanwata amaryata inyi renonta"yace yana yar dariya,
Kiran waya ya katse musu hira"kagan ta yar halak tana kirana"
"Shegiya mara kunya"cewar Abdallah yana bata fuska, kyalkyale dariya bilal keyi lokacin da yaga black yayi parking ya fito ya nufosu yayi murmushi "black yane"ya kai masa hannu suka gaisa,
"Lafiya lau boss komi normal any moment insha allahu komi zai wuce"....gyada masa kai bilal yayi ya sara masa da hannu sukai sallama,
Abdallah ya gyara tsayuwa "kaga tun dazun a WhatsApp wata number ke turomin record da videos bazan bude ba saina isa gida sauri nake zan tsaya a leventis in sai gwaiba ma jiddah"
Dariya bilal yayi "mashaaaa Allah mun samu karuwa kenan allah ya raya"
Murmushi Abdallah yayi "so get ready ka kusan zama Abbiey"sukai dariya ko wanne ya shiga motarsa....
******
Ya ibrahim ke magana da ummah da abbah akan aurensa da zainab suna tattaunawa "amma Ibrahim ina fatan ka rage wanan zucuyar taka saboda aure zakayi yanzun nasan ka"
Yar dariya ya Ibrahim yayi yana sosa keya,abbah ya karbe zancen "ikon allah,gashi bamu basu aure ba mu sun bamu auren yarsu alhamdulillahi dama haka rayuwa take komi nufin allah ne
"Allah yasa alheri yasa albarka,nan da sati hudu ne ai biki uku a tare"ummah tace tana murmushi....
*****
Tun shigowar Abdallah,ramlah taji shigowarsa tana kaiwa da komowa da waya a hannunta ta rasa wanan wace number ce ta turo mata recording na maganarta da Bilal lokacin da tayi kokarin fallasa video irin maganganun data fada ashe akwai record,lalle bilal shedani ne gabanta ne kawai ke faduwa ga babbar damuwar da ke tare da ita shine satin ta buyu tana yawon asibiti result daya ake fada mata na cewar bazata haihu ba, Dora hannu tayi akai tana kaiwa da komowa cikin dakin, shikenan yanzun ta zama bora don ta tabbatar jiddah ciki gareta kuma karami don tagama lura da yadda ta sauya da yadda take ciye ciye...."nashiga uku"tace a fili daidai nan Abdallah ya shigo da jallabiya a jikinsa,yaji furucinta yasa yadan bata fuska "menene kike cewa kim shiga uku?"
Girgiza kai tayi gabanta na tsananin faduwa tana kallonsa cike da tashin hankali,kallom wayar hannunsa takeyi ta sauke ajiyar zuciya ji take kamar ta fallasa kanta tace ana kokarin mata sharri to idan baa tura masa ba fa?
"Kinyi shiru"yace yana nazarin yanayin nata,jimm tayi takara fadawa duniyar tunani kallonta yayi yadda take gumi ya zagayo da hannuwansa kwankwasonta yana shafawa "zani parlor tunda bazaki fadamun ba kisameni zan kalli labarai"yace yana kallonta,gyada masa kai tayi ta bisa da kallo shima har yakai kofa ya juyo yana kallonta ya kada kai ya fice.....
Lumshe ido bilal yayi yana kan gadonsa Yana online yaga Abdallah a online yasan tabbas yazo ne ya bude abinda ya fada masa da suka fito a office.....murmushi yayi yau karyarki zata kare.....
Tunda ya soma sauraren voice dinda aka turo masa jikinsa ke rawa,kallon jiddah yayi wadda takeshan zobo baby suga tana zaro ido jikinta ya kama rawa tana kallon Abdallah yana kallonta,
Milk colour din kayan bacci tasa ta fito tsaye tayi tana kallonsu jikinta na rawa kallo daya zakai mata ka hango tsoro da furgici a tare da ita juyawa tayi da niyyar tafiya ya dakatar da ita jikinsa na Bari jijiyoyin kansa dik sun fito....amai ne ya tasowa jiddah saboda furgici da tashin hankali ta soma kelaya amai....
ZUWA GOBE ZAN KARASA LONG PAGE 40 DA NAKEYI RASHIN WUTA YASA KUKAJINI SHIRU INSHA ALLAHU
SLIMZY CE✍🏼
[11/5, 7:50 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
INA MASOYANA📢📢📢 MASOYA LITTAFIN *AUREN* *FARI* GA RANARKU DON NUNAMIN TSANTSAR KAUNA, KUYI RUGUNTSIMI MU HADU A LITTAFIN *RAMIN MUGUNTA.....* AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 KACAL YANZUN HAKA *RAMIN* *MUGUNTA* YA FITA....HADE SUKE DA *RAMUWAR* *GAYYA* DAGA MARUBUCIYAR ZAMANI FEEDHOM....MASU BUKATAR SIYEN TAGWAYE BIYU ZASU BIYA 300
TA WANAN ACCOUNT DIN
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
2255398727
Zenith Bank
Amina jibril
Shedar biya tun tunbi wanan number 07042277401
LAST PAGE...THIS PAGE IS DEDICATED TO *ANTY KHADIJA* A.K.A *INNAH WURO* ILUSM🥰❤️
*40*
Babu inda baya rawa jikin ramlah,gumi ne yake karyo mata kamar an kwara mata ruwa,....wani kallo Abdallah ke watsa mata cike da tsana idanuwansa sunyi jajir ya ma rasa abinda zaice jinsa yake tamkar mutum mutumi,gashi recording din be gama ba ya cigaba da yi amma gaba daya bashi da sauran common sense a jikinsa.....cikin karsashi ya kira sunanta "Ramlah"gabanta ya yanke ya fadi saboda yadda ya kira sunanta,dagowa tayi ta kallesa tayi saurin sunkuyar da kai cikinta na kara murdawa kamar ta saki fitsari....."Ramlah meye jiddah tayi miki haka da kikaci amanarta a matsayinta na aminiyarki a matsayinta na yar uwa data daukeki metayi miki haka Ramlah ko ince meye mukayi miki?"ya zabura ya mike yana takowa cikin daga murya yake maganar,itako ramlah ji take kamar ta kwasa a guje batada bakim magana,har ya tako gabanta ya tsaya...jira kawai takeyi taji saukar duka...."Ramlah na dade da yin bincike akan cewar dik ranan da bilal zaizo gidan nan wajen jiddah kema kina zuwa, tun daga ranar nasa ko kwanto a cikin zuciyata nasan kinada masaniya kuma kinada hannu,dalilin da yasa bance miki komiba banida kwakkwarar hujjar da zan turkeki akan hakan,yau saiga muryarki baro baro kina cewa bilal zaki tona mishi asiri ta hanyar turamin video dinsa yana taba nonon matata"...jikinta na rawa ta shiga girgiza kai "Abdall....ah dan allah kayi hakuri wallahi sharrin shedan ne da sharrin zucuya....da soyayy....ar"ai bata karasa ba ya zabga mata mari ya shiga nunata da yatsa yana karkada kai cike da fushi "karki kuskura ki kira shedan kice sharrinsa ne don ke kanki ma shedaniyar kanki ce da kanki Ramlah....kinyi amfani da zuwa inda take kinci amanarta kin cutar da ita Ramlah"ya fuzgota ya kai mata duka a fuska tayi saurin durkushewa a kasa Abdallah ya shiga dukanta ta ko ina ko gani bayayi ganin hakan yasa ya saketa yaje jikin kofa ya rufe kofar ya nufi daki,
Cikin tashin hankali jiddah ya yunkura tana ganin jiri ga rashin karfi tunda suka soma ta kanta takeyi dan amai takeyi sosai har ya fito da gajeran wando da belt a hannunsa ya shiga kaiwa ramlah ta ko ina tana ihun ceto,
Mai gadi kuwa daga nesa yake jiyo ihu kamar ana duka sai tayi tunanin makota ne jin ihun yaki karewa yasa ya mike ya nufo cikin gidan yana kokarin murda kofar yaji Abdallah na fadin "kin cucemu ramlah kin shiga tsakanin mata da miji,kin shiga tsakanin aminai kin farraka ahalinmu kika shigo cikin mu dik saboda aminiyarki"....rike baki baba mai gadi yayi a fili yace "kwai ya fashe kenan....tou Allah ya kyauta"ya juya cikin sauri ya nufi gate din gidan inda ake horn,
Motar bilal ce ta shigo ta haske harabar cikin gidan,yana jiyo ihun ramlah ya shafa sajensa sanan ya kashe motar ya fito shida afee ne yana sanye da kananan kaya riga shirt da blue din wando tana sanye da tsadaddiyar jallabiya baka ta yane kanta,
Zaro ido afee tayi "yaya bee kanaji fa ihu nakeji cikin gidan nan kamar ihun anty ramly"
Tana kokarin bude motar a guje ta nufi kofar shiko bilal cikin takun kasaita yake takowa ya karaso wajen da afee take tsaye tana murda kofa taki buduwa ta koma jikin window tana bubbuga window din amma shiru.....cikin tashin hankali take salati "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"
Jiddah dakyar ta saisaita kanta ta dakawa Abdallah tsawar da batasan tayi ba "ya isa Abdallah.... kabarta haka,ko a hakan ka kyaleta ta gane kuskurenta domin wanan dukan da kai mata ko jaki akai mawa saiya mutu"tana maganar idonta cike da masifa da tsiwa ta gefe daya kuma kwalla ce cike da idonta,ta cigaba da magana "Abdallah....dik abinda Ramlah taimun nima inada nawa kamashon a ciki domin tabbas me hali irin nawa indai macece tou zaai mata Wanda yafi wanan,na tabbatar ramlah tana sonka tana kaunarka shiyasa tayi amfani da damar datasamu daga gareni na rashin rike sirrina dana gidana ta cutar dani"...hawaye ne ya gangaro a idon jiddah,..
Kallom jiddah Abdallah yakeyi yana kokarin magana aka bude kofar aka shigo,kusan a tare suka shigo afnan da bilal ne ....mamaki ne ya kashe Abdallah ganin kofar daya rufe ambude sai yaga maigadi ne ashe yayi amfani da extra key din dake hannunsa incase wani abu ya faru basa nan ya bude,tabbas kuskuren da yayi rufe kofar ya kuma cire key din da bazasu samu shigowa ba,
Kallon kallo akeyi a parlorn,afnan kuwa wadda batasan komiba ce cikin damuwa da sanyin muryarta tace "wai meyake faruwa ne?ya Abdallah kaga dukan da kaiwa anty ramlah kamat kasamu dan fashi?kasheta zakayi?"
Daga mata hannu Abdallah yayi "ki rufemun baki kafin in ji miki ciwo wanan da kuke ganinta maciyiya amana ce bari kuji"...jikinsa na rawa ya shiga WhatsApp ya kunno recording din da aka turo masa nan da nan afee kafafuwanta suka soma rawa tana kallon bilal....shiko ko darrr beyi ba sai wani kallo da yake watsawa ramlah mai cike da tsana,
Abdallah ne ya kasa hakuri ganin bilal yaki cewa komi yace "man meyasa ka boyemun dik abinda ya faru lokacin da wanan makirar wadda zata shiga wutar jahannama sanadin munafunci da hassada tayi?kaki fadamun komi ka biyemun mukaita tashin hankali"
Murmushi kawai bilal yayi ya nemi waje ya zauna sanan ya nunawa abdallah kujera"zauna mana"....kamar bazai zaunaba ya zauna sanan ya dubi su afnan da jiddah da sukai cirko cirko "kuma ku zauna tsayuwar zaku gaji musamman ma ke jiddah da bakida lafiya".... luuuuuuu idonta yakeyi mata kamar ta yanke jiki ta fadi haka take laluben hanya dik hasken da yake parlorn duhu take gani ta nemi waje ta zauna duka dakin yayi shiru sai shasshekar Ramla.....
"Tou Abdallah ranar wanka baa boyon cibi,sanan dik abinda mutum ya shuka komi daren dadewa komi shekarun da zaai matukar ba alheri bane sai ya fito..... alhamdulillahi Allah na godewa wanan rana da tazo kaji komi da kanka ba daga garemu ba saidai inyi maka fatan hakuri danima ka yafemun neman matarka da nayi"
Cikin kuka ramlah ta ke fadin"dan allah kayi hakuri Abdallah kada kaimun hukuncin da bazan iya dauka ba,wallahi ina sonka"
Wata tsawa jiddah ta dakawa ramlah "karki kara cewa kina son mijina,maciyiya amana na dade banga shedaniya kamarki ba ke ramlah shedan ma idan ya ganki tsoronki zaiji kai kin cuceni"....ta ruga da gudu ta fada jikin Abdallah ya rungumeta sosai yana shafa kanta hannunsa daya a kasan mararta yana rada mata a kunne "ki daina kuka kinga babynki shima zaiyi kuka momynsa tana kuka"dago idanuwanta tayi suna hada ido ta kama dariya tana kuka,.
Sosai suka bawa su afnan da bilal shaawah,murmushi afnan tayi ta daga hannu sama "alhamdulillahi....."hawayen dadi ne ya gangaro mata ta kalli bilal ya kashe mata ido ta daga masa hannu 👍🏼
Dakyar ramlah ta iya mikewa jikinta na rawa dik ya farfashe yayi jajir tana kokarin shiga daki Abdallah ya kira sunanta ta juyo gefen fuskarta ya kumbura "karki kwana mun a gida dan idan na cigaba da ganinki ko shakar numfashinki zan iya kasheki kafin safiya kije na sakeki saki uku"yana nunata da yatsa yana rungume da jiddah yana bubbuga mata baya.....
*******
Washe gari....gidan su ramlah....
Umman Ramlah cikin tashin hankali take kallon yadda udon ramlah ya kumbura gaba daya kamanninta sun sauya "ummah ki taimakeni asan yadda zan koma hannun Abdallah ummah ina son Abdallah"
Wata harara da ummah ta watsa mata hade da jan tsaki tace "ai idan bakiyi wasa ba keda aure saidai a kiyama,kai ramlah albasa batayi halin ruwa ba Allah ya sani niba haka nake ba wallahi,kinyi asara kin tafka babban kuskuren da idan bakiyi wasa ba bazaki auru ba ramlah kinaji kina gani keda aure saidai a kiyama ke wallahi kin cuceni kin batamun suna"ummah ta fashe da kuka ta rufe ramlah da duka...
*******
Tunda daddyn bilal ya soma magana Abdallah ya sunkuyar da kai "kayi saurin saki Abdallah dikda tayi laifi amma Allah yana yi mana laifi muyafe masa"
Ummahn Abdallah data fito daga daki tasamesu a parlornta tace "aiko be saketa ba nida kaina zan saki wanan almurar,me akeyi da munafuki mai fuska biyu?haba daddyn Abdallah"
Abban Abdallah kasa magana yayi sai girgiza kai kawai yakeyi,shi ya dade da lura da yanayin ramlah da dabiunta irin na munafukai shiyasa yaki yarda da maganar aurenta......
Nan suka cigaba da tattauna matsalolin su cike da takaicin abinda ramlah tayi kowa na tofa albarkacin bakinsa...
********
Cikin wata daya da kwanaki akayi auren bilal da afnan,akayi na yaya ibrahim da zainab inda zasu zauna katsina saboda makarantar zainab ya maida kasuwancinsa can lokacin jiddah ta gyagije tayi kiba daka kalleta kasan tana dauke da ciki tayi matukar kyau sosai....
Bayan shekara biyu,
Yan biyu maza masu kamanni da juna ne suke wasa a harabar gidan abdallah inda jiddah ke wasa dasu ga karamin ciki tanadashi....da sauri ta ruko dayan me zuciyar tsiya yana kaiwa dan uwansa duka "haba bilal....ya zaka rinka dukan Abdallah haka saboda kaga ka girmeshi? to ai girman na mintuna ne"
Dariya Abdallah yayi ya ruko hannun jiddah yana murzawa "saikiyita magana da yara kamar kinayi da manya ji yadda kikewa bilal magana"
Bilal ya koma gefe ya murtuke fuska Yana duban su Abdallah ya karasa ya ruko hannun dan uwansa ya mika masa biskit din da suke fada akai....
Horn din mota ne da akayi yasa suka maida hankalinsu ga gate din gidan tunda sukaga motar sa yaran gidan suka hau ihu suna wasa suna tsalle "oyoyo abbiey oyoyo abbiey"jiddah ta fadada faraarta "mr and mrs bilal maska ne"
Afnan ta fito mota da tsohon cikinta dakyar take tafiya fuskarta babu walwala koda yaran ke mata oyoyo sama sama tai musu "ya naganki haka maman biyu"
"Hmmm bari kedai anty jiddah mutuwar ramlah ta girgiza ni,ramlah ta mutu mota ta bugeta kwana uku yau"
Shiru jiddah tayi jikinta ya mutu idonta ya cicciko da hawaye tana kada kai tace "Allah ya jikanki Ramlah,nayafe miki dik abinda kikamun duniya da lahira"...shiru Abdallah yayi jiki Babu kwari suka nufi daki shida bilal suka biyosu.....
Kuyimun afuwa rashin wuta kwana biyu ne.... alhamdulillahi angyara mana wuta....
TAMMAT BIHAMDULLAH....
SADAUKARWA GA HAUWAU MUAUZU AMIR RUMA ..UMMU AFEE INA KAUNARKI FISABILILLAHI INA ROKON DIK WANDA YA KARANTA PAGE DIN NAN YAYI MATA ADDUA ALLAH YA BATA RABO MAI AMFANI NA HAIHUWA YA BATA RAYAYYE MAI ALBARKA ALLAH YA ALBARKACETA DA HAIHUWA YASA AYIWA AFEE KANWA......
0 comments:
Post a Comment