Sam Be jira cewarta ba ya tashi motar suka bar harabar gidan mom na ɗaga musu hannu tareda Fadilah suka kama hanyar TARABA STATE, cikin nutsuwa muzaffar ke tuka motar tamkar ba wannan hamshaƙin matashin da ƙarti ke tukawa a mota ba, lokaci-lokaci yakan ɗaga manyan idanunsa ya kalli Ummie ta mudubin dakw gaban motar gaba ɗaya duk ta zama wata iri sabida damuwa, wata siririyan ajiyan zuciya sauke a ransa yana ƙara jinjina buwaya da hikima irinta ubangiji, yanzu banda Allah waya isa yay wannan?
Ummie ta Rabu da Ahalinta tsahon kimanin shekaru 35 amma se gashi cikin ikon Allah ɓatansa ya zama sanadiyar haɗuwarta da Yayanta, tabbas komai na ubangiji yanada iyakansa shiyasa Allah ya jefo musu wannan al'amarin a matsayin zannan ƙaddararsu gabaɗaya.
******
Se wajen qarfe 10pm na dare sannan su moddibo suka iso cikin garin taraba sannan ya fara shirin kama hanyar Rugarsu kokaɗan be damuda duhun da garin yayi ba, jefa ƙafarsa kawai yakeyi tsabar sabida tsabar tanda zuciyarsa ke ke tafasa da baƙin ciki, gabaɗaya jiyake komai na dawo masa a ƙwaƙwalwarsa tamkar a lokacin abin ke faruwa, wasu zafaffan hawayene suka zubo masa yasa hannunsa ya share still be dena tafiya ba, a haka har ya iso cikin Rugar tasu tun kafin ya isa ga ƙofar gidansa jama'ar garin wasu suka dinga kallonsa kamar sun samu Tv kasancewar yanzu basa bacci da wuri sabida tsaron lfyarsu,
ko kaɗan be damu da irin kallon da suke binsa dashiba hasalima baƙin cikin dake ransa ma baze barshi harya damu da irin kallon ɗa suke masan ba, Direct ƙofar zagayayyen karan daya kewaye ɗakunansu dashi ya nufa ya shige gidan ba tareda ya iya furtawa jama'an dake biye da bayansa koda kalma guda ba, Bamanga ne yay ƙarfin juyawa da saurinsa ya nufi gidan malam Iro zuciyarsa fal farin ciki donya shaida masa cewan Amininsa moddibo fa Allah yayi masa dawowa cikin ƙoshin lfy.
Da sauri malam Iro ya miƙe tsaye lokaci guda kuma ya fara jerawa Allah kirari da sunayensa mafiya kyau, da murmushin me ɗauke da zallar farin ciki ya Raɓa ta gefan Bamanga ya fita da sauri zuwa gidan moddibo, ta cikin jama'ar dake tsaye ya raba ya kutsa kansa tsaye cikin gidan yana me ƙwallawa Moddibo kira with so much love and caring.
Tsayawa moddibo yay cak yana bin Malam Iro da Kallo batareda ya iya furta ko kalma guda ba, da sauri malam Iro ya matso gareshi ya Rungumese yana me shafa kwantaccen vaƙin gaskin kan Abokin nasa hawaye na zubo masa. Shima kansa moddibon kukan yake sabida murnan ganin abokin nasa da kuma taron jama'an dukda suka taru sabida shi. Cikin farin ciki malam iro yace "haqiqa Allah mai iko ne akan komai, haka kuma babu shakka wannan yaro yanada sufa irinta ƴan aljanna wato cika alqawari, kamar yanda yay mana alqawari akanka gashi kuwa ya cika cikin yardan ubangiji da kuma amincewansa, tabbas yayi namijin qoqari musman yanda yake ɗaukar nauyin duk wani ci da sha na iyalinka har zuwa yau da Allah ya nufeka da dawowa garemu, bama iyalinka kadai ba kaf wannan Rugar babu wanda be amfana da arziqin wannan yaro ba, haqiqa duk inda wannan yaro ya fito to tabbas iyayensa mutanan kirki ne kuma masu karamci.
Ƙura masa idanu Moddibo yayi babu ko ƙiftawa harya gama magana bece da malam iron Qala ba, haka kuma shima malm iron sam be damu da yanayin dake kan fuskar moddibon ba yafi danganta hakan da ƙaton cikin dake jikin Inna laure ne ya haifar da wannan sauyin a fuskar abokin nasa. Ajiyar zuciya malam iro ya saki a ransa yace "toya muka iya da lamarin qaddarar da Allah ya hukunta?
Se'a lokacin Moddibo ya lura da Laure dake zaune bisa ƙofar ɗakinsa ta miƙe ƙafafunta Ga uban Ciki ya fito yayi girma ta tsareshi da manyan idanunta da suka gama koɗewa sabida kukan daya zama abin yinta koda yaushe.
Wani irin bugawa qirjin Moddibo yayi lokacin dayay arba da wannan tulelen cikin dake jikin laure, kasa magana yayi illa wani irin ja da idanunsa sukayi lokaci guda kuma jijiyoyin kansa suka mimmiƙe kamar wanda ke shirin gabza dambe a filin daga, da ƙyar ya iya tattara kalmomin bakinsa ya firta "Innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!!!!!
Hakanne yay daidai da tsaiwar wata jibgegiyar baƙar mota jib ƙirar companyn Ford gabaɗayanta an lulluɓeta da baƙin tinted wanda ya mugun ƙarawa motar kyau da kwarjini........
Comment
Nd
Share
Thanks 4d love💕 yanzu kam insha Allah babu tsayawa harse mun gaba dukda cewan befi 3 pages or 4 mu gama book ɗin gabaɗaya ba, ammafa idan naga Ruwan comment ne zanyi hakan 😁
Sushmah ✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :45
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️Tun daga cikin motar yake kallon yanda jama'ar rugar suke gudu suna neman maɓoya wasu wasu kuma na tsaye ƙyam hannunsu riqe da sandinansu sunyi shirin kai duka, ganin da sukai babu wanda ya fito daga cikin motar ne yasa suka qara himma wajen damqe sandinan dake hannun nasu tamkar kace ket su zura a guje.
juyawa yayi a sanyaye yana kallonta da manyan idanunsa waƴanda suka faraa sauya launi tun bayan tasowarsu daga Abuja, cikin tattausar muryanshi me ɗauke da amo a cikinta yace "kin tbbata nan shine garinku mulaikha?
Sunkuyar da Kanta tayi tana wasa da igiyar belt ɗin motar dake daure a jikinta kamar wadda ya tilasta mata dole setayi maganar tace "Sure.
Kallonta yayi kimanin 4second sannan ya ɗauke fuskarsa ya maida kallonsa waje yana nazarin mutanan dake tsaye suna jiran fitowar mamallakin motar da wannan uban daren, hasken ƙwan gaban motar ne ya zame abin kallo wanda shi kuma ta ɓangaren Edyan hasken shine ya bashi damar qarewa mutanan dake gurin kallo harya karancin yanayinsu, ba zato ba tsammani ya bude murfin motar ya fito sanye yake da jeans and Tshirt wanda sukai masifan yi mishi kyau dukda cewar baya cikin yanayi me daɗi amma sam hakan be hana baiyanar kyansa da kuma kwarjinin dayake dashi ba, ganin hakan yasa itama ta buɗe murfin motar ta ɓangare ta ta fito idanunta nakan mutanan dake tsaye suna kallonsu tamkar sun samu Tv, nan take su Bamanga dukai kan Edyan da nufin su Rufeshi da duka cikin wani irin yanayi me fitar da Amo ta kallesu cikin tsawa tace "Shin mutumin dayay wa ɗiyarku alkhairi ya taimaketa a lokacin datake buqatar taimako shine kuke qoqarin illatawa?
Tsayawa sukai cak suna kallonsa ba tareda sun juyo sun dubeta ba, shikuwa Edyan yana tsaya bisa digadigansan s ayana kallonsu ba tareda ya motsa ba, qraasowa tayi gurin tana kallonsu ido cikin ido suma ɗin kallonta suke irin kallon nan dayafi kamada na rashin sanayya.
Se'a lokacin ta tuna da canjin da rayuwarta ta samu a Sanadin Partner ɗinta Edyan kamar yanda take kiransa tun bayan haɗuwarta dashi. Ba lallau bane mutanan dake gurin su ganeta ba don haka da sauri ta isa gabansa ta tsaya shi kuma Edyan din na tsaye qyam a bayanta be motsa ba.
Bamanga ne ya ɗaga sandan hannunsa take ya sauke matashi a saman goshinta kafin kace me tuni gurin ya fashe ya fara fitarda jini, a gigice tayi baya zata faɗi sabida wani jirin azaba daya ɗibeta cin zafin nama bamanga ya sake ɗaga sandar da nufin ya saukewa Edyan Rabe dake qarin faɗuwa ta cikin wani irin mugun zafin nama da bata taɓa zaton tanadashi ba tayi wuf ta sake shiga gaban Edyan ɗin take sandar ta sake sauka bisa gefan fuskarta. Cikin ƴar daƙiƙar da bazata wuce 2 ba ta faɗi ƙasa sumammiya.
Ganin jinin dake fita ta bakinta da kuma goshinta ne ya mugun fusata Edyan dake tsugune bisa kanta yana ƙwala mata kira cikin wani irin karaji me cikeda nuna tashin hankali, da ƙarfi yake kiran sunanta tamkar wani zararre ya miƙe kamar mayunwacin zaki yay kan Bamanga da duka ƙarfinsa ya shiga gabza masa naushi yana faɗin "how dare you dazaka sa sanda irin wannan ka daki Mulaikha ta?
Bakajin tashin komai se ihun Bamanga wanda ya cika gurin sabida duhun daya farayi, ihunsa ne ya jawo hankalin Moddibo da malam iro wanda ke tsaye a cikin gidan da sauri suka fito don ganin abinda ke faruwa, kasancewar hasken fitilar gaban motar a kunne yake shine ya basu damar ganin abinda ke faruwa a tsakanin Bamanga da Baquwar fuskar dake gabzar bamangan kamar Allah ya aikoshi.
Da sauri suka nufeshi da nufin su ƙwaci Bamangan a hannun Edyan amma sam hakan ya farkara, daga can gefe ya tsinkayi muryar Rabe wadda ke Rawa sabida Azabar bugun datasha a hannun bamanga tace " plz partner stop beating him he's my.....uhm.. He's mmmmm.... My brother!!!!!
Cak Edyan ya tsaya da dukan kamar wanda aka matsawa remote, a hankali ta miqe tsaye dukda jirin dake ɗaukarta kamar ance ta juya idanunta suka sauka akan Mahaifinta Moddibo wanda ke ƙoƙarin ɗaga Bamanga Wanda jini ke fita ta bakinsa, da wani irin gudu Rabe ta kwasa ta nufi moddibo tana wani irin kuka tana kiran "Babana wayyo Allah babana is that you!!!!! Faɗawa tayi jikinsa ta saki wani marayan kuka wanda yasa gabaɗaya mutanan gurin suka dare suna bita da kallo.
Da qyar ta iya tsagaita kukan ta ɗago tana kallonsa cikin ido cikeda shauqin si irin na ƴa da ubanta tace "haqiqa Babba ka cika alqawarinka gareni sedai ni ban cika maka wanda nayi maka ba babana! Ko kaɗan A tsakanina dakai tasirin qaddarar yayi kaɗan ya zama silar rabuwata dak........... Wani irin kuka ne ya sake qwace mata a karo na biyu.
Gabaɗaya Moddibo kasa motsin kirki yayi illa wasu zafafan hawaye dake masa zarya a saman kumatunsa, qura mata idanu yayi sannan ya buɗe bakinsa dayayi masa nauyi yace "so tari a Rayuwa wasu al'amuran sunfi qarfi rai da gangar jiki ya iya musalta ɗacinsa, shiyasa tasirin zanan qaddara yasha banban da komai a rayuwar ɗan Adam, haqiqa Allah mabuwayin sarki ne kuma mai jida ganine shi shiyasa ya taqaita min zafin jarrabar rayuwar danake ciki ba tareda nasha wahala mai tsanani wajen nemanki ba!!!!
Duk mutanan dake gurin seda suka tausaya musu ciki kuwa harda Edyan wanda ke tsaye yana fitarda numfashi, ganin abin nasu bana qare bane yasa ya koma mota ya buɗe wata qaramar box dake sit ɗin baya ya ɗakko wata madaidaiciyar box ya dawo inda Rabe da moddibo ke rungume da juna suna aikin kuka ya kama hannunta ba tareda ya lura da irin kallonda mutanan gurin suke masa ba ya zaunar da ita a ƙasa dirshen sannnan ya buɗe box ɗin ya fito da soft cotton with hydrogen ya fara goge mata ciwon dake goshinta yana fitarda jini, seda ya gama tsaf sannan yasa mata flasta ya rufe gurin yana kallon tsakiyar kwayar idanunta with so much love and emotion. Sauke idanunsa yayi a hankali ya mayar kan box ɗin tareda ɗakko wani ƙaramin magani wanda aka rubuta pain reliver a jiki ya ɓallo ya miƙa mata yace "let bring the water for you. Ya faɗa yana miqewa ya koma mota can se gashida bottle water ya miqa mata ta karɓa tasha maganin tana wani yatsina fuska.
Gabaɗaya mutanna dake gurin kowa kallonsu yakeyi inda wasu daga ciki suke mamakin rashin kunyar da Edyan, musamman yanda sukaga yana kama mata hannu, basu ida shiga mamaki ba seda sukaga ya Kama hannunta yana qoqarin miqar da ita tsaye.
Gabaɗayansu zaro idanu sukai suna binta da wani irin kallo se'a lokacin ta lura da abinda ta aikata ɗin ba shiri ta fusge hannunta daga ruqon da Edyan ɗin ya mata ta koma kuda moddibo ta tsaya se faman raba idanu take kamar wadda tayiwa sarki qarya. A haka taron ya watse kowa da abinda yake saqawa a gameda Edyan da Rabe.
Sosai moddibo ya tarbi Edyan kamar ze goyashi sabida yanda Raben ta gaya masa irin alkhairin dayayi mata a rayuwarta tun bayan haɗuwarta dashi, hakan ba qaramin dadi yayiwa modɗibo ba harya kasa ɓoye hakan a fili dukda irin tashin hankalin da zuciyarsa take ciki a gameda halinda ya dawo ya samu Laure a ciki, kasancewar dare yayi sosai ne yasa Moddibo ya raka Rabe bukkarta ya kunna mata fitilar lagwanin dake ɗakin sannan ya zaunar da ita bisa katifar ciyawar dake ɗakin ya dubeta yace "wanene wannan matashin da kuka taho taredashi?
Ajiyar zuciya ta sauke me nauyin gaske a hankali ta maida kallonta qasa ta shiga korawa mahaifin nata bayani akan Edris da kuma irin kulawa da qaunar daya nuna mata a rayuwa. Shiru moddibo yayi yana kallonta bece komai ba akan maganar ya dubeta yace "ki kwanta ki huta zuwa safiya zamuyi nagana. Kwanciya tayi idanunta na kallon saman ɗakin tayi lamo da ita sannan ya fita tareda kashe mata fitilan lagwanin.
Yana fita ɗakinsa ya nufa inda yabar Edyan don haka ya shimfiɗa masa zanin gadonsa meɗan haske ya kalleshi yace " Cikin gurɓatcciyar hausarsa yace ka kwanta yaro dare Yana yi kuma gashi kun kwaso hanya. Yana gama faɗin Haka ya juya jikinsa a salube ya bar ɗakin yay canta bayan bukkokinsa ya fashe da wani irin kuka..............
Chubado✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :46
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
Not edited🙅♀️
_____✍️Wani irin kuka yakeyi tamkar ransa ze fita seda ya ɗau lokaci me tsayi yanayi sannan ya danni zuciyarsa yayi shiru, dafe kansa yayi da duka hannayensa biyu yana me tausayawa kansa bisa jarrabawar da Allah yayi masa gefe kuma ga iftila'in daya faɗawa iyalinsa wannan wace irin musiba ce haka ace iyalinka na ɗauke da cikin da Allah kaɗai yasan ubansa.
Maza sama da uku ace sunwa mace fyɗe at same time wa zaka nuna a matsayin uban wannan yaro?
Gabansa ne yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma ya dafe saitin zuciyarsa dayaji tana masa wani irin zafi, miqewa yayi daqyar ya nufi bukkarsa inda Ya sauki Edyan a ciki ya fara laluben ƴar qaramar jakar da ya shigo gidan da ita wadda ke ɗauke da magungunansa na Asbiti ya ɓalla ya afa a baka, ya jima zaune sannan ya ɗan samu relif da ace yabar wannan jakar a gidansu Muzaffar a sanadin Ganin Danejo dayayi da besan inda ze tsoma ransa ba.
Fita ya sakeyi zuwa bukkar da Laure ke ajiye shirginta ya kwanta acan ya barwa Edyan ɗakin shi kaɗai donya sake, yanajin fitar moddibo ya miƙe ya zauna tareda kunna fitilar wayarsa take hasken ya game ko wace kusurwa ta ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke me qarfin gaske sabida wani irin ciwo dayaji haqarqarinsa na dama ya farayi sabida rashin saboda irin wannan makwancin, ɗan buɗa idanunsa yayi tareda shafa kwantacciyar sumar gefan fuskarsa sannan ya miqe ya fara zagaya ɗakin yana tunanin yanda za'ai ya iya baci akan katifar ciyawan dake ɗakin, take yaji zuciyarsa ta mugun karye wasu siraran hawayen tausayin su moddibo ya fara zubo masa
"Taya za'ai ace mutum ya iya rayuwa a cikin irin wannan Dajin?
Edyan yayiwa kansa wannan tambayar, take wani ɓangare na zuciyarsa yace dashi "ba gashi nan su suna rayuwa a ciki ba.
Hannunsa yasa na dama ya shafe ƙwallar data zubo masa a hankali ya furta "Alhamdulillah ya Rabb dakaimin ni'imar da ba kowa kayiwa kamarta ba, na tabbata ka haɗani da mulaikha ne don kawai a sanadinta nazo naga irin rayuwar da sukeyi Don kawai na Qara imani akan Rayuwa, ya Allah ka qara mana sutura duniya da lahira don Alfarman manzon Rahama (S.A.W). A haka Edyan yayta tufka da warwara har bacci ya fara ɗaukarsa,
Kamae wanda aka mintsina yay firgigit ya tashi sabida wani irin kukan qwaro daya addabeshi, koya ya rufe idanunsa da nufin yayi bacci seyaji ya kasa sabida qarar kukan gyaren daya cika ɗakin, wani sirin tsaki ya saki tareda miqewa ya zauna a saman katifar kamar ze saki kuka sabida takaicin kukan qwaron da kuma rashin sabo da kwanan irin wannan gurin, duk irin gajiyan dayayi kasa baccin yayi yanda yaga rana haka yaga dare.
Wannan shine abinda ya faru a Rugar Arɗo.
*******
Ɓangaren su muzaffar kuwa basu shigo cikin Gyambu ba se wajen qarfe 11:00pm na dare, direct wani babban hotel suka nufa muzaffar yay musu booking ɗakuna guda biyu Ummie tareda Zainab shi kuma nasu shida Abie
Bayan kowa ya nufi ɗakin baccin nasu ne Muzaffar ya buɗe ƙofar ɗakinsu ya fito zuwa inda nasu Ummie yake, a zaune ya sameta bisa saman dadduma da Alama sallar ishsha'i ta gama gabatarwa, tsayawa yayi daga bakin qofar yana kallon yanda damuwa ke baiyane qarara a saman fuskarta take wani irin tausayinta ya gama cika zuciyarsa, a salube ya tako zuwa gareta ya zauna daga gefanta tareda kamo hannayenta cikin nasa yana ɗan mammatsaya cikin sugar rarrashi yace "Ummie nasan yanda kikeji a ranki sam ba abubane me sauki da mutum ze iya handling dinshi cikin sauqi, bt dukda hakan ya kamata ace kin qarama kanki qarfin gwiwa akan jarrabawar datazo miki a rayuwa, don Allah ki ragewa kanki damuwa sabida kar wani abun ya sameki na tabbata Baffa ze fahimceki kuma delensa ya karɓe yunda keɗin jininsa ce no matter what, koda ace sular rabuwa bata gifta a tsakaninki dashi ba dole wata sekun rabu tunda tun ran gini ran zane Allah ya rubuta muku hakan a zannan qaddarar ku.
Ajiyar zuciya muzaffar ya sauke me qarfun gaske sannan yaci gaba da cewa " ummie qaddara ba abarda ɗan adam zeyi shawara a kanta bace, rubutu ne tun daga mafari kafin ayi halitta don haka babu yadda muka iya dole tsarin Allah shine a saman komai indai har baffa ɗan uwanki ne na haqiqa wllh zeyi miki uziri akan dukkan abinda zaki faɗa masa, don haka ki dena sa damuwa a ranki insha Allah everything is going to be alright kinji Ummie na?
Muzaffar ya faɗa yana jawota jikinsa yay hugging ɗinta with so much love between son to his mother.
Kuka Ummie keyi qasa-qasa tareda miqa godiyarta ga Allah daya bata ɗa irin muzaffar wanda yafi darajar kilo giram 70 na zinare a idanunta.
Ya jima tareda ita sannan ya miqe yay mata sallama zuwa ɗakinsu, bisa ga mamakinsa a zaune ya samu Abie shima ya kasa rintsawa duk a dalilin damuwar da Aisharsa ke ciki, zama muzaffar yayi daga gefan abie ba tareda ya kalleshi ba yace " Abie wani al'amari ne a rayuwar Ummie wanda har yake sanyata zubar hawaye irin haka?
Kallonsa Abie yayi da sauri lokaci guda kuma yay qasa da idanunsa yace "koma menene zakaji komai da zarar mun isa ga moddibo. Abie na gama faɗin haka ya haye gadon yaja ɓargo ya rufe jikinsa dukda cewar idanunsa a soye suke babu alamar bacci a cikinsu.
(o'o see love don Allah, wllh duk duniyar nan babu abinda yafi samun miji na gari ni'ima da kwanciyar hankali, so pls my dearest sisters wake up and keep praying for miji na gari, wllh idam kika saki vaki kina bacci cikin dare ba tareda kin miqe kin roqi miji na gari ba your life is in danger malama, becouse duk duniyar nan babu abinda yakai samun miji na gari daɗi. ya Allah ka zaɓawa ƴan matan mu da mazajen mu mata na gari tareda zuriya ɗaiyiba ))
Washe gari tun 7:00am suka haɗa komai nasu suka kama hanyar rugar Arɗo, tun daga irin jejin da suke ratsawa ta ciki suna tafiya zuciyar Abie ta fara tsinkewa, babban abinda ya ɗaure masa kai shine taya za'ai ace mutum me rai ya rayu a cikin wannan qungurmin dajin?
Haka muzaffar ya dinga ratsawa ta cikin labi (hanyar shanu) harya isa cikin rugar, motar daya hanga a tsaye ce tasa ya qara qaimi don ganin ya isa kusa da motar.
Parking yayi a saitin motar yana qare mata kallo harya fito daga cikin tasu motar, zaro idanu yayi lokacin da idanunsa sukai tozali da bayan motar da kuma sunan dake manne a saman lambar motar me ɗauke da harufa guda biyu kamar haka......................
Comment
Nd
Share
Don't forget to vote on whatpad
Chubaɗo✍️
[3/3, 5:39 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :47
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
*_Miɗoyatta himɓe jeɗo tokka'am bomiɗotora Allah barkiɗinamon thnks so much for the love 👏_*
Yau dai kam Na saka fulatanci a wannan page ɗin sosai sedai ayi haquri dani 😂
BANYI EDITING BA🙅♀️
____✍️Da mamaki kwance saman fuskarsa ya isa jikin motar wanda zuciyarda ta gama aiyana masa ta Edyan ce, ya jima yana nanata harufan sunan dake saman jikin lambar motar kamar me koyon karatu, tambayan dake addabarsa a wannan lokacin itace "shin me Edyan keyi a nan kuma meya kawoshi?
"muje mana ka tsaya kana kallon mata.
Abie ya katse masa tunani wannan hakan yay daidai da fitowar Moddibo da kuma Edyan daga gidan, da sauri Ummie ta nufi inda moddibon ke tsaye wanda yanayinsa ya mukun sauyawa daga ganinta cikeɗa ɓacin rai yace "* _ta'awara kumbi'am danejo, miɗa mimeta milara ma hotoha aburti_* ( karki matso kusa dani Danejo banason na qara ganinki a rayuwata ki koma inda kika fito) ya faɗa yana nunata da yatsa cikin ɓacin rai.
Wani irin zubewa Umnue tayi bisa qafafunta tareda haɗa hannayenta duka biyu cikin harshen fulatanci tace " Hamma useli waɗɗu munyal na'aibiyamma nonnon Allah arti bindi plss. (don Allah yaya kayi haquri ba laifina bane haka Allah ya rubuta a qarqashin qaddarar mu).
Cikeda fushi gamida ɓacin rai moddibo ya nunata yace "An'asamte abiya miwaɗa munyal Danejo? (yanzuke bakiji kunyar kallona kice min nayi haquri ba Daneji?)
Gabaɗaya gurin zuba musu ido akayi ciki kuwa harda Edyan wanda kansa ya mugun gama ɗaurewa da maganganunsu, daga Abie har Muzaffar babu wanda yay qoqarin dakatar da wani a tsakaninsu sedai dukansu sunajin zafin zubar hawayen Ummien, musamman muzaffar da har yanayinsa ya fara canzawa din haka da sauri ya isa inda Ummien ke zube tana kuka shima ya zube nasa gwiwoyin tareda haɗa hannayensa guri guda alamar roqo yace "bansan wani laifi Mahaifiyata ta aikata maka ba Baffa amma dukda hakan a matsayina na ɗa a gareta ina roqa mata alfarmar yafiya a gareka don girman Allah ka yafe mata ba tareda kayi tunani akan irin girman laifin data aikata maka ba, kada ka manta baffa komai na rayuwa yana tafiya ne da zannan qaddara kuma idan har ubangiji ya rubuta hakan to babu shakka se'abin ya tabbata don haka nake roqonka arziqi don girman Allah ka yafe mata kodan darajarmu nida mahaifina!!!!!!
Muzaffar ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubo masa Sabida jinɓzafin zubar hawayen mahaifiyar tasa dayakejin zubarsu tamkar zubar tafasasshiyan dalma asaman zuciyasa.
Gabaɗaya kallonsu mutanan dake tsaye a qofar gidan sukayi kunsan mutanan mu da kallo idan sukaga baqon abu lol 😂
Kasa cewa qala modɗibo yayi sabida masifan kunyar muzaffar ɗin dayakeji, badan darajarsa ba wllh ko kallon ummien bazeyi ba haka kawai yakejin kimar yaron a idanunsa ta yanda yakejin zai iya sadaukar masa da komai nasa Muddin mallakinsa ne. Juyawa yayi ya shige gidan ba tareda ya iya sake futa koda kallama guda ba
Matsowa Edyan yayi inda Abie ke tsaye tareda ɗan rissinawa ya gaidashi, da sakin fuska Abie ya amsa masa tareda dafa kafaɗunsa yace "ai tun jiya nake jarraba number Cp amma na kasa samunsa.
Edyan yayi murmushi yace "he's fine Abie, be jima da dawowa ba ai. Ya faɗa yana kallon Ummie wadda ta miqe da sauri tabi bayan moddibo
Qarasawa gurin yayi yana kallon muzaffar wanda shima ɗin ita yake kallo jikinsa a matiqar mace ya sauke kallonsa ga barin Ummie sannan ya dubi Edyan da mamaki kwance a kan handsome face ɗinsa yace "meya kawoka nan kuma dude?
Yatsina fuska Edyan yayi yace "i bring my baby to meet with her parents ne thats why I'm here. Ya faɗa with so much emotion on his face.
Take hanjin cikin muzaffar suka wani irin juya a lokaci guda nan da nan zuciyarsa ta wani irin buga da qarfi amma kuma seya dake ya saki wani ɗan banzan murmushi wanda ya ɓoye weakness dinsa yace "waw thats nice dude.
"Kaifa meya kawoku ? Edyan ya faɗi hakan yana tsareshi da manyan idanunsa.
Ɗan jim kaɗan muzaffar yayi kamar bazeyi magana ba ya ɗan saci kallon cikin mota yaga still zainab na bacci sannan yace "is just a family issues. Taɓe baki Edyan yayi yace "ok tashi mu shiga ciki
Miqewa yayi daga tsugunnen dayake ya koma mota ya tada zainab sannan suka shiga cikin gidan gabaɗayansu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa.
Suna shiga direct ɗakin moddibo sukaiwa kansu masauki dukda cewar moddibon be wani sake dasu ba amma yayi qoqari sosai wajen danne zuciyarsa akan abinda qanwar tasa ta aikata masa. Bayan sun zauna ne modɗibo yasa Rabi'atou ta kawo musu tafasashshen madara da kuma damammiyar dawo wadda taji uban kayan qamshi irin na Asalin fulani.
Ƙura mata idanu Ummie tayi tana kallonta lokaci guda kuma ta saki wani tattausan murmushi wanda ya baiyana ainihin kyanta da kuma irin kamar da suke da moddibo. Itama Rabi'atoun kallonta takeyi sannan ta durqusa ta gaishesu dukda cewar batasan daga nahiyar da duke ba, kokaɗn hankalinta bekai ga muzaffar wanda ke zaune a kusada Edyan ba hakan yasa ta miqe ta fara qoqarin fita
Daqyar ya iya bude bakinsa sabida wani masifan kyau dayaga ta qara masa a sanadin canjin data samu yace "uhm you don't know how to great right?
Tsayawa tayi cak ba tareda ta samu zarafin juyowa ba sabida tsabar ruɗun data shiga a sakamakon jin muryar mutumin da kullum zuciyarta ke bugawa dason sake jin sautin muryarsa a rayuwarta, da ɗan sauran qarfin daya rage mata ta tattara ta juyo a hankali take idanunsu ya sarqe cikin na juna,
Gabaɗayansu zuciyarsu bugawa take kusan duk a lokaci guda haka kuma kowa da abinda yake saqawa a ransa gameda abokin gamin nasa. Sauke idanunta tayi da sauri kamar me koyon magana tace "g..ood morning! Sam bata tsaya sauraron respond ɗinsa ba ta fice daga ɗakin zuciyarta na bugawa.
Ɗakin da bata taɓa zaton zata iya sake shigarsa ba ta nufa sabida tsabar ruɗanin dake tareda ita, a hankali tasa hannunta ta ɗaga labulan buhun dake jikin bukkar tareda kunna kai ciki still tayi tana kallon Inna Laure dake zaune dirshen da uban ciki qafafunta duk sun kumbura.
Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta take shauqin da murna suka yaye mata hujabin tsoron lauren data daɗe tanaji ta nufeta da wani irin excitement on her face ta rungumeta, ko babu komai itama zata haifa mata qanin daze dinga ɗebe mata kewar kaɗaicin data taso a cikinsa.
Duk yanda taso ta Ta kali fuskar inna Lauren sam abin be yuwu mata ba dole ta haqura ta fara qoqarin matsa mata qafar yanda zata ɗanji dama-dama
A ɓangaren zuciyar Laure nadamace zallarta dukda cewar bata fito mata da hakan a fili ba, gabaɗaya kunyar yarinyar takeji musamman idan ta tuna irin zaluncin data dingai mata a rayuwa ba tareda haqqinta ba, tayi mata alkaba'i me tarin yawa wanda bakinta baze iya qayadewa ba se gashi tun ba'aje ko ina ba Allah ya mayar matada mugun nifinta a kanta, hawayene suka zubo mata amma kuma setai saurin sa hannunta ta goge gudunɓkar Rabi'atoun ta gani.
A haka har aka kwashe lokaci meɗan tsayi suna tare tana matsa mata qafar.
A ɗakin moddibo kuwa shirun ne ya fara gundurar kowa amma banda Ummie wadda ke zaune jefi-jefi takan ɗaga idanunta ta kalli yayan nata. Abie ne ya katse shirun ta hanyar cewa "salati goma ga manzon Allah (S.A.W) nan take kowa ya amsa aka shiga jerawa manzon Rahama salati bayan sun kammala Abie ya ɗaga kansa ya kalli modɗibo yace "da farko dai ina mai baka haquri bisa abinda ke tsakaninka da Aisha bawai a matsayin suruki ba a'a ina magana ne a matsayina na Abdulwahab Abdalla kuma ubaga ɗanda Aisha ta haifa, haqiqa Aisha tayi kuskure musamman data gaza haquri ta zauna tareda danginta sakamakon iftila'in daya faɗa mata, gabaɗayan mu dagani harkai babu wanda ze iya misalta irin ciwon da zuciyar Aisha ke ciki tunda gabadayan maza ne ba mata ba amma kuma dazamu ɗora kanmu a matsayinta na tabbata hukuncin data zartarwa rayuwarta muma irinsa zamu yanke kokuma akasin hakan, banaso ka kalli aisha a matsayin mace mara tausayi kokuma adalci sabida sam siffarta ba haka take.
A iya zaman danai da ita kimnain shekaru talatin da biyar na karanci halaiyarta ta yanda ko ina naje zan bada labarin wacece ita.
"amma kuma ai hakan be hanata iya guduwa tabar Ahalinta ba duk sabida wani dalilinta mara tushe!!!!! Moddibo ya faɗi hakan ransa a matiqar ɓace. abie zeyi magana Moddibo ya kalli su muzaffar da Edyan se kuma zainab dke zaune suna raba idanu yace "maza ku tashu ku bamu guri zamuyi magana.
Ba musu gabaɗayansu suka miƙe suka fita kamar yanda modɗibon ya buqata sannan ya dubi Abie yaci gabada cewa "duk na saurari batunka nima yanzu zakaji abinda na riqa a matsayin hujja dukda cewar ba lallai Danejo ta sanar dakai ba, kamar yanda ka faɗa a maganganunka na baya tabbas ni kaina mai iya bada shaida fiyeda yanda ka bayar ne akan Danejo sabida tun batasan kanta ba nake rainonta da hannayena, nasha haqura da abubuwa da dama a rayuwarta don kawai na inganta Rayuwarta to amma meye laifina don kawai qaddara ta Fyaɗe ta faɗawa rayuwarta shikenan seta gudu ta barni ba tareda ta sanar dani inda zataje ba har tsahon shekara 35?
A matsayinka na uba wanda keda ƴaƴa mata ka ɗora maganata akan mizani shin wani irin hukunci zaka yankewa Aisha a lokaciɓ da qaddara ta sake haɗaka da ita?
Shiru Abie yayi zuciyarsa cikeda zallar tausayin modɗibo he wish to see his sister kamar yanda modɗibo yaga tasa qanwar wadda tun bayan rasuwar mahaifinsu da aka musu rabon gado ba jimawa mijinta ya ɗauketa sukabar garin ba tareda ya sanar dashi ba, tunda suka tafi har yau be qarajin duriyarsu yayi neman harya gaji duk kuɗinsa da kuma shahararsa har yau babu wani labari akan Balaraba qanwarsa. Nan take Abie ya fashe da kukan tausayin kansa
Seda yay me isarsa sannan ya ɗaga kai ya kalli moddibo yace "ina roqonka Arziqi ɗon Allah ka yafe mata wllh da kasan irin wahalar da Aisha tasha akan tunaninka na tabbata zaka yafe mata ba tareda ka tsaya dogon nazari ba, tundaga lokacin dana tsinci Aisha a bakin hanya babu numfashi a jikinta har zuwa lokacin dana fara soyayya da ita har mukai Aure Aisha bata taɓa samun kwanciyar hankalin manta ka ba, haka kuma munje numan yafi a qirga amma kuma bamu sameku ba se bukkokinku da aka sakawa wuta suka qone, dukda haka Aisha bata yanke qauna ba kuma bata fasa zuwa numan ba akan kozata samu labarin inda kuka koma.
A qarshe da abin yayi tsamari ɗaukarta nayi kacokan na maida ita india da zama kozata rage yawan damuwar dake ranta. A qarshe kuma ina me maka wasilci kan cewar Allah ma munayi masa laifi kuma ya yafe mana ba tareda ya duba girman laifin da muka aikata masa ba.....
Hawayen dake idanunsa Moddibo ya share sannan ya kalli ummie dake zaune tanata gurzar kuka a karon farko tun shigowarta ɗakin yace" na yafe miki Danejo Allah ubangiji ya yafe mana gabaɗaya 😭
Zabura tayi ta riqe qafafunsa tace "nagode Hamma Allah ya qara girma.
A haka kowannensu zuciyasa ta cika da farin ciki mara misaltuwa, fitowa Abie yay daga bukkar bisaga mamakinsa muzaffar na kan wani dutse wanda ke facing ɗin ɗakin moddibon daga ɗan nesa, fara'ar kan fuskar Abie ce ta bashi tabbacin cewar baffan ya yafewa mahaifiyar tasa. Misalta irin farin cikin da muzaffar ke ciki abu ne da baze yuwu ba don haka suka rungume juna da Abie shikuma Edyan yanata baza uban murmushi wanda ke nuna farin cikinsa ga abokin nasa.
Tun'a safiyar ranar labari ya gama karaɗe rugagen dake maqotaka datasu moddibo kan cewar Danejo da Rabe sun dawo harda ɗanta saurayi ma da kuma mijinta, don haka akwai taron al'ada wanda za'a habatarwa da Danejo da kuma ɗanta wanda ba'ayi mata ba tun shekarun baya *_(niko nace kuji bidi'a don Allah 🤣)_*
Kafin kace me jama'a kowa ya fara halarta zuwa bikin Al'adar Auren danejo da kuma mijinta.
Bayan Azahar aka kawo kayan sakin da Ummie da Abie zasu saka wanda ya kasance launin blue da yallow a cikin wasu qwarya guda biyu kowada nasa se kuma takalman roba suma guda biyu da kuma lulluɓi, su muzaffar da Edyan ma sam ba'a barsu a baya ba sedai su nasu kayan na farin saqi ne kamar na sauran ƴan gaiya, bayan anyi sallar la'asar ne Bulo handi tazi tasa Ummie ta sanya kayan saqin da aka kawoma ummien sannan ta umarceta dataje ta taimakwa mai gidan nata ya shirya tunda tasan yanda ake komai. Ba musu ta fita daga fakin zuwa inda Abie yake
Seda ta tabbatar ta taimaka masa ya gama saka komai na biki al'adar sannan ta ɗakko cinkon saqaqqiyar igiyar kaban dake gefe ta rataya masa suka fito tare, a waje suka cimma su muzaffar da edyan da zainab suma sun shiya cikin farin saqin suna jiram fitowarsu.
Kusan a tare suka nufo inda ake gudanar da shagalin bikin al'adar daga muzaffar har Edyan seda abin ya nemi ya basu tsoro musamman yanda sukaga an gangama uban itace uwa naci gefe kuma nawa saniya guda ne a banqare ana gasashi gabaɗaya fuskokin mutanna dake gurin duk an fenteta da uban farin fenti da yellow irindai kwalliyar fulanin jeji, har aka kabbara kiran sallar magrib ba'a fara shagalinba har seda kowa yay sallar magrib tukunna
Sosai abin ya burge zainab don haka ta fito da wayarta tana ɗaukar vedio tun daga zuwansu Abie har kujerar da suka zauna seda ta dauka a vedion , kafin kace me tuni shagali ya kankama abin babu kama hannun yaro sannan Rabe suka qaraso gurin itada ruqatu da kuma Modɗibo, gabaɗyansu tsareta sukai da ido daga muzaffar ɗin har Edyan ɗin, nan take zuciyar muzaffar ta fara aiyana masa kan cewar yaje gareta.
Yana shirin miqewa Edyan ya rigashi miqewa ya nufeta fuskarsa ɗaukeda wani hamshaqin murmushi tareda fito da wayarsa ya fara ɗaukarta hotuna tana dariya, yana zuwa kusa da ita yace "looking so Masha Allah partner. Washe haqora tayi tace "thank you partner and you too.
Matsawa yayi dab da ita yace "can I snap a picture with you babe?
Why not. Ta faɗa tana gyara tsaiwanta sosai kusa dashi
Duk abinda suke idanun muzaffar na kansu babu abinda zuciyarsa keyi banda tafasa, a fusace ya miqe daga inda yake zaune ya nufi inda suke ɗaukar hoton har idanunsa nayi masa sabida ɓacin rai............ Hannunsa yaji an riqe ta baya don haka ya tsaya chak jikinsa na wani irin rawa yana juyawa yaga zainab ce ba shiri yay hugging ɗinta still jikinsa na rawa, a tsorace take binsa da kallo Cikeda tsoro ta zare jikinta daga nasa tace "what's wrong bro? talk to me pls.
Comment
Nd
Share
Dont forget to vote on whatpad.
Chubaɗo
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :48
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
*ɗan tsokaci a gameda masu cewa ya kamata ace muzaffar yasan dalilin dayasa mahaifiyarsa tabar Rugarsu zuwa wani guri na daban, ina so kuyi aiki da basirar da Allah ya baku a matsayinku na ƴan Adam masu tunani, inaso ku ɗora kanku a matsayin da Muzaffar kekai shin ya zakuji idan akace yau wani ɗan fashi ya hauro gidanka kuma yayiwa mahaifiyarka Fyaɗe? Na tabbata da ace hakan ta faru gara ace ƴan fashi sun shigo gidan ka sun kashe mahaifiyarka se hankalin ka yafi kwanciya da ace wani ɗan iskan banza ya ketwa mahaifiyarka alfarmarta, bawai ban karɓi qorafinku bane a'a kawai dai inaso ku ɗora lamarin a mizanin dedaito da hankali ne👏*
BANYI EDITING BA🙅♀️
_____✍️A ɗan wannan taqin abubuwa dadama sun faru masu daɗi da kuma marasa daɗi, lokacin da zuciyarta ta gama tabbatar mata da cewar lallai muzaffar ya tafi a irin yanayin data gama tabbatarma da kanta cewar baze sake waiwayarta ba se kawai ta sake fashewa da wani irin kuka wanda it kaɗai tasan ma'anar abinta, haqiqa ita kanta tasan bata kyauta masa ba musamman data nuna masa halin ko'in kula a lokacin datasan yana matiqar buqatar hakan, to Amma yata iya bazata iya barin Edyan ba sabida ya haskaka rayuwarta ta ɓangarori da dama. Don haka kowa yanada mahaimmancinsa a idanunta da kuma zuciyarta.
*******
Ɓangaren Edyan da abokanan tafiyarsa kowa ya isa gida lfy haka kuma kowa da abinda zuciyarsa ke tufka masa ta ɓangaren abinda ke wakana a zukatansu, lokacin da Edyan ya isa gida Direct part ɗinsa ya nufa tareda faɗawa toilet ya sakarwa kansa ruwa me zafin gaske sabida gajiyar dake taredashi, ya jima a toilet ɗin sannan ya ɗaura alwala ya fito ɗaure da wani babban towel wanda ya tsaya masa iya digadigansa, ko mai bai shafa ba ya Buɗe tangamemiyar drower ɗinsa dake manne a jikin bangon ɗakin ya fara bin side ɗin inda qananan kayansa suke, wata riga mara nauyi ya ɗakko da wandonta mallakin companyn Pajamas ya saka sannan ya tada sallar dake kansa, yana idarwa ko tasbihi beyi ba ya miqe ya hau kan makeken gadonsa sabida wani irin bacci dake muqurqusarsa, cikin mintuna kadan bacci mai nauyi ya ɗaukeshi.
Al'amarin Muzaffar kuwa tun bayan dawowarsu gabaɗaya zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa sabida tarin damuwar dake kwance a qasan zuciyarsa, duk hada-hadar dayakeyi daurewa kawai yakeyi yana gabatar da wasu abubuwan don haka yay wata iri Rama wadda sedata girgiza Mommy, dukda irin damuwar dayake ciki sam be fasa gudanar da yanayin aikinsa ba don haka nasarori kullum qara samuwa suke a sanadinsa.
Zaune yake a cikin hamshaqin office ɗinsa yana matsa na'urar laptop ɗin dake gabansa, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci he is doing something important on his system ɗin. Ahankali take takowa cikin takunta na isa da qasaita harta samu nasarar tura qofar glass ɗin dake office ɗin, da hanzari sectary ɗinsa ya nufota yana faɗin "I'm sorry ma'am but my boss said he don't want to see any client karnabar kowa ya shiga senan da 1 hour. tsayawa Hajar tayi jikinta duk a mace sabida tasan halinshi sarai muddin ya faɗi abu aka saɓa tofa bashida sauqi ko kaɗan ta wannan fannin.
Makeken glass ɗin dake manne a fuskarta ta zare tareda ɗaga qafafunta ta nufi gurin da aka tanada don zaman baqi masu jiran iso idan sunzo, badan ranta yaso ba ta zaro wayarta tana wani latsawa tamkar babu abinda ke damunta. Tana nan zaune Ta hangi fadilah cikin shigar wata arniyar baqar suite with street siket se faman walwalin baqi takeyi, kanta kuma ɗaure cikin rolling irin na mutanna qasar misrah a nitse take takowa cikeda nutsuwa tamkar ba stubborn Fadilah ɗinnan ba me shigen nuna isa da kuma wulaqanci ba, Direct office ɗin ta shige hannunta ɗauke da wani file ko lura da Hajar dake zaune gurin batayi ba.
Ta jima a ciki sannan suka fito taredashi hannunsa bisa kafaɗar Fadeelah ɗin suna dariya, still tayi tana kallonsu ba tareda sun lura da ita ba fadilah ne ta kalleta lokaci guda kuma ta zaro ido tace "oh Hajar long time no see ya kk? Ta faɗa tareda matsawa ga Hajar ɗin wadda ta kafe Muzaffar da wani mayen kallo kamar zata cinyesa ɗanye, wani irin masifan kyau taga yayi mata a cikin Royal blue ɗin Korean suit ɗin dake jikinsa wadda tai masifan karɓar jikinsa. A dabuce ta saki murmushi Ba tareda ta iya furtama Fadilah dake tsaye komai ba.
Kallonsa Fadilah tayi tace "Yaya lemme back to my office I have a client that are still waiting for me. Ta faɗa tareda barin gurin tana dariyar yanda taga ya wani sauya fuska duk sabida ganin chiwebegum ɗin nasa kamar yanda take kiran Hajar ɗin dashi.
Kamar zatayi kuka ta qaraso gurin da yake tsaye ta kafeshi da mayun idanunta tana kallonshi tace "kayi haquri my ster kawai bazan iya zaman jiranka har zuwa lokacin da kasawa ranka zakazo gidan mu bane, kwanaki can da daɗewa kace min zakazo gida muyi magana amma kum......... Kuka ta sakin masa sabida yanda takjin ciwon abin a ranta.
Ɗan wara manyan idanunta yayi sabida yanda ta mugun bashi mamaki, hannunsa yasa ya dafe kansa tareda firzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa yace "look Hajar I don't want any trouble plz oya tashi muje badai rashin zuwa gidanku bane kawai matsalar ? To muje . Ya faɗa yana nuna mata hanya
Takawa ta farayi tana share hawayen dake sakko mata suka fito farfajiyan companyn, kallonsa tayi zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar cewa"ki shiga motarki zan biki a baya banson problem, juyawa tayi da sauri ta shiga motan ta sannan shima ya shiga nasa guards ɗinsa na take masa baya a haka har suka isa gidansu Hajar Ɗin ya ɓalle murfin motar dayake ciki ya kalli Solomon yace "ku jirani a nan base kun shigo ciki ba nan da 5minute zan fito insha Allah.
Be jira cewarsu ba ya tura qofar get ɗin ya shiga cikin gidan, a hankali yake takawa cikin takunsa na isa da jinkai harya isa maine qofar da zata sadashi da pard ɗin Mom Edyan ba tareda ya tsaya ga hajar wadda ta ƙwafe a guiding tana jiran ya qaraso susha hirar love ba.
A nitse ya shiga falon da sallama tareda fara qoqarin zare rufaffan takalmin fatar dake qafarsa, dakatar dashi Mom tayi ta hanyar cewa bar takalmin ka ka shigo dashi son. Ta faɗa tareda yalwata murmushin fuskarta
Cikeda kunya ya durqusa har qasa yace "mom ina yini? "lfy lau muzaffar yau kaine a gidan namu? "ae wllh mom nine dama nazo ne nayi muku godiya bisa ɗawainiyar da kukayi da Rabi'atou. Haɗe rai mom tayi ta sake kallonsa tace "banda abinka muzaffar Ai rabi'atou ƴa take a gurina koda ace babu alaqar jini a tsakaninka da ita, haka kuma bamuyi mata don ka gode mana ba komai mukayi mata wllh munyi mata shine don Allah badan neman jiran saka mako ba.
Shafa gefan kansa yay cikeɗa da kunya sannan yace "mom Edyan yana nan kuwa? Ba tareda ta kalleshi ba tayi murmushi tace yana part ɗinsa be jima da dawowa daga office ba. Zeeyadah ce ta shigo falon hannunta ɗauke da flet wanda ke ɗauke da fruite a ciki, da sakin fuska gamida girmamawa ta iso falon tana faɗin sannuda zuwa ya muzaffar yau kaine a gidan namu?
Murmushi yayi mata wanda ya qarawa fuskarsa kyau yace "yeah. Murmushin dake kwance kan fuskarta ta qara faɗaɗawa tace "your highly welcome.
Miqewa yayi tareda faɗin "thank you dear kafin yama mom sallama ya nufi part ɗin Aminin nasa Edyan, a hankali yake tafiya zuciyarsa ɗauke da wani al'amari wanda yakejin masifar nauyinsa tamkar an ɗora masa gingimemen dutse me girman gaske, ko kadan bayaso mace ta shiga tsakaninsa da Babban Amininsa shiyasa yake qoqarin ganin ya yaqi al'amarin dake ransa gameda Edyan ɗin, yana matiqar martaɓa Edyan tayanda yakejin cewar qimarsa takai ya iya sallama masa komene muddin hakan zai sanyashi farin ciki koda kuwa ace Rabi'atoun ce kuwa.
A hankali ya murɗa babbar qofar dake falon tareda kunna kai ciki, babu kowa a falon se Tv dake ta faman aiki don haka Direct ya nufi qofar bedroom ɗinsa, da sallama ɗauke a bakinsa ya tura qofar tareda sauke manyan fararen idanunsa Akan kowace kusurwa dake cikin ɗakin, sakin qofar yayi ya Still yaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin harya isa bakin makeken gadon dake ɗakin ya zauna yana me zubawa qofar toilet ɗin dayaji zubar ruwa idanu.
Seda ya kwashe kimanin 3minute zaune sannan Edyan ya fito sanye cikin farar jallabiya yana sauke hannun rigar zuwa qasa da alama Alwala yayi, kafeshi da ido muzaffar yayi batareda yace dashi qala ba, murmushi Edyan yayi tareda qarasowa ga aminin nasa ya zauna daga gefansa yana me qara yalwata murmushinsa yace "anya kuwa idanuna daidai suke nuna min kokuwa dai gizo kake min? Idan har zan iya tunawa daidai rabonda mu haɗu irin haka tun a Gyambu. Ya faɗa yana dafa kafaɗun muzaffar ɗin wanda ke kallosa har yanzu baice qala ba
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan yace "nazo ne kawai na ganka nima sabida inaji a jikina cewar Nayi Kewarka Edyan !!! Muzaffar ya faɗi hakan yana kallon Edyan ɗin yana murmushi shima, amma kuma a ransa yana me tausayawa Edyan ɗin sabida wata shegiyar rama dayayi wanda yake da tabbacin cewar irin damuwar dake addabarsa kullum a zuciyarsa irinta ce ke addabar Aminin nasa Shima, take wani irin tausayinsa yay masa dirar mikiya a ransa.
Seda suka ɗan taɓa hira kimanin tsahon mintuna 5 sannan nuzaffar ya miqe yana murmushin qarfin hali yace "zan wuce gida zuwa anjima mayi waya ko?
Ajiyar zuciya Edyan ɗin yaɗan sauke sannan yay murmushi cikeda qarfin hali yace "ok thank you so much for the visit. Kallon tsaf muzaffar yay masa sannan ya dafa kafaɗunsa lokaci guda kuma ya fice daga ɗakin cikin takunsa harya ɓace idanun Edyan na kansa a ransa yana me tausaya masa shima.
Koda ya fita direct guiding ɗin ya nufa inda yake da tabbacin cewar Hajar na gurin tana Aikin jiransa, tunda ya nufo gurin ta kafshi da idnu tamkar zata haɗiyeshi sabida so harya samu guri ya zauna still tana kallonsa, yana zama ya sarqe qafafunsa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubeta a karon farko a rayuwarsa yace "Hajaaaar!
Wani irin Amsawa qirjinta yayi sabida wannan shine karon farko dataji sunanta a bakinsa, wani irin farin ciki taji yana ratsa zuciyarta nan take hawayen farin ciki ya farayi mata zarya, bakinta yana rawa ta fara magana daqyar tace "haqiqa yau itace rana ta farko a rayuwata wadda tazo min da tarin alkhairai ciki kuwa harda wannan zaman da mukai da juna dakai a yanzu, wllh Muzaffar zuciyata me rauni ce indai har akan son da take maka ne na shiryawa dukkan abunda ke shirin yimin katanga dakai Koda kuwa hakan na nufin Rasa Rayuwata ne gabaɗaya!!! Don Allah ka fahimci damuwata kada ka hukuntani da abinda bazan iya ɗauka ba plssssss.
Tunda ta fara magana ya kafeta da tsimammun idanunsa waƴanda suka tashi daga launin farare suka surka da launin ja sabida tausayinta, a hankali ya dubeta tareda sauke numfashi yace "Haqiqa na tausaya miki Hajar kuma babu shakka kin samu nasarar dasa tausayinki a zuciya ta, nasani jarrabawar soyayya ba qaramin Abu bane haka kuma duk mutumin daya samu kansa a ciki abu ne mawuyaci ya iya samun kwanciyar hankali harse zuwa ranar da ya samu abinda ransa ke muradi, sedai dukda hakan ina me baki haquri bisa abinda bakina ze furta miki a yanzu wllh hajar a halin yanzu sam ba relationship bane a gabana I have a lot of abubuwan dake gabana wanda sam bazan iya haɗasu da soyayyah ba, koda ace ma zanyi soyayya to zuciyata tanada wadda takeso kuma take Qauna banajin cewar zan iya son wata mace kamar yanda nake sonta! Wannan dalilin yasa bazan iya amsar soyayyarki ba koda kuwa ace na Rasa daman Auren wadda zuciyar tawa takeso.
A hankali sautin kukanta ke tashi cikin wani irin yanayi na zallar tausayin kanta da makomarta tace " sonda nake maka a cikin jinina yake yawo banajin cewar haquri ze iya wadatar da zuciyata harya sa na iya cireka a raina, amma don Allah shin zaka iya sanar dani dalilin dayasa bazaka iya karɓan soyayya na ba?
Murmushi ya saki wanda ke baiyana zallar tausayawarsa gareta sam bayaso yay hurting ɗinta daqyar ya iya buɗe bakinsa yace " sabida baki dace da irin tsarin matar da zuciyata keso ba Hajar!! addinin mu ya horar damu cewar idan zamuyi aure to mu zaɓama ƴaƴan mu uwa ta gari bawai kuma ina nufin keɗin ba mace ta gari bace a'a hajar sam ba haka nake nufi ba, kawai dai bazan iya zamada matar data maida rayuwarta irinta turawa ba kamar dai yanda kike a yanzu, wllh da ace qanwarki zeeyadah ce ke sona kamar yanda kike sona tabbas zan iya Aurenta kuma na zauna da ita badan komai ba kodan sabida kyawawan halayenta......... Yana kaiwa nan ya miqe idanunta sun sauya kala sabida yanda yake tausaya mata bisa dakon soyayyarsa data daɗe tanayi tsahon lokaci.
A haka yabar gurin ko waiwayonta beyi ba. Zubewa Hajar tayi a gurin lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka mecin rai gaamida zallar tausayin makomar rayuwarta.
Yana zuwa ya shiga mota Solomon sukaja motar sukabar harabar qofar gidan.
Tun bayan dawowarsu daga Gyambu muzaffar ya tattara lamarinta ya ajiye a gefe tareda maida dukkan hankalinsa ga aikinsa, sosai yake wata irin rama sabida yanda abin ke cinsa a rai fiyeda duk zaton mai karatu amma tsabaragen kafiya da taurin zuciya ya hanashi samarwa zuciyarsa abinda takeso. A haka rayuwa ta dinga tafiyar masa da daɗi babu daɗi still yaqi koma mata kamar yanda take mafarki a kowace wayewar garin safiya.
Kamar yanda Ummie ta sanar da Moddibo cewar zata sake dawowa bayan sati ɗaya hakan kuwa akayi, tun ana washe garin ranar dazata tafi Gyambun ta kammala shirya duk kayayyakin dazatayi musu tsaraba dashi, zaune take a tsakiyar falonta ta miƙe ƙafafunta tana duba kayayyakin da Abie ya shigo dasu wanda zatayi musu tsaraba dashi, Baba Hajara ce ta shigo falon hannunta ɗauke da wani ƙaranin bokitin roba cike taf da dambun naman kaza, inda ɗaya hannun nata kuma take ɗauke da farantin silver cike taf da kwaɗon zogale wanda yaji uban quli-quli da tumatur, fuskarta ɗauke da murmushi ta qaraso inda Ummie ke zaune ta miqa mata farantin zogalen tace "Ranki ya daɗe ga zogalen an kammala haɗawa.
Da mamaki Ummie ta ɗago tana kallon baban hajaran sannan tace "haba baba don Allah ? So nawa zan gaya miki cewar ki ɗena ɗorawa kanki hidimata tunda kema kanki ba lafiyarce ta isheki ba?
Nidai don Allah baba karki sake bawa kanki aiki da sunan zaki wahalta min don girman Allah. Ummie ta faɗi hakan yayinda take kallon baba hajarar wadda keta faman murmushi
Cikeda dattako Baba Hajara tace "haba Ranki ya daɗe ai wannan sam ba aiki bane me wahala da har zaki damu kanki don kawai nayi miki shi, don haka sam ki dena damun kanki akai ne jikina ya daɗe da warwarewa. Zatayi magana kenan Muzaffar da Fadilah sika shugo falon bakinsu ɗauke da sallama yana gaba Fadilah na binsa a baya a haka suka shigo tsakiyar falon idanunsu duk akan farantin dake gaban ummie cikeda uban zogale wanda aka baɗeshi da quli gamida tumatur me yawan gaske, zama suka sannan Fadilah ta gaida Ummie tana dariya tace "Ummie muqaddiman naku kukeyi kenan keda Baba Hajara akan aiki ko?
Da sakin fuska tace kin ganta nan wllh Fadilah kullum senayi fama da ita akan magana ɗaya dai amma taki ta bari miqewa baba hajara tayi tareda miqawa muzaffar bokitin dambun naman datayi masa don tasan yana sonsa sosai, faɗaɗa murmushinsa yayi tareda karɓan bokitin yace "kai lallai matar nan kin iya kula da mijinki yanda ya kamata. Ya faɗa yana ɗiban dambun yakai bakinsa
Dariya sukai gabaɗaya sannan Ummie ta miqe ta wuce ɗakinta, sun jima suna aiki a system tareda Fadilah se wajen dabda magrib suka gama aikin tsaɓ sannan kowa ya koma ɓangarensu.
Washe gari gabaɗayansu Ahalin gidan suka raka Ummie airport ciki kuwa harda Mom da baba Hajara da kuma zainab, har seda sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida ita kuma Ummie jirginsu ya nufi birnin na Yola.
******
Gyambu (taraba state)
Jirginsu na sauka wasu lafiyayyun motoci guda uku baqaqe wuluk sukazo ɗaukarta cikin qanqanin lokaci Ummie ta fito cikin shigar doguwan riga me shegen kyau, take guards ɗin suka buɗe mata motar dake tsakiya ta shiga ta zauna sannan suka ɗauki hanyar gyambu.
Sosai moddibo yay farin cikin da zuwan ummien har hakan ya gaza ɓoyuwa a kan fuskarsa, don haka ya shiga hada-hadan haɗa mata duk wasu abubuwa dayasan tana masifan sonsu tun tana qarama.
Sosai Ummie kejan Rave a jikinta don haka yarinyar ta ɗan saki jiki da ita ko babu komai ganinta na rage mata kewar Abin Qaunarta muzaffar. A haka rayuwa ta dinga tafiya kullum zuciyarta na azabtuwa da kewar zaratan mazajen datai rayuwa dasu kuma har zuciyarta ta afka a qoramar saboda su.
Sosai ummie kejin daɗin zaman garin hkaa kuma wata irin shaquwa ta musamman na qara giftawa a tsakanin Moddibo da kuma qanwar tasa, wannan dalilin yasa ta qara tabbatarwa da kanta cewar maganar bahaushe gaskiya ne dayake cewa "kowa yabar gida tofa gida ya barshi. Sosai take kula da yanayin cikin laure wanda yay masifar girma don haka ummie ta dubeta da kulawa tace " Amma laure wannan cikin naki kun taɓa zuwa Asbiti akan batun awo kuwa? Ni watansa nawa ne ma tukun na?
Jikinta a mace laure ta kalli ummie tace..........
Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :49
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
Banyi Editing ba🙅♀️
____Jikinta a mace tace "ai kinsan yanayin yanda muke rayuwa A nan Danejo don haka ban fahimci abinda kike kira da wannan sunan ba.
Murmushi kawai Ummie tayi a ranta tana taya ɗan uwan nata samun haihuwa a karona biyu, addu'arta ɗaya ce Allah yasa Laure ta haifa masa zaratan maza guda Biyu kodan ƴaƴansu su samu yawaitar ƴan uwa ba kamarsu ba da suka kasance su uku rak a gaban iyayensu. A haka moddibo ya shigo gidan ya samesu fuskarsa ɗauke da murmushi yaja ɗaya daga cikin kujerar tsugunon dake gefan ummie ya zauna hannunsa dauke da baƙar leda meɗan girma kaɗan Gamida qatuwar qwarya wadda aka rufeta faifai.
Da kulawa Ummie ta dubeshi cikin harshen fulatanci tace "sannuda isowa hamma.
Murmushin dake kwance a saman fuskarsa ya qara yalwatawa ya dubeta yace " yauwa Danejo maza tashi ki ɗakko min ƙwarya kizo mu kasa wannan goron ɗaurin Auren. Bakinta sake ta dubeshi fuskarta ɗaukeda mamaki tace "Goron ɗaurin Aure kuma Hamma?
Bece mata qala ba illah Ajiye qwaryar dake hannunsa da yayi wadda ke ɗauke da farin saqi tass a cikinta gamida mayafinsa se kuma takalmin roba guda biyu a gaban Ummie kana ya sauke ajiyar zuciya yace "Danejo ga kaYan tsaida maganar Auren Rabi'atou nan iyayen BAMANGA sun kawo yanzunan.
Kafeshi da idanu Ummie tayi gabanta na dukan tara-tara, abu ɗaya ne ke dabaibaye da zuciyarta shine tausayin Muzaffar wanda tasan ba lallai bane ya iya jure rashin Rabe a taredashi ba. Amma kuma a zahiri se Ummie tayi murmushin irin na ɓoye damuwar nan sannan tace "masha Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya kumasa ayi damu, amma Hamma wata nawa kasanya musu kafin Auren?
A taqaice Moddibo yace "sam ba watanni nasaka ba Danejo kwana biyu kawai na saka jibi-jibin nan zan ɗaura mata Aure. Yana kaiwa nan ya miqe yabar gurin ba tareda ya damu da irin kallom mamakin da ummie da Inna Laure kebinsa dashi ba yay gaba abinsa
Rabe dake tsaye jikin ƙofar karan dake jingine da ɗakinta sam batasan sanda ta sulale akan qafafunta zuciyarta na bugawa da mugun qarfi ba, Allah ya sani sam bazata iya hana zuciyarta abinda takeso a wannan gabar ba ko kaɗan, sedai tasan koda giyar wake tasha sam bazata iya bijirewa mahafinta akan muradinsa na Aurar da ita ga Bamanga ba,
Komai da mafarinsa tasani sanin kanta Bamanga ba shine zaɓin Zuciyarta ba to amma idan harta bijirewa wannan Auren tamkar ta kunyata mahaifinta ne, Aure ta da Bamanga tamkar igiyar kabar da aka daɗe ana tufkata ne tunkafin tasan kanta, ma'ana dai Aurene da iyayensu sukai alqawarin faurawa tun a ranar da aka haifeta don haka dole ne tayi haquri da Bamanga a matsayin mijinda Qaddara ta zaɓa mata shi.
Daga Ummie har Inna laure babu wanda ya tanka akan lamarin hukuncin da Moddibon ya zartar, dole tasa suka amince da hukuncinsa dukda cewar a zukatansu sunada ja akan abinda yake shirin zartarwa akan Raben.
Tun daga Ranar Rabe ta ɗaura da zubar da hawaye gamida tilastawa kanta faɗawa a qoramar tunanin zaratan mazan da suka shigo rayuwarta a baya, sosai ta rame tayi wani irin duhu duk a kwana ɗaya kachal tamkar ba ita ba, ko abinci se Ummie ta matsa mata kana take iya cinsa shima ba wani sosai take cin ba.
Tun'a daran jajiberen Aurenta da Bamanga Rabe ta gama saddaqarwa da kanta cewar tabbas tayi rashi a rayuwarta irin rashinda bazata taɓa mayarda kamarsa ba, a hankali take ɗaga qafarta harta iso bakin qofar bukkar da mamie ke kwana, sunkuyawa tayi kana ta shiga cikin bukkar bakinta ɗauke da sallama, a zaune ta samu Ummie wadda keshan fura se faman murmushi takeyi da alama video call takeyi itada su Zainab da kuma Abie. Tana ganin shigowarta Ummie ta kashe wayar tareda maida hankalinta ga Rabe tace " Dota na Amarya shigo mana kika tsaya kamar kuwa kinsan yanzu nake shirin nabiki ɗaki akan maganar shirin bikin sekuma gashi kinzo da kanki, yau insha Allah Adda Maryamu da yafendunki Gwaggoji duk yau zasu iso insha Allah daga yolah.
Kanta a qasa tayi murmushi kawai ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba, ko babu komai har a ranta ta ɗanji sanyi dajin batun zuwan qanwar Mahaifiyarta da kuma kakarta wadda ta haifi Mahaufiyarta wadda sike kirada (gwaggoji) ko babu komai tasan zata ragewa kanta damuwa muddin ta tattauna matsalarta da wani
Kanta a qasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Ummie ki bani aron wayarki zan kirasu mom.
Shiru Ummie tayi a ranta tana mamakin yanda yarinyar kejin nauyinta sannan tayi murmushi ta miqa mata wayar Ta karɓa tabar ɗakin tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, tana fita ɗakinta ta koma tareda buɗe qatuwar jakar da Edyan ya lafto mata uwar siyayya lokacin daze dawo da ita gida tayi lokaci guda kuma ta zaro wani qaramin card, qurama card ɗin idanu tayi zuciyarta na wani irin racing sannan ta shiga danna numbers ɗin jikin katin a jikin wayar sannan ta kara a kunnenta tareda lumshe idanunta tana jiran ya ɗauka.
Can ɓangaren wanda ta kira ɗin zaune yake cikin katafaren ofinshinsa wanda aka qawata da kayan alatu na morewa rayuwa ya ɗora dogaren santala-santalan qafafunsa duka biyun a saman table ɗin dake gabansa, a hankali ya ɗaga hannunsa na dama yana me sassautawa kansa necktie ɗin dake ɗaure a wuyansa.
Qarar wayarsa ce ta katseshi wadda ke ajiye bisa gefansa a nitse yakai hannunsa ya ɗauka tareda zubawa number dake kiran nasa tsimammun idanunsa kamar baze ɗauka ba se kuma can ya ɗaga tareda karawa a kunnensa yay shiru ba tareda yace qala ba.
Daga ɓangarenta Ajiyar zuciya ta sauke me qarfin gaske sannan ta buɗe bakinta wanda yayi mata nauyi tace "yaya Edyan nice mulaikha c.....!!! Se kuma ta fashe mishi da wani irin kuka wanda yasa ba shiri Edyan ya miƙe tsaye cikin kiɗima gamida tsagwaron tashin hankali yana faɗin "meya faru dake mulaikha ? Meyasa kike kuka irin haka?
Edyan ya jefa mata waƴannan tambayoyin duk a lokaci guda, daqyar ta iya buɗe bakinta tace "don Allah partner kazo I wanted to see you tomorrow plss.........!
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya gyara zamansa kamar tana gabansa yace "look mulaikha don Allah ki ɗena kuka kinji babe, kin sani banason kukan ki sabida it really hurts me so please don't cry again OK?
Ɗaga masa kanta tayi kamar yana gabanta lokaci kuda kuma tace "uhm. Murmushi yay kaɗan sannan yace"not hmmm mulaikha na just promise me cewan bazaki sake kuka irin haka ba kinji?
Bakinta ta buɗe a hankali tace "i promise!
"yauwa that's my girl bye. Ya faɗa yana me katse kiran ba tareda ya tsaya jin abinda zatace ba.
Ƙurawa wayar manyan idanunta tayi tana kallon wayar kamar bazata dena ba, tana riqe da wayar wani sabon kiran ya shigo wayar Ummie da sauri ta ɗauka ta kara a kunnenta sabida duk a zatonta Edyan ɗinne ya sake kiranta a karona biyu.
Daga ɗaya bangaren zainab tace "Ummie gaskiya ya kamata ki dawo haka nan wllh sabida bro Qurraty bashida lfy jiya ko office bai samu yaje ba, pls Ummie don Allah ki dawo koke ze iya sanar dake abinda ke damunsa.
Sakin wayar Rabe tayi sabida tsabar bugawar da zuciyarta dayi da mugun qarfi loƙaci guda kuma ta sulale qasa jiɓirrrr kamar zubewar gini............
Chubaɗo ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page:50
*_I Dedicate this special page for you SADIYA SIDI SA'ID (SIDIYA the writer of GIDAN MISBAHU) na rantse da Allah tukuicin Qaunar da kikemin kyautar shafi guda na littafin dana sadaukar miki yayi kaɗan ya zama tukwici a garki, amma nasan Ɗan gidan gima shine ke halin girma duk inda akace akazo al'amarin ki na gado ne bana taka haye ba, na daɗe ina cin karoda mutane daban-daban a rayuwata Amma wllh ban taɓa karo da wadda ta qaunace ni bisa gaskiya da Amana kamar ke ba. I'm so proud of you malamar FARSAFA kokuma in kiraki da kwalba uwar Alkhairi Don bazance Uwar sharri ba 😂_*
*_MASU YIMIN ADDU'AR ALKHAIRI AKAN EXAM ƊIN DANAKE GABATARWA ALLAH UBANGIJI YA SAKA DA ALKHAIRI KUMA YABAR ZUMUNCI❤️_*
___✍️Sulalewar datayi zuwa qasa ne ya bawa hannunta damar danna kiran number Zainab ba tareda tasan tayi hakan ba sabida tsabar tashin han kalin data samu kanta a ciki, daga ɓangaren zainab murmushin qarfin hali ta saki kana tace "Ummien mu!!
Jin sunan data ambata ne yasa Muzaffar dake kwance bisa cinyar mom ya kaleta da idanunsa waƴanda suka canza launi sabida halinda zuciyarsa ke ciki ba tareda ya iya cewa komai ba ya miqa mata hannu alamar ta bashi wayar, ba musu ta zainab ta miqa masa ya karɓa tareda kara wayar a gefan kunnensa yace " Ummiey na!
Wani irin bugawa Qirjinta yayi da qarfin gaske a lokacin data tsinkayi amon muryarsa ta doki dodon kunnenta.
Wani irin zaro ido tayi se kawai ta saki wani irin kuka daga qasan maqoshinta tareda sanya hannunta ɗaya ta rufe bakinta gam dashi, tabbas tasan tayi kewar muryarsa kwatankwacin yanda zuciyarta ke bugawa a ko wace rama, haqiqa yau ta gama tabbatarwa da kanta cewar numfashinta gabaɗayan sa yana fita ne da sirkin ɗigon kewar muzaffar me tsananin gaske a cikinsa, haka kuma batajin cewar zata iya ɗauke kanta daga barin tunaninsa koda kuwa ace badashi zata rayuwa ba a nan gaba!!!
Ajiyar zuciya muzaffar yaɗan sauke sannan yayi murmushi mara sauti yace "Ummie kada ki damu wllh ba wani serious ciwo bane kawai rikicin Qurra ne so ki gama abinda kikeyi a nitse kafin ki dawo. Ya faɗa yana katse kiran ba tareda yaji sautin kukan nata ba ko kaɗan
Miqewa tayi jikinta a mace ta kaiwa Ummie wayarta sannan ta fito ta koma ɗaki ta kwanta sabida wani irim juya mata da kanta keyi ta wani ɓangaren kuma ji take kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito.
*********
A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah kamar yanda moddibo yayi alqawari hakan ne kuwa ya kasance, don haka tun ana gobe ɗaurin Auren Rabe da Bamanga Edyan da mom ɗinsa da kuma zeeyadah suka iso garin, tunda suka yanko hanyar Rugar zeeyadah da Mom suka cika da ɗumbin mamakin yanda jama'ar garin suke Rayuwa ba tareda fargaba ko tsoro ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace "Allah ɗaya gari banban. Dukda kasancewar mom Edyan cikakkiyar Bafulatar yolo hakan be hanata shiga mamakin irin yanayin dajin da Raben ta fito ba, A haka motarsu ta iso tayi parking a gaban gidan still suna qara jinjina lamarin a ransu , Suna tsayawa ba jimawa sega motar su Abie ma ta iso tareda Driver ɗinsa da kuma wasu jibga-jibgan haɗaɗɗun jib baqaqe wuluk se baza qyallin sabunta suke suna take masa baya, sannan suka fito daga cikin motocin duk a lokaci guda.
Da sakin fuska gamida girmamawa Edyan ya isa ga Abie tareda rissinawa ya gaisheshi, fara'ar dake kan fuskar Abie ce ta qaru a lokacin dayaga Edyan ɗin sannan ya amsa masa da kulawa a haka suka antaya zuwa indasu Ummie ke tsaye suna jiran qarasowarsu.
Sosai ummie tayi farin ciki da zuwan Matar C.p ɗin don har hakan ya gaza ɓoyuwa a saman kyakkyawar fuskarta, hugging ɗin zeeyadah Ummie tayi tana Murmushi tace "bansanki ba Edyan kawai na sani shima don yana zuwa gurina ne duk sanda yaje india, nan dai sukai murmushi gabaɗayan su sannan suka antaya zuwa cikin gidan inda bukkokinsu suke.
Sosai Ummie ta taka rawar gani wajen ganin ta cikawa su Mom Edyan da Zeeyadah gabansu ta kayan qwalan da maqwalashe, kafin kace me tuni har Inna Laure ta dama musu lafiyayan Fura da kuma nono wanda yaji Uban suga, sosai Zeeyadah ya buɗe cikinta tasha furar kamar bazata dena ba sabida an jima ba'a gamu ba 😂
Se bayan ta gama cika cikinta ta kalli Ummie tace "Banga Amaryar tamu ba pls where is she?
Hararar wasa Mom ta jefa mata tace "ja'ira se yanzu zaki tambayeta tunda kinci kin qoshi ko? "no wllh mom ba haka bane tunda mukazo garin nan take raina kema ai kinsan hakan. Zeeyadah ta faɗi hakan tana dariya
Edyan ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama hannunsa Rike da babban kwanon sha ya kalli Ummie yace "Ummie Abie yace ki qra masa Suger a ciki. Ya faɗa yana miqa mata kwanon yana murmushi
Karɓa tayi itama tana dariyar tace "hmmmmm nikam ban taɓa ganin mutum me son suger kamar Abie ba ko tsoron shan zaqi bayayi. Ta faɗa tana karɓar kwanon tareda zuba masa suger ɗin ta miqa masa ya karɓa ya fice daga ɗakin, yana fita zeeyadah ma ta miqe tabi bayansa da sauri tace "ya Edyan wai ina ne ɗakin mulaikha ne ?
Murmushi ya sakin mata tareda nuna mata bukkar sannan yay gaba abinsa, da sauri Zeeyadah ta nufi ɗakin cikeda zumuɗin ganin mulaikhanta bakinta ɗauke da sallama ta shiga
A kwance ta sameta idanunta a lumshi bisa qaramar katifarta, da sauri zeeyadah ta isa gareta tareda faɗawa jikinta tana dariya, buɗe lumsassun idanunta Rabe tayi waƴanda sukai mata masifar nauyi akan zeeyada lokaci guda kuma ta miƙe zaune ta rungumeta, kukan data daɗe tana dannewa ne ya samu nasarar kufce mata don hkaa ta shiga rerawa a jikin Zeeyadan tamkar dama jira takeyi ta ganta
Ɗan buɗa idanunta Zeeyadah tayi cikeda damuwa ta zarota daga jikinta tana kallon fuskarta wadda ta jiqe da hawaye tace " meyasa kike kuka irin haka Mulaikha shin bakya tsoron kanki yazo yanayi miki ciwo? Koma dai wani abin ne yake damunki ne?
Hannunta tasa ta goge fuskarta sannan ta kama hannun zeeyadah tace "ina so naga Partner yanzu pls!
Wayar hannun zeeyadah ta karɓa da sauri ta shiga kiran Edyan, bugu ɗaya ya ɗauka tareda faɗin ya akai ? Duk a zatonsa zeeyadah ce
Bakinta na Rawa tace " i wanted to see you plssssssss!
Take qirjinsa ya wani irin buga wanda sam be shiryawa hakan ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yace "ok bt where are you nw?
Zan jiraka a bayan gida wurin shanu. Rabe ta faɗi hakan a taqaice
Katse wayar yayi tareda zubawa qasan gurin idanu sannan ya miqe ya fita yabarsu Abie da moddibo sunata hira abinsu, jikisa a saluɓe haka ya isa gurin ya sameta a tsaye ta sarqe hannayenta duka biyun a qirjinta tana jiran isowarsa.
Ya jima a tsayen sannan ya buɗe baki yace "kinaso ki faɗamin wani abun ne? Hawayene suka zubo mata sannan tasa hannunta ta goge ba tareda ta kalleshi ba tace " inaso na gaya maka abinda ya kamata ace ka sani ne patner, dukda cewar kusancinka da muzaffar ya wuce akirashi da abota sedai a kira hakan da sunan ƴan'uwantaka, partner Muzaffar yanada wata budurwa a Rayuwarsa wadda ya jima yana ɓoye abinda ke ransa tsahon lokaci.
Ɗago idanunsa yayi cikeda matiqar kaɗuwa ya dubeta yace "wannan wace irin magana ce kikeyi haka Mulaikha?
Ae haka maganar take Partner amm......." toni meyasa kike zaɓi da ki gayamin wannan wannan maganar bayan kuma shida bakinsa be taɓa gayamin ba?
Hawayen daya zubo mata ta sake gogewa tace " wasu maganganun da wanda yake qaunarka kawai zaka iyayinsu Yaya Edyan, musamman akan abinda ya shafi rayuwar ka!
Ni kawai abu ɗaya na sani shine wannan Auren daza a ɗaura min a gobe muddin na Bari akayishi shine kuskure mafi girma da zan aikata a rayuwata, wllh partner banason shi kaina gaba ɗaya ya gama kullewa banaso na aikata abinda ze taɓa kimar mahaifina!!!!!!! Ta fadi hakan tana fashewa da wani irin kuka.
Kafeta kawai da idanu Edyan yayi a ranaa kuma yana aiyana wani al'amari wanda shi kansa bazece ga matsayar daya samu a ransa ba, tabbas yasani har cikin zuciyarsa yake qaunar Rabe so me tsananin gaske, to waishin ta ina ma ya kamata ya fara ne?
A hankali yake jan qafarsa harya bar kurin ba tareda ya rarrasheta ba, guri ya samu daga can nesa da gidan ya zauna har yammacin al'muru ya fara ketowa, a hankali yaji saukar hannun mutum a saman kafaɗunsa don haka ya ɗago da sauri yana kallon wanda ya dafashin.
Moddibo ne tsaye bisa kansa yana murmushi yace "ai tun ɗazu nake cigiyar ka shine Abou muzaffar yace min kanata nan wurin. Ya faɗi hakan yana zama daga gefan Edyan ɗin, shiru ne ya ratsa gurin tsahon lokaci sannan moddibo ya dubeshi yace " na rigada na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna. Da sauri Edyan ya ɗago yana kallonsa zeyi magana moddibo ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Ba yanzu ba tukunna zan baka damar magana amma fa har sena gama tawa tukunna.
Wanda takeso ɗin na zauna dashi a yanzu dukda cewar shiɗin be taɓa furta abinda ke zuciyarsa akanta ga kowa ba, dukda cewar yasan hakan kurkurene me girman gaske amma kuma yake qoqarin ya aikata ɗin, nariga na gama Fahimtar komai Edriss nariga na gama gane wanda Rabi'atou take Qauna har cikin Ranta,, idan harna Aurar da ita ga wanda bataso tabbas na cutar da ita mafi girman cutarwa, nasani damace ubangiji ya bani a yau wadda zan iya gyara kuskuren danake qoqarin tabkawa a baya ta hanyar turo min kai zuwa nan, koda wasa bazance Bamanga da Rabi'atou basu dace da juna ba amma to ya muka iya da zannan abinda qaddara tazo mana dashi?
Zuciyata tana gayamin cewar kaine mutumin dayafi dacewa daya mallaki Rabi'atou. Da sauri Edyan ya kama hannun moddibo lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga fuskarsa yace "aa baba sam be kamata kayi haka ba, kamata yayi ka zauna da Rabi'atou kaji ra'ayinta akan Aurensu da bamanga muddin ta nuna batason haka toseka sake bata wata damar a karo na biyu inyaso seta gaya maka waye zaɓin ranta da bakinta!!
Da hka hirar tasu ta dasa Aya.
Ɓangaren su Mom Edyan da Ummie kuwa sosai suka kacame da hidimar dafe-dafe da kuma sarrafa wasu abubuwan daza'a gabatar na al'adah, sosai mata suka cika gidan anata shewa da kuma aikace-aikace kafin kuma gari ya waye a shaida ɗaurin Aure. Bayan sallar Isha su Abie da Edyan da kuma gurds ɗinsa suka yada zango a farfajiyar qofar gidan kafin lokacin kwanciya yayi, miƙewa moddibo yayi ya nufi bukkar Rabe da sallama ɗauke a bakinsa ya ɗaga labulan dake saqale jikin bukkar, zaune suke ita da zeeyadah tanata faman bata labarin school Rabe nata murmushi a haka ya qasa shigowa ɗakin, cikeda girmamawa Zeeyadah ta gaisheshi sannan ta miqe a nitse tabar ɗakin don ko ba'a faɗa mata ba tasan magana zayi da ita wadda take buqatar sirri.
Zeeyadah na fita ya nemi guri ya zauna daga ɗan gefanta kaɗan yana kallonta kimanin wasu mintuna Sannan yay ajiyar numfashi yace" idan kinada matsala da wannan auren sam karki ɓoye min kawai ki sanar dani insha Allah zaki sameni a matsayin uba me adalci a gareki.
Matsowa tayi tareda kwantar da kanta bisa kafaɗunsa tace " aa baba sam banida matsala da Auren bamanga sabida ya cancanci mallakata tsahon lokaci, don haka kawai a ɗaura wllh har cikin raina na amince da hakan!!!!
Ta faɗa tana kallonsa tareda qoqarin mayar da kwallar dake qoqarin zubo mata, ko kaɗan bataso ta nuna gazawarta kodan sabida ta tsirar da kimar mahaifinta a idanun jama'ar garinsu, badan haka ba tabbas bataga dalilin dazesa tabar zaɓin ranta ta ɗau wani ba.
Duk yanda moddibo yaso ya gano abinda take ɓoyewa a ranta ta hanyar kallon idanunta sam ya kasa gano komai dole ya tabbatarwa da kansa cewar lallai har cikin ranta takeson Auren Bamangan. Ƙarfe tara na dare dedai Kakar Rabe wadda ta haifi mahaifiyarta sukazo daga Yolah tareda qannen mahaifiyarta guda biyu, sosai sukai farin cikin da zuwan nasu misamman ma Rabe wadda har hakan ya gaza ɓoyuwa a tareda ita a haka dai gidan ya dinga kacamewa da abikanan Arziqi tamkar a lokaci za'a ɗaura mata Auren.
****
Washe gari tunda sanyin safiya jama'ar Rugar Arɗo suka gama hallara a bakin qofar gidan moddibo wanda aka shimfiɗa manyan tabarmin kaba fa farfajiyar, Abie ne ya fito sanye cikin wata rantsatsiyar gizna fara fat da ita wadda taji uban aiki irina manyan masu kuɗin dake matiqar jida kansu, kallo ɗaya zakayiwa Abie ka fahimci zallar kar da suke da muzaffar tamkar Abie yayi kaki, bayansa kuma moddibo ne shima sanye cikin wata hamshaqiyar gizna farar tas da ita wadda tabawa kyawunsa damar fitowa abinka da bafulatanin Asali wanda yay gadon kyau ba taka haye ba lol😂
A haka suka fito suka zazzauna bisa tabarmin inda Jama'ar ke zaune, can na hangi Oga Edyan ya ɗau harami shima cikin wata shadda irinta mutanam sinigal brown wadda tayi masifar masa kyau, sedai fuskarsa sam babu yalwar murmushi kamar yanda ya saba. Nan moddibo ya shiga gaisawa da abokan arziqi har ya kammala amma shiru babu labarin Isowar iyayen Ango, tun anasa ran isowarsu har mutane suka fara cire rai da zuwan nasu nafa aka fara tsegumi qana nan maganganu suka fara tashi, can kamar daga sama aka jiyo muryar Hashimu Maroqi yana faɗin "Sanarwa daga bakin uban Ango Jauro ibrahimu Bawuro cewar sun janyen batun Auren Ɗansu Bamaga da kuma Rabi'atou ɗiyaga Moddibo ɗan lamidon Arɗo bisa wani babban dalili da basu baiyana ba, fatan malam moddibo ze gafarce su.
Take gaban moddibo yay wata irin faɗuwa lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da qwallar baqin ciki, yanzu shikenan Bamanga ya gama yiwa Rayuwar ɗiyarsa illah sabida a tsarin al'adarsu muddin wata matsala ta gifta a ranar ɗaurin Aurenki har takai ga an fasa ɗaura auren tofa har Abada bazaki taɓa yin aure ba a haka zaki zauna har mutuwarki ta riskeki.
Kamar daga sama Ya tsikayi muryar Edyan a saman kunnensa yana faɗin , dama can Mulaikha ba sa'ar Aurensa bace don haka ka koma ka sanar da qananan mutanen da Suka turoka cewar a yau base anjima ba za'a shaida ɗaurin Auren Rabi'atou da wanda ya dace da ita.
Edyan ya faɗi hakan yana me zaro bandir ɗin ƴam dubu-dubu Guda biyu daga aljihunsa ya ajiye a gaban moddibo yace "Baba ina me nemawa kaina Aurenta idan har zaka bani, lokaci guda kuma Abie ya matso dabda moddibo yace "ni nan zan zame masa wakili daze karɓa masa Aurnta, cin qanqanin lokaci moddibo ya ɗago manyan idanunsa yana kallon Abie cikin wani irin yanayi wanda yafi kamada na zallar kaɗuwa yace"................
Sushmah ✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page :51
*_WRITING BY: CHUBAƊO_*
____✍️"taya hakan zata kasance kuma Abdulwahab? Murmushi abie ya saki irin nasu na dattijawa yace "karka damu Moddibo sam be kamata mutanan da aka tara sabida ɗaurin Auren nan a bari su watse haka nan ba, ɗan jim yayi kaɗan sannan ya maida kallonsa ga Edyan Yay masa murmushi se kuma ya kalli moddibo da malam iro wanda sukai shiru suna nazarin abin a ransu, cikin mintunan da bazasu gaza 5 ba jama'ar dake gurin suka shaiɗa ɗaurin Aurn Rabe da wani daban saɓanin Bamanga wanda iyayensa suka janye Auren sabida wani dalili nasu na daban wanda har yanzu basu firta ba.
Nan da nan aka shiga raba Goron ɗaurin Aure da kuma manyan alawori masu tsadar gaske kamar dama an shiryawa abin, zanso team Edyan kuga yanda ango Edris yake washw baki tamkar wanda akaiwa bisharada gidan Aljanna, a haka taro ya watse kowa yana sambarka tun a yammacin Ranar iyayen Amarya da kuma gwaggwanninta sukai shiga kimtsa amarya sabida gabatar da bikin al'ada kamar yanda suka saba, sedai duk yanda Edyan yaso ya haɗu da ita sam abin ya gagara sabida an riga an keɓanceta za'a gabatar mata da abinda suke kira da biddom, idan akace biddom ana nufin wankan amaryar da fulanin daji keyiwar ɗiyarsu ne da zallar madarar shanu gamida wani sinadari na musamman wanda ya kasance sirrin su ne musamman ta ɓangaren mallakar miji da kuma inganta rayuwar Aurataiyarsu.
A lokacin dasu Ummie da mom sukaji da wanda aka ɗaura Auren sosai abin ya girgizasu musamman ma Ummie, ita kuwa mom Edyan sosai hakan yayi mata daɗi tamkar dama abinda take burin ya kasance ɗin kenan, a haka suka gabatar da bikin al'adar jikin Ummie a matiqar sanyaye don harga Allah tana matiqar tausayawa muzaffar Ɗinta, to amma yata iya tunda haka zanan qaddara yazo masa dashi.
A gurguje pls
Bayan an kammala bikin al'adar sosai Zeeyadah ta kaɗu da yanayin da Rabe ke ciki sabida zallar damuwar dake cinta a ranta, gaba ɗaya duk ta gama ramewa a tsaye amma sabida tsabar qarfin hali irin nata taqi bari wani yasan halinda zuciyarta take ciki, babban abinda ke qara ɗaga mata hankali shine ta ina zata fara rayuwar da Bamanga a matsayin mijin Aurenta? Sabida harga Allah bata san abinda ke faruwa da lamarin Aurenta ba, Yafendunta Bintu ce ta shigo ɗakin da aka gama kafata da murmushi akan fuskarta tace " Baddo.
Kuka Rabe ta sakin mata lokaci guda kuma ta faɗa jikinta tana rerawa, kaf cikinsu babu wanda yay yunqurin hanata kokuma rarrashinta badan komai ba sedan ta samu peace of mind, seda tai me isarta sannan tasa tafukan hannunta tana share hawayen kamar ba itace ta gama gurzar kuka a jikin Yafendu Bintu ba, Inna Laure ce ta shigo ɗakin tana jan qafa da qyar hannunta ɗauke da wata qaramar qwarya wadda akai mata jiqo na musamman ta miƙawa yafendu Binto tace " maza ki bata ta shanye zuwa anjima Ammi Ruqatu zata kawo ɗayan se'a jiqa kafin wayewar garin gobe masu ɗaukar Amarya suzo.
Murmushin Yafendu Bintu tayi tace "Ae lallai Laure kin dage sekin haɗa ƴar nan taki Allah dai ya saka miki da alkhairi bisa ɗawainiyar da kikayi, Allah kuma ya rabaki da cikin jikinki lfy.
Kasa magana Inna laure tayi sabida wata qwalla data taso ta kwanta a saman qwayar idaninta, nan da nan ciwon dake cinta a ranta ya dawo mata sabo fill a lokacin data tuna cikin su waye a jikinta , da hanzari ta juya ta fice tana me zubarda kwallar baƙin ciki da nadama.
A haka dai abubuwa suka dunga tafiya masu daɗi da marasa daɗi Har garin Allah ya waye Kusan a tare su mom suka fara shirin komawa Abuja, gabaɗaya bakin Edyan ya gaza rufuwa sabidaTarin farin cikin Da yake ciki
Qarfe shidan safe daidai Aka kimtsata cikin wani Blue ɗin saqi wanda yay masifar karɓar jikinta, gabaɗaya fuskarta an zane mata ita da wani farin fenti gamida ratsin yallow, kallo ɗaya zakai mata ka tabbatarwa da kanka cewar kaka cikakkiyar Asalin BAFULATANAR DAJI wadda ta amsa sunanta ƴar fillon gaske babu sirki. Ɗakin Moddibo aka fara kaita, nan ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki wadda a zuciyarta takejinta tamkar nasihar bankwana yake mata, sosai take kuka daga cikin mayafin saqin da aka rufe mata kanta dashi, ba zato ba tsammani ta miqe ta isa ga mahaifin nata ta rungumeshi tamau tana gurzar kuka kamar bazata dena ba. Daqyar suka ɓanɓareta suka fita da ita zuwa bukkar inna Laure, nan ma ba qaramin kuka Rabe tayi ba hakama Ɓangaren Lauren Itama, nan dai laure ta roqi yafiyar mahainiyar Allah Rabe, duk yanda taso ta miqe ta isa gareta kasawa tayi sabida nauyin cikin dake jikinta, har gabanta Rabe ta isa ta durqusa daidai yanda zata iya rungumarta tace "dukda cewar kin raine ni bada soyayya ba wllh kodedai da rana ɗaya bantaɓa jin cewar na tsaneki ba, komai ya fito daga bakinki akaina idan kika furtashi ban taɓa sashi a raina ba balle harya dameni sabida nasan komai na duniya yanada limit, don haka kisa a ranki cewar kema matsayin uwa kike a gareni na yafe Miki har Abadah!!!!!!
Ta faɗa tana fashewa da kuka.
Gaba ɗaya Laure ta kasa magana sabida kukan datakeyi a haka aka fita da Rabe zuwaga kakarta wato Mahaifiyar Babar ta, nan ma nasiha sosai Gwaggoji tayi mata me ratsa jiki akan Rayuwar duniya da kuma mutanan dazatai Rayuwa dasu waƴanda suka kasance a kwai banbanci me tarin yawa a ɗabi'unsu da kuma irin nata, nan dai Rabe ta Fahimci Auren waye a kanta.
Ko kaɗan batai baqin ciki dajin wanda ta Aura ba abu ɗaya kawai ta sani shine komai Muqaddari ne daga Allah, haka kuma ba komai muke so a rayuwa muke samu ba. Duk inda miji na gari me tattalin matarsa yakai wllh tasan Edyan ya wuce haka shiyasa bazata taɓa baƙin ciki da Aurensa ba indai har ta cika ƴar Halak kuma wadda tasan halacci.
Duk irin sabon dake tsakanin moddibo da ɗiyarsa sam hakan besa ya zubar da hawaye ba don haka har suka fito da Abie idanunsa rass kamar baya kewarta, hannun Abie ya kama yana kallon tsakiyar idanunsa yace "zan roqeka wata alfarma Alhaji tareda yaqini da sanya ran cewar zakayi min ita.
Da kulawa Abie ke kallonsa yace "kafi qarfin haka a gurina wllh kawai ka faɗi me kakeso wllh zanyi maka shi.
Murmushi moddibo yayi wanda ya baiyana dattijantakarsa yace "so nake da zarar kun isa inda zakuje don Allah karkubar Rabi'atou ta kwana a wani gida wanda bana mijinta ba.
Da kulawa Abie yace "insha Allah zan cika maka wannan alqawari naka kuma nida kaina zan kaita har ɗakinta ba tareda na fari an tsaya gabatar da wata bidi'a ba.
A haka ummie ta fito jiki a mace sukai sallama da kowa dake gurin suka shiga motocinsu, a wannan halin babu abinda Ummie ke tunani kamar gudan jinin ɗanta Muzaffar wanda tasan wajibi ne ya shiga gagarumin tashin hankali idan har ya samu wannan labarin marar daɗin ji a kunne.
A haka suka isah Airport, bayan zuwansu da minti 15 jirginsu ya ɗaga zuwa birnin taraiya, jirginsu na sauka iyalan C.p suka tarar da manyan motoci na jiran isowarsu, nan dai sukai Sallama da Mom Edyan da Ummie kowa yayta kansa akan cewar insha Allah qarfe 4pm zasuzo ɗaukar amaryarsu. Sam ba haka Edyan yaso ba yaso ace yay gabada matarsa amma kuma sam besamu damar hakan ba.
*****
Ɓangaren Muzaffar kuwa tun bayan lafawar da ciwon da kansa ke masa ya koma bakin aikinsa, duk irn zafinda zuciyarsa keyi sam hakan besa ya baiyanawa Mom da Fadilah Damuwarsa ba, Baba Hajara ce kawai tasan Halinda yake ciki sabida irin sonda take masa, dukda kasancewarta me aiki a gidansu shi sam ba'a hakan yake kallonta ba kallon kakarsa yake mata kuma wadda yake Qauna.
Zaune yake a Office se faman danna system yake amma sam hankalinsa baya taredashi, haka kawai yakejin gabansa na faɗuwa wanda gabaɗaya ya rasa dalilin hakan, a haka ya mike jikinsa a mukun mace yabar office ɗin zuwa gida.
Ɓan garen Edyan kuwa yana zuwa gida wani sabon uban wanka ya ɗauka cikin wata shaiɗaniyar shadda milk colour wadda kera baza uban yararin tsada da maiqo, fakar idon mom yay ya ɗau motarsa ya nufi gidansu Muzaffar don ganin Amaryarsa sabida bayajin cewar ze iya jurar har zuwa Lokacin dazasu kawo masa ita.
Parking yayina tsanaki ya sakko yana qawata fuskarsa da wani hamshaqin murmushi, a nitse ya fara takawa harya isa part ɗin muzaffar don duk a tunaninsa yana ciki, a katafaren perlourn Aminin nasa yayiwa kansa masauki tareda zaro wayarsa yana qoqarin kiran muzaffar ɗin.
A nitse gurds ɗinsa suka parker motar ya fito batareda ya tsaya jiran su buɗe masa ba ya nufi part ɗinsa, duk irin qarar da wayarsa keyi sam bebi takanta ba harya shiga parlourn
Tsayawa yayi cak yanabinsa da kallo don beyi tsammanin ganinsa ba sam a wannan lokacin, murmushin qarfin hali ya sakar masa tareda qarasawa gareshi fuskarsa ɗauke da mamaki yace " uhmmm looking so masha Allah kamar wani sabon ango. Muzaffar ya faɗi hakan yana wani male baki cikeda tsokana
Dariya Edyan yayi yace "ae mana ai bakayi makuwa ba pls go and take Shower kazo ka rakani ɗakin matata.
Ɗan buɗe manyan idanunsa muzaffar yayi yace "your not serious. "wllh da gaske nake inada ɗakin matana zaka rakani an ɗaura min Aurn bazata yau ɗinnan ba tareda na shiyawa hakan ba amma idan kana tantama akai ka tambayi Abie ze gaya maka.
Ɗan jim kaɗan muzaffar yayi amma dayake yasan Edyan ɗin be taɓayi masa qarya ba yasa har a ransa ya amince da abinda ya faɗa ɗin. Tilasta masa Edyan Yayi har seda yay wanka kuma ya buɗe drower ɗinsa ya ɗakko masa wata milk ɗin shadda sak ta jikinsa ya bashi ya saka sannan ya ɗora hula tareda ɗaura wani shaiɗanin agogon rolex wanda ya haska tsintsiyar hannunsa, take ya baiyana a Cikakken matashin ɗan kasuwar nan meji da nairah wati C.e.o of zafar Enterprises
A haka suka fito harabar gidan se baza qamshi suke, yayi mamaki sosai dayajiyo hayaniya hirar mutanen gidan a ɓangaren Ummie, don haka kai rsaye can suka fara nufa, da sallama suka shiga falon buskarsa babu yabo babu fallasa, Abie ummie mom Fadilah Zainab kai harma da baba hajara duk suna zaune a falon except Amaryar Rabe.
Kafesu da idanu gabaɗaya jama'ar dake falon sukayi a nitse suke takowa har suka shigo falon suka zauna babu wanda yace "dasu qala har sukasha jinin jikinsu, kallon ummie Muzaffar yayi yace " Ummie sannunku da dawowa ya hanyar?
Murmushi tayi tace "lfy lau son ya jikinta?
Da kulawa ya amsa amma kuma bisa ga mamakinsa babu fara'a kota ɗigo a saman fuskar mom, kallonsu Baba hajarah tayi tace "Edirisa Ashe kuma ka ɗauka Aure, to ubangiji ya sanya alkhairi.
Sosa kai Edyan yayi cikeda jin kunya. Muzaffar zeyi magana kenan Abie yace "oya ku tashi muje, ba musu suka miqe sukabi bayansa.
Parking space direct Abie ya nufa suna biye dashi, wata baqar bugati suka nufa Abie ya bude bayan motar ya shiga sannan Edyan ma ya shiga muzaffar kuma Ya shiga baya Divern yaja motar zuwa cikin can saman layinsu kaɗan, tun kafin su isa inda zasuje abie yay dailing wata number be jima yana magana ba ya katse, a gaban wani tanfatsetsen gida na gani na faɗa suka tsaya sannan Abie ya matsa wani qaramin remote take get ɗin ya buɗe suka kunna kai zuwa cikin gidan.
Parking sukai a haɗaɗɗen parking space ɗin dake gurin sannan suka fito gabaɗayansu amma banda driver ɗin, cikin gidan suka tasarwa kowa da abinda yake saqawa a cikin ransa daga muzaffar ɗin har Edyan, a haka suka shiga perlourn da sallama take wani qamshi na musamman ya daki hancinan su, wani irin lumshe idanu sukai duka su biyun
A gurguje pls
Fadar irin tsara yanayin falon a gareni abu ne mawuyaci, don hkaa kawai kuyi hasashen haɗuwar gidan da kanku, zama abie yayai lokaci guda kuma ya ɗago yana kallon muzaffar yace "haqiqa nasan abinda zan sanar dakai a yanzu dole ne ya ɗaga maka hankali muzaffar , amma kuma idan kayi haquri da irin hukuncin dana zartar a kanka na tabbata kaima zuriyarka da zaka haifa nan gaba wajibine suma suyi maka biyayya kamar yanda nakesa ran cewar zakayi min yanzu, na zartar da wani hukunci akanka wanda nake da tabbacin cewar idan har kayimin biyayya akansa zaka samu sakamako me girma a gurin Allah. Haka kuma rayuwarka zatai albarka sakamakon biyayyar dakayi min..
Ɗagowa yay da manyan idanunsa yana kallon Abie wanda shima ɗin shi yake kallo yace "bt abie wannan wani irin abu ne haka Dayasa kake min wannan dogon jawabin?
"Aure na ɗaura maka muzaffar batareda sanin ka ba Bayan an kammala ɗaura Auren Edriss!! Abie ya faɗi hakan a taqaice
Gabansa ne yay wani irin faɗuwa a lokacin dayaji abinda Abie ɗin ke faɗa, lokaci guda kuma yaji kansa ya wani irin sara masa
Ajiyar zuciya Abie ya sauke me ɗan nauyi sannan yace "wannan abinda na zartar a gareka iko ne dane jin cewar inadashi akanka, haka kuma nan gidan ka ne daga yau kar in sake ganin qafarka a gidana ba tareda wani babban dalili ba har tsahon sati guda, Sannan kuma ban amince ka cutar musu da ƴa ba don kawai tana qaunarka wajibi ne ka kyautata mata sabida ita ɗin amanarka ce, muddin ka zalinceta dedai da ɗigon qwayar zarra bazan taɓa yafe maka ba.....
Abie ya faɗi hakan yana miƙewa daga inda yake ya kalli Edyan yace "muje in kai maka matarka kamar yanda nayiwa mahaifinta alqawari. Be jira cewarsa ba yay gaba Edyan na take masa baya suka bar Muzaffar zaune sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki.
Ya jima a zaune yana tufka da warwara gefe guda kuma ga wani masifar ciwo da kansa ke masa, miqewa yayi a hankali zuciyarsa na suya ya nufi wani ɓangare dgaa hannunsa na dama wanda ya tabbatar Da kansa cewar A nan ɗakuna gidan suke, qofofi ya gani guda biyu duk suna facing juna tsaki yaɗan ja kaɗan don harga Allah beyaso ya buɗe wanda maiyar yarinyar da aka liqa masa take.
A hankali ya isa ga ɗaya qofar wadda tafi kusa dashi ya kara kunnensa kimanin ƴan mintuna sannan ya ɗauke da sauri sabida shashsheqar kukan dayaji, tsaki yayi sannan yabar gurin da sauri zuwa ɗaya ɗakin ya shige abinsa, bin ɗakin ya dingayi da kallo sannan ya hau buɗe drowers na ɗakin yana bin kayan da aka zuba a ciki da kallo kamar dama shiya zaɓo abinsa.
Toilet ya shiga ya sakarwa kansa ruwa kimanin tsahon lokaci sannan yay wanka tareda ɗaura al'awalar sallar isha ya fito ɗaure da towel ba abinda ya shafawa jikinsa a ranar duk son qyaleqyalensa, wasu kayan Baccu ya ɗakko qirar Pj-mas Ya saka jikinsa Sannan ya tada sallah abinsa, ya daɗe yana addu'a bayan ya idar sannan ya miqe ya kashe fitilar data gauraye ɗakin ya haye kan makeken royal bed din dake ɗakin.
Kamar daga sama ya dinga jin shasheqar Kuka kamar a ɗakin akeyi, duk yanda yaso yay bacci kasawa yayi sabida sautin kukanta ya gama cika masa ciki da takaicinta. Agogon dake manne a jikin gadon ya kalla yaga har 12 tayi ne yasa yaja wani uban tsaki ya miqe a fusace ya nufi ɗakinta, tura qofar yayi lokaci guda kuma ya fara bin ko wace kusurwa ta ɗakin da kallo har idonsa ya sauka akan dogayen zarazaran yatsun Qafarta, kwance take kan makeken gadon dake ɗakin ta bawa ƙofar shigowa ɗakin baya babu abinda take se kuka wanda har hakan ya haifar mata da dashwar murya, jikinsa ne yay mugun sanyi daya tunada maganar Abie don haka a ɗaqile kamar an masa dole yace "malama ba kuka zakizo kisani a gaba kinayi min ba, dama tunda kika Auri irina ai kinsan me kika Aura ki tashi ki shiga toilet kiyo alwala ki sameni a ɗakina muyi sallah.
Ya faɗa kamar wanda akayima dole, juyawa yayi ya fice seda ta tabbatar da fitarsa sannan ta miƙe a hankali ta shiga toilet don cika umarninsa, duk irin yanda taji zafin kalamansa besa taqi bin umarninsa ba ta jima a banɗakin sannan ta fito ta ɗauki qaton mayafinta da aka kawota dashi me launin Royal blue ta fita zuwa falon kanta a qasa.
Tsaye ta sameshi saman dadduma ya wani haɗe rai kamar yaga mala'ikan mutuwa, ko kallonta beyiba ya daidata tsaiwarsa bisa daddaumar ya tada sallarsa, itama tsayawa tayi a bayansa sannan ta kabbara sallar basu jima ba suka idar a ranta tana me tausayin makomar ta.
Ya jika yana tasbihinsa ba tareda ya juyo ba harya fara jiyo hammarta alamar tanajin bacci sannan ya juyo gareta yana wani male baki kamar yaga kashi yace " ki buɗe fuskarki malama zan miki tambayoyi akan abinda ya shafi addini!
Gabanta ne yay wata irin faduwa a lokacin data tsinkayi Amon muryarsa a cikin dodon kunnenta, da wani irik mugun sauri ta yaye mayafin saqin dake jikinta hannke yay daidai da saukar idanunsu cikin na juna!!!!!
Bakinsu na rawa suke kallon juna ba tareda sun samu zarafin iya futa komai ba Muzaffar ya wani irin fuzgota Ta matso dabdashi, nan da nan jikinsa Ya ɗau rawa daqyar ya iya buɗar baki yace "m....m....my...fu...fu....fulani girl!!!!!!!!
Comment
Nd
Share
Don't forget to vote on whatpad pls
Sushmah✍️
[3/3, 5:40 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
Page:52
Writing by: chubaɗo✍️
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
____✍️Kafeshi tayi da manyan idanunta lokaci guda kuma ta faɗa jikinsa tana faɗin " Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimussalihata se kuma ta saki kukan daya taso mata. Wani irin farin ciki ne ke kwarara a saman zuciyarta wanda bakinta da gangar jikinta sunyi kaɗan su iya Expressing ɗin irin mode ɗin datake ciki, a ɓangarensa shima hakanne don haka ya sake qanqameta cikin faffaɗan qirjinsa wanda yayi mata masauki dashi.
Zare jikinsa yayi daga nata tareda saita goshinsa Deda danata har hancinsu na gugar na juna wanda hakan ya haifar musu da Sarqewar numafashi me ɗauke da wani sirrin magana ɗisu A cikinsa, da hanzari ya zare jikinsa daga nata Ya nufi daddumar da suka idar da Sallah ya fuskanci gabas donyin sujudu shukur duk a sanadin mallakar zaɓin ransa dayayi a matsayin matar Aurensa, ya jima a sujjadar sannan ya ɗago Tareda zuba mata tsimammun idanunsa waƴanda ke cike taf da zallar sonta gamida zazzafar Qaunar ta.
Rasa inda ze tsoma ransa yayi sabida tsabar Farin cikin dayake ciki, babu abinda yake maimaitawa a ransa se Alhamdulillah inda wani ɓangare na zuciyarsa ya dinga sufawa iyayensu Addu'ar alkhairi wadda ta haɗa da yi musu fatan liɗifin duniya da kuma na lahira. Ɗagowa tayi tana son ta saci kallon handsom face ɗinsa aiko caraf idanunsu suka sarqe cikin na juna, Kashe mata ido ɗaya yayi da sauri ta sauke idonta qasa don bazata iya jura ba
mikewa yayi zuwa kitchine Donya sama mata abinda zata sa a cikinta, Bin ko Wace kusurwa Dake kitchine ɗin ya dingayi da kallo kamar me neman wani abu, wata qatuwar leda ya gani fara A ajiye bisa kan sink direct ya nufeta ya fara buɗewa don ganin abinda ke ciki, da wasu manyan daqwalen kaji yaci karo se tiriri Da baza qamshi sukeyi sunji uban kayan haɗi wanda yafi kamada na musamman, ɗayar ledar kuma manyan fresh milk ne a ciki Na qatuwar roba guda biyu masu madaidai cin sanyi
Flet ya ɗauka meɗan girma ya saka kazar Guda ɗaya a ciki tareda glass cup guda biyu se kuma sansanyar fresh milk ɗin itama daga gefen farantin ya fita xuwa falo, a inda ya barta a nan Ya dawo ya sameta kanta a qasa.
murmushi ya sakin mata cikeda shauqin sonta ya Ajiye flet ɗin tareda janyota jikinsa cikeda tattali Ganida zazzafar qaunar ta yace "are you hungry?
Nodding kanta kawai tayi sabida wani abu datakeji yana wani irin taso mata a sakamakon haɗuwar da jikinsu yayi dana juna, a nitse ya zuro ɗaya hannunsa na dama Ta bayanta ya janye mayafin Saqin dake jikinta wanda yake ganin tamkar yana shiga rayuwarsa ne ta hanyar zama hijabi a tsakankinsa da kyakkyawar fuskarta da tasa, Nan take bakin gashinta wanda yaji uban gyara ya baiyana a gareshi se baza wani tattausan qamshi yakeyi.
Wani irin yanayi ne ya baqunci gaba ɗaya sassan gabobin halittar dake jikinsa take yanayin ya haifar masa da wata irin gagarumar kasala Wadda ke ɗauke da zallar muradin, so gently ya fara feeding ɗinta tana ci shima yana ci har suka qoshi Dukda cewar a takure takejin kanta sabida wasu qananun abubuwan dake gudana a tsakanin su, kayan da suka gamaci ya tattara sannan ya miqe ya kai Su kitchine ya dawo ya kama hannunta suka nufi bedroom ɗinsa saɓanin nata
Be dire ko ina da ita ba se Cikin katafaren toilet Ɗinsa ya zaunar da ita bisa wata qaya taccen wani abu wanda yafi kamada kujera amma kuma A zahiri ba kujerar bace, sabon expensive maclean ɗin dake saqale ya ɗaukko tareda sabon brush ya nufota ya fara Nannaɗe mata rigar dake jikinta Don gudun karya jiqa mata jikinta, take fararan santala-santalan cinyoyinta suka baiyana gareshi ba tareda wani shamaki ba, zuciyarsa ce ta amsa da qarfin gaske take jinin jikinsa ya fara tafasa kamar wanda ake jonawa lantarki, a daddafe yay mata brush ɗin cikeda zallar nuna kulawarsa gareta harya gama mata shima yayi nashi, ko kaɗan bata kawo komai a ranta gameda shi ba itadai kawai ta miqawa Allah lamarinta ne tunda tasan baze taɓa cutar da ita ba, tsinkayar muryarsa tayi a tsakiyar kunnenta Cikin wani irin sauti wanda ya kasance baqo a gareta yana faɗin "do you want to Bath?
Da wani irin sauri ta ɗago tana kallonsa se kuma tayin saurin sauke idanunta Qasa aa hankali cikin sanyinta tace " no
Kama Hannunta yay suka fice daga toilet ɗin tareda zaunar da ita bisa dogayen laps ɗinsa , a hankali yake binta da kallo tun daga kan yatsun hannunta har zuwa kan dukiyar fulaninta, sosai yaji wani irin abu nabin jinin jikinsa lokaci guda kuma yaji tamkar tana fuzgar zuciyarsa zuwa gareta Ne, Se'a lokacin ya samu zarafin qare mata kallo sanye take cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar riga less fari me Yarfen blue a jikinsa wanda ya kasance me taushin gaske Sosai rigar ta mugun kmata daga saman qirjinta gashin kanta gaba ɗaya a waje yake se wani uban light make-up da ummi tasa akayi mata tun bayan zuwansu garin Me shegen kyau, Gabaɗaya a takure takejin kanta musamman yanda taji mazaunanta akan Abinsa lakadan ba ajalan ba 😂
nasihar da ummie tayi mata Ɗazu ce ta fara dawo mata cikin kanta tamkar a lokacin takeyi mata ita, babban abinda yafi komai tsaya mata a rai shine abinda mom Edyan ta dinga gaya mata Tun a cikin jirgi ne akan zamanta kewar rayuwar Aure da kuma abinda shi kansa Auren ya qunsa, ta gargaɗeta sosai akan cewar karta taɓa bari tayiwa mijinta gaddama akan komi koda kuwa tanajin zafin abinda yake gudanarwa a gareta ne. Lallai ta zama me biyayya a gareshi tareda karɓar duk wata larura tasa
A hankali taji saukar tattausan red lips ɗinsa a saman nata wanda hakan yasa ta dawo daga duniyar tunanin data afka, wani irin kissing yake mata tamkar ze cinyeta ɗanya nan da nan kuwa ya fara birkita mata lissafi, bagon yanayin data samu kanta a ciki ne ya haifar mata da rawar jiki tamkar wadda ake kaɗawa gangin farauta😂😂
Shi kansa Muzaffar ɗin kwatankwacin yanayin datake ciki a wannan yanayin a gareshi ma hakan take, iya lips ɗinta kawai yake kissing amma ji yake tamkar an tsomashi a cikin wata qoramar nutsuwa ne don haka gogan naku ya qara qaimi😂
Cikeda qwarewa gamida salonsa dake birkita mata lissafi Yay amfani harya rabata da rigar dake jikinta zuwa faffaɗan qugunta take dukiyar fulaninta ta baiyana cikin wata milk Ɗin breziya shara2 Wadda tai masifan mata kyau tamkar dama dan ita akayi ta, cikin yanayi na fitar haiyaci ya ɓalle wuk ɗin brar tata nan da nan abubuwan nata suka baiyana ra'ayil aini a gareshi Batareda da wani hijabi a tsakaninsa dasu ba, yayi mamaki qwarai dayaga irin girman tagomashin alkhairin da qirjin nata ke ɗauke dashi, koda wasa be taɓa zaton girmansu yakai haka ba a hankali ya sauke lumsassun idanunsa a fuskarta wadda ta lumshe idanunta tana karɓar saqwannin nasa cikin sauqi, suking boobs ɗiɓta ya shigayi kamar he's life depends on it har seda ta fara jinn zafine ta sakin masa kuka sannan ya sarara mata.
A wannan dare dai gabaɗaya muzaffar kasa controlling kansa yayi har seda ya ratsa ta Tsakiyar Majalisar ɗinkin duniyar BAFULATANAR DAJIN tasa 😂
A wannan dare haukata muzaffar ne kawai Rabe batayi ba, babban abin mamakin ma shine duk girman dayake dashi Gamida cikar zatinsa tsaf ta iya ɗauke Larurarsa ta tsahon shekaru 35 kamar ba yarinya Ƴar shekaru 18 ba, Tasha wahala sosai a hannunsa amma kuma sam bata nuna gajiyawarta a kai ba har seda ya gama samun nutsuwa da ita, tayi kuka sosi harta godewa Allah tun hawayen na zubo mata harya kasance hawayen ya dena fitowa sabida Azabar datakeji a qasanta
lokacin da komai ya lafa ne ya dubeta Yaga irin halin daya sanyata a ciki se kawai ya fashe mata da kuka Yana me qanqameta a saman qirjinsa sabida tsabar tausayinta dayay masa dirar mikiya, babu abinda yake iya furtasa se kalmar haquri. Albarka ya dinga sanya mata tareda kaf wani Dangi nata Dake cikin wannan duniya, kuka takeyi sosai marar sauti sabida tsaɓar Azabar datasha a hannun sadaukin nata sedai kokaɗan bataji haushinsa ba sema alfahari datake dashi a can qasan zuciyarta.
*******
A gurguje pls sabida qarancin lokaci
A haka rayuwa ta dinga tafiyar musu cikin aminci da kuma Qaunar juna Marar misaltuwa kullum yana manne da ita kamar ze maida ita ciki sabida so, bayan faruwar Auren muzaffar da kwana 2 ne suka Shirya shida ita ita zuwa gaida su Abie, tun da sanyin safiya suka gama shiri wajen qarfe 11am, inda ta shiya cikin wata baqar jallabiya me yawar stones wadda tayi mugun karɓarta kasancewarta fara sol da ita. Shigo muzaffar sanye yake cikin wani farin yadi sol dashi wanda yay masa ɗas a jikinsa a haka suka iso parking space ɗin hannunsu sarqe dana juna.
Buɗe mata qofar motar yayi ta shiga sannan ya zagaya ya shiga driver Sit yaja motar suka nufi gidansu kasancewar basu da nisa sosai ne gidan suka iso cikin sauqi, buɗewa get ɗin yayi suka kunna kai ciki ya samu guri yay parking
Koda suka fito hannunta yake qoqarin kamawa amma fir taqi yarda dole tasa ya qyaleta yay gaba ita kuma tana take masa baya, part ɗin mom suka fara shiga inda suka sameta itada Fadilah sunacin kwaɗon zogale, washe baki mom tayi ta miqe tsaye tana faɗin oyoyo my doter.
Durqusawa Rabe tayi cikin gurɓatacciyar hausarta ta fara gaida mom Fadilah kuwa dariya ta dingayi tana kallon muzaffar cikeda tsokana tace "ooooo yaya ka mallaki zaɓin ran naka yanzu shikenan no more headaches again ko?
Hararar wasa yayi mata sukasa dariya gabaɗaya, kallon mom yayi yace "wai Ina Qurraty ne?
Dariya Fadilah tayi tace "young bride zakace tana gidan angonta ai Allah sarki sisina sarkin rigima. Gabaɗaya kan muzaffar ɗaurewa yayi yana shirin magana kenan mom ta katseshi tace "oya muje part ɗin Ummie Abie nason ganin mu Gabaɗaya, ɗunguma sukai zuwa part ɗin Ummie nan suka tarar da Edyan a Nan shida Amaryarsa sun hallara.
A lokacin da suka shigo falon hannun Edyan a riqe yake cikin nata dukda cewar ita ɗin wata masifar kunya ce tayi mata dirar mikiya a lokacin da muzaffar Suka shigo falon shida Fulanin sa, Da sauri ta janye hannunta daga cikin na Edyan ɗin don kar wani ma ya gansu
Ɗan buɗe manyan idanunsa yayi ya dubesu da zallar mamaki bt still ya kasa magana. Nan da nan idansu ya sarqe cikin na juna da Zainab wadda Ke zaune a gefan Edyan tafi uban wani dakakken less yace "Yana ganku a nan kukuma?
Murmushi Edyan ya saki ya dubeshi yace "canji da zanan qaddarar muce Allah ya rubuta mana ita a guri Ɗaya kamar yanda ya rubuta taku Qaddarar kaida Rabi'atou!
Haqiqa na girgiza sosai a lokacin Dana Gane kana ɓoyemin gaskiyar abinda ke ranka akan Rabi'atou amma kuma dukda hakan na fahimci irin sonda kake mata Kwance a tsakiyar kwayar idanunka, Mun zaɓi Muyi maka hakanne ta hanyar cike gurbin daya rage mana a tsakanin Amintakar mu Nida kai kuma gashi nayi nasarar Yin hakan, Edyan ya faɗi hakan yana murmushi sannan yaci gaba da cewa
"Duk zaman danai da ita ban taɓa jin cewar ina sonta ba illa kawai tasausayinta danakeji A raina, shiyasa nayi amfani da wannna damar don na zaburar dakai harka baiyana abinda ke cinka a rai amma kuma se gashi ka gaza yin hakan.
Sosai jikin Muzaffar yay wani irin sanyi take hawaye ya Cika idanunsa ya juya yana kallo n mom wadda itama shi take kallo yace "yanzu dama duk abinda ya faru a baya har zuwa Aurena da aka ɗaura da ita duk kun sani amma kuma kuka gaza sanar dani?
Ya faɗi hakan a lokacin da hawayen dake maqale a manyan idanunsa ya fara zubo masa da wani irin mugun sauri ya Nufi Edyan ya rungumeshi Yana faɗin "thanthankSo much friend wllh I can't explain how much you mean to me, ina roqon Allah ya gina maka gida a gidan aljanna!!
Dariya suka dinga masa har Ummie da Abie dake tsaye a bakin ƙofar perlourn hatta baba Hajara ma ba'a barta a baya ba har ita aka haɗu a falon Abie ya haɗesu dika yay musu nasiha me ratsa jiki, tofa a nan ne Muzaffar kejin Auren Edyan da kuma qanwarsa Zainab sosai yay farin ciki da hakan don yasan waye Aminin nasa.
Sosai Muzaffar yaji daɗin hakan ba kaɗan ba har hakn ya gaza ɓoyuwa a tareda shi, huggin zainab yayi yace "congratulations Qurraty to have my best friend as your husband.
Dariya tayi sannan tace "same to you my handsome bro. Se yamma liqis sannan suka Koma gidajensu gabaɗaya.
A haka dai Rayuwa ta dinga tafiya da daɗi babu daɗi har Lavarin haihuwar inna laure ya iso musu cewar ta haihu ɗa namiji amma sedai Ɗan bezo da rai ba, kukan farin ciki laure da moddibo suka dingayi daga bisani kuma suka koma rayuwar daidai kamar wani abu betaɓa faruwa Mara daɗi a tsakaninsu ba
Sosai zumunci ya qullu A tsakanin zuriyar C. P mahaifin Edyan da kuma zuriyar 'Abie sakamakon Auren Zainab da kuma Edyan.
Ɓan garen Hajar kuwa tayi kuka kamar ranta ze fita a lokacin data samu labarin Auren muzaffar a hakan ma wai da wadda tafi tsana a rayuwarta. Tasha wahala sosai akan sonda take masa har hakan ya kaita ga kwanciya a gadon asibiti , a haka dai ta dinga rayuwa da tabon sonsa a ranta har Allah ya haɗata da wani bawon Allah me suna Ibrahim amma ana kiransa da Khalil, babban ɗan kasuwa ne shima a jirgi suka haɗu dashi har hakan ya kaisu ga Aure ammafa har zuwa wannan lokacin Namiji ɗaya ne a ranta Shine Muzaffar Abdulwahab Abdullah, Haka kuma har duniya ta tashi bazata taɓa iya dena sonsa ba!!!!! (Tabbas jarrabawar sosayya sam bata da daɗi, ya Allah ka rabamu da son maso wani)
A wannan tsukun Allah ya haɗa Fadilah da wani hamshaqin Ɗan kasuwa kuma mammallakin companyn kansa me Sulah Salahudden sukai Aure, a haka suka dinga gudanar da rayuwarsu a tare sedai tunda sukai auren shiru ne babu batun qaruwa Ta haihuwa a tsakaninsu.
****
Soyayyar da rayukan biyu sukeyi wa junansu kullum qara haɓaka take tana Qara naso, har Allah ya kawo Rabo a tsakaninsu inda Rabe ta haifi zaratan twins Ɗinta maza masu matiqar kamada ubansu, zaso kuga murna Da farin ciki a gurin Abie da mom abin har seda ya fara bawa Ummie tsoro, ranar suna yara sukaci sunan Abdulwahab da kuma Abdulkharim Wato sunan moddibo da kuma na Abie, inda suke kiran Me sunnan Abie da LAMIƊO, shikuma Ɗayan MODDIBO A sanadin haihuwar wannan yara mutanan rugar Ardo suka samu ƴancin da bazasu taɓa mantawa ba inda aka sanya musu matakan tsaro ta ko wani fanni tareda Gina musu wani babban Asibiti da kuma makarantun boko Don suma su tafi da zamani, sosai yanayin garin ya canza daga yanda yake a baya zuwa Wani Hatta fasalin gidan MODDIBO A wannan lokacin za'a iya kiransa da gini na musamman kuma abin kallo A aria ɗin gabaɗaya, A haka rayuwa ta dinga tafiyar musu da cigaba kala2 duk a sanadin Auren Rabe da Kuma Muzaffar ɗinta.
Bayan wasu shekaru
Zuwa yanzu su Lamiɗo da Moddibo sunyi girma sosai don Shekarunsu Ya kai biyar, kana kallon yaran zasu shiga ranka sabida yanda sukai gadon kyau bugu da qari kuma gasu ɓul2 dasu.
Kwance suke kan gadonsu lamiɗo muzaffar ya kalƙeta cike da so yace "ma'am nifa na kasa gane miki A ƴan kwanakin nan wllh jarabarki tayi yaw.......... Bata bari ya qarasa ba ta haɗe bakinta da nasa tana kissing ɗinshi kamar dama her life defined on it, duk yanda yaso karya biye mata seda tayi galaba a kansa zare bakinsa yayi daga nata yace "pls ki bari karfa yaran nan masu ɗan banzan surutu suzo su gan mu haka nan.
Aiko kamar daga sama sukaji muryar Lamiɗo da Moddibo suna faɗa akan cewar Lamiɗo ya hana Moddibo shiga ɗakin shi kuma yace dole seya shiga, a haka iyayen nasu suka iso gurin suna tambayarsu meyake faruwa?
Turo baki Moddibo yayi yace " Mommy bashi ne ba wai bazan shiga ɗakin ba, sassauta murya muzaffar yayi yace "Lamiɗo meyasa ka hanashi shiga?
Turo baki shima lamiɗon yayi yace "uhm Dady to ai refreshing kuke kaida Mommy shiyasa na hanashi shiga don karya gank......... Toshe masa baki Rabe tayi se faman raba idanu take kamar tayiwa sarki qarya, gaba ɗaya ji tayi kamr zata nitse sabida Kunya gefe kuma mamakin Wayo irin na Lamiɗo Takeyi
Daka musu tsawa tayi tace " oya go to bed kuma wllh idan na sakejin such words na fita a bakinka irin haka wllh sena dakaku gabaɗayan ku A gidannan !!!!!! Da gudu yaran sukai ɗakinsu ba tareda sun juyo ba
Kallonta muzaffar yayi yace "aiga irinta nan kin gani, jawoshi tai jikinta tana wani Narke masa se raba idanu Take tace "pls sweet muje Wllh i need you so badly!
Ba yadda ya iya hkaa ya bita don shima kansa a buqace yake da ita, kullum ya ziyarce ta ji yake tana qara masa garɗi tamkar ana qara mata ni'ima ne , babban abinda ke qara masa sonta shine juriyarta Ga lalurarsa da kuma biyayyar ta a gareshi.
Murmushi ya saki sannna ya firtaA filli yace"Haqiqa mace me wayo ita kaɗai ce take gane sirrin biyayyah........
*_Tammat bi hamdillah a nan na kawo qarshen wannna littafi me take BAFULATANA RETURN, Abinda na faɗa daidai Allah ka bani ladansa kuskuren dake ciki kuma Allah ka gafarta min 🤲_*
*Darasin dake ciki kuma Allah ka bamu ikon aiki dashi Amin🤲*
*_Waƴanda na bawa haushi A sakamakon wannan littafi ku gafarceni kunsan ɗan Adam tara yake be cika goma ba Duk yanda kaso ka kyautatama mutane wani bazaka taɓa iya masa ba😊_*
*Semun sake haɗuwa daku a cikin sabon littafina me suna*
👇
*MURADIN RAI*
(Abou Hateem)
Camment
Nd
Share
Don't forget to vote on whatpad
Sushmah✍️
0 comments:
Post a Comment