Labarina 'kir'kirarren labari ne, haka zalika banyishi don wata ko don wani ba, idan yay yanayi da labarin ka kayi ha'kuri akasi aka samu😃.
Ya Allah yadda na fara lafia Allah ubangiji ka bani ikon gamashi lafia, Allah sa ya amfani al'uma amin.
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿1⃣to2⃣
'Kauyen 'yar kadde wani garine dake 'kasarmu ta Nigeria, garine dake jihar nasarawa, garine da ya had'a mutane daban daban. Ya had'a yaruka da dama, 'karamin garine wanda ya had'a mutane musulmai da arna, garine mai tattare da zaman lafia, ga tarin ni'ema. A kwaisu da noma iri iri.
A cikin garin yau na yada zango, gani tsaye a 'kofar wani d'an ma dai-dai cin gida, gida ne dai irin namu na 'kasa, kusa da gidan kad'an akwai wani 'karamin asibiti, gaba dashi akwai wani 'karamar primary school.
Shiga gidan nayi domin d'ako muku rahoto.
""Joy yau dai kinsan cewa a kwai Church ko?"" Shiru tayi kamar bada ita uwar take ba, "" Joy ina magana kina jina, baki tashi tsiyarki sai Sunday, da zarar ance yau Sunday ne shikenan sai ki kama nu'ku nu'ku, to maza ki shirya ki tadda ni can, time nata kurewa, saura kuma ki'ki zuwa"" tai 'kwafa tare da tale mata kai.
Har uwan tabar wurin bata tashi ba, tana nan zaune inda ta barta, bata tashi a wurin ba sai kusan hour1.
A kuma wannan lokacin ne na'kare mata kallo, yarinya ce 'yar karama da ita, shekarun ta bazai wuce 16 years ba, farace doguwa yanayin fuska kuwa ita ba mummuna ba haka zalika ba kyakkyawa ba, wato tsaka tsaki kenan.
Tana da diri mai kyau, yanayin ta mai cike da natsuwa, tana sanye cikin kayan barci Wanda suka zauna d'as a jikin ta.
Cikin natsuwa taje kitchen, d'iban d'umamen shinkafa jallof tayi a kwanan miya kamar Wanda za'a bawa d'an shekara biyu, koma wa tayi d'aki taci ko gama cinyewa batai ba taje ta aje tare da sake ruwan wankan a bokiti tayi bayi.
Ta'bata lokaci sosai sanan ta fito, ta shiya cikin wata 'karamar riga da dogon wando, rigan tad'ame ta sosai wanda ya fito da shape d'in ta.
Gara gashin tada yake ba'ki, mai Kyau dashi tayi Wanda ya kwanta a gadon bayan ta.
Babu wani kwalliya a fuskan ta tad'au Bible d'in ta ta rufo gidan nasu ta nufi hanyan church, shima Church d'in ba nisa yake dasu ba.
Tafiya take a hankali cikin natsuwa, komai nata masha Allah.
A haka tazo wuce wata wurin wasu samari da talura kullum safe wurin zaman su kenan koda ana sanyi damuna .
Wani daga ciki tunda ya hango ta yafara had'iye yamu, yana lashe le'be, har tazo ta wuce su duka zuka zuba mata ido kamar zasu lashe ta.
Lumshe ido yayi saurayin tare da cewa "" gayu al'kur'an yarinyan nan tayi, komai yaji wallahi ta zata yadda dani hmm da abin ba'acewa komai. Kai dana more"".
Wani cikin su ya sake cewa "" yarinyan badai kaya ba, sai shegen miskilanci da jijji dakai, ni da zata yarda wallahi da auren zanyi, kaji baza wawa shashsha madace fah kuma arniya, meye gamun buri da kada? ina laifin mu lalla'bata mu kwashi ra'ba?"" Wani wanda bakin sa ba'ki'kirin dashi yake cewa haka.
"" Ah Allah yarinyan zatai taurin kai, guma kawai na aura domin na bari ta su'buce min hmm inaga sai na kusa zaucewa. Wa zai yarda ma har ka aure ta?, ai duk tsiya indai yarinyan ta yarda ai angama"".
Haka dai suke ta zancen ta, itako bata San ma sunayi ba.
Koda ta'karisa church har an tashi, domin mutane har sun fara fita, da murna ta saki wani murmushin dake saka kuma tunta lotsawa, hakan kuma na'kara 'kawata fuskan nata.
Da mamaki nake kallon ta, tana tsaye kusa da church d'in saiga maman ta tafito ita da wata 'kawanta.
Da mamaki suke kallon ta uwan ta fusata domin gani ta ganta bata ko tsorata ba saima kafeta da ido da tayi kamar yadda tayi.
Don haka cikin zafin rai ta nufeta tana cewa "" yanzu don ubanki sai yanzu kika zoko?"" Tai mata ran'kwashi, taji zafi domin harda runtse kyawawan idanuwan ta.
"" Joy mekike so?, meke damun ki? bansan wata irin yarinyan gareni ba Sam baki maida addinin ki abakin komai ba, baki da hankali sam "".
'Kwanta tace "" madam Gloria kenan ai na fad'a miki indan baki raba yarinyan ki da watanan musulman ba sai kinyi kuka watarana"".
Haka maman tai ta mata fad'a ko damuwa batayi ba, itako 'kawar maman sai faman zugata take.
***
"" Mami Allah baza niba, indai ba Dady bazai je yasa su canza ba bazani ba, haba kamata a rasa inda za'a turani sabis sai wani gari ko nace 'KAUYEN 'YAR KADDE, ina bazai yuwu ba, i can't believe this"".
Yace cikin zafin rai, murmushi mai ciwo mamin tayi sa'an nan tace ""Auwal kasan kowe mahaifin ka, idan ya kafe to babu wanda ya isa ya tankwara sa, bai magana biyu tunda yace sai kaje to kayi ha'kuri kasan baso nakeyi ba don haka sama ranka salama kaje kawai Allah yaba sa'a"".
Numfasa yayi tare da kwanciya a kushin d'in da yake, zuwa tayi kusa dashi tare da d'aura kansa a cinyan ta tana shafa masa lallausan gashin kansa yana ta lushe ido, zuwa can barci ya kwasheshi.
Share
&
Comment
Comments d'in ku zaisa nagane yayi muku
Sai najiku
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Dedicated to my son Muhammad, Allah ubangiji yaji'kan ka yayi maka rahama amin.
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿3⃣to4⃣
Mami na zaune har kusan hour amma bai tashi ba, tana ta faman shafa masa kai, tana ta kallon yaron nata cike da tausayin shi. Sallaman yayan sa yaron ta na biyu yasa ta d'ago kai tare da amma sa masa sallah mansa bayan sa matar sace da yarinyan su mai kimanin shekara biyar da watanni.
Itama d'auke da tata sallamar, "" mami shi kuma wannan lafia? ko shagwa'bar tasace ta motsa?"" hararan sa tayi tana mai ansa gaisuwan matar tasa.
Yarinya da suka zoda ita ta 'kariso gare su tana mai cewa "" tashi uncle, ka tashi zan sha ice cream"" tana mai girgiza shi, bud'e idanuwan sa idon cike da barci domin barci bai isheshi ba, koda yaga bebyn sace a gabansa sai ya tashi da sauri yana mai cewa "" oyoyo my beby, kece haka da safen nan?, uhum uncle, tashi muje ka kaini yawo sai mu biya shan ice cream"".
"" Angama my beby bari naje nai wanka, to uncle ina jiranka fah karka dad'e, okay "" sai lokacin yaga yayan nasa don haka sai ya 'bata fuska domin harda shi a son yake 'kauye fatar sa ta lalace, ko kula maman yarinyan baiyi ba ya huce. Itako cikin tsokana tace "" ohni waya ta'ba min maigida nane?" hararan ta yayi tare da wucewa fau.
Dariya suka kwashe dashi sai da mami ta harare su sanan suka daina.
"" Granny waya ta'ba uncle? waya ya 'bata masa rai? gasu nan kishiyan a gaban ki, UMMAH kece ko da abbah, kubar 'batawa uncle rai zai mutu idan kuna 'bata masa rai"" mai zasuyi inba dariya ba, harda kakan sai data dara.
Ganin suna mata dariya sai ta fashe da kuka harda birgima.
Ba shiri suka gintse bakin su, mami ta tashi tayi d'akin ta tare da iman.
Itama ikilima ta biyo su tana cewa "" baruwa na mami ni banma autan ki komai ba, oho dai kwaji dashi daga ke har munafikin mijin ki "".
"" Kai mami ni d'in ne munafiki? eh kai ko bakai ne kaja za'a turamin auta sauro ya kashe min shiba?"" Shiru yayi yana Sosa kai.
"" Kaban ansa mana"" tace tana mai zama akan sofa dake ciki d'akin nata.
Ya'ki bata ansa domin yasan bai dai gaskiya sai ma wayan cewa yayi da cewa "" bari na wuce office idan nataso zanzo d'aukan su, oho maka kuma ta Allah bata mutum ba insha Allah babu abinda zai samamin yaro, kuma mutum yasani nan gani nan bari ehey mutum ya fita harkan yarona, 'kwarai ma kuwa mami na"" yace yana mai shigowa d'akin.
"" Ga sojan ki can na hango sa yana parking motar sa, shima karki raga masa mamina kija masa kunni, harda shi bakin su d'aya Sam basu so suganni kusa dake sai sukama cewa wai bana abinda ya dace, kome nakeyi mara Kyau oho musu"" ya'karisa yana turo baki.
Dariya iman tayi tana cewa "" uncle kabar yin shagwa'ba kaga ka girma idan ba haka ba ko 'kawayena suka ga kana haka dariya zasu ma"" dariya suka soyi, amma sai suka matse. Domin yadda mami ta had'a fuska zataci 'kaniyan su.
Sun d'anyi shiru na wani lokaci shiko Auwal yana ma'kale kusa da mami kamar zai shige mata ciki so kawai yake babban yayan nasu ya shigo ayi masa nasa sanan yabar wurin.
Aiko sai gashi da alama tsaikon nashi yatsaya gaisawa da masu aikin gidan kamar yadda ya saba.
Aiko daga Auwal har mami suka had'a fuska kamar hadari.
Gaisuwar matarsa kawai ta ansa shiko sai faman hararan sa take.
Murmushi kawai yayi domin yasan kwana nan zancen don haka sai yace cikin ladabi "" Allah huci zuciyar mami ayi ha'kuri don Allah, mami kuma ma ai taimakon 'KAUYEN zaiyi, aikin lada zaiyi idan kikaga matsalan doctors da suke saikin zubar masu da hawaye "".
"" Kum...........,yimin shiru malam, ai ba haka bane kad'ai hanyan da za'a taimaka musu ba, kuna iya nemo wasu kukai masu ba yarona ba, mami taimako fah kuma ma babu ruwan mumu bamu muka turasa ba, Allah mami har ina shi'awan idan yagama bautan 'kasan sai mune masa aiki koni nar'inka biya tunda aikin laddane"".
Cikin fad'a "" tace tofar da yamun bakin ka ba'inda yarona zashi ka tura matarka mana ainaga aikin ta ne"".
Auwal yace "" mami duk nagane su so kawai suke yaronki ya'kara baki wani cuta ya kama mikini, ba'kin ciki kawai suke dani"" hararan sa yayan yayi ganin zai sake magana sai yayi kamar zai makeshi sai yayi shiru tare da mi'kewa yana tura baki.
"" Bebyna muje, ke kuma ina Akram da Mufida?" Yace da matar babban yayan tasa, "suna gidan mu,"" yayi amma aikin san yau nan gidan suke wuni tare dani to shi kenan na barku lafia "" yace yana mai ri'ke da hannun iman.
***
Haka maman tata tagama mata fad'a ko gezau, haka ta tasa 'keyar ta sukayi gida. Suna komawa wanke wanke tafara domin batayi ba ta tafi, maman kuma ta tafi kasuwa domin yo cafenen girki.
Koda Joy tagama ta gara gida sai ta sakayo gidan tayi gidan su Aisha 'kawar ta.
Bayan ta gaida iyayen Aishan sai ta shiga d'akin Aishan, da farin ciki ta rungume ta kai kace sun dad'e basu had'u ba.
Fira suka farayi duk da Joy ba wani fira take ba domin bata iya surutu ba miskilace na'karashe, suna tsanani 'kaunar junan su ita da Aisah akwai kyakkyawa fahimta a tsakanin su.
Iyayen Aisha basu ta'ba karanta ko 'kamanta ba, suna nuna mata soyayya irin ta yada suke nunawa Aisha domin suna mata 'kwad'ayin musulunci.
Wacece Joy?
Joy dai haifaffiyar Abia state ne, maman ta Gloria 'yar garin abia ne, iyayen ta haifafun garin ne, su arnane gaba da baya, iyayen ta ita kad'ai suka haifa sai suka d'au son duniya suka d'aura mata uban ta ba wani mai shi bane sai dai rufin asiri.
A hakan bai hana kulawa da 'yar tasa fiye da tsamanin Kuba masu karatu.
Watarana Allah ya had'a Gloria da wani musulmi, ba'kone ba d'an gari bane , soyayya suke sosai batare da sanin iyayen ta ba, sanda soyayya tai nisa sanan ta sanar musu suka nuna basu amince ba, tayi kamar zatai hauka, ciwo riris kamar zata mutu.
Badon iyayen sunso ba suka amince, amma da sharad'in idan wani abu ya taso karta nemesu, haka ko tayarda batare da tasan asalin mutumin ba sukaje sukai aure.
Auren su da wata uku yayi had'ari ya mutu, tayi kuma kamar me haka ta ha'kura.
Komawa wurin iyayen ta tayi suka'ki kar'banta, don haka sai tabar garin tayo nasarawa state cikin wani gari mai suna 'YAR KADDE.
Zuwanta garinne tafara laulayi, anane ta haifi Joy don haka joy batasan kowa nata ba sai maman ta sai gidan su Aisha.
Tare suka gama primary school d'in garin baban su Aisha yane ma musu wani acikin gari suke tafiya.
Wannan shine ta'kaitaccen tarihin joy.
More comments more typing.
Share & comment pls🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
[11/5, 9:49 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Dedicated to Muhammad Ahmad Bashir
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿5⃣to6⃣
Yau Monday, Monday tushen aiki wanda akace ko bature na tsoron sa, Joy ce zaune cikin uniform d'inta, mai kalar white and green, karya wa take cikin natsuwa. Tana idar da karyawan ta d'au bag d'in ta, cikin sanyi murya mai za'ki ta kalli maman ta tana mai cewa "" mama na tafi, to my dota a kula banda wasa kullum ina mai gargad'in ki daki kula kiyi karatu domin shine gatan ki idan kika kula yesu zai dafa miki, kije Allah tsare banda shashshanci.""
Cikin gamsuwa da zancen uwan ta gyad'a kai tare da fita daga d'akin.
A 'kofar gidan suka had'u da Aisha saura kad'an su gwara kai, dariya Aisha tayi tare da cewa "" inace baki shirya bane, naga har kusan 8pm gashi mashin na mana wuya anan balle muhau, kisan idan munyi latti basu d'aga mana 'kafa basu duban daga nesa muke"".
Smile joy tayi tare da cewa "" muje parrot ai ko magan nan naki yasa mu'kara makara, eh naji ai guma ni, anfi san mutum mai surutu da kurma"" murmushi still ta sakeyi batare da sake ce da ita komai ba.
Tafiya suke cikin natsuwa, majalisa dai tanan yauma kamar kullum, kuma mafiya yawancin masu zaman wurin 'yan iskan 'KAUYEN ne, kuma suna zama kawai domin gani suran jikin dake rikitasu, yake hanasu sukuni, dare ma saboda tsabar jaraba ya hanasu barci isah ko saboda tsanani son da yake mata yakan sa har yagamsar da kansa da dare saboda tunanin ta da yake yawanyi.
Yana son tunkaran ta ko nace dukansu ko don bu'katarsu amma kwarjinin da take musu yake musu shamaki.
Tunda ya hangota yake matse 'kafa, haka suka wuce su basu bar kallon suba, har sai da suka 'kule musu.
"" Kai wallahi wad'ancan gayun 'yan iskane , sun cika kallon mutane, ina lura dasu idan suka ganki kamar mayu harda lashe baki suke"" Aisha tayi zance tana dariya, ta'be baki joy tayi ba tare da ta kokula zancen nata ba, domin sam basa gaban ta.
Itama sarai tana lura dasu sosai.
Sai da suka kusa barin garin sannan suka sami mashin guda d'aya, kamar yadda suka saba haka sukai wato hawa su biyu.
Sai makaranta, sai muce a dawo lafia su Joy.........
***
Ga Muhammad Auwal kuwa barcin sa kawai yake ta shararawa a safiyar Monday bayan yasan Dady yace lallai yau ya wuce idan ba haka ba ransa zai mugun 'baci.
Mami ta shigo yakai sau biyar bai tashi ba, haka ma yanzu ta le'ko haka zalika bai tashi ba, don haka 'karisawa gare sa tayi tare da niyan tada sa, domin tana tsoron Allah ta tana tsoron mijin ta.
"" Son tashi haka don Allah, tukan Dadyn ka yafarga baka shirya ba"" tace tana mai girgiza shi.
Mi'ka yayi tare da shagwa'ba fuska tare sauke lumsheshun idanuwan sa a fuskan ta.
"" Mami kin tasheni ina barci na mai dad'i bayan kisan sai one o'clock zan tashi, please mamina in koma"" girgiza kai tayi tana mai jinzafin ba yadda zatai da mai gidan nata.
Ganin ta cikin tsananin damuwa sai yaji baiji dad'in hakan ba don haka sai yasakin mata murmushi tare da cewa "" mamina bar damuwa zan rin'ka dawo wa kullum bashine damuwanki ba?, a'a son ban yadda ba bason yawan bin mota ga gari mai nisa bari kawai, kuma ma Dadyn ka yace wai sai Kai five month sanan zaka zo sau d'aya......ina mami bazan yada ba, bazan iya ba sam, komi dady sai yarin'ka tsauwalamin, why mami?"" Yace, kwalla na taruwa masa a ido.
Shafa fuskan sa tayi tare da cewa "" yi ha'kuri son tashi kawai mubar maganan nan tashi maza ka shirya kazo Ahmad ya yakai ka"". Bai sake cewa komai ba ya mi'ke.
Bayan ya fito d'aure da towel a jikin sa, d'aya kuma na hannun sa yana share kai.
Mami ya gani zaune tayi tagumi, yarda towel d'in hannun sa yayi da sauri tare da nufan ta.
Cire hannun da tai tagumin dashi yayi tare da cewa "" mami kibar damuwa nan don Allah, idan ba haka ba Allah bazani ba sai dai Dady ya kasheni"" yana mai d'aura kansa a cinyan ta.
'Digar hawayen sa yasa taji jikin ta yayi sanyi, don haka kauda damuwar dake kan fuskar ta tayi tare da share masa tana sakin murmushi ya'ke.
"" My boy, yaushe zaka zama jarimin mazane? kuka sam baima wuya, ehey sweetheart d'ina?"".
Zum'bura baki yayi tare da cewa "" mami nifa jarumine niba ragon maza bane"".
""Okay naji maida wu'kar, nunamin zahiri, maza shirya muje, ka tada hankali sister d'inka why Auwal? yanzu haka mijin ta yasanar min sai kuka take wai sai tazo Nigeria"".
"" Oh my god! sorry my heartbeat, mami nakasa jurewa ne, mami banso bata nan ba, naji bazan iya tafiya ba tare da nasanar mata ba"".
"" Mami na yanzu ya zanyi? oho ma sanda zaka sanar mata meyasa baka tambayeni ba sai yanzu, kasan dai ciwon ta baisan damuwa da hayaniya ko?, ance kar a gayamata, kasan lamarin tsakanin ku sai Allah bata son damuwar ka ko kad'an. Yanzu don Allah mamina bazaki kawo mafita ba, my love na can banso ciwon ta yatashi, kuma ma Allah mami said a nace mata takwantar da hankali ta, insha Allah babu abinda zai sami 'kanin ta. Ta kuma nunamin ba komai fah"" yace yana mai jin zafi a zuciyar sa.
Tausayi ya bata sosai ga time na tafiya don haka sai ta lallla'bashi tare da cewa "" maza shirya zansan yadda zanyi, Allah mami na?"" gyad'a masa kai tayi.
Turo baki yayi tare da marai rai ce, "" mami to kirata yanzu"" yace yana mi'ka mata wayar sa.
Ganin yadda ya marai rai ce, yasa ta nisa cikin tunani domin bata da abinda zata lallashi Rahama dashi, bata yadda da maganan kowa indai akan 'kannin nata ne, Indai bashi ne yace ba.
Don haka sai tace "" son kirata kace mata da yadda nka zaka insha shi kenan, ki tabbata mami zata yadda? Eh mana"".
Don haka bai sake cewa komai ba sai dealing number ta da yayi.
Da 'kar ya shawo kanta, tare da masa fatan alkhairi.
Wani gagarumin nfashi ya sauke.
Tare da rungume mami "" yes mamina ta ha'kuri, to haka dama nakeso maza shir........bata ko rufe baki ba taji ehun mijin ta.
Don haka sauri ya shirya dama trolley sa tujiya mami ta cika masa da kaya.
Koda suka fito sai fad'a yake, basu ce komai ba illah fita da sukayi gaba d'aya harda yayan sa Ahmad da zai kaisa........
Fatan alkhairi sukayi masa duka iyayen nasa, Dadyn kansa sai da yayi 'kwallah, shi kansa bada son ransa zai tura shi ba, amma guma yayi masa haka 'kila ya natsu yasan ba komai mutum ke samu ba duk kud'i sa.
Kila ya daina 'kaman talaka, yasan talaka shima mutum ne ba abin 'kama ba.
Haka suka d'auki hanya.
***
Bai ta'ba zuwa nasarawa ba sai wannan karan, da fari da yaga garin sai yace yana mai murmushi ""yaya amma garin nada Kyau fah, shine d'an isakan can yace 'kyauye zani"" dariya kawai yayan yayi masa bai ce dashi komai ba.
Gani yayi anata tafiyan, sai ya sake cewa "" yaya wai haryan zu?, eh ai munkusa"".
Daga nan suka yi shiru duka sai da sukaje kwanan fiyanku sanan suka d'auki hanya, a nan ne zuciyar sa ta tsinke da gaske 'KAUYEN zashi.
Bai sake mamaki da ba'kin ciki ba sai da yaga suna sama da 'kasa.
Tafiyan suke kamar zasu tuntsura domin hanyan sam ba Kyau.
Hawaye yaji yana zubo masa don haka cikin kuka yace, "" yaya yanzu 'kiyayyar da kuke min har takai haka? Yaya nifah 'kannin kune, autan Ku, uwa d'aya uba amma kuke min 'yan ubanci...........""
Wani gugugum da yaji yasashi yin shiru..........
Camment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳 🌳🌳🌳🌳🌳
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Masoya godiya nake, Nagode da bibbiyan na da kuke, inajin dad'i matu'ka iya wuya anatare🤝🏻🤝🏻
Antyna kina inah? ga sa'kon dubun gaisuwa ezuwa gareki (Sister Naje'atu).
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿7⃣to8⃣
"" Kutimelesi, yaya ji wuri fisabilillahi, ji wani rami, Allah har na sada'kar mutuwa zan, yaya please kamaidani, kumin rai Allah mutuwa zanyi, Allah ko sauro sai ya kasheni. Kaikakai, yaya ji wancan gadan cinyayye, don Allah mu koma, idan ba haka ba kuma shikenan yaron mami taka ta'kare wayyo autan mami, wayo d'an gatan Rahamatu, pls yaya mu koma kaga kai kana da masu maka addu'a ni kuma fah?, wanda zata haifanma ba'a haifeta ba bare azo......., zaci uban kafa, kasan dai niba sa'an ka bane ko? ko dun kaga kanata iskancin ka ban tankaka bako? to gargad'in mami ne, bancin haka sai na faffashe bakin rashin kunya, banza shashasha, guma kaje ko maji sa'kat. Allah ka sake magana sai naci uban ka, don wallahi ka fara isata zan aje zancen mami a gefe inci 'kaniyan ka, idan yaso idan naje na bata ha'kuri sa'ba mata danai"" yaja tsaki.
Gum yayi da bakin sa domin yasan ba 'karamar aikin sabane ya sassa'ba masa, don haka da ganin fuskan nan guma yayi shiru kawai don ba mai 'kautarsa.
Haka koda suka zo gadan rutse ido yayi yana mai jin fad'uwan gaba, suna wuce wa ya sauke wani nannauyan ajiyan zuciya tare da kallon yayan, harara ko yasamu don haka bai sake cewa komai ba har suka isa cikin garin.
Aiko yara sai faman tururuwa suke gurin biyo motar manya ko sai kallon motar suke harda baki da hanci, kai gaskiya 'KAUYEN ci baiyi ba loz.🤭
Shiko Auwal sai faman yatsina yake da harare harare.
Basu zame ko ina ba sai bakin clinic d'in, shiga ciki sukayi sukai parking asibiti ba wani mai girma bane, 'karamin asibiti ne sosai dagani da d'add'an asibiti ne, domin pentin duk ya kurkurje.
Koda suka fito daga motan sai Auwal ya kama rufe hanci.
Buge masa hannun yayan yayi tare da gargad'i san nan ya saura rawa kansa.
"" Yaya"" waigo wa yayi tare da hararan sa, bai damu ba yasake cewa ciki marai rai cewa kamar zaiyi kuka "" yaya inyi magana don Allah, idan kayi sai naci 'kaniyar ka, basan jin shirmen ka yanzu "".
Turo baki yayi irin na yaran nan 'yan shekaru uku had'u.
""Toni bani ne zanyi maganan ba ai yaya, bakina ne keson yayi maganan"" dariya ne yaso su'buce ma yayan amma sai ya matse tare da mai kashed'i da ido.
Don haka sai yayi shiru bai sake cewa komai ba.
Office d'in babban mutum dake kula da asibitin suka shiga, domin yayan sai da yazo satin can suka gama komai da komai da mutumin.
Kawai kawo sa dama yayi.
Domin har wurin kwana ansa mar masa wani gida madai daici mai d'an kyau dashi kusa da asibitin ne.
Gidan na kusa da nasu Aisha, yana kallon jikin gidan su Joy, sayan gidan yayan yayi kawai don 'kanin nasa kar ya takura sosai.
Komai na bu'kata ya samar masa harta kayan abinci ya zuba masa wanda sai yafi shekara anaci sai dai abama wasu.
Don haka koda suka gama da ogan sai suka fito ya rakosu domin kai Auwal gidan sa.
Bayan ya gama duk wani abu da zai masa sai yayi sallama da 'kanin sa tausayin sa fal a ransa amma guma su masa haka, don haka kila ya sassautawa Kansa.
Suna saran 'kila yayi hankali.
***
Bai dawo gidan ba sai da yaga tashin yayan nasa sanan ya juyo gida ba'kin ciki dam a cikin ransa.
A cikin gidan parlour ne mai dai dai ci, sai da kwai toilet da kitchen a cikin parloun, d'aki gudu biyu.
'Daya ne aka saka masa gado mai d'an kyau, sofa da kayan bu'katan d'a namiji, suturu da sauran su.
'Dayan ko dam da kayan abinci.
Kitchen ma komai yasa masa haka ya zaga ya duba komai na gidan, ya yaba da 'ko'karin d'an uwan sa, domin yasan babu wanda zai masa sai shi.
Don haka wanka yayi tare da kintsa kansa cikin gajeran Wanda da farin singlet, domin garin da zafi.
Shiga kitchen yayi domin yanaji yunwa, domin sabda maganan tafiyan nan ba wani abu yake ci ba, baida kwanciyan hankali ci.
Don haka kar yama kansa horo da yawa, sai ya dafa abu mai d'an sau'ki yaci, bayan ya gama yaji kiran sallah la'asar don haka sai ya saka milk d'in jallabiyan tare da fito wa daga gidan bayan ya rufe ko inah.
Kalle kallen wurin ya tsayayi na wani lokaci sa'an nan ya nufin masallacin da yake hango wa nesa da gidan nasa.
***
Tunda ya fito mutane sai faman kallon sa suke, maza da mata, muslmai da arna, ba wai yau suka saba ganin 'yan birni ba, amma wanann na daban ne, gani ma suke yafi wad'an can.
Kallon da suke masa haka yana 'bata masa rai.
Har a masallacin ma bai tsira ba, wasu har 'kus'kus suke suna tambayan wanan baturen daga inah? mai kuma yazo yi?, babu ansa don haka suka 'karici gulman su sukai shiru.
Cikin 'kan'kani Auwal yayi sallah, ana idarwa ya fito domin tsami kawai yake ta sha'ka "" wai ai sai cikina ya kumbura, fut"" ya tofar da yamu.
Nufo gida yayi yana mai yatsina, yana gaf da 'karisowa gidan nasa ya hango 'yan mata biyu suna tahowa da uniform a jikin su, kallon d'aya ya musu ya d'auke kai a zuciyar sa ko yace "" yanzu dama da makaran ta a garin nan shine 'KAUYEN ci da gidadanci bai barsu ba? hu'um"".
Aisha tayi gida tana ce da Joy "" besty don Allah gobe banda latti, kinji?"" Kai kawai ta gyad'a mata ta shige gida itama tayi gida, dai-dai nan shima yazo jikin gidan nasa bud'e wa yayi ya shiga yana mai ta'be baki.
"" Wow, ashe akwai masu d'an waye wa?"" Domin tunda suka gansa suka d'auke kai.
Basu damu da ganin ba'kon fuskan da suka gani ba.
"" Kai amma faran nan zatai girman kantsiya, matsiyaci ji gidan su, kai zatai girman kai"" tsaki yayi.
"" Wayyo mami, zufa zai illatani, fanka ne kawai, ga inji ba, yanzu ya zan mami na? kum.......
'Karan wayar sace tasa yayi tare da zuwa wurin wayar.
Ganin mai kiran nasa yasashi saki lallausan murmushi.
Da murmushi a fuskan sa yace "" My love ya kike?, bros kana lafia dai ko? babu wani damuwa ko? idan akwai please kagayamin kaji d'an 'kanina, ina sauraron ka, tell me kaji my boy?"" .
Zum'ba baki yayi yace "" am not a boy, I' m a big man"" smiling tayi ''naji to, yanzu ka girma ko?" banza da ita yayi.
Da gangan tayi, tasani sarai baison a kirasa da yaro, "" autan mami shalelen Rahama baka jina ne?, ina sauraron ka, fad'a min mai kake so "".
Turo baki yayi kamar tana gaban sa ya shagwa'be murya "" ba komai, yanzu yaushe zaki dawo, kimin al'kawarin bazaki dawo da ciwon nan a tare dake ba, please sister ki warke da wuri 'kaninki na bu'katarki kusa dashi kinji?"" tausayin 'kanin nata ne ya kamata.
Hawaye taji na sauka akan kyakkyawan fuskan ta.
Sharewa tayi tare da cewa "" very soon zan dawo kaji, okay promise?, y promise "".
"" Yanzu dai kace baka bu'katan komai ko?"" lumshe ido yayi sanan ya jadda mata baida bu'katan komai.
Sun d'au tsahon lokaci suna waya kamar karsu rabu.
Haka mami ta kirasa itama sun dad'e suna waya ta kuma kwantar masa da hankali.
Kowa na gida ya kirasa, kowa ya nuna damuwa akan sa, hakan yasa ya rage damuwan da yake ciki.
Don haka wunin ranan cikin kwanciyan hankali ya kwana.
***
Washe gari zai ya d'an tashi da wuri, saboda yasan zashi asibiti, bayan yayi sallah sai ya koma barci, bai tashi ba sai kusan 7:00am, don haka wanka yayi a sukuni, yayi break fast ya shirya ciki kayan N Y C E, kayan sun ba'in yin masa kyau, sun kar'besa sosai.
Kusan takwas saura a fito gidan yana rufe 'kofar gidan su Joy suka fito daga gidan su Aisha da shirin makaranta a jikin su ko ba'a fad'a maka ba, kasan makaranta zasu.
Kamar jiya kallo d'aya Aisha ta masa ta d'auke kai, Joy kuwa kallon ma bai samu daga gare taba.
Shima haka take a gare sa.
Hanyan asibiti ya nufa suma dole tanan ne hanyan su, suna gaba yana bayan su, yana mai mamakin girman kan yaran.
"" Ji wancan ita kuma bata san tana tana da 'kiba bane ta d'inka kaya yana baiyanar da suran jikin ta, jifah, anya ba 'yar iska bace, ji yadda take kad'asu, oho god help me kada damuwa na ya motsa"".
Samun kansa yayi da 'kin kauda idon sa har suka 'kule masa shi kuma ya shiga asibiti.
Sunyi nisa suna ta ta'ba fira Aisha tace ""besty wallahi ba'kon birnin can ya tafi da emani na, ya had'u wallahi, banci yafi 'karfina da nace inaso"".
Tsaki Joy ta saki kamar bazatai magana ba kuma sai tace "" amma dai ke banza ne, kina mace ki zubar da 'kimanki ta 'ya mace, tir miki wallahi "".
Dariya Aisha tayi tare da cewa ""haka kawai sai na cuci kaina bazan fad'i abinda ke raina ba, wash har naji sa'kin abinda ke damuna saboda na fad'a wa besty na, jiya fa ko barci na kasa, don ko makaranta dare na kasa zuwa, saboda tunanin sa ya hanmin 'karfi da kuzari"'.
"" Besty don Allah idan mun dawo ki rakani wurin sa, na sanar ma ina tsanani 'kaunar sa"".
Wani uban hararan da Joy ta wurga mata yasa ta had'iye sauran maganan ta.
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳 🌳🌳🌳🌳🌳
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Bismillahir Rahamanir Rahim
🅿9⃣to1⃣0⃣
Yau har suka fita 'KAUYEN basu samu mashin ba, haka suka 'karisa makarantan a 'kasa, domin sai da suka kusa zuwa makaranta sannan suka samu, Aisha zata tsaida, Joy tace "" Allah baza mu hauba, da yake mu asararrune mukusa makaranta sai mu hauko? to badani ba, yau akaiwa baba kud'in sa"" dariya Aisha tayi "" kai besty"" bata kulata ba suka cigaba da tafiya har suka 'karisa makarantan, Joy na ba'in tsoron bulala amma miskilancin ta baisa mutum ya gane domin ba nunawa take ba.
Aiko sunsha dukan late, domin sai da aka musu bulala har goma, ko gezau Joy batayi ba, Aisha ko sai da tai kuka.
Sai faman tsine wanda ya bugesu take a zuciyar ta, "" basu da imani basu la'akari da nisan da mutum yake"".
Haka taita 'kun'kunai har suka shiga class.
******Auwal kuwa bayan ya shiga asibitin abinda ya kawo shi ya fara, sai faman yatsina yake.
3:00pm dai-dai yabar asibitin, gida ya dawo yayi wanka tare da dafa cous cous yaci, ya kwanta domin ya huta, ko ina na jikin sa sai faman ansawa yake alamun gajiya ne zaryan atare dashi.
Kai wannan Auwal d'in akwai la'kaumanci, ya saba komai masa ake, sai abinda ba'a sashiba zaka gansa kan gaba.
Girki kam ko mace albarka, domin sai dai mami bata shiga kitchen ba, indai tana ciki shi kuma yana gida zagewa yake yana taya ta aiki.
Saboda tayata da yake ba wani nau'in abinci da bai iya ba, banda wanan Auwal bada son jiki ba, kuma bai iya komai ba bayan wannan.
Amma akwai 'ko'kari sosai ta fannin karatu.
3:45pm ya tashi yayi masallaci, bayan an idar da sallah sai ya fito, zama yayi a 'kofar gidansa yana ganin masu kai da dawo wa, duk wanda zai wuce sai ya kafa masa ido yana kallon sa kamar zasu cinye sa.
Yana zaune Aisha ta fito daga gidan su, dauke da littafain a hannun ta, ga hijabi har 'kasa dagani islamiya zata.
Kallo d'aya ya d'auke kansa, wuce shi tayi ba tare da ta kulasa ba.
""To ita d'ayar fah?"" yace a cikin zuciyar sa, can kuma sai ya ta'be baki tare da cewa "" to ina ruwana"" haka ya d'au tsahon lokaci zaune a wurin nan, domin har lokacin tashin su Aisha a makaranta yayi ta dawo ta same sa a wurin da ta barsa.
Sai da yayi magriba da i'sha sanan ya koma gida.
***
Yau kwana Kwana uku kenan Joy na fama da ciwon ciki, kuma ciwo irin sosan nan, miskilanci ya hanata nunawa a fuska balle ta bud'i baki tayi magana.
Saboda miskilancin ta shiyasa sam uwar bata gane ba, da dare yayi haka ta tashi zata fita.
Har takai bakin 'kofa uwan tace ""where are you going?"" turo baki tayi sanan tace "" gidan su Aisha zani, kina ganin dare yayi sosai ko?"" d'aga mata kai kawai tayi.
"" Karki dad'e"" shima d'aga kai tayi ta 'kara gaba.
****Auwal zaune a 'kofar gidan sa, yana shan iska, abin dad'i da 'KAUYEN nan sam basu da sauro, kasan cewan ana zafi shiyasa ya fito yana shan iskan waje.
Dare ne, babu wuta sam a garin amma farin wata kamar rana.
Yana d'an kalle kallen sa, sai yaga Joy tsaye a 'kofar gidan su kamar meneman wani abu.
Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai, tare da koran shed'an.
Domin sanye take da guntun vest da gajeran wando, wanda ko rabin cinyan ta baiyi ba.
"" Anya wanan yarinyan ba karuwa bace kuwa? A fuska kamar MUMMiNA SADI'QA (littafin sis rukyn Mamah, kuyi maza masoya ku garzaya karku bari abaku labari, domin ta baza basira da fasaha a cikin mashahurin littafin nan nata)., amma a zahiri abin ba kyan gani, kai Allah mana tsari da kyan d'an mazuru, tur"".
"" I hate her"" yace tare da to far da yamu.
Itako bata san yanayi ba sam, shigewa gidan su Aisha tayi da sallama d'auke a bakin ta.
Baban Aisha n da maman ta suna daga d'aki, Aisha ce kawai a tsakar gidan itace ta ansa mata tare da kallon ta da mamaki d'auke a fuskan ta.
Cikin 'kasa da murya tace "" besty meye haka?"" cikin yatsina ta kalle ta tana neman 'Karin bayani.
Tashi tayi ta jata cikin d'akin ta, Allah yasa babu 'kannin ta duk sunyi barci.
"" Besty meye haka don Allah? look at you"" ta'be baki tayi tana mai kallon jikin ta.
Ta gane sarai mai take magana akai amma sai tai biris da ita, neman wuri ma tayi ta kwanta.
Tana mai cije le'be, domin a wanan lokacin ciwon taji ya taso mata.
"" Besty don Allah kibar irin wanan shigan, domin baida tsari sam ko addini ma ya han........., tsaya malama, kina manta cewa addini nan da naki ba d'aya bane ko? mu bamu takura sai kije can ki 'kara malama"" tace cikin masifa.
Da mamaki take kallon 'kawar tata, domin hakan ba halin ta bane sam, komai tace mata tana binta da idone kawai.
Kuma takan d'auki magana ta da mahimmanci, sa'banin yau.
Gani ta dafe ciki hawaye na zubo mata yasa ta 'karisa da gudu gare ta, tana cewa "" menene besty? "" shiru bata tanka taba, tana ri'ke da ciki
"" Nine ko?, sorry na bari bazan sake ba, kiyi ha'kuri besty bansan kina irin wanan shigan sam, domin zai bawa 'yan iska ko wad'an da basu kai zuciya nesa ba yin miki fayd'e, amma kiyi ha'kuri idan yayi miki zafi bazan sake ba "" tace cikin sanyin murya.
Shiru bata tanka taba, sai dai tabar hawayen, idon tama ta rufe kamar zatai barci.
Ta d'au tsahon lokaci a haka kafin ta tashi tayi gida ba tare da ta kulata ba.
Addu'a Aisha tayi a zuciyar ta "" ya Allah kaceto wanan baiwa taka"".
Barcin ranan batayi shiba, domin cikin ya matsa mata.
***
Washe gari Sunday, rana da Joy tsaneshi a rayuwar ta bata san meyasa ba, batason ranan.
Ko nace ta tsani zuwa church, indai maman ta tasa ta sukaje to mudin taje to sai ta kwana da ciwon kai mai tsanani.
Ranan ne ranan ni'ku ni'kun ta, balle yau ya had'e mata da ciwon mara.
Tuda madam Gloria ta tashi take mata fad'an ta tashi tayi duk abinda zatai, "" yau banzan d'au iskancin da kikayi na satin can ba,, ki tashi maza"" ko cikan ka batace mata ba.
Bata damuba domin ta saba da hakan.
Ciwon na cinta ta tashi 6:37am tayi bayi, wanka tayi ta fito, shiryawa tayi cikin gajeran blue d'in riga, ta wuce guwwa.
Rigan tayi mata kyau sosai, ta fitar mata da shape d'in ta sosai.
Tea uwan ta mi'ka mata "" ki kwana kinasha na tafi karki zo a kan lokaci, yau sai ma'kota sun 'kwaceki"".
Tayi 'kwafa tare da fita bubble d'auke a hannun ta kannan yasha gashin doki.
Toshi ina Joy ta samo suma ne?😁. gare Ku fan's ina jiran ansa.
Ruwan zafin kawai ta shanye bread d'in ta aje, d'aukan siririn gyalen ta ba'ki ta yafa ta rufo gidan ta fita.
Tafiyan ta na yau yafi na kullum nawa, daurewa kawai take take taka wan, domin duk d'aga 'kafan da zatai sai taji cikin kamar ba nata ba.
A haka taje church d'in wurin 8:20am, lokacin har sun fara wa'ke wa'ken su da raye-rayen su.
Shiga tayi cikin ba'kin ciki.
Uwan na ganin ta ta banka mata harara, bata damu ba taje can baya tai kwanciyan ta hankali kwance.
Ciwon ranga ranga ya taso mata da kwanciyan ta kad'an.
Bata san sanda ta 'kwala ehu ba.
Ehun ta yasa uwan ta nufota tana surkulensu.
Kan kace me hankali kowa ya dawo kanta, pastor ya fara mata addu'a, yanayi yana tatta'bata.
Ganin yaune damanshi na 'karshe da zai maida miyonsa yasa yace akaita gidan sa zai mata addu'a na musamman.
Wani saurayi ne yace akaita asibiti kawai, basu jada maganan saurayin ba suka kinkimeta sai asibiti.
Pastor nan na tsine ma wannan saurayi a zuciyar sa.
****
Asibiti.........
Sunje aka kar'be su cikin gaggawa, sai dai me wanda zai duba ta baizo ba aka sanar masu.
Cikin kuka da tashin hankali madam Gloria tace "" ku taimakeni karta mutu kunemoshi kunji Ku taimaka"" tausayin ta suka ji fita wani yayi ya nufi gidan Auwal duk da jiya ya sanar zai rin'ka huta wa duk weekend.
Da 'kar da sud'in goshi Auwal ya biyo wanan saurayin suka nufo asibiti.
Sai mita yake.....
Direct d'akin da take yanufa ana nuna masa, yana gaf da shiga maman ta tace "" don Allah doctor kaceto mini yarinyan yaya,ita kad'ai gareni"" tsaki yayi a zuciyar sa, "" yanzu akan 'kazaman arnan nan ne banzan can ya tasoni?"" Tsaki yayi ba tare da ya kulata ba yayi ciki.
Shigo masa da kayan aiki akayi ya fara duba ta batare da yaga fuskan taba.
Koda ya gama ya gano matsalan don haka fita yayi bayan yayi mata aluran da zai rage mata zugin.
Yace ma maman ta samesa a office d'in shi.
Bayan tazo bayani yayi mata da cewa "" yarki zata fara al'ada ne"" nan dai yayi mata bayani dangane da damuwar 'yar NATA ya rubu ta musu magungunan da zasu siya.
Godiya tayi masa ta tafi sayowa a cikin asibitin.
****Da alluran barci ya had'a mata don haka bata farfad'o ba har sai bayan la'asar, bata abinci sukayi sa'anan tasha magani.
Taji dama dama sosai, don haka sukaje suka sanar dashi .
Yazo kwanan da zai sa dashi da d'akin saiga Aisha, kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai.
Shiga d'akin yayi itama ta mara masa baya.
Idonnun sa basu sauka a ko'ina ba sai kan fuskan Joy......................
0 comments:
Post a Comment