π
Ώ1⃣1⃣to1⃣2⃣
"" Haba biri yayi kama da mutum, ba banza ba ashe ba musulma bace"" yace a zuciyar sa. Shanye mamakin sa yayi tare da
Matsewa ya shiga, dudduba ta yayi tare da mata tambayoyi, tana basa ansa yana rubutawa, koda ya gama tunda yaga ta samu sau'ki sosai kawai sai ya sallame su tare da cewa yana mai kallon maman ta "" madam zaku iya tafiya, ba wani matsala bane sosai mata da yawa suna irin wanan ciwon, a kula da shan maganin ta"". Godiya tayi masa shi kuma ya fita ba tare da ya sake ko kallon taba, tattara kayan su suka bar asibitin, bayan sun dawo gida uwan ta cigaba da kula da ita, har tasamu lafia, duk da bawai ya bar mata bane, yana mata kawai dai tana daurewa ne.
Yana tashin mata lokaci zuwa lokaci, shi kuma Auwal da sanin sa ya sallame ta, domin haka kawai yaji bazai iya juran ganin ta ba, kuma ma wai shine zai rin'ka duba ta.
Yasan dai in dai suka kula da maganin zataji dama dama, domin mafiya yawancin irin wanan ciwon sai mace tayi aure take bari.
Ya sallame ta amma bai huta ba sam, domin sallaman kawai yayi amma hankali sa nakan yarinyan, bai san mai yasa tunanin ta yasashi gaba ba kusan kwana biyu kenan.
Kuma tun daga ranan bai sake sata a idon saba, tunin ta yayi masa yawa wanda har yana son shafan aikin sa, dare bai da sukunin barci yadda ya kama ta, idon sa photon yarinyan kawai yake gani, musamman wasu surori na jikin ta dake firgita shi, duk lokacin da ya tuno wani sura na jikin ta, to tabbas sai yasha magani yake samun sukuni.
Safe ma haka kai a ta'kaice wuni yake cikin tunanin ta, ya Kuma rasa dalilin hakan. Yau kusan sati bai sata a ido ba ko 'kawarta bai sake gani ba, don haka wani iri yakejin sa. Monday ne yau amma sam yaji baisan zuwa asibitin, ko wanka bai ba ya fito waje ya tsaya daga bakin 'kofar gidan sa, lokacin wurin 7:35pm ne, ko minti biyar da tsayuwa baiyi ba sai gashi sun fito daga gidan su Joy d'in, jikin su sanye da uniform, idon ya kafa mata a fakaice ya d'auke kai. Ajiyan zuciya yayi tare da cewa yana kallon su suna tafiya cikin natsuwa, "" ta rame sosai, kar dai nace ciwon ne har yanzu?"" yana mai cigaba da binta da mayatatcen kallo.
"" Oh, my god, duk ni naja hakan, laifi nane, bazan cire miki ba, amma da zan iya kula dake ki samu sau'ki fiye da yadda kika samu. Sorry! "" yace kamar tana gaban sa.
Bai koma gida ba har sai da suka 'kule masa, shiga gida yayi yana mai jin 'karfi a jikin sa.
Wanak yayi tare da had'a breakfast sa'an nan ya fito gidan domin wuce wa asibiti.
***
Abu ya zama wa Auwal kamar ibada, kullum sai yazo ya tsaya duk safe yaga wuce war su makaranta sa'an nan yake samun sukuni, ya rasa maike damun sa game da yarinya, ya damu sosai da ita.
Yanzu haka kimanin watan sa hud'u kenan a garin kuma tsahon wanan lokacin tunanin yarinyan ya'ki barin 'ka'kalwar sa.
Satan kallon ta ya zama masa kamar ibada, duk ranan da bai ganta ba bai samun sukuni.
Sau da dama yakan tsare kansa da tambaya "" meyasa Auwal, meye gamunka da ita?, ba musulma bace ba"". Ire-iren wad'an nan tambayan dama wasun su yake wa kansa, kuma har wa yanzu babu wanda yazo duba sa, domin Abba ya hana, tun ya damuwa da 'bacin rai har yazo ya ha'kura. Yanzu ya saba da garin yana jin dad'in garin sosai, ya saba da mutane garin, harta madam Gloria suna mutunci sosai da ita, watarana ma har girki dashi take tana kai masa har gida, kyakkyawa alaqa ke tsakanin su, har yanajin tana d'ebe masa kewan gida sosai.
Ba musulma bace, bata 'kaman musulmai, domin har yanzu tana tsanani son mijin ta duk da ya dad'e da mutwa.
Yau weekend, zaune yake a 'kofar gidan sai ga Joy ta fito daga gidan su Aisha, sanye take da kayan da kusan kullum indai ba makaranta ba yake ganin ta dasu, kayan da duk yagan ta dasu yanzu yake jin ba'kin ciki sosai.
Riga ne white mai hannun vest, da gajeran wando, kayan sun matseta sosai.
Kallo d'aya ta masa ta d'auke kai, ciza yatsa yayi tare da 'kwafa.
Gida tayi bayan ta yabi da kallo, gauda kai yayi da sauri idanun sa sunrine saboda ba'kin ciki, "" ita dai yarinyan nan kullum cikin shigan karuwai take"" yace yana mai da nasanin zaman sa.
Yana zaune madam Gloria ta fito zata anguwa, bayan ta Joy ne ta fito domin mata rakiya.
Da fara'a a fuskan ta tace "doctor hutawa ake?, eh madam"" yace yana hararan Joy, "" kutuman uba"" inji Joy.
"" Lafian ki kuwa?, keda wa?"" murmushi tayi domin bata San maganan nata ya fita ba, "" name mama, na 'kaniyan ki, ba zagi naji kinyi ba?, a'ah, zagi kuma? ni banyi wani zafi ba"" tace tana rama hararan da yayi mata.
"" Ina wuni"" yace da ita, "" lafia qalu doctor, ya aiki dai?" "lafia qalu, za'a fita kenan?, eh doctor, to Allah tsare"".
"" Amin doctor, nagode"" tace tana murmushi, shi kuma yayi mata sai ta dawo.
Wuce shi sukai, raka uwan tayi da nisa saida ta samu mashin sannan ta dawo, zata cikin garine saro kaya domin kayan da take siyarwa duk sun 'kare.
Dawo wa tayi tana zancen zuci, "" shege kawai d'an isaka, haka kawai ban maka komai ba ka kama hararan ta da shegun idanun nan naka mai kama da na mayu, shiyasa tunda naga take taken sa d'an iskan yanzu na gummaci ciwo ya kasheni da dai ya duba ni, ba ta'kaman sa da girman kan sa don yaga shike duba mutum ba?"" tayi 'kwafa.
"" Ai ba kyauta kakeyi ba bare k.........."" Sai kuma tayi shiru tana cije le'benta.
Kwnan da zatai gida ta had'u da Isah, kallon ta yake kamar maye dama a haushi take kawai sai tace "" d'an iska lafia kallon? "" "" ni kika cewa d'an iska?, eh ance d'in idan ba d'an iska bane kai meye na bin mutane da kallon iskanci?"".
Zuciya ta ciwo isah, kawai sai ya biyo ta, guduwa tayi ya bita yana cewa "zan nuna miki isancina yau dan ubanki, zanga uban da ya tsaya miki a garin nan, wawuya banza, akwai d'an iska ma irrin uwarki?, ina ubanki yake?, ba cikin shege uwarki tayi ba ta gudo garin mu? wa yasan asalin ku?"".
Tsaya wa yayi cikin ba'kin ciki da kuka "" tace Kaine d'an iska ba uwata ba, banza wawa shashsah 'kazami........"" kif ya kifeta da mari.
"" Shegiya angaya miki bamu sani bane, to agari nan ta haifeki, banza yau sai naci uban ki, ke uwarki zance domin baki da uban. Kuzon an taimaka muku ba'a karaku ba shiyasa kikewa mutane tsiya da iskanci ko?"".
"" To yau zannu na miki ni cikakken d'an island,yau zan maida kwad'ayi na, inga uban da zai 'kwaceki duk fad'i garin nan "".
Yace yana janta tana tirjewa, kafiyan tsiyan da da miskilanci ta yasa ta'ki neman taimako duk da tulun tsoron dake cinta.
'Dukan ta yayi cak yayi bayan gari da ita, tafiya suke yana ta surfa mata zagi tana ramawa, sai faman kiciniya take domin 'kwatan kanta amma ta kasa.
Ganin suyi nisa ba kuma mutum ko d'aya nane cikin ta ya d'uri ruwa.
Sai asanan ta kama ehu, amma babu mai jinta.
Nan ta yanke shawaran basa ha'kuri, sai dai ta makara, domin lokacin ne ya kawota dajin da babu maceci sai Allah.
****Auwal kuwa bayan wuce wansu yayi tsaki da cewa "" ni kika harara ko beb........... "" sai kuma ya kasa 'karisawa, ""zaki zo ki sameni yau sai kin gayan idan ni sa'anki ne, sai na gara miki zama, har 'yan iskan kayan dakike sawa sai kinbar skasu badai uwar taki bata ba, hmmm har ciki zanje sai an'kona kayan duka"".
Yana nan zaune sai ga uwan ta dawo da allama wani abu tazo d'auka domin bai isa ace har taje ta dawo ba.
"" Sannu da dawo wa" "" yauwa Auwal ban maje ba, mantuwa nayi na dawo"" tace tana shiga gidan ta.
"" Joy, Joy, shiru d'aukan jakanta tayi tafito tana mamaki rashin ganin ta a gidan, "kuma war haka Aisha na makaranta bare nace tana gidan su, kuma bata shiga indai Aisha bata sai da 'kau'karan dalili"".
Yana zaune ta fito, ya gama tunanin ina tayi sai ga tambayan madam Gloria.
"" Doctor nace don Allah bakaga yarinya taba?, bata dawo ba bayan wuce war mu?"" tana tambayan tanjin fad'uwan gaba.
Shima fad'uwan gaba ne ya ziyarce shi.
"" A'ah gaskiya, bata dawo ba"" yace yana mai dafe zuciyar sa.
"" A'ah ina tayi?, bata yawo fah, kuma baka a shigan ta gidan nan ba?"" tace tana nuna gidan su Aisha da kallo.
Kafin ya bata ansa sai ga 'kanin Aisha ya fito daga gidan.
"" Yauwa Muhusin abokina Joy tana gidan kune?"" cewan Auwal, "" a'a bata"" Muhusin d'in yace.
Kallon mai mashin d'in da ya kawo ta tayi tace "" malam ko zaka tafine? zanje neman yarinya na"".
Duk da Auwal na cikin damuwa bai hansa dariya ya'ke ba yace "" kije kawai madam nasan ba nisa taiba 'kila ki ganta yanzu, baza 'bata ba insha Allah "".
"" Nagode yarona, bari naje, idan ta dawo kace mata kada taje ko ina, ta jirani na dawo please kaji"".
Gyad'a mata kai yayi, ita kuma ta hau suka wuce.
Kasa cigaba da zama yayi zarya ya farayi "" ina yarinyan nan tayi?"".
Gaban sa nata cigaba da fad'uwa ya tashi ya rufe gidan sa, ya jawo masu Joy 'kofar su yabi hanyan da suka bi.
Duk taku d'aya fad'uwan gaba sa na 'karuwa ne.
***
Kokuwa suka kama, ya yayyaga rigan nata, ganin na shanun ta awaje madai daita dasu sai faman wal'kiya suke, yasa kwad'ayin sa ya sake tasowa, kamo ta yayi tare da fara shafosu.
Dukan sa take tana ehu tana basa ha'kuri amma a bazan, kai tamkar ma tana 'kara zuga sa.
Laushin su ya gigitashi, "" beby dama haka kike, gaskiya beby zaki dad'i, ashe ba banza ba muje birin wurin kawuna 'kato dashi yake cewa matar sa beby ba"".
Kai bakin sa yayi kan nata ta gantsara masa cizo, ehu yayi ya sake ta da sauri.
Tashi tayi ta fara gudu, binta yayi yana cewa "" shegiya bazan ta'ba bari daman nan ya wuce ni ba "".
Gudu take yana binta, ranan ko kamar an hana mutanen garin fitowa.
Babu kowa har ta kusa da barin bayan garin, gajiya tayi jiri ya kamata ta yanke jiki ta fad'i.
Hamdala yayi tare da rufa mata.
Shafata yake ba'ka'k'kautawa, ganin hakan zai 'bata masa lokaci sai yakai hannun sa maran ta.
Cire mata......
Comment & share pleaseππ»ππ»
Luv u all my fan'sπππππ
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³π³
(Ta'kai taccen labari)
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
Bismillahir Rahamanir Rahim
π
Ώ1⃣3⃣to1⃣4⃣
Neman keta mata had'i yake da gaske, cikin tsoro tace murya a sha'ke "please kaji tausayi na, na daina ma rashin kunya" ina bai san ma tanayi ba, 'ko'karin cinkan burin sa kawai yake. Kuka take kamar ba gobe ta ciza ta yakusheshi ina basan ma tanayi ba, ya ciro abinsa zai zurma kawai yaji an buga masa 'katon itace a kai.
Ehu ya saki tare da fad'uwa gefe, ita ko idon ta dake rufe ta bud'e sakamakon jin 'karan da taji.
Ganin shi yashe gefe tayi hamdala a zuciyar ta tare da yun'kurin mi'kewa.
Ganin Auwal tayi tsaye ya juya mata baya, ta gane shine saboda kayan jikin sa.
Kasa mi'kewa tayi domin ta wahala wurin yun'kurin 'kwace kanta a wurin isah.
Wani marayan kuka ta saki, baiko waiwayo taba ya fara tafiya ransa na masa 'kuna.
"Please ka taimakeni na tashi" ya tsinci maganan ta, kamar bazai tanka ba, tama cire ran zai taimake ta sai taga ya mi'ka mata hannu sa, kallon sa tayi sai taga ko kallon ta baiyi ba.
Mi'ka hannun tayi, taimaka mata yayi ta mi'ke, tana mi'kewa ya fisge hannun sa.
Tare da fara tafiya yana tangad'i.
"Bazan iya tafiya ba, don Allah ka kamani" cikin zafin rai ya waigo yace da ita yana jifan ta da mummunan kallo.
"Arniyan banza da hofi kidaina had'a ni da Allahn da ya haliceni, kinsan Allah ne? ai kafirai basu sanshi ba, da kinsan shi da baki rin'ka shigan karuwai ba" yace yana mai tofar da yamu.
Tafiya ya farayi ba tare da ya sake kallon taba.
"Wayyo mama, mama kizo ki taimakeni" tace cikin mawuyacin hali.
Dawo wa yayi tare da sake mi'ka mata hannun sa d'aya kamar d'azu ta kama.
Tafiya take da'kar, shiko hannun ta dake nasa ji yayi kamar an watsa masa garwashin wuta.
"Na tsani 'kyauyen nan gaba d'aya" yace a zuciyar sa yana mai share hawaye dake shirin zubo masa.
Har sunyi nisa sai ya d'an saci kallon ta, gani yadda take yayi matu'kar firgita sa, ga wani malulun ba'kin ciki da ya rufesa.
Kamar wada akama dole yace yana mai zame hannun sa daga nata "don iskan a haka kike nufin zamu tafi da yagaggen riga? ko dama ai ba damuwar ki kayan mutunci sukayi ba, ansaba, hakan ya nuna baki tubaba, baki saduda ba. Hmmm" yaja ga garumin numfashi.
"Bazan iya tafiya dake a haka ba gaskiya, in anbinci kama kekika gayyace shi, kila bai miki yadda kike so bane shiyasa kike neman wani. Toni ba d'an iska bane, sanan ban mu'amala dasu, tir, fasi'kanci baiyi ba Sam, Allah tsare mu ya kare mu, amin".
Yace yana mai takawa abinsa.
"Ni nayi nan, Allah had'a ki da dai-dai ke sai aje can a 'karata , misssss".
Ya cigaba da tafiyan sa, kuka ta fashe dashi mai tsanani, ha'ki'ka yaci mata mutunci tace cikin zuciya, zuciya nata na mata 'kuna.
" Wato nufinsa ni karuwa ce ko? hmmm" tace tana cije le'ban ta.
"Ba komai ba laifin ka bane, kuma nagode da taimako" bai masan tanayi ba domin yayi nisa.
Tayi nisa cikin tunani sai ta tuna inda take aiko bata san sand ta mi'ke da gudu ba tama manta bazata iya tafiya ba, duk da taji a jikin ta, amma guma ta tsira da mutunci ta.
Tafiya take tana tattare yagaggen rigan ta tana rufe 'kirjin ta dashi.
A haka ta kawo har gida mutane nata kallon ta amma ko ajikin ta, hakan bai dame taba sam.
Tura 'kofar gidan su tayi ta shiga, wurgar da yagaggen rigan tayi ya rage daga ita sai d'an guntun siket d'in ta.
'Daura ruwan wanka tayi, domin a lokacin babu abinda take bu'kata da ya wuce hakan.
***
Auwal kwance a gadon sa yana ta rafka uban kuka kamar wani mace, kuka ya'ke bil ha'ki da gaskiya, yayi dana sanin ganin ba'kin abinda ya gani a idonsa.
Zuciyar na masa zafi mai tsanani, da ya rufe idanun sa abinne ke bayyana masa kamar yanzu ake a gaban sa.
Yana hango abun dake fizgan zuciyar sa gare ta a hannun wani yana sarrafasu yadda ya gadama.
Wani irin 'kara ya saki tare da ri'ke kansa.
"Duk ita ta janyo ta jama kanta, musulunci yayi, Allah ka 'kara mana imani" yace tare da dafe zuciyar sa.
"Kullum bata da shiga sai wanda zai hankali mutum gare ta, kai anya ba ita tanemai ba?" yace yana cije le'be.
Kiran sallah ya tayar dashi, mi'kewa yayi direct toilet ya shiga wankan yayi sa'an nan yasa white d'in jallabiyan sa ya fito bayan yayi alwallah domin tafiya masallaci.
Jin idanuwan sa sun masa nauyi yasa shi saka gilasa a fuskan shi, domin baiso a gane damuwar sa.
Yana rufo gidan sa, yaji motsin tafiya, bayan ya rufe ya juyo domin tafiya, sai yaga Joy tsaye kusa da gidan nasa, ta jingina da bangon gidan su Aisha, hannun ta rungume a 'kirjinta.
Idanu wan ta nakan sa tunda ya fito, d'auke kai yayi kamar bai ganta ba tare da had'e fuska ya fara tafiya.
"Nagode doctor" tace cikin za'kin murya, tsayawa yayi cak, tare da sauke 'boyeyyen numfashi.
Can kuma mai ya tuno kawai sai ya wuce fauuuuuuu.
Murmushi ta saki tare da lumshe idanuna ta, tana mai bin bayan sa da kallo.
Bata bar kallon sa ba har dai ya kure mata.
Sa'an nan tayi gidan su Aisha.
Manager please
Share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³π³
(Ta'kai taccen labari)
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
*π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«*
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
A fuwan my fan's, bakuyi fushi bako? nama sani baza kuyi ba domin kun kasance masu ha'kuri dani, ina godiya sosai sosai.
Dedicated to my fan's, luv you guysπ₯°
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
π
Ώ1⃣5⃣to1⃣6⃣
Shiga gidan su Aisha tayi, maman Aishan ne zaune a kusa da murhu tana fiffita wuta, "sannu da gida mama" tace tana d'an du' kawa kad'an.
"Yauwa Joy" tace fuskan ta d'auke da murmushi, "mama Aisha ta dawo kuwa?" "a'a, amma yanzu zaki ganta don zataje islamiya anjima, okay" tace tana mai zama a kan turmi dake tsakar gidan.
Suna zaune shiru sai ga Aisha tayi sallama, ansa mata mama tayi. Ita dai Joy kallon ta kawai take.
"Besty yakike" cewar Aisha lokacin da ta'kariso gaban ta.
"Lafia" kawai tace da ita "zo muje ko?" Aisha tace, mi'kewa tayi sukayi d'akin Aishan.
Kwanciya kawai tayi a katifar Aisha daga shiga d'akin.
Kallon ta kawai tayi ta kyauda kai, domin tunda taga haka to miskilancin ne tsaba ya tashi.
Sai dai abin mamaki gani kawai tai lokacin da ta waigo tana ta faman murmushi.
Cire hijabin hada tayi tare da d'aukan na islamiya ta saka.
Zama tayi kusa da ita tare da cewa "besty zani islamiya, zanje na dawo nasha labari domin da alama dai wanan murmushi da ake saki zanji labari mai dad'i".
Ta'ba baki tayi tare da mi'kewa " sai ina kuma besty? inace zaki jirani na dawo ne?" "Uhu'um" tace da ita tare da riga ta barin d'akin.
Sometimes tana mamakin 'kawar nata, "wata irice ita gadai tanan".
Fito wa tayi lokacin har takai 'kofar gida, 'kofar gidan su ta tsaya tana kallon gidan Auwal.
Fitowan Aisha yasa ta kauda fuskan ta daga wurin ta maida kan Aishan.
" Besty sai na dawo ko?" d'aga mata kai kawai tayi, ita kuma ta wuce makaranta ta.
"Baki gajiya kedai, kullum makaranta, ina zan iya wannan wahala, ga wani abu biyabiya dashi".
Tace tana ta'be baki tare da barin kallon 'kawar tata.
Tsawon lokaci tana tsaye a wurin kafin tayi cikin gida.
Koma wanta da kad'an maman ta ta dawo, saukan ta a mashin Auwal ya fito daga gidan sa, da murmushi ya'ke yace "sannu da zuwa, yauwa yaron kirki" tace dashi "Joy ta dawo kuwa?".
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tokare masa, amma ya daure yace " uhmm".
Shiga gida tayi shi kuma ya wuce inda zashi.
****
Watan Auwal shida a 'KAUYEN 'YAR KADDE, abubuwa da dama sun faru, daga ciki akwai yawan shige masa da Joy keyi, kamar idan ta gansa ta gaishe sa da dai sauran su, ta rasa maike damun ta dangane dashi, kuma sau goma zata masa magana bazai tanka taba, duk sanda ya ganta idan a hanya ne canza hanya yake, idan kuma ta tasame sane sai ya d'auke kai yayi kamar bai ganta ba.
******Auwal kwance yana waya da mami sai faman narke mata yake tana biye masa "mami don Allah ki ro'ki Dady ya yarda na dawo, wallahi mamina nayi missing d'in ki, ga 'kauyen ko dad'i babu, har yanzu ban saba dashi ba".
" Ga sister zata dawo nan da sati mai zuwa,".
"Ni Auwal bansan yadda zanyi ba, nayi nayi koni nazo na ganka ya'ki, bansan yadda zanyi ba nima inason naga boy d'ina" tace tana murmushi.
Turo baki yayi tare da cewa "mami niba boy bane gaskiya na girma" "da gaske my son? uhum".
"Amma mami na haka zanta zama sai na shekara sanan zan ganku?, eh son tunda haka Dadyn ku yake so".
" Haba sai kace mara gata, mara galihu? hab fisabilillahi kamata haba mami na, do something ".
" Hmmm, bari zan jaraba Allah sa adace, amin mami na, ko kuma kawai kisa 'yan gaban goshin sa agaba nasan suna cewa zaiyi na'am".
"To bari suzo muga" "yauwa mamina shiyasa nake tsananin 'kaunar ki, love you mum" yace tare da sakin masa kiss ta wayar.
Dariya tayi tare da kashe wayar, shiko wani farin cikin da yadad'e baiyyi ba yaji ya mamayeshi smiling kawai yake.
Tashi yayi daga kwancen tare da shiga toilet yayi wanka, T-shirt mai ratsin baki da fari yasaka da ba'kin wando, kayan sun matu'kar kar'ban sa.
Kallon kansa yayi a mirror shi kansa yasan ya had'u, smiling yayi tare da cewa "yaron mami ka had'u" tare da cewa yima kansa kiss ta mirror d'in.
Bayan ya kintsa ya fito domin le'ka asibiti lokacin la'asar ne sakaliya.
Yana rufe gida ya juyo yaga mutum a bayan sa, kauce wa yake ninyan yi ta tare, tace tana ya mitsa fuska "doctor cikina na ciwo ko zaka taimakamin please?".
Kansa na kallon gefe yace " nan ba asibiti bane, baya ga haka kije kinemi wani not me".
Kallon sa take ta 'kasan ido, "zaki iya bani hanya na wuce" yace fuskan sa kamar wanda bai ta'ba dariya ba.
"Kayi Kyau" tace a hankali tare da matsa masa a kan hanya.
Ya fara tafiya yaji kamar ana binsa a baya, bai waigo ba sai da yaje 'kofar asibiti sanan.
Ganin wace ke bayan sa ya had'e rai tare da shigewa.
Cigaba da bin nasa tayi har 'kofar office d'in sa, bud'e wa yayi tare da shiga, zai rufe ta turo jikin ta.
"Kibar wurin nan", " doctor nazo fa domin lafia tane, da gaske banda lafia ka yarda dani" ganin kallon da yake mata yasa tace haka.
Bud'e mata yayi ta shiga, zai duba ta kodon maman ta.
Zama yayi a kujeran sa, ita kuma tana nan tsaye, nuni yayi mata da hannu alaman ta zauna.
Zaman tayi sa'an nan yayi shiru yana jira daga gare ta.
Tasani sarai tagane nufin sa amma ta share sai ma 'kare masa kallo da take.
Gajiya yayi ya mi'ke domin zuwa duba marasa lafia, itako tana nan zaune ko motsawa batayi ba.
Fita yayi ya barta ba tare da yace da ita komai ba.
Kallon office d'in take lungu da sa'ko, ba wani babba bane tunda na 'kauye ne, amma da yake na d'an gata ne ba laifi yayi Kyau.
Tashi tayi taje kan 'karamin bed d'in marasa lafia da yake office d'in ta kwanta tana mai lumshe ido lokacin ne taji ciwon ya taso mata, don haka sai ta fara mur'kususu.
Dai-dai nan Auwal ya bud'e 'kofar, ganin bata a kujeran da take yasa shi ajiyan zuciya tare da cewa "mayya kawai ta tafi......." Bai 'karisa zancen saba yaji nishi .
Waigawa inda yake jiyowa yayi kwance ya ganta a gadon.
Tana mur'kususu, d'auke kansa yayi kamar bai ganta ba, abinda yazoyi yayi ko ya gama don haka sai ya tattara abinda yazo dashi domin koma wa gida.
Aje key d'in office d'in ya aje tare da ninyan fita yana cewa kamar mai ciwon baki "idan kin tashi sai ki rufe musu office d'in su".
Kuka mai had'e da ehu ta saki tare da cewa " wayyo doctor zan mutu kataimakeni please, mama tace nazo ka dubani".
Dawo wa yayi tare da cewa idon sa na kallon gefe "meke damun ki?" "tunjiya da dare nan kemin ciwo, ina kenan?" yace ba tare da yajuyo ya kalle ta ba.
"Nan" tace, shi kuma yace cikin gajiya da 'kufula "shi wurin baida suna ne?" shiru tayi tana mai cigaba da kukan ta.
Haushi yaji zai fita, itako ta dage iya 'karfin ta tasaki ehu mai 'karfi.
Toshe kunnin sa yayi tare da kallon da azafafe ya nufo ta.
Kamar zai bugeta yace "wallahi kika sake min 'kara a kunni sai naci....." sai kuma yayi shiru.
"Ina kemiki ciwo? yace yana hararan ta.
Maimakon ta bashi ansa sai ta cigaba da kukan ta.
" Tashi kibarmin office yanzun nan kafin ranki ya 'baci" yace yana matsowa kusa da ita.
Bai aune ba kawai yaji ta kama masa hannun, da mamaki da ba'kin ciki yake kallon ta.
Bai gama mamaki na yaji hannun sa a lallausan jikin ta.
A han maran ta ta d'aura hannun nasa.
Cikin kuka tace "nan ne kemin ciwo" fisge hannun sa yayi cikin masifa yace yana tofar da yamu.
"Banza 'kazamiya, amgaya miki kowa 'kazami ne irin ki? ko ance miki ni Auwal irin karnikan kine 'kazamai Wanda basu san inda yake musu ciwo ba irin ki".
"Zan miki gargad'i da babban murya ni Auwal nafi 'karfin ki, nafi 'karfin 'kazan taccen jikin ki, kuma ki fita harka ta, idan ba haka ba ki kuka da kanki".
" Banza kawai, Auwal ba jaki bane, kisani koda ni mazinaci ne irinki to bancin sauran wasu, kina mace mai aji da kima da daraja amma kinzubar dasu, koba abun abun mamaki bane arna zasuyi fiye da hakan".
Ya sake tofar da yamu idanun sa ya rufe yayi ta surfa mata ba'ka'ken maganganu.
Koda ya gama bai damu da kukan da take da juye-juyen da take ba.
Yabar office d'in tare da sanar da mai gadin wurin idan ta tafi ya rufe masa office d'in ya'kara gaba.
Tafiya yake yana ganin dishi-dishi domin abinda yafaru yana ganin sa a idanuwan sa kamar yanzu ake.
Kuma ya tabbatar da zarginsa 'yar iskance ita......
Tofah fan's kunji fan
Kubiyoni domin jin yadda zata kaya, amma hakan bazai samu ba sai naga comments.
Comment & share pls
'Yar Aliyu ce✍π»
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
*Dedicated to my family*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
π
Ώ1⃣7⃣to1⃣8⃣
"Dole na cire ki a raina, kota halin 'ka'ka kuwa, zuciya baki min adalci ba, taya zaki sa naso wacce bata dace dani ba? yes bata dace dani ba, bata cancan ceni ba. Ni mai tsaftane ita 'ka zama, ya Allah fitar da ita a zuciya ta". yace yana mai rintse ido, lokacin yana kwancen a bed d'in sa, babu abinda yake tunani sai ita, tunani halin da ya baro ta kawai yake.
***Ta d'au tsawon lokaci a wanann yana yin, tana cikin damuwa mai tsananin, abu uku ke damun ta. Na farko 'kama da Auwal ya kira ta hakan yayi mata zafi sosai, ta gane cewa yana zargin ta da aika ta fasi'kanci, abinda bai sani ba, zina abune da take matu'kar 'kama, hakan da ya matu'kar tsaya mata a rai.
Na biyu ciwon maran dake damun ta, ba'kin ciki yasa ya rage mata kaso hamsin na ciwon.
Na uku tsananin 'kaunar sa da bata san tanayi ba sai yau, gashi Auwal yayi mata nisa, kalman sa kawai yasa ta gane tsananin kiyayyar da yake mata.
" Ina son ka, wallahi ina son ka, ina tsananin 'kaunar ka, 'kaunar ka shine ajalina zan rayu da son ka duk da nasan baza ka ta'ba sona ba".
Tace tana mai fashe wa da kuka mai tsanani, a daddafe ta bar office d'in nasa, idan nun ta nata zubar 'kwallah.
A haka taje gida bata damu da kallon da mutane kema taba sam.
Tana shiga ta tadda uwar ta a tsakar gida, ganin yana yin da 'yar tata ta shigo yasa ta isa gare ta da sauri ta taro ta.
Tare da tambaya ta abinda ke damun ta, shiru tayi mata tana mai cije le'be.
Tambaya duniya nan uwar ta mata amma ta share ta, ganin haka uwar ta fita harkan ta duk da yanayin da 'yar tata ke ciki na damun ta.
Kwanciya tayi tana mai tsine ma isah domin shi ya janyo mata tsana da 'kiyayyar da Auwal yake mata.
••••••••••••••••Yau kimanin kwana hud'u kenan Auwal ya'ki fita ko waje komai a gida yake yin sa, duk yayi wani iri saboda damuwa dake d'awainiya dashi.
Ta kai ta kawo har da Kuka, kwancen yake yana tunani da ya zame masa abinci domin abincin ko damuwa dashi baiyi.
"Na sani ina sonki, so mai tsananin ma kuwa amma sai dai ya kasheni da dai na auri sauran wani, na tsaneki ban sanki daga yau" yace yana maiji zafi a zuciyar sa, domin tuno cewa ita sauran wanine ya hadda sa masa damuwa fiye da nada.
Wanda har tsanan ta wani sashi na zuciyar sa yake.
'Karar wayar sa ce ta dawo dashi daga halin da yake ciki.
Kallon wayar yayi na wani lokaci kafin ya d'ako, ganin mai kiran sa yasa shi peaking tare da sakin murmushi da ya kwana biyu baiyi ba.
Kafin tai magana ya riga ta da cewa "sweetheart" yana jan numfashi.
Dariya tayi tare da cewa "na'am sweet bros, yakake d'an 'kanina?" shiru yayi kamar mai tunani.
"My Auwal kanajina kuwa?" shiru ba ansa ta sake cewa "kana lafia kuwa my bros? talk to me please " tace cikin tashin hankali.
Sanin halin ta yasa shi
'bata rai tare da cewa "sister ba 'kalau nake ba sam".
" Oh my god!!! what happen?, sister my heart" sai kuma yayi shiru.
"Mai ya same ta?, ciwo take sister, kaje a duba ka mana".
" Na'ki gida kawai nake son dawo wa, mai yasa?" tace dashi, "'kauyen babu dad'i, ina son na dawo kafin ki dawo, don Allah ki ro'ki Dady na dawo".
" I miss you sister nd mamina, Auwal kenan Dady fa ya kafe ya nace yace sai ka gama sannan zaka dawo, kuma ma idan nazo dole nazo na ganka".
"Kad'an mafa ya rage maka, sister baza ki gane ba Wallahi ni gida nake so".
"Yanzu ya kake son ayi?, ki ro'ke sa nasan zai amince na dawo kinji tawa".
Shiru tayi ya sake cewa " pleaseeeee" .
"Naji, amma kamin al'kawari zaka koma duk lokacin da aka bu'kaci hakan".
" Na amince" nan dai sukai sallama.
°°°°°
Kwana hud'un nan Joy ta kasance cikin tsananin damuwa, damuwa ba d'an kad'an ba.
Tana son ganin sa, tana son jin murya sa, amma ta yaya? tunda ya'ki fita daga gidan.
"Inason ganin sa, bazan iya barci ba yau idan ban gansa ba" tace cikin damuwa.
Mi'kewa tayi tare da shirya wa, yau anyi abin arzi'ki, domin shigan dogon riga mai roba d'in nan tayi.
Yayi mata Kyau matu'kar gaya, har dasu rolling.
Da yake yau Sunday akwai church madam Gloria ta dad'e da tafiya.
Ta fashe jikin ta da turare mai dad'in 'kamshi, tana gama shirya wa ta kulle gidan sanan ta nufi gidan Auwal gaban ta na mugun fad'uwa.
Tura 'kofar tayi taji ya bud'e, tana jin mugun fad'uwan gaba tayi cikin gidan cikin sand'a kamar wata 'barauniya.
Tunda ta shigo take jin 'kamshi girki da mamaki ta 'karisa shigo wa.
Babu kowa a tsakar gidan don haka d'akin taga an sakayo ta nufa.
Tura wa tayi wani sanyin dad'i da ni'ima taji, "hmm, komai naka cikin tsarin yake kuma mai kyau ne. Ina son ka my man".
Shiga tayi babu kowa a parlour, zama tayi a d'aya daga cikin kushin d'in parlour.
Tayi kusan 5mint babu alamar sa, don haka sai ta nufi bedroom d'in sa.
Fito war sa kenan daga toilet, towel d'aure a jikin sa, d'aya kuma yana goge fuskan sa.
Tana ganin haka ta dawo baya tana mai runtse ido tare da dafe 'kirjin ta dake bara zanan fashe wa.
Ga wani mugun tsoron sa da taji ya ziyar ce ta, don sai yanzu take da nasanin shigo masa gida.
" Oh my god!! bari na bar masa gida tunda bai ganni ba, don idan ya ganni Allah kad'ai yasan abinda zai min".
"Uwa uba zargin sa zai 'kara tabbatar wa" tace tana mai fita daga parlour kamar yadda ta shigo, haka har ta fita gidan.
Tana fita ta fara sauke numfashi kamar wacce tai gudu, tana cewa "thank god! I'm safe".
Tana mai dafe da 'kirjin ta.
Jin kamar motsi tabar jikin gidan da gudu ta koma nasu Aisha.
" Ashe ba kowa bane" tace tana dariya da tunda nake da ita ban ta'ba ganin tayi ba.
Kuma dariyan ba 'karamin kyau yayi mata ba.
Tana nan tsaye na kisan 30mint sai gashi ya fito cikin shiga na alfarma.
Farar shadda yasa, shaddar tayi matu'kar 'kar 'bansa.
Bai lura da ita ba sam har ya rufe gidan nasa, yazo zai wuce ne ya gan ta.
Kauda kansa yayi tare da had'e rai, gaban ta taji ya fad'i amma ta daure tace cikin sanyin murya "doctor barka da safiya" yayi banza da ita.
"Doctor I'm sick" nan ma ya share ta, domin tafiyar sama yake.
"Hmm" tace tare da lumshe idanun ta, tana mai kallon bayan sa har ya 'bace mata.
"Allah tsareka ya kareka my one nd only" tace farin ciki na cika ta.
°°°°Shiko Auwal yaje sayowa su mami tsaraba ne domin anci nasara Dady ya yarda ya dawo yayi kwana goma.
Saboda farin ciki yasa yaje har cikin garin keffi yayi musu tsaraba na gani na fad'a.
***Joy ko bayan tafiya sane ta nufi church tana ta faman murmushi, koda tazo uwar tayi garin ciki sosai domin bata ta'ba zuwa da wuri irin haka ba.
Bata tashi zuwa sai an tashi ko an kusa tashi, duk fitinan uwan da masifar ta bai sa gobe taje da wuri.
Bayan sun tashi barin uwar tayi tayo gida domin ganin sanyin idanun ta.
Koda tazo bai dawo ba, don haka sai ta bud'e gidan su ta shiga, wanka ta sake she'kawa .
Bayan tai wanka ta zauna ta tsantsara kwalliya, tasaka riga da wando, rigan mai dogon hannun sai dai ya kamata cif.
Wandon ma dogo ne amma ya matse ta, a shekarun nan nata tana mamaki girman halintatan ta, tana ganin wad'an da suka girme ta da shekaru goma ma basu da cikin halita irin tata.
Komai ta mallaka, jujjuya jiki ta kamayi tana kallon mirror, ta saki wani 'kaya tattacen murmushi.
"Kai ma nasan kana 'kasa wa, nasan ina burge ka, nasha jin anace wa maza nason irina".
" Kama kana so ko?" tana mai kashe ido d'aya, dariya ta fashe dashi.
"My man, humm, kana mugun burgeni, kana tafiya da imani nah" tai 'kwal-'kwal.
Cikin tausayin kanta tace "zaka aure ni?, ka aure ni don Allah, wallahi babu wanda ya ta'ba sanina, ban ta'ba fasikanci ba. Zina! Na tsane sa, abinda baka sani ba inda tsoro bazan iya bawa wani kai na ba".
" Nasan darajan kaina, ganina da d'an iskan nan da kai Wallahi fyad'e yake son min, bai min komai ba shine ka ceceni".
"Ka bar zargi na don Allah" ta fashe da wani irin kuka mai tsanani bayan ta gama surutun ta.
Sai da tayi mai isan ta sanan taje ta wanko fuskan ta, wanan karon powder kawai tasa sai man baki
Fita tayi waje, ganin 'kofar gidan sa a rufe yasa ta tsaya 'kofar gidan su idon ta nakan hanya don ganin 'bilowar sa.
Tana nan tsaye Aisha ta fito, ido Aisha ta kura mata kamar wacce bata ta'ba ganin taba.
Hararan ta Joy tayi tare da d'auke kai, dariya ta bawa Aisha, 'kariso wa gare ta tayi tana mai cewa "Allah besty kinyi kyau, wanan da dama dama dai, Allah sa kidai na saka irin wad'an nan ki dawo saka namu".
" Shigan mutunci sai yafi kyau dake" ta 'karsa murmushi d'auke a fuskan ta.
"Bazai ta'ba yuwu wa nasa kaya irin naku ba, ke bazan iya ba sam, haka kawai nasa kayan da zai rin'ka damuna".
" Uhum'um bazan iya ba, ku muslmai gaskiya addinin Ku da kawai takurawa".
"Muko namu sam babu ta kura, za kai shigan ka yadda kaso".
" Ni wallahi kinzo kina ma damuna, kina samin ciwon kai kina ta sani surutu".
"Allah baki ha'kuri besty nayi nan" ta gane sarai fishi tayi amma ko a gefen gyelen ta.
Tafiyan Aisha da kad'an sai ga Auwal ya fito daga taxi.
Kayan sa ya fara fito wa dashi, bayan ya gama fito wa dasu tas ya sallami wanda ya kawo sa.
Waige yayi ko zai sami wanda zai taimaka masa, kawai sai yaga Joy tsaye tana kallon sa.
'Dauke kai yayi tare da bud'e gidan sa ya fara shiga da kayan.
Ya kai na farko da na biyu duk tana tsaye, ya dawo domin sake kwashe sauran.
Ya kai hannun sa da ninyan d'auka itama takai nata.
'Daga kai yayi tare sa wurga mata wani hararan mai firgitar wa.
Ta tsorata matu'ka amma bata dan dara ba.
Yana d'auakn wanda takai hannun yayi ciki dashi ita kuma ta kwashe sauran ta bisa.
Ya aje kenan ya juyo sukai karo.
Sakin kayan tayi tare da sakin 'kara "wayyo Allah doctor akawai zafi sosai wallahi" tace cikin shagwa'ba.
Cikin masifa yace "amma dai ke jakace ko?" shiru tayi cikin jin zafin maganan sa tana kallon sa.
"Dai na kallo na mayyah da 'ki'kiya, ballagaza, shashsha sauran maza".
" To duk mai tanki nafi 'karfin ki wawuya kawai, fice min a gida idan ba haka ba" yayi 'kwafa.
Kuka ta fashe dashi tare da cewa "ni kazaga?" Yace cikin tabbatar wa "eh dan ubanki ko kina da abinda zakiyi ne?".
Zuciyar ta taji yana ta farfasa, don haka tace " karka sake zagin ubana idan ba haka ba zakai nadama".
"Nadamar uwarki zanyi wawuya?, to ance ubanki ke uban naki ma yaci uban sa, kakanki kenan".
" To wallahi duk maitarki haka zaki bar Auwal, fita maza".
Son da take masa yasa ta kasa yin abinda tai ninya don haka sai ta tashi tabar masa gidan sa.
Ganin comments zai taimaka matu'ka wurin cigaba da labarin nan.
Amma banyi al'kawarin kullum ba, idan na samu time zakujini. Kuyimin uzuri don Allah, ba'a son raina bane, ina tsananin 'kaunar Ku masoya na farin cikin ku shine nawa ngdππ»
Comment & share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
*Dedicated to my family*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
π
Ώ1⃣9⃣to2⃣0⃣
°°°°°°
Joy tunda ta tashi take jin ta wani iri, haka take shirin makaranta cikin sanyin jiki, bayan ta gama ta sallami maman ta ta fito, tsaye take a 'kofar gidan su tana kallon gidan Auwal tana jin fad'uwan gaba mai tsanani a tare da ita. A haka Aisha ta fito ta ganta, 'kariso wa wurin ta tayi tare da ta'ba ta domin tayi nisa a tunani, tace da ita "besty muje" figit ta dawo daga dogob tunani da ta tafi.
Har sun fara tafiya ta waigo tana mai sake kallon gidan Auwal, gani take zai fito, "lafia kuwa kike besty?" Shiru babu ansa sai ma kauda kanta tayi idon ta fal da hawaye jikin ta na bata cewa wani mummunan abu zai same ta.
Wani zazza'bi taji yana son kama ta, domin fad'uwan gaban ta 'karuwa yayi wanda har sai da Aisha taji.
Tsayawa tayi tare da ru'ko ta, tana ware ido cikin tsoro da damuwa tace "besty baki da lafia ne?" kallon ta tayi tare da bud'e baki da ninyan yin magana, amma ta kasa sai ma fashewa da kuka tayi tare da zamewa ta zauna a dam'ban kan hanya.
Dur'ku sawa Aisha tayi itama har ta fara kuka, domin Allah ya saka mata tsananin 'kaunar Joy d'in.
Kamo ta tayi da ninyan d'ago ta amma ta'ki bata dama.
Cikin kuka tace "besty tashi mu koma gida tunda baki da lafia" girgiza mata kanta tayi, alamar a'a.
"Meke damun ki besty? kanki d'aya kuwa?, kina ganin inda kike zaune kuwa?" shiru babu ansa sai cigaba da kuka take mai matu'kar ban tausayi.
Rungume ta tayi suka cigaba da kukan su babu mai lallashin wani, ga garin shiru-shiru da yake anyi ruwa sama da asuba kowa ya 'boye a d'aki saboda sanyi.
°°°°°
"Ya zanyi na sami motar da zata kaini gida?, shegen 'kauye babu ko taka mamman mashin bare ka samu mota, wallahi yaya kun cuceni" cewar Auwal da ya gama shiri tuntuni yana mai burzar da isaka.
"Wayyo mamina ya zanyi yanzu?" d'ako wayar sa yayi tare da dialing number mamin tasa.
Tana peaking ya fashe da kuka kamar wani yaron goye.
"Menene son?" shiru ya'ki magana sai cigaba da kukan sa yake.
"Na shiga uku son meya faru kuma? yi magana mana, koso kake ka ruguza farin ciki na? ina murna zaka dawo yau na ganka amma kana kuka, oh Allah na yaushe yaron nan zai girma".
Cikin shagwa'ba yace " mami babu mota fah a garin nan, yanzu ya zanyi na taho? ko mashin basu da".
"Jiya da zani cikin gari ba'karamin wahala nasha ba" .
"Yi ha'kuri my son, ka fita kaje cikin gari ka nemo taxi ya kawo ka, ko nawa zan biya kaji? maza my son".
" To mami na, amma fah da wuya 'kafana bai kumbura ba, jiya mafa 'kafana na taka har na kusa barin garin sanan na samu mashin".
"Insha Allah bazai kumbura ba, da yarda Allah kana fita zaka samu maza yaron mami".
Kashe wayar yayi tare da mi'kewa ya fita, sanye yake cikin 'kananun kaya kayan sunyi matu'kar kar'ban sa, saboda sanyin da ake sai ya sanya jacket akan kayan.
Tafiya yake cikin natsuwa, da kagan sa kaga had'ad'an gaye.
Har yanzu suna nan zaune suna ta faman kuka kuma cikin sanyin, fad'uwan gaban ta yana 'karuwa, jikin ta na bata yana kusa da ita.
Waigen hanyan gidan su tayi ta hango sa gaf dasu, murmushi ne ya su'buce mata, tare da kafeshi da ido tana share hawaye dake zubo mata.
Da mamaki Aisha ke kallon ta, murmushi da bata ta'ba gani ba a fuskan 'kawar tata ce ta gani kwancen a fuskan ta.
" Besty kece kuwa? wallahi kinyi mugun kyau, ko dama ke kyakkyawa ce, kin 'kara kyau" Aisha tace tana mai ta'ba ta.
Ta'ba tan da tayine ya fargar ta ita 'baran-'bara man da take son tafkawa.
Domin tayi al'kawari ko son sa zai kashe ta ko uwar ta baza ta sani ba har sai idan ya furta mata cewa yana son ta.
Kauda kanta tayi daga kallon sa don kar Aisha ta d'ago wani abu.
Murmushi gefen baki tayi tare da cewa cikin miskilancin ta tana mai kallon sa da ya kusa inda suke.
"Nagode" tace tare mi'kewa, mi'kewa itama Aisha tayi tana cewa "besty kin 'bata kayanki, kuma kinsa mun makara sosai mu koma gida tunda haka kike so".
"Amma wai don Allah me yasaki kuka ne haka? kuma lokaci d'aya kin ware?".
Share ta tayi tana mai du'kar da kai 'kasa, domin Auwal yazo dai-dai dasu.
Yana ganin su ya d'auke kai fuska a murtuke, yana wuce wa Joy ta sani numfashi tare da dafe zuciyar ta.
Tayi shiru na wani lokaci sannan ta fara tafiya, biyo bayan ta Aisha tayi tana mamakin miskilancin bestyn nata.
Haka suka zo har gida babu mai ce da d'an uwan sa komai.
Aisha ce dai tace da Joy lokacin har tasa 'kafar ta a cikin zauren gidan su " sai anjima besty" kai kawai ta d'aga mata tare da shige wa gida.
***"Lafia kika dawo yanzu? anya ma kuwa?, bakuje makaranta taba" cewar maman Joy.
Jefar da jakan makarantan tayi a tsakar d'akin ta zauna a kujera tayi shiru na wani lokaci.
Sannan tace cikin 'kasa da murya "bamu sami zuwa ba. Meya sa to" cewar uwan shiru nayi bance komai ba sai ma kwanciya ta da nai ina mai lumshe ido.
Girgiza kai mama tayi tare da cewa "ubangiji ya shirye ki" ta shige cikin d'aki.
Murmushi nayi tare da cewa a hankali "ameen, handsome ina zaka ne haka cikin kyakkyawar shigan dani kad'ai ya cancanta na gani?".
" My man karka kalli kowa please, zama makaho kaji, ka zama kurma kaji".
"Allah sa karsu kallan min kai" tace tana dariya a hankali tare da rufe fuska.
A haka mama ta fito ta same ni, "anya bazan kaki a duba 'kwa'kwalwarki ba?, kwana biyun nan baki da aiki sai dariya da magana ke kad'ai".
Kallon mama nayi tare da shagwa'be fuska ina mai cewa " lafia ta qalau" na mi'ke, cire uniform d'in nayi tare da shiga cikin d'aki na d'ako zani na d'aura a 'kirji.
Har zanyi bayi sai mama take cewa "bari na le'ka 'kawata na dawo, tunda yau kin'ki makaranta sai ki mana abinci" har ta fita ta dawo ta sake cewa "Joy kina ganin doctor kuwa?" shiru nayi ina maijin sanyi a raina danaji an anbaci masoyina.
"Ina magana kina jina kuma, banson iskanci" cikin sanyin murya nace "a'ah" kawai nayi toilet.
Ina jinta tana cewa "ko lafia yake oho" ta fice.
Na fito wanak kenan naji 'karan mota, gabana naji yayi mugun fad'uwa don haka banjira komai ba nayi waje da d'aurin 'kirji.
Mota nagani a dai-dai gidan Auwal, tsayawa nayi tare da kallon gidan inajin wani yanayi .
Ganin wani ya fito a gidan da kaya yasa nayi cikin gidan.
Karo mukaci dashi, "asshhh" nace ina dafe goshi na.
Kallon sama da 'kasa yayi min tare da tofar da yamu ya ra'ba ta gefe na ya kwashe kayan da suka zuba ya fita ya barni a wurin.
Shiga cikin parlour nayi naga kaya a tsakar parlour harda akatin kayan sa.
Zama nayi ji'bus tare da ri'ke kaina da ya saramin.
Bansan sanda hawaye ya zubomin ba, ina zaune ya shigo shida mutumin ko yasan Allah yayi ruwana a wurin kwashe sauran sukayi tasa ina kallo hawaye nata kwaranya.
Bayan sun gama fita da kayan ya dawo don rufe gida, tsaye yake yayi shiru don baison magana ta had'a su ko kad'an.
Bai aune ba yaji an rungume sa tare da cewa "ina zaka doctor? nine ko? yi ha'kuri daga yau na bar maka magana don Allah ka zauna" nace ina kuka mai cin rai.
Wani irin mugun abu yaji yana fuzgan sa, domin ta mana masa a bubuwan ta a jikin sa.
Ji yayi 'kafa funsa suna neman gagaran sa, yun'kurin ture ta yayi amma ina ta 'kan'kame sa.
Cikin wani yanayi yace "don Allah rabu dani tafiya ce a gaba na, nd sau nawa nake gaya miki ki rabu dani ki fita harka ta?".
" Nifa ba d'an iskan bane" "nima haka" nace cikin kuka ina zare jiki na.
Tsare sa da ido nayi tare da cewa "ina zaka?".
" Inda kika aiken uwata" yace yana hararana.
Murmushi mai ciwo nayi tare da cewa "na takura ka ko?, oho miki, sanan banda lokacin kini sai kibi wani bani ba don ni Auwal gaba nayi".
Dur'ku sawa nayi gaban sa tare da son ri'ke 'kafar sa, han'barina yayi tare da cewa " fita min a gida na rufe malama".
Ko motsi banyi ba, wata irin tsawa ya daka min, ba shiri na mi'ke nunamin hanya yayi tare da cewa "maza barmin gida na, maza ko kuma na caza miki kaman nu".
" Kuma gargad'i na 'karshe ki fita gona ta" yace yana mai sake daka mata tsawa.
Da gudu na fita, domin ya mugun firgitani.
Rufe 'kofar parlour da gidan yayi tare da shiga mota suka bar wurin .
Ina tsaye a cikin zaure ina kallon sanda motar tabar 'kofar gidan.
Kuka na na cigaba dayi na dad'e ina kukan, ban bari ba sai ma shiga gida da nayi ina cigaba da kuka na, babu maganan girki sam don na manta da lamarin sa, kuka kawai nake ta...
••••••••••••••••••°°°°°°°°°°°°°•••••••••••••••••
Tunda Auwal yaga sun kusa layin su wani irin farin ciki yakeji, yau dai zai ga mami zai kwanta a cinyan ta, zata basa abincin ta mai dad'i zata cidashi.
Haka yayi ma mai taxi kwantan ce har suka zo 'kofar gidan su.
Horn driver yayi, mai gadi ne ya fito har wurin motan yazo tare da kallon mai taxi d'in yana cewa don sam bai lura da Auwal ba.
"Wa kake nema ne malam?" Kafin ya bada ansa Auwal ya fito daga cikin motan.
Hararan sa yayi tare cewa "zaka bud'e ko sai ka rasa aikin ka?" da gudu ya nufi get d'in yana cewa "yi ha'kuri alhaji bansan kai bane".
Koma wa motar Auwal yayi driver ya tada motar suka shiga, mai gadi na cewa " barka da dawo wa " hannun kawai ya d'aga masa.
A compound d'in gidan Auwal yace wa mai taxi ya tsaya, yana tsayawa ya fita a motar .
Mai aikatan gidan dake kai kawo suna ganin sa suka nufo wurin da gudu sauri-sauri.
Sannu da zuwa suka masa ya ansa yana shige wa ciki, yana shiga 'kayataccen parlourn gidan babba dashi wanda aka 'kawatashi da ababen more rayuwa.
"Mamina where are you?, am back, your handsome is back" yace yana kalle-kallen parlour don ganin ta ina mamin tasa zata fito.
Da murmushi farin ciki uwar ke sakowa daga steps .
Da gudu ya 'karisa gare ta, yana isa gare ta ya rungume ta.
Cikin farin ciki tace "oyoyo my happiness, godiya ga ubangijin tali kai da ya dawo min da farin ciki na lafia, welcome back autan mami, jarumin jarumai".
" Fitilar gidan Kabir Mu'azam, farin wata shakallo, sannu da zuwa shalelen Rahama da mami".
Wani irin farin ciki da natsuwa yakeji jinsa a jikin mamin sa.
Cikin shagwa'ba yace "mamina I miss you so much" kamar zaiyi kuka.
Bubbuga bayan sa tayi tare da cewa "nima haka son, muje kayi wanka sai kaci abincin ka huta".
Tana ri'ke dashi sukayi d'akin sa, had'a masa ruwan wankan tayi tare da kama sa, sai da takai sa bayin sanan tace " maza kayi wanka ka fito my handsome " ta fita.
Sai da ta fitar masa da kaya sanan ta sauka, zaune ta tarar da Baraka cikin girmama wa tace "HAJIYA wanda ya kawo autan ki yana jira a sallame sa".
" Ayyah yana ina?" "yana compound, okay kun bashi abinci kuwa?".
" Eh" "okay ina zuwa" tace tare da wuce wa d'aki.
Kud'i ta d'ebo masu yawa bata damu da ta duba ko nawa bane ta fito.
Har inda yake taje ta basa tare da masa godiyan kawo mata yaro cikin 'koshin lafia.
Godiya shima yayi sosai yana mamakin karamcin da aka masa, yana mamakin irin kud'in da aka basa .
Cikin farin ciki yabar gidan bayan ya fitar musu da kayan Auwal d'in.
°°°°Cikin jin dad'i yayi wankan sa, gurje jikin sa yayi sosai da sosai, kai kace zai sake fata.
Yana fito wa ya wani fad'a bed d'in sa yana cewa "Allah sa mami karta yadda na koma wanan 'kauyen mai cike da 'kazamai".
Tsaki ya saki domin Joy ce ta fad'o masa a rai.
Tashi yayi tare da shafa mayuka maau tsada sai 'kamshi suke.
Kayan da mami ta fitar masa ya saka tare da feshe jikin sa da turaruka.
Fito wa yayi sak Auwal d'in mami ba na 'kauye ba.
Tunda ya sako mami ta kafe sa da ido har ya 'kariso gaban ta.
Hawaye taji nason zubo mata amma ta matse, ta'ba wuyan sa tayi lokacin ya zauna kusa da ita.
" Auta ciwo kayi ne wai?" turo baki yayi tare da cewa "mami ba sai da na gaya miki ba?, ai wanan 'kauyen babu abinda bazai sa mutum ba. Don Allah mami na kada ki bari na koma idan ba haka ba sai kinyi kuka idan kika ga yadda yaron ki zai koma".
" Kayi ciwon kenan?, a'a kawai 'kauyen ne babu dad'i ga...ga........" sai ya kasa fad'a.
"Ga me son?" kasa magana yayi.
Cikin damuwa tace "son gaya min don Allah".
" Idan na gaya zaki hansu mai dani?".
"Uhum fad'a kaji my boy" turo baki yayi domin ya tsani a kira sa da boy.
"Mami niba boy bane, don Allah kibar cemin haka dani boy ne aida ba ai yun'kurin yin min fyad'e ba".
" What!!!" mami tace tana mi'kewa................
0 comments:
Post a Comment