🅿2⃣1⃣to2⃣2⃣
Ya mutsa fuska yayi tare da had'e rai yana cigaba da cewa "da gaske nake mamina, har cikin gida wata shegiyar arniya tazo min fyad'e".
" Kutumar uban can, waye uban ta shegiya da zata lalata min yaro?, amma dai bata maka komai ba ko?" shiru ya mata.
Kallon sa tayi na wani lokaci sanan tace tana mai koma wa inda ta tashi "my son tell me the truth".
Shagwa'be fuska yayi tare da cewa " yanzu mami na baki yadda da yaron ki bako?, tom shikenan ai inaga sai tamin ciki zaki yadda".
Fashe wa da dariyan babban wansu dake tsaye tun fara shirmen Auwal yayi.
Waiga wa sukayi dukan su suna kallon 'kofar parlourn.
Hararan da mami ta jefa masa ne yasa shi gintse dariyan sa.
"Na shigo?" yace yana mai danne dariyan sa, a zuciyar sa kuwa yana mai mamakin yadda mamin tasu ke zama tana sauraron shirmen autan nata.
Mai da fuskan ta tayi kan Auwal tare da cewa "oho ma, kuma mutum ya daina mana la'be ko autana?, uhmm mami na, kuma na sani sarai sai ya kai maganan gaba. kuma kin san wani abu?" yace yana mai kai bakin sa kunnin ta don kar yayan yaji, nima bai bani daman jiba.
Sai mamin da take cewa "sun ma isa ne" kawai mukaji.
Tako wa yayi ya shigo ciki, yana mai jefa ma Auwal d'in mugun kallo.
"Mami kin gansa ko?, meka masa daga dawo wan yaro?, ban san fitina fah. A saki ma yaro na mara yayi fitsari, Allah wanan karon ran kowa zai 'baci a gidan nan".
Gyad'a kai Auwal yayi kamar wani yaro, hakan ma yake jin kansa indai yana gaban mamin tasa.
" Tashi muje kaci abinci idan ka huta ma 'karisa magana".
"Ku 'karisa shirme dai" cewar yaya nasa murya 'kasa-'kasa, "mai kake cewa?".
" A'ah, ni bance komai ba mami, kama ce " tace tana 'kwafa.
Dining sukayi, jan masa kujera tayi ya zauna yayan na kallon su ta fara feeding d'in sa.
Ganin ba zai iya jure kayan takaici ba yace "mami ina wuni" "lafia" tace tana mai cigaba da bama shalelen ta abinci.
Shiru ya zauna kafin ya mi'ke tare da cewa "sai anjima mami" ya fara tafiya.
Cikin d'aga murya tace "dawo" dawo war yayi "shin baka ga auta ya dawo bane?".
" Na gansa, shine ko gasheshi da hanya bakai ba?" zaro ido yayi tare da cewa "kai mami shine gaba dani koni? tayaya bai gaidani ba ni na gaida sa?".
" Amma ai kasan daga uwa duniya ya fito ko?, sai kabari ya huta idan bai gaida kaba sai kace amma ba yanzu ba, maza masa sannu da hanya".
Kamar zai kuka saboda ba'kin ciki yace "wallahi abinda kike baki kyau tawa sam mami".
" To ubana nuna min abinda zanyi" "idan bai nuna miki ba ni gani nazo zan nuna miki" cewar dady dake shigo wa parlourn.
Shiru tayi kawai bata iya cewa komai ba.
Kar'ban jakar hannun sa yayan yayi sukayi sama suka bar su nan.
"Mamina mai yasa Dady bai sona?" Auwal yace yana mai jin zafin yadda Dadyn ya nuna halin ko in kula a kansa.
"Mami yau fah na dawo amma duba babu ko farin ciki a tattare da Dady, anya kuwa mami? anya shi ya haifeni?" yace hawaye na fita daga idanun sa.
"Shishhh autana, dai na zancen nan Dadyn ka na tsananin 'kaunar ka, yafi sonka fiye da 'ya 'yan da.." sai tayi shiru.
Lallashin sa tayi, bayan ta gama lallashin sa sai suka mi'ke daga dining d'in suka nufi sama hannun sa sar'ke cikin na mami.
Dai-dai 'kofar part d'in Dadyn tace "muje ka masa sannu da zuwa ko yaron kirki?".
" Hmm" kawai yace sukai knocking suka shiga.
Zaune suka taddashi yana ma Yusif bayanin wani abu.
Zama mami tayi a kusa dashi, Auwal ya dur'kusa kusa da 'kafar ta tare da cema Dady "ina wuni Dady" cikin sanyin murya.
Da fara'a a fuskan Dady ya ansa masa, tare da cewa "maraba da autan mami shalelen RAHAMA".
" Yaushe a gari?" turo baki yayi tare da cewa "d'azu".
" Madallah, ya hanya? Alhamdulillah".
"Masha Allah" Dadyn yace yana mai cigaba da abinda suke.
Suna zaune suka gama ya sallami Yusif d'in.
Bayan fitar Yusif d'in ne take cewa "sannu da zuwa alhaji, yauwa madam, ya gidan?".
" Lafiya qalau, ya aikin?". "Sai godiya ubangiji" cewan dadyn. "idan kin sallami yaron naki sai ki sallameni nima" yace yana nufar bedroom.
Shafo gashin kan Auwal tayi dake she'ki kamar na larabawa.
"Son jeka huta ko ina zuwa na baka labari" murmushi yayi tare da mi'kewa yace "to mamina, barci ma zanyi idan nai sallan la'asar".
" A'a my son ba kyau barcin yamma ban yadda ba kuma kar ayi".
"Kaji?" "tom first love bazan ba" ya fita daga d'akin.
'Dakin sa ya nufa, bayan yayi alwallah yayi sallah sai ya d'an kishin gid'a yana kallon t.v, barcin yakeji "amma tunda mami ta hana ba zanyi ba" yace yana mai barin d'akin gaba d'aya.
'Dakin mami ya shiga, wurin da take aje keys d'in mota yaje, duba nasa yayi bai gani ba.
Sai ya d'au na RAHAMA guda d'aya ya fito.
Koda yazo wurin motocin sai yaga duk sunyi 'kura da alama dai ba'a anfani dasu tunda ya tafi, daga nasan har na RAHAMA.
Koma wa yayi ya d'ako na mami ya shiga, bata wuta yayi tare da danna uban horn tun kan yaje get d'in.
Da gudu mai gadi ya bud'e masa, fita gidan yayi.
Direct gidan wansa Sani yayi, horn yayi aka bud'e masa yayi ciki parking yayi tare da fita a motan yayi ciki.
Da sallama a bakin sa ya shiga parlour ansawa sukayi yayan har da Ikiliman.
Da gudu Iman ta nufo sa tana cewa "oyoyo uncle" cafe ta yayi tare da d'aga ta sama.
Yace "oyoyo my angle" dariya tayi, zama yayi tare da Iman d'in.
Ikilima tace "oyoyo mijin kwali" ta'be baki yayi tare da cewa "gayi nan a gaban ki, don nafi 'karfin kwali nine na 'karfen maza azo ayi tarba ta musamman ko kuma mutum ya koma gidan su".
" Gida kuma? a'a ai mutu karaba nida kai, mai zakaci a kawo maka?".
"Abinda mijin ki yaci"
"Babban magana to ya 'kare" d'auke kansa yayi kamar magidanci yace "a kirka wani yanzu".
" Wallahi baka isaba dan ubanka, haka kawai kasa matata aiki da yamman nan, sa Larai ta masa".
Murmushi gefen baki yayi tare da cewa kamar gaske "oh yaya dama kana nan?" bai tanka masa ba ya 'kara da cewa "ina wuni yaya" bai damu da ansa wan saba ya cigaba "mun same ku lafia?" nan ma shiru.
Dariya Ikilima ta fashe dashi tare da cewa "Allah shirye ka Auwal, mami ta gama 'bataka wallahi. Antura ka 'kauyen nan ko zakai hankali ne ashe dai akwai aiki".
Murgud'a baki yayi kamar mace yace "'kila da naki nake yawo".
Bata barsa haka ba tace " inaga kuma sa aure kawai idan ya fara tara yara zaiyi hankali ".
" Maza kuyi" yace yana mi'kewa.
Ganin zai fice tace dashi "dawo 'kanin na dafa maka, banci mamina ta cika min ciki".
"Daga nan sai inah" banza da ita yayi, Iman ta'ba ta fuska tare da cewa "momy don Allah Ku daina wa uncle haka" tana mai zum'buro baki ta bisa.
Har ya shiga mota ta 'kariso, "uncle kayi ha'kuri kaji" murmushi yayi tare da janyo ta ya d'aura ta a cinyan sa.
"Da akayi me baby na?" turo baki tayi irin yadda yakeyi, domin yarinyan tana mugun kama dashi, idan kuka ga Akram bancin 'karami ne zaka ce shine.
"Ba momy ta 'bata maka rai ba?" .
"Ko d'aya my baby, muje gidan su Mufi, daga nan sai mu wuce duka gidan mami Ku kwana ko?".
" Yeeeeeeeee, muje uncle " dariya yayi tare da sata a kusa dashi ya tada motar suka bar gidan.
Zai shiga yayan zai fita ganin motar mami yasa Yusif tsayawa yana mamakin ganin mami bancin bai dad'e da barin gidan ba.
Ganin Auwal ne cikin motar yasa yayi tsaki tare da ficewa.
Dariya Auwal yayi tare da parking, shiga sukayi Iman ta fara kiran "Mufy" da 'karfi, aiko sai ga Mufyn da gudu.
Akram a bayan ta, tafiya yake sak Auwal, sai dai shi miskiline na 'karshe.
Zuwa yayi ya rungume Auwal tare da cewa a hankali "sannu da zuwa uncle".
" Yauwa yaro na" haka itama Mufy tace.
"Ina Momyn ku?, tana sama" cewar Mufy.
"Okay Ku muje idan na gaida ta sai mu wuce gidan mami don yau gidan mami zaku kwana".
Mufy ta saki eyhun murna, shiko Akram murmushi kawai yayi sam bai da hayaniya.
Suna hawa tana sakkowa, da murmushi tace " uncle mai yara yaushe a gari?".
"Au mijin ki bai fad'a miki ba? ruwan shi d'azun, barka da zuwa na mami".
" Muje kasha ruwa, Iman ina momy? ".
" Tana gida, ina wuni Anty" "lafia lau ta uncle".
Fridge taje ta kawo musu abu mai sanyi, kur'ba kawai Auwal yayi ya mi'ke "mun tafi" cewar Mufy.
Kallon Auwal tayi ya d'auke kai sai tace "ina zaku yaran uncle da yamman nan?".
" Gidan grandma okay ku gaishe ta " suka bi bayan Auwal da ya fice da gudu.
Mami zaune ita da Dady a parlourn suka shigo, da gudu suka nufe kakannin nasu.
"Oyoyo, oyoyo amarena, oyoyo abokina" cewar Dady yana runguman su d'aya bayan d'aya.
"Da zabiya da bilaki, to Ku 'kara gaba banan ba baza ku ta'ba kasuwa ba. Don na kere Ku babu abinda zaku rud'e sa dashi".
" Can miki me zanyi da tsohon mijin ki? sai dai ko Iman" cewan sarkin tsiwa da rashin kunya Mufy.
"Iye mijin nawa ne tsoho?, uhum" tace tana turo baki.
"Auta mai kaka wo min rasai tamin a gida?".
" Mami ni yarana duka masu kunya ne ko Mufy na?, eh uncle " suka ce tare da tafawa.
Ta'be baki tayi tare da cewa "zamu had'u idan sun tafi".
Dariya Dady yayi tare cewa "gumma ya kwaye muku ko yaro na yayi hankali, kinbi kin 'bata min yaro".
" Haka ma zaka ce ko?, to mezan ce dama idan ba gaskiya ba".
Share shi tayi tare da cewa tana kallon Akram "miskili kai kenan kullm a haka, auta kukai yaron Ku asibiti da wuri fah tunkan abin yafi 'karfin Ku".
Ta'be baki yayi tare da mi'kewa " ina zuwa my son?" hanyan steps ya nufa.
Sai da ya hau sannan yace "d'akin ka?" a hankali.
"Me zakyi?, kwanciya. Ka bari sai bayan isha babu kayu kwanciya magrib".
Bai ce dashi komai ba sai dawo wa da yayi ya zauna nesa dasu.
°°°°°°°°°°°°
Kwace madam Gloria ta dawo ta tadda ta sai faman rizga kuka take, da sauri uwan ta nufe ta.
'Dago ta tayi tare da cewa cikin tsananin damuwa.
Share hawaye fuskan ta tayi tare da du'kar da kan ta 'kasa.
Tatta'ba fuskan ta tayi tare da cewa cikin sanyin murya " what happened? why are you crying?".
Murmushi ya'ke tayi tare da cewa "nothing".
" Ya zaki ce haka? bayan fuskan ki ya nuna kin dad'e kina kuka?".
"Ina lura dake kwana kin nan kina cikin damuwa, wato kina 'boye min damuwar ki ko?. Wakike da bayan ni? ashe ban cancanci sanin damuwar ki bako?".
Kukan da take matsewa ne ta fashe dashi.
Ganin bata da ninyan barin kukan yasa uwan tace " kenan ni zaki 'boye wa wani abu? ba damuwa na bar ki" tace tare da mi'kewa.
Ri'ko hannun uwan tayi tana girgiza kai tare da cewa "a'a mama, nothing of that sorts".
" To fad'a min " cikin kuka nace "I'm in love with him" sai nai shiru tare da cigaba da kuka na.
Zaro ido mama tayi tare da cewa "who?".
" Doctor...... doctor Auwal.... " kallon ta tayi cikin mamaki, amma da ta tuno baya sai mamakin ya gushe.
Hasali ma mikin ta taji yana son tasowa, don haka cikin tsananin tausayi 'yar tata tace "idan na fahim ta bai sani ba?" d'aga mata kai tayi.
Sauke numfashi tayi tare cewa "kisa same sa ki fad'a masa".
" Ya tafi" nace ina mai sake fashe wa da kuka mai tsanani.
Cikin damuwa tace "ina ?, ban sani ba amma kaya da yawa yasa a taxi suka tafi".
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace " to yanzu ya za'ai? ko ki manta dashi kawai, kinga soyayyar sa ma zaki rabu da ita ki huta, tunda bamu san inda yake ba".
Hawayen idanun ne suka 'kafe tare da cewa "I can't, I cannot forget him or stop loving him. I love him mama" nace ina mai fashe wa da kuka.
Cikin tausayi ta tace tana mai ruruguma jin ta tana shafa mata baya alaman rarrashi "don't cry joy. I am here for you".
" Nasani mama, amma shifa ? bashi baya tare dani".
"Kiyi ha'kuri ubangiji zai duba komai"..................
Comment
&
Share
'Yar Aliyu ce✍🏻
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
🅿2⃣3⃣to2⃣4⃣
Hawaye idanuna ne suka 'kafe tare da cewa "I can't, I cannot forget him or stop loving him. I love him mama" nace ina mai fashewa da kuka. Cikin tausayi ta, tace tana mai rungume ta, tana shafa mata baya alaman rarrashi "don't cry joy. I am here for you", " nasani mama, amma shifa? bashi tare dani, kiyi ha'kuri ubangiji zai duba komai kinji ".
Gyad'a kai kawai nayi tare da tsayar da kuka na, jin nayi shiru yasa mama ta d'ago da fuska na, share min hawaye tayi tana murmushi tare da cewa " yauwa yarinyar kirki" had'e da jan min kuma tu.
Murmushin ya'ke kawai nayi, "kinci abinci kuwa?" Sai lokacin na tuna da cewa mama ta sani girki, shiru kawai nayi mata.
Sake tambayan ta tayi "nace kinci abinci?" turo baki nayi tare da cewa "a'a" ta sigan shagwa'ba.
"To mai yasa Joy?, ya tsina fuska nayi sannan nace " ban girka ba" cikin 'kasa da murya.
Ba tace komai ba sai mi'kewa da tayi, cikin gaggawa ta musu abinci mai sau'ki ta kawo min har gado.
Ansa nayi tare da mata murmushi nace "nagode momana" jan kuma tuna tayi tare da jifana da murmushi ita ma.
"Maza kici ki 'koshi 'ya guda, duk da ba wani cin kirki kike ba, shiyasa gaki nan kullum kaman one".
Dariya na fashe dashi tare da cewa " kai mama nine kamar one?, uhum maza ci ni ina zuwa" tace tana mi'kewa.
Wanko hannu na nayi a roban da ta d'ebomin ruwa domin haka na fara cin abinci na, duk loma d'aya sai na dad'e kafin na had'e.
Domin tunanin abin 'kauna yayi min katutu, duk wani dariya da murmushi da nakeyi inayi ne kawai domin mahaifiya.
Don tafiyan Auwal yayi matu'kar tada hankali na, tuno irin kayan da naga anloda a motar kuwa na samin fad'uwar gaba mai tsanani.
Haka dai na daure naci kwatan abincin na tura gefe, lokacin ne mama ta dawo d'akin.
Kallon kwanon tayi sanan ta maido da idon ta kaina, tace cikin had'e rai "har kinme Joy?".
Turo baki nayi tare da had'e fuska don banso ta matsaminci.
Nace " na'koshi" girgiza kai kawai tayi tare da d'auke abincin ta fita dashi.
Zuwa tayi ta 'kara wani akai don mama akwaici ta kamaci.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Auwal kuwa hankali kwance yake rayuwar sa, yama manta da wata yarinya wai ita Joy.
Kwana biyar da zuwan shi yayar sa ta dawo 'kasar tamu, zo kuga murna wurin Auwal, yanda ku kasan yaron goye haka ya zama, ashe shagwa'ban da akewa mami kad'an ce.
Tsaraba ko yasha shi, kai kace don shi akayi tafiyan, a tsaraban harda na matan sa, cewar yayan tasa.
Dariya kawai mutanen palon suka kwashe dashi, wanda har sai da Ikilima ta kasa shiru tace "mutumin da bai da budurwa inashi ina zancen aure, kawai a bamu".
Hararan wasa Rahma ta jefa mata tare da cewa " ba sai kuzo ku danneni ba ku 'kwace, ai tari zan dunga wa 'kanina har zuwa lokacin da zuciyar mu zata zo. Bare ma jikina na bani 'kanina ya fara soyayya".
Sai a wannan lokacin ya tuno da wata aba Joy, duk da bawai ya manta da ita kwata -kwata bane, duk da hakan shine burin shi.
Amma ina can cikin 'kar'kashin zuciyar sa itace ciki male-male.
Tuno ta da yayi ya haddasa masa 'bacin rai sosai, domin har da mummunan ganin da yayi mata da Isah ya tuni.
Auwal mutum ne mai tsananin kishi, musamman akan abinda yake 'kauna.
Girgiza san da RAHAMA tayi shine ya dawo dashi daga dogon tunanin da ya lula tare da kafe ta da idanuwan sa
Yanayin yadda fararan idanuwan sa suka koma yasa ta tsorata.
Idanun ta suka ciko da 'kwalla, domin a duniya RAHAMA ta tsani abinda zai ta'ba mata d'an 'kanin ta.
Lumshe idanuwan nasa yayi na wani lokaci, domin ganin yanayin ta ya sani sarai yanzu sai ta tada hankali ta ciwon ta yazo ya tashi.
Shiyasa ya lumshe idon don idanun su dai daita.
"Meye Auwal? meke damun ka? mai ya 'bata maka rai?" ta jero masa tambayoyin nan a lokaci d'aya, kuma cikin kuka.
Jin kukan ta damun sa ta 'karu, amma sai ya danne damuwa nasa tare da bud'e idanuwan nasa akan ta.
Ya sakin mata 'kayataccen murmushi, ya ri'ko fuskan ta yace "babu komai my love, bar kukan haka" kallon cikin 'kwayan idanun sa take don tabbatar da zancen sa.
Kauda kai yayi tare da cewa "da gaske babu komai Anty na".
Jan hanci tayi tare cewa " Auwal zaka fad'an gaskiya ko sai ranka ya 'baci?".
Turo baki yayi irin yadda yara keyi yace "kice su fita to" hararan sa ikilima tayi tare da cewa tana mi'kewa "nayi nan tun kafin a koren".
Itama Momyn su Akram ta bita tana murmushi.
" Sun fita ina sauraron ka" kwanciya a cinyan ta yayi tare da ri'ko hannu ta d'aya ya dam'ke a nasa.
Zuciyar sa na bugawa, "ina jira fah Auwal" tace gaban ta na fad'i domin da gani ba'karamin abu bane ke damun sa.
Kuma bai ta'ba 'boye mata damuwar saba.
Jin shirun nasa yayi yawa yasa tace "idan 'karya kake son fad'a min ba gaskiya ba to kari'ke kayan ka".
Ganin kaman tayi fishi yasa tashi a jikin ta tare da janyo akwatin da tace wa matar sa ta sayo.
Ya bud'e tare da kallon tulin kayan dake ciki yana nazarin su yana murmushi.
Waigo wa gare ta yayi idon ta na kansa, yace " Anty duka nata ne?" banza dashi tayi .
Bai damu ba ya fara ciro kayan d'aya bayan d'aya yana kallo tare da murmushi a fuskan sa.
"Anty zasu matu'kar yin mata kyau amma ban son ta yanzu" yace cikin ransa na 'kuna.
Matsowa tayi kusa dashi tace "ban gane ba?" kallon ta yayi tare cewa "abinda kikajin nan shine kawai" idanun sa sun 'kara rinewa fiye da dah.
Ganin halin da 'kanin nata keson jefa Kansa yasa tace tana murmushi ya'ke tare da ri'ko hannu sa.
Kwantar dashi tayi a cinyan ta tare da shafa masa gashin kansa, ta d'au lokaci tana haka shi kuma yana ta wani irin numfashi.
Zuwa can yayi barci, jin yayi barci yasa ta sauke ajiyan zuciya tare da hamdala.
Tana ro'kon ubangiji a zuciyar ta tace "ya Allah ka San yaya mishi zuciya, idan ba alkhairi a tsakanin sa da yarinyan ya Allah kaman tar dashi ita, Allah kasa ya farka bashi da damuwar komai".
Tace tana kallon fuskan sa mai cike da haiba da zati.
" Mai kika masa haka? nasan ba 'karamin abu bane ya 'bata wa Auwal rai".
"Ina kike? ina zan ganki ? inason sanin ki da sanin mai kikawa my 'kani na?" numfashi taje tare da d'aura kanta a jikina sa.
Nan itama barci ya kwashe ta.
~~~~~~~~~~~~
Damuwa yayi wa Joy yawa kullum kwana nan duniya baza ido take tana kallon hanyan da Auwal zai dawo, tunanin ya zame mata jiki, kuka ko shine abinci ta a halin yanzu, tun maman na lallashi har ta kai ga yanzu ta zuba mata ido, makaranta kuwa yanzu ta sauke sa saboda bata son Auwal ya dawo bata.
Yadda take son mai da kanta da rayuwar ta na matu'kar damun 'kawar ta da mahaifiyar ta.
Kuma saboda zurfi ciki har yau kusan satin Auwal d'aya da kwana biyu Aisha bata san meke damun 'kawar taba.
Tayi tayi ta sanar mata ta'ki , tayi fushi akan haka har takai ga ta sakko domin tasan waye 'kawar ta akan zurfin ciki.
Kwance take da wurin 'karfe 11:00pm idon ta kuri kamar kowacce dare tun bayan barin Auwal garin.
Tana abinda ta saba wato kuka.
"Shin yanzu idan kabar ni ina zan sa raina?, yaushe zaka dawo? ji yadda na rame dama ba akauki ne dani ba. Tunani da fargana bazaka dawo ba yana mugun d'agamin hankali, yanzu ne nagane irin tsanani son da nake maka, inaga kuma shine ajalina mudin baka dawo gare niba . ka aminta dani don Allah shine burina . Kada kabarni doctor kada ka gujeni kasoni kada ka'kini".
" Idan kabar ni bansan inda zansa raina ba, yaushe zaka zo gare ni kace ina soki Joy? " tace tana 'kan'kame filo tare da fashewa da kuka.
Kuna ta tambaya to gashi na daur nayi, yadda na faran ta muku inason nima Ku sani farin ciki.
Comments d'in Ku shine 'kwarin guwar mu mu writer's.
Sai naji Ku, idan ba haka ba kuji shiru.
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*My fan's godiya marar adadi, Allah bar 'kauna*
*Dedicated to Heart beat🥰*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
🅿2⃣5⃣to2⃣6⃣
Auwal ya riga RAHAMA tashi, jin motsin sane yasa ta farka tare da d'aga sa, kallon sa tayi shima ita yake kallon bayan ya tashi a jikin ta, murmushi ta sakin masa shima ya mayar mata.
"Anty kema barcin kikayi?, eh d'an 'kanina" tace tana jan mai kuma tu.
"Har kun tashi?" a tare suka wai ga, mami ce ke tambayan su, "eh mami munsha barci, ko ban ninyan barcin ba ga wanda ya sani nan" cewan RAHAMA tana kai masa dungurin wasa.
Dariya mami tayi tare da cewa "ai kun saba dama ba yau bane farko, maza tashi kije sashin ku tun d'azu mijin ki ke mana safa da marwa".
Turo baki tayi tare da cewa " kai amma gaskiya Salisu nada neman magana, meye kuma na sintiri?, toni gaskiya ina tare da 'kanina ban gaji da ganin sa ba".
"Banson shashanci maza tashi kije" ba don taso ba ta mi'ke tare da kama hannu Auwal.
Kallon ta mami tayi tare da cewa "ina zaki kuma dashi?" .
"'Bangaren mu mana" janye hannu sa yayi tare da cewa "Anty ni bazani ba gaskiya, saboda mai?".
"Kawai" yace da ita tare da koma wa gadon 'yan matamcin ta ya kwanta tare da lumshe ido.
Kallon sa tayi tare da cewa tana mai maida idon ta kan mami "mami kice masa ya tashi muje, yaje ina? ina tunda kika dawo kuke tare? maza bar nan banson shashanci".
Fita tayi ba don ranta yaso ba, tana fita mami ta nufo wurin d'an nata.
Zama tayi gefen gadon tare da cewa " meye damuwar ka yaro na?" shiru yayi kamar mai barci amma tasani sarai ba barcin yake ba.
"Da kai fa nake kanaji na ina magana kai banza dani" bud'e idanun sa da sukai masa yaji-yaji saboda hawayen dake cikin sa.
Sunyi ja jazur dasu yana kallon ta dasu "lafia Auwal?" tace tana mai d'ago sa.
Bai shiryawa zuban hawaye ba kawai sai gashi sun zubo masa.
"Mami na" yace cikin in ina, "ya akayi ne d'an mami ? fad'a kada kai shiru zaka samu sau'ki kaji?".
" Mami inason ta ina 'kinta, mami ki nake kamar zan mutu na kuma manta da ita, amma zancen Anty yasa na tuno ta, don barcin nan da nai har mafarkin ta nai".
"Mami zan koma gobe" daga haka yayi shiru yana mai dafe 'kirjin sa yarasa taka mai man maike damun sa.
"Auwal ban gane zancen kaba, ban gane inda maganan ka ta dosa ba, mai kake nufi?".
" Fad'a min wacecce kake so, kuma wacecce kake 'ki".
"Duk itace" yace yana mai kallon mamin.
"Fahimtar dani, yaro na ya fara soyayya? kome?".
Ganin ta kafesa da ido yasashi kauda kai tare da sanar mata da labarin komai na dangane dashi da Joy.
Amma koda yazo zancen fyad'e ya kasa fad'a kuma hakan ya'kara masa zafi a zuciya fiye dada.
" Yaka tsaya? inajin ka, shikenan ai mami" bai fad'a wa mami cewan ba musulma bace.
"To meyasa baka fad'a mata ba?" shiru na wasu d'aki'ka yayi sannan yace "yarinya ce sosai mami shiyyasa ban sanar mata ba".
" Yarinya kamar ya? bata isa aure bane?. tukunna dai mami bata wuce 16 years ba fah, yanzu haka ina tunanin JS3 take".
"Ai ta isa aure kam, sai dai kace kawai baka son ka auri yarinya, to mai zai hana a d'aura aure ta ta dawo nan da zama? idan yaso daga baya sai ayi biki bayan ta gama secondary d'in ta".
Turo baki yayi tare da cewa " kai mami to meye ma'anar haka? baki tunanin ta'ki maida hankali a karatun ta?".
"Kuma mani a'a sai ta girma, don bazan bari ayi taje kuma.....kawai.......umm ni dai a'a kawai".
" Shikenan tunda hakan yafi maka, amma shawara ta ka sanar mata tunda wuri ".
" Humm" yace kawai tashi tayi ta fita ta barsa, shi kuma kwanciya yayi yana tunani.
°°°°°°°°°°
Washe gari samakon tashi Auwal yayi, da shirin sa tsaf na tafiya ya fito, lokacin da ya fito babu wanda ya fito sai masu aiki dake kara kanya.
Don duka daga sallan asuba kowa ya koma barci amma banda shi.
'Dakin mami ya nufa duk da yasan ba lalai ya same ta irin wannan lokacin a d'aki ba.
Koda ya shiga babu kowa a ciki, kiran layin ta yayi sai da yakira yafi a 'kirga kuma yana ringing ba'a d'aga ba.
Ganin time na tafiya yasa ya zari key d'in motar sa da kayan sa ya fita a d'akin.
Wurin ma'a danar motocin gidan ya nufa, motar sa ya bud'e tare da jefa kayan sa yayi ciki.
Tada motar yayi ya bar gidan ba tare da sanin kowa ba sai dai masu aiki tsiraru da mai gadi suka gansa.
Sai muce Auwal Allah tsare hanya........
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
"Joy ki tashi haka mana, barcin ya isa haka" tashi nayi ina tura baki had'e da mi'ka.
"Mama Allah kin cuceni ina cikin barci na mai dad'in gaske kin katseni" nace a cikin zuciya ta.
"Tashi kinji yau bikin Bola, tashi kishirya muje, ba inda zani" nace ina ninyan koma wa na kwanta.
"Tashi ki karya to, ba yanzu zan karya ba, kinsan ko 'karfe nawa ne yanzu kuwa?".
" Um'um, 12:30pm ne yanzu, maza tashi ki karya saiki wanka ki kwanta ni Narasa wani tsiya kika tsiro yanzu, da dare baza'a barci ba sai safe yayi akama barci".
"Kibarni please mama ki tafi abunki" nace tare da gyara kwanciya na.
Girgiza kai kawai tayi tare da cewa "sai na dawo, ah" nace ko wai gawa banyi ba.
------------------------
11:00am yayi wa Auwal a 'kofar gidan sa na 'YAR KADDE, parking yayi a jikin gidan fito wa yayi a motan tare da rufewa bayan ya ciro kayan sa.
Bud'e gidan sa yayi ya shiga tare da tura 'kofar yayi ciki, kallon gidan yake duk yayi datti.
Bud'e 'kofar shiga d'akin yayi jefa jakar kayan sa yayi tare da tu'bewa ya fara gyara gidan.
Tsaf ya gyara ko'ina gida ya fito shar dashi, lallai yaron mami yayi 'ko'kari.
Bayan ya kamala gyaran gidan yayi wanka, shiryawa yayi cikin 'kananun kaya , kayan sun kar'besa sosai, a lokacin ne yaji anfara kiran sallan azahar don haka sai yayi alwallah tare da fita don zuwa masallaci.
Bayan an idah salla ne ya fara tunanin mai zaici, fito wa yayi daga masallacin yayo gida.
Joy ta fito daga cikin gida da nufin shiga gidan su Aisha sai taga mota a jikin gidan Auwal.
Kallon motan take kamar shine a ciki, a zahirin gaskiya bata ta'ba ganin mota irin wannan a cikin 'KAUYEN ba.
Motan ta bala'in d'aukan hankalin ta, zuciyar ta na raya mata cewa Auwal d'in ta ya dawo.
Farin cikin da na dad'e bangani ba a fuskan ta shine kwance har da darinyan ta.
Ji take kamar ta zura da gudu tashiga gidan sa, amma ina a wanan lokaci ne miskilancin ta ya tashi, tsaye kawai tayi tana kallon gidan.
Tana tsaye Auwal ya dawo, tun daga nesa ya hango ta, tafiya yake kawai amma idanun sa ita yake kallo.
Murmushi ya saki lokacin da ya 'kariso, idon sune ya sar'ke ana juna.
Kallon junansu suke na tsahon wani lokaci, Joy ne ta fara jenye nata tare da juyawa gida.
Dariya ya fashe dashi kuma tajisa sarai tai shige wanta, "'yar rainin wayo kawai, sai da tagama kalle kyakkyawan mami tsaf kamar ta lashe, kuma hakan take marmari nagano tsaf, wai ita miskila ta wani juya fuw tayi gida".
" Dawo ki cigaba da kallon abinki " yace yana murmushi tare da shige wa nasa gidan yana girgiza kai "hmm, yarinya kenan wai ita aji, bari ya tsinke muga sai inga ta tsiya".
Yace dai-dai da iso warsa farfadan gidan, zama yayi a fararen kujerun sa dake gefe a tsare a gidan.
Yamitsa fuska yayi tare da cewa " ta rame wallahi, ta rame sosai Allah sa dai ba ciwon cikin bane, ko......." sai yayi shiru yana nazari.
Murmushi yayi tare da cewa "kai so ba'ine, so masifa ne, yunwa fa nakeji amma sakamakon ganin masoyiya ya tafi. Hmmm"
•••••••••••
Dariya nima nayi lokacin da na dawo cikin d'aki, don sai lokacin tazo "jishi kamar aljani saboda kyau, Allah yayi wa Auwal kyau tamakar shi yayi kansa".
" Allah sa ya dawo ne yace yana sona, wuw da nayi farin ciki mai tsanani ".
Kwanciya ta nayi tare da lumshe idanuwa na.....
Share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*Dedicated to my lvly fan's*
*Musamman*
*MY besty (maman Muhammad)*
*Bilqess*
*Maman Aliu*
*Fauxy*
*Fulani Gal*
*Maman Inteesar*
*Jidda h garba*
Da dai sauran su ina tsanani 'kaunar Ku fan's , much luv sisters iya wuya ana tare🤝🏻🤝🏻
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
🅿2⃣7⃣to2⃣8⃣
6:10pm na sake rangad'a wankana na zauna na tsantsara 'kwalliya na, nayi masifar kyau, kamar a sace a gudu, ina zaune a far fada, ina duba notebook d'ina. Sai ga mama ta shigo tunda na d'aga kai na naga ita ce na mai da kai na a littafi na, na cigaba da nazari.
Ban sake d'ago wa ba sai da naji tace "shigo mana doctor", sa'an nan na d'ago gaba na na fad'i na jin ankira rayuwa ta.
Shigo wa yayi muka had'a ido dashi, hannu sa ri'ke da kaya, idon sa na kai na yace " a ina za'a aje?" mama tace "bani nan yaron kirki na aje".
Murmushi yayi mai 'kaya tarwa tare da cewa " nu namin kawai na aje" yace yana mai kauda fuskan shi daga kallon na.
Murmushi gefen baki nayi tare da cewa "sannu da dawo wa mama".
" Yauwa Joy sannu da gida", ban ansa ba ina kallon sa tage fen ido mama ta nuna masa inda muke aje kayan abincin mu ya aje.
"Sannu kaji? nagode fa, bari na kawo maka ruwa kasha, ko Joy kawo masa bari na duba cincin mu ya rage sai na bashi yau ya dawo yace, gashi bamu dafa abinci ba sai ya faraci kafin na d'aura yanzu".
Kamar ba dani take ba, ko motsi banyi ba, don kamar maye haka ya kafeni da ido.
" Joy ba magana nake ba" mi'kewa nayi ba don naso ba nayi kitchen.
Cup mai kyau na d'ako tare da d'ebo ruwan randa na fito.
Ina zuwa na aje a gaban sa na wuce, lokacin ne mama ta fito da ba'kin leda a hannu ta.
"Joy ansa ki sayo masa zo'bo mai sanyi ya rage yunwa kafin na dafa abinci"
Kar'ba nayi tare da nufan hanya, shi kuma ta mi'ka masa cincin d'in. Ransa idan yayi ba'ki ya 'baci, babban matsalan shi da Joy kenan shigan banza.
Kuma shine sulan 'kwad'ayin wasu, ko yau da dama-dama.
Bin bayan ta yayi mama tace "kabari ta kawo yanzu zata dawo".
Murmushi ya'ke yayi tare da cewa " idan ta dawo na kar'ba" don Allah Allah yake yaje ya han ta tafiya.
"Auwal kenan kai wai har yanzu baka saki jiki damu ba, jeka to" murmushi ya sakeyi tare da rufa mata baya.
Koda ya fito da yake ba sauri gare taba ya tarar da ita tana gaf da gidan zo'bon, domin daga gidan su, gida uku ne sai na masu zo'bon.
"Joy" ya 'kwala mata kira, wai gowa tayi don jin muryan sa, fuska d'aure ya kauda kansa ganin ta juyo.
Tsaye take daga inda take tana kallon sa, ita ba tai gaba ba, ita ba tai baya ba.
Ido kawai ta zuba masa, jin shiru bata dawo ba kuma tasan sa rai kiran ta na nufin ta dawo ne .
Sai ya wai go don ganin tsayuwan da take kuma gashi gaba da gidan da take tsaye majalisan maza ne.
Wani sa'in harda d'an iskan saurayin ta (Isah), ya tofar da yamu tare da tsaki.
Kallon sa kawai take, ganin zai waigo yasa na kauda kai na tare da d'aga kai don cigaba da tafiya.
Cikin jin haushi yace "dawo bansha" yadda zataji, "to ai bakai ka aikeni ba bare ka hanani tafiya" nace a zuciya ta tare da cigaba da tafiya ta bako wai waye.
Cije le'be yayi tare da girgiza kai, ransa ba'kin 'kirin, yana hangen yadda samarin 'kyauye suka kafe ta da ido.
Wani har da hanci wurin kallon.
Shige wa gida yayi don ba'kin ciki tare da buga 'kofa garau.
Zama yayi a fararen kujerun sa na far fada, tare da jingina ya rintse ido, tuno ranan da yayi mummunan ganin yayi.
Dafe zuciyar sa yayi saboda yadda take mugun bugawa.
•••••••••••••
"Mama gashi" cewar Joy a bakin kitchen, waigo wa mama tayi tare da cewa "baki gansa waje ba?, uhum" kawai nace.
"To taimaka ki mi'ka masa a gida, nasan yana nan".
" To" nace tare da fita gidan, koda naje 'kofar gidan nasa na dad'e ina tunanin yadda zan shiga.
Kudum bala nayi na daure na tura 'kofar gaba na na fad'i.
Shiga nayi na gansa zaune idanun sa a rufe, jin motsin tafiya yasa ya bud'e idanun sa dasu kai jajazur dasu.
Ganin itane yasa ya maida ido ya rufe, zuwa gaban sa nayi na aje zan juya ba tare da nace dashi komai ba.
Yace "d'auki" kallon sa nayi still idon sa na rufe, juyawa nayi don tafiya ta.
"Nace ki d'auka ko?" cikin tsawa, niko taurin kai sai nai kamar banji sa ba nasa kai.
Banyi taku uku ba naji an ri'ko hannu na, waigo wa nayi ya wurgamin wata matsiyaciyan harara tare da sakin min hannu nawa, yayi min nuni da zo'bon da na aje.
Tura baki nayi ina cewa "mama tace na kawo ni, amma kafin ki sayo mai na sanar miki?".
Ya tsina fuska nayi sa'an nan nace kamar mai ciwon baki " gani nayi ai bakai ka aiken ba" tare da zum'bura baki.
"To sai ki d'auka kisha, don ni banshan 'kazan ta" kallon sa nayi shima ya d'ago daradaran idanuna sa.
"Eh, yadda kikajin nan" "ummm, hakan yayi" nace tare da matsawa na d'au zo'bon zan wuce.
"Shanye shi anan " yace fuska a d'aure kamar wanda bai ta'ba dariya ba.
Tsoro ne ya kamani na kafa kai bayan na bud'e goran .
Bige goran yayi ya zube min a jiki, sanyin zo'bon har cikin kaina.
Kallon sa nayi shima ni yake kallo, fuska babu walwala yake "duk ranan da na sake ganin ki da irin wad'an nan tsuma ko makaman tansu, tabbas rai zai mummunan 'baci".
" Fita min a gida" yace cikin tsawa daya firgitani, da gudu na fita.
"Sai yanzu naji sa'ki a zuciya ta, na fanshe haushi na" yace tare da shige wa d'aki, alwallah ya gaba tar don anfara kiran sallan magariba, ya fito don tafiya massalaci.
•••••••••••••
"Mugu kawai" nace lokacin da na shigo gida, "kada wa Joy?" cewar mama daga kitchen.
"Ba kowa" nace tare da nufan d'aki ina jin ta tana cewa "kin zama mahaukaciya ba ai dole" bance komai ba na bud'e gana mazgo na don canza kayan jikina.
Kallon kayan nayi ina tunanin maganan sa, don gaskiya na tsora ta sosai.
Ganin haka bai min ba na zazzage kayan ciki kaf a tsakar d'akin.
Da 'kar na samu wani dogon riga mai gajeran hannu ya wuce guwa nasa ina mai cewa "ka nunan kayan da zam saka tunda kasayo min" ina mai murgud'a baki kamar yana gaba na.
°°°°°°°°°°°°
Shiru- shiru har 9:30pm mama bata gansa ba, don haka tace "tashi ki kaima doctor abincin nan".
Zabura nayi tare da cewa " Allah mama bazani ba, doctor d'in nan fiti nan nene" zata sake magana sai ga Aisha ta shigo.
"Yauwa tunda ban isa da d'ayan ba nasan wannan baza ta'ki ba" ya tsina hanci nayi tare da ta'be baki.
Dariya Aisha tayi tare da cewa "waya ta'ba min besty? eyeh? mai mukayi ne mama" duk cikin tsokaana tayi.
Hararan ta nayi tare da gyara kwanciya ta.
"Uhum mama bani sa'kon mai zan miki kiga cika aiki yanzu tunda wata bata son albarka".
Tsaki nayi mama tace " ma'kocin ku likitan nan zaki mi'kawa abinci".
"Aiko yanzu na barsa waje yana shan iska, yauwa kai mai" mama tace tana mi'ka mata.
'Kar'ba tayi ta fita, bata jima ba ta dawo ko nace suka shigo tare hannu ta d'auke da kwanon abinci.
Waiga dukan mu mukayi kallon d'aya na masa na d'auke kai da sauri saboda hararan da yayi min.
Duk da dare ne akwai farin wata kamar rana.
Turo baki nayi, "Auwal ya haka?" lokacin da Aisha ta aje abincin.
Murmushi yayi tare da cewa "nagode mama naci abinci ko?" yace yana zama kusa dani kad'an.
Cikin 'kasa da murya yadda babu wanda zaiji yace "bakijin magana ko?" kallon su mama nayi naga hakalin ta naga abincin da aka aje Aisha cema naga tana kallo na.
"Bani da wasu sai irin su" nace a hankali, zaiyi magana mama tace "yanzu ka kyauta?, haka mukayi da kai?".
" Ayi ha'kuri gobe zanci" yace yana murmushi kad'an, "to nayi".
Fira suka d'an ta'ba da mama ya tashi yayi mata sai da safe ya fita, ba tare da ya kalleni ko ya sake kulani ba.
Kamar ma baiji mai nace ba..
Washe gari ina cikin barci safen da na saba, naji muryan sa yana ce da mama " mama yanzu naga waccen yarinyan da suke tafiya makaranta da Joy ta tafi, nace lafia bata tafi ba, ko ta riga ta gaba ne?".
"Wai Joy ai tayi kwana biyu bata zuwa, nayi nayi ta'ki, kuma ko jiya bayan kafita maganan makaranta yarinyan tazo mata, amma fir tace baza taba, ko naji tana ce da ita next week zata".
" To mai yasa?, oho gata can bata da sana'a kullum sai barci, don ko church yanzu taba tafiya, nai magana har bakina yayi tsini amma ta'ki haka ma zuba mata ido".
Inajin su sukai ta magana, har takai ga yace mama ta tasoni, zuwa ko tayi tashi na d'in nayi kamar ina barci.
Kiran suna na ta fara, da yake ban cika nauyin barci ba da safe, nafi barci harda minshari da dare, don saboda tsaban barci kana iya saceni ka gudu.
Tayi kira yakai uku na'ki ko motsi, sai ta fara jijjigani amma ko didim.
Auwal na tsaye yanaji gashi ya tsaida Aisha a waje .
Don haka sai ya shigo d'akin kawai yana cewa "mama bani ruwan sanyi kawai" bata musa ba kuwa tace "to tare da shiga bangi da don d'ako masa.
Bata jima ba ta kawo, jin tace " gashi" yasa na mi'ke a zabure, ina zare ido fuska ta a had'e.
Dariya mama tayi tare da cewa "dama ai nasan kinaji na, dakin cigaba da 'kaliya ai dakin ga aiki".
Turo baki nayi tare da zuro 'kafafuna a 'kasa, shiko kamar wani ubana yana wani kauda kai ya had'e rai yace " tashi kisa uniform mu tafi" kallon sa nayi tare da hararan sa.
Zuwa can nace "ai nayi latti , sai kuma gobe".
" Baki isaba tashi kisaka uniform nace" "uhum banyi wanka bani, ba'a bu'kata wuce ni kina 'batan lokaci" yace tare da barin d'akin.
Yana daga waje yace "ina jira minti biyar na baki, kika wuce rai ya 'baci".
" Kiji fa mam, sai kace wani ubana, to wai meye ruwan shi dani".
Bugen baki mama tayi tare da cewa "karki shirya ki tsaya yau naga duka" daga haka ta fita itama.........
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*Dedicated to Safiyya A W fan's club, kuna bani nishad'i godiya mai tarin yawa*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
🅿2⃣9⃣to3⃣0⃣
Bayi na shiga, wanka ta nayi sannan na fito, koda na fito ganin kayan makaranta na da school bag d'ina a gefen katifa da kayan shafa, nasan duk aikin mama ne.
Janyo kayan shafan nayi ina hararan uniform d'in kamar shine ya min laifi, shafa mai nayi kawai na d'au kayan na saka, fuka babu komai na fito, tunda na fito ya kafeni da ido.
Kauda kaina nayi daga gare sa tare da tsaki a zuciya ta, nufan hanya fita nayi ba tare da na kula mama koshi ba.
"Baki sallame taba", kamar ba dani yake ba na 'kara gaba.
Girgiza kai kawai yayi mama tayi murmushi tare da cewa " nagode yaro na, ubangiji ya taimake ka" "ameen" yace tare da bin bayan na.
Ina fito wa naga Aisha tsaye, muna had'a ido na d'auke kai na.
Cikin masifa ta nufo ni, tana cewa "ai da baki fito ba, da ya barki, kinje kin shanya mutane, kuma muje yau sai kinsha duka biyu, gana rashin zuwa gana latti".
Kamar ba dani take ba na nufi hanya, lokacin ne ya fito motar sa ya bud'e, yana mai cewa Aisha " shiga muje na kai ku" da farin ciki ta nufi motan.
Ina jin su ban ko waigo ba, tana shiga ya tada motan.
Ya fara tafiya a hankali, don garin namu hawa da sauka ne, ga wasu shegun duwatsu, har da uban ramu ka, gomnati ta'ki kawo tallafi. Koda yazo dai-dai inda nake sai ya tsaya ba tare da yayi magana ba.
Ganin haka na bud'e bayan motan na shiga tunda Aisha na gaba.
Ajiyan zuciya ya saki tare da lumshe idanun sa na wani lokaci, kafin ya nisa ya bud'e a hankali ya sauke su akan fuska ta.
Ta madubin motan, wani irin nishad'i naji yana tsarga 'kashi da 'bargo na, shima ta 'barayin sa hakan ne.
Aisha ko washe baki take ta shiga motan da bata ta'ba shiga ba.
Fara tafiya yayi, a hankali yake tu'kin mota shiru kamar kurmaye, sai aukin kallo kamar zai cinyeni.
A haka har muka fito bakin titin shiga cikin gari, yana ganin sa a kwanlta yace yana mai kallon gefen da Aisha take "inane hanyan makaranta?" .
"Nan hanyan zaka bi" ta nuna masa gefen dama, daga nan ne ya fara tu'ki cikin kwarewa, da taimakon Aisha ya kawo mu makaranta .
Yana parking muka fita, kiran Aisha yayi don yaga sai faman had'e rai nake tunda muka fito.
Dawo wa tayi tare da le'ka kanta ta gilas d'in motan, kud'i ya mi'ka mata yace "kuyi break" godiya tayi masa sa'anan ta biyo bayan na da nake ta tafiya ta ba tare da na jira ta kona waigo ba.
Yana kallon na har na shiga class sa'anan ya bar wurin cike da tsanani 'kauna ta.
"Wai besty yau Allah ya d'aga mu, kuma Allah ya cece mu, da yanzu muna can hanya muna cin kwakwa, amma gaskiya yana da kirki, kalli kud'in da ya bamu, da har inajin haushin tsaida ni da yayi", kallo d'aya nayi na d'auke kai na, " ga naki, banso" nace.
" Kai amma guy d'in nan ya had'u, idanun sa farare 'kar dasu, gashin giran sa masu tsanani kyau da tsari, inama inama besty ohhhhhh Allah na" tace tana rugune hannun ta a 'kirjin ta
Esha ke cewa bayan mun zauna, zancen ta na sufan tamin habibi yayi ba'in 'bata min rai amma ban nuna ba nabar abin a raina yana cin raina, bamu dad'e da zuwa ba aka fara tsaron latt, malami ya shigo muka fara karatu.
****************
Muna fito wa daga cikin makaranta muna tafe Aisha sai zuba take ita d'aya kamar kad'anya .
Bamu lura dashi ba sam, sai jinsa nayi dai-dai saitin kunni na yace "ku nake jira" cikin daddad'an muryan sa.
Bugawa zuciya ta tayi, na d'an juya kad'an na gansa gab dani, yana cikin kyakkyawan shiga, Aisha dajin muryan sa ta washe baki tare da cewa "sannu da zuwa yaya".
" Kutumar uban can" nace a zuciya ta, murmushi yayi mata tare da cewa "yauwa 'kanwa ta, kun tashi lafia? ya karatu dai?".
"Lafia qalu, alhamdulillah" "masha Allah, muje ko?" yace yana mai nuna mana inda motar sa take.
Tare muka jera yana ta gefen hagu na, koda muka zo shiga motan bayan ya bud'e .
Zan shiga baya kamar yadda nazo da farko ya daka tar dani, tsayawa nayi ina kallon sa har iso gareni.
"'Kanwa ta koma baya" yace da Aisha data hakince a gaba.
"To" tace tare da fita ta koma baya, "shiga" yace yana tsaye tare da kallo na, ban ce komai ba na shiga ya rufe 'kofar tare da zaga yawa ma zaunin shi na drive ya shiga muka d'au hanya.
Kamar tafiyan farko haka mukayi wannan ma.
Bai tsaya a ko ina ba sai 'kofar gidan mu, bud'e 'kofar motan mukayi a tare kowa ya fita.
Aisha na cewa "mungode yaya, Allah ya saka", " ameen" yace yana murmushi idon sa na kaina da nake ninyan shiga gida ba tare da na waigo ba.
"Tsaya 'kanwata ki kar'ba" bud'e but d'in motan yayi tare da ciro ledan shopping ya mi'ka mata.
Godiya tayi tana kallon sa cike da sha'awa a zuciyar ta tana raya "ashe yana da kirki?" tayi gida tana waigen sa.
Shiru yayi bayan shige wansu yana sosa kai da key d'in hannun sa.
Kallon kayan dake dam motar yayi, yana na zarin yadda zai kwashe su.
Ganin babu mafita yasa ya fara fidda kayan yana ajewa a zauren gidan, yana cikinyi 'kanin Aisha ya fito, kiran sa yayi tare da mi'ka masa wani leda yace "shiga min dashi kaji aboki?".
" To" yace ya shiga gidan su Joy dashi ya mara masa baya, Joy ne zaune tsakar gidan lokacin da ya shigo zaune da d'aurin 'kirji ga bokiti a gaban ta tana ta faman ya tsina fuska.
"Sannu da dawo wa Anty Joy" Muhusin yace, d'ago da kai tayi tana kallon sa tare da cewa "yauwa yaro kirki".
Aje kayan kusa da ita Auwal yayi shima Muhusin yayi hakan.
Haka Auwal ya kwaso kayan nan tasa tana zaune yana shigo wa dashi ba tace dashi ci kanka ba.
Duk da taso cewa wani abu, bakin tane yayi nauyi shiyya sa.
Sai da ya shigo dana 'karshe ya sallami Muhusin tare da zama kusa da ita.
Kallon sa tayi da mamaki domin wurin da 'kura amma ba tace komai ba.
Jan nufashi yayi murya can 'kasa yace " Joy" ido kawai ta tsira masa.
"Ina son ki" sai yayi shiru, murmushi ne ya su'buce min a take, kallo na yayi shima ya saki murmushi tare da kauda kai yace "alhamdulillah, don alamu sunnuna itama tana son sa".
Cigaba da cewa yayi " ina tsanani 'kaunar ki, kuma ina da kishi mai tsanani akan ki, ga kaya nan don Allah kirin'ka sawa kibar sa wad'an kike sawa don zuciya ta na 'kuna duk lokacin da nagan ki dasu".
"Duk da nasan addinin mu ba d'aya ba, amma zuciya ta tafi na'am da kayan mu, ki daure ki saka su".
Juyo wa yayi gaba d'aya yana kallon ta, yace " kina sona?" babu kunya na d'aga masa kai ina murmushi.
Farin ciki na ya'ki 'boyu, kallon na yake cike da 'kauna .
"Har da irin wannan zaman a dai na please" yace yana nuna d'aurin 'kiri dake jikin ta.
Rufe fuska tayi tare da cewa "wanka zanyi shiyya sa" a hankali.
"Zaman me kike to baki shiga bayin ba?" shagwa'be fuska tayi tare da cewa "na gaji ne shiyya sa" dariya yayi tare da mamakin ta.
Kafeshi da ido tayi kamar zata lasheshi, "kallon fa?" yace yana mai gintse dariyan sa .
"Kafi kyau idan kana dariya, Allah ko?" yace yana 'kale mata ido d'aya.
Kallon a gogon hannun sa yayi tare da cewa "muje na miki ankusa kiran sallah" zaro ido tayi tare da cewa "a'a, na yafe, hmmm, shikenan ai aukau lokacin da ko kince bazan bari ba. Mama fah?, tana barci" tace tana kallon cikin idanu wansa.
"Ta kyau ta, ki dai na kallo na haka idan ba haka ba akwai babban matsala" dariya nayi tare da cewa "tom, bari naje nayi wankan Allah har da yunwa nakeji, nima haka" yace yana shafo cikin sa.
Cikin tausayawa tace "bari na kawo maka kaci" tace tana mi'kewa, yamu ya had'iye kut tare da kauda kai da sauri.
Bata 'bata lokaci ba ta dawo hannun ta d'auke da tire, dire wa tayi a gaban sa tare da zama.
Bud'e kwanon tayi, shinkafa ne da miya, gaskiya bazai iya cin wannan shinka fan ba.
Don haka sai yace "kici kawai bari naje masallaci" 'bata fuska tayi ba shiri ya fasa mi'kewa.
Tura masa kwanon tayi gaban sa, kallon ta yayi ta masa nuni da yaci.
"Bani to" yace yana bud'e baki, kallon tsabtataccen bakin sa tayi, yayi matu'kar burge ta.
Babu damuwan komai ta saka cokali ta d'ebo ta nufi bakin sa dashi.
Ta bashi kusan sau biyar aka kira salla, don haka ya dakatar da ita.
"Maza kiyi wanka kafin na dawo mu cigaba da fita" yace yana gab da fita.
"Oho har da abinci kici kinji?" d'aga kai nayi ina mai jefan sa murmushi, shima ya mayar mini.
Comment & share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*Tell my mistake to me, not to others. Because my mistakes are to be corrected by me, not by others.*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
0 comments:
Post a Comment