*_All names and characters are fictitious and imaginary. Any resemblance to any person living or dead, is purely coincidental, and not intentional._*
***KADUNA
K'arfe d'aya saura kwata na dare, Alh. Badaru cikin tsananin gajiya da k'osawa yake danna horn din motar, wanda ya razanar da Mal. Idi mai gadi da ke ta kwasar bacci har da munshari.
A hargitse ya mik'e tare da janyo torchlight d'inshi ya haska, hakan yasa ya fahimci mai gidan ne ya iso, wanda hakan ba bakon abu ba ne a wurinshi, a cewar zuciyarshi ma yau mai gidan ya dawo da wuri. Horn din da ya k'ara dannawa ne ya sanya shi gaggawar wangame k'ak'k'arfan tangamemen k'yauren gate din, tare da rissinawa yana fad'in
"Barka da zuwa Yallabai."
Bai damu da gaisuwar ta shi ba, ya figi motar a sikwane ya shige, ya gyara parking, sannan ya fito ya fara tuttular da ruwan masifa.
"Haba da Allah Mal. Idi, wannan wane irin bacci ne sai kace na mutuwa? Na fi minti biyar ina maka oda, amma ka yashe baki kana zubar da ruwan sale6a, wallahi ba zan lamunci baccin nan naka ba, Allah ya kaimu gobe in yi wa Garba security waya ya canja mun kai."
Ko alama Mal. Idi bai girgiza ba da maganar ta uban gidanshi, asali ma idan da sabo, ya ci ace ya saba da wannan banbamin wanda yayi ma lakabi da ihunka banza, kasancewar yau shekarunsu biyar kenan suna tare da Alhajin, wanda kusan kullum kuma sai ya maimaita cewar zai sa a canja shi. Har k'asa ya rissina yana fad'in
"A yi hak'uri Yallabai. Ka san jiki da jini, ga kuma girma ya kawo kai."
Banza yayi da shi ya fara dukan k'ofar shiga cikin gidan, ga mamakinshi ya ji ta a bud'e, ya ja mugun tsaki, tare da murda handle din, sannan ya wuce ciki.
Zulaiha babbar 'yarshi ya fara cin karo da ita, kudundune cikin bargo tana ansa wayar masoyinta, kunnuwanta dad'e da earpiece, da alama bata san wainar da ake toyawa ba.
Hannu yasa ya yakice bargon, domin yadda take mutsu-mutsu a cikinshi, shi ya tabbatar mishi da cewar idanuwanta biyu.
"Uban mi kike da wannan tsohon daren a palo ke d'aya? Ina Mamanku?"
Ganinshi bai sa ta zabura ba, illa mikewa zaune da tayi, tana gyara maballen gaban rigarta wanda bata san lokacin da ta balle su ba, dad'in tana waya da masoyinta.
"Ba ki ji me nace ba ne? Kin kafe ni da ido."
"Waya nike yi, su kuma ina jin sun yi bacci."
"Mtsewww. Tashi wuce mun a nan Dallah."
"Ina wuni."
Ta fad'a tana yayime bargonta, ya ansa da
"Lafiya."
A dakile. Ya zube a kujerar da ta tashi, yana mai cire hular da ke kanshi. Hamma ya saki mai tattare da yunwa da gajiya, dan rabonshi da kyakkyawan bacci yau kwana biyar kenan, tunda wannan siyasar ta matso basu da sauran lokacin kansu, sai na meeting, kullum sune a wannan hotel, gobe a wancan. Gurinsu d'aya tak, Alh. Mahabub ya lashe kujerar gwamnan jahar tasu kowa ma ya huta.
Da wannan tunanin ya mik'e ya bud'e fridge ko ya samu wani abu mai d'an dama-dama ya jefa a cikinsa, dan bayan gajiya har da yunwa ke dawainiya da shi, gashi kuma bai sanar da matarshi dawowarshi ba, balle yace ta tanada mishi wani abu, yayin da a wani bangaren yana tunanin ko ma da ya sanar da itan, ba lalle ya samu abinda ranshi ke so ba.
Babu komai a fridge din, sai lemunan gwangwani da na kwali, sai kuma wata furar roba, wacce itama din shine ya sha ya ajiye sauran a kwana biyar da suka wuce ranar da zasu tafi Abuja taron karrama gwamnoni masu jiran gado.
*****
Washe gari, da sassafe ya ke jiyo hayaniyar yara 'yan makaranta, ya ja tsaki, tare da janyo wayarshi ya duba, karfe takwas saura 'yan mintina, ya mik'e ya shige bandakinshi dake cikin dakin yayi alwalla ya fito yayi sallah, har ya gama bai daina jiyo hayaniyar yaran ba, sannan ya fita ya same su har yanzu basu gama shiri ba, lokacin takwas da rabi har ta kawo kai.
'Ahmad da Samahir wadanda sune na k'arshe a yaran, yan biyu masu shekaru hudu, suka ruga da gudu suka isa gare shi suna
"Oyoyo Baba."
Hannuwansu ya kama suka k'arasa cikin palon, suka zauna, sannan ya kai duba ga Zulaiha mai danne-dannen waya.
"Ke baza ki je makarantar ba ne?"
Sai a sannan ta d'ago
"Ai mu mun gama waec tun wancen satin. Ina kwana."
"Lafiya lau."
Mukhtar mai bi mata ya shigo palon yana kiran
"Ke Dallah malama wai ina kika saka mana socks dinmu ne? Ki taso ki dauko su wallahi ko in fasa miki baki."
Kici6is, idanunshi suka yi da na mahaifinsu, a kaikaice ya shafi tarin sumar da ke kansa.
"Baba ashe ka dawo? Ina kwana?"
"Lafiya lau Mukhee. Wai ya aka yi har tara saura baku tafi makaranta ba? Ina Mamantaku?"
"Ga wadda ta tsaida mu nan, ta kama socks din mutane ta cusa a kayan wanki, kuma ta san sarai dokar school din mutum ba zai taba zuwa babu socks ba."
"Ke tashi je ki duba musu mana, ki sanar da Mamanku ina kiranta."
"Yo ni fa Baba ban san inda suka sa kayansu ba, kuma ma shine fa baya tashi bacci sai ya ga karfe takwas tayi, bayan ya san suna zuwa makaranta, kullun sai an musu bulalar latti."
"Gara mu bulalar latti ake mana, ke kuwa fa? Kullun ana kama ku da samari a bayan Computer lab. Dallah malama ki nemo mana socks mu kawai."
"Kai Dallah ku rufewa mutane baki, wannan wane irin iskanci ne ina magana kuna yi."
Duk da haka ba su yi shirun ba, suka mik'e suka yi hanyar dakunan kwanansu, suna jifar junansu da mugayen kalamai, tamkar ba wadanda suka fito ciki daya ba.
"Uhnmmm. Ashe ka dawo?"
Muryar uwar gidanshi Hajja Fati ta sanya shi dakatawa daga ansa wayar da suke da Party Chairman, ya dube ta yana gyada mata kai, ba tare da ya ajje wayar ba.
Zama tayi, sannan ta kama Samahir tana cewa
"Wai yarinyar nan bata k'arasa shirya ku ba dama? Kai ina jakar taka take?"
Ta karashe tana kallon Ahmad. Yayin da Alh. Badaru ya mik'e ya fita yar farfajiyar gidan yana cigaba da ansa wayarshi, ganin surutun nasu na shirin wuce gona da iri.
A hargitse dai aka gama shirya yaran, inda a d'aki aka cigaba da damben tsiya tsakanin Mukhtar da Zulaiha, kan ta k'i ta dauko musu safa.
Alhaji na gama waya da Chairman, kiran gwamna mai jiran gado ya shigo, ya dauka suka tattauna batun na siyasa, tare da shaida mishi meeting da suke da shi a yau din nan karfe sha biyu na dare, wanda shine kiran da Chairman din yayi mishi.
Ya kashe wayar ya juya da dan murmushi, domin kuwa kiran na Chairman ya mishi dad'i, zaune ya ganshi rakube, jikinshi sanye da uniform, bayanshi goye da jakar makaranta.
"Baba ina kwana."
"Lafiya lau Tareeq, kai ka shirya kenan?"
"Eh su nike jira."
"To yayi kyau..."
Zaiyi magana wayarshi ta hau k'ara, ya duba yana dariya, wannan karon Women Leader ta kasa ce ta kira, ya dauka a gaggauce ya fice kofar gida yana ansawa.
Sai da suka gaji dan kansu suka saki junansu, domin kuwa duk irin maganar da Hajja Fati ta musu, bai sa sun daina fadan ba, k'arshe tace
"In kun ga dama ku kashe kanku."
Ta juya ta kama hannun Ahmad da Samahir suka fita, ta dubi Tareeq wanda halayyarshi ta sha ban-ban da ta 'yan uwannashi tace
"Kama su ku shiga mota."
Ya mik'e ya kama hannuwansu, suka fita inda driver yake jiransu tun karfe takwas, suka shiga suka zauna suna jiran fitowar Muktar.
Har mintuna biyar suka shude Mukhtar bai fito ba, haka zalika Alh. Badaru yana tsaye k'ofar gidan har yanzu yana ansa wayar Women Leader.
"Baba Ado ko zaka kaimu ka dawo ka d'auke shi? Na san yanzu an fito break sai mu samu mu koma class ba sai an mana bulalan latti ba."
"Kana ganin babu wata matsala? Ka fa san halin mutuminnaka."
"To ai kaga har yanzu bai fito ba, k'arshenta ma ba zai je makarantar ba wallahi."
"To shikenan Tareeq, barin kaiku din in dawo."
Ya tada motar suka dau hanya.
www.lubabatumaitafsir.com
www.wattpad.com/iLubieee
www.instagram.com/hausa_novelss
www.facebook.com/taskarlubieemaitafsir
Lubiee♡
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
December, 2016
{03}
Misalin takwas saura na dare Hajja Fati ta dawo gidan, a gajiye liss ta shigo, ta ci karo da Tareeq da Khalid wanda suka dawo daga masallaci zaune a palon suna kallo. Gabanta ne ya yanke ya faÉ—i, kafin ta daure ta k'arasa ciki jiki babu k'wari.
"Yau kune a gidan?"
Ta faÉ—a tana kallon Khalid.
"Wallahi fa Hajiya. An dawo lafiya?"
"Lafiya lau. Ya mutan gidan?"
"Duk sunce a gaishe ku."
Bata k'ara cewa uffan ba, ta mik'e zata shige ciki.
"Sannu da zuwa Mama."
Tareeq ya faÉ—a yana kallonta. Ta juyo a hankali tana dubanshi, sai taji wani irin yanayi tare da tausayin yaron sun mamaye dukkan zuciyarta. Shiru tayi tana karantar yanayinsa, ta rasa me sa take jin kamar bata yi mishi adalci a cikin gidan, kasancewar yadda take fita ta bar su ba tare da ta tsaya ta kula da bukatunsu ba. 'Ai akwai kunnenshi.' Wata zuciyar ta tunatar da ita, hakan yana nufin ba shi ne abin tausayi ba kenan, kuma ma ai ta bar Zulaiha a gidan, ga kuma Asabe mai aiki, ta tabbatar zata taimaka musu. Murmushi ta saki tana k'ara dubanshi.
"Yawwa Tareeq. Ina su Samahir?"
"Suna ciki."
"Zulaiha fa?"
"Tunda muka dawo ban ganta ba ni dai."
"Gidan ub**wa ta tafi ni da na bar mata tsaron gida. Ina Mukhtar?"
"Ya fita da abokanshi shima."
Jin hayaniyarta yasa su Samahir fitowa suka yo palon, bata damu da su ba ta dai-daita tsayuwarta
"Tashi wuce kira mun Mukhtar, nasan ba zai wuce gidansu Deeni ba. Akwai sak'o da na manta in anso gidan Hajiya Maryama. Ita kuma zata dawo ta same ni."
Daga haka tayi ciki, Tareeq ya kalli Khalid wanda ya kasa cewa komai, illa a cikin zuciyarsa da yace
'Me zai hana yara yin abinda suke so, bayan ke kanki baki tsaya kin kula da tarbiyyarsu ba.'
Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya cigaba da zancen zucinshi.
'Yanzu da wani zai ce mata Mukhtar mai shekaru sha bakwai ya san ko wanne kalar kayan shaye-shaye, da babu abinda zai hana su hau sama da koma wanene.'
"Barin je in kira shi Uncle."
Muryar Tareeq ta dawo da shi daga dogon nazarin da ya ke. Ya kalle shi da É—an murmushi,
"Barin zo muje ko?"
Dariya Tareeq yayi, mai bayyanar da jin daÉ—in kulawar Khalid a gare shi yace
"Ba nisa sosai uncle, can layin na gaba ne fa. Barin je in dawo kawai."
Ya mik'e, tare da ajje remote É—in hannunsa ya wuce zuwa k'ofa.
"Tareeq."
Khalid ya kira shi yana dubansa da murmushi, duk kuwa da sauyin yanayin da yake ji a zuciyarsa dangane da fitartashi.
"Na'am Uncle."
"Ka bari inzo muje kawai."
"Allah Uncle ba sai ka je ba, yanzun nan zan dawo in sha Allah."
"Alright, but idan baya gidan da tace kar ka matsa ko ina, ka dawo gida kawai. Duk ma inda yake zai dawo da kanshi."
"To shikenan."
Yana 'yar dariya ya saka takalmansa ya fito, suka gaisa da Mal. Idi, sannan ya buÉ—e k'ofa ya fita.
*****
Duk wanda ya san Kinkino Road da ke cikin Unguwar Rimi, ya san unguwa ce ta manyan mutane, haka kuma babu yawaitar al'umma ko kaÉ—an a titinan unguwar, zata iya kasancewa ayi kisa a binne, ba tare da wani ya farga ba, haka zalika abu ne mai matukar wahala kaga yara masu shekarun Tareeq suna yawo a cikin unguwar a dai-dai irin wannan lokaci. Manyan ma ba kowa ke fita a kafa ba, illa 'yan tsiraran motoci da sukan zo su wuce da gudun fanfalak'i, ba tare da wani ya gane wanda ke cikin motar ba.
Yau ma unguwar shiru, sai dogayen street light É—in da suka haska lafiyayyen titin, tare da dogayen bishiyoyi masu yalwar rassa da suke kaÉ—awa, suna bada iska mai daÉ—i kasancewar yanayin na damana. Amma cikin rashin sa'a sai fargaba, da faÉ—uwar gaba suka dinga kai farmaki a zuciyar Tareeq cikin wannan dare ma'abocin sanyin iska da haskakawa.
Bai kawo komai a zuciyarsa ba ya cigaba da tafiya, cikin sauri-sauri, har ya kawo kwanar da zata sada shi da titin gidansu Deeni. Sai dai wannan karan sam zuciyarsa ta kasa natsuwa, kasancewar yadda yake jin tamkar wani na biye da shi, amma da ya juya baya ganin kowa, haka zalika layin nasu babu yawaitar haske irin na main street É—in da ya baro.
A firgice ya iso kofar gidan, ya É—ora hannu zai buÉ—e gate É—in, ya ji an cafki hannunnasa, yana juyowa suka yi ido huÉ—u da Mubee, wanda shima abokin Mukhee ne, yana É—aya daga cikin wanda suka je gidansu a É—azu.
Sauran mutum biyun ne bai ida tantancewa ba, suka sa k'yallen da ke hannunsu, suka É—aure idanunsa gam-gam har sai da ya saka wani razanannen k'aran da ya kiÉ—imar da su, sai dai cikin jarumtaka, suka k'ara sanya wani tsumman suka É—aure bakinshi, Sino ya kalle su yace
"Ku É—auko mun shi."
Tabbas Tareeq ya san mamallakin muryar da tayi magana, sai dai tsananin ruÉ—anin da yake ciki yasa ya kasa banbance mai ita a tsakaninsu.
A kafaÉ—a Deeni ya É—auke shi, cikin gaggawa suka k'arasa inda motar Sino ke ajje, suka jefa shi ciki, duk da irin shure-shuren da yake yi; haka suka shige, Sino ya buga engine motar suka bar layin baki d'aya.
Kuka Tareeq yake irin kukan da baya fita, saboda tsananin azabar da yake ji a cikin idanunsa, domin kuwa sun musu wani irin k'ulli, wanda da wuya ya k'ara morar idanunnashi zuwa gaba.
Cikin wani uncompleted building dake karshen layin suka shige da motar, Sino ya gyara parking sosai, sannan duk suka fito, tare da kamo Tareeq, suka mikar da shi tsaye.
"Kwantar da shi a nan kaga."
Babu gardama Deeni ya fara kiciniyar kwantar da shi, amma ya tokare, hakan yasa Mubee da ke tsaye, ya taimaka masa wurin doke kafafunsa, a take ya zube a k'asa.
Farin dogon wandon da ke jikinshi Sino ya zare, shima ya cire nashi ya wulla ma Mubee, ya rage daga shi sai _boxers_, ya kalle su yayi wata shu'umar dariya, sannan ya cire _boxers_ É—in, ya dawo dashi dai-dai kafafunsa, a karo guda ya fara k'ok'arin tura jikinshi ta bayan Tareeq.
Kuka yaron yake wanda baya fita, kasancewar bakinshi da suka É—aure, yana amfani da hannayensa wurin ceton kansa, amma haka Sino ya sanya rashin imaninshi, ya turmusa hannayensa cikin k'asa, sannan ya É—ora nasa akai, ya saka kirjinshi ya danne kanshi da ke É—agowa, yayi mishi kyakkyawan rik'on da bai isa ya k'ara wani motsin kirki ba, a karo guda ya daddage da iya k'arfinsa, ya tura jikinshi a bayansa.
Wani irin ihu Tareeq ya saki, har da zillewa, saboda irin raÉ—aÉ—in da ya ji, a take kuma ya komar da kanshi sharaf, wata irin azaba yake ji tana ratsa ko wanne sashe na jikinshi, a karo guda wata zufa ta karyo ma Sino, domin ba karamar wahala ya sha ba, kafin ya samu hanyar da ya shigar da kanshi cikin jikinnasa.
Wannan bai zama bakon abu a wurin Sino ba, domin kuwa ya daÉ—e da sabawa wurin keta haddin k'ananan yara, ya Allah waÉ—anda suka shiga gonarshi, ko kuma waÉ—anda ya ji ya kwaÉ—aitu da sigar jikinsu.
Ya kwashi kusan mintina ashirin yana abu É—aya, sannan ya samu natsuwar kansa, ya mik'e yana kallon Deeni, wanda shima din É—an hannu ne. Ya murmusa yana É—aura belt É—in wandonsa.
"Ya zaka É—ana ne?"
"That one na confirm."
Deeni ya faÉ—a tare da dirowa daga kan _bonnet_ É—in motar, ya cire wandonshi, ya cigaba da aiki daga inda Sino ya tsaya.
"Dan Allah kayi sauri Deeni, ka ga fa dare nayi."
Mubee da ke cikin mota ya faÉ—a yana duba agogonshi, wanda shi É—in irin harkar bata sha mai kai ba, illa shaye-shaye da farka mutuncin k'ananan 'yan mata.
A gaggauce Deeni ya mik'e, ya gyara wandonshi tare da gyara ma Tareeq wanda bai san duniyar da ake ba shima na shi wandon, suka kama shi, suka saka a motar, sannan Mubee ya tada suka tafi.
A nesa kaɗan da gidansu suka yi parking, yayin da Deeni ya kuma saɓarshi a kafaɗa, ya matsa kusa da wani _culvert_ na gefen gidan ya kwantar da shi. Da gudu ya juya suka shige motar, suna ihu, suka tada suka bar unguwar.
*****
Fitar Tareeq ke da wuya, Mukhee ya shigo gidan yana ciccika fuska, da ka ganshi ka ga wanda yake a wata duniya ta daban.
"Ina Tareeq É—in?"
Khalid wanda tun tafiyar Tareeq hankalinsa ya kasa kwanciya, ya tambaya tare da mikewa yana duban Mukhtar.
"Wane Tareeq kuma? Ni me haÉ—ina da shi?"
"Ba shi ya kira ka ba?"
"Malam ni fa ban ga wani Tareeq ba, kada ka dame ni Dallah."
"What? Mukhtar ni sa'anka ne da zaka rink'a gaya mun magana haka? Kai wane irin yaro ne marar É—a'a?"
"To nace ban ganshi ba ko, me kuma zaka ishe ni."
Ya buga tsaki ya wuce yana cewa
"Mutun da gidan ubansa haka kawai a zo ana takura masa."
Yana shiga suka haÉ—e da Hajja Fati, ta bi bayanshi tana cewa
"Sai yanzu ka zo? Dama gidan Hajiya Maryam zaka je mun idan ban takura ka ba."
"Ai kema kinsan babu yadda za'ayi in tafi Kawo yanzu, goma saura fa, wallahi bazan je ba. Ga wancen wawan ma yana neman É“ata mun rai Dallah."
"Ai shine nima naga goma ta kusa. Shi kuma wancen ka bar ni da shi, kwanan nan zanyi maganinshi wallahi. Ina dalili."
Bai tanka ta ba ya wuce zuwa É—akinshi, itama nata É—akin ta faÉ—a, inda ta bar su Samahir a É—akin Asabe suna wasa da Musa É—anta da take goyo.
Hankalin Khalid kwata-kwata ya kasa kwanciya, yayin da ya rasa dalilin rashin natsuwartasa, ya kalli agogon da ke É—aure a hannunsa, karfe tara har da mintuna ashirin da biyu, ya mik'e da zumar fita ya dudduba inda Tareeq É—in ya tsaya, ya ji an tura k'ofar palon an shigo.
Ajiyar zuciya ya saki ya koma ya zauna tare da zuba ma k'ofar idanu.
www.wattpad.com/iLubieee
Lubieee ce♡
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
December, 2016
{02}
Kusan minti biyar Alh. Badaru yana tsaye a wurin bayan tafiyarsu, sannan ya koma ciki. Da sauri-sauri ya fad'a wanka ya fito yana tsaka da shiryawa, ya fara k'walla kiran
"Hajja Fati. Hajja Fati."
"Tana wanka."
Zulaiha ta bashi ansa. Ya ja tsaki ya gama shirinsa, yana kokarin É“alle links É—in wuyan rigarsa, wayarsa wacce tun yana banÉ—aki ake kira, ta sake É—aukar wani k'aran da ya sanya shi mik'a kai yana son gano mai kiran.
Ya É—auki wayar ya danna, sannan ya buÉ—e hands free ya cigaba da abinda ya ke yi.
"Barka da asuba Yaya. Ya aiki?"
"Barka dai Khalid, ya gida?"
"Alhamdulillah. Kana gari kuwa?"
"Eh to, amma gani nan zan fita. Lafiya?"
"Lafiya lau. Dama akwai maganar da nike son muyi ne, zan zo yau in sha Allah."
"Sai ka zo É—in. Amma ba lallai ka same ni ba gaskiya, dan ina da meeting mai muhimmanci."
"Ba komai, zan jira har ka dawo É—in."
"To madallah."
Daga haka suka yi sallama, ya É—auki É—an k'aramin trolley daya zuba kayan buk'atarsa, ko da kwana ya ka kama shi.
A shirye tsab ta fito itama gyalenta a kafaɗa, da alama fita zata yi, suka yi kiciɓis, ta dube shi ta k'ara duban jakar hannunsa tana faɗar
"Sai ina kuma?"
Ya ajje jakar yana dai-daita zaman hularsa
"Muna da meeting yau 12:00am sharp, ban sani ba ko zan dawo ta gida idan mun tashi, ko kuma mu kwana can, a gobe ma haka dole mu wuce Abuja saboda taron Party na k'asa."
Kai ta rausayar, sannan ta juya idanunta.
"Hakan ma yayi, nima kasuwa zan fita akwai abubuwan da muke buk'ata."
Bai ce kala ba ya ciro kudi ya kirga, ya mik'a mata, ta ansa ta saka a jakar dake sagale a hannunta, tare da juyawa ta fara taku zuwa waje, yayin da shima ya É—auki jakarsa yana biye da ita.
A palo suka tar da Mukhtar da Zulaiha, Alh. Badaru ya dube shi, yayi kicin-kicin da fuska yana ta faman hura hanci, shi a dole yana cikin É“acin rai.
"Mukhee."
Alhajin yayi kiransa, tare da sauke jakar yana dubansu, hakan yasa Hajja Fati ta dakata itama.
"Baka je school É—in bane?"
Yana cika fuska ya fara nuna Zulaiha da yatsa
"Ga wacce ta É“ata mun rai nan, wallahi Baba ko ka mana tsakani da yarinyar nan ko kuma wata rana zan iya sumar da ita."
"Ya isa da Allah, tashi muje in sauke ka in wuce."
"Yasin ba zan je ba, ai ta ja ma makarantar ma kawai Allah."
Zuciyar Alhaji Badarun ce ta motsa, ya juya yana kallon Hajja Fati
"Kin ga yaronki ko?"
"Nima nayi iyakar yina, tun safe ma suke faÉ—a babu wanda ya saurare ni cikinsu, ya kake so in mishi? Kanshi ya yi ma ai ba wani ba."
"Idan ka ga dama daga yau kar ka k'ara zuwa makarantar dan gidanku."
Alhaji ya faÉ—a a faÉ—ace, yana nuni da Mukhtar.
Gunguni ya fara mishi, ya juya yana yarfa hannu, yayin da shi kuma ya É—auki jakarsa ya fice, Hajja Fati ta juya ta kalli Zulaiha
"Kice da Asabe ta tabbatar ta gama duk wasu ayyukan gidan nan da Allah, ta ba Ado driver abincin su Tareeq ya kai musu. A tabbatar dai an gama komai kafin in dawo."
"Zan faÉ—a mata."
Daga haka ta fita, Mukhtar ya rufa mata baya, tayi inda motarta ke ajje, yayin da shi kuma ya isa ga Baban yana shafa kai, da alama kuÉ—i yake nema, duk kuwa da rashin annurin fuskarsa.
Dubu biyar ya mik'a mishi, duk kuwa da abinda Mukheen yayi, bai sa mahaifinnashi jin haushinsa ba, asali ma shine yaro mafi soyuwa a birnin zuciyarsa. Ya tada motar ya fice, Hajja Fati ta rufa masa baya kowannensu ya kama hanyarsa.
****
Alhaji Badaru haifaffen garin Kaduna ne a cikin unguwar Tudun Wada. Gawurtaccen É—an siyasa ne, wanda ya É—aukaka daraja da mutuncin siyasarsa fiye da komai da ya mallaka a doron k'asa, daga ciki kuwa har da iyalinsa. Matarsa Hajja Fati 'yar Maiduguri ce, wacce suka haÉ—u a can Maidugurin lokacin da suka je wani taron siyasa shi da uban gidansa gwamnan Kaduna mai ci, a wancen lokacin.
Ko da suka yi aure, Alhaji bai tsagaita daga yawace-yawacen siyasarsa ba, illa ma gaba da abin ya rink'a yi kasancewar girma da ya fara zuwa masa, hakan yasa ya k'ara k'aimi a harkar siyasartashi, ya zama wani zakaran gwajin dafi, mai faÉ—a a ji, a siyasar ta garin Kaduna, domin kuwa matsawar zasu fitar da gwaninsu, to da wuya su faÉ—i k'asa ba nauyi, abin nufi dole su lashe kujerar da suke kwaÉ—ayi, ko da masoya kujerar sun tasan ma mutum hamsin.
Wannan yasa Hajja Fati zama mace mai 'yanci a cikin gidanta, ta fara huÉ—É—a da manyan mata masu abincin gobe, hakan ne kuma yayi sanadiyyar karkatar da hankalinsu daga bayar da kyakkyawar tarbiyya ga yaransu guda biyar.
Zulaiha ce babba, mai shekaru goma sha tara wacce ta gama secondary school, sai Mukhtar mai bi mata, yana da shekara goma sha bakwai, wata mai tsayuwa zai cika sha takwas, yana SS2 zuwa SS3 Tareeq mai shekara goma sha É—aya, yana JS1, sai Ahmad da Samahir masu shekaru huÉ—u da suke Kindergarten, wanda daga su Hajja Fati tace baza ta k'ara haihuwa ba.
Rayuwar gidannasu rayuwa ce mai cike da 'yanci, rashin kwaɓa, da rashin tarbiyya. Hakan yasa kowanne yaro yake tata rashin mutuncinshi dai-dai da iyawarsa, babu wanda zai hana su kasancewar wani lokacin sai su kwashi sati ɗaya zuwa biyu ba tare da sun saka mahaifinsu a idanunsu ba, yayin da mahaifiyarsu kam bata damu da kula da yanayin da suke ciki ba ko kaɗan, ta ga damar ta fita tun safe, ba ita zata nemi hanyar gida ba sai taga dare ya kawo kai, duk kuwa da cewar ba aiki take ba, ba kuma sana'a ba.
Khalid kanin mahaifinsu, shine ma ya kan zo ya kwashi 'yan kwanaki a gidan, shine kuma mutum ɗaya jal, da yake tsawatar musu, wanda hakan yasa ko alama Zulaiha da Mukhee basa k'aunar zuwanshi. Domin kuwa namiji ne mai tsare gida, wanda baya son wasa baya kuma son reni, haka kuma kaf dangin Alhaji Badarun babu wanda ya isa ya raɓe shi, shima Khalid ɗin dan Hajja Fati bata da yadda zata yi da shi ne, kasancewarshi wanda suka fito ciki ɗaya da Alhajin.
*****
Karfe biyar na yamma yaran suka dawo a gajiye, kasancewar har islamiya a can suke yi, wannan ne ma ya taimaka musu wurin samun ilimin addinin, wanda da ba dan haka ba, da babu wanda ya san yadda rayuwartasu zata ida gurɓata.
Ahmad da Samahir ne a gaba, cikin murna suka isa ga Khalid da ke zaune a palon yana kallo. Cikin jin daÉ—i suke tambayar
"Uncle Khalid yaushe ka zo mana?"
"Tun kusan 4:00 twins, ina abokina?"
A dai-dai nan Tareeq ya shigo, da gudu ya isa gabanshi, suka rungume, tare da jin daÉ—in ganin junansu. A take ya nemi gajiyar da ya shigo da ita ya rasa.
"Uncle yaushe ka zo?"
"Ban daÉ—e da zuwa ba Tareeq, ya school?"
"Lafiya lau Uncle. Ina su Hajiya?"
"Suna nan lafiya, duk suna gaishe ku. Mukhee fa?"
Dan siririn tsaki Tareeq ya saki,
"Baka ganshi ba? Ai bai ma je school É—in ba yau. Barin cire uniform inzo in baka labari."
Bai jira ansarshi ba, ya juya ciki da murnarshi, domin a duniya babu abinda yake k'auna irin ya ga Uncle Khalid ya zo gidannasu, ko ba komai shine kawai ke taka ma 'yan uwannashi birki idan suna wani abun. Shine kaÉ—ai kuma da ke bashi cikakken lokacinsa tamkar shi ya haife shi. A wasu lokutan ma ya kan ji inama ace Uncle Khalid É—in ne ya haife shi, ya tabbata da ya fi ko wanne É—a sa'a a wannan duniyar.
Yana shiga ta corridor É—in da zai sada shi da É—akunansu ya fara jiyo hayaniya daga É—akinsu, take ya ji annurin fuskarsa ya É—auke, dan ya tabbatar ba zai wuce Mukhee da lalatattun abokanshi ba.
Ya É—an saki tsaki a hankali, tare da k'ara mikewa zuwa É—akin, ga mamakinshi yana shiga ya gansu zaune gaban tv sun tattara hankalinsa, wurin kallon alfasha,(subhanallah) gabansu da katuwar shisha pot wannan yana sha yana ba wannan.
Cikin zafin zuciya ya isa yayi kwallo da pot É—in, hakan ya dawo da hankalinsu gare shi, duk suka É—ago suna duban yadda fuskarshi tayi jajir, idanunsa cike taf da hawaye.
"Kai wane irin banza ne Dallah? Uban me haka zaka mana wurgi da abu?"
Mukhee ya mik'e a fusace, gadan-gadan yayi kan Tareeq wanda ke rik'e da school bag, yana shirin kai masa duka.
"Nooo please. Kyale shi Dallah Mukh, ba da kai yake ba, da mu yake dan ya ga mun zo gidansu ne yake neman raina mana hankali."
Cewar É—aya a cikin abokan, wanda da alama zai kai shekaru ashirin.
"Ka bar ni in koya mai hankali Sino, in banda iskanci ni sa'anshi ne da zai raina ni a cikin mutane haka."
"Share mana da Allah. Guys ku tashi mu wuce."
Sino ya kara maimaitawa yana kallon sauran samarin biyu, waÉ—anda hankalinsu baya tare da su daga dukkan alamu.
Suka mik'e suna É—an tangaÉ—i suka wuce, Tareeq ya bisu da wani mugun kallo mai tattare da tsana, da kuma tsangwama.
Dai-dai kunnenshi Sino ya matso
"You'll regret this T-boy."
Yayi 'yar dariya, tare da buga kafaÉ—arshi, suka fita a gidan baki É—aya.
Nuna shi Mukhtar ya fara yi da hannu,
"Zaka sani yaro. Wallahi duk ranar da ka kara yi mun irin shirmen nan sai na fasa dogon bakinkan nan. Idiot."
Ya juya ya kashe tv, sannan ya bi bayan su Sino suka fito. A palo suka haÉ—u da Khalid, wanda da alama bai san da zuwanshi ba. Cikin wani sabon takaicin ya sakan mishi harara a kaikaice, dakyar ya iya cewa
"Sannu fa."
Ya sanya kai dan bashi da buk'atar ansarshi.
Kai kawai Khalid ya jinjina, a zuciyarshi yana nema ma Mukhtar É—in shiriya a wurin mai kowa da komai.
www.wattpad.com/iLubieee
Lubieee♡
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
December, 2016
{04}
Zulaiha ce ta shigo, a gaggauce Khalid ya mik'e yana kallonta, sanye take da bak'in _skinny jeans_, wanda ya samu wuri ya lafe a cikin jikinta, ya fitar da matashiyar surarta muraran a fili ana kallo. Bak'ar _t-shirt_ mai _turtleneck_ ta ɗora, sosai ta bayyanar da cikakkar halittar kirjinta, hannunta sagale da farar _hinge jacket_, wacce da alama a saman kayan ta ɗora ta, kafafuwanta lulluɓe cikin fararen _sneakers_, a kanta farin gyale ne, ta buga lafiyayyen daurin _turban_ wanda ya cika sosai, ya fito da yarinta da kuma asalin k'uruciyarta.
Kallo ta bishi da, ganin yadda yake kallonta itama, a karo guda ya sauke ajiyar zuciya tare da gyara tsayuwarsa yace
"Daga gidan wa kike cikin daren nan Zulaiha?"
Kallon da take yi mishi ne ya canja salo zuwa ga na wulakanci, ta juya idanunta tana turo baki, a karo guda tana gyara rik'on da ta yi ma jacket É—inta tace
"To kai kuma me naka a ciki?"
"Aoh, haka ma zaki ce?"
K'asa tayi da idonta ganin ya taho gadan-gadan yana nuna mata yatsa, ta san idan tayi wasa zai iya É—auke ta da mari ba damuwarsa ba ce. A dai-dai nan Hajja Fati wacce hayaniyarsu ta fito da ita ta k'araso ta shiga tsakaninsu tana cewa
"A'ah Khalid, kar ka fara. Wai me yaran nan suka tsare muku a duniya da kuka É—auki karan tsana kuka É—ora musu? Zan lamunci komai, amma kar ka kuskura ka É—ora hannunka kan yarana. Haka kawai. Wuce ki shige ciki ke kuma."
Ta juya tana yi mishi kallon 'a haka zaka kare', ta wuce ciki, Hajja Fati ta rufa mata baya, suka bar Khalid da hannu a sage yana mai bin bayansu da kallo.
"DUNIYA ce."
Ya faÉ—a a bayyane, a karo guda ya shafi tarin sumar kansa, kafin ya k'ara da cewar,
"TA FI BAGARUWA IYA JIMA!."
A fusace ya zira takalmansa ya fita zuwa k'ofar gida.
Zaune ya samu Mal. Idi a bakin k'ofa, ya mik'a mishi hannu suka gaisa, sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai cigaba da dubansa.
"Baka ga dawowar Tareeq ba da Allah?"
"Har yanzu bai dawo ba gaskiya, ni kaina nayi mamakin fitar tashi ma, dan da wuya ka ganshi waje a irin wannan lokutan."
"Wallahi fa, gashi har kusan awa biyu da fitarshi yanzu, kuma yace mun gidan ba wani nisa."
"Ina ne ya je?"
Mal. Idi ya tambaya tare da mik'ewa tsaye ya fara k'ok'arin buÉ—e k'ofa.
"Wai gidan su wani yaro abokin Mukhee, ko Deeni ne ko menene. Yaran nan dai abokanshi da suke shigowa."
Yana biye da bayan Mal. Idi zuwa k'ofar gida yake wannan maganar.
"Ayya, Deeni? Can wancen titin da yayi haka, da ka mik'e, gida na hudu, nan ne gidansu."
"To barin duba in ga."
Ya zuba hannayensa cikin aljihu ya fara takawa, sassanyan iskan da ke busawa yana ratsa sassan jikinshi, sai dai kuma zuciyarsa tayi bulaguro zuwa ga rashin natsuwa da kuma kwanciyar hankali.
Wata mota ce ta taho a sikwane, hasken fitilunta ya taimaka wurin k'ara haskaka tsakiyar titin, daf da zata wuce gefenshi ya hangi mutum shimfiÉ—e a k'asa, bai k'arasa tantance gaskiyar lamarin ba, motar ta wuce fit, tare da tayar da yar k'aramar k'ura a saman titin.
Gabanshi ne ya tsananta faÉ—uwa, yayin da ya É—an k'ara sautin tafiyarsa, a takun da bai wuce goma ba ya isa wurin cikin matsanancin firgici da tashin hankalin ganin wanda ke kwance.
"Tareeq!!!"
Muryar Khalid cikin kakkausan amo ta furta, ya duk'a tare da birkito shi daga ruf da cikin da yake, idanunshi É—aure da wani kyalle mai tambarin Gucci, wanda ya fi kama da _muffler_. A gigice Khalid ya shiga warware daurin, cikin kidimewa ya rataya kyallen a wuyanshi, ya kwance na bakin sannan ya dago shi da zumar wucewa da shi zuwa gida.
Ihu ya saki ganin jini daskare jikin farin dogon wandon da ke jikinshi, hakan ya jawo hankalin Mal. Idi da ke tsaye k'ofar gida, kasancewar ba wata tazara mai nisa tsakaninsu.
"Ya mutu."
A cewar Khalid lokacin da ya saki Tareeq ya zauna daɓas, zuciyarsa tana wani irin bugu fat-fat, tamkar zata fasa kirjinshi ta fito.
"Lahaula wala quwwata. Me ke faruwa haka? Me samu Tareeq É—in?"
Mal. Idi da ya iso a sikwane ya tambaya yana tattaba hannun Tareeq wanda bai san duniyar da yake ciki ba.
"Daure ka kama shi a kai shi asibiti Haladu, dubi halin da yaron nan ke ciki, da alama dogon suma ce yayi."
"Ya mutu Mal. Idi."
Khalid ya faÉ—a a lokaci guda yana mai tallabar kanshi da ya fara sarawa da duk hannuwansa biyu.
"Bai mutu ba. Da alama wani gagarumin abin ne ya same shi. Kama shi mu je."
Dak'yar Khalid ya mik'e, ya saɓi Tareeq a kafada, suka iso k'ofar gida. Ya mik'a shi ga Mal. Idi yana fad'in
"Kama shi in fito da mota Mal. Idi."
Babu gardama ya kama shi, ya shiga ya fito da motarshi a kiÉ—ime, dan kwata-kwata natsuwarshi bata tare da shi, har ya ma manta da batun Hajja Fati mahaifiyar Tareeq, wacce da alama bata damu da rashin dawowartasa da wuri ba.
Mal. Idi ya shige baya yana rungume da Tareeq, yayin da Khalid ya tada motar suka É—au hanya. Asibiti mafi kusa suka je, cikin gaggawa Khalid ya É—auke shi zuwa ciki. Wata nurse ce ta iso da sauri, tana nuna masu wata k'ofa da ke hannun hagu, inda aka rubuta Emergency Room, Khalid ya shige, ya shimfiÉ—ar da shi a saman gado. Birkito shi nurse É—in tayi, a take ta fahimci halin da Tareeq ke ciki, hakan yasa ta fito daga cikin tent É—in da yayi mata katanga da Khalid, ta juya tana dubansa.
"Baza mu taɓa shi ba sai ka kawo police report, ko kuma ka taho da police ɗin."
"What? But why?"
"He's raped."
Daga haka ta juya ta wuce, tana mai jaddada mishi ya fita da shi idan ba zai yi É—aya daga abinda ta umarce shi ba.
Dukewa Khalid yayi, ya tallabi kanshi da hannuwansa biyu, wasu zafafan hawaye ya ji sun silalo ta gefen idonshi, tunawar da yayi da rayuwar Tareeq na gilgilwa ya sanya shi share hawayen, ya fito da sauri ya wuce police station.
A hargitse ya shiga, ya bada jawabin abinda ke tafe da shi. Bayan 'yan cike-cike, da rubuce-rubucen jawabi, suka taho da 'yan sanda biyu, suka koma zuwa asibitin, sai kuma a lokacin Khalid ya fara k'ok'arin kiran mutanen gidan domin shaida musu halin da ake ciki.
****
Wayar Mukhtar da ke jone jikin chaji ne tayi É—an k'aramin k'ara, alamar shigowar sako, yayi saurin mik'a hannu ya É—auka yana dubawa, hakan ya sanya shi sakin É—an gajeran murmushi, tare fara rubuta ansa ya mayar ma sak'on.
Cikin minti É—aya ta k'ara beeping, ya karanta yana mai faÉ—aÉ—a murmushinsa, sannan ya ajje wayar, fuskarsa na bayyanar da farin cikin da ke mamaye da zuciyarsa.
Bugun da ya juyo daga k'ofar É—akinsu ne ya sanya shi mikewa, ya isa ya buÉ—e yana duban mahaifiyartashi da fuska a É—aure, tamkar ba shi ya gama murmushi yanzu ba.
"Kaji wai Tareeq aka kai asibiti yanzun nan Khalid ya kira yana faÉ—a mun."
"Asibiti kuma? Me same shi to?"
"Ban sani ba wallahi. Tun É—azu da na aike shi kiranka ina jin bai dawo ba, fito muje dai muji, sunan asibitin kawai ya faÉ—a mun, daga haka ya kashe wayarshi, na kira na kira bai É—auka ba."
"God! Me faru da shi haka?"
Mukhee yayi maganar yana mai zira takalmansa, fuskarshi na bayyanar da damuwa k'arara.
Cikin 'yan mintoci suka isa asibitin, inda suka samu Mal. Idi da Khalid wanda ya kasa zaune, ya kuma kasa tsaye, illa kaiwa da komowa da yake ta yi a gaban É—akin da aka shiga da Tareeq, bayan an gama gabatar da hujjoji a gaban polisawan da suka zo tare.
Hotunan Tareeq suka É—auka a yanayin da yake ciki, sannan kayan jikinshi da aka cire, aka saka su a leda mai haske aka mik'a musu, haka kuma suka shiga suka É—auki hotunan raunukan da ya samu, sannan aka fara aikin ceton rayuwarshi.
Duk iya tambayar da Hajja Fati tayi dan son sanin me ke faruwa Khalid bai ko kalle ta ba, Mal. Idi ne ma ya kora mata jawabin a halin da suka samu Tareeq ɗin, hakan yasa taji gaba ɗaya jijiyoyin jikinta sun ɗaure, yayin da jinin da ke gudanyawa a cikin jikinta ya dakata na wucin gadi. Daɓas, ta zauna a ɗaya daga kujerun da ke girke, hakan ya ba Khalid damar cigaba da watsa mata hararar da yake yi, yana jin a duniya babu halittar da ya tsana irinta.
Cikin matsanancin fushi Doc É—in da ya anshi Tareeq ya fito, a hanzarce Khalid ya isa gabanshi, yana tambayar yanayin mai jikin. Mukhee wanda tun labarin da Mal. Idi ya bayar kirjinsa ke dukan tara-tara, ya daure ya taka inda su Khalid ke tsaye, yana sauraren su.
"Doc ya jikin nasa?"
Shiru Doc yayi, amma fuskarsa ta kasa É“oye fushin da zuciyarsa ke ciki, a lokaci guda ya mika file É—in hannunshi ma nurse É—in da ke biye da shi, ya cire farin glasses É—in idonshi, ya É—an fara takawa, sannan ya fara magana.
"Alhamdulillah, an fitar da shi zuwa dakin Hutu."
Har suka shiga ofishin likitan, suka zauna, amma bai kara cewa komai ba, haka zalika alhinin da ke kan fuskarsa, ya k'ara bayyana k'arara, hakan ya k'ara taimakawa wurin dagula lissafin Khalid wanda ya zauna jiki babu k'wari a É—aya daga kujerun da ke girke gaban teburin likitan.
"What's wrong with him please?"
A hankali Doc ya sauke hannunsa daga kan haɓarsa da ya tallaba, ya ɗago a tsanake yana duban Khalid.
"He's raped. Kuma alamu sun nuna ba mutum É—aya ba ne yayi amfani da shi."
"WHAT? Rape? Damn't!"
Mukhee da ke tsaya ya faÉ—a tun k'arfi, yana girgiza kai, yayin da Khalid ya dafe kanshi, yana ambaton kamar
"La ila ha illallahu, wahdahu la shari kala, lahul mulk wa lahul hamd, wa huwa ala kulli shai'in qadir."
Duk da kasancewar ya san damuwar ta Tareeq, amma jin ba ma mutum É—aya bane yayi amfani da shi, ya k'ara jefa zuciyarsa cikin ruÉ—ani.
Hajja Fati wacce ke tsaye bakin k'ofa tana saurarensu, ta silale ta zauna daɓas, bugun kirjinta na daɗa karuwa, tana son tuna a wacce duniyar ta ke ciki.
"Me hakan ke nufi?"
Ta tambayi kanta, zuciyarta na harbawa, cikin gaggawa.
"He will be fine in sha Allah, and mun yi duk wasu gwaje-gwaje, luckily enough baya auke da ko É—aya daga STDs (Sexual Transmitted Diseases), illa ciwuka da ya samu wanda muka riga muka É—auki hotunansu, kafin mu fara aiki, yanzu haka suna hannun police."
"Thank you, thank you Doc. Nagode sosai."
Khalid ya mik'e yana bashi hannu, amma da alama zuciyarsa bata tare da shi, idanunsa sun kaÉ—a sunyi wani irin ja, mai ban tsoro.
"Ina mamakin duniyar da muke ciki."
Likitan wanda ya mik'a hannunshi ma Khalid ya faÉ—a, fuskarsa babu walwala, sannan ya cigaba.
"Cikin wannan watan, mun samu irin case É—in nan ya kai guda shidda. I don't even know who to blame. Yaran ne ko kuma iyayensu? But don't worry, in sha Allah, Allah zai tona asirin waÉ—anda suka yi mugun aikin nan."
Jinjina kai Khalid kawai yayi, shi kadai ya san kudirin da ke ranshi, kamar yadda yake jin babu wanda ya kai shi jin bakin cikin da yake ji a k'asar zuciyarsa.
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
December, 2016
{05}
Inspector Khamis wanda ya kasance mai duty a ranar da al'amarin ya afku, ya kai duba ga Khalid da ke zaune gabanshi yana tambayar
"Menene alak'arka da yaron?"
"D'an yayana ne."
Ya bashi ansa. A karo guda ya k'ara tambayar
"Ko zaka iya sanar da mu abinda ya faru, da kuma yanayin da ka ganshi kafin ka kawo shi asibiti?"
Babu gardama Khalid ya zayyana mishi komai, tun daga fitar Tareeq, har izuwa lokacin da ya same shi kwance a gefen titi, yayin da d'ayan d'an sandan da ke gefe yake rubutawa ko wane jawabi na Khalid a tsanake, sannan ya d'ago yana fad'in
"Zamu neme ka zuwa wani lokaci."
Ya mik'e ya shige ofishin likitan, inda ya k'ara jin jawabai daga bakinshi nan ma. Ya kuma tambayar ainahin yadda suka ga yanayin na Tareeq, da raunukan da suka samu a jikinshi.
"As you can see, ba mutum d'aya ba ne yayi wannan aika-aikar Officer, a binciken da nayi, semen din mutum biyu na gani a jikinshi. Komai dai gashi nan a rubuce, zaku iya amfani da wannan."
Ya mik'a mishi file mai d'auke da fararen takardu. Yasa hannu ya ansa ya dan duba sama-sama, kafin yayi mishi godiya ya fita, a cewarsa, zasu dawo zuwa safe, domin jin ta bakin Tareeq.
A ranar yadda Khalid ya ga rana, haka ya ga wannan bak'in dare mai cike da abubuwan al'ajabi da tashin hankali. Hajja Fati kam ta rasa menene abin yi, bata iya k'wak'k'waran motsi, hankalinta ya gama tashi a yanayin da ta ga Tareeq d'in, yayin da a k'asar zuciyarta take jin wani abu mai kama da na sanin rashin tsayawa ta kula da rayuwar yaranta. Sai dai abinda bata sani ba shine, abin kukan na gaba.
Layin Alh. Badaru ta sake kira wanda yake a kashe tun zuwansu asibitin, har kuma a yanzu bai bud'e wayar ba, hakan yasa ta saki wani kuka marar sauti, wanda ta rink'a jin hawayensa na 6ul6ulowa daga k'asar zuciyarta.
*****
Razanannen k'aran da Tareeq ya farka da, shi yayi sanadiyyar jan hankalin Khalid da ke alwala a bandakin da ke cikin d'akin. Da gudu ya fito, ya ganshi dafe da idanunsa, jikinsa na kyarma, kadan ya rage ya fad'o daga saman gadon da yake kwance.
"Subhanallahi. Tareeq, me kake yi haka?"
Ya kama shi yana shirin kwantar da shi, a take abubuwan da suka faru suka shiga dawowa a zuciyar Tareeq, hakan yasa ya shiga kwace jikinsa, yana fad'in
"Dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ba zan k'ara ba."
Idanunsa a kulle gam-gam, fuskarsa na bayyanar da asalin tsoron da zuciyarsa ke ciki.
"Nine Tareeq. Bud'e idonka ka ga, Uncle Khalid ne."
Amma ina, hankalin Tareeq baya tare da shi, ihu yake yana zillewa, a cikin duhun idanunsa yana ganin tamkar abinda ya faru da shi ne zai kuma faruwa, har sai da Khalid yasa hannu ya rungume shi a jikinshi, yana shafa sumar kanshi a hankali yana fad'in
"You're safe my boy, it's your Uncle."
Sautin kukan da suka ji a gefensu ne yasa Khalid kai dubanshi wurin, Mukhee ya gani ya durkushe yana wani irin kukan bakin ciki, daga bisani ya share hawayensa, ya mik'e fuskarsa a murtuke ya ciro wayarsa ya danna wata number, sannan ya fita.
Fitarshi ke da wuya, Hajja Fati ta shigo, ko kallonta Khalid bai yi ba, ya kwantar da Tareeq, ya fita domin kiran likita. Mukhee da ke waya, yana ganin fitowar Khalid, yayi gaggawar datse wayar, ya jefa ta aljihu, ya juya yana ciccika fuska. Cikin rashin fahimta Khalid ya dube shi, daga bisani ya girgiza kai, sannan ya wuce zuwa ofishin likitan.
Ko da likita ya zo babu yadda bai yi da Tareeq kan yayi magana ba, amma ya kasa. Har kuma a yanzu idanunsa a kulle suke, ya kasa bude su, balle ma ya gane mutanen da ke tsaye gabansa.
Da hannu likitan yayi ma Hajja Fati alamar ta isa ga Tareeq ta lallashe shi, a tunaninshi hakan zai taimaka wurin samun natsuwarshi, har ma a samu ya fad'i abinda ake son ya fad'a. Sai dai bai sani ba babu wannan shakuwar ta d'a da mahaifi, a tsakanin Hajja Fati da dukkan yaranta.
Wani tattausan hannu ya ji, ya kama nashi hannun, a karo guda ta rungume shi zuwa kirjinta, hakan yasa ya fahimci ba kowa bace, bayan mahaifiyarsa. A tsawon shekarunsa, ba zai iya tuna sadda jikinshi ya had'u da nata ba, ba zai iya tuna lokacin da ya samu natsuwa daga mahaifiyartashi ba. Shiru yayi, yana mai sauke ajiyar zuciya, har kuma yanzu bai bud'e idanunnashi ba.
"Bud'e idonka kaga."
Likitan ya fad'a tare da zama a gefenshi, 'yan sandan da suka shigo, suma suka samu gefe suka tsaya, sai kuma Mukhee da ke raku6e can a bakin k'ofar fita.
Kai ya girgiza, alamar ba zai bud'e ba. Likitan ya kama hannunsa da murmushi a kan fuskarsa, duk da cewar Tareeq d'in ba kallonsa yake ba.
"Kana jin ciwo a wani wuri ne?"
Hakan bai sa Tareeq yayi magana ba, har sai da likitan ya dora hannunsa a gefen fuskarsa, sannu a hankali ya fara shafa saman idonsa, a karo guda Tareeq ya saki k'ara, wanda ya sanya likitan sauke hannunsa cikin gaggawa. Kuka Tareeq ya dinga yi yana sauke ajiyar zuciya, haka kuma babu tambaya daya da ya ansa daga duk wasu tambayoyi da likitan ya masa, har ma da wanda 'yan sanda da suka shigo suka mishi su ma.
Ganin wankin hula na shirin kai su dare, yasa duk suka fito, da zumar zasu dawo zuwa wani lokacin.
"Su kuma 'yan sandan can me zasu dawo yi?"
Hajja Fati tayi maganar tana kallon Khalid fuskarta babu walwala.
Kamar ba zai ansa ta ba, sai kuma ya daure yace
"Suna son su samu hujjojin da zasu had'a su tura kotu ne."
"Ko me?"
Idanunta a zazzare ta tambaya tana kallonshi.
"Kotu mana. Ko kina zaton wanda yayi aikin nan zai tafi a bati?"
"Baka isa ba Khalid. Kamar yadda suma basu isa su kara tako da k'afarsu cikin d'akin nan ba. Mu zaka tona ma asiri? Wallahi baza ta sa6u ba. Haba, wannan abun kunyar har ina? To wai da sa hannun waye zasu kai maganar kotu ma?"
Ta wuce da gaggawa tana k'ara kiran Alh. Badaru, cikin rashin sa'a har zuwa yanzu wayar tashi a rufe take ruf, bata 6ata lokaci ba ta fara tura mishi sakon da ta san matsawar ya ci karo da shi, hankalinsa ko yayi dubu dole ya tashi, haka kuma dole ya bar duk abinda ya ke, ya shigo Kaduna a yau din nan. Ta
koma ta fara kaiwa da kawowa a k'ofar d'akin, domin baza ta ta6a yarda da wannan mugun abun kunyar ba. Taje kotu tace an yi ma d'anta fyade? Ita kuma tana ina a lokacin?
"Kai ba fa zata sa6u ba."
Tayi maganar a bayyane, sannan ta wuce cikin d'akin.
A d'age ta shigo tana kallonsa, hakan yasa shima ya bi ta da kallon da ya fi yanayi da na wulakanci, har ta isa ta zauna a doguwar kujera mai cin mutum uku, wacce Mukhee ke zaune, kanshi a k'asa ya had'a hannayensa ya tallabi ha6arsa, da alama bai san wainar da ake toyawa ba saboda tsabar nisa da yayi cikin tunani.
"Tareeq dai ni na haifi abuna, dan haka ina mai baka shawarar ka gaggauta tattara ya naka ya naka ka bar mun d'ana, dan wallahi baka isa ka tona mana asiri a bainar jama'a ba Khalid. Shin wai aje kotu ace me? Ace mun kasa tsayawa mu kula da shi har ta kai ga an mishi fyade? Ai wannan babban abun kunya ne, daga nan kowa zai rink'a yi ma yarona gani-gani. To wallahi bazan dauki wannan cin kashin ba. Bari Alhajin ya zo."
Duban da yake mata yanzu, duba ne irin wanda aka fi yi ma mahaukatan da haukansu bai kankama ba, sa'annan ya maida hankalinsa ga kofin shayin da ya gama ba Tareeq da ke hannunsa. Ya ajje saman d'an teburin da ke gefensu, sannan ya juya yana mai k'ara fuskantarta. Kamar zai yi magana, sai kuma ya tuna da koma meye zai fito bakinsa, ba lallai ya zamana mai dadi ba, haka zalika ba zai juri gaya mata magana a gaban yaranta ba.
Misalin sha d'aya saura na dare Alhaji Badaru ya fito daga tangamemen d'akin taron da suka gama gudanar da muhimmun taron jam'iyyarsu ta ADP. Hularsa ya cire, tare da gyara zaman babbar rigarsa, a sa'a guda yana mai k'ok'arin fito da wayarsa da ke cikin aljihu, wacce ya manta rabon da ya kunna ta, saboda tsabar shagaltuwa da yayi ga abubuwan da suka fiye mishi komai muhimmanci.
Bayan ya ansa wayar wata bak'uwar number da ta shigo, ya kashe yana 'yar dariya, kasancewar ya gane mai kiran, a karo guda sakon Hajja Fati ya shigo, da mamaki yake kallon sakon, domin ba al'adarta bace tura sako, a zahirance ma, ba zai iya tuna rabon da suyi musayar sakonni ba, in ko har zai tuna, to baya wuce kafin suyi aure, lokacin suna saurayi da budurwa.
Da haka ya bud'e sakon, har sai da zufa ta yayyafo masa bayan ya gama karantawa. Kugunsa ya kama da hannu d'aya, yana firfita fuskarsa da hular da ke d'ayan hannunsa, ya kalli agogon wayarsa, karfe sha d'aya har ta buga da 'yan mintuna, ya kuma tuna da taron da suke da shi a gobe karfe goma na safe, a lokaci guda ya k'ara kallon sakon Hajja Fati, bai jira komai ba ya yanke shawarar shiga mota ya tada, a lokaci guda ya d'auki hanyar Kaduna, a cewarsa, zai yi k'ok'arin dawowa a gobe kafin lokacin taronnasu.
www.wattpad.com/iLubieee
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
December, 2016
{07}
Wasa-wasa sai da 'yan sanda suka jera kwana ukku suna zarya asibitin, duk da artabun da suke sha da Hajja Fati, kan baza suyi magana da yaronta ba, hakan bai sa sun dakata da zuwa a kowacce rana ba, har kuma inda yau take, babu Alhaji, babu labarinsa, muhimman tarurrukansa, sun sha masa kai fiye da tunanin mai tunani.
Babban abinda ke É—aga hankalin 'yan sandan, bai wuce yadda zasu É“ata lokaci suna jera tambayoyi ma Tareeq ba, amma cikin ikon Allah, ya kasa fuskantarsu, balle su saka ran samun ko da k'alilan ne daga ansar tambayoyinnasu.
Yau ma kamar kullun suka shigo É—akin da sallama, cikin sa'a babu kowa sai Khalid da ke shingiÉ—e yana duba wata _fashion magazine_ da ma'aikatan asibitin su kan ajje a É—akunan majinyatan, Inspector Khamis tare da abokin aikinsa mai suna Sergeant Buba suka isa tare da mik'a hannu ma Khalid. Bayan 'yar gajeruwar gaisuwa, suka nemi wuri suka zauna a gefensa, daga bisani Khamis ya mike da murmushi, ya isa ga Tareeq, yana mai dubansa cikin tausayawa, kasancewar har zuwa wannan lokacin, hankalin yaron baya tare da shi, hakan ya kara k'aimi ainun, a zuciyar Khamis, na son samun wani k'wak'k'waran abu, wanda zasu iya aika shi ga ministry of justice.
Yayin da ta É“angaren Tareeq, ganin kallon da Khamis ke masa, ya sanya shi gaggawar runtse ido, ko alama baya son ganin mutanen nan, uwa uba, baya k'aunar tambayoyin da suke tsare shi da su, domin kuwa basa k'arinsa da komai, face fami da suke yi ma zuciyarsa, na abubuwan da suka faru da shi.
Zama Khamis yayi, yana mai faÉ—aÉ—a murmushinsa, domin a cewarsa yau duk yadda za ayi, sai Tareeq É—in ya sanar mishi ko da kaÉ—an ne daga abinda ya wakana a ranar da aka kawo shi asibiti.
Hannunsa ya kama yana É—an shafawa a hankali yana faÉ—in
"Tareeq ya jikinnaka?"
Ido ya zura masa yana kallonshi, sannu a hankali ya fara zare hannunsa daga nashi, daga bisani ya juya masa baya.
"Haba abokina. Wai ko baka son abotar da ni ne? Kullun fa sai na zo, amma ko kallona baka yi. Haba Tareeq. Kalli nan kaga"
Khamis ya faɗa lokacin da ya zagaya gabanshi ta ɗayan ɓangaren da ya mayar da kansa, yayi maganar da laɓɓaansa k'unshe da murmushi, yana mai ɗaga farar ledar Mr. Biggs, mai ɗauke da burger da shawarma, waɗanda Khalid ya shaida masa sun kasance ababen so a wurin Tareeq ɗin.
Shiru yayi yana dubansa, sai dai tsananin tsoron da ke cikin zuciyarsa, ba zai taɓa bari ya sanar da su abinda suke son sani ba.
Ya runtse ido yana son kaucewa tunanin da ke kawo farmaki a zuciyarsa, inda ya tsinkayi muryar Khamis da ke mik'a masa shawarma yana faÉ—in
"Zaka iya tuna abinda ya faru ranar laraba bayan kun dawo daga makaranta?"
A take hotunan abubuwan da suka wakana a ranar suka dinga sintiri cikin k'wanyarsa, a lokaci guda ya saki wani irin kuka, wanda sautinsa baya fita sosai, yana jin tamkar tashi ta kare a wannan duniyar. Tsananin tausayinsa ne ya kai ziyara a zuciyar Khamis, ya tabbata haka duk wani bil adama da ya tsinci kansa a yanayin da Tareeq ke ciki yake ji, haka yaran da aka yi wa fyaÉ—e suke ji, waÉ—anda basu ji ba, ba su gani ba, haka ake dasa bakin ciki, tsoro, da firgici a kasar zukatansu, wasu daga nan shikenan sai su koma wasu mutane na daban, sanadiyyar É—aukewar walwalarsu, yayin da wasu kuma hakanne ke yin sanadin buÉ—e hanyar lalacewarsu. 'Me zai sa ba zai taimaki mutane irin Tareeq masu bukatar taimako ba? Me sa iyayensa ke son É“oye wannan mummunan al'amarin da yake barazana da hankali da tunanin yaronsu? Dole su samu hanyar da Tareeq zai yi magana, ko dan ayi komai a gama cikin kankanin lokaci.'
Surutan da ya rinka yi a kasar zuciyarsa kenan, daga bisani ya kama hannunsa, yana mai bubbuga bayansa cikin sigar lallashi ya fara magana.
"Kada ka ji tsoro Tareeq, babu wanda zai k'ara yi maka abinda aka yi maka, ni zan tsaya maka, ga Uncle Khalid, shima zai tsaya maka. Zamu kama duk wanda yayi wannan abun, zan kaishi gaban alkali ya bi maka hakkinka. A yanzu taimako É—aya zaka mana, ka faÉ—a mana ko da kaÉ—an ne daga abinda ka sani. Ka ji?"
Wannan bai sa Tareeq ya tsagaita da kukansa ba, haka Khamis ya cigaba da magana cike da lallashi, Amma sai ya zamana tamkar yana ingiza zuciyar Tareeq É—in ne, a k'arshe suka fito jiki babu k'wari, zuciyarsa babu daÉ—i, yana jin tamkar babu nasara a abunnasu.
Hak'uri dai Khalid ya k'ara basu, yana mai jaddada masa zai cigaba da bashi tasa gudunmawar har zuwa yadda hali yayi. Suka masa sallama, suka kama gabansu.
A gaba ɗaya wunin ranar al'amarin Tareeq jagulewa yayi, ga shi dai a zuciyarsa yana son sanar da 'yan sandar amsar tambayoyinsu, sai dai idan ya tuna azabar da ya sha a hannun mutanen da suka keta haddinsa, sai ya kasa, ya ji tamkar zasu ruɓanya masa ne a wacce suka mishi a baya. Haka Khalid yayi ta faman lallashi, haka kuma Tareeq ɗin ya k'i yarda ko nan da can ya matsa, ya kama hannunsa ya mak'ale yana sauke ajiyar zuciya.
Har dare haka suka wuni, sai wurin sha É—aya sannan bacci ya sace shi, a gefenshi Khalid ya shingiÉ—a, shima bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi.
"Ku yi hak'uri. Ba zan k'ara ba. Kuyi hak'uri dan Allah."
Muryar Tareeq cikin tsananin kuka yake magana yana jujjuya kansa, ko ina a jikinsa mazari yake yi, ya kama hannun Khalid karkadam ya rik'e, baya da niyyar sakinsa.
A hankali ya farka yana dubansa, baiyi wata ba ya zare wayarsa ya danna _recoding_ jin yana ambaton wasu kalmomi masu kama da sunayen mutane.
Ya É—auki kusan minti biyar cikin wannan hali, kafin ya saki kuka mai k'arfi, wanda ya sanya Khalid rungumesa, yana zubar da hawayen shima, ya kashe _recording_ É—in, ya jefa wayar aljihu.
******
Misalin takwas da wani abu na safiyar washe gari su Hajja Fati suka shigo ita da Zulaiha, har suka zauna amma bai ga Mukhee ba, yau kusan kwana ukku kenan rabon da k'afarsa ta taka asibitin.
Ba tare da ya tambaye su dalilin da ya hana shi zuwa ba ya mik'e, dama Allah-Allah yake su zo, domin ya samu hanyar fita zuwa ofishin 'yan sanda. A tsaitsaye suka gaisa da Hajja Fati, ya wuce tana mai binshi da kallon tuhuma, a zuciyarta bata aminta da fitartashi ba da sassafen nan, haka suka shiga suka zauna jigum, kasancewar har a lokacin Tareeq bai farka ba.
Yana fita inda yayi parking motarsa ya isa, tunda suka zo asibitin yau ce rana ta farko da zai fita, kayan sawarsa ma a boot É—in motar suke, dama tunda yaje gidan bai fitar da su ba. Ya shiga ya É—auki hanya, zuciyarsa na azalzalarsa, yana rokon Allah yasa k'arshen wahalarsu kenan.
A dai-dai junction ya ga mai siyar da kati, ya mik'a masa dubu É—aya ya bashi, kafin a basu hannu su wuce, ba tare da ya duba kujerar da ke gefensa ba ya ajje katin, da canjin da aka bashi, a karo guda aka basu hannu, ya fisgi motar, cikin 'yan dakiku ya iso ofishin yan sandan.
Cikin rashin sa'a Inspector Khamis bai kai ga isowa ba, hakan yasa ya koma cikin motar da zumar É—aukar katin da ya siya ya loda, domin ya kira shi a waya.
Cak idanunsa suka tsaya kan _muffler_ dake ajje a kujerar gefenshi, yana kallonta yana son tuna inda ya same ta.
"Oh Allah!"
Ya faÉ—a a bayyane, yana mai loda katin cikin gaggawa, ya kira Khamis wanda ya shaida masa yana gaf da station É—in.
Hamdala ya dinga yi, a cewarsa wannan _muffler_ ma wata hujja ce, matsawar aka kama mutanen da Tareeq ya dinga kira cikin baccinsa, a wani É“angaren yana tunanin tamkar ma ya taba ganin wani da _muffler_ É—aure a wuyansa. A hasashen zuciyarsa ma, a nan kusa-kusa yake tunanin wanda ya taba gani da ita.
www.wattpad.com/iLubiee
_This page goes to My Niece (Mudassara Mahmoud), Yasmeenah, Aunty Karofee and Aysha Zubayr. Thank you guys so so very much, I'm much grateful for the support, and encouragement. And I love y'all my people♡♡♡_
0 comments:
Post a Comment