Ya tambaya yana duban Khalid wanda shima tambayar da ke yawo a cikin kansa kenan.
"Shine sunan da Tareeq ya rink'a kira jiya a cikin baccinsa."
"Na ji fa. Shin baka san shi ba ne?"
Yayi maganar yana mai k'ara sauraren recording ɗin.
_"To ni me nayi muku? Dan Allah Mubee kuyi hakuri. Wallahi ba zan k'ara ba, ni gida zan je ku sake ni dan Allah. Mubee ka ce ya sauke ni. Wayyo Allah na.."_
Muryar Tareeq cikin k'araji take fita daga speaker wayar. Ya kashe, kafin ya maida hankalinsa ga Khalid.
"Duk da kasancewar wannan recording ɗin a matsayin hujja mai kwari, ina mai tabbatar maka da ba ko wanne police bane zai yi considering nashi. Ina fatan ka san da wannan?"
"Na sani Inspector, amma ina kyautata zatona a kanka, na tabbata zaka fita zakka a cikin 'yan sandar kasar nan, haka kuma wannan zai wanke ku daga zargin da jama'a ke maku kan baku san yin aikinku. Zai kuma sa mutane su dai na yi muku kuɗin goro."
Murmushi Khamis yayi, tabbas akwai ɓata garin ma'aikatan da sukan ja musu zagi daga bakin al'umma, amma ya ci alwashin a kan wannan case ɗin, zai shayar da dubban mutane mamaki, zai kuma tabbatar ma duniya cewa ba duka aka taru aka zama ɗaya ba.
"I'll try my possible best Khalid, da ikon Allah sai na gano wanda suka yi aikin nan, ba dan komai ba, sai dan ina jin Tareeq tamkar k'anena, ko kuma ince ɗan da na haifa a cikin cikina."
"Nagode, nagode, Inspector, har ban san da bakin da zanyi maka godiya ba wallahi, Allah ya k'ara ɗaukaka ka, Allah ya sa a dinga samun jami'an 'yan sanda da zasu yi koyi da halayenka."
Murmushi yayi, ya kara da cewar
"Duk koma wanene wannan, to Tareeq ya san shi, tunda har kaji ya ambaci sunansa. Amma ka bari zan shiga unguwar da kaina domin gudanar da bincike."
"Allah ya taimaka. Uhnmm, na manta, ga wannan."
Ya mik'a masa muffler da ya ɗauko daga motarsa, ya ansa yana dubawa, kafin yace
"Wannan fa?"
"Abinda na samu ɗaure da idanunsa kenan, naga yayi kama da abin amfani, ina ji a zuciyata, tamkar na taɓa ganin wani da shi ma."
"Amma me sa baka gabatar da shi ba tun farkon zuwanmu asibiti?"
"Na manta da shi ne kwata-kwata, sai yanzu da na zo nan ne na ganshi a seat ɗin motata, kafin na tuna."
"Babu laifi, amma kayi tunanin ko kasan mamallakin abun."
Godiya yayi masa, sannan ya tura masa recording ɗin a tashi wayar, kafin ya fita da zuciyarsa duk a hargitse, yana ayyana tabbas ya taɓa jin sunan Mubee, sai dai ya kasa tuna inda ya san shi.
Hannun motarsa ya kama yana shirin buɗewa, take ya tuna wata rana da ya taɓa zuwa gidan ya ga wasu abokan Mukhee na shan sigari a gefen toilet ɗinsu da ke BQ, inda yayi musu magana kan su fita waje, har Mukhtar yayi masa rashin kunya, ya juya yana mai duban matasan yace
"Dallah Mubee ku zo mu ware."
Da sauri ya koma ciki, ya shaida ma Khamis inda ya san Mubee, sai dai bai san ina ne gidansu ba.
"Wannan ba zai yi wuya ba Khalid, ka bar komai a hannuna."
Fuskarsa sake, ya juya ya fita, amma ya kasa gaskata ko Mubeen na da hannu a abinda ake tuhumarsa.
**11:00am
A k'ofar gidan Engr. Garba Bukar mahaifin Mubee suka tsaitsaya suna jiran fitowar mai gadin da suka k'wank'wasa ma k'ofa.
"Barka da aiki Yallaɓai."
"Yawwa, Barka dai Baba."
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau. Ina fatan nan ne gidan Engr. Garba Bukar?"
"Nan ne. Amma baya gari."
"Yaronshi Mubarak ai yana ciki ko?"
"A'a, yana makaranta."
Kamar daga sama, sai ga motar Sino tayi parking, Mubee ya fito wandonsa kamar zai faɗi k'asa, ya juya ya bama sauran guys ɗin cikin motar hannu, sannan ya nufi k'ofar gidansu, da alama gudowa ya yi daga makarantar, ganin wandon uniform a jikinshi, ya cire rigar ya ɗaure a kugunsa, sai farar long sleeve t-shirt, sanye a jikinsa.
Kasancewar babu uniform a jikinsu, sai bai kawo komai a ransa ba lokacin da ya tsinkayi muryar mai gadin yana faɗin
"To ai gashi nan ma."
"Mubarak ko?"
"Eeehh ni ne."
Yayi maganar kansa tsaye, idanunsa cikin na Khamis.
I.D card ɗinsa ya ɗaga masa daga inda yake tsaye, kafin ya k'ara da cewar
"Muna buk'atar ganinka a police station, akwai tambayoyi da ya kamata ka ansa mana."
Wani irin k'ara cikinsa ya saki, a take wani nauyi ya kai ziyara ma kafafunsa, yana jin tamkar baza su iya ɗaukar gangar jikinsa ba. Tunawar da yayi a gaban wanda yake, ya sanya shi dakewa, yayi ta maza ya ɗago yana kallonsa.
"Kamar na me kenan?"
"Kar ka damu, idan mun je zaka ji komai."
Ya juya gabas, ya juya yamma, inda yaga babu wani mahaluki da zai taimake sa, mai gadin da ke tsaye ma ya riga ya koma bakin aikinsa. Sumar kanshi ya shafa yana faɗin,
"Barin shiga in sanar da mutanen gidan ko?"
"Kar ka damu, ba wani lokaci mai tsawo zaka ɗauka a can ba. Shiga muje."
Khamis yayi maganar yana nuni masa da motar da Sergeant Buba ya buɗe bayan, yana rik'e da murfinta.
Cikin tashin hankalin da baya son fuskarsa ta nuna, ya shiga motar, kirjinsa na bugawa cikin sauri, sai dai yana da tabbacin babu yadda za ayi asirinsu ya fallasu.
A ofishin 'yan sanda suka tsaya, Khamis ya fito Mubee na biye da shi, yayin da Sergeant Buba ke rufa masu baya har zuwa inda aka tanada domin tuhumar masu laifi irinsa.
Kujera Khamis ya nuna masa ya zauna, shima ya zauna yana fuskantarsa, tare da aika masa duba na tsanaki, mai tattare da tuhuma da son gane ainahin wanene shi duk a lokaci guda. Wannan yana ɗaya daga aikin 'yan sanda, a duk lokacin da suka ci karo da mai laifi, sai sun gama karantarsa, kafin su san hanyar da zasu iya jifarsa da tambayar da watak'ila zata yi sanadiyyar tona asirinsa.
"Wanene Tareeq?"
Duuuum! Gaban Mubee da ke harbawa ya k'ara bugawa tun k'arfi, fuskarsa ta bayyanar da alhinin zuciyarsa, amma ya dake, yana duban Khamis da idanunsa da suka fara komawa jajaye saboda shaye-shaye.
"Wane Tareeq fa?"
"C'mon. Yaro da ke kwance a asibiti mana."
"Owh, Tareeq?"
Ya faɗa yana shafa k'eyarsa. Khamis ya murmusa yana k'ura masa ido.
"K'anin abokina ne."
Sai kuma yayi shiru.
"Ehhn. Ina saurarenka. Mai yayi haɗinka da shi a ranar laraba ashirin da biyar ga watan December?"
"Ni kuma?"
Ya faɗa yana zara idanunsa waje.
"Kai mana Mubee."
"Ni wallahi babu abinda ya haɗa mu. Kawai dai na san mun je gidansu ranar muna zaune a ɗakinsu ya shigo yayi mana wurgi da shisha pot."
"Shi yasa kuka keta haddinsa a daren ranar kenan ko?"
Khamis ya jefe shi da tambayar kai tsaye, idanunsa a kansa yana son gane gaskiyar maganar da yayi.
"Ban gane ba? Ni ban san abinda kake magana a kai ba."
Murmushi ya saki, yana k'ara dubansa,
"Kai da waye kuka je gidannasu a ranar?"
"Friends ɗina."
"Su wa kenan?"
"Deeni, da Sino, sai yayanshi abokinmu."
"Da misalin karfe nawa kuka je gidan? And wurin karfe nawa kuka baro gidan?"
Yayi shiru yana nazarin abin cewa, ya nisa yace
"Wurin biyar na yamma muka je, muka fito misalin shidda da rabi."
Ya ɗago daga rubutun da yake yana k'ara tambayar
"Tun daga lokacin kuna tare da abokan naka har zuwa karfe nawa?"
Shiru yayi, yana tunanin karyar da zaiyi, har sai da Khamis yace
"Ko sai na maimaita maka tambayar ne?"
"Daga nan muka rabu na wuce gida, kuma ban k'ara fita ba."
"Kana nufin a daren ranar baka fita ko ina ba kana cikin gidanku har sai da gari ya waye?."
Yayi shiru yana juyar da kansa, hankalinsa ya gama mikewa, yayin da zuciyarsa ke cikin hali na ruɗanin da bai san yadda zai fassara shi ba.
Hannu Khamis yasa ya k'wank'wasa teburin da ke tsakaninsu yana lek'en fuskarsa.
"Kai nike saurare."
"Ina gida fa. Ko friends ɗina zaka tambaya ban fita a daren ranar ba."
"Kada ka bamu wahala Mubee, kai ma kuma ka ba kanka, ka sanar da ni gaskiya, hakan ne zai sa in taimaka maka."
"Gaskiyar ce na faɗa maka ai."
Ya faɗa yana cika fuskarsa, a zuciyarsa yana tunanin babu yadda za'ai Khamis ya gane gaskiyar da yake son ganewa.
"'Yan gidanku kowa da kowa ya san kana gida daga karfe shidda da rabi (06:30pm) har zuwa safe baka k'ara fita ba?"
Ba tare da yayi tunanin komai ba ya ansa da "Eh," a cewar zuciyarsa, ya tabbatar iyayensa zasu rufa mai asiri.
"Ba ni number mahaifinka."
"Ai shi baya k'asar ma, sai dai ta Mamana."
"Kawo ta Maman."
Babu gardama ya karanta ma Khamis, yana rubutawa a wayarsa, kafin ya mik'e, ya fara kira.
Bayani ya shiga yi ma mahaifiyartashi bayan ta ɗauka, kafin ya shaida mata cewar ana buk'atar mutanen gidan su zo domin suyi shaidarshi.
"Shaidar mi kuma?"
Ta tambaya hankalinta a tashe, sai dai bai sanar da ita komai ba, ya kashe wayar yana mai jaddadada mata da su iso cikin gaggawa.
Ya dawo ya zauna gabanshi,
"Yanzu ina abokannaka suke?"
"Ehhh..? Ban san inda suke ba."
"Amma ai kana da number su ko?"
"Eh ina da akwai."
"Bani numbers ɗinsu dukansu."
Daga haka ya bashi layinka su Sino, Deeni, har ma da Mukhee, kafin ya k'ara buk'atar ya gaya masa gaskiya ba sai ya ba kanshi wahala ba, amma haka ya murje ido, yace shi fa iyakar gaskiyarsa kenan.
Idanunsa da ke kansa ya sauke ya maida dubansa ga sergeant Buba da ya k'ame wuri guda, yace
"Ku ansa wayarsa, da duk wani abu da ke jikinsa, ku shiga da shi ciki."
Ya juya ya fara tafiya, Mubee yayi gaggawar kama rigarsa,
"Ban gane su shiga da ni ciki ba, wallahi iyakar gaskiyata kenan. Kai fa kace ba daɗewa zan yi a nan ba. Haba Officer."
"Kar ka damu, idan masu shaidarka sun zo, zasu bayyanar da gaskiyar da kake da. Daga nan sai ka wuce gida."
Bai k'ara bi ta kansu ba, ya juya ya fice.
Cikin cell aka tura Mubee, yana ganin abun kamar da wasa, yayin da zuciyarsa ke raya masa babu fa inda maganar zata je, sai dai idan ya tuno da Deeni, ya kan ji faɗuwar gabansa ta tsananta, dan ya san ba k'aramin matsoraci ne ba, ya tabbatar kuma dole ne Khamis ya bukaci ganawa da su.
Tuna yadda al'amarin ya faru yake yi, ya tabbatar babu wanda ya gansu a lokacin, hakan ya bashi tabbacin babu inda hargagin Khamis zai je, ko ba komai ma ai iyayensu na da kuɗi, baza su taɓa bari wani abu ya faru da su ba.
'Aikin banza.'
Ya faɗa a k'asar zuciyarsa, sa'adda ya sa hannu ya daki dogayen k'arfunan da ke mak'ale da k'ofar cell din.
****
Cikin mintunan da basu haura talatin ba Hajiya Karima mahaifiyar Mubee da yaranta mata guda ukku suka iso, ba tare da ɓata lokaci ba, Khamis ya gabatar da buk'atarsa gare su.
Shiru suka yi bayan jin tambayar Khamis, tabbas a ranar sai misalin sha biyu na dare ma Mubee ya dawo gida, har Hajiyar na masa faɗa kan yawan kai dare a waje, amma bata da yadda zata yi, dole ta san abin cewa ko dan ta ceci yaronta, namiji ɗaya tilo a cikin 'ya'yanta, daga hannun masherantan mutanen nan.
Ta kalli Khamis a ɗiririce, kafin tace
"Mubarak a gida yayi sallar maghriba, kuma bai sake fita ba, sai washe gari."
Hasina yayarsa da ke gefe tace
"Tare da shi ma muka kalli wani series da muke kallo a Novella E1, bai shiga ɗaki ba ma sai wurin karfe sha ɗaya."
Haka sauran 'yan uwansa suka goya ma mahaifiyarsu baya, a zatonsu hakan zai kuɓutar da ɗan uwannasu daga gagarumin laifin da yayi.
Bayan gama rubuta jawabansu Khamis ya ɗago yana kallon yadda duk suka sha jinin jikinsu, ya tsaida dubansa ga Hajiya yana cewa
"Tare kuke da driver ba?"
Kai ta gyaɗa tana tunanin abinda zai biyo baya. Sannan yace
"Ki taimaka ya taho mun da mai gadin gidanku idan babu damuwa."
Daram, kirjinta ya buga, bai jira ansarta ba ya mik'e, ya shaida ma driver ya je ya taho da Baba mai gadi.
Bayan wasu yan dakiku suka dawo da mai gadin wanda Khamis ya bukaci ganawa da shi a gabansu.
Hankalinsa ya maida gare shi, kafin ya fara magana.
"A ranar larabar da ta gabata, ashirin da biyar ga wannan watan, Mubarak ya fita gida da misalin karfe biyar na yamma, shin Baba zaka iya tuna ko karfe nawa ya dawo gida a ranar?"
Shiru Baba yayi yana nazari, yayin da Hajiya Karima ta kafe shi da idanu, sai dai bai san wainar da take toyawa ba, ya ɗago yana duban Khamis yace
"Misalin sha biyu da wani abu na dare wata mota ta sauke shi a k'ofar gida."
'Alhamdulillah'
Khamis ya faɗa cikin ransa, ya dubi mai gadin da murmushi
"Zaka iya gane kalar motar ko kuma waɗanda ke ciki?"
"Gaskiya ba zan gane ba, domin har na fara bacci, na jiyo tsayuwar motar, sai kuma daga baya na ji yana buga k'ofar gidan."
"Babu laifi, nagode da wannan Baba."
Hajiya ta fashe da kuka tana duban Baba mai gadi,
"Ka ji tsoron Allah Hamidu, ka tuna fa tun maghriba Mubarak ya dawo gida ranar, ga 'yan uwansa nan duk muna tare a lokacin. Haba Hamidu, yanzu duk abinda Engr ke maka da wannan zaka saka mana, ka lak'a ma yaronmu sharri? Allah ya isa wallahi, domin ba zan taɓa yafe maka ba."
Hankalin Baba mai gadi ba k'aramin tashi yayi ba, shi kam iyakar gaskiyarsa ya faɗa, bai kuma san abinda hakan zai haifar ba. Hak'uri ya shiga ba Hajiya, amma ina ta inda ta shiga, ba ta nan take fita ba, dole yasa Khamis daka mata tsawar da ta sanya ta shiga taitayinta, ba tare da tayi niyya ba.
www.wattpad.com/iLubieee
Lubiee ce..
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{09}
A ranar yadda jama'ar gidan Engr Bukar suka ga rana haka suka ga dare, Baba mai gadi kam daga ofishin yan sanda Hajiya Karima tayi masa korar kare, suka isa gida cikin tashin hankalin da ya fi gaban tunani. Mai gidanta ta kira ta shaida masa komai da ke faruwa, yayin da ya dinga faɗa, ta inda ya shiga ba ta nan ya ke fita ba, domin yana sane sarai da halayyar Mubee ta bibiyar abokan banza, wanda kuma mahaifiyarsa ce ke k'ara sangartar da shi.
Duk da bai gama abinda ya je yi K'asar Italy ba, amma ya basu tabbacin cewar su tsimayi zuwansa cikin satin da zai kama.
***Washe gari.
Layin Sino Khamis ya fara kira, a bugu na ukku ya ɗaga, da muryarsa wacce ya kasa banbance mace ce, ko kuwa namiji.
Sallama ya fara yi, bayan ya ansa ya tambayi
"Hassan ne ko?"
"Eh ni ne."
"Kana ina ne Da Allah?"
"Ban gane mai magana ba ai."
"Ka san abokinka Mubee ba?"
"Na san shi mana. Lafiya?"
"Yana neman taimakonka ne ko za ka iya shedarshi a nan police headquarter."
"Ehhh? Uhnmmm! Yanzu dai matsalar ni bana gari, naje PH tare da Dad ɗina sai dai ko idan na dawo."
Yayi maganar da ɗan sauri, kafin ya katse wayar da gaggawa, ba tare da ya jira me Khamis zai k'ara faɗa ba.
K'ara kiran wayar yayi, amma ya ji ta a rufe ruf, hakan ya sanya shi laluben layin Deeni.
Tambayoyin da yayi ma Sino, su ya jera mishi, inda shima ya shaida masa cewar baya gari, ya je Zaria ganin kakanninsa.
Shiru Khamis yayi, yana nazarin manufar yaran duk biyun, zuciyarsa na tabbatar masa da wani zargi da ke kasanta, sai dai baya son ya gaskata hakan.
Wayar Mukhee ya laluba, cikin rashin sa'a ya same ta kashe, hakan ya sanya shi yin shiru yana nazarin abinda ya kamata yayi, daga k'arshe ya yanke shawarar, bari ya basu awa arba'in da takwas, matsawar babu wanda yayi yunkurin zuwa, shi zai san abinda ya kamata yayi.
***Asibiti.
Khalid da Zulaiha ne zaune a ɗakin, sa'adda Tareeq ke kwance idanunsa na fuskantar ceiling, zuciyarsa tayi baki, ya rasa abinda ke masa daɗi.
Tabbas tashi ta kare, rayuwarsa ta gama gurɓata, baya kuma tunanin idan har yana da sauran amfanin da zai iya yi ma rayuwartasa. 'Anya burinsa na zama kwarrarren lawyer zai cika kuwa a yanayin da ya samu kansa? Baya tunanin zai iya cigaba da zuwa makarantar ma, dan ya san nuna shi za'a rink'a yi ana masa dariya.'
Hawaye suka kwaroro ta gefen idanunsa, yayin da hannun Khalid da ya karaso gefensa, ya dafa kafaɗarshi, hakan yayi sanadiyyar dawo da shi daga dogon tunaninsa.
Kai ya girgiza masa, alamar ya daina kukan, cikin rashin kuzari ya saki kukan da ya ke ta faman makalewa a hankali, hakan ya sa hatta Zulaiha sai da ta ji ta tausaya masa, a zuciyarta kuma ta fara addu'ar Allah ya tona asirin waɗanda duk suka jefa kunci a zuciyar ɗan uwannata, sai dai har yanzu, tana jin haushi yadda Khalid ke zak'ewa a kowanne lamari na Tareeq, tamkar shine mahaifinsa.
Wayar Khamis da ke jone jikin chaji ne ta fara k'ara, ya juya ya kalli Tareeq da ɗan murmushi, kafin ya isa ya ɗaga wayar da sallama.
"Ba ka da kirki Jarma. Sai yau kake nemana?"
Yana ɗan murmushi yake sauraren wanda ya kira da Jarma, kafin ya ce
"Wa ke faɗa maka? Dan ko su Hajiya basu sani ba fa."
Ya koma bakin gadon Tareeq ya zauna yana rik'e da wayar a kunnensa.
"Mukhtar fa? Ina ka ganshi kai kam?"
Yayi maganar hankalinsa na ga Tareeq da ke son mik'a hannu ya ciro tissue amma ya kasa, dole ya sanya hands free, ya ajje wayar ya mik'e ya ciro masa tissue ɗin, yayin da ta ɗayan ɓangaren aka cigaba.
"Yana nan tudun wada ai, yau three days kenan."
"You must be kidding. Mukhee a tudun wada har da kwana? Me ya je yi ne?"
"Ni kaina sai da nayi mamaki, but then, he told me Tareeq aka kwantar a asibiti, kuma gidan ba kowa."
Jinjina kai Khalid yayi,
"Haka ne kam, shaa, thanks buddy, ka gaishe mun da Hajiyata. Sai munyi magana ba?"
"Yh, sure. Ka duba mai jikin."
Daga nan suka datse wayar, sai dai zuciyar Khalid ta yi nisa zuwa wani tunanin na daban. (Jarma cousin ɗin su Khalid ne, ɗan Kawunsu da suke zaune gida guda da iyayensu, kowa da ɓangarensa.)
***Bayan kwana biyu.
Gidan Alhaji Barau mahaifin Sino, tsohon ministan man fetur, wanda yayi zamani da Obasanjo suka isa.
Alhajin na shirin fita, hakan yasa bai maida hankali gare su ba, a zatonshi ma irin mutanen nan ne, masu 'yar banzar maular tsiya, kasancewar ba uniform ne a jikinsu ba, yayi gaggawar ɗaga gilashin ɓangarensa, yana tunatar da direban da ya taka motar da sauri su je.
Cikin gidan suka k'arasa, inda suka samu wani matashi da ke wankr motoci a gefe suka umarce sa da yayi musu sallama da Sino.
Bayan kamar mintina biyar sai ga shi ya fito sanye da pink ɗin t-shirt, wacce ta kama shi sosai, wandonshi carrot da ya sauka k'asar gwiwarsa kaɗan, kanshi ya sha relaxer, ya kwanta luf-luf, bakinsa sai shining yake alamar an k'awata shi da lip gloss, ya ya taho cikin takunsa, tamkar na budurwar da ta hango saurayinta.
Mamaki sosai ya kashe Inspector Khamis wanda ya gama karantar yanayinsa tun daga lokacin da ya dumfaro su, har izuwa sa'adda ya iso gabansu.
'Tabbas akwai alamomin tambaya dangane da shiga, da kuma ɗabi'unsa, wanda zubinsu ya fi kama da yanayin mata.'
Khamis ya ayyana a k'asar zuciyarsa, yana mai k'ara dubansa.
"Sino right?"
"Right man."
Ya faɗa yana kallon yanayin Khamis tun daga kansa har k'afarsa, a zuciyarsa yana yaba tsarin halittarsa. Tunaninsa ya katse lokacin da Khamis ya ɗaga I.D card ɗinsa yana faɗin
"Inspector Khamis Zubayr, ni na kira ka kwanaki biyu da suka gabata ka shaida mun kana PH. Well, idan ba damuwa zamu je da kai station domin kayi shedar abokinka."
Wani abu ne ya ji tun daga kansa, ya sauka har zuwa babbar yatsan k'afarsa, hankalinsa sosai ya kai kololuwa wurin tashi, yace
"Ni fa ban san wanda kake magana a kai ba."
"Kana nufin Mubarak Garba Bukar ɗin ne baka sani ba?."
Daram! Kirjinsa ya ansa, yana tunanin abin faɗa, Khamis ya katse shi ta hanyar cewa
"Zamu iya tafiya ba?"
"To ai yanzu matsalar ina ɗan wani abu ne, ka bari zuwa wani lokaci mana."
Murmushi yayi, yana faɗin
"Tambayoyi ne 'yan k'alilan zaka ansa mana. Ba zai ɗauki dogon lokaci ba. In banda yanayin aiki ma da sai in maka a nan, amma yanayin case ɗin na shi ne bai bani damar yin haka ba. Let's go."
Bai iya cewa komai ba, illa juyawa da ya yi ya fara tafiya, yayin da suke binsa a baya har zuwa inda suka ajje motarsu.
Gidan Prof. Bello Hassan mahaifin Deeni, Vice-chancellor na Kaduna State University (KASU) da ke bayan layin suka k'arasa. Hakan ya k'ara jefa zuciyar Sino a tashin hankali.
Cikin rashin sa'a basu samu ganin Deeni ba. Mahaifiyarsa Barr. Zainab, da suka samu damar ganawa da ita tana shirin fita, ta shaida musu cewar ya je Zaria ganin kakanninsa, yau kwana takwas kenan.
Lissafi Khamis ya fara yi a k'asar zuciyarsa, inda ya gano yaron ya bar garin ne a ranar da abun ya faru. Ya kalle ta, yana mai gyara tsayuwarsa.
"Kamar misalin karfe nawa ya bar a gida a ranar?"
Shiru tayi tana nazarin Khamis, kamar zata ce wani abu, sai kuma ta buɗe motarta ta shige, tana mai faɗin
"A office na wuni ranar, ban san lokacin da ya tafi ba. Excuse me please, I've a case to attend."
Ta tada motar ta wuce, tana jimamin alak'ar case ɗin Tareeq da yaronta mafi soyuwa a birnin zuciyarta, cikin su biyar da Allah ya azurta ta da.
Shiru Khamis yayi yana tunanin abin yi, kafin daga bisani ya isa ga mai gadi yana tambayar unguwar kakannin Deeni a cikin garin Zaria.
"Ni ina zan sani Yallaɓai? Ka ganni daga bakin gate ɗin nan, ban taɓa matsawa wani wuri ba."
Bai ce komai ba, suka juya da zumar shigewa mota, a dai-dai lokacin Yayar Deeni wacce ya ke bi wa, ta fito cikin shirin fita, da taimakonta suka samu adireshin inda Deeni ya ke, ba su ɓata lokaci ba suka wuce station da Sino, yayin da ya haɗa Sergeant Buba da wasu 'yan sanda, kan su wuce Zaria, su taho da shi.
A gefe kawai ya ajje Sino wanda yake ta raba ido yana son gano ta inda Mubee ya ke amma ba hali, Khamis ya kira wayar Mukhee har ba adadi, sai dai har zuwa yanzu a rufe take ruf.
Cikin awa biyu da mintina ashirin da wani abu, su Sergeant Buba suka shigo tare da Deeni, wanda yanayinsa kaɗai ya isa ya bayyanar da tashin hankalin da yake ciki.
Kallo ɗaya tak, Khamis ya masa, zuciyarsa ta raya masa tabbas ba zai rasa sanin wani abu ba dangane da laifin da ake tuhumar abokinsa.
Tare da Sino ya haɗa su, kafin ya bayyana masu makasudin kirannasu, tuni idanun Deeni suka raina fata. Uwa uba da ya fara jera masu tambayoyin da suke neman zauta tunaninsa.
Da murmushi shimfiɗe saman fuskarsa yace
"Abokinku ya shaida mana kuna tare da shi a gidan Alhaji Badaru mahaifin Tareeq a ranar laraba ashirin da biyar ga wannan watan da misalin karfe biyar na yamma. Shin ko zaku iya tuna misalin karfe nawa kuka bar gidan?"
Wata mashahuriyar zufa ce ta karyo ma Deeni, yana k'ok'arin gyaɗa kansa, sai dai ya dake ya tura hannu a aljihu ya ciro handkerchief ya share zufar, kafin ya kauda kai daga duban da Khamis ke mishi yace
"Ni wallahi na manta."
Da sauri Sino da ya kekashe zuciyarsa yace
"Wurin karfe shidda da wani abu muka fito."
Kallon tsanaki Khamis ya bisu da shi, sannan ya tsaida dubansa a kan Sino, "kun fito misalin shidda da wani abu, daga nan kuna tare har zuwa wane lokaci?"
Hannuwansa ya tura tsakanin kafafunsa, zuciyarsa na bugawa da sauri, a lokaci guda yana tunanin abinda ya kamaya ya faɗa.
"Uhnmm, daga nan? Daga nan masallaci naje ni, bayan nayi sallah sai na wuce gida."
"Kana nufin daga nan kuka rabu da abokanka, baka k'ara ganinsu ba."
"Eh. Daga nan gida na tafi, muna tare da Mukhee ma muna kallon ball har kusan goma da wani abu."
"Amma kuma ai kace kun rabu da su, ko daga baya shi Mukhee ɗin ya bi ka ya same ka a gida?"
"Ehh? Uhnmm, shi tare da shi muka tafi."
Hannunsa da ke rik'e da biro, yasa ya tallabi haɓarsa, ya tsaida idanunsa a kan Sino, sai dai ko alama ya k'i yarda su haɗa idanu. Murmushi ya saki, ya juya yana kallon Deeni, wanda dakyar idan fitsari bai ɓata wandonshi ba.
"Kai fa? Kana ina daga misalin shidda da rabi zuwa safe?"
"Eh? N.. Ni.. ni yau kwanana takwas ma bana gari."
"Na san baka gari, amma ai ka bar garin ne a ranar da abun ya faru, kuma abokinka ya shaida mana cewar tare da kai kuka je gidan su Tareeq a ranar har kuka samu saɓani da shi. Haka ne ko ba haka bane ba?"
"Ehh? Uhnmm. Eh haka ne, amma daga nan na tafi Zaria ai."
"Bayan kun yi shiri, kunyi targeting Tareeq, kun faɗa masa ba tare da wani ya ganku ba, sai ka ce bari ka gudu Zaria, sai komai ya lafa kafin ka dawo. Ko ba haka bane ba?"
"Ni wallahi ban san fyade za'a masa ba."
"Then what?"
Yayi maganar a tsawace yana dubansa.
Wata irin ruɗewa Deeni yayi, domin a zahiri, bai san sa'adda yayi maganar ba, a daburce yace
"Ina nufin ban sani ba wallahi Officer."
Kasa-kasa Khamis yayi da muryarsa yace,
"Ok, misalin karfe nawa ka tafi Zaria?"
"Ehhh..? Hmmmm.. wuraren bakwai na tafi."
"Ka isa can da misalin karfe nawa?"
"Karfe takwas na isa."
"Ok, bani number wani a can Zaria ɗin."
Ya d'ago cikin kaɗuwar zuciya, idanunsa sunyi rau-rau, yana shirin fara hawaye, yace
"Uhmmm, bani da number su."
"Do not mess with me young man, ka faɗa mun gaskiya in kuɓutar da kai."
Hawaye ne suka silalo masa, zuciyarsa na harbawa da sauri, yace
"Ka yarda da ni Officer, dan Allah, ka bar ni in tafi."
"Ka bani number su, then I'll let you go."
Wayar ya fitar yana shirin karantawa, Sino ya dinga zungurarsa, amma da ya ke basirarsa ta ɗauke, a ganinsa yana bashi number zai tafi gida, haka ya karanta masa, bai ɓata lokaci ba ya danna kira kafin ya mik'e tsaye.
Mace ce ta ɗauki wayar, da alama dattujuwa ce, haka Khamis ya fara tambayar lokacin da Deeni ya shiga garin Zaria.
Cikin muryarta wacce da wuya tayi karya, ta tabbatar masa da ya shigo garin ne misalin karfe goma sha ɗaya da wani abu na dare. Godiya Khamis yayi mata, ya kashe wayar ya koma ya zauna.
Murmushin samun nasara ya saki, ya tsaida dubansa ga Deeni da yake kuka bil hakki da gaskiya yace
"Bincikena ya nuna kana da masaniya akan abinda ake tuhumar abokinka, shin zaka faɗa mun gaskiya ko har sai jikinka ya gaya maka?"
Fitsarin da yake ta matsewa ne ya tsiraro ta tsakanin kafafunsa, ya duk'a yana ɗaga hannuwansa yana rokon Khamis
"Dan Allah Officer ka yi hakuri."
"Zaka faɗa mun gaskiya ko baza ka faɗa ba?"
Shiru yayi, ya kasa magana, hakan yasa Khamis ya mik'e ya fita daga ofishin, yayi kiran 'yan sand'a guda biyu, kan su shiga da shi suyi ta dukansa, har sai lokacin da ya shirya sanar da su gaskiyar abinda ya ke ɓoyewa.
Ya juya ga Sino wanda tuni gwiwarsa ta gama sakewa, dan ya riga ya san halin Deeni, muddin ya ji wuya, zai iya fallasa sirrin da suke ɓoyewa.
"Kaima gaskiyarka ce kawai zata kuɓutar da kai. Muna nan tare har sai an gano inda abokinka ya shiga."
Ya k'ara janyo wayarsa, yana mai sake kiran number Mukhee, wacce har yanzu a kashe take, dole ya tada 'yan sanda guda biyu, ya basu adireshin duk wuraren da Sino ya ce za'a iya ganin Mukhee domin su taho da shi.
www.wattpad.com/iLubieee
Lubiee ce..
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{10}
_««This page is for Khadijah Taheer and Marjanah. It's more than a pleasure to meet yu guys. Thank you so so very much for the love and the courage. I'm grateful.»»_
Da gidan Alhaji Badaru suka fara, cikin rashin sa'a basu samu kowa gidan ba sai mai gadi da Asabe wacce ta shaida musu cewar yau kwanan Mukhtar biyar kenan, rabonshi da gida.
"Tabbas na ga dawowarshi yau da safen nan, sai dai ko in k'ara fita yayi."
Cewar mai gadin yana duban 'yan sandan da ke tsaye gabansa.
"To Baba kayi masa sallama mana. Mun nemi layinsa ya fi a kirga, amma baya shiga."
"Babu damuwa."
Cewar Baba mai gadi lokacin da ya juya zuwa cikin gidan.
Ga mamakinsa babu Mukhee babu labarinsa, haka ya dawo ya shaida musu, kafin ya koma bakin aikinsa.
Duk wani wuri da aka tabbatar musu yana zuwa, babu inda basu je ba, sai dai basu samu damar ganin ko da mai kama da shi ne ba. Titin Badarawa suka dauka, wuri na karshe a wuraren da suke da tabbacin samunsa, suka isa _shisha joint_ din mai cike da matasan maza da mata, suka fara dubawa, kamar hadin baki, nan din ma ba su samu ganawa da shi ba. Mutane daya bayan daya suka dinga bi suna tambaya, dak'yar suka samu wanda yace ya san shi, kasancewarsu ma'abota zuwa wurin shi da abokansa, sai dai ya tabbatar musu yau kusan sati guda kenan ba tare da wani a cikinsu ya lek'o _joint_ din ba. Daga nan ya juya, domin ci gaba da sabgar gabansa, yayin da suka yi kiciɓis da wani matashi da ya daki kafaɗarsa yana faɗin
"Mazaaa.. lefin me kayi naga Officers sun tsare ka?"
Dariyar jin daɗin ganin abokinnasa yayi, ya bashi hannu suka tafa.
"Kaii, ni a su wa? Neman Mukhee suka zo."
"Wane Mukhee fa?"
"D'an dogon gayen nan da suke shigowa da yaron minister."
"Owh.. Yau da safen nan ko kamar na ganshi yana shiga tudun wada naje zan kai Hajiya wurin wata ta'aziya."
Daga haka suka juya zuwa ciki, suna ci gaba da labaransu, ba tare da sanin cewar duk abinda suka fad'a ya shiga kunnen polisawan ba.
'Tudun wada?'
Cewar ɗaya a cikin 'yan sandar a k'asar zuciyarsa, a zahiri kam babu wanda yayi magana, daga bisani suka isa inda suka ajje motarsu.
Bayan sun shiga sun fara tafiya, d'an sandan da ke zaune kujerar mai zaman banza ya juya yana duban direban yace
"Mu je tudun wadar."
"Kana da tabbacin inda zamu ganshi a can ɗin ne?"
Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, daga bisani yace
"Mahaifinsa ɗan can ne, na taɓa jin anyi fira da shi a radio, inda yace shi haifaffen cikin tudun wada ne."
"Chap, lallai Officer kanka na aiki da har ka iya rik'e wannan."
"Kana wasa da k'wanya irin tawa kenan."
Suka dara, kafin suka sha hannu, a sa'a guda ya canja akalar motar suka ɗauki hanyar tudun wada, duk da cewar basu da tabbacin zasu ganshin, ko baza su ganshi ba.
Sai da suka sha tambaye-tambaye, kafin suka samu wanda ya kwatanta musu gidannasu Alh. Badaru, suka k'arasa layin, kafin suka sake tambayar wani, wanda ya shaida musu cewar k'ofar gidan ne ke ɗauke da majalissar matasa.
A tare suka fita suka k'arasa wurin bayan sun tsaida motar, ɗaya bayan ɗaya matasan da ke zaune suke dubansu, yayin da suka katse su ta hanyar ba su hannu suka fara gaisawa. Ba su sha wahalar tambayar wani inda Mukheen yake ba, kasancewar yana zaune a wurin, shine mutum na k'arshe a dogon bencin da suka yada zango.
"Bari mu ganka mana."
D'an sandan ya faɗa yana nuni da Mukhtar, wanda yanayinsa babu yabo, babu fallasa.
Ba tare da gardama ba ya mik'e ya isa gabansu, suka ɗan ja gefe, kafin suka gabatar da buk'atar da ke tafe da su.
Shiru yayi kamar mai nazarin wani abu, kafin ya ɗago yana faɗin
"Mu je, babu damuwa."
Ganin sun shige motar 'yan sandan ya sa sauran matasan mamakin mahaɗarshi da su, sai dai babu wanda ya iya cewa komai, illa addu'ar neman tsari da suka masa, kafin suka maida hankalinsu ga firar da ta sha gabansu.
Sino na zaune yana jin yadda 'yan sanda ke dukan Deeni, zuciyarsa gaba ɗaya tayi bulaguro zuwa firgici da tashin hankali, duk da kasancewarsa mutum mai jajircewa da rashin tsoro. A haka su Mukhtar suka shigo, kirjinsa ya saki wani k'ara mai k'arfi, ya k'ura ma Mukhee idanu, hakan yasa a take ya fahimci maganar da ke k'asar zuciyarsa.
Khamis da ya fito daga _cell_ ɗin su Deeni ya k'araso gabansu yana son fahimtar yanayin kallon da suke jifar junansu da, haka kawai ya ji zuciyarsa bata aminta da duk su biyun ba.
Kujerar da ke fuskantarsu ya zauna, tare da maida dubansa ga Mukhee ya ce
"Mukhtar."
"Na'am."
Ya ansa yana dubansa, a lokaci guda yayi k'asa da idonsa.
"Ya kuke da Tareeq?"
A tsanake ya fara magana
"K'anena ne, Uwa ɗaya, Uba ɗaya."
"Wannan fa?"
Yayi nuni masa da Sino da ke zaune gefensa.
"Abokina ne."
"Very good, na san baza ka k'i Tareeq da kuka fito ciki ɗaya ka so wani ba. Right?"
Yayi shiru, idanunsa a k'asa bai ce komai ba, haka Khamis ya ci gaba
"A dai-dai lokacin da aka tura Tareeq kiranka, kana ina?"
"Ehhh?"
"Ehnnn. Ai ka ji me nace ba."
Yayi shiru yana nazari, daga bisani yace
"Muna tare da abokaina
"Su wa kenan?"
"Mubee, Deeni, sai wannan."
Ya nuna Sino wanda ya jefe shi da mugun kallo mai fassarar 'haka za kai mun?'
"Hakan yana nufin tunda kuka fita a gidanku da misalin karfe shidda da rabi kuna tare da su kenan ko?"
Muryar Khamis ta dawo da shi daga nazarin kallon da Sino ke masa. Ya ansa da
"Eh muna tare."
"Har zuwa karfe nawa?"
"Har wurin karfe tara da wani abu na dare."
Murmushi Khamis ya saki kafin yayi dogon rubutu a takardar gabansa, ya ɗago yana k'ara duban Mukhee.
"Daga karfe tara da wani abu na dare da kuka rabu, ka tsaya wani wuri, ko gida ka wuce straight?"
"Daga nan gida kawai suka ajje ni."
"Bayan sun ajje ka kuma baka k'ara fita ba?"
"Eh ban k'ara fita ba."
"Masha Allah. Amma abokinka ya shaida mana cewar kana tare da shi a gidansu kuna kallon ball, tun da kuka fita daga gidanku da misalin shidda da rabi na yamma, har zuwa k'arfe goma da wani abu na dare, while kai kuma ka tabbatar mana da cewar sun ajje ka gida da misalin karfe tara da wani abu, shin maganar wa kake ganin ya dace mu dauka?"
"Ehhh,? Uhnmm.. eh, muna tare, amma."
"Eh.. Amma. Amma what?"
"Eh muna tare. Daga gidansu na dawo gida."
"But kace kuma su suka sauke ka a k'ofar gida. Hakan yana nufin daga wani wuri ma kuka dawo."
Shiru yayi, ya rasa abin cewa, haka kuma kirjinsa na harbawa cikin sauri, sosai yana jin tsananin tausayin abokannashi.
'Duk laifin banzan Khalid ɗin nan ne ai.'
Ya ayyana a k'asar zuciyarsa, yayin da maganar Khamis ta dawo da shi daga duniyar da ya tsunduma.
"Kai nike saurare Mukhtar."
"Uhnmm, eh na manta ne, daga gidansu ne na taho ni kaɗai, ba su suka sauke ni ba."
"Ka faɗa mun gaskiya Mukhee, if not zaka sha mamakin abinda zai biyo baya. Cuz Khalid ya riga ya faɗa mun fitar Tareeq ke da wuya, kai kuma ka shigo gidan. That's tsakanin tara da wani abu na dare. Hakan yasa na fahimci wani abu, i mean abokanka na sauke ka, suka bi Tareeq a baya, suka ɗauke shi, suka je inda suka je suka keta mutunci da haddinsa. Ko ba haka ba ne ba?"
Ya karashe cikin wata irin tsawa mai tsoratarwa, wacce ta kaɗa 'yan hanjin Mukhee, har ma da na Sino da ke zaune.
"Ni wallahi ban sani ba, ni suna ajje ni gida na shiga."
Murmushin takaici Khamis ya yi, ya tsaida dubansa a kanshi, tabbas abinda ya faɗa gaskiya ne, haka kuma baya tunanin idan da sa hannunsa a abun da ake tuhumar abokinnasa.
Mikewa yayi, ya fara kiran Khalid, bayan ya ɗauka ya tambayi mutanen da ke gida lokacin da Mukhee ya dawo gida a ranar da al'amarin ya afku.
Bai ɓata lokaci wurin shaida masa ba, yayin da ya k'ara da cewar ya haɗo kansu su zo station, domin a ɗauki jawabinsu.
Bayan gama wayar ne ya juya yana duban Sino wanda idanunsa ke jifar Mukhee da wani gawurtaccen kallon da Khamis ya kasa fassara shi.
"Shin zaka faɗa mun gaskiya ko kai ma sai jikinka ya baka labari?"
Yayi firgit, ya maida hankalinsa ga Khamis
"Ni fa wallahi Officer iyakar gaskiyata kenan, ka yarda da ni dan Allah."
"Iyakar gaskiyarka kenan, right?"
Ya girgiza kai, alamar haka ne.
"Okay, give me your phone."
Ya faɗa yana mik'a hannunsa, amma Sino ya dake, ba ma shi da alamar motsawa, balle yayi yunkurin fitar da wayar.
Wata gagarumar tsawa ya buga masa, ya k'ara da cewar
"Zaka bani ko sai na ansa da kaina?"
Ba tare da ya girgiza da tsawartashi ba, ya cire wayar ya mik'a masa.
"Faɗa mun number wani a gidanku in kira yanzun nan."
Shiru yayi, ya juyar da fuskarsa, a zuciyarsa yana tunanin layin wanda zai bayar. 'Na yayanshi da ɗakinsu ke manne da juna, wanda yake da tabbacin ya san abinda ya ke aikatawa, haka kuma a ranar ma sai da ya masa bala'in kai dare da yake a waje, ko kuma na mahaifinsa wanda ya kusan anshe makullin motarsa a ranar, saboda yawon dare?' Bai gama yanke shawara ba, Khamis ya razanar da shi da gigitacciyar tsawarsa
"Baka ji abinda na faɗa bane?"
"Ehmm,.. number ta na nan ciki ai."
Yayi nuni da wayarsa da ke hannun Khamis.
"Wane suna ka saka ma number?"
"Uhnmm..."
Sai kuma yayi shiru.
"Ehhnnn."
"Kb D'an bala'i."
Ya faɗa yana tuna sadda ya adana layin yayannashi da sunan, ranar da ya kusan hallaka shi, ya shigo ɗakinshi ya ganshi da wani _Boyfriend_ ɗinsa bakinsu ya kusa haɗewa da na juna.
Girgiza kai Khamis ya yi, domin a zahiri sunan ba k'aramin dariya ya basa ba, haka ya maze ya fara kiran layin D'an bala'in.
Har ta katse ba'a ɗaga ba, sai dai da katsewarta, da biyo bayan kiran duk ɗaya. Ya ɗaga da sallama, suka gaisa, daga bisani yayi masa bayanin kirannashi.
"Eh to, a gaskiya wurin sha biyu da wani abu ya dawo gida, dan ba zan manta ba a lokacin da na ji dawowarsa, sai da na fita ina mishi magana, inda ya shaida mun cewar ya je kai wani abokinsa Zaria ne, motar ta tsaya musu a hanya. Lafiya dai ko?"
'Ya tabbata akwai sa hannun dukansu ukkun kenan!' Khamis yayi maganar a k'asar zuciyarsa, a fili kam yace
"Babu damuwa, na gode Kb."
Ya kashe wayar yana jifar Sino da wani mugun kallo, shima idanunsa cikin na Khamis ɗin, duk kuwa da dukan tara-tara da kirjinsa ke yi.
"You're messing with the wrong person Kiddo."
Ya faɗa yana nuna masa hannu, kafin ya zauna jiran isowar Khalid da tawagarsa.
*****
Tun daga kan Baba mai gadi, Asabe, Khalid da Hajja Fati suka ɗinguma zuwa ofishin yan sandar, yayin da aka bar Zulaiha a wurin Tareeq, domin kula da shi da bukatunsa.
Tun da suka taho Hajja Fati ta dinga ruwan masifa tana tsine ma Khalid tana faɗin
"Wallahi matsawar wani abu ya faru da yarona, ina mai tabbatar maka da sai na ga bayanka Khalid. Haba, wannan masifa har ina? Gashi nan kana neman janyo mana wani sabon alkaba'in."
Ta k'arashe tana kiran layin Alhaji Badaru, bayan ya ɗauka ta fashe da kuka tana shaida masa yadda Khalid ke neman ja ma ɗansu bala'i.
Ta ɗayan ɓangaren shima masifa ya shiga yi, kafin ya tabbatar mata da cewa yau ɗin nan, ba sai gobe ba, zai shigo, kuma sai Khalid ya bar masa gidansa, har ma da iyalinsa. A k'arshe yace
"Ke ni da Khalid ma har abadan abada. Haba, ina dalilin masifa."
Ya kashe wayar yana ta bala'i, a haka suka isa ofishin na 'yan sanda, babu ɓata lokaci Khamis ya ci gaba da gudanar da aikinsa.
Da mai gadi ya fara, wanda ya tabbatar masa tabbas su Sino ne suka ajje Mukhee a k'ofar gida, kuma fitar Tareeq kenan su kuma suka iso. Sai dai ya shaida masa cewar daga nan, Mukhee bai k'ara fita ba, har sai lokacin da suka je asibiti suka same su shi da Khalid.
Hajja Fati ma haka ta tabbatar ma Khamis, haka Asabe, haka kuma Khalid, illa basu da tabbacin yadda akai Mukhee ya dawo gida, su dai sun ganshi ya shigo kawai.
Dogon rubutu Khamis ya yi, ya ɗago yana duban Sino, kafin ya fara magana
"Da waɗannan tarin hujjojin da mutanen nan suka bayar, gaba ɗaya sun dakushe labaran k'anzon kuregen da kuka zo da shi kai da abokanka, hakan kuma ya tabbatar da cewar akwai sa hannun ku duka ukkun a abinda ake tuhumar abokinku."
Ya yi maganar a faɗace, kafin ya mik'e cikin fushi yana kiran
"Sergeant Buba.."
"Yes Sir."
Ya iso da gudu, ya sara masa.
"Take him in, ku cigaba da bugunsu, har sai sun ansa laifinsu"
"Yes Sir."
Ya kuma sara masa, kafin ya tusa keyar Sino wanda tashin hankalinsa ya bayyana muraran gaba, zuwa _cell_ ɗin da sauran abokansa ke ciki.
Daga nan ya koma ga su Mukhee, suka yi duk abinda ya kamata, kafin ya sallame su domin wucewa gida.
Wani kyakkyawan murmushi ne kwance saman fuskar Khalid, sai dai kallon da ya ga Sino da Mukhee suna jifar junansu ya jefa zuciyarsa a kogin tunani, uwa uba da ya tuna cewar Jarma ya shaida masa kwanakin da Mukhee ya kwasa a tudun wada...
www.wattpad.com/iLubiee
Ana wata ga wata kenan... What do you think will happen in the next chapter? Drop yo comments, lemme hear....
Lubbatu ce... ♡
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
_This is for ya'all mutanen Taskar Lubiee Maitafsir. I'm more than excited for the love, courage and the support. Yu guys means a lot to me, and I love y'all so very much, to the moon round and back._
{11}
Har suka iso gida Hajja Fati bata daina jifar Khalid da mugayen kalamai ba, sai dai uffan, bai ce da ita ba, a zahiri hankalinsa baya tare da shi ma, tunaninsa gaba ɗaya ya raja'a a son sanin dalilin Mukhee na tafiya tudun wada har ya kwashi kwanaki biyar, abinda tunda ya zo duniya bai taɓa yi ba.
'Shin hakan yana nufin yana da masaniyar abinda abokannasa suka aikata ko kuwa?'
Ya tambayi zuciyarsa, yayin da wani fannin yayi gaggawar bashi ansa da cewar
'Ba haka ba ne.'
Jin k'aran faɗuwar abu, da kuma buga k'ofar gaban motar da Mukhee ya fita ne ya dawo da shi daga dogon nazarin da ya auri zuciyarsa, ya ɗago firgigit, ya dube shi, a lokacin har ya kama hanyar cikin gida, kafin ya maida hankalinsa ga son sanin abinda ya ji faɗuwartasa. Cikin rashin sa'a bai ga komai ba, hakan ya sanya shi taka motar yana shirin barin gidan, a dai-dai nan motar Alhaji Badaru ta shigo.
Tun bai k'arasa gyara parking ba ya fito yana nuna masa hannu
"Dama saurin da nike in same ka a cikin gidan nan, dan daga nan baza ka koma ga Tareeq ba, sai dai ka koma inda ka fito. Ba zan lamunci tozarci da cin mutunci a cikin gidana ba. Ina zaman zamana cikin rufin asirina, ka zo ka tona mun shi, wannan bai ishe ka ba, har sai da ka ja yan sanda suka kama mun yaro. Allah ya taimake ka basu masa komai ba, amma wallahi da kai ma sai ka raina kanka. Kuma daga rana irin ta yau, na maka katanga da gidana Khalid. BABU KAI, BABU IYALINA!"
Shiru ya yi, har sai da ya gama masifartashi, kafin ya ja motar ya fita a kiɗime, wata zuciyar na ingiza shi kan ya yi abinda Alhajin ya umarce sa, abin nufi ya kaurace ma iyalannasa, yayin da wata ke tunatar da shi abinda hakan zai haifar. Watak'ila nisantarshi da iyalin alhajin, musamman ma Tareeq, zai iya sawa suyi watsi da gaba ɗaya al'amarin na Tareeq, duk kuwa da cewar baya da haufi a kan Khamis, ba ma kamar tun da abin ya haɗo da mutanen cikin unguwa. Canja akalar motar yayi, ya ɗauki hanyar asibitin, sai dai duk wacce za'ayi ayi.
****
Kaiwa take tana kawowa a tsakiyar tangamemen palon da ya wadatu da komai na jin daɗin rayuwa. Sallamar direban mai gidannata da ya shigo da jakarshi ce ta dawo da ita hayyacinta, ta iso da sassarfa ta anshe jakar tana duban bayan direban, domin a zahiri babu abinda take muradi wanda ya wuce mata tozali da Engr. Bukar.
"Barka da sauka Engr."
"Barkanku da gida Hajiya."
Ya faɗa yana k'arasa shigowa cikin palon, yayin da direban ya juya ya fita ba tare da hajiyar ta ansa gaisuwar da yake ta faman mikawa ba.
"Ya hanya ya kuma hidimomi?"
Ta faɗa sa'adda ta zauna a gefenshi, tana k'ok'arin gyara ajiyar jakar hannunta a kan _carpet_.
"Alhamdulillah, mun gode Allah."
Ya cire farar _cardigan_ ɗin da ke samar bakar _long sleeve_ ɗinsa, a sa'a guda yana gyara zama. Hajiya Karima ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace
"Ban ji kayi batun yaron nan ba, har fa yanzu yana can, ko abinci aka je kai masa basa bari a ganshi, ni yanzu abinda ya fi ɗaga mun hankali bai wuce yadda jiya 'yan sandan ke shaida mun cewar wai sun gama duk wani bincike sun kuma gano da sa hannunsa, har ma da na abokansa guda biyu. Ka ji sharri dan Allah Engr, yanzu ina Mubarak ina wannan mummunar ɗabia? Yaron da duka-duka shekarunsa goma sha tara a duniya. Wallahi ba zan ɗauki wannan mugun kazafin ba, gara ka tashi muje duk wacce ma za'ayi ayi."
Shiru yayi yana sauraren yadda take magana hawaye na zuba a idanunta, ya nisa ya ce
"Kin ga illar abinda nike faɗi miki kenan, shi yasa a kullu yaumun nike ce miki su 'ya'ya amana ce ta Allah a hannunmu, amma son zuciya ya rufe mana idanu, musamman iyayen wannan zamanin, muna ganin bayar da ingantacciyar tarbiyya ga yaranmu, tamkar mun tauye musu wani hak'k'inasu ne, bayan kuma ba haka Islam ya tsara ba, annabin rahama kanshi sai da ya nusar da mu akan kula da abokan 'ya'yanmu, amma kullun na tashi yi wa Mubarak faɗan ɓata garin abokai, kece kike shiga bayansa. Yanzu ki gaya mun, wa gari ya waya?"
Shiru kawai tayi, har yanzu hawayen take zubdawa, dakyar ta shafe su da gefen mayafin jar abayar da ke jikinta, kafin ta ce
"Duk wannan ba maganar da zamu yi yanzu ba ce Engr, ka taimaka ka tashi mu isa ga 'yan sharrin can, tun basu tura abin nan wurin alkali ba."
Bai iya k'ara magana ba, hakan yasa ta shiga ta fito da jakarta, sannan ta ajje masa tashi a ciki, inda ta samu har ya fita, da sauri ta wuce itama, direba ya iso da motar suka buɗe gidan baya duk suka shiga.
Ofishin 'yan sandar suka dumfara, da zuwansu Engr ya bukaci ganawa da Khamis wanda mutanen wurin suka shaida masa alhakin _case_ ɗin yana hannunsa.
Har ofishinsa ya isa, bayan sun gaisa cikin dattako, domin kuwa shi ɗin mutumin kirki ne mai nasibi da sanin ya kamata.
"Sunana Engr Garba Bukar, nine kuma mahaifin Mubarak, yaro da ke nan tsare a hannunku."
"Masha Allah. Akwai abinda kake buk'atar sani ne?"
Khamis ya faɗa yana dubansa da ɗan murmushi.
"Eh nayi tafiya na dawo ne sai Hajiya ke sanar da ni abinda ya faru, amma zan so in ji karin bayani ta bakinka."
Biron da ke hannunsa ya ɗora saman _file_ ɗin da ya ke cikewa, daga bisani ya fara magana inda ya yi ma Engr duk wani bayani dangane da case ɗinnasu, ya k'ara da cewar
"As soon as muka gama rubuta report zamu tura su court ne, so advisable ku je ku fara fafutukar neman lawyer."
Shiru Engr yayi, kafin ya ɗago yace
"Su fa sauran yaran? Iyayensu na da labari kuwa?"
"I don't know actually, dan babu wani daga danginsu da ya zo."
Bai ce komai ba, ya mik'e ya fara kiran layin Alhaji Barau mahaifin Sino, a zahiri ba zai iya cewa komai ba, har sai iyayen sauran yaran sun iso. Jin muryar wanda ya kira tana ansa kuwwa a kusa da shi ya sanya shi juyawa da sauri, inda suka yi arba da Alhajin wanda labari ya same shi ba da jimawa ba, ya iso ofishin na 'yan sandar.
Zaman babbar rigarsa ya gyara, yana duban Engr, da fuskarsa mai bayyanar da ɓacin rai, ya bashi hannu kafin ya ɗora da cewar
"Ka riga ni isowa kenan? Wannan masifa har ina? Haka kawai dan dai an tsani yara, sai a ce su suka aikata wannan mugun alkaba'in? Sam ba zan lamunci abin nan ba wallahi. Wai ashe yau har kwanansu biyu ma kenan, amma sai yanzun nan nike jin labari a bakin mai gadi, shima wai a cikin unguwa yake jin maganar. Ni duk a zatona ma yayi tafiya zuwa wani gari ne, ashe ina can an kamo mun yaro an garkame ana jifarsa da mugun kazafi."
"Ya isa haka Alhaji, mu jirayi isowar Barr. Zainab, dan na ga Hajiya tayi kiranta, na san duk inda take tana kan hanya yanzu, in yaso sai mu san abinda ya dace."
Ya k'ara baza babbar rigarsa, yana faɗin
"Ka san Allah Engr? Daga nan babu inda zan matsa sai sun fiddo mun yarona. Da mutuncina da komai ace na kasa taɓuka komai a kan wannan ɗan k'aramin sharrin? Ba zan yarda ba!."
Engr bai ce komai ba, dan yana da tabbacin Khamis da sauran yan sandar wurin duk suna sauraren abinda ke faruwa. Suna nan tsaye Barr. Zainab ta iso cikin tashin hankali, basu tsaya wata doguwar gaisuwa ba, suka yi wasu 'yan maganganu, sannan suka rankaya ofishin Khamis, wanda ke zaman jiran tsammaninsu.
Kallonshi Barr. Zainab ke yi, tabbas ta san fuskarshi, sai dai a yadda suka je gidannasu, bata zaci suna zargin yaronnata ne ba. A zatonta ko tambayarsa wani abun zasu yi, kasancewar yana shiga gidan Alhaji Badarun.
Engr ne ya katse mata tunani ta hanyar fara yi musu bayanin komai kamar yadda Khamis ya masa, kafin Alhaji Barau ya ɗora da cewar
"Wannan maganar banza."
Ya juya yana kallon Khamis, a lokaci guda yana kankan da muryarsa,
"Kaga Officer, idan wani abu kake so, ba sai ka biyo mana ta wannan hanyar ba, ni mai iya baka duk abinda kake bukata ne, ba tare da aljihun wani a nan yayi kuka ba, dan haka muyi tsada da kai, ka sakan mana yaranmu tun muna shaida juna."
"Yawwa. Yanzu na ji batu."
Cewar Hajiya Kareema da idanuwanta ke zubar da hawaye. Murmushi mai tsada Khamis ya saki, ya gyara zamansa, hannuwansa duk biyun yasa y tallabi haɓarsa, yana kare ma Alhajin kallo, a sa'a guda yana bin sauran jama'ar wurin da duba, yana ganin yadda suke jijjiga kai alamar sun aminta da maganar ta Alhajin, daga ciki kuwa hadda Barr. Zainab, wacce ta san hukuncin abinda suke shirin aikatarwa.
Ya tsaida dubansa ga Alhaji Barau da murmushi kunshe da laɓɓansa yana faɗin
"Gwamnati ta ɗauke ni aiki ne ba don komai ba, sai dan in kwato ma yan kasa waɗanda aka zalunta hakkinsu. Nayi duk wani bincike, na gano da sa hannun yaran nan a abinda ake tuhumarsu, dan haka ba gudu ba ja da baya, dole na mik'a rahotansu a gaban kuliya. Yan kuɗi kalilan da zaka bani, baza su taɓa tseratar da ni daga wutar jahannama ba a ranar gobe kiyama, sakamakon karya alkawarin da na ɗauka da kake son nayi. ina shawaryarku, ku adana kuɗinku, na tabbatar a gaba zasu muku amfani."
Wata zufa ce ta karyo ma Alhaji, yana jin maganar Khamis da ke dukan dodon kunnensa tamkar da guduma.
"This the best for all of us Inspector. Ka ansa tayin da mu kai maka tun yanzu, kafin ka zo kana cizon yatsa zuwa gaba."
Barr. Zainab ta kauda shirun da ya ratsa wurin na d'an lokaci. Kafin Hajiya ta kara da cewar
"She's right Inspector. Kada ka bari wannan opportunity ɗin ya wuce ka, a k'arshe ka zo kana da na sani."
Kan Khamis a k'asa, zuciyarsa na tafasa da maganganun da suke jifarsa. 'Me aka ɗauki ɗan sanda a wannan k'asar tamu? Maha'inci? Ko kuwa maci amanar aikinsa? Ba zan iya jurewa wannan kallon da mutane suke mana ba, dole ne in tabbatar musu da cewar ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Dole in kare hakkin al'ummata, in kuma kwato ma Tareeq 'yancinsa da aka raba sa da shi. Dole in koya ma mutanen nan hankali, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar aikina. I dont care.'
Yayi maganganun duk a k'asar zuciyarsa, ya ɗago yana dubansu kafin yace
"My decision is final. I'm not one of those so called police da kuke bribing ku tauye hakkin wanda aka zalunta, so babu nera ɗaya taku da nike buk'ata haka kuma kaf k'asar nan babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga tura rahotan nan Ministry Of Justice."
Ya karashe cikin ɓacin rai, wanda ya sanya Alhaji Barau mikewa yana nuna shi da hannu.
"Be careful ɗan sanda! Ka bar ganin na biyo ta hannunka ka nemi ka manna mun hauka. Ka manta a wace kasa muke ne? Nigeria ce fa, the most corrupted country in the whole world! Haka kuma ka san da wa kake magana, dan mu ke da k'asar. Kuma sai na fitar da yarona ko ta wane irin hali, kayi addu'ar kada insa a kore ka daga wannan gurguwar kujerar taka..."
Bai bari ya kai aya ba ya mik'e shima.
"A haka kuke kiran kanku shuwagabanni? Kuna kiran kasarku da corrupted country? A haka kuke tutiya da mukaminku? Ni Inspector Khamis Zubayr, I promise, I'll prove you wrong Alhaji Barau. Sai na mik'a yaran nan gaban kuliya ko ta wane irin hali."
"Ya isa, ya isa da Allah. Dan Allah ku zauna mu fuskanci juna, ku tuna ba fa abinda ya kawo mu nan kenan ba."
Cewar Engr da ya mik'e yana dubansu, amma ina tuni Alhaji ya buga babbar rigarsa bayan ya nuna Khamis da hannu yana faɗin
"Wait and see Inspector."
Ya fice cikin matsanancin fushi.
0 comments:
Post a Comment