Engr wanda ya koma ya zauna ya tambaya yana duban Khamis. Ya nisa, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Babu wata mafita Engr, saboda yaran nan sun aikata lefin da ake tuhumarsu, shawara d'aya zan baka, shine kuje ku fara neman lawyer da zai kare su tun wuri."
"Kana nufin babu wani abu da zaka iya taimaka mana da shi?"
"Wallahi babu, there's nothing i can do about it."
Bai iya kara cewa komai ba, ya mike zuciyarsa babu dad'i, ya fita, dan dama shi d'aya yayi saura a ofishin, tuni sauran jama'ar suka rufa ma Alhaji Barau baya.
A waje ya same su suna ta faman sak'a da warwarewa, daga bisani Alhajin yace
"Ku bar komai a hannuna, ni zan je in ga commissioner Of Police din ma da kaina."
Daga haka suka wuce gida a kan cewar su had'u gobe da misalin karfe goma na safe.
Komai Engr bai ce ba, daga nan kowa ya kama gabansa, zuciyoyinsu duk a dagule, ba ma ya Alhaji Barau da ya kullaci abinda Khamis ya masa.
***Washe gari.
Alhaji Barau, Hajiya Karima, da Barr. Zainab ne zaune a ofishin CP. Badamasi wanda ya shaida ma Alhajin cewar yana kan hanyarshi ta zuwa, kasancewar Engr na da muhimmin taro, shi yasa bai halarci wurin ba, yayin da Prof. Bello har yau bashi da masaniyar abinda ya faru da yaronnasa, a cewar Barr. Zainab, zasu yi komai su gama, ba tare da mahaifinnashi ya samu labari ba.
A gaggauce CP. Badamasi ya shigo sanye da kakinsa wanda ya anshe sa ainun, hularsa mak'ale tsakanin gefen kirjinsa da hannunsa na dama, ya k'arasa da sassarfa ya mik'a hannu ma Alhajin, suka gaisa, kafin ya koma kujerarsa ya zauna, sannan suka gaisa da su Hajiya.
Jin Alhajin zai fara magana ya sa ya kai duba ga d'an sandan da ke tsaye a k'ame, yayi masa nuni da waje ta hanyar amfani da idanunsa. Da sauri ya fita, ya rufe musu k'ofar, kafin Alhaji ya cigaba da jawabin duk abinda ke faruwa.
Yana jinjina kai ya ke dubansa
"Haba Yallabai, in dan yar wannan matsalar, ai ba sai ka zo da kanka ba, ko da a waya ne ai ma iya tattaunawa. Kar ka damu, wannan ba abinda zai tashi hankalinka ba ne, I'll see what i can do."
Da sauri Alhaji ya washe baki, a sa'a guda yana mai k'ara gyara zaman babbar rigarsa, ya dubi CP. Badamasi, kafin ya fara magana.
"Ni na san da haka ai, idan da hali a koyar da Inspector aikinsa, na lura bai san ta kan aikin ba."
Murmushi mai bayyana hakora Commissioner yayi, ya shafi gefen fuskarsa mai cike da gargasa, daga bisani ya dunkule hannayensa, ya dora a teburin gabansa yana kallon Alhaji Barau cikin idanu.
"Ka san bani da wasa Yallabai, dan haka ka sa a ranka cewar anyi duk yadda kake so an gama."
Wannan kalamin ne ya sanya Alhajin duban sauran matan yana musu kallon 'me na fada muku.' Kafin ya fito da bandiran 'yan dubu-dubun da har bai san adadinsu ba, ya dora a teburin CP yana fad'in
"Ba yawa, ka k'ara mai a mota."
Ya murmusa, kafin ya mik'e, da ganin haka su Hajiya suka mike suma suna ta faman zuba ma commissioner godiya. Mikewa CP. Badamasi yayi, fara'a shimfide a kan fuskarsa, ya mik'a hannunsa na dama ma Alhaji, tare da sara masa da d'ayan hannun na haggu. Suka masa sallama, kafin suka juya suka fita.
Ya koma ya zauna yana mai bin kyawawan kudin da kallo, ya murmusa kafin ya kwashe ya adana su a lokar dake jikin teburinsa.
*****
Yau da sassafe Khamis ya iso, kasancewar duk wani rahoto da ya kamata ya had'a babu wanda bai had'a ba, hakan yasa ya iso da k'arfin gwiwarsa, ya dakata a ofishinsa ya gama tsara takardun, kafin ya mik'e ya wuce ofishin CP, domin gabatar da rahotannin.
Da sallama ya shigo, ya same shi a kan waya, amma haka ya k'ame, ya sara mishi, kafin yayi masa nuni da kujerar da ke gaban teburin, ya samu wuri ya zauna yana jiran gamawarsa.
"How may I help you?"
Ya tsinkayi muryar CP. Badamasi, wacce ta dawo da shi daga dogon nazarin da ya tsunduma.
"Sir about that rape case."
"Ehhn, wanne rape case kenan? Na jiya ko wanda aka kawo shekaran jiya?"
"No Sir, na yaron nan da ya faru three weeks ago, da nake fad'a maka ya k'i yayi magana."
"Owh, ina fatan kun gama gudanar da duk wani bincike da ya kamata?"
"Yes Sir, har ma mun kama suspect din, I'm here to present the F.I.R (First Information Report.)"
"Very good."
CP. Badamasi ya fad'a da fuskarshi mai bayyanar da yalwataccen murmushi, yasa hannu ya anshi rahoton, ya gama dubawa a tsanake, ya tabbatar da shine case d'in da Alhaji Barau ya ke son ayi masa aiki a kai. A takaice ya d'ago da makirin murmushinsa
"Zan san yadda nayi na aika da shi Ministry Of Justice. Kaje kawai abinka."
"But Sir..."
"Ehnnn?"
"Sir alhakin case d'in yana hannuna, a dokar aiki kuma kamata yayi ace ni nayi delivering musu da kaina."
Ya ajje wayar hannunsa, a sa'a guda ya tallabi habarsa yana mai zuba ma bakin Khamis kallo, ganin yadda yake fidda kalamansa hankali kwance. Sai da ya kai aya, kafin ya fara magana.
"The unpredictable Inspector Khamis."
Yayi shu'umar dariya, kafin ya mik'e tsaye ya cigaba.
"Alhaji Barau, tsohon ministan man fetur ya sanar da ni yadda ta gudana tsakaninku. Sai dai na shaida masa cewar kai d'in, d'an yaro ne wanda har yau bai san makamar aikinsa ba. To ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau, ka saurari abinda zan fad'a maka."
Da sauri Khamis ya d'ago yana dubansa, gaba daya annurin da ke kan fuskarsa ya d'auke, tamkar bai taba dariya ba. Yayin da shi kam bai damu da kallon da Khamis ke masa ba, ya ci gaba
"Ina so ka saka ma ranka cewar wannan case din bai taba faruwa ba, ta haka ne kawai zaka samu damar yin yadda kake so a karkashina, zan kuma yaga maka kaso mai tsoka, wanda ya fi wanda na yaga ma abokan aikinka, abin nufi 'yan sandan da suka taya ka bincike, domin na riga na gama da su."
Kan Khamis a k'asa ya fara girgiza shi, a zuciyarsa yana fad'in 'Ina mutanen duniya suke shirin zuwa da hakkin 'yan uwansu bil adama? Shin hakan na nufin CP ma yana cikin bata garin ma'aikata?' "No.."
Ya fad'a a bayyane, hakan yasa Commissioner juyowa a fusace, ya nuna shi da hannu yana fad'in
"Who are you? Kai waye da zan baka order kace baza ka bi ba? To ka saurare ni da kyau Inspector, matsawar kace zaka daga wannan maganar har wani ya ji, ma'ana ka kafe a kan tura case d'in Ministry Of Justice, ina mai tabbatar maka da k'arshen aikinka ya zo kenan. Dan haka ka zaba tsakanin kakinka da tura report d'in nan."
Ya karashe yana mai tura takardun gaban Khamis, wanda kirjinsa ke bugawa, ya d'ago da jajayen idanunsa yana kallonshi, bai ce komai ba ya d'auki file d'in, ya mik'e ya sara masa, kafin ya juya ya fita.
"So brave!"
CP. Badamasi ya fad'a yana murmushin makirci, a zuciyarsa yana ayyana tabbas babu inda hargagin Khamis zai je, kasancewar sanin da ya masa a matsayin mutum masoyin aikinsa, wanda ya sanya aikinsa a gaba da komai na rayuwarsa bayan addininsa. Ya san dole yayi abinda yake so, ko dan ya kare kakinsa. Ya saki dariya kafin ya koma kujerarsa ya zauna.
A hargitse ya koma afishinsa, ya ajje file d'in kan teburin da ke gabansa, a sa'a guda yana cire hular da ya ke jin ta masa nauyi saman kansa.
Hannuwansa duk biyun yasa ya tallabi fuskarsa, sosai ya zurfafa a kogin tunani, hakan ya sa bai lura da lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke doguwar fuskarsa ba. Babu abinda ke yawo a kansa, sai ranar da suka isa asibiti, suka samu Tareeq a halin da yake, an keta mutuncinsa, an d'auke masa walwala da gaba d'aya jin dad'insa, an jefa kunci, firgici, tashin hankali da kiyayyar mutane a zuciyarsa. Ta ya za'a ce ya manta da wannan mummunan al'amarin? Ta ya zai iya runtse idanunsa yayi bacci, bayan ya san bai fitar da hakkin aikinsa ba? Sannan kuma ya zai ji a ranar da irin hakan ta kasance a kan yaronsa? Zai mance da abun ne? Ko kuwa zai yi pretending kan abun bai taba faruwa ba?
"That's impossible!"
Ya fad'a cikin daga murya, a sa'a guda ya kifa kansa a teburin, ya rink'a kuka marar sauti, a zuciyarsa yana addu'ar Allah ya kawo masa mafita, yana kuma jin ina ma yana da ikon tura rahotan nan ba tare da amincewar wani babba ba.
Kuka ya ke mai sosa zuciya, tamkar ba Inspector Khamis din da aka sani ba, daga bisani wata shawara ta fad'o masa, ai ba ta hannun Commissioner ne kawai report d'in zai bi ya je ga alkali ba. A gaggauce ya mik'e ya share hawayensa, kafin ya dora hularshi, ya gyara zaman igiyar da ke sargafe a gefen kafadunsa duk biyun, wanda suka kasance na karramawa da aka daura masa lokacin da ya kama wasu gagaruman barayi da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja. Ya wuce cikin takunsa mai fad'i, ya dumfarin ofishin DPP (Director Of Public Prosecution.)
Na san ni mai laifi ce, amma sai kunyi hakuri da yadda kuka same ni wannan karon. Abubuwa ne sun matse ni, da kuma yanayin labarin, dan har yanzu ina kan bincike ban gama samun komai a hannuna ba. Ku k'ara hakuri mutanena. ILY'all.
www.lubabatumaitafsir.com
www.wattpad.com/iLubieee
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{14}
Mal. Idi mai gadi ne ya sanar da su Alhajin baya gari, hakan yasa suka bukaci ganawa da Hajja Fati, wacce yanzu ba laifi ta kan dan zauna a gidan, sai dai matsawar aminiyarta Hajiya Maryam ta kira ta, to fa dole ta bar duk me take, domin ta ansa kirannata.
Ta fito sanye da gyalenta a kafadar, ganin sune ya sa ta yi musu iso har zuwa palon baki. Bayan sun natsu sun gaisa, Engr yayi mata jawabin abinda ke tafe da su wanda ta riga ta san da kwanan zancen, hakan ya yi sanadiyyar kara dagula lissafinta, ya kuma bayyanar da tashin hankalin da take ciki, a sa'a guda tana kokarin fahimtar da su yadda suke kin zuwan maganar kotu, ta karashe tana fad'in
"Yanzu wannan abun kunyar sai da ya fito sarari?"
"Kin ga wannan?"
Alhaji Barau ya mik'a mata takardar da ke hannun Prof Bello, ta ansa tana dubawa, sannan ya ci gaba
"Sammaci ne aka aiko ma kowannenmu dazu-dazun nan, magana ta riga ta isa kotu."
"Ba za ta sabu ba Alhaji, barin kira mai gidan, dole a san abun yi."
Ta dauki waya ta fara kiran Alhajin, kamar ba zai dauka ba, sai ga shi ya daga da sallama yana tambayar ko lafiya.
"Ina fa lafiya. Mai afkuwa ta riga da ta afku."
Kafin yayi wani yunkuri ta gama labarta masa komai.
Fadan da ya fara yi, bai sa tayi mamaki ba, domin a zahiri ya ma fi ta rashin kaunar zuwan maganar kotu, a cewarsa tunda dai tsautsayi ya ritsa da Tareeq d'in, ayi hakuri a bar maganar mana. Bai bata lokaci ba ya datse wayar, ya fara lalubar layin Barr. Jay.
Zaune take ta saka desktop computer da ke ajje gaba, hankalinta gaba d'aya yayi bulaguro a aikin da ya sha mata kai, wani kyakkyawan yaro mai shekarun da baza su haura na Tareeq ba ya shigo da wayarta a hannu.
"Mammy ana kiranki."
Ta d'ago a tsanake tana dubansa da murmushi ta ansa wayar a hannunsa tana fadar
"Na gode handsome nawa."
A sa'a guda ta ansa kiran, ta dora a kunnenta da sallama.
"Barka da wuni Alhaji. Ya aiki."
Tsab ya nemi masifar da ya kira da ita ya rasa, ya kasa gane dalilin sanyin hali irin na Barrister nan, ya kuma rasa dalilin da yasa ya ke daga mata kafa a lokuta da dama.
"Errrnmmm.. Barka dai Barrister."
Da fadar haka ya yi shiru, hakan ya bata damar ci gaba
"Ka ga yadda abu ya koma ko? Ina ta son na kira ma aiki ya sha gabana."
"Amma me sa kika yi mun haka? Bayan na riga na baki uzurina, haba Barrister."
"Kada ka ga laifina Alhaji, na yi iyakar yina kada case din nan ya fita, amma abun ya ci tura, dan har maida case din nayi ma, amma ogana yace sam bai san maganar ba, k'arshe ma ban san ta ya aka aika da report din ma alkali ba. Dan Allah kayi hakuri, nd trust me, nothing gonna happen, zan yi k'ok'arin tsaya ma Tareeq har sai gaskiya tayi halinta."
Ya yi kasake yana saurarenta, a sa'a guda ya aminta da duk wata kalma da ta fito bakinta, ya sauke ajiyar zuciya yana cewa
"Ba wannan ba ne damuwata Barr. Matsalar daya ce, abun ya hado da makwaftana, ban san da wane ido zan kalle su ba."
Shiru tayi na dan wani lokaci, ba komai take ji ba sai tsagwaron tsanar iyaye masu halin Alhaji Badaru. 'Wato ya fi jin ta iyayen mutanen da suka haddasa bakin ciki a zuciyar yaronsa, kan ta yaron da aka zalunta wanda bai ji ba, bai kuma gani ba. Lallai abin mamaki baya karewa.'
"Kina jina kuwa?"
Hakan ya dawo da hankalinta jikinta, ta kai hannu ta shafi sumar yaron da ya kawo mata waya, wanda ya karaso ya dora hannayensa a kanta, yana mai kallon allon computer gabansu. Yadda take jin soyayyar dannata, kusan haka take jin Tareeq a ranta, a sa'a guda tana kwatanta inda a kan yaronnata ne abinda ya samu Tareeq d'in ya faru.
Sai da ta danne bacin ranta, sannan ta fara magana
"Duk makwafcin da ya san ya keta mutuncin yaronka, ina mai tabbatar maka da ba makwafcin gaskiya bane ba, haka zalika idan ma ka ga irinsu, inda hali canja ma kanka mazauni daga kusa da su. Ai irin wadannan mutanen Alhaji, ba mutanen da ya kamata a daga ma kafa bane. Though, nothing I can do about it, tunda dai alkali ya riga ya gama tsaida ranar shari'ah."
Ba don ya gamsu da magana d'aya tata ba, ya sauke numfashi kafin yace
"Kina nufin babu wani abu da zaki iya yi a kai?"
"Babu fa Alhaji, su nemi lawyer kawai mu had'u a kotu ranar shari'ah."
"A gaskiya ni kam ba'a kyauta mun ba, ina dalili."
Bai mata sallama ba ya kashe wayar, sai kuma yanzu yake ta faman bambami, ya kuma rasa kalma daya da zai ce da su Alhaji Barau da ke zaune a palon gidanshi.
Ganin bashi da mafita ya sanya shi kashe wayar gaba d'aya, ya koma dakin taronsu, zuciyarsa sam babu dad'i ko alama.
Bayan shudewar kusan mintuna ashirin suna jiran shigowar kiransa amma shiru, har sai da Hajja Fati ta dauki tata wayar ta fara kira, a bugun farko ta same ta a rufe. Ta k'ara kira, amma labarin dai guda daya ne, ta d'ago a diririce tana yi ma su Engr bayani.
Wannan yasa mutanen fara tunane-tunane, har suna ganin kamar duk laifin na Alhaji Badarun ne. Watak'ila shi ya asassa shigar da k'aran. 'In ya san wata, ai bai san wata ba.'
Cewar zuciyar Alhaji Barau da ya mike a fusace, ya jefi Hajja Fati da mugun kallo, daga bisani ya kada kansa ya fice ya bar sauran a zaune.
"Me zamu jira muma?"
A fadar Prof. Bello sa'adda yake mikewa, hakan yasa Engr. Bukar tashi shima, yana fad'in
"Mum gode Hajiya, idan kun samu damar yin magana da shi, ko da zuwa anjima ne, dan Allah ki kokarta kiran Hajiya dan ki sanar mata."
"In sha Allah Engr. Kar ku samu damuwa."
Suka fita suka samu Alhaji Barau da ke takawa yana sake-saken zuci, ya juyo ya dube su,
"Mutanen nan suna neman rena mana hankali Engr, na riga na yanke shawarar mu samu hatsabibin lawyer wanda ya san ta kan aikinsa domin ya tsaya ma yaranmu. Ko ya kuka gani?"
Prof. Bello ya nisa, ya ce
"Shawarar da nike ta yi kenan, amma tunda ga Barr. Zainab, me zai hana ita ta jagoranci abun?"
"Baza ta iya ba."
Cewar Alhaji Barau, kafin ya ci gaba.
"Ita mace ce, kasan zata yi rauni, gara mu samu wanda bai san yaran nan ba, wanda ko da sun sanar da shi kan sun aikata laifin, ba zai karaya ba, saboda irin makuden kudaden da za mu shaka masa. Ko ya kuka gani?"
"Maganarka tana kan hanya gaskiya, nima na fi ganin a samu bare wanda bai sansun ba."
"Babu laifi, hakan ma ya yi. Yanzu menene abin yi?"
Cewar Prof. Bello yana dubansu.
"Ku bar komai a hannuna, zanyi waya da wani hatsabibin Barr. Hisham da ke Abuja, ina mai tabbatar muku ba zai taba watsa mana k'asa a ido ba. Idan ya shigo goben, sai mu had'u muyi magana da shi."
Duk gaba dayansu sun amince da shawarar ta Alhaji Barau, daga nan suka yi sallama, kowa ya kama hanyar gidansa, bayan sun jaddada ma Prof. Bello cewar direbobinsu su same su a gida.
****
Bak'in gilashin da ya boye idanunsa, bai hana damuwar da ke kasan zuciyarsa bayyana muraran a fili ba, jikinnasa tamkar wanda bashi da lakka, haka yake cire foot mats din da ke shimfide k'asar motar yana wurgarwa a tsakiyar car wash din.
"Oga Khalid ai ba sai ka ba kanka wahalar fitarwa ba, duk da ka bari ma zan fitar da su. In sha Allah daga yau baza ka k'ara kai wankin mota ko ina ba in har ba wurin nan bane ba."
"Motar ce tayi datti sosai, dan ba zan iya tuna sadda aka wanke ta ba, dan Allah ka tabbatar ka wanke har saman seats din nan."
Ya karashe yana mai zaro abin takawar da ke shimfide a gaba. K'aran faduwar abu da ya ji ne ya sanya shi maida dubansa cikin motar, bakar Samsung galaxy wacce bai tantance model dinta ba ya ga ta fad'o, sakamakon janyo abun takawar da yayi tun k'arfi. Cikin mamaki da tunanin mamallakin wayar ya sa hannu ya dauka, ya latsa wayar ko da haske zai kawo, amma rashin sa'a sai ya same ta a kashe. Ba tare da damuwa ba ya jefa ta aljihu, kafin ya k'arasa fitar da abubuwan, ya d'ago yana kallon mai wankin motar
"Yawwa, zan dawo zuwa anjima abokina."
Daga nan ya wuce gida. Yana isa gida dakinsa ya zarce ya jona wayar jikin chaji, dan dama akwai wuta, sai da ta d'auki yan dakiku kafin ta kawo, hakan ke nuni da ta d'auki dogon lokaci a kashen. Bayan kamar mintina ashirin, sannan ya bud'e ta, tunaninsa ko zai samu abinda zai fallasa asirin mamallakinta, sai dai babu hoto ko d'aya, hakan ya sanya shi lekawa akwatin adana sakonni. Duk yawancin sakonnin cikin inbox din numbers ne kawai babu suna, sai wasu daga kamfanin MTN, wasu kuwa na VTU ne da akan saka kati ta hanyar amfani da shi. Kamar ya fita ya zabi lamba daya daga cikin lambobin da babu suna ya kira, sai dai zai zuciyarsa ta fi aminta kan ya k'ara bincika k'asar sakonnin, cikin sa'a ya hangi sako daga wata lamba da aka adana sunan mamallakinta.
A gaggauce ya bud'e sakon, a karo guda ya zare gilashin da ya lullube fararen idanunsa, ya na mai ci gaba da dubawa cikin karaji da tsantsar tashin hankalin da zuciyarsa kawai, ba za ta iya dauka ba, dole ya fallasu saman fuskarsa.
*****
Hankalinsa tashe ya shigo, sau daya ya kai duba inda Tareeq ke kwance ya d'auke kansa, a haka ya fara bincike palon, gaba daya cushions din kujerun da ke zagaye sai da ya watsar da su a k'asa.
Tareeq da ke kwance a gefe yana kallon yadda fuskar dan uwannasa ta canja, ya rasa me ke hana shi walwala.
Duk da kasancewarshi ba ma'abocin dariya ba, amma a lokutan baya idan aka yi sa'ar faruwar wani abun dariyar ya kan dan dara, sai dai a yanzu tun bayan afkuwar al'amarin nan na Tareeq, ba zai iya tuna rana daya da ya samu sukuni a birnin zuciyarsa ba, balle har ya murmusa da fatar bakinsa.
Kasar carpet ya zauna ya tallabi kansa, ya rasa menene yake masa dad'i a gaba d'aya rayuwarsa, Hajja Fati ta fito tana duban yadda aka hargitse mata palo, sama ya dawo k'asa.
Bata damu da yanayin da yaronnata ke ciki ba, ta yarfa hannu tana fadar
"Me zan gani haka? Wane irin shirme ke damunka kuma yau da zaka hargitsa mun wuri haka?"
Banza yayi tamkar ba zai ansa ta ba, haka shima Tareeq wanda ya dawo wani gashi nan ya ke binta da idanu, dan babu kalma daya da zai iya bata ansa da ita.
"Mukhtar fa! Ko ba da kai nike magana ba?"
"Haba Maa daAllah, wayata nike nema mana, kema kinsan bayan da haka babu abinda zai zaunar da ni a wurin nan mana."
"Saboda kana neman wata wayarka can, shine zaka hargitsa mun palo haka? To baka isa ba, tashi ka mayar mun da cushion dina yadda ka gansu. Ina ruwana da wata banzar wayarka can."
"Banzar waya can?"
Ya mik'e yana maganar a fusace, da idanunsa da suka kankance sun kuma canja kala zuwa wani irin ja, mai ban tsoro.
"Ko zaka dake ni ne dan nace wata sheg*yar waya? Wata tsiya ce a wayar da zata sa ka tsaya kana daga mun murya."
Ya kare mata kallo tsab, kafin ya saki dan karamin tsaki, sannan ya juya ya fita ba tare da ya gyara cushion din ba. Haka ta ci gaba da fad'anta, daga k'arshe tayi kiran Asabe domin ta gyara kujerun.
*****
A babban palon Alhaji Barau duk suke zaune, Barr. Hisham wanda kallo daya zaka masa ka san tabbas ba karamin hatsabibin bane kamar yadda Alhajin ya fad'a, domin a zahirance ilimin da ya kwankwada ya bayyanar da kansa. Matashi ne wanda da wuya idan boko ta barshi ya yi aure, asalin bafulatani ne, kamar yadda sumar kansa ta nuna.
K'afarsa daya ya dauka, ya dora kan daya bayan ya gama sauraren bayanan da su Engr suka kora masa.
Lafiyayyen murmushi ya saki ta gefen kumatunsa, ya sauke wayar da ke hannunsa a kan teburin da aka cika samarsa da kayan motsa baki, ya kai duba ga su Alhaji da suka mik'a dukkan hankulansu suna son jin ta bakinsa.
"In dai wannan ne kawai Alhaji, ba zai taba zama problem a gare ni ba. Cuz murder case na gama last week din nan, kuma yaron da na fitar ya tabbatar mun shi yayi kisan, dan haka ina mai tabbatar muku wannan zai zama cikin cases mafi sauki da na taba jagoranta a gaba d'aya rayuwata. So trust me, I'll bring your boys back home."
Ya karashe sa'ar da ya d'auki kofin lemu ya kurba a bakinsa. Alhaji ya murmusa yana duban su Professor.
"Me na fad'a muku? Ni na san wanene Barr. Hisham."
Wannan batu na Alhaji ya k'ara hura kan Barristern, hakan ya sanya shi sakin wadataccen murmushi, ya mik'e yana gyara zaman necktie d'insa, ya d'auki briefcase dinshi yana fad'in
"Zan je in ga yaran a prison."
Daga nan duk suka mik'e suma, dan dama sun gama yin tsada, Alhajin yana fad'in ya saurari alert a account dinsa. Ya yi musu sallama ya fita cikin takunsa na masu takama da tunkaho.
Alal hak'ika ganin Barr. Hisham ya kwantar da zuciyar iyayen yaran ba kadan ba, domin yanayinsa ya fallasar da kalar jajircewarshi, hakan yasa suka rabu zuciyoyinsu sawai, ba ma ya Prof. Bello wanda wannan ya taimaka wurin rage jin zafin matarsa, wacce a jiya ma sai da suka kai ruwa rana saboda maganar.
www.lubabatumaitafsir.com
_This is for Snowwhite and Maman Khayree. Guys I appreciate everything, thanks a ton.._
Lubbatu ce..
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{15}
Hankalinsa kaf, yayi nisan kiwon da bai san ta ya zai dawo jikinsa ba, tabbas ba gizau idanunsa ke masa ba, ya k'ara karanta sakon yana mai jin wata lema-lema na bin kumatunsa, ya sanya hannu ya shafi fuskar, inda ya tabbatar da hawaye ne suke kwarara babu kakkautawa.
'Shin wai wacce irin duniya muke ciki? Ta ya dan uwan da kuka fito ciki d'aya zai iya yin abinda Mukhee ya yi ga Tareeq? Shin lefin na wanene? Na yaran ne ko na iyayensu?'
Tambayoyi barkatai, haka suka dinga kaiwa suna kawowa a zuciyar Khalid.
'Menene abin yi?'
Ya tambayi zuciyarsa da ke harbawa da sauri-sauri, tamkar zata faso faffadan kirjinsa ta fad'o k'asa.
'I need to see Khamis ASAP'
Ya tunatar da kanshi, hakan yasa ya mike da sauri yana shafe idanunsa, tare da zira takalmansa ya wuce zuwa k'ofar gida.
Mashin din Jarma da ke zaune a gefe ya ansa ya fara rafsa gudu, tamkar wanda zai bar garin na Kaduna, bai tsaya ba, har sai da ya isa police headquarter, sannan ya tsagaita ya fito ya nemi izinin ganawa da Khamis a wurin yan sandan da ya samu a tsaitsaye.
Zaune ya same shi ya dukufa sosai a rubutun report din wani case, ya shigo a hankali tamkar wanda kwai ya fashe wa a ruwan ciki, sallamarsa a ciki-ciki, ya samu gefe ya zauna yana duban Khamis.
"Khalid."
Ya yi maganar yana mik'a masa hannu, ya miko da nasa suka gaisa, sai dai bakinsa ya gagara furta ko da kalma d'aya.
"Lafiya?"
Khamis ya tambaya bayan ya dora biron hannunsa saman teburin gabansa, ya tallabi habarsa, tare da zuba idanunsa a kan Khalid din.
Hannu ya saka a aljihu ya laluba wayar da ya tabbatar ta Mukhee ce, ya zaro a hankali, yana k'ok'arin mik'a ta ga Khamis, a sa'a guda wata zuciyar ta gargade shi a kan illar abinda ya ke shirin aikatawar.
Wayar ya mayar a aljihu, ya samo murmushin dole ya dora a fuskarsa,
"Na zo ne inji inda magana ta kwana."
"Magana ai ta riga ta fita hannuna Khalid, I'm sure yanzu an gama tsaida ranar shari'ah, wata Barr. Jameela ce zata tsaya ma Tareeq d'in, ko jiya kamar haka tazo tayi mun wasu tambayoyi, ya aka yi baka da labari?"
"Mun samu problem da shi brother din nawa kan maganar ai, so shi yayi insisting kan sai na bar masa gidansa, shi yasa ni kuma kawai na koma gida, shi yasa ban samu labarin komai da ake ciki ba."
"Haka ne, da kuma laifina da ban kira na sanar maka ba, hakuri dai zaka yi, kasan aikin lada sai wanda ya daure."
"Haka ne kam, amma zan samu ko da number ita Barrister din ne a wurinka please?"
"No, bani da number ta gaskiya, but I'm sure zata neme ka dole ai, ko ka manta kaine zaka yi shaidar halin da ka samu Tareeq a sadda ka kaishi asibiti?"
"Haka ne, bari zan jira har lokacin to."
Ya mik'e ya yi masa sallama, zuciyarsa na cikin hali na tarabbabin rashin sanar da shi komai a kan sakonnin da ya samu a wayar ta Mukhee.
Gida ya koma, zuciya da gangar jikinsa sam babu kuzari, yana kwance k'asar carpet, wayarsa ta d'auki k'ara, yasa hannu ya cire jikin chaji yana duba bakuwar number da bai san mai ita ba. Sallama ya yi bayan ya daga wayar, aka ansa ta d'ayan bangaren, tare da fad'in
"Sunana Barr. Jameela. Dan Allah ko ina magana da Khalid ne?"
Hakan ya sanya shi mikewa zaune da sauri, ya ansa mata da shi ne, inda ta mik'a bukatarta ta son ganinshi idan babu damuwa.
Daman zaman jiran kirannata ya ke, danhaka bai bata lokaci ba ya ansa mata, yana tambayar inda zai zo ya same ta.
Motarshi ya dauka daga wurin wanki a gaggauce ya je ya same ta a wurin da ta kwatanta masa, bayan sun gaisa, ta fara jera masa tambayoyi, ta nan ne ta gano alakarshi da Alhaji Badaru, a nan ne kuma ya yi mata bayanin komai dangane da rayuwar gidan Alhaji Badarun, da sa'insar da ta shiga tsakaninsu, da kuma jajircewar da ya yi kan dole maganar ta isa ga yan sanda, illa abu daya da ya boye mata, duk kuwa da yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da son ya nuna mata wayar Mukhtar da ya tsinta.
Ta yi shiru bayan ta gama saurarensa, tabbas dama zuciyarta na raya mata da akwai wani gagarumin abu da mutanen suke boyewa, sai dai ta ci alwashin taimakon Tareeq ta ko wanne irin hali.
Daga nan sallama suka yi ma juna, bayan ta shaida masa zata k'ara kiransa zuwa wani lokaci.
****
Sanye yake cikin bakaken suit da suka anshi farar fatarsa, sai farar riga daga ciki, da bakin rufaffen takalmi sanye a k'afarsa. Ya daidaita zaman necktie d'insa, a sa'a guda ya dauki briefcase din da ke ajje a kujerar mai zaman banza, sannan ya fito ya tasan ma k'ofar shiga prison d'in.
Ba tare da bata lokaci ba, akai masa iso har zuwa dan k'aramin d'akin da su Mubee suke, kamanninsu tsab, sun fita daga hayyacinsu.
A kujerar da ke fuskantarsu ya zauna, ya gabatar da kanshi, a matsayin lauyan da zai kare su, sannan ya k'ara da cewar
"Kada ku samu damuwa, dan haka ku sanar da ni komai da kuka sani dangane da abinda ake tuhumarku."
Deeni ne ya muskuta zai fara jawabi, a sa'a guda Sino ya watsa masa wani mugun kallon da ya sanya shi hadiye maganarshi ba tare da ya shirya ba.
"Ehnnn, ina saurarenku."
Barr. Hisham ya yi maganar yana dubansu.
"Mu fa bamu san komai ba akai Barrister, wallahi sharri kawai aka mana."
Sino ya fad'a yana matse kwalla, Mubee ya anshe
"Wallahi sharri aka mana, kawai dan dai mu dama can an tsane mu."
Deeni kam kuka ya fashe da shi, ya kama hannun Barr. Hisham ya rik'e karkadam,
"Dan Allah ka taimaka ka fitar da mu daga wurin nan."
"It's okay, it's okay please. Ya isa haka. Kun tabbatar da gaskiyar abinda kuka fad'a?"
Duk suka girgiza kansu alamar gaskiyarsu kenan, sai dai Barr. Hisham ya jisu ne kawai, ba wai dan ya yarda da abinda suka fad'a masa ba.
Tambayoyi ya cigaba da yi musu, inda suka dinga bashi ansa daya bayan daya, daga bisani ya mik'e yana fad'in,
"Zan k'ara dawowa kafin ranar da za'a fara sauraren shari'ah."
Ya juya ya fita, yayin da guardrobber ya tusa keyarsu, ya maida su ciki.
****
Bai damu da gaisuwar da 'yan sandan ke ta faman mik'a masa ba, ya baza babbar rigar danyar shaddar jikinsa, wacce kamanninta kadai sun isa su kayyade adadin dinbin tsadarta. Ya tura kai ofishin Commissioner Badamasi tare da sallama yana kallon setin da kujerarsa take, sai dai baya zaune a wurin.
Ta bayanshi ya tsinkayi gyaran murya, ya juya da sauri ya sauke idanunsa cikin na C.P Badamasi wanda ya fito daga bandakin dake cikin ofishin. Ya washe baki yana fad'in
"Barka da zuwa Yallabai. Ya kokari?"
Ya karashe yana mik'a masa hannu, yayin da Alhaji Barau ya noke nashi hannun, yana ci gaba da watsa masa wani malalacin kallo.
"Ba wannan ne ke tafe da ni ba. Kudina da na baka nike son ka fito mun da su yanzu ba wai sai anjima ba, in kuma ba haka ba in fallasa asirinka kowa ma ya ji, kasan ba damuwata ba ce ba."
Murmushin da ke kunshe da labbansa ya yi saurin gushewa, ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar Alhajin wanda babu ko da digon sassauci a fuskarsa.
"Duk me ya yi zafi haka Alhaji?"
A fusace ya dan buga teburin da ya mamaye kusan rabin ofishin, cikin daga murya ya ce
"Kada ka raina tunanina Badamasi, sanin kanka ne bana jerin mutanen da ake takawa a wanye lafiya. Bayan ka bari an wuce mun da yaro prison baka yi komai a kai ba, sannan ka tsaya nan kana neman raina hankalina? Ba zan d'auki wannan cin kashin ba ko alama. Ka fito mun da kudina kawai shine rufin asirinka."
Ba k'aramin tashin hankali bane ya ziyarci zuciyar Commissioner Badamasi, ya karashe yana tunanin ta yadda aka yi Khamis ya samu guts din fitar da FIR din da ya yi masa barazanar rasa aikinsa ta dalilinshi. 'Tabbas zan shayar da shi zumar mamaki.'
Wannan ne furucin da yayi a k'asar zuciyarsa, kafin ya maida hankalinsa ga Alhaji wanda alamunsa kaf, na rashin mutunci ne.
"Ka yi hakuri Alhaji, wallahi ba ni da masaniyar abinda ya faru gaba d'aya, amma nayi alkawarin sai na koya ma yaron nan hankali, bai kuma isa ya ja da ni ya zauna lafiya ba."
"Me ye ruwana a cikin wannan kuma?"
Alhaji ya fad'a yana watsa hannu, sannan ya ci gaba
"Ba ni da sauran matsala da kai da kuratan yan sandanka, ka ba ni kudina kawai, shine kwanciyar hankalinka."
Shiru kawai Commissioner ya yi, ya rasa menene abinda ke yi masa dad'i.
"Shikenan, ka yi hak'urin zuwa anjima, da kaina zan zo har gida in dawo maka da kudinka. In sha Allahu."
"Da dai ya fi maka, dan ni bana asara ko da kuwa ta yawun bacci ne."
Ya buga rigarsa ya fice, tare da banka k'ofar yana faman banbami a k'asar zuciyarsa. Da sauri Commissioner ya fito ya yi kiran wani dan sanda ya umarce sa da ya yi masa kiran Inspector Khamis.
Kai tsaye ya shigo ofishin, dan dama ya san wannan ranar tana nan zuwa, sai dai ya tanadi nashi shirin, wanda yake jin shine kawai zaiyi maganin kudirin da Commissioner ya ke da a kansa.
Sai da ya sara masa, sannan ya ce
"You call for me Sir."
"Yes!"
Ya bashi ansa a gajerce, cikin tsananin fushin da ya wanzu a saman fuskarsa.
"How dare you? Kai ka isa ince ga abinda za ayi ka canja mun Khamis? Kai din duk guda nawa ne? Ka gaggauta sanar mun wanda ya shige maka kayi presenting FIR din da na yi maka hanin fitarsa daga headquarter nan. Oyaa, ina saurarenka."
Kan Khamis a k'asa, ya fara magana cikin taushin murya, ba tare da ya kuma girgiza daga fadan na C.P ba.
"I'm sorry Sir."
"Sorry for yourself Inspector. Ka yi abinda na ce maka tun muna shaida juna."
Ya shafi gefen fuskarsa, a hankali ya d'ago suka had'a ido da shi, ya sauke kansa kafin ya fara magana.
"Babu wani wanda ya taimaka mun Sir. Ni naje da kaina nayi presenting ma DPP. A shirye nike da ansar duk wani hukunci da zai zo daga gare ka, sai dai kaima ka shirya ansar naka hukuncin daga inda ya kamata."
"Heeey! Enough of this bullsh*t. What are you trying to say? Ka sanar da DPP abinda ke faruwa?"
Kanshi tsaye, ya ansa da
"I told him. Sai dai na roki alfarmar ya dage maganar har zuwa muga naka hukuncin da zaka dauka."
"God of Mercy."
Cewar Commissioner yana kewaya tangamemen ofishinnasa, wanda ya wadatu da kayan more rayuwa. Cikin borin kunya ya ke nuna shi,
"Sai nayi maganinka Khamis, sai na gwada maka taurin kai ba al'ada mai kyau ba ce. Get out of my sight, you stubborn man."
"Sorry Sir."
Ya fad'a bayan ya kame ya sara masa, ya fice yana gintse dariyar da ta taho masa, ya koma ofishinsa, domin ya san ya riga ya gama daure duk wata jijiya da ke jikin C.P Badamasi.
*****
Cikin unguwar ta fara zagayawa bayan ta fito gidan na Alhaji Badaru. Tunanin irin artabun da suka sha da Tareeq take yi, wanda ya gagara ansa ko da kalilan ne daga tambayoyin da ta dunga jera masa, sai dai ta samu kwarin gwiwa daga irin amsoshin da Mal. Idi mai gadi ya bata.
A hankali take takawa, ko Allah zai sa ta samu ko da mutum daya ne, wanda zata iya jin ta bakinsa dangane da dabi'u da kuma halayyar su Deeni da mutanen unguwar.
Wani buzu ta hanga zaune a nesa kadan da gidansu Tareeq yana sauraren radiyo, da alama mai gadi ne a k'ofar gidan da yake zaune. Ta k'arasa suka gaisa, cikin hausarsa da bata fita sosai.
"Baba dan Allah Idan babu damuwa zan dan maka wasu tambayoyi."
"Babu laifi yarinya, lafiya dai ko?"
"Lafiya lau Baba. Ai kasan abinda ya faru da yaron nan makwafcinku dan gidan Alhaji Badaru ba?"
"Eh to na ji dai ana labarin a unguwa."
"Eh zaka ji labari kam, tunda ai yaran da suka yi abun yan unguwar nan ne."
"Kai haba da Allah?"
Buzu ya fad'a idanunsa waje yana kallonta.
"Wallahi Baba. Su wani Hassan yaran gidan tsohon ministan can, kuma dan rashin imani, suka kawo shi nan suka shimfidar a gefen titi, wanda suka tsince shi ma sun zata ko ya rasu."
Shiru Buzu yayi, ya fad'a dogon tunani, har sai da Barr. Jay ta kuma magana sannan ya dago
"Za su aika yaran nan, domin takadarai ne na kirkin gaske. Yaushe ne abun ya faru?"
"Kana nufin basa jin magana dama? Zai kai kamar wata guda yanzu."
"Basa jin magana, tabbas. Haka kuma in har faruwar abun zai kai wata guda, to kuwa tabbas naga sadda motar shi yaron ministan ta tsaya a can."
Ya yi nuni da nesa da inda suke kadan, sannan ya ci gaba
"Sai kuma naga sun fito da abu sun matsa wurin kwalbatin can sun yar da shi, amma wallahi ban kawo ko a raina cewar mutum ne ba, naga sun koma sun ja motar da sauri sun tafi."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Baba ka tabbatar da abinda kake fad'a?"
"Ban sanki ba yarinya, babu dalilin da zai sa in miki karya."
Taku biyu zuwa ukku ta k'ara yi, ta matso daf da shi ta duk'a
"Ka tabbatar ko kotu na gayyace ka, zaka iya fadar irin abun da ka fad'a mun a nan?"
"Shakka babu, domin Allah ya san na gansu, dan haka zan iya sheda ko a gaban wanene."
"Alhamdulillah Ya Allah."
Tayi maganar a bayyane, fuskarta d'auke da murmushi. Number Buzun ta ansa ta adana a wayarta, tayi mishi sallama kafin ta wuce inda tayi parking motarta.
*****
Gidannasu shiru tamkar babu halittar dan adam da ke rayuwa a ciki, bai yi mamaki ba, dan ya san sauran yaran duk suna makaranta, haka ya tura kai cikin palon kamar yadda ya saba ba tare da sallama ba.
Tareeq ne kadai kwance yana bacci. Duk kuma da kasancewar lokacin bayan sallar la'asar, ba shi ya sanya Alhaji Badarun damuwa ba, haka ya sanya kai zuwa ciki. Har zuwa yanzu bai ji alamar motsin mutane ba, ya dan daga murya yana kiran Hajja Fati, amma shiru bai samu ansar kowa ba.
Ya dai san yaran suna makaranta, tana yiwuwa Hajja Fati bata gidan, Asabe fa?
Ya tambayi zuciyarsa. Bai samu ansar tambayar tasa ba, hakan ya sa ya yanke shawarar karasawa d'akin Hajja Fatin.
Kallon rashin sani, mai hade da na tuhuma ya ke bin matashiyar budurwar da ke mike samar gadon matarshi da, Hajja Fati wacce fitowarta wanka kenan, tayi kicibis da Alhajin wanda dama al'adarsa ce rashin kiran waya a duk sadda zai dawo gida.
Da sauri budurwar ta mike tana mai jan mayafi domin lullube kanta da ya ke bayyane.
"Ashe ka dawo?"
Hajja Fati ta fad'a muryarta na kyarma, ya juya ya fice kafin ta biyo bayansa yana fad'in
"Na dawo ina ta sallama naji shiru, dama zan tambaye ki ya kuka kare da su Alhaji Barau?"
A diririce ta shiga yi masa bayani, tana maganar tamkar wacce aka yi ma dole, kamar kuma hankalinta baya tare da ita. Ya rasa menene dalilinta na shiga damuwa tunda ta ganshi, domin kuwa fuskarta ta fallasa sirrin zuciyarta.
Sai da ta gama sannan yace
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya fa, me faru?"
"Naga kamar kina cikin tashin hankali."
"Ba komai fa."
"To, ita kuma waccen ta d'aki wacece? Naga dai kamar budurwa ma ce, balle inyi tunanin ko kawarki ce."
"Ehhh? Uhnnmm.. Ai.. ai kanwar Hajiya Maryam ce ta zo daga Kano, shine tace ta zo ta gaishe ni."
"Ya yi kyau. Idan kuna da abinci a taimako mun da shi, domin yunwa nike ji ba kadan ba."
"Aiko dai babu, na rana ya kare kuma ba a gama na dare ba, sai dai ko indomie in zaka ci in sa Asabe ta dora?"
"Ki barshi kawai."
Daga nan ya wuce dakinsa, itama ta juya tana tabe baki, ta koma dakinnata inda ta samu budurwa ta gama kimtsa kanta, tana sagale da jaka a kafadarta.
Ta kalle ta da murmushi kunshe a bakinta, tana mai kankan da idanunta.
"Ban gane ba?"
Sai da tayi farr da idanunta, kafin ta tako ta zauna a gefenta, fuskarta a shagwabe, sannan ta fara magana bayan ta dora kanta a kafadar Hajja Fatin.
"Naga Alhaji ya dawo, kinga ai gara in had'a kayana tun ba a kore ni ba."
Ta sa hannu ta shafi kan yar budurwar
"Wallahi ban san zai dawo yau ba, cuz wasu lokutan ya kan kwashi sati har biyu baya nan, amma kar ki damu, zan shigo ta gidan Hajiya Maryam ai zuwa gobe, so ki kula mun da kanki kinji?"
Ta mike ta fara tafiya, jin takun takalma na dumfaro d'akin na Hajja Fati.
Mikewa itama tayi, ta isa gaban wardrobe dinta ta fito da kudi ta mik'a mata tana fad'in
"Ki gaishe da Hajiya Maryam din. A dai-dai lokacin Zulaiha ta shigo, ta bi bayan budurwar da kallo yayin da ta k'araso ta zauna a gefen gadon mahaifiyartata.
"Maaa wannan fa?"
A kufule ta juyo tana dubanta,
"Ke kuma meye naki a ciki?"
"Naga ban taba saninta da ke ba ne."
"Ai ni da yake na san wadanda kike hudda da ba? Ko kuma na taba saka ki gaba na tsare ina bin diddigin inda kike zuwa kullun da sai kin fita a gidan nan."
"To? Daga tambaya kuma sai abu ya zama fad'a? Uhunmm. Ni kinga tafiyata."
"Ki gaida su, ina dalili da zaki saka ni a gaba da tambayoyi sai kace yar jarida."
Ta maida kanta ga shafa manta, kafin ta ja tsaki, ta d'auki waya ta fara kiran aminiyarta Hajiya Maryam.
***KOTU.
www.lubabatumaitafsir.com
www.wattpad.com/iLubiee
_This is for my biggest eff right from day one. No one but Ummy Sama aka Mrs. Gentle. She's gentle herself. I appreciate everything Mrs. Thank you._
Lubbatu ce..
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{16}
'FEDERAL HIGH COURT KADUNA.'
Ta maimaita a k'asar zuciyarta, bayan ta gyara parking.
Cike da kwarin gwiwa ta fito sanye da bakin long pencil skirt, leith top dinta fara, mai V-neck, yayin da farin jabot dinta ya taimaka wurin lullube wuyanta, da gaba d'aya kirjinta da rigar ta bayyanar. Bakin gyalenta mai tambarin Channel da adon fararen flowers ta yane kanta da, sannan ta dora jacket dinta, hannunta na dama rik'e da handbag dinta, yayin da wig da bak'ar gown dinta ke rik'e a hannunta na hagu.
Kusan duk wani da shari'ar ta shafa ya hallara a wurin, hatta da su Deeni an iso da su. Bata damu da kallon da Barr. Hisham ke yi mata ba, ta wuce ciki tare da abokin aikinta Barr. Nasib.
Ta 6angaren dama Alhaji Badaru ne da Hajja Fati, Khalid sai Zulaiha. Ta 6angaren hagu kuwa Engr. Bukar ne da iyalinsa, Alhaji Barau sai Yayan Sino, kasancewar mahaifiyarsa basa tare da Alhajin, mutuniyar Taraba ce, sai kuma Prof. Bello tare da Barr. Zainab, da yayyen Deeni mata su biyu.
Kallon da 6angarorin biyu suke jifar junansu da, ya katse lokacin da alkali ya shigo, kowa da ke zaune ya mik'e, kamar yadda dokar kotun ta tanadar.
Bayan Alkali ya zauna, sannan sauran jama'ar wurin duk suka koma mazauninsu, hakan ya ba Registrar da ke zaune gaban teburin alkalin yana fuskantar al'ummar cikin kotun damar mik'ewa ya ce
"Case No.24 ku matso kusa."
A haka aka shigo da su Deeni, aka zarce da su wurin da ya kamace su, daga nan Registrar ya gyara rikon farar takardar da ke hannunsa, ya fara karantawa kamar haka:
"A yau ranar talata, ashirin da d'aya ga watan daya, shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, zamu saurari k'ara tsakanin Director of Public Prosecution, da Mubarak Garba Bukar, mai shekaru goma sha tara, Hassan Alhaji Barau, mai shekaru ashirin da daya, tare da Zahraddeen Bello Hassan, mai shekaru goma sha tara, wadanda ake zargin yin fyade ga Tareeq Alhaji Badaru mai shekara goma sha d'aya a duniya."
Ya juya cikin girmamawa ya mik'a takardar ga alkali kafin ya koma mazauninsa.
Bayan yan rubuce rubuce alkalin ya dago tare da fadin
"Ina lawyer wanda ya ke k'ara?"
Jay ta mike cikin natsuwa da girmamawa, ta rissina kadan.
"My Lord, Sunana Barr. Jameela Ahmad. Ni ce Lawyer wanda ya ke k'ara. Tare dani akwai Barr. Nasib Mukhtar."
Barr. Nasib dake zaune kusa da ita ya mike ya rissina tare da fadin
"My Lord."
Bayan sun zauna aka bukaci ganin Lauyan wanda ake k'ara.
Barr. Hisham ya saki dan guntun murmushi ta gefen kumatunsa, ya mik'e cike da izza.
"Sunana Barr. Hisham Saifullah. Ni ne lawyern da zai kare wadanda ake k'ara."
Bayan ya zauna alkali ya d'ago tare da kai dubansa setin da su Mubee ke tsaye ya ce
"Kun ji abinda ake k'ararku da shi. How do you plead? Guilty or not?"
A tare suka hada baki wurin fadin
"Wallahi ba mu bane."
Kamar yadda Barr. Hisham ya gargade su, ana gobe za'a shiga kotun. Hakan da suka yi ya sanya shi sakin dan gajeran murmushi, wanda daga shi sai zuciyarsa kawai suka san manufarshi.
Cikin tsanaki alkalin ya tsaida idanunsa a kansu, daga bisani ya gyara zaman farin tabaran da ke manne da fuskarsa, ya duk'a yana mai ci gaba da wasu 'yan rubuce-rubuce, kafin ya d'ago yana duban sashen da Barr. Jay ke zaune.
"Prosecution counsel, are you ready?"
"Yes My Lord."
Ta fad'a da azama, cikin muryarta mai cike da kwarin gwiwa.
"You can proceed."
Alkalin ya ce da ita, a sa'a guda ta mike, ta fito gaban kotun cikin tsanaki, ta kai kallonta ga alkalin wanda shima din ita ya ke kallo.
"A ranar Ashirin da biyar ga watan sha biyu shekara ta dubu biyu da goma sha shidda, mutanen nan da ke tsaye gaban kotu, sun aikata laifin fyade ga dan karamin yaro mai shekaru goma sha daya. Hukuncin laifin fyade ya zo a section 282&284 na Penal Code and Child Sexual Abuse."
Ta dan yi taku d'aya zuwa ukku, cike da confidence, sannan ta ci gaba.
"My Lord zaluncin da suka yi masa ya sa6a ma Fundamental Human Right da ke chapter IV na 1999 Constitution wanda ya hada da section 33 Right to Dignity of Human Person. Ina neman alfarmar wannan kotu mai adalci, da ta ba ni dama domin gabatar da sheduna."
Alkalin ya d'ago yana fuskantarta,
"Kotu ta baki dama."
"Na gode My Lord."
Ta koma gaban teburinta, inda ta fito da wasu takardu, kafin ta juya tana fad'in
"Wannan medical report ne wanda likitan da ya fara duba Tareeq ya rubuta, wannan kuma wanda muka yi ne bayan mun dauko Tareeq, daga asibitin da ya shafe sati ukku yana kwance."
Ta mik'a report din ma Registrar, ya mik'e ya isar da shi ga alkali. Ya ansa yana dubawa, hakan ya ba ta damar ci gaba da fadin
"My Lord, idan aka yi duba ga sakamakon asibitin da na gabatar, za'a ga semen din mutum biyu ne aka samu a jikinshi. A tare da ni akwai hotunan raunukan da ya samu, wanda duk mai imanin da ya ga ni, zai tabbatar Tareeq ba k'aramar azaba ya sha a hannun mutanen ba."
Ta kuma mika hotunan gare shi, sannan ta ci gaba.
"Da wannan nike rokon wannan kotu mai adalci da ta yi adalcinta ga Tareeq, ta hanyar hukunta wadannan criminals din, domin ya zama izna ga masu hali irinnasu."
Ta k'arashe tana nuni da setin da su Mubee suke, sai dai kafin tayi wani motsi, tuni Barr. Hisham ya mik'e yana fad'in
"Objection My Lord. Barr. Jameela bata da damar da zata kira clients dina as criminals, saboda bata da hujjar da zai sa ta zartar da hakan, har yanzu a matsayin suspects suke."
Alkali ya d'ago ya kai dubansa gare ta.
"Ki kula da furucinki Barrister."
"Thank you My Lord."
Ta fad'a bayan ta rissinar da kanta, sannan ta koma ta zauna, ya d'ago yana kallon Barr. Hisham.
"Lauyan wanda ake k'ara, ko kana da abun cewa?"
"Yes My Lord."
Ya fada bayan ya mik'e ya fita gaban kotun, ya dai-daita tsayuwarsa, kafin ya fara magana cikin k'warewa da sanin makamar aikinsa.
"My Lord, medical report da Barr. Jameela tayi presenting, ba shi ya ke nuni da wadanda ake zargin su suka aikata laifin da ake tuhumarsu ba, cuz babu inda alama ta nuna cewar su din ne suka aikata laifin, kamar yadda ta bayyana ma kotu cewar semen din mutum biyu bincikenta ya nuna mata, a nan kuma ta gabatar da mutum ukku a matsayin suspects dinta."
Ya murmusa, kafin ya ci gaba.
"Duk wani mai hankali idan yayi duba ga labarin da Barr. Jameela ta bayar, zai tabbatar da cewar bata da madafa, haka zalika k'age kawai take son dorawa a kan clients dina. Cuz idan tace semen din mutum biyu ta gani jikin victim d'in, mutum dayan da ya yi saura, da laifin me take zarginshi? That is to say idan har da gaske crime din ya faru ma."
Ya gyara tsayuwarsa, ya juya yana fuskantar alkalin, sannan ya k'ara da cewar
"Da wannan nike rokon wannan kotu mai alfarma, da tayi duba ga wannan rashin madafa na Barr. Jameela, ta yi watsi da case din nan."
Ya rissina cikin salonsa, kumatunsa kunshe da makirin murmushin da ya k'awata santalar fuskarsa.
Cikin tashin hankalin jin kalaman Barr. Hisham Jay ta mik'e,
"My Lord, Barr. Hisham ba shi da damar da zai yanke hukunci kai tsaye, wannan huruminka ne. Haka zalika idan aka yi la'akari da report din da na yi presenting, ba na private Hospital ba ne kadai. Akwai na SARC Division, wanda gwamnati ta tanadar ma rape victims, inda kwararrun likitoci suka sake duba shi, wanda duk muna da masaniyar ba za a taba samun fake result ba."
Ta karashe da muryarta na karkarwa, daga bisani ta d'auke idonta daga duban jama'ar cikin kotun, ta maida kai ga alkalin, sannan ta ci gaba.
"My Lord, ina neman alfarmar kotu da ta bani dama domin gabatar da shedata ta biyu."
Sai da alkalin ya yi dogon rubutu, ya d'ago da hannunsa mai rik'e da biro ya ce
"Kotu ta baki dama."
Bayan samun izinin Alkali, ta nemi ganin Khalid da Malam Idi, wanda ba su bata lokaci ba wurin bayyana a gaban kotun, suka k'arasa ga yar katangar da aka tanada domin masu bada shaida irinsu (Witnessbox).
Bayan kotu ta sanya su sunyi rantsuwar fadin gaskiya. Jay ta taka ta isa gabansu, tana fuskantar Khalid, kafin ta fara tambayar
"Dan Allah ko zaka iya shaidawa kotu cikakken sunanka da alakarka dake tsakaninka da Tareeq?"
Ya girgiza kai, sannan ya ci gaba.
"Sunana Khaleed Abdullah. Ni kanin mahaifin Tareeq ne."
"Malam Khalid, zaka iya sanar da kotu abinda ya faru a ranar ashirin da biyar ga watan sha biyu na shekarar da ta gabata tsakanin karfe takwas da rabi na dare zuwa goma?"
Ya gyara tsayuwarsa, ya fara bayani tiryan-tiryan. Tun daga fitar Tareeq har izuwa lokacin da ya same shi kwance a gefen titi.
"Na gode Khalid. Me zaka iya cewa dangane da halayyar Tareeq fa? I mean ya halayyarshi da mu'amularshi da mutane suke?"
"All I can say, Tareeq is a good boy. Very calm, baya da hayaniya, yana da ladabi, biyayya da uwa uba rikon addini, baya had'a hanya da shashatan mutane."
"Na gode da wannan Khalid."
Ta juya ga Mal. Idi,
"Baba ko zaka iya sanar ma kotu ainahin sunanka da dangantakar da ke tsakaninku da Tareeq?"
Mal. Idi ya gyara zaman hularsa, ya hadiye yawun da ya taran masa, sannan ya saita kansa ya fara magana.
"Sunana Mal. Idi. Na shekara bakwai yanzu kenan ina aikin gadi a gidan Alhaji Badaru mahaifin Tareeq."
"Mal. Idi ina so ka sanar ma kotu a halin da kuka samu Tareeq a daren ranar ashirin da biyar ga watan sha biyun shekarar da ta wuce."
"Ai duk wani abu da zan fada Khalidu ya riga ya fadi Hajiya, duk haka maganar take, don misalin karfe kamar takwas da rabi na daren ranar ina zaune bakin k'ofa, Tareeq d'in ya zo zai fita har muka dan yi wasa da dariya da shi kamar yadda muka saba kasancewarshi yaro mai faran-faran da son raha. Bayan kamar awa d'aya sai na fara tunanin abinda ya hana shi dawowa, domin da wuya ka ganshi waje a irin wannan lokacin, can sai ga Khalidu ya fito nemansa, shi yake shaida mun ai gidan su Deeni aka aike shi, daga nan ya wuce ni kuma ina tsaye bakin k'ofa, a haka dai muka same shi cikin mummunan yanayi har muka garzaya da shi asibiti."
"Madallah Mal. Idi. Dan Allah ko zaka iya sanar da kotu alak'ar wadancan mutanen da gidan na Alhaji Badaru?"
"Eh to, kusan kullun sai sun zo gidan wurin abokinsu Mukhtar Yayan Tareeq d'in."
Ta juya ga Khalid.
"Shin ko kana da masaniyar wata matsala ko kuma wani sabani ya taba shiga tsakaninsu da Tareeq? Abin nufi ko wata yar rashin jituwa ta taba giftawa tsakaninsu?"
"Gaskiya ban dai sani ba, abinda na sani guda daya ne, Tareeq baya shiga hidimarsu, a wasu lokutan mu kan labarta rashin jin dad'in yadda yayannasa ke abuta da su ma."
"Na gode da wannan Khalid."
Ta juya tana duban Alkali
"Iyakar tambayoyina kenan My Lord."
Dogon rubutu ya yi, sannan ya d'ago yana duban Barr. Hisham
"Lauyan wanda ake k'ara, ko kana da tambayoyin da zaka musu?"
"Yes My Lord."
Ya fada sa'adda ya fito gaban kotun, ta gefen idanunsa yake duban Barr. Jay, yana aika mata sakon wani murmushi wanda ya sanya bugun kirjinta k'ara tsananta. Ya isa gaban witnessbox din da su Khalid ke tsaye, a lokaci guda ya fara watsa musu tambayoyin da har suke neman zauta tunaninsu.
"Duba da yanayin rayuwar da muke ciki ta rashin tsaro da lalacewa, kuma kowa kokari yake ya natsar da danshi a gida daga inda maghriba ta fara doso kai, amma ku kuma kun aiki yaro karami a cikin duhun dare har wata uwa duniya a unguwar da kuka san ababen hawa ma gaggawa suke su wuce ta saboda tsananin rashin mutanenta, shin baku yi tunanin me zai je ya dawo ba?"
"Ai gidan ba nisan duniya bane, kuma ba mu san Tareeq da rawan kai ba bare ya nufi wurin da ba'a aike shi ba, kuma fitarshi ba dadewa dan uwanshi da aka aika ya kira ya shigo gidan, kuma kowa yasan barci kadai ke raba abokan."
Khalid ya bashi ansa kamar yadda ya buk'ata.
"Okay da wannan ne kuka yanke hukuncin cewar su suka aikata lefin kenan? Ko ka bi bayanshi ne kaga faruwar abin?"
"Objection My Lord."
Cewar Barr Jay. Alkali ya gyara zaman tabaransa yana fad'in
"Ka kula da tambayoyinka Barrister."
Ya russuna alamar daukar gyara, tare da mayar da dubansa ga Mal. Idi.
"Kaine Maigadin gidan Alhaji Badaru na tsawon shekaru bakwai, ka kuma ce ku kuka fara riskarsa a halin da aka ambata haka ne?"
Ya amsa da
"Kwarai ma kuwa."
Ya murmusa, ya shafi gefen fuskarsa sannan ya ci gaba.
"Idan har gadin gidan ka ke ya kamata ace ka jajirce wurin ganin ka kare wannan amanar ta hanyar kare su daga ko wacce irin cutarwa, Shin Mal. Idi kana ina har aka aje yaron a Kofar gidan ba tare da kaji ko da motsi ba? Ko kuwa in dare yayi daki kake shigewa kayi ta shirga baccinka?"
Wani juyi cikin Mal. Idi ya yi, cike da rawar murya yace
"A'a ko daya Barritta (Barrister) ina naga ta bacci a wanna lokacin bayan an bar min amanar gida?"
Ya saki tsadadden murmushinsa ta gefen kumatu, ya tura hannuwansa aljihu ya ci gaba da fad'in
"To Malam Idi ya abin yake?"
Ya kauda kai daga duban da Barr. Hisham ke jifarsa da, ya muskuta ya ce
"In mutum zai aikata sharri ai yana toshe duk wata kafa da ya san zata toni asirinsa, kuma da suka tashi ba gaf da k'ofar gidan suka ajje shi ba. Sai da suka bada zira'i kusan ashirin ta yadda babu wanda zai ji.."
Ya yi gaggawar katse shi,
"Owh, Mal. Idi dama har akwai hanyoyin da ake bi wurin aikata mummunan abu ne? Har kasan yanda akeyi ma ashe? Wasu irin hanyoyi ne haka?"
"Objection my Lord, Barr. Hisham na kokarin wuce limit da tambayoyinsa."
Alkali ya dago ya ce
"Objection substained."
Hakan ya sa Barr Hisham ya rissinar da kai, kafin ya ci gaba.
"Ehhnmm Mal. Idi ka ce ka bishi har ka bude masa kofar da kanka shin ba ka ga inda ya nufa ba? Abun nufi ba ka ganin ko ya dan sauya hanya ya bi ta wata hanyar don zuwa gidansu Deeni din?"
"A'a gaskiya anya?"
Wani kallo Barr Hisham ya tsareshi dashi, da sauri ya ce
"Kai a'a, ai hanyar daya ce ta zuwa gidan, babu ko tantama don ba wani nisa ne tsakaninmu da su ba, kuma Tareeq ba mai yawo bane bare ace ya biya wani wuri, su kuwa wadannan yaran dama kowa ya san halin..."
Da azama Barr. Hisham ya dakatar da shi ta hanyar cewa
"To.. to Malam Idi na gode"
Ya juya ga alkali da ya kafe su da idanu yace "Iyakar tambayoyina kenan ya mai shari'a."
Jiki a sabule ya koma ya zauna, gaba d'aya ya sake da al'amarin na Barr. Jay, bai taba zaton kanta na ja har haka ba.
"Lawyer wanda ya ke kara, ko kina da sauran tambaya?"
Alkali ya tambaya yana fuskantar bangaren da Barr. Jay ke zaune.
"Yes My Lord."
Ta fada da kwarin gwuiwarta, bayan ta mike, a gefe guda tana furzar da murmushin nan nata mai matukar kayatarwa. Tabbas Barr. Hisham ya zo ringizo aikin da bai san hanyar da zai bi ya ida sa ba, dan haka ita zata watse masa shi ba tare da bata lokaci ba. Ta kalli Mal. Idi wanda ya ke zaman jiran tambayarta ta ce
"Malam Idi su wadannan yaran bisa ga alama ba wai ka waye su bane ko?"
"Hakane 'yar nan."
"Masha Allah, shin ko zaka sanar ma kotu ko da kadan ne daga halinsu da ka sani?"
Ya sharce zufar da ta yayyafo masa, ya k'ura ido yana kallon setin da suke, daga bisani ya fara nuna su da hannu.
"Wadannan yaran a duk fad'in unguwar nan babu wanda bai san halinsu na shaye-shaye ba, sam basu da tarbiyya basu ganin kowa da gashi domin banyi mamaki ba da naji an cafkesu a matsayin wadanda suka aikata laifinnan."
Kyakkyawan murmushin da ke kan fuskarta ya k'ara bayyana, ta san abinda ta so fada kenan Barr. Hisham ya dakatar da shi. Ta juya tana fad'in
"Sannu Mal. Idi, da fatan duk sanda muka sake waiwayenka zaka bamu hadin kai?"
"Da gudu kuwa, dole mu tsaya a kwatar ma bawan Allah hakkinshi. Yaro mai hankali, bai ji ba bai gani ba."
Yana ta 'yan surutanshi, aka sallame su suka koma inda suka fito, alkali ya dukufa da dogon rubutu, ya dago ya bukaci jin ko wani a cikinsu yana da sauran wani abin cewa.
Barr Jay ta mike, ta kuma fita gaban kotun har kuma yanzu murmushinta bai disashe ba.
"My Lord. Ina rokon alfarmar wannan kotu mai adalci da ta daga wannan k'ara zuwa wani lokaci, domin in samu damar da zan gabatar da sauran sheduna."
Alkalin da kansa ke k'asa, ya d'ago ta ajje biron hannunsa;
"Kotu ta dage wannan k'ara zuwa ranar goma ga watan da zai kama."
Daga nan ya buga kundin da ke gabansa, gaba d'aya jama'ar wurin suka mike tare da fad'in
"Koooooootu..."
Ya baza rigarsa ya fita, da haka sauran mutane duk suka fara fitowa su ma, suka ci gaba da maida yadda aka yi.
0 comments:
Post a Comment