Cewar Alhaji Badaru lokacin da suka koma gefe guda suna jiran fitowar Barr. Jay. Hango ta da ya yi tana dumfaro inda suke tsaye ya sanya shi hadiyar wani mugun yawu da ya taran masa, a karo guda ya nemi maganar da ke son fitowa bakinsa ya rasa.
"Ana ta shari'ah babu victim. Ko kina tsoron abinda zai je ya dawo ne? Ma'ana ko kina gudun ya kunyatar da ke?"
Da sauri ta juya inda sautin maganar ke fita, Barr. Hisham ta gani hannayensa rungume a kirji, yana jifarta da wannan malalacin murmushinnasa, wanda ya kan tsananta faduwar gabanta, a wasu lokutan har ma ta ji ta karaya. Sai dai kasancewar ita din mace ce da take da full confidence, with a high self-esteem, hakan ya kan sa ta kuma zage damtse ta kudurtan ma ranta sai ta mayar da murmushin nan nasa zuwa hawaye idan bai yi wasa ba.
Ta gyara tsayuwarta, a sa'a guda ta kara rungumar gown dinta, tattausan murmushinta ta jefa masa, daga haka ta girgiza kai ta juya da zumar karasawa wurin su Alhaji.
Khalid ne ya yi gaggawar fara magana
"Sannu da aiki Barrister. Ya kike ganin abin nan kuwa? Akwai alamar nasara?"
Duk a lokaci guda ya jera mata tambayoyin, hakan ya sanya ta sakin ajiyar zuciya a bayyane, ta murmusa ta ce
"I've no idea Khalid, al'amurran Barristern can suna neman dagula tunanina, but don't worry. I believe Allah yana tare da mai gaskiya, ina kuma da yakinin da taimakonshi ne kawai gaskiyar zata yi halinta."
"Ni wallahi abinda nike ji kenan, dama shi yasa tun wuri na ce ayi hakuri da maganar kotun nan, amma kuka kiya. Ga ni da muhimman tarurruka, haka na baro su na taho na bata lokacina a nan a banza a wofi."
Alhaji Badaru wanda ya kasa saita idanunsa cikin na Jay ya yi maganar tare da sakin dan gajeran tsaki. Ta dube shi cikin tsagwaron tsana, domin a zahiri ta rasa gane wani irin uba ne shi da ya fifita sabgogin gabansa fiye da iyalinsa. Dakyar ta iya fad'in
"Kar ka damu Alhaji, mai hakuri ai shi yake dafa dutse har ma ya sha romonsa."
"To, mu dai Allah ya sa ayi abun nan lafiya a gama, amma wallahi hankalina sam ya kasa kwanciya da shari'ar nan, ina jin tamkar wani gagarumin abu na shirin faruwa."
Hajja Fati ce tayi wannan jawabin tana duban Jay, hakan ya sanya Khalid sanya hannunshi a aljihu, wayar da ya tsinta ya shafa ya ji lafiyarta, sai dai baya tunanin zai taba fallasa wannan sirrin, yana kuma ji a jikinshi zai iya tafiya da shi har makwancinsa na k'arshe a doron k'asa.
'Me hakan ke nufi kenan?'
Wani bangare na zuciyarsa ya buk'ata, yayin da a lokaci guda wani sashen ya bashi ansar da ta sanya shi girgiza kai yana fad'in
'Hakan ba zai taba faruwa ba'
A k'asar zuciyarsa.
"Khalid barin ganka mana."
Maganar Barr. Jay ta dawo da shi dai-dai, ya bi bayanta suka koma gefe, yayin da ta yi ma su Alhajin sallama.
Alhaji Barau ya gyara zaman malunmalun d'insa, ya kalli Barr. Hisham duba mai cike da tuhuma da tsantsan tashin hankali ya ce
"Haba Barrister. Ta ya zaka yi sanya a kan matar can? Ban sanka da wannan sassaucin ba sam, ban kuma san sadda ka koma haka ba. Ina had'a ka da Allah, kada ka watsa mana k'asa a ido. Dan dukkanmu nan da kai kawai muka dogara."
Ya shafi gefen fuskarsa, ya furzar da iska mai zafi, a sa'a guda ya murmusa kadan ta gefen kumatunsa
"Ka yarda da ni Alhaji, ka kuma kwantar da hankalinka, yaranku tamkar sun fito sun gama ne. Ka ga yadda nayi ta k'ok'arin kare su ai, wannan tsohon ne ya kwance mun aiki gaba d'aya. Amma next time."
"Make it possible please."
Cewar Prof. Bello yana dubansa. Barr. Zainab ta yi gaggawar anshewa
"Ban ji kayi maganar belinsu ba Barrister? Kana nufin haka yaranmu zasu yi ta zama tsakiyar prison har sai wani mugun abun ya faru da su?"
"Very good. Abinda ke zuciyata kenan. Gaskiya ka nema mana belin yaranmu, in yaso a gama shari'ar suna gabanmu."
Cewar Hajiya Karima.
"It's not a big deal. Kwata-kwara na shafa'a ne fa, kaina ya dau chaji ba kadan ba, ina ganin kamar Barrister can zata yi saukin kai, ashe ba haka abun ya ke ba. In sha Allah a next zama zan bukaci belin nasu, in har ba ayi watsi da shari'ar bama baki d'aya."
Hakan da ya fad'a ya dan sanyaya zuciyoyinsu, daga nan suka yi sallama da juna suka kama hanyar gida, sai dai zuciyar Alhaji Barau sam ta kasa kwanciya, a take ya kudiri wani al'amari a k'asar zuciyartasa, wanda ya tabbatar zai amfane su duk gaba d'aya.
****
A gajiye sosai ta shigo gidan, motar mijinta da ta hanga a harabar adana motocin, shi ya sanya ta sakin murmushinta mai tsada, a sa'a guda ta nemi gajiyar da ta shigo da ita ta rasa. Bayan ta gyara parking ta fito da jakarta a hannu, a dai-dai lokacin wata yarinya mai shekarun da basu haura goma zuwa sha daya ba, ta fito da sauri ta iso gabanta ta anshe kayan tana fad'in
"Sannu da zuwa Mammy. Daddy ya dawo."
"Na gode Rukayya. Na ga motarshi, amma shine ko ya kira ni ko? Ina handsome nawa? Ban ga ya fito ansar jakata ba?"
Bata kai ga bata ansa ba ta hange shi ya had'e rai ganinta ya sanya shi tasowa da gudu yana fad'in
"Mammy kinga Daddy da Rukayya ko? Daga zuwanshi har sun fara tsokanata."
Ta fadada murmushinta, lokacin da idanunta suka sauka tsakiyar na mai gidannata, ta narkar da ido tana dubansa a sa'a guda tana magana da Jafar wanda ya shige jikinta.
"Sorry handsome, manta da su ka ji, I'm here for you."
Daga haka sauran yaran guda biyu suka fito, Sadam Junior yana gaf da shekara ukku, sai Fatima mai shekaru biyar da wani abu yanzu, ta cika fuskarta da foundation, ta zana brows dinta yadda ya mata, ta cika bakinta da jan baki, wanda ya haura har saman hancinta. Suna kallonta duk suka saka dariya, hatta da SS wanda ya k'araso ya zauna a gefensu.
"Fatima yaushe zaki daina shirmen kwalliyar nan dan Allah? Kalle ki kamar aljana fa."
Jay ta fad'a tana dariya, SS ya k'ura mata ido, kafin ya maida dubansa ga Fatima wacce ta turo baki idonta sun cika taf da kwalla.
"C'mon. Manta da su kinji. Dan sunga kin fi su kyau ne ai."
"Mammy yarinyar nan dama ai kama take da aljannu, kalle ta fa."
Rukayya da ta iso da tray mai d'auke da cup da goran ruwa ta fad'a bayan ta zauna itama.
"Wait. Ina Junior wai?"
Tayi maganar tana kalle-kallen inda zata hango shi, yana tsaye gefen kujera ya cika ya batse, yana tunanin menene ya hana Mammyntasu daga shi sama ta jujjuya kamar yadda Daddy ke mishi.
"Laaaah.. Mammy gashi nan ya labe bayan kujera."
A cewar Fatima lokacin da take leka shi, tana ta faman kyalkyata dariya, domin ta manta da nata abun haushin da suka mata. Da kanta ta isa ta kamo shi, ta daga shi sama tana dariya, shima dariyar ya saki yana yi ma sauran yaran gwalo.
"Oyaaa.. a kwashi kayana a kai mun ciki, kowa ya je yayi homework d'insa. Okay?"
Da gudu suka yi ciki, in banda Rukayya da Jafar wanda suka bisu a baya, alamun girma da hankali duk ya bayyana a tare da su.
Ganin shigarsu ya sa ta sauke idonta a kanshi, shima din ita yake kallo, bai ce komai ba ya kama hannunta suka wuce sashenshi, bakinta ya kasa rufuwa, domin a zahiri zuwan bazata ya musu, haka kuma yau ba juma'a ce ba, sai dai fuskarta kawai za'a kalla a san ta ji dad'in zuwannasa ba wai kadan ba.
"Barka da zuwa Mr. SS. Ya hanya ya aiki?"
Tayi maganar a setin kunnensa, cikin wata kasalalliyar murya, domin yanayin rikon da ya mata, yasa maganar na neman disashewa gaba d'aya.
"Alhamdulillah Barrister. Ya kika ji da shari'ah?"
"Hmmmm. Ka bari kawai, Allah ne kadai ya kwace ni yau din nan. Cuz wani lawyer ne mutanen suka dauka, baka ga yadda yake kayar mun da gaba ba wallahi."
Ya sa hannu ya zare gyalen da ke kanta, ya tura yatsunsa cikin tarin gashinta, a lokaci guda ya fara magana wacce ta fi kama da rada.
"C'mon Angela. Kada kiyi saurin karaya mana. I'm sure, you're going to win this case. In sha Allah. Okay?"
Ya karashe yana dubanta cikin idanu, yana jifarta da murmushinsan nan mai sanya ta k'ara kewarsa a duk sadda baya nan.
"I hope so Ya Sadic. So, me ya dawo da kai yau, after all ba weekend ba ne."
"Surprise."
Ya fad'a lokacin da ya zaunar da ita, ya umarce ta da ta kulle idonta.
Daki ya shiga, ya fito da wata takarda a hannunsa, ya iso ya kama hannunta, ya dora a kai.
"There you go Mrs. SS."
Ta bude ido tana kallonshi, yayi mata alamar ta bude ta gani da idonsa, hakan yasa ta warware da sauri ta fara dubawa. Canjin wurin aiki ne (transfer) da kuma karin girma na zama babban manajan Zenith Bank reshen jihar Kaduna.
"Ya Allah. You must be kidding Ya Sadic."
Tayi maganar da tsananin farin ciki saman fuskarta, har tana sa hannu tana toshe bakinta.
"No, I'm not Angela."
Ya zauna a gefenta, tare da sargafo hannunsa a wuyanta yana ci gaba da duban fuskarta. Har kuma a yau babu digon canji da ya samu daga tsantsar soyayyar da yake mata. A hankali ta furta
"Congratulations Ya Sadic."
Ya yi mata kallon 'ki gyara kalamunki' ta murmusa sannan tace
"Oops. Mr. Manager."
"Now you're talking."
Ya saki dariya tare da kwantar da kanta a kafadarshi. Wayarta da tayi kara ne ya sanya ta saurin dubawa, credit alert ta gani har na naira million d'aya da rabi, sai dai babu suna ko wata alama da zata tabbatar da wanda yayi depositing kudin a account dinta. Illa wata alamar B da ta fito a wurin da ya kamata sunan wanda ya tura kudin ya fito.
"Duba ka ga?"
Ta mik'a masa wayar cike da mamaki.
"Wannan fa? Daga ina?"
"Nima haka kawai na ganshi fa."
"May be anyi mistake ne wurin depositing din, in dai ba naki bane na san zasu fitar da abunsu. So, don't worry. Kinji?"
"Uhnmm."
Shine kawai abinda ta iya fad'a, ta mik'e ta wuce ciki, domin zuciyarta na saka mata abubuwa kala da kala.
****
Layin Buzu mai gadi take kira ya kai sau goma amma babu alamar zai ansa kiran, ta san muddin bata samu damar magana da shi ba, to tana tattare da kalubalen da bata san yadda zata fassara shi ba. Shine kawai shedar da take da shi a gobe, shine kuma mutum d'aya jal da zai taimaka wurin tabbatar da rashin gaskiyar su Mubee.
'Menene abin yi?'
Ta tambayi zuciyarta, a sa'a guda tana mai kwankwasa steering wheel din hannunta. Bata da sauran zabin da ya wuce mata karasawa wurin aikinshi, domin ta tabbatar da lafiyarshi ma a karon farko.
Da wannan ta canja akalar motar, zuwa kinkino road, sai dai irin bugun da kirjinta ke mata, ta rasa gane dalilinshi, haka ta iso k'ofar gidan tayi parking, ta fito ta k'arasa tana bubbuga kakkarfan k'yauren.
Ganin buzun ne ya bud'e k'ofar, ya sanya ta sakin ajiyar zuciya cikin sauri, ta gaishe shi tana fad'in
"Baba ina ta kiran wayarka ba'a dauka. Lafiya dai ko?"
Ya murmusa, a lokaci guda ya fito k'ofar gidan.
"Wallahi wayar ce ta shiga salunn (silent), ni ban gani ba, sai da yanzu yaron gidan nan ya zo yace Alhaji yana ta kira ban dauka ba, ya anshi wayar ya duba ya fidda mun. Har yace wata lamba ma ta kira kusan so goma, to ban san ke din bace 'yar nan. Ya aiki?"
Ta murmusa da jin kalamansa,
"Lafiya lau Baba. Dama batun wannan maganar ne, gobe ne za'a shiga kotun, shine zan ce ka zama cikin shiri dan Allah."
"Kar ki damu yarinya. In sha Allahu a shirye nike. Lokaci kawai nike jira."
Ta ji dad'in da har ya kasa boyuwa a k'asar zuciyarta, ta bayyanar da shi ta hanyar sakin murmushi mai sauti, ta yi masa godiya tana fad'in
"Sai goben Baba. Sai na ganka."
"Allah ya kaimu 'yar nan."
Ta juya ta shige mota hankalinta kwance, ta bata wuta, sai dai cikin rashin sa'a gaba d'aya abinda suka yi a kan idon Barr. Zainab wacce ta fito daga makwaftan gidan da Buzu ke gadi.
Duk wasu maganganu da suka yi a kan kunnenta, hakan yasa Jay na juyawa, ta daga waya ta fara kiran Barr. Hisham.
Gaba d'aya komai da ta ji, ta zayyana masa, daga nan ta kashe wayar tana murmushin jin dad'in bayanin da Barr. Hisham din ya mata.
Idan har tana da sauran damuwa a yanzu, bai wuce inda zata ga mai gadin gidan Engr Bukar ba wanda ya bada sheda a police station. Ina zata ganshi? Ita ce tambayar da ke yawo a cikin kanta, domin ta ziyarci gidan, inda ta samu sabon mai gadin da ya tabbatar mata an dad'e da korarsa. Ta tambaye shi garinsu, amma yace bai sani ba. Tabbas tana da bukatarshi, domin shine kawai zai bayyana ma kotu cewar basa gida a ranar da al'amarin ya faru. Da wannan tunanin har ta iso gida, ta wuce ta adana motarta, kafin ta k'arasa ciki.
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{18}
Yau ma kamar kullun, kotun cike take mak'il har ma da wadanda shari'ar bata shafa ba. Shigowar alkali ce ta dakatar da cece-kucen da mutanen cikin kotun ke yi, suka mik'e tsaye, ya k'arasa ya samu wurin zamansa, sannan kowannensu ya koma mazauninsa.
Ba tare da bata lokaci ba Alkali ya bada umurnin a ci gaba da sauraren shari'ar, daga haka aka dora daga inda aka tsaya.
Cikin natsuwa Barr. Jay ta mik'e,
"Ina rokon wannan kotu mai alfarma, da ta bani dama domin gabatar da wasu 'yan tambayoyi ga mutanen da ake tuhuma."
"Objection My Lord. Duba da yanayin clients dina, na kwanakin da suka shafe a prison, wurin da ya kasance bako a gare su, bana jin suna da karfin da zasu iya ansa tambayoyin da Barrister take shirin yi musu."
Barr. Hisham ya yi jawabin cikin muryarsa mai karfin amo. A sa'a guda Alkalin ya kai duba gare shi
"Mutanen da suke tirjiya ma guardrobbers din da suke shigo da su, sune ba su da karfin da zasu ansa tambaya da fatar bakinsu? K'orafi bai kar6u ba Barr. Hisham. So, Barr. Jameela, you can proceed."
"Thank you My Lord."
Ta rissina cikin girmamawa, kafin ta isa inda su Sino ke tsaye, idanunta cikin na Deeni, sannan ta fara magana
"A ranar laraba ashirin da biyar ga watan shekarar da ta wuce, kun samu sa6ani tsakaninku da Tareeq a cikin gidansu haka ne ko ba haka bane ba?"
Duk shiru suka yi, tamkar baza su ansa ta ba, Sino ya d'ago ya ansa mata da
"Haka ne."
"Shin ko zaku iya bama kotu labarin menene ya asassa hatsaniyar taku?"
Bud'e bakin Deeni zai fara bayani, Sino ya murje babban yatsarshi ta kafa, dan ya san duk koma me zai fito bakinsa, ba lallai ya zamana mai dad'i ba.
"Ya wurgi mana da shisha pot ne, shine Yayansa ya tashi zai dake sa amma na hana shi."
"Thank you. Shin menene ma'anar furucinka na 'you'll regret this T-boy?' Ko zaka iya yi ma kotu bayanin abinda kalmar regret take nufi?"
"Objection My Lord. Barr. Jameela tana neman wuce limits na tambayoyinta."
"Korafi bai kar6u ba Barr. Hisham. Carry on Barrister."
Ya nuna Jay da hannunsa, hakan ya bata damar rissinawa
"As My Lord pleases."
Cikin kunar rai Barr. Hisham ya koma ya zauna, a zuciyarsa yana addu'ar kada Allah yasa su watsa masa kasa a ido.
"Ina saurarenka."
Tayi maganar tana fuskantar Sino.
"Eh? Ni ban san me kike magana a kai ba. Ni ban ce haka ba gaskiya."
Ta juya ta nuna Deeni.
"Ka tafi Zaria a ranar, da misalin karfe nawa ka tafi?"
Yayi shiru yana mai neman abun fad'a, daga k'arshe ya ansa da cewar
"Wurin karfe shidda na tafi."
"Ka isa can da misalin karfe nawa?"
"Misalin bakwai na isa."
Ta juya tana kallon Mubee.
"Kai kuma kana ina bayan wannan lokacin?"
"Ina gida."
Ya bata ansa a gajerce.
Ta kalle shi kafin ta girgiza kai, ta juya ga Sino tana son had'a ido da shi, sai dai babu halin yin hakan, kasancewar kanshi a k'asa yana wasa da yan yatsunsa.
Ta juya ga alkali
"A ranar laraba ashirin da biyar ga watan December na shekarar da Ta gabata, mutanen nan sun shiga gidan Alhaji Badaru cikin d'akin kwanan Tareeq da yayansa abokinsu, inda wata yar tangarda ta gilma tsakanin Yayan da shi Tareeq, wanda ya same su suna shaye-shaye a d'akin, a lokacin ne Hassan ya furta kalmar 'you'll regret this T-boy' a kunnen Tareeq. Bayan nan sun fito gidan da misalin shidda da rabi na yamma, inda Deeni ya shaida ma yan sanda ya bar garin Kaduna zuwa Zaria da misalin karfe bakwai na dare, ya isa can da misalin karfe takwas. Yayin da a nan ya shaida ma kotu cewar ya tafi misalin karfe shidda, ya isa can wuraren karfe bakwai na dare. Bayan kuma binciken yan sanda ya nuna cewar, bai ma isa can din ba, sai misalin karfe goma sha daya na dare. Mubarak ya tabbatar ma kotu yana gida daga karfe shidda na yamma har zuwa washe garin ranar, sai dai bayanin da yan sanda suka rubuta, ya tabbata bai koma gida a ranar ba, sai wurin karfe goma sha biyu na dare."
Ta gyara zaman rigarta, ta fara takawa a hankali, sannan ta ci gaba.
"My Lord. Ta yin la'akari da samuwar banbancin statement din mutanen nan da ke tsaye a yanzu, da kuma wanda ke rubuce a nan jikin police report hakan na nuni da cewar tabbas dukansu ukkun suna da hannu dumu-dumu a abinda ake tuhumarsu."
Barr. Hisham ya mik'e yana fad'in
"My Lord. Har fa yanzu Barr. Jameela bata da damar da zata zartar da hukunci a kan clients dina, domin babu wani abu da tayi presenting wanda ya tabbatar da cewar su din suka aikata abinda ake zarginsu."
"Objection sustained."
Ta rissinar da kanta,
"As My Lord pleases."
Sannan ta cigaba.
"Wannan shine cikakken bayanin da suka yi ma yan sanda, wanda ya banbanta da wanda suka yi a nan gaban kowa da kowa."
Ta mik'a shi ga registrar, wanda ya mik'e ya isar da shi ga alkali.
Wani malalacin kallo Barr. Hisham ya jefe ta da, a sa'a guda ya juyar da kanshi. Ba komai yake bashi mamaki ba, sai irin rawar kan da take, ita a dole ga wadda ta san makamar aikinta. Tabbas sai ya rusa duk kowanne shiri ta shigo da shi a yau din nan, a k'arshe ya karfafa ma kansa gwiwa cewar sai ya san yadda yayi alkalin ya yi watsi da gaba d'aya shari'ar ma.
Ta kauda kai daga dubansa, ta maida shi ga alkali tana fad'in
"My Lord, ina neman alfarmar kotu, da ta bani dama in gabatar da shedata ta gaba."
"Kotu ta baki dama."
Ya fad'a bayan ya d'ago daga rubutunsa, yana gyara zaman gilashin fuskarsa yana dubansu.
Buzu mai gadi ya iso gaban witnessbox ya tsaya, ya yi rantsuwa tare da alkawarin fad'in gaskiya, sannan Jay ta k'arasa gabansa tana dubanshi fuskarta kunshe da d'an murmushi.
"Baba dan Allah ko zaka iya sanar ma kotu cikakken sunanka da alakarka da gidan Alhaji Badaru?"
Ya daidaita tsayuwarsa, a lokaci guda ya k'ara rik'e yar katangar da yake tsaye a cikinta, kafin ya fara jawabi.
"Sunana Mal. Habibu. Ni mai gadi ne a makwaftan gidan Alhaji Badaru."
"Na gode Mal. Habibu. A ranar ashirin da biyar ga watan sha biyu na shekarar dubu biyu da goma sha shidda da misalin karfe tara na dare kana ina?"
"Ina gida a dai-dai wannan lokacin."
"Shin zaka iya tuna abinda ya wakana a tsakanin lokacin da na ambata wanda ya danganci mutanen can da suke tsaye?"
Ta karashe tana nuni da bangaren da su Mubee ke tsaye, sannan ta dawo da hankalinta gare shi.
"Eh to, ina zaune daga cikin gida na gama had'a shayi na sha, sai na fito k'ofar gida domin dauraye kofinan kasancewar hakan al'ada tace. Yanayin unguwar akwai haske na dogayen fitilu, shi kuma ya taimaka mun wurin ganin su yaran can sun taho da wani abu kamar kaya masu nauyi a hannunsu, sun jefar da shi a gefen kwalbati, sun kuma koma sun shiga mota sun ja sun tafi, sai dai ni ko a kaina, ban kawo cewar mutum bane suka jefar, domin shi wancen Hassan shine na gane da kuma motarshi gaskiya."
"Da kyau Mal. Habibu. Shin su wadannan yaran ya halayyarsu da dabi'arsu take a cikin unguwa? Ko zaka iya yi ma kotu bayani?"
Ya shafi gefen fuskarsa, a karo guda ya dubi inda su Deeni ke tsaye, kafin ya sauke kai daga kallonsu, ya ci gaba
"A zahirin gaskiya, kowa ya sani yara ne marassa jin magana, ga su dai ba wasu manya ba, amma duk wani shaye-shaye babu wanda basa yi, basa ganin darajar kowa a unguwa, hakan yasa kowa ma shayin shiga shirginsu ya ke."
Wani matsanancin farin ciki ne ya lullube zuciyarta, ta kalle shi tana fad'in
"Na gode Mal. Habibu."
A lokaci guda ta fuskanci Alkalin da ya k'ura idanunsa a kansu, yana sauraren dukkan jawabin Buzu.
"Iyakar tambayoyina kenan My Lord,"
"Lawyern wanda ake k'ara, ko kana da abun cewa?"
"Yes My Lord."
Barr. Hisham ya mik'e bayan ya fito da wata brown envelop daga desk dinshi, ya k'araso gaban kotun kafin ya fara magana
"My Lord. Babu wata tambaya da zata had'a ni da mahaukaci, mutumen da bai san ina ke masa ciwo a cikin jikinsa ba, wanda ya shafe shekaru biyar yana jinya a gidan mahaukata da ke nan cikin garin Kaduna."
Ya kai dubansa ga Jay ya sakar mata makirin murmushinsa, sannan ya ci gaba.
"Wannan medical report ne na Buzu Mal. Habibu, mai gadi a gidan Col. Shu'aibu Tukur, wanda ya shafe shekaru biyar yana fighting hankalinsa a gidan mahaukata. A tare da ni akwai likitan da ya rubuta wannan report din, wanda shine likitan da ya rink'a duba sa lokacin da yake psychiatric."
Hayaniya mutanen cikin kotun suka fara yi, daga ciki kuwa hadda Buzu da aljabi ya bayyana a kan fuskarsa duk da cewar ba komai na maganar Barr. Hisham ya gane ba.
"Order in court.."
Alkalin ya dinga fad'a cikin daga murya, yana mai buga kundin gabansa da katuwar gudumar da ke ajje. Cikin dan lokaci wurin ya koma ya yi tsit tamkar babu halittar dan Adam.
Wani dogon mutum sanye cikin labcoat ya iso gaban witnessbox din da ke fuskantar na Mal. Habibu, yayi rantsuwar fad'in gaskiya kafin Barr. Hisham ya isa gabansa.
"Dr. Ko zaka iya sanar ma kotu cikakken sunanka da aikinka?"
"Sunana Dr. Rilwan Hamza, ni psychiatrists ne da nike aiki da asibitin mahaukata na nan cikin garin Kaduna."
"Dr. Rilwan. Me zaka iya cewa dangane da wannan report din? Shin ko ka shaida wancen mutumen da ke tsaye gabanka kuwa?"
"Ni na rubuta wannan report shekaru biyar da suka gabata, lokacin Mal. Habibu yana fama da cutar tabin hankali."
"Shin zaka iya sanar da mu ya yanayin ciwon nasa yake?"
"Eh to ya kan d'auki lokaci yana cikin hayyacinsa, yayin da idan cutar ta motsa, yana acting ne cikin natsuwa, sai dai kuma baya cikin hankalinsa, kamar yanzu da yake tsayen nan, alamun hankali sun bayyana gare shi, amma kuma baya tare da shi. Domin kuwa har gobe yana ansar magani, ma'ana bai ida komawa cikin hankalinsa ba."
"Na gode Dr. Rilwan."
Ya juya ga alkali ya mika takardar, kafin ya ci gaba da fad'in
"Mal. Buzu Habibu kamar yadda Dr. Rilwan ya shaida ma kotu ya shafe shekaru biyar yana jinyar kwakwalwarsa a gidan mahaukata, na san kotu da kanta ma, baza ta taba d'aukar shedar mutumen da bai san ciwon kansa ba, balle ya san ciwon wani. Da haka nike rokon alfarmar wannan kotu mai adalci da tayi watsi da shedar Mal. Habibu, ta kuma hukunta Barr. Jameela na kawo mutumen da ta san baya cikin hayyacinsa a matsayin wanda zai bada shaida, duk kuwa da cewar tana sane da hakan ya saba doka da alkadarin wannan kotu mai alfarma."
Wani irin tashin hankali ne ya daki zuciyar Jameela, wanda har sai da ya bayyana a kan fuskarta, hakan ya sa ta rasa abin cewa, Barr. Nasib ne ya yi k'arfin halin mikewa yana fad'in
"Objection My Lord. Kamala, yanayi, zubi, da tsarin Mal. Habibu, duk wanda ya kalle shi ya san bai yi kama da mahaukata ba. Dan haka ina rokon alfarmar wannan kotu da ta bani dama domin yin tambayoyi ga Dr. Rilwan."
"Kotu ta baka dama."
Ya isa ga Dr. Rilwan wanda zufa ta gama jika farar rigarsa, har ana iya ganin sawunta. Ta kafe shi da ido, sannan ta fara magana.
"Dr. Ka sanar da kotu cewar Mal. Habibu ya kwashe shekaru biyar a gidan mahaukata, shin ta wane dalili ne bayan fitarshi kuka barshi ya fara aikin gadi a gidan mutane, ba kwa tunanin rayuwar mutanen da yake gadi tana cikin hadari?"
Ya daidaita zaman gilashinsa
"Bani da masaniyar ranar da ya fara aiki da su, kaga wannan ba laifina ba ne ba. Watak'ila kuma suna da masaniyar larurar tashi, taimako ne ya sanya suka d'auke shi."
"Amma bayan da ka gano hakan, me ya sa baku bincika ba?"
"My Lord. Tambayoyin da Barrister ke yi ga Dr. Rilwan ba huruminsa ba ne ba, ina ga tunda Mal. Habibu ya bar hannunsu ai basu da sauran wata mu'amula tsakaninsu da shi."
"Objection overruled."
Cikin rashin kwarin gwiwa ya rissinar da kai
"My Lord."
Daga nan ya koma ya zauna. Hakan yasa aka sallami Mal. Habibu, da Dr Rilwan suka koma inda suka fito, yayin da zuciyar Jay ta rink'a harbawa, cikin matsanancin sauri.
"Lawyern wanda ake k'ara, ko kana da sauran abun cewa?"
"Yes My Lord. Ina rokon kotu ta bani dama domin gabatar da shedata ta gaba."
"Kotu ta baka dama."
Mai gadin gidan Engr. Bukar wanda ya bada sheda a police station ne ya bayyana gaban kotun, bayan ya yi rantsuwa Barr. Hisham ya isa gabansa, idanunsa cikin nasa ya fara magana.
"Baba ko zaka iya sanar ma kotu ainahin sunanka da alakarka da mutanen can?"
Gabansa na faduwa ya kai duba inda hannun Barr. Hisham ke masa nuni, ma'ana wurin da su Mubee ke tsaye. Ya sharce zufar da ta yayyafo saman goshinsa, kafin ya dago ya fara bayani.
"Sunana Mal. Buba. Ni mai gadi ne a gidan Engr. Garba Bukar mahaifin Mubarak."
Daram! Zuciyar Jay ta buga. Tabbas shine mai gadin da ta rink'a nema, wanda aka tabbatar mata da cewar sun kore shi. 'Me ya dawo da shi yanzu?' Ta tambayi zuciyarta tana kallonshi, a sa'a guda ta yanke hukuncin tabbas akwai wata kullalla a k'asa.
Barr. Nasib da ke zaune a gefenta, ya rankwafo da kansa ya na yi mata rada, ganin tsananin tashin hankalin da ta shiga.
"Oh Allah help us."
Ta fad'a cikin muryarta mai sanyi, sannan ta tattara hankalinta ga sauraren abinda Barr. Hisham zai fad'a.
"Shin Mal. Buba, ko zaka iya tuna karfe nawa Mubarak ya dawo gida a ranar laraba ashirin da biyar ga watan sha biyu na shekarar da ta gabata?"
Ya kalli mutanen cikin kotun da idanunsa a waje, sannan ya hadiye wani kakkauran yawu da ya taran masa
"Misalin shidda da rabi ya dawo gida."
"Bayan nan ka k'ara ganin fitarsa ne?"
"Bayan nan bai k'ara fita ba sai washe gari da safe."
"Na gode Mal. Buba. Shin ko zaka iya sanar ma kotu ya halayyarsu Mubarak take?"
Ya kama hularsa ya daidaita, ya kai duba ga Barr. Hisham, ya ga fuskarsa babu alamar sassauci, cikin rawar murya ya fara magana.
"Ai su Mubarak kam, sai san Barka. Yara ne da suka San darajar na gaba da su. Ga su da taimakon na kasa da su. A wani lokacin har na kan ce Allah ya ga kyawawan zukatansu; da har ya had'a su suka zama abokai."
Barr. Hisham ya murmusa, jin yadda Mal. Buba ke bayani cikin natsuwa. Ya juya ga alkali ya rissinar da kai
"Iyakar tambayoyina kenan My Lord."
"Lawyern wanda ya ke k'ara, shin kina da tambayoyin da zaki masa?"
"Ina da su My Lord."
Ta iso gaban Mal. Buba, ta kalleshi, kallo na tsanaki, ta marairaice fuska tana fad'in
"Kayi rantsuwa da alkawarin sanar da kotu gaskiya tsakaninka da Allah. Ka tuna zaka mutu ka je ka tar da Allah Mal. Buba, me sa ka canja statement dinka?"
"Eyieee? Ai iyakar gaskiyata kenan yarinya. Abinda na sani ne na fad'a."
"Amma ka sanar da yan sanda cewar Mubarak baya gida a ranar, bai dawo ba sai misalin sha biyu na dare, mai yasa ba zaka maimaita hakan a gaban kotu ba?"
Ta sauke gauron numfashi, kafin ta ci gaba.
"Ka dubi darajar girmanka da shekarunka ka fad'i iyakar gaskiyarka Mal. Buba."
"Objection My Lord. Barrister na neman wuce gona da iri, da son tursasa witness dina a kan abinda bai ji ba bai gani ba. "
"Be careful."
Alkalin ya ce da ita. Ta rissinar da kai, zuciyarta na gaf da tsinkewa. Me yake shirin faruwa da ita a yau?
"Shin Mal. Buba menene yayi sanadiyyar barin aikinka a gidan Engr. Bukar na kusan wata biyu?"
"Ehh? Ai ban bar aiki a gidan ba, na dan samu rashin lafiya ne, shine na koma gida na dan yi jinya. Bayan na warke kuma sai na dawo.
"Madallah Mal. Buba."
Ta juya ga Alkalin ta ce
"Iyakar tambayar kenan My Lord."
Daga nan aka sallami Mal. Buba alkalin ya dukar da kansa k'asa ya dukufa a dogon rubutu, kafin ya d'ago yana fad'in
"Where's the victim? Is he in court today?"
"Yes My Lord."
Tayi nuni da inda Tareeq d'in ya ke. Da haka dan sandan da ke tsaye a kame, ya leka dan k'aramin office din, yayi ma Khalid da Tareeq magana da suke zaune. Tashi Khalid yayi ya kama hannunsa, har yanzu tafiyarsa bata koma dai-dai ba, kamanninsa gaba d'aya sun canja, ya yi rama sosai tamkar ba shi ba.
Hannuwansa duk biyun ya sa ya rirrik'e na Khalid lokacin da suka shigo tsakiyar court din. Wani razanannen k'ara ya saki sadda suka iso gaban Alkali, a lokaci guda ya zube k'asa a sa'ar da ya kai dubansa setin da su Mubee ke tsaye.
www.lubabatumaitafsir.com
www.wattpad.com/iLubieee
_This one is yours. Nd you alone jama'ar *TASKAR LUBIEE MAITAFSIR*. A ci gaba da gashi mutanena. Lubbatu na kaunarku._
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubbatu Maitafsir
{19}
_This one is yours *QUEEN DANKANO*. Thank you for been a great fan._
Salati mutanen cikin kotun suka d'auka baki d'aya, da sauri Khalid ya fara jijjiga shi, a sa'a guda alkalin yana buga kundin gabansa yana fadar
"Order... Order in court."
Dak'yar suka daidaita surutunsu, yayin da Khalid ya dauke shi a kafada, hakan ya bama Alkalin damar gyara zaman gilashin fuskarsa, ya d'ago yana fuskantar mutanen
"Zamu ci gaba bayan mun dawo break."
Daga haka ya mik'e ya fita, Jay tayi gaggawar bin bayan su Khalid, haka Hajja Fati, Zulaiha, Alhaji Badaru, har ma da Mukhee wanda dakyar aka samu ya halarci zaman na yau. Ruwa mai matsakaicin sanyi aka yayyafa masa, sai da ya d'auki kusan mintina ukku, kafin ya ja wani dogon numfashi, ya fashe da kuka. Idanunsa a lullube, haka ya damki hannun Jay da ke rik'e da kanshi, ya ci gaba da kuka yana fad'in
"Dan Allah kuyi hak'uri. Kuyi hak'uri dan Allah. Ku kyale ni, ni gida zan tafi."
Surutai barkatai ya ci gaba da yi, sai da suka sha wuya sosai, kafin tunaninsa ya daidaita. Jay ta fara mikewa, ta umarci Khalid ya kamo shi su k'arasa chamber inda judge ke jiransu, kasancewar ta lura ya fi shakuwa da Khalid din a kan iyayensa.
"Me kuma za ayi a wani Chamber? Wai wannan wane irin masifa da bala'i ne ya ke tunkararmu haka? Haba jama'a. Kina gani fa da idonki yaron nan ya fad'i ya suma saboda kawai kallon fuskar Alkalin can, shine kuma zaku kara maida shi wurinsa? Sam, ba zan lamunci wannan ba wallahi. Ina dalili. Babu inda yarona zai je Allah."
Hajja Fati tayi maganar tana k'ok'arin kwace hannun Tareeq da ke cikin na Khalid. Barr. Jay ta gyara tsayuwa tana mata duba mai cike da tsagwaron tsana, ranta idan yayi dubu, gaba d'aya ya baci a wurin.
"Haba Hajiya."
Ta fad'a tana nuna ta.
"Wai ku wadanna irin iyaye ne dan Allah? Ki kalli halin da yaron nan ke ciki, duk waye yayi sanadiyyar jefa shi in ba ku ba? Ko kin zata bani da labari ne? Ko kin zata ban san irin rikon sakainar kashin da kike yi ma yaranki ba? Ko a zatonki ban san wacece ke ba? To komai na sani Hajja Fati, rufin asiri ne nike miki a matsayinmu na musulmi, nd for your information, faduwar Tareeq bata da nasaba da kallon fuskar Alkali, azzaluman da suka keta haddinsa, su suka jefa shi a yanayin da ya tsinci kansa. Nd please. Ku bar ni inyi aikina da Allah."
Ta juya cikin matsanancin fushi,
"Kama shi mu je Khalid."
Bai bata lokaci ba ya kama hannunshi suna takawa a hankali, zuciyar Khalid fes-fes, dan kuwa ba kadan ba ya ji dad'in abinda Jay tayi ma Hajja Fati. Haka suka yi sororo daga ita har Alhajin, suna duban juna cike da tuhuma, yayin da maganar Jay ta tsaya masa ya rink'a maimaita 'ko a zatonki ban san wacece ke ba?'
"Shin wacece matartashi? Me kuma hakan ke nufi?'
Bashi da amsar ko daya daga tambayoyin, dole ya koma ya zauna, itama ta silale a wurin zuciyarta cike dam da da na sani da takaici.
Sa'adda suka shigo Alkalin na zaune a kujerar da ta fi sauran kujerun wurin tsawo, dan sai an taka stairs har ukku, kafin a cimmasa. Barr. Jay tare da Barr. Nasib na zaune a bangaren dama. Khalid da Tareeq suka zauna a kujerun da ke fuskantar Alkali, yayin da Barr. Hisham ke daga bangaren hagu yana bibiyarsu da wani makirin kallo.
Shiru duk wurin ya yi, har zuwa lokacin da Alkalin ya d'ago daga rubutun da ya ke, ya sauke dubansa ta bangaren Jay.
"Da alama baki dade a practice ba ko?"
Ta d'an muskuta, kanta a k'asa ta ansa da
"Yes My Lord."
Wani murmushin kasaita ya zubar, domin yadda take abubuwan nata ne ya bashi damar fahimtar hakan, a sa'a guda Barr. Hisham ya saki murmushin jin amsarta, a zuciyarsa yana fad'in 'ashe ma learner ce' kafin duk suka maida hankali ga abinda Alkalin ke fad'a.
"You can proceed."
Yace da su. Hakan ya sanya Jay mikewa, ta cire wayarta tare da danna recording, sannan ta k'arasa cikin natsuwa, ta isa gaban teburin da su Tareeq ke zaune. Murmushi kyakkyawa, na ban mamaki ta dauko ta dora ma labbanta, ta dube shi da fuskarta me sanya shi murmushi, ya ko murmusa a sa'a guda ta fara magana cikin kwantar da murya.
"Tareeq Sweetheart, me ya baka tsoro naga ka fadi lokacin da ka kai dubanka bangaren da su Mubee ke tsaye? Ko akwai wani abu da ya taba shiga tsakaninku?"
Jin ta ambaci sunan Mubee ya sanya shi matse hannun Khalid da ke cikinnasa, hawayen da bai tantance ba suka silalo a kan kumatunsa, ya fara girgiza kai, duk a lokaci guda.
Hannunshi Khalid ya rik'e da kyau, yana dubansa, da ido ya masa alamar yayi magana, amma ya ci gaba da girgiza kansa, duk kuwa da cewar a yanzu babu abinda ya fi bukata wanda ya wuce ya amayar da ciwon da ke ci masa zuciya, abinda ke hana shi bacci, yake kuma sanya shi yin mugayen mafarkai a kowanne dare. Sai dai tunanin abinda hakan zai haifar yake yi, yana gudun kada mutanen su k'ara yi masa abinda suka yi a baya.
"Sune suka sa aka kaika asibiti ko?"
Ta tambaya a karo na biyu, yayin da Barr. Hisham ya juya gare su
"Barrister kina son kiyi forcing dinshi fa, da alama yaron nan bai ma san abinda kike magana a kai ba. Please kinsan bamu da lokacin batawa..."
Bai kai ga rufe bakinsa ba, suka tsinkayi muryar Tareeq.
"Ban san me na yi musu ba."
Ya yi maganar cikin sheshshekar kukan da ya tsuma zuciyar Jay, har ya sanya ta matse nata kwallan, tana girgiza masa kai alamar bashi kwarin gwiwa. Haka ma Khalid ya rik'e hannunsa, ya na mai karfafa masa gwiwa ta wannan hanyar.
"Shine ya d'auke ni a kafadansa.... Uhnmm.. Ya saka ni cikin mota, nace yayi hakuri ya kyale ni, amma... amma baya jin me nake cewa. Ni.. Ni wallahi banyi masu komai ba,.."
Ya fashe da kuka mai ciwo, ya kwantar da kanshi a kafadar Khalid, hakan yasa ya dinga shafar kanshi. Sai da ya tsagaita da kukan, sannan ta k'ara tambayar
"Da ya saka ka a mota sai mai ya faru?"
Cikin ruwan hawaye tayi maganar, a lokaci guda tana murmushin karfin hali, wanda a zahiri ya fi kukannata ciwo.
Shiru yayi tamkar ba zai ansa ba, har sai da ta maimaita tambayar. Kanshi a k'asa ya ce
"Tafiya suka yi... ina ta kuka amma basu sauke ni ba, a wani wuri suka tsaya, sai wani yace su fito da ni su kwantar da ni...."
Kukan da yake yanzu, tamkar a lokacin da abun ya faru ne, kuka ne mai tsuma zuciyar mai sauraro, hakan yasa hatta da Alkalin sai da ya tausayawa yanayin da ya ga Tareeq d'in ya shiga.
"Me sa baka gudu ba bayan sun fito da kai?"
Ta tambaya a tsanake, tare da addu'ar Allah yasa ya bada ansar tambayar da tayi a dunkule.
Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke, kansa a k'asa idanunsa na zubar da kwalla, muryarsa na karkarwa ya na fad'in
"Ai shine..."
Sai kuma yayi shiru. "Ehnnn.. fada mun inji Tareeq, shine me?"
"Shine.. ya kwantar da kaina a cikin k'asa... Shi kuma... shi kuma sai ya zauna a kaina."
Hawayen da take mak'alewa suka silalo, ta fashe da wani irin kuka mai tsantsan radadi da zafi, tasa hannayenta duk biyun ta toshe bakinta, shima Tareeq kukan yake yi, haka Khalid hawaye ke fita a idonsa, sai da suka yi mai isarsu, kafin ta juya tana fuskantar Alkalin wanda ya tallabi habarsa da hannunsa mai rik'e da biro yana kallonsu.
Fuskar Barr. Hisham tayi wani irin ja, abinka ga farin mutum, hankalinshi ya tashi matuka, jin bayanan da Tareeq ya yi, cikakkar sumar kansa ya sanya hannu ya shafa, kafin ya maida duba ga Alkalin. Wata kwarin gwiwa ya ji ta saukar masa dan da nan, ya saki malalacin murmushi sannan ya fara magana.
"This is crazy. Ta yaya victim d'in rape zai rinka magana haka? Ya kamata ace Barrister ta biyo ta wata hanyar ba dai wannan ba, dan duk wanda ya ga abinda suka yi, ya san acting suke yi. Tabbas sai da suka tsara shi kafin su shigo nan. To be honest, ban yarda da ko magana d'aya tasu ba My Lord."
Ta shafe hawayenta, ta kashe recording din da tayi, ta juya ta fuskanci Hisham, fuskarta babu digon walwala, ta jefe shi da wata irin hararar da ta sanya shi shan jinin jikinsa, sannan ta waiwaya ga Alkalin.
"My Lord, babu karya ko wani abu wai shi acting a abinda ya gabata, ina rokon kotu tayi duban tsanaki ga bawan Allahn nan, ta kuma bi masa hakkinsa."
"Zaku iya jira a waje."
Alkalin ya umarci Khalid, yana nuni musu k'ofa da hannunsa, hakan yasa suka mik'e suka fita, yayin da shima ya mik'e tsaye, Barr. Nasib, Jay, da Barr. Hisham suka rufa masa baya.
A wannan dawowar kotun ta k'ara cika, kowa yana zaune tsit, hankalinsu ya ta'allaka ga bayanan da Alkalin ke fitarwa cikin harshen turanci.
"A gajeruwar ganawar da nayi da victim d'in, na fahimci wasu abubuwa masu rudani dangane da shari'ar tamu. Amma kafin nan, ina lawyer wanda yake k'ara?"
Ta mik'e tana fad'in
"My Lord."
"Shin ko kina da wani abu da kike son sanar ma kotu?"
"Yes My Lord."
Ta bashi ansa, sannan ta k'ara da cewar
"Ina rokon alfarmar kotu, da ta taimaka, ta dawo mun da Dr. Rilwan, domin gudanar da wasu 'yan tambayoyi da na manta in masa."
"Objection My Lord."
Hisham ya fada a razane, sa'ar da ya mike tsaye ya ci gaba
"Babu dalilin da zai sa Barr. Jameela ta dawo da witness dina, bayan kowa a nan ya shaida sai da ya amsa dukkan wasu tambayoyin da suka masa."
Girgiza kai Alkalin ya yi, bai kuma ga laifinta ba, dan ta sanar mishi bata dade a practice ba, hakan ne kawai zai sa ya bata uzuri. Ya kalli Barr. Hisham
"Korafi bai kar6u ba."
Ya juyar da kallonsa gare ta.
"Kotu ta baki dama."
Barr. Hisham ya koma lagwab, jiki babu k'wari. Yayin da ta rissina tana fad'in
"Na gode My Lord."
Daga nan aka shigo da Dr. Rilwan, wanda idanunsa kadai za'a kalla, a san gaskiya bata tare da shi.
Ta isa ta kama yar katangar da yake tsaye a ciki, ta saita idanunta a kansa, sannan ta fara magana.
"Dr. Rilwan ka shaida ma kotu cewar, kana aiki da gidan mahaukata. Idan babu damuwa zan so ka banbance ma kotu asibitin da kake aiki da shi."
Ya daidaita gilashinsa, ya sharce zufar da ta yayyafo saman goshinsa, kafin ya ansa da cewar
"Ina aiki da Hikma international psychiatric."
Ta murmusa, tana ci gaba da dubansa
"Private hospital kenan?"
Ya girgiza kai, alamar haka ne. A lokaci guda murmushin samar fuskarta ya gushe,
"Hakan yasa aka had'a baki da kai, aka ci fuskar witness dina, aka lakaba mishi kazafin da bai ji ba, bai kuma gani ba?"
"Objection My Lord. Barrister na k'ok'arin shiga hurumin da ba nata ba."
"Objection sustained. Counsel ki kiyaye."
Sai da ta rissina, ta ce
"As the court pleases."
Ta maida dubanta gare shi,
"Dr. Rilwan ka shaida ma kotu cewar, ka shekara biyar kana kula da larurar Mal. Habibu. Haka ne?"
"Haka ne."
Ya fad'a a k'agauce.
"Okay, shin a bola kuka tsinci Mal. Buzu Habibu lokacin da yake cikin haukan, kuka dauke shi zuwa psychiatric, ko kuwa wani dan uwanshi ne ya kawo muku shi domin ku kula da lafiyarsa?"
Shiru Dr. Rilwan yayi, ga wata irin zazzafar zufa da take yanko masa, tamkar babu na'urar sanyaya d'aki a wurin, ta kwankwasa yar katangar da yake jiki, hakan ya dawo da hankalinsa daga yawon da ya tafi na wucin gadi.
"Kai nike saurare Dr."
"Eh? Uhnmm.. ai wani dan uwansa ne ya kawo mana shi."
"Masha Allah Dr. Rilwan. Na tabbata tunda har wani ne ya dauko shi cikin hauka ya kawo muku shi domin ku kula da lafiyarsa, I'm sure baza ku rasa contacting juna kai da shi ba, kamar yadda kace har yau bai daina shan magani ba, ta yiwu ta hannun wanda ya kaishi din ne maganinsa ke bi ya isa gare shi. Dan haka ina rokon da ka taimaka ma kotu da number dan uwan na Mal. Buzu, domin mu kira shi, mu ji ta bakinsa."
"Objection My Lord."
Hannu, Alkalin ya daga masa, tun bai kai ga yin suka ga maganar tata ba, a sa'a guda ya girgiza mata kai alamar ta cigaba yana mai kallonta, a zuciyarsa yana yaba hazakarta, ya san tabbas a zuwa gaba zata zama daya a jerin lauyoyin da za'a rink'a alfahari da su a k'asar ta Nigeria.
Rissinar da kai tayi ga Alkalin, kafin ta juya ga Dr. Rilwan.
"Bani da number wayarshi gaskiya."
"Address dinshi fa?"
Ta jefa masa tambayar tana ci gaba da dubansa.
"Ta yaya zan gane inda yake zama mutumen da ban taba ganin shi ba?"
Kamar wanda aka gwabji bakinsa, haka maganar ta fito, a sa'a guda ya tallabi kansa, domin a zuciyarsa yayi maganar, bashi kuma da yak'inin cewar zata bayyana kowa ya ji.
Murmushin alfarma tayi, ta juya ga Alkalin.
"My Lord, idan aka yi la'akari da medical report da Dr. Rilwan yace ya rubuta shekaru biyar da suka gabata, wanda ya kasance na asibitin kudi, za'a ga cewar Barr. Hisham da shi Dr. Rilwan suna son yin wasa da hankalin shari'ah ne, haka kuma zata iya yiwuwa biyansa aka yi, ya rubuta report din, kasancewar asibitinnasu dama neman kudi suke da shi. Abu na biyu a nan, Dr. Rilwan ya sanar ma kotu cewar dan uwan Mal. Buzu ne ya dauke shi da hannunsa ya kaishi wurinsu, a lokaci guda kuma ya sanar ma kotu cewar bai taba ganinsa ba. Ta ya ma hankali zai d'auki wannan soki burutsun?"
Ta murmusa cikin takunta mai cike da kamala, sannan ta ci gaba.
"Haka zalika a shekaru biyar din da Dr. Rilwan yake magana, Mal. Buzu Habibu bai ma shigo kasar nan ba, kamar yadda yaron gidan Col. Shu'aibu Tukur zai sanar mana a yanzun nan ba sai anjima ba. Da wannan nike neman alfarmar kotu da ta gabatar mun da Mu'azzam Shu'aibu Tukur."
Dogon matashi ne d'an hutu, mai cikar gashin kai ya bayyana a gaban kotun, ya tsaya a bangaren da ke fuskantar na Dr. Rilwan.
Rantsuwa kotu ta sa shi yayi, tare da alkawarin fad'in gaskiya. Sannan Jay ta k'arasa gabansa.
"Idan babu damuwa zan so ka sanar ma kotu cikakken sunanka da alak'arka da Buzu Mal. Habibu."
"Sunana Mu'azzam Shu'aib Tukur, Buzu Mal. Habibu yana gadi a gidan mahaifina."
"Shekarun Buzu nawa kenan Da fara aiki a gidanku?"
"Shekara d'aya kenan da wata biyu ina ga."
"Shin a cikin garin Kaduna kuka san Mal. Buzu? Ko kuma kafin nan ya sanar muku cewar ya taba aiki a wani gidan kafin ya fara aiki da ku?"
"No, ba KD muka san shi ba. Kuma gidanmu ne gida na farko, da ya fara aikin gadi. Cuz tsohon mai gadinmu mutumen Maradi ne da ke k'asar Niger, lokacin da zai koma gida, ni mahaifinmu ya had'a da shi, na mayarsa gifa, tare da alkawarin idan mun je zai had'a mu da sabon wanda zai ci gaba da yi mana gadi, a lokacin ne ya had'a mu da Mal. Habibu, wanda a wannan zuwan ne kuma zuwan shi Nigeria na farko a gaba daya rayuwarsa."
"Shin kun taba fuskantar wani boyayyen al'amari a tattare da shi? Ko kuwa kun taba ganin shi cikin wata siga da ta fi kama da ta mahaukata?"
"No, gaskiya bamu taba ba."
Cikin tsananin farin ciki ta furta
"Na gode Mu'azzam."
Ta saita dubanta ga Alkali wanda ya ke kule da duk abinda ke faruwa sannan ta fara magana.
"Kamar yadda Mu'azzam ya shaida ma kotu Buzu Mal. Habibu shekararshi ta daya kenan a kasar nan, haka kuma bai taba zama a gidan mahaukata ba. Da wannan nike rokon alfarmar kotu da ta yi watsi da shedar da Dr. Rilwan ya bayar, cuz gaskiya ta bayyanar da kanta cewar sharri kawai suka masa domin suyi wasa da hankali, da kuma tunanin shari'ah. Haka kuma ina so kotu ta fahimci cewar statement din Buzu Mal. Habibu da tayi condemning gaskiya ce ziryan, babu k'age ko sharri a ciki, kamar yadda ya yi rantsuwa ga kotu cewar ya ga mutanen can lokacin da suke ajje gangar jikin Tareeq a gefen gidansu, wanda hankalinsa bai bashi cewar bil adama ne ba."
Ta rissinar da kanta, kafin ta koma mazauninta.
Alkalin bai k'ara magana ba, sai dogon rubutun da ya dukufa da yayi, daga k'arshe ya d'ago yana fuskantarsu
"Akwai mai sauran abun cewa?"
Da sauri Barr. Hisham ya mik'e.
"Ina rokon alfarmar kotu da ta bani belin clients dina har zuwa lokacin da za'a cimma k'arshen shari'ar nan."
Rubutu mai matukar tsawo Alkali ya yi, a k'arshe ya d'ago yana duban Barr. Hisham ta k'asar gilashinsa.
"Kotu baza ta bayar da belinsu ba, cuz of the nature and gravity na offence din, had'i da nauyin evidences d'in da muke da su a k'asa. For now, kotu zata cigaba da tsare su saboda wasu kwararan dalilai."
Kalmar inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, kawai Barr. Hisham ke nanatawa a k'asar zuciyarsa. A sa'a guda yana tambayar kansa wannan wace irin bak'ar rana ce? Muryar Alkalin ce ta dawo da shi daga dogon tunaninsa yana tambayar
"Counsel, kuna da sauran abun fad'a?"
A tare suka girgiza kai ita da Barr. Nasib, hakan ya ba ma Judge damar ci gaba
"Ku duba diary dinku, akwai mai shari'ah on twenty eight of this month?"
A tare suka shiga dubawa hadda Barr. Hisham, suka kuma dagowa a tare suna sanar da shi cewar babu.
Gyara zamansa yayi, ya k'ara rik'e bironsa da kyau, yana fuskantar mutanen cikin kotun, sannan ya fara magana.
"Duba ga yanayin shari'artamu ta yau, kotu zata dage wannan k'ara zuwa ashirin da takwas ga wannan watan."
Daga nan ya buga kundin da ke gabansa. Ya bukaci Registrar da ya yi kiran k'ara na gaba.
Hajja Fati da Alhaji Badaru babu mai bakin magana lokacin da aka fito, itama Jay bata bi ta kansu ba, ta isa inda Tareeq da Khalid ke tsaye, ta duk'a tana shafar kanshi labbanta kunshe da murmushin birgewa.
"Da yardar Allah sai na kwato maka hakkinka Tareeq. Ka taya ni da addu'a ka ji?"
Kai ya girgiza yana mata murmushi, ta mik'e ta shafi gefen fuskarsa, sannan tayi musu sallama ta juya, domin k'arfin hali kawai take yi, Allah kadai ya san yanayin da zuciyarta ke ciki.
Tana dagowa suka had'a ido da Alhaji Barau, kallon k'urilla suke mata su duka, har ma da Barr. Hisham, hakan ya sanya ta tsarguwa, ta kawar da kanta cikin sauri, ta doshi inda ta adana motarta.
Handle din motar ta rik'e a kasalance, tana k'ok'arin latsa makullin hannunta, ga mamakinta ta ji motar a bude, ta sauke gauron numfashi a bayyane, ta furta
"Owh Allah, wahala ta sa na ma manta ban rufe motar ba."
Ta zubar da kayan hannunta a kujerar mai zaman banza, a sa'a guda ta bama motar wuta ta wuce harabar kotun baki daya.
Gudu sosai take yi, domin burinta d'aya ta isa ta saita idanunta cikin na habibinta, watak'ila zai k'arfafa mata gwiwa, a yadda take jin tamkar duniyar ta juya mata baya.
Ta mirror ta hango wani bakin kato ya mik'e zaune daga durkushin da yayi a bayan motar, ya saita kan bindigarsa ta gefen fuskarta, addu'ar da ta rink'a nanatawa a k'asar zuciyarta ne kawai ya hane ta sakin steering da ke hannunta.
"Shut the f**k up."
K'aton ya ce da ita, yana kallonta ta madubi.
"Ki d'auki hanyar bypass."
Bata da wani zabi da ya wuce mata yin abinda yake so, ta kuma tabbatar da Allah ne kawai zai iya cetonta daga halin da ta fada, kasancewar gaba daya gilassan bayan motar, lullube suke da leda mai sanya duhun gilassai. Yana ganin haka ya sanya hannu ya d'auke jakarta, ya laluba wayarta ya dauka ya kashe, sannan ya jefa ta aljihu.
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
©Lubabatu Maitafsir
{20}
_Nd this one is for *NAFEESA MAITAFSIR* & her #team. Guys sakon gaisuwarku ya same ni. Nd I appreciate everything. #DTBIJ rocks..._
Tun daga yanayin gate din gidan da Kato ya kai ta, wanda da remote yayi amfani wurin bude shi, ta fahimci girmansa. Yanayin tsarinshi sosai ya sa ta shagaltu a kallonshi, har tana kokarin manta halin da take ciki, a lokaci guda tana mamakin ashe akwai irin gidajen nan a garin Kaduna? Upstairs ne, wanda a yadda take daga waje, baza ta iya tantance ko hawa nawa ne ba, baki sake, ta karkatar da akalar motar zuwa karkashin tangama-tangaman parking shades din da suka k'ara fito da tsaruwar gidan, ta tsaida motar kamar yadda ya bata umarni, ya fito amma duk tana zaune, har kuma yanzu bai sauke bindigar daga saitinta ba, ya bude mata k'ofa, sannan yayi mata umarnin fitowa.
Wata doguwar baranda suka bi, wacce aka k'awata gefenta da dogayen vases na flowers, wanda kanshinsu kawai, ya isa kawar ma mutum duk ko wacce irin gajiya ya kwaso. Gaban yar karamar na'urar da ke makale da kofar palon ya isa ya danna wasu numbers, a sa'a guda kofar ta bude, ya yi mata nuni da ta wuce ciki, ta hanyar amfani da bindigarsa.
Suman tsaye Barr. Jay tayi, sa'adda ta tura kanta cikin makeken palon ma'abocin sanyi da kanshin dad'i, mai k'unshe da manya-manyan leather cushion kalar ruwan k'asa mai haske.
Silky curtains din da suka yi ado wa palon ma haka kalar su take, dogon t.v stand wanda ya dauka tun daga bangon dama, ya k"arashe a bango na hagu, sai katuwar LED t.v manne da bango, wacce bata tantace product dinta ba. Lallausan cream din carpet, shimfide a tsakiyar palon, sai centre table wanda k'irarsa iri daya ce sak, da ta t.v stand din.
Daga bangaren hagu madaidaiciyar drawer ce mai fadi anyi jeren frames, da k'ananan flower vases.
Tunaninta ya katse, sa'ar da Kato ya mik'a mata waya, yana fad'in
"Ansa nan mai gida zai yi magana da ke."
Tana kyarma ta ansa wayar, ta dora a kunnenta, kafin ta kai ga sallama aka ce
"Ya kika ga gidan? Do you like it?"
Wani mugun yawu ne ya tokare wuyanta, ta had'e dakyar, tunawar da tayi da girman gidan, wanda tana yiwuwa nan inda take ciki, shine palo mafi karanta a cikin sauran.
"Da wa nike magana Dan Allah?"
Ta furta cikin sanyin murya.
Dariyar ban girma aka saki ta wancen bangaren, cikin wata kakkausar murya ya ce
"Matsawar zaki yi watsin Allah tsine da shari'ar da ke gabanki, ina mai tabbatar miki zaki mallakin gidan da kike ciki, har ma da nera million d'aya da rabi din da suke cikin account dinki. Ya kike gani?"
Idanunta waje, mamaki ya cika fuskarta ta ce
"Dama kune kuka tura kudi ta account dina? Dan Allah Malam me kuke so da ni? Me nayi muku?"
"Babu abinda muke so da ke sai alkairi Barrister. Dan haka ki ci arziki ki barshi a inda kika ganshi. Wannan dama ce ta same ki, sabanin haka kuwa, ina mai tabbatar miki, rayuwarki tana cikin mummunan hadari. Amma zan baki daga nan har zuwa kwana ukku, kiyi tunani, haka kuma idan kika yi yunkurin sanar ma wani, ina mai jaddada miki da sai kinyi mamakin abinda zai faru a kan yaranki guda hudu. Ina da address din makatantarsu, na kuma san ajin da kowannensu yake."
Ya saki shu'umar dariyar da ta kada yan hanjin Jay, kafin tayi wani motsi ya datse wayar, Katon da ke gefenta ya anshe, ya kuma tusa k'eyarta zuwa waje.
Tunani barkatai, suke yawo a kwanyarta, babu komai da ta iya furtawa banda kalmar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel."
Haka ta isa gida sukuku, babu wani kwarin jiki a tare da ita, duk da sanyin idaniyartata da ta dora a idanunta a kai, hakan bai rage ta da jin tashin hankalin da take ciki ba. Ya zata yi da wannan mummunan had'arin da mutanen nan ke shirin jefa rayuwarta? Sai tayi yunkurin sanar ma SS, sai kuma ta tuna da furucin mutumen na k'arshe, hakan ke sa ta yi masa karyar babu komai a duk tambayar da zai mata.
****
Alhajin na lura da yanayinta, tunda suka taho bata da sukuni, kadan-kadan kuma ta kan kai duba ga wayarta, wacce ake ta faman kira amma ta k'i dagawa.
Suna isa gida ta fito da sauri, ta wuce ciki, ta ansa kiran da ya k'ara shigowa, ta kara a kunnenta.
"Haba Hajiya Maryam, kin fa san ina kotu game da shari'ar Tareeq, a matsayinki na aminiyata, ai kyayi hak'uri koma menene in dawo gida, ba wai ki rink'a kira ba, har kina tura mun sakonnin cin fuska, wanda ban ma san ina suka dosa ba."
Cikin hargagi Hajiya Maryam ta ansa da cewar
"Ina ruwana da shari'ar wani Tareeq? Menene hadina da shi da har zan daga miki kafar cin amanar da kika mun? Tabbas kin zama butulu Hajja Fati, za kuma ki san kin shiga gonar da ba taki ba. Ke har kin isa kiyi takara da ni? Kin manta ni na rene ki a barikin? To wallahi baki isa ki so abinda nike so ba. Sanin kanki ne duk duniya, ban had'a Baby Nice da ko wacce mace ba. Ki saurari abinda zai biyo baya."
Ta kashe wayar ta bar Hajja Fati cikin tsananin rudu, da tashin hankali.
'Ya akai Hajiya Maryam ta san tarayyarmu da Baby Nice?'
Ta tambayi zuciyarta, a karo guda ta kara da cewar
"Shin wai wane munafikin ne ya sanar mata?'
Bata da ansar ko da d'aya daga tambayoyin, dole ta sanya ta mikewa, ta zari jaka da makullin motarta ta fito. Rashin ganin motar Alhaji Badaru ya tabbatar mata ya wuce meeting din da yace yana da shi, hakan yasa bata ko kalli bangaren da yarannata suke ba, ta shige mota ta wuce gidan Hajiya Maryam.
Yau ma kamar kullun gidan cike yake da matasan yan mata, ta shigo da sallama, sai dai babu wanda ya yi mata tarbar da suka saba. Dakin Hajiya Maryam ta k'arasa, kyakkyawar budurwar da kallonta kawai ke sanya nishadi a zuciyar Hajja Fati, wato Baby Nice, (matashiyar da Alhaji Badaru ya samu a dakinta kwanakin baya) tana kwance tana latsa waya, a lokaci guda tayi matashin kai da kafar Hajiya Maryam.
Da sauri ta sauke kallonta gare ta, ta samu gefe ta dosana mazaunanta, tana mai jin wasu kibiyoyin kishi suna kai suka a k'ahon zuciyarta.
"Wata tsiya ta shigo da ke gidana? Me kike nema a wurina kuma?"
"Haba Hajiya Maryam. Wai ya kike magana haka? Me yake faruwa?"
"Aow, baki ma san me yake faruwa ba ko?"
Ta fad'a lokacin da ta dora kan Baby a pillow, ta mik'e tana nuna ta da hannu.
"Munafuka, ma ci amana, butulu da bata san muhimmancin aminci ba. To gwada ki nayi dama Hajja Fati, ashe hasashena ya zama gaskiya, ta yanayin kallon da na ga kina yawan bin Baby da shi yasa nace ta gwada ki mu ga, munafuka, ashe ko abinda ke zuciyarki kenan? To asirinki ya tonu, kuma ina mai tabbatar miki daga kaina kin gama cin amanar wani."
Ta wuce da sauri tana kiran
"Riirii.. Riirii. Kuna ina?"
Da sauri wacce aka kira da Riirii ta shigo, Hajiyar ta kalle ta tace
"Kira su Helen ku shiga kuyi mun maganin k'aramar yar barikin can."
Da haka ta wuce zuwa d'akin da ke kallon nata, yayin da Riirii ta mik'e zuwa aikin da Hajiyar ta saka su.
Kallon Baby Nice Hajja Fati tayi,
"Tabbas kin ci amanata Baby. Yanzu duk irin kauna da makuden kudaden da na rinka kashe miki, da abinda zaki saka mun kenan? Lallai kin cika makira."
Murmushinta mai tsada ta saki, ta jefe ta da wani kallon wulakanci, kafin ta maida hankalinta ga chatting dinta.
Hakan da tayi ba k'aramin k'ular da Hajja Fati yayi ba, ta ja mugun tsaki, kafin ta juya da zumar barin d'akin, a dai dai lokacin suka yi kici6is da tawagar Riirii da suka doso kai ciki.
Kafa suka sa suka tokare ta, vs tare da bata lokaci ba ta fad'i k'asa sharaf, suka bita suka ci gaba da bugunta ko ta ina, a lokaci guda Hajja Fati ta fara ihu, hakan ba k'aramin dariya ya ba Baby Nice da ke hakimce saman gado ba, nan da nan ta cire wayarta ta fara videoing nasu.
Irin bugun da suke mata, tunda ta zo duniya ba'a taba yi mata ko da rabinsa ba, haka yara kanana, ya'yan cikinta suka dinga pacing da ita sai kace kwallo. Wannan ta mangare ta, ta mik'a ma wannan, har sai da suka yaga mata riga, hannun rigar ya bar jikinta gaba d'aya, amma makullin motarta wanda shi kadai ta iya yima kyakkyawan riko, duk kuwa da bugun da suke mata bai sa ta yar da shi ba, yana nan mak'ale a hannunta. Dakyar ta kwaci kanta, ta rantama da gudun bala'i, amma haka suka bita suka ci gaba da kwalfarta, har Allah ya taimaka ta kai ga k'ofar gida, idonta guda ya kumbura suntum yana zubar da jini, haka gefen fuskarta, har ma da hannunta na dama.
K'arfin hali ne kawai ya sanya ta tuka motar, kanta ko kallabi babu, balle ayi maganar gyale, a haka ta iso gida, tamkar mahaukaciyar da ta fara hauka a ranar.
Tambayar duniya babu wacce yaran ba su yi mata ba sa'adda ta iso, sai dai tace accident ta yi, amma hankalinsu sam, bai dauka ba, ganin babu ko da k'warzane a jikin motarta. Wata Nurse da ke makwabtansu ta aika Asabe ta kira, ita ta dudduba ta, ta bata magani, bayan ta tafi ta koma d'aki ta kulle, sai a lokacin abinda ya faru ya rink'a dawo mata, bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Kuka take mai tsananin zafi, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, da na sani da takaicin rayuwa ya gama bayyana a kan fuskarta. Idan akwai abinda ke saka ta kuka, baya wuce idan ta tuna yaran da suka wulakanta ta, wanda a shekaru idan sun girmi Zulaiha, to da kadan ne. Ta k'ara fashewa da kuka mai radadi; a lokaci guda ta ji gaba d'aya duniyar ta mata nauyi.
Har bayan isha'i, ta gagara fitowa daga d'aki, tunaninta da wane idon zata kalli yarannata? Yayin da su kam suke zaune shiru, duk da ba wata shakuwar kirki suka yi da ita ba, amma abun ya matukar razana su, mussamman ma Tareeq, wanda tashin hankalin nasa ya zama biyu.
Karan wayar Zulaiha ne ya sanya su maida kallo gare ta, ta duba wata class mate dinsu ce, bayan ta dauka tace mata ta shiga whatsapp da sauri, ta tura mata wani abu.
Suna kashe wayar ta duba whatsapp din, tun bata kai ga isa ga number kawartata ba, ta fara cin karo da video din mahaifiyarta sadda kananan yara ya'yan cikinta, suke dukanta tana ihu a wani group dinsu 'Just Chill' mai cike da matasan 'yan mata da samari.
Wani lafiyayyen zagi ta dauko ta dora, hakan ya jawo hankalin sauran yan uwan da ke zaune gabanta, ta mik'e da sauri, suna tambayar lafiya? Amma bata ko bi ta kansu ba ta isa ta dinga dukan d'akin mahaifiyartasu.
"Haba Maaa dan Allah, wane irin hauka nike gani haka?"
Na fada sa'ar da Maman ta bud'e k'ofar, ta tura kanta ciki ta wurgi mata da wayar.
"Haukan ub***n me? Wata tsiya ta faru kuma?"
"Zaki ce haka dama, gashi ki gani da idonki, ko kina da bakin karyatawa?"
Ta fashe da kuka tun k'arfi, ta nuna ta da hannu
"Wannan wane irin cin fuska ne tsakani da Allah? Kin gama zubar min da class a idon friends dina. Me kike so ince da wadanda suka san ke kika haife ni? Wai ma Dan Allah me ya hada ki da kananan yaran nan, 'ya'yan cikinki har suka miki tashancin nan?"
Cikin matsanancin borin kunya ta daga hannu ta kwalfe ta da mari,
"Ke har kin isa Zulaiha? Yaushe kika yi k'warin wuyan da har zaki na jifata da wadannan muyagun kalaman? Ki shiga taitayinki wallahi."
Wani mugun kallo ta watsa mata,
"Ni kika mara kan na fada miki gaskiya? To fiye da wannan ma sai in miki a yanayin nan, ni kinsan irin kunyar da kika saka ni?" You're a disgraced!"
Ta buga mugun tsaki, ta juya da zumar d'aukar wayarta ta fice, taga wayan hannun Mukhee, ya kuma ga video din, har ma da wasu daga comments din mutanen group din.
Bacin ran da ke kan fuskarshi ya dama na Zulaiha, nesa ba kusa ba, idanunsa da suka koma jajaye already ya sauke a kanta.
"Kin gama wulakanta mu Maaa wallahi. Me hadinki da kananun yara haka? Fi sabililLahi minene fassarar abinda kika yi? Wallahi shi yasa ni sam jinina bai hadu da naki ba. Nd bazan taba yafe wannan abun kunyar ba wallahi."
Yayi wurgi da wayar ya wuce cikin tsananin fushi, haka Zulaiha ta duka ta d'auki abunta, ta buga mata harara, ta ja mugun tsaki ta k'ara gaba.
Ahmad da Samahir da suke kallon komai, kuka kawai suka saka, kamar had'in baki suka juya suka bi bayan yayyennasu suma.
Tareeq ne ya k'araso gabanta, hannunta ya kama, ya shiga shafe hawayen da suke sintiri saman fuskarta, yayin da shima nashi idanun cike suke taf da ruwan hawaye.
"Maaa me kika musu haka?"
Shiru tayi, ta kasa ansa shi, ya mik'a mata goran ruwan da ke hannunsa, ya k'ara da cewar,
"Ko ma me kika yi, bai kamata su miki haka ba. Kiyi hakuri Maa, kar kiyi fushi kin ji?"
Ta fashe da kuka ta rungume shi tsam a kirjinta. Ita din wace irin uwa ce da ta cutar da yaron da ya fi kowa jin k'anta? Tabbas laifinta ne abinda ya faru da Tareeq d'in, ta cutar da rayuwarsa, ta kuma tabbatar da ta kashe masa future har abada. Amma me sa take bakin ciki da justice din da za'a nema masa? Alal hakika a duniyar nan, bata da idanun da zata daga, ta sake kallonshi.
"I'm sorry Tareeq."
Shine kadai abinda ta iya furtawa, ta kuma fashewa da wani sabon kukan mai cike da da na sani.
0 comments:
Post a Comment