K'ura masa idanta tae da suka kad'a sukai jajir tamkar gaushin wuta, hatta bak'in idanta nata ya ya dawo kalar jajaja sabida tsabar tashin hankalin datake ciki, kuka wannan bata iyayi sedai idan nan ya dinga zogi tamkar an yayyafamai dakakken yaji, murmushi shi kuma yake cike da k'eta yana tsane ruwan kanshi bayan daya fito daga wanka
"Billy kallon na menene ehhh? Zugi wurin yake miki ko? Mazan kenan asaman kanki yarinya, shine banbancin jan zaki da kuma sauran maza masu kalar lagwani" ya k'arashe maganar cikeda shak'iyanci yana me zama suna fuskantar juna. Wani azababben yawu me asalin yaji ta had'iya tanaso k'wallan nan yae ambaliya koda zata samu damar had'iye wannan d'unk'ulallen dutse daya mulmule ya mak'ale mata a wuyan ta, da k'yar ta iya tattaro kalamanta wurin furta
"Kamal kaji tsoron Allah, ka sani wannan abin dakake sakani yi haramunne, haramtaccene acikin halataccin abubuwan da Allah ya mana halacci dayi, ka sani niba matarka mace, ka tausayawa maraicina kamal, idan har ka zab'i tarawa dani ta wannan hanyar tabbas bakamun adalci ba, idan tarawar dani shine kad'ai matsalar ka ka dena sanyani sab'on Allah, ka aureni kamal, namaka alqawarin zan sadaukar da farin cikina in aureka" Mik'ewa yae yashiga tapa hannayenshi yana shewa yana wata irin hatsabibiyar dariya
"Billy kenan, ke kina ganin da cewar dannaci baya in rasa wacce zan aura se sauran jagwalgwalon thugs? Dama wasu mutanen kirkin ne suka amshi budurcin ki zan iya aurarki kinamun gadi da aikace aikacen gida kafin in auro matar so, amma kai inahhh!!!!!" K'ololon daya tokare mata wuya ne ta had'iya da k'arfin gaske kan tace
"Ba komai kamal, wlhy ka sani Allah yana kallonka, sabida kaga banida gata shine dalilinka na cimun zarafi har haka?" Dariyarsa ya k'ara sakawa me mata mugun ciwo
"Kai Billy bada kanki zakiyi? Kece bakida gata, ke billy Bee cefa, ko kin manta in tunasar dakene?" Wani lokaci cen baya ta tunano lokaci d'aya ta runtse idanta, bud'ewan dazatayi ta ganshi tsirara a kanta
"Yaya ko zaki k'ara munne? Ehhh kindai ganta tsaye kik'am bata gajiya da ragowar thugs" muryanta yanzu kam ya soma rawa alamun zatayi kuka
"Kayi hak'uri kamal, wlhy da zafi abin nan, ko yanzu wurin yanamun azabar zafi daurewa kurun nake" d'age kafad'un sa duka biyu yae alamun keta shafa
"Tashi ki watsa ruwa mu tafi" Da k'yar ta dafa gadon ta mik'e batare datayi magana ba, da d'ingishi ta isa toilet d'in ta jima sosai tana gasa wurin tana zubar da k'walla me ciwo kan daga bisani ta watsa ruwan ta busar da gashinta da hand dryer ta fito, yana zaune harta suturta jikinta tace dashi
"Mu tafi na kimtsa" hannunsa yakai ya daki heeps d'inta cikeda shaqiyanci ya soma rera wak'ar "Na tsundumaa.. Kogin zumaa.. Idan har kika qini zakisa naji kunya, amma in kika soni zana fad'a kogin zuma.." Batace masa komai ba ta d'auki mayafinta ta yafa sannan ta d'auki jaka da wayar ta, rungumota yae ya tsoma bakinsa cikin nata yafi 5mns yana kissing nata cikeda azaba dan kuwa seda lips nata sukai ja suka soma mata zafi kan ya sake su yana nan rungume da ita a tsaye yakai d'an yatsansa ya zagaye lips nata
"Inama ace wasu banzaye baki damar rigana kwasar wannan garab'a sar ba billy? Da tabbas babu abinda ze hanani aurarki, ina mugun sha'awarki wulgawa wannan idan kikai wlhy sena tsirga" kawar da kanta tae gefe zuciyarta tana mata suya kanta janye jikinta daga nashi cikeda kasala da b'acin rai
"Kamal ummana zata nemen wlhy, shidan yamma fa" janyota yae ya rungumota gaba d'aya
"Inama ummanmu tasan 'yarta ta girma? Dame zatace? Kona sanar mata ne?" Muryanta na rawa tace
"Kamal ina maka dukkan biyayya, ko mijina dazan aura banaji zanwa fin haka, dan Allah kamal ka tallafeni ka dena aikata sab'o dani" murtuk'e fuskar nan yae
"Ke a tunaninki zan bari kiyi aure ne? Mahaukacin inane ni dazan bari kiyi aure?" Batace masa komai ba ta sadda idanta k'asa tana hawayen bak'in cikin halin da rayuwa ta jefata aciki, saketa yae ya juya, gaba ya shige suka fita ya rufe gidansa ruf, kallon sa take yanda yakeda kyau, haiba da cikar kamala ga k'warjini amma sam besan Allah ba ko kad'an! .
Umma na zaune tayi sallama parlor d'in ta shiga, kallonta umman tae cikeda tausayi
"Billy Bee tawa, an dawo ne" murmushin k'arfin hali tae
"Ummana na dawo, yau zazzab'i nakeji wlhy"
"Ayya sannu Bilkina, Allah ya baki lapia ki tabbatar kinsha magani, kwanakin nan zazzab'in nan ya sakoki agaba na rasa dalilin shi" murmushi tae ta wuce ciki uwar tabi bayanta da kallo, kodai hadda k'afafuwanta ciwo suke ne? Kalli yanda take tafiya ta ayyana a ranta, bata daice komai ba akan hakan.
"Abin duniya ya dameta matuk'a, batada lapia ko kad'an, tana tsoron idan ba ciki bane ba, takuma gagara zuwa asibiti, tayi kukan bak'in ciki batasan yaya zatayi da rayuwar taba tayi danasanin abubuwa da dama ciki kuwa hadda zuwanta jami'a, itace sanadin komai shekarunta 18 yanzu amma tana fuskantar bak'in cikin rayuwa fiye da tunani, runtse idanta tae kafin ta yanke shawarar ziyartar private clinic amata ultrasound agano damuwar ta!!!
Bincike dai anyi batada wani cikin har hoto tayi, amma menene wannan ciwon datake a tsaitsaye, ita dai tabbas tasan wlhy batada lafiya, sabida abin amaimakon yae baya kullum se gaba gaba yakeyi, abubuwan datakeji tawa doc. Bayani ya bata magunguna.
A hankali ta tura k'ofar office d'insa ta shiga, fuskar ta ba annuri kallo d'aya zaka mata ka tabbatar cewar tana cikin tsananin fargaba, zama tayi a kujerar dake fuskantar tasa tace muryanta yana rawa
"Barka da war haka kamal" kallon ta yake cikin b'acin rai
"Kamal ne sunana anan ko sir?, ban hanaki ba?"
"Kayi hakuri kuskuren baki ne sir" tsaki yaja me tsayi sosai ya daki table d'insa
"Ya mukai dake ne? Ban sanar miki cewan lallai kullum dole ki waren lokaci naba? Jiya naje gidanku kikaqi fitowa nayita neman layinki kin rufe wayar haka kikamun asarar tanadin danawa kaina a kanki hakan kika zab'a ko?" K'wallan daya taru mata ta share da bayan hannunta
"Kayi hak'uri sir, inata faman zazzab'i ne, jiyan daka aika kirana ummana aka tarar ni ina d'aki kwance tasan ban lapia setace ace ina bacci, kuma itane ta karb'e wayoyina akan in huta dan Allah karka tona sirri na zan maka duk abinda kakeso" murmushi yae
"Yau a gidana zaki kwana" da sauri ta d'ago kanta ta kalleshi cikin tashin hankali
"Ka rufan asirina sir, mezan ce da ummana?" Mik'ewa yae
"Tonuwar asirin naki kikeso kenan? Koba haka ba?" Muryanta na rawa tace
"Kayi hak'uri zance mata inada test gobe a hostel zan kwana" Murmushin gefen baki yae
"Da wuri zanzo d'aukarki k'arfe 4" marairaice fuska tae
"Motana fa? Dashi na saba zuwa school ka sani" Tab'e bakinsa yae
"Ki sanarwa Umman ana satar mota a hostel badashi zaki ba" haka ta mik'e jikinta ba k'wari ta nufi hanyar barin office d'in, harta rik'e door handle d'in ya kira sunanta
"Bilkisu" waigowa tae murya yana rawa tace
"Na'am sir"
"Zokisha wannan" ya mik'a mata wata k'wayar magani dake a tafin hannunsa, lokaci d'aya ta rikice ruwan idanta ya k'aru cikin tsananin firgici take magana
"Sir ka rufan asirina dan Allah, na tuba wlhy bazan kuma ba har abada"
"_meye bazaki kuma ba? Ya mukai dai? Ko sirrin kikeso na tona ne?" Da sauri ta zube akan gwiwanta
"Sir zan kwana ina bautar wahala akan inshaa wannan ka tallafeni" mik'ewa yae cikin fusata
"Idan bazaki shaba seki bari ai, nikuma nasan abinda zanyi" mik'ewa tae
"Ka rufan asirina sir zan sha" daganan ta karb'a agabansa tasha k'wayar dake tayar mata da tsananin sha'awa wacce kuma ke sakko mata da rashin gajiyawa da abun koda za'a shekara anayi, tabar ofishin cikin tsananin hawaye da kuka mara sauti.....tasani yau setasha fama.
Slimxy✅✅
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpad@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*DAGA ALK'ALUMA SHIDA*
_Free page_
*3*
tada motarta tayi ta fige ta da gudu tabar harabar cikij asibitin... kallo yabi bayan motar dashi har ta fice sanan kamar wanda ya tuna wani abu shima cikin sauri ya fice daga harabar asibitin ,a kofar fita ya tari mai mashin ya haye tare da yi masa bayanin inda zasuje,
Gudu sosai takeyi akan kwalta kamar wadda ke tseren gudu cikin kwarewa take murza sitiyarin motarta,tuki takeyi zuciyarta na cigaba da bugawa sauri da sauri minti minti takan sauke numfashi yayinda dodon kunnenta ke kara tariyo mata muryar gayen da yayi mata sallama dazun...da ta tuno muryarsa sai gabanta ya fadi ta rasa dalilin hakan saidai abinda takeji a ranta dangane da muryar tafi tsanarsa akan tsanar da takeyiwa kamal...to wanene mai wanan muryar?a ina tasan shi?abinda yake daure mata kai kenan,ta karyo kwanar shiga unguwarsu hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya da danasanin ta waigo ta kallesa kota san muryarsa....
Tun daga nesa take hangen motarsa a kofar gidansu yayi parking hakan ba karamin faduwar gaba ya haifar mata ba a fili ta furta "nidai na shiga uku ni bilkisu"take kwalla ta cicciko idonta ,tasan tunda be ganta a makaranta ba yasan tana gida shine dalilin da yasa ya biyo bayanta...me kamal yake nufi da ita ne?shikenan batada wani amfani a wanan duniyar face yi masa bauta?... parking motarta tayi ta kifa kanta akan sitiyarin motar tana sauke numfashi hade da faduwar gaba wanda batasan dalilinta na hakan ba amma dai tasan yanada nasaba da ganin kamal da tayi a kofar gidansu wanda dik sanda zata gansa sai gabanta ya fadi,...wani miyau ta hadiya wanda ya tsaya mata a wuya mai daci sanan ta mika hannunta da niyyar kwasar wayoyinta da jakarta kiransa ya shigo,...kallon wayar takeyi harta tsinke sanan ta lura ashe yayyi mata misscal,dakyar ta sanya kafarta ta fito daga motar ta rufe ta soma takunta wanda ya zame mata jiki kamar mai tausayin kasa....
Kwantar da kansa yayi a jikin kujerar mota yana tunanin irin hukuncun da xaiyi mata har shine zai rinka kiranta a waya tana kin daga wayarsa?yanzun haka yana kallonta ta side mirror dinsa tayi parkin motarta ya kira batayi picking ba?me billy ta taka haka?tana wasa da rayuwarta koh?tana ganin bazai iya tona mata asiri ba?hmmmm ya sauke lallausan murmushinsa na mugunta ya shafi sajensa ya lumshe ido hangota da yayi ta shige gate din gidansu batare da tazo gareshiba bayan tasan shine,zai horata dangane da abinda tayi sai yayi mata kaca kaca ta kasa tashi...ya lumshe idanuwansa ,
Mahaifiyarta na zaune a parlor,gabanta dan karamin table ne da aka ajiye mata hollandia milk da glass cup sai dan plate da aka yayyanka mata fruits danginsu apple kankana da abarba da spoon a gefe,
Sallama bilkisu tayi cikin sassanyar muryarta kamar koda yaushe...."assalamualaikum"tace hade da shigowa parkorn hannunta rike da hand bag dinta dik ta gaji ga rashin karfin jiki saboda dan ciwon da takeyi a tsaitsaye..."waalaikumussalam bilkisu kece haka da tsakiyar rana?badai har kin gama da asibitin ba"mahaifiyarta ta tambayeta cike da kulawa tana kuma kare Mata kallo,
"Nagama ummah shine ma nakaraso gida,naga doctor da wuri dayake yau ba ranar ganin marasa lafiya bane sosai"
"An duddubaki yadda ya dace koh?kin kuma yi masa bayanin yadda kikeji da rashin bacci kog?"..guadawa ummah kai tayi "nayi masa ummah ya duddubani ya bani teses akan indawo nanda sati biyu an dibi jinina zaayi examining,ya kuma bani wasu magunguna yace inyi amfani dasu kafin ranan"
"Toh allah yasa mudace ga abinci can a dining tun dazun zaliha ta gama ,injidai yau bakuda lectures koh naga baki cika lectures Friday ba"
"Ehh ummah"...ta amsa a takaice,wayarta ce tayi karar shigowar massage da sauri ta duba ganin sunan wanda yayi mata massage din gabanta ya tsananta faduwa,
" *Billy kenan harni zan kiraki a waya kiki picking?inzo kofar gidanku inyi parking ki wuce motata?me kika taka ne?ko kin tanadi maganganu da kalaman da zaki fadawa duniya idan asirinki ya tonu?...cikin minti uku da seconds asirinki zai tonu zai watsu a duniya hatta mahaifinki da ya mutu sai sunansa ya baci,dan haka ina mai tunatar dake cewar kamal ne kike wasa dashi wasa dani kuwa* *tamkar wasa da damusa ne dan haka kiyi gaggawar fitowa cikin minti biyar kacal na baki dan inada* *bukatarki a tare dani idan ba haka ba asirinki dayake lullube a kasa zan toneshi* jikinta ne ya soma rawa bayan ta karanta massage dinsa zuciyarta ta shiga harbawa tamkar zata fasa kirjinta ta fito ga wani tsoro daya lullubeta yasa ta soma zufar dole...sosai massage dinsa ya tada mata da hankali dan tasan indai kamal ne zai aikata abinda yafi hakan tunda har ta Bata masa rai ya ji haushi,
Kafe ta da ido ummah tayi tana karantar yanayin yartata kamar wadda gagarumin abu ya sameta...itako bilkisu idonta yana kan wayar hannunta na karkarwa,
"Bilkina..lafiya?naga jikinki yana rawa haka?meyafaru ne?" A dan furgice ta dago kai ta dubi ummanta "ummah babu abinda ya faru kawai dai massage meenah tayi mun wai munada test yanzun dik inda nake intaho gashi ummah nagaji ko karatu banyi ba ma"idonta suka cicciko zuciyarta nayi mata suya,
Murmushi ummah tayi "haba bilkina shine dik kika tada hankalinki haka?insha allahu zakici test din dik inda kike kinatare da addua ta gabanki da bayanki allah zai karemunke kinji bilkina?kullum nasihata a gareki shine ki kama mutuncunci ki rike maraicinki kinji har allah ya kawo miki mijin aure nagari"...kalaman ummanta sun sanyaya mata jiki sosai takejin tausayin mahaifiyarta wadda batasan hakin da take ciki ba halin da ta jefa kanta...cije lebenta tayi tare da hadiye kukan dake neman kwace mata,
"Ummah na sai na dawo kinji?"
"Allah ya tsaremunke bilkina"tabi yar tata da kallo yadda take tafiya a gajiye tana hada hanya ta fice daga parlorn...
Hango fitowarta yasashi sauke murmushin mugunta yana karewa halittar jikinta kallo wanda yake kara susutashi da shaawarta harta karaso ta bude motar ta shigo ta dan tsuke fuskarta ta zauna ta kuna rufe motar batare da ta ko kallesa ba,
Gyara zama yayi idonsa kurrr akanta yana karantar "da kin saki fuskarki da kin siyarwa kanki tsira daga fadawa tarko na dan bazaki shigo motata ki dauremun fuska tamkar wadda aka aikowa da sakon mutuwa ba gara ki saki jiki dan ina mai tabbatar miki da yau sai nayi round hudu "da sauri ta kallesa hawaye na bin fuskarta,
Gira ya daga mata "yess round hudu zanyi shine sakamakon kin daukar wayata da shanyani da kikayi,shine punishment dinki,gobe bazaki kara hakan ba dan haka kima saki jikinki dan bazan dawo dake gida ba sai dare saina moreki yadda ya dace"
Hannu tasa ta share hawayenta wasu na kara zubo mata"kamal bazan taba gushewa ba inayi maka nasiha da kaji tsoron allah,idan babu duniya akwai lahira akwai kuma filin hisabi kaji tsoron mahaliccinka kamal dan allah ka tausayamun ka tausayawa maraicina ka daina sani aikata zina"ta fashe masa da kuka,
"Billy kenan"ya kai hannunsa ya rukota yana shafa gefen hannunta cikin wani irin salo kamar mai susan kadangare,"da kin adana kalamanki kin fadesu a inda ya dace da yafi don ni bana bukatar jin su idan kuma kika matsa to abinda kike gudu zai faru zan tona miki asiri"da kakkausar murya ya fada,
Haka yasa ta girgiza kai cike da bakin ciki ta tsuke bakinta bata kara cewa komi ba ya tallafo kanta yakai bakinsa lips dinya yayi mata light kiss yana cigaba da shafa wuyanta idonsa nakanta yana kallon yadda ta lumshe ido ya saketa yana dariyar mugunta "dadina dake saurin daukar carji cikin seconds zaki fara daukar sakwanni shiyasa nake sonki nasan kinsan babancin jan zaki da kuma sauran maza masu kalar lagwani"ya kashe mata ido ta fashe da kuka ya maida kansa ya tada motar ya diba a guje ya fice daga unguwar...tana cigaba dayi masa kukada rokonsa bema san tanayi ba sai sauti daya saki a motar yana bin wakar...
**********
Jujjuga cokali kawai yakeyi tunda aka zuba masa abincun gabaki daya hankalinsa da dik wani tunaninsa ya tafi akan yariyar daya gani a asibiti dazun....ya rasa dalilin da yasa zucuyarsa takasa natsuwa sai tunaninta yakeyi dik yadda yaso ya kauda tunaninta abin ya gagareshi kusan awa uku kenan da ganinta amma ya rasa natsuwarsa,gabaki daya ya mance da abinda ya kaisa asibiti ya mance da wani abu dayake damunsa tunaninsa ya karkata a kanta be wuce yadda zaayi ya sake ganinta ba dan besan daga inda take ba dik yadda yaso mai mashin din daya hau ya bi bayanta ta bace masa battttt....tunani daya ne ya fado masa shine yayita ziyartar asibitin ko zai sake ganinta dikda appointment dinsa sati biyu ne,
Wayarsa ya janyo yayi dialing wata number a karo na goma sha biyar ta soma ringing ya kafe wayar da kallo harta tsinke baa daukaba,wani kululun bakin ciki ya tokare masa wuya nan da nan idonsa sukai jajir saboda bakin ciki abu goma da ashirin a kansa...dafe kansa yayi dake barazanar tarwatsewa,yana sauke numfashi a hankali ya kwantar da kansa akan katuwar katifarsa dake cikin dakin ya rufe ido kamar me bacci yana cigabada tunaninta...
*********
Karfe tara na dare kamal ya fito daga toilet daure da towel a kwankwasonsa da karami a hannunsa yana goge jikinsa gashin jikinsa sun kwakkwata saboda ruwa,
Kallo daya tai masa kuka ya taso mata hade da tsananin tsanarsa data darsu a cikin zuciyarta ta lullubeta,ji takeyi tamkar ta mutu ta huta da wanan bakin cikin da kamal ke kunsa mata kiri kiri kamal ya maidata matarsa sai yadda yayi da ita dik lokacin daya bukaceta dole tazo idan ba haka ba tasan abinda zai biyo baya bata da zabin daya wuce ta cigaba da bauta masa har mutuwa ta risketa dan tanada tabbacin kila wataran zata hadiyi zucuya ta mutu,
Karasowa gabanta yayi ya tsaya yana kare mata kallo dik ta galabaita ta gaji kukan da takeyi ma baya fitowa saboda wahala shi kansa yasan cewar ya dirjeta yadda ya dace "billy da kin daina wahalar da kanki kina zubar sa hawayenki da yafi miki gara ki adanasu saboda gaba"..
"Haba kamal haba kamal ka maidani kamar wata matarka kamar wata baiwarka?"tana shasshekar kuka tai maganar,
"Au dama bakisan kedin baiwata ce ba baiwar shimfidata?ai bakida wani amfani wanda ya wuce in hauki a lokacin dana gadama in sauka a lokacin dana gadama billy kedin ta dabance zakinki ya zarce zuma dadi"ya kashe mata ido daya,
Dakyar ta duro daga gadon tana taka kafar dakyar saboda yadda takejin zafi da zugi a kasanta ga ciwo da dik gabobin jikinta yakeyi mata haka ta watso ruwa ta fito tasa kaya suka fito tare ya nufo gida da ita,....
***********
Karfe biyun dare amma ta nemi bacci a idonta ta rasa saboda tunanin gayen da yayi mata magana dazun gashi bata juyo tagansaba bataga ko wayeba muryarsa ce kawai takeyi mata yawo akai tamkar zata fasa mata kwakwalwa dik yadda taso ta janyo baccin dole tayi ta gagara tunanin inda tasan irin muryar takeyi da kuma yadda ta tsani mai irin muryar....
*Bayan sati biyu*
Yana zaune a reception ya jingina da kujera yana kukan zuci wanda yafi na fili ciwo ta shigo...dikda irin bakin cikin dayake ciki a wanan lokacin be hanasa zabura ya bi ta da kallo ba ,tayi kyau harta gaji atamfar dake jikinta ba karamin haskata tayi ba ,shi kansa dinkin straight skirt din ba karamin kyau yayi mata duba da kirar jikinta ba mai kiba bace...ya shagala da kallonta har ta shige wajen doctor....
Tura kofar tayi bakinta dauke da sallama,..likita ya amsa mata yana cigaba da kallon takaddun dake kan table dinsa ,
Tsayawa tayi ,ya dago kansa "ah ah bilkisu kece?dama yanzun sakamakom tests dinki ya fito sune ma yanzun haka nake dubawa bismillah zauna mana"ya nuna mata kujera ta zauna a sanyaye gabanta natsabanin faduwa, hantar cikinta dik ta kada ta shiga ambatar sunan allah cikin zuciyarta....
Yadda take zare idon yasa likintan kare mata kallo,gabaki daya ko baa fada ba ansan tsorone dankare a zuciyarta saboda fuskarta da kwayar idanuwanta sun bayyanar da hakan...
"Malama bilkisu ki kwantar da hankalinki ni natsu ki fahimceni saboda case din dik mai sauki ne"
Kallonsa takeyi ta kasa cewa komi ya cigaba da magana "babu tashin hankali a al'amarin allah da abinda ya rubutowa bawansa face kayi imani da ita kaddarar kowa da irin tasa ta wani tafi ta wani sanan allah baya saukar da cuta face da maganinta hade kuma da addua sai kasamu waraka cikin sauki"kalaman doctor suna barazana da tarwatsewar zuciyarta da gushewar hankalinta hakan yasa kwakkwaran motsi ta kasa sai tsananin faduwar gaba...
"Cutar dake damunki mataki mataki ce akwai matakin farko akwai ta biyu alhamdulillahi taki matakin farko take wadda indai mukai saa kinashan magani da bin dokoki to tabbas zaki warke"...gabaki daya ta kosa taji me doctor zaice dan cikinta murdawa kawai yakeyi fatanta ba cutar HIV gareta ba,sai zufa dake karyo mata dikda sanyin Ac Dake office din,..ganin yana kallonta yasa dakyar ta motsa harshenta da yayi mata nauyita furta "likita ka fadamun meke damuna"muryarta na rawa,
"Sorry to say bilkisu kinada cutar hipatitis A wanda hausawa suke kiransa da ciwon hanta"... innalillahi wa innah ilaihi rajiun shine abinda ta ambata ta mike tsaye zumbur kamar an tsimareta,
"Ki kwantar da hankalinki bilkisu zaki iya warkewa idan kinbi dokoki"...
Hawaye ne suka shiga gudu a fuskarta kamar an bude famfo "ta yaya zan warke likita?bayan wanan cutar baa warketa mutuwa akeyi"
"Ita mutuwa da kika kira bilkisu sai kwananka ya kare amma ina mai tabbatar miki tunda taki A ce to zaki iya warkewa tunda batakai mataki na biyu ba wato B"kujera ya nuna mata alamun ta zauna dakyar ta dofana ta zauna tana cigaba da zubar hawaye dik yadda likita yaso ya lallasheta abun ya faskara kuka kawai takeyi babu kakkautawa haka ta fito dakin likita rike da takaddun result da kuma takaddar magani....
*DAGA ALK'ALUMA SHIDA AKAN DARI BIYAR ZAKI SAMU LITTAFAI SHIDA IDAN KUMA DAYA KIKESO DARI BIYU KACAL KI NEMI WANAN NUMBER 08166177830 KO* *07084161619*
Rike yake da takaddar maganinsa yana tunanin yadda zaayi yasamu wanan kudade da aka lissafa masa na ciwonsa gashi babban tashin hankalinsa likita ya tabbatar masa da ciwonsa ya hau mataki na biyu wato B ... shikenan bazai taba warkewa ba kenan?shikenan rayuwarsa ta fada cikin garari da mummunar halaka...dik yadda yaso da yayi hawaye ko zai samu sassauci abun ya faskara,...shesshekar kukanta ce ta farkar dashi daga tunanin da ya lula da tsananin bakin ciki da yake ciki ...
Da sauri ya mike ganin yadda ta fita hayyacinta saboda kuka ,jikinsa ya soma rawa tausayinta ya lullubesa tun kafin yasan abinda yake damunta yaji ta bashi tausayi,nade takaddunsa yayi ya zura aljihu yabi bayanta..tana tafe tana kuka harwajen motarta Yana biye da ita bece mata komiba,
Jikin motarta jingina tana kuka mai ban tausayi tana furta "na shiga uku shikenan rayuwata ta kare banida sauran amfani a duniya,..kaicona ni bilkisu..."ta jingina da jikin motar, tunanin ummanta ya fado mata tausayinta ya lullubeta tayaya zata farawa ummanta bayanin tanada ciwon hanta?ta yaya zata cigaba sa muamala da sauran mutane?bayan wanan ciwon ana daukarsa ta ko wani irin yanayi?....runtse idonta tayi bakin ciki ya lullube mata zuciyata kamar ta hadiyi zucuya ta mutu kawai takeji...
kasa daurewa da kukanta yayi yasa yayi mata sallama a karo na farko "assalamualaikum"yace,...dik kukan da takeyi saida ta tsagaita ta dago fuskarta da sauri ta kafesa da ido fuskarta jike da hawaye, ..tozali tayi da kyakkyawan saurayi wanda be wuce shekara talatin da uku ba a duniya,...kwarjini yayi mata yasa ta kasa cigaba da kallonsa,tunaninta ya banbanta dayadda taji muryar da kuma wanda ta gani,hakan ne yasa ta cigaba da rera kukanta,
"Haba baiwar allah be kyautu ace musulma kamarki hausa fulani takasa juriya da imani da kaddarar da ta sameta ba dikda bansanabinda yake damunki ba amma a hasashena bai wuce hakan nada nasaba da lafiyarki ba,dan allah kiyi shiru ki daina wanan kukan da kikeyi dan kaunar sa kikewa manzon rahma"....sosai ya kashe mata jiki yasa ta tsagaita da kukan tana cigaba da kallonsa,saidai a kasan zuciyarta kukan takeyi ,
"Zanso ace kin sanar dani abinda yake damunki ko inada maganinsa ko kuma inada shawarar da zan iya baki idan akwai sararin hakan"...yadda yake magana kadai ke haifar mata da faduwar gaba,
Samun kanta tayi da mika masa takaddar result dinta batare da tace komi ba ta juyar da kanta ta cigaba da hawaye....
Jimm kadan yayi yana karanta takaddar,sanan ya dago kansa ya dubeta hade da murmushin takaici....kare mata kallo yakeyi karamar yarinya ce yar shekara goma sha takwas take fama da wanan ciwon gashi ko baa fada ba ta fito daga babban gida yar masu kumbar susa ce duba da yanayinta da fatar jikinta da hutu ya zauna...ko babu komi tanada yadda zatayi tarabu da abinda ke damunta dan sunada halin siyan magani shikuwa fa?wanda sanadiyyar siyan maganin ya jefa kansa cikin mummunan hadarin da yake danasani,
.ajiyar zucuya ya sauke "ko zamu shiga daga cikin motarki inaso inyi magana dake"
Babu musu ta bude motar ta shige shi kuma ya zagaya ta dayan bangaren ya shiga da kudurin kwantar mata da hankali da yi mata nasiha......
*SLIMZY✍🏻*
08166177830
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*4*
Wajen zaman driver ta zagaya ta zauna,yayida matashin saurayin ya zauna a gefen mai zaman banza ya rufo kifar,sanan ya kura mata idanuwansa wadanda suka canja launi zuwa kakar ja, gabaki daya tausayin yarinyar yakeyi yadda take kuka cikin mummunan tashin hankali kadai ya isa dik wani musulmi yaji tausayinta yarinya karama da ciwon hanta?...ya tambayi kansa tare da dafe goshinsa babu abinda yake furtawa a zuciyarsa sai innalillahi wa innah ilaihi rajiun....ya furzar da wata iska mai zafin gaske sanan ya cigaba da kallon yadda hawaye ke gudu a idanuwanta Babu kakkautawa,yana karantar yanayin nata sanan yana karewa halittar fatar jikinta kallo, Wanda kallo daya zakai mata ka hango tsantsar hutu da jin dadi a fatar jikinta balle suturar dake jikinta har akaiga motar da take hawa,
Ita kuwa bilkisu gabaki daya babu abinda zuciyarta keyi banda harbawa minti minti takan tsinci kanta cikin tsananin faduwar gaba musamman idan muryar wanan matashin ta bugi dodon kunnenta sai taji tana barazana da tarwatsa mata zuciya....muryarsa ke haddasa mata faduwar gaba da tsantsar tsanar wanda tasani me irin muryar fiye da yadda take tsanar kamal wanda ya zame mata karfen kafa mai wuyar shaani....wanan karon dago fuskarta tayi ganin shirun yayi yawa idanuwansu sukai karo da juna a karo na farko gabanta ya yanke ya fadi take kwarjininsa da haibarsa yasa ta kasa kara hada ido dashi ta sunkuyar da kanta cikin rawar murya tace "bawan allah kayi shiru?kace kanason magana dani amma bakace komi ba,dan allah idan kanada maganin lalurar dake jikina ka taimakeni ka bani ka fiddani cikin hadarin dake tunkaroni a karo na biyu"
Cikin seconds da basu wuce uku ba yaji idanuwansa sun kawo ruwa saboda tsananin tausayinta da kalamanta wanda suka sanyayar masa da dik gabobin jikinsa...cije lebensa yayi gudun kada hawaye su zubo mata ya karyar mata sa zuciya ya nisa ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya soma magana cikin muryarsa mai sanyi da dadin sauraro "sunana abdulhrahman amma mutane da abokanaina da yan uwana suna kirana da abdul,ni mazaunin garin nan ne inada kanne uku biyu mata daya namiji magaifinmu ya rasu sai magaifiyata"...ya dakata da maganar ganin tunda ya soma magana ta kafesa da ido tana sauraron muryarsa wanda ke haifar mata da faduwar gaban da batasan dalili ba,
Cigaba yayi da maganar,"hakika banida maganin ciwonki yan mata saboda hakikanin gaskiya taki matsalar kika sani bakisan matsalar wani ba dikda nima tawa matsalar ce ta kawoni wanan asibitun har na ganki kwanaki yau ma gashi muka kara haduwa...inaso ki kwantar da hankalinki kidaina kukan da kikeyi domin ciwo ba mutuwa bane,dik wani ciwo da kikagani ya samu bawa to dama rubutaccene daga mahaliccinsa cewar zai samesa da dabarar mu ce da bamu hadu da jarabawoyi kala kala ba,allah yana jarabatar bawansa ne ya gwada imaninsa da hakurinsa da tawakkalinsa sanan da tsoron allahn sa,idan har ya kiyaye wadanan abubuwa sai kiga allah yayi masa rangwame a al'amarinsa kinji?wanan kukan da kikeyi ba shi bane maslaha inaso ki kwantar da hankalinki da izinin allah zaki samu lafiya kinji?kiyita addua sanan dik maganin da aka doraki akansa ki daure ki jure ki rinka sha in allah ya yarda allah zai kawo karshen matsalarki kinji?"....runtse idanuwanta tayi ji takeyi tamkar ana watsa mata garwashin wuta a jikinta saboda yadda jikinta ya dauki zafi na zazzabi cikin minti talatin ,saidai kalaman abdul sun matukar sanyaya mata jiki,sanan ta wani fannin ta dan samu saukin radadin da takeji a zuciyarta....
Kallonsa tayi tankar bazata ce wani abuba sanan tace "nagode abdul allah ya saka maka da alheri na wanan tunatarwar da kaimun insha allahu zanyi addua zanyi yadda kace"ta karashe maganar harshenta na rawa hawaye na zuba a idanuwanta,
Gabaki daya tausayin yarinyar ya lullubesa ga wani abu da yakeji dangane da ita yana yawo a sassan jikinsa wanda ya haifar masa da muguwar kasala...dakyar ya daga harshensa da yayi masa matukar nauyi "babu komi bilkisu allah ya baki lafiya kinji?"batayi mamakin kiran sunanta da yayi ba dan tasan ya gani ne a jikin takaddar result dinta...
Yana kokarin bude kofar ta dakatar dashi cikin rawar murya tamkar mejin sanyi "dan allah...yaayahh abdul...idan bazaka damu ba ka iya mota ka taimakeni ka kaini gidan mu bazan iya driving ba"...cakkkk ya tsaya yana dan wani nazari sanan ya nisa yace "shikenan babu damuwa bilkisu na iya mota ina ne unguwar taku?".. take tai masa bayani tiryan tiryan sanan ya bude motar ya fita itama ta zagaya inda yake zaune ta bude motar ta shiga ya zaga mazaunin driver ya tada motar yaja suka bar harabar asibitin....
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA NEMI* *WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 07084161619*
Da gyalen jikinta ta lullube jikinta sosai saboda iskar dake kada ta ga zazzabi da ya lullubeta mai zafin gaske ..minti minti takan kallesa ta sadda kanta tana nazarinsa da yanayinsa ,kallo daya zakai masa kama sa suturar jikinsa da kamalarsa da kalamansa ka tabbatar da kamili ne shi me rukon addini ga kyau da haiba da allah yayi masa...ajiyar zuciya ta sauke da ta tuna da ummanta dake gida tana jiran dawowarta da result din asibiti na rashin lafiyarta....ta yaya zata sanarwa da ummanta tanada ciwon hanta?shin a ina ta sameshi ?gabanta ya yanke ya fadi take ta tsure dik hankalinta ya kara mugun tashi ga kira da takeji yana shigowa wayarta tun dazun ,dikda bata duba ba amma tasan wanan azzalumin ne kamal....
Tuki yakeyi Amma gabaki daya hankalinsa na wani waje babu abinda yake tunani sai yadda akai yarinya kamar bilkisu yar shekara goma sha takwas a duniya ta samu ciwon hanta,shin ta yaya ta sameshi?ga alamu sun nuna ita din yar masu kudi ce ko baa fada maka ba kasan yar manyan mutane ce....
Wayarsa ya zaro a aljihunsa yayi dialing wata number har ta tsinke baa daukaba,tsakin da ya ja ne yasata saurin daga ido ta kallensa,take ta hango damuwa bayyane a fuskarsa amma hada idon da sukayi ne yasa ya sakar mata wani tsadadden murmushi kayatacce Wanda yasa tai cakkk tana kallonsa dikda busassun hawayen dake fuskarta....
Kwanar da zaa shiga unguwarsu ya karya daidai wanan lokacin ya katse mata tunani ta hanyar jefa mata tambaya "bilkisu gamu mun shigo ta ina zamu bi ne?naga wajen shiru ne allah yasa dai ba saceni zaki ba"yayi maganar cikin sigar tsokana amma ga mamakinsa sai yaga ta sadda kai idonta yana kawo ruwa,dakyar ta matse ta dago Kai ta nuna masa wani tankamemen gida dake fuskantarsu...da sauri ya kalleta ganin gidan data nuna...lallai biri yayi kama da mutum tabbas bilkisu yar manyan mutane ce wanan tankamemen gida wanda tunda allah ya haliccesa bai taba ganin irinsa ba nan ne gidansu?aljannar duniya....haka ya karasa yayi patking kofar gidan ya kalleta,
"Toh bilkisu ni zan tafi kinji amma baxan tafi ba sai kinyimun alk'awarin kindaina kuka zaki kwantar da hankalinki ki fadawa mahaliccinki halin da kike ciki"
Girgiza masa kai tayi "banyi alkawari ba yaayah abdul domin kuka?yin kansa yakeyi a wanan halin dana tsinci kaina ciki daina kuka cikin wanan karnin ba abu bane me sauki saidai ka tayani addua kawai kuma kaga gidanmu kodan saboda wata rana"...jakarta ta bude ta ciro karamin katinta ta mika masa hade dayi masa godiya,
Jiki babu kwari abdul ya fito daga motar cike da tausayin bilkisu,daidai wani me napep ya ajiye wasu a wani gida yasawa mai napep din hannu ya shige hade da daga mata hannu itama ta daga masa,ta kifa kanta a jikin motar gabanta na tsananin faduwa batasan yadda zata farawa mahaifiyarta bayanin halin da take ciki ba....
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: 💥 💥 *IZZA TA......*💥
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of expert and perfect writers)*
_Wattpad@slimzy33_
*SLIMZY✍🏼*
*DAGA ALK'ALUMA SHIDA.....*
_Free page_
*2*
"Amma nifa Bilkisu nidai na tsani wannan kwanan a hostel, kinsan halin mutane yanzu sai kinji ance kin zama 'yar mace, na baki dama kina shek'e ayarki kina abinda kikeso son ranki" murmushin takaici tayi,
"Ummana, ki kwantar da hankalinki babu wanda zaisa ace hakan, kuma dandai kwana d'aya? Wadda zata koyan karatun nan cewa tayi dole sai da daddare takeda time umma, so kike na fad'i jarabawa azo kuma ana cewa dama cen yawo nake ba karatun ba?" Jinjina kai umman tayi cike da gamsuwa da kalaman y'artata
"Hakane kuma Bilkina Allah ya miki albarka ya kare min ke gabanki da bayanki"
"Ameen" ta amsa a sanyaye kafin ta mik'e, ta dan taka, saida taje k'ofa sannan tace,
"Ummana anan zanbar motana fa bazan je da itaba" kallonta umman tayi
"Bus zaki hau kenan to saboda me?"
"Satan mota ake a hostel, ba wani security barin motanka a wajen nan ummah bazai haifar ma d'a me ido ba" jinjina kai umma tayi
"Allah ya kyauta" daganan ta juya ta fita, a gate ta hangi motar sa taje ta bud'e gidan gaba ta zauna tana mayar da numfarfashi sama sama, bata kalleshi ba shi d'inma seda ya tashi motar sa ya saita ta kan titi da kyau sannan ya waigo ya kalleta, d'ayan hannunshi yana kan sitiyarin motar yakai d'ayan a saman wuyanta yana murzawa a hankali fuskarsa dauke da murmushin nan nasa wanda baka iya gane nufinsa,
"Billy manyan mata, babu ko gaisuwa yau, ko baki fara daukar chargy bane ba?" Hannunta takai ta rik'e nashin cikin kasala,idonta yayi rau rau da hawaye dake makale cikin idonta tana jin ciwo akan abin amma babu yadda ta iya,
"Haba kamal, dan Allah tuk'i fa kakeyi" murmushin sa ya fad'ad'a
"Muryanki kawai ya isheni shaidar cewa kin fara daukar chargy hajiya" bata kula shiba sukaci gaba da tafiya har zuwa k'ofar gidan sa, suna zuwa wani kuka ya taso mata lokaci d'aya ta kasa controlling kanta ta shiga rera kuka abinta, inda sabo ya saba da wannan kukan duk sanda sukazo hakanne ya sanya ko kallonta baiyiba,
haka kuma dan dole tabi bayansa zuwa cikin gidan har cikin d'aki.......
Kallon kayan daya watso mata akan gado tayi ta had'iyi wani mugun miyau kafin tace
"Mezanyi da wannan kuma kamal?"tana kallonsa ido cike da hawaye,... D'age kafad'unsa yayi duka biyu sanan yace,
"Ki k'ona mana" jin bak'ar maganar tasan mai yake nufi,a sanyaye ta mike jiki babu kwari zuwa toilet, ta watsa ruwa,ta d'auro towel ta sako hijab ta dawo d'akin, kallonta yayi cikin ido kafin yace
"Yau wanan turaren na keso ki shafa,ga shi ki saka kayan dana baki ki sameni a parlor bakuma nason wannan mugun hijab d'in kinmaji na gaya miki"
haka taje tayi sallar isha ta shirya yanda yace tazo parlor.
Wani irin kallo ya bita dashi,hade da lashe lebensa, kafin ya kai hannunsa ya janyota ta fad'a kan cinyar sa ya sanya yatsansa yana yawo dashi a sassan jikinta da ramin gadon bayanta yana mata tafiyar tsutsa,
"K'amshin nan yamin dad'i ki dinga saka turaren koda yaushe" ko kallonshi batayi ba saboda mugun takaicin dayayi mata katutu a wuyanta, dakyar ta hadiyi wani mugun miyau na bak'in ciki, lokaci d'aya ta soma zubar da k'wallar takaici, yatsansa yakai ya dangwali ruwan hawayen ya kai yatsan bakin sa yana murmushi idonsa akanta da shu'umin kallo yace,
"Yaya zanyi wasa da wannan ruwan mai daraja, bai kyautu ba ace kina zubar min dashi kinamun asara"dago idonta tayi ta kallesa muryanta na rawa tace
"Haba kamal, nifa ba matarka bace ya kamata kaji tsoron allah" be kulata ba yakai bakinsa saman kuncinta cikeda salo yake lasar hawayen dake gangarowa daga idanuwanta,
"Ni nace miki bana tsoron Allah?, ubangijin daya halicceni ai dole inji tsoronshi Billy, ki daina wannan maganar anan" zare fuskarta tayi daga tashi hade da kauda kanta tana cigaba da hawaye
"Kodai mai zakace wallahi Allah sai ya sakamun akan ka, kuma yana sama yana kallonka mugu kawai azzalumi" Dariya yayi cike da jin dad'i abinda yakeso kenan
"Koma dai mai zakice saina mora" ya lashe lebensa yana cigaba da murmushi, saukowa tayi daga kan cinyar sa, ta durk'uda asaman gwiwiwinta cikin sigar tausayi tana mai ci gaba da zubar hawaye ta furta a sanyaye,
"Ka taimakeni kamal, ka tallafi maraicina ka fadamun sai yaushene a rayuwa zaka daina sanyani aikata zina? Ban maka komai ba kamal, dannace bana sonka shine kawai laifi na, idan hakane ina sonka kamal, ina sonka sosai amma ka daina wannan mugun aika aikar dani dan k'aunarka da kakewa annabin rahama" murmushi yayi
"Billy kenan, me kike tunani? Tayaya zan daina shanawa da hutawa dake? Lokaci kike tambaya? Na dainawa? To babu lokaci har abada kina nan amatsayin ki na matata kuma baiwar shinfid'ata" Muryanta na tace
"Dan Allah badan niba kayi hakuri kamal, ka sassautamun ka tallafeni ka tallafi rayuwata kaji? Ka aureni koda akan sha'awar da kakeyi tawa ne zan jure dik wata wahala dazaka bani batare da qorafi ba, ni kawai zinar ce banaso"
Mik'ewa yayi yana kwasar dariya harda tafa hannu yajima yanayi kafin ya tsagaita ya kalleta yana cigaba da murmushi
"Billy kenan, wannan shine iska tana wahalar da mai kayan kara, lokacin dana so in aureki kece kika gujeni, yanzu kuma kinga kin zama tsohuwar riga iya kacinki goge datti" bata kara ce kishi komai ba, ya sanya hannayenshi duka biyu ya ciccibeta yayi d'aki da ita....
*washe gari*
Koda gari ya waye Billy bata ko iya tsayawa da k'afafuwanta,
tayi kuka harta gaji ta godewa Allah,dana sani na abubuwa da dama suka taru suka mata yawa!
********
Tunda take zaune agurin jiran Dr. Ya kafeta da ido,ko kiftawa bayayi,saboda yadda ta tafi da imaninsa, dukda yake yana ayyana a ransa tafi k'arfinsa,
haka bayan layi yaxo kansa yaga Dr, saida yajirata ta gama, a parking lot ya jirata tana xuwa kai tsaye gun motarta taje cikin yanayinta mai sanyi,bai tsaya b'ata lokaciba wurin k'arasawa wajen nata
"Assalamu Alaikum" ya furta mata cikin muryarsa me dad'in sauraro"
Muryan sa ya daki k'irjin ta ya haifar mata da bugun zuciya babu kakkautawa, lokaci d'aya ta tuna wani lokaci can baya daya wuce,,runtse idonta tayi cikin wani irin yanayi na tsananin bak'in ciki, koma waye wannan da bataga fuskar saba tafi k'aunar kamal da tafi tsana fiyeda kowa aduniya akansa,
Bata juyo ta kallesa ba, kamar yanda bata ko kulasa ba tasa kai cikin motarta...
Ga mai bukatar shida garabasa akan 500 kacal ya nemi numbers din nan 08166177830 ko 07084161619 *SLIMZY* *CE* 😍🥰
*SLIMZY✍*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*6*
A wahalce ya dago jajayen idanuwansa da suka sauya kala lokaci daya saboda tsananin sha'awar bilkisu dake ratsa ilahirin jikinsa yadda yake wasa da jikinta, ya kara karfafa masa sha'awarta dake yawo a jikinsa a wanan lokacin,kallon yadda hawaye ke ambaliya a idanuwanta yakeyi, gaba daya tayi laushi kallo daya zakai mata kasan a wahale take,gyada kansa yayi ya tallabota jikinsa yana jifanta da wani irin kallo mai dauke da maana kala kala cikin kwayar idonsa zai iya nuna maka tsantsar mugunta da kiyayyarta da yakeyi,hakan yasa ya dake fuskarsa yace mata "muyi a nan ko mu shiga cikin daki"ya tsareta da shanyayyun idanuwansa kirr akanta.
Cikin murya kuka ta soma rokonsa "dan allah kamal ka taimakeni ka ceci rayuwata ka daina aikata zina dani kamal na tuba dan allah kaji?wallahi wanan abun da kakeyi dani allah yana ganinmu kuma shine yayi hani da zina da alfasha amma kake tilastani kullum saimun sabawa mahakiccinmu"bakinta har rawa yakeyi saboda kukan da takeyi ga tsoronsa da takeji tabbas khamal ya kusanceta tasan azabar da zata sha , dik lokacin da zai kwanta da ita,dakyar take iya tashi,
Katse mata tunani yayi ta hanyar daka mata wata irin tsawa "ke billy karki kuskura kice zakimun waazi kinji nafada miki au kinsani kike take sani kenan?koko abinda kikayi kina tunanin befi wanan muni ba a idon duniya?idan bakya bukatar in moreki insha romon da nakesha, zan iya dainawa ni kuma in tona miki asiri a duniya kowa yasan abinda diyar bala dan maliki mai hadarin naira ta aikata".. girgiza kai ta shigayi hawaye na cigaba da zuba a idanuwanta hade da ajiyar zuciya da take saukewa,ji takeyi tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu da wanan bakin ciki da kamal yake kunsa mata,
"Ciremun kayan jikinki"ya bata umarni cike da isa,....a sanyaye ta mike tana shirin cirewa wayarta ta soma ruri a cikin jaka da sauri takai hannu zata dauki jakar yace a fusace "ke?mekike shirin yi?nasaki kiyi abu zaki aiwatar da abinda kikai niyya batare da kin tambayeni ba?kin isa?"jikinta na rawa ta saki jakar ta fadi kasa, ta shiga cire kaya jikinta na sassarfa tanayi tana kallonsa shiko ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi.....har tayi tsirara...
Kara dialing numberta abdul yayi a karo na biyu amma shiru baa daukaba,wanan yasa shi jefar da wayar gefen katifarsa dama yayi kokarin kiran nata ne yaji ya jikin nata,....runtse idonsa yayi kunnensa na tariyo masa amon sautin muryar kuka mai hade da kuwwa da kururuwar neman taimako a wani lokacin baya wanda yanaji har ya koma ga mahaliccinsa bazai taba mantawa da wanan muryar ba kuma harabada bazai taba daina danasanin wanan abu ba daya faru a can baya ba zai taba yafewa kansa ba harabada,...babban abinda ya jefasa a damuwa be wuce sautin kukan yarinyar nan bilkisu ba wanda yakeyi masa yawo a kunne tamkar ya tabajin kuka mai kama da haka a rayuwarsa,bude jajayen idanuwansa yayi ya shiga girgiza kai cikin tashin hankali,har yaushe zai manta da sautin kuwwar wanan yarinyar ta can baya?dik lokacin da zai zauna shi kadai saita fado masa a rai, babban abinda ya damesa yau shine ganin wanan yar yarinyar yar shekara goma sha takwas a wanan yanayin ga gunjin kuka tanayi tamkar sautin muryar da take yawan fado masa lokaci zuwa lokaci, idanuwansa gaba daya sun sauya kala zuwa launin ja tankar garwashin wuta,mikewa tsaye yayi ya soma kaiwa da komowa cikin dakin ...furzar da iska yayi daga bakinsa ya jingina da bango yana tunanin halin da shi kansa yake ciki, ....menene makomarsa?
Billy tanaji tana gani khamal ya tasata a gaba zuwa cikin bed room dinsa ya zauna gefen gado ya tsaida ita a tsaye yana karewa halittar jikinta kallo lumshe idanuwansa yayi ya budesu hade da sakin murmushin k'eta ya lashe lebensa ya janyota ta fada jikinsa ya soma sarrafa ta....
Dik abinda khamal yakeyi da ita hankalinta na wajen wayarta dake cikin jaka wadda takeso taga waye yayi mata misscal?, hakan nan take jin kanta gabaki daya hankalinta baya jikinta to ko ummanta ce takira?
*********
Hawayen bakim ciki suka zuraro a idon abdul wanda rabon da yaga hawaye a idonsa har ya manta, ganin dik kiran da yakewa bawan allahn nan ya dauki wayarsa yaki dauka?gashi yau baya maganin ko sisi kuma yasan tabbas zainab jiransa takeyi akan maganar kudin jarabawarta, ya dubi agogo karfe shida saura minti goma sha biyar na yamma ya mike jiki Babu kwari ya fito daga dakinsa sai gumi ke karyo masa,kallo innah tabishi dashi itama zainab dake gefe tana yankan alayyaho kallon nasa takeyi dik tausayin dan uwan nata ya lullubeta tunda ya dawo yake cikin damuwa gashi basusan meke damunsa ba,tanaso taji ko zai bata kudin waec din nata?amma ta yaya zata tambayesa?
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA* *DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU YA* *NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO* *07084161619*
**********
Kallon agogo ummah tayi har shida saura bilkisu bata dawo ba,fuskarta dauke da damuwa ta kalli sashen da hajiya hafsat ke zaune kanwar mahaifin bilkisu, gefenta yarta cesa budurwa wadda zasuyi saa da bilkisu tanata danna waya tana kallon tv.
A zuciyarta adduar allah yasa lafiya kawai takeyi tunda gashi har yanzun bata dawo ba kuma fitarta babu jimawa suka shigo gidan nasu dan ta duba lafiyarta da akace musu bata da lafiya,
Hada ido sukayi da ummah sukaiwa juna murmushi hajiya hafsat ta sauke ajiyar zuciya hade da duban agogo "toh nidai hajiya har yanzun bilkisu bata shigo ba gashi yamma tayi kila dai an rikesu a makaranta ne inaga zamu wuce idan tazo kyace nazo duba jikinta nida mutuniyarta khairee"
Gyada mata kai ummah tayi dauke da murmushi,cikin karfin hali tace "ehh hajiya inaga dai yau malamin masu ya rikesu ne har wanan lokacin basu dawo ba dan wasu lokutan sukanyi lectures karfe hudu zuwa shida na yamma insha allahu zan sanar mata kinzo kuma zatazo gida ta gaisheki angode"
mikewa tayi tana murmushi da niyyar tafiya,ta dubi khairee dage gefenta "tashi muje mutuniyar taki bata dawo ba a gaida mana ita yamma nayi"
wata yar matashiyar budurwa tayi sallama cikin parlorn rataye da jaka,
Ummah tai saurin cewa "yauwa gasu ma sun dawo tunda ga nafisa ta shigo tare suke da bilkisun"....cakkk wadda aka kira da nafisa ta tsaya tana bin su da kallo gabanta na faduwa,tooo meke faruwa?gashi ummah tace gasu sun dawo,ita kuma tazo duba lafiyar bilkisu ne dan kwana biyu basa haduwa ko a makaranta,
Muryar ummah ce ta dawo da ita daga dan tunanin da ta fada "nafeesa ina bilkisun?kun dawo?"..murmushin karfin hali nafisa tayi sanan tace "ehh ummah mun dawo gata nan shigowa tare muke da ita tana tare da bako ne a waje" sai lokacin ummah tayi ajiyar zuciya,ta dubi hajiya hafsat tace "gasu ma sun dawo hajiya bari ta shigo "
"Ah ah yamma tayi mu zamu wuce allah ya kara mata lafiya"tasa kai khairee na take mata baya suka fice daga parlorn,
Gyara zama umma tayi akan kujera hannunta rike sa remote tana kokarin canja tasha,
nafisa durkusa har kasa ta shiga gaida ummah cike da ladabi,ummah na amsa mata cikin sakin fuska
"ina yini ummah?"
"Lafiya lau nafisa ya karatun?"
"Alhamdulillahi ummah"
"Ki shiga sashen nata ki huta bari insa shaawah ta kawo miki abinci"
"Toh ummah"shine nafisa tace ta mike jiki babu kwari ta nufi sashen bilkisu,
Safiyya dake gefe tana mopping ummah ta bata umarni da "ke safiyya jeki kitchen kicewa shaawa ta kaiwa nafisa abinci kawar bilkisu yi sauri"
************
Tafe yake hankalinsa gaba daya baya tare dashi yana can wani waje daban ya kusa da gidan da zaije ta gabansa aka shigayi masa horn da ya kauce da sauri ya dago kai ya dubi motar yayi saurin kaucewa,idonsa na kan motar gabansa yadan fadi yabi motar da kallo,tabbas wanan motar bilkisu ce yarinyar dazun da suma hadu a asibiti,tambayar kansa ya shiga yi abinda ya kawota wanan unguwar da wanan yamman?kuma yana tsammanin kamar daga daya daga cikin estate din can ta fito,to me tazoyi can din?shiru yayi yabi motar da kallo har ta bace zucuyarsa cunkushe da tunani kala kala...
Tuki take akan titi amma gaba daya hankalinta baya jikinta,babban abinda ke gabanta shine ta shiga gida ga magriba tayi tasan ummanta na can na jiranta,sanan kuma mutumin da tayiwa horn dazun yayi mata kama da wanda ya tukota daga asibiti zuwa gida...waigawa tayi bayanta ko zata gansa bataga kowa ba haka ta maida kanta kan titi tana sharara gudu tasamu ta isa gida da wuri,ga zazzabi da takeji cikin jikinta tanajin wani irin ciwo a kirjinta yadda takeji ga ciwon kai idonta sunyi jajir...
*********
Ta karyo kwanar unguwar da motarta gabaki daya hankalinta baya jikinta dik ta kosa ta karasa gida ta duba wayarta taga me kiran ta ko ummah ce?gashi yamma tayi,kamar ance ta waiga taga giftawar motar hajiya hafsat kanwar mahaifinta, a gefenta khairee ce da alama daga gidansu suke, gabanta ne ya yanke ya fadi take taji ta tsure kila dama kiran da akeyi mata kenan? innalillahi wa innah ilaihi rajiun tasan taxo duba jikinta ne,ta dafe kanta bataso hakan ba,dik mugun nan ne kamal ya janyo mata hakan take ta sakejin tsanarsa ta darsu a zuciyarta,dakyar take murza sitiyarin motarta ta shigo cikin street dinsu zuciyarta cunkushe da bakin ciki... Haka ta karaso gidan ta shiga dannawa mai gadi horn aguje ya fito ya wangale mata gate tayi ciki a guje,
Parking tayi ta fito idanuwanta kozai kozai dik hawaye sun bushe mata a fuska haka take takawa zuwa cikin gidan nasu dik inda ka waiga a harabar gidansu hadaddun flowers ne masu ado kala kala da furanni masu kamshi wadanda suka kawata gida....mai bawa flower ruwa ya tsugunna "barka da dawowa hajiya"daga masa hannu kawai tayi alamar amsawa yabi bayanta da kallo sanan ya mike ya cigaba da abinda yakeyi.
Takun takalminta yasa ummah saurin kallon kofar shigowa parlorn "assalamu alaikum"da sallamarta ta shigo idonta na kan mahaifiyarta tana kokarin gano wani abu a fuskarta,
"Waalaikumussalam bilkisu kin shigo kenan"
"Ehh ummah wallahi...." Zatayi magana nafisa dake bayanta tai saurin katseta gudun kada ta kwafsa
"Ke billy tun dazun kinki shigowa kina waje kina hira ko?daga cewa shiga gida gani nan zuwa kin shanyani toni tafiya ma zanyi"ta dan harareta,
Ajiyar zuciya bilkisu ta sauke dan ta fahimci abinda nafisa ke nufi hakan yasa tasamu kwarin gwiwa "haba pheey kiyi hakuri mana bagani na shigo ba?kinga yanzun haka ma bakon be tafi ba nace ya jirani gani nan zuwa zanzo wajenki dan nasan halin fitinarki baki da hakuri bakida uzuri muje ciki"ta mike ta dau jakarta tayi gaba nafisa tabi bayanta har sashenta,
Suna shiga daki nafisa ta soma kallon bilkisu daga sama har kasa gabaki daya ta rame sai uban fari da tayi idanuwanta sunyi zuru zuru... Murmushin takaici bilkisu tayi,ta jefar da jakarta da gyalenta akan gado sanan ta karaso ta dafa kafadar kawar tata idanuwanta na kawo ruwa,
"Pheey nasan kallon nan da kikeyi mun kona meye ne ba sai kin kaiga tambaya ta ba,amma dan allah kiyi mun alfarmar kada kice zaki tambayeni halin da nake ciki da dik wasu abubuwa dake faruwa kinji?dan banida amsar su ban kuma shirya yi miki bayanin komi ba yanzun"ta karashe maganar hawaye na gudu a fuskarta,
Ita ma pheey din kwalla ce ta ciko a idonta ta shiga girgiza kai "shikenan billy tunda kin rigada kin yanke hukunci da gaggawa batare da kin tsaya kinji mezance ba,nasan kafiya da taurin kai irin naki tunda kika rigada kika yanke hukunci bazaki taba fadamun ba,amma abu daya zan rokeki shine dan allah kome ke damunki ko wani hali zaki tsinci kanki kada kiyi wasa ta feature dinki kinji?kidaina wasa da karatun ki dan allah kodan farin cikin mahaifiyarki don dik ranar da wani abu ya faru baa fata bazataji dadi ba zuciyarta ba zatayi farin ciki dake ba billy".....gyada mata kai billy tayi ta kauda kanta gefe hawaye na cigaba da zuba a idanuwanta,
Gefen gado pheey ta zauna ta share kwallar dake fuskarta "nayi wanan dabarar ne saboda kada ummah ta fahimci ba tare muke ba tunda nazo na tararda ummi hafsa tazo duba lafiyar jikinki,kuma da alama sun dade zaune bakyanan, shiyasa nayi wanan karyar da kina shigowa na fito dan kada ki kwafsa"
Rungumeta bilkisu tayi tana hawaye,itama pheey din bubbuga Mata baya takeyi "is ok besty,yanzun kije waje tunda naji kince bakom be tafi ba nasan kina nufin akwai bako a waje" dan murmushi bilkisu tayi,"babu wani bako nace hakan ne dan na fahimci karatun naki"
Dariya tabawa pheey ta kai mata duka billy ta goce tana murmushin karfin hali,
********
Ana kiraye kirayen sallahr magriba kamal ya fito sanye da blue din shadda ta karbi jikinsa da hula hannunsa rike da agogonsa da alamar alwala yayo zashi masallacii,
Yana tsaye a jikin gate din gidan yana kokarin kara kiran numbersa ya fito ,wani kallo yayi masa batare da yace masa komi ba yasa kai yayi hanyar masallcin unguwar inda mutane keta fitowa daga gidajensu dan zuwa sallah...
Bakin ciki ya tokare masa kirji ya sauki nannauyar ajiyar zucuya yabi bayansa shima don yasamu jam'i a masallacin dayaga ya nufa...
Sauri sauri yakeyi bayan an idar da sallar saboda ya samesa a gidan amma ko kafin ya karaso kamal yaja motarsa a guje hade da tada kura ya bar unguwar.....cakkk ya tsaya yana bin motar da kallo batare da ko motsin kirki ba,ya kusan minti goma sha biyar tsaye sanan ya daga kafarsa ya soma tafiya,yana tafe yanajin wani jiri na dibarsa saboda tsabar takaici da bakin cikin abinda yayi masa haka ya iso bakin titi ya tari me mashin ya hau zuciyarsa na masa wani irin tafarfasa.....
*GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO* *LITTAFIN IZZA TA DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN* *NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619*
DAGA WANAN PAGE DIN INAGA ANGAMA BADA FREE PAGE MESON SIYAN LITTAFAN MU GA NUMBERS NAN YA TUNTUBEMU DA NUMBER TA CIKI INAWA MASOYA FATAN ALHERI
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*5*
"Amina yanzun tun bayan fitar bilkisu tun safe har yanzun baku gyara mata sashenta ba keda safiyya?yanzun idan tazo kukayi fada da ita ai bazakuji dadi ba tun tuni bakuyi abinda tasaku ba to kuna me?"
Shiru sukayi duka su biyun batare da sunce komi ba sai zare ido sukeyi,...mai aikin abinci ce ta shigo hannunta dauke da babban faranti wanda ta dorowa ummah abincinta akai da lemo ,ta dire akan karamin table din dage gefen kujerar da ummah ke zaune,
"Sannu shaawa har kin gama abincin rana?"...wadda aka kira da shaawa ta dagawa ummah kai cike da ladabi "ehh ummah na gama dama yanzun nake shirin tunda na karasa in gyarawa anty bilkisu bangaren nata tunda su safiyya basuyi ba"
A dan fusace ummah ta soma magana "bazakiyi ba su zasuyi shi dan biyansu zaai kamar yadda kema zaa biyaki,aike ba inji bace dan haka ki koma bangarenki na girki da gyaran kitchen suma suyi aikinsu tunda ai neman kudi sukazo suka baro gidan iyayensu idan kuma bazasuyiba in tarkatasu inkira uwale ta kwashesu ta maidasu kauye"
Mikewa shaawa tayi batare da tace komiba ta juya da nufin tafiya,ta hada ido dasu a tare ta kifta musu ido alamar su biyota aiko tana gaba suna biye da ita ummah ta watsa musu harara a fili ta furta "shashashan yara kawai mtswwe "ta janyo table din zata soma cin abinci bilkisu ta shigo parlorn hannunta rike da jakarta da gyalenta da ya zame idanuwanta sunyi jajir fuskarta kanta ta canja kala tayi jajir,kallo daya ummah tayi mata gabanta ya yanke ya fadi,ta dire cokalin tana kallon yar tata cike da faduwar gaba,
Kasa hakuri ummah tayi tace cike da fargabar yanayin da taga yar tata ciki,"bilkisu lafiya na ganki haka?meyake faruwa?meya faru dake naganki a wanan yanayin bilkisu"lokaci daya ta jerowa bilkisu wadanan tambayoyin cike da rud'ani,
Zama bilkisu tayi batare da tacewa ummahn nata komi ba sai wasu sababbin hawaye masu zafi da suke gudu a fuskarta babu kakkautawa ga zufa dake karyo mata ta ko ina daga sassan jikinta,
Wani wahalallen miyau ummah ta hadiye hade da mikewa tsaye ta tako ta karaso inda bilkisu ke zaune tana zubar hawaye,nan da nan idon ummah ya cicciko da hawaye ta girgiza bilkisu cikin kosawa "bilkisu ki fadamun meyafaru dake?wani irin hali kike ciki haka da yasa na ganki haka ga kuka kina famanyi?"...girgiza kai bilkisu tayi a raunane tabude baki tace,
"Ummah rayuwata tana cikin garari ummah, rayuwata ta nakasa ummah da kananan shekaruna,na tsinci kaina cikin mummunan yanayi mummunan rashin lafiya me hadarin gaske.....ummah na ciwon hanta gareni wanda a turance ake kiransa da hipatitis"ta fashe da kuka mai ban tausayi,
Daskarewa ummah tayi a tsaye jin kalmar karshe da bilkisu ta furta mata, take taji wata juwa na dibarta kwakwalwar kanta na barazanar tarwatsewa da jin mummunan furucin da yartata tayi,
"Innalillahi wa innah ilaihi rajiun,allahumma ajirni fi musibati"ummah ta furta kwallar da ta ciko a idanuwanta ta sulalo a fuskarta ta nemi gefen bilkisu ta zauna jagwab,take kanta ya soma sara mata...
Kuka sosai bilkisu takeyi ganin yanayin da umman nata ta shiga,take tausayin kansu ya kamata ta sa hannuta dafa kafadar ummanta ta soma magana a raunane "ummah na "ta kira sunanta tana kallonta,a hankali ummah ta dago idanuwanta da suka jike da hawayen bakin ciki da tashin hankali ta dorasu akan y'ar tata,
"Ummah na banida wadda ta fiki a fadin duniyan nan,ya zanyi da rayuwata idan ke bakikasance me karfafani ba akan wanan jarabawar da allah yayimun?kece uwa da koda yaushe take zama garkuwa da sanadin farin cikin d'anta idan ke kina kuka ni inyi yaya ummah na?ki share hawayenki in samu sassauci a zuciyata ummah na ke kadaice farin cikina dik fadin duniyar nan "...
Rungumeta umman ta tayi suna kuka mai ban tausayi a tare,zuciyarta tayi mata rauni sosai tausayi da soyayyar yar tata kwaya d'aya tilo shine abinda yake yawo jikin jini da tsokarta a wanan lokacin,jin jikin na bilkisu ya soma daukar zafi yasa ta sassauta rungumar da tayi mata ta sharewa bilkisu hawaye "bilki na kiyi shiru ki daina kuka cuta ba mutuwa bace kuma allah yana sane dake shiyasa ya jarrabaki ta wanan yanayin yaga tawakkalinki da imaninki kinji? kiyi shiru kidaina kuka yanzun kitashi ki shiga ciki kiyi wanka kizo kici abinci kinji bilkina?"
Gyada mata kai tayi wani sabon kuka na kokarin kwace mata ta danne zuciyarta "toh ummah na"ta mike a sanyaye ta kwashi jakarta da gyalenta tayi hanyar sashenta ,umman nata tabi ta da kallon takaici,ita kanta hawaye ne ya sulalo mata a fuskarta....
********
Zaune yake a farar kujerar roba ya jingina da jikinsa sosai yayi nisa cikin tunanin wanan yarinyar daya hadu da ita a asibiti,haka kawai yakejin sa cikin wani yanayi wanda ya kasa fassara hakan,tausayin yarinyar yakeyi sosai wanda hakan yasa ya mance da tashi lalurar da yake tattare da ita,....ta dade tsaye a kansa kusan rabin awa tana tsaye amma alamu sun nuna bemasan da ita a wajen ba hakan yasa ta dan bubbugi gefen kujerar "abdul...abdulll yaya dai?tunda ka dawo gabaki daya baka cikin hankalinka meke damunka ne?kasamu ka siyo maganin kuwa?ko jikin naka ne?"
Runtse idonsa yayi ya bude hade da sauke ajiyar zuciya yace "innah babukomi kawai dai banajin dadin jikina ne nagaji"ya kirkiro murmushin karfin hali,
"Toh ga abincin ranan ka nan a kula na ajiye maka kaci nasan kana jin yunwa tunda tun safe ka fita gashi yanzun har karfe uku na rana kuma ko karyawar kirki bakayi ba ka tafi asibitin nan"
Mikewa tsaye yayi ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa "banajin yunwa"shine abinda yace a takaice ya sa kai yayi hanyar dakinsa,.kallo mahaifiyarsa ta bisa dashi cike da mamaki tunda abdulhrahman yake bata taba ganin damuwa karara a fuskarsa kamar na yau ba,gaskiya akwai wani al'amari da yake damun abdul,
Ajiyar zuciya innah ta sauke ta juya da niyyar shiga daki,yar matashiyar budurwa dake tsaye a kofar daki fuskarta dauke da damuwa ta katsewa innar tata hanzari "innah wai menene yake damun yayah abdul?tundazun daya dawo nagansa tamkar bashi da lafiya,dazun ma har hawaye naga yanayi innah"... girgiza kai innah tayi "bansani ba zainab yadda kika gansa haka nima nagansa,fatan dai allah yasa lafiya "innah ta shige daki zainab ta zauna tai shiru tana tunanin halin da yayan nasu yake ciki
*********
Fitowarta daga wanka kenan daure da towel light blue ta saki gashinta a bayanta yana lilo, fuskarta tayi fayau idanuwanta sun fada kadan har wata ramar dole tayi,gaban madubin ta ta tsaya tana kallon kanta daga sama har kasa tanajin wani bakin ciki na kara lullube mata zuciya,wayarta dake kan bed side drawer ce ta soma ruri ta dan juyo ta kalli gefen da wayar take ta cigaba da shafa mai sama sama saboda zafin da takeji ta feshe jikinta da turaruka sanan ta karasa wajen wardrobe dinta ta bude ta ciro doguwar jallabiya baka ta zura tana shirin ficewa a dakin wayar ta sake ringing,dan tsaki tayi ta karasa wajen wayar ta dauka ta duba me kiran nata kamal ne tagani,gabanta ya yanke ya fadi wani kululun bakin ciki yazo ya lullube zucuyarta kamar bazata daga wayar ba har ta kusa tsinkewa sanan ta dauka ta kara a kunnenta zuciyarta na harbawa batare da tace komiba,
Daga can bangaren yayi yar dariya daga kwancen da yake ya shafi sajen fuskarsa sanan yace "billy billy har kin kai matsayin da zan kiraki a waya kina kallo kiki dagawa ko?"dakyar yake maganar cike da gadara da isa,
Haushi ya bata batace komiba sai dan tsak7i da tayi wanda yayi karaf a kunnen kamal,hakan yasa yayi zumbur ya mike daga kwanciyar da yake ya furta "what?....tsaki billy?tsaki fa kikaimun,koda yake banyi mamaki ba dan kinyimun tsaki amma wanan karon zaki d'and'ana kudarki wallahi wanan tsakin da kikaimun ya janyo miki yau saina hau kanki sau shida saina tabbatar da bakya motsi sanan xan kyaleki"..a furgice cike da tsoro muryarta tana dan rawa ta soma magana cikin in ina..."..kama..l dan allah kayi hakuri ba tsaki nayi maka ba,kaji?ka tausayamun kamal ka daina azabtar dani ta wanan hanyar kaji? wallahi idan aurena kakeso xan yarda ka aureni koda babu sadaki ne da ka rinka aikata zina dani kamal ka taimakeni ka tausayamun kada in kare a wanan mummunan aiki"kwalla ta ciko a idonta,
Murmushin k'eta yayi sanan yace "billy nafada miki kidaina bata bakinki wajen rokona in aureki,bazan taba iya aurenki ba billy tunda na rigada na d'and'ani zumarki nasan yadda kike bakida sauran amfani a wajena banda kicigaba da zama baiwar shimfidata,a dik lokacin dana bukaceki dole kizo in biyawa kaina bukata batare da ko sisina ba idan kuma kika musa in fallasaki a idon duniya cikin seconds da basu wuce talatin ba zaasan wacece bilkisu bala dan maliki me hadarin naira"..kuka ne ya kwace mata ta shiga yi masa magiya da rokonsa,
"Kina bata lokacinki billy kawai dai yanzun ina bukatarki don haka minti talatin kadai na baki kisameni a gidana,idan kuma bakizo ba ko kika batamun lokaci kin kirawa kanki me alewa bakida kudin siya"yana gama maganar yayi difff da wayar...kallo tabi wayar dashi hawaye na sauka a idanuwanta a fili ta furta "na shiga uku"...tana cigaba da kallon wayar ummah ta turo kofar ta shigo,d'an razana tayi tana kallon umman nata cike da tsoron allah yasa bataji me take fada ba....kallo ummah take bin bilkisu dashi,
*WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903*
*******
Hawaye ne kawai yake zuba a idon abdul ganin dik kiran da yakewa wanan guy din baya dauka...to meyake nufi dashi kenan? gashi ya kirasa yafi sau hamsin a yau be dagawa kiran karshe da yayi masa call waiting ya gani,bayan ya gama wayar ya kara kiransa sai ya danna masa busy....
Shikenan nufinsa bazai basa kudin da zai sai maganin da zaisamu lafiyarsa ba?kenan ya tashi a fanko kenan?....dafe kansa yayi da yake sara masa kamar zai rabe biyu...take bilkisu ta fado masa a rai ya zabura ya shiga duba katinta da tabasa yasan bazai rasa number wayarta a jiki ba ..
*******
"Bilkisu naga kamar kuka kikeyi kina waya meya faru ne?kodai kim kira kinfadawa wani halin da kike ciki ne?"ajiyar zuciya bilkisu ta sauke jin umman nata bataji wayar tata ba take dabara ta fado mata "ummah na wallahi kuka nakeyi yanzun kawata pheey ta kirani wai ashe anyi mata test din english yau bansamu halartar test din ba ina asibiti shine take shedamun yace dik wanda beyi test dinba sai ya basa carry over"...cike da damuwa ummah ta dan zaro ido "yanzun ya zaayi bilki na"
"Ki kwantar da hankalinki ummah pheey tasameshi ta fada masa banida lafiya naje asibiti wajen likita shine yace inzo karfe hudu na yamma zai mun makeup da sauran wadanda sukeda uzuri kamar nawa zai mana tare yanzun haka jirana ma pheey take a makaranta sai nayi zamu dawo tare"..ajiyar zuciya ummah tayi "toh alhamdulillahi maza ki shirya kada ki makara a fara kina nan kuma karki fadawa kowa halin da kike ciki ki gyara fuskarki kinji?kada kije kina tunane tunane da koke koke"
Gyada mata kai bilkisu tayi,tausayin umman nata ya kamata...allah sarki mahaifiya...
"Maza ki shirya ki fito kidanci wani abu kafin ki fita nasa shaawa tai miki fruit salad"
Kwalla ce ta ciko idonta ta juya baya kada ummahn nata tagani...ummah ta juya ta fice ta rufo mata kofa...tana fita bilkisu ta fada kan gadonta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai da bakim ciki....ta dauki lokaci tana aikin kuka kafin ta tuna da mintunan da kamal ya bata ta zabura da sauri cike da tsoro ta shiga shiryawa ko brazia bata sa ba ta gyara guskarta ta lullube kanta da siririn gyale gashinta kwance a gaban goshinta,dikda halin da take ciki hakan be hana fuskar bilkisu yin kyau kamar koda wani lokaci ba....
A gaggauce tasha fruit salad din tayiwa ummanta sallama "a dawo lafiya bilkina allah ya tsareki ya karemun ke marainiyar allah"
"Ameeen"tace kawai ta fice...
*******
Zaune yake a kasan carpet a parlornsa gabansa tukunyar shisha ce yana famar zuka yana busar da hayakin ta hanci ta baki parlorn gabaki daya ya kaure da hayaki bilkisu ta turo kofa bakinta dauke da sallama a sanyaye ta sunkuyar da kai,....bude hannuwansa yayi alamar ta taho garesa,batama san yanayi ba kusan seconds talatin jin shiru yasa ya kara zukar shisha ya gurzar da hayakin sanan cike da isa yace "au bazaki taho kimun oyoyo ba?da kikasamu darajar wanan faffadan kirjin na jan zagi gaba da maza masu kirar lagwani?"rau rau tayi da ido tana kallonsa ya kara bude mata hannu,jiki Babu kwari gabanta na tsananin faduwa ta karaso ta fada jikinsa kamar yadda ya umarceta hawaye kuwa ya kubce mata jin yadda ya cafki boobs dinta yana murzawa a hankali...yana kallon kwayar idonta hawaye na gangarowa ta gefe "kin kyauta da baki bani wahala wajen kakaba wanan rigar da kike boye halittun kirjinki dasu"...cikin shasshekar kuka ta soma magana "kamal dan girman allah inayi maka wasiyya da kaji tsoron allah kadaina fasikanci dani haka ka kyaleni inji da zunubin da muka kwasa,ko kuma ka aureni wallahi zan amince"....kallonta yakeyi sanan yakai bakinsa yana tsotse hawayen fuskarta a hankali yake lasa yana cigaba da matsa boobs dinta da suke mata azabar zafi....runtse ido tayi saboda zafin da takeji "washhhhh allah na"tana cigaba da hawaye....
Yar dariya yayi "kin soma daukar carji koh?sakon ya fara isa inda nakeso....ina fatan kinshiryo yadda ya dace dan banajin yau yadda nakejin yunwarki zanbarki ki koma gida"
Zaro ido tayi cike da fargaba da tsoro,gira daya ya daga mata hade da kafeta da idanuwansa kamar wani maye yana lasar bakinsa....kallo yadda idanuwanta sukai jajir yayi suka kankace saboda tsabar. Bakim ciki da kuka da takeyi baka iya ganin farin idonta sai bakim daya rikide da farin daya koma launi. Ja....
********
Gumi kawai ke karyowa abdul wajen neman katin da bilkisu ta bashi dakyar ya tuna da inda ya ajiye katin cikin aljihun wandonsa da sauri ya zaroshi ya karanta sama bilkisu bala dan maliki....shine cikakken sunanta...rasss gabansa ya yanke ya fadi zufa ta fara karyo masa ta ko ina, bilkisu bala?a ina ya tabajin wanan sunan?tabbas yasan wanan sunan a wani waje dikda yau ya soma tozali da ita....idan hakane itace yar attajirin nan daya rasu shekara hudu da suka wuce Wanda akeyi masa lakabi da mai hadarin naira?...zuciyarsa ta gargadesa da anya abdulhrahman wanan yarinyar zaka iya kulla alaka da ita?bayan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa?.... idan be manta ba yasan kanwar mahaofinta hajiya hafsat matar major mai kudin nan da kowa yasan da zamansa a wanan jihar.....hannu yasa ya share zufar dake karyowa a fuskarsa ga wutar kaunar yarinyar dake ruruwa a zuciyarsa kawai ya yanke shawarar kiran number dake jikin katin....ya ciro wayarsa ya soma daddana numbobin daya gani.....
GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA DUMA LITTAFAN GUDA SHIDA DARI BIYAR NE KACAL...MAI BUKATAR LITTAFIN IZZA TA KADAI ZAI BIYA DARI BIYU YA NEMI WANAN NUMBERS DIN....08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*8*
Dago rinannun idanuwanta tayi ta saukeso akansa wanda hakan yayi daidai da d'ago nasa fararen idon masu kama da yanajin bacci ya kafe ta dasu,wani irin shu'umin kallo yakeyi mata hade da murmushi mai cike da mugunta da k'eta,haushinsa da tsanarsa suka kara lullubeta,nan da nan miyaun bakin ya ya kafe sai wani d'aci da takeji a cikin bakinta,hakan besa ta kasa magana ba cikin wata iriyar murya tace.
"Yanzun menene dalilinka na zuwa gidan mu?kazo ne ka nemeni a gidan ubana?ko kazo ne ka sanarwa da ummah ta ka gama lalata rayuwar yarta da jefa ta cikin garari?"ta kafe sa da kallo mai cike da tsana.
Nisawa yayi sanan ya dage kafadarsa sama "kanki akeji billy,dik abinda kike fada inajin su a kunnuwa na ne tamkar busar sarewa amma cikin zuciyata kwad'aice nake da kebewa dake dan nayi kewar zumarki"ya karasa maganar yana lashe bakinsa.
Bude baki tayi da niyyar maida masa da martani,maganar ummah ce ta katse mata hanzari.
"Kamak kasamu kaci abincin kuwa?ko a dafa maka wani abu ne bakason wanan din?".
Sun kuyar da kansa yayi cikin jin nauyin ummahn "ummah a koshe nake ko kafin in fito ma naci abinci a gida wallahi dama cewa nayi bari inzo in dubaku in gaisheki"ya karasa maganar yana kokarin mikewa.
"Aiko nagode sosai kamal allah yayi maka albarka kaji?"
"Ameen ummah".
"Ka gaishemun da hajiyar insha allahu idan nasamu fitowa zan bullo wajen naku nagode"
Ya kama hanya da niyyar ficewa parlorn,ummah ta kalli bilkisu dake zaune Bata da alamar motsawa,ummah ta harareta tai mata alama da ta rakasa mana,hakanan badan ranta yaso ba,kuma batason ummah ta fahimci wani abu yasa ta kauda kanta gefe tana boye hawayen da suka cicciko a idanuwanta tabi bayansa.
Har wajen motarsa tabi sa yana sane da tana biye dashi dan haka ya juyo ya sakar mata murmushi sanan ya bude motar ya shiga,daga inda take tsaye yake kare mata kallo daga sama har kasa,sanan ya dan tamke fuskarta ya yafito ta da hannu alamar tazo,tsaye tayi a wajen ko alamar motsawa batayi ba ya sake mata alama da tazo taki zuwa,a kausashe yace "idan har bakizo ba abinda kike gudu ne zai faru a nan wajen dan wallahi fitowa zanyi in rungumeki a wajen inyi miki abinda na gadama tunda na tabbatar ummah bata ganin mu,iyaka dai mai gadi gashi can da malam iro mai yankan fulawas su ganki,kinga idan kina musu wata barazana sai su san kedin mutuniyar banza ce".
Bata da zabin da ya wuce bin umarninsa dan tasan zai aikata abinda yafi haka, dan haka yasa ta karaso ta tsaya gaban motar tasa ta juyar da kai.....shiko wani irin shu'umin murnushi yakeyi kasan zuciyarsa kuwa babu abinda yakeji dangane da itan,yanayi ne domin ya guma mata.
"Inaso gobe in ganki a makaranta da wuri sanan a wajen lectures dina da zan gabatar karfe bakwai na safe dan bayan na gama lectures zan gabatar da test inaso ki rubuta shi idan idan baki rubuta ba bazanyi miki makeup ba sanan daga makarantar ina bukatar muje guest house dina dake nayi kewar lallausar fatar bilkisu sarauniya,yarinya mai kyau mai kwarjini yarinyar da jami'ah kowa ke rububin yi mata magana yarinya mai aji da yanga uwa uba ga dukiya yarinyar da kowa burinsa ace yana magana da bilkisu dan maliki mai hadarin naira"ya kashe mata ido ya tada motarsa.
Da sauri taja da baya ganin yadda yake kokarin taka ta da mota,hawayen bakin ciki ne suka sulalo a fuskarta,tasa hannu ta share sanan tayi hanyar garden dan bazata iya shiga cikin gida da wanan fuskar ba ummah ta fahimci wani abu sai kawai ta karasa garden ta zauna a kujerar da ta zame mata wajen zamanta a koda yaushe.
WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATAR SIYAN DUKA ALKALUMA 6 KO LITTAFIN IZZA TA YA TUNTUBI WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 08103943903
Ta dau minti goma zaune wajen zuciyarta na tafarfasa tunanin makomarta kawai shine abinda takeyi,shin idan ta mutu a wanan halin me zata cewa mahaliccinta?zina?menene illar zinar a nan gaba?wani labari zata bawa mijin da zata aura idan ya same ta baa cikakkiyar mace ba?,wace amsa gareta da zata sanar masa na ainihin abinda ya jawo hakan?.....nisa tayi cikin tunani hawaye na gudu a fuskarta bata ma san cewar Iro yazo gareta ba yana kiran sunanta,"hajiya".
Bubbuga gefen kujerar yayi sanan tayi furgigit ta juyo garesa tana kallonsa ba tare da tace masa komi ba,sosai tabawa iro tausayi dikda besan dalilin da yasa ya ganta cikin wanan halin ba,"dama bako ne kikayi a waje,tun dazun yazo yace a sanar miki da sunansa abdulhrahman ya kira wayarki baki daga ba".
Hannu tasa ta share hawayen ta tayi shiru tana tunanin inda tasan mai suna abdulhrahman,ta kasa tunawa saboda yanayin da take ciki zuciyarta na ayyana mata tace masa yaje ya dawo kawai,wata zuciyar kuma na bata shawara tace ya shigo taga ko waye mana?tunda batasan daga ina yake ba,samun kanta tayi da cewa iro "jeka shigo dashi nan idan ka kawosa sai ka shiga ka cewa safiya ta kawo mun lemo da ruwa"
"Toh ranki ya dade"ya mike cikin sauri, ita kuma ta maida kanta gefe cikin sauri ta gyara fuskarta da hannunta gudun kada wanda yazo ya fahimci halin da take ciki dikda batasan ko waye ba,tunani kawai takeyi ita bata da aboki namiji,sanan bata da wani saurayi da zaizo wajen ta kuma har gida to waye wanan?bata karasa tambayar kanta ba ganin wanda ya nufo inda take shida iro yasa ta mike tsaye zumbur kamar wadda aka tsikara....rikide mata yakeyi yana juye mata wani mutum wanda siffarsa tayi dai dai da ta wanda ke tahowa gareta jiri ne taji yana neman dibarta saura kadan ta fadi kasa,nunasa takeyi da yatsa tana shirin furta masa mai ya kawo sa wajenta?sai kuma taga wanda take tunanin bashi bane wanan abdul din da ta hadu dashi ne a asibiti,zama tayi jagwab akan kujerar ta dafe kanta,zuciyarta na cigaba dayi mata lugude,nan da nan taji wani abu nayi mata yawo a jiki mai zafin gaske....me yake shirin faruwa dani ne?meke damuna haka? innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ta furta a zuciyarta ba tare da ta dago ba,sallamarsa ta katse ta daga wanan halin da ta tsinci kanta.
"Assalamu alaikum barka da yammaci kanwa ta ni na biyo ki tunda ko cigiyata bakisa anyi ba,na saurara a gidajen radio inji ance ana cigiyata daga kanwata amma shiru"ya karasa maganar da janyo daya daga cikin kujerun wajen ya zauna.
Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta dago fuskarta batare da ta hada ido dashi ba ta k'ak'alo murmushin da daka gani kasan iya fuskarta yake,"barka da zuwa yayah abdul ni nayi fushi ai kaida nake ta sa idon ganinka?"
Murmushi yayi sanan yace cikin muryarsa mai cike da kamala "to ai gara ni na nemeki ai tunda na kira wayarki kwana kin baya baki daga ba,kuma baki biyo misscall dina ba,sai yau dazun ina hanyar zuwa nan naga kiranki sai ban daga ba tunda ina hanya zanzo duba jikin naki ya jikin naki yanzun?"ya karasa maganar da jefo mata wanan tambayar.
Shiru tayi tana sauraren muryarsa dake yi mata amsa kuwwa a kunnuwanta wadda dik lokacin da zaiyi magana sai gabanta ya fadi tayaya zata gasgata zaton ta na muryar wanda take ji a yanzun yana yi mata yanayi da muryar wanda tafi tsana fiye da kowa a duniya?ta yaya zata kasa gasgata zatonta ga ya abdul shine wanda ko mutuwa tayi ta farka yayi magana zata gane shine?kirrrr tayi da ido tana kallonsa,...shiko mamaki ne ya lullubesa yadda take kallonsa har yasa ya tsargu ya kalli jikinsa yaga mai take kallo haka,amma bega komi ba sai kawai ya hura mata iska a idonta,hakan yasa ta lumshe idanuwanta hade da sauke sassanyar ajiyar zuciya,wani zugi taji cikin zuciyarta wanda yasa taji tsohon mikin ciwon dake zuciyarta na kokari famuwa a sanadiyyar muryar wanda ke gabanta....idanuwanta ne suka cicciko da hawaye amma basu zubo ba tana kokarin maida hawayen ta cije bakinta kadan sanan ta bashi amsa da "yaayah abdul wallahi tun bayan rabuwarmu jikin nawa ne yak'i dadi shiyasa ban nemeka ba koda yake ma ban karbi number wayarka ba am sorry"ta rike kunnuwanta tana kallonsa idonta fal da hawaye.
Tsintar kansa yayi da kasa daina kallonta yadda ta rike kunnuwanta,da kallon da take yi masa shi ya narkar masa da zuciya ya saukar masa da wata irin muguwar kasala da ya kejin sabon yanayi a cikin jikin nasa,yanayin da bazai iya fasaltawa ba,ga wani tausayin yarinyar dake yawo a jinin jikinsa ya lullubesa daga sama har kasa....sun kai minti goma suna kallon juna tana rike da kunnuwanta,ganin yadda yake kallonta ya kara fadar mata da gaba,ta tuna da wani mayen kallo da bazata manta dashi ba a rayuwarta...katse sa tayi cikin sanyin murya "yaayah abdul baka sha lemo ba bari in zuba maka sai in sanar da ummah na zuwanka sai ka shiga ka gaidata koh?".
Maimakon ya amsa sai kawai ya kifta mata ido cikin wani salo da baisan yayi hakan ba,ita kanta wani iri taji da har kunya ta kama ta ta sadda kanta k'asa.....
**********
"Yayah kamal wai yaushe zaka samo mana anty ne wadda zaka auro mana ita mu rinka zuwa gidan ka hutu muma muce yayanmu yayi aure?"afee tayi maganar cike da zumudi.
Ko kallon ta kamal beyi ba abbah da yake cin abinci kusa da kamal din ya karbe zancen da "yauwa auta ashe bani kadai nakeso kamal ya samo matar aure ba harda ku kuma kunaso kenan yayi aure koh?ya sama muku anty"
"Ehh abbah munaso wallahi kawayen mu a school suyi ta cewa matar yayanmu matar yayanmu kaza muko saidai muyi shiru"sosai nawal da afee suka bawa abbah da momy dariya,kauda maganar kamal yayi ta hanyar sako wani zancen da "yauwa momy dazun naje gidan Abbah dan maliki gaida ummah tace in gaisheki tana ta so tazo wajenki wai bilkisu ce bata da lafiya"
"Assha"ummah tace cikin alhini,"ya jikin bilkisun inji dai da sauki koh?"
Cikin yanayi na ko in kula kamal ya amsa da "ehh da sauki ta warware alhamdulillahi "ya cigaba da cin abincinsa,momy kuwa da abbah kallon juna kawai sukayi sukai murmushi,karaf a idon afeee sai ta toshe baki ta soma dariya k'asa k'asa.
Wani kallo nawal take mata "injidai bani kikewa dariya ba koh?kinsan na tsani wanan dabiar taki afnan ta dariya haka kawai"
"Abbah ne naga yayi wa momy wani kallo shine nake dariya"gaba daya wajen har kamal suka soma dariya banda momy da tai wa afnan dakuwa tana murmushi "ungo naki kaga ja'irar yarinya"...girgiza kai kawai kamal yayi ya mike ya fice daga parlorn hannunsa rike da wayarsa....
Yana tafe hanyar sashensa wayarsa tayi kara ya duba yaga wata number ce babu suna dikda yaso gane number sai kawai ya danna recieve ya kara a kunnensa,daga can bangaren aka soma magana,"haba kamal ashe zakaci moriyar ganga ka yada gwauronta batare da ka cika alkawari ba?kaidin ba musulmin kwarai bane,yau kwana nawa ina kiran wayarka baka picking waya ta saboda ka samu biyan buka ta ko?...hmmm to kasani wallahi abinda kake gudu ne zai faru dan inada komi a ajiye nima,idan kana tunanin ka rabu dani ne to baka tsira ba bana gudun dik abinda zai faru ya faru".
Murnushi yayi mai cike da isa "ka gama maganar in kashe?"
"Au haka ma zakace?"kafin yace wani abu kamal ya kashe wayar yana murmushi ya jefata a aljihun gaban rigarsa....
WANAN LITTAFIN NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*7*
Tuki yakeyi cike da natsuwa,kallo daya zakai masa kasan lallai shi din maiji da aji ne da isa hade da izza,sanan ga kwarjini da kyau da tsantsar ruwar kamala daya bayyana a fuskarsa,cike da natsuwa yake murza sitiyarin motarsa da gaba daya zuciyarsa na can wani waje har ya karyo kwanar da zata sadashi da gidansu dake malali G.R.A tafe yake yana sauraren cool music a cikin motarsa har ya iso kofar wani tankamemen gida mai shegen kyau wanda ko baa fadawa mai karatu ba yasan gidan na manya ne....tunani ya shigayi ya shiga da motarsa ne ko yayi parking a kofar gida?jimmm yayi na dan wani lokaci sanan yayi parking a daidai kofar gate dinsu ya dade cikin motar sanan ya fito ya rufe motar hannunsa rike da wayoyinsa,kunnensa sanye da kunne daya na ear pice wanda dashi yake amsa waya....
Shigarsa cikin harabar tankamemen gidan yasa da sauri mai gadi yadan rusuna "barka da zuwa ranka ya dade kamalu"...murmushin gefen fuska kamal yayi sanan ya dan rusuna yace
"Haba baba dauda nasha fada maka banason wanan durkuson da kakemun kana gaidani,nine ya kamata in durkusa in gaisheka ba kaiba,koba komi kayi jika dani"
Jinjina kai me gadi yayi cikin jin dadin kalaman na kamal yasa ya danyi murnushi kaunar yaron na kara ratsa zucuyarsa "allah sarki kamalu ai durkusawa wada ba gajiyawa bane girma ne allah ya baka tunda dik gidan nan kaine babba Kuma bayan mahaifinka alhaji kai zamu girmama a matsayin magajinsa kaga ko dole in girmamaka ko?"....murmushi kamal yayi ya katse baba da maganar ta hanyar gaishesa "barka da yammaci baba dauda ya aikin?"
"Lafiya lau kamal alhamdulillahi,allah yayi albarka"
"Ameeen"shine abinda kamal yace ya mike yayi gaba hanyar shiga cikin gida,...kallo baba dauda yabi kamal dashi yana jinjina kai, Yana mamakin girmama na gaba dashi da kirki irin na kamal tamkar baa turai yayi karatu ba,tamkar badan alhaji mubammadu ba,mai kudin nan da sunansa ya zagaye jihar,bama jihar kadai ba kasa baki daya amma allah yasa masa natsuwa da hankaki tare da ibadah da muamala mai kyau d mutane,uwa uba ga kyauta....jinjina kai ya sakeyi sanan ya koma mazauninsa ya zauna.....
Sallama yayi cikin parlorn "assalamu alaikum"...be karasa shigiwa ba wata mata fara tass kyakkyawar gaske mai matukar kama da kamal wadda ko baa fada ba ansan mahaifuyarsa ce tai karaf tace "yauwa kamak ga afee nan tun dazun nake fama da ita ta tashi taje tai sallar magriba ta ajiye wayar nan abu ya gagara sai cemun take inbari abu take turawa"
Yar matashiyar budurwa ce hannunta rike da wayarta kanta yasha sabon kitso babu ko dankwali akanta take kallonsa, a tsorace bakinta na rawa cikin in ina,tace "sannu da zuwa ya kamal"...wani kallo ya watsa mata wanda yasa taja da baya tamkar zata saki fitsari a wando zucuyarta na ci gaba da harbawa,
Daka mata tsawa yayi "mai kike jira da bakije kinyi sallah ba?ubanme kike a wayar da har yafi ibadah gaida mahaliccinki"...girgiza masa kai tayi cike da tsoro ,jiki babu kwari ta ajiye wayar akan centre table batare da tace komi ba ta wuce ta gabansa sumi sumi tankar kwai ya fashe mata a ciki,
"Kuma insake ganinki kanki babu dankwali yar kauye kawai"
Karasowa yayi cikin parlorn ya dan rusuna yana gaida mahaifitarsa
"Ummi barka da yamma ina wuni"
"Lafiya kalau kamal,ko gaisawa bamuyi ba daga shigowarka nasaka magana da afee wallahi bataji kwata kwata allah dai ya shirya,ya aikin ya makaranta ya dalibai?"
"Lafiya lau ummah,abbah be shigo bane?"
"Yana masallaci nasan amma yau wuni yayi gida be fita ba yana hutawa a gida kasan tun gajiyar tafiyar nan be huta ba"
Wata yar budurwa ce ta shigo parlorn waccw zata girmi ta dazu sanye take da hijabi tace cikin siririyar muryarta "barka da zuwa ya kamal"
Fadada murmushinsa yayi sanan ya amsa mata "barkanki dai nawal ya makaranta?"
"Lafiya lau yaya yanzun ka shigo hala"
"Ehh yanzun na shigo me kukayi a gidan ne ki kawo min?"...mikewa tayi cike da natsuwa tai hanyar dining,
Kamal ya dubi mahaifuyarsa "ummah kinga nawal dinki sarkin natsuwa da hankali ko ba irin autarki ba"
Hararar wasa ummah tai masa "kaga banason cin fuska,autar tawa ce batada natsuwa?itama yarinta ce dududu kwaya nawa afee take?banson haka".. dariya kamal yakeyi sosai lokacin da nawal ta karaso hannunta dauke da jug da cups "yayah kamal ga wanan kafara sha kafin su hajjoh su karasa abincin na duba dining baa karasa saura ba"
Jinjina mata kai yayi "jazakillahu nawal dina,bari abbah ya shigo inaso in rokesa umarar bana dake zaa"...wani irin tsalle nawal tayi cike da farin ciki sanan ta koma kujera ta zauna tana ta washe baki,
Kallonsu ummah tayi ta mike "bari inje inga autata halin da take ciki dan baa isa an samun ita kuka ba"cikin faraa ummah take maganar ,tabar khamal zaune da nawal suna hira....
*********
*Bayan kwana biyu*
Zaune suke ko wanne a fararen kujerun dake cikin kitchen din sun hakince,yadda sukai zaman bazaka taba cewa masu aikin gidan bane,saidai suturar jikinsu da kwalliyar dake fuskokin mutum biyu daga cikinsu kadai ba sai anfada maka ba kasan yan kauyen kayau ne...
Medan jikin dake tsaye yar doguwa hannunta rike da kitchen napping tana goge sink ta kallesu yadda suna bararraje suna kwasar labari,
"Wai nikam safiya,kinga yadda anty bilki ta koma?dik ta rame ta koma wani iri ni tafara bani tausayi wallahi kome ke damunta oho",...wadda aka kira da safiya ta kada kai
"Kila dai tayi fada da saurayinta ne yasa take wadanan abubuwan kwana biyu dan ko jiya cikin dare na farka daga dakin mu na fito da nufi zuwa fitsari inajin numfarfashinta tana shasshekar kuka"
Girgiza kai shaawah tayi hannunta rike da kitchen napping "nidai babu ruwa na idan anzo anjiku kuna gulmar sai kusan abinda zakuce musamman ke safiyya me fadi baa tambayeki ba, harda cewa tayi fada da saurayinta koh?"......tabe baki safiyya tayi "sai kace nice na kawo maganar ba amina bace?dan kawai na tofa tawa?sai kice ni to Kinga tafiya ta ma zanje in tsinki ganyen taba taba da nake shanyawa zan kaiwa innah ta "
Rufe baki amina tayi tana dariyar mugunta ,itama shaawah dariyar take tana fadin "allah ya hadaki da hajiya taga ganyen da kike shanyawa kin kusa buhu daya taci ubanki"ta kwashe da dariya,
Sosai safiya taji haushin dariyar da sukeyi mata sai kawai tasa kai da nufin fita kitchen din aikuwa cikin rashin saa ta ingije bilkisu dake rike da cup da juice ya zube mata a jiki kofin ya fadi kasa ya fashe ji kake tassss....da sauri safiyya taja da baya tana karkada kai cike da tsoro da tashin hankali wanda ya bayyana a fuskarta zuciyarta ta harbawa jiran saukan mari kawai takeyi ta jingina da bango ta runtse ido hade da dora hannu akai,
A guje shaawah da amina suka fito corridor din da abin ya faru sukai tsuru tsuru ganin yadda lemo ya batawa bilkisu milk color din material dinta dukkansu zaro ido sukai suna jiran suga mai zatayi musamman safiya da ta fara kuka ga gumi na karyo mata,ga mamakinsu sai sukaji tace cikin sanyin muryarta "shaawa jeki daki na zakiga karamin towel ki dauko min da ruwa in goge material din nan da ya lalace gashi yau shi nakeson sawa"da sauri shaawah ta nufi aiken da akai mata ummah ta fito daga sashenta tana jiyo sautin shassheka kuka tana karasowa taga safiyya jikin bango tana rusa kuka "halan tayi miki wani wauwatar ta kauyanci ko?narasa yadda zanyi da yaran nan safiya da amina akan wanan halin da suke na kauyanci ji yadda take ihu dan allah kamar an yanka ta"
Girgiza kai bilkisu tayi "ba abinda nayi mata indai safiya ce ni nasan dama ba hankali ta cika ba tunda itace karamarsu idan nace zanyita dukanta jaka zan maidata"
"Dalla tashi kije sai kuka kike kamar an yanka ki kuma ki dauko tsintsiya da mopper ki share wajen ki goge shasha sha"
Wayar bilkisu ke ringing shaawah ta fito da sauri ta miko mata ta karba ganin me kiran yasa taki picking call din har ta katse wayar tana bin call din da kallo,
Karasawa parlor sukai ita da umman ta nan ma kiran ne ya sake shigowa a karo na uku still tana dubawa taga kamal ne ta ajiye wayar gefenta har ta karaci ringing dinta ta katse..... daga karshe ma daukar wayar tayi tai hanyar dakin ta wayar still ringing take,wani bakin ciki ne ya lullubeta hade da tokare mata wuya har bata ganin gaban ta ta nufi daki da wayat ummah tabi bayanta da kallo tana kissima abubuwa da dama....
*******
Zaune yan matan suke a jikin bishiya hade da samari suna hirarrakinsu wasu kuma suna kai kawo a cikin makarantar dik inda ka waiga yan mata ne da samari suke harkokin su wadanda basu da lectures masu lectures kuma wasu suna hall wasu suna classes anayi.....
Tun daga nesa suke hangen takun sa na girma yana sanye da farin yadi mai shegen kyau da tsada anyi masa dinki irin na zamani ya kafa hularsa baka wadda ta dace da aikin da akaiwa yadin mai surfani na bakin zare....hannunsa rike da wayarsa yake tafiyar gabaki daya hankalinsa na wajen kiran da yakeyi bata picking gashi yau kwana biyu kenan idan ya kira wayarta bata dauka idan yayi mata tex bata reply ko me hakan yake nufi oho?....to kodai bata da lafiya ne?ya tambayi kansa yana tafiya don karasawa inda yayi parcking motarsa,
Wata yar matashiyar busurwa ce dake gefe ta taba ta kusa da ita "pheey wai nikam ina billy ne?kwana biyu bana ganinta a makarantar nan ko an canja mata makaranta ne ta koma makarantar yaran manya?kinsan su manya"
"Baa canja mata makaranta ba batada lafiya ne yasa bata zuwa kwana biyu shine kawai dalili"
"Nikam pheey ba gulma ba wai meyasami kawarki ne kwana biyu dik ta canja?kamar ba billy da muka sani ba kamar ba bilkisu bala dan maliki ba meke faruwa ne?ko dai malam kamal akwai wani abu tsakaninsu ne?"dan tsaki pheey tayi
"Kedai ummi gulma a wajenki?dik wadanan tambayoyin na menene?ina ruwanki da rayuwarta?to nima bani da amsar tambayarki kingane?ki kama bakinki"...tabe baki ummi tayi
"Naga dai ai kawarmu ce shiyasa na tambayeki tunda bazaki fada ba ai shikenan laifi na ne ma dana damu har na tambaya...mtswwe"ta mike taja jakarta tai gaba pheey tabi ta da kallo har tai nisa sanan ta girgiza kai itama ta mike ta ja jakarta tai gaba...
*******
Guest house dinsa da ya saba zuwa can ya nufa yana shiga ko dakinsa be shiga ba ya ajiye yar jakar dake hannunsa ya zauna a kujera ya dauki remote ya kunna tv sanan ya janyo tukunyar shisha nan da nan ya hada ya soma zuga yana fesar da hayakin ta hanci ta baki idanuwansa sunyi jajir saboda tsananin takaici da yake ciki,kamar shi ya rinka kiran billy a waya tana kin picking call dinsa?har ta isa ta wulakantasa?ita din banza?lallai ta taro match din da bazata iya bugawa ba kwana biyu kenan yana kiran wayarta bata picking kuma be ganta a makaranta ba me take nufi?ya tambayi kansa saidai bashi da wanan amsar tambayar da yake yiwa kansa wani bangare na zuciyarsa ke raya masa to kodai bata da lafiya ne?ko wani abu ya same ta ne?idan haka ne gidan ya dace ya shirya yaje kawai ai gidan nasu ba bakonsa bane,da wanan shawarar ya sauke ajiyar zuciya ya ture shisha pot din dake gabansa ya mike ya zare rigar jikinsa ya nufi bedroom dinsa,kayan jikinsa ya karasa cirewa ya fada toilet dan ya watsa ruwa....
WANAN LITTAFIN NA KUDI NE MAI BUKATAR SIYAN ALKALUMA SHIDA KO WANAN LITTAFIN YA TUNTUBI WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 08103943903
*********
"Ya Abdul tun jiya nake tunanin zakaimun maganar kudin jarabawar nan bakayi mun ba gashi saura sati daya a rufe"
Sosai tabashi tausayi yadda tai maganar a marairaice idonta na kawo ruwa,
"Zainab ki kwantar da hankalinki insha allahu zaki biya kudin jarabawar nan kuma zaki zana jarabawar sanan kuma zakici jarabawar da izinin allah kinji? kedai kawai kiyi addua yanzun fita zanyi zanje wani waje idan nadawo zamu san abunyi kinji?"yayi maganar yana kallonta,...cike da gamsuwa da maganar yayan nata ta gyada masa kai tana murmushi "toh yaayah saika dawo allah ya tsare"
Innah dake gefe tana sauraren hirarsu dikda rabin hankalinta naga labaran radio da take saurare,ganin ya mike zai fita tace "abdul sai ina kuma?"
"Innah zan fita indawo ne bazan dade ba insha allahu zan dawo"
"Amma kasha maganinka"wanan tambayar tasa gabansa ya fadi dan bashida amsar da zai bata,besan ya zataji ba idan ya sanar mata da ainihin gaskiyar bashi da ko kwandalar da zai siyi maganin wanda yayi mata karyar ya siya yana sha,
Katse masa tunani tayi "ka dauko maganin kasha ga ruwa a gefe na dan daganin yadda kayi baka sha maganin ba"...inda inda ya shigayi dakyar ya saita kansa gaba daya a dururuce yake "innah baki yarda da abdul dinki bane?innah nasha fa ai bandade da gama cin abinci ba nasha innah,bari inyi sauri abokina na jirana tare zamu fita"kafin tace wani abu yayi gaba yana fadin sai ya dawo...daga inda take ta amsa da "allah ya tsare"
Da kafarsa yake takawa gefen titi da niyyar zuwa ganin yarinyar daya hadu da ita a asibiti,yanaso yasan halin da take ciki kusan kwana uku kenan yau,gashi tun ranan daya kira wayarta batayi picking ba Kuma bata biyo call dinsa ba yake cikin damuwa,da tunaninta yake kwana yake tashi ya rasa dalilin da yasa yarinyar ta shiga ransa,dik motsi idan yayi sai ta fado masa a rai....
******
Kwance take a makeken gadon dan kasar waje wanda gefe da gefensa aka kawata sa da manyan teddies masu kyau da tsada idonta a lumshe yake tana tunani kala kala,da sauri ta mike zaune ta janyo wayarta ta shiga key ta cire kamar wadda ta tuna wani abu ta shiga dube dube a wayarta tana laluben number da akai mata misscall kwanakin baya sai yanzun abun ya fado mata,cikin saa kuwa taga wata number da akai mata 2 misscall ko baa fada ba zuciyarta na ayyana mata wanan number ce.. tayi dialing...
Parking Kamal yayi a harabar gidansu ya ciro wayarsa a aljihu ya kara dialing number ta ga mamakinsa sau yaga number busy...murmushin keta yayi ganin wato tana sane da calk dinsa kenan dauka ne bazatayi ba yasa tunda gashi tana waya...rufe motar yayi ya nufi hanyar shiga gidan.
Da sallamarsa ya shigo parlorn ummah na zaune tana kallo gabanta plate ne tana shan fruit salad,ganin kamak yasa ta fad'ada faraarta "ah ah maraba da kamal d'ana maraba da kamal sannu da zuwa"..durkusar da kansa yayi cike da kunya ya karasa har inda ummah ke zaune ya tsugunna "sannu ummah ina yini"
"Lafiya lau kamal ya aiki?yasu hajiya inata cewa zan leka ta to bansamu na fita ba saboda jikin bilkisu da bata cika lafiya ba kwana biyun nan"gabansa ne ya fadi,amma sai ya dake "allah sarki ashe bataji dadi ba?"
"Ehh baka ga baka ganinta a makaranta ba?ai bata da lafiya ne,kamal mike mana ka zauna a kujera kamar bako?"murmushi yayi batare da ya kalli ummah ba ya mike ya koma kujerar can gefe ya zauna ya ciro wayarsa a aljihunsa,
"Bari insa su shaawah su kawo maka abinci da lemo ko sai ayiwa bilkisun magana ku gaisa"ummah ta mike ta nufi kitchen fuskarta dauke da faraa tanajin son kamal cikin ranta saboda natsuwarsa da kamalarsa ga uwa uba ilimi da ibadah da yake dashi shiyasa take jinsa tamkar yarta bilkisu...minti kadan ummah ta dawo shaawah da amina na biye da ita da babban faranti da aka jero kayan ciye ciye aka dire gabansa,
"Amina jeki kira bilkisu kice ga kamal yazo"
"Toh"
******Shiko abdul ganin kiran wadda zaije wajenta sai abun ya basa mamaki hakan yasa yayi murmushi ya maida wayar aljihunsa dan babu amfanin daukar wayar tunda wajenta zaije saidai ya gaji zai biya wajen abokinsa ya huta ya danyi hira idan rana tayi sanyi sai ya karasa gidan nasu yaga yadda jikin nata yake....
********
Tura kofar dakin amina tayi bakinta dauke da sallama,ta tsaya daga kofar dakin,wani kallo bilkisu tayi mata "umhmm ina jinki ya akayi?"
"Hajiya ce tace kizo ga ya kamal yazo"tana gama fadin haka ta fice bata jira cewar bilkisu ba,
Mikewa tayi ta zauna take taji wani abu nayi mata yawo a jikinta ji takeyi kamar ta fasa ihu saboda bakin ciki,nan da nan jikinta ya dauki rawa,bataso hakan ba babu abinda ta tsana a rayuwarta sama da hada ido da wanan azzalumin kamal wanda yayi kakagida ya zame mata karfen kafa a rayuwarta,wanda ke shirin barin ta da mummunan tabo Wanda bazata taba yafewa kanta ba,me yake nufi dani ne?kasheni yakeso yayi ko me?wato na nisance shi shine ya biyoni har gidan ubana kenan?dame zanji?da mummunar kaddarar da nake tare da ita ta wanan ciwo da nake tare dashi?kwalla ce taji tana shirin zubo mata a ido hakan yasa ta hadiyi wani mugun miyau mai daci da ya tsaya mata a wuya ta sauko ta dauki dankwalinta ta yane kanta dashi ta bude kofa tayo parlorn kada ummah ta biyo sahunta ta ganta a wanan yanayin....
Kamshin turarenta ya sanar masa da isowarta hakan yasa ya dago manyan idanuwansa ya saukesu akan fuskarta,ga mamakinsa kauda idonta tayi taki bari ta hada ido dashi,shiko jifanta yake da wani irin kallo me wuyar fassarawa...
Mikewa ummah tayi "ga bilkisun nan ma bari inyi sallah inzo kamal"
"Toh ummah "ya amsa mata amma ta fice a parlorn,
Sai lokacin ta kallesa da wani irin kallo mai cike da tsananin tsana da bakin ciki fuskarta babu walwala,...."da zaki murmushi da yafi miki domin ummah ta ceceki daga hukuncin da nayi niyyar dauka akanki nazo ne in tabbatar da dalilin da yasa bakya zuwa makaranta kuma bakya daukar wayata sai ummah ta sanar dani cewar baki da lafiya hakan yasa na goge laifin da kikai a cikin zuciyata...saidai ina mai tabbatar miki da nayi kewarki cikin yan kwanakin nan"ya sakar mata murmushin mugunta da k'eta yana ci gaba da jifanta da wanan kallon nasa da tafi tsana a rayuwarta....
Runtse idon ta tayi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa ji take tamkar ta shakesa ya mutu ta huta da bakin cikin da kamal ke shaka mata,har gida ya biyo ta yake sanar mata da yayi kewarta?wanan wace irin masifa ce?ya biyota har gidaj ubanta da maganar banza?.....sanan abin takaici ummah ta daukesa d'anta tamkar ita ta haidesa saboda batasan ashararancin da yake aikatawa da yarta daya tilo bane,batasan shine silar ruguza dik wata tarbiyya da ummah ke ginawa yar tata daya tilo ba....runtse idonta tayi kirjin ta nayi mata zafi hawaye na shirin zubowa a idonta....adduar neman tsari ta shiga jerowa cikin zuciyarta da take mata zugi da radadi....
GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA KO WANAN LITTAFIN NA IZZA TA YA NEMI WADANAN NUMBOBIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*11*
Durkusawa yayi akan gwiwoyinsa ya soma magiya "abbah kaimun rai dan allah kada ka auramun bilkisu wallahi bana sonta banajin d'ugo na soyayyarta a zuciyata kallon nawal da afee nakeyi mata abbah inada wadda nakeso"
Kauda kai abbah yayi ya maida hankalinsa kan news din dare da aka soma,sai kawai ya mike yabar dining area din ya nufi parlor ya nemi waje ya zauna,..kamal kuwa juyawa yayi yana fuskantar momy idonsa tafff da hawaye,"momy kiyimun rai kisamun baki wajen mahaifina ban taba son bilkisu ba inada wadda nayiwa alkawarin aure,saboda ni aka hanata kula kowa momy ki tausayamun kisa baki"
Ajiyar zuciyar momy ta sauke "tohhh kamak niko banga wani aibu akan yarinyar da akace ka aura ba ka furgice kamar an watsa maka tafasasshen ruwa, bilkisu yarinya ce mai hankaki da natsuwa yarinyar da magana bata dameta ba?ko kana tunanin yarinyar da zaka auro tafi bilkisu asali da natsuwa uwa uba addini?"
Girgiza kai yayi jikinsa har rawa yakeyi ya mik'e tsaye a zuciye ya tsaya cikin tsananin fushi abinda be tabayi ba "wallahi momy bazan aure ta ba ainine zan zauna da ita ko?baku bane zaku zauna mun da ita wallahi bazan aureta ba idan an matsamin kuma zaku nemeni ku rasa dan bazan karya alk'awarin da nayiwa Zahra ba"yana gama fadin haka ya wuce parlorn yayi habyar fita,a zabure Momy ta mike cikin tashin hankali ta biyosa da sauri tana kiran sunansa "kamal kamal inayi maka magana kana tafiya?kamal bazaka tsaya ba saina sassaba maka?"
Mikewa abbah yayi cikin fusata "ke hauwau dakata da kiran nan nasa ki rabu dashi tunda bazai tsaya ba yaje zan gani idan shi ya haifeni ko nina haifesa,idan besonta shine zaiyi mana hauka?ya nuna mana shi isasshe ne kenan?"
Rau rau momy tayi da ido kamar zatayi kuka ta karaso parlorn fuskarta cikin damuwa ta dubi abbah "nikam alhaji da anbi yaron nan a hankaki ko?tunda ysnzun baa auren dole balle ga namiji,sanan kamal yaro ne me biyayya da natsuwa tunda kaga yayi hakan to baya sonta ne alhaji ka dub..."tsawa abbah ya daka mata ya d'aga mata hannu "kimun shiru nafada miki idan yanada biyayya yana da kunya ke ba uwarsa bace zai mike tsaye ne yana fada miki magana?ohhh wato farko ya soma roko da lallama zaice bari yayi tsiya to zanga uban da zai tsaya masa kuma wallahi idan na gadama zan daura auren idan ya gadama ya kasheta ko ya gudu ya koma birnin sinn dik tsiyarsa ya taba auren yar alhaji bala dan maliki"yadda abbah ke masifa tunda take bata taba ganin haka ba momy jikinta ne ya kama rawa tana kokarin rukosa tai masa magana ya daka mata uwar tsawa "kyaleni inga gudun ruwansa dan ubansa zai fadamun waye ubansa ko karatun da yayi da abinda yake takama dik waye yayi masa idan ba niba?dik tsiyarsa dani yake takama dani zai bugi kirji yace nine ubansa to ya canja"ya juya ya fice da sauri jikinsa sai rawa yake ko wayarsa be dauka ba ya fice....
Jagwab momy ta zauna ta dafe kai a kujera "innalillahi wa innah ilaihi rajiun shine abinda take ambata da hasbunallahu wa niimal wakheel....wanan wace irin masifa ce ke shirin shigo mun gida?meye wanan alhaji yakeyi yake shirin yi na shiga uku"...nawal da afee kuwa gefen momy suka zo suka zauna cikin tashin hankali,tun tasowarsu basu taba ganin abbansu cikin wanan fushin ba,sanan yaayansu basu taba ganin yayi haka ba,nawal ce ta fashe da kuka tayi hanyar dakinsu,afee ta mara mata baya,mony kuwa mikewa tayi tana kaiwa da komowa a parlorn da waya a hannunta tana faman kiran layin kamal din a kashe ya kashe wayarsa....
***********
"Bilkisu ki kula da kanki kinji?ina nafisar tayi bacci ne?"da sauri ta Shiga waige waigen gefenta bakinta na rawar karyar da zata shararawa ummah,kallon wayar tayi ta maida kunne "kinga ummah tashinta nakeyi ma inbata wayar taki karba saboda tagaji yau din nan gashi tana ramakon azumi saidai da safe zanbaki ita"
"Kada ki tasheta bilkisu sanin halinki yasa na kyaleki har kike kwana a makaranta nasan bazaki zubar mun da mutuncinki ba ki rike kanki kikai budurcinki gidan miji kinji bilkina"wasu hawaye ne masu zafi suke gudu a fuskar bilkisu jin furucin ummanta take taji tsanar kanta ta kara kamata wani bakin ciki ya ziyarceta
"Bilki na bakyaji na ne?"cewar ummah da taji shirun yayi yawa,gyaran murya bilkisu tayi cikin sanyin jiki tace "ummah bacci ke fuzgata Saida safe saina dawo"Bata karasa magana ba ya banko kofar dakin ya shigo,a razanr bilkisu tayi jifa da wayarta ta dirro daga kan gadon ganin yadda ya shigo kamar mahaukacin zaki tana binsa da kallo,shima kallonta yakeyi cike da tsana da k'yama,cikin d'aga murya ya soma magana "billy"a razane ta kallesa hantar cikinta ta duru ruwa "wato kin zagaya kinbi da bayan gida kin sanarwa da mahaifina kinaso ki aureni shiyasa yazomin da maganar aurenki ko?eyeeeeee"ya daga murya a furgice take kallonsa batare da fahimtar abinda yake nufi ba karasowa yayi ya girgiza ta kamar zai bugeta ta ja da baya ta jingina da jikin drawer sa "wato tunda na huta dake kin dandana zuma ta yasa bakiso ki rabu dani kikacewa abbah kina sona ko ya aura miki ni ko?"
Girgiza kai ta shigayi wasu sababbin hawaye suka soma zubowa a idonta,wato ya bata mata rayuwa ya gama da ita yasa yake neman maraba da ita,ya tsaneta saboda yasanta a ya mace,ya tsaneta saboda yasan tsiraicinta yasan sirrinta?ya tsaneta saboda yasan muamalar auratayya da ita ba tare da aure ba shiyasa be kaunar ya aureta gara ya yasar da ita ta jewa mijin aurenta a fanko babu budurci a tattare da ita?babu wani sauran yanci a gidan aurenta matukar bataje da wanan mutuncin na y'a mace ba,dik tsiyar namiji yana ganin mutuncin mace matukar shine ya fara rabata da budurcinta wajen raya sunnah...."innalillahi wa innah ilaihi rajiun...take ambata jiri ne ke dibarta,dishi dishi take ganinsa ko bude idonta batason yi "bilkisu idan kika bari abbah ya aura miki ni wallahi sai kin gwammaci zaman gidan yari da zaman gidana,sai kin gwammaci ki dibi garwashin wuta kisa a bakinki da ki aureni wallahi saina miki azabar da zaki gwammaci kwanciyar kabari da zaman gida na na tsaneki wallahi na tsaneki kuma saina wulakantaki dan bangama wulakantaki ba saina maidaki abar kwatance"a razane take kallonsa cikin tsananin tsoron yadda ya furgice jijiyoyin kansa na goshinsa sun fito sunyi rada rada idonsa ya rufe,a wanan daren zai iya halaka ta....bata gama tunani ba ya janyota ya wurgata kan gado ya danneta,ta soma rera kuka cikin mugunta ya bankare mata hannu yake kusantar ta wani irin mugun azaba ke ziyartarta yadda yake yi da ita tun tana kuka har ta kasa dakyar take jan numfashi sanan ya daga ta yana bin ta da wani irin kallon tsana,ita kanta kallonsa take hawaye na gudu a gefen fuskarta "wanan kadan kika gani kuma indai akan aure na ne zan kulla miki abinda sai kinji ko sunana bakison a ambata....sanan zan kyaleki zan rabu dake na wani lokaci saboda insamu natsuwar raina insamu in auri Zahra yar gidan tarbiyya Zahra wadda tasan darajar dan adam wadda ta fito gidan mutunci wadda zatazomin da budurcinta gida na in bareta a leda ba saura ba,bazan taba auren macen da ta yada mutuncinta ba bazan iyaba nafison wadda zan zama nine wanda zanfara saninta"
Dakyar ta yunkura ta mike idanuwanta a rufe dakyar ta furta "allah ya sakamun allah ya isa tsakanina dakai azzalumi,insha allahu bazaka taba samun abinda kakeso a rayuwa ba kamal yadda ka batamun rayuwa haka zaaiwa naka,yadda ka tsaneni haka na tsaneka nafi kaunar mutuwata dakai kamal saboda kai azzalumi ne,bakajin tsoron allah,bakasan hukuncin zina ba da kasani da baka rinkayi dani ba kamal amma allah yana gani kuma kaci amanar iyayena da suke maka kallon mutumin kirki,kamal na tsaneka"ta karasa maganar da rushewa da kuka.
Daddana waya yake cikin tashin hankali yake kiranta bata dauka...
Da sauri ta janyo wayarta ta mike ta ture kan sa daga kirjinta ya kai mata runguma "kai dakata mijin aure na na kirana kamal ne?"tabe baki saurayin yayi yana bin ta da kallo,jiki na rawa tayi picking call din "assalamu alaikum habeeby"tai muryar tamkar tana bacci
"Zahra inaso inzo gidanku zan iya zuwa?"cikin tashi hankali ta dubi saurayin bakinta na rawa tace "ehh zaka iya zuwa amma ina gidan anty a can zan kwana lafiya dai ko masoyina? wallahi bacci ya fara dauka ta ka kirani na gama karatun kuranina kenan"
Jan nunfashi yayi "ganinan zuwa paradise"
"Owk "tace ta kashe wayar,suna hada ido da saurayin ya fashe da dariya... "Zahra Zahra batdakama wato karatun kur'ani?kingama nishin dadi kina a kara zakice karatu?ni tsaya in dan sha madara kafin yazo"ya kai mata cafka ya kafa baki a kirjinsa,ta daddage ta hankadesa "kada ka tadamun da shaawa infita inkasa sukuni ai nan zamu kwana ka bari yazo ya tafi"girgiza kai saurayin yayi yana dariya ya janyo kwalin sigari ya dau daya ya kunna ta galla mai harara "ka ragemun fa"suka kyalkyale da dariya....
Kallonta kamal yayi kamar ya shaketa yadda take mutsu mutsun azaba shikowutar tsanarta ke ruruwa a zuciyarsa "tashi ki ficemun a gida,dan bazaki kwana a nan ba yau bilkisu,gida zakije dan a yau zan iya illataki kafin safiya zanyi miki fata fata ko in halakaki"
A hankaki ta sako kafarta daga kan gadon ta sakko dakyar ta iya tsaida kafarta saboda azaba ta zura jallabiyarta ta dau gyalenta ko yafawa batayi ba ta dau wayarta dakyar take takawa ta fice daga bedroom din hada hanya kawai takeyi ta dau key din motarta....ta fito adduar allah ya kaita gida lafiya kawai takeyi karfe goma saura minti goma na dare ta kunna mota ta fice.....
********
Wayarsa da makullin motarsa ya dauka yana azamar fita daga gidan ya yaye lalubule ya hada ido dashi,dan ja da baya yayi yana yi masa wani kallo mai cike da rainin wayau...."kai lafiya kazo nan?meya kawoka nan? ubanme kazomin a gida?"
Wucesa yayi batare da yace komi ba ya karasa parlorn ya tsaya tsaye ya ware kafafuwa yana jifan kamal da wani irin kallo.
Kallonsa kamal yake yana mamakin wanan karfin hali ga zuciyarsa da take cike tafff da kunci idonsa sunyi jajir "malam ka shigomin gida ina tambayarka kaki magana"
Murmushi kawai ya sakarwa kamal sanan ya maida fuskarsa ya daure tamkar be taba dariya ba "kamal kenan anci moriyar ganga an yada gauronta ka kyalemu ko nida sauran abokan aiki,to kasani wallahi idan kana takama da kudi da isa da izza da dik wani mukami na duniya cikin minti daya allah zai halaka ka,ka gama kwanciya da yar mutane kuma ka koreta kana kwantawa da ita kamar bunsuru tana ihu kana tilastata aikata abinda batai niyya ba to allah zai saka mata yadda tace,ina cikin gidan nan tun shigowarka tunda idan nakira baka dauka inada bukatar kudi idan ba haka ba dik kulin da mukayi tare da kai inadashi a ajiye zan fasa kwai kuma direct hukuma zan mikawa saidai nida kai dik mu fuskanci hukunci,dan ni yanzun haka bana gudun hukuncinka kaidin azzalumi ne mamugunci "
Taku kadan kamal yayi yana kallonsa yana murmushi fuskarsa Babu alamar tsoro ko furgita bece masa komi ba ya tako ya karaso parlorn ya mika hannunsa kan wata bakar jaka ya zuge jakar saiga kud'i ya ciro ya nufoshi da su yana murmushin mugunta....
********
Bubbuga parlorn gidan billy takeyi tana durkushe kirjinta kamar zai tsage gida biyu saboda ciwo ga kanta dake sarawa zazzabi dik sun hadu mata,...fitowa ummah tayi daga dakinta tana kallon agogo karfe goma da rabi to waye yake buga kofar ko barayi ne ta tambayi kanta cikin tashin hankaki jikinta sai rawa yake ta kasa motsawa...kara bugun kofar yasa ta kara furgita tana kallon agogo,a guje safiya ta fito daga daki tana "munshiga uku barayi"ummah tai mata dakuwa da hannu ta komabda gudu daki cike da tsoro...
Durkushewa bilkisu tayi tana bugun sashin,jin baa bude ba yasa maigadin gidan fitowa ya karaso inda take yana kiran sunan ummah..."hajiya hajiya ki bude bilkisu Babu lafiya"kamar daga sama ummah taji abinda ake fadi nan da nan jikinta ya dau rawa ta shiga neman makulli a parlorn.....
0 comments:
Post a Comment