Runtse idanuwanta tayi kalamansa da yayi amfani dasu yayi nasarar samun raguwar damuwarta kashi goma cikin dari,inama ace zai kasance silar goge bakin cikin dake dankare a zuciyarta?inama ace zai zame mata sanadiyyar farin ciki kamar yadda yake fada?anya zata samu farin ciki kuwa?.... tunawa da tayi da matukar kamal be mutu ba ko be kyaleta ba to bazata taba fita cikin damuwa ba kila shine zaiyi silar ajalinta,koda ace kamak ya bar rayuwarta to tabbas wanan ciwon da yayi gyambo cikin zuciyarta yayi mata rami yake fidda ruwan azaba bazata taba warkewa ba har karshen rayuwarta...ajiyar zuciya ta sauke tasa hannu da sauri ta goge hawayen fuskarta hango amina da tayi tana tahowa buguzum buguzum kamar an jehota ta tsaya akanta tace cikin daga murya.
"Anty wai hajiya tace kizo kibar zaman wajen nan ya isa haka yamma tayi"
"Wai ke amina mahaukaciyar ina ce?har yaushe zakiyi hankali ki iya magana?har yaushe zaki daina wad'anan dabiun irin na yan kauye?dalla dubi yadda kikazo kinamun magana kamar an jefoki"...cike da takaici take duban amina dake tsaye k'ik'am taci uban jan baki kamar zaiyi magana a bakinta ga uwar dammara da taci "dalla dubi kayan jikinki?kullum jiya iyau keda safiya watanku shida a gidan nan amma ko kwalliyar arziki baki iya ba dalla bacemun daga gani kafin inyi kutubal dake ballagaza kawai",hankado baki gaba amina tayi saboda iya cin mutunci bilkisu ta kare mata,ta dubi uwar kwalliyar da taci amma tace bata iya komi ba? mtsww anajin tausayin ta ashe da sauranta dikda batada lafiya sai tayiwa mutum masifa,amina na tafe tana kunkuni bilkisu na biye da ita har cikin gida parlor inda ummah take zaune safiyya na tayata wankin kafa suka shigo.
Turusss bilkisu tayi tsaye tana kallon fuskar safiyya kamar anyi b'arin hoda,sai kawai ta fashe da dariya harda k'yak'yatawa tana nuna safiya tana kallon ummah,ita kuwa ummah mamakin ganin faraar yarta yasa taji wani sanyin dadi na lullubeta rabon da taga hakan a wajen yar tata harta manta, alhamdulillahi shine abinda ta furta a zuciyarta sanan cikin zolaya ta harari bilkisu tace "lafiyanki wai?daga shigowarki zaki hau dariya kamar kinga abun dariya?meye haka ne bilkisu"
D'an tsagaitawa tayi da dariyar sanan ta karaso parlorn ta nemi waje ta zauna "ummah yau yan matan gidanki kwalliya sukeji ashe,ni inacan inawa waccen mara kan fada,ashe zan shigo in tarar da kawarta da nata,to allah ya kyauta nidai nayi iya nawa,sanan gobe idan na dawo makaranta zan samu lokaci in fidda muku kayan da zan baku kyauta saura kuma inga kunyi hauka dashi".
"Toh ai sun gode bilkisu,wai bayan tafiyar bakon ne kika Kuma zauna a can har yamma?inata sa ido inga shigowarki domin inada tambayoyi da zanyi miki su fal cikina dangane da yaron da yazo dikda dai kamalarsa da alkunyarsa ya tabbatar mun daga gidan mutunci ya fito"
Murmushi kawai bilkisu tayi hade da sauke gwauron numfashi da niyyar amsa maganar ummah,wayarta ce tayi karar shigowar tex da sauri ta janyo wayar ganin sunan wanda yayi mata massage din,da sauri ta bude ta soma karantawa kamar haka.... *hi billy baby ganinki ya haddasamun son kasancewa dake,abu daya zaisa yau bazan* *bukaci ki kwana tare dani ba sai dan uzurin rashin lafiya da na tabbatar da ummah* *baza taimun karya ba,amma alamomi sun nuna kin warke tunda kike neman mun taurin* *kai saboda gidanku nazo,well ki shirya sosai domin gobe bayan lectures zan wuce dake gida na can zamu kwana* *kina duty...kitaho da dik abinda kike buk'ata idan ba haka ba wallahi wallahi abinda kike ganin bazanyi ba kamar wasa ne?cikin* *seconds goma zan aikata....*
Gabanta ne ya soma faduwa kirjinta na sauka sauri da sauri nan da nan taji wani abu ya tsaya mata a kahon zuciya, idanuwanta suka kankace.
Ummah kuwa batare da ta kalli inda bilkisu take ba ta cigaba da zancen ta da,"Allah sarki kamal yaron kirki ko ya yaje gida oho?kamal yaro ne mai tsabanin tarbiyya da kunya wanda sam rayuwar duniya da kudin mahaifinsa basu dameshi ba akwai girmama na gaba dashi uwa uba ga alkunya ,ki duba yadda yake gaisheni cikin natsuwa da tarbiyya".
Mik'ewa bilkisu kawai tayi ba tare da tace komi ba ta nufi sashen nata,dakyar take d'aga kafafuwanta saboda bakim cikin da ya lullubeta ,meyasa dik lokacin da zata tsinci kanta cikin nishadi sai wani abu yazo ya lullube farin cikin nata da bakin ciki?...shigarta d'aki keda wuya ta fad'a kan gado ta fashe da kuka kawai,bata da option din da ya wuce tayi kukan,tana tsaka da kukan ne abdul ya kira wayarta da sauri kamar an tsikare ta tadauki wayar tasa hannu ta share hawayenta sanan cikin dasasshiyar muryarta ta soma magana ,"hello ya abdul"jimm kad'an yayi yana sauraron muryar tata har saida ta sake kiran sunansa a karo na biyu sanan ya ansa mata da "lilly ya naji muryarki haka?jikina ya bani kuka kikeyi koh?wai shin bazaki daina kuka ba ke kuwa?ko bakiyi imani da k'addarar da ta fad'a miki bane?ke taki k'addarar kenan allah ya jarabceki da ciwo ya gwada imaninki yaga zakiyi hakuri?umm?yanzun kuka kike fad'amin meyasaki kukan?"
Girgiza kanta tayi tamkar yana ganinta ta shiga goge fuskarta da sauri,a shagwabe tayi maganar "bakomi yaayah...nidai yanzun yaushe zaka dawo?"
"Kina so in dawo ne?"ya jeho Mata tambayar yana sauke murmushi da numfashi cikin wayar.
Shiru tayi kamar baza tace wani abuba saboda ita kanta yadda tayi maganar ma batasan tayi ba samun kanta tayi da yi masa shagwaba "yaayah dama...naga yau da kazo bamuyi wata hira ba sai gaisawa da ummah da kayi ka wuce saboda yanayin da ka tadda ni"
"Toh shikenan,zan duba ingani idan ina da lokaci zanzo insha allahu zanyi miki surprise kanwata"
Gyada masa kai tayi kamar yana ganinta,sukayi sallama ta jefar da wayar kan gado ta dafe kanta da ya dau zafi jijiyoyin kanta tamkar zasu tsinki saboda yadda suke harba mata,wani bako ya shigi rayuwarta amma batajin zata iya sakewa dashi saboda yadda zuciyarta ke gargadinta dashi,sosai take fargaba da faduwar gaba dik lokacin da zaiyi mata magana takan tuna da wata murya da bazata taba mantawa da ita ba wanan murya ita ce takesa dik yadda takeson hira da abdul da yayi mata magana sai taji wani abu ya tokare mata a kirji.....
********
Ta b'angaren abdul kuwa,ana ta kiraye kirayen sallar magriba amma yayi nisa cikin tunaninsa bashida mafita a rayuwarsa, ya fara wani tunani dangane da bilkisu,anya ba bilkisu bace dik lokacin da zai kwanta bacci ko zai keb'e shi kadai sai yaji amon sautin ta lokacin da take yi masa magiyar neman taimako?....girgiza kansa yayi lokaci daya zufa ta shiga karyo masa,gaskiya ba ita bace wanan yarinyar amma ta yaya take rikid'e masa take neman ruguza masa tunaninsa gabaki daya idan Yana wanan calculation din kwakwalwarsa tsayawa take yi cakkkk dan tun haduwarsa da ita yake ji tamkar ya santa a wani waje.....
Yaye labulen dakin mahaifiyarsa tayi "abdul lafiyanka kuwa har yanzun baka tafi masallaci ba gashican an tada sallah?"da sauri ya dubi innah da jajayen idanuwansa da suka cicciko da hawaye
"Ko dai jikin naka ne?meyake damunka haka?kaga yadda kake zufa idanuwanka suka canja kuwa?"
Mikewa yayi tsaye "wallahi innah kaina ne yake ciwo sosai shiyasa,kinsan inacan ina wani tunani naji kiran sallar wallahi,bari in karasa masallacin"be jira cewarta ba ya fice kawai
*********
"Ya kamal wanan kwalliya haka da kaci daddaren nan kodai wajen antyn mu zakaje ne?hmmm sai kamshin turare kakeyi tamkar kayi wanka a kanfanin turare?"
Jan hancin nawal yayi tayi dariya wayarsa na kare a kunnensa cikin murya mai taushi yace "ki kwantar da hankalinki kinji?gani naj zuwa kwana biyu abubuwa ne sukai mun yawa sosai wallahi,amma yau zan cika miki alkawari yanzun haka na fito na shirya ma zan gaida momy ne sai in taho kicewa su muhseen ina gaisuwa gani nan zuwa" ya datse wayar ya dubi nawal da take ta kallonsa tana ta smiling.
"Ke kuma me kike cewa nawal din yaayah kamal?wato kema kin iya muna funci irin na afee koh?"
"Ba haka bane yaayah kawai dai kayi kyau sosai wallahi ga kamshi kana ta zubawa,yanzun dai wacece antyn namu ne?ko ya bilkisu ce?"da sauri ya kalle ta nan da nan ya hade girar sama da ta kasa,ganin haka yasa gaban nawal ya fadi ta sunkuyar da kanta cike da fargabar canjawar yayan nata,..rike bakinta yayida yatsunsa babu walwala a fuskarsa "kada in sakejin kin kira sunan bilkisu a matsayin antyn ku kina ji na koh?"ta gyada masa kai idonta na kawo ruwa kamar zatayi kuka,kallon yadda tayi yasa ya dan saki fuska dan yana mugun son nawal saboda natsuwarta da kamalarta ga addini yarinyar ga kokarin makaranta...kasa yayi da muryarsa "am sorry sweet heart kinji?antyn ku ke kadai zan sanar miki da sunanta"
Washe baki nawal tayi idonta cike da kwallar da ta makale mata "yaayah ya sunan ta kuma a ina take?"
Momy ce ta fito daga kitchen sanye da hijabi da alama sallah ta idar ta leka kitchen din kallon yaran nata takeyi cike da kauna yadda kamal ya sunkuyo da fuskarsa yana yiwa nawal magana kasa kasa cike da kauna ita kuma tana murmushi "toh me ake tattaunawa ne aka makale a parlor aka waremun auta ta ita baayi da ita"
Kafin momy ta karaso kamal ya gargadi nawal da karta fadi abinda suke tattaunawa,cike da gamsuwa ta daga masa kai dukkansu sukasa dariya yace cikin nishadi "oya give me five sweet heart"suka tafa da nawal tana dariya momy ta karaso inda suke ta tsaya tana cigaba da magana "au kyaleni ma kukayi ina tambayarku mai kuke tattaunawa?an kyalemun auta a daki?"
Yar dariya kamal yayi "bakomi fa momy tsakaninmu ne dama yanzun zan shigo in gaidaki saboda zan fita yanzun sai zuwa karfe tara da rabi zan dawo"
"Umhmmm kamal kodai zance zaka?"
"Wani irin zance kuma ummah?ba zance zani ba aboki na ma yana jirana yanzun haka zamu tattauna akan wani harkar company din su abbah shine zanje?"
"Toh a dawo lafiya allah ya tsaremun kai kamal,a dai ji tsoron allah a dik inda ake kaji?ka kula da kanka da mutuncinka da addininka"
"Insha allahu momy"
Da sauri ya duba tex din da yaji shigowarsa wayarsa sunan sama an rubuta...my paradise sai massage din an rubuta _I'm waiting for you_ _paradise_ ❤
wani sanyi yaji a zuciyarsa ya furta"am coming for u" ya fice momy tabi bayansa da kallo tana girgiza kai tana kara jin son d'an nata ns ratsa zuciyarta duban nawal tayi "kira afnan kice ta ajiye wayar nan tazo kuyi tilawar karatun hadda gobe zaku hadda kinsani".
"Toh momy"
Zama momy tayi ta dau remote ta rage karar tv din tana jiran zuwan yaran nata
*********
Dik yadda yaso bacci ya daukesa ya kasa gabansa kara tsananta faduwa yakeyi har wajen karfe sha biyu na dare tabbas bilkisu itace wanan yarinyar da yake hasaso wa....dafe kansa yayi hawaye na zuba a idanuwansa innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...shine abinda yake furtaww dikda bai gama tabbatar da hasashen da yake yi ba amma zaisan mafita.....
*********
Sauri sauri kamal yakeyi ya gama shirinsa tsaf domin tafiya makaranta saura kad'an ya makara dik wani abu da yake buk'ata ya dauka ya dauki jakar laptop dinsa da wasu kayansa kala daya ya saka cikin jakarsa a parlor ya tarar da momy dasu nawal suna breakfast dik sunyi shirin makaranta
"Ya dai kamal bazakayi breakfast bane?gashi yau naga harda jaka ka dauka?"
"Ehh momy am already late yanzun haka inada class da zan gabatar ma da yara harda test dama zance miki idan kinjini shiru zan kwana a wajen shaheed dan akwai ayyuka akaina sosai dan ko questions na exams banyi setting ba kuma saura 5 days a soma exams yanzun haka zan gabatar da ayyuka na"
"Toh allah ya tsare a rike kai dai kamal kai musulmi ne banda bin yan mata da nufin aikata ashha nasan waye yarona"
"Bye sai nadawo"ya fice...
Driving yakeyi hankalinsa kwance wayarsa tai kara ya duba number da ake kiransa ce saida yayi misscall biyu a na uku ya dauka ya daka masa tsawa da "wai kai mahaukacin ina ne da zaka rinka kirana babu rana babu dare?idan kudi kake bukata zan baka ka daina damuna mana?kaidai kasan nafi karfin daga naira daya zuwa million dari koh?to be care ful"
"Ka bani mamaki amma nima zan baka nawa mamakin domin inhar baka yarda ka hadu dani ba a yau to kaima ka shirya kalaman da zaka fuskanci iyalan gidanku dana gidan dan maliki dashi na fada maka kuma inada bukatar kudi da bukatar magana dakai"
K'arar over taken da akai masa ta gaban motarsa yasa ya saki wayar da sauri ya rike sitiyarin motar da kyau yabi farar motar da kallo billy dan maliki aka rubuta a baya....hannu yasa ya shafe kansa hade da cije lebensa yana sauke numfashi ya furta a hankali "billy......"hmmmm ya sauke lallausan murmushi da har hakoransa suka fito.....zaki gane kuranki yau,yaja motar a guje yabi bayanta....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN NAIRA DARI BIYU YA NEMI WADANAN NUMBERS DIN 08165177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻🔥*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*10*
Kusan a tare motocinsu ke tsere a hanya minti minti yakan dubi bayan motarta ya bugi sitiyarin motarsa,yaja giyar motar a guje ya kawo daidai inda take daidai nan kuma traffic light ta tsaidasu hankalinta kwance,kamar yadda ta saba tana driving takan makala glass dinta baki a fuskarta Wanda ta dan kwana biyu bata sashi ba,yau kam babu laifi fuskar nan tayi fayau da ita tayi wani sihirtaccen kyau ga fari da ta kara dikda ta nade gyale a wuyanta be hana kwantaccen gashin gaban gosinta fitowa ba hancinta zir tamkar ya tabo bakinta.....koriyar danja ce ta nuna alama wanda hakan yasa kamal take motarsa yasha gabanta,da badan ta rike kan motar da kyau ba da babu abinda zai hana ta yin accident gaba daya hankalinta na wani waje,furzar da iska tayi mai zafi daga bankinta sanan ta cigaba da driving hankalinta kwance tasan shine haka take biye dashi har manyan kofofin shiga jamiah....yadda ya take mota ya shiga a guje haka ta take itama....
Waje daban daban sukai parking sauri sauri ys fito daga motarsa tafe yake wayarsa na makale a kunnensa yana amsa waya yana murmushi da alama yana jin dadin call din da yakeyi dik saurinsa be wuce ya rigata shiga hall dinba da yayi combining class din nasu ajujuwa biyu.
"Pheey dubi k'awarki billy ta shigo kalli wata arniyar abaya da ta zubi daga ganinta mai tsada ce"wata matashiyar budurwa dake gefe take wa nafisa nuni da bilkisu,ita kuwa batare da ta d'ago kaiba tace "amma kedai kinada gulma idan ba gulma ba tayaya zakice bilkisu ta sako doguwar riga arniya maitsada bayan kinsan wanka irin na billy"mtsww ta dan ja tsaki.
Da'fa kafadar nafisa billy tayi kamshin turaren nata yasa pheey saurin dagowa fuskarta dauke da k'ayataccen murmushi "ohhh my god oyoyo billy i miss u"take tai tsit ganin shigowar kamal hall din ji kake tsit tamkar babu wata halitta a ciki nan da nan kowa ya shiga taitayinsa,da sauri pheey ta matsawa billy waje ta zauna gefenta ta zare glass din idonta ta maida hankali.
"Kai...gayen nan akwai wanka dubi yadda kayan nan sukai matukar karbar jikinsa na lura da yana son blue colour"
"Ba ke kadai ba wallahi da zai aureni koda kullum zai rinkamum shegen duka ne wallahi ina sonsa,musamman yadda yake komi nasa ga addini gashi be kula mata ko kada"
D'an tsaki billy tayi ta juyo ga yan matan da suke tattaunawa kasa kasa "dalla kuyi mana shiru mu saurari lectures idan kuna sonsa ku bari idan angama lectures kuje ku kai request"
Wata uwar harara suka jefe ta dashi suka maida kai suna sauraren yadda yake watsa turanci a lectures din daya dauki awa d'aya da rabi yana gabatarwa sanan bayan ya gama ya dubi mutanen dake cikin hall din,daga nesa yake hangota ta cikin bakin gilashinsa yayi murmushin k'eta ya dan daga murya ya kira sunanta "bilkisu bala dan maliki"....dammm gabanta ya yanke ya fad'i zuciyarta ta shiga bugawa jikinta ya hau rawa amma ganin kowa ya kaso kunne yaga dramar da zasu kwasa sai ta dake ta had'a rai batare da ta motsa ba,nan da nan class ya dauki side talks.
A kasashe yayi magana 'bilkisu bala dan maliki stand up"....wani mawiyacin miyau ta hadiye sanan ta mik'e tsaye kanta a kasa,bece komi ba ya kalli class yace "we are going to have our C.A test now hope u are all ready"
"Yes sir"
"Come out bilkisu and seat here"yayi poiting wani seat babu kowa ,murmushi tayi domin ta fahimci inda ya dosa bayan ya manta cewar ya sanar mata da zaiyi test yau kuma tasamu ta dan bincika handout dinsa da asuba bayan tayi sallah,babu faduwar gaba ko tsoro ta fito, yabi bayanta da kallo,dikda cikin glass ne amma wasy daga cikin dalibai suka fara nunawa juna suna taba juna harta zauna sanan ya juya ya soma karanto question na test din.
********
Zaune yake a office dinsa yana famar aiki akan laptop dinsa,ta turo k'ofar office din idonta sanye da glass din dazun,ta maida k'ofar ta rufe sanan ta shigo bakinta dauke da sallama,zuciyarta babu dadi sanan cike take da fargabar abinda zai sanar mata,tsaye tayi ba tare da tace komi ba shima bece mata komi ba har saida ta gaji cikin sanyin murya tace "gani sir"...wanan murmushi nasa yayi yana cigaba da danna laptop dinsa yace "ina fatan kin shiryo da shirin zuwa guest house dina ko?ai na sanar miki da maganar inason kebewa dake nasan kinyi missing dina ko?"sai lokacin ya dago ido ya kashe mata ido yana lashe Baki.
Zare glass din idonta tayi tanayi masa wani kallo mai cike da ban tausayi "haba kamal haba kamal,dalilin da yasa na shareka kenan ko ka kirani a waya bana daukar wayarka saboda gudun kada ka cigaba da sani aikata alfasha kamal,na sanar dakai cewar inhar zaka aureni wallahi tallahi zan amince in aureka in biya maka bukatar ka ta hanyar raya sunnar annabi amma bata hanyar ba"karasa maganar tayi hade da tsugunnawa gaban table dinsa nan da nan idonta sukai jajir savoda tashin hankali da tsananin bakin ciki da ya ziyarceta take "kamal ka tausayawa rayuwa ta ka kyaleni haka ka daina bibiyata da sharri ka daina kusantata haka saboda bamuyi aure ba babu komi a tsakaninmu wanan abun da mukeyi zina ce kuma allah zai mana hukunci saboda hakan,ka tausayamin ka canjani daga matsayin da ka bani gara in koma matarka ta sunna"hawaye suka gangaro mata.
Yar dariya yayi "billy billy billy manya ashe kin iya waazi kinsan wadanan kalaman,to nima ina rokonki da ki adana kalamanki domin babu muhallinsu a wajena aurenki kuwa ko a kafa aka dauramun ke saina kwance wallahi domin bakida muhalli a zuciyata ke ba irin matan da nakeso in aura bane?kina jiko karma insakejin kin furtamun kalmar aure idan ba haka ba zanbaki mamaki,sanan ina mai sanar miki idan ma baki shirya ba ki shirya kije gida tunda bakida sauran abunyi karfe hudu na yamma dik abinda kikeyi kada ki bari inkiraki a waya kinji nafada miki"...wasu hawaye ne masu zafi suke kwarara a idanuwanta,tana nan durkushe ya nuna mata hanyar kofa "ficemun a office kafin wani ya shigo ya sameni ya maidani mutumin banza"a kausashe yayi maganar hakan yasa ta razana ta goge fuskarta da tai jajir da sauri ta fice a office din nasa ta rufo masa kofa,komawa yayi ya zauna ya jingina yana latsa waya tex din my paradise ya shigo wayarsa ya sauke lallausan murmushi....
Bilkisu kuwa bata tsaya ko ina ba sai inda tayi parking motarta ta shiga ta tada motar a guje ta fice makaranta....
"Kinga ba billyn da kike jira bace ta wuce gata can ta barki?"da sauri pheey tabi motar da kallo amma inaaa ta fice....
*********
Gefen titi tayi parking motar saboda yadda jikinta yake rawa ga zazzabi da yayi mugun kama ta mai zafin gaske zuciyarta nayi mata tsananin suya ga hadari sosai da garin yayi bakinkirin tun safe dama haka aka tashi,kwankwasa glass din motar yasa tai saurin dago kanta tana hangen me bugawa,murtsika idonta tayi da sauri ta bude murfin motar,ya sakar mata lallausan murmushi "kanwata a mashin nake naga motarki gefen titi kinyi parking shine na sauka nace ko lafiya kikai parking gefen hanya?"batasan lokacin da ta sakar masa murmushi ba hade da ajiyar zuciya "ya Abdul shigo mana"shigowa yayi ya rufo kofar motar sanan ya juya yana kallonta,itama shi take kallo kansa babu hula sanye da kananan kaya gashin kansa a kwance,shagala tayi da kallonsa,ganin haka shima yayi murmushi"wanan kallo haka?kodai kinga yau nayi miki kama da dan bola ne?wallahi tashina kenan na koma bacci bayan nayi breakfast inajin alamun ciwon nan nawa kamar zai motsa ne"ya karasa maganar cikin wata iriyar murya,sosai taji wani tausayin kansu ya kamata haka kawai taji tadan samu natsuwa a tare da ita haduwarta dashi cikin minti goma taji ta manta damuwar dake neman haddasa mata bakin ciki.
"Ya abdul idan zaka iya kayi driving dinmu in kaika gida sai in wunce daga nan"
"Toh ai daga nan babu nisa da gidanmu dan daga bayan can na hayo mashin muje kiga ummah na da kannena"gyada masa kai tayi ta fito ta koma side din me zaman banza shima ya koma mazaunin driver,kallonsa sosai take yadda yake driving din tana jin wani abu na ratsa zuciyarta haka kawai takejin yana burgeta saidai muryarsa dake barazanar tarwatsa mata tunani,ta ajiye wanan tunanin a rai don haka kawai takeji a jikinta ba wancen azzalumin take tunani bane,murmushi tayi da suka karya kwanar unguwar "ya abdul ka iya driving amma kuma baka da mota ya akai hakan"murmushi ya sauke mata "abun allah kenan budurwa da jika"zaro ido tayi tana dariya sosai kalmar daya fada har sukai parking a kofar wani gida mai feshi da karafuna sanan ya dubeta "amma kinsan dole mushiga ki gaida innah?"shiru tayi tana kallonsa yadda pink lips dinsa ke motsawa shaawa suke bata"wai lil sis lafiyanki kuwa?"sosai ya bata kunya ta rufe fuskarta tana dariya,shima dariyar yakeyi yana kallon kwantaccen gashin gaban goshinta da jallabiyar dake jikinta mai stones golden "to mune lil sis kinji?"ta bude motar ta fito dikda jikinta babu kwari haka take takawa zuwa cikin gidan nasu......
********
Kurbar lemu yayi ya ajiye glass cup ya dubi matashiyar budurwar dake gabansa tana sanye da jan leshi yayi matukar dacewa da kalar fatarta chocolate mai sheki da daukar ido...kallon da yakeyi mata yasa ta saki murmushi da har wushiryarta ta bayyana "my paradise na dauka ai bazakazo ba da nai maka kiran gaggawa"ta dan hararesa.
"Wane ni?nina isa in ki amsa kiran sarauniyata matata uwar yarana insha allahu?wanan ai dolena ranki ya dade kinsan yadda nakejinki a zuciyata kuwa?"
Cike da kunya ta girgiza kai tana sadda kanta kasa,wani irin son kamal take kamar ranta bazata iya rasashi ba,cigaba yayi da magana "ina jin sonki cikin jinin jikina,kullum Godewa allah nakeyi da na sami matar aure kamila yar mutunci yar gidan mutunci wadda zataiwa yarana tarbiyya ta kwarai kan turbar da allah yace kinga ko alhamdulillahi dole inji dake babyna"rufe fuska tayi cike da farin ciki bakinta ya kasa rufuwa....kiraye kurayen sallar laasar aka somayi ya kalli agogo yaga lokacin da zasu hadu da billy ya kusa dan haka ya dube ta kadan "idan princess ta amince to zan tafi yanzun saboda inada departmental meeting da zamuyi da HOD kinji?dama ganina kikeso ko?to ai gani nazo"
Sunkuyar dakai tayi tana wasa da gyalenta,ya yunkura ya mike itama ta mike ta soma taka masa zuwa wajen motarsa inda yayi parking ya kunna motar ta Soma daga masa hannu yaja ya karasa wajen gate din gidansu tana tsaye,wani irin sanyi takeji a zuciyarta idan tana tare da kamal,bazata taba hakura da sonsa ba yadda yake sonta saboda d'abiunta na b'addakama da takeyi bazata bari damar ta wuce mata ba dik samarinta da take dasu babu wanda yakai kamal kyau da aji uwa iba ga kudi,dikda kudinsa be dameta ba domin ita dinma ubanta kowa yasanshi a garin nan.....tana nan tsaye tana tunani tayi murmushi tunawa da tayi d'an rigimarta yana can cikin gida anty binafa ta zaunar dashi ta juya da sauri ta shige gida aguje....
**********
Driving yake hankalinsa kwance yana jin nishadi a zuciyarsa na ganin zahra da yayi...a koda yaushe soyayyarta na kara shiga zucuyarsa saboda natsuwarta da kamun kanta uwa uba addini da take dashi ga alkunya,kiran wayar abbah ce ta katse sa daga duniyar tunanin da ya lula,da sauri yayi picking calk din cike da ladabi yayi sallama "Kamal kana ina ne haka?"
"Abbah ina hanyar zuwa school ne inada meeting akwai wani abune?"cikin ladabi da sadda murya yake magana.
"Ehh ba wani abubane na tada hankali bari daddare kazo muyi maganar insha allahu koh?dafe kai kamal yayi sam beson komawa gidan dan yanason kasancewa da bilkisu yau din nan ya sauke bukatarsa..."toh abbah zanzo dikda akwai aikin da naso kwana yi amma babu matsala idan nazo muka tattauna sai inkoma"
"Toh ba laifi"cewar abbah sukai sallama ya kashe wayar,wani huci yayi ya dialing number ta...
*******
Sosai bilkisu taji wani nishadi kasancewa a gidansu abdul da mahaifiyarsa suna ta hira tare harda zainab kanwarsa,taci shinkafa da wake da latas,tayi sallahr laasar tayi shirin fitowa taga call dinsa,dan tsaki tayi kawai zuciyarta babu dadi ta dauki wayar ta kara a kunnenta
"Kina ina?"
Shiru tayi kamar bazata ce wani abuba a sanyaye tace "on my way"ta kashe wayar nan da nan fuskarta ta sauya,abdul kansa beji dadi ba haka taiwa innah sallama zainab ta biyosu har kofar gida dan rakiya,ta shiga motar sosai sanan ta zuge jaka ta ciro kudi masu yawa ta mikawa zainab tace gashi a sai kayan kwallita,sosai zainab ke godiya ta karba ta shige gida ta barsu.
"Fuskarki babu annuri akwai wani abu ne?"
Girgiza kai tayi ta kwantar da kai "babu komi yaayah please take care of your self gobe zanzo muje asibiti tare tunda gobene check up dinmu"
Murnushi yayi badan ya yarda ba,domin yana hango tashin hankali da damuwa a kwayar idonta,sosai yakejin kansa cikin wani yanayi badan yaso ba sukai sallama taja motar,yana tsaye har ta bace,tausayi take bashi sosai ya zaiyi da abinda yakeji dangane da ita?gashi tafi karfinsa?babban tashin hankalinsa shine yadda yakeji tamkar yasan ta a wani waje....yakai hannu ya yamutsa sumar kansa ya shige gida zucuyarsa cunkushe da begenta kamar kada ta tafi tanada saurin sabo da shiga rai...
**********
Sanye yake da gajeran wando ta turo kofar parlorn ta shigo,kallonta yakeyi daga sama har kasa sanan ya kauda kansa gefe ya cigaba da kallon tv, karasowa tayi ta zauna a d'arare kanta a sunkuye,"sai yanzun kika gadamar zuwa?"
Ta dago idonta cike da hawaye taffff "ya kamal"
"Dakata karkicemin komi matso nan domin a yunwace nake kuma ina fatan kinzo da niyyar kwana don zan fita indawo zanje wajen abbah na amma zandawo tare zamu kwana"
Hannu yasa gefen kujera ya ballo maganin da ya saba bata,tana ganin haka ta fashe da kuka,mika mata yayi jikinta na rawa ta karba yayi mata nuni da ruwa ya maida kansa gefe ta dauka ta koma ta zauna,fakon idonsa tayi ta jefa maganin gefe tayi kamar ta sha ta ajiye gorar suwan din...
Tana kallo ya dauki waya Yana waya da budurwarsa zahra yana sheda mata ya koma gida lafiya yanzun yana wani abu zai kirata yayi mata sallama,ya mike bayan ya ajiye wayar ya karasa inda take zaune fuskarsa dauke da faraa.
Dago ta yayi yasa harshensa yana lasar fuskarta da busasshen hawayenta hannunsa rike da habarta,kamar jira yake yazo bakinta ya cafke ya soma tsotsa cikin wani irin salo mai cike da mugunta haka yake tsotsar lips dinta da karfinsa,mutsu mutsu ta shigayi saboda zafin dake ratsata a labbannta,ta soma hawaye....haka ya zame gyalen data yane kai dashi ya soma yamutsa gashinta yana yawo da harshensa a bakinta,dan sakinta yayi idonsa sunyi jajir yaga yadda take a furgice ya d'aga Mata gira "are u ready?kinfara hawa network ko? gashi nan idonki har sunyi jajir... Dadina dake hawa network da wuri"hawaye suka zubo mata yasa yatsansa yana wasa da hawayenta ya sunkuyo wuyanta yana tsotsa yana mata tafiyar tsutsa a jiki....cakkk ya dauketa yana tafiya zuwa bedroom dinsa bakinsa na kan nata yana tsotsewa....
*******
Kuka sosai takeyi a kan gado ya fito daure da towel yana tsane gashin kansa,tsanarsa ce ta darsu cikin zuciyarta tai masauki fiye da ko yaushe kallonsa takeyi zuciyarta nayi mata kuna idonta sunyi jajir kamar gauta baka ganin farin idonta sai bakin,motsin kirki bata iyawa saboda yadda kasanta keyi mata radadi da azaba...wayarsa dake kan side drawer ta cigaba da ringing,ta dan saci kallon number da ake kiran nasa tun dazun baya dagawa....aka kara kira takai hannu zata dauka ta mika masa ya daka mata tsawa "uban wa ya baki damar kai kazamin hannunki kan wayata?"tai maza ta girgiza kai,ita kuwa number da akeyi masa kiran takeso ta kalla domin tasan kallo daya zatai ta haddace sai tasan meyasa beson daukar wayar dikda dazun ya dauka yana tsaka da sex da ita ya kashe
Karasowa yayi ya dau wayar "kai....wai mena fada maka?"batasan me akace ba daga can bangaren taga ya saki murmushi
"Nidin?to ina jira,amma kasan nidin ba matsoraci bane ko?saidai ina gargadi ka da fadawa halaka domin tsaf zansa a batar dakai idan kai yunkurin abinda kakeson aikatawa"...dibbb ya kashe wayar gaba daya ya jefar da wayar gefe ya karasa gaban mirror ya soma shafa mai da turarukan sa "ki tashi kiyi wanka kijirani zanje gida indawo"ya bata umarni cikin isa....
Gabanta ne ya fadi jin abinda yace,ummahnta ta fado mata allah sarki ummah tana can tana jiranta gashi wanan azzalumin yana nan yana zaluntarta kai allah ya isa tsakaninta da kamal,memakon tayi magana kuka tasa masa beko kalleta ba ya fice daga bedroom din ya dauki wayarsa yayi gaba.... dakyar ta janyo jiki ta sauko ta fada toilet tayi wanka tayo alwala ta fito ta maida kaya ta dau wayarta ta kira ummanta ta shaida mata tana gidan momy hafsa can zata kwana kanwar mahaifinta tunda tasan ba tambayarta zatayi ba....
*********
Tare suka ci abinci da abbahnsa da kannansa yanayi yana tsokanar afnan dake famar shagwaba
"Kamal"abbah ya kira sunansa
"Naam abbah"
Kasan dalilin kiran naka da nayi?"sounding serious abbah ke maganar,hakan yasa gaban kamal yadan fadi
"Ah ah"ya girgiza kai kansa a kasa,wajen yayi shiru tamkar ba mutane
"Munyi magana da mahaifiyarka munga dacewar tunda baka da matar aure,maana baka da wadda ka tsaida da nufin aure mun yanke hukuncin hada zumunci da iyalin bala dan maliki dikda baya raye,amma inada iko da iyalinsa inada damar da zan yanke hukunci akan iyalinsa kuma subi,hakan yasa nayi maka shaawar auren bilkisu".....cakkkk network din kan kamal ya tsaya besan lokacin da ya dago idonsa da sauri yake bin iyayensa da kallo ba cike da tashin hankali....
Kallonsa momy keyi cikin faraa"alhamdulillahi aiko kamalu kayi mata domin bilkisu ta hada komi kyau asali da kuma tarbiyya"
"Yeeehhhh "afnan ta mike tana farin ciki.
Juwa ce ke neman dibansa dikda a zaune yake wanda ya tabbatar da a tsaye yake faduwa zaiyi,cikin tashin hankaki ya soma magana muryarsa na rawa "abbah bilkisu fa?"
"Ita fa kamal menene aibunta?ko tana da wani aibu ne yasa kai wanan furgitar kamar anfada maka mutuwa?"
Girgiza kai ya shigayi "abbah kaimun rai wallahi inada wadda zan aura inada Zahra ita nakeso ita zan aura abbah munyi alkawarin aure da ita,har abbanta yasan da zama na bata kula kowa saini,kamar yadda kuke ikirarin bilkisu nada tarbiyya haka zahra take inasonta abbah,wallahi bana son bilkisu banajin sonta ko kada,bazan iya zaman aure da ita ba bazan iya ba abbah kaimun rai".....
Durkusawa yayi kan gwiwoyinsa cikin seconds saiga hawaye a idon kamal,zaro ido momy tayi sanan ta subi abbah abinda basu taba gani ba hawaye a idon kamal....
*WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA* *AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA* *AKAN NAIRA DARI BIYU KACAL YA NEMI* *WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903*
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*12*
Yana karasa parking ya kira wayar zahra ta fito sanye da dogon hijabi har kasa tana waige waige,daga nesa ta hango motarsa ta karaso cikin sauri,kallo daya tai masa ta fahimci yana cikin wani haki, gabanta ne yadan fad'i amma sai tai masa sallama,memakon ya amsa mata,sai kawai ya bude mata gaban motar ganin haka tasan abinda yake nufi ta shiga ta dan zauna sanan cikin sarkewar murya ta Soma magana"lafiya kuwa paradise na ganka cikin daren nan?yanzun haka ummah tambayana tayi waye yazo zan fita da wanan daren,shine na sanar mata da kaine kakeson ganina,ina fatan dai lafiya kake mijina dikda naga sabanin hakan a fuskarka"cike da natsuwa take maganar cikin tattausan lafazi mai kwantar da hankaki,..hakan yasa kamal sauke ajiyar zuciya,jin muryar zahra kadai ya saukar masa da 70%na halin damuwar da yake ciki,wani irin shauki na soyayyarta ke kara dibarsa,dik wanda ya mallaki zahra a matsayin matar aure hakika yasamu aljannarsa ta duniya saidai fatan samun ta lahira....wani irin kallo yakeyi mata mai nuna tsantsar do da kauna ,itama kallobsa tayi ganin ya shagaltu da kallonta yasa ta sunkuyar da kai ta cigaba da magana "meyake faruwa mijina?ko akwai wani abu ne da zaka boyemun a matsayina na matar aurenka?umm mijina farin cikina ganin ka kadai Yana warkar dani daga dik wata damuwa ko bakin ciki ina fatan in kasance matarka a nan duniya da gidan aljannah,bazan iya rayuwa da ko wani namiji ba mijina matukar kace bazaka aureni ba bazan samu sukuni ba har kila saina bakunci lahira"
Davsauri ya dago Yana kallonta,me zai hango a idanuwanta?wasu hawaye ne makale cikin ramun idonta yana iya hango zallar soyayyarsa a kwayar idonta,abinda yayi niyyar sanar mata yaji ya kasa,ya tabbatar idan ya sanar mata bazata iya bacci ba yau balle ga furucin da tayi?idan ta mutu ya auri wa?ya tambayi kansa.
Lallausan murmushi ya sakar mata "zahra shiyasa koda yaushe nake kiranki da paradise domin kedin aljannar duniya ce ga namijin daya mallakeki zahta ina sonki hakan yasa bacci ya kauracewa idona nazo ganin sanyin idaniyata"lumshe ido tayi tana kallonsa badan ta yarda da kalamansa ba saidai bataso tai masa musu ya gano lagwanta ..
Dan turo baki tayi cikin sigar shagwaba "shine zaa tasheni a harci?"ta kashe masa ido,wani abu yaji ya tsarga masa a cikin jikinsa yadda tai masa maganar cikin shagwabar hakan yasa ya shagaltu da kallonta har saidavta hura masa iska a ido..."paradise tunda ka ganni kazo ka wuce gida kawai kaga dare yayi inaso in kwanta saboda zan tashi sallar dare kashe mata ido yayi "kiyi mana addua banaso in rasa ki"da sauri ta kallesa alamar kamar ta gano wani abu hakan yasa ya kauda kai ya basar ya kunna motarsa suka soma sallama ta fice,saida taga fitarsa sanan ta sauke ajiyar zuciya ta kalli kanta da hijabin dake jikinta ta saki wani irin murmushi a zuciyarta kuwa cewa take "amma dai kamal kamar wawa ya kasa gane babu kaya a jikinta tsirara take saboda batason sa kaya ta Kara cirewa....juyawa tayi da sauri ta nufi cikin gida...
A parkor ta tarar dashi yana busa sigari yana furzarwa ga wani film dayasa anata zuba iskanci ta shigo,da sauri ta zare hijabin jikinta ta karasa kareshi ya bude hannunsa ta fada kirjinsa tana dariya k'asa k'asa tana sunnar da kanta Yana shinshina wuyata Yana yawo da hannunsa a jikinta dago fuskarta yayi "zahrah zahrah zahra batda kama wato kinje kinyi masa wasan kwaikwayo kin dawo ko?"murnushi tayi masa ta kaiwa sajen fuskarsa shafa "wasu mazan saida haka musamman irinsu kamal masu tarbiyya"hannu yasa yana wasa da breast dinta "ya zamu koma aiki ne?"gyada masa kai tayi hade da daga. Gira "mezai hana kasan bana gajiya da kai"hada ido sukayi ya kyalkyale da dariya....
*********
Hawaye kawai kebin fuskar ummah bayan ta ballo magani ta bawa bilkisu ta sha,ta dan rungumota jikinta tana kallon yartata "amma bilkisu abin da mamaki yaushe yaushe mukai waya dake na jiki lafiya lau sai gaki kindawo kina tafiya dakyar kodai akwai wani abu daya sameki ne bilkisu?yanzun haka da kika mike zuwa wanka a ina kallon yadda kike tafiya kifadamun gaskiya"
Murmushi tayiwa ummah cike da faduwar gaba sanin inda maganar ummah ta nufa yasa ta kauda tunaninta da "ummah na kindaisan inada ciwon kafa ko?sanan kinsan yadda nakeyi idan inajin zazzabi har kasa tsayuwa nakeyi yanzun haka jiri jiri nake gani ummah,ciwona ne inaga yake neman tashi "
"To ai lafiya lau na jiki bilkisu dazun"
"Muna gama waya dake naje na watsa ruwan sanyi shine fa ya tasomin da zazzabin nan kuma dama tun rana inajin alamun ciwo na, yanzun bacci nakeji ummah na"
Cike da gamsuwa ummah ta kwantar da kan bilkisu akan katifa sanan tace "tou ayi bacci lafiya bari in kashe miki wutar dakin ko?"gyada mata kai bilkisu tayi tana bin ummahn nata da kallo tanajin radadin kalaman kamal a gareta saidai tanaji a jikinta akwai ranar ramuwa...dikda bata da tabbacin akwai ranar da zata rama din..kashe mata wuta ummah tayi ta juyo tana hangenta cikin duhu ta bude kofa ta fita ta rufo kofar...
Ajiyar zuciya bilkisu ta sauke fuskarta dauke da murnushi mai ciwo ta dago wayarta ta kalli agogo karfe biyu da minti goma na dare ta maida kanta a pilow tasa hannu ta kunna dumm light nan da nan wutar tasa dakin yayi blue....tunani takeyi tana tambayar kanta ko yayi bacci oho?haka kawai takejin wani abu dangane da ya abdul tex ta rubuta masa " *fatan kana lafiya yayaahna just missing d fun we shared yesterday afternoon...hmmmm ka shirya gobe tare zamuje asibiti ganin likita"*......tayi masa sending ta kifa wayat ta soma tunani tana lumshe ido bayan kamar minti goma da mata massage din taji karar shigowar tex da sauri ta daga wayar ta duba " *owk habeebty kanwata ki kula da kanki make sure u sleep right now ok?"*....kwantar da kanta tayi tana jin bugun zuciyarta na karuwa ta dayan bangaren kuwa kalaman kamal suke yawo a dodon kunnuwanta,tasa hannu ta toshe kunnenta tanajin wani irin radadi hawaye na bin gefen fuskarta....
**********
*Washe gari*
Da wuri kamal ya shigo hidansu fuskarsa daure tamkar be taba dariya ba har wata yar rama yayi saboda damuwar dake cunkushe a zuciyarsa....kasantuwar saturday ne dik yaran gidan suna gida haka abbah yana parlorn sanye da jallabiya me ruwan kasa kansa babu hula jefi jefin furfura ne suka fara fito masa idonsa sanye da bakin glass kamal yayi sallama ya shigo,kallo daya abbah yayi masa ya kauda kansa ya cigaba da dubawa afnan assignment momy kuwa dake kokarin mikewa ganinsa yasa ta zauna ta kasa daina kallon dan nata,sosai tausayinsa yake kamata da abbah zaiji nata tunda kamak beso a fasa.
Tsugunnawa yayi kamar yadda ya saba"abbah ina kwana?antashi lafiya"
"Lafiya lau na dauka ka tafi kenan ka shiga duniya bazaka dawo ba"be cewa abbah komi ba ya sunkuyar da kansa shiru sanan yadan dago ya dubi momy
"Ina kwana momy"
"Lafiya lau kamal kana lafiya?".
"Lafiya lau"ya amsa muryarsa a dashe ,kallon nawal yayi itama kallonsa takeyi idonta sun ciko da hawaye sam batason ganin yayan nata cikin wanan hali,ganin kwalla a idon nawal yasa ya girgiza mata kai alamar kada tayi kuka,ta gyada masa kai ya kashe mata ido da murmushin gefen baki, itama murmushi ne ya subuce mata najin dadi...afeee kuwa kai mata duka yayi a kai ta goce tana yar dariya "yaayah manta dan kwalin nayi"
Mikewa yayi "ashe kinsan menake nufi"yana gama magana yasa kai zai fita momy ta dakatar dashi da ce masa "ga abincin karyawarka nan a dining"
Girgiza kai yayi daga inda yake beko kalli uwar ba "banaci "yasa kai ya fice tabi bayansa da kallo....
Ajiya zuciya momy ta sauke "Abba "ta kira sunansa,wata harara ya watsa mata yasa tayi shiru "idan maganar yaron nan zakimun kima kyaleni dan bazan saurareki ba dan bake bace bakinsa da zaki ci masa albasa zan nuna masa tawa kangarewar da kafewa",...sanin halin abbah yasa ta kama bakinta ta tsuke bata sake cewa komi ba saidai tunanin mafitawa wanan lamarin kawai takeyi...
*********
Bayan ya fito wanka yana tsane kai da towel yaga kiran waya ya shigo yana dubawa yaga zahra ce,besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ya danna picking ya kara a kunnensa "ranki ya dade farin cikin rayuwar kamal aljannar duniyarsa"
Yar dariyar jin dadi tayi "ka tashi lafiya?"
"Lafiya lau paradise,yanzun nake shirin kiranki sai gashi kin kirani"
"Au haba sweet"
"Yess ki shirya ki roki abbah ya barki zamu fita anjima muje park mu dan sha ice cream daga nan ki rakani supermarket"
Wani dadi ne ya lullube zahra na zata fita da kamal,wanan wata dama ce tazo mata na nunawa kawayenta mijinta da take mafarkin aura na kece saa,dan haka dan saisaita kanta tayi "yauwa paradise dama ko na tambayi ummah zanje gaida hafsat ilham kawata kaga bata da lafiya"
"Tou shikenan daganan sai muyi siyayya mu biya mu ganta koh?"
"Toh"
"Yauwa paradise ki shiraya da kyau fa kiyi kwalliya kinji kada kisa hijabi gyale zakisa saboda kinga inda zamuje ko?ki roki ummah"... dariya yaso bata ta gimtse bakinta "tou babu laifi bari in shirya"
"Tou Sweet heart"...
Tana kashe wayar ta buga tsalle,anty dinta dake gefe tayi dariya "shegiya zahra batdakama to maza ki shirya kiyi gida dan kinsan gida zaije daukarki besan kina nan ba,amma ina guje miki ranar da kamal zaisanki a ya mace"
Tabe baki zahra tayi "tsaff zan gyare kaina dan ba lallai ya gane ba,tunda banga alamar ya taba sex ba balle yasan wani abu waishi budurci"
Dariya suka kwashe dashi ta dau makullin motar antyn tana sauri sauri taje gida sanye da hijabinta har kasa dan kada momy da abbah su gane....
*********
Tafe suke hanyat fitowa a asibiti kallo daya zakai musu kasam cewar sun dace da juna wani mugun kyau sukayi duka su biyun,bilkisu na sanye da less blue mai touch din fari da stones mai shegen kyau da tsada anyi mata dinkin bubu gown tayi kyau ta yane kanta da farin gyale,tsakiyar kanta tayi parking gashinta,abdul kuwa sanye yake da farar shadda farin agogo da farin takalmi kansa babu hula haka suka gitto asibitin maaikata ma kallonsu sukeyi tamkar ango da amarya,sosai bilkisu ta dan saki ta mance da damuwar zuciyarta dikda tayi alkawarin bazata sanar da ummah labarin da kamal ya bata ba,idan ba hakaba zatace inbasa soyayya meyasa suke haduwa?
Sun kusa wajen mota ya danyi murmushi "habeebty i feel soo special today"ta kallesa ta dage masa gira daya "kai yaayah why?"
"Because of u,naga yau kinata nishadi sosai,sanan kuma habeebty bansan kalmar da zanyi amfani da ita ba wajenyi miki godiya,kiri kiri kim kawo ni asibiti dai kin biyamun kudin magani kinyimun komi kinki bari inbiya da kudina menene hakan ke nufi"
Batace masa komi ba ta bude mota ta shiga ta zauna mazaunin driver,tsayawa yayi yana kallonta ,tasan meyake nufi yasa ta katsesa kafin yayi magana "yaayah ni zanyi driving tunda kaine ka kawomu inason indam motsa jini"
Gyada kai yayi ya zagaya wajen zaman gaba ya bude ya shiga ta tada motar suka bar harabar asibitin....me bawa fulawa ruwa kallo ya bisu dashi harga allah wadanan mata da mijin sun dace,ga yadda suke tafe suna zuba soyayya....
Gudu sosai takeyi a titin raba road unguwar rimi gani yayi ta sauya hannu ya kalleta da sauri "ina zamuje?"
"Inaso insha ice cream daga nan kuma inaso mudan huta a wajen sai mu wuce gida ko?"
Ba haka ransa yaso ba dan beso ya hadu da wani yayi masa wani tunani na daban,musamman ganinsa da bilkisu yar alhaji bala dan maliki yanzun zaai masa fassarar kwadayi ganin yanayinsa ya canja kamar tasan abinda ke zuciyarsa tace "ka kwantar da hankalinka kai yayana ne dik wanda ya ganka yace maka ka sanni kace kai cousin dina ne"mamakinta ya kamashi har ya kasa magana yadda take saurin karantar mutane.....
Parking tayi dakyau sanan suka fito,kicibis tayi da motar kamal gabanta yadan fadi amma saita dake tazo ta inda abdul ke tsaye "muje ko" tare suka jera zuwa ciki,tun daga nesa yake hangensu,kallonta yakeyi yana mamaki tamkar ba ita ba gani yayi tamkar gizo takeyi masa,tambayar kansa yakeyi ya kara tabbatar da bilkisu bin maza take dubi yadda ta shigo tana murmushi,wato ta samu farin ciki ko?
Be karasa tambayar kansa ba yaga sunyi masauki nesa dasu kadan ta zauna shi kuma abdul ya mike ya shige domin yi musu order,waige waige kamal yakeyi ganin zahra ta zagaya bata dawo ba ya mike domin karasawa inda take ya tabbatar mata da ya ganta....
Zaro wayarta tayi jin abdul shiru ta soma replying massage a WhatsApp,kamar daga sama taga mutum akanta....
Zahra ce ta fito hannunta dauke da ice cream tana waige waige bata gansa a inda suke zaune ba....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU YA NEMI WADANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*13*
Da sauri ya juya gudun kada zahra din ga ganshi,ya karasa inda take yana mata murmushi,tura baki tayi "ina kaje?na fito ban ganka ba nidai"cikin sigar shagwaba tayi maganar,shiko maimakon yace wani abu murmushi yayi mata ya karbi ice cream din duka biyu "oya mu karasa ranki ya dade,saida nace miki kibari inje in karbo kikace ke zakije saboda ki samu ladan mijinki ko?"ya dage mata gira,badan ranta yaso ba ta washe masa baki ta karasa suka zauna suka soma sha sunayi suna kallon juna yana sakar mata murmushin wani dadi yakeji a cikin zuciyarsa da natsuwa dake ziyartarsa....
Abdul yana fitowa be tsaya ko ina ba sai inda billy ke zaune ya ajiye mata nata a gabanta "gashi habeebty ko saina bawa kanwata da kaina?"farrrr tayi da ido sanan tace "ai duty dinka ne kula da kanwarka a koda yaushe zanso haka nima,saidai kuma banaso yaayaah na ya rinka shan wahala amma next time,umm?"
Gyad'a mata kai yayi yana murmushi yana bin dan karamin bakinta da kallo,sosai take burgesa komi nata kyau yakeyi maasa uwa uba yanajin tausayinta haka kawai kodan tanada siffar masu tausayin oho,dago kai tayi lura da yana kallonta yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana murnushi tajanyo gyalenta ta rufe fuskarta "au rufemun fuskar akeyi baaso ingani?"dariya takeyi tana shan ice cream dinta cike sa nishadi,kallonsa tayi "yaayah muje mugaida innah ko sanan mu wuce gidanmu ka gaisa da ummah sosai,amma kafin nan mu shiga cikin wajen nan inkara ice cream din"
"Toh ranki ya dade"yace yana murmushi ya mike,itama mikewa tayi yan mata da samarin wajen kowa su yake kallo saboda kyawun da sukai ga fuskokinsu dauke da farin ciki dukkansu murmushi suke,hakan yasa wata budurwa da saurayinta suka karaso inda suke tsaye suna kokarin shiga ciki tsaidasu budurwar tayi "ammm sorry excuse me please"cakk bilkisu ta tsaya shima tsayawa yayi kallon rashin sani suke mata ganin haka yasa tayi murmushi "wallahi kun burgeni kun matukar yimun kyau kuma kun dace da juna daga gani ku din amarya da ango ne"murmushi kawai billy keyi jin dadin furucin budurwar yasa abdul kallon billy "kinji wai haka ne habeebty?"ga mamakinsa sai ta daga kai alamar ehh....wani dadi ne ya lullubesu duka su biyun sukayi hoto tare dasu sanan billy tayi exchanging number da budurwar suka shige....
Dik wanan abun a idon kamal sukeyi hakan yasa wutar tsanar billy ta kara ruruwa a zuciyarsa,haka kawai yakejin bayaso ya ganta tana farin ciki da nishadi,dik yadda zaiyi ya bijiro mata da wani abu zaiyi kodan yasa ta zubar hawaye,kila kawai fallasa ta zaiyi yasamu sukuni....dan tabosa zahra tayi "wai lafiya kuwa paradise nake ganin yanayinka tamkar akwai wani abu a wajen nan daya sanya ka sauya?kadaisan ba haka mukazo ba,bazanji dadi kana tare dani ina ganin damuwa a kwayar idonka ko akasin farin ciki ba"idonta yayi kwalkwal kamar zatayi kuka...
Rike kunnuwansa yayi "cool down my paradise ni na isa ma ina tare dake,inji wata damuwa ko bacin rai bayan ga aljannar duniya a gaba na?"murmushin jin dadi tayi "tou tunda mun gama muje ko tunda munada wajen zuwa da yawa "
"Your wish is my command wife"
Murnushin jindadi tayi suka Kama hanya zuwa inda sukai parking mota..
********
Bilkisu kuwa ice cream din da ta siya kannen abdul su zainab ta kai mawa harda innah,haka kawai innah keson yarinyar saidai tana hangowa abdul surutun mutane tunda kowa yasan waye mahaifin bilkisu a gari kuma kowa yasan irin tarin dukiyar da mahaifinta ya mutu ya bar mata ya daya tilo wajen dan maliki mai hadarin naira,dan canji ne kuma dan kasuwa ne daya shahara.....
Innah na cikin dakinta abdul ya shiga "bari in yiwa bilkisu rakiya zuwa gida ta dameni sai naje na gaida ummanta ummanta dai tou gara inje innah"
Kada kai kawai innah tayi sanan tace "a dawo lafiya kuma kadaiyi hankali idan ka dawo zamu tattauna,sanan kayi mata godiya don fitarka dazun zuwa masallaci ta fita da zainab tayo siyayyar kayan abinci ta kawo gidan nan sanan ga kudi nan masu yawa ta bawa zainab zata biya kudin waec da jamb wai nikam tsoro nakeji kada iyayenta suce a biya su kaga bashi garemu ba"turuss abdul yayi yana sauraren innah cike da mamakin abinda bilkisu tayi batare da tayi shawara dashi ba to me hakan ke nufi?tambayar kansa yake zainab ta leko tace "ya abdul anty billy na jiranka a waje"juyawa yayi da sauri ya fice zainab ta karaso cikin dakin fuskarta dauke da faraaa hannunta rike da robar ice cream tana sha....
*******
"Alhaji "momy ta kira sunan abbah cikin sanyin murya,"ya dai"
"Maganar kamal nakeso inyi maka dama akan maganar auren nan nasa shida bilkisu alhaji,a ganina tunda kamal bayaso to ka kyaleshi kawai tunda baa sanarwa mahaifiyat bilkisun ba tukunna koh?kaga shifa auren zumunci idan yayi dadi yana kyau idan beyi ba baci yake musamman ga kiyayyar take wajen namiji dama ita ce zamu iya hakura alhaji"
Shiru yayi abbah kamar bazaice wani abu ba sai kuma yayi gyaran murya "tou shikenan naji maganarki nima inada tunanin hakan saidai kuma banji dadi ba abinda kamal din yayimun na nunamin iyaka ta,dik yadda nakeyi masa shaawar rayuwa ingantacciya da yarinya yar asali wadda kowa yasan iyayenta a garin nan ya dubi idona ya dibi kasa ya watsamin a idona,amma badamuwa shikenan tunda shi ya haifemu bamu muka haifesa ba zaai masa yadda yakeso"
Jikin momy sanyi yayi sosai da kalaman abbah ta kasa furta koda kalma daya,hakikanin gaskiya abinda ya fadi hakan ne kuma ita kanta zataso ace ta hada jini da zuriah da hajiya mahaifiyar bilkisu dan macece mai karamci da dattako ga hakuri da take dashi sanan yar itama tanada tarbiyya sosai ga ta shiru shiru,bataso kamal ya bijirewa wanan hadin ba amma gudun kada a hada yarinyar tazo tana wahala yasa ta hakura kawai take tausasa alhajin...
Zamowa tayi kasan carpet inda yake zaune ta tsiyaya masa ruwan lemo me sanyi ta mika masa ya karba yana sha tana jansa da fira jefi jefi yana amsa mata suna kallo amma hankalinta na wajen inda kamal yake allah yasa yazo gidan tayi magana dashi....
*********
Tankamemen parlor ne da yaji kayan alatu na zamani da aka zuba masa royal chairs masu launin sararin samaniya da golden Haka labulayen parlorn ma iri daya da kujerun sai tangamemen plasma dake makale a jikin bango a kunnw tashar sunnah tv suke kallo macece zatai shekara hamsin sai wani dan dattijo wanda yake zaune ya maida hankali akan tv yana sauraron waazi.
Zahra ce tayi sallama hannunta niki niki da kaya ta shigo parlorn,ta cikin glass yake kallonta kallon da yake mata kadai yasa jikinta ya soma rawa haka yasa ta zube kayan a kasa ta karasa cikin parlorn ta zube a kasa "abbiy barka da yamma ina yini"
"Lafiya lau zahra ina kikajene?"
"Abiy mun fita da kamal ne shine yace in rakasa siyayya ashe ma ni zaiyiwa siyayyar kuma na sanarwa da ammiey kafin in fita"
"Tou kindaisan banason yawon banza ko?sanan inaso infada miki ki sanar masa da ya turo magabatansa na bashi sati biyu idan dagaske yakeyi"
"Tou abbah insha allahu zan fada masa,dama na dawone in sanar maka da anty binafa bata da lafiya tace inje gidanta in kwana abban sahla yana UK har yanzun be dawoba kuma ammiy tasan me aikinta ta gudu"shiru yayi sanan yayi gyaran murya "tou babu laifi sai ki shiga ki shirya ko dan yamma tayi already karki tsaya ko ina zan kuma kira binafar inji idan kin isa,sanan a rike ibadah banda wasa da sallah"
"Tou abby insha allahu"saida suka gama magana ta dubi ammiey ta sakar mata murmishi itama murmushin taiwa yartata tana son zahra sosai saboda natsuwarta yarta ce dakeda tarbiyya fiye da kowa cikin yaran gidan gashi bata hayaniya batada yawan samari ma..."Fatima aje aci abinci domin mutuminki akai alkubus yana nan nasa miki naki daban a kula"cike da jin dadi zahra ta mike ta fice parlorn ta haye matakalar sama tana murna a zahiri farin ciki take don tasan yau idan bata cikawa T.J alkawarin da tai masa na kwana wajensa ba ta banu da rigimarsa yanzun nan zata kira anty bina kafin ta kwafsa mata koda abbah ya kirata tai muryar rashin lafiya...nan da nan ta kira number anty bina ta shaida mata halin da ake ciki,cikin sauri ta shirya ta dibi kananan kaya wanda zataje party dasu dan ya fada mata sunada birthday din abokinsa...
********
"Yaudai gani ga abdul din bilkisu "murmushi abdul yayi ya sunkuyar da kansa batare da yace komi ba "kadaina jin kunyata abdul ka daukeni tankar mahaifiyarka da bilkisu koba bilkisu kai dana ne kaji?bilkisu ta fadamin taimakon da kayi mata a asibiti lokacin naji dadi kwarai,idan nasamu lokaci zansa ta kawoni in gaida umman naka mu kulla zumunci "
"Tou ummah nagode"
Mikewa ummah tayi ta barsu a nan parlorn tayi hanyar kitchen tana kwalawa shaawah kira....
********
Zuciyarsa nayi masa tantama akan yarinyar nan ,dik lokacin daya tuna da wannan mumunan abu zuciyarsa nayi masa zafi sosai yanajin wani irin tukuki da ciwo a cikin zuciyarsa dangane da wanan abun bakin ciki,sosai yarinyar take masa yawo a zuciya,sai yaanxun yake kara danasani a rayuwarsa wanda be taba irinsa ba,da wani ido zai kalli duniya ranar da wanan kwai ya fashe?shin tayaya zai fara?.....
Tayaya zai fuskanci mahaliccinsa da wanaj zunubi daya aikata?shin a ina ma zaiganta ya nemi gafararta data iyayenta?ya sanar musu da mummunan abinda ya faru?bazan taba samun sukuni a zuciyata ba dik lokacin dana tuna da wanan gyambo dake zuciyata,wanda dik daren allah sai naji sautin kukanta a cikin kunnuwana yanamun yawo..... innalillahi wa innah ilaihi rajiun...zufa kawai ke zuba a jikinsa kamar yayi karya...
Wayarsa ya janyo ya shiga laluben numbers da sauri
*********
"Kamal ka nemi abbahnka ka bashi hakuri akan abinda kayi na bijirewa umarninsa kaji dikda baka kyauta amma nayi masa magana kuma ya amince da maganar aurenka da wadda kace"da sauri kamal ya dubi mahaifiyarsa ya kasa boye mamakinsa da farin cikinsa sanin hali irin na mahaifinsa da kafiya akan abu,gyada masa kai momy tayi tana murmushi besan lokacin da yasaki wata yar kara ba cike da doki "momy dagaske abbah ya amincemun da auren zahra?"
Harararsa tayi"ya amince mana ja'irin kaya harda murna kake a gabana lallai yar nan ta ciri tuta yadda kamalu ya kasa boye soyayyarta"
"Momy banaso in rasa kyawawan hali na mace ta gari irin na zahra,ke kanki nasan zaki tabbatar da kinyi dace da suruka sboda zahra Yar mutunci ce yar manyan mutane wallahi na amince kuyi bincike akanta idan kunsamo wani hali ko wata dabiah mara kyau daga gareta kada ku amincemun aurenta momy"
"Shikenan zan sanarwa da mahaifinka dikda dazun munyi magana akan ranar jumaa zasuje gidan shida alhaji ali mai shadda da alhaji tahir kasan dasu zashi sune aminansa zasuje neman aure inaga da sadakinsu zasuje don abbanka yace bayaso auren ya wuce nan da sati shida"murna ce tasa kamal mikewa ya rungume mahaifiyarsa da sauri yana kwararo mata addua da godiya,shafa kansa tayi tana murmushi "allah yayi maka albarka,nima zansamu umman bilkisu mu tattauna akan maganar auren naka saboda tare zamu gabatar da shirye shirye da maganar yadda zamuyi ordering kaya a dubai"kasa cewa mahaifiyarsa komi yayi jikinsa har rawa yake ya mike ya ciro wayarsa a aljihu yayi dialing number ya fice a parlorn yana waya fuskarsa dauke da nishadi.....
"Hmmmm kaidai bari ai dole inyi murna samun nagartacciyar mace kamar zahra ai ba abu bane me sauki wallahi na kosa a kawomin ita a matsayin matar aurena"
.dariya sosai abokin yakeyi a waya "su kamal zaa angwance zaa kwashi garar amarci,saidaifa naga a matse kake da auren nan kamar wani tuzuru dududu kwaya nawa kake?kardai garin zumudi ka afkawa yar mutane ka kassarata"
Yar dariya yayi cike da kasaita "hafeez kenan ai nasan yadda akeyi tunda inada ku abokai maau aure dole zakuyimin bayanin yadda zan tafiyar da yar mutane tunda nasan zahrata zata kawomin mutuncinta gida na"
"Shege abokina ka kosa kasha romo"dukkansu dariya suke cike da nishadi suna tattauna abubuwa dangane da bikin....
*******"
Hafeez ne ke tuki kamar zai tashi sama,da sauri yaja burkin mota ganin abinda yake gani a gefensa ,da sauri yayi wining class din motar yana kara kallonsu sosai....kai gaskiya ba ita bace wanan kama ce kawai ba zahrar da kamal ya tura masa hotonta bace yanzun bayan sungama magana,kamanni ne wanan kawai da kuma darene yasa yaga kamar ita,kuma shi kansa yasan yarinyar da abokinsa ke nema yar alhaji Mahmoud yar mutunci ce gidan mutunci ne gidan malamai ahalusunnah...sai kawai yaja motarsa yayi gaba ....
********
Bilkisu itace ta fadowa kamal a rai yana zaune yana cin abincu yana kallon tv a dakinsa dake gidansu dagashi sai gajeren wando da ves ya mike ta hude fridge ya ciro madarar Hollandia ya zuba a cup ya kurba sanan ya koma ya zauna murnushin mugunta kawai yakeyi shi kadai..... zanbarki ki shana ya furta a fili amma zan dawo gareki... zanyi wasan kura dake billy....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU YA NEMI WADANAN NUNBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 7:07 AM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*14*
Maida kai kamal yayi ya rufe idanuwansa ruffff badan bacci ya daukesa ba sai dan siffofin Zahra da sukeyi masa yawo a idonsa,shagwabarta,salon soyayyarta?uwa uba salon zatuttukanta da kalaman soyayyarta masu ratsa zuciya da sanyaya zuciyar mai sauraro....ya tanadar mata dik wata soyayya da tarairaya da kulawa da kauna tsantsa a darensu na farko....bude idanuwansa yayi da suka kankace,ya gyara kwanciyarsa gefe daya ya janyo wayarsa yana kallon hotuna,hoton billy ne yazo kai yayi murmushin mugunta a fili ya furta "zan barki ki wataya a cikin kwanakin nan domin banida lokacinki a yanzun,nan gaba kadan zaki dana sanin zuwanki wanan duniyar,zan haddasa miki bakim ciki zan fama miki ciwon da bazai taba warkewa ba har karshen rayuwarki,saj farin ciki ya zame miki tankar kudin guzuri,da kina cikin sa zai kare ya barki da bara!!!!!
**********
"Ya kikeji dangane dani habeebty?kinajin wani canji a rayuwarki dangane da kasancewa dani?inajin wani abu a cikin kundin zuciyata da yayi rassa tankar bishiya me reshe a cikin zuciyata,wani abu nakeji kamar so da kuma tsananin kaunar kanwata da yayimun shigar sauri,taya hakan zai kasance? meyasa soyayya zata makantar dani inso wadda tafi karfin dangina kafff ballantana ni kaina? bilkisu"ya kira sunanta cikin wata iriyar murya mai ban tausayi,bugun zuciyarsa da nata duka sun tsananta,...sosai ta runtse ido zufa na karyo mata yayinda take makale da wayar bakinta ya kasa furta koda kalma daya tunda ya soma magana,sosai takejin faduwar gaba yayinda muryarsa gaba daya ta rukide mata zuwa azzalumin da tafi tsana a rayuwarta hakan yasa ta kashe wayar tana maida numfashi sama sama daga kai tayi ta kalli fankar dakinta dake aiki da AC da ta kure a karshe amma hakan be hanata gumi ba,mikewa tayi ta kunna wutar dakin haske ya gauraye dakin,tsaye tayi rike da wayar lokacin da kiran wayarsa ta kara shigowa a karo na biyu kallon wayar takeyi tana jin faduwar gaba,hakika babu tantama ya abdul yanada alaka da me wanan muryar dikda zuciyarta ta gama aminta da bashi bane.....
Hannunta na rawa ta danna recieve ta kara a kunnenta,muryarsa ta bugi dodon kunnenta a karo na barkatai bugun zuciyarta ta tsananta"kiyi hakuri bikkisu da kalamaina hakika zuciyata ta makance da tsananin kaunarki,sanan zuciyata bataimun halarci ba da ta kamu da soyayyarki lokaci daya babu wata dabara,kyautatawarki da kulawar da kika nunawa kannena da mahaifiyata su suka bada gudun mawa wajen rura wutar soyayyarki a zucuyata,nasan ban dace dake ba domin ke yar babban gida ce kuma yar manyan mutane.....ajiyar zuciya ta sauke a lokaci daya hawaye ya zuraro mata a ido daya ta dafe gefen zuciyarta dake barazanar tarwatsewa"ya abdul....ka daina cewa baka dace dani ba,hakika kaine ka dace dani ka dace da rayuwata,anma na gama yanke shawarar bazan taba yin aure ba harabada"tana gama fadin haka ta fashe da kuka sosai,ta shiga rera kuka a waya yana jin sautin kukanta ji yakeyi tamkar ana zuba masa wuta a zuciya,kiran sunan ta ya shigayi cikin dasasshiyar mirya,amma ta kasa amsa masa,bata da bakin da zata labarta masa ita din farko ce sauran wani kato kamal....mezata fada masa ranar daya risketa baa cikakkiyar mace guda ba?ranar da yasan cewa ira din fanko ce ?kuka kawai takeyi,ya shiga kiran sunansa amma bata sauraresa ba kawai ta kashe wayar cikin sauri ta danna switch off ta jefar sa wayar kan gado ta zauna dirshan akan carpet din tsakar dakinta ta dafe kai gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuska tana rera kuka.....
Anya zata yarda kamal ya ci bulus?anya zata yarda yaci bulus ya yaga leda?kuma tana kallonsa da wata mace a matsayin matar aure?meyasa kamal bazai aureta ba ya rufa mata asiri a matsayinsa na Wanda yasan ta a ya mace yayi fata fata da ita ta zama sauransa,zuciyarta ke gargadin ta ta hanyar tunato mata da kalaman kamal kamar Haka"na tsaneki bilkisu wallahi na tsaneki idan kika bari abbah ya aura miki ni sai kin gwammaci zaman gidan yari da gidana,sai kin gwammaci ki dibi garwashin wuta ki watsa a bakinki saina wulakantaki saina maidake abar kwatance"runtse idonta tayi ta toshe kunnuwanta tanaji tamkar a lokacin yake fada mata maganar,a zabure ta mike tankar mahaukaciya cikin layi ta fada kan gadonta ta saki kuka,anya zata iya barin kamal tana gani ya auri wata ya mance da ita yaci bulus?kamal ya cuceta ya cuci rayuwarta amma zata gwada saarta akansa,da wanan shawarar ta kwanta hawaye na cigaba da ambaliya a idanuwanta....
*********
Safiyya ke mopping a parlor wajen karfe goma na safe dik ta kashe kayan wutan ta nade carpet ta jingine gefe hajiya hauwa tayi sallama,sanye da lafaya mai ruwan zuma tayi kyau sosai ta fito a ainihin matan shuwa na kasar bare bari lafayar jikinta kadai zata haura dubu dari balle zobinan dake sanye a yatsunta jere sai daukar ido sukeyi ba ruwan gwal ga kambu na zinare makale a hannunnta na dama hannunta na hagu kuma agogon diamond ne sai walwali yakeyi,sakin mopper safiyya tayi tana kallon hajiya hauwa wadda take ta kwada sallama sosai matar tai mata kyau dikda ba yau ta soma ganinta ba amma tasan ba bata bace wajen daukar wanka,ganin sakin bakin safiya yayi yawa yasa hajiya hauwa mahaifiyar kamal karasowa cikin parlorn "ke dalla shashashar ina ce inata sallama kina jina kin kasa amsawa sai kallona kike kamar zaki cinye ni?ina matar gidan take?"tana maganar tana kokarin zama,sai lokacin safiyya ta washe baki ta tsugunna "ankwana kalau hajiya?"
"Ji wata gaisuwa dan Allah,waikedin yar kauyen ina ce?umm?ba haka ake gaisuwa ba,kusan shekararku nawa keda amina a gidan nan har yau baku waye ba bansan ranar da zaku waye ba shashasha"zatai magana ummah ta karaso parlorn sanye da jallabiya baka mai shegen kyau tana fadin"lafiyanki safiya kike magana ke kadai a parlor kamar tababbiya?"ai bata karasa zancenta ba suka hada ido da momyn kamal a tare suka sakarwa juna murmushi cike da jin dadi ummah tace "lale lale lale marhabin da zuwan hajajju inata cewa zanzo zanzo allah beyi ba gashi ke kinzo ,kai amma banji dadi ba"rungume juna sukai suna kara gaisawa sanan ummah ta kwalawa shaawah kira tazo "a kawowa hajiya breakfast din mu na yau nasan zata soshi mutumin ne"
"Kunun gyada?"momy ta tambaya cikin faraa duka sukasa dariya
"Ummah yanzun ma ba zuwanki bane zuwan danki ne,domin zuwa nayi in sheda miki danki ya tattago maganar aure kuma kinga ai dole kisani da wuri dan ki shirya zaki suruka"
Dan guara zama ummah tayi cikin zumudi "kamal nawa ne zaiyi aure?"
"Kwarai dagaske zakiyi suruka kin kusa zama kaka"daga hannu ummah tayi tana fadin "alhamdulillahi alhamdulillahi Allah ya nuna mana,lallai goron albishir dinki daban ne hajiya,kamal zaiyi aure?allah sarki nayi murna yar wacece yar inace"
"Yar gidan alhaji auwal ce ahalussunnah sunan yarinyar fatima amma zahra akece mata don yanzun haka na baro gida algaji ya fita zuwa gidan amininsa ya sanar masa da maganar auren yau zasukai sadaki shine nazo in fada miki don shirye shiryen kayan lefe yana hannunki"
Cakkkkk billy ta tsaya ta fito da sauri hannunta rike da dankwalin atamfarta da gyale dayan hannun jakarta ne,don tayi latti na makaranta,a kunnenta saukar sunan zahra aauwal ya sauka sunan matar da kamal zai aura....wato kamal yar gidan mutunci ustaziya ya dauko yar manyan malamai na kasa wadda bata sheke ayarta ba a duniya,wadda zai bareta a leda galll zai angwance da ita,ita kuma ya barta ta tanadi kalaman da zata fadawa mijinta a darenta na farko?idonta ne ya cicciko da hawaye ta karasa fitowa parlorn,momy ta bude hannu fuskarta dauke da faraa "oyoyo my baby zo in rungumeki nayi missing dinki dikda fushi nakeyi dake"cije lebe billy tayi ta karasa ta rungumo momy hawaye na kokarin sakkowa a fuskarta ta boye fuskarta,kallon yadda ta rame tayi fari tass momy keyi "lafiya babyna?meke damunki haka?umm?"tana kokarin kallon kwayar idon billy amma ta shiga boye fuskarta dikda momy da ummah sun hango makalalliyar kwalla a kwarmin idonta,jiki babu kwari ta gaida momy "ummah nayi latti zan shiga school saina dawo"ajiyar zuciya ummah tayi tabi bilkisu da kallo tana mamakin sauyawar yar tata dikda tasan tana cikin farin ciki a kwanakin nan da take tare da Abdul, Kuma lafiya lau suka gaisa da asuba har sukai azkar tare suna dan taba hira to canjin na menene?
Ta bangaren momy kuwa tunaninta be wuce cewar kodai akwai wani abu a zuciyar bilkisu ba yasa ta hango damuwa karara a idanuwanta? kuma da alama ta jiyo tattaunawarsu da mahaifiyarta...kiran sunanta da ummah tayi yasa momy saurin sakin fuska hade da washe baki hakoran makanta biyu suka bayyana...suka soma tattaunawa akan maganar lefen....
Wangale babban gate din gidan mai gadi yayi tun hangowar fitowarta ta nufi parking lott zuciyarta zugi takeyi mata hakan yasa motar da ta saba fita da ita kawai ta canja ta dauki wata bakar mota mai shegen kyau sai walwali take daga gani sabuwace dalll ranan zata soma fita da ita,take motar tayi tayo riverse tayo hanye fita sai horn takeyi maaikatan gidan zubewa suke a kasa tayo fita ta hango sa tsaye da rigar Manchester ja tai masa kyau da blue jeans,kallonsa sosai takeyi ta cikin mota ta glass din gaba yake hangenta shima kallonta yake,murmushi ta sakar masa ta karasa fitowa sanan tayi parking tayi horn ya karaso ta sauke glass din"barka da zuwa ya abdul kaine da safen nan?"tana jifansa da wani irin kallo mai dauke da sakwanni,"dole inzo da safe inganki habeebty domin sautin kukanki shi ya rinkamun yawo a kunne na kasa bacci inaso inganki koda ace bazaki sake saurarena ba,"yayi narai narai da fuska,ciccikowa idonta sukai ta matse "yaaaa abdul mana,idan kana fadin haka inaji tamkar nidin ta dabance ba yar adam kamarka ba niba kowa bace kuma ban isa ince bazan amshi tayin soyayyarka ba,face nice nake tsoron abinda gaba zata haifar mun"ta tsaresa da ido,wani murmushi yayi mata yasa taja dogon numfashi kirjinta ya soma sauka "ya abdul nayi latti we talk later take care i miss u?"ta kashe masa ido ta figi mota a guje tana daga masa hannu tana dariya, shima dariyar yakeyi yana daga mata hannu har tayi nisa sanan ya kada kai ya sauke ajiyar zuciya ya juya yana tafe yana jin kansa cikin wani nishadi...
*******
Tarba sosai iyayen zahra sukawa mahaifin kamal da manyan aminansa guda biyu wanda har yasa sukaji kunyarsu,anyi musu tarba irinta mutunci tarba irinta mutanen kwarai tare da abokanan mahaifin zahra wanda sune suka karbi sadakin zahra million daya da mota sabuwa dalll kyauta daga surukarta...dakyar mahaifin zahra ya karbi wanan kyauta,sanan suka tsaida musu da ranar aure nan da wata daya abin ya bawa mahaifin kamal mamaki shi da yaje da zummar sati shida...kowa nata sambarka haka suka rabu...
A guje zahra ta shiga gidan anty binafa tana ihun murna,tun daga waje take kwalawa antyn nata kira sahla ta gani babbar yarta a patlor "ke ina amminki"
Hanyar dakinta ta nuna mata ta cigaba da wasa da yar babynta,tura kofar tayi anty binafa ta fito daga wanka kenan "anty....nanda sati daya iwar haka na zama amarya"
Washe baki anty tayi "ohh wanan yarinya bata da kunya haka zaa kaiki kina rawar kai?koda yake kedin batda kama ce saidai bansan yadda zata kasance miki ba da wanan batda kamar taki zahra"dan bata fuska zahra tayi "kamar ya?"
"Kamar yadda kikasani samari sun waye sun kuma san mace virgin sun san wadda ba virgin ba dan haka sai a samu mafita domin ki tanadi kalaman da zaki sanarwa da kamal yadda akayi"
Murmushi Zahra tayi "anty kenan wanan mai sauki ne inada kawa hafsat ilham kuma tacemun hajiyarsu nada yan uwa a sokoto can zamuje a hadani indawo budurwa gal a leda"
"Kina yaudarar kanki zahrau"tace tana kallon zahrar da sai murmushi take wayarta ce tai kara cikin jaka da sauri ta zarota taga an rubuta paradise "kinga dan halak shike kirana"
"Assalamu alaikum habeeby"ta furta cike da ladabi,tamkar yana ganinta "zahra gamu a kofar gidanku daga makaranta muke nida abokina yazo ganinki ina kofar gidan anty bina dan naje can akace kinyo nan"murnushi tayi kamar yana ganinta tai farrr da ido "gani nan zuwa ranka ya dade"anty binafa kuwa sakin baki tayi tana kallon yadda zahra ke ladabi a waya tamkar wata salaha,dik shedancinta zahra ta fita domin zahra gaba daya mutane kallon mumina suke mata,"anty ya naga kina kallona"
"Mamaki kike bani zahra kedin shedaniya ce allah sarki kamal gwanin tausayi besan abinda zai dakkoba bawan allah salihi me kyakkyawar zuciya"tabe baki zahra tayi ta fice....
Tahowa take amma hafeez idonsa kirrr akanta,tafe take da hijabi amma kallon kurilla yake mata wanan jan bakin da eye shadow na idonta exactly irin wanda ya gani a idon ta jiya,shin anya ba ita bace suke haduwa a night club da wani abokinsa TJ?...wani miyau me kauri hafeez ya hadiye,zuciyarsa nayi masa kokwanto,to anya kuwa itace?toh wanan yar alhaji auwal ne babban malamin nan da kowa yasanshi a garin nan kuma attajiri wanda dukiyarsa ta habaka ta harkar kasuwanci....yarinya mai mutunci me shigar kamala wadda ko magana batayi a cikin mutanen unguwa,be gama tunani ba kamal ya zungoresa "malam tunanin me kake haka?ka ganta ko nafada maka ba ita bace shiyasa na dauko ka"
Dammm gaban zahra ya fadi cijewa tayi cikin jarumta tace "bafa zakuzo kunamin yare irin na samari ba asanar dani wacece ake ba ita bace?domin kaina ya daure"
Waskewa hafeez yayi gudun kartasan meye tunda dai ba itan bace yake gani "amaryarmu amaryar sati hudu masu zuwa menene plan din aurenki?kema kinason a rakashe ayi shagali asha rawa?"yayi maganar cikin sigar tsokana da kauda waccen maganar dikda idonsa kyarr akanta yanayi mata wani kallo,itama kuma wani kallo tai masa da takejn faduwar gaba
Cike da kunya ta sunkuyar da kai tana murmushi ta kasa magana,dadi ne ya kama kamal ya karbe zancen "karkazo ka takurawa matata da tambaya fa kasan ita bame yawan magana bace"
Dago kai zahra tayi cikin dabara taga har yanzun hafeez ita yake kallo amma wanan karon babu wata alama a fuskarsa ta sauke ajiyar zuciya ta saki jiki kadan.....
**********
Inda suka saba zama billy ke zaune ita kadai cikin makaranta,batasan sanda hawaye ya wanke mata fuska ba,kiran numbersa take amma baya picking daga karshe idan ta kira sai ya danna mata number busy,gashi taga fitar motarsa daga makaranta,yaje wajen amaryarsa kenan yar mutunci wadda yake mararinta ita kuwa ya lalata mata rayuwa yana kokarin yasar da ita,anya kuwa zata amince da hakan?dole ta tunkari kamal da wanan yakin dan bata tanadi amsar da zata fadawa mijin da zata auraba uban yayanta ba,bata tanadi hawayen da zata rinka zubarwa da namiji idan yayi mata gorin besameta a cikakkiyar mace ba,kallo wayar take tati dialing numbersa a karo na barkatai ta soma ringin kenan taji an taba kafadarta da sauri ta boye wayar kasa kada pheey taga sunan wanda take kira"billy billy billy wai lafiyanki kuwa menene haka ya sameki da kiketa boyemin a rayuwarki?"tai maganar cike da danmuwa tana tsaye bata zauna ba,bilkisu ta ruko hannunta ta zaunar da ita a kujerar dake fuskantarta,tasa hannu ta share hawaye sanan ta jefa wayar cikin jaka ta fuskanceta,tanaji. Karfin gwiwar sanar da pheey komi dangane da ita har sirrin dake tsakaninsu da kamal wanda yake barazanar tarwatsa mata rayuwa dashi amma kuma wata zuciyar na kwabarta da tabarita fuskanci kamak din kafin ta sanarwa da nafisa komi,matukar kamal be amince da rufa mata asiri ya aureta ba to ya zama dole tasamu wanda zata fayyacewa sirrin nan tasamu sassauci a zuciyarta.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*[6/13, 2:25 PM] My Airtel: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*15*
Kuka sosai billy takeyi me ratsa zucuya,mai ban tausayi,hakan yasa zuciyar nafisa karaya ganin kukan da kawartata takeyi sosai takejin tausayinta dikda batasan abinda ya sameta ba batasan meke damun kawar tata ba,amma ita kanta samun kanta tayi da zubar da hawaye,batasan lokacin da hawaye ya soma bin fuskarta ba tana rike da hannu billy,kusan minti goma ya shude suna zaune a haka sanan ta share hawayenta ta fuskanci bilkisu cikin sigar lallashi "banason ganin hawayenki ko kadan kawata,idan naga kwalla a idonki nakan tsinci kaina cikin wani irin hali mai wuyar fada kiyi shiru ki daina kukan haka, damuwarki damuwata ce bilkisu inaso insan matsalarki amma na fuskanci baki damu da hakan ba baki so insan matsalarki"ta ja numfashi bilkisu sanan ta dubeta da jajayen idanuwanta da suka kada sukai jajir cikin kwayar idonta tamkar gudan jini babu farin sai launin bakin daya hade da jan da yayi kallo daya zakai mata ka kauda idonnka"pheey"ta kira sunan kawar tata cikin sarkakkiyar murya
"Naam billy "
"Kin cancanci kisan komi dangane dani kisan fiye da hakan ma amma ban daukeki a matsayin kawa kawai ba yar uwata na daukeki dan haka ki kwantar da hankalinki zan kwance miki kullin da babu wanda yasan shi dik fadin duniyar nan zan sanar dake sirrin zuciyata da rayuwata gaba daya da nake boyewa,kiris ya rage kisani amma kidan saurareni kadan"ta karasa maganar tana gyadawa pheey kai wadda tai shiru tana saurarenta "toh shikenan bilkisu amma ki share idonki ki wanke fuskarki ki tashi mubar nan mutafi gida yamma tayi"
Babu musu bilkisu ta bude ruwan gorar dake gabanta ta dan mike ta matsa daga rumfar da take zaune ta wanke fuskarta sosai sanan ta ciro farin towel dake cikin jakarta ta goge fuskarta,babu laifi fuskar ta rage ja saidai idonta da suka dan tasa ta ruko hannun pheey suka bar wajen suka soma taku zuwa inda ta saba parking motarta...
Tafe suke a motar pheey tana yiwa billy hira jefi jefi har ta dan saki jikinta ,dan murmushi tayi da ya fado mata a rai ta dubi nafisa sanan ta kara volume din radiyon motarta tana sauraren wakar umar m sharrif mai take zan rayu dakai zan mutu dakai abadan dani da kai zamu zauna...satar kallonta nafisa tayi tayi murmushi "kawata kodai dama kukan soyayya kikeyi ne hakan?"
Murmushin da tayi dimple dinta saida ya dan lotsa fararen hakoranta suka bayyana "zuciya ta dai keson yimun rashin adalci a halin da nake ciki kuma takeson jefani tsundum cikin kogin soyayyar wani wanda nakejin tsoro"
"Tsoro kuma?wani irin tsoro billy?kina bani mamaki wallahi kasantuwar yadda kika canja daga billyn da nasani jaruma kika koma wata ta daban"
Karya kwanar layimsu pheey sukayi billy ta dubeta "babu jarumi a soyayya hajiyata kedai kawai sai mun hadu zamu tattauna dan ina tunanin mutumina yazo gida jirana"
"Lallai wanan shine jarumin maza samun soyayyar bilkisu bala dan maliki billy aji ba karamin abu bane lallai ya iya yaki a soyayya"dariya sukai gaba daya suka tafa sanan billy tace "kyaji dashi uwar surutu ki gaidamun da ummah dasu sabirah dan allah ina nan zuwa musu weekend"
"Kamar gaske kedin?"ta harari pheey sanan taja mota tana daga mata hannu....
*********
A gajiye ta shiga harabar gidansu daga parking lot tana taku tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki sanan cikin zuciyarta allah allah takeyi ta kebe ita kadai domin gudanar da abinda zuciyarta ke bata karfin gwiwa a kai...a ciki tayi sallamar amma be hana wadanda ke zaune a parlorn amsa sallamarta ba dikda muryar ummah kawai tajiyo batare da ta kalli sashen da suke zaune ba tace "ummah barka da gida"
Yar dariya ummah tayi ganin bataga wadanda ke zaune parlorn ba ta tsaidata "barkanki da zuwa yar makaranta,bilkisu yar ummah amma ki jiyo kiga abun mamaki mana"....cakk ta tsaya badan ranta yaso ba ta juyo idonsu ya hadu dana juna yar kara tayi suka rungume juna "khaireee my khaireee ohh my god shine babu ko waya zakuzo?"cike da zumudi take maganar
Harararta khairee tayi "aike momy tayi fushi dake tunda munzo gidan nan duba jikinki bakizo gidan mu ba kuma nasan ummah ta fada miki munzo shine nace ya yusuf ya kawoni inzo inganki masoyiyata tunda kindaina sona"..bata fuska tayi cikin sigar wasa,dariya sosai billy tayi sanan tai mata kiss a kumatu "sorry my beta half ni ai ban isa ba"duka suka sa dariya sanan ta dubi ya yusuf "ina yini ya yusuf"
"Nayi fushi ai tunda saida kika gama gaisawarki da khairee sanan kikasan dani"yadan harareta yana kashe mata ido,kauda kai tayi tamkar bata gansa ba tana dariya nan taja hannun khairee sukai sashenta suna ihu da dariyar murnar ganin juna...
Ummah kuwa faraa sosai takeyi Tana son ganin bilkisu cikin walwala,sosai take tsintar kanta cikin farin ciki domin bata da wadda ta fita a fadin duniyar nan daya kasance bata da kowa a garin...
Sun fito zasu tafi gida ya rakosu parking lot abdul ya turo gate din gidan ya shigo,yana sanye da farar polo shirt da bakin jeans,yayi kyau sosai ya gyara gashinsa,sakin baki bilkisu tayi tana kallonsa kamar yau ta taba ganinsa,sosai yayi mata kyau musamman yau da yayi gyaran gashi,kyawunsa na ainihi ya bayyana saidai yanayin shigar tasa ya nuna shi din bame hali bane,zungurarta khairee tayi tana tabe fuska "malama muyi sallama kafin kije soyayyar wajen wanan kodadden tabdijan billy?wai sonshi kike haka?dama naji jita jita a gari ai,nasansa bayan unguwarmu yake"murmushi billy ta sakar masa yayinda ya jingina da jikin bangon gefen gate dinsu yana hangenta...
Shigewa mota khairee tayi cike da takaicin wanda yar uwar tata take soyayya dashi, Wanda class da komi ta fishi mtswww ta danyi tsaki"yaushe zakizo?"
"Sunday"bata karasa bata ansa ba khairee ta rufe motar tana tura baki hade da hararar billy,itako batasan aziki na bori ba dagawa ya yusuf hannu tayi shima ya daga mata suka ja suka kara gaba....
Cikin takun ta mai daukar hankali ta karasa wajen da yake tsaye tana aika masa da murmushi da kallo mai dauke da sakwanni irin na masoya,sakin baki yayi yana bin ta da kallo bugun zuciyarsa na karuwa,wutar soyayyarta na ruruwa a zuciyarsa...
*********
Karfe takwas da minti goma ta fito sanye da gown na material jajaye hannunta rike da makullin mota ta fito parlor bata ga ummah ba,amina ke zaune a kasan carpet ta kure tv da ido tamkar ranar ta soma ganin tv din,dan daka mata tswa billy tayi "ke yar kauye"a gigice amina ta juyo kamar ta saki fitsari saboda tsananin tsoro da furgici "ina ummah na"
"Tana daki sallah take"
"Idan ta fito kice mata naje pharmacy akwai maganin da ban karbo ba a asibiti zanje in siya zan dawo babu dadewa"
Daga bayanta ummah ta karbe zancen "banason driving din dare billy kiyi sauri ko dawo dan allah kinji allah ya tsaremun ke"
"Ameeen ummah na"tace mata tana murmushi ta juya ta fice,ummah ta bita da kallo,haka kawai ummah kejin faduwar gaba a yan kwanakin nan idan ta kalli yadda bilkisu ta koma....
**********
Ta karyo kwanar shiga unguwarsu kamal da mota ta hangosa ya fito daga gida yana kokarin shiga motarsa da yayi parking a kofar gate din gidan,sai kawai tayi dialing wayarsa tana hangensa lokacin da ya ciro wayar yana kallo ganin itace yasa ya maida wayarsa aljihu,haushi da takaicinta ya lullubesa wanan yarinyar uban me take nema dani da take damuna da kira kamar naci mata bashi?
Be gama tambayar kansa ba call dinta ya sake shigowa sai kawai ya maida wayar aljihu ya shige motarsa ya tada,ganin ya mike ta sama yasa ta tada motarta tabi bayansa,wasu hawaye masu zafi ke zubowa a idanuwanta,gabanta na tsananin faduwa,dama ace babu abinda zai sake hadata da kamal,dama ace bata taba saninsa ba a rayuwarta,wani abune ya tokare mata mako gwaro tana tunanin makomarta idan ta sameshi tunanin abinda zai biyo baya take amma bata da zabin daya wuce tabi bayan nasa sai kawai ta tada motarta tabi bayan motarsa,tana biye da shi taga ya nufi guest house dinsa inda ya saba haduwa da ita,inda suka saba zuwa ya keta mata rigar mutunci,wani tururun takaici ne ya taso ya rufe Mata idanuwa har ta karasa yana kwana da motarsa cikin gate din itama ta take masa baya ta shigo....
Cakkk ya tsaya yana kallon motar da ta shigo gate din gidan ta cikin madubin motarsa yake kallonta, itama shi take kallo ganin ya tsaya cikin motar yaki fitowa sai kawai ta kifa kanta a sitiyarin motar ta fashe da kuka....
Ganin bata fito ba yasa ya yanke shawarar fitowa,aikuwa haka akayi ya fito daga motar ya hada girarsa sama da ta kasa ya kulle motar ya nufi cikin gida,itama ta fito ta kulle motar ta bi bayansa gabanta na tsananin faduwa tana tunanin makomarta yadda zata kasance musu.....
Bakinta dauke da sallama ta shigo dakin yana zaune kan kujera yana latsa wayarsa ta karaso beko amsa mata sallamarta ba bata kuma damu da hakan ba ta nemi kujera ta zauna,shiru bece mata ba bata ce masa ba gar ya gama danne dannensa sanan ya dago idonsa ya kalleta itama shi take kaloo nan da nan idanuwanta suka cicciko,sai kawai ya sakar mata murmushi sanan ya soma magana cike da gadara "billy billy billy duniya meya kawoki gidana batare da na bukace ki ba?ko har kin fara missing sandar girma na ne?"ya daga mata gira daya,wani takaici ne ya turniketa da har hawayen da take boyewa suka zubo mata sanan taja numfashi ta dubesa "babu kewar ka a tare dani ba kuma abinda kake tunani bane ya kawoni,domin koda kake ketamun mutunci bada son raina kakeyi ba memakon inji dadi ma sai akasin haka saboda baa nan zuciyata take ba kuma ina tsoron allah,babban abinda ya kawoni shine dama ka sanarmun da maganar aure har kace bazaka aureniba saboda tayin da abbah yayi maka,well saika je ga abbah kayi amfani da kalmomi masu dadi da soyayyar da sukeyi maka ka shawo kan iyayenka suka amince da zabinka,kake tunanin ni zaka yasar dani saboda kaci moriyar ganga,toh kamal kasani idan har kayimun haka bakaimun adalci ba kamal,idan har baka aureni ba to bansan ya rayuwata zata kasance a gaba ba bansan makomata ba kamal banida kalmomin da zanyi amfani dasu wajen gansar da mijin daya riskeni a fanko,banajin sonka ko kadan cikin zucuyata saidai inada bukatar ka aureni kodan ka rufamin asiri ka karemun mutuncina daga zubewa daga idon wanda zaizo ya aureni gaba,kamal ka taimakeni koda bazaka kusanceni ba koda zan zama borar gidanka wallahi na zabi hakan da abinda nake gudunwa kaina a gaba"tana maganar hawaye na gudu a fuskarta kamar an bude famfo wani irin bugu zuciyarta keyi da tsananin fargaba hakan yasa ta kada jure zaman kujerar ta zube a kasa ta durkushe a gabansa tana gunjin kuka....
Wani kallo kamak ke jifanta dashi,nan da nan jijiyoyin kansa suka fito sukai rudu rudu wani irin tsanarta fiye da ko yaushe yayi masauki a zuciyarsa ji yake tamkar ya shaketa tabar duniya,wato tama ci uwar rainin wayau hakan yasa a fusace ya daka mata tsawa "bilkisu"a razane ta dago kai fuskarta shabe shabe da hawaye gyalen kanta ya zame gashin kanta ke tashi sakamakon iskar fanka dake kadawa...
"Me kike nufi?au kiran da kikemun kenan a waya ki rokeni in auri fankan fayau ?kiran da kikemun ne ki rokeni in ajiyeki a gidana a matsayin matar aure?toh in kalleki a mene?in kalleki a matsayin karuwata wadda muka gama sheke aya a waje kuma na shigo da ita gidana"...jikinta har rawa yake idonta kirr akansa bakinta naso ya furta wani abu ta kasa,ya cigaba da magana "ko kinaso kicemun in ajiyeki a matsayin uwar da zata bawa yarana tarbiyya?uwar yayana?in rasa wa zata haifamun yara saike bilkisu?to hell with you wallahi da kinsan yadda na tsaneki bilkisu da bakizo min da wanan furucin na auren kazama irinki ba,wallahi wallahi koda nake hada jiki dake bana hada jiki dake don jin dadi?inayi ne domin in kuntata miki in cigaba da wulakantaki da kaskantaki har karshen rayuwarki kuma daga karshe in tona miki asiri"
Wani zabura tayi ta mike tana kallonsa ido cikin ido hawaye na zarya a idonta ta shiga zagayeshi a parlorn yana bin ta da kallo cike da mamaki kamar wadda tasamu tabin hankali"ya isheni haka kamal wulakanci da munanan maganganunka sun isheni kamal nagaji nagaji kamal abinda kaimun sai allah ya saka mun kuma ina mai tabbatar maka da zan fallasa sirrin da kakemun barazana dashi zan tonawa kaina asiri kamal nadainajin tsoro bana gudun a kalleni ta ko wace irin siga kamal....amma kasani da izinin allah sai kayi kuka da hawayenka yadda ka tozartani kacimu. Zarafi sai kaima anci maka naka kamal....matukar baka aureniba bazan taba yafe maka ba duniya da lahira kuma bazan taba sonka ba natsaneka"bata karasa maganar ba ya watsa mata mari ta kara dagowa ta kara mata ta dayan side din cikin rawae jiki a fusace ya nuna mata hanyar fita "fitarmun a gida tunda bada ubanki muka hada kudi muka sai gidan ba karuwa"...
Wata irin kara ta kwalla tana gunjin kuka ta mike ta ja gyalenta tana hada hanya tai habyar kofa har zata fita ta waigo ta kallesa idonta falll da hawaye ta kada kai ta fice....
Driving take tana kuka ta janyo wayarta karfe goma saura na dare,number pheey kawarta take lalube idonta ya rufe ta danna kiranta bugu daya ta dauka da tsokana ta dau wayar,jin shasshekar kukan bilkisu yasa ta dan furgita "lafiya kawata?menene?meke faruwa?naji kamar tuki kike a daren naj"
"Pheey ki shirya kitaho gidanmu idan kinsamu lokaci gobe in sanar dake wani sirri da nake boyewa zan sanar dake dik abinda ke faruwa da abinda nayi"tana kuka take maganar...
Jimm kadan pheey tayi "toh kawata insha allah but sorry to say gobe zamuje bichi kanin abbanmu ya rasu zamu dan kwana biyu saboda zamu taho da iyalansa dama inataso inkiraki nabari da safe in sanar miki amma insha allahu da mundawo zamu tattauna amma ki kwantarmun da hankalinki zan kiraki idan kinje gida muyi magana"
Gyada mata kai tayi kamar tana ganinta "toh allah ya dawo daku lafiya" ta datse wayar ta maida hankaki kan tukin da takeyi hannunta har rawa yake...
*********
Kallon agogo ummah tayi ta dubi abdul dake zaune tun bayan fitarta ya shigo "kayi hakuri abdulhrahman kaji har yanzun bata shigo ba,fatana dai allah yasa lafiya dan naga dare ya soma yi ko zakaje gida"
Fuskarsa dauke da damuwa ya dan kalli ummah ya sunkuyar da kai "zan jirata ummah"
"Laaaaa kaji horn din motarta ma kamar gata nan ta dawo"ummah ta mike ta leka window hasken fitilar motar billy take hangowa daga can wajen gate tana kokarin shigowa....
********
Sintiri yakeyi a cikin parlorn sa tun bayan fitarta,sosai yakejin wani irin haushi a zuciyarta dangane da billy tama gama rainasa wallahi tunda har ta iya takowa gidansa don ta rokesa ya aureta,to shi ko mata sun kare a duniya bejin zai auri bilkisu wallahi,tazo ta bata masa mood dinsa,har Tana iya fada masa zata fallasa abinda yake mata barazana dashi?lallai ma yarinyar nan ya rika zaiyi maganinta nasan ta inda zan bullo mata saina koya mata hankali saitaji ko sunana taji me irinsa saitaji tsanarsa....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/13, 2:25 PM] My Airtel: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*16*
"Bilkisu lafiya naganki haka?meyake faruwa ko barayi ne suka tareki?"shiru tayi kamar bazatace komi ba saboda batason ummah ta fahimci wani abu yasa wata karya ta fado mata "ummah na wallahi na fito pharmacy ne nayo gaba wasu suka sha gabana da mashin,nai kokarin kauce musu amma sukai ta bina sai kawai nayi parking motata a gefen hanya shine suka bude motar suka nunamin wuka sukace inbasu kudi da waya,na mika musu wayata nace banida kudi a hannuna sai waya shine fa daya ya mareni"..mikewa ummah tayi cikin fusata take dubanta "ya mareki?har sunkai matsayin da zasu saka hannu a fuskar ki bilkisu yan wani unguwa ne?"
Ganin yadda ummah ta fusata yasa bilkisu tadan tsorata,ga kanta da yake sara mata sai kawai ta yatsina fuska"karki damu ummah na bada report wajen yan sanda na bada order akama dik saurayin da aka gani a wanan sashen"...juyawa tayi kafin ummah tayi magana ta dubi abdul suka hada ido kallo daya yayi mata jikinsa yayi sanyi hango shacin hoton yatsu a farar fuskarta,sanan kwayar idonta ta sanar masa da dik abinda ta fadawa ummah tsarata kawai tayi ba gaskiya ta fada ba,furzar da iskar bakinsa yayi ya kashe mata ido ya mike "ummah ni zan koma dare yayi"
"Abdul har zaka koma?aiko nagode da gaisuwa sosai ya dace ka kawomin zainab inganta inajin labarinta wajen bilkisu na"yar dariya yayi ya sosa keya "zaa kawota ummah"yayi gaba bilkisu ta take masa baya har harabar gidansu daya wadatu da hasken fitilu ko ina bakajin komi sai kukan tsuntsayen dake bishiyoyin fruit na gidansu,wani waje sukaiwa kansu masauki jikin wasu flowers masu kamshi,tunda suka tsaya yake kallonta kallon tuhuma,hakan ne yasa tayi ajiyar zuciya ta dubesa a sanyaye "nasan cewa kallon tuhuma kakemun domin ina ganin rashim yarda da kalamaina a kwayar idonka habeeby hakan ne banaso hankalin ummah ya tashi har ta fahimci wani abu dangane dani dikda kai din ma bakasan komi ba"
"Nadade da fahimtar akwai wata boyayyar damuwa dake lullube cikin zuciyarki da bakim kyalle,amma ya dace ko bayyana mun ita domin inzama haske a rayuwarki bilkisu, bakisan yadda soyayyarki taimun kawanya ta mamayemun zuciyaba da baki horar dani ba ta hanyar jefa kanki cikin damuwa ba da hakan zai iyayi miki illa ko barazana da rayuwarki"
"Nasan kana sona ya abdul kuma nima ina sonka inaji a jikina kaidin haskene ga al'amura na kaine fitilar da zata haska duhun dake cikin rayuwata,ba na kasa sakin jiki da soyayyarka bane amma inaso kadan karamin lokaci inajin sonka a jinin jikina inajin kaidin wata kyautace daga allah zuwa gareni"hawaye sun wanke mata fuska kafin ta karasa maganar amma idonta cikin nasa take maganar,shima kuma kallon nata yakeyi cikin tausayawa da tsananin kaunarta dake azalzalarsa a rai....sassanyar ajiyar zuciya ya sauke "is ok bitty na yarda dake amma ki daina hawayen dan hakan zai iya haifarmun da rashin natsuwa koda naje gida zan iya kasa runtsawa sweetheart"murmushi tayi wanda iyakarsa labbanta sanan ta share hawayen daya bata mata fuska ta sauke masa kyakkyawan murmushi "nadaina habeeby"
"Good girl idan kika sake zuwa zanyi cikin dare inyi miki bulalar soyayya"hararsa tayi sanan suka cigaba da hirarsu cike da nishadi abdul yake kokarin kwantar mata da hankali can cikin kasan zuciyarta tamkar ansa mata garwashin wuta haka takeji amma daurewa kawai take gudun yaji haushinta....
***********Bayan wasu kwanaki.....
Tun bayan rabuwarsu da kamal Bata sake ganinsa ba bata kuma sake nemansa ba kuma hakan da yayi mata besa ta ji rashin son bukatar da taje masa dashi ba domin ta gwammaci wulakancinsa da wulakancin da mijin aurenta zaiyi mata idan ya tarar da ita a hakan,sosai bilkisu tayi muguwar ramar da kashin wuyanta suka firfito manyan idanuwanta suka kara girma sai tsawo da hancinta ya karayi tafe take cikin yauki da yangar nan tata da sarautarta wadda a jininta ne tafiyar kasaita da yanga,tunda ta nufosa yake kallon surarta da kyawu irin nata hakan yasa abdul ya lumshe ido ya bude ya ambata a fili fatabarakallahu ahsanal khaliqeeen....ya ilahi bilkisu tubarkalla,ganin bakinsa na motsi yasa tana karasawa tadan hararesa" kaidawa kake magana kuma naga kai kadai ne a wajen nan sai earpiece dake kunnenka?" Yar dariya yayi cike da nishadi ya kashe mata ido yana cigaba da yi mata murmushin nan nasa me tsada wanda yake kara narkar mata da zuciya cikin shagwaba tace "kodai budurwa kake magana da ita ta wata, wacece takeson yimun kutse a fadar mulki na?"
Dariya yayi sosai yace "ummm kaji masu fadar mulki ashe fadar mulki gareki baki kaini kin nadani sarauta ba a cikinta?"cikin sigar tsokana yake maganar yana kallon yadda ta hada ranta..."banida fadar data wuce fadar dake shimfide a zuciyarka inda na shuka bishiyar soyayyata tayi rassa da jijiyoyi yasa nake gudun wata tsuntsuwa can daga wani waje tai masauki a wanan fadar harta zuba sheka"...dariya abdul ya fashe dashi yanajin wani dadi a zuciyarsa yadda ta saki jiki dashi suke gudanar da soyayya ga wata shakuwa da yayi da ita..."kin manta bishiyar taki tsuntsaye biyu basu iya zama jikinta saida izininki?kece fa sarauniyar bishiyar kece keda yayan itattuwan dake jikin bishiyar dole saida izininki zaa tsunkesu balle wani yazo ya shiga inuwarta"...farim ciki ne ya lullubeta sanan ta rufe fuskarta cike da kunya shima kansa dariya yake,juyawa tayi kamar me duba wani abu daga nesa ta hango ummah tasha leshi na alfarma tana dube dube da alamar ita take nema "laaaa ya abdul na mance fita zamuyi nida ummah zamuje unguwa wajen shirye shiryen bikin wani family friend dinmu yaron abokin abbah na ne wlhy ni taketa jira tuntuni na banu"yadda take maganar kadai ke Burgesa ya kafe karamin bakinta da ido harta gama sanan yace "tohhh idan kin gagara zaman can ki kirani inzo indaukoku keda ummah in dawo daku yanzun ma muje nine zan kaiku "
"Ah ah yaayah kabari kawai bakazo da shiri ba kuma zamu biya gidan kawar ummah na shiyasa amma idan zamu dawo zan kiraka ka dauko mu"
Murmushi yayi sanan sukai sallama a hankali ya bude gate din yana daga mata hannu itama shi take dagawa bakinta yaki rufuwa...
**********
Zazzaune suke a parlor ya shigo sanye da blue shirt kansa babu hula ya danyi kiba ya kara fari,kallonsa tayi ta kauda kanta gabanta na faduwa,...zubewa yayi a gaban ummah "ummah na ina yini"
"Lafiya lau dan ummah ya shirye shirye?"
Sunkuyar da kansa yayi cike da kunya ya kasa amsa mata,sanin kamal din me kunya ne yasa ummah tai dariya"ammah ya dace akawomin surukata gida in ganta,koda yake abu yazo tunda gashi yau saura kwana biyu a daura aure bayan biki a kawomin ita inganta inyi mata tawa kyautar ta musamman"
Momy ta amshe zancen da "umm umm hajiya wato dai kinaji da surukar nan taki ko?to nima kwanan nan yata bilki zata kawomin suruki na wanan biki nawa ne"duka suka sa dariya,maman su khairee ta karbe zancen da "aini dik na dauka yar gida zamuyi da yata ashe wata zai dauko mana to allah yasa albarka"
Kauda zancen momy tayi dan ta fahimci inda maganar hajiya ta dosa da bilkisu take nufi itama taso hakan to hali irin na dan yau....
*********
"Hmmm kinsan me wai sir kamal aure zaiyi?yanzun haka shirye shiryen aurensa akeyi shiyasa kikaga yayi mana covering komi saboda zai angwance da yar alhaji auwal ahalussunnah wanan yar tasa zahra"
Dafe kirji wadda akebawa labari tayi jin an ambaci sunan Zahra,badai zahrah yar alhaji auwal ba malamin addinin nan dayayi fice a garin nan yarinyar dake claiming ustazanci amma tantiriyar yar iska ce har lakabi ake mata da Zahra bat da kama...."ke ina baki labari kinyi shiru aiko sir kamal yayi saa dan ni na dauka ma tsanar bilkisu da yayi soyayyace ashe bakomi tsakaninsu yadda nayi bincike ma yar uwarsa ce"
Itadai shiru tayi domin tunaninta ya tafi ga ko jiya daddare sun hadu a club da zahra anata ihun tazo bankwana ashe aure zatayi auren ma salihin mutum kamar sir kamal....zahra baa iskanci kadai ta tsaya ba zahra shedaniya ce allah yasa kada tai sanadiyyar rugujewar farin cikin gidansu....
***********
Washe gari ana gobe biki tun safe su billy suke gidan tana fakon shigowarsa cikin gidan dan tanason ganinsa a karo na biyu dan har yanzun bata makara ba,kamar gilmawar walkiya ta hangi wucewarsa cikin sashensa daga dayan bangaren da zai zauna da matarsa inda aka gyara akai gini kerarre tamkar baa kasar nan ba,kallon nawal tayi da taketa faman fifita lalle da akai mata "baby sis ina zuwa bari inga ya kamal yanzun zan dawo"gyada mata kai nawal tayi tabi ta da kallo tana murmushi.
Wucewarta kenan momy ta fito dauke da tray da soyayyun kaji ciki dankam "nawal ina anty billyn taku tazo ta hada mana pepe meat din nan"
"Taje wajen ya kamal wai"
"Wajen kamal kuma?"
"Ehh momy"shiru momy tayi jikinta a sanyaye take duban nawal da itama akwai magana a bakinta a iya fahimtarta tamkar akwai damuwa a tattare da antyn tasu....
**********
"Zahra ki tabbatar kin matsa wanan abun danayo miki domin tafiyayya yake daga agadaz,shi ake cewa tantanin budurci,shine yake hade mace wanan rariyar ta budurci ta tsuro babu me gane kinyi yawon duniya,amma kin tabbatar mun bazaku hadu da tj ba yau balle ya batamun aiki?"dan turo baki zahra tayi "ehh toh da dai zamuyi na bankwana anty"babu kunya ba tsoron allah zahra ke wanan maganar tana kallon antyn tata, itama batare da wata shakka ba tace to kije amma ki dawo da wuri ajwai jijjibi da zaakawo yau zaki cinyeshi sanan akwai turaruka na tsugnno da zakiyiyyisu yau yadda zai rikice ma bazai gane yadda kiken ba"tsalle zahra tayi ta rungume anty bina tai mata kiss a kumatu "i love you sis am proud of u Being my lovely sister"yar dariya anty binafa tayi ta mike "kibani key don zanje gida taya su ammy aiki zandawo da wuri kema ki dawo da wuri please"
"Angama antyna allah dai yaja kwana"suka kwashe da dariya....
********
"Wai ke mayyar ina ce da nafada miki bazan aureki ba koda gida da mota da kudi da jari wanda zanci dake ko babu kwanciyar aure bazan taba auranki ba bilkisu ki sararawa rayuwata ki kyaleni tun banyi miki rashin mituncin da zakice banida imani ba,tunban wulakanta rayuwarki ba"tsugunnawa tayi akan gwiwoyinta "ya kamal ka ceci rayuwata ka ceci mutunci na dan allah ka ceci martabar iyayena a garin nan ka lullubamin sutura ka aureni wlhy zan zauna dakai ya kamal"sa kafa yayi ya hambareta ta fadi kasa ta dafe gefen cikinta tana wani irin kuka wata azaba ta ziyarci wajen take taji numfashinta kamar zai dauke hawaye ko sai ambaliya yake a fuskarta ko kallonta beyi ba ya dau makullin motarsa yana waya da hafeez abokinsa ya fice.....
Ta dade a dakin sanan ta rarrafa ta fito dakyar hannunta dafe da gefen cikinta tai kicibis da afee tace ta dauko mata jakarta da makullin mota zata fita ta dawo cikin sauri ta kawo mata ta karasa dakyar ta tada motarta sanan ta kira wayar pheey da taga miss call dinta "pheey i just saw your miss call ya "
"Banza ina unguwarku naje saloon yanzun haka angama jiya muka dawo ina hanyar gidanku"jan numfadhi billy tayi sabbin hawaye suka zubo mata ta wani bangaren kuwa farin ciki ne ya lullubeta yau zata sanarwa da babbar aminiyarta labarinta dama gidansu tai niyyar zuwa sai kawai ta karya akalar motarta tayi gidansu,kusan a tare suka iso da pheey suka shige ta fito dafe da gefen cikinta da ya dan rage mata zugi fuskarta sharbe da hawaye suka shige can sashen billy suka isa sukai masauki a dakin pheey ta nemi gefen gado ta zauna tana bin billy da kallo ta kasa magana...itako kallon pheey tayi ido cikin ido tace "doctor kamal ya cuceni ya cuci rayuwata ya wulakantani ya gama da rayuwata banida sauran amfani"cikin rashin fahimta pheey tace "me kuma ya hadaki da sir kamal keda ko magana bakuyi?"
Cikin takaici ta cije lebenta wasu sababbin hawaye na gudu tace "A fili babu abinda yake hadani dashi wabda mutane suka sani a zahiri kuma zancen yasha banban nafisa yau zan fede miki biri har wutsiya"
Sosai mamaki ya lullube nafisa tace a sanyaye "inajinki kawata"...murmushi mai ciwo tayi "nafisa kinsan dai ni wacece kinsan kuma takena,kinsan waye ubana a garinnan,kinsan dukiyar da na mallaka kinsan gata irin wanda nakedashi wajen uwa da uba kin kuma san motoci wanda nake hawa kinsan arziki irin na mahaifina kinsan nidin wacece"hawaye na gudu a fuskarta take maganar cike da izzar ta...nafisa gabanta ya fadi fargabar abinda zataji take yasa tace "hakane inajinki"...juyowa tayi ta zauna gefenta ta ruko hannunta sanan ta sauke ajiyar zuciya da numfashi mai karfi........
0 comments:
Post a Comment