Cije lebenta tayi memakon ta tashi tai wanka tai sallah,sai kawai ta fada kan gado ta saki wani sabon kuka,ga ruwa dake bulbula a jikinta saboda yadda kullum sai ta hada maganin mata da madara tasha don ta burgesa amma kullum bata ganin alamar ma yana gamsuwa da ita,kallon agogo tayi bakwai saura kwata da sauri ta duro daga gadon ya fada toilet ta sakarwa kanta ruwa tana wankan tana hawaye tana saka da warwarar abinda zatayi dikda Anty bina tace tasameta haka ta fito jiki babu kwari sauri sauri ta gabatar da sallah ta zura Riga mai siririn hannu iya cinyarta ta saki gashinta ya karasa bushewa ta fada kitchen....
Kamshin turare yake zubawa yayi kyau iya kyau domin kayan da kamal yasa sun amshi jikinsa ya fito a ango sak saidai fuskarsa babu walwal yana kokarin sanya hula tajiyo motsin fitowarsa tai saurin fitowa daga kitchen har tana cin tuntube,kallon yadda yake daukar ido ta tsaya yi yayi kyau sosai wani kishi ne ya taso mata, ganin bashi da niyyar kulata yasa ta hadiyi wani mugun miyau "barka da tashi ina kwana?"ko kallonta beyi ba ya basar,kamar bazai amsa ba sai kuma har ta mance ta gaishesa ya amsa da "lafiya"...yasa kai da niyyar ficewa ta danyi gyaran murya "ammm.... sweetttt ina zakaje ga breakfast nan inata kokarin karasawa na gama ma ka tsaya kai breakfast ko?"..kallon da ya watso mata yasa yayi mata kwarjini ta sunkuyar da kai "aka ce miki da yunwa na kwana?koko ni nasaki ki tashi kiyimun breakfast ne?ko karuwancin zaki gwadamun da safe ne?wato kinsamun abinda zanci inji ina shaawarki kamar yadda jiya nake zargin kinsamun kwaya a hollandia ko?"wani kallo yake mata mai cike da tsana da kyama,har ta tsargu ta shiga kallon jikinta sanan ta dago idonta da sukai jajir suka cicciko da hawaye "haba kamal wanan kalmar da kake jifana da ita a matsayina na matarka ta sunnah be dace ba zaka bata aurenka,kuma bazakaji dadi a kira daya daga cikin kannenka da karuwa ba"
"Ke zahra"ya kira sunanta cikin daga murya da karaji "karki kuskura ki sako kannena a cikin wanan maganar domin kaf zuriar gidanmu data danginmu babu karuwai babu wadanda suke amfani da hijabi suna cin zarafin addini,babu wanda suke anfani da wata fuskar saboda su dau hankalin jamaa kinaji ko idan kika sake kiran yan uwana da karuwa wallahi saina datse miki harshe"..
Zaro ido tayi gabanta na faduwa,hadiye maganar da tai shirinyi tai sai kawai tace masa "zan fita zanje ingaida ammi da abby zan je inyiwa su anty binafa bangajiya"
"Kina iya zuwa idan kin fita zaki iya biyawa wajen kwartayen naki su biya miki bukata domin ni na gama wata hulda data danganci haka dake inajin tsoro karma in dau ciwo"ya ja tsaki ya fice cike da takaicin bata masa lokaci da tayi....sashensu momy ya nufa .
Zaune tayi ta rasa abinda keyi mata dadi sam ta mance da dankali da ta zuba cikin mai saida ta soma jin kauri ta zabura ta shiga kitchen din a tsorace.....
**********
Gyara zama billy tayi cikin motar tana kare masa kallo,ya dan rame mata daga jiya zuwa yau sanan kallo daya zakai masa kasan yana cikin danuwa,kallonsa take tanajin wani iri a jikinta dik yadda ta kwana da mararin soyayyarsa?da kafin safe soyayyarsa ta lullube ilahirin jikinta da bargo ta mata mayafi ga yadda ta kosa tai tozali da sanyin idaniyarta saita ganshi a haka?,shiko dik kallon da take masa yana kallonta ta gefen ido dikda driving yake sai yaji babu dadi sai kawai ya basar ya kalle ta ya kashe mata ido "yau sarauta akeji ranki ya dade?inata jira a gaisheni inji sassanyar muryar nan me riki tani?"
Turo baki tayi kamar zatai kuka "to ba kai bane tunda na shigo ma ba ka kalleni ba balle ka yaba da kyaun da nayi?dik kokarin da nakeyi in hada ido da farin cikin rayuwata?fitilar dake haskemun duhun da ya dade cikin rayuwata?
Yar dariya yayi "ohhh billy rigima my baby...am sorry my princess good morning LOML"yace hade da sakin tsadadden murmushinsa..."morning my blood how was ur nyt"tace cike da nishadi... kashe mata ido yayi "alhamdulillahi,yanzun idan mun shiga school din a ina zan saukeki?"
"Parking space zamuje ka saukeni sanan ka rakani har kofar inda zamuyi leactures kaji?"kallonta yayi yana karewa fuskarta kallo yadda tai kicinkicin da fuska ga shagwaba da take kokarin yi sai ya fashe mata da dariya daidai nan suka karya kwana zuwa gate din makarantar...."annnnn kanamun dariya ko?"
Kai hannu yayi zai buge bakin data turo ta kauce tana dariya sosai takejin kanta cikin wani irin nishadi.....suna shiga motar kamal na shiga, shigowar hadaddun motoci guda biyu cikin makarantar yasa yadan dau hankalin dandazon daliban dake harabar makarantar dikda wasu samm hankalinsu baya waje,...can nesa sukai parking kamal kuwa wajen inda ya saba parking yayi ya fito hannunsa dauke da tulin littafai da jakar laptop dinsa,...suma fitowa sukai a tare suna dariya juyowan da Abdul zaiyi suka hada ido da kamal....itako billy dariya take tana zuba shagwaba shima abdul biye mata yake...
Tafe suke Kamal na biye dasu a baya "hubby nifa kai zaka dawo ka daukeni kaji?kaga bazan hau motar haya ba tunda kai ka kawoni kaga ai kai ya dace kazo ka dauki matarka"
Murmushi abdul yayi "tou ai dolene in dau abuna kada ki hadu da wasu fataken da zasuyi gaba dake suje su cutarmun dake?"yayi maganar da satar kallon ta,jikinta yayi darrrr nan da nan ta danyi sanyi kodai kamal ya sanar dashi wani abu dangane da ita ne?bata gama tambayar kanta ba ta tsaya cakkk kamal ya cin musu "bilkisu bala take dis books to the hall am coming"ya bata umarni cike da isa da izza .....murmushin mugunta tayi kawai batare da tace komi ba ta karba,dik tunaninsa bazata karba ba....sai ya canja hanya har hall din abdul ya raka ta kowa kallonsu take cike da shaawa ko baa fada maka ba ansam masoya ne.. pheey ce ta karaso suka gaisa da abdul ya dubi billy ya kashe mata ido "ki kulamun da kanki sai na dawo"ta gyada masa kai hade da binsa da kallo cike da soyayya da begensa....zunguro ta pheey tayi "billy ina kika samo hadadden guy haka?wai kinga yadda kuka haska mutane cikin makarantar nan kuwa kowa sai kallonku yake"
Dukan wasa billy takai mata "kaji kawata sarkin zugi to shine abdulhrahman da nake baki labarinsa wallahi mugun sonsa nake,amma fa some times muryarsa ta kanyi mum gizo da azzalumin daya rabani da martaba ta"sai kuma tai kwalkwal zatai kuka..."come on my friend wanan laanannen ko a lahira bana fatan Allah ya hadaku saidai ya hadaku don ya saka miki abinda kikaimai ko kim yafe masa?"
"Ko uwarmu daya uban mu daya bazan taba yafe masa na nafeesah harabada"zatai kuka pheey taja hannunta hango kamal da tayi yana tahowa "muje ga azzalumin can can zuwa"...juyawa bilkisu tayi suka hada ido ta maida kanta tana biye da kawarta cike da takunta mai kama da yanga....
Sosai class mates dinta sukai mamakin ganinta da littafansa ta dire a table sanan ta koma tana takunta ta karasa inda kawarta ke zaune ta zauna gefenta,ta mika hannu ta karbo hanan jaririyar da fatima muazu amir ta haifa wata class mate dinsu maman abdallah...."maman abdallah amma fa abdallah yafi hanan kyau mudai team dinsa muke"murmushi fatima tayi "kindaisan mutuminki ke leactures yanzun zai dagaki ,ga mamakin maman abdallah sai ce mata tayi "da nafi kowa farim ciki".....karaf sai a kunnen kamal da dik wani motsinta akan idonsa take bakinta ke mugun bashi shaawah ta cikin glass be taba karewa karamin pink lips dinta ido ba sai yau "bilkisu bala you are disturbing my class please get out you and your colleague "murmushi maman abdallah tayi tasan zaa rina sai kawai ta kwashi takaddunta tai gaba bikkisu ta take mata baya da hanan a kafadarta sukaiwa kansu masauki a bakin kofa....
Bayan ya gama leactures ya kalli kofar ya yafito bilkisu da hannu ta shigo fuskarta a daure wanan karon itama ta kwafa glass dinta a ido sai kawai ya mika mata takaddun daya bata dazun yace ta bishi office dashi...wani kululun bakim ciki ya tsaya mata a wuya lallai kamal wani sabon rainin wayau ya dawo dashi daga hutun angwanci?tabdijan aiko indai akan massage din da yayi mata jiya daddarene zasu kwashe....
*********
Shiru zahra tayi tana sauraren antynta har ta gama koro mata bayanin shawarar da ta bata,motsin kirki zahra ta kasa sai faduwar gaba da take faman yi fatt fatt zuciyarta na ci gaba da bugawa cike da tsananin tsoro da fargaba ta nisa tace "anty,yanzun kina ganin hakan shi ya dace?wallahi tsoro nakeji"
Hararta anty binafa tayi "to sokuwa zauna ke yana kiranki da karuwa kinji?ai ki kwantar da kanki kada ki nuna masa komi ki bullo masa ta bayan gida kawai ki dasa masa ciwon da bazai warke ba har karshen rayuwarsa kuma hakan zaisa yayi laushi sosai"
"Allah Anty?"
Gyada mata kai Anty binafa tayi hade da bata kwarin gwiwa ta cigaba da dasa mata bama baman da zatai anfani dashi wajen karya kadarin kamal cikin sauki...murmushin keta zahra tayi ta share hawayenta "Antyna ke bala'i ce"
"Aini haushi kika bani wallahi dik wayonki?dik yawon barikinki ki kasa ramawa?mtsww kinma ban haushi wallahi sakarya kawai"
Murmushi zahra tayi sai lokacin ta share hawayenta ta saki jiki suka cigaba da hira tana kissima yanda zata bullowa kamal me kiranta da suna KARUWA!!!
*********
Kusan minti arbain da shigarsa office babu bilkisu babu dalilinta,minti minti yakanji kamar motsin zaa shigo amma yaji shiru yanzun haka ya yanke shawarar kiran wayarta kenan ta turo kofar ta shigo idonta sanye da bakin glass fuskarta babu annuri sallamar ma a ciki tayi ta,cike da yanga ta karaso gaban table ta dire masa da niyyar ficewa ya dakatar da ita "na tura miki tex jiya daddare akan idan kinzo kizo inason magana dake a office dina,da na ganki da saurayinki nai miki dabara na baki books dina na nufi office ko zaki biyoni baki biyoni ba....hmmm billy kenan wato yanzun kinaso ki rinkamun taurin kai ko?kina ganin kamar bazan iya watsaki a duniya ba kenan?"
Tunda ya soma maganar take sauraronsa tana karewa yadda yake maganar kallo cikin izza da isa yakeyi tamkar wani basarake amma a kwayar idonsa tana iya gano akwai sanyi a lamarinsa,hakan yasa ta tattari dik wata jarumta tata dikda kwarjinin da yayi mata amma be hanata juya masa baya ta soma magana ba "kamal kenan,da zaka fidda video din nan a yanzun kafin in fita office din nan da sai nafi kowa farin ciki da hakan,koba komi zaka saukemun wani nauyi wanda ya dace insauke shi na kasa bismillah ga fili ga mai doki zaka iya turawa,idan kayi hakan dan ka rabani da farin ciki ka habani aure ka rabani da masoyina fine is ok dama nikadai nazo duniyar ba kuma lallai sainayi rayuwar jin Dadi a cikinta ba,amma maganar kayi zina dani ka gama harabada,ka gama hada jiki dani na tsaneka wallahi"Tana maganar muryarta na rawa ta dake ta shanye hawayen dake kokari ya kubce Mata ta juyi ta kallesa yadda yake juyi a kujara yana latsa wata ta fice a office din ta bugo masa kofa.....
Bugun table din yayi ya mike tsaye ya furzar da iska mai zafin gaske cike da tashin hankali ya shiga kaiwa da komowa cikin office din amon muryarta kawai keyi masa yawo a kunne zuciyarsa nayi masa wani irin lugude.....bilkisu ke fada masa wadanan kalaman kamar a mafarki?meyasa yayi kuskurene?yayi kuskure da bai amsa tayin ta ba na aurenta kodan ya tozartata tozarci da kaskanci?me zuciyarsa ke kokarinyi masa na rashin adalci?kardai soyayyar bilkisu ce takeson dawowa sabuwa cikin zucuyarsa?...runtse idonsa yayi ya budesu yana bin inda ta tsaya da kallo ko zai kara ganinta.....wani abu keyi masa yawo a jikinsa da mararsa....ga shaawarta dake barazana da rayuwarsa yakejin zai iya mutuwa idan be kusance ta ba, yakai hannunsa kan dick dinsa yaji yadda ta tsaya kyammmmm innahlillahi wa innah ilaihi rajiun meyake shirin faruwa dani yake tambayar kansa....
*********
Suna tare da abdul taga tsayawar motarsa cikin gidansu ya bude ya rufe hannunsa rike da waya ya nufi cikin gidan kallon abdulhrahman tayi "muje ostrich inason cake da bread ba sai na Shiga gida ba am ok a hakan"
"Your wish is my command my luv"ya kashe mata ido ta sakar masa murmushi....
Sosai ummah tayi farin ciki da zuwansa "aiko bilkisu tana tare da abdulhrahman kila ma taga zuwanka bari in aika amina ta kira ta ku gaisa ya amarya da su hajiyar?"
"Lafiya lau ummah tace in gaisheki itama zahrar jibi zan kawo miki ita ta wuni a nan"
Amina ce ta shigo zata wuce kitchen da cups din da ta dakko inda su bilkisu suka zauna "amina jeki kira bilkisu tazo su gaisa da kamal"
"Sun fita da uncle abdul yanzun nan wai zata siyo abu a wani waje"...kamal najin haka yasan cewar ta ganshi plan ne wanan tayi sai kawai ya cije lebe "ummah kada ki damu bari ai zan sake dawowa yanzun ma daga wajen aiki nake "
"Toh kamal a gaidamun da amarya sai tazo"
"Toh ummah"ya mike jiki babu kwari ya fice a parlorn....
Driving yake jikinsa na rawa tabbas dole ne ya dau mataki akan yarinyar nan da wanan yaron da takeso yake zuwa wajenta dikda yana masa kallom sani amma dai zai bincika ko dan gidan uban waye sai ya rabata dashi....
Da wanan tunanin ya iso gida cike da takaici dik gaisuwar da maaikatan gidan keyi masa beko san sunayi ba ya shiga parlorn momynsa tana ganinsa gabanta ya fadi "kamal lafiya dai na ganka haka?"...shafa kansa yayi yana rike da hularsa ya sakar mata murmushi sai lokacin ya lura da zahra dake koyawa su afee karatun kurani a parlorn....beko san da ita ba dik yadda take bin sa da kallo momy na lura da ita saita mike ta basu waje aiko tana barin parlorn tace "barka da dawowa"ganinsu nawal sun tsuro masa ido ya amsa kawai ya fice ta mike ta take masa baya....
**********
Karfe tara na dare daddy ne a parlorn su bilkisu yana tambayarta inda ta samo abdul ta yarda dashi ta damka masa dukiyarta, cike da natsuwa tai masa bayani tun daga farkon haduwarsu har karshe saida ta gama ya bata umarni da ta turoshi yazo gida ya sameshi yanason ganawa dashi.....
Dago fuska tayi a furgice ta dubi daddy sanan ta sadda kanta kasa "toh daddy insha allahu"gabanta ya shiga faduwa haka kawai jikinta ya kama rawa ummah na lura da yanayinta tasan akwai matsala.....
**********
Da asuba Abdul ya yankewa kansa hukunci haka kawai ya ciro kayan da rabon daya sasu tun ranar da yayi mata fyade yasa su,haka kawai yakejin faduwar gaba ya ciro hular mask din da yasa ya rike a hannunsa ya fito tamkar mara lafiya rike da makullin motarsa a daki ya samu innah a tsaitsaye ya gaisheta ya fice ya shiga motarsa ya nufi gidan dan ya dauketa zuwa makaranta.....
A kofar gidan ya tsaya ya juya baya ya kira wayarta da sauri ta fito yana hannunta rike da littafai tana duba lokaci don tayi latti tana karasowa ta gansa gabanta ya fadi ta watsar da takaddun dake hannunta da niyyar kwasawa a guje sai kuma taja ta tsaya tana kallonsa shima kallonta yake yana sanye da mask zuciyarsa tankar ta faso kirji ta fito....hawaye ne ya wanke fuskarta "kar kacemun kazo kofar gidanmu ka daukeni kaimun fyade a karo na biyu,ko kazo ne ka tonamun asiri a gaban masoyina ka sanar dashi batamun rayuwa da kayi?azzalumi na tsaneka.....na tsane..."maganarta ce ta makale da ya zare mask din tai tozali da Abdul....ja da baya tayi gabanta na tsananin faduwa idonsa ya rikide sakkk irin na azzalumin da yayi mata fyade....hawaye ya cigaba da gudu a fuskarta "waye ya ara maka kayan nan kazo kai bankwana dani ka shaidamun ka daina sona?ko an nuna maka video din da akaimun tsirara akai amfani dani ne?na tsani dik wanda yaci amanata abdul kacemun bazaka rabu dani ba wallahi fyade sukaimun"ta durkushe a kasa tana kuka ...hawayen yakeyi bata lura da hakan ba muryarsa ta tsinkayo yana fadin "nine nayi miki fyade"...kamar ya dasa mata mashi taji ta zabura ta mike tana ja da baya hannunta rike da kanta ...
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
SLIMZY✍🏻[6/30, 2:01 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*26*
Kallon da ummah ke jifanta dashi yasa hankalinta ya kara mummunan tashi, irin yadda ummah ta kafeta da wani irin kallo jikinta na rawa tamkar mazari ya kara rudawa bilkisu ciki tayi wanibirin zabura tana jan jiki da baya zuwa karshen gadon,ba bilkisu ce kadai ta furgita ba har nafeesa tayi mugun furgici da ganin yadda fuskar ta sauya lokaci daya gumi kawai ke karyo mata,daga bilkisu har nafeesah ido waje suke kallon yadda hawaye ke gudu a idon ummah kamar famfo,kirjinta kuwa sama da kasa yake,kallon ummah kadai zakai idonka ya ciko da hawaye a kwayar idonta zaka hango tsantsar karaya da tashin hankali.....nufo bilkisu tayi ta fizgota cikin zafin rai "bilkisu?menakeji kina fada? Allah yasa abinda naji da kunnena kina furtawa wasa kikeyi ba gaskiya ba ki fadamun?waye kikace yayi miki fyade?"cikin daga murya tai maganar,da sauri nafeesa tasa hannu ta toshe kunnuwanta idanuwanta na ambaliya da hawaye.
Shake bilkisu ummah tayi idonta suka kakkafe hawaye na gudu a fuskokinsu duka su biyu "gwara in kasheki bilkisu,gwara insan nice nai sanadiyyar mutuwarki,kifadamun gaskiya bilkisu waye yayi miki fyade?karkicemun abdulhrahman ne yayi miki fyade yayi sanadiyyar kamuwarki da ciwon hanta"sassauta rukon tayi Mata da hannu daya,batai wata wata ba ta sharara mata mari....
Jikin bilkisu rawa yakeyi nan da nan ta kware ta soma tari saboda shakar da ummah tai mata,ganin ummah zata kashe bilkisu yasa nafeesa zamowa daga gadon ta zube a gaban ummah da gwiwoyinta biyu Tana kuka "ummah dan allah kiyi hakuri ki sassautawa bilkisu wanan hukuncin Dan Allah ummah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki zata fada miki gaskiya"ruko kafafuwan ummah nafeesa tayi Tana rokonta,dakyar ummah ta saki bilkisu taja da baya tai zaman yan bori a wajen ta fashe da kuka ta kama kanta tana kuka "kai cona nashiga uku ashe ina zaune ne cikin balai da masifa ban saniba,ashe an cuci marainiyar Allah amanar da alhaji bala ya barmun nakasa rikewa"
Zubewa bilkisu tayi akan gwiwoyinta ta ruko ummah "hakika nayi ganganci da rashin sanar miki da halin da nake ciki,ummah na ki gafarceni nayi hakan ne domin in kare martabar gidan nan da sunan mahaifina da baci a idon duniya yana kwance a kabarinsa,ummah kiyafemun boye miki halin da nake ciki da nayi amma yanzun zan sanar miki da ainihin hakin da nake ciki"....wasu sababbin hawaye ne suka zubo a idon bilkisu kallon juna suke ita da ummah cikin tashin hankali kuka sukeyi mai ban tausayi kallo daya zakai musu ka zubda hawaye...."hakika abdulhrahman shine yayi mun fyade ummah,yayimun fyade tun da dadewa ba yanzun ba,bantaba sanin shine ya rabani da martabata ba sai jiya yau ummah,dikda mafi yawan lokuta ina jun hakan a jikina,hakika na tsani azzalumin da yayimun fyade ummah amma sai Allah yasamun soyayyar abdulhrahman a cikin zuciyata ,a yau da nasani kuma naji dik duniya babu wanda na tsana kamarsa"
Jikin ummah ya kwashi rawa cikin kumfar baki da karaji tace "hakika bazan taba kyale wanan yaron Abdul ba saina tozarta sa saina wulakan tasa daga karshe saina sa ya karasa rayuwarsa a gidan prison,bazan taba kyale wanda yayi sanadiyyar lalata rayuwar yata daya tilo ba ko waye koda ciki daya muka fito kuwa"
Kallom juna bilkisu da nafeesa sukai,sanan ta maido da kallonta ga ummah,wani murmushi tayi mai ciwo ta kada kanta cike da tsananin takaici da kunar zuciya,dakyar ta hadiyi miyau mai daci "ummah na abdulhrahman so daya takkk yayi anfani dani,bashi kadai bane yayi sanadiyyar lalacewa ta ba ummah "
Wani irin kallo ummah ke jifan bilkisu dashi batare da tace komi ba kallonta takeyi tana neman karin bayani "ummah kamal dan uwana kamal danki da yayi aure shine ya maidani matarsa ta sunnah wajen biyan bukatarsa a dik lokacin da ya gadama dani ta hanyar yimun barazana da video din fyaden da abdul yayimun hakan yasa nake tunanin shida abdul suna da wata alak'a idan ba haka ba tayaya kamal kadai zai mallaki video din fyaden da akai mun?".....kuka bilkisu ta rushe dashi,ummah kuwa kallon bilkisu takeyi tamkar wawuya tunda ta soma kiran sunan kamal gabanta ya tsananta faduwa,take taji wani fitsari na kokarin kubuce mata,ta rasa wani irin yanayi take ciki a wanan lokacin?mamaki?al'ajabi kokuwa mafarki takeyi?rufe idonta tayi kusan minti goma sha biyar sanan ta budesu a hankali sunyi jajir gumi na karyo mata,dakin takebi da kallo tana adduar Allah yasa mafarki takeyi ta tashi a wanan lokacin.... Allah yasa ba gaskiya bane abinda kunnuwanta suke jiye mata a yanzu....dora kwayar idonta tayi akam bilkisu dake kan gwiwoyinta tun dazun...idanuwanta sun canja kala sunyi jajir baka ganin fari a idonta sai bakin daya hade da ja fuskarta tamkar ta shafa jar hoda .....bakin ummah na rawa take fadin "sanar dani abinda yake faruwa yata sanar dani komi kada ki boyemun ni mahaifiyarki ce tabbas ba abdulhrahman kadai ya dace in dau fansa akansa ba harda kamal,amma ta yaya kamal zai batawa kanwarsa rayuwa?tayaya kamal zaiyi haka?kamal daya kasance kamilin yaro kamal yaro mai biyayya da kunya da ibada hade da tausayin na kasa dashi?kamal yayanki fa dan aminin mahaifinki ya bata miki rayuwa? innalillahi wa innah ilaihi rajiun...."dakin ne ya shiga juyawa a idon ummah ta runtse idonta hawaye na gudu.....
"Kamal ba kamili bane ummah,dik suffofin da kika suffanta kamal dasu yana amfani dasu ne a fuskar jamaa amma can cikin zuciyarsa yafi firauna kafirci,kamal azzalumi ne,kamal bashida tausayi kamal mugu ne ummah na yanzun zan sanar dake ainihin abinda kw faruwa tsakanina da kamal dangane da yadda ya maidani tamkar matarsa"...idon ummah a rufe yake ji take tamkar zucuyarta zata fasa kirjinta ta fito,lallai lokaci yayi da zata gayyato jarumta ta rikide ta fuskanci wanan yakin da ya taso koda kuwa da jininta ne balle aminin mijinta ...
Kallon juna pheey sukai da billy,pheey ta share hawayenta ta gyadawa bilkisu kai tai mata alama da ta sanar da ummah komi kada ta boye mata,....cikin sanyin murya bilkisu ta fara labartawa ummah....
*********
Tunda abdulhrahman ya soma bawa innarsa lbarin abinda ke faruwa,ta sandare a zaune network din kanta gabaki daya ya dauke,duniyar ta shiga juya mata ta soma gani bibbiyu,da taimakon hasbunallahu wa niimal wakeel ta samu ta soma gani daidai....kukan zuci takeyi a zaune,wani irin tashin hankali ta tsinci kanta ciki,lallai abdulhrahman ya dauko musu masifar da Allah kadai zai yayyafa mata ruwan sanyi, Allah kadai ne zai cecesu daga halaka a cikin garin nan"abdulhrahman ka cuceni,ka cuci tarbiyar da na baka,wanan ba tarbiyyata bace abdulhrahman,dik wanda yace bazaibi maganar uwarsa ba dama haka take kasancewa dashi,gashi nan tun baakai ko ina ba asirinka ya tonu,baka da gaskiya baka kyautawa bikkisu ba ka cuci rayuwarta cuta ta harabada,ka keta mata haddi sanan ka manna mata mummunar cuta,wallahi kai ba dan halak bane"
Da sauri abdul ya kira sunan innah "innah....wallahi tallahi..m"be karasa ba ta daka masa uwar tsawar da saida ya saita kansa "daka ta mun mayaudari ma cuci wallahi bilkisu bazata taba yafe maka wanan abun da kayi mata ba harabada,kuma wallahi nima sai ka fuskanci fushi na domin nima babuni babu kai babu ruwanka Dani abdulhrahman kuma kasan abinda zaka fada a gaban hukuma,saboda ni babu ruwana kaji na fada maka"hawaye ya gangaro a idon innah,ta mike jiki a sanyaye ta fito ta shige dakinta.
Tana shiga zainab ta mike tsaye tana kallon innah,ganin innah tana hawaye yasa itama hawayenta suka karu cikin rawar murya ta shiga tambayar innar"innah... menene ya faru da yaayanmu meke faruwa innah?kifadamun dan allah inna kinji?wallahi na shiga damuwa, Allah yasa dai ba kama mana yayanmu zaaiba"
Tausayinta ya lullube innah ta fashe da kuka,rukota tayi bazata iya fada musu abinda dan uwan nasu yayi ba gudun kada raini ya shiga tsakaninsu saboda nan gaba,sai kawai ra rungume zainab tana kuka "ku kwantar da hankalinku kinji kuyi wa dan uwanku addua yana bukatar adduarku a halin yanzun amma kada ku matsa sai kunsan abinda yake faruwa"... rungumeta sosai tayi tana bubbuga bayanta tana shafa kahtat, shasshekar kuka kawai zainab keyi anya zata iya hakuri kuwa yau? Dole ne ta ziyarci anty bilkisu don tasan menene yake faruwa....
Kwantar da kai abdul yayi akan pillow hawaye na gudu a fuskarsa dafe kansa yayi dake sara masa,yanaso yayi kuka mai sauti ko zai samu sassauci a zuciyarsa amma ina....gashi bazai taba iya runtswa ba a daren yau matukar baiyi tozali da bilkisu sanyin idaniyarsa ba....
*********
Kuka sosai nawal takeyi jikinta na bari lokacin da maza biyu suka rirriketa wasu suka rirrike driver hade da sa masa wuka a wuya "motsi kadan Kayi zan afka ka lahira"cewar wanda ke rike da wukar....
Nawal cikin sassanyar muryarta da sautin kuka ta soma magana "bayin Allah don allah kada kuyi mana komi ku tausaya mana mu yara ne,idan kudi kukeso yayan mu zai baku daddyn mu zai baku don allah kada ku cutar damu"
Matse mata hannu dayan yayi ta saki muguwar kara "idan kika sake magana saina kasheki shegiya mai surutun tsiya,babu abinda zamuyi muku abu daya muke bukata shine budurcin kanwarki kadai shi mukeso munada kudi dik abinda kikasani muna dashi idan kika kuma magana harda ke zamu hada"ya sharara mata mari ta saki kuka.
Kuka sosai afee take lokacin da daya daga cikinsu yake kokarin cire mata kayan jikinta cike da mugunta yake yaga su har yayi musu kaca kaca,a idon nawal ya zare wandon jikinsa ya haye saman afeee.....wata razananniyar kara ta saki saida wajen ya amsa,da sauri yasa hannu ya toshe mata baki....cikin jin dadi yake biyan bukatarsa da kankanuwar yarinya mai shekaru goma sha biyar,cikin mintuna da basu wuce talatin ba yayiwa afee fyade ya rabata da mutuncinta wadda ta dade da sumewa ...
Nawal kuwa itama sumewa tayi ganin abinda akewa yar uwarta,ko a film bata taba ganin yadda namiji ke kwanciya da mace ba sai akan kanwarta,katon namiji ya turmusheta yayi mata fyade,koda ya dagata taga idon afee a kakkafe yasa tayi luuuu itama ta sume tana rike a hannun mazan....
Driver hawaye ke gudu a fuskarsa kallon afee a kwance kamar gawa,sosai hankalinsa ya tashi tausayin afee yasa hawaye gudu a fuskarsa ko motsi batayi,...dariya suka saki ganin yana hawaye wanda yayiwa afee fyade ya dago fuskar driver yana kallon yadda yake hawaye "hawayen me kakeyi?na imani koko tausayi?koko ta biya maka rai ne in bude kafarta kaima ka d'ana a haka?"
Jajayen idonsa ya dago yana kallonsa dikda baya ganin komi a fuskarsa har kwayar idonsa a boye yake sai kawai ya fashe da kuka ya kasa magana,hankadasa sukai ya fadi kasa ya kume da dutse sai jini ya balle a goshinsa...."da kaina zan kira gidanku in sanar da inda kuke saboda azo a taimakawa wadanan yan shilan kada su sheka lahira kaima in taimakeka domin tsafff yayansu zai ce kaine kai musu wanan mummunan aikin..."
Kallon yaransa yayi "ciromin sabon sim din nan insa a waya ta"
"Toh oga"
Nan da nan wanda akaiwa umarni ya ciro sim card a aljihunsa ya mika masa ya shiga kokarin cire na wayarsa yasa.....
*********
Kallon bilkisu ummah tayi lokacin da ta gama karanto mata dik abinda ya faru daga farko har karshe "tabbas bazan taba barin hakkinki ba bilkisu koda bani da kowa zan hada karfina dana allah da kudin mahaifinki in nema miki yanci,dole ne inje in sanarwa da iyalan alhaji muhammadu abinda dansu kamal yayi domin bazan taba yafewa ba"cike da jarumta ummah ke maganar kana iya hango tsantsar masifa da balai a kwayar idonta.....
"Ummah na dolene inrabu da abdulhrahman saboda a halin yanzun na tsanesa shima bashida gaskiya yayi amfani a fuskar mutanen kwarai yazo ya cuceni daya samun soyayyarsa cikin zuciyata"hawaye bilkisu keyi.
"Bazan kyale Abdul ba bilkisu dole shima zai fuskanci hukunci abu daya ne matukar abdul ya sanar dani gaskiyar abinda ya faru ya kuma tonawa kamal asiri hade da kwararan shedu?to tabbas zai wanke kansa cikin wanan masifar idan ba haka ba dagashi har kamal sai sunyi prison"
Gyada kai bilkisu tayi cike da gamsuwa da kalaman mahaifiyarta,bata taba jin tasamu sassauci da sanyi a zuciyarta ba sai yau da ta amayar wa da ummanta halin da take ciki....babban tashin hankakinta shine yadda zaai ta cire soyayyar abdul cikin zuciyarta,koda yake abu mai sauki ne domin yanzun koda ya sanarwa da duniya abinda kamal yayi bazata taba yarda dashi ba ta gama tsanarsa kenan....
Mikewa ummah tayi "ku tashi kuyi sallah gashi can ana kiran sallar magriba,nima sallar zanyi zan kira hajiya hafsa tazo gidan nan ko kuma ma bazan kirata ba gidan zanje yanzun idan na idar da sallah"..
Tausayin ummanta ya kamata ta kada kai kawai, Allah sarki ummah ita kadai zatayi yakin bata da mataimaki sai allah....wasu sababbin hawaye taji na sauka a fuskarta ..
********
Alwalar magriba yayi momy ta tsaidashi "kamal har yanzun su nawal basu shigo ba fa kuma nayi trying number afee bata shiga saboda itace take zuwa da waya makaranta"...
Ya bude Baki zaiyi magana kira ya shigo wayarsa hakan ya dakatar dashi ya zaro wayar a aljihun gaban rigarsa yana dubaea bakuwar number ce,haka kawai gabansa ya yanke ya fadi jikinsa ya hau rawa ya danna recieve ya kara wayar a kunnensa zuciyarsa na bugu sauri da sauri.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/30, 2:01 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*25*
K'ara bilkisu ta kwalla ta runtuma a guje ta shige gida,yadda idonta ya rufe ko ganin gabanta batayi wani duhu ne ya lullube idonta tankar makauniya,saar da taci shine tana shigewa parlorn ummah ta shiga dakinta babu kowa sai shaawah da safiyya da suke kokarin gyaran parlorn,rufo kofar tayi ta sa key ta ciki ta fada kan gadonta ta saki wani irin kuka mai gunji,zabura tayi ta mike tamkar wata zararriya tai jifa da wayarta,ji kaje tasssssssss ta fadi kasa ta fashe, dankwalinta ta kwance tai jifa dashi tana rike da kanta jiri na dibarta garin fadawa gado ta buge bakinta ya fashe ta kwantar da kai a pillow ta shiga rera kuka mai ban tausayi zuciyarta ta karye shin metaiwa maza a duniya akeyi mata haka?meyasa ta kamu da soyayyar mutumin da tafi tsana a duniya takejin sonsa fiye da kowa?dama abdul shine mutumin da yayi sanadiyyar fadawarta cikin mummunan halin da uwar da ta haifeta batasani ba?abdul shine sanadiyyar da yasa ta kamu da mummunan ciwon da take tare dashi a yanzun,dik soyayyar da Abdul yakeyi mata ashe karyane yasan cewar shine yayi mata fyade kallon fanko yakeyi mata kenan?tari ne ya taso mata tana kuka tana tari hakan yasa taji numfashinta na kokarin daukewa amai na taso mata ta mike jiri na dibarta ta fada toilet ta shiga kwarara amai mai jini jini a ciki,zafin da kirjinta keyi mata tamkar an hura mata wuta a cikinsa,zuciyarta na barazanar fashewa tun tana iya amai har ta kasa yunkurin amain kawai takeyi.....
Ummah kuwa tsaye tayi a parlor tana dubansu shaawah shiru tayi domin tabbas taji kara a parlor sanan taji karar fashewar abu kamar daga sashen bilkisu,"ke shaawah"
"Naam ummah"shaawah ta amsa tana sadda kanta kasa "naji kamar karar fashewar abu a sashen bilkisu waye cikinku ya shiga gyara mata daki bayan fitarta makaranta?"
Kallon juna sukai da safiyya "ummah ai bataje makaranta ba tun dazun ta shigo ta wucemu a nan ta shige dakinta inaga kamar ma bata da lafiya ne"
"Subhanallahi"ummah tace ta juya da sauri tayi sashen bilkisu,tura kofar tayi taji a rufe daga waje tana iya jiyo sautin marayan tarin da takeyi hakan ya furgita ummah ta shiga bugun kofar dakin "bilkisu bilkisu ki bude kofar mana,ya zaki shiga ki rufe kanki ancemun baki da lafiya"
Gaban bilkisu ya fadi jiyo muryar ummah a bakin kofar,da wani ido zata kalli ummah ta sanar da ita anyi mata fyade ta boye mata?da wani idon zata kalli ummah ta sanar da ita cewar abdulhrahman shine wanda yayi silar rabata da budurcinta?zufa ce ke cigaba da karyo mata yayinda hawayen da ke ambaliya a idonta suna cigaba da zubavsharrr sharrr tamkar famfo...shin wani irin dacin zuciya ummah zata shiga idan taji anyiwa yarta daya tilo fyade?.....bugun kofar da ummah tayi da karfin tsiya ta kira sunan bilkisu "bilkisu ki bude kofar nan inga halin da kike ciki"ta buga kofar...shiya razana bilkisu ta janyo jiki daga toilet din da jan duwawu ta karaso kofar idonta a rufe ta sa hannu ta laluba key ta bude tai saurin jan jiki baya fudun kada ummah ta bugo kofar....
Tozali da bakin bilkisu dake zubar da jini yasa ummah tai saurin ja da baya halin da taga yar tata ya haifar mata da mummunan faduwar gaban da tai taga taga zata fadi kasa,sai kawai ta dafe bango tana kiran yar tata "bilkisu...bilki..na menene? meyasameki wani mummunan abu ya sameki ne?koko abdul ne yayi miki mummunan wani abun?jini nake gani a bakinki bilkisu ki sanar dani halin da kike ciki"a rude ummah ke maganar ta nufo wajen bilkisu cike da karfin hali ta tallabo ta ,zafi rauuuuu jikinta sai kawai bilkisu tayi luuuuu ta fadi jikin ummah sumammiya.....
Kifa kai Abdul yayi a cikin motar Yana rera kuka mai ban tausayi hawaye kawai ke gudu a fuskar yan maza hannunsa na rike da wayarsa jikinsa na rawa yake kiran numberta amma ga mamakinsa a kashe.....dora hannunsa yayi akai zuciyarsa na harbawa sauri da sauri,bashi da sha maki da shiga gidan amma ta yaya zai hada ido da ummah cewar shine yayiwa yarta fyade?...kuka ya fashe dashi shikenan rabuwarsa da bilkisu tazo lokaci yayi da zai fuskanci hukuncin Allah na aikata mummunan aiki da yayi a rayuwarsa ...me zai fadawa mahaifiyarsa dangane da rabuwarsa da bilkisu,ya sanar mata da cewar ya taba aikata fyade a rayuwarsa?dik yadda take masa wasilci da jin tsoron Allah?......"ya hayyu ya kayyum inama ace ban kai wanan lokacin a raye ba?ya allah ka kawomin dauki"...kuka yake sosai....soyayyar bilkisu na kara azalzalarsa ta yaya zai iya rayuwa batare da ita ba......
*******
Dik yadda kamal ke gabatar da lectures hankakinsa na kan seat din da bilkisu ta saba zama minti minti yakan kalli wajen,waigawa yayi a karo na barkatai suka hada ido da maman abdallah wadda keta rubutu a dan littafinta,murnushi tayi don tasan bilkisu yake waige sai ta tabo nafeesa dake gefe "wai shin ina kawarki ne yau batazo ba naga sir kamal sai kallon wajen zamanta yake ko kewarta yake"fakon idonsa nafeesa tayi ta galla masa hararar takaici sanin tasan shidin waye ta dan ja tsuki tacewa maman abdallah "can ta matse masa shi ya sani"
Karar wayar sir kamal ce ta janyo hankalin daliban dake class din da sauri yasa hannunsa a aljihu ya zaro wayar da niyyar rejecting...sunan ummah ya gani hakan yasa jikinsa ya basa wani abu nan da nan ya danna recieve ya kara a kunne cike da natsuwa yayi sallama da muryarsa mai dadi "Assalamu alaikum ummah barka da safiya"...
"Babu lafiya kamal ina cikin tashin hankali"
Gaban kamal ne ya yanke ya fadi kirjinsa ya shiga bugawa kodai bilkisu ta sanar mata da tsakaninsu ne masifa ta auku?be karasa tambayar kansa ba maganarta ta katse sa "kamalu idan baka komi kazo yanzun dan Allah nakira doctor din da yake dubani a gida yazo ya duba bilkisu be dauka ba,don jikin ba dadi ne da asibitin da take zuwa zataje kana ina dan allah"
"Innalillahi wa innah ilaihi rajiun ummah gani nan zuwa ina makaranta amma yanzun zan taho ganinan please"
"Owk".
Ta datse wayar cikin tashin hankali kamal ya dubi daliban ya shiga harhada takaddunsa "am sorry class pardon let's us meet next class please"jikinsa har rawa yake.....to meye ya sameta haka?tambayar kansa yake yana kokarin ficewa cikin class din....
*********
Kuka sosai abdul yake a gaban innarsa kannensa suna zagaye dashi sunyi zugum zugum kamar anyi mutuwa babu kamar zainab da babu wuya hawaye ya sauka a idonta "innah....na tafka babban kuskure nayi abinda ke kanki idan kikaji abinda nayi karshenta ki tsinemun ko ki cireni sahun yaran da kika Haifa,innah nayi miki laifi dik nasihar da kikemun ganin na zamto nagari na guji rudin zuciya hakan be yuwuba rabuwa ta da bilkisu ne tazo"
Zaro ido kannensa sukai a tare muryar zainab har rawa take wajen jeho masa tambaya"me kayi mata haka yaaya?meyake faruwa?ka jefamu cikin rudani yaaya,ka fayyace mana abinda yake faruwa".
Innah kuwa shiru tayi Tana kallon yadda idonsa ke zubda hawaye jijiyoyin kansa sunfito a goshinsa ta rasa abun cewa sai sauke ajiyar zuciya da takeyi minti minti can kasan zuciyarta hantar cikinta a kade take jira kawai takeyi taji sammacin yan sanda ko taji jiniyar motar sojoji anzo tafiya dasu,yaci kudin yar mutane koko ya cucesu ne oho?tou meye haka yayi da yake wanan kukan yana ambatar cewa shi rabuwarsu tazo?"abinda bake guje maka kenan Abdul shiyasa tun farko banso alakarka da wanan yarinyar ba banso wani abu ya shiga tsakaninku ba harta daukeka ta doraka akan dukiyar mahaifinta,tai ta barnar kudi wajen faranta maka itace harda siya maka kaya baka aikinti ta dauki makullin sabuwar mota ta baka,ko sati baaiba da ta siyo kayan abinci ta kawo mana,tunda ka hadu da yarinyar nan take hidima damu abdulhrahman nasan sharrin zuciya da shedan yanda yake babu abinda bazaisa ba musamman harka ta kudi,ka fadamun abinda kayi tun wuri mu hada kayanmu kafin a kawo maba sammaci domin Babu wanda zai karbo mu idan an kadamu a ruwa a garin nan bazamu shawu ba"innah ta tsagaita Tana kallonsa cikin tashin hankalu nan da nan bakinta ya bushe idonta sunyi jajir wani miyau mai dacin gaske ta hadiye ta cigaba da kallonsa, shima ita yake kallo hawaye kawai ke gudu a idonsa batare da yace komi ba "Ina sauraronka"
Shiru yayi zuciyarsa nayi masa zafi ina ma ace abinda innah take hasashe hakan ne?da sai yafi masa sauki da radadi fiye da wanan abun dake tunkararsa bashida sauran mutunci a idon kowa a duniya bashida sauran mutunci har a idon kannensa matukar sukaji abinda ya faru...memakon yace wani abu mikewa yayi ya fice a dakin yana ganin duhu duhu a idanuwansa a nan ya yadda makullin motar da sauri zainab ta dauka cikin tashin hankali ta dubi innarta zatai magana innah ta yunkura ta mike ta mara masa baya.....
Tagumi sukai kannensa ko wanne da abinda yake sakawa a zuciyarsa musamman zainab da tafi kowa shiga damuwa kudurawa tayi a zucuyarta idan ta fita islamiyya zata biya wajen Yaya bilkisu....
**********
Shigowa yayi a parlor ya tadda ummah rike da hannun bilkisu har doctor din ummah yazo kafin ma ya iso,kallon yadda take sauke numfashi yakeyi,be tabajin tausayin wata halitta a duniya ba yadda yaji tausayinta ya darsu a zuciyarsa lokaci daya,kallon yadda bakinta ya fashe yayi idonta a rufe tana sauke nunfashi a hankali....
"Kamal ka iso?kaganmu yanzun nan doctor sadik ya tafi muna gama waya dakai saigashi ya shigo ashe a mota yake yaga kirana yana gani yasan ba lafiya shine ya taho kawai"
Tsugunnawa yayi gaban ummah "ummah ina yini?ya jikin nata?"
"Alhamdulillah ta samu bacci"
"Wai meyasameta haka ne?
"Wallahi ta fita Abdul yazo zai wuce wajen aiki zai sauke ta a makaranta na shiga daki ko kafin infito sai ihunta naji shine fa shaawah ke shaidamun sunga ta shigo ido rufe kila bata da lafiya ne ciwonta ya tashi"
Shiru kamal yayi gabansa na faduwa wani irin ciwo gareta haka?tou kodai ciwon zuciya gareta?tambayar kansa yake cike da tsoro,meye ya faru tsakaninta da abdul din?dik bashi da amsar tambayoyinsa.
Motsawa tayi dik abinda sukeyi tana jinsu ji take tamkar ta tashi ta shakesa saboda wani tukuki da zuciyarta keyi kwata kwata ko muryar maza batason ji ta tsana,batajin zata sanarwa da ummah wanan labarin na fyade da abdul yayi mata,koda zata sanar mata ba yanzun ba domin ummah zata dau zafi a wanan lamarin sanan tanada hawan jini zai iya tashi idan taji halin da yarta ke ciki dik ciwo zai kamasu...hawaye masu zafi ke bin gefen idonta ..
Kafe ta da ido yayi yadda hawaye ke gudu a fuskarta idonta a rufe ya haddasa masa da faduwar gaba.. .ya dade zaune sanan ya mike sukai sallama da ummah....
********
Yana shiga gate din gidan yaci karo da nawal da afee zasu tafi makaranta dik suna sanye da uniform mai ruwan kasa suna sanye da safuna hijabinsu har kasa afee fuskar nan tasha hoda da lipbalm tana ganinsa ta sakar masa murmushi "yaayah barka da zuwa"shafo kanta yayi "yaayah afee zaa tafi islamiya ne?"gyada masa kai tayi kallon nawal yayi ya sakar mata murmushi ta maida masa "yar aljannah an fito?"itama kada masa kai tayi ..hadesu yayi ya rungume yana jin soyayyarsu cikin zuciyarsa......
"TJ ka shirya tsaf ko?banaso a samu matsala kaji?dik abinda kake bukata zanyi maka shi a wanan duniyar,kaimun rai TJ please"
Zatai magana ya turo kofar parlorn ta kife wayar tana gyara zama "barka da zuwa hubby"
Ko kallon inda take beyi ba fuskarsa babu rahma babu annuri tamkar be taba dariya ba haka ya wuceta yayi hanyar dakinsa,kallo ta bishi dashi wani sonsa na karuwa cikin zuciyarta,ajiyar zuciya ta sauke ...idonta ya cicciko ta mike tabi bayansa ta tambayesa koda abinda yakeso yake bukata...
********
Tafe suke a mota kamar an tsaida motar motar ta tsaya cakkk gefen hanya,tsaki driver yayi "Allah yasa ba tayar mota ce tai mana tsiya ba domin tun daga gida nakejin kamar akwai abinda ke damun motar nan"
Nawal dai batace komi ba hannunta rike da alkuraninta tana cigaba da maimaita haddar da zata bada afee ce tai tsaki ta ciro waya ta jingina da jikin glass din motar bayan ta bude,driver kuwa ficewa yayi yana kokarin daukar abu ta kasan motar kamar daga sama afee taji an wafce wayarta an bude motar an fizgo ta waje.....
********$
Ganin pheey ba karamin dadi bilkisu taji ba suna cikin dakin bilkisu,pheey na gefe tana kallon yadda bilkisu ta koma cike da tausayawa "kawata ashe baki da lafiya amma ciwon yau da safe ya sameki ko?don munyi waya lafiya lau kikace zakizo school ganin ban ganki ba yasa da naje gida nai wanka nace bari inzo induba lafiya"
Matso hawaye billy tayi ta gyara kwanciyarta "pheey ciwo dole ya sameni domin ina cikin tashin hankali mara misaltuwa"....
Ummah dake kokarin shiga dakin sai ta fasa ta dakata domin jin abinda bilkisu zata fada dake sata cikin tashin hankali dama tana zargin akwai wani abu...
Gyara zama pheey tayi "kawata menene meke faruwa dake?kifadamun kawata nima kinsani a rudani banason ganinki kina hawaye"
"Pheey abdulhrahman da nakeso na mutu a kansa nakejinsa a jinin jikina nakejin dik duniya babu abinda zai rabani dashi to shi ya jefani a mummunan halin da kikasani ashe bansani ba"ta fashe da kuka...
"Meyayi miki kawata?kinsani a duhu kibar kukan ki sanarmun"
"Abdulhrahman shine azzalumin da yayimun fyade"......
Jikin ummah ya kama rawa jin kalmar fyade yasa idonta ya rufe ta fado dakin kamar daga sama bilkisu taga ummah tsaye a gabanta.......
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[6/30, 2:01 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*27*
Tsaye yayi kare da waya a kunnensa har aka gama karanto masa abinda zaace bema san an gama fada masa har an kashe wayar ba yadda yayi cakkk yana kallon gefe daya kana iya hango yadda kirjinsa ke sama da kasa ya tadawa momy hankaki hantar cikinta tayi mummunan kadawa cikin furgici da fargaba bakinta na rawa ta tabosa sai kawai wayar dake kare a kunnensa ta sulale kasa ji kake tasssss,zaro iro momy tayi ganin hakan yasa cikin tashin hankali ta kira sunansa "kamal....meke damunka haka?meyake faruwa?daga amsa waya tamkar wanda aka sanarwa da wani faruwar mummunan lamari?kayi shiru bakacemun komi ba ka sanar mun"....leko fuskarsa tayi kawai tayi tozali da hawaye na gudu a idonsa guda daya gashi ya kafe gefe daya da ido,tsoro da furgici da tashin hankali ya sake shigar momy a rude ta girhiza sa "kamal kayi shiru kace wani abu mana?dan allah ka sanarmun meyake faruwa kamal meyafaru da yarana?inaji a jikina wani mummunan lamari ya samu su nawal haka ne?ka sanar mun dan allah"muryarta na rawa take maganar tana kokarin rushewa da kuka....jikinta be daina rawa ba ta fuzgo kamal tana girgiza sa tana tambayarta,kallonta yayi cike da tausayawa hawaye ya cigaba da gudu a fuskarsa dakyar ya motsa bakinsa ya ambaci "momy.....kiyi hakuri an sanarmun da cewar an kama su nawal da afee har anyiwa afnan fyad...."ai be karasa ba ta kwalla mummunar kara ta kara ruko rigarsa gammm jikinta na karkarwa a guje malam dauda ya nufo inda ya jiyo karar beyi wata wata ba ya zube a kasa cikin fargaba ya soma tambayarta "hajiya meyake faruwa ne?wani mummunan abu ne ya faru?"
Kuka ta rushe dashi tana cigaba da kara tamkar zautacciya ganin haka yasa malam dauda furgita ya bar wajen ya koma bakin aikinsa , Zahra ce ta iso da sauri har Tana cin tuntube wajen matakalar hayowa corridor din da kyar ta hayo ganinsu cikin wanan yanayin ba karamin furgita tayi ba bakinta na rawa "momy lafiya me yake faruwa?"
Cikin kuka momy ta sanarwa da Zahra abinda yake faruwa,wani irin shock zahra tayi jikinta ya kama rawa bakinta ya soma karkarwa "yanzun me muke jira momy a nan?ya dace muyi wani abu zaman haka zai iya jefa su cikin wani hali"
Matso hawaye momy tayi cikin kunar rai "an cuceni an cutar dani an tonamin asiri an wulakanta a halina, dik wanda yayiwa wanan yarinyar mummunan hukuncin nan bazan taba yafe masa ba bazan bar ko waye ba dik ranar da asirinsa ya tonu sai ya dandana kudarsa.....saina sa an azabtar dashi mafi mummunar azabtar wa,wayyooo allah afnan a cikin wani hali kike oho"sai lokacin zahra ta dubi kamal yadda gumi ya jikasa gabaki daya kamanninsa sun canja,ba karamin tsorata tayi da yanayin nasa ba,furucin momy su suka karfafa kamak yaji karfi yazo masa da jarumta nan da nan jijiyoyin kansa suka firfito ya fuzge hannunsa daga rukon da momy tayi masa kawai yayi waje zahra ta rufa masa baya,a kofar gate kusan ture malam dauda yayi jikinsa na rawa ya bude motar ya shiga ya tada zahra na gefen mai zaman banza,....jikinta sai rawa yake zufa ce kawai take karyo mata a goshinta ga fitsari da takeji tankar zai kubce mata,minti minti tana kallon yadda yake sarrafa sitiyarin mota har suka fice a unguwar suka hau titi....mahaukacin tuki yakeyi ba tare da ganin gabansa ba ga hadari da yayi bakin kirin a gari sai walkiya ake zubawa.....
Momy kuwa fitarsu ta saki sabon kuka dik yadda taje trying number daddy tana shiga amma baya picking,gaba daya duniyar tayi mata zafi wani irin bakin ciki take ciki wanda bata taba shiga ba tana tsaye ta rasa inda zatasa rayuwarta bacin hawaye dake kwaranya a idonta aka bude labulen dakin da sauri ta d'ago kai gani daddy ne pa ruga da gudu ta fada jikinsa ta saki sabon kuka,...jikin alhaji muhammadu na rawa ya shiga tambayar momy abinda ke faruwa ya ganta cikin wanan halin "alhaji....alhaji afeee na alhaji yara na"gaban daddy ya yanke ya fadi,amma dayake akwai jarumta irinta maza sai ya dake dikda yadda kirjinsa ke bugawa "meya samesu?meyake faruwa?"
"Alhaji azzalumai sun tare su afnan a hanyar komawar su makaranta sunyiwa afnan dina fyade"ta kara rushewa da kuka,cikin tsananin rawar jiki alhaji ya tureta a jikinsa ya zare gilashin fuskarsa "what?mekike fada are you trying to tell me anyiwa yata afnan fyade?"...kallonsa tayi cikin yanayi na karaya ta gyada masa kai "innalillahi wa innah ilaihi rajiun"...ya zaro wayarsa jiki na rawa "zanyi reporting yanzun zan sanarwa da yan sanda"...da sauri ta ruko hannunsa ta fuzge wayar tana gunjin kuka "alhaji kada ka sanarwa da police wanan lamarin tamkar tonon asirinmu ne damu dakai musamman kai da duniya ta sanka ciki da waje"
"Kina so ko sanarmun da cewar bazan kwatarwa yata yanci ba?me kike nufi?hauwau "cikin daga murya yake maganar dakin na amsawa... girgiza masa kai takeyi tanajin radadi a kasan zuciyarta kamar an zuba mata rushin wuta.....
"Matukar ka sanarwa da yan sanda to tabbas ka bankade asirin yarka,sanan ba lallai bane a iya kama wadanda sukai wanan aikin,kaga mun bata goma biyar bata gyaru ba"
"Bazan kyale kowaye yayi wanan mummunan aikin ba hauwa u ina mai tabbatar miki da cewar bazan bar wanan case dinba wallahi sai anyi tracking dinsu an kamasu ".....yasa hannu ya sharcw zufar dake gudu a fuskarsa dikda fanka da AC dake aiki amma hakan be hanawa alhaji karyowar gumi ba......wucewa yayi ta bi sa da kallo ta jingina da jikin bango ta hada kai tana kuka.....
********
Ummah kuwa a gaggauce tayi sallar magriba da ishai ta fito sanye da hijabinta ta bude kofar dakin bilkisu tana zaune a kan dadduma ta idar da sallah ta jingina tana kiran sunayen Allah "bilkisu ina nafeesar?"
"Ta wuce ummah, yayansu yazo suka tafi kina sallah dama shi take jira yazo daukarta kuma sun wuce"kanta a sunkuye take maganar murya a sanyaye,wani irin kunyar ummah takeji ahalin yanzun bazata iya hada ido da mahaifiyarta ba "taso muje gidan mamanki domin tanada hakkin jin wanan al'amarin tunda kanwar mahaifinki ce idan mun tattauna sai musan yadda zamuyi in tunkari alhaji muhammadu"
Kwalla ce ta taru a idon bilkisu "ummah na,banaso momy hafsa taji wanan labarin domin kuwa tankar tonon asiri na ne kuma kinsan tanada yara bazata boye musu komi ba zata sanar musu zasu rinka kallona da abun koda bamuda wasu dangi labarin a hankali zai karade gari nafiso nidake muyi yakin mu batare da sanin kowa ba"
Shiru ummah tayi a jikin kofar sanan ta tako ta shigo dakin ta nemi gefen gado ta zauna "yanzun me kikeso ayi?"
"Inaso kiyimun izinin zama da abdulhrahman in zanta dashi ya sanarmun yadda akai video din yaje wajen kamal har yakemun barazana dashi, idan ya bani hadin kai hade da kwakkwarar hujja to tabbas zan cireshi cikin lamarin saidai muji da guda daya ummah na"
"Haka ne bilki na allah ya shige mana gaba yanzun ya zaai kiga abdul har ki zanta dashi?"
Shiru tayi tana tunani sanan ta dubi ummah "gobe da yamma zan shirya zanje har gida in daukoshi in kawosa idan bamu samu yadda mukeso ba kawai musa a kamashi....
Mikewa ummah tayi ranta babu dadi har ta kai kofa ta juyo ta dubi bilkisu "idan kingama ki sameni a parlor kici abinci kada wani ciwon ya kamaki don tun safe bakici wani abu ba"
Gyada ma ummah kai tayi Tana murmushin karfin hali "toh ummah na"....
*********
Zaune suke sunyi tagumi dagashi har zahra a kujerun dake jere a gefen emergency room inda aka Shiga da Afnan domin nawal ita suma tayi tuni ta farka tana kwance a wani daki.....
Likita ne ya fito hannunsa sanye da gloves da labcutt irinta likitici da stethoscope a kunnensa a zabure kamal ya mike "yayadai likita ta farfado? ansamu anyi aikin kuwa?"
"Sa meni a office"
Likita na tafe kamal na biye dashi faduwar gabansa ta tsananta ...
Ganin tafiyarsu tasa zahra zaro wayarta daga cikin hijabi da take Allah Allah ta duba taga mai kiran nata,misscall goma sha biyar ta gani dik mutum daya wato TJ ta gane numbersa cikin sauri tayi dialing wayarsa tana waige waige babu kowa a wajen sai ita kadai "yaya TJ kana ta kirana muna tare da mijina a asibiti kasan babu damar dauka"
Yar dariya TJ yayi jin yadda take magana a rikice daga jin muryarta a tsorace take "zahra kenan kura,ga tsoro ga ban tsoro dik wanan furgicin na menene?na anyiwa kanwar mijinki fyade?nasan kina nan kina zare ido kina kuka bayan kinsan komi,koda yake kedin batdakama ce bada sauri ake gane ki ba,dik dai ta kare na cika miki alkawarinki domin nayiwa yarinyar nan kaca kaca kuma video din full ya sauka akan WhatsApp dinki sauran aikin naki ne zahra"....murmushi ne ya subuce mata sai kuma ta dake tana waige waige,"Tj ka cika alkawari nasan kaidin masoyin gaskiya ne don haka sadakin ka sai mun hadu gobe"
Mika tj yayi daga inda yake kwance yayi yar dariya "zahra kenan zanyi komi don farin cikinki,abu daya ya rage kizo gobe kibani sadaki na harda lada"....bata kara cewa komi ba ta datse wayar,tagumi tayi gabanta na faduwa farin ciki takeji ko akasin haka?tunanin yadda zata gabatarwa da kamak video din take batare da ya gane wani abu ba.....
Tunda kamal ya zauna gabansa ke faduwa likita kuwa rubuce rubuce kawai yakeyi kusan minti goma saida ya cika takadda da rubutu sanan ya dago ido ya dubesa "kaine waye nata?"
"Nine yayanta"muryarsa na rawa ya amsa cike da furgici...."tou munyi bincike sosai munyi gwaje gwaje mungano anyi mata mummunan fyade,wanda hakan yasa saida mukai mata minor surgery,dinki ciki da waje mukayi mata alhamdulillahi gwajin wajen mafitsaararta bai samu matsala ba,saidai allah ya kiyaye gaba sanan teses na ciwuka munyi alhmdllh for now babu wata matsala"
Hawaye ne ya gangarowa kamal a idonsa tsoro da tausayin Afnan suka lullubesa,nan da nan wani irin tsanar kansa ya darsu a zuciyarsa yaji wata irin nadamar abinda yayi ta lullube masa zucuya, yanzun da iyayen bilkisu sunsan anyi mata fyade haka zasuji?hasko fuskar momy yayi awanni uku da suka wuce yadda take kuka an ketawa yarta mutunci to ya ummahn bikkisu zataji?ita da batada uba kenan marainiyar allah?da wani ido zai kalli ummahn bilkisu?insha allahu ma asirinsa bazai tonu ba,kuma zai roki iyayensa su rufe maganar fyaden afee kada duniya tasani....
Shiru likita yayi yana nazarin yadda kamal ke kuka babu sauti tausayin kamal ya rufe likitan wani iri shi kansa yakeji lokacun da yakeyiwa yarinyar dinki tausayinta yakeji yadda akai gardi ya hau wanan yarinyar "ka kwantar da hankalinka ranka ya dade,insha Allahu zata samu sauki yanzun haka ma zata farka babu ciwo saidai na ciwon jiki, sanan kuma ka sanarwa da wanda zai kula da ita cewar a rinka sata a ruwan zafi safe da yamma tana gasa wajen amma ba Wanda zai warware dinkin ba ba mai zafi sosai ba"
.share hawaye kamal yayi "likita zan iya tafiya da ita gida?"
"Zaka iya tunda anyi mata dik abinda zaai mata idan kanada bukatar wani taimako zan baku kati na koda kana gida ka kirani inzo in dubata Allah ya bata lafiya"
"Ameeen".... dakyar kamal yayi karfi da jikinsa ya karbi takaddar ya fito office din likita...tafe yake yana jin zuciyarsa cikin kunci da radadi....idan beyi saa ba tabbas zuciyarsa zata harbu da mummunan ciwo...gashi yanzun babu wanda yakejin sonta a rayuwarsa kamar billy,ko wani hali take ciki oho...jan kafarsa yake har ya iso bai ga zahra ba be kuma damu ba sai ya nufi dakin da yake jiyo sautin kuka yana shiga nawal ce rike da hannun afee dake faman bacci fuskarta ta kumbura sai ajiyar zuciya take da busasshen hawaye a fuska....karasowa kamal yayi ya rungume nawal ya fashe da kuka yadda suke kuka kadai yasa jikin zahra yayi sanyi....wani irin soyayyar kamal ke ruruwa a zuciyarta nawal kuwa sambatu take "yaayah kana gani sunyiwa kanwata fyade a idona yaya a idona azzalumai suka kamamun afee suka lankwashe hannunta"ta fashe da kuka rungumeta yayi yana shafa bayanta hawaye na gudu a fuskarsa....janyeta yayi "muje ko bari in dauki afee a hankali mutafi gida tunda dik abinda zaai mata anyi mata ina malam yahya dreba?"
"Yaje masallaci shima anyi masa dinki a goshi yaje Rama salloli ne"bata rufe baki ba ya shigo kansa da plaster...sunkutar afnan yayi a kafada nawal na rike a hannun zahra suka fice suka bar cikin asibitin.... can inda sukai parking suka shiga nawal da zahra sune a baya rungume da afee da take bacci malam yahya na zaune gaban mota....
Rike kamal yake da hannun afee misalin karfe daya na dare dukkansu babu wanda ya runtsa saboda har yanzun bata farfado ba,motsi ta soma yi a hankali dukkansu idonsu na kanta,da sauri momy ta matso ganin afee ta bude idonta "afee na kin farfado sannu kinji Allah ya saka miki"a raunane momy tayi maganar
Hawaye ne ya shiga gangarowa afee ta juyo suka hada ido da yayanta,kallonsa take cikin radadin azaba dakyar ta bude bakinta da ya bushe tace "zafi.....zafi nakeji a kasa na yaayah....zafi"
Kwalla ce ta gangaro masa a ido ji yake tankar ya cire mata radadin da takeji a kasan nata amma babu damar hakan,take bilkisu ta fado masa dik lokacin da zai kusanceta sai tayi kuka sai taji azaba yau haka kanwarsa taji?haka bilkisu ashe taji takan ce zafi zafi...ashe dagaske ne akwai zafin.... innalillahi wa innah ilaihi rajiun....shine ya janyowa Afnan wanan mummunar kaddarar....be gama tunani ba ta kira sunansa cikin wani irin marainiyar murya "yaayah"
"Afeena sannu kinji menene?me kikeso?"
"Yaayah wai fyade akaimun?ashe haka yake da azaba yaayah....zan mutu wayyooo zafi yaayah"...ta fashe da kuka....da sauri daddy ya fice a dakin yana hawaye....momy tabisa da kallo,nawal kuwa hade kai tayi da gwiwa wani irin tausayin kanwarta takeji ji takeyi dama ita sukayiwa ba afnan ba....
********"
*Washe gari*
Bilkisu ta gama shirinta tsaf ta fito tana sanye da milk colour din hijab be hannu idonta sanye da bakin glass tana rike da wayoyinta "bilkisu ki sanar masa da cewar nice na umarceki da ki dakkosa ki kawosa gidan nan idan kuma yaki amincewa to ki kira hukuma su kawo mun shi"
"Kada ki damu ummah dolensa ya biyoni idan yaki kuwa zai dandana kudarsa abinda nakeso kawai shine ya sanar mana da alakarsa da kamal da yadda akai yasamu video da dalilin da ya ketamun mutunci idan yayi alkawarin tonawa kamal asiri tou tabbas zamu ciresa zamu kyalesa"yadda bilkisu ke maganar kadai zai nuna maka kwarin gwiwarta a wanan karon dikda radadin da takeji a zucuyarsa...
"Bilkina kiyi yadda ya dace sanan idan har ya bamu hadin kai zaki yafe masa".."kona yafe masa ummah bazan taba sonsa ba domin na tsanesa banajin zan yafe masa da sunan cigaba da wata muamala"
Tana gama maganar tasa kai ta fice,parking lot taje ra bude mota ta shige ta ja aguje ta shigayiwa mai gadi horn ya bude mata ta fice kamar zata tashi sama....
Tun daga nesa yake hangen motat,gabansa ya fadi yana zaune ya tasa bokiti a gaba da ya zuba ruwa da sunanyin wanki,kayan wankin na gefensa ya zabga tagumi....yadda ya hango tana driving kadai ya sheda masa bada lafiya tazo ba. .. innalillahi wa innah ilaihi rajiun ya shiga ambato yana bin motar da kallo har tayi parking a kofar gidan ta fito....kallon fuskarta yake sanye da glasss babu annuri babu faraa yasa ya sandare tsaye ....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
SLIMZY✍🏻
[6/30, 8:27 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*28*
Yadda ta tsaya daga nesa dashi yasa ya tako har gabanta ya tsaya,zare glass din idonta tayi ta dora masa kyawawan fararen idanuwanta masu narkar masa da zucuya,irin kallon da takeyi masa yasa,yaji wani abu mai daci daga cikinsa ya taso kirjinsa zuwa bakinsa,wata irin hadiyar miyau yayi mai cike da furgici...kasa magana yayi ya kauda idonsa daga cikin nata ganin haka yasa ta saki murmushi mai ciwo "Abdulhrahman kenan,babu yadda zaai ka iya hada idanu dani dama,saboda ka cutar dani kaci amanata,ka yaudareni saboda tun farko kasan nidin wacece a wajenka ka yaudareni da salon soyayyarka,domin ni da nasan kaine da sharar gidanmu saita fika mutunci a idona domin na gwammaci ganin ajalina da hada ido dakai"...wata irin faduwar gaba ce ta ziyarci abdul cikinsa ya murda ya dago shanyayyun idanuwansa ya dora mata irin kallom tsanar da take jifansa dashi yasa wata kwalla ta ciko a idanuwansa dakyar ya bude baki da niyyar magana yace "amma bilkisu....kin..."daga masa hannu tayi cike da masifa cikin daga murya tace "dakata bakada sauran kalaman yaudara da zakaimun amfani dashi saboda kai fasikine,mazinaci ne sanan azzalumi ne"
Dago idonsa yayi da sauri yana kallon yadda idanuwanta suka kankance tana kiransa da mugayen kalamai marasa dadi,bugun zuciyarsa ya tsananta ya kosa ta sanar masa da dalilin zuwanta wajensa ya kosa ta umarcesa da ya bata dik abinda ta mallaka masa,sanan ya baza kunnuwansa yaji karar jiniya ta shigo domin daukansa zuwa gaban hukuma,cikin kakkausar murya ta nisa tace "banazo nan domin akwai sauran digon soyayyarka a zucuyata bane nazo ne in daukeka in tafi dakai gaban ummah na,ka sanar mana da dalilin da yasa kaimun fyade kayi video ka turawa kamal muhammad leacturer na kuma dan abokin mahaifina"...gabansa ya yanke ya fadi biyu biyu yake ganinta a gabansa nan da nan jikinsa yayi sanyi hawaye ya gangaro a idonsa na dama...."idan ka shirya mu shiga daga cikin mota mutafi"..bata jira cewarsa ba tayi gaba abinta ta bude mota ta shiga ya dau seconds a tsaye sanan ya yanke shawarar bin nata....beko bi ta kan kayansa dake zube a kofar gidan ba ya bude gaban motar ya shige,yana shiga ta maida gilashin idonta ta tada mota tai wani burki da motar tai kara ta tada kura tayi gaba.....
Jin karar mota ya razana zainab ta fita a guje lokacin innah tana bayi,...hango bayan motar ya shaida mata da bilkisu ce tazo ta juya gefen ta ga kayan yayan nasu nan a tsube a gefe har wayarsa da agogon hannusa dik a gefen dandamali....kirjinta ya soma dokawa yana sama da kasa,wasu zafafan hawaye suka zubo mata a idonta...."innalillahi wa innah ilaihi rajiun"ta furta ta tsugunna ta dauki wayarsa da agogon hannunsa tayi cikin gida hawaye na bin fuskarta,innah na alwalar sallar walha zainab ta shigo jiki babu kwari....har innah ta idar da alwala bata lura da zainab dake tsaye akanta ba saida ta dago suka hada ido da juna,'ke zainabu lafiya na ganki haka?"
Cikin kuka zainab tabawa innah amsa da "antafi da yaayahm mu ina nan naji karar mota ko kafin in fita sunsha kwana innah,ina iya hango bayan motar"
Kada kai innah tayi cike da takaicin abdul "halan yan sanda ne sukazo suka tafi dashi"tai maganar batare da wata damuwa ba "ba yan sanda bane innah anty bilkisu ce tazo ta tafi dashi"
Maimakon innah tayi magana gaba tayi abunta rai babu dadi tanajin radadin abinda danta ya aikata saboda abun duniya dikda tasan ba halinsa bane amma tasan tabbas rudarsa akayi da kudi a lokacin da yake tsananin bukatarsu,meyasa bazai bari ya mutu ba?meyasa bazai bari su su mutu da yunwa ba daya aikata mummunan aiki sabida kudi?.... shimfida dadduma tayi hawaye ya sakko a idonta ta tada kabbarar sallah.....
*********
Hawaye ne masu zafi ke sauka shaff shafff a fuskar afee wadda ke zaune a kujera,dik iyalin gidan suna zazzaune suna breakfast,ko baa fada maka ba kallo daya zakayi musu kasan cewar suna cikin tashin hankali kowa ya tasa breakfast din ne amma bawai suna jin dadinsu ba...
Farfesun kifi ne da yaji kayan hadi sai kamshi yakeyi da tea mai kauri a gefenta Kamal ke zaune hannunsa rike da plate din yana dibowa yana mika mata tana karba,sau uku ta karba ta kauda kai tana hawaye "yaayah bazan iya cin komi ba na gwammaci mutuwa ta da wanan halin da nake ciki yaayah natsani rayuwata"
"Sorry my baby kiyi hakuri insha allahu dik wanda yayi miki hakan allah bazai barshiba asirinsa zai tonu kinji?"yana kallonta cike da tausayawa gyada masa kai tayi ta mike tsaye batacewa kowa komi ba ta nufi hanyar dakin su tana takawa dakyar kafarta a ware take tafiyar tana dingishi...
Duka kallo suka bi ta dashi nawal ta mike ta rufa mata baya,kallon momy kamal yayi ya hango hawaye kwance a idonta "momy kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki zai wuce,yanzun zanyi wanka zan tafi office din abbah don naga ya dau zafi akan lamarin amma inajin tsoron ya fidda abun nan sunan mu ya baci a garin nan daga karshe yarinyar nan taki auruwa"
Hadiye yawu mai kauri momy tayi "tunani na kenan kamal ka lallashesa domin ya tabbatar mun da zai kai ga hukuma ni kuma ina tsoron hakan"...furzar da iska yayi mai zafi ya mike ya fice batare da ya cewa momy komi ba.....
Tana zaune tana latsa waya a parlor gabanta soyayyen dankali da kwai ne tana kurbar tea ya shigo dakin,tana ganinsa ta mike tsaye "hubby zo kaga wani video yanzun nan aka turomin shi video din da akayi raping afee ne"...ai tana fadin haka network din kansa ya dauke cakkk ya tsaya jikinsa na rawa tana lura da yanayin nasa wani dadi ya kasheta dabarar ta tayi ya amsa hannunsa har rawa yake ya soma kallo....be karasa ba ya mika mata wayar ya fadi jagwabbbb a kujera fuskarsa cikin tashin hankali yace "bani number wayar da akai miki sending"
Ba musu ta karanto masa yayi dialing number a kashe ya ga alamar massage ta WhatsApp yana budewa number da zahra ta bashi ce an turo masa videon shima tare da dan rubutu a kasa kamar haka..... *muna fatan zakaji dadi sosai wajen kallon wanan video din na tsiraicin kanwarka....kuma* *kada ka zargi kowa da yi maka wanan sai halinka da mummunan furucinka ya ja maka...*
Gumi ne ke digowa a fuskarsa,jikinsa rawa yakeyi kamar ana watsa masa ruwa kallom zahra yayi kamar zaice wani abu ya kasa harshensa yayi masa nauyi ita kuwa wani shaukin soyayyarsa kw ratsa mata jijiyoyin jikinta ga shaawarsa dake fuzgarta...."zahra"ya kira sunanta cikin dasasshiyar murya....
"Naam hubby"
"Zahra dan Allah ki rufa mun asiri da video din nan ko su momy banaso su san an turo miki wanan video din dan girman allah inaso ki zamemun matar rufin asiri na"...murmushin mugunta tayi...tabbas kamal ya fada tarkonta... gyada masa kai tayi kawai batare da tacw komi ba Haka ya mike yana hada hanya ya shige side dinsa ya rufo kofa.....
Kan gado ya zauna gumi na barko masa ta ko ina hawayen bakim ciki ya shiga zubowa kamar am bude famfo...sautin ihun afee keyi masa yawo a kunne na video din wanda yayi daidai da sautin kukan bilkisu na video dinta dake wayarsa....furzar da iska yayi ya kai hannunsa ya dora akansa... Allahu akbar billy ..ashe haka akeji?hawaye suka zubo masa soyayyarta ta da ta dawo masa sabuwa ta lullube duka sassan jikinsa da jijiyoyin da jini ke yawo a jikinsa....
**********
Tun shigowarsu parlorn ya sunkuyar da kansa bugun zuciyarsa ya tsananta kusan awa daya kenan babu ummah babu bilkisu ko ina suka shiga oho?ko kuwa suna shirya yadda zaai a kamashi ne? Allah sarki innah da zainab da bintu da surayya kannensa?ya dace ace yayi sallama dasu kafin ya fito domin ba lallai bane ya koma garesu....hawaye ke duga akam rigarsa,kamshin turaren bilkisu ya gauraye parlorn lokacin da ta iso ummah na biye da ita,muryar ummah ce ta saita masa tunaninsa "shaawah ki dora abinci da wuri saboda ina dan wani abu a nan dik abinda ya dace kiyi kiyi,kisa amina da safiya su gyara kayan miya koda yake naji kunce amina ta canja suna zuwa slimzy ko?tazo birni ta waye"
Dariya bilkisu tayi "ummah ai tuni amina ta koma slimzy dagaji ranan na zageta da sunan nace slim shikenan inda zaki shaketa batasan maanar ba ma tsabar iskanci irin ta dan kauye,da safiya da amina idan suka waye mun shiga ukku"...sosai ummah tayi dariya "keda wadanan yaran bilkisu sai allah kuma sonsu kike"
Zama ummah tayi a kujera ,bilkisu ta zauna can nesa ta dauki remote ta rage karar sanan ta dubi ummah tai mata alama da suyi magana.....cikin natsuwa da dattako ummah ta kira sunan Abdul "Abdul yi hakuri mun tsaidaka tum shigowarka muka shiga ciki wani dan abu mukayi sanan toh gani nadawo gareka abdul inaso ka sanar dani yadda akayi ka lalatawa yata rayuwa,inaso ka sanar dani dalilinka wani ne yasaka Koko kaine kayi niyyar hakan?"
Shiru abdul yayi sanan daga bisani ya nisa yace "banida niyyat cutar da kowa a rayuwata,saidai cuta ce tayi sanadiyyar da na cutar da bilkisu"
Kallom juna ummah da bilkisu sukayi ya cigaba da magana kamar haka...
"Kamar yadda kuka sani sunana Abdulhrahman balarabe, mahaifiyata sunanta saadatu amma innah muke kiranta,muntaso cikin tsananim talauci da babu kasantuwar mahaifina makeri ne a kasuwa yanada dan uwa malam habu,sai mahaifina yayi wahala muke samun abinda zamuci saar mu daya daya kasance baa gidan haya muke zaune ba gidan kanmu muke a wanan halin nake makaranta kafin inje makaranta ko idan nadawo ina zuwa kasuwa wani shago babba na kayan masarufi a nan nake dako idan an siyi kaya a biyani in dauka ta wanan sanaar da kyautuuka da nake samu nake biyawa kaina makaranta insiyi littafai har kannena,ina matakin karshe a university ciwon ajali ya kama mahaifina ga karatu yayi zafi bana ko zuwa kasuwar da nake rabawa ga mahaifina a gida a wahale muke abinda zamuci ma bamu samu makota ke tsan mana idan kanwata zainab taje tayi tayin aiki kusa da gidan mu saita kawo mana a rarraba muci mu kara da ruwa da yamma....daren ranan wata alhamis ciwon mahaifina yayi tsanani gashi bamu da kudin magani haka muna kallo yake aman jini ta hanci ta baki saidai mu zauna muyi tagumi muna kallonsa ranan muna zagaye dashi ko wannenmu idonsa hawaye yakeyi ya dubeni yace "Abdul ga kannenka nan surayya da bintu da zainab ka kula dasu ka tsaya ka inganta rayuwarku,kada kabari kannenka su wulakanta ka inganta rayuwarsu ta hanyar basu ilimi da tarbiyya ni tawa ta kare abdulhrahman"abinda ya iya cewa kenan yayita shakuwa daga bisani rai yayi halinsa...dani da innah ta da kannena munyi kukan rashinsa sosai saboda yadda yake kaunarmu yake kulawa damu da dadi babu dadi....bayan rasuwarsa haka na rungumi kannena muke zaune watarana mukan wayi gari mu kwana bamuci ba a haka rayuwa ta cigaba da tafiya a wahale na gama karatu na,innah ta wankau takeyi ta ciyar damu...
Bayan wata daya da gama karatu na nasoma rashin lafiya a tsaitsaye wata rana naje shagon mu inda nake aiki haka nake daukar Kaya da zazzabi dik kayan jikina sun jike da gumi da idan zazzabin ya sauka yake karyo min ga wani irin suka da nakeji a kirjina nayi cinikin dari takwas da sabain a wajen ina kwance zazzabi ya lullubeni sai rawar sanyi nakeyi abokina sunusi ya dau Kaya ya kai ya ganni gefen shago kwance kudaje suna bina beyi wata wata ba ya tambayeni abinda ke damuna bana ko iya magana sai cikina da nake nuna masa yana mun ciwo ya taba jikina yaji zafi rauuuuu hawaye yake bin fuskata ya tallaboni ya tari mai napep muka tafi gidan mu.
Innah na zaune tayi dambu na gari ko mangyada babu taga ana kokarin shigowa dani take ta fashe da kuka ta soma fadin "shikenan na shiga uku gatana ya kare ya zanyi da raina?meyasameka abdulhrahman dan allah kada ka mutu kabarmu kaine jigon gidan nan meyake faruwa dakai?"...kuka takeyi sosai ta kasa magana ganin tana kuka yasa nakasa magana sai hawaye bintu itace bataje islamiyya ba saboda yunwa sauran suntafi itama kukan tasa haka makota aketa shigowa ganina....
Daddare kwana mukayi babu bacci saboda ciwon da nake ciki ga amai da nakeyi kore sharrr wani irin suka nakeji a cikina haka innah ta nemi garin bagaruwa take bani a cewarta ulcer ce kamar yadda wata makociyarmu ta fada mata ranan kwana mukai a haka washe gari abokina yazo ya daukeni da innah mukaje asibiti....asibitin gwamnati mukaje munsha wulakanci kafin aka karbeni aka dauki jinina gwajin typhoid da malaria akayi farko babu akayi na siga shima babu anayin na hanta ya nuna inada ciwon hanta....tashin hankali!!!!!inna ta durkushe a asibitin tanata kuka canjin dake cikin aljihuna da dubu biyun da abokina ya bada aka biya kudin test babu na magani....haka muka juyo gida jiki babu kwari....ikon allah ranan nadanji sauki ta jinginar dani a jikin bango da pillow ta tsuramin ido "abdul ko muje mu nemi taimakon malam habu ne kanin mahaifinka ko zaa samu na maganin?"ta tambayeni tana hawaye....girgiza mata kai nayi alamar ah ah idona cike da hawaye dakyar na iya ce mata "innah kin mance ranan bamuda abinda zamuci kwananmu biyu munashan farau farau mukaje yace babu shi babu mu?"...innah batace komi ba sai kuka.
Sati na daya ikon allah nasamu sauki ranan da ciwona ya kara tashi ina wajen wani bakanike inda nakoma ina zuwa ina tayasa aiki sabida shagon mu tuni aka koreni saboda ciwon hanta ranan ina gefen benchi zaune wani hadadeen saurayi dan masu kudi yazo ya paka motarsa ya fito ya shaidawa oga motarsa na zubarda bakin mai cikin mintina aka gyara masa motar ya bimu da kudi dubu daya daya yana miko mim hawaye ya gangaro a fuskata cike da farin ciki hannuna har rawa yakeyi na karba na kasa yi masa godiya lokacin rawar sanyi nakeyi ya kureni da ido kamili ne shi a fuskarsa babu mugunta har ya juya ya dawo ya yafitoni da hannu "meyake damunka ne?naga na baka kudi ka karba kana kuka sanan naga kamar baka da lafiya kada kace na shiga rayuwarka da tambaya"cike da tausayawa yake maganar ganin hakan yasa hawayen da nake kokarin boyewa suna zubomin ya kafeni da ido yana kallona cike da tausayawa haka kawai nakeji a jikina zai taimakeni hakan yasa nafada masa halim da nake ciki na rashin lafiya da kudin magani take ya kirgo kudi dubu goma ya bani naki karba dakyar na amsa cike da tsoro,ya bukaci inbashi lambar wayata na bashi mukai sallama ya shiga motarsa yabar wajen,bin motar nayi da ido cike da fargaba haka kawai naji gabana yana faduwa ranan banje gida ba saida na aunar mana shinkafa yar hausa da garin tuwo naje gidan da murna ta,....innah tayi murna kwarai ta tambayeni inda na samu nake fada mata tai masa addua sanan taimun gargadi da inbi a hankali rayuwar nan babu yadda musamman yanzun da maza suke lalata da maza kada in saki jiki yazo ya nemeni da iskanci.....
*Bayan kwana goma*
Kwatsam ina kofar gida ranan naga mota ta tsaya inata kallon motar kamar wawa wanda nagani ya fito daga motar yasa na washe baki na karasa na mika masa hannu shima murmushin yayi "jiki yayi kyau malam dama can naje wajen aikinku akace katashi shine akaimun kwatance nazo gida duba jikin naka"
"Nagode ranka ya dade allah ya saka maka da alheri Allah ya bar zumunci"...
"Sunana kamal muhammad ba ranka ya dade ba"...dariya nayi naga wata yar budurwa a gaban motarsa na daga mata hannu sunada kama da kamal kamar yadda ya kira sunansa,dik yadda naso da ya shiga ya gaida innata yaki mundade muna hira kafin yacemun zaizo washe gari ya canjamum asibiti inda zaa duba lafiyata da kyau....
Har kukan murna nayi ranan sanan ya sauke mana buhun shinkafa daya kawo mana na shiga dashi gida innah bataso hakan ba saidai gargadi da takeyimun na sheda mata mutumin kirki ne,washe gari ya kaini asibitin da muka hadu dake bilkisu ya kaini wajen likita aka dubani akasake gwaje gwaje aka rubutamun magunguna kusan dubu ashirin da shida ya kashe mun sanan muka dawo,muna tafe muna hira ina mamakin dama akwai irin wadanan mutanen a rayuwa?tsoro da mamakinsa ke kamani don yadda yakemum tamkar dan uwansa saidai maganarsa tamkar basarake yake yinta sanan be fiye faraa can ba saidai murmushi....
Tunda kamal ya tafi bansake ganinsa ba wajen wata daya da kwana goma magungunan da nakesha suka karbeni suka kare banida kudin siyan wani maganin ga ciwo daya taso ranga ranga abinda zamuci bamuda shi daga ni har zainab a kwance muke bamuda lafiya rai a hannun allah musamman zainab da mummunar ulcer ta kamata saboda yunwa saidai in tasata inyita kuka kawai nima ga ciwo ina fama dashi ranan da yamma yaro ya zo yace ana kirana a waje wani mai mota....jikina har rawa yake inaji a jikina kamal ne ina fita na ganshi tsaye da kananan kaya wanan karon fuskarsa babu annuri ina isa ganinsa haka gabana ya fadi kallona sosai yakeyi ta cikin gilashinsa me dan duhu sanan ya budemun mota yacemun muje,gabana na faduwa na shiga gaban motarsa tafiya muke babu kakkautawa har muka isa wani GRA gida ne babu kowa nada ne shikadai naga alamar haka ne da ganin manyan hotunansa dake manne a babban parlorn da muka shiga....
Tsaye yayi baya ko faraa "abdul dalilin dakkoka na kawoka nan shine don in sharema hawaye in cireka daga kangim talauci yayinda kaima zaka sharemun hawaye ka cikamun burina da kuduri na ta hanyar karbo budurcin wata yarinya da nakeso kayimun"... hantar cikina ta kada na zabura na mike inaja da baya idona tamkar zasu fado kasa har nakai jikin bango....bece komi ba ya janyo shisha pot ya kunna ya soma zuka yana busarwa.....tambayarsa nufinsa nayi babu wani shayi ko tunani ya sanar dani yanaso inyiwa wata budurwarsa fyade!!!
Ban jira cewarsa ba na fice daga gidan jikina har rawa yakeyi ko waige banayi haka na fito titi na tari me mashin na hau ina zuwa gida na tarar da tashin hankali ...zainab ce rungume jikin innah ta a galabaice tana hawaye dik ta amare jikinta cikin aman babukomi sai ruwa da jini jini... yunwa yunwa kawai zainab ke ambata tana fadin kirjina kirjina ...yaya ka nemo kudi ka kaini asibiti banaso in mutu banyi karatu na amfanar da alummar musulmi ba banaso in mutu inbarku kaida innah da bintu.....idona rufewa yayi hawaye kawai nakeyi innah kanta muna hada ido na hango damuwa karara a idonta ga ramar da tayi saboda yunwa.....banida option a wanan lokacin karfe takwas na dare kawai juyawa nayi na fuce tsakiyar layinmu na tsaya na saki wata kara na ruga da gudu saman layi na dawo na rasa inda zansa rayuwata ga masokiya dake sukana a cikina jiri na neman kada no saboda yunwa....kamal na ambata shikadai zai taimakeni hawaye suka gangaromin a ido...da kafata naje wajen kamal ya fito kenan zai tafi ya ganni ya saki murmushi zubewa nayi a kasa na ruke kafarsa ina rokonsa ya taimakeni yadda allah ya taimakesa na shiga fada masa halin da nake ciki da kanwata...dakyar nake magana saboda yadda nakejin ciwo a jikina...."matukar zakai mun abinda nakeso to tabbas zan dau nauyin maganinka,zan dau na kanwarka cinku da shan ku dik zan dauka zan kuma baka kudi masu yawa matukar zakaimun wanan aikin".... hawaye nakeyi cikin tsananin bakin ciki da rayuwar da muke ciki na daga hannu sama nace Allah ka gani.... Allah...haka nan na amince da bukatar sa shi ya kawo mutum ukun da suka daukoki a daren mukai magana sanan ya daukeni mukaje ya kaini gida ya dibo kudi masu yawan gaske ya bani.....
Kwana uku tsakani komi ya lafa ranar da zanyi miki fyade ranan na shiga rudani da tashin hankali na tsani kaina na tsani rayuwata gabaki daya ina ma ace banzo duniyaba?....
Hawaye ke gudu a fuskar abdul lokacin da ya gama maganar sanan ya durkusa a kan gwiwoyinsa "bilkisu ki yafemun"...daga masa hannu tayi tana hawaye...kuka takeyi mai ban tausayi "inhar babu zatasa ka aikata abinda ka aikata to tabbas kai ba musulmin kwarai bane kuma bakai imani da kaddara ba kamar yadda akeson musulmin kwarai...don Haka wallahi tallahi na yafe maka amma bana sonka banajin digon soyayyarka a zuciyata".....tana gama fadin haka tabar wajen kamar zata tashi sama dakinta tayi ta rufo kofar ta fada kan gado ta fashe da kuka....
Ummah kuwa share hawayenta tayi "abdul tashi kaje dikda ban gama dakai ba amma nayafe maka kuma zan nemeka a matsayin shaida domin yanzun gidan su kamal zanje zaayita ta kare"....jiri abdul ke gani yanajin zazzabi na neman rufesa ya godewa ummah sanan ya fice ta bisa da kallo ta girgiza kai....
Can nesa da gidan ya zauna ya hada kai da gwiwa koda bilkisu ta tuko ummah zasuje gidansu kamal suna kallonsa ummah tabi sa da kallo billy kuwa ko kallonsa batayi ba tuki takeyi zuciyarta cunkushe da tukukin bakin ciki.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/1, 7:43 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*29*
Tunda ummah ta soma bayani momy ta mike tsaye ta shiga kaiwa da komowa cikin parlorn,wani irin tukukin bakim ciki ke taso mata yana lullubeta,mamaki da al'ajabin kalaman su takeyi lallai ma wato bilkisu ta gama yawon ta zubar dinta saboda ta rasa mijin aure zaa zo a manna wa danta cewar ya lalata mata rayuwa?ta yaya zaace kamal shine yake kwanciya da bilkisu kamar matarsa,shiru parlorn yayi ummah tana sauraren furucin da momy zatayi dikda ta lura da take takenta tunda ta soma bayani "hajiya nayi magana nazo na kwatarwa yata marainiyar Allah hakkinta amma yanayin ki ya nuna baki gamsu da wanan maganar ba"
Wani kallo momy ta watso musu cike da masifa jikinta har rawa yakeyi "wanan makircin shiryayye ne hajiya, yanzun na gano inda kuka dosa daga ke har yar taki wato ta rasa mashinshini ta gama yawon banza zakuzo ku mannawa yarona sharri kuce ya lalata mata rayuwa?tou wallahi karyarku tasha karya tsofaffin munafukai"
Zaro ido ummah da bilkisu sukayi cikin tsananin mamaki suke kallon yadda momy ke jifansu da kalamaai masu zafi har tana cewa wai bilkisu ta gama yawon ta zubar dinta lallai duniya babu gaskiya ko a mafarki bazasu taba tunanin hajiya hauwah zata jefesu da wadanan munanan kalaman ba hakan yasa ummah cikin fushi da zafin rai ta zabura "cin amana ya kare akan danki da ya cuci zumunci yaci amanar zaman tare yakewa yata barazana da video yana kwanciya da ita yana zina da ita bada son ranta ba,kin bani mamaki hauwa dama soso ne sonkai yafi amma wallahi tallahi kisani yadda ya lalata rayuwar yata shima sai an lalata rayuwar kannensa tunda yanadasu"
Zahra ce ta shigo dakin a furgice jin hayaniya ta cika gidan kallon momy tayi ido waje take tambayar "momy lafiya nakejin hayaniya?"...ta juya ta kalli bilkisu da hawaye ya gama wanke mata fuska "Zahra wadanan macutan ya da uwar ne sukazo da niyyar kullawa yarona sharri wai mijinki kamal shikewa bilkisu barazana da videon tsiraici yana amfani da ita wai shine yasa akai mata fyade" zaro ido zahra tayi taja da baya gabanta na faduwa wani kallo ta watsawa bilkisu daga sama har kasa ganin haduwa da zati irin na bilkisu ya girgiza zahra kyawu na halitta allah ya hore mata,take kishi ya lullubeta,no wonder kamal keyi mata wulakanci a wajen kwanciya ashe yana tare da karuwar waje kallon uku saura kwata zahra keyiwa ummah da bilkisu "momy wanan makirci ne amma ninasan miji na ba mazina ci bane idan anzo a kulla masa ne saboda a aurar mun miji wanan karya ne don haka bazai taba yuwu wa ba"....fizgo bilkisu ummah tayi "muje bilkisu kuma wallahi summa tallahi saina daukar miki fansa dikda banida kowa a garin nan sai allah na tabbatar allah baya bacci baya barin hakkin wani da wani kuma kijira abinda zai biyo baya hauwa"
"Iyaka dai kice zaki mikawa hukuma to ina hira mu hadu a kotu".....ummah da idonta ya rufe bakin ciki yasa ko uffan bata sake cewa ba har suka dau hanya a mota....
*******"
Kamal zaune a kujera a gaban table din mahaifinsa a office dinsa suna magana duka fuskokinsu babu walwala kallo daya zakai musu kasan suna cikin matsala "kamal naji hujjarka na cewar kada ayi bincike akan lamarin fyaden ummul khairi afnan amma fa kasani bawai na kyale abun bane abun yana cikin zuciyata ko nan gaba zan iya tada case din sanan zan cigaba da bincike ta karkashin kasa"
Jinjina kai kamal yayi ya sunkuyar da kai,wayar abbah ce tayi kara ya dago ya duba momy ce ke kiran cikin sauri ya dauka ya kara a kunnensa "hello "...ai yana amsawa yaji momy na bambamin masifa baya iya fahimtar me take cewa kashewa yayi ya dubi kamal "gida babu lafiya tashi muje"
Zaro ido kamal yayi "meyake faruwa daddy jikin afnan ne?meyasameta?"ya jerowa daddy wadanan tambayoyin,...hada takaddun table din daddy ya shigayi yana fadin "kalma daya zuwa biyu na fahimta a kalaman momynka naji kamar tana cewa ummah da bilkisu sunzo wai sunce wai ko ka lalatawa bilkisu rayuwa ta hanyar video?oho dai ban fahimta ba"....zaro ido kamal yayi zuciyarta sa bada rasssss tashin hankali wanda baasa masa rana....jikinsa ya hau rawa fitsari na neman kubuce masa abbah kuwa bema san halin da kamal ke ciki ba yadai san cewar ya fada masa koda ya dago da niyyar yiwa kamal magana gumi ya gama sharbe fuskarsa har diga yakeyi "kamal lafiya kake wanan zufar?meye ke faruwa kaga yadda ka fita hayyacinka cikin seconds ko maganar dana fada maka momynka tace ta furgita ka?...calmdown maganarsu ta mata ce muje gidan inji meke faruwa?"....
Dakyar kamal ya yunkura ya mike be lura da kujerar dake gabansa ba yaci karo da ita yayi tuntube kadan ya rage be kai kasa ba "yi hankali kamal kada ka fadi,be a man mana"...abbah yayi gaba kamal na biye dashi dik inda suka gifta cikin maaikatar gaida abba akeyi cike da girmamawa har suka karasa parking space kallon kamal abbah yayi "mu shiga motana kaja sai mubar taka a nan ko"
"Toh abbah"kawai yace ya zagaya wajen driver ya shiga saida ya tada motar abbah ya bude ya shiga shima....
*********
Hawaye ke gudu a fuskar Abdul yayinda yake durkushe a gaban innarsa ya hade hannuwansa yana rokon gafararta "innah kiyafemun dan girman allah wallahi nayi hakan ne in tseratar da rayuwa ta da ta kanwata,nayi hakan ne domin in ceci rayuwata data zainab a lokacin da muke cikin kangin rashin lafiya da tsananin talauci innah"tsaigaitawa yayi da kukan sanan ya kwashe labarin dalilin da yasa yayiwa bilkisu fyade ya sanarwa da innah,
Sosai jikin innah yayi sanyi batasan lokacin da itama ta soma kukan ba tausayin kansu ya kamata wani irin kaunar danta ke ratsa mata zucuya,soyayya irinta d'a da mahaifi batasan lokacin data ruko hannun Abdul ba tana zubarda hawaye ta shiga murza masa hannu "nayafe maka abdulhrahman nayafe maka duniya da lahira,abu daya ne zanyi maka gargadi dashi shine nan gaba koda talauci zai kashemu abdul koda zamu mutu bamuci ba kada ka aikata zunubi ka ciyar damu da haram gara mu mutu inhar saida haram zaka ciyar damu tawakkali da allah shine cikar imani fa musuluncin musulmi na kwarai bakaji annabi yace cikar imanin mutum shine imani da kaddara mai kyau da mara kyau?yanzun da ka mutu a wanan halin kaga shikenan ka mutu tare da fushin ubangiji domim zina kayi ka mutu me zaka cewa allah?ka roki gafarar bilkisu da mahaifiyarta idan kanason zaman lafiya"
Jan numfashi yayi yasa hannu ya sharce gumi da hawayen da suka dame fuskarsa "innah bilkisu ta yafemun haka ma mahaifiyarta matsala daya ce innah bilkisu bata sona ta tsaneni ni kuma ina sonta nine mutumin daya dace da in aureta in share mata hawaye saboda nine na yage yanar budurcinta da karfi da yaji amma ta tsaneni ko ganina batason yi niko yanzun wutar soyayyar ta ke kara ruruwa a cikin zuciyata"....
Girgiza kai innah tayi cikin alhini da tausayin halin da abdul ke ciki hakika soyayya masifa ce zama yayi dirshan ya rike kansa dake barazanar tarwatsewa yana cigaba da zubar hawaye....innah kuwa tagumi tayi tana kallonsa dik yadda ya rame ya zabge ya koma kamar sabon kamu na hauka.....
*********
Kaiwa da komowa zahra takeyi a sashenta sosai takejin zafi a cikin zuciyarta tabbas a idanuwan bilkisu da ummah tana iya hango tsantsar gaskiya a kwayar idanuwansu tabdijan akwai yaki a gabanta....shiko kamal sashensa yayo kawai da suka shigo da abbah tsananin fargaba da zancen zuci yasa ya shigo ko sallama babu kallo tabi shi dashi "hubby ko sallama babu"
A daburce kamak yace"sorry billy nayi sallama"...zaro ido tayi kirjinta na bugawa a hargitse a daburce tace"nice billy au bilkisu kake kirana dashi?"
Daka mata tsawa yayi jin yadda take masa magana cike da isa"ke har kin isa ki samun doka ko kiyimun gyara mutuniyar da ta gama watsar da mutuncinta a titi?au zakimun barazanar ustazancin ne karuwa?ke kinsan darajar sallama ne zahra karki kuskura kice zaki shigar mun hanci kiyimun gyara"....
Wani tsalle zahra ta daka Tasha gaban kamal "kai dakata tsohon munafuki?auuuu ni kake kira da karuwa ma?ai idan ni karuwa ce kai ma mazinaci ne"...ya daga hannu ya sharara mata mari ta dago ya kara kai mata wani jikinsa har rawa yakeyi yana kallonta idonsa a kankance "ni kike kira da mazinaci?nine mazinaci da uwarki nai zina?"
"Uwata tafi karfin tayi zina dakai wallahi ai mazinaci baya aure saida mazinaciya don haka allah yasa ka aureni a tunaninka ka samu mace malama bayan ka gama lalata yar uwarka?kazo kaimun borin kunya har ka daga hannu ka mareni to wallahi ka dibo ruwan dafa kanka domin abinda kuke dukunkunewa zan fallasa wallahi saina tonawa iyalan gidan naj asiri saina watsa wanan video din wallahi"aiko kamal yayi kanta ya fuzo wayar ya maka ta da kasa....maimakon zahra yaga taji haushi sai yaga ta fashe da dariya"aikin banza ka fasa wayar ne?tou wallahi na tuttura a inda zaa ajiyemin ka sani ni allah ne ya kashe ya bani makamin yaki da kai saboda kai azzalumi ne"...
Jikin kamal yayi sanyi ya tsaya cakkkk gabansa na faduwa ita kuwa wucesa tayi tai cikin daki ya rufa mata baya yana kiran sunanta...."zahra zahra look tsaya kiji"...bata ko sauraresa ba ta fito da gyalenta ya sha gabanta "look kiyi hakuri tsaya kiji"yadda yayi maganar idonsa na kawo hawaye sai ya baka tausayi murmushin mugunta tayi "umhmmm ina jinka"
"Ina zakijr?dan allah kada ki fita ki tonawa yar uwata asiri xahra"kwalla ta ciko a idonsa "bazanyi ba zan siyo waya ne kaga wanan karamar call kawai nake amsaewa ina bukatar babbar waya"
"Ok ok is ok bari inyi miki transfer ki siyo iphone x tayi miki ko?"...gyada masa kai tayi tana murmushi tana kauda kai take yayi mata transfer "driver yaji sauki ai ya kaiki "
"Dama shi zai kaini"
Tana fita ya zauna jagwabbbb a kujera kansa na sara masa abubuwa suntaru sunyi masa yawa....wayarsa ce tayi kara ya janyo abbah ke kira jikinsa ya soma rawa gabansa ya soma faduwa....dakyar ya dauka ya kara a kunne "dik inda kake kazo yanzun"da kakkausar murya abbah yayi maganar.....
********
A kofar siyan wayar suka hadu da TJ da zahra murmushi sukayi ganin driver yasa Zahra tace "yaya tj ina yini?"ta kifta masa ido take ya gane karatun ya dubi driver da har yanzu bakinsa be gama warkewa ba suka gaisa....sosai driver yake kallon kwayar idon TJ idon mutumin da yayiwa afnan fyade ya dawo masa a ido nan da nan jikinsa ya soma rawa yana kallon yadda zahra keyi masa magana tana karya murya.....
********
Shigar kamal parlorn daddy ya daka masa tsawa "kamal mahaifiyarka tayi wawanci tayi rashin tunani banji dadin yadda ta wulakanta ahalin dan maliki ba banji dadin yadda tayiwa bilkisu yar aminina ba.....bawai na yarda da cewar ka aikata bane amma dan yau yafi karfin a yarda dashi kamal kai mutumin kirki ne kanada natsuwa kamala addini iya bakin kokarina nayi wajen yi maka tarbiyya amma dikda haka ban amince da baka aikata hakan ba kamal.... matukar ka aikata haka to tabbas zaka fuskanci hukunci na kamal menene alakarka da bilkisu da abdul rahma da video na fyade da akayi mata kake using dinsa kana amfani da ita?"....daga momy har abbah zubawa kamal ido sukayi momy gabanta faduwa yakeyi allah yasa kamal be aikata ba kamal dinta bazai taba aikata hakan ba.....shiko abbah nazarin kamal ya shigayi ...hawaye ne ya gangaro a fuskar kamal jikinsa yayi sanyi sosai nadama ta shigesa ta yaya zai sanarwa da momy da abbah cewar yayi zina?wanan wani irin masifa da abun kunya ne?......hawaye ke gudu a fuskar sa kawai ya durkusa akan gwiwoyinsa ...momy jikinta ya kama rawa...runtse idonta tayi tana adduar Allah yasa be aikata ba...shiko kunyar idon mahaifinsa yakeji shine yayi zina da bilkisu.......
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA KA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/2, 7:47 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*30*
Sunkuyar da kansa yayi hawaye na gudu a fuskarsa kasa magana yayi,jikinsa ne yake rawa ga gumi da yake sauka a fuskarsa kamar an watsa masa ruwa....nazarinsa sosai daddy yakeyi yana kare masa kallo cike da mamaki da al'ajabin yanayin nasa "kamal kai nake jira kayi magana,ka barmu tsaye dagani har mahaifiyarka inaso inji daga gareka domin ni ba irin mahaifiyarka bane bazanyi shedar dan yau ba dan haka bismillah ina sauraronka idan kuma kafi so mu dunguma muje can to"
"Kai kamal ka wanke kanka kaji na fada maka ko?"momy tayi kwafa ta hade girar sama da ta kasa...
Dakyar kamar ya saita natsuwarsa gabansa na cigaba da faduwa "daddy.....momy...ku gafarceni tabbas na aikata son zuciya na aikata zina da bilkisu sanan nine nasa akayi mata fyade...."...ai bai karasa maganar ba daddy ya zabga masa mari ya dago ya rike kuncinsa na dama ya kara zabga masa ta dayan sashen "amma ka cika cikakken dan isaka mayaudari maci amana mai fuska biyu wanda kake amfani da kamanninka kake rudar mutane kake rikida kamar hawainiya, ba bilkisu ka cuta ba harda ni domin ka cuci amintata da mahaifinta"...juyawa dady yayi kamar zai bar gaban kamal ya juyo a fusace ya kara zabga nasa mari "fyade...ka aikatawa yar mutane? innalillahi wa innah ilaihi rajiun"...afee da nawal kamar daga sama suke jiyo sautin hayaniyar daddynsu hakan yasa nawal ruko hannun afee suka fito parlorn a razane daddy bai lura dasu ba "fyaden da ka aikatawa yar wasu kasa akayi mata shi ne ya bibiyi kanwarka batasan komi ba aka aikata mata mummunan aiki ashe kaine kaja mata kaiwa yar uwarka cin zarafi ta hanyar keta mata rigar mutunci"
Toshe kunnuwanta afeee tayi kalaman abbah keyi mata yawo a kunne suna barazanar tarwatsa mata zuciya ta kwalla kara cikin parlorn,a razane suka juyo har kamal da fuskarsa ta jike da hawaye suka hada ido tai saurin kauda kai tana gunjin kuka "yaayah kamal ka cutar dani ka cuci rayuwata yaayah ashe dik tarbiyyar da kake kokarin doramu akai kana mana kulle hatta social media ka hanamu ashe abinda kake aikatawa anty billy kenan"....hawaye ke sauka a fuskarta ta ruga da gudu hanyar dakinsu ta zame ta fadi saboda rashin kwarin jikinta da kafarta "afnannnn"kamal ya kira sunanta ya ruga da niyayar dagata "dakata yaayah kada ka tabani wallahi idan ka tabani saina kashe kaina"cakkkk kamal ya tsaya jikinsa na rawa yana kallon yadda afnan ke jifansa da kallo mai cike da tsana,yamutsa fuska tayi tana jin ciwo a kwankwasonta zafi ya dira a kasanta da dinkin be gama warkewa ba tace "wayyooo Allah yar uwata nawal zoki dagani ina kaunarki".....sosai tausayin afee ya mamaye abbah ya zare glass din fuskarsa ya goge kwallar data taru a fuskarsa...
Kamal kuwa iya tashin hankali ya tsinci kansa ciki tunda ya taso bai taba ganin hawaye a idon mahaifinsa ba yau dalilin abinda ya aikata yasa mahaifinsa na kuka akansa? innalillahi wa innah ilaihi, runtse idonsa yayi ya rarrafa har gaban mahaifinsa ya ruko kafarsa "abbah ka yafe min kai min dik hukuncin da zakaimun amma banason ganin hawaye a idonka"
Hankade kamal yayi "ka cuceni kamal ka cuci kanwarka ni ba mazinaci bane mahaifiyarka ba mazinaciya bace dangin mu kaff babu mazinaci kamal saikai kiri kiri ka rufe idonka ka cuci yar mutane,ashe dalilin da yasa kace bazaka aureta ba kenan?ashe dalilin da yasa kaki karbar tayin aurenta?saboda ka riga kaci moriyar ganga?shiyasa ka watsamun kasa a ido kace baka sonta bazaka aureta ba?"
Kuka kamal yakeyi "wallahi abbah ina sonta ina son bilkisu a yanzun daidai nake da in amsheta a matsayin matar aurena na gano cewa bilkisu itace abokiyar rayuwata itace rayuwata gaba ki daya daddy ka tausayamun kayafemun"
"Dalla gafara can ai kabar shiri tun rani ka kuma cuci kanka wallahi banajin bilkisu zata amince da aurenka da ta gama sanin kai azzalumi ne kuma ka cuci rayuwarta.....bansan da wani ido zan kalli iyalan alhaji bala dan maliki ba marayun Allah ubanta ni ya mikawa amanarsu da ita da uwarta kasantuwar mahaifiyarta yar nijar ce mahaifinta yaxo garin nan yayi aure ya haifeta shi kuma ya aura iyayenta a hanyar komawa nijar gaida iyayensa sukai hadari suka mutu koda taje nijar batasan kowa ba bataga dangin iyayenta ba ta dawo take zaune da alhaji Bala harta haifi bilkisu wadda daga ita bata kara haihuwar kowa ba amma ka cuceta da wani ido zan kalli wadanan bayin allah"....juyawa abbah yayi ya rike kansa da ke sara masa takaicin kamal ya gama lullubesa....
Wani irin kallo abbah ke warsawa momy dake zaune jikinta a mace motsin kirki ta kasa "kinji kunya da kika rufe ido kika wulakanta wanan baiwar allah dik yadda takeson danki amma kika goyi bayan danki,kingani baa goyon bayan dan yau hajiya hauwa"
Sunkuyar da kai momy tayi tai shiru parlorn yayi tsittt na dan wani lokaci karar fanka kawai kakeji sai sautin kukan afnan da nawal dake dakinsu...
Wani kallo abbah ya watsawa kamal "ka je ka canjo kaya kazo muje gidan domin dakai zaa kaida mahaifiyarka dikda idan naje bansan me zamuce musu ba"
Mikewa momy tayi tai dakinsu nawal ta tura kofar a rungume da juna ta tarar dasu suna kuka nawal ke lallashin afee itama tana nata kukan..."ku taso zamuje gidan su antyn ku bilkisu"
Girgiza kai afee tayi "ni bazanje ba domin bansan da idon da zan kalli anty billy ba"tausayin su ya kama momy kwalla ta ciko idonta ta karasa dakin ta zauna gefensu ta ruko hannuwansu dik ta Shiga lallashinsu dakyar suka amince sukayi shiru suka share hawayensu suka biyo momy.....
*********
Zaune ummah take a parlor ta rafka tagumi tana rungume da bilkisu dake faman kuka ,tun shigowarsu bilkisu ke kuka taki magana ajiyar zuciya take saukewa minti minti cikin gunjin kuka bilkisu ke zubar hawaye tana fadin "ummah na dik duniya banida kamarki ina sonki ummah na,yanzun hakan zamu cigaba da rayuwa bamu da dangi bamu da gata? Allah sarki abbah na allah ya jikanka kayimun gata kana sona allah ya rabani dakai ina sonka abbah ka tafi ka barni a hannun azzalumai"...cakkkk abbah ya tsaya a parlorn yana sauraron kukan bilkisu da takeyi kallon juna sukai shida momy ta kauda kanta...
"Ummah na shikenan bamu da gata?"
Daga bakin kofar abbah ya furta da karfi da kwarin gwiwa "kunada gata bilkisu yata gani nine gatanki nazo gareki"...yunkurawa bilkisu tayi daga kwanciyar da tayi gashin kanta a baje tamkar mahaukaciya take kallon abbah fuskarta jike da hawaye kallonsa takeyi ko kiftawa batayi , har suka karaso patlorn a tare nawal na rike da hannun afee da momy kamal na biye dasu "nine gatanki bilkisu meyasa ina raye kike fadin baku da gata kin manta nima mahaifinki ne?dik abinda mahaifinki zaiyi miki bilkisu zanyi miki fadamun me kikeso inyi miki?wani hukunci kikeso in yankewa wanan azzakumin dan uwan naki?"
Dukkansu a tsaye suke bilkisu na bin ko wannensu da ido jajir saboda kuka bakin idonta kawai kake gani gudan idonta tamkar gudan jini Haka ya koma....ummah kauda kanta tayi zuciyarta na tururi kallon kamal ta kasa yi dakyar ta bude baki cikin bakin ciki tace "sannunku da zuwa alhaji,ku shigo ga wuri ku zauna bari a kawo lemo da ruwa "
Dagawa ummah hannu abbah yayi "bama bukatar komi hajiya mu yanzun gareki mukazo neman gafara da yafiya dikda abinda akayi muku yafi karfin yafiya wallahi idan har bilkisu tace bata yafe ba da hannuna zan mika kamal hannun hukuma su hukuntashi a mikasa gidan yari sanan a zartar masa da hukunci"cikin daga murya da kakkausar murya yake maganar hade da tsananin fushi.....tsitttt parlorn yayi kowa baya iya magana zubewa kamal yayi akan gwiwoyinsa a gaban ummah ya fashe da kuka ya ruko kafafuwanta "bani da isassun kalmomin da zanyi amfani dasu wajen rokonki gafara uwata,hakika na tafka babban kuskure na bi rudin zuciya nayi anfani da kudi da *IZZA TA* wajen aikata mummunan aiki ga yar uwata kanwata bilkisu ....babu abinda zance face zan dauki dik wani hukunci da zaku yanke mun,..saidai zan iya abu daya wajen kokarin wanke kaina da rufawa yar uwata asiri shine in aureta.....
Daga kofar parlorn aka amshe da "baka cancanci auren bilkisu ba kamal domin nine na dace da in aureta tunda nine sanadiyyar rabuwarta da mutuncinta da budurcinta"....abdul rahman ke maganar yana hawaye babu karsashi a tare dashi sai karfin hali da karfin gwiwa da innah ta bashi wajen rakoshi neman gafarar bilkisu....tsaye sukayi a bakin kofar patlorn shida innah wadda ke tsaye gefensa sanan zainab tana biye dasu a bayansu....
K'ara mai karfi bilkisu ta kwalla ta ruga aguje tayi cikin dakinta ta rufo kofar......
Sunkuyar da kai momyn kamal tayi cike da takaici da bakim cikin wanan balai sanan shin ya ma zaai kamal yace zaiyi aure yanzun yaushe yaushe yayi aure ko wata daya cikakke baayi ba?....
0 comments:
Post a Comment