Gyara zama zahra tayi hannunta rike da na TJ a parlorn anty binafa yayarta,kurbar fanta tayi mai shegen sanyin gaske gass ya ratsa kanta ta lumshe ido sanan ta budesu suna kallom juna da tj kafin daga bisani suka fashe da dariya....jin sahun takun anty bina yasa ta saki hannun tj da take murzawa a hankali yana lumshe ido...
Hannun anty bina rike da plate guda biyu da abinci lafiyayyar jealouf sai tururi takeyi da nama ta ajiye akan centre table "ya naji kuna ta sheke dariya ne meye kuma ya faru wace muguntar kuka sake hadawa shegu biyu"
Neman kujera tayi tana fuskantar su,yar dariya zahra tayi ta karkace fuska tana dariyar mugunta ta shiga kwaikwayon yadda kamal ya rude yana kuka ranar da akaiwa afee fyade,kungani har cewa yayi "momy afee ce akaiwa fyade wasu azzalumai"sai hawaye sharrre kamar mace,da anty bina da tj dariya suke sheke dashi tj ya buga kujera "shegiya zahra batdakama zahra shedaniya ce ke kamal ya dibo ruwan dafa kansa"...dariya sosai zahra tayi ta kaiwa tj duka a kafada "bega komi ba tunda ya kirani da karuwa wanan kadan ya gani idan Allah ya cikamun burina ma saina maida afee cikakkiyar karuwa mai lasisi da garanty"
Suka kara fashewa da dariya "sanan yanzun inada makami a hannuna, wallahi dik wanan abun da nayi nayisa ne saboda yaji zafin kirana karuwa da yayi sanan yaga yadda akai amfani da wanaj ficiciyar kanwarsa mai k'ugu kamar na bazawarin kare,kai tj kayi kokari ma da ka hau wanan abar domin kasusuwa zakaita karo dasu don yarinya ce gashi ba jiki gareta ba siffar masu sickla gareta"
Tj dariya harda hawaye "shegiya zahra ke wallahi kwankwaso ne batadashi dikda take yarinya tanada hips sananfa itama akwai zuma don da zan hadu da ita karawa zanyi,saidai ban sakar mata nauyi na ba dan tsaf zan yagata har bayanta kindai san yadda nake"ya shafa gemunsa yana kada kai yana murmushi...
Kada kai zahra tayi ta sakar masa dariyar mugunta ya kifta mata ido....
"Yaki na gaba shine shi kansa yanzun tuhumarsa akeyi da yiwa yar aminin mahaifinsa fyade"
Zaro ido tj da anty binafa sukai "kai zahra gaskiya bamu yarda ba wanan karya ce kina nufin salihin mijinki shima dan hannu ne?"
Gyada musu kai tayi tana kada kafa "dan hannu ne wallahi inba haka ba Babu yadda zaai yasan mace cikakkiya guda,sanan yanzun na tabbatar momy bata amince da abinda akace yayi ba amma daddy zai amince nasan zaace zaa aura mishi ita tou wallahi bazan taba zama da kishiya ba muna sharing sandar girma ta mijina wai kunsan yadda yake kuwa?dadin kamal daban ne bantaba samun cikakken namiji mai zati da haiba irinsa ba gwarzo a fagen kwanciya ba don haka bazan barshi da wata ba matukar yayi yunkurin aurota to zaai mutuwar kasko"...tana fadin haka ta mike tsaye tana kokarin daukat gyalenta tace "antyna waya na fito siya fa muka biyo driver na jirana dikda sai shiru shiru ne amma zan gargadesa "
Mikewa anty binafa tayi "akwai wata zuma da na siyan miki ita bari in dauko miki da kinje gida kisa a kofi kisa madarar peak ta ruwa ki juye ki shanye yau ko kogi bazai kaiki zubar ruwa ba da rab'a sai ya rude"...tsalle zahra ta daka "kai antyna nagode sosai Allah ya saka da alheri"anty ta wuce bedroom...
Wani irin kallo tj keyi mata cike da duniyanci "kina nufin kin murza hannuna kin tada mun da shaawa zaki tafi ki barni haka?"....zaro ido zahra tayi ta waiga "kai anty zataimun hauka koda tai duniyancinta batayi da aure don haka kabar maganar nan gobe zn kiraka zamuyi magana"
"Promise?"ya kashe mata ido itama tai masa,fitowar anty binafa suka basar ta karba suka rakata har bakin mota driver har ya soma bacci ga rana wajen karfe uku na rana....
Kallon Tj driver yayi yana karewa kwayar idonsa kallo ganin haka yasa zahra daka masa tsawa "meye Haka?wani irin iskanci ne zaka rinkawa yayana wanan kallon?"
"Yi hakuri ranki ya dade"kawai yace ya kunna mota hade da hadiyar wani mugun miyau kwatttt
********
Bayan fitowar bilkisu komi ya lafa daddy ya dubi innah "baiwar Allah kin cika mace ta gari mai tarbiyya da kula da sanin ya kamata da har kika iya namijin kokari wajen biyo danki nemawa danki gafarar wadda ya zalunta allah ya saka miki da alheri"
"Ameeen"innah ta karba kallon kowa yayi yanda parlorn yayi shiru ya juya ga bilkisu da ta sunkuyar da kanta kasa "bilkisu ke akaiwa laifi da mahaifiyarki dik dalilin haka ya kawomu don haka ni na ari bakin kamal da abdulhrahman wajen rokar musu gafararki kiyafe musu don Allah"
Jan hanci billy tayi sabbin hawaye suka gangaro mata "daddy hakika har gobe har jibi kai mahaifi ne a gareni babu abinda zaka nema a rayuwa banyi maka ba,domin kaine gatanmu katangar da ta zame mana garkuwa a garin nan don haka ko a lahira wani yana cin arzikin wani hakan yasa nayafewa abdulhrahman da kamal laifin da sukaimin duniya da lahira"ta fashe da kuka daddy yayi kabbara "Allahu akhbar bilkisu diyar albarka ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki zuria da yara masu tarin yawa kinji"
Jinjina masa kai kawai tayi tana hawaye innah tasa gefen hijabinta ta share hawaye saboda tausayin bilkisu da takeji,zainab kuwa rarrafawa tayi ta karasa gaban bilkisu tana dago ido suka hada ido bilkisu tai murmushi fuskarta sharkaf da hawaye suka fashe da kuka a tare...afee da nawal karasowa sukayi suka zagaye bilkisu suna kuka ganin hakan yasa bilkisu share hawayenta ta rungumo afee jikinta taji yadda zazzabi ya lullubeta da sauri ta kama hannunta cikin dasasshiyar murya "muje daki inbaki magani akwai zazzabi a tattare dake afeen anty billy"..makale kafada afee tayi duka mutanen parlorn kallonsu sukeyi cike da shaawa, Banda daddy da tausayinsu duka su biyun da halin da suke ciki ya lullubesa afee ta mike tabi bayan bilkisu nawal da zainab murmushi sukayi wa juna suka mike suka bi bayansu....bayan tafiyarsu daddy yayi gyaran murya "naso ace a cikinku kamal ya auri bilkisu saboda abinda yayi Mata"da sauri abdul ya kalli abbah idonsa sunyi zuru zuru tausayin abdul yasa abbah datse maganar da "a cikinku duka ku biyun kuje ku nemi soyayyarta ku sansanta Wanda takeso ko ta amince da aurensa ni zanyi komi in biya sadaki"..sunkuyar da kai kamal yayi yanajin wata sabuwar kunyar ummahn bilkisu ta lullubesa yanajin kunyar mutanen dake cikin parlorn,sammm idan har abdul ya auri bilkisu to tabbas shi mutuwa zaiyi a halin da yake ciki bazai taba iya bari wani ya kusanci bilkisu ba a matsayin mijin aure....
Sunkuyar da kai abdul yayi yana tunanin yadda zai fuskanci bilkisu ya lallasheta ya dawo da soyayyarsa dikda yasan abu ne me wuyar gaske...makullin motar da bilkisu ta bawa abdul ya ciro ya dubi ummah dake zaune tai zugum abun duniya ya tattaru ya tare mata a zuciya Tana zaune ne amma tunani takeyi na daban "ummah ga makullin motar nan da bilkisu ta bani kafin hakan ya faru"
Murmushi ummah tayi "abdul bilkisu kyauta ta baka ko jiya ta fadamun bazata amsa ba kuma ka cigaba da zuwa aikinka kamar yadda ta dora ka akai bazata kwace ba"
Shiru yayi abdul yana mamakin halin dattako irin na ummah,innah ce taita godiya sanan fitowar nawal dasu afee yasa innah mikewa "muje zainab abdul tashi muje,mungode Allah ya saka da alheri"
ummah ta mike ta raka su innah har wajen gate sanan ta dawo ta tarar da kamal ya mike kansa a kasa momy ce sai lokacin ta iya magana domin ji tayi tamkar ta mace "hajiya saadatu zamu tafi sai munyi waya ko saina shigo gobe"
Dariyar yake ummah taiwa momy "badamuwa momyn yara Allah ya kyauta gaba allah ya tsare"...
"Ameeen"ta fito ta rakasu har mota sanan ta dawo....
Jin motsin shigowar ummah yasa bilkisu fitowa daga sashenta ta fada jikin ummah ta fashe da sabon kuka "ummah na an cuceni an rigada an cuceni nashiga uku"
"Kulll kada in sakejin kim maimaita zancen tunda kim rigada kin furta kin yafe bani da yadda zanyi bilkisu sanan alhaji muhammadu tamkar alhaji bala yake a wajenki mahaifi ne kiyi hakuri....amma sammm banajin zan so daya daga cikinsu ya aureki zanfi so wani daga waje yazo ya daukeki zaifi sanin darajarki"ummah ta share hawayen da suka gangaro mata ta rungume bilkisu tsammm a jikinta tanajin kaunar yarta na ratsa zuciyarta...
*********
Tun shigowarta gidan take kallon agogo har shida saura basu dawo ba dukansu ina sukaje?badai gidansu bilkisu ba kaddai aure aka daurowa kamal da bilkisu,mikewa tsaye tayi kamar zararriya "bazai ma yuwu ba babu wadda miji na zai so ta wallahi sai ni kadai"ta tsaya tsaye jin karar bude gate da horn din mota yasa ta ruga ta yaye labulen window...motarsu ta hango sunyi parking da afee ta fara fitowa tayi cikin gida fuskarta a daure nawal na biye da ita sanan momy da daddy suka bi banyansu...tana iya hango kamal ya hade kai da siriyarin mota yayi shiru ko tunanin me yakeyi oho....
Tunda ya hada kansa da gwiwa yake tunanin yadda zai bullowa bilkisu to ta yaya?ya zaai ta sauraresa?anya harabada bilkisu zata soshi zata sauraresa?akwai aiki a gabansa,babba mai girma domin bazai taba barin abdul yayi galaba akansa ba wani haushin abdul din ma yakeji da kishinsa,ta yadda akayi har ya barshi ya amshi budurcin bilkisu ya dandana ta...mtswww tsaki yaja...dole idan yayi magrib ya ziyarci hafeez abokinsa domin ya sanar masa da abinda kw faruwa ya bashi shawara....
Bilkisu kuwa Kiran pheey aminiyarta takeyi tun dazun bata picking,massage ne ya shigo wayarta da sauri ya bude sunan abdul ta gani a saman massage din gabanta ya fadi.... runtse idonta tayi zugi da radadi ya ziyarci zuciyarta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*To fa zaa kafta kenan.... Anya kamal zaiyi nasara kuwa?...tou fa ga abdul da zafinsa....* 😂🏃🏻♀
*SLIMZY✍🏻*
[7/4, 7:53 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*32*
A gaggauce bilkisu ta mike daga dadduma bayan ta idar da sallar magriba,hangen wayarta na haske yasa ta karasa ta dauki wayar pheey ce "hello pheey ina kika shiga inata trying number wayarki bana samunki?"
"Kawata wlhy bana kusa da wayar yanzun nazo naga calls dinki hope kina lafiya meye labari?ya ake ciki?"
Ajiyar zuciya billy ta sauke ta nemi kujerar gaban madubinta ta zauna hannunta makale da wayar ta lumshe idonta ta bude su "meye ma baayi ba kawata?hmmmm case din dan daddy yaji ya kuma kashe case din"
"Alhamdulillahi yanzun ya ake ciki?"....pheey tayi tambayar cike da zumudi,
Yatsina fuska billy tayi "please kizo gobe mu tattauna ki kuma rakani asibiti inada appointment gobe"
"Ba damuwa zanzo insha Allah,zan tashi da wuri inyiwa mama aiki sai intaho"...
"Tou kawata"sukai sallama da pheey ta sauke ajiyar zuciya ta tsurawa wayar ido ganin ke kiran nata,abdul ne a karo na barkatai kenan bayan barinsu gidan da yake kiranta me yake kirata ya fada Mata?....shiru tayi tana bin wayar da kallo,
Safiyya ce ta turo kofar dakin bakinta dauke da sallama fuskar nan kamar koda yaushe tadau hodarta jajir bad'ani jaka ga jambaki radau bakin nan kamar akuya taci dusa,murmushi ne ya subucewa billy "yadai hajiya safiya ya akai"
"Ummah ce tace kizo kuci abinci ke take jira kuma zaai film din jamaira ja yau"
Murmushi billy tayi Allah sarki ummah "kice ganinan zuwa bari inyi sallar ishai sai inyi wanka infito gaba daya"
"Tou"safiya ta juya ta rufe mata kofar,jefa wayar tayi akan gado ta koma kan dadduma ta tada kabbarar sallah....
********
Kallon kamal kawai hafeez yakeyi cike da al'ajabi har kamal ya gama rattafo masa zancen da ya kawoshi "tabdijan kamal kayi kuskure babba a tunanina wanan laifin da bilkisu tai maka be kai ka maidata tamkar sarki da bawa ba,ko bayin sarki yana daga musu kafa saiya sha iska yake kwanciya dasu,ban taba tunanin haka kake kai kwallon dan iska bane sai yau tirrrr da wanan aikin danasani da kayi kuma bana tunanin billy zata soka bayan ka gama lalata mata rayuwa ka cuceta baka da sauran mutunci a idonta da na mahaifiyarta"
Hannu kamal yasa yashafa sumar kansa ya furzar da iskar bakinsa mai zafi,zuciyarsa na tururi ga wutar sonta da ta dawo masa sabuwa fillll idanuwansa sunyi jajir kuka kawai yakeso yayi yaji dadi,cikin rawar murya ya furtawa hafeez "ka taimakeni ka sanar dani abinda zanyi mata ta saurareni koda bazata soni ba ta amince mun da soyayyarta wallahi zan iya mutuwa idan na rasa ta"
Wata uwar harara hafeez ya watsa masa cike da takaici dikda yadda yaga kamal din yayi laushi kamal din da ya sani me ruda mata da shanyayyun idanuwansa yau shine yake roko a koya masa yadda wata zata soshi?lallai duniya tayi sabon lalle"kamal bazan boye maka ba ka tafka kuskure kayi Halin yahudawa sanan ka nuna rashin sanin Allah a tattare dakai,wallahi na dauka wani gagarumin laifi bilkisu tayi maka da kacemum kayi zina da ita,ai laifinta be kyautu kai mata wanan hukuncin ba duba da a addini ma ance mata rauni garesu sanan a lankwashe suke tunda da hakarkarin namiji aka haliccesu idan aka takura musu a lankwasa su karyewa zasuyi wato kai sai ka afkawa yar mutane kanwarka da zina"
Hawaye suka gangaro a fuskar kamal kansa sarawa yakeyi sosai ga zazzabi da yakeji a cikin jikinsa ji yakeyi tamkar zai bakunci lahira,kalaman hafeez sun sanyaya masa jiki dikda hafeez ba wani ilimi garesa ba kuma ya taso maraya shi kadai yake rayuwa amma yasan wadanan abubuwan shida yake alfahari da claiming ustaz mai sani idonsa ya rufe ya fada aikin dana sani...."hafeez ina danasani akan abinda na aikata kuma na tuba nayi taubatan nasuha wallahi, yanzun damuwa ta shine yadda zaai bilkisu taso ni"
. Tausayin kamal ya kama hafeez yayi shiru yana auna laifin da kamal yayiwa bilkisu kusan minti goma sha biyar babu me yiwa wani magana sai cannn hafeez yace "inada mafita da shawara"
A zabure tamkar wanda aka tsikara da allura ko wani sabon mahaukaci kamal ya ruko hannun hafeez "ina sauraronka aboki na ka taimakeni"
"Calmdown my friend kabi a sannu lets talk"
"Owk ina jinka"
Kiran wayan tahir ne ya shigo wayar kamal yana dubawa yaga shine yayi tsaki ya maida wayar aljihu domin shi bashi ma da abinda zai cewa tahir yasan kiransa yayi ya masa tsiya kila tun biki ko kiransa beyi ba dikda yana son kiran nasa ya shiga wanan balain......hafeez ya soma magana a nutse yayinda kamal yayi tsittt yana sauraronsa....
Tahir zaune yake a gefen gadonsa ganin kamal be dau wayarba yasa ya shiga gallery din wayarsa ya fiddo hoton bilkisu Wanda camera man ya tuttura musu na bikin kamal ya soma kallo wanda hakan ya zame masa tamkar jiki.....yar matashiyar budurwa ce ta shigo dakin hannunta dauke da plate da lemon chivita da glass cup tana sanye da riga doguwa mai igiyar daurewa a baya,har ta ajiye lemon be saniba,tai tsaye akanshi Tana kallon yadda yake duba hoton bilkisu yana zooming fuskarsa dauke da kayataccen murmushi "ya tahir ana nan ana sanaar ne?"tai maganar cikin sigar tsokan,
Hade rai yayi ya kife wayar "ke ina wasa dake ne ni kike cewa ina nan ina sanaar ne meye nakeyi na sanaa dan ubanki"
Turo baki tayi gaba "ya tahir baka da wata sanaa data wuce kallon hoton anty bilkisu gashi bata san da kai ba,muko dik gidan nan munsan labarinta ya kamata ka shirya kaje neman soyayyarta kafin kayi latti"shiru yayi yana nazarin maganarta "haka ne Ayrah maganarki gaskiya ce ko jiya da mukai maganar da ummah cewa tayi in shirya inje kaduna wajenta tunda inata neman wanan dan iskan kamal a waya yaki dauka yana can yana amarci"yar dariya Ayrah tayi "idan ka tsaya kallon ruwa kwado zai maka kafa saidai ka zauna kana kallon hoto wayasani ko har kiss kanayi mata"tana fadin haka ta runtuma aguje tayi parlor ya rufa Mata baya...
Bayan ummah ta boye a tana numfarfashi shiko tsaye yayi yana watsa mata harara "lafiya babban kwabo koda yaushe sai ka biyo wanan tar tatsitsiyar yarinyar ko kunya bakaji daddaren nan sai kun saida hali"
"Ummah Ayrah ta rainani fa tsokanata takeyi"
Daga bayan ummah Ayrah ta leko da kai "kamasa nayi yana sanaar"
Ummah ta karbe zancen da "ta kallon hoton bilkisu ko?"suka kwashe da dariya sanan ta kallesa "yaushe zakaje wajen yar ku sasanta domin na matsu da akawomin suruka gidan nan nagaji kaga shikenan Ayrah tayi anty ko?daddynka ma ko jiya da mukai maganar yace yana dawowa london zaije nema maka auren"
Murmushi tahir yayi "gobe kaduna nayi".....ayrah tai ihun murna duka suka sa dariya....nan ya zauna gefen ummah suna shan fruit salad tare har karfe goma sanan ya mike ya nufi dakinsa ya dauki waya ya Shiga rubutawa kamal massage....
*******
Juyawa yayi misalin karfe sha biyu na dare bacci ya gagaresa ga zazzabi mai zafi daya rufesa minti minti yakan ja numfashi ya sauke ajiyar zuciya,gajiya yayi ya janyo wayarsa ya bude yayi tozali da massage din tahir kamar haka..... *Hey man I have been calling you since last week baka picking tou...albishir zanyi maka* *da inaso mu hada zumunci soyayyar yar uwarka bilkisu ta hanani sakatttt ko bacci banayi shine nake kiranka kafara* *nemamin aure kafin inzo,amma dadin amarci yasa baka daukan call insha allahu gobe zan zo kaduna ina fatan zakaimun rakiya....*
Ko kafin kamal ya gama karantawa gumi ya jikasa sharkafff da zufa sabon zazzabi ne ya rufesa shin meyake faruwa dashi ne?daga wanan masifar sai wanan daga wanan tashin hankali sai wanan?shin me tahir keso yace?zai nemi auren bilkisu daga sama zaizo yayi soyayya da ita?bayan shi yake nemawa kansa mafita yasan irin yadda yakejin ciwon soyayyar bilkisu a ransa?tashi yayi ya zauna a tsakiyar gadon ya raka tagumi dikda irin zazzabin da yake yi hakan be hanasa zufa keto masa ba,
Turo kofar dakin akayi cikin duhu yake kallon jikinta rabin ta tsirara ta shigo tana gantsarewa wani bakin ciki ne ya lullubesa kamar ya tashi ya shaketa Zahra ce yasan abinda ya kawota domin yana kallon hade haden da ta sha dazun,cikin wata iriyar murya mai kama da maye ta furta "hubby....bakai bacci ba kake zaune a tsakiyar gad,what wrong?"tana maganar ne tana hayowa gadon ta karasa kusa dashi tana goga jikinta a nasa,tayi mika ta gantsaro kirjinta ta goga masa "ina tambayarka...kayi shiru nace bakai bacci bane"
"Ummmm"kawai kamal ya iya cewa cike da bakin ciki ta kara matsowa daff dashi yana jiyo sautin nunfashinta "nace hubby ummm...i cant sleep wlhy sai juyi nakeyi ina bukatarka please "tayi wata mika ta kai masa runguma ya tureta "meye haka ne zahra?wai meke damunki?"
"Meke damuna?yaushe rabon da ka bani hakkina na aure?yanzun na biyoka kanamum silly question....please kamal wallahi a matse nake'
Haushinta ya kara lullubesa kamar ya shake ta ,amma sanin akwai jikakkiya tsakaninsu yasa ya kamo hannunta ya kai wuyansa wani zafiii rauu taji sanan cikin wata iriyar murya ya marairaice "zahra banida lafiya kiyi hakuri ki taimakeni zazzabi nakeji kinji?banida karfin hawa kanki yanzun gashi ke baki gajiya"...wani kululun bakin ciki ya tokare mata wuya tausayinsa ya kamata ta rungumosa jikinta "shikenan lets sleep together kila in tage zafin a haka"badan yaso ba ya kwantar da kai kirjinta tana wasa da gashinsa gabaki daya hankalinsa baya wajenta hankalinsa ya rabu waje biyu tahir da bilkisu musamman bilkisu wadda ko sunanta ya tuna sai gabansa ya fadi sabon zazzabi ya rufesa,rawar sanyi ya shigayi cikin daren hawaye na gudu a gefen fuskarsa....sai wajen asuba bacci mai nauyi ya figesa banda zahra da tuni tai bacci tana jan numfashi.....
Cikin sauri yayi shirinsa da safe kasantuwar weekends ne yasa zahra ke kallonsa da mamaki "ina zakaje ne haka kake sauri"baiko kalleta ba ya cigaba da shirinsa saida ta kara tambayarsa cikin kosawa ya furta "H.O.D meetings garemu dole inje"tabe baki tayi ta cigaba da breakfast,shiko kamal bayaso tahir ya samesa a gida yasa yake wanan saurin koda ya fito ta window momy ke hangensa ya kalli side dinsu kamar zai shiga ya fasa dik Tana kallonsa tausayinsa ya lullubeta yadda ya rame ya koma kamar wani yaro dik jikinsa yayi sanyi idonsa sunkara fitowa sosai motarsa ya nufa cikin sauri ya bude ya shaga ya tada sanan yayi gate.....
*******
Rabonsa da gidan har ya manta inda suka saba haduwa da bilkisu yaje yana budewa idonsa yayi tozali da bakim dankwalinta da ranar da tazo karshe ta barshi dakin yayi datti sosai da sauri ya karasa ya dauki dankwalin ya rike a hannunsa yakai hancinsa kamshin turaren arabian oud tamkar yanzun akasa ya cigaba da shinshinawa fuskarta ta fado masa lokacin da ta durkusa gashi ya zubo a gaban goshinta tana kwasar wayoyinta da yayi mata korar kare tana hawaye,besan lokacin da ya fashe da kuka wiwi ba harda majina ya zauna dirshan a tsakiyar dakin yana rungume da dankwalinta yana kuka yana fadin "ina sonki billy soyayyarki dik ita tai silar jefani cikin wanan halin,bazan Bari in rasaki a karo na biyu ba na shirya yakin da koma waye don allah ki soni bilkisu nine na cancanta da soyayyarki nine na cancanta da in aureki in goge laifin da nayi miki,nine wanda na maidaki tamkar matata nake kwanciya dake bada son ranki ba lokacin da kike rokona akan inji tsoron allah,shedan yanamun kida a kunne.....wallahi na tuba inajin tsoron allah"kuka yakeyi yayi matukar zufa da sauri kamar Wanda ya tuna wani abu ya ciro wayarsa ya danna switchh offff ya jefa wayar kan kujera,kamar sabon mahaukaci hannunsa rike da dankwalin ya shiga bedroom ya tsaya gizo take masa a ido lokacin da ya sharara mata mari ya hankadata kan gado ya fada kanta ya hau amfani da ita, runtse idonsa yayi ya karasa ya fada kan gadon ya cigaba da kuka wiwi ya rungume pillow tsammmm....
*******
Shigowar tj gidan har gaban momy ta kaisa a matsayin yayanta ya gaida momy sanan ya suka nufi sashen zahra shiga ta zare hijabi ta bayyana tsirara ya kai mata runguma be tsaya wata wata ba yakai bakinsa kan breast dinta yana tsotsa ya ciccibeta sukai daki.....shigo driver yana makale yana kallonsu sanan ya seta camera dinsa ganin sun Shiga bedroom yayi saurin rugawa ta bayan bedroom din saidai window a rufe yake... dafe kansa yayi yana jiyo nishin da zahra ke saukewa sama sama yaji tana sambatu "tj naji kishi da ka haye waccen yarinyar"
A rude tj ya ansa da "wacece babu yar da zanji dadinta kamarki"
"Afee da kayiwa fyade mana"
Zaro ido driver yayi yaja da baya nan da nan yayi pausing recorder sa ya bar wajen cike da tsoro....
*******
Tafe suke a mota itada pheey tana tausarta akan suje gidan su abdul shine yafi dacewa da ita shi ya cancanta ta auresa ta yafe masa bilkisu ta karya akalar motarta kiran ummah ya shigo wayarta da sauri ta dauka "hello ummah na"
"Kina ina bilkisu na"
Kallon pheey billy tayi cikin in ina tace"muna hanya munbaro asibiti da nafisa "
"Tou kizo kinyi bako daga abuja,kiyi sauri yana parloen baki idan kizo"dibbb ummah ta kashe wayar,faduwar gaban bilkisu ya tsananta pheey ta dubeta "yadai kawata muje muga abdul din ko?zaiji dadi kuma zai warke ciwon dake damunsa"
"Muje gida ummah na tace nayi bako daga abuja inyi sauri"
"Toooh bako kuma?"
Billy batace komi ba ta canja giya tai kona,ta dau hanyat gida tanata sake saken waye gareta da zaizo daga abuja?....
Shigowarsu unguwar ta hangi motar abdul a kofar gida sai kuma wata dalelliyar motar da batasan waye ba..hangen abdul tayi a gefen motarsa tsaye ta dubi pheey "kinga Wanda da zamuje gidan su?"
Dago kai pheey tayi "kai aiko shine,to kodai shine ummah keyi miki wasa"
"Banjin shine nafi zaton waccen sabuwar motar"....tana karasowa ta sauke glass suka hada ido da abdul.....wani abu taji zirrrrr a cikin jikinta.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*MUJE ZUWA🏃🏻♀A KAFTA....*
*SLIMZY✍🏻*
[7/5, 7:49 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*33*
Horn tayi mai gadi ya rugo da gudu ya bude musu gate "barka da zuwa ranki ya dade?"Abdul na hangenta ta dagawa mai gadi hannu,itama ta cikin glass take kallonsa suka shige mai gadi ya maida gate ya rufe,...ajiyar zuciya Abdul yayi ya dubi agogon hannunsa kusan karfe biyu na rana yunwa sosai yakeji amma bazai iya cin abinci ba sai yaga bilkisu yayi magana da ita,to gashi ta dawo har ta kalli inda yake da alama ta sakko to kodai zata fito ne ya jirata?wata zuciyar ke bashi shawarar shiga cikin gidan,take ya gargadi kansa da bazai iya hada ido da ummah ba dikda komi ya wuce...komawa yayi cikin motarsa ya zauna ya rufe motar ya kunna AC sanan ya kwantar da kansa jikin seat hade da lumshe idanuwansa.....
Suna shiga parlorn ummah na zaune shaawah na tayata wankin kafa a gajiye billy ta karsa ta jefar da jakarta kan kujera pheey ma ta nemi waje ta zauna "ummah ina yini barka da Rana"
Da yar faraa ummah ta ansa "barkanki dai ranki ya dade nafeesah wato tun ranan da kika tafi ban sake ganinki ba sai yau ko?"
"Ummah ba haka bane wallahi"tai maganar tana dariya,
Kallon bilkisu ummah tayi "daga ina kuke haka a rana faram faram kamar an koroki musamman ke auta umm"ummah tai maganar tana taba kafadar bilkisu dake zaune jikin hannun kujera, turo baki billy tayi cike da shagwaba "ummah na asibiti mukaje kin manta yau inada appointment? gashi nayi saa yau akwai mutane ba laifi sanan andibi jinina zaai mun tes ance in koma sati mai zuwa"
"Tou masha Allah kutashi aje aci abinci idan kuma a nan zakuci tou dik daya,amma ke bilkisu ki tashi kinada baki a wancen parlorn don can nasa aka bude masa tunda naga kamar daga nesa yake,yama ce daga abuja yake".....yatsina fuska bilkisu tayi kamar bazata ce wani abu ba can tace "ummah nikam wa gareni daga abuja?"
"Ki tashi kije mana idan kinje kya gani haba"pheey ta amshe maganar,yar harara billy tai mata ,cire dankwalin kanta tayi ta ja gyalenta ta yane kan dashi tana sanye da fitted gown ta less maroon ta yafa milk din gyale tayi parking gashinta gaman kanta dik a kwance ,baki bude ummah ke kallonta "Haka zakije wajen bakon ko dankwali babu?"
Kara turo baki gaba tayi "ni fa ummah kinsan banason dankwali damuna yakeyi wallahi kinsani"tabe baki ummah tayi ganin rikici karara a kwayar idonta tasani sarai idan ta matsa zatace bazata je ba hakan yasa ta gimtse bakinta kafin daga bisani tace "a dawo lafiya"...baki gaba ta tura tana tafe har ta kai kofar fita ta juyo suka hada ido da pheey tai mata dariya ita kuma ta watsa mata harara....
Jingine yake da kujera ya ajiye hularsa akan hannun kujera hannunsa rike da waya yaji karar takun takalmi hakan yasa gabansa ya dan fadi kafin daga bisani turarenta ya gauraye parlorn tun kafin ta karasa shigowa yayinda bugun zuciyarsa ya tsananta ..."Assalamu alaikum"tace cikin siririyar muryarya gyara zama yayi ya ajiye wayarsa gefe sanan ya dago fuskarsa ya dora idanunsa akan kyakkyawar fuskarta,lulu eyes dinta yasa yaji numfashinsa na barazanar daukewa farare tassss da pink lips dinta da yasha lipgloss sai kyalli yakeyi kwantaccen sumar gaban goshinta baki sidibbbb gashin kanta yasha gyara kanta a kasa ta karasa kujera domin ta zauna yabi kyakkyawar surarta da kallo,besan lokacin da ya hadiyi wani miyau mai kauri makwattttt ba,har ta zauna be sani ba kusan minti biyar jim shiru yasa bilkisu dan jin haushi ta dago fuskarta ta motsa labbanta a hankali "barka da zuwa"
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi "barka da zuwa sarauniyar kyawawan mata ta dik duniya,lallai kinci suna bilkisu mai gadon zinari domin kin dace da sarauta"...
Murmushi tayi da jin kalamansa tamkar almara "ban dace da sarauta ba saboda mu din ba jinin sarauta bane"
"Ke din ko kika dace da sarauta domin ko bakuda sarauta nina baki sarautar sarauniyar fadar zuciyata,sarauniyar fadar gida na"yayi maganar yana murmushi,batayi magana ba wanan lokacin face murmushi da tayi ta sadda kanta kasa tana yar dariya kalamansa sun bata dariya sosai,"sunana Tahir,ni mutumin kano ne iyayena duka haifaffun kano ne amma muna zama a Abuja dalilin aiki da ya kai mahaifina can muka koma nikadai ne yaron mahaifina sai kanwata Ayrah da take 100 level a nile University"..shiru yayi yana kallonta bayan ya gama gabatar da kansa,dakyar ta jinjina kai sai lokacin ta sauke manyan idonsa akan kyakkyawar fuskarsa,na seconds ashirin lallai tahir kyakkyawa ne ajin farko saidai kuma ya mata kama da wanda ta taba sani a wani waje tamkar tasan fuskar...."nikam tamkar na taba saninka"
Murmushi yayi hade da jinjina kai "kin sanni mana domin na taba ganinki da wata kawarki lokacin bikin abokina kamal"da sauri ta kallesa gabanta na faduwa wato abokin kamal ne?meye haka playing dinta sukeson yi ko me?koko shi ma an turosa ne ya gwada saarsa akanta?katse mata tunani yayi da "tun lokacin na ganki naji ina sonki tou na nunawa abokina ina sonki beyi serious ba,be kuma bi takan maganar ba har na koma gida na sanarwa da mahaifiyata da kanwata tai murna sosai tace in nemi kamal din to kona kirasa be daukar wayata har tex nayi masa akan ya nemamun soyayyarki bilkisu amma bebi ta kaina ba ko reply bemun ba shine nayi takakkiya nazo da kaina in gwada saata ko Allah zaisa nine me rabon da zan daukoki daga cikin ruwa,kinsan ance mace allura ce cikin ruwa mai rabo ke dauka"....sai lokacim ta sauke ajiyar zuciya taji wani sanyi a ranta Allah ya kawo lokacin da zata gasawa kamal Aya a hannu dikda bataso masa ramuwar gayya ba saidai a kalaman tahir ya nuna kamal yaki bin maganarsa ne saboda Yana kishi,dikda tsanar da take kwance cikin zuciyarta akan kamal ta kudiri aniyyar ko lamarinsa bazata bi ta kai ba Amma zata hada masa gadar zaren da daga karshe ciwon zuciya ya kamasa, tunani ta shigayi kafin daga bisani ta dago fuskarta tana wasa da yatsunta ta dubesa suka hada ido taga ita yake kallo ta sakar masa murmushi.....lumshe ido yayi ganin murmushinta yasa yaji sanyi cikin zuciyarsa yasawa ransa cewar yayi nasara...zaro wayarsa yayi a aljihu nan da nan nayi dialing number ummahn sa bugu daya ta dauka yasa speaker "ummah barka da rana"
"Barka sai tahir dan ummah yanzun nake tunaninka fatan ka sauka lafiya ko?an kuma dace?"kallon billy yayi yaga tayi murmushi ta sunkuyar da kai domin kwarjini yayi mata
"Ummah tou ganinan dai amma ina tare da ita yanzun hakan"
"Bani ita mugaisa inji muryar yar tawa"da sauri ya taso ya karaso gaban bilkisu ya durkusa kan gwiwarsa ya mika Mata wayar kunya ce ta lullubeta dakyar ta kara wayar a kunne tayi sallama,ta gaida ummah cike da ladabi tana tambayarta ummanta ta amsa dakyar saboda nauyin mata ta mika masa wayar,kallon ta yayi ya kashe mata ido "hello ummah"
Cike da zumudi Ayrah ta ansa "ba ummah bace,yaayah nice nidai nayi fushi ni a bani anty billy tunda ta gaida ummah"mikawa billy wayar yayi suka gaisa sanan ya koma wajen zamansa....ita ko mamaki ne ya rufeta yadda akai iyayensa da kanwarsa suka santa batare da yazo ma ya nemi soyayyarta ba,shiru tayi tai zurfi cikin tunani har ya kashe wayar bata sani ba,"kina mamakin yadda kikaji ummah da kanwata ko?..h....mmmmm soyayyarki"
Murmushi tayi har fararen hakoranta suka bayyana...haka suka cigaba da hira har laasar sanan ya dubeta "zab tafi amma gobe kafin in koma Abuja zanzo muyi sallama sa mun numberki"ya mika mata wayarsa babu musu ta saka masa sanan suka fito har sunkai harabar gidan tace "ba kaiwa ummah sallama ba"
"Dole inyi mata sallama kin mance zan dawo gobe?"...jinjina masa kai tayi suna tafe a tare har kofar gate ta rakosa ya fita ya nufi motarsa yana daga mata hannu....can ta hangi motar abdul a cikin rana,kara kallon motar tayi hmmm be tafi ba kenan ta tambayi kanta sanan ta juya tayi cikin gida.....
********
Tafe yake hannunsa rike da waya dayan hannun yana driving,trying number kamal yakeyi tun dazun a kashe sai kawai ya yanke shawarar zuwa gidan kawai,ajiye wayar yayi ya kara volume din radio yana bin wakar a hankali mai taken i will love you ohh my luv,wani irin nishadi yakeji cikin zuciyarsa ga wata irin soyayyar yarinyar da tayi rassa a jijiyoyin jikinsa da jinin dake yawo a jijiyoyin sa zuwa zuciyarsa....a kofar gidan yayi parking domin no need ya shiga da motar tunda fitowa zaiyi...
Itako zahra sanye take da jallabiya ta dora mayafi suka fito daga daki ita da TJ shiko sai faraa yakeyi yayi wata mik'a yana lashe baki yana biye da ita har kofar parlor "yanzun sai yaushe my zahra,naji dadin kasancewa dake fa sosai,nayi missing dinki musamman abun wasa na"
Harararsa tayi tana masa wani irin kallo "menene abun wasan naka?"yakai hannunsa kan nononta da ko braxia babu ta turesa "kada ka tadamun hankali kasanni yanzun sai in dau carji dole mu koma office"...wata yar iskar dariya ya sheke da ita "a nan zaki barni?ai kamata yayi ki rakani har gate kada aga na fito nikadai kuma kince ni yayanki ne sai a zargi wani abu"
"Haka ne"ta zura flat shoes dinta dake kofar shiga patlorn "muje"suka fito a tare ta rakashi har wajen kusa da gate,kallon da driver dake zaune a kan benci na malam dauda mai gadi shi yasa TJ da zahra suka sha jinin jikinsu kafesu yayi da wani irin kallo hakan yasa tj ya rada mata yana cije harshe "nifa guy dincan gani nake tamkar ya ganeni,gaskiya ina zargin kallon da yakemun kimun izini mu sheka sa kawai"
"Ah ah barni dashi kawai nasan ta inda zan bullo masa tsafff zansa ai waje dashi"tai murmushi shima yayi....
TJ na fita tahir ya shigo gate din suka hadu da zahra "ah ah amarya bakya laifi inata kiran wayar mijinki a kashe na shigo gari nace bari inzo in dubasa kila yana gida kin boye sa"yayi mata wani irin kallo,kauda kai tayi cike da kunya da yak'e "kaikam ka fiye tsokana,tou tun safe ya bar gidan nan baya nan"zatai magana kamal ya turo kofar gidan hannunsa rike da kansa idonsa sunyi jajir fuskarsa ta kumbura cikin tashin hankali zahra tace "gashi ma ya dawo hubby daga ina?kamar kun hada hanya yanzun abokinka ya shigo"
Dago rinannun idanuwansa yayi ya dorawa tahir "ah ah friend barka da zuwa yaushe a garin?"
"Mu karasa ciki mana a nan zamu gaisa kamar ana gudu?sanan amaryarka tai mana shariah dikda kaidin sirikina ne yanzun?"kauda kai kamal yayi ya basar da maganar ya ruko hannun tahir sukayi sashen su....
Suna zaune a parlor zahra ta ajiye musu lemo mai sanyi da kulolin abinci ta shiga ciki,jimm kadan ta fito da plate ta dora a centre table din da serving spoon da spoons ,sanan tayi cikin dakinta ta barsu ,sauya tasha kamal yayi sanan ya gyara zama a kujera "ya bayan saduwa abokina"
Nazarin yanayin na kamal tahir yayi "yadai naganka a hanka abokina meyake damunka?mezai dameka kana tare da sabuwar amarya dallll a leda"dan tsaki kamal yayi "kaifa dan iska ne ka fiye maganganu wallahi yanzun meye labari"
"Hmmmm labarai kuwa tunda soyayyar kanwarka tasa nazo kaduna babu shiri inata neman wayarka in sanar maka ka fara shigar dani baka picking yanzun haka daga wajenta naje, alhamdulillahi nasamu karbuwa daga dukkan alamu saidai fatan nasara Allah yasa dai bata fidda miji ba"
Wani abu ne yazo ya tokare wuyan kamal yayi masa kulu ji yayi tamkar ya shake tahir saboda wani kishi daya taso ya rufe masa ido da kirjinsa,besan lokacin da yace"aiko ta boye maka ne domin anyi mata miji"cakkk tahir ya tsaya hannunsa rike da cokalin shinkafa,ya maida plate din ya ajiye yana kallon yadda kamal ya tsare gida babu alamar wasa ko zolaya a fuskarsa "kace ta fidda miji?anyi mata miji fa kace?"
Gyada masa kai yayi yana kallonsa ido cikin ido "ta tsaida mijin aure,ta boye maka ne bata fada maka ba kila saboda kai abokina ne tanajin kunyarka amma ta fidda miji bilkisu"
.zufa ce ta karyowa tahir a goshinsa ya dire cokalin shinkafar take yaji ya koshi,kallonsa kamal yayi "kaci abincin mana"
"Ah ah bazan iyaba kamal,wallahi bazan iya hadiyar komi ba a yanzun da naji wanan labarin,ina son yarinyar nan ina mata so na tsakani da Allah,sanadiyyarta yasa bana kallon ko wace mace a matsayin mace a namiji nake kallon mata yanzun nabar abubuwa da dama ta sanadiyyar soyayyar da nakeyi matan...dikda haka ban karaya ba zan shiga sahun manema tunda ba aure aka daura mata ba"tamkar zaiyi kuka yake maganar....shiko kamal wata irin tsanar Tahir ce ta dira cikim zuciyarsa,wani irin kishi da haushi ne ya lullubesa ya hade girar sama da ta kasa bai sake cewa tahir komi ba ya cigaba da kallonsa,shiko tahir mamakin yadda kamal yayi masa yake tamkar besanshi ba?tamkar ba amininsa da sukai karatu tare ba?tamkar bashi bane suke wasa da dariya da zolayar juna ba?amma yazo gidansa yana treating dinsa haka?kodai wani abu yayi masa yake haka?beji dadi ba dame zaiji da albishir din bakin cikin da yayi masa koko da yadda yake masa daure daure?...kusan minti talatin suna tare a haka sanan Tahir ya gyara hularsa "zanje masauki yamma tayi can zan kwana da safe zanje muyi sallama da ita sanan in wuce"
Cike da basarwa kamal yace "babu laifi"ya mike tsaye yayi gaba tahir yana biye dashi cike da mamaki.......
********
"Pheey kina ganin wanan da yazo anya yana sona kuwa?nifa tsoron maza nakeyi sanan abokin kamal ne kuma dagaske sona yakeyi har ummansa ya bani da kanwarsa muka gaisa inajin tsoron ko wani tuggun suka hadamun shida kamal"
Shiru pheey tayi sanan tace"tabdijan gaskiya kawata kiyi tunani mai kyau daddaren nan"
.tafe suke suna yar hirarsu billy ta rako nafeesa zata tafi gida "amma kawata kina ganin waye yafi cancanta Dani a yanzun haka?hmmm wallahi tallahi zuciyata na cikin rudani jiya kwana mukai abdul nayi mun massage fa,naga misscall din wanan dan iskan kamal"
Yar dariya pheey tayi "kawata ki zauna da ummah kuyi shawara sanan kiyi addua kiyi istihara akansu duka amma dai abdul na bani tausayi,saidai kamal fa bedace yaci banza ya tafi ba dik wanda zai aureki sauran kamal zai dauka"
Ajiyar zuciya billy tayi "kawata wallahi na tsani kamal natsanesa natsani ko jin sunansa domin shine silar komi shine silar dik wani bala'i da nake ciki ko na tsinci kaina wallahi sainayi anfani da tahir na muzguna masa"
"Ban hanaki ba amma dai kibi a hankali kada kiyi saka a mugun zare gobe zamu hadu a school zamu tattauna"pheey ta fice billy na tsaye jikin kofa har yanzun motar kamal na nan,kallon billy tayi "ke mutuminki na nan fa dan allah ki sauraresa bilkisu wallahi tausayinsa nake ji"
"Owk,kiyi masa magana ku hadu a parlorn baki idan ya shigo yacewa mai gadi ya kaisa ya jirani"tai cikin gida Tana daga mata hannu....
Kwankwasa glass din pheey tayi da sauri ya bude motar ganin nafisa ya kirkiro murmushin karfin hali "pheey"ya kira sunanta yadda taga idonsa sunyi jajir ba karamin tausayi ya bata ba idonsa sun kumbura daga gani bacci yayi a motar,jikinta yayi sanyi sanan dakyar ta iya karfin hali suka gaisa "bilkisu na jiranka a ciki tace ka fadawa mai gadi ya kaika parlorn baki a bude yake ka jirata a nan"
"Tou nagode nafeesah"sukai sallama ya nufi gidan nafeesa ta bishi da kallo cike da tausayawa.....
Zaune yake a parlorn yana jiranta jin alamun motsi yasa ya dago kai da sauri ya zurawa kofar ido,tsaye tayi a jikin kofar ta harde hannuwa tana kallonsa,kare masa kallo takeyi yadda ya rame sosai hancinsa ya kara tsawo....kallonsa takeyi shima kallonta yakeyi besan lokacin da hawaye ya wanke masa fuska ba,itama hawayen takeyi a tsaye...sai kawai ya zame ya durkusa yayi kneeldown akan gwiwoyinsa....
*******
Kamal durkushe a gaban abbah a parlornsa yana kallon labarai, tun bayan fitar tahir ya nufi sashen abbah...cikin kuka yake rokon abbah "banaso bilkisu ta kubucemun a karo na biyu abbah,kai kadai ne zaka tsaya mun in samu soyayyar bilkisu idan ba haka ba inaji ina gani wani daga waje zaiyi nasara akaina,kuma dani ta dace abbah nine ya kamata in mallaketa inyi mata gata a matsayina na dan uwanta,nine ya dace in mallaketa in goge mata dik wani tabo dake cikin zuciyarta abbah kaimun rai wallahi ina sonta zan iya rasa Raina"kuka yakeyi dik ya fita hayyacinsa yayinda abbah ya zuba masa ido yana kallonsa,sosai kamal ya bashi tausayi domim yana hango tsantsar gaskiya a kwayar idonsa mai cike da nadama saidai bazai tauyewa bilkisu hakkinta ba dikda yana da right din zaba mata miji amma ba dansa ba idan yayi hakan tamkar yayi son kai.....
"Banida damar yin hakan kamal,domin rashin adalci ne saidai idan kana sonta ka kai kanka ka gwada saarka idan ta zabeka zanfi kowa farin ciki amma ni yanzun banida abin ce maka"yana karasa maganar ya mike yabar kamal nan zaune ya shige bedroom dinsa....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/7, 8:08 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*34*
Kusan minti goma sha biyar daddy be fito daga bedroom dinsa ba hakan yasa kamal share hawayen da ya bushe a fuskarsa sanan ya sawa zuciyarshi jajircewa da jarumta akan dik wani kalubale da zai fuskanta akan wanan yakin dake gabansa,bazai taba yuwuwa ba aciku da yaki a barku da kuturun bawa,mikewa yayi har zai fita yasa hannu ya kashe TV sanan ya fice ya rufo kofar ya nufi sashensa,dikda karfin gwiwar da yake tattare dashi amma hakan besa yabar jin radadin da yakeji cikin zuciyarsa ba ga wani ciwon kai da yake tattare dashi,
Tana zaune a parlor hannunta rike da glass cup ta dora kafa daya kan daya lokacin da ya shiga,kallo daya yayi mata yaji wani mugun haushi ya lullubeta,wata tsanarta ce ta darsu cikin zuciyarsa da wani duhu daya lullubesa remote ya dauka ya canja tasha tana bin sa da kallo yayinda wani maganadisun soyayyarsa ke fizgarta,mamakin yadda yake rama yake canjawa takeyi kwana biyu bata gane kansa dikda irin wulakanci dama da yakeyi mata samun yancinta shine yiwa afee fyade da akayi,kurbar lemo me sanyi tayi sanan ta dire cup din akan centre table ra fuskancesa ya hada girar sama da ta kasa "hubby"ta kira sunansa cike da karairaya,yadda tai maganar haushi ya kara lullubesa ya danja tsaki,shiru tayi na dan dakiku sanan ta nisa tace "kamal....ni matarka ce amma sam banida martaba da kima a idonka ka maidani tamkar wata mujiya ina lura da yanayinka gabaki daya, sanan a kwanakin nan ina lura da tamkar kanada damuwa tamkar bakada lafiya kanada wata matsala"
Tsaki yaja ya watsa mata harara yace "ehh tabbas banida lafiya kuwa kamar yadda kika fada rashin lafiyar tawa kuwa ciwon soyayya ne.....sanan abu na gaba damuwata da kike gani be wuce auren karuwa da nayi ba,hakan ne yasa ma nakamunda soyayyar kanwata yar uwata jinina wadda nake burin aurota inkawo ta gidan nan a matsayin matar aurena"
Mikewa tsaye zahra tayi tamkar wadda aka tsikara "karya ne....karyane wallahi wallahi baka isa ba kamal baka isa ka auri wata bayan niba,har yaushe ka auroni da kake tunanin karo aure?....au koda yake banyi mamakin hakan ba saboda kai din ma fajiri ne kamar yadda kake kirana karuwa,ai inada labarin komi ai naji dik mugun abun da ka aikawa bilkisun daga baya allah ya jarabceka da sonta....sanan idan har ni karuwa ce to kanwarka ma ummul khairi karuwa ce itama kuma ba cikakkiyar mace bace".
Kafin ta karasa ya sharara mata mari ta dago kai ya kara kai mata mari jikinsa har rawa yakeyi zufa kawai ke keto masa ta ko ina "ke har kin isa ki kalli tsabar idona ki kira jini na karuwa?"
"Tou mecece inba karuwae ba na kuma na fada karuwa ce ke zakayi?kuma baka isa kaimun kishiya ba baka isa ka auro wata bayan niba wallahi idan kuma zaka auro bismillah"
Ya kai mata duka ta doje jikinsa rawa yake yana kokarin zare belt din jikinsa "wallahi ka kara kai hannunka jikina saina baka mamaki kuma wallahi bazakai auren ba kuma saina tonawa kanwarka asiri a idon duniya"
Cikin daga murya kamal ke fadin "sai meeeeee.....idan kin fasa zahra kin raina Allah n daya halicceki karuwa"
Cikin daga murya tace "kai kuma fasiki ko"yaki kukan kura zai Kai mata duka ta doje ya bugi centre table take ya fashe hannunsa ya yanke jini kuwa ya soma tartsatsi ganin haka yasa ta fice tana kuka tayi sashen su momy a guje ya mara mata baya....
*********
"Bilkisu matukar na rasaki na rasa aurenki tabbas nayi asara kuma hakan zai iya barazana da rayuwata ki gafarceni ki yafemun ina sonki ina miki so fiye da komi a duniya matukar zan mallakeki a matsayin matar aure to tabbas gama samun farin ciki a rayuwata ta duniya sai ta lahira....hakika na cutar dake naci amanarki bilkisu"yana maganar Yana hawaye,hannu tasa ta share hawayenta sanan ta tako ta karasa shigowa cikin parlorn ta nemi kujera ta zauna...kallon da take aika masa dashi mai cike da sakwanni na so da kauna kadai yasa ya soma murmushi hawaye na gudu a fuskarsa
"Kayi matukar kyau da wanan yanayin domin murmushi da hawaye ba dik namiji ba,kai din na daban ne abdulhrahman sanan kai dan halak ne ka cika cikakken namiji,son da nakeyi maka ya dawo sabo a yanzun haka ta dalilin fallasa kanka da kayi da kanka,nadade da fahimtar cewar akwai wani boyayyen al'amari a tattare da kai abdul saidai hankalina ya gushe da soyayyarka mai cike da tsafta,ina ma ace zan kai maka budurcina gidan ka?da nafi kowa farin ciki saidai kaddara ta riga fata kaine ka amshi budurcin a waje ta sanadiyyar mummunar kaddara data gifta,shin meyasa bazan yafe maka ba bayan kaine ka gayyato farin ciki rayuwata?kaine sanadiyyar da na manta da rabin bakin cikin da nake dashi dikda kaine sila ka bude hanya amma banida yadda zanyi zuciyata bazata iya jurewa da ganinka cikin kunci ba bayan kaine silar warwarewar lamurana"tsagaitawa tayi ta fashe da kuka shasshekar kuka takeyi hakan yasa abdul runtse idanuwansa sababbin hawaye masu zafi na zuba a idonsa tausayinta ya lullubesa gashi shasshekar kukanta kuma ta haifar masa da wani radadi cikin zuciyarsa..inama ace zai iya rungumarta ya lallasheta a wanan lokacin?daya rungumeta ya kaita babban birnin maji dadi....
Karasowa yayi gabanta yana kallon kwayar idonta da ta jike da hawaye ko kifta idon bayayi hakan yasa ta turo baki gaba cike da shagwaba "nika bar kallona nidai umhmmm"ta tabe baki baisan lokacin da ya fashe da dariya ba itama dariyar tasa ta dauki pillow din kujera ta kai masa duka ya goce dik dariya suke cike da nishadi....nan suka cigaba da hira....
*******
"Amma baka da hankali kamal yanzun saboda kishiya da zakai mata yasa ka gaggaura mata mari harda duka?dubi kumatunta yadda cikin minti biyar sun kukkunbura kamar mai hangun"momy ke maganar cike da bakin ciki tausayn zahra ya gama lullubeta wani mugun kallo ta watsawa kamal da sai mazurai yakeyi zufa ta gama wankesa kallo daya zaka ka fahimci cike yake da fargaba,sosai ya furgita da yanayin zahra tsoronsa daya ne kada ta fallasa videon fyaden afee ga momy domin ba karamin damuwa zasu shiga ba da bacin rai sanan daddy zai kara daukar zafi dashi ba kuma yaso yarinyar ta shiga matsala sanadiyyar damuwar da take ciki dama bata gama warkewa ba,momy ta katse masa tunani "bacemun daga gani mugu azzalumi kawai kuma wallahi sainayi maganinka idan takamarka ka auri bilkisu ka wulakanta Zahra to ka makaro dan tsaff zansa maka kara inga yadda zaai kai auren shashasha mara hankali, bacemun daga gani kafin in hadaka da mahaifinka"
Kallom zahra yayi ta galla masa harara hawaye na cigaba da zuba a idanuwanta tamkar ambude famfo radadin marin da yayi Mata akan wata yafi mata ciwo hakan yasa ta kudiri aniyar saita tarwatsa masa rayuwarsa da farin cikinsa baki daya taja hanci "taho nan ki zauna zahra kiyi shiru kiyi hakuri nasan maganinsa shasha sha kawai solobiyo"
********
Washe gari ummah tayo shirinta tsafff ta fito kisalin karfe sha daya na safe ta samu bilkisu zaune a parlor amina na taje mata kai hannunta rike da waya sai blushing takeyi,tabe baki ummah tayi "tou sarking chatin wato har nazo kanki bakima sani ba ko?"da sauri bilkisu ta kife wayar Tana dariya "ummah na fita zakiyi ne?shine baki fadamun ba na shirya na rakaki?"
"Tou bindi na babu inda zakije wanan unguwar ba taki bace don haka kiyimun adduar dawowa lafiya kawai"bata fuska bilkisu tayi kamar zatayi kuka "kai ummah na"
Ummah tayi gaba rataye da jakarta tana sanye da lafaya ja da jaka baka a hannunta "kanki akeji kingani nayi nan"ummah tayi gaba bilkisu ta bita da murmushi "a dawo lafiya ummah na Allah ya tsare"
"Ameeen yar ummah"ta fice abinta,
Da sauri bilkisu ta dago wayarta dake vibration tahir ne kada kai tayi "assalamu alaikum"ya furta bayan ta daga wayar "barka da hantsi"
"Barkanki sarauniya ina kofar gate"
"Ka shigo mana?"
"Sauri nake akan hanyata ta abuja nake yanzun haka nazo muyi sallama ne na hadu da ummah yanzun mun gaisa "
"Owk"tace ta kashe wayar ta mike gyalen jallabiyar ta taja ta yane kanta ta kalli amina "saura ki tashi kijirani yanzun"
A tsaye yake jikin murfin motar idonsa na kan gate din gidansu ta fito sanye da bakar jallabiya da bakin gyale,tayi kyau dikda babu kwalliya a tare da ita koda yake ya fahimcu bame yawan son make up bace,hada ido sukayi ta sakar masa murmushi shima yayi mata ta karaso ,kare mata kallo yake faduwar gabansa ta tsananta tunawa da yayi ta fidda miji a cewar kamal amma be karaya ba abbansa bazai rasa sanin abbahta ko wani abu daya danganceta ba tunda yaga alama tanada ruwa da yan nijar,ummah kama take da buzaye kuma abbansa dan nijar ne cikakke....
"Tou nazo sallama zan tafi amma bawai dan inaso ba domin inda so samune da kullum saina kalli kyakkyawar fuskar nan taki"murmushi tayi masa haka kawai taji yana burgeta yana kuma bata tausayi "baka rabo da zolaya kaidai"
Bude mota yayi ya ciro kayayyaki cike da leda katuwa ya dire mata a gaba "ga wanan sarauniyar kyau na kawo naga maabociyar dogayen riguna ce ke na kawo miki domin kyautatawa"..kallonsa ta tsaya yi cike da manaki ta kasa furta komi har ya gaji yayi mata tafi a fuska sanan tai furgigit "naga kina kallona ne"
"Kwayar idonka ke rikidemun tana komamin tamkar na ummah na haka kawai naga kana fuzgen kama da ummah na,sanan kuma ummah na iyayenta yan nijar ne kai kuma dan nigeria ne"a sigar shagwaba tai maganar
Langabe kai yayi yana dariya sosai saboda burgesa da tayi "tou ai abbah na dan nijar ne babyna,dole kiga ina kama da su domin nine mai kama da abbah kuma idan kika gansa tamkar yaya na"
Yar dariya tayi ta sunkuyar da kanta kasa "tou zan tafi wani sako kika bani inbawa ummah na da Ayrah?don nasan suna jira indawo suji amsar da zanzo musu da ita"ya kafe ta da ido cike da karaya,kallon sa tayi kamar zaiyi kuka yasa ta dauki jakar ledar daya ajiye mata ta juya da sauri tana daga masa hannu "zamuyi waya nidai"dariya yayi yana bin ta da kallo har ta shige gida.....sanan ya shiga motarsa yayi ribas ya mike hanyar fita unguwar,motar kamal ta kunno kai yana tuki da hannu daya saboda bandaji dake nade da dayan hannun,sam tahir be lura da kamal ba amma shi ya gansa,takaici ne ya rufe kamal idonsa duhu yake gani ya wani ja motar kadan ya rage be hadu da ginin gidan dake dab dashi ba yayi parking a kofar gida ma yana sauke numfashi sama sama......
Bubbude kayan bilkisu takeyi tana juyawa tsala tsalan dogayen riguna ne kala goma da agogunan hannu da turarrukan oud kala kala,lumshe ido tayi wato har yasan irin turarenta....yadda kamal ya shigo parlorn yasa bilkisu dan zabura don taji tsoro,ganinsa yasa ta kauda kai zuciyarta tayi bakin kirin hannunsa nade da bandeji...."bilkisu"ya kira sunanta da karaji,ko kallonsa batayi ba ta cigaba da kallom kayan tana lumshe ido "kinajin ina magana kinyi banza dani?koni banida darajar da zaki amsamum magana?"
"Dama kayi sallama kila da kasamu darajar sallamar miyaun bakina ya amsa maka koda zakasamu lada ka rage dumbim zunubin dake dankare a kanka"...jikinsa ne yayi sanyi ya sauke ajiyar zuciya "assalamu alaikum"yace jiki babu kwari....mikewa tayi tana hada kayan "waalaikumussalam idan da gaske sallamar take na amsa ne saboda hakiin musulumci"
Sosai kalamanta ke kona masa zuciya amma ya danne "bilkisu wajenki nazo dan allah ki saurareni muyi magana,dik hukuncin da zakimun kiyimun koda kin tsaneni ina rokonki da ki aureni"ya zube a kasa sai hawaye sharrrr sharrr a fuskarsa,wani kallo tai masa mai cike da tsana take abunda ya faru baya ya dawo mata lokacin data tsugunna a gabansa tana rokonsa dan allah ka aureni ya kamal ka rufamin asiri koda zan zama bora a gidanka kaimun lidifi ka zamemun hijabi....yasa kafa ya hambareta ta fadi gefen cikinta ya kulle,take kwalla ta ciko mata ido saboda bakin cikin tozartata da yayi...."nine na cancanci in aureki in zauna dake domin nine silar lalacewar rayuwarki nine wanda ya dace in aureki saboda abinda nayi miki na maidaki tamkar karuwar gida ta hanyar kwanciya dake ki taimakeni ki tallafi rayuwata kece first love dina ke nafara so bilkisu zafin zuciya da sharrin shedan sukai tasiri wajen ingizani aikata aikin danasani"... Daga masa hannu tayi cikin daga murya "ya isa"jikinta har rawa yake yana hango kwalla kwance a idonta ga tsanarsa dake kwance kwayar idonta ta bude baki zatai magana ya zaro yar karamar wuka a aljihunsa... jikinsa na rawa ya seta wukar a wuyansa "matukar kikace baki sona kim tsaneni bazanji zafi ba mafi munin kalma shine kice bazan mallakeki in maidake sarauniyar matan duniya ba".
Kallonsa take tamkar wani sabon mahaukaci anya kamal be haukace ya soma shaye shaye ba kallon yadda ya fita hayyacinsa takeyi yadda ya runtse idonsa hannunsa na rawa yana kokarin yanka jikinsa...bata gama tunani ba yakai wukar ya yanki kafadarsa kafin tace wani abu yasa ya yanki hannunsa ya soma rubuta sunanta jikin hannunsa jini na tartsatsi...ga dayan hannunsa da bandeji...yanayi zufa na zuba a fuskarsa hawaye ba cigaba da wanke fuskarsa.
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/8, 7:46 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*35*
Zahra ce sunkuye da kai a gaban ammiey mahaifiyarta kuka takeyi tamkar zata shek'e,wani kallo mahaifiyar tata tayi mata "Amma kin bani mamaki zahra'u ashe ilimin naki na banza ne tunda har kike wanan kishin na banza saboda mijinki zaiyi aure kike wanan haukar kina koke koke?a tunaninki kukan naki shi zai hana?tou tun wuri ki san nayi kafin mahaifinki yazo yaji shashancin da kikeyi saboda mijinki zaiyi aure"
"Amma ammi ki duba kiga kofa wata uku bamuyi da aure ba"
Tsaki ammie taja cike da takaicin zahra tamkar ta sharara mata mari takeji "sai me idan baku dade da aure ba?ko ranar aurenku ne fa yace ku biyu zai aura akwai wanda ya isa ya hanasa auren?idan kika kara magana zan tattakaki zan kuma ci miki mutunci shashashar banza mara wayau kuma tun wuri kibar gidan nan kafin mahaifinki yazo yaci miki mutunci don ni nayi miki me sauki wawuya kawai"ammiey ta nemi waje ta zauna ta maida hankalinta akan katon plasma tv din dake manne jikin bango tana kallon hijirah tv,kuka sosai zahra takeyi tana shassheka ta kwashi kusan minti goma a haka sanan ta mike fuskar ta sharkaf da hawaye ta dauki hand bag dinta ta rataya,cikin dasasshiyar muryarta tace "ammi na wuce"
"Allah ya tsare ki gaida hajiya hauwa da yara kuma ina nan zuwa gidan naki inga zaman da kukeyi da kijin naki,sakarya"zahra haka ta fice zuciyarta cunkushe da bakin ciki har ta kai jikin gate zata fice tasamu driver tayi dialing wayar tj bugu daya ya dauka jin muryarta kamar tana kuka ya mike daga kwancen da yake rungume da wata "ya dai Zahra meyake faruwa"
"Mu hadu gidan anty bina"shikawai tace ta datse wayar ta bude mota ta shiga gidan baya,ta zauna ta jikin madubi driver ya kalleta "ranki ya dade gida mukayi!"
"Gidan Anty bina,alkali road"tace tana sauke numfashi cike da kunar rai ga zuciyarta dake tafarfasa da tsananin kishi da ta tuna abinda kamal yayi mata zuciyarta zafi takeyi ga mugun sonsa da takeyi da kishinsa dake azalzalarta.....
Daukar hanya sukayi yana sake sake driver,tabbas ko baa fada masa ba tsayuwar da tayi jikin gate din gidansu tana waya to tabbas wanan mutumin ta kira kuma akwai wani abu,dole ne ya mike tsaye ya fidda ogansa daga halin da yake ciki ya warware kullin dake cikin gidan tunda yanada gamsasshiyar sheda akan hakan....
********
Cikin farin ciki suke innah tayi fankasau suna ci da miyar taushe dik kannen abdul suna zagaye dashi "ya abdul wallahi na kosa kayi nasarar auren anty bilkisu domin kundace,kai wanan aure akwai shagali"cewar bintu cike da farin ciki,
"Tou uwar azarbabi wato daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zaqi?dik wanan murnar da kukeyi da farin ciki na mun daidaita da bilkisu ne tou idan tace bazata aureni ba fa?"
Zumburo baki zainab tayi "bazai ma yuwu ba insha allahu "dariya yake musu yana kallonsu cike da farin ciki suma farin cikin sukeyi har innah dake gefensu batace komi ba sai murmushi kawai takeyi amma kallo daya zakayi mata kasan tana cikin farin ciki....
*******
Idanuwan bilkisu jajir take bin Kamal da kallo yadda jini ke zuba a tiles dinsu gashi ya runtse isonsa hawaye takeyi gumi ke karyo masa a goshi,bakin ciki ya lullubeta "kai a tunaninka wanan haukar da kazo kanayi da barazana da kakeyi shi zaisa in soka?shi zai goge tsanar da nayi maka cikin zuciyata?kayi ganganci kamal ka manta lokacin da nazo gareka ina rokonka alfarma kasoni ka aureni ka rufamin asiri kaimun lullubin sutura?ka watsawa idonka toka kaimun wulakanci hade da korar kare to kasani ko kashe kanka zanyi inga gawarka kwance a nan saidai in tsallakeka in wuce bazan taba sonka ba na tsaneka kamal,na tsaneka bana sonka,kuma ka fice mana a gida"cikin daga muryar take magana idonta jajir jijiyoyin goshinta sunyi rudu rudu.....bata kai karshen kalamanta ba taji saukar mari "ke bilkisu abu baya wucewa a wajenki?wace irim zuciya gareki da kike wulakanta jininki dan uwanki kamal?da kike cewa ya fita,yadda kike takama bala dan maliki ubankine haka shima haka"jikin ummah har rawa yake saboda bacin rai ta juyo ga kamal dake tsugunne akan gwiwarsa Yana bude idonsa a hankali a hankaki,dishi dishi yake gani ga jiri dake dibarsa a wajen suna hada ido da ummah,batasan lokacin da hawaye ya soma zubo mata ba kallon kamal takeyi yadda ya koma tamkar bashi ba,juyowa tayi ga bilkisu wadda tayi poster hannunta rike da gefen fuskarta hawaye ya wanke mata fuska,kirjinta ya tsananta bugu mamakin ummahnta take yadda ta sharara mata mari saboda kamal bayan abinda yayi kallon ummah takeyi kwayar idonta dauke da sakwanni masu yawa,hakan yasa ummah ta kauda kanta gefe daya "kamar nasan haka na faruwa na juyo na dawo saboda nakai laila plaza naga motar kamal ta wuce nayiwa mai napep umarni da ya juyo dani gudun abinda zai faru don naga tahir anan,....bilkisu tabbas baki kyauta ba kalamanki sunyi tsauri akan dan uwanki sanan kinbani mamaki,yata bilkisu nasanta da yafiya da rashim ruko tunda kika bude baki kikace kin yafe masa bai dace ki jefeshi da wadanan kalaman ba bayan kema mai laifi ce a gareshi,baki wuce kaddarar Allah ta fada miki ba kema,abinda ya faru bamu da ikon kaudashi tunda yana rubuce a cikin kundin kaddararki,kema kinayiwa mahaliccinki laifi Kuma ya yafe miki sanan kin fada a gaban jamaa cewar kinyafe to meyasa kike maida hannun agogo baya,....bilkisu"ummah ta kira sunanta cikim wata iriyar murya cikin karaya.....cikin shasshekar kuka bilkisu ta amsa "naam ummah"
"Babu Wanda ya dace dake da soyayyarki sama da kamal,kamal shine ya dace da ki aura domin sai yafi kowa ganin darajarki saboda shine masoyinki na farko,sanan sanadiyyar soyayya yasa idonsa ya rufe ya yanke miki wanan hukumcin daya yanke miki kuma kema mai laifi ce"hawaye ya gangaro wa ummah ta cigaba da magana "abdulhrahman fyade yayi miki kawai,bai maidaki matarsa kamar yadda kamal ya maidake ba be moreki kamar yadda kamal ya moreki ba, meyasa bazai aureki ya karasa laifinsa ba?"
Cikin kuka da gunji bilkisu ta shiga girgiza kai "ummah kiyimun rai bazan auri kamal ba kona auresa bazan taba sonsa ba bazan taba yi masa biyayya a matsayin mijin aure ba,bazan taba ganin darajarsa ba ummah kiyi mun rai"bilkisu ta zube gaban ummah ta ruko kafafuwanta tana kuka,murmushin takaici ummah tayi "harabada bazan mance da halarcin alhaji muhammadu ba,domin ana barin halas dan kunya saboda haka umarni ne na baki kamal shine zabina shi nakeso ya zamo abokin rayuwarki ko bayan rai na"
Zabura bilkisu tayi tana kuka tamkar mahaukaciya "wallahi ummah bana sonsa na tsanesa bazan auresa ba wallahi da in auresa gara na auri tahir ....banason kamal banason sa bazanyi zaman aure dashi ba"ummah ta gaura mata mari bilkisu ta runtuma aguje tayi dakinta a guje....
Kallom kamal ummah tayi wanda idonsa ko motsawa bayayi sosai jikinsa yayi sanyi,zuciyarsa ta kara karaya,lallai ummah yar halak ce,sanan besan wace irin mace bace ita,itadin ta dabance dik duniya babu wanda zaai masa wanan laifin ya yafe,sababbin hawaye ke gudu a fuskarsa,fuskar ummah dauke da murmushi ta goge hawayenta ta karaso inda kamal yake sau kawai ya durkushe ya rike kafafuwanta yana kuka....shafa masa kai takeyi ta nemi kujerar dake gefen su ta zauna "ya isa kamal....kukan na menene?umm?"tayi maganar muryarta na rawa itama kukan takeso tayi,tana jiyo sautin kukan bilkisu da ihunta tankar zararriya... tana jin zafin hakan cikim ranta tamkar ta shiga ta lallasheta amma bazatayi hakan yanzun ba saboda condition din da bilkisu ke ciki a halim yanzun....
Waya ta ciro wayarta tayi daga Jakarta cikin sauri tayi dialing wata number ta Kara a kunnenta,"hello doctor,dan allah inada bukatarka a gida na yanzun dan allah,yarona ya samu injury a hannu inason azo ai masa treatment na gaggawa"
"Owk hajiya gani nan zuwa ina unguwar taku"
"Owk sai kazo"ta dire wayar ta dago kan kamal"share hawayenka kamal banaso likita ya shigo ya sameka a haka gashinan zuwa zaizo ya wanke ciwon ayi maka dressing sai muje gidan tare"kallo kawai kamal yake bin ummah dashi tamkar mutum mutumi....ta mike tsaye Tana kwalawa safiya kira,sai gata tazo "dakko mopper da sababbin towel din da na siyo don goge goge kizo ki gyara wajen nan kafin tiles din ya kama kinga fari ne,yi da jiki nasan kinfi amina karsashi kalankasa ce"
"Tou hajiya"ta juya,jimm kadan sai gata da bocket da ruwa da mopper nan da nan ta shiga goge wajen da ruwa da omo tana matsewa cikin mintuna goma ta gama ta mike da niyyar barin wajen likita yayi sallama hannunsa rike da first aid box "sannu ummah"
"Barka dai ka iso? bismillah ga waje nan"
"Kamal karasa garesa a wanke maka ciwon ko?"ba musu ya ja jiki ya karasa gaban doctor da ya bude yake ciro kayan aiki,koda kamal ya bude hannunsa sunan bilkisu radammmm a farar fatarsa...kallomsa ummah keyi cike da tausayawa ta mike ta nufi dakinta....
*********
Nawal da afnan suna zaune a parlor suna kallon zee series momy ta fito hannunta rike da plate,fried rice ce da kaza a sama da cikula guda biyu ta ajiye a gaban yaran nata sanan ta dubesu "oya ga abincinku nan maza kuyi kuci afnan aci abimci saboda farin cikin momy kinji?"momy ta kalleta afee ta gyada Mata kai,kamal ne yayi sallama hannuwansa suka biyu an nannade hannun rigarsa kallo momy tabisa dashi be tsaya ko ina ba sai gaban kannensa dake zaune suna cin abinci, afnan ce tayi kicin tayi kicin kicin da fuska nan da nan zuciyarta tayi bakim Kirin Allah yasani ko ganin yayanta bataso saboda shine ya janyo Mata halin da take ciki,dik wani masifa shine sila,gimtse bakinta tayi yana kallonta ta kasa tauna abincin karbar spoon din nawal yayi ya dibi abincun ya kai bakinsa,yana taunawa ya dibo ya kaiwa nawal baki babu musu ta ansa tana taunawa,ya dibo ya kai bakin afnan....sai kawai ta soma hawaye,ta kasa motsawa tanajin haushin sa bata ganin kimarsa a idonta domin dik halin da ta shiga shine sila,ganin tana kuka ya ciro towel a alijihunsa yakai hannu yana share mata dukkansu a tare suka ga sunan bilkisu da ya rubuta a jikin hannunsa,tausayin kamak yasa nawal hawaye...tabbas soyayya gaskiya ce kuma so daban yake,
Jikin momy yayi matukar sanyi lokacin da taga yaranta uku dukansu hawaye sukeyi a tarw cikin tsananin damuwa ....mkarasowa tayi ta zauna gefen kamal ta rungumosu jikinta tana kuka mai ban tausayi ta ruko hannun afee "ki yafewa yaayah ko?umm afeen yayah kamal?kin tuna yayanki shine meyi miki wanka?me baki abinci a baki?yayanki meyin games dake?me koya miki assignment?me kaiki makaranta a bayansa ya dauko ki?yaayanki meson farin cikinki?yayanki me sonki din nan?kin tuna ...haba afee meyasa kika kullaci yayanki kikaji yanzun baki sonsa?meyasa kika tsani yayanki da kike matukar so fiye da kowa a da?"...hawaye ke bulbula a idon afee tana kokarin motsa bakinta"momy... dik nasani amma natsani yayah saboda shine silar jefani cikin wanan halin,shine silar lalacewar rayuwata da batani da akayi,dik abinda kayi sai anyi maka inji malamin islamiyyar mu,fadar annabi ce,da yace dik Wanda yayi zina da dan wani sai anyi da nasa,dik wanda ya bata dan wani sai an bata nasa,ko kanwarsa ko yarsa ko matarsa,tayaya bazaa bata rayuwata ba bayan yayana ya kasance yana bata yar wasu?....momy ki gafarceni natsani yayana saboda shine silar jefani cikin wanan halin da ina tunanin da wuya in auru" ..kuka afee ta rushe dashi, d'ago kai momy tayi abba na tsaye akansu yana kallonsu jiki a sanyaye basusan shigowarsa ba....mikewa kamal yayi da nufin barin wajen sabida zafin kalaman kanwarsa a garesa da tsananin tausayinta da yakeyi,alhakin bilkisu yasa ya auri mazinaciya wanda momy basu sani ba dama ance mazinaci Baya aure saida mazinaciya,sanan akaiwa kanwarsa karama fyade na rashin mutunci,bashi da kalmomin da zai roki afnan gafara gara ya nisanci shigowa sashen nasu....har ya Kai kofa afee ta daga murya "yaayah....."ta kira sunansa a karaye cikin kuka,ya tsaya "ina sonka ka dawo na yafe maka"..... dariya momy takeyi tana hawaye, Allahu akhbar dan uwa mai dadi,shi kansa abbah hannu yasa ya zare gilashin idonsa ya goge kwallar da ta taru a kwayar idonsa.....
*********
Tahir kuwa sai wajen karfe biyar ya isa abuja,ya isa ya tarar da wani farim cikin dadynsa ya dawo daga london,duka zaune suke cikin nishadi lokacin da tahir ya ciro wayarsa a aljihu ya fiddo hoton bilkisu ya mikawa dadynsa "daddy kaga hoton surukarka mai tsokanata da ina mata kama da jinin yan nijar"dariya ummansa tayi "kaidai baka da kunya tahir ka kasa boye son yarinyar nan don rashin kunya mahaifinka kake nunawa budurwarka?xamanin mu ba haka akeyi ba"dariya sosai dady yayi yakai hannu ya amshi wayar ya sa glass dinsa....kallon hoton sosai yakeyi amma hoton yarinyar na rikide masa zuwa yarsa saadatu...saidai wanan yarinya ce jikin dady na kyama yace "kai Tahir ina kasamo yarinya mai kama da yar yayana?saidai wanan karama ce waccen ko zatayi shekara arbain a duniya sunanta saadatu"shiru tahir yayi sanan ya lumshe idanu "tabbas daddy inaga mahaifiyar bilkisu itace saadatu domin kama sukeyi sosai da mahaifiyarta,akwai hotonsu da mahaifiyarta da ke kan dp dinta a WhatsApp bari in fiddo ka gani"..da sauri ya amshi wayar ya lalubi sunan bilkisu a WhatsApp ya fito da hoton dake dp dinta suna sanye da blue lace hoton da sukayi ranar bikin kamal kafin su fita....kallo daddy keyi yana murmushi cike da farin ciki yace "alhamdulillahi alhamdulillahi...tsarki ya tabbata ga Allah,hakika saadatu itace mahaifiyar bilkisu kuma yar yayana ne daya rasu a nan...bilkisu yar uwarka ce tahir"mikewa tahir yayi besan lokacim da ya fasa ihun murna ba ya runtuma a guje yabar parlorn, daddy bakinsa yaki rufuwa ya kalli ummah "alhamdulillahi wanan abu yayi mun Dadi dole mu dunguma sati me zuwa muje kaduna"Ayrah ta mike cike da murnar sunsamu yan uwa sanan matar yayanta....
*******
Kamal na shirin zuwa magriba driver ya shigo parlor sai mazurai yakeyi,kallo suka bishi dashi duka ya zube ya gaida daddy da momy sanan yayi shiru,kallon juna momy da daddy sukayi,momy na kokarin magana kamal ya rigata "kai lafiya?meke faruwa muka ganka a haka? akwai wani abu ne?"
Shiru yayi gabansa ya tsananta faduwa tsoron abinda zai biyo baya ya cikasa kada reshe ya juye da mujiya yazo ya rasa aikinsa,shiru yaki magana kamal ya daka masa tsawa "wai kai lafiya kayi magana kazo ka tasamu gaba ka gurfana gabanmu kamar me rokok gafara"afee da nawal idonsu a kansa kamar zai fado kasa....sosa keya yayi kirjinsa na bugawa cikinsa ya murda saboda tsoro dakyar ya hadiyi miyau me kauri yace..."dama barayin da ..."
Yayi shiru cikin kosawa kamal yace "barayin da sukai me?"
"Da suka taremu zankai su nawal makaranta,shugabansu Wanda yayiwa afee fyade Yana cikin gidan nan yanzun haka a dakinka tare da matarka"ya karasa maganar muryarsa na rawa cike da tsoro da fargaba.....
*Gare ku readers nasan zansha surutu akan neman mallakawa kamal auren bilkisu da nayi.....tou a dai takaice* *kamal shi yafi dacewa da auren bilkisu domin shine silar lalacewarta...sanan tun farkom littafin shine topic akansa na gina labarina......don haka ku* *bini kuji karshen labarin.....*
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*[7/9, 7:50 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*36*
Ummah ce sanye da hijab bayan ta idar da sallah ta fito har ta fuskanci shiga dakin bilkisu ta fasa,ta dade tsaye tana jiyo sautin kukan bilkisu, shasshekar kuka takeyi tamkar ranta zai fita,shiru ummah tayi har takai hannunta zata taba handle din kofar ta koma tamkar an hanata, zuciyarta nayi mata kuna tafarfasa takeyi mata,jin radadin kukan bilkisu yasa kwalla ta ciko a kwayar idonta,sauke numfashi ummah tayi ta juya tayi kitche,a tsaye ta samesu su uku sun hade kai kamar anyi musu mutuwa,kallon kallo sukeyi ita dasu "shaawah,yadai naganku a haka?...ke amina meye yake faruwa kike kuka kamar anyi miki mutuwa"
Safiya ta nisa"kawai bama jin dadin yadda muke ganinku da halin da Anty bilkisu ke shiga shine muke jaje"girgiza kai ummah tayi tana kallonsu,sosai taji sun burgeta "shaawah zan fita zan dawo ku fito parlor ba kowa a parlor kunji zan fita zanje in dawo"
"Tou ummah Allah ya tsare a dawo lafiya"
"Allah yasa"ta juya cikin sauri ta dauki yar jakarta ta fice da sauri....
A kofar gate malam mai gadi ke zaune yana jin radio,yana hangota yayi saurin dire radion daidai isowarta ya tsugunna "barka da fitowa hajiya"
"Barka dai,zan fita bazan jima ba zan dawo dan allah kada ka bari kowa ya shiga gidan nan ko waye yazo kaji na fada maka"
Shiru yayi ganin yadda ta hade girar sama da kasa "a dawo lafiya"kawai yace ya bude mata gate ta fice tsaye yayi yana hangenta yana kada kai,daga dukkan alamu kwana biyu marayun gidan da uwar da yar babu lafiya suna cikin damuwa duba da yanayin nasu,yana hangenta keke napep ya dire wani ta shige,girgiza kai yayi ikon Allah,hajiya saadatu bata da girman kai ko kadan dubi tankamemen gidan nan da motoci saidai yarta ta hau kawai ita bata damu da dukiya ba bata damu da rayuwar duniyar ba gaba daya....juyawa yayi ya rufe gate din ya koma mazaunin sa ya zauna ya Kara volume din radion sa ya kara a kunne....
********
Zaune yake a kofar gida cikin duhu wayarsa ta soma wuta ya ciro be kai ga duba me kiran nasa ba yaga tsayawar napep,tsaida me keken tayi ya gyara parking ta nufo gidan,tun daga nesa ya gane ko wacece ko baa fada masa ba wanan ummah ce take tahowa saboda wadataccen hasken farin wata dake layin da hasken pitilu , gabansa ne ya fadi sanan ya kalli wayarsa dake vibration yaga sunan baro baro RABBATULBAIT...sunan da yasawa bilkisu kenan, innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ya shiga ambato karasowa yayi ya zube a gaban ummah,"barka da zuwa ummah"
"Ah ah Abdul ashe kaine dama yanzun nake lalube cikin duhu domin banson wannene gidan daga ciki ba ashe kana kusa kenan"
Shafa kansa yayi gabansa na cigaba da faduwa "ehh ummah"wayarsa na cigaba da vibration...
"Mu shiga daga ciki ko?innar taka tana nan ko?"
Muryarsa na dan rawa yace "ehh tana ciki"
"Kafin mu shiga mu tsaya daga nan akwai muhimmiyar maganar data kawoni,amma kafin nan ga tambaya,ina fatan bilkisu bata kira ka ba"tana fadin haka kiran bilkisu ya kara shigowa "ehh ummah gashi dai yanzun take kira"
"Tou kada ka dauka mu karasa can muyi magana naga ga wajen zama"..jiki babu kwari abdul yayi gaba ummah na biye dashi,gefen benci ya tsugunna yayinda ummah ta zauna...
Tamkar zata fasa ihu haka bilkisu takeji wani jiri ke dibarta haka take kai kawo cikin dakin wayarta rike a hannunta,idonta ya kekashe ta kasa kukan ma muryar abdul itace kadai zata sanyaya mata zuciya,itace kadai zata kashe wutar gobarar dake ci a cikin zucuyarta a halin yanzun itace kadai zata rage mata radadin azabar da takeji,soyayyar sa ke yawo a jinin jikinta,me yakeyi take kiransa yanzun yana danna mata busy?dazun kuma baya dauka?kodai ummah can taje ne?idan ko ummah can taje ta shiga uku ta kuma mamayeta.....dakyar ta runtse idonta wata kwalla ta ciko idonta tamkar an bada mata tarugu,ruwa da iska zafi da sanyi rani da damuna bazata rabu da abdul ba matukar ummah na kan bakarta to tabbas akanta zaa Soma auren maza biyu ...sanan saita tabbatar wa duniya itace mace ta farko da zaa buga a mujalla ta auri maza biyu don wallahi mutuwa da daukewar numfashi da zaman kabari su kadai ne zasu rabata da abdul shima da anayi mutum biyu da sun mutu rana daya an rufesu a kabari daya....cikin karsashi ta furta "abdul ka dauki wayata....ka taimakeni kaji halin da muke ciki....mu nemi mafita tun wuri kafin lokaci ya kure mana,ji takeyi tamkar ta hada kayanta su gudu subar garin amma idan ta gudu ya zatayi da alhakin ummah da bata da kowa a garin nan?ya zatayi da ummahnta da ita kadai gareta?...hawaye suka gangaro mata ummah why,ya zakiyimun haka?wallahi bazan auri kamal ba"kamar zautacciya take magana ita kadai ta durkushe a kasa ta rushe da kuka tayi jifa da wayar gefe ...
*********
Jikin kamak tsuma yakeyi lokacin da driver ya ciro vivo daga aljihunsa sai gumi yakeyi ya cire key din wayar,nan da nan ya shiga videos saiga video ya kunna muryar zahra tangaras .."kai wai meye tsoron driver kakeji kada ya gane Kaine kayiwa afee fyade?..to idan ma ya gane meye ainice nasaka,idan haka ne kuwa zanyi gaggawar sanadiyyar da zai bar aiki gidan nan....ai wanan hukuncin nayi ne saboda karuwa da yaje kirana saboda bai sameni a cikakkiyar mace ba"
Kafin video din ya kare kamal ya saka wata kururuwa,momy kuwa salati ta saka tana tafa hannu cikin tashin hankali ta rushe da kuka.... mikewa yayi jikinsa na rawa ya shiga kitchen a guje ya dauko wuka caraffdd daddy ya rikesa "dakata kamal kada ka dauki doka a hannunka,ba an tabbatar da cewar yana cikin gidan nan ba kuma suna tare?tou bari in kira hukuma sanan zan bada umarni kada suyi jiniya kada suyi harbi da sun iso sai mu shigo dasu a damkesu"....jijjiga jikin kamal yakeyi tamkar ma yunwacin zaki,da nawal da afee kuka suka fashe dashi,
Kallom driver daddy yayi "ruga ka sanarwa mai gadi idan yan sanda sun iso ya shigo dasu kawai karkuma ya bari kowa ya fita cikin gidan nan"ba musu ya mike dik a furgice yake ya nufi fadin sakon daddy....
Shiko daddy waya yasa ya sanarwa da inspector akan ya turo yaransa da motoci guda biyu domin anga wanda yayiwa yarsa fyade,tunda already an shigar da report sun san da maganar....dibbbb ya kashe wayar...momy mutuwar zaune tayi ta kasa furta komi sai sauke numfashi da takeyi,sautin kukan su nawal shine ya cika dakin,kamal kuwa daddy na rike da rigarsa domin yana sakinsa fita zaiyi da wanan wukar....
Sun fito suna tafe ta harabar gidan ta baya sun bullo yan sanda suka dira wasu suna cikin gidan wasu sun zagare gidan da bakin gate...driver cikin sauri ya shiga main parlor inda su kamal suke "ranka ya dade yan sanda sun iso sanan,naga kamar mutanen takun fitowarsu yanzun haka"yana maganar yana haki,hannu daddy yasa ya fuzge wukar hannun kamal ya jefar a patlorn duka suka dungumo suka fito cakkkk Zahra ta tsaya turus tana bin yan sanda da kallo sai zarar ido takeyi,tj kuwa mutuwar tsaye yayi,suna hada ido da afnan ta fasa ihu ta furta "shine.......take kanta ya soma sarawa duniyar ta soma juya mata ta rike kai tana juya juya ta fadi kasa sumammiya.....momy da nawal suka tallabota momy ta shiga girgiza afee ko motsi batayi...nawal ta saka ihun kuka,kamal kuwa kukan kura yayi yai kan tj dake tsaye....
********
Innah sosai tai murna da ganin ummah,sun dan taba hirar minti goma sanan ummah tai mike "dama dubiya nazo yi nan wani asibiti dake bayanku shine na biyo"
Cikin faraa innah tace "aiko nayi murna sosai hajiya na kuma ji dadi naji dadi sosai kin faranta mun rai da kikazo indamuke"
Cikim zumudi zainab da bintu har suna hada baki sukace "ina anty billy ummah"
Jimm ummah tayi "aiko tana gida don tana sallah na fito,nasan idan har ta ga tahowa ta zata biyoni Niko banson ta rinka tukin dare"...makulli abdul ya dakko a daki ya fito"ummah to in kaiki mana "
Girgiza masa kai tayi "kaide muje me napep na jirana"tayi gaba suka biyota dukkansu suna tsaya a soron gidan suna mata allah ya kaita gida lafiya,abdul ko tsallakawa yayi ya tsaya jikin napep yana jiranta,kallonsa tayi tai murmushi ta girgiza kai....sadda kansa yayi yana dan murmushi,saidai bashi da kwarin jiki ko kadan....daga mata hannu abdul yayi me napep yaja....tana barin wajen kiran bilkisu na shigowa....jan numfashi yayi yana saukewa,ya dauki wayar babu karsashi...jin sautin kukanta yasa yayi shiru yana sauraronta,bayason kukanta ko kadan bayason ganinta cikin damuwa hawayenta dake sauka ji yakeyi tamkar ana zuba masa garwashin wuta.....
Tana zaune a parlorn ta Kara waya a kunne tana hawaye tana kuka mai ban tausayi ummah ta shigo,misalin karfe tara saura na dare...kallonta ummah tayi ta kauda kai yayinda bilkisu tabi bayan ummah da kallo tana hawaye.....
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA AKAN DARI BIYU KACAL YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903.....
*sosai kalamanku readers suka caja mun kai sukasa zuciyata zafi.....wasu sun yankemun hukunci...sunyi concluding komi...ina* *godiya zuciyata radadi take yadda akaimun kalamai marasa dadi.....*
SLIMZY✍🏻
[7/12, 7:53 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*37*
Sautin kukan ta ke taba masa zuciya,ji yakeyi tamkar yayi tsuntsuwa yaje ya sameta ya lallasheta,jin yaki magana bilkisu ta dan saurara da kukan,"kaji hukuncin da ummah na ya yanke game da auramun kamal ko?wai wanan azzalumin wanda besan darajar dan adam ba,wanda shedan ke buga masa ganga yayi aika aika daga baya yazo yana danasani shine ummah na keson hadani dashi aure to wallahi ya Abdul idan ban aureka ba aka auramun shi kasheshi zanyi"tana cikin maganar ummah tasa hannu ta fizge wayar ta kara a kunnenta "abdurahman,kadaiji abinda na fada maka ko?"...jimmm kadan taji ummah tace "Allah yayi maka albarka kaji"...turus tayi a tsaye Tana cigaba da hawaye,kallon ummah takeyi tamkar ba ita ba tamkar ba ummah me sonta ba tamkar ba ummah meson farin cikinta ba zubewa tayi a gaban ummah "ki ceceni ummah ki ceci rayuwata wallahi bazan auri kamal ba bazan iya rayuwa dashi ba"....kukan bilkisu na taba Mata zuciya dik yadda zata fahimtar da ita akan kud'irinta bazata amince ba kamar yadda ta dauki alwashi bazata taba fasawa ba sau kud'irinta ya tabbata,daure fuskarta tayi ta hade girar sama da kasa "matukar bazakiyi mun biyayya ba bilkisu niko bazaki sake ganin walwala a wanan fuskar tawa ba,inaso ki cikamun burina da k'udirina bilkisu"..girgiza kai bilkisu takeyi cike da bakin ciki,tabbas yiwa iyaye biyayya yana daga cikin shika shikan da zasuyi maka hanya zuwa aljannah,amma akan auren kamal sai taga abinda ya turewa buzu nad'i....hannu tasa ta goge hawayenta ta mike tsaye ummah na satar kallonta ta gefen ido amma idonta yana kan tv yayinda hannunta rike da plate dan karami tana cin dambun nama,ci takeyi amma zuciyarta bakin kirin take ganin yarta daya tilo cikin wanan hali.....juyawa tayi tana hada hanya ta nufi sashenta tana tafe Tana hawaye tana waigen ummahn ta...
*********
*Washe gari*
Police station
Ko kafin safiya yan sanda sunyiwa tj mugun duka wanda saida ya fita hayyacinsa,tun yana magana Yana ihu har ya kasa,
Motar kamal ce tayi parking a harabar headquarter ta yan sanda dake gabasawa a jihar kaduna,dik wani wanda ya kwana ya tashi yasan nan ne headquarter ta yan sanda daga ita sai kotu, fuskar kamal tamkar be taba dariya ba haka ya fito, sanye da farar dakakkiyar shadda da takalmi baki yasha punish haka yake taku tamkar wani basarake a ciki ya tarar da abbah da driver wadanda suke ta famar rubuta report akan abinda ya faru musamman driver wanda shi yasan komi,tsaye yayi a gefe ya harde hannunsa yana kallon yadda zahra ta fita hayyacinta fuskarta tayi Baki Baki tana hada ido dashi ta fashe da kuka "dan allah mijina ka yafemun ka yafemun laifin dana aikata maka,soyayyarka ce sila itace tasa naji zafin kalaman da kakemun nace nima sainasa an raba kanwarka da budurcinta yadda zataje gidan miji itama mijinta ya rinka kiranta da karuwa dan allah ka yafemun ka rufamin asiri ka maidani dakin aurena idan abbah na yaji zai rabu dani zai cireni cikin sahun yaransa ka taimakeni ka tallafi rayuwata"ta rushe da kuka,wani kallo kamal yakeyi mata mai cike da tsana zuciyarsa tayi bakin kirin ji yakeyi kamar ya shekata lahira saboda takaici,zaro farar envelope yayi a aljihunsa tana ganin ya ciro ta furgice da kuka da burari cikin wajen,wata tsawa wata yar Sanda ta daka mata take tayi tsittt kamar ruwa ya cinye ta,can kamar wadda aka tsikara Tana kallon irin yadda yake watsa mata wani mugun kallo ta shiga girgiza kai"dan Allah kada ka sakeni wallahi ko ka sakeni ka rabu dani ni bazan rabu da kai ba, kamal kaine rayuwata Kai ne jinin jikina ina sonka kamal ka tallafi rayuwata kada ka fadawa iyayena"
Girgiza kai yayi dakyar ta iya furta "in zauna da fasika?me kawo namiji har gadom aure na?hmmmm Zahra na tsaneki fiye da yadda na tsani mutuwa ta don haka yanzun haka daga gidan ku nake"
Tana jin haka ta zaro ido,"ehh daga can nake nakai musu takaddar saki uku da nayi miki kuma na shaidawa mahaifinki dik abinda kikamun sanan na biyoki nan inbaki wata takaddar saboda ta zama biyu taki da tasu,na sassauta hukuncin da nayi niyyar miki amma kije da ni da ahalina muna miki allah ya isa tsakanin mu dake don kim cutar damu in Allah ya yarda sai...kin"abbah ya rukosa "haba be a matured man mana muje kawai mubarwa yan sanda su mungama namu zaa mikasu kotu daga nan zaa zartar musu da hukumci,don haka muje kawai"hannu zahra ta shiga mikawa kamal hawaye na gudu a fuskarta kafin ta fasa uban Kara tana kiran sunansa "kamallllllllll"zabga mata mari yar sanda tayi "yi mana shiru kwartuwa azzaluma"
Ko waigensu kamal beyi ba yana tafe zuciyarsa nayi masa tsananin zugi idonsa sunyi jajir sosai,takaici da nadama ta kara shigarsa driver yaja motar abbah da kamal suna baya a zaune,sun danyi tafiya mai nisa kamal ya dubi abbah sa yadan rusunar da kai "dama abbah inaso muyi maganar nemamun auren bilkisu ,inso samu ne ma kada a wuce sati daya ayi komi"
Kauda kai abbah yayi tamkar beji sa ba,kamal yana lura da nufin abbah,nisawa yayi "hajiya saadatu ta amince zata auramun bilkisu"da sauri abbah ya dubesa idonsa cike da tambayoyi da mamaki,jinjina kai kamal yayi "kwarai dagaske abbah ta yafemun zata auramun bilkisu ta amince yanzun kaine kawai zakayi maganar"
Murmushi irin na manya abbah yayi '"alhamdulillahi naji dadin wanan labari kamal hakika babu abinda zamu cewa iyalan gidan alhaji Bala sai sambarka dikda irin wautar da kayi"sunkuyar da kai kamal yayi,daidai nan suka iso kofar gidansu sukayi parkig abbah da kamal suka fito sukayi cikin gida,direct kofar parlorn gidan suka nufa a tare suka shiga,
Kwance afee take hawaye shabe shabe a fuskarta sundawo asibiti da momy ,itama momyn hawaye ne makale a idonta tsaye dady yayi akan afee yana kallon yadda ta koma tayi fari tass ta d'ashe tamkar babu jini a jikinta duban momy yayi "ya jikin nata?fatan an dubata sosai ko?"
Jinjina kai momy tayi tana mai jin zafin furucin da zatayi amma babu yadda ta iya dole ta fada "Alhaji ko kafin muje asibiti jini ya wanke afee a mota jini kawai ke zuba mata ko bayan da ta farfado,da mukaje bayan likita ya Shiga da ita ya dubata sai ya rubuta mana scanning take mukayi result ya nuna ciki tasamu amma ya lalace"cire hula daddy yayi "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"kawai ya furta , momy tana kuka tana fadin "yaron nan da yarinyar nan sun cucemu sun cuci rayuwarmu bazamu mance dasu ba a tarihin rayuwar mu gabaki daya,ga fyade ga ciki,inda Allah ya rufamin asiri ma da cikin ya lalace shine akayi mata wankin ciki aka karasa fiddo wanda ya tsaya a mahaifarta,fatan Allah ya tashi kafadarta kawai....
Neman waje kamal yayi ya zauna,ya kasa magana,ikon Allah lallai Allah buwayi gagara missali tabbas abinda yayi ne akai masa ko fin ma Wanda akayi masa tunda gashi afee ita harda ciki tasamu Allah ya rufa asiri ma da cikin ya fadi.... shi kansa daddy kasa magana yayi ya fice kawai daga parlorn saboda takaici yayinda wajen yayi tsittt sai saukar ajiyar zuciyar afnan wadda idonta ke rufewa a hankali bacci na neman daukarta.....
******
"Malam ka taimaka kaje kayo bellyn zahra dan allah kada kace haka,hannunka batai rubewa ka yanke ka yar"ammiy ke maganar cike da damuwa,
"Kina nufin inje in karbo yata tayi sanadiyyar lalacewar rayuwar yar wasu?koko inje insa hannu a bani yata tayi zina da aurenta?hmmmm ni inada sani saboda haka ta sanadiyyar zahra bazan shiga jahannama ba,don haka idan duniya zata hadu bazanje domin neman belly na zahra ba hukunci nakeso ya hau kanta na lefi biyu,babban hukuncin ma shine a jefeta tunda tayi zina da aurenta ina rokon Allah yasa a mikata kotun musulumci, saboda masu hali irin nata ya zama izina a garesu,inaso ayi mata hukunci saboda ta samu sassauci gobe kiyama ko kayan ya ragun Mata"yana gama magana yasa kai yabar parlorn,ammy ta kalli Anty bina waccw dik jikinta yayi sanyi kallo daya zakai mata kasan tana cikin tashin hankali da tsananin nadama,hawaye ta shigayi tana mai jajantawa yar uwarta makomarta,tasani ko zasu mutu mahaifinsu bazaije karbo zahra ba domin kaifi daya ne shi,nadamar abinda ta aikata a rayuwa yasa hawaye ya shiga gudu a fuskar zahra.....
**********
Kwana biyu kenan Abdul bezo wajenta ba,babu shi babu dalilinsa,dik yadda takejin radadin rashinsa da zazzabi da takeji haka tayi maneji tayi wanka ta fito da niyyar zuwa ganin abdul da gidan kanwar mahaifinta ta kai kukanta gareta ko zata samu ummah ta janye da maganar auren wanan azzalumin,
A parlor ta tarar da ummah,waya takeyi hankalin bilkisu ya koma kanta jin sunan wanda ta kira tana wayar "Abdulhrahman,naji dadi nagode da biyayyar da kaimun kuma kada ka karya mun alk'awarina kaji?har lokaci yayi da nima zan nemi abinda zan biyaka dashi"jimm kadan ummah tayi sanan tace "nagode"ta dire wayar ta kalli bilkisu da dik ta rame ta lalace sosai,"ina zakije kuma da izinin wa?"
Bakin bilkisu na rawa cike da tsoron yanayin na ummah "dam...a dama gidan momyn khairee zanje ingaisheda khairee saboda zazzabi da takeyi"dabara ta fado mata,take ta saita natsuwarta "ayya Allah ya sauwake ki gaida momyn taku nima zanje insha allahu "batacewa ummah komi ba tasa kai ta fice ummah tabi bayanta da kallo zuciyarta a karye amma baxatayi kasa a gwiwa ba wajen kudirinta wajen ganin ta karbarwa bilkisu yanci kamar yadda tayi niyya.....
Tun daga nesa ya hango motarta,yana zaune jikin motarsa bugun zuciyarsa ne ya tsananta,tayaya zai fuskanci bilkisu a yanzun bayan alkawarin da yayiwa ummah?me zaicewa bilkisu? innahlillahi da yasan zatazo da ya guji haduwarsu da ita,gudun karya alkawarin ummah,gudun ta karya masa zuciya ta sosa masa inda ke masa kai kayi, dikda yayi kewarta yana sonta soyayyarta ke masa yawo a zuciya....tanayi parking ta sauke glass ta zuba masa ido nan da nan hawaye ya soma sauka a fuskarta kamar ruwan sama....sandarewa yayi daga inda yake zaune ya kasa motsin kirki kusan minti biyar,dakyar ya mitsa jijiyoyinsa da suka daina aiki dakyar ya motsa kafarsa ya taka zuwa wajen motar ya bude ya Shiga.....
********"
Daddare bayan sallar isha,i abban kamal bayan ya bar massallaci mota ya shiga direct gidan alhaji Bala ya nufa,ciki ya shiga da motarsa yayi parking sanan ya fito ya nufi hanyar shiga gidan yana tafe har kofar parlorn yayi sallama,
Jim muryar ko waye ummah tayi saurin gyara zama da gyara gyalenta "barka da zuwa sannu da zuwa"
"Yauwa "yace yana karasa shigowa cike da faraa fuskarsa ya nemi kujera ya zauna suka gaisa saiga shaawah da tray da lemo da cup ta ajiye ta tsiyaya masa ta ajiye ta wuce,daukar lemon yayi ya kurba ya ajiye "kin ganni daddare ko?danki ne ya tasoni wallahi,dama munyi maganar da rana dashi"
Sunkuyar da kai ummah tayi tana murmushi "Allah sarki kamal,ya hannun nasa da yaji ciwo?"
"Yayi sauki alhamdulillahi ai ya kame ciwon "
Shiru na dan wani lokaci "dama akan maganarsa da bilkisu nazo,tou yau dama nakeda niyyar zuwa to an samu hatsaniya da me dakin nasa har sun rabu sakamakon wani dalili Wanda insha allahu zan sanar dake a gaba,ya shaidamun kin amince masa da ya auri bilkisu yata saidai baki nemi shawarata ba wajen amince masa hajiya da kinbar sa yadan sha wahala ko"yar dariya ummah tayi batare da tace komi ba "koda yake bazan shiga tsakaninku ba tsakanin d'a da mahaifi sai Allah,tou tunda abu na gida ne ina ganin ba sai an tsaya wani kace nace ba duka yara tsatso daya suke dom haka me zai hana jumaa mai zuwa a daura aure?"
"Dik yadda kace ai kaine mahaifin yaran duka fatan mu Allah ya tabbatar da alheri"
Sosai abbah yaji dadin furucin ummah yayi mata godiya sosai ya tafi......
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/13, 8:04 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*38*
Misalin karfe biyu na dare bacci ya kauracewa idanun bilkisu,alwala tayi tazo ta shimfida dadduma ta fuskanci gabas tayi sallah raka'a biyu ta zauna ta daga hannunta sama nan da nan hawaye ya wanke mata fuska jerowa Allah kirari ta shigayi tana kai kukanta wajen Allah,gabaki daya ta karaya da lamarin ummahn ta da Abdul ta rasa gane kansu musamman yau da taje wajen Abdul da niyyar su gudu suyi aure a wani waje amma yanayin yadda ya nuna mata ya sanyayar mata da jiki tana kyautata zaton ummah ta sanarwa da abdul halin da aje ciki yasa ya canja mata ga soyayyarsa dake azalzalar zuciyarta sanan mummunan labarin da ta tarar be wuce yadda ummah ta shaida mata cewar sun yanke zaai aure ranar jumaa ba hankalinta ya tashi tanaji tana gani ummah na kokarin mika ta hannun azzalumi kamal.....kuka sosai takeyi tana jan carbi ta jingina da jikin bango har bacci ya dauketa.....
*Washe gari*
Tana ta shirin makaranta tana zaune parlor shaawa ta kawo Mata soyayyen dankali da kwai da plantain cin dankali takeyi tamkar tana cin magani,sallamarsa ce tasa tayi saurin juyowa suka hada ido,yasha blue din voile na maza sai sheki yakeyi yasha hula,kallom da yakeyi mata yasa ta dauke kai tamkar bata gansa ba,zagayowa yayi ya tsugunna a gabanta ya dauki dankali yakai bakinsa yana taunawa yana kallonta,sosai yakejin soyayyarta ta fuzgarsa irin kallon da takeyi masa shi ke sanyaya masa jiki dakyar ya bude baki a sanyaye yace "barkanki da tashi matata"wani kallo tayi masa taja tsaki ta yinkura ta mike ummah ce ta shigo parlor rike da plate din soyayyen dankali itama ta wuce ummah kamar wata kububuwa ummah tabita da kallo ta girgiza kai ganin kamal ta fad'ada faraarta ta karaso parlorn ya tsugunna ya gaisheta ta amsa cike da faraa "ya wajensu hajiyar taka?"
"Suna lafiya tace in gaisheka"
"Zauna mana bari shaawah ta kawo maka abun karyawa ko?"
Girgiza kai yayi kansa a kasa "ah ah ummah wallahi na karya " wucesu tayi abinta ko kallonsu batayi ba ta fice,tashin motarta kawai sukaji....
Tafe take tana driving gabaki daya bata da sauran kwarin gwiwa batada inda zataje da maganar nan basu da dangi wadanda zasu share mata hawaye,gidan kanwar mahafinta da taje ta tarar sunyi tafiya basa kasar tafiyar gaggawa ta kamasu ciwon yayah yusuf ya tashi sunje london momy hafsa itace hope dinta kuma bata kasar,hawaye ya zuraro a fuskarta sosai takejin zafi a ranta haka ta isa makarantar,tun daga nesa ta hango pheey nayi mata waving,hakan yasa ta maida glass din fuskarta gudun kada wani ya gane halin da take ciki karasawa tayi suka ruko hannun juna suka karasa harabar wajen bishiyoyi suna zama ta hango motarsa ta shigo makarantar kallon pheey tayi "waye muke da shi first period?"
"Sir kamal"ta bata ansa a takaice "to wallahi bazan shiga ba naso muyi magana ne bari inje cafeteria idan kungama kiyi flashing dina "mamaki ne ya kashe pheey dikda tasan abinda ke tsakanin su bata matsa ba ta amsa mata da toh kawai ta mike tabar wajen...
********
Zaune yake a office Yana shigar da assessment dinsu yana aiki ne amma tunaninsa na wani waje mamaki yakeyi yadda yau gaba daya taki shiga class dinsa kuma tana cikin makarantar,me hakan ke nufi?kiyayyar sa har ta kai ta guje shiga daukar karatunsa ma?koda yake zai Koya mata sonshi be cire rai zata soshi ba a rayuwa.....
********
A gurguje ....
Daren jumaa kwana bilkisu tayi tana kuka musamman daya kasance gobe ne daurin aurenta da kamal,aure sai kace bazawara babu kowa da yazo maganar aurenta sai wata kawar ummah da tazo daga Abuja da ummah ta sanar mata zatayi auren yarta me yakai wanan takaici?basu da dangi sai Allah nawal ta shaida mata a waya gidansu cike yake da mutane wato sune marayu basu da kowa sai Allah.... massage ne ya shigo wayarta da sauri ta janyo wayarta jikinta na rawa ko abdul ne yaga massage dinta ya kunna wayarsa turus tayi ganin me sakon tahir ne yake shaida Mata gobe suna tafe kwansu da kwarkwata zuwa kaduna harda mahaifinsa yayi missing dinta.... runtse ido tayi wasu zafafan hawaye suka zubo mata allah sarki bawan allah,ita masifar da take ciki tasa ta manta da wani tahir,gobe kafin ka iso garin nan misalin karfe sha daya na zama matar wani azzalumi inama ummah ta auramun kai a memakon kamal da dai in aureshi,ta rushe da kuka.....
Kawar ummah ce zaune gefen gadon ta "long time saadatu bamu hadu ba sai yanzun da bikin bilkisu ya tashi,kin ware kanki kina rayuwa ke kadai kwal sai yarki meyasa haka?ni baki daukeni matsayin yarki ba da bamu dauki wanan lokacin bamu hadu ba,ke kinsan na zazzo ko bayan mutuwar mijinki,yanzun fisabilillahi kinaji kina gani zaki aurawa yarki kwaya daya tilo ga Wanda bataso ? saurara kijiyo kukanta a daki"ta tsagaita da maganar fuskarta dauke da alhini....
Kukan da take shanyewa tsawon kwanaki ummah shi ta fashe dashi ta ruko hannin aminiyarta "hajiya saude,wallahi banida yadda zanyi na shiga tsaka me wuya an cutar dani da yata bamu da yadda zamuyi mu dauki fansa,an wulakanta rayuwar bilkisu hajiya banida karfin ikon da zan maka aminin mijina a kotu dan dansa yasa anyiwa yata fyade"...wani zabura hajiya saude tayi taja da baya ta dafe kirji "fyade fa kikaje hajiya saa"gyada mata kai tayi hawaye na gudu a fuskarta "fyade hajiya saude,na matukar yarda dake ne yasa zan Baki wanan labarin daya faru da yarki bilkisu"jikin hajiya saude yayi sanyi tun kafin taji meya faru jikinta yayi laasar idonta yayi jajir tana jiyo kukan bilkisu ga kuma mahaifiyarta nayi tun kafin taji komi,tausayi ya kamata ta ruko hannunta "inajinki saadatu "nisawa ummah tayi ta soma magana....
******
Kamal kuwa dik wani farin ciki yana cikinsa kallo daya zakayi masa kasan yana cike da nishadi burinsa ya kusa cika ya auri matar da yafi so a rayuwarsa yarinyar da rashinta zai iya sawa ya rasa rayuwarsa, yarinyar da soyayyarta itace ta zama jinin jikinsa take yawo a jijiyoyinsa yanzun,sallama yayi cikin sashen tun daga kofar parlorn yake jiyo hayaniyar mutane wadanda momy ta dan gayyata gogaggun kawayenta da yan uwanta dake yola sunzo wasu daga ciki yana shiga abokanan wasansa suka soma tsokanarsa washe baki yake tamkar gonar auduga,momy kuwa tsintar kanta tayi cikin farin ciki ganin kamal na farin ciki ko baa fada ba ya Soma dawowa hayyacinsa dik inda ya gifta yaga mutane saiya tsugunna ya gaishesu wucesu yayi ya bi ta kofar baya cikin sauri saboda hafeez abokinsa dake jiransa,yana shiga ya samesa zaune rike da waya suka tafa "ango kasha kamshi ana ganinka akaga annuri a fuskarka"murmushi yayi me dauke da tsantsar fari. Ciki ya kaiwa hafeez duka ya goce suna dariya "dole ka ganni cikin farin ciki saboda burina gobe zai cika na mallakar farin cikina,mallakar rabin rayuwata samun bilkisu shine cikar farin cikina rasata tamkar rasa rayuwata ne gaba daya"
Murmushi hafeez yakeyi "tou baban soyayya"suka fashe da dariya....
*******
Suna zaune har daya na dare da hajiya saude tana sanar mata kafin daga bisani takai mata karshen abinda ya faru...."tabdijan lallai hajiya saadatu kinga rayuwa kin kuma yi namijin kokari lallai macece ke mai kamar maza kwari ne kawai babu,a cikin maganarki kin shaidamun kinada shirin daukarwa yarki fansa wace fansa zaki dauka tunda tafaru ta kare kin kuma amince da ta auri azzalumin da be cancanta dashi ba?"
Hawaye ummah ta share "koda nimfashina zai dauke saina daukarwa yata daya tilo fansar bakim cikin da aka jefata na shekaru,sana daukar mata fansar budurcinta data rasa a ta dalilinsa,banida damar mikasu ga hukuma gudun tonuwar asirin dangin mu da yartawa da sunan mijina marigayi da zai baci amma nasamo wata hanyar da zan dauki fansa mai ciwo wadda harabada bazai mance dani ba koda hakan shine zai zama sanadiyyar rabuwata da iyalan alhaji muhammadu"....ta share hawayenta ta kamo hannu hajiya saude "kawo kunnenki"ta matso da sauri sun dade tana mata magana kasa kasa daidai kunnenta kafin hajiya saude taja jiki Tana murmushi "sai yanzun nasamu kwanciyar hankali,lallai hajiya saadatu kin shirya kuma hakan yayi"murmushi ummah tayi kafi daga bisani ta share hawayenta......
WANAN LITTAFIN IZZA TA NA KUDI NE GA MAI BUKATAR ALK'ALUMA SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL KO LITTAFIN IZZA TA YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/14, 8:15 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*39*
Washe gari da safe da zazzabi bilkisu ta tashi,ga wani ciwon kai da ta tashi dashi idonta yayi jajir saboda kwana da tayi tana kuka,dakyar ta iya watsa ruwa mai zafi ta fito ta zauna gaban madubi, kallon kanta takeyi a madubi babu dankwali akanta gashin kanta ya kwanta luffff ta rame sosai sai idanuwanta da sukayi zuru zuru suka kara fitowa,hancinta saboda ramar da tayi ya kara fitowa,wasu hawaye ne taji sun cika mata ido, dik a dalilin auren kamal ta fada wanan halin,ga mahaifiyarta da ta zame mata kwaya daya tilo tana fushi da ita a dalilin bijirewa da tayi da auren kamal,anya tayiwa ummahnta me sonta adalci kuwa?jikinta yayi sanyi tsanar kamal ta kara darsuwa a cikin zuciyarta,shine ya tarwatsa mata rayuwa tsawon lokaci,yanzun kuma yazo ya tarwatsa zamanta da mahaifiyarta,tunda take bata taba bijirewa ummah ba akan dik abinda takeso uwarta mesonta meyi Mata dik abinda ya dace na rayuwa ....hawaye ya gangaro mata dole ta nemi gafarar ummah ta yada makaman yaki tayiwa ummah biyayya saidai koda ta auri kamal bazata taba masa biyayyar aure ba da sunan mijinta wai... motsin shigowa yasa tayi saurin share hawaye,amina ce ta shigo fuskarta Tasha hoda bad'ani jaka ga uban janbaki da ta lafta babu laifi amina kyakkyawa ce saidai kwalliyar yan kauye da bata bari ba skirt da rigar atamfa ne jikinta Wanda ta Bata,tayi kyau amma gyalen taci dammara, hannunta dauke da faranti an jera kayan karin kummalo ta ajiye ta juya a sanyaye zata fita ta waigo ta dubi bilkisu da itama ita take kallo,murmushi bilkisu tayi mata aiko amina kamar jira take ta washe baki alamar jin dadi...kada kai bilkisu tayi dikda bakin cikin da take ciki idan ta tuna amina ta koma slimzy sai tayi dariya dan kauye kenan.....
Doguwar rigar atamfa ta saka ta fito kanta babu dankwali a parlor ta sami ummah da hajiya saude da wasu samari zaune momy ta basu umarni akan yadda zasu shiryawa bilkisu gado da kujeru wadanda akayo order su daga dubai....neman waje tayi ta zauna ta dubi hajiya saude "ummah ina kwana antashi lafiya?"
"Lafiya kalau balkisu ya kike kina lafiya koh?"gyada mata kai tayi saboda kuka da ya taso mata shiru tayi bayan ummah ta sallami bakin ta dubeta a sanyaye idonta cike da kwalla "ummah na ina kwana"yadda tai maganar ya karyar wa da ummah zuciya ta tabbatar da bilkisu ta yada makaman yaki tausayinta ya kamata "lafiya lau bilki na"farin ciki ne ya lullube bilkisu ta rarrafo ta kwantar da kai Akan cinyar ummah ta soma shasshekar kuka hannunta na rike da na ummar, itama ummah hawaye ya soma zuba yaba diga akan hannun bilkisu hakan yasa tayi furgigit ta dago kai fuskarta sharkaf da hawaye tana kadawa ummah kai "ummah na kibar kuka dan Allah wallahi na amince da auren kamal zan auresa zan zauna dashi kiyafemun"rungume ummah tayi hajiya saude dake gefe hawaye ya soma sauka mata tausayin ya da uwa ya cikata Allahu akhbar d'a da mahaifi sai Allah.....ana haka pheey ta shigo da sallamarta muryarta tasa bilkisu sakin ummah ta ruga da gudu ta rungume nafeesa,alamar suje ummah tayiwa nafeesa suka nufi dakinsu....
*******
Kamal yasha shadda fara kal takalmi fari agogo fari hatta hular kansa fara ce jin kansa yakeyi cikin tsananin nishadi nan da nan abokanan abbah suka cika gidan anata haramar zuwa daurin aure,dik inda kamal ya gifta kamshin turare kawai yakeyi tare da abokinsa hafeez da wani abokinsa lecturer suka fito....gida ya dau guda momy sai faraa takeyi fuskarta dauke da farin ciki ta shiga daga musu hannu sanda suke haramar fita....
******Kayan abincin da ummah tasa akayo a hotel sune suka iso harda wadanda zasuyi serving saboda masu daura aure sanan ta gayyaci wasu daga cikin abokanan mijinta mahaifin bilkisu zasuzo indan ta ita ne basai mutane sunzo ba.....hayaniyar isowar mutane yasa ummah da hajiya saude suka shirya ko wacce ta nada lafaya mai shegen kyau da tsada nan da nan maaikata suka soma aikinsu aka shiga fita da carpet carpet harabar gidan inda tasa samarin dazun suka kwafa rumfa....
Daddy mahaifin kamal yasha shaddarsa da hula yasha malum malum...kamal ummah ta hango yanata washe baki cikin harabar gidan yanata gaisawa da mutane,cije baki tayi saboda wani kululun bakin ciki daya taso mata nan da nan tsoron ciwon dake zuciyarta ta fama shi sakin labulen tayi ta juya da sauri....
Tunda suka shigo unguwar kirjin tahir ke bugawa duba da jerin gwanon motoci daya hango kofar godan su bilkisun abbansa ya dubesa "unguwar tasu cike take kamar ana daurin aure"kasa amsawa tahir yayi gabansa na cigaba da faruwa ummah ta karbe zancen "babu ko tantama wanan daurin aurene kuma kamar a gidan da zamu akeyi tunda yace wancen gidan ne number 12 ko"shiru tahir yayi bece komi ba....."kai tahir magana akeyi kayi shiru kamar ansa maka magana"
Dakyar yaja numfashi daidai motarsu ta tsaya ya dubi ummah "ummah bansani ba wallahi,kinadai gani tare muke da ku ai"...wani iri Ayrah tayi taana kallon yadda yake gumi ta jikin madubin mota kasantuwar a gaba yake zaune....dik jiki babu kwari suka fito a motar kallon ginin gidajen street din Ayrah keyi amma bata da karfin gwiwa haka suka kama hanya zuwa gate din gidan....
*******
"Inaso inji muryar Abdul na karshe a rayuwata nafeesa inaso muyi magana dashi kafin a dauramun aure da wancen azzalumin,inaso inji muryarsa kafin in mutu"
Zaro ido pheey tayi "ki mutu fa kikace bilkisu?taya zaai ki mutu?"
Girgiza kai tayi "kwarai dagaske matukar aka dauramun aure da kamal to tabbas nazama matacciya domin bazan taba moruwa masaba rayuwata zata koma tamkar gawa,kiran wayarsa nakeyi baya dauka kingani ta katse ma"muryarta na rawa take maganar "kara kiran nasa mugani a karo na uku"
Danna kira tayi kawai taji wayar a kashe wanan karon zamewa kasa tayi kan Chinese carpet ta fashe da kuka ta kifa Kai a kasa....
******
Daya daga cikin abokan alhaji bala,wato alhaji mansoor shine ya zama a matsayin wakilin bilkisu da zai bada aure ga mahaifin kamal wanda yake fuskantar alhaji mansoor nan da nan maroka suka soma kirari ana busa da kalangu.... Alhaji mansoor ya daga murya bayan yan adduoi yace "ku shaida ni alhaji mansoor wakilin auren bilkisu na mika auren yata ga Abdulrahman akan sadaki dubu dari biyar".....haka yayi daidai da mika hannun wani mutumi yana faraa "alhamdulillahi mun karba"....."dakata alhaji mansoor bafa sunan yaron alhaji muhammadu abdul ba kamal sunansa"cewar abokin mahaifin kamal....cakkkkk numfashi kamal ya tsaya hango ummah da yayi ta fito sanye da lafaya tana taku, abdulhrahman na biye da ita cikin manyan kaya milk colou din shadda da akayi mata aikin surfani....shiru wajen yayi ganin ummah na tahowa kallon kamal takeyi yana kallonta ido cikin ido fuskarta babu annuri kafin ta daga hannu sama"Alhamdulillahi irin wanan ranar nake jira ranar da bilkisu yata zatasan itadin me yanci ce ranar da nayi alkawarin haddasa maka bakin ciki a cikim zuciyarta kamar yadda ka haddasamun nida yata bakim cikin da har yanzun yana dashe a cikin zuciyar mu"hawaye ya shiga gudu a fuskar ummah "banida damar da zan mika ka ga hukuma saboda halarcin mahaifinka bazan iya mika ka ga hukuma ba domin hakan tozarci ne a garemu amma kanaji kana gani zan hana maka auren bilkisu wadda ko a lahira bana fatan ya kasance ka zame mata mijin auree,na tabbatar wanan daukar fansar sai tafi maka ciwo fiye da komi a rayuwarka kamal"
Turo kofar gidan akayi suka kuya a tare abbah mahaifin tahir ne ya shigo cikin gidan wanda dik abinda ke faruwa suna sauraran komi hakan yasa yana kallonta ya ganeta "ke saadatu meye haka?mezan gani haka?harshenki kawai akeji daga waje kina wanan ikirarin?wanan ba tarbiyyar mahaifinki bace".....kukanta ne ya tsananta tabbas kanin mahaifinta ne abbah na gangare.....kuka ta rushe dashi tana takowa.....
Numfashin kamal ne ya soma tafiya yasa hannu ya danne gefen zuciyarsa dake wani irin bugu take ya soma ganin duhu yana kokarin saita kansa ta hanyar dakewa da kokarin janyo jarumta,amma inaaa....ta yaya zai rasa bilkisu a gabar da yake ganin ya sameta?tayaya yanaji yana gani zaa daura aurenta da wani a gabansa a maimakonsa?mai yafi wanan tozarci da kaskanci kasawa zuciyarka son abu kiris ya rage ka mallakesa a hanaka?.... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun duhu ne ya lullube idonsa take ya dafe kirjinsa yayi baya ya fadi kasa ji kake timmmmmmm..... innahlillahi wa innah ilaihi rajiun mutane suka dauka sukayi kansa cikin tashin hankali...jini kebin hancinsa yana gangarowa, hafeez ya dago kamal yana girgiza sa "kamalllllllll"shiru babu alamar numfashi "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun wayyoooo Allah abokina dan allah ka tashi kada ka mutu kamar yadda kake fadin dik ranar daka rasa bilkisu zaka mutu idan baka mutu ba zaka zama da rai babu anfani"sambatu hafeez ya shigayi cikin jamaar daura aure family doctor din ummah yayi saurin kai hannunsa hannun kamal ya ruko jijiyar dake bada pulse rate yana jin yadda take harbawa ya furta a hankali "be mutu ba"......
*NOTE:team kamal nasan zakuyi korafi amma tabbas haka labarina yake....zakuyi tunanin tamkar na canja shawara saboda yadda nake shiga comments section ina kare kamal to haka nake dik book idan anayi inabin* *negative side ne....haka nake mabiya littafai na sun sani....ina wanan....sanan dik yadda littafina yazo hk na tsara abuna Rabbi yasani....*
08166177830 OR 08103943903
*SLIMZY✍🏻*
[7/15, 8:23 PM] 🥰slimzy🥰: *💥💥IZZA TA......💥*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*
_Wattpadd@slimzy33_
*SLIMZY✍🏻*
*ALK'ALUMA SHIDA*
*DOMIN SAMUN WADANAN LITTAFAI SHIDA AKAN 500 KACAL SAI YA NEMI WAD'ANAN NUMBERS* *DIN 08166177830 KO 08103943903....WAD'ANAN LITTAFAN SUNE👇🏻*
*HAYATUDEEN..RAHMA NA LELE*
*IZZA TA...SLIMZY*
*TANA K'ASA TANA DABO* *...SAFIYYA GALADANCI*
*DA CIWO A ZUCIYATA...KDEEY*
*GIDAN RINA...JIDDAH ALIYU*
*BURIN ZUCIYA...AISHA DAN SABO*
*40*
Cikin sauri doctor ya dubi hafeez "daukarsa muje parlorn can inaga akwai kayan aiki a cikin motata ina zuwa"be jira cewarsu ba yasa kai yana kutsawa cikin mutane nan da nan wuri ya dauki hayaniya....dafe kai mahaifin kamal yayi zuciyarsa nayi masa suwa tabbas tunda yake a rayuwarsa bai taba kunyata hakan ba amma dole ce tasa ya kunyatan domin komenene dansa kamal shi ya janyo shine sila,zuciyarsa na tururi ya furzar da iska a kunyace ya mike yana gyara malum malun jamaar dake wajen suka bisa da kallo, abokanan sa sune sukai karfin halin take masa baya....ummah kuwa ruko hannun Ayrah tayi tana kare mata kallo sosai take kama da bilkisun ta "muje daga ciki"tace musu tahir gabaki daya bashi da laka a jikinsa haka suke biye da ummah abdul na biye dasu tunda suka doso parlorn suke jiyo sautin kukan ta da shassheka suna shiga suka ganta durkushe a gaban hajiya saude Tana rera kuka kamshin turarensa yasa tai saurin dago fuska kanta babu dankwali, kallon kallo suka tsaya yi bin su take da kallo tamkar mutum mutumi,hannu tasa ta murje idonta ganin abdul cikin dakakkiyar shaddah mai tsadar gaske kyawunsa ya kara bayyana,kallom ummah tayi tana bin mahaifin tahir da ido da umman tahir da kanwarsa sanan ta kara kallon ummah tana jiran karin bayani...share hawaye ummah tayi "congratulations bilkisu,alkawarin Allah ya cika nasan kinamun kallon nakasa cika miki alkawarin da nayi miki na daukar miki fansar abinda kamal yayi miki,kayya dik abinda nakeyi donke nakeyi domin nayi masa ramuwar gayya wadda ake cewa tafi ta gayya zafi"zurawa ummah ido tayi hawaye na cigaba da gudu a fuskarta,bata fahimci bayanin ummah ba ko kadan ganin hakan yasa ummah ta ruko hannunta "bilkisu na cika miki burinki ta hanyar aura miki farin cikin rayuwarki gashi nan Abdul"ummah ta nuna abdul da hannu tana murmushi idonta cike da hawaye,kallon abdul billy tayi da sauri suka hada ido yadan kifta mata ido batare da kowa yagansu ba sanan ummah ta cigaba da magana "sanan ana tsaka da wanan tashin hankalin yan uwana yan uwan mahaifina suka bayyana domin wanan da kike gani tamkar kakanki ne dashi da mahaifina uwarsu daya ubansu daya kinga tahir a matsayin kawunki yake"dariya bilkisu ta fashe dashi ga kuka tanayi a lokaci daya nan da nan kukanta ya rikide daga bakim ciki ya koma na farin ciki....ta ruga da gudu ta rungume ummah tana gunjin kuka ....
********
Jiniyar motar gidan yari ce ta gifta motarsu abbah kamar ance ya waiga yaga Zahra a tsakiyar yan sanda da tj gefenta suna sanye da kayan gidan yari,da alama can zaayi dasu dik bakin cikin dayake ciki be hanasa ciro waya yayi dialing number inspector ba bugu daya ya dauka cikin dasasshiyar murya a sarke abbah ke tambayarsa yanzun yaga wicewar motar gidan yari da zahra nan inspector ke shaida masa an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar bayan nan mahaifin zahra ya bada umarni akan ayi mata hukuncin musulunci tunda tayi zina da aurenta akan gadonta na sunnah ta kuma amsa a jefeta koda shi tj bazaa jefesa ba tunda baasan iyayensa ba daga enugu yazo kaduna....ajiyar zuciya daddy ya sauke take tausayin zahra ya lullubesa jiki babu kwari ya kashe wayar,lallai mahaifin zahra yanada imani kuma cikakken musulmi ne tunda da kansa ya mika yarsa a jefeta wanda dayawa daga cikin mutanen wanan zamanin abinda kw cutar dasu kenan,danka yayi laifi ka kasa ganin laifinsa ka goya masa baya koda kisan kai yayi kuwa sai kasan yadda kayi ka amsosa balle wanda yayi fyade da idan ya dade yayi awa ashirin da hudu an karbosa abinda ya kara asassa fyade yayi yawa kenan a kasar...ga abinda dansa kamal yayi nan kasantuwar baai masa hukuncin shariah ba Allah keyi masa hukunci yana azabtar dashi....kwalla ce ta ciko a idon abbah daidai nan yayi parking a kofar gidan.....
********
Sosai doctor tayi zufa yana kokarin ceto numfashin kamal wanda saika kura ido sosai zaka hango alamar Yana numfashi,cikin kwarewa da aikinsa yayi masa wata allura a jijiya, cikin mintoci goma sha biyar ya sauke ajiyar zuciya a hankali alamar ya farfado ya dawo cikin hayyacinsa... idonsa a rufe hawaye masu zafi kebin fuskar kamal "shi kenan tafaru takare na rasa bilkisu,na rasa farin cikina...harabada bazan taba samun farin ciki ba......nayi mata laifi nasani ummah tayimun horon da na fada danasani mara amfani wanda inaji ina gani narasa bilkisu kenan....narasata narasata lokacin da nake bukatar ta"tallabosa hafeez yayi "calmdown kamal kayi shiru baka da lafiya ka kwantar da hankalinka baka rasa ta ba"... bude idonsa yayi ya saukesu akan hafeez cikin sigar tausayi wani irin kuka ne ya tasowa hafeez ya danne harshensa da hakorinsa ya shanye kukan....kallon doctor hafeez yayi "doctor ka taimakamun zuwa mota dashi tunda ya farfado mu tafi.....gyada masa kai yayi shi kansa doctor din jikinsa yayi sanyi sosai yakejin tausayin kamal dikda besan irin zunubin da ya aikata ba.....
*********
Suna zazzaune parlor ummah na zayyanawa kanin mahaifinta labarin abinda ya faru daddy yayi sallama hannunsa rike da afnan da momy Tana biye dasu,kukan afnan yasa parlorn yayi tsitttt lokaci daya.....suna shiga cikin rawar murya daddy ya soma magana "hakika saadatu banji haushin abinda kikayi ba domin kamal shine yaja komi shine yayi muku laifi....ga afnan nan yadda rayuwar bilkisu ta lalace haka tata ta lalace domin a hanyarta ta zuwa makaranta akayi mata mummunan fyade wanda zahra matar kamal itace sila....fadar ubangiji ce dik abinda kayi sai anyi maka gashi nan an lalata kanwarsa,yadda kikejin zafi saadatu haka muma mukejin zafi da muna boyewa amma na kawota ne in fasa komi in sanar daku,gara ke yarki ta samu mai aurenta amma ni ba lallai bane insamu me auren yar tawa"daddy yasa handkachief ya share hawayen da yakeyi,durkushewa afee tayi tana kuka a parlorn hatta mahaifin tahir saida jikinsa yayi sanyi....ummahn tahir batasan sanda ta fashe da kuka ba kallo afee da tayi yar karamar yarinya mai shekara sha biyar gata ba Kumari ba wani katon namiji mara imani ya cuci rayuwarta....mikewa bilkisu tayi ta karasa gaban afnan dake kuka ta dagota ta rungumeta ta fashe da kuka.... ummahn bilkisu ta mike ta hadesu ta rungume tana kuka zama daddy yayi ya kasa magana saboda bakin ciki momy ce tayi karfin hali "hakika munso kanmu da bamuyiwa kamal hukuncin daya dace ba amma wanan hukuncin shine daidai dashi....domin yana ji yana gani ya rasa abinda yakeso a rayuwarsa harabada baxai samu ba sanan shima dik wanda ya auri kanwarsa sai ya korota idan har besameta cikakkiyar mace ba saboda alhakin bilkisu"momy ta shiga rera kuka.....shiru parlorn yayi sautin kukan bilkisu da afee ne kawai,tahir yayi karfin hali dikda ciwon da yakeji na rashin samun bilkisu be hanasa furta "ummah na da abbah na zanyi jihadi fisabilillahi idan kun amince"...parlorn yayi tsit ummah tasan inda ya dosa ta daga masa gira cike da kwarin gwiwa ya dubi abbansa shima ya daga masa kai "daddy idan ka amince zaka bani auren afnan zan aureta a haka zan kuma zauna da ita tsakani da Allah sanan bazamu koma ba sai an daura mana aure zantafi can da ita zansata a makaranta zan rufa mata asiri,zan inganta rayuwarta....bazan tabayi mata gori ba domin ba a son ranta bane yayanta ne ya janyo mata"...dago kai bilkisu tayi tana kallon tahir ta sakar masa murmushi shima ya sakar mata.....sosai daddy da momy sukayi mamaki kallon kallo sukeyi don basu amince da maganar da tahir yayi ba Dan besan wayeshi ba,ummah ta fahimci hakan "hajiya hauwah tahir kanina ne domin wanan da kuka gani kanin mahaifina ne"daddy farin ciki ne ya lullubesa bana komi ba saina ummah ta hadu da danginta itama domin ba karamin tausayi take bashi ba.....
Ayrah ce ta mike ta karasa tana sharewa afee ido cike da tausayawa "kina son yayana?ki auresa kinji "kuka afee takeyi yana gyadawa ayrah kai suka ruko hannu suka rungume juna....
*******
Bayan sallar ishai daddy da abban Tahir suka sa shedu abdul da tahir da kuma abokin mahaifin kamal aka daurawa tahir aure akan sadaki dubu dari biyu take abban tahir ya bada....wani iri farin ciki mara misaltuwa ummahn bilkisu ta tsinci kanta,saidai bata taba nadamar abinda ta aikatawa iyalan alhaji muhammadu ba mahaifin kamal.....
Bilkisu kuwa ummah tayi mata umarni da tayi wanka ta shirya abdul zaizo ya dauketa su wuce gidansu,sosai bilkisu ke mamakin halarci da dattako irin na mahaifiyarta hakika bata da kamarta a rayuwa wato dik bidirin da takeyi umman ta kallonta kawai takeyi hatta gidan da zasu zauna itace ta sai musu tasa akayi funitures da komi a gidan....durkusawa bilkisu tayi a gaban mahaifiyarta ta sunkuyar da kai "hakika banida kamarki ummah na..samun uwa irinki a wanan zamanin tabbatas sai an bincika kece uwata kece ubana inayi miki matukar godiya ina kaunarki ummah na"muryarta na rawa ummah tasa hannu ta shafa mata kai "Allah yayi miki albarka bilkisu allah ya zaunar daku lafiya keda mijinki".....
Kowa fuskarsa dauke da farin ciki a parlorn shaawar uwa da yar ta kamasu bilkisu ta rarrafo ta tsugunna a gaban momy mahaifiyar kamal kafin tayi magana momy ta dagota ta rungumeta tana bubbuga bayanta,hawaye bilkisu takeyi....juyowa tayi ta kalli abdul tsaye yana jiranta sai ga amina slimzy da ghana most go da safiyya da takalminsu a hannu sun tsaya,kallom rashin fahinta ummah keyi musu ita ko umman tahir mamaki da dariya suka cika ta,ummah ce ta nisa "amina wadanan kayan fa?na menene?"zumburo baki tayi da manyan idonta batace komi ba saboda kiris take jira ta fashe da kuka safiyya ce ta boye fuska cikin hijabi "anty billy zamubi dom tace dik ranar da tayi aure damu zata nida silinzy"yadda safiyya tayi maganar da kiran silinzy yasa har abbahn tahir yasa dariya...
Girgiza kai ummah tayi tasan zaai haka da mutanen bilkisu,kafin ummah tayi magana bilkisu tana hawaye "allah sarki safiyya da amina zanyi kewar rashin jinku sosai nasan kuna Sona kuyi hakuri dole ummah zata bani ku domin aikin gida zaimun yawa ga zuwa makaranta"ruko hannunsu tayi tana lallashinsu,
Hajiya saude da pheey dake daki suka fito "ke mijinki na jiranki ki bisa"turo baki bilkisu tayi "ummah kice pheey ta rakani"
"Idan ta rakaki wazai dawo da ita?"cewar hajiya saude...ummah kuwa kallon yarta takeyi cike da kauna....wani irin abu ne ya taso mata ya tsaya mata a wuya shikenan yau bilkisu zatayi kwanan gidan miji ba gidanta ba shikenan ya guda yar lelenta zata nisanceta ya daya tilo....kwalla ce ta cicciko a idon ummah dakyar ta daurw hajiya saude da momy da umman tahir suka rike bilkisu suka fita da ita har cikin mota....
Can dare wajen sha daya momy da daddy suka bar gidan da afee suka nufi gida suka bar su ummah a nan abban Tahir da tahir suma zuwa sukayi suka kama hotel.....
Suna shiga cikin gidan su a parlor bilkisu tayi turus tana kallon irin dukiyar da mahaifiyarta ta narka wajen kawata gidan royal chair golden color sune a patlorn dik inda ta waiga kaya ne fadar haduwar parlorn bilkisu bata baki ne batasan lokacin da ta durkushe a kasa Tana hawaye tace "Allah sarki ummah na alherin Allah ya tabbatar miki"karasowa abdul yayi ya tsugunna gabanta ya bude hannu ta fada ya rungumeta tsammmmm yana sauke numfashi da ajiyar zuciya.......farin ciki ne ya lullubesa ya rufe idonsa yana hawayen Dadi yanayiwa Allah kirari da hailala....
*******
Kamal kuwa da safiya tayi ko motsi be iyawa yana daki da zazzabi ya kwana da ciwon kirji gefe daya Yana jin zafin rashin bilkisu yanaji yana gani wani ya mallaketa bashida damar amsota bashi da damar da zai hana.....hawaye yakeyi ya mike tsaye ya yana hada hanya wayarsa dake jikim carji ya ciro ya fito da hotonta ya kura mata ido....."kece first love dina kuma kece last bazan taba so wata mace a rayuwa yadda nasoki ba bilkisu bazan taba daina sonki ba sai ranar da na wayi gari bana numfashi....rashin ki rasa rabin rayuwata da kuma farin cikina ne gaba daya"sambatu yakeyi besan zuwan hafeez ba har ya karaso ya zare wayar a hannunsa ya zauna gefensa yana fuskantarsa "haba kamal wanan hukuncin shine ya dace dakai wallahi banji zafin abinda umman billy tayi maka ba domin shine daidai da kai kamal....wanan zaiyi maka zafi kuma harka mutu bazaks mance ba,gobe idan zakayi hukunci cikin fushi da zafi bazaka yanke hukuncin da hankali bazai dauka ba ...kome billy tayi maka mutuncin uwarta ya goge ka maida yarta matarka kana gurzarta kamar kasamu jaka"kuka kamal ya rushe dashi daddy yayi sallama dakin ganin yadda kamal ya koma ya kayar masa da gaba,gabaki daya ya fita hayyacinsa sosai sai ya dake "kazo kayi sallama da afnan domin abuja zasu tafi da mijinta, Allah maji rokon bawa ya aiko da wanda zai tallafi rayuwarta duba da zuciyarta tsarkakakka ce kuma kaine kaja mata"..zabura kamal yayi kamar mahaukaci ya bi bayan daddy har harabar gidan hango afee da nawal rungume da juna suna kuka yasa ya saki yar kara ya fashe da kuka ya tsaya nesa dasu kadan,momy ya hango da wata mata wadda bazai mance da kamanninta ba ya ganta jiya sanan ya hango tahir ya doso inda yake gabansa ya soma faduwa badai tahir abokinsa bane ya auri kanwarsa?tahir din da ya wulakanta a gidansa da yazo kwanaki?bai gama tunani ba tahir ya mika masa hannu kasa mika masa yayi murmushi tahir yayi "abokina ka kwantar da hankalinka nine na auri kanwarka kuma zan rike maka ita amana,da ka sanar dani abinda kaiwa bilkisu da nayi sanadiyyat daka sameta domin abbah na uba yake ga mahaifiyar bilkisu yanzun haka Ayrah kanwata munbarwa ummah ita saboda kada ta zauna cikin kadaici tunda bilkisu tayi aure,kaimun addua Allah ya bani ikon rike amana"Yana Gama magana ya juya da sauri saboda tausayin kamal da kuka da ya taso masa.....ruko afee momy tayi zuwa mota tana dagawa nawal hannu suna kuka tq juya ga kamal tana daga masa hannu...dakyar ya daga hannunsa yana mata bye bye yana hawayen nadama shine silar tarwatsa rayuwar family din gabaki daya....yarinya yar shekara sha biyar batasan soyayya da dadinta ba amma an daura mata aure an tafi da ita uwa duniya dik a sanadinsa....juyawa yayi ya nufi dakinsa cikin bakim ciki.....
*******
Rungume yake da bilkisu tana sanye da rigar baccin da ta gani a wardrobe komi sabo cikin drawers harda set din akwati ta gani aikin ummanta kenan diki inda ta kalla farin ciki ke lullubeta....ga masoyinta a gefe wata irin soyayya mai tsafta Abdul ke nunawa bilkisu tun a daren jiya ya kasa saurara mata... yanzun ma rungumeta yayi ta baya tana tsaye jikin fridge din parlor tana kokarin budewa ya manna mata kiss ya rada mata a kunne "bangaji dake ba ranki ya dade mu koma ciki mana"hararsa tayi dikda ita kanta abdul ya jiyar da ita dadin da bata tabaji ba a rayuwarta amma ta sunne kanta cike da kunya ta shige kirjinsa ya rungumeta yana kissing goshinta ...
******
Bayan sati bitu afee ta saki jikinta da tahir kasantuwar me barkwanci ne shi a haka ta saba dashi sosai yana koya mata sonsa har ta saki jiki ta soma farin ciki shike kaita makaranta ya dakkota kasantuwar dama ss3 zataje tana ss2 ne nawal ke ss3 hk ta saba da mutanen da ta hadu dasu a makarantar.....
****
Bayan wata uku kamal sosai ya fita hayyacinsa rayuwar gaba daya ta canja masa haka ya koma shiru shiru ko magana bayayi sosai koda yaushe idan ya zauna tunanin bilkisu yakeyi dare da rana.... shikenan ya rasata ta sanadiyyar son zuciyarsa....
********
A gurguje
Bayan shekara daya bilkisu ta haifi yan biyu maza da Abdul akasa musu sunan abban bilkisu da abban Abdul ana kiransu sudais da shuraim farin ciki wajen wanan family baa magana sanan cikin watannnin abdul ya habbaka kamfanin bilkisu wanda dukiyarta ta karu taci uban nada abun sai sam barka......
Dik yadda daddy da momy sukayi na lallashin kamal ya nemi matar aure yaki dikda komi ya wuce families din uku sun hade kansu waje daya tamkar uwa daya uba daya kamal ki yayi momy tausayinsa takeyi tunda likita ya sheda musu ya samu ciwon zuciya sanadiyyar tunani take kaf kaf dashi saidai kullum zuciyarsa na wajen bilkisu da danasanin abinda ya aikata mata yakeyi...sanan kullum idan ya tuna ya rasata rasawa na harabada sai yayi kuka ya zubar da hawaye......
TAMMATBIHAMDULLAH....A NAN NA DIRE ALK'ALAMINA SAI MUN HADU A LITTAFI NA NAN GABA NAGODE SOSAI MASOYA SLIMZY WADANDA SUKA SIYA DA WADANDA BASU SIYABA SUKE KARANTAWA KYAUTA INA KAUNARKU FISABILILLAHI.....ALLAH YA YAFEMUN KURA KURAINA DA NAYI A CIKIN LITTAFIN NAN NAGODE
08166177830 NUMBER SLIMZY KENAN INA GODIYA....
ALHAMDULILLAHI ALHAMDULILLAHI ALHAMDULILLAHI DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH.......
0 comments:
Post a Comment