"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!! Innalillahi ilayhirrajun!! Yanzu Baba Malam *SAMIMAN* ce _Macijiya!!!_?"
Nisawa Malam ya yi ya kalli Mahaifiyar Samima wacce zufa duk ya wanke mata fuska sabida tsananin tashin hankalin da take ciki, ya ce.
"Tabbas, shakka babu *SAMIMA MACIJIYA CE* kuma sihiri aka yi mata ta zamo haka, ba ƙaramin sihiri bane, kuma dole wacce ta yi mata ita ce zata ruguza wannan sihirin, in ba haka ba zata ci gaba da kisa ga duk wanda ya tabota, kuma a zahirin gaskiya ba ita ke kisan ba, miyagun da take tare dasu su ne suke kisan, sabida itama basu barta ba, lokaci zuwa lokaci su na gana mata azaba, ba ƙaramin babban yaƙi bane rabata dasu, kuma na gaya maki dole wanda ta yi mata wannan sihirin itace zata warware shi, kuma ta cikin gida ce ta yi mata wannan sihirin" share hawaye Umma ta yi ta ce.
"Malam, kana ta faɗin ta cikin gida ce, to wacece kenan?" shuru Malam ya dan yi yana nazari kafin ya nisa ya ce "a gaskiya baya cikin tsarin aiki na gaya maki, amma sabida Samima tana bukatar taimako cikin gaggawa yasa zan faɗa maki, ba kowa bace ta yi mata wannan sihirin illa *ASABE*" a zabure Umma ta miƙe ta ce.
"Baba Malam!!!? Asabe!!! Asabe!! Asabe fa ka ce!!? Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!! to me na yi wa Asabe? Ko kuma nace me Samima ta yiwa Asabe? Abun da Bamu haɗa Miji ba, balle nace ko kishi ne yake nukurkusanta da zai sa ta yiwa ƴata asiri , ina da ƴa mace tana da mace, to miye haɗina da ita da har zata mai da Samima rabi mutum rabi Macijiya?" murmushi Baba Malam ya yi ya ce.
"Kadan daga cikin halin Ɗan Adam, *ZULAIHA* shekara na 30 kenan a garin nan tun kuna ƙanana a lokacin da muke tare da iyayenku kafin Allah ya ɗauki ran mahaifinki, nine Malamin da da yawan yan unguwan nan ake kawo min su laluri, kumq alhamdulillah Allah ya horemin baiwa iri da kala, bazan iya gaya maki dalilin da yasa Asabe ta mai da Samima Macijiya ba, kije da kanki ki binciko wannan lamarin dan taimakon yarinyarki ɗaya tilo, tashi kije Zulaihatu, nima nan zan din ga tayaki da addua, dan kuwa aiki ne ja a gabanmu" share majina da gefen mayafi Umma ta yi ta miƙe ta yiwa Malam godiya sannan ta fice, Malam ya nisa cike da damuwa dan kuwa Samima tana cikin babbar matsala.
A hanya Umma tana tafiya tana zancan zuci.
"Asabe!? Asabe!? Asabe fa? Lallai kam na yarda da karin maganar da ake cewa ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa, yanzu me nayi wa Asabe? Da har zata cutar dani ta wannan hanyar? Dole ne naje na ji dalilin da yasa ta yi min wannan mugun aikin dan bazan iya gani a hallaka min ƴata ba" ta sake share hawayen da ya gaza tsayuwa a idanuwanta, ta nufi gidan Asabe.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Kwance take a dakinta a kan ɗan karamin gadonta, sai juyi take yi tana ihun azaba, dan wani irin raɗaɗi ne take ji a kowani sassa na gangar jikinta, tamƙar ana wanke mata fatar jikinta da narkekken ruwan dalma, har kwakwalwarta take jin wannan azaban zafin, a hankalin bakinta ya fara zufar da hayaƙi wanda kafin giftawar ido da bismillah daƙin ya gauraye da hayaƙi, gurnani ta fara tana murkususu, idanuwanta tamƙar jini haka suka rine, kafin nan da ɗan wani lokaci ta galabaita, a hankalin jikinta ya fara b'anb'ara yana fitar da sab'an maciji, ihu ta ci gaba da yi tana huci ,ta kumbure ta koma ta sab'e, wani razananniyar kara ta saki lokacin da ta ji kamar an soka mata mashi a tsakiyar kirjinta, fatar jikinta ya hau sabulewa, kafafunta ya hau babbanƙarewa, daga kafarta ne ta fara rikiɗewa, nan ta ci gaba da juyi tana murƙususu tana gurnani, nan jelar maciji ya fara bayyana daga kafafunta, nan ta koma rabi mutum rabi macijiya, wani juyi ta yi ta sake sakin ƙara fuskarta ta yi jajur kamar wacce ta ƙone, a ihun ne gabaki ɗaya ta rikiɗe ta koma macijiya, wanda girman wannan macijiya ya cika ɗan ɗakinta, nan ta kananneɗe ta haɗe rai sannan ta sauƙo kasa ta sulale ta fice tabar gidan.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
😂😂😂😂😂😂
*_ARADU BAZAN DOGON TYPING.. BA SAI NA GA RUWAN SHARHI, MA'ANA DAI KO KUN KARBI BOOK DIN, SAI MU ƊORA, KARKU MANTA NA GAYA MUKU GAJERAN LABARI NE_*
_GA MASU BUKATAR CI GABAN LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH RETURNS, MAI TAKEN SUNA *GAWURTACCEN SOJA* ZAKU SAME SHI AKAN FARASHIN #300 VIP #500, GA KUMA *AHLAN* WANDA ZAKU SAMESU AKAN FARASHI MAI SAUKI WA INDA AMINAI BIYU NE ZASU GWANGWAJEKU, IDAN DAYA KIKESO #200 NE, IDAN BIYU NE #300 VIP #500, VIP NA MUTUM ƊAYA #400, DUK A LITATTAFAN MU MASU TAKEN SUNA *AHLAN, NA ZAHRA ABDUL (MOMYN AHLAN) DA KUMA, WACECE KARUWAR? NA RASHEEDAT USMAN(UMMU NASMAH)* KARKU BARI A BAKU LABARI_.
MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻
[02/09 à 08:44] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA BIYU. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_MA SHA ALLAH! GASKIYA NAJI DADIN YADDA KU KA KARBI WANNAN LITTAFI, NA GA SAKONNIN DA DAMA ALLAH YA BAR KAUNA, WANNAN PAGE DIN NAKU NE, WA IN NAN GRPS DIN_* 👇🏻
*SLIMZY FANS GRP*
*MSS FLOWER*
*MASAUTAR A GARKUWA*
*FADAR MOM FAREESA*
*XAHRA FAROOQ*
_DAMA SAURAN GRPS DIN DA BAN AMBATA BA, DUK WANI MASOYIN BUK DIN NAN, SONSO DOMIN ALLAH_💓💓
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
"Assalamu alaykum!!! Asabee!!! Asabeee!!!?" Umma ta shiga gidansu Asabe tana sallama har tuntube take yi" Asabe dake uwar daki taji sallamar Maman Samima, wani shu'umin murmushi ta saki sannan ta miƙe daga gefen gadon da take zaune, wani kullin magani ne a hannunta ta yi saurin je fa shi ƙasan gado, sannan ta miƙe ta fito a yangace, tana fitowa ta sauke idanunta akan Maman Samima wacce kallo ɗaya zaka mata ka gane halin da take ciki na tashin hankali, wata uwar harara Asabe ta wurgawa Maman Samima, sannan ta turo ɗankwalinta gaban goshi, cike da rashin mutunci ta riƙe ƙugu ta ɗora dayar hannun nata a bakin kofa, har jijjiga jiki take yi, ta ce.
"To fa!! Su Zulaiha wannan uwar kiran da kike kwala min ta menene iyeee!!? Ko dai nima anzo a kasheni ne ,ni da ƴata? Kin ga Malama dan Allah ki wuce ki fice min daga gida ehe, karki goga min tsiya!!" da mugun mamaki Umma ke bin Asabe da kallo, da ace wani ne yake faɗa mata Asabe ce ke wannan maganganun zata karyata, amma sai ga shi ma ita ake gaya ma wa, uwa uba kuma Malam ya ce ita ta yiwa Samima asiri ta koma macijiya, amma yanzu kalli abun da take yi, tamkar bata san abun da ta aikata ba, Umma bata gama tunanin zucinta ba, ta ji Asabe na cewa "Dan Allah ni kam ki wuce ki fita min a gida" cikin ƙunar zuciya Umma ta ce "Allah ka rabamu da masu fuska biyu, wanda zasu gwada mana su na son'mu a fuska amma a zuciyarsu ba haka abun yake ba, Asabe!? Me na aikata maki a rayuwa!? Me nayi maki da har kika zauna kika kulleceni da wannan abun!? Asabe!? Na daukike tamƙar yar uwan da muka fito ciki ɗaya da ke, ni a tunani na duk abun da zan miki ko Samima ta yi miki bai kamata ki saka mana ta wannan hanyar ba, Asabe ina haɗaki da Allah ba dan ni ba,idan har ni ko Samima mun yi miki wani abu marar kyau a rayuwa dan Allah Asabe kiyi hakuri ki yafe mana, dan adam ajizi ne bai fi ba ko a wajan Allah mai laifi ne, balle kuma mu bayi masu kura-kurai da zunubai, dan Allah na roƙeki Asabe ki mai da min da Ƴata ta koma mutum, kinsa yanzu an fara gudun Samima, duk in da ta gitta a cikin unguwa sai da a din ga ce mata *SAMIMA MACIJIYA CE* idan kuma aka yi rashin sa'a ranta ya b'aci sai ta yi kisa, shekaran jiya tare-tare aka din ga yi da matasan unguwa su na so su kasheta, kuma Baba Malam yace ba ita ke kisan ba, na roƙeki ki mai da min da ƴata yadda take a da can baya, ko me muka miki kiyi hakuri a rashin sani ne, ko kuma ki fada me kikeso a wajan'mu, dan Allah Asabe ki karya asirin da kika yiwa Samima" Umma ta haɗa hannunta alamun roƙo ta zube guiwowinta a ƙasa a gaban Asabe ta saki marayan kuka tana ci gaba da roƙon Asabe, wani dariyar shekiyanci Asabe ta sake gami da cewa 'Ayyyyyriiriiii nanayeee!! Inyee!! Zulaiha? Sharrin naki ta kai har haka? Ki zo har cikin gidana ki min sharri? To ni ina ruwana dama sun kasheta!! Yarinyar da ta addabi kowa a garin nan, waye bai san da cewa *SAMIMA MACIJIYA BA CE??* kuma dan munafurci da sharri ki ce ni na mai data macijiya? To akan me? Ke da yarki masu kama da mayu sabida shegen kyau? Wallahi!! wallahi!! Wallahi!! Zulaiha kinji na rantse miki ko? Idan ba ki tashi kin fice min daga gida ba zan saka maki ihu, idan jama'a sun shigo abun da zan faɗi har ki mutu idan kikaji an kira sunan Asabe sai kin girgiza, dan za ki san wacece ake kira da Asabe ikon Allah wanda naci dubu sai dai ceto wallahi, ba a mai da ta mutum din fice min!!" Asabe ta fara yiwa Umma korar kare, ingizata ta dinga yi har ta fito da ita kofar gida ta cillata ta faɗi kasa, sannan ta yi mata kallon wulakanci ta mai da ƙyauren gidanta ta rufe, a hankali Umma ta miƙe jiki ba kwari ta kama hanyar gida tana tafiya tana kuka gami da tunanin jarabtar da Allah ya jarrabe ɗiyarta, yanzu wacce hanya zata bi wajan ganin ta taimaki ƴarta ta dawo asalin mutum? ba rabi mutum rabi macijiya ba? tana kan tunaninta kenan tana shawo kwanar gate din gidanta taji wani uban guguwar hayaniya na tashi, da gudu ta diba dan ganin meke faruwa, tana zuwa ta ga ciccirindon mutane matasa yan unguwa ko wanne dauke da mugun makami a hannunsa, daga gani a tunzure suke matuƙa har da masu fetur da cerozin ga ashana, zaro ido Umma ta yi ta karaso tana tambayarsu lafiya kuwa? Wani matashi ne ya zo gaban Umma ya ce "Maman Samima ki shiga ki fito mana da Samima,yau babu shegen da ya isa ya hanamu yin gunduwa-gunduwa da Samima" ɗaura hannu akai Umma ta yi tana salati ta ce " Habu? haba Habu? Me Samiman ta yi?"
"Taya za ki ce ba ki san abun da ƴarki take aikatawa ba a garin nan yanzu? To kalli abun da ta yi" ya faɗa yana nuna mata gawar wani ɗan matashin saurayi wanda ga tabon saran maciji a goshinsa da wuyansa, baya-baya Umma ta yi tana furta "Innalillahi wa inna ilayhirrajiuna!!!!! Na shiga uku ni Zulaiha' injiwa ya ce Samima ce ta kashesa!?"
"Dalla ki rufa mana baki!! Da wa yasan cewa ƴarki ba mutum bace? Shekara nawa kenan tana kashe mutane, ban da kwanan nan da muka san gaskiya, wallahi ko ki fito mana da Samima ko mu ƙona gidan nan kuma sai kun bar garin nan ehe" cewar wani mutum,wani ma ya ce "to wai ma me muke jira ne? da ba zamu fara ta kan Uwarta ba!!" suka yi kan Umma yuuuu, da sauri Umma ta yi wuff ta shige gida, ta danne karamin kofar dake jikin gate ta wuce ciki da gudu ta ɗaga waya ta kira mahaifin Samima ta faɗa masa halin da ake ciki, sannan ya tambayeta ina Samiman ta ce masa bata ganta ba ,bata gida kuma kafin ta fita sai da ta kulle ta dan Baba Malam ya ce a daina bari tana fita, Baban Samima ya ce "to a garin ya ma ta fita tun da kin kulleta? Kin ga kwantar da hankalinki gani nan zuwa" yana faɗi ya ajiye wayar ya tashi da sauri ya fara tattara kayansa, ya fito kenan zai shiga ƴar motarsa ta rufin asiri mai su na toyota sai ga yaron ogansa wanda shine Manager a Companyn, yana ganinsa ya ce "ah Baba, ina kuma zaka je na gan ka a haka? cikin tashin hankali da damuwa mahaifin Samima ya sunkuyar da kansa ya kasa ba wa yaron ogan nasa amsa dan yana jin kunyarsa ba kadan ba, dan yaron akwai natsuwa da hankali da sanin ya kamata ga shi da girmama mutane, tun da ya dawo daga ƙasar waje shekara shidda kenan yanzu bai taba yi masa rashin kunya ba, duk inda ya gansa zai duƙa ya gaishesa Baba sama Baba kasa, ranar da ya ga Samima kuwa ya ce yana sonta da Ƙanwa dan shi ma shi ɗaya ne a wajan iyayensa, shaƙuwa mai karfi ne a tsakanin *NUREN* da Samima, dan haka taya zai fara gayawa Nuren cewa Samima Macijiya ce? Jikin Mahaifin Samima ne ya fara kakkarwa tamkar mai jin sanyi sai ga hawaye na zuba a idonsa, abun da Nuren bai taba gani ba kenan, ganin haka ya sake ɗaga masa hankali ya shiga jerowa Baban Samima tambaya, amma ganin ya kasa ba shi amsa yasaka shi cewa "to Baba ina zaka je sai muje tare?" da kyar mahaifin Samima ya furta cewa "Gida" sannan Nuren ya karbi key din motarsa ya bude masa ya shiga sannan ya shiga shima ya dauki hanyar unguwarsu Samima, da dan sauri yake driving din, su na zuwa suka ga ana wanke gidan su Samima da fetur ana shirin cinnawa gidan wuta, da karfi Nuren ya ce "heyyyyyyyyy!!!!!! Stoppppp!!!" juyowa kuwa suka yi gami da tsayawa cak su na kallon Nuren, dan gidan ALHAJI IBRAHIM MAI AGOGO wanda babu wanda bai san shi ba a cikin garin ADAMAWA, da sauri ya karaso yana tambayar meke faruwa, nan wani yake faɗa masa ai ga abun da yake faruwa, Samima Macijiya ce, a ruɗe ya juya ya kalli mahaifin Samima wanda yake share hawaye da hannun rigansa abun tausayi, lallashin mutanen Nuren ya yi ya ce suyi hakuri su tafi za a san abunyi yanzu suje ayiwa wannan mamaci wanka a kaisa makwancinsa, da kyar dai suka hakura suka bar kofar gidan yayinda wasu sukayi alkawarin idonsu idon Samima sunanta gawa itama, bayan sun watse Nuren ya kama hannun Baban Samima suka kwankwasa gidan amma Umma ta ƙi budewa sai da baban Samima ya kirata a waya yace ta bude su ne kafin tazo ta bude, bayan sun shiga suka zauna a parlour Nuren ke tambaya ya ce "Umma, Baba, inaso ku fadamin zahirin abun da yake faruwa karku boyemin komai, shekarata shidda da dawowa,kuma tun da na dawo muke tare da ku , ni har ga Allah a matsayin iyayena n daukeki, idan kuma kun daukeni matsayin Ɗa kun ga kenan Samima Ƙanwata ce, sabida haka bai kamata a boyemin komai ba, a faɗa min meya samu ƙanwata meke faruwa da ita,miye gaskiyar magana akan macijiyar da aka kirata da shi?"
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
(WAIWAYE ADON TAFIYA)
WACECE SAMIMA?
WACCE A HALIN YANZU TA KOMA RABI MUTUM RABI MACIJIYA? YA DANGANTAKA YAKE TSAKANIN UMMA ZULAIHA DA GWAGGO ASABE?
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Samima, shine asalin sunanta, Mahaifinta mai suna Malam Nasiru wanda a halin yanzu yan unguwa suke kiransa da suna Alhaji Nasiru Baba Iyali, kasancewar yaje ƙasa mai tsarki, su asalin fulanin Adamawa ne, Mahaifiyar Samima kyakkyawar bafulatanar usuli ce, haka zalika mahaifin Samima Malam Nasiru, Malam Nasiru su biyu ne a wajan iyayensu shi da Yayansa mai suna Malam Basiru wanda shine Miji ga *ASABE.*
Tun da Asabe suka yi aure da Malam Basiru bata taba barin wata ba, hakan kuwa ba ƙaramin ta da mata hankali ya yi ba, kasancewar Malam Basiru yana matuƙar kaunar yara, duk da ko a fuska bai taba tunawa Asabe ba, tun da ba asan matsalar daga wajansa bane ko wajanta,amma abun da ya sani shine komai na Allah ne, lokacin da Nasiru ya jijjib'o maganar aurensa da Zulaiha, san da Asabe ta ga Zulaiha a take taji wani tsanarta ya kamata, kasancewar kyawun da Zulaiha ke da shi, babu yadda Asabe ba tayi ba wajan ganin auren Nasiru da Zulaiha bai yi ba amma ina abun ya ci tura, sabida duk abun da Ubangiji ya tsara babu mahalukin da ya isa ya wargaza, har Allah yasa Malam Nasiru ya auri Zulaiha, shekarar farko da ta zagayo Allah ya azurta Zulaiha da samun ciki, Asabe ɗaki ta shiga tayi ihu tayi ihu dan baƙin ciki, taya ma za ace ita shekararta nawa da aure bata samu ciki ba, sai Zulaiha wacce aka auro yanzu-yanzu ace tana da ciki, inaa sam ha zai yu ba, ba zata lamunta ba, ta bangaren Zulaiha kuwa sosai take ba wa Asabe girmanta kasancewar su na matar Wa da Ƙani, ko da sau ɗaya ne Asabe bata taba jin son Zulaiha ba, ga shi tun da Nasiru ya auri Zulaiha Allah NA ƙara buda masa hanyar samu yake yi, har ta kasance shi ke daukar nauyin gidansu baki daya, kasancewar a lokacin gida daya suke zaune, kullum Asabe da kalar habaicin da zata din ga yiwa Zulaiha, ita kuwa bai taba damunta ba, ta na yi mata biyayya dai-dai gwargwadon iyawarta, sau biyu tana samun ciki yana b'arewa wanda an rasa sanin ummul'aba'isin faruwar hakan, a na ukun ne ya zauna, duk da Zulaiha tasha matuƙar wahala sosai akan ciki kamar ba zata rayuwa ba, da haka har Allah ya sauketa lafiya ta samu kyakkyawar Ƴarta wacce ta fita kyau da komai wanda duk unguwarsu babu wanda ya kaita kyau, ranar da Asabe ta ga jaririyar da Zulaiha ta haifa ta ci alwashi akan yarinyar, haka ranar suna yarinya aka saka mata suna *SAMIMA* murna a wajan Malam Basiru abun har ba a cewa komai sai ka rantse ma shi aka yiwa haihuwa sabida son yara da yake yi Allah bai ba shi ba, amma ga shi ya ba wa kaninsa, Samima na da shekara daya Zulaiha ta kan dauketa ta miƙawa Asabe ita, wanda a halin yanzu bata nunawa Samiman kiyayya a idon mutane sai bayan sun keb'e, shekaran Samima daya da wata biyu itama Asabe Allah ya bata ciki, tayi murna da hakan, inda take ta addua Allah ya bata Ɗa namiji, amma lokacin da ta tashi haihuwa sai Allah ya bata mace, wacce ko kafar Samima bata kamo a kyau ba, kuma Malam Basiru baya ɗaukin ƴar tamƙar yadda yake yiwa yar ƙaninsa Samima, hakan ne ya kara tunzura Asabe, ta kara tsanar Samima, ranar suna aka sakawa yarinya suna *SHA'AWANATU*,a haka rayuwa take tafiya Samima da Sha'awa su na tasowa a tare kasancewar Sha'awa tana da girman jiki,wani lokaci ma idan sun fita wasa sai a din ga cewa Sha'awa itace gaba da Samima, Mahaifin Samima shi ne yake biyawa yaransu kudin makaranta dan kuwa shima yana yiwa Yayansa kara, baya nunawa Samima so kamar yadda yake nunawa Sha'awa, rayuwa tana tafiya yau fari gobe tsumma, lokacin da Samima ta shiga shekara 13 a lokacin kyawunta sai kara fitowa yake yi, yarinya ga ilmi,natsuwa sanin ya kamata, mai hankalin manya, ga kokari duk inda tasha gaban Sha'awa ke nan, sabida ita kuwa ko a makarantar ma bata gane komai sai bakar rashin kunyar tsiya, sabida da haka mahaifiyarta ta raineta, ga shi ta cusa mata tsanar Samima a ranta, da haka mahaifin Samina ya gina gida dan madaidaici mai kyau ya bar wa Yayansa wanda suke ciki a da, ga shi yana zuwa aiki, shi kuwa Malam Basiru shagon sai da maganin hausa yake da shi, ba komai bane ke damun Asabe illa baƙin ciki da hassada.
Lokacin da Nasiru ya tafi aikin hajji, Asabe yawo tsirara ne kawai bata yi ba, dan kuwa tayi rabin hauka dan taji bakin ciki, har taje ta samu mijinta Malam Basiru akan cewa ƙaninsa ya raina masa hankali ga shi yana aiki uwa uba ya ketara hazo yabar shi a cikin a kulki amma da shike shi shanyeyyen zuciya ne garesa ba zai gane cewa Nasiru baya kaunarsa ba, maganganu dai na batanci marasa dadi, inda a take Malam Basiru ya taro matarsa inda ya rufe ido ya hau ta da faɗa, tun da ga lokacin Asabe ta lashi takwabin sai ta raba tsakanin Nasiru da Basiru, tabbas ta yi nasarar yin hakan, dan sai bayan ta mai da Malam Basiru *MIJIN KAN TACE* kafin ta bazama shiga Malamai inda ta samo wani mashahurin boka a can ƙusa da ƙasar enugu wanda su ne suka mai da Samima Macijiya, tun tana da shekara sha huɗu hakan kuwa ta faru ne ta sanadin *NUREN* sabida tun da Nuren ya dawo Sha'awa ta ɗaura idonta a kan shi ta ji ta kamu da mugun kaunarsa wanda har sai da tayiwa Mamanta barazana da rayuwarta muddun ta rasa Nuren, wanda Asabe gani take yi kamar akwai soyayya tsakanin Nuren da Samima, wanda shine dalilin da yasa Asabe ta mai da Samima Macijiya sabida son zuciya, da kaunar da take yiwa ƴarta Sha'awa, wanda a halin yanzu Samima tana da shekara 19 da haihuwa shekararta biyar a matsayin macijiya, wanda take iya rikiɗewa lokaci guda, ga shi Samima yarinya ce wacce tun tana yar shekara biyar take son kwalliya tana son ta zama tailor na fashion dress wanda a halin yanzu Nuren ya buɗe mata babban shop dinta, wanda hakan ba karamin sake tunzura Asabe ya yi ba.
WANNAN SHINE A TAKAICEN TARIHIN SAMIMA.
Wanda a yanzu kimamin watanni uku kenan da iyayen Samima suka san da cewa ta zama macijiya inda suka bazama nemawa ƴarsu magani dan ta dawo mutum, Baba Malam , malami ne mai baiwa inda a karshe aka kai masa Samima da fari ya ƙi fada musu gaskiya sai da gabaya da ya ga tabbas yarinyar zata iya hallaka kafin ya gaya musu, kullum kuma zai ce musu yar gida ce ta yiwa Samima asiri in da a karshe ya fadawa Maman Samima Asabe ce ta yi mata.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Ci gaban labari.
Cike da sanyin jiki Umma ta bawa Nuren labari da cewa *SAMIMA MACIJIYA CE* an mai da ta macijiya, ga shi yanzu babu wani shiri ko jituwa tsakanin Baban Samima da Yayansa Malam Basiru, bayan Umma ta gama basu labari cikin tashin hankali Nuren ya miƙe tsaye ya kalli su Umma ya ce " Umma nayi alkawari ko da zan rasa raina sai na nemowa Samima da magani ta koma mutum In sha Allah" yana gama faɗi ya fice cikin rikicewa.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
WASA FARIN GIRKI , KUUU BIYONI MASOYA, 🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
KAR DAI KU MANTA GAJERAR LABARI NE.
UMMU AHLAN TA KU CE👍🏻
[02/09 à 08:45] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA UKU. ✍🏻
Follow me on my wattpad. 👇🏻
I just published "5&6" of my story "SAMIMA (MACIJIYA CE)🐍🐉". https://my.w.tt/sBBYEYDsa9
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_SADAUKARWA GA DUK MAI KARANTA LITTAFIN SAMIMA MACIJIYA CE, ESPECIALLY MASU YI MIN SHARHI, ALLAH YA BAR KAUNA, KUNA DA YAWA WALLAHI, BAZAN IYA AMBATAR SUNAYENKU BA, AMMA NA SADAUKAR DA PAGE DIN NAN GAREKU NGD SOSAI_*
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
A hankali ta turo kofar gidan nasu gabanta na faduwa, har cikin parlour ta furta "Asaalamu alaykum" a sanyaye, Umma da Baba da suke zaune su na jimami tun fitar Nuren babu wanda ya motsa a cikinsu ko yace uffan, Samima ganin iyayenta su na zaune sunyi jingum-jingum ne ya saka gabanta faduwa da karfi, dan kuwa ta tuno da cewa Mamanta tace mata karta fita, kamar kuwa Umma tasan tunanin da Samima ke yi, tana tashi ta dauketa da mari, sai da Samima ta kifu a kasa, da sauri Babanta ya miƙe yana cewa "haba Zulaiha!! Miye haka, a halin yanzu Samima rarrashi take bukata, to ma duk ba wannan ba miye abun duka da zaki ɗaga hannu ki mareta?" cikin kuka Umma ta ɗago Samima tana magana tana jijjigata "Samima, me na ce miki iyee? Bana ce miki karki kuskure ki fita a gidan nan ba? Shi ne kika kama hanya kika sa kafa kika fita ko? Da yanzu yan unguwa sun ganki da sai dai a dawo min da gawarki!!" Umma ta faɗi tana sake fashewa da kuka, Samima ganin irin kukan da mahaifiyarta ke yi ba karamim ɗaga mata hankali ya yi ba, saurin rungume Ummanta ta yi itama tana kuka ta ce "dan Allah Ummana kiyi hakuri, wallahi bansan lokacin da na fita ba, ban san ya aka yi na fita ba, Umma me nayiwa yan unguwa da zasu kasheni? Dan Allah ni dai Umma ki daina min kuka, dan malaman'mu sun ce idan har iyaye su na yiwa ƴaƴansu kuka rayuwar wannan ƴaƴa bata albarka, kuma tab'ewa suke yi, dan Allah Ummana kiyi hakuri" Samima ta rungume mahaifiyarta gam tana kuka Mamanta na kuka, Babanta shima na share hawaye gami da yin tasbihi ga Allah subhnahu wata'ala da irin kalar jarabtar da ya musu, dan kuwa shi ne cikar mumini na gari idan alkhairi ya sameka ka godewa Allah idan ma akasin hakan ne duk ka godewa Allah, ta haka ne Allah yake gwada imanin bayinsa, sun jima a haka su na kuka, kafin daga bisani Baba ya din ga rarrashinsu har suka yi shuru.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Fitan Nuren daga gidansu Samima gidansu ya wuce kai tsaye, yana shiga ya wuce wajan mahaifiyarsa a daki ya sameta zaune a bakin gado tana waya, kwanciya ya yi akan kafafunta, ta kallesa cike da kulawa duk da bata katse wayar da take yi ba, ta hau shafa kwantacciyar sumar kansa, sai da ta gama wayarta tukunna ta dube shi a tsanake ta ce "Nuren, me ke faruwa? Ya na ga kamar kana cikin damuwa, ko dai baka da lafiya ne?" dagowa ya yi ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Momy, yau naji abun da ya dameni, kai duniya ba gaskiya, mutane basu jin tsoron Allah, kwata-kwata wasu mutane basu tuna cewa wannan duniyar fa ba zama muka zo yi ba" sai ga hawaye na zuba a idon Nuren dan kuwa yana bala'in tausayawa Samima, cikin tashin Hankali Momy ta ce "ban fahimce ka ba, Nuren, meke faruwa ne kam ka fada min mana"
"Momy, Samima ce"
"To me ya faru da Samiman?"
"Momy, *SAMIMA MACIJIYA CE*, Momy an mai da min da Ƙanwata Macijiya" a firgice Momy ta miƙe ta ce "iyeeeeeeee!!?? Ban gane Samima Macijiya ba ce?? Nuren ban sanka da shaye-shaye ba, Allah yasa dai ba shi ka fara ba?"
"Tabbas,Momy Samima Macijiya ce, duk da nima sai yanzu nasan da hakan, iyayenta ma sai yanzu suka sani, yanzu haka daga gidansu nake, shi ne ake bani labari" nan Nuren ya ba wa mahaifiyarsa labarin da Umma ta ba shi akan Samima, Salati Momy tasa tana tafa hannu cike da al'ajabi ta ce "wannan wani irin tashin hankali ne haka? Labari sai kace a film ko a littafi? amma dai Allah ya wadaren masu son zuciya, yanzu ina Samiman?"
"Nima Momy har na bar gidan ban gan ta ba"
"To yanzu miye abun yi?" cewar Momy tana kallon Nuren, ya ce
"Momy, nayi alƙawari zan taimaka mata, na zo neman izininki ne, ki bani goyon baya, dan Allah karki hanani" cikin sanyin jiki Momy ta kamo hannun ɗanta ta ce "duk wanda zai taimakawa Samima a halin yanzu ba karamin jahadi zai yi ba, taya ma zan hana Ɗana aikata aikin lada? Ina goyon bayanka Nuren, kuma zan samu Abbanka da maganar zamu taimaka musu da yardan Allah indai su na bukatar hakan daga garemu" cikin murna da farin ciki Nuren ya rungume mahaifiyarsa yana mata godiya sannan ya tashi ya fice, part dinsa ya shiga ya hau jeka ka dawo yana tunanin ta ina zai fara, dole ne ya je ya samu Asabe tunda ance dole sai ita ce zata iya karya sihirin da ta yi, in ba haka ba kuwa tabbas wata rana za a hallaka Samima, rintse ido ya yi yana hango kyakkyawar fuskarta wacce bata rabuwa da fara'a, abu na farko da zai fara dole ne ya rin ga janyota jikinsa fiye da Ɗa dan ta rage fita da mu'amala da mutane, har su shiga hidimarta ita kuma ta kashesu, da wannan tunanin ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi, duk da lokacin sanyi ne amma wani masifaffen zafi yake ji, bayan ya fito daga wanka ya gama shirinsa ne ya kira Abokinsa Suhail yana ɗagawa ya ce "hlo Suhail kana ina ?"
"Gani a shagon Samima, kasan muna ta faman shiri na kayayyakin da muka ɗinka din nan, sabida da shi ne za ayi show, ka ga yadda kayan suka yi kyau kuwa? Barin ma wanda Samima ta dinka kaii gaskiya yarinyar Allah ya bata basira da fasaha, shi yasa ko a wajan shiga gasan aka bata ta uku, nasan idan aka fita show dole ne ma a bamu na daya, dan kasan yau saura wata daya ne show din kuma....."
"Kaiiiiiii!!! Dakata Dan Allah parrot! Ni fa kawai tambayarka nayi kana ina, amma ka hau zuba min zance ai duk na san da haka ta gaya min, ni yanzu ba b'ata lokaci nake so ba gani nan zuwa shagon zamu yi magana dan akwai babbar matsala"
"Ok to ba damuwa sai ka zo Nuren" Suhail ya katse wayar yana tunanin me ya sa mu Nuren dan ya ji muryarsa yana cikin damuwa, bai fi mintuna ashirin ba sai ga Nuren a babbar shop din Samima mai suna *SAMIMA NASIRU FASHION DRESS DESIGNER* yana zuwa aka bude masa kofa ana miƙa masa gaisuwa kasancewar sun san shi sosai ma'aikatan wajan, sama-sama ya amsa gaisuwar tasu dan ba a cikin natsuwar shi yake ba, inda yake tunanin Suhail na zaune wajan ya tunkara direct, yana zuwa ya ja shi gefe, nan ya zayyane masa komai bai boyewa Suhail komai ba, a tsorace Suhail ke bin Nuren da kallo yayinda ya ji wani fitsari ta kamasa sabida tsananin tsoro, ga zufar da ya fara tsantsafo masa ta ko ina, "Innalillahi!!! Nuren Samiman? Samiman ce Maci...." Nuren bai barsa ya karasa ba ya toshe masa baki dan kar wani ya ji, yaja hannunsa suka fice, mota suka shiga Suhail ya kasa katabus ban da rawa da jikinsa ke yi, NUREN ya ce "haba Suhail, miye haka kake yi ne kam? be a man mana, na fa gaya maka ne dan mu samawa Samima magani ta warke kamar sauran mutane " Suhail ya ce "to kai ka taba ganinta a macijiyar ne?" sai da Nuren ya numfasa kafin ya ce" a'a, ko iyayenta ma basu taba ganinta a macijiyar ba"
"To amma kai Nuren anya ba karya......" da sauri Nuren ya dakatar da Suhail da cewa "tabbas, da ace ba daga bakin iyayenta maganar nan ya fito ba, sai nayi ma wanda ya fada shegen duka kafin na karyata shi, amma iyayenta ne suka fadamin da bakinsu, kuma naje na samu mutane a kofar gidansu, in takaice maka zance da shirin ƙonawa Baba gida zasu yi kuma da Umma a ciki"
"Hummmm!!!" Suhail ya sauke gaurowar ajiyar zuciya ya ce.
"To yanzu ta ina zamu fara?, me kake so nayi?"
"Yanzu zamu bazama neman malamai ne dan a karya sihirin"
"Amma kana ganin hakan zai yu kuwa? Tun da Umman Samima tace Malam yace wanda ya mata shi zai warware"
"To mu fara zuwa gidan Gwaggo Asaben mu roƙi alfarma idan ta ƙi ba sai a haɗata da hukuma ba ko ya kace?"
"Idan muka yi haka kuma zasu sake saka Samima cikin hatsari" cewar Suhail, kifa kansa Nuren ya yi wanda ya ji yana masa barazanar tarwatsewa saboda tashin hankali, mota yaja Suhail na tambayarsa ina zasu je, bai iya ya bawa Suhail amsa ba, har suka je wani babban gida wanda yake dauke da almajirai da yawa, parking din mota Nuren ya yi suka fito tare da Suhail wajan babban Malamin Abbansa ya zo dan ya yi masa bayani halin da Samima take ciki, da sallama ya shiga babbar zauren yayinda aka yi musu Umarnin shigowa, bayan sun shigo suka gaishe da Malam cikin girmamawa, Malam yake tambayar Nuren ya mahaifinsa ya amsa masa da yana lafiya, sabida ya dauka ma ko mahaifinsan ne ya aikosa, cikin natsuwa Nuren ya fara yiwa Malam
Bayanin abun da ya kawosu, girgiza kai Malam ya yi, ya ce " gobe ku taho da ita yarinyar da iyayenta da ku gaba daya" Nuren ya amsa da "to Malam,kamar da wani lokaci zamu zo?" Malam ya ce " ku zo da rana" godiya suka yi wa Malam sannan suka fita,basu zarce ko ina ba sai gidansu Samima, da kyar Nuren ya tilasta Suhail suka shiga inda a cikin ransa yake karanto suratul jinnu, sallama suka yi a kofar parlour Umma ta amsa ta basu izinin shigowa, bayan sun shigo a daddafe Suhail ya zauna, Nuren ya ce "Umma ina Baba ya fita ne?" murmushin karfin hali Umma ta yi ta ce "mu kuwa ina mu ka ga ta zama Nuren, ai zama bai ganmu ba ya fita" gyara zama Nuren ya yi, sannan ya gayawa Umma yadda suka yi da Malamin mahaifinsa godiya Umma ta yiwa Nuren gami da sa masa albarka, ya ce.
"Haba Umma ki daina min godiya nayi alkawari kuma a shirye nake da sadaukar da rayuwata akan Samima, iyayena ma sunce idan ana bukatar gudumawarsu zasu bayar, ina Samiman? Ba dai bata dawo ba?" share hawaye Umma ta yi wanda ya zame mata jiki ta ce "mun gode fa Nuren Allah ya yi albarka, ta dawo tana kwance a dakinta" Nuren ya ce "zan iya shiga na ganta ko kuma ki kira ta Umma"
"Ah haba dai dakin kanwarka ce ai kana iya shiga" a hankali Nuren ya miƙe ya shige dakin Samima, Umma ta kalli Suhail ta ce " Suhail, baka da lafiya ne?" yaƙe Suhail ya yi, ya shiga girgizawa Umma kai alamun a'a,aransa ya ce "Umma ba za ki gane bane.
da Sallama ya shiga ya sameta kwance a nannaɗe, ganin yadda ta nannɗe ba karamin ba shi tsoro ta yi ba, a hankali ta kira sunansa cikin daddadar muryarta mai dadin sauraro, karasowa gabanta ya yi ya duka, ya ce "fatan kina lafiya?"
"Eh Yayana lafiyata kalau, kai fa?"
"Nima ina Lafiya"
"To madalla yanzu sauri nake yi zan tafi dan an kusan kiran sallar magriba ko da wani lokaci za a iya kira, gobe ku shirya zamu je wani waje kinji?" ta amsa da "to Yayana Allah ya kaimu" tashi ya yi ya fice da sauri sabida kukan da ya ji yana shirin kwace masa, ko da ya fito sallama kawai ya yiwa Umma suka wuce, sai da suka yi sallar magriba da isha'i kafin ya ajiye Suhail a gida shima ya wuce gida.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
0 comments:
Post a Comment