"Haba Nuren ka ɗaga mana, anata kiranka dare ne fa, kasan ko waye, ga shi ba Samima bamu koma gida ba, kasan dole hankalin iyayenmu ya tashi" cikin dasheshshiyar murya Nuren ya ce.
"Bakuwar lamba ne fa"
"To sai me Nuren? Ka ɗaga mana ka ji"
Ba dan Nuren ya so ba ya ɗaga wayar a masifance ya ce.
"Dalla waye!!!?" muryar Samima yaji tana sheshshekar kuka, da sauri ya ce.
"Ƙan...Ƙanwata!!? Kina inane? Samima kina jina?" da shike ta gane in da suka yi da ita,tun da ba rufe mata fuska suka yi ba, nan cikin kuka ta hau yiwa su Nuren kwatance inda take, da saurin Nuren ya karbi driving daga hannun Suhail yana bin kwatancen da Samima ke masa, gudu kawai yake shararawa har ya iso wajan, a karkace ma ya parka motar ya fito ya b'urma cikin gidan, nan ya ji ta gam a kulle, sai da ya din ga bugawa shi da Suhail su na ambatar sunan Samima, Samima wacce ta haɗa kai da guiwa tana kuka ta ji muryar Nuren da Suhail da sauri ta zo ta buɗe musu kofa, ganinta yasa Nuren cewa.
"Me kike yi anan? Me aka miki? Yana ga jikinki duk jini? Me ya faru dake?" su waye suka kawo ki nan?" tambayoyi Nuren ke jerowa Samima cikin tashin hankali, ta kasa ba shi amsa illa matsawa gefe da tayi kanta a sun kuye tana kuka, da sauri Nuren da Suhail suka danna kansu a cikin gidan, nan suka yi arba da maza biyar kwance anyi musu fata-fata, ta ko ina saran maciji ne a jikinsu, bisa alama kuma sun mutu,dan ihu Suhail ya yi yana furta.
"Innalillahii!! Astaghfirullah!!! Allahu Akbar!! Alhamdulillah!! Ma sha Allah!!! Subhnallah!!! Wa'iyazubillah!!!!" duk ya bi ya ruɗe, yana shirin fita da gudu da sauri Nuren ya kamosa yana masa magana da ya natsu amma ya kasa tsayuwa balle ya natsu, da iyakacin karfinsa Nuren ya wanke Suhail da mari inda ya tsaya cak, sannan ya fizgi hannunsa dana Samima ya fice dasu ya saka su a mota shi ma ya shiga ya tada motar, bai tsaya a ko ina ba sai gidan su Samima, yana tsaida mota ya kallesu ya ce "ku fito" Samima wacce har yanzu bata bar kuka ba ta fito, shima Suhail jiki na rawa ya fito, Nuren yasa Samima a gaba yana binta a baya, shi kuma Suhail yana bin Nuren a baya, da sallama suka shiga su Baba da Umma su na zaune kusan ɗaya da rabi na dare, da sauri Umma ta taso da niyyar rungume Samima amma sai ta ja ta tsaya cak tana bin ta da kallo sakamakon jinin da ta gani a jikinta, muryar Umma na rawa ta ce.
"Samima!!?? Samima!!!? Samima!! Wannan jinin miye a jikinki!!? Nuren, Suhail me ya faru!!?" kallonta Nuren ya yi suka haɗa ido ta durƙushe a wajan ta sake sakin kukan tashin hankali, cikin kuka ta shiga zayyano musu abun da ya faru tun tafiyar Nuren daga makarantarsu, da abun da ya haɗata da Amir, da kuma zaman jiran Nuren da ta din ga yi, har izuwa tashin da tayi da niyyar zata dawo gida, su Amir suka kundumeta, har izuwa gidan da suka kawota da niyyar keta mata haddi, ta kara da cewa.
"Wallahi ban san me ya faru ba, nasan dai kawai su na gaf da cimma burinsu a kaina, na ji azaban da nake ji idan zan koma macijiya, bayan na koma ban kara sanin komai ba, sai da na tashi na ga su Amir kwance a cikin jini, nima ina kwance a gefensu" ta ci gaba da kuka, Umma nan ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, da sauri su Nuren da Baba da Samima suka yi kan Umma su na jijjigata, Nuren ne ya cewa Samima ta kawo ruwa a yayyyafawa Umma, da sauri Samima ta tashi ta kawo ruwan aka hau yayyafawa Umma amma Umma ko motsi bata yi, ba shiri suka fita a cikin daren aka kai Umma asibiti, sai wajan uku da rabi Umma ta farfaɗo babu wanda ya rintsa, Samima sai aikin kuka take yi, tun tana kuka mai hawaye har ta koma kukan zuci, ko da Umma ta farka da kuka mai ciwo ta farka inda likita yake cewa ta yi a hankali dan jininta ya hau sosai, ko sauraron likita Umma bata yi ba, dan zata iya cewa ma bata ji me ya ce ba, su Baba, Nuren, Samima,Suhail ne suka shigo dakin da Umma ke kwance, Umma tana ganin Samima ta yi saurin juyar da kanta gefe tana kuka, ta ce.
"Dama Asabe ta kasheki ne na ga gawarki da watakila hakan zai fi min kwanciyar hankali akan abun da ta saka ki kike aikatawa Samima!!!! Wallahi gwanda ace wannan gawarki ce!!! Tun da dama dukkan mai rai mamaci ne, Samima yau ke ce sara wannan ta mutu!! gobe kace sara wannan ya mutu!!! jibi ke ce sassare wa innan sun mutu!! Samima ina kike so na saka rai na!!!" Umma na magana tana kuka cikin rauni daban tausayi, Nuren ya fara lallashinta akan ta yi shuru tunda likita ya ce jininta ya hau, Umma ta ce.
"Nuren? Ina kuwa jinina zai sauka? Gaya min taya jinina zai sauka Samima tana cikin wannan halin? Ya Allah a ko da yaushe sai na kawo maka karar baiwarka, ni dai a iya tunanina ban yi mata komai ba, Ya Allah ka isar min abun da ta yiwa ƴata" Umma ta ci gaba da kuka Samima na gefe tana tayata, har aka kira sallar asuba, su Abba Nuren Suhail suka tafi masallaci su Umma kuma suka yi sallah a daki, ko kadan Umma ta ki yarda ta kalli Samima, bayan sun idar da sallah Samima ta ce.
"Umma ina kwana?" shuru Umma ta yi ta ƙi amsawa, matsowa Samima ta yi ta kama hannunta ta ce.
"Ummana kina jin zafina ko?" sai ga hawaye, girgiza kai Umma ta yi.
"To Umma me yasa kin ƙi kallona, na gaisheki ma ba ki amsa ba" nan ma shuru Umma ta yi illa hannun Samima da ta sake damƙa cikin nata, maganar duniyar nan Samima ta yi amma Umma ta ki kulata, har su Abba suka dawo daga masallaci, sai wajan karfe tara na safe Umma ta ce a sallameta, hakan kuwa aka yi, aka bawa su Umma takardan sallama suka wuce gida, bayan sun koma gida Nuren ya umarci Samima da ta shige daki bai yarda ta fito ko da tsakar gida bane, haka ma gayawa su Umma akan cewa kar abar Samima ta fita, Baba da Umma suka yi musu godiya su na sa musu albarka, ya kalli Suhail ya ce "muje" mota suka shiga basu zarce ko ina ba sai gidan su Asabe, yau Asabe ranta fesss take jinta dan jiya ta tabbata idan ba a kashe Samima ba, to sauran gawarta ce ya rage, kuma ta tabbata Nuren zai kawo kansa ya ce yana son Ɗiyarta Sha'awanatu, tana cikin tunani ta ji sallama, ba a jira umarnin shigowa ba suka danno kai, Asabe na ganin Nuren ta saki Shu'umin Murmushi a ranta ta ce.
"Wayyo dadi, rago daga sama gasheshshe" wani kallo Nuren ke aikawa Asabe na wulakanci kafin ya ce.
"Gwaggo Asabe!!!?"
"Na'am sirkina Nuren" Asabe ta amsa cikin izgili.
"Gwaggo Asabe me Samima ta yi miki da har kika zabi mai da ita macijiya? Dan Allah na roƙeki da lallama ki karya asirin da kika yiwa Samima, idan ba haka ba ni din nan Nuren zai nemawa Samima magani kuma zata warke da yardan Allah, ko da kuwa zan rasa raina!!" shewa Asabe ta yi tana tafa hannuwanta harda guɗa ta ce.
"Ashe dai da gaske ne? Soyayya ta yi nisa, dama ka daina wahalar da kanka akan wannan yarinyar da ta yi kyawun maciji, au namanta ashe ma fa macijiyar ce ko?" rintse ido Nuren ya yi dan ya ji zafin maganar Asabe.
"Dama ka rabu da macijiya ka so mutum, ga yarinyata shalele Sha'awanatu, ka dai na wahalar da kanka akan wacce bata da garantin rayuwa" Suhail ya ce.
"Amma dai ke kam anyi tsohuwar banza, jahila, ke yanzu kina da garantin rayuwar ne?" Asabe ta ce.
"Kai kuma fa? Daga ina? Bangane ka ba? To idan Asabe ta yi kashi, bata kasa da mutum ba ya kwashe ya kan fuskanci hukunci mai tsanani!!" ta faɗa tana nunawa Suhail yatsa, Nuren ya ce.
"Karya ya yi, ina dai ba za ki karya asirin da kika yiwa Samima ba?"
Asabe ta ce.
"Wacece kuma me wannan sunan?" ta faɗa tana murmushin sheɗanci, Nuren ya yi kwafa ya nuna mata yatsa ya fice kawai, Suhail ya bi bayansa da sauri, ya zo fito Sha'awa ta zo shigowa tana ganinsa ta saki ihu da tsallen murna, tsawa Nuren ya daka mata ya ce.
"Ballagaza kawai!!! Watsatstsiya!!!" yaja dogon tsaki ya yi gaba, Suhail ya kalli Sha'awa da sauri ya bi Nuren mota suka shiga ya bulawa Sha'awa ƙura ya wuce yabarta tsaye tana huci, da sauri ta shige gida tana kunkuni.
"Wai ni Inna me yasa ba za a kashe Samima kowa ma ya huta ba?" dariya Asabe ta yi da murya babu dadin ji ta ce.
"Kwantar da hankalinki yarinyeta, mun kusan fara shiga manya-manyan motoci ana jan mu a baya, amma fa sai kin zama matar Nuren"
"To Inna taya hakan zata kasance bayan Samima tana raye?"
"Ah me kike ci na baka na zuba? Ai Samima abun da zan mata sai ta gwammaci mutuwa akan halin da take ciki"
"Hali kuma Inna? Wani hali take ciki?"
Murmushi Asabe ta yi ta ce.
"Bana so kina fiye tambaya akan abun da ba shi da amfani a gareki, ke dai ba dai Nuren kike so ba, ko ba haka bane?" cikin zumuɗi Sha'awa ta ce.
"Haka ne Inna"
"To ki mai da hankalinki akan shi, za ki same shi kwanan nan ba kwanan can ba"
Sha'awa ta miƙe da murna ta sake ficewa, dan Sha'awa bata zaman minti biyar a gida zata fice,kuma Asabe babu ruwanta da tambayar Sha'awa ina take zuwa, Malam Basiru kuma an mai da shi fanko marar amfani dan baya iya magana akan komai sai dai ido, a mota Suhail ke cewa.
"Nuren, wannan yarinya mai kama da gwaggon birin fa? Ba dai ita bace ake tallata maka?"
Nuren ya ce.
"Ita ce" dariya Suhail ya saka har yana riƙe ciki ya ce.
"Allah na tuba, Nuren wannan ai sai dai ka siyeta ka ajiyeta a gidan zoo ana zuwa kallonta dan kama take da birirrika" Nuren ya yi ɗan guntun murmushi, ya ce.
"Gwaggo Asabe na lura har yanzu babu nadama a wajanta, dan haka sai mun miƙe tsaye in ba haka ba, abun Samima kullum ƙara gaba yake yi, inajin tsoron ranar da jami'an tsaro zasu kama Samima, ai dama gobe ne zamu tafi maidugurin nan, gwanda muje musan abun yi, ayi ta ta kare" ya fada yana kiran Baba ya shaida musu akan su shirya gobe zasu kama hanyar maiduguri, sannan ya ajiye Suhail a gida shi ma ya wuce gida, dan kansa ciwo yake masa sosai yana so yaje ya watsa ruwa ya ɗan kwanta ya yi bacci ko zai ji dai-dai.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*NA GODE MUKU DA ADDUOINKU, JIKIN YARINYATA DA SAUKI SOSAI ALHAMDULILLAH*
UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻
[02/09 à 08:47] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA BAKWAI. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Da washe gari, Nuren, Abba, Umma, Samima,Suhail, suka kama hanyar maiduguri, basu da isa ba sai magriba, Nuren ne ya kai su gidan wani abokin Abbansa, inda a nan ne aka basu masauƙi, bayan sun yi sallar isha'i ne suka nemi ganin Malam Abba, inda wani almajirinsa ya musu iso, bayan sun shiga inda yake ganawa da baki, suka zauna da sallama Malam Abba Albany ya fito daga ɗan wani karamin ɗaki, ya zauna a bisa shinfiɗarsa, musabaha suka yi da Baba, sannan suka yi dasu Nuren, bayan nan ne Umma ta gaishesa ya amsa, Samima ko kallonsa bata yi ba, Umma ta ce.
"Samima, ba ki gaishe da Malam ba" amma kamar ba da Samima ake yi ba, wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa sai faman huci take yi, dan tun shigowarsu ta ji warin wani magani wanda ya gigita mata lissafi, murmushi Malam Abba ya yi, ya kalli Samima da kyau sannan ya girgiza kai, ya ce.
"Ahh, ki rabu da ita kawai, Samima zo nan, matso" ƙin matsowa Samima ta yi Malam Abba ya ce.
"Malam Nasiru, Nuren, ku matso da ita nan" tun kafin Baba da Nuren su kama Samima ta saki wani ihu da amo marar dadin ji wanda gaba ƙi ɗaya dakin sai da ya ɗauka, Nuren ya ce.
"Baba, ka bari kawai ni zan iya matsawa da ita" Baba ya ce.
"Ka tabbata Nuren?"
"Eh Baba zan iya"
Da iyakacin karfinsa Nuren ya finciki Samima ya tura ta gaban Malam, Malam Abba ya ɗauki wani roba da ruwan magani, ya kurb'a a bakinsa na tsawon mintuna biyar sannan ya fuzarwa Samima shi a fuska, nan ta zube ƙasa ta fara ka nannaɗewa tana murƙususu, Malam Abba ya sake ɗauko wani ruwa a kwarya ya watsa mata, wani tsalle Samima ta yi wanda yasa Umma da Baba matsawa gefe da Suhail wanda tuni ya koma bakin kofa ya makale yana kakkarwa gami da karanto ayatul kursiyyu, Nuren ne kawai ya yi yunkurin riƙe Samima amma ya kasa, sakamakon tsallen da ta rin ga yi, da kyar Nuren ya zo fizgota ba tare da zato ko tsammani ba ya ji an bankaɗesa ya faɗi kasa wanwar, da sauri Malam Abba ya miƙe ya damƙo Samima wanda a halin yanzu ba ita bace, manya-manyan shaiɗanun da Asabe ta aiko mata dasu ne, Malam Abba yana damkar hannunta nan take ta fara rikiɗewa, da sauri Malam Abba ya saki Samima, bai yi ƙasa a guiwa ba, ya ƙara dauko wani ruwan magani ya ci gaba da addua yana watsa mata, nan take Samima ta koma sintimemiyar macijiya, adduoi Malam Abba ya ci gaba da yi bai tsaya ba, yana kan watsa mata ruwan magani, tun macijin na harbin iska yana so ya sare Malam Abba har ya zo baya iya wani katabus ya zube a gaban Malam Abba, Malam Abba ya ce.
"Ina so ku tashi yaron da ku ka bige yanzun nan, kafin muje ga magana na gaba" cikin wani murya mai ban tsoro macijin ya fara magana.
"Malam,ina ruwanka damu da zaka shiga rayuwarmu? Me muka tare maka, ba kai ka sakamu aiki ba, to miye damuwarka damu? Shi kuma wannan yaron ya cika zaƙewa da yawa ne, an bamu aiki a kansa amma mun kasa yi masa komai sabida Samima" numfasawa Malam Abba ya yi ya ce.
"To yanzu dai ina so ne ku tashesa, kafin muje ga magana na gaba, duk maganar da zamu yi ina so ne muyi ta ta fahimtar juna, ku tashi Nuren" a hankali wannan katon macijiya ya yi kan Nuren, Baba wanda zufa ya gama wanke masa ko wace kofa na gashin jikinsa ya yi saurin cewa.
"Malam karya cutar da Nuren, ya saka masa dafi, naga yana shirin sa masa baki!!" murmushi Malam Abba ya yi, ya ce.
"Kwantar da hankalinka Malam Nasiru, babu abun da zai masa, ba zai cutar da shi ba" nan take wannan maciji ya ɗuka da bakinsa saitin fuskar Nuren ya hura masa wani haske ya fito ta bakinsa, nan take Nuren ya farka da sauri ya ja da baya ganin katuwar maciji a kansa, har kusan sumewa ya yi,dan numfashinsa sai da ta ɗan ɗauke, Malam Abba ya ce.
"Sannu Nuren, babu inda yake maka ciwo ko?"
"Eh Malam, ina lafiya" ya faɗa yana matsa wuyarsa da ya ji ya masa tsami, Malam Abba suka fuskanci juna shi da macijin nan, Malam ya yi gyaran murya ya fara magana.
"Me yasa ku ka zabi cutar da wannan yarinya ƴar ƙarama haka? Me ta yi muku?"
"Mu bata yi mana komai ba, akasari ma mu kam aiki shugabanmu ya bamu a kanta sabida wata mata da tazo neman taimako a wajanmu,kuma bamu muka nemeta ba ai,ita ta nememu, to mu miye laifinmu?" Malam Abba ya sake numfasawa dan kuwa ya hango jar aiki wajan raba Samima da wa innan shaiɗanun, dan da wuya a gama lafiya ba tare da an rasa rai ba.
"To ina so ne tun muna gane juna daku, ku rabu da ita ta koma mutum kamar yadda aka haifeta a da ,ku daina cutar da ita,ku daina sakata tana kisan kai alhali ba ita ke yi ba ku ke yi, abun da nake so da ku ke nan, ta lallama nake so mu rabu daku, amma idan ku ka ƙi zamu yi uban watsi daku, karku manta har da shi ogan naku wanda ku ke kiransa da suna shugaba ogiduwa zan iya tarwatsa shi da mulkinsa balle ku!!" dariya wannan maciji ya sheƙe dashi ya ce.
"A'a Malam baka iyawa da Shugaba Ogiduwa, dan shi ɗin babu wanda ya isa ya je gabansa, Samima kuma ba zamu rabu da ita ba,dan mun saba da ita, ƙiris ya rage mu dauketa gaba ki daya daga duniyar mutane, mu mai data duniyar macizai, dan kuwa *SAMIMA MACIJIYA CE* ko da na fita a jikinta hakan ba zai sa ta zama mutum ba, dan mu sittin da takwas ne a jikinta, mu sitti duka macizai ne kowa da yaren da yake ji, ita ma a karan kanta wacce ta yi mata aiki sawa ta yi a maidata macijiya, mu kuma aiki muke yi a kanta, ko da mun fice daga jikin Samima ba shi zai hanata zama macijiya ba, har sai wacce ta yi sanadiyyar komawarta macijiya taje ta fasa kaskon da muka bata, ta daina haɗa siddabarun tsafin da asirin da muka bata, sannan ta je ta tone maganin da Shugaba Ogiduwa ya bata ta binne da gashin Samima da matacciyar katuwar macijin tsafin da muka bata,kuma mun bata sharaɗi, wanda idan wannan aiki ya kare zata haɗu da gamonta ta ce mana ta amince, dan haka ko da mun fita a jikin Samima ita karan kanta Samiman macijiya ce, tunda ba a haƙo asirin da aka binne da gashin kanta ba,balle ma ba zamu fita ba, tun da Shugaba Ogiduwa ya bamu umarnin zama a jikinta ne" nan aka hau drama babu yadda Malam Abba bai yi ba akan su fita amma firrr sun ƙi fita, ga dare ya tsaƙa sosai, Baba da Umma sun ga tashin hankali wanda ba a saka masa rana, Suhail kuwa tuni numfashinsa ta daina aiki tun sadda Samima ta koma macijiya ya suma a tsaye, dan shi tun da aka haifesa bai taba ji ba ko a kanun labarai ba, balle ya gani, sai ga shi yau ya gani da idonsa, babu wanda yasan halin da Suhail yake ciki sai Malam Abba wanda da ya lura da hakan ya aike Nuren waje da ya kira masa almajiransa guda biyu, ko da suka zo ya basu umarni su dauki Suhail su tafi da shi, su tabbatar kuma sun ba shi rubutu ya sha, dan ya dawo hayyacinsa, suka amsawa malamin nasu cikin girmamawa kafin suka ciccib'i Suhail, ruwan magani mai zafin gaske Malam Abba yake watsawa macizan dake jikin Samima, wani ɗumi mai fitar da zafi gami da turiri ne yake tashi a ɗaki, daga karshe ma Malam Abba ya cewa su Baba da Umma su fita, aka bar shi daga shi sai Nuren, Malam ya yi iya yinsa inda a karshe ya fara tari, da kyar ya samu ya ƙona ɗaya ya kori biyu, macijin da ya yi magana a jikin Samima da ya ji azaba ya cewa Malam Abba.
"Zan je na dawo, zan je na sanarwa Shugaba Ogiduwa halin da ake ciki, amma karka sakawa ranka cewa mun rabu da Samima kenan dan zamu dawo" da haka ya yi wani juyi na maciji sannan ya zube ƙasa, kamar da minti ashirin da biyar Samima ta fara komawa mutum, har ta zama mutum, ba zato ba tsammani sai ga hawaye na bin fuskar Malam Abba wanda yasa Nuren shiga Babban damuwa, a kiɗime Nuren ke tambayar Malam Abba akan me ya saka shi kuka, kallonsa Malam Abba ya yi ya ce.
"Muje muyi sallar asuba dan lokaci ma har ya gota"
"To Malam, Samiman fa, a bar ta a nan?"
"Eh ka bar ta, babu abun da zai sameta"
Nuren ya gya ɗa kai, Malam ya yi gaba shi kuma ya bisa a baya yana waigen Samima cike da tausayawa, ko da suka fita aka raka Umma cikin gidan wajan Matan Malam, mahaifin Samima da Nuren suka yi alwala suka wuce Masallaci a tare da Malam, har aka yi sallah aka idar Nuren bai ga Suhail ba, tambayar wa inda suka fita da shi da dare ya yi, suka ba shi amsa da yana can a kwance ya kasa tashi yace sallar ma a daki zai yi, tsaki Nuren ya yi mai cike da haushi, sai karfe bakwai da rabi kafin suka koma ɗakin Malam, su na shiga suka samu Samima zaune sai aikin zare ido take yi da sauri Nuren ya karaso ya ɗuka a gabanta ya ce.
"Ƙanwata!? Kin ganeni!?" ta gya ɗa masa kai ba tare da tayi masa magana ba, Malam Abba ya ce.
"Samima matso nan" a hankali ta matsa gaban Malam Abba, ya ce.
"Kina jin wani abu a jikinki?" nan ma ji ta yi ta kasa magana, dan kamar an rike mata baki haka ta ji, Nuren ya ce.
"Innalillahi!! Malam ba dai sun mai da min da Ƙanwa kurma bane?"
"A'a Nuren, ba su mai da ta kurma ba, amma a cikinsu akwai kurame mutum uku, akwai baibaye mutum uku, akwai gurgu mutum ɗaya,akwai kuma kuturu mutum ɗaya, shaiɗanu sittin kuma dukkansu manyan shaiɗanun macizai ne, yanzu haka ma ba ita bace, kurman ne a jikinta shine ya hau,amma su wannan ba wani gagarumar matsala ba ce, sittin din nan su ne wasu ƙaramin yaƙin da zamu yi, yanzu ga wannan ruwan maganin ka bata da bismillah ta sha" Nuren yasa hannu biyu ya karba ya tallabo Samima ya bata ta ƙi karba, sai da ya matse mata baki ya ɗura mata kafin tasha, nan ta hau jera masa attishawa guɗa uku, kafin ta sake sulalewa a jikinsa, zafafan hawaye ne masu matuƙar tururin gaske Nuren ya hau yi, dan ƙaramin tausayi Samima ta ba shi ba, tun jiya take shan wahala, Allah ne kadai yasan abun da take ji, amma dai Allah ya isanta wa Asabe wallahi, yake faɗi a cikin ransa, yan mintina da basu gaza sha uku ba, a hankali ta fara buɗe idanunta wanda suka mata nauyi sosai ta ɗora su a fuskarsa, muryarta wanda da ka ji za ka san cewa ta wahala ta furta.
"YAYANA?" Nuren kasa magana ya yi illa gya ɗa mata kai kawai da yake yi, Malam Abba ya ce.
"Samima?" a hankali ta juyo ta ɗukar da kanta kasa ta amsa a sanyaye cikin girmamawa.
"Na'am Malam"
"Kina jin wani abu a jikinki"
"Malam, jikina ciwo yake min sosai, ko wace gaba ta jikina kamar an canzo min ba nawa bane"
Girgiza kai Malam Abba ya yi, ya ce.
"za ki iya tafiya?"
"A'a Malam" Malam Abba ya ɗaga waya ya kira ma'aikatan Matansa, suka zo ya basu umarnin su taimakawa Samima su kai ta cikin gida wajan Matansa da mahaifiyarta, suka amsa masa da to sannan suka kama Samima suka yi da ita gida, ko da suka shiga Umma ta rungume ƴarta suka sha kukansu, Matan Malam Abba su uku mata nagari wanda basu ruwansu, nan su ma suka din ga tayasu kukan, ruwan mai zafi aka hadawa Samima sai ka ce wacce za ayiwa wankan jego, Malam Abba ya aiko da garin magani yace ayi mata wankan da shi, Umma ce da kanta ta yiwa ɗiyarta wanka da ruwa mai zafi sosai ta gasa mata jiki, har ta ɗan ji dama-dama, abinci mai rai da lafiya aka shirya musu, amma na Samima daban kasancewar an saka mata magani a ciki, Malam Abba tare dasu Baba suka yi karin kumallo, inda Nuren sai aikawa Suhail harara yake yi, Suhail kuwa ya yi kamar bai san Nuren na yi ba, bayan sun gama karyawa ne Malam Abba ya ce, ya yi magana da Malam Habibu zasu taho yau shida Baba Malam, da wasu hazikan almajiransa wanda zasu yiwa Samima addua, fatan samun narasa suka yiwa juna, Malam Habibu su ma basu samu damar shigowa maiduguri ba, sai dare, a daren suka hau aiki akan Samima inda suka ci bakar wuya,ita kuma tasha baƙar azaba, da kyar da suɗin goshi aka samu ashirin suka bar gangar jikinta,kuma a hakan duka magana ɗaya suke maimaitawa akan cewa ko da sun fita jikin Samima, ba shi zai sa ta zama mutum ba har sai an tone sihirin da aka binne, inda Baba Malam ya ce a kamo Asabe a kawota maidugurin idan ta ji azaba dole ne ma ta tona sihirin, Malam Abba ya girgiza kai ya ce.
"Wannan yasha bambam da sauran sirihin da ake yiwa mutane, karku manta ɗayan biyun ne, wajan ganin kamo Asabe a tilasta mata haƙo wannan sihiri idan ba muyi a hankali ba zata ita kashe Samima" mu bi komai a sannu mu dage da addua, ai Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Ihu Asabe ke yi a daki sakamakon marin da ake dauketa dasu, ga amo na tashi a cikin dakin, gargaɗi ake yi mata akan cewa karta sake ta mance alkawarin da ta dauko, idan kuma wannan sihirin ya karye kar ta manta da abun da zai sameta, sannan sun gaya mata kuma ta amince hako wannan sihirin tamkar ta tono ramin kabarinta ne da kanta mai macizai, tace ta amince, marin da suka din ga dauketa dasu kuma na azaban da aka gana musu ne suka rama, dan haka ta yi a hankali, dan Malamai sun hadu akan Samima su na yi mata adduoi da magani, sannan yaron nan Nuren a shirye yake dan ya bada rayuwarsa wajan ganin Samima ta samu lafiya, dan haka tasan abunyi dan ko da wani lokaci komai zai iya ce'be mata, da haka suka tafi suka bar Asabe da fuska a kumbure baki ya koma gefe dan kuwa ta maru, mari ba a hannun aljanu ya mutum zai koma? Nan Asabe ta kudirtawa ranta ko sama da ƙasa zai haɗe ba zata taba tono sihirin nan ba,kuma Nuren sai ya auri shalelenta Sha'awanatu, kuma abun da ya mata akan abokinsa zata rama, dan sai ta kashe *SUHAIL* shi ba zata yi kashesa ba, tin da Sha'awa tana son shi, amma sai ta dauki fansar canza mata kamannin da yasa aka yi, duk a zuciyarta Asabe ke shan wannan alwashi, ta miƙe da kyar idanunta basu gani sosai, ta ja ruwa ta haɗa ruwan zafi ta yi bandaki.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
_KUYI HAKURI JINA SHURU KWANA BIYU, LAMARIN BA A CEWA KOMAI SAI ADDUA ALLAH YASA MU DA CE._
KARKU MANTA LITTAFIN SAMIMA GAJERAR LABARI NE WANDA YA ZO MUKU DA SABON SALO, NI DAI BA ZAN FASA GODIYA DA GAISUWA GA MASOYANA BA, NA GODE.
*UMMU AHLAN TA KU CE*👍🏻
[02/09 à 08:47] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA TAKWAS. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Yau kwanan Samima biyu bata san a wace duniya take ba,sakamakon maganin da ake mata na fidda mata shaiɗanu, su Malam Abba Albany sunyi matuƙar kokari dan kuwa a kwana biyu sun fatattaki shaiɗanu arba'in da takwas a jikin Samima inda ya rage saura shaiɗanu ashirin, sunyi-sunyi su sake fidda wasu amma abun ya gagara inda Baba Malam ya zo zai mata magani ya duba taurarinta ya ga haɗe suke da na *NURAIN* dan haka ya sanar dasu Malam Abba da Malam Habibu, akan cewa su ne mi Nuren ayi masa magana, indai ana so su kara samun nasara, tunda taurarin Samima haɗe yake da na Nuren din, ke nan zanen kaddararsu ɗaya ne, kuma Baba Malam ya yi bincike sosai idan har Nuren ya auri Samima wani duhu zai bayyana ga Asabe, hakan zai sa ta samu tawaya a wajan wani sihirinta, dan haka Malam Abba da Malam Habibu suka ce zasu ne mi Nuren da wannan maganar tun da ya ce zai iya bada rayuwarsa akan Samima ta samu lafiya.
Malam Abba da Malam Habibu ne suka kira Nuren, nan Malam Abba ke magana kamar haka.
"Nuren, a gaskiya zai fi kyau ace ka auri Samima, sabida wani magani da zamu yi mata, kuma mun ga zanen kaddararku daya ne da Samima, amma kai ya kake gani?" shuru Nuren ya yi yana nazari kafin ya ce.
"Malam, bazan ƙi Samima ba, kuma a shirye nake da na auri Samima, amma ina so na gayawa iyayena, dan su na da hakki a kaina a matsayina na ɗansu, duk da bana shakka a kansu zasu amince" Malam Habibu ya ce.
"Tabbas ni shaida ne akan iyayenka, Alhaji Ibrahim da Hajiya Amina mutanen kirki ne sosai, ka ne me su kuyi magana idan ya so sai mu ci gaba, In sha Allah nan da kwana biyu abubuwa zasu ɗan iya dai-daita da yardan Allah" Nuren ya jinjina kai ya fice, ko da ya fita Suhail ya fara gaya ma wa, inda Suhail ya ce.
"Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi" dan kwana biyun nan Suhail baya jin dadi,kwata-kwata ya kasa gane kan shi, kallonsa da kyau Nuren ya yi, ya ce.
"Suhail? me yake damun ka ne kwana biyu duk ka canza, ko sabida ka ga Samima a macijiya ne?" girgiza kai Suhail ya yi ya ce.
"Nima ban san meke damuna ba, haka kawai wani lokaci zan din ga jin kaina na min ciwo sosai ga faɗuwar gaba"
"To me ya sa hakan?" cewar Nuren, maƙe kafaɗa Suhail ya yi alamun bai sani ba, kyalesa Nuren ya yi, dan ya danganta hakan da tsoro ne irin na Suhail, waje ya fita ya ba wa Suhail waje ganin baya son magana, Nuren na fita kuwa Suhail ya kwanta yana dafe kansa tare da karanto kalmar "Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!" sakamakon sarawar da kansa ke masa, ko da Nuren ya kira iyayensa ya shaida musu, Abba ya fahimcesa inda ya nuna masa amincewarsa ya musu fatan alkhairi tare da yiwa Samima adduar Allah ya bata lafiya,amma nan Momy ta tubure ta ce sam bata ji ba, bata gani ba, ace ɗanta ɗaya tilo aurensa na fari ya fara da macijiya, ba shagali biki ba komai, ina sam ba zata amince ba, bata lamunta ba, Abba babu yadda bai yi da Momy ba, amma ganin da gaske take yi nan shi ma ya rufe na shi idon ya kalleta cikin b'acin rai ya fara magana.
"Amina kin ban mamaki wallahi!!! ashe son da kike yi wa Samima bai kai zuci ba?" cike da masifa Momy ta ce.
"Ya kai zuci mana, amma Ɗana ƙwalli ɗaya ne ya auri macijiya ne ban amince ba, duk son da nake mata kuwa, haka kawai ya aureta ta zo ta kashe min shi na shiga uku, nan fa a gabanka ya kiramu yana kuka akan cewa Shaiɗanun sun ce ko da sun fita a jikin Samima, Samima Macijiya ce? Ko ba haka ya ce ba? Tun da Gwaggonta ta tirje ita ba zata mai da ta mutum ba, ga shi bata rikiɗewa sai dare, sai su na kwance kawai ta sare min shi? Tabbb!!!! Sammm!!! Ban amince ba in dai ni ce Uwar Nuren wanda na sha wahalar ɗaukar cikinsa na sha wuyar nakuɗarsa ban amince ya auri Samima ba, na dai yarje masa ya taimaketa amma ban da aure" sosai Abba yake bin Momy da kallo kamar yau ne ya fara ganinta, ji yake yi kamar an canzo mi shi Aminarsa wannan ba ita ba ce, amma kasancewar tunowar da ya yi ɗan adama tara yake bai cika goma ba ya saka shi kama hannunta suka zauna cikin sanyin murya ya ce.
"Amina? Yanzu misali ace ke ce kike da Samima, ace Samima ƴarki ce, Nuren kuma Ɗan Zulaiha ne, ga dai ƴarki Samima tana fuskantar jarabawa, aka zo maganar taimako a matsayinki ta Uwa Mahaifiya idan Nuren ya ce ba zai auri ƴarki ba, domin ya taimaka mata ya za ki ji a ranki? Ki faɗa min gaskiya tsakaninki da Allah ya za ki ji? Karki manta duniya da faɗi, idan ka taimaki wani a yau, kai baka san wanda zai taimakeka a gobe ba, ina so ne ki fahimceni da kunnen basira, babu wanda yafi karfin jarabawa, ki amince ɗanki ya auri Samima dan ba ki san iya tarin ladar da Allah ya ba wa yaronki ba, ta sanadiyyar taimako, Allah yana son mutane masu taimako, karki kasance da son kanki da yawa Amina, son kai babbar illa ne ga rayuwar ɗan adam, sabida yana kai sa ga hallaka, fatan za ki yiwa maganata muhalli ki karbeta hannu biyu?" jikin Momy ne ya yi sanyi idanunta ya taru da hawaye ta tashi da sauri ta bar Abba,murmushi Abba ya yi dan yasan ya samo kanta.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Magana kamar wasa, a kwana biyu aka ɗaura auren Samima da Nuren a garin maiduguri, Abba shi da Momy sun zo in da manyan malamai suka halacci ɗaurin auren, Samima bata so auren Yayan nata ba, sabida tsoron laluran da take ciki, bayan an gama ɗaura aure Suhail na tsaye a gefe take ya ga gilmawar wani baƙin duhu wanda ya yi sanadiyyar faduwarsa ƙasa, da sauri Nuren ya ɗagosa yana jijjigasa yana ambatar sunansa cikin tashin hankali, nan aka cika akan Suhail, Malam Abba ya sa hannu ya dafe kan Suhail, sannan ya dafa ƙirjinsa, da sauri Malam Abba ya furta "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!!" tuni zufa ta shiga wanke wa Nuren fuska ya ce.
"Malam, me ya faru? Me ya samu Abokina!!?" Malam Abba bai tsaya ba wa Nuren amsa ba, ya bada Umarnin a dauki Suhail a kai sa daki, da sauri almajiran Malam suka karbi Suhail da kyar daga hannun Nuren, aka wuce da shi, Nuren na biye da su a baya, nan aka rufu akan Suhail dan kuwa jinkiri kadan za ayi Asabe ta kashesa, adduoi Malamai ke yi wa Suhail ana bunka shi da hayaki, tun safe karfe sha ɗaya har yamma ana abu ɗaya da kyar da suɗin go shi aka samu Suhail ya farfado, kafin wannan lokacin idon Nuren sun kumbura suntum dan gani yake Suhail ya mutu, ga shi an hanasa shiga ya ga Suhail din, lokacin da aka gaya masa Suhail ya farka da gudu ya shiga ya rungumesa yana tambayar me ya sa me shi, nan ta ke Baba Malam ya ce.
" *ASABE CE*"
da sauri Nuren ya kalli Baba Malam.
"Asabe kuma? Asabe fa? To me Suhail ya mata?"
"Kashesa ta so yi" daga Nuren har Suhail idanu waje suka kalli Baba Malam, Malam Abba ya ce.
"Dama na faɗa muku zai yi wuya a gama ba tare da an rasa rai ba, sai dai wani ikon Allah"
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!! wai me Asabe ta ke son zama ne?" cewar Nuren da jikinsa ke b'ari, Baba Malam ya ce.
"Ka dai ka bar mutum din da ya kauce hanya, idan har bawa zai din ga amfani da zugin zuciya tana ingiza shi zai iya zuwa ya aikata abun da ya fi haka, Allah ya rabamu da b'ata, ya tsaretar da imaninmu" aka amsa da ameen, Nuren ya ce.
"Ina ga zan koma Adamawa gobe dan na haɗa Asabe da hukuma" girgiza kai Malam Habibu ya yi, ya ce.
"Hakan ba mafita bane dan ba case din hukuma bane, mu kwantar da hankalinmu komai ya yi farko yana da karshe, wata rana sai labari, kuma Allah yana bai wa bayinsa masu aikata mugun nufi lokaci su ta aikata b'arna a ɗoran ƙasa, idan suka ƙi gyarawa Ubangiji shi yasan yadda yake yi da bayinsa, ko ba komai yanzu na tabbata Asabe ta samu tawaya, abu na farko auren Nuren da Samima dan mun rushe baƙin bangon sihirin da ta kulla a tsakanin Nuren da Samima, kuma shaiɗanun sun ra gu zuwa goma, a hankali komai zai dai-daita" jinjina kai suka yi, amma Nuren a zuciyarsa ya kudirta idan ya koma adamawa sai ya yi wa Asabe shegen duka.
@@@@@
A dayan bangaren kuwa Asabe ta ƙone a hannun sabida bata samu nasara akan Suhail ba, kuma ta sake tabbatar da duk sharrin Malaman da suke yi wa Samima magani ne,a madadin ta saduda sai kawai ta kwashe kayanta da ƴarta suka koma wani gida ba tare da kowa ya sani ba, baƙin ciki ya mata yawa ga aljanu sun fara addabarta, sabida sihirin da yake tsakanin Nuren da Samima ta rushe, tana so ta koma wajan bokanta a enugu dan ya sake yi mata aiki mai zafi wanda ya fi wannan, inda ta yanke shawarar ba zata sake yiwa Samima komai ba har na tsawon kwana biyu,ta inda zasu baro maiduguri su dawo adamawa ta samu ta kara aikata kudirinta akan Samima,kuma dole Nuren ya auri Sha'awa, dukiyar mahaifinsa ya dawo hannunta, da wannan shawarar da zuciyarta ta bata ta yi na'am da shi, kwana biyu ta ɗagawa Samima kafa, sosai kuma Samima ta ji sauki bata jin komai, da dare zata yi baccinta, ganin haka ya sa ta cewa ita fa ta ji sauki, Malam Abba ya yi murmushi ya girgiza kai shi kadai ya ga abun da ya gani, ya ce.
"Samima kina son komawa Adamawa ko?" ta yi dariya ta ce.
"Malam, na ga na ji sauki ne bana jin komai, duk da ance ba zan koma mutum ba, watakila a haka zan mutu, nayi tawakkali na karbi kaddarata, kuma muna da wani show ne yau saura kwana hudu shi ya sa"
Shuru Malam ya yi dan maganarta ta ba shi tausayi, da haka Malam ya kira Malam Nasiru mahaifin Samima akan cewa zasu iya komawa gida a gobe inda aka haɗasu da magani kala-kala, dama su Abba da Momy basu zauna ba,ranar da aka ɗaura aure da washe gari suka baro maiduguri, sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Umma da Matan Malam dan su na da matukar kirki, da washe gari asubanci su Nuren suka yi suka kama hanyar Adamawa, sai yamma lilis suka isa, a gajiye suke, Nuren ya ajiye su Umma a gida sannan ya ajiye Suhail, kafin shima ya wuce gida, ya watsa ruwa kafin ayi magriba ya zauna yana tattaunawa da Momy akan maganar ko Samima ta tare, ya ce.
"A'a baya so adamawa a san ya auri Samima sai ta ji sauki gaba ki ɗaya, sabida idan Asabe ta sani zata iya kashe Samima dan babu burbuɗin imani a zuciyarta" da haka suka ajiye magana.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Yau kwanar su Samima biyu da dawowa adamawa, yau kuma ta kama lahadi, haka kawai ta ji tana sha'awar shiga skull shiryawa ta yi ta gayawa Umma zata je makaranta Umma ta ce.
"Samima har ga Allah bana son fitarki, dan ni kam idan kika fita baya zame min alkhairi" murmushi Samima ta yi ta ce.
"Wallahi nima Ummana bana son fita, yanzu Sauda ta kirani take gaya min wai na b'ata b'at ba'a jina, kuma anyi paper dayawa bani nan kuma sun yi min,shi ne nake so na je karba na duba tun da sun ce su na cikin makaranta, gwanda naje mu haɗu mu gaisa" Umma ba sabida ta so ba ta ce.
"To shi kenan, ina fatan dai kin gayawa Nuren ya amince? Dan kinsan da da yanzu ba ɗaya bane ko?" dan yatsine fuska a boye Samima ta yi ta kwakulo yaƙe dan ba za ace dariya ko murmushi ta yi ba ta ce.
"Haba Umma, ke ma kinsan bana komai sai da izinin Yayana, ai na gaya masa kuma ya amince" cike da gamsuwa Umma ta ce "to a dawo lafiya" dan Samima yawancin shawararta da Nuren take yi, amma yau a zahirin gaskiya bata gaya masa ba dan bai san cewa zata fita ba, fita ta yi gabanta na faduwa tana adduar Allah yasa kar yazo Umma ta ce masa bata nan kuma ta gaya mata akan cewa ta tambayesa, neman napep ta tsayayi, kamar daga sama ta hango Sha'awanatu tana tafiya bazar-bazar tana lafcen ƙura, ko daga ina take oho sai kace almajira, girgiza kai Samima ta yi ta hau ɗaga mata hannu, Sha'awa tana ganin Samima ta ja dogon tsaki, kamar zata yi kuka, dan ganin Samima sai kace balarabiya, ita ma Samiman abun hawa ta hau ta kama gabanta ganin kallon wulakancin da Sha'awa ta yi mata, kar taje ta yi mata magana ta kama yi mata tijara a unguwa ga shi dama nemanta ake yi ruwa ajallo, dan har kwanar gobe kisan da ta yi akwai masu nemanta su kasheta,duk da ita ko kyankyaso bata taba kashewa ba, tana isa skull dinsu, a department dinsu ta iske su Sauda Sarah Sally Hidayan Abbas cikin murna ta miƙa musu hannu suka gaisa, ita ma ta zauna, Sally ta ce.
"Kee Samima kin ga yadda kika yi wani kyau kuwa?"
"Hummm Sally bana son tsokana, ni da nake ta fama da jinya bani da lafiya" Sarah ta ce.
"Gaskiya kam kin rame sosai Samima"
Hidaya ta ce.
"Amma me ke damunki haka Samima? Wannan ciwo ya ƙi barinki ki huta, wani irin ciwo ne?" Samima ta ce.
"Cutar sirri ne" suka kwashe da dariya su na tafawa hira suka ɗan taba na dan wani lokaci kafin suka fara yi mata bayanin abun da aka yi bata nan, suka bata papers dinta, godiya ta yi musu sosai, tare da adduar Allah ya barsu tare, ai da haka ake yi da an samu ci gaba a cikin al'umma, kowa ya cire bakin ciki da hassada da kyashi, bayan sun gama hirar karatu suka bige da hiran show din da za ayi gobe monday, Samima ta nuna musu kaɗan daga cikin kayan da ta ɗinka a wayarta, sauran ta ce sai an hadu gobe da dare zata nuna musu idan an zo fitowa, Sauda ta ce.
"Yauwa, ni kam Samima kinji labarin mutuwarsu *AMIR* kuwa?"
Dumm!!!dumm!!!dumm!! Gaban Samima ya buga ta miƙe a zabure ta gwalalo ido waje kamar zasu faɗi kasa, a firgice ta ce.
"Me kika ce!!?"
"Wallahi muma labarin mutuwarsu muka iske ranan a skull, shi da abokansa su biyar, aka gawarsu a wani gidan Amir din wanda Babansa ya gina masa, amma ba a zarge kowa ba, sabida saran macizai aka gani a jikinsu, ko da aka yi bincike ma shine ya kashesu,amma abun da ya ɗaurewa mutane kai shine baƙin macijin Babba ne, idan aka ce za ayi bincike ta ina ma za a fara, ga shi ance gubar maciji mai karfi ne, ke kin ga su Amir wallahi kamar ba su ba, sai kinyi kuka, kai Allah yasa mu cika da imani" sauran suka amsa da ameen, ban da Samima da ta shiga tashin hankali, take hawaye suka ce bismillah ga su nan ta fe, kamata su Sauda suka yi suka zaunar da ita, kuka sosai Samima ke yi kamar ranta zai fita, Sally ta ce.
"Haba Samima wannan kukan fa? Sai kace ance miki mahaifinki ne ya rasu? Dan Allah ki bari ya isa haka,kin ga har kin fara tara mana jama'a, wannan kuka da kike yi ina ga ko iyayensa ma basu yi ba" Samima a ranta ta ce.
"Ina kuwa zasu yi irin kukana, ni ina kuka ne sabida nice sanadi" wani zuciyar ya ce mata a'a Samima ba ke bace Sanadi alhaki yana kan Gwaggo Asabe, Sarah ta ce.
"Sally dole ne Samima ta yi kuka, sabida ranar sunyi rigima da Amir din har yake cewa....." Sauda ta dakatar da Sarah da cewa.
"Plss Sarah ya isa haka, yanzu fa sun mutu bai kamata a fadi maganar marar kyau ba, ance falyakul khair au yeslimunt" murguda baki Sarah ta yi ta ce.
"Shi yasa a ko da yaushe ake yi mana wa'azi muji tsoron Allah mu zauna da kowa lafiya ta yadda idan muka mutu mutane ne shaidarmu, kuma dole ne wata rana ayi maganarka in ma ka aikata alkhairi ko sharri, ALLAH ya bamu ikon aikata alkhairi dan mu samu shaidar mutane wata rana idan an zo maganarmu" suka amsa da ameen, suka ci gaba da lallashin Samima, da kyar ta yi shuru, har yamma su na skull din tana bitan karatun da bata yi ba, su Sauda tana taimaka mata, da misali biyar da rabi Umma ta fito tsakar gida tana mita Samima bata dawo ba, ko dai Nuren ya biya ɗaukota ne? Umma bata gama rufe baki ba sai ga Nuren na Sallama, amsawa Umma ta yi ta ce.
"Au ashe ina mita ku na tafe, ina Samiman?"
"Samima kuma Umma?" sake baki Umma ta yi tana kallon Nuren ta ce.
"Eh mana, dazu da safe Samima ta fita akan cewa zata je skull har nake tambayarta ta gaya mata ta ce min eh, kuma ga shi yanzu har biyar da rabi na dauka kuna tare ne ai" ɗan murmushi Nuren ya yi ya dafe kansa ya ce.
"Au Umma kin ganni da mantuwa ko? Ashe fa haka muka yi da ita"
"To tana ina? Ko tana wajan Momy ne?"
"A'a Umma ai na ma manta ne ban ɗaukota ba, dazu naje ɗaukota tace min basu gama ba, ina zuwa" ya fice da sauri yana murmushi amma a zahirin gaskiya ransa a b'ace yake dan Samima bata taba b'ata masa rai irin ta yau ba, da zata yi masa karya, ta fice bai sani ba tun safe shine har yamma dan ta raina masa wayo" motarsa ya shiga ya bata wuta bai tsaya ko ina ba sai universityn'su, yana parkinga kuwa su na fitowa ita da su Sauda, bata ma gan shi ba, Sarah ta ce.
"Amma dai Samima Allah ya shiryeki bamu sanki da karya ba" ido Samima ta ɗago wanda suka kumbura sabida kukan ra tasha ta ce.
"Karyan me kuma nayi Sarah?"
"Kince Yayanki ba zai zo daukarki ba, to yanzu wanene wancan?" Samima ta sake ɗaga ido inda Sarah ke mata nuni ta hangosa tsaye a jikin mota ya naɗe hannuwansa ya kirji yana kallonta, gabanta ne ya yi mummunar faduwa jiki na b'ari ta ce.
"Na shiga uku, Hidaya,Sally, Sauda, Sarah,sai mun hadu idan Allah ya kaimu goben a wajan show" ta wuce har da ɗan gudunta, tana zuwa bakinta ya hau b'ari ta rasa me zata ce masa, "shiga mota" ya faɗa ransa b'ace, da sauri ta shige ya tada motar ya bar wajan, sun danyi tafiya su na gaf da isowa gida ya tsaida motar a gefen titi ya parka ta ya kalleta ya ce.
"Samima? Yaushe kika fara karya ban sani ba uhum?" shuru ta yi tana aikin zare ido, ta kasa ba shi amsa.
"Kin taba ganin fushina?" ta girgiza kai jikinta na kyarma.
"To karki so ki gani, dan idan nayi fushi ba za ki iya tsayuwa a gabana ba, akan me za ki fita har ki yi wa Umma karya akan cewa wai kin faɗa min na amince? Lokacin da ba ki da aurena ma kafin ki fita kina gaya min, shine yanzu dan kin ga da aurena akan ki za ki sa kafa ki fice baki sanar dani ba ko? To wallahi karki sake na sake gani, kina wuce wa idon maza na kan ki ko? Kin fita kin kama kin yafe gyale a matsayinki ta matar aure, a madadin kisa hijabi da liƙabi, tun da kin raine ni ko?" mita sosai Nuren ke yi yayinda idanunsa suka ƙanƙance, hakuri Samima ta shiga jera masa, ko kulata bai yi ba ya ajiyeta a kofar gida ko shiga bai yi ba ya kama gabansa tare da danna mata kashedi ko gate karta sake ta fito, tun da har yanzu ba wai ta warke gaba ɗaya bane ya wuce rai b'ace, ko da Nuren ya ajiye Samima a gida akan idon Sha'awanatu uwar gantali, tana gani ta wuce gida ta sanarwa da Uwarta, Asabe ta ce yau sai ta yiwa Samima abun da zai sa ta kashe kanta da kanta, Nuren kuma zata dage da aiki akansa shi da kansa zai kawo kansa.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
0 comments:
Post a Comment