Bayan haka ina kira ga matan aure manyan mu da kananan mu, please idan kin tabbatar your marriage is not working, idan kin tabbatar kin je limit dinki na hakuri a gidan auren ki, please walk out of the marriage. Allah ya halatta saki for a reason, wani lokacin rabiwar tafi alkhairi akan cigaba da zaman. It is better a kiraki da bazawara then ki kasance in maryam sanda's shoes.
Sannan iyayen mu dan Allah ku dube mu da idon rahama, ku tausaya mana, dan Allah idan yarinya tazo gida tace ta gaji da zaman auren ta please ku bincika sosai, idan tana da gaskiya kuyi supporting dinta, kar ku tura yarku ga halaka, karku tura yarku zuwa wuta.
Now, let's continue with labarin Diyam maybe anan ma da akwai darasin da zamu dauka.
Da mamaki karara fuskarsa yake kallona, maybe bai taba tsammanin zan iya mayar masa da magana haka ba. Yace "ke? Kin san dawa kike magana kuwa? Ni din ne ma kike cewa za'a makala miki?" Na cigaba da kallon sa cikin ido duk a cikin kokari na na nuna masa cewa bana jin tsoronsa, amma zuciyata in banda lugude babu abinda take yi. Ya daga hannu da niyyar wanka min mari sai kuma ya kalli gidan inda hayaniya take fitowa daga tagogin sama, ya fahimci yana dukana zan tara masa jama'a dan haka sai ya dunkule hannunsa sannan ya sauke, ya nuna ni da dan yatsa yace "in kika sake kika shigo gidan nan sai na karya ki" na fusge hijab dina daga hannunsa nace "not today, kuma ni bani zan shiga gidan ka ba sai dai a shigo dani dan dole" na juya na tafi na barshi anan ina jin dadi a zuciyata, ashe dai Sadauki bai tafi da dukkan Strength din nawa ba, ko kuma maybe a time din wannan hug din ne yayi passing some of his strength and courage to me.
Muna komawa gida na wuce direct zuwa dakin inna, na gaisheta tana ta washe baki tace "kun dawo? Ya gidan?" Na tashi ina ninke hijab din dana cire nace "lfy lau" tace "lfy lau? Shikenan abinda zaki ce? Bayanin gidan zaki yi min inji dame dame aka saka kuma menene ba'a saka ba" nace "Inna ban sani ba nikam, ban shiga ciki ba a waje na zauna" nan fa takama fada, ni kuma nayi shiru har saida ta gama sannan nace "Inna yace inna shiga gidan sa sai ya kashe ni" sai ta girgiza kai tace "fada kawai yake yi, shima fushi yake yi saboda an matsa masa akan maganar nan, daga ke har shi ba kwaso amma abinda mu iyayenku muka hango ku ba zaku hango shi yanzu ba sai nan gaba zaku fahimta".
Washegari ina kwance kamar kullum sai ga aike wai ana kiran Inna, ta tashi ta tafi can kuma ta dawo sai naga cards a hannunta. Ta miko min tana kallon fuskata har na karba na karanta. Katin daurin aure ne, sunana da sunan Saghir, date din kuma nan da kwana uku. Na ajiye su akan cinyata ina jin dan kuzarin dana samu jiya yana draining kawai sai hawaye na ya fara zuba akan cards din. Na tuno abinda Sadauki ya gaya min "how litres of hawaye zaki zubar ne acikin wata daya?" "Be strong" he said, sai na kara karfin kuka na, wanne Strength ne dani kuma bayan bani da gata? Bayan ana so ayi amfani dafarinciki na gurin faranta wa wanda yake da gata? Saboda namiji ne shi nikuma mace? Ko saboda yana da uba a duniya ni bani da? Sai Inna ta zauna a kusa dani ta kwantar da kaina a kafadarta tace "Alhaji yace za'a hada daurin auren da addu'ar kwanaki arba'in din baffan ku, sai bayan daurin aure da sati daya sannan zaki tare, saboda ki samu damar gayyatar kawayenki da sauran shirye shirye". Na dago kai ina sake kallon date din, sai nayi realizing shine date din da za'a yi resuming school.
Tun daga lokacin taste din abinci ya dauke daga bakina, nayi kuka kamar idona zai cire har bana gani sosai, nayi addu'a na gaya wa Allah, kullum kuma sai na gaya wa Inna "Inna bana son auren Saghir" amma kamar busa sarewa nake yi, babu wanda ya dube ni, babu wanda ya mayar da damuwa ta wani abu mai muhimmanci ba kowa sai yace "zata daina ne, daga anyi auren shikenan ai ita mace mai rauni ce" ni kuwa jinsu kawai nake yi dan bana tunanin akwai ranar da zata zo wadda zan ji ina son Saghir.
Ranar Lahadi, 28 September aka daura aure na da Saghir. Ranar tun dana tashi da assuba na shiga toilet na rufe kaina na kwanta kan tiles nake kuka har aka gama daurin auren ban fito ba. Sai da Mama tazo sannan da kyar na bude mata kofar toilet din ta shigo ta fito dani, ta kori duk wadanda suke dakin ta zaunar dani akan gado ta bani Alqur'ani tace "kiyi ta karantawa zaki ji sauki a zuciyarki. Kiyi ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah zai sanyaya miki zuciyarki kuma yasa hakan ya zamo abu mafi alkhairi a gare ki" itama sai ta dauko Alqur'ani ta zauna muke karantawa tare, har sai da hawayen fuskata ya tsaya. Ranar daga ni sai ita muka zauna a dakin, ta saka ni a dole naci abinci duk da cewa da kyar yake sauka cikina. Sai kuma na cigaba da karatun ina jin nutsuwa tana samu na, ina jin karfin guiwar karbar kaddara ta, sannan kuma na gabatar da adduoi ga Baffa da Ummah, sannan na yiwa Sadauki addu'ar fatan alkhairi a duk inda yake. Na kuma samu kaina da tambayar kaina ko ya sani? Ko ya san an daura min aure da Saghir yau?
Kwanakin da suka biyo bayan nan shirye shirye ne kawai akeyi na biki. Hajiya Babba baki har kunne sai shiga take yi tana fita tana ta tsare tsare. Inna babu abinda take yi, gaba-daya tayi wani irin shiru da ita sai dai ta saka ni a gaba tayi ta kallo. Ni kuma na zama kamar mutum mutumi, bana kuka amma bana uhm bana uhm uhm. Mama ce tazo ta debi wasu daga cikin kayan lefe na ta kai aka dinka min, sannan ta yiwa Asma'u itama dinkuna tare dasu Rufaida. Sai tace min "Diyam babu wani abin da zaki shirya ne? Ko yar walima haka ke da kawayenki?" Ban kalle ta ba nace "Mama kawayena ai duk sun koma makaranta, ss1 zasu shiga, ni kuma gidan miji zan shiga, waye zai bar karatunsa yazo bikina?"
Sai tayi shiru bata bani amsa ba amma tana komawa gida sai ga yaya Mukhtar ya kawo Rumaisa, Rufaida da Muhsina sun taho da kayansu zasu zauna har sai an gama bikin. Hajiya Yalwati ta saka aka ware mana daki saboda yan uwan mu da zasu zo daga Kollere zasu sauka a dakin Inna. Ranar Rumaisa ta kawo min wa蓷ansu littattafai guda biyu 'rayuwar aure a musulunci' na daya dana biyu tace "ki karanta zaki samu idea akan zaman aure" na karba kawai nace "Nagode" sai kuma tayi dariya tace "ni ban san me kike yiwa fushi haka ba. Mijinki kyakykyawa, kinsan da ina da crush akan hamma Saghir amma yanzu na hakura tunda ya zama mijinki" na tabe baki kawai a raina ina cewa ina ma dai zamu iya chanjen place da ita? Ita ta zama matar tasa ni in koma ita?
Ana gobe kamu Aunty Fatima tazo da mai kunshi zata yi mana, ranar sunga taurin kaina dan da kyar na zauna akayi min dan haka duk wanda baisan bana son auren ba sai daya sani a ranar. Ana gama wa kuma na saka hannu da gangan duk na damalmala kunshin ya chabe. Aunty Fatima kamar ta rufeni da duka dan haushi amma a haka ta kyale ni. Da daddare tace muje saloon sai na saka mata kuka a dole ta kyale ni kar in tara mata jama'a.
Ranar kamu sai da inna tazo ta sakani a gaba sannan na tsaya akayi min kyalliya. Mun zo zamu tafi gurin da aka shirya dan yin kamun kenan naji wata tayi comment "kunga amaryar kuwa? Yar mitsitsiya" ai kuwa ina jin haka na juya na koma daki a dole sai mai kamun ce ta bini dakin ta kama ni a can. Ranar yini kuwa ni wuni nayi da zazzabi dan haka suka dai suka sha bidirin su.
Washegari kai amarya, tunda safe Mama tazo, yau ne kadai na ganta tun da aka fara bikin. Tana zuwa yau ma duk ta kori su Rumaisa da dama duk sun addabeni, ta saka ni a gaba yau ma muka yi ta karatu kamar ranar nan, tare muka ci abinci mukayi sallah tare kuma sam bata yi min wata magana data danganci aure ba har magrib tayi sannan ta saka ni nayi wanka ta dauko min wani lace fari tas tace in saka. Ta gyara min fuskata simple make up sannan ta saka min sarka da dan kunne tayafa min farin mayafi ta kuma feshe ni da turare. Na zauna a bakin gado ta rufe min fuskata da mayafin sannan ta mike zata fita, na rike rigarta nayi mata tambayar da ta jima tana yawo a zuciyata, nace "Mama Sadauki ya sani? Ya san an daura min aure?" Ta dauke kai tace "ban sani ba Diyam, na kira layinsa baya shiga maybe ya chanza layi ne" sai ta fita, an jima suka dawo tare da wata matar dana fahimci daga baya cewa kanwar Hajiya Babba ce.
Tana zuwa ta bude fuskata tace "Masha Allah. Tubarkallah. Lallai Sagjir yayi dace da kyakykyawar mata. Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka, Allah ya baku zuri'a ta gari" Mama tace "ameen". Sai suka kamani a tare suka fita dani. Sam ji nayi zuciya ta dake bana jin wani kuka kuma. Muka shiga dakin Inna anan na tarar da ita tana kwance ashe wai bata da lafiya tun safe. Na durkusa a gabanta tace "Allah yayi miki albarka Halima, biyayyar da kika yiwa iyayen ki Allah yasa kema naki yayan suyi miki. Allah yasa wannan auren shine mafi alkhairi" muka ce ameen muka tashi. Zamu tafi part din Alhaji Babba aka ce mana wai baya nan ya fita tun safe. A raina sai naji ina kewar Baffa, ba zai taba fita ba ranar da yasan zan bar gida in tafi gidan miji. Gidan kawu Isa muka shiga yayi min fada shima, sannan muka shiga mota muka tafi sauran motocin suna biye damu.
Har muka je gidan banyi kuka ba. Muka shiga ciki sannan naji mun fara gawa stairs sannan muka shiga wani palo sai kuma wani daki. Aka zaunar dani akan gado Mama ta rufo kofa tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna ta fara magana a hankali
"Diyam ki saurare ni sosai kiji abinda zan gaya miki. Yanzu kin zama matar aure, kin bar karkashin iyayenki kin koma karkashin mijinki haka zalika aljannar ki ta koma karkashin mijinki. Bauta zakiyi, amma ki saka a ranki cewa ba Saghir zaki bautawa ba Allah zaki bautawa. Auren Saghir shine kaddararki, shine jarabawarki. Biyayyar Saghir a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addinin ki. Na sami cewa ba'ayi miki adalci ba, na sani cewa iyayen Saghir basu kyauta ba sun kasa tankwara yaron su tun yana danye har sai daya bushe tukunna sannan kuma suka dora hakkin tankwara shi a kanki, duk da kasancewarki mai kankantar shekaru amma ni nasan zaki iya, in dai har zaki yi masa biyayya, ki kula da cikinsa da shimfidarsa, ki kasance mai tsafta mai hakuri da juriya da kawar da kai a lamuransa, to kuwa duk girman kansa sai kin mayar dashi tamkar rakumi da akala musamman tunda kina da kyau kuma shine abinda aza da yawa a yanzu suke so".
Ta jima tana yi min nasihohin hanyoyin da take ganin zan bi in jawo hankalin Saghir ya soni, ni kuma sai nayi wa kaina tambayar "ta yaya zan saka wanda bana so ya soni? Biyayya ga abinda baka so is extra hard right?"
[1/29, 10:18 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty Nine: The Lost Flower
Warning: Emotional Episode
Ta mike zata fita sai na rike zanin ta na kifa fuskata a cinyarta na fara kuka mai tsuma zuciya amma sai tasa hannunta ta cire hannuna daga zaninta ta juya ta fita. Na rufe fuska ta da hannayena ina kuka, ji nake kamar wannan auren shine karshen rayuwata, ji nake ina ma mala'ikan mutuwa yazo ya dauki raina, anya kuwa zan iya yiwa Saghir biyayyar aure kamar yadda ya kamata? Kuma gashi aljanna ta tana defending on wannan auren alakakai din and I so much want to go to jannat idan na mutu, wannan yasa na fara addu'ar Allah yasa in mutu a wannan ranar.
Ina cikin kuka na su murja suka shigo suka zagaye ni, Rumaisa tace "ke baki san yanzu an daina kukan aure bane ba wai? Wannan ai sai ki bada mu in abokan ango suka zo" murja tace "suka zo ina? Wai nan gidan? To ni kam bada ni ba babu wani siyan baki da zan zauna yi yazo ya hada mu ni da amaryar ya huce haushin sa akan mu" Rumaisa tace "ke dan Allah ki daina fadar haka ai sai ki saka taji tsoro". Suna ta hirarrakin su ni dai na mike nayo alwala na gabatar da sallar isha ina kaiwa Allah kuka na.
Ina nan kan sallayar sai na jiyo muryar yaya Mukhtar daga palo, sai ga Rufaida ta shigo tace "wallahi yaya Mukhtar yace duk ku fito mu tafi in ba haka ba sai dai ku kai kanku gida dan shi tafiya zaiyi. Wannan unguwar tasu kuwa ba abin hawa zaku samu ba, angon kuwa in ya zo ko suma kuke ba zai kaiku gida ba" kusan duk a tare suka mike suna harhada kayansu. Na kalle su da kumburarrun idanuna nace "yanzu tafiya zaku yi ku barni ni kadai a gidan nan?" Rumaisa tace "da anjima angonki zai zo, kuma ai naga kuna da maigadi" Murja tace "idan yayi tafiya kiyi min waya sai inzo in taya ki zama, amma in yana nan ba zan zo ba". Yaya Mukhtar ya sake kwala musu kira dan haka suka fice da sauri.
Ina jinsu suka sauka daga bene, ina jinsu suka fita daga palon kasa suka rufe kofa sannan naji sun shiga mota an bude musu gate sun fita, na tashi da sauri na leka ta window na hango hasken motar su har sun dau hanya. Sai kuma na tsaya ina kare wa unguwar kallo, babu gidaje sosai sai kwangwaye wannan ya kara wa unguwar duhu. A bakin gate naga mai gadi a zaune akan benchi da radiyo a gefensa. Sai naji wani irin loneliness sannan kuma naji wani irin tsoro.
Na haye kan gado da sauri sai kuma wani tunani yazo min sai na tashi da sauri na bude kofa na fita. Sai na ganni a cikin wani palo madaidaici wanda aka kawata da kujeru da kayan kallo da adon frames a bango da sauran tarkace. Kofofi uku ne a palon, na fara bude su daya bayan daya ina neman kitchen amma sai naji daya a rufe take dayar kuma wani bedroom din ne kudan irin wanda na fito daga ciki sai banbancin colors. Na sauka daga bene da sauri shima palon ne amma yafi na sama girma da tsaruwa, sai wadansu kananan bedrooms guda biyu da dining room mai hade da katon kitchen. Ban tsaya kallon komai ba saboda yadda jikina yake karkarwa saboda tsoro, na shiga kitchen din na fara bude drawers ina neman abinda ya kawo ni, can naga set dinsu, wukake, na dauki wadda naga tafi kowacce girma na boye a rigata na sake fita da sauri na haye sama. Dakin da aka kaini na koma na tura kofa da niyyar locking amma sai na ga babu key a jiki. Na fara fara neme neme cikin lockers din dakin amma babu key babu alamarsa. Na shiga toilet na duba nan ma babu. Sai na dawo na zauna akan gado kamar zanyi kuka amma tears din sun tsaya, maybe sun kare. A hankali nace "Sadauki, Please come and take me away from here".
Sai na kwanta na dunkule a guri daya, na jima a haka sannan bacci ya fara fusgata ina yi ina farkawa a tsorace cike da mafarkai, wani mafarkin wai Sadauki tazo yace in tashi mu gudu, wani kuma wai Saghir yazo ya zare belt dinsa yace ba yace kar in sake inzo gidan nan ba?
Cikin baccin naji karar bude gate, na tashi zaune a tsorace, sai nayi sauri naje na kashe fitilar dakin sannan nazo na leka window, mota naga ta shigo tayi packing, sai kuma ya fito yana tafiya unsteadily. Ina lura da maiigadi yana gaishe shi amma bai ko kalle shi ba ya taho cikin gidan. Nayi sauri na tura kofar dakin da na ke ciki sannan na dauki wukata na tafi can lokon gado na kudunduna a cikin duvet, naji ya bude kofar palo ya shigo amma banji ya rufe ba, najiyo shi yana hawowa sama sannan naji ya bude kofar dakin da yake kusa da inda nake, sai kuma takunsa yana tahowa sannan naji ya bude dakin da nake, na dauke numfashi na ina kara addu'ar Allah ya dauki raina.
Ya kunna fitila sai can kuma naji ya kashe amma na tabbatar ya ganni, sai kuma naji ya karaso inda nake kudundune ya saka kafarsa mai sanye da takalmi ya dake ni da ita "ke!" Na dunkule hannuna a handle din wukata na mike da sauri ina nuna shi da ita, fuskata cike da hawaye nace cikin murya mai karkarwa "if you dare touch me!" Ya tsaya yana kallona ta kasan ido, da mamaki a fuskarsa sannan cikin wata irin murya da tafi yi min kama data yan maye yace "what? What will you do?" Na sake nuna shi da wukar "in ka kara wani takun kusa dani na rantse I will...." Ya tako step din without hesitation yace "you will what?" Gabadaya jikina karkarwa yake yi hatta wukar hannuna rawa take yi tana neman faduwa, hannu daya yasa ya doke hannun nawa sai wukar ta fadi. Na dunkule a kasa "don't touch me please" sai yasa hannu ya kamo wuyan rigata ya mikar dani tsaye, ya hada ni da bango sannan ya kawo fuskarsa dai dai tawa, wani wari naji daga bakinsa, ba warin kazanta ba amma wani wari marar dadi, nayi saurin dauke kaina yace "mena gaya miki zanyi miki in kika sake kika shigo gidan nan? Kin dauka wasa nake yi dake ko?" Nace "wayyo Allah na, wayyo Sadauki" ya saki wuyana yana kallona "Sadauki? Sunan saurayin naki kenan? To yazo ya nuna sadaukan ta kar tasa in gani" nayi shiru a raina ina fatan zaizo din, yace yana kara matsowa jikina "bana ce miki karki zo gidan nan ba?" Na girgiza kai nace "nima kawo ni akayi, Bani nazo da kaina ba. Please ka mayar musu dani kace ba ka sona" yace "with pleasure. Amma kafin in mayar dake sai na yi musu proving abinda na gaya musu su kaki yarda. Kinyi min kankanta da aure" yana fadin haka sai ya saki wuyana, sannan ya hankada ni na fada kam gado kaina ya bugu da jikin frame din gadon. Na fara ganin dusu dusu a idona amma duk da haka sai nayi kokarin mikewa sai dai nauyin da naji a kaina ya sa na kasa ko motsi. Amma sai na takarkare tun karfi na zunduma ihun kiran Sadauki a lokacin da naji zani na ya bar jikina. Sai kuma naji wani piercing pain daya taho tun daga kasana ya dire har cikin kwakwalwata. Sai muryar ihun ta dauke, numfashi na ya dauke, naga wani haske a idona. The last thing da naji kafin hankali na ya barni shine muryar Sadauki lokacin da yake ce min "everything is going to be alright".
A short episode. But mu fara jajanta wannan lamarin tukunna.
Dear parents, This might be what will happen to your daughter in kuka rufe idon ku kuka aura mata wannan lalataccen dan masu kudin da bata so, ko wannan alhajin da yake zuwa a babbar mota, ko kuma wannan dan uwan naku da yaki aure shekara da shekaru kukayi tunanin bara ku hada su dan inganta zumunci. It might not always be the right choice, especially idan wanda za'a hada ta da shi din ansan bashi da halayya mai kyau. Yaya amana ne a hannunmu, don't trade them for wordly things please.
Yes, addini ya yarda iyaye su taya 拼a拼ansu zaben mijin aure, amma kuma bai ce a tirsasa musu ba. Akwai ingantaccen hadisin ma da ya nuna haramcin hakan.
Allah ya sa mu dace.
[1/30, 11:56 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂� DIYAM 鉂�
By
Maman Maama
Episode Thirty : The Empty Heart
Sama sama nake jin maganganu a kusa dani, a hankali ake maganar amma sai naji tamkar wanda ake hayaniya saboda ciwon da kaina yake yi min. Na kai hannu a hankali na dafe goshina sai naki ance "sannu Diyam. Ta farka" naji muryar kamar na santa amma sai na kasa gane mai ita. Wannan yasa nayi kokarin bude ido na amma sai naji sunyi min nauyi. Na mayar dasu na rufe. Sannan na fara tunani where am I? What happened? A hankali pictures din abubuwan da suka faru suka fara yi min yawo a kaina. Mutuwar Baffa da Ummah, bankwana na da Sadauki, auren dolen da akayi min, abinda Saghir yayi min da daddare. Nayi saurin bude idona sannan nayi kokarin tashi zaune ina girgiza kaina hoping in ganni a gidan mu in ga cewa duk wannan wani mugun mafarki ne nayi. Amma wani irin azaba da naji daga kasana wadda cikin second daya ta gauraye duk sassan jikina ita tasa na koma da baya na kwanta, bana bukatar assurance, wannan ciwon ya tabbatar min cewa ba mafarki nayi ba, ya tabbatar min cewa Saghir raped me. Na runtse idona ina so hawaye yazo min amma yaki zuwa sai wata irin kuna da zuciyata take yi min. Na tuno alkawarin da Sadauki yayi min "ki saka a ranki cewa Sadauki zai kasance tare dake a koda yaushe, kome ya faru dake ko me kike yi ki saka a ranki cewa I will always be watching over you. This is my promise to you" sai nace "where were you Sadauki?" Duk sanda yayi min al茩awari yana cikawa amma ta gaza cika wannan. Na kai hannu zan taba inda nake jin tamkar anyi min tsarki da attaruhu sai naji an rike min hannu, na bude idona naga Adda Zubaida a zaune a bakin gado tana rike da hannuna, nabi dakin da kallo, bakin dakin nan ne dai da aka kawo ni jiya aka ajiye tamkar akuyar da akayi sacrificing dan a kama zaki, dakin da zakin kuma yazo ya karasa destroying rayuwata, ya karasa karbar dan sauran abinda nake rakama dashi.
Na sauke idona kan Adda zubaida da fuskarta take nuna tsantsar tausayi na. Ta kara cewa "sannu Diyam" sai naji wata muryar kuma a gefe na itama tana yi min sannu, na juya naga wata mata da muke kira Uwani, kamar kanwa take a gurin hardo dan haka kamar kaka ce a gurin mu. Na kalli jikina naga doguwar riga ce yar kanti marar hannu. Na koma na kwanta a hankali nace "Adda ki kirawo min Inna dan Allah ki ce nace dan Allah tazo ta daukeni daga gidan nan" ta girgiza kai tace "Diyam ba zan iya ba, bazan iya gatawa innarki wannan mummunan labarin ba. Da wanne zata ji. Na dai gayawa su iyayen tantirin. Su san ga abinda dansu ya aikata" Uwani tace "to ya zasu yi? Sai addu'a" Adda tace "wallahi uwani duk abinda Saghir ya zama a duniya da sa hannun mahaifansa. Basa son laifinsa, soyayyar da suke yi masa ta rufe musu ido ko me yayi basa tsawatar masa. Duk dukiyar Alhaji fa ta salwanta a hannun Saghir kullum in ya di ba ya tafi sai sun kare zai dawo, in muka yi magana ace masa ai kasuwanci yake yi bayan mun san babu wani kasuwanci da yake yi sai iskanci. Sai yanzu kuma da lokaci ya gama kurewa sannan suke son su gyara shi. Yanzu kalli uban kudin da aka kashe aka sai masa auren nan aka sai masa gidan nan aka dauki kankanuwar yarinyar nan marainiyar Allah aka bashi amma dan iskanci shine a ranar da aka kawo ta yayi mata wannan wulakancin ya tattara kayansa ya gudu" uwani tace "au wai tafiya yayi? Ina ya tafi?" Adda tace "to wa sani ne. Da assubar fari ya kira wayata wai in taho gidansa Diyam zata mutu, ina jin gaka nasan yayi tsiyar. Haka nazo na samu Diyam tana numfashi da kyar maigadi ya gaya min tun assuba yaga ya saka akwati a mota ya fice, na sake kiran wayarsa bata shiga. Ni kuwa na kira uwar da uban nace to ga abinda Saghir ya aikata nan kuma ya gudu. Alhaji yayi ta salati, in ba sa'a muka ci ba in anjima kiji shi a asibiti hawan jini ya tashi, kuma hawan jinin mun san Saghir ne ya sama masa. Ita kuma Hajiya Babba saboda tsabar son kai ina gaya mata sai ta kama rokona wai dan Allah kar in gaya wa kowa mu bar maganar a tsakanin mu, in kai Diyam asibiti amma kar in gaya wa kowa. To ni wa zan iya gayawa wannan kayan takaicin ne?".
Uwani tace "hmmm, ni ina bacci ai taje ta same ni wai dan Allah in taho gidan nan in taimaka wa Diyam, ina ji nasan an yi aika aika kenan. Kuma dan dai ya saka mata karfi ne, amma in da a hankali ya bita babu abinda zai same ta" Adda tace "to ina zai bita a hankali? In yayi haka ai bai cika dan iska ba" sai tayi tsaki "ni ban ma san yadda zanyi ba wallahi. Na daiyi mata ruwan dimi na dan gasa ta, ni ba zan iya kaita asibiti ba wallahi wannan ai abin kunya ne, in je ince musu me? This is a rape case zasu iya cewa sai na dauko police" ta sake yim tsaki "Allah wadaran naka ya lalace. Amma ai duk wanda ya sai rariya dama yasan zata zubar da ruwa". Sai kuma ta dauko waya tayi kira. "Hello, sister Asiya dan Allah in kina off ki taimaka min, wata kanwata ce akayi wa aure jiya kuma yar karama ce wallahi.....to kinsan halin maza... Dan Allah in baki address din kizo ki duba min ita" sai kuma tayi mata godiya ta katse, ta sake tsaki tace "this is very uncomfortable wallahi".
Duk maganar da suke yi ina jin su amma na rufe idona kawai dan bazan iya tankawa ba. Addu'a kawai nake jerawa a cikin zuciya ta "ya Allah duk wanda yake da hannu akan wannan wulakancin da aka yi min ya Allah ka saka min. Ya Allah tafiyar nan da Saghir yayi Allah kasa yayi hatsarin mota ya mutu kar ya dawo. Ya Allah ka hada shi da yan fashi a hanya su sabauta shi kamar yadda ya sabauta ni. Ya Allah ka saka ginin gidan da zai sauka ya fado masa cikin dare ya tarwatsa shi kamar yadda ya tarwatsa rayuwata".
Ina nan kwance matar tazo, ina jinta suka gaisa da Adda zubaida da Uwani. Sannan ta zauna kusa dani tace "amarya" na bude ido na kalleta na rufe, tace "kar ki zama raguwa mana. Tashi tsaye mu gani" nayi saurin girgiza kaina sai ta kama kafafuwana tayi bending dinsu, nayi kara saboda jin cinyoyi na nayi kamar wadda nayi frog jump, ta bude rigata tana dubawa tace "babu tear, the place is just sore kuma akwai bruises" ta rufe rigar tace "zanyi mata allurar da zata rage mata pain sannan zan rubuta muku magani ku siyo mata. Sai take amfani da ruwan dumi sosai" Adda tayi mats godiya sai ta juyo tana kallona tace "ina angon? Yazo ya mayar dani gida" ita as a joke ta fada ni kuma kalmar angon ma bata min rai tayi. Har zata fita ta juyo ta sake kallona tace "amma yarinyar nan tayi kankanta da aure wallahi Zubaida. Wai dama har yanzu fulani kuna irin wannan auren?" Ban dai ji amsar da Adda ta bata ba suka fita.
Ranar har dare Adda Zubaida tana guri na, kuma ta saka ni na shiga ruwan zafi sosai sannan kuma ta dafa min abinci mai kyau ta matsamin na ci. Sai kuma ta saka ni nayi tafiya wadda sanda ina yi ji nayi kafafuwana kamar ba'a jikina suke ba. Uwani ce ta zauna ta kwana a gurina washegari sai ga kayanta Alhaji Babba ya saka a aiko mata dasu yace ta zauna a gurina har sai Saghir ya dawo daga tafiyar da yayi. Sai da nayi kwana uku a sama ina jinyar kaina sannan na iya saukowa kasa, ina saukowa daga bene idona ya sauka akan katon hotonsa ya sha shadda army green wadda ta kara haska farar fatarsa, ya turo hular nan gaban goshi fuskarsa dauke da murmushi, sai a lokacin nayi tunanin kamar ban taba ganin murmushin sa ba. Na taka naje har gaban hoton na tsaya ina kare masa kallo sai kuma na saka hannu na ciro hoton na sauke shi kasa sannan na juya shi ya koma kallon bango.
Jikina ya warke, amma tabon zuciyata yana nan kuma banajin zai warke har abada. Saghir kuma kullum zuciyata kara tsananta tsanarsa take yi. Ko mai irin sunansa baba son inji an ambata ballantana shi. Babu sallar da zanyi ba tare da nayi addu'ar neman sakayya tsakani na dashi da duk wanda ya aura min shi ba. Kullum kuma da fargabar dawowarsa nake kwana da ita naje tashi. Ko wani kwakwkwaran motsi uwani tayi sai na firgita ballantana in naji an taba gate. Muna da kayan abinci wadanda aka kawo da sunan kayan gara, kudi kuma duk karshen sati Alhaji yana aiko mana dashi shi dai kawai burinsa in zauna a gidan. Uwani tana tare dani, kuma duk weekend su murja ko su Rumaisa sukan zo su kwanar min biyu, wannan sosai yakan rage min kewa amma a zahiri a zuciyata kuwa empty nake jin heart dina.
Kwanaki suka wuce haka satittika, sai watanni suka biyo baya har nayi wata uku a gidan Saghir amma babu shi babu alamar sa. A ranar da na cika wata ukun ne Hajiya Babba tace mu shirya muje gida mu kwana biyu. Da wuri driver yazo ya dauke mu muka tafi. Tun daga bakin gate na lura da yadda gidan ya chanja, ma'aikata sun ragu, motoci ma haka, gidan kuma yayi datti flowers sun mutu.
A main palo muka samu Hajiya Babba, har da mikewar ta tsaye ta tarye mu da fara'a "sannunku da zuwa uwani" ta jawo ni jikinta zata rungume ni sai na zame na durkusa na gaisheta, ta amsa da fara'ar ta ni kuma na mike na nufi dakin inna ta ina jin missing dinta a raina, ina jin Hajiya Babba tana cewa "Masha Allah, lallai Diyam, wannan girma haka kamar ana hura ki?"
Ina shiga na tarar da Inna tana ta murnar zuwa na itama. Na je na rungume ta tana ta dariya ta dan tura ni baya tace "Diyam kinyi girma haka? Alhamdulillah, naji dadin ganin ki sosai. Ni ina nan ina ta fargabar halin da kike ciki gashi Saghir ance yayi tafiya kasar waje business ya rike shi" na zauna akan gado ina rungume da Asma'u ina dariya. Ta zauna gefe na tana ta yi min tambayoyi game da halin da nake ciki ni kuma ina bata amsa a takaice. Tace "naso inyi miki girki tunda aka ce zaku zo, nasan kina son tuwo amma kinsan bana girki a gidan nan" na kalle ta sai na lura da yadda ta fada tayi baki bakinta duk ya bushe. Nace "inna ku ya kuke ciki? Lafiya dai ko?" Tace "hmm, lafiya lau" nayi shiru dai ina kallonta dan na fahimci ba karshen maganar ba kenan. Sai nace "Inna an saka Asma'u a makaranta kuwa?" Tace "eh an saka ta" sai ta sake shiru, ta jima kuma sannan tace "na jima inata faman bi akan zancen makarantar yarinyar nan, da kyar na samu aka saka ta amma wai ga makarantar da sauran yaran gidannan suke yi sai aka dauke ta aka saka a makarantar gwamnati. Tana kallon yaran zasu shiga mota a tafi dasu makaranta ita kuma sai dai ta tafi a kafa, har kuka sai da tayi min wai ita makarantar su siyama take so amma haka ba bata hakuri saboda babu yadda zanyi"
Naji zuciyata tana zafi nace "to Inna ke ki saka ta ata kudin mana? Ina kudin da ake samu a garejin baffa duk wannan watannin ayi amfani dashi mana a saka Asma'u a makaranta mai kyau" tace "hmmm. Diyam kenan. Wanne gareji kuma kike magana? Tun a lokacin bikin ki nayi wa Alhaji maganar gare jin kinsan me yace min?" Na girgiza kaina tace "yace garejin shi aka siyar akayi miki kayan daki" na bude baki ina kallon ta nace "garejin? Da duk motocin da suke ciki?" Eh kawai tace, na sunkuyar da kaina sannan nace "filin Sadauki fa? An bashi kayansa?" A can kasa ta amsa tace "har dashi ya sayar".
Na tashi na shiga toilet na hada kaina da kofa, rabona da in kira sunan Sadauki tun ranar da aka kaini gidan Saghir amma ni kadai na san me nake ji a zuciyata, I missed him so badly dan tunda nazo duniya ban taba yin wannan dadewar ba tare dana ganshi ba yanzu kuma ambatar sunansa ya tayar min da mikin dake cikin zuciyata. Na tuna ranar da yaje school gurina da murnarsa yake bani labarin Baffa ya saya masa fili, kuma da kudinsa daya tara masa ya siya masa his hard earned money amma wai Alhaji Babba ya siyar. Ban roki Allah sakayya bama saboda nasan tabbas zai yi maybe slowly but surely.
Bayan na dawo dakin ne uwani ta shigo suka gaisa da Inna ta kuma kawo min mangwaro na dana siya a hanya. Inna ta karba tana cewa "wannan mangwaron Diyam ai bai nuna ba aka baku shi" na karba na fara sha ina cewa "yafi dadi ai" sai ta tsaya tana kallona sannan ta juya ta kalli uwani tana girgiza kai sai naga uwani ta gyada mata kai, sai kuma suka juyo suna kallona a tare ina ta rasgar danyen mangwaro. A raina nace "su kuma wadannan menene naga suna magana da ka kamar kurame?".
Not edited
[1/31, 9:21 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman maama
Episode Thirty One : The Broken Heart
Inna ta saka na zagaya na gaishe da mutanen gidan, kuma kowa naje sai ta yi comment akan girman da nayi, ni kuma sam banga wani girma da nayi ba na dai san cewa kirjina ya kara cika amma bayan shi ban kara komai ba. Ina dawowa dakin inna na tarar an aiko min da abinci kala kala daga gurin Hajiya Babba, inna tace "da yake surukar ta tazo shine ta aiko mata da abinci, amma mu yaushe rabon da muga kwano daga dakinta" ni dai bance komai ba na fara bubbuda flasks din zaben abinda zanci, na samu wani farfesun kaji na ja gefe na fara ci. Ina cikin ci Hajiya Yalwati ta shigo, ta kalli lodin abincin tace "hmmm. Ana cewa babu kudi bayan kudin suna can a inda aka ajiye su" Inna tayi dariya tace "ke kam ba kya rabo da bakar magana".
A dakin Inna na wuni, sai da yamma ta tura ni inje in gaida Alhaji, kuma in shiga gidan Kawu Isa suma in gaishe su. Sai a lokacin na fahimci cewa ashe Alhaji Babba bashi da lafiya yana kwance. Ina dawowa sai ga sako dafa Hajiya Babba wai inje an gyara min daki a gurinta inje in sauka a can. Naki zuwa nace ace mata na gode amma a gurin Inna zan zauna, sai nayi sa'a kuma innar bata matsamin in tafi din ba.
Da daddare Inna take gaya min cewa gobe ne zata fita daga takaba, ashe shine dalilin da yasa aka dauko ni. Sai na tambayeta "Mama zata zo goben?" Inna tace "inajin zata zo, wani abun ne?" Nace "dama wata tambaya nake so inyi mata" ta zauna a kusa dani tace "tambayar me fa?" Sai na fara jujjuya hannuna ina feeling uncomfortable, ni ban saba irin wannan maganar da Inna ba dama Ummah ce da sauki. Sai data sake tambayata sannan nace "so na ke inji, wai dama in mutum yayi aure sai ya daina period? Dama matan aure basayi?" Sai ta tashi ta bude wardrobe kamar mai dauko wani abu, ta jingina kanta da kofar tace "yaushe rabon da kiyi?" Nace "tun kafin.....tun kafin biki" tace "wata uku kenan ko?" Na ce "eh" tace "matan aure sunayi Diyam, sai dai in matar aure tana da ciki ne bata yi" naji kaina ya kulle nace "ciki?" Sai kawai ta juyo tana kallo na, na dan yi shiru ina tunanin kalmar ciki sai kuma lokaci daya naji tamkar an ciro zuciyata an buga ta da kasa ta tarwatse. Nayi saurin rike kirjina na zamo daga kan gadon na fado kasa, a hankali na fara kiran innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Inna ta taho da sauri ta rike ni tana kokarin daga ni amma na dunkule a guri daya danji nake yi tamkar idan na mike zuciyata zata fado daga kirjina. Amma hawaye yaki zuwa idona, kalmar ciki ce kawai take yawo a kaina, wai ciki nake dashi ni Diyam kuma cikin ma wai na Saghir wannan wacce irin jarabawa ce, wannan wacce irin rayuwa ce. Har yanzu banyi accepting Saghir a matsayin miji na ba ballantana kuma in karbe shi a matsayin uban yayana. Inna ta rike ni tana cewa "haba Diyam, menene hakan kuma daga maganar ciki? Ciki yar kyautar Allah ne in aka same shi murna ya kamata ayi a kuma godewa Allah" sai na kifa kaina a jikinta ina jan numfashi da kyar. Na rufe ido na ina tunano fuskar Sadauki. Wannan cikin tamkar yayi sealing aurena da Saghir ne, tamkar ya tabbatar da rabuwa ta da Sadauki kenan.
Ranar yadda naga rana haka naga dare. Ina jin ko lokacin da aka daura min aure da Saghir ban shiga irin wannan tashin hankalin ba. Sai bayan nayi salllah asuba sannan nayi bacci dan haka har mutane suka fara zuwa yiwa Inna gaisuwa da kuma taya ta murnar fita daga takaba ban tashi ba, dagabaya ma dana farka sai na yi kwanciya ta har saida naji muryar Mama sannan na tashi na gaisheta. Ta bini da kallo kamar mai accessing dina, wannan yasa na koma na kwanta na lulluba dan ji nake yi kamar duk wanda ya ganni yana iya hango cikin jikina.
Ina kwance Mama ta shigo tace "Diyam taso ki raka ni unguwa" da sauri na mike ina straightening hijab dina dan ba karamin gajiya nayi da gidan da duk mutanen da ke cikinsa ba. Muna shiga muka shiga motar da tazo da ita, Mukhtar yana ja muka tafi sai na gan mu munzo wani asibiti, naji gabana ya fadi ina tuna ranar da aka kaini asibiti naga gawar Baffa, ranar da rayuwata ta tarwatse. Na tambayeta "Mama waye bashi da lafiya?" Tace "ba kowa, ke na kawo kiga likita" sai na sunkuyar da kaina a raina ina cewa Inna ta gaya mata kenan. Da yake asibitin kudi ne dan haka muna zuwa aka dauki jini na for a confirmation test, mu ka zauna jira sai kuma aka kira mu dakin likita, muka shiga suka gaisa da Mama sannan nima na gaishe shi ya dauko result din yana kallona yace "Halima Usman Kollere?" Na gyada masa kai, yace "how old are you?" Nace "14" sai naji kalmar 14 din tana burning a kirjina. Ya girgiza kai yana kallon Mama yace "how comes? Yarki ce?" Ta gyada kai tace "yar yaya tace, mahaifinta ya rasu shine yan uwansa suka aurar da ita ga dansu" ya girgiza kai yana kallona sannan yace "well, she is pregnant. Zamuyi scanning dai muga wata nawa ne sannan muga in ya shiga yadda ya kamata, za kuma mu duba lafiyar mahaifarta in zata iya daukar nauyin cikin" nayi sauri dago kai ina kallon doctor din, da rawar murya nace "doctor please ka cire cikin nan bana so" Mama tace "kul Diyam, kar in sake jin kince ba kyason abinda yake cikin ki. Allah ne fa ya baki ajjiya, ba naki bane ba na Allah ne kuma shi kadai zai karbi kayansa a lokacin da yake ganin ya dace".
Muka je na kwanta akan gado Mama tana rike da hannuna da yake rawa saboda tsoro. Doctor ya zuba min wani abu mai sanyi a mara ta sannan ya fara goga wata roba akai yana kallon screen din gabansa, can sai naji yace "wow wow." Ya juyo yana kallon Mama yace "we are having twins here".
Bayan an gama scanning din mun koma mun zauna yace "gaskiyar magana yarinyar nan tayi kankanta, bayan rashin shekaru gashi kuma tana da kankantar jiki, she can carry the pregnancy but I strongly suggest that kar a barta tayi labor, musamman tunda she is carrying multiple a shawarce da ta kai around 36 weeks ku kawo ta a cire babies din saboda lafiyar ta" Mama ta gyada kai da sauri tace "insha Allah doctor hakan za'ayi" ya tura mu mukayi sauran tests sannan ya rubuta mana drugs ya sallame mu.
Hankalina idan yayi dubu to duk ya tashi, dan tunda doctor yace twins ne bankara magana ba dan in nayi ma inajin muryar ba zata fita ba. Wato ba daya ba, 拼a拼an Saghir guda biyu ne a cikina. Har muka zo gida bance komai ba ina dai jin Mama tana tayi min bayanai da yadda zan kula da kaina da abincin da ya dace in ke ci, ni dai na jingina jsina da kofar mota kawai na rufe idona.
Muna packing su Salma suna fitowa ita da Aysha zasu tafi gidajen su, bana son magana dan haka ko kallon su banyi ba nazo zan wuce ta kusa dasu Salma tace "oh su Diyam manya, kamar ba itace nan take ta koke koke ba wai bata son auren hamma amma gata nan harda ciki. Ni ko zanso inga yadda akayi cikin nan". Sai suka kyalkyale da dariya. Har na taka step zan shiga palo sai na tsaya ina juya kai, it is hardly a gaya min magana inyi shiru and this is not going to be the first time. Na juya na sha gabanta nace "yes bana son yayanki kuma har duniya ta nade ba zan so shi ba ko da kuwa zan haifa masa duk mutanen da suke duniyar nan. Ni ma kuma zanso ace kinga yadda akayi wannan cikin dan a lokacin ne zaki tabbatar cewa yayanku is nothing but a monster, a big for nothing monster". Mama tazo da sauri ta jani muka wuce, amma naji dadi a raina.
Mu da muka zo da niyyar kwana biyu sai da mukayi sati. A cikin satin na fahimci abubuwa da yawa, na farko shine arzikin Alhaji Babba ya ragu sosai, dan naji ana cewa yanzu shagunan sa na kantin kwari ne kadai suke functioning. Abu na biyu Inna tana cikin damuwa game da negligence da take fuskanta a gidan, babu wanda yake daukan abinsa ya bata dan zumunci sai dai idan ta roka, hatta sabulun wanka da wanki sai ta roka za'a bata.
Da safiyar ranar da zamu tafi Inna ta dauko wasu kudi ta bude hannu na ta saka min, nace "kudin menene wannan?" Tace "kudin sadakin kine" na kalli kudin ina jujjuya sannan nace "me zanyi dasu?" Sai tayi murmushi tace "ki sayi wani abu dasu, duk abinda kike so" a hankali nace "ni babu abinda nake so Inna, ni yanzu babu abinda nake tunanin zai saka ni farin ciki, Sadauki shine farin ciki na kuma a yanzu bana jin zan kuma ganinsa har abada" sai na bude hannunta na saka mata kudin nace "ki karbi wannan kudin inna dan Allah ki dauki Asma'u ku bar gidan nan. Ki koms gida ki samo masu rabon gado su fitar wa da Ummah gadonta a gidan mu ki danka a hannun yaya ladi ko Sadauki. Misali in aka fitar masu da dakunan Ummah sai su fitar da kofa daban. Dakunan ki kuma zaki iya saka yan haya a ciki ke kuma sai ki zauna a dakunan Baffa. Kinga kudin hayar zaki iya wani abu dashi sannan kuma zaki samu security yafi ki zauna ke kadai. Kudin nan kuma dubu hamsin sai ki kama sana'a dasu, idan ba zasu isa ba sai ki siyar da kayan dakin ki ko na dakin Baffa ki kara. A yanzu abinda zai sani farin ciki inna shine in ganku a farin ciki" sai naga hawaye yana fita daga idonta, tayi sauri ta goge tace "Diyam. Ni a tunani na abinda nayi miki shine dai dai, amma na rasa me yasa na kasa jin farin ciki a zuciya ta" sai ta dawo min da kudin hannuna tace "bazan karbi sadakin ki ba Diyam. Ki ajiye su, wata rana zasu yi miki amfani" nace "to Inna zaki tafi din?" Nan ma sai ta girgiza kai tace "ba zaki gane ba Diyam".
Sai nayi shiru ina kallonta, sai nayi realizing wani abu, ba wai gidan Alhaji Babba ne bata son bari ba but she is not strong enough to stand on her own, tana bukatar shoulder da zata jingina da ita. Na tuna cewa a kauye aka haife ta a can kuma ta girma ba tare da tayi karatun boko ba, sannan aka aura mata Baffa ya raho da ita kano ya ajiye ta a gida. Tunda na taso ban taba ganin inna da kawa ba, babu wanda ta sani sai Mama da Aunty Hafsa sune kawayenta, in dai Inna ta fita unguwa to in ba gidan su ba to gidan Alhaji Babba ko kawu Isa, gaba daya rayuwarta tayi revolving ne around them. Wannan ne ya kara banbanta ta da Ummah tunda ita Ummah tayi karatu a hannun Alhaji Bukar dan haka ta waye sosai tayi kawaye. Wannan yasa yanzu it will be hard for Inna ta tsaya da kafafuwanta, ko kuma tayi challenging Alhaji Babba. Maybe nan gaba.
A ranar da muka koma gida ni da uwani sai naji gidan yayi min wani iri, kuma nasan hakan yana da dangantaka da sanin da nayi cewa ina da ciki, twins, cikin Saghir. Da dare sai na bude balcony din da yake hade da palon sama. Na tsaya na lunshe idona ina jin dadin iskar da take kadawa, na bude idona naga sky ta cika da stars ga wata ya zama full. A hankali nace "Sadauki where are you?" Sai na tuno abinda ya taba fadamin "You Are The Only Star In My Sky" na shafa marata ina tunanin babies din da suke ciki amma sam banji wata soyayya tasu a raina ba. I can give anything to have them taken away from me. Da Sadauki na shirya haihuwa, dashi na shirya rayuwar aure. Da Sadauki nayi wannan plan din, dashi na shirya zanyi rayuwar aure har in samu ciki har in haifa mana ya'ya. Mace mukayi fatan zamu samu daga farko sai mu saka mata subay'a sunan yar tsana ta, daga nan sai mu haifi namiji mu saka masa sunan Baffa mu kira shi da Junior.......... Ya Allah take my life please, ya Allah end my suffering please. Sai na rike railers din gurin na durkusa ina kuka a hankali. The first tears da nayi shading tun first night dina a gidan.
[2/2, 8:57 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Two and Three : The Lost Treasure 1 & 2
Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na tashi daga gurin na dawo palo, sai naji zuciyata tayi min dadi dan at least na dan samu relief na zafin da take yi min. Na zauna a kujera ina karewa kayan gurin kallo, kayan da aka ce an siya min with my father's life time earnings. Sai na tuno da yadda kullum Baffa da Sadauki suke fita tun safe suna aiki a gareji basa dawowa sai magrib basu da weekend basu da public holidays kullum cikin aiki suke. Na hango yadda Sadauki yake dawowa a gajiye kayansa duk bakin mai ya bata su inyi tayi masa dariya. Na tuna sanda yake bani labarin filinsa "anan zan gina mana gidan mu ni dake Diyam". Na lunshe idona a hankali nace "Allah ya isa".
Washegari su Rumaisa suka zo, a lokacin ne suke gaya min cewa anyi hutun first term, sai na samu kaina da tambayar kaina 'ko yaushe za'a saka ni a makarantar da akayi min alkawari? Nasan in nayi magana ma yanzu cewa za'ayi ga ciki kuma wacce makaranta zan shiga sai dai in bari sai na haihu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar min cikin kunci da bacin rai, ga kuma laulayi daya sauko min a lokaci daya, bani da damar inci abinci sai na amayar dashi. Baba son kamshi kwata kwata kona turare ko na sabulu, ga kadaici. Inda Allah ya taimake ni ina tare da uwani wadda take taimaka min sosai dan kusan duk aiyukan gidan ita take yi, sannan tayi min girkin duk abinda nace inaso, wani lokacin kuma ina gama ci zan shiga toilet in amayar dashi gaba daya sannan in dawo ince mata wani nakeso daban. Uwani tana daga cikin mutanen da bazan taba manta alkairin su ba.
Ciki na yana wata biyar, amma in ka ganshi zaka dauka yayi bakwai saboda girma. Lokacin kuma laulayi na yayi sauki sosai. Sannan kuma a lokacin ne muka sake komawa scanning ga mamaki na muna hanya sai ga wayar Alhaji Babba yana cewa da Mama wai a duba masa sex din babies din. Ina jin Mama tana mita "shi Alhaji Babba wai har yanzu ba zai dauki ishara akan wannan son yaya mazan nasa ba? Shin Saghir ba zai zamar masa darasi ba?" Ni dai bance komai ba amma a zuciya ta ina ta addu'a "Allah kasa mata ne, ya Allah kasa mata ne" amma muna zuwa doctor ya duba ya kalleni yace "congratulations, you are having twin boys" na runtse idona, it is official, bani da sa'a a rayuwa ta. Sai kuma nayi sauri nayi istigfari akan sabon da nayi.
Tun a asibitin Mama ta kira Alhaji Babba tayi masa albishir, ai kuwa daga nan direct gidansa yace a kawo ni ya ganni. Muna zuwa muka wuce part dinsa muka same shi zaune a palo shida Hajiya Babba muka gaishe su, yace "Diyam ba dan bani da isassun kuda de ba da kasar waje zan fita dake ki haihu a can. Amma yanzu ma ina saka ran wasu kudade, indai sun samu kafin lokacin haihuwar ki to duk kasar da kike so nan za'a kaiki ki haihu" Hajiya Babba tana ta washe baki tayi min godiya ni kuwa ko ci kanka bance masa ba. Sai ya dauko wasu kudi a envelope ya miko min yace "nasan masu ciki da kwadayi. Gashi kya ringa siyan abinda kike so" nayi godiya har zamu tashi sai kyma ya tambaye ni "kuna waya da mijinki kuwa?" Na girgiza masa kai da sauri ina mamakin tambayar, ni da bani da waya kuma banma san number din Saghir ta yaya zamuyi waya dashi? Amma sai na fahimci wani abu, suma kansu basu san inda yake ba so suke suji koni na sani.
A gurguje muka shiga muka gaishe da Inna, sai na ajiye mata kudin da Alhaji Babba ya bani muka tafi.
A ranar da daddare har na kwanta sai naji yunwa, kuma uwani ta riga tayi baccinta dan haka dole na tashi da uban cikina na sauko kasa. Na karanto adduoi na kunna fitilar palo sannan na shiga kitchen na dauko cornflakes na fara hadawa kawai sai jikina ya bani ana kallona. Nayi saurin juyawa na kalli bakin kofa kawai sai idona ya sauka akan Saghir, ya harde hannaye a kirji ya jingina da kofa ya zuba min ido. Cup din hannuna ya zame ya fadi kasa, na ruga a firgice zuwa back door din kitchen din na bude jikina yana karkarwa na fice daga gidan na rufe kofar ta waje, ban tsaya anan bama sai na kara mai sai dana dangane da katangar gidan sannan na tsaya na toshe bakina da hannuna ina numfashi sama sama, na jima ban tsorata ba irin ranar. Sai da hankali na ya dawo jikina sannan na fahimci a inda nake sai kuma wani sabon tsoron ya sake shigata na koma wajen building din da sauri, na leka tagar kitchen sai naga babu kowa, na zagaya ta gaban gidan na leka palo shima babu kowa sannan babu mota wannan yasa na sauke ajjiyar zuciya. Wato mutumin nan har ya fara yi min gizo kenan ko?
Duk da tsoratar da nayi saboda abu irin na mai ciki sai dana karasa hada cornflakes dina sannan na koma sama na sha a daki na wanke bakina nayi addu'a nayi kwanciya ta a raina ina cewa "aniyar Saghir ta koma kansa". Dasafe kamar kullum bayan na gama karatu na da azkar dina na tashi uwani muka fara gyaran gida tare, muna yi muna hirarrakin mu har muka gama da sama muka dauko kasa, dama mun saba indai mukayi wannan saukowar kuma to sai dare zamu sake hawa dan anan kasa muke wuni. Tana cikin mopping ninkuma ina goge tv kawai sai mukaji motsi kamar ana saukowa daga sama, muka kasa kunne a tare sai kuwa muka tabbatar lallai saukowar ake yi dan haka muka fa ee猫ra rige rigen neman gurin buya sai kawai ga Saghir ya sauko. Yaci kwalliya kamar kullum, sai kamshin turare yake yi, nayi sauri na buya a bayan uwani ina jin tsanarsa tana karuwa a raina. Kallo daya yayi mana daga ni har uwanin ya cigaba da tafiyar sa zai fita daga palon, sai kuma naga ya tsaya ya juyo yana kallona, amma vani yake kallo ba cikin jikina yake kallo, na saka hannayena na rufe cikin dasu, sai ya juyo ya doso inda nake tsaye yazo daf dani ya tsaya, ya kalli cikin yace "meye wannan?" Na tattaro duk sauran rashin kunyar da take tare dani nace "oho, nima bansan menene ba" muka tsaya muna kallon kallo, ya tsare ni da ido ni kuma naki cire nawa idon daga cikin nasa. Uwani tana gefe tace "kyautar Allah ce, kyautar da babu wanda zai baka sai shi. Sai a karba kuma a gode masa" bai kyalleta ba yace min "so this is your plan ko? Wannan shine abinda kika shirya dan ki zauna a gidan nan?" Na girgiza kaina nace "believe me, a zuciyata bayan kiyayyarka babu kiyayyar abinda tafi karfi irin ta abinda yake ciki na, and one day, ranar dana haifesu a ranar zan baka kayanka and then it will be my turn to run away" ya hade rai yace "su?" Na daga gira daya nace "yes, su biyu ne" ya sake kallon cikin sai kuma ya kalleni yace "Allah ya kaimu. Ranar da zaki bani su din" ya juya kamar zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace "ohhh, and I didn't run away kamar wani marar gaskiya, tafiya ce ta same ni" sai daya fita daga palon sannan na sauke ajjiyar zuciya saboda tunda ya tsaya kusa dani na rike numfashi na saboda tsoro da kuma kamshin turarensa da yake kokarin sakani amai.
Uwani ta fara jera min wa'azi. Ba'a yiwa miji haka, namiji shi tarairayarsa akeyi da kalamai masu dadi, hakan shine zai siya miki martaba a idon shi. Nace "shi kuma fa, menene zai siya masa martaba a nawa idon?" Ta bini da kallo kawai ta rasa amsar bani. Na leka ta window ina hangoshi har ya je gate, naga yayi magana da mai gadi sai kuma ya fita daga gidan a kafa. A raina nace "ina motar?".
Bai dawo ba sai dare, ina kitchen ina wanke wanke naji shigowar sa ya haye sama ya shiga dakinsa. Sai ga uwani ta shigo kitchen din tace min "mijinki ya dawo, maza ki zuba abinci ki kai masa" na bita da kallo kamar wadda tayi sa蓳o. Taga bani da niyya sai ta zuba ta dora a tray tace inje in kai masa. Na dauka kamar gaske na tafi, naje kofar dakinsa na ajiye dai dai bakin kofa a raina ina addu'ar yana fitowa yayi tuntube dashi ya bata kayansa. Sai na shiga daki na na dan zauna kadan dan kar taga na koma da wuri sannan na dawo gurinta.
Haka muka kasance for about a week. Ko magana ta fatar baki bata hadamu kuma kullum d sassafe ya ke fita sannan ya dawo da dare, kuma kullum sai uwani ta saka ni na kai masa abinci ni kuma sai in ajiye a bakin kof inyi tafiya ta, ranar nan naje ina ajiye abincin sai ya bude kofar, na maze nayi kamar wucewa nazo yi shi kuma ya hade rai yace "ke, zonan" na tsaya ina kallonsa yace "ubanwa kike jerawa abinci a bakin kofa kamar dakin bera? Nan an gaya miki gurin ajjiyar abinci ne?" Nayi shiru still ina kallonshi. Yayi tsaki yace "ga tsaurin ido kuwa, anayi mata magana tana tsatstsare mutane da ido. Ki dauka ki shigo dashi ciki nace" na dauka nazo na wuce ta gabansa na shiga, first time dana shiga dakinsa, naga wani table a gefe na dora tray din akai ina lura da irin dattin da dakin yayi, kaya a barbaje har kan gado, takeaway packs sun cika waste basket. Na dauke kaina zan fita ya zauna a bakin gado yace "zuba min abincin" naji raina ya fara baci, wata zuciyar tana gaya min in zuba masa abincin aka in fita da gudu. Na bude na zuba masa shinkafa a plate na dauko miya zan zuba yace "mayar, bana cin shinkafa" na daga kafada na mayar da ita na juye na dauki tray na zanyi gaba yace "menene a wancan bowl din?" Na bata rai nace kwadon zogale ne, ni nayi zanci shine uwani tace in zuba maka wai ko zaka ci" sai naga ya dauke kai yana murmushi, sai kuma ya hade rai ya miko hannu yace "bani" na ajiye tray din na dauki bowl din na mika masa. Charaf ya kama hannuna, na saki bowl din ya fadi akan carpet zogalen ya zube, na fara kokawar kwace hannuna da dukkan karfina amma ko zegau, kuma wai hannu daya fa kawai ya saka ya rike ni. Sai da na gaji da kokawa ta sannan na tsaya ina mayar da numfashi ido cike da hawaye, ya gyara zamansa yace "kin gama kokawar?" Na gyada kaina, yace "good, then listen to me. Am sorry for what I did to you ranar nan. I was drunk" nayi noticing yadda ya fadi drunk din as if it is a normal thing, ya cigaba "bama zan iya tuna details of what happened ba, nasan dai kinyi min rashin kunya kuma ke shine problem dinki baki da kunya, I remember you even threatened me with a knife. But har cikin raina ni banyi niyyar tabaki ba saboda kamar yadda na fada wa Alhaji amma yaki yarda, kinyi min kankanta. Yanzu kin yafe min?" Nayi saurin girgiza kaina, yayi ajjiyar zuciya yace "maybe later. But look on the bright side, babies, har guda biyu. Ni da bansa ran ko daya ba sai gani da guda biyu. Alhaji yace min boys ne ko?" Ban bashi amsa ba sai yayi dariya, the first time da naga yayi dariya, yace "twin boys, in kika haifi twins din nan kin gama biyawa Alhaji bukatar sa ta duniya, you will be his second favorite person bayan ni" ya saki hannuna nayi saurin ja da baya ina goggoge hannun da hijab dina. Yace "Hajiya tace min SC za'ayi miki at 36 weeks ko?" Na dauke kaina nayi hanyar waje yace "how many weeks ne yanzu cikin?" Sai dana bude kofa sannan na juyo nace "oho, ban sani ba, amma ai zaka iya lissafawa saboda kai kafi kowa sanin ranar da akayi cikin" na juya da sauri na fita ina jinsa yana cewa "still with the rashin kunya ko?"
Tun daga ranar ya dan fara kulani, misali in zai fita zai neme ni yace min ya fita, in ya dawo kuma uwani zata saka lallai in kai masa abinci. A lokacin ne nake lura cewa most of the times a buge yake dawowa gida, ni kuma dana ji wannan warin a tare dashi zan gudu. Duk lokacin zuwa asibiti na, Mama ce take zuwa da kanta ta dauke ni muje bata taba fashi ba, kullum kuma tana gaya min "dan lafiyar ki nake yin wannan abin Diyam ba wai dan yayan cikin ki ba, in an haife su dole zan so su saboda jikoki nane amma a yanzu lafiyar ki tafi su muhimmanci". Alhaji Babba kuwa lokuta da dama da kansa yake zuwa har gida wai yazo ganina ya duba lafiya ta, Hajiya kuma kullum tana cikin aiko min da kayayyakin kwalama wai duk cikin nuna kulawa ne, ni kuwa nasan bani suke yiwa ba abin cikina suke yiwa. Sai na samu kaina da tunanin inba sa'a naci ba yadda suka lalata Saghir haka zasuyi wa duk abinda zan haifa, ni kuwa I can't even begin to imagine myself as a mother of yaya masu halayyar Saghir har guda biyu. A haka har cikina ya kai 32 weeks, and that's when it happens.
Ranar wata laraba, Saghir ya dawo kamar yadda ya saba dawowa ni kuma na zuba abinci na kai masa kamar kullum. Ina shiga dakin naji wannan familiar warin dan haka na tabbatar yau ma a bugensa yake. Na ganshi a kwance daga shi sai singlet da gajeren wando yayi dai dai akan gado, na lallaba na ajiye abincin na juya zan fita kenan sai ganinsa nayi a gaba na yana kallona kasa kasa fuskarsa da murmushi, sannan cikin irin voice din da bazan manta ba yace "wai ke kullum sai ki shigo min daki kina wani lallabawa a tsorace kamar dakin dodo, ko ni dodo ne?" Ban bashi amsa ba na chanja hanya sai naji ya damko hannuna ta cikin hijab dina ya dawo dani baya, na fara kokarin ture shi nace "don't touch me" ya maimaita cikin kwaikwayon muryata "don't touch me, shikenan dai kullum don't touch me sai kace wani abin tabawar ne a jikin nata, bayan bata da komai haka aka kawo ta gidan nan, kirjin ma sai dana mammatso su sannan suka fito" naji hawaye yana bin fuskata, na ture shi na bude kofa da sauri na fita palo amma kafin inyi nisa ya kuma kamo hijab dina da karfi ya finciko ni baya, naji bayana ya amsa da karfi na saki kara. Ya zare hijab din yana cewa "ke dai kiyi ta yawo da wannan dogon abin, ke ko zafi ba kya ji?" Na sakar masa hijab din na durkusa a kasa saboda bayana da naji ya kasa mikewa straight, Sai kuma idonsa ya sauka kan dogon gashina da ya zubo har saman bayana ya bude ido yace "well well well, what do we have here. I always have a thing for mata masu dogon gashi" sai ya nannade hannunsa a cikin gashina ya dago ni tsaye da gashin, naji tamkar fatar kan gabaki daya yake cirewa, ba shiri na saki bayana dana rike na kama kaina na saki kara. Ban kuma jin abinda yake cewa ba saboda azaba sai jin muryar uwani nayi tana cewa "Saghir baka da hankali? Ka sake ta mana, baka ganin halin da take ciki?" Sai kuma ya sake ni, uwani tayi saurin rike ni muka bishi da kallo ya tafi dakinsa yana harhada hanya.
Uwani ta kama ni ta kaini dakina tana yi min sannu. Na durkusa a kasa inajin kaina kamar zai tsage da baya na shima ya rike. Sai naga ta dauko wayarta tana waya amma bana jin me take cewa na dai ji ta ambaci sunana da sunan Saghir. Daga nan baccin azaba ya dauke ni. Sanda na farka cikin dare ni kadai ce a dakin a kwance a kan gado, wani irin mugun ciwon baya ne ya tashe ni nakasa mikewa ma tsaye ballantana in fito in nemi taimakon wani, haka nayi ta murkususu ni kadai akan gado ina karanto duk adduoin da suka zo bakina. Ban samu bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah.
Sai da gari ya fara haske sannan na lallaba na tashi nayi sallah, nayi azkar sannan na kuma kwanciya akan sallayar na sake komawa wani baccin. Lokacin dana sake farkawa sai naji ciwon kan ya lafa sosai sai bayan ne har yanzu amma shima ba kamar cikin dare ba. Na fito na duba agogo naga 20:32, nasan already Saghir ya fita dan haka na sauko kasa gurin uwani. A zaune na same ta da jakar kayanta a gabanta ga mayafinta a kusa da ita. Na tsaya ina kallon ta nace "wannan kayan kuma fa? Wanki zaki bayar?" Tace min "zauna Diyam" na zauna a kusa da ita tace "dazu da sassafe mijinki ya shigo nan, yazo ya same ni ya kare min zagi tas wai ni munafuka ce na hada shi da mahaifiyarsa. Yace min in fita in bar masa gidan sa kar ya dawo ya same ni" na mike tsaye zan fara masifa "lallai ma Saghir din nan, yanzu ke din zai yiwa wannan rashin kunyar?" Tace "ni dai abinda nasan nayi shine jiya da naga yana neman halaka ki na kira uwarsa, ni kuma abinda yasa na kira ta shine naga halin da kike ciki wai ko za'a zo a kaiki asibiti ko kuma a turo ma'aikaciyar lafiya ta duba ki, ni bansan me ta kira shi tace masa ba shine yazo yayi min wannan diban albarkar" nace "kira hajiyan to sai mu gaya mata abinda yayi, ita zata san abinda zata yi akai" tace "hmmm. Ai yana fita ita din na kirawo, tunda tun farko ai ita ce tace inzo in zauna din, amma dana gaya mata abinda yace sai cewa tayi in tafi can gidan kawai tunda yace baya son zama na anan din. Tace zata samo wata ta turo miki take kula dake" naji raina ya kara baci, hawaye yana bin fuskata nace "wannan wacce irin rayuwa ce, yanzu ace mutum babu yadda za'ayi yayi abu ba daidai ba a gyara masa sai ya zama laifi. Yanzu jiyan da ace ba kyanan Allah ne kadai yasan abinda zaiyi min. Ni ba zan zauna ba uwani, kina tafiya nima binki zanyi, bazan zan zauna ya kashe ni ba" uwani tace "a'a, ba zaki bini ba Diyam, ina tafiya dake cewa za'ayi nazo na kashe miki aure. Ni dai yanzu in naje zan gayawa mahaifiyar ki halin da kike ciki, itace take da hakkin zuwa ta tafi dake".
Ina ji ina gani uwani ta dauki jakarta ta fita, na raka ta har bakin gate ina hawaye tayi sallama da mai gadi wanda har sun saba dashi sosai, na tsaya ina kallonta har tayi nisa sannan na dawo cikin gida na rufe kofa. Na kwanta akan kujera ina tunanin wannan wacce irin kaddara ce ta hau kaina, wacce irin tarbiyya Saghir zai yiwa yayan mu bayan shi kansa ba tarbiyyar ce dashi ba? Ina nan kwance dai har yunwa ta kamani na tashi na shiga kitchen sai na tarar ashe uwani ta ajiye min dumamen tuwon jiya dan tasan ina so. Na dauko na dawo palo na zauna ina ci kawai naji ciwon bayan ya dawo and this time yafi na dare karfi. Yayi ya lafa ya sake dawowa kamar bayana zai rabu da jikina. A haka azahar ta same ni, la'asar ma tazo, sai dari ya fara duhu. A lokacin ciwon bayan ya hade har da cikina da mara ta. Na lallaba na koma sama ina tunanin wannan wanne irin ciwo ne haka tunda ni dai cikina ai bai isa haihuwa ba ballantana inyi tunanin ko nakuda ce. Bayan nayi sallar magrib ne kuma sai na kasa kofa tashi daga kan sallaya ta saboda azabar ciwo, ban taba addu'ar ganin Saghir ba sai a wannan rana na ringa addu'ar Allah yasa ya dawo da wuri ya kaini asibiti, wannan wanne irin ciwo ne haka? Ga yunwa dan tun tuwon safe ban kuma cin komai ba, ga babu waya a hannuna ballantana in kira in nemi taimako.
Shiru shiru babu Saghir babu labarin sa tun ina duba agogo har na daina. Sai kuma kamar daga sama naji tsayuwar motarsa, na daddafa da kyar na mike amma ina tsayuwa sai naji kamar an bude famfo ruwa yana fita ta kasana, nace na shiga uku ni Diyam fitsari nake a tsaye ko me?
Tun daga yanayin yadda yayi packing nasan cewa yau ma ba kalau yake ba, ina jin motsin shigowar sa palo sannan naji ya hawo sama, sai dai banji ya bude dakinsa ba. Na jima ina tattaro karfina sannan na fara bin bango na fita daga dakin. A palon sama na same shi, ya cire rigarsa ya jefar a gefe, ya kure ac ya kwanta a kan carpet. Da rarrafe na karasa inda yake nayi masa magana "Saghir, Saghir" shiru, na dan jijjiga shi, nan ma babu alamar motsi a tare dashi. Da daga hannunsa naji ya saki. Banbancinsa da gawa shine kawai shi yana numfashi. Na fara kuka "hamma Saghir ka taimaka min zan mutu, wayyo Sadauki" amma da wani ciwon ya sake tahowa sai na nemi kukan na rasa. Lallai wani abin yafi gaban kuka.
Na tuna da maigadi a waje dan haka nayi kokarin ganin ko zan iya zuwa gurinsa ya samo min taimako, duk da cewa ba makota ne damu ba. Amma tashi ya gagare ni, kamar kafafuwana sun daina aiki. Na durkusa na kankame kujera yayinda wani irin nishi wanda bazan iya rikewa ba tazo min, ina ji har dan jaririn ya fito daga jikina, na sauke wani numfashi jikina sharkaf da gumi duk da acn da take palon. Na saka hannu na dauko shi, the smallest most cutest baby dana taba gani a rayuwata. Komai nasa irin na babansa ne except dan karamin 蓷agaggen bakin sa da yake irin nawa, nayi murmushi ina jin sonsa for the first time yana huda zuciyata. But baya kuka, baya numfashi, aren't babies suppose to cry in aka haife su? Na jijjiga shi, "wake up little soldier" shiru, na dora bakina akan nasa ina hura masa iska irin yadda naga anayi a film amma shiru, na saka fingers dina guda biyu ina danna masa little kirjinsa shima shiru.
Wani ciwon ne ya sake dawo min, babu shiri na jawo rigar Saghir da ya ajiye na dora babyn akai na koma fagen fama har na haifi dan uwansa. Na dauko shi shima ina kallon fuskarsa, kamarsu daya da dan uwansa kamar an tsaga kara. Na dan jijjiga shi da dan saurin karfin daya rage min sai naga yayi motsi ya danyi kuka kadan sai kuma yayi shiru. Na ajiye shi kusa da dan uwansa ina feeling very dizzy, a lokacin ne na lura da jinin da yake malala akan tiles din palon. Na koma na kwanta kusa dasu a ina kallonsu. And it occurred to me that karshen rayuwata kenan, sai naji dadi saboda ina ganin nayi shahada na samu kyakykyawan karshe, my only regret a lokacin shine mutuwa without seeing Sadauki again.
Not edited
[2/3, 9:48 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Four : My Savior 2
Bansani ba ko bacci nayi ko kuma suma nayi, amma cikin either baccin ko suman ne nayi mafarki ina tsaye a cikin cincirindon mutane hannayena biyu a rike da babies dina, hawaye yana fita a idona ina kwalla kiran neman taimako amma kowa yana ta harkokin gabansa babu wanda yako kallo inda nake, can sai ga Sadauki yana kutso kai ta cikin mutanen yana tahowa inda nake amma yawan mutanen da suke gurin ya saka yakasa karasowa sai ya tsaya daga nesa yana miko min hannu, kawai sai na zubar da babies din hannuna na kama hannunsa amma ina kamawa sai ya bace ya barni ni kadai a tsakiyar mutane. Na kwalla masa kira "Sadauki! Sadauki!! Sadauki!!!" Amma bai dawo ba.
Ji nayi ana rirrike ni ana 茩o茩arin kwantar dani yayinda ni kuma nake ta yunkuri ina kiran Sadauki. Na bude idona naga nurses suna tura ni akan gadon marasa lafiya, ga Inna tana biye dasu a baya zani a hannu har suka tura ni wani daki suka rufe kofa, sai kuma naji shigar allura a hannu na, daga nan na koma baccin ko suman ne ban sani ba.
Sanda na kuma farkawa I was feeling much better, dan a hankali na bude idona na sauke su akan ledar ruwan da take sakale a jikin karfe sannan nabi tube din da ya taho daga kasanta da kallo har zuwa inda ruwan yake shiga jikina. Na fara karewa dakin kallo ina kokarin recalling abinda ya kawo ni nan. Idona ya sauka akan Inna da take zaune rashe rashe a dandaryar kasa duk kuwa da cewa akwai kujera a dakin. Kuka take da iyakacin karfinta, sai na tambayi kaina "kukan me take yi?". Abinda na fara tunawa shine kyakykyawar fuskar jarirai na, sai naji wani relief yazo min cewa ban mutu ba at least zan sake ganin su, zan dauko su in rungume su a jikina. Sai naji xewa yanzu na sami wani source of happiness din bayan Sadauki.
Nace "Inna" sai naga ta juyo da sauri gurina tana share hawayenta da gyalenta, tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna wanda babu ruwan a jiki "sannu Diyam" na gyada mata kai kawai, zuciyata tana so ta tambayeta ina jarirai na amma sai baki na ya kasa furtawa. Ta tambaye ni "menene yake miki ciwo yanzu?" Na rasa me zance mata saboda duk ilahirin jikina ciwo yake yi tun daga kaina har yan yatsun kafata. Na tuna irin wahalar da nasha dan ko a mafarki ban taba tsammanin haka haihuwa take da azaba ba, na tuna mafarki na, sai naji ina jin haushin Sadauki me yasa ya rabu dani in the first place, mai yasa duk sanda nake bukatar sa nake samun bayanan?
Inna ta tashi da sauri ta fita, sai gasu sun dawo tare da wata nurse da tazo tana yi min sannu sannan ta auna bp na ta duba idona da hannuna tace da Inna "har yanzu mijin nata bai zo dawo ba? Yarinyar nan fa in ba'a kara mata jini ba za'a iya rasata, gashi har ta fara kumbura. It is a miracle ma da take a raye wallahi" Inna ta karkata kai "nayi ta kiransa wayar bata shiga wallahi, nayi ta kiran mahaifiyarsa ita ma bata dauka ba, yanzu babu wani abu da za'a iya yi mata kafin kanwata tazo? Tayi tafiya zuwa Abuja ne amma tace min yanzu zasu taho ita da mijinta" nurse din ta girgiza kai tace "gaskiya babu wani abu da zan iya yi mata ni dai, jinin nan dai shi za'a kara mata kamar leda uku first sannan kuma muga yadda za'ayi" Inna ta gyara mayafinta tace "bara in fita in je gidan da kaina" har ta kai bakin kofa kuma sai ta juyo "babu komai idan na tafi na barta ita kadai?" Nurse din tace "babu komai, allurar baccin ma zan sake yi mata. Amma kiyi sauri, in babu kudin ma ki samo maza wadanda za'a iya dauka a jikin su" Inna ta sake kallo na sannan ta fita da sauri. Nurse din tazo kaina tana zuko allura tace "ki godewa Allah yarinya, you are very lucky" tana yi min allurar na tambayeta "ina babies din dana haifa?" Ta girgiza kai tace "ban sani ba gaskiya, ke kadai aka kawo ki nan tun cikin daren jiya" daga nan bacci ya dauke ni ina wandering ina babies dina?.
Sanda ma kuma farkawa Inna na gani tana waya tana kuka "wallahi Hafsa babu ko dari a hannuna a yanzu, gashi suna ta tsorata ni da yana yin jikin nata. Naje gidan babu wanda ma na samu duk sun tafi asibiti gurin Alhaji" naji kamar kaina ya kara nauyi,nayi kokarin daga hannuna naji shi kamar ba a jikina yake ba, eyelids dina ma kansu sunyi nauyi. Na sake cewa "Inna" ta ajiye wayar da take yi ta taho gurina da sauri ta rike hannuna "sannu Diyam, Allah zai dube mu kinji? Allah zai dubi maraicinki ya bamu yadda zamuyi".
Kamar amsa maganar ta sai ga wani doctor sun shigo shida nurse, hannunta dauke da ledojin jini guda biyu tazo da sauri ta fara kokarin dauka min. Inna ta mike "jini? A ina aka samu jini" kana jin muryar ta zaka fahimci wani relief a ciki. Doctor ya juyo yana kallonta yace "ba ke kika kirawo wani dan uwanku ba?" Tayi saurin girgiza kai, "ni ban kira kowa ba, ban samu kowa ba da naje gidan" doctor yace "but baki dade da fita ba wani yazo yace dan uwanku ne, mun dauka ke kika turo shi, yace a debi jininsa, kuma muna aunawa muka ga yayi matching, shi leda ukun ma yaso bayarwa mu muka ce kar ya zama affected shi kuma. Ya biya dukkan bills dinku na gado da kudin magunguna duk mun rubuta masa ya biya har da kari wai ko wani abin zai taso" Inna ta koma ta zauna akan kujera "to waye wannan kuwa?"
Nurse din tace "Halima Usman Kollere dai yace yana nema. Ya shigo nan ma ya tarar tana bacci sai ya fita". Inna ta rasa bakin magana.
Nurse ta gama daura min jinin ta juya suka gama rubuce rubuce ita da doctor sannan suka fita yayin da Inna ta zauna tana ta jera addu'a zuwa ga savior dina. "Allah ya bashi abinda yake so duniya da lahira. Yadda ya bude mu Allah ka bude shi shida zuri'arsa, Allah ya biya shi da gidan aljanna" na gyara kwanciya ta ina kallon window, dare ne, meaning na kwana na wuni kenan da haihuwa. Ina 'ya'ya na?
Washegari sanda na farka naji muryar Mama suna magana da Inna, sai kuma hayaniyar su Asma'u da Muhsina. Na bude ido ina kwallon su, they looked like twins, ina twins dina? A tare suka taho gurina suna rige rigen rije hannuna, nayi musu murmushi ina shafa kawunansu, Mama ta taso itama "sannu Diyam, ya jikin naki?" Nayi gyaran murya nace "da sauki Mama" tayi murmushi tace "naji dadin yadda na ganki, da duk hankali na ya tashi, ai mun auna arziki sosai" Inna tace "gashi kinga har ta fara sabewa, amma jiyan nan duk a kunbure take. Wannan mutumin Allah ya biya shi da aljanna" Mama tace "ni nafi tunanin irin masu bin asibitin nan ne suna taimaka wa mutane, maybe ya tarar ana zancenta shine ya nuna kamar dan uwane, tunda dai kinga yanuwan duk mun tambaya sunce basu bane ba". Ni dai ina jinsu ina jiran inji sunyi hirar jarirai na amma shiru. Tare suka kamani suka tashe ni tsaye, na tashi da kyar ina cije lebe, sannan Mama ta hada min ruwan zafi sosai ta kaini toilet da kanta ta gasa min jikina ta kuma saka na shiga ciki. Muna fitowa take ce da Inna "ashe bata karu ba" inna tace "eh fa, haka nurse tace min. To ai yaran ne baki gansu ba yan kanana dasu, ni ko a bakwaini ban taba ganin masu kankantar wadannan ba" Mama tace "Allah sarki. Allah yasa masu ceton ta ne" gabana ya fadi, na juya ina kallon Mama sai naga duk jikinta yayi sanyi, na saki cup din tean data miko min na rufe fuskata da hannayena. Tayi sauri tazo ta rungume ni a jikinta tana jijjiga ni kamar yarinya "kiyi hakuri Diyam, Allahn da ya baki su shi zai baki wadansu. Kuma yayi al茩awarin aljanna ga duk iyayen da ya karbi ran yayansu suka yi hakuri" na kifa kaina a kafadarta nayi ta kuka, sai naji duk ciwon jikin da naje ji ya barni dan wanda nake ji a raina yafi na jikin ciwo. Sai naji muryar da naji jiya ta cewa ban mutu ba ta koma, naji tamkar rayuwa bata da amfani a gare ni. Na rufe idona ina tuno their cute little faces.
Sai da suka samu na tsagaita da kukan sannan suka saka ni a gaba na basu duk labarin abinda ya faru. Gabaki daya suka dauki salati. Inna tace "amma dai Saghir ya cika makaryaci, cewa fa yayi ita ce ta shiga daki ta rufe kofa sai daya ji shiru ya balla kofar ya shiga ya same ta a haka" na matso hawayen idona nace "wallahi karya yake yi. Shi ya kashe min yara na. Ta sanadiyyar shaye shayensa suka rasa rayuwarsu, bazan taba yafe masa ba wallahi". Mama tace "duniya ce Diyam, ki barshi da duniya ta ishe shi darasi shi da iyayen nasa dukka. Tun yanzu ba gashi nan sun fara gani ba" Nace "me ya faru?" Mama tace "ai daya gama mayen nasa ya farka ya ganku shine ya dauko ku babies din ko cibiya ba'a yanke ba ya taho daku gida a gigice, a nan aka jere wa Alhaji Babba su a gabansa innarki kuma Saghir din ya dauko ta tare dake ya kawo ku nan, dan wulakanci kuma babu wanda yayi kara ya biyo ku su ta yayan da suka riga suka mutu suke yi. Sai gashi Saghir yana kawo ku nan aka kira shi wai kuma gobara ta tashi a kantin kwari, shagunan Alhaji Babba gabaki daya sun kone kurmus babu abinda aka fitar, yanzu dai Alhaji ya yanke jiki ya fadi, hawan jini ya tashi, har yanzu yana asibiti unconscious".
Na karbi tean da Inna ta sake hado min na kurba ina jin zafinsa yana kona min bakina. A raina sai nayi wani tunanin irin hikimar ubangiji da take cikin haihuwar wadannan yaran, sannan kuma na saka a raina cewa mutuwar su tamkar wata sabuwar jarabawa ce a gareni, kuma nayi niyyar yin iyakacin kokarina wajen cinta. Twins dina sunzo sun tafi, ko picture dinsu bani dashi sai wanda nayi saving a memory na, kuma bazan taba mantawa dasu ba har in tafi inda suka tafi.
Kwana na biyar a asibitin na warware sai abinda ba'a rasa ba, sai dai something is bothering me deep inside sai dai na kasa magana a kansa. Ina zaune ina cin abincin da Inna ta zuba min ne ina tunanin yadda rayuwata take, kaddara upon kaddara haka take samu na and I wondered wacce kaddarar ce kuma next.
[2/4, 11:21 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman maama
Episode Thirty Five : A Glimpse
Yan uwa da yawa sunzo sun duba ni kuma sunyi min gaisuwar twins dina. Aunty Fatima tazo har sau biyu ita da yaranta, Adda zubaida tazo itama, sai daga baya sai ga kawu Isa nan yazo shida iyalinsa, sai a lokacin yake tambayar inna nawa ne kudin asibitin? Tace masa kawai an biya shikenan sai ya bar maganar ba tare da yaji yadda aka yi aka biya din ba ko kuma waye ya biya ba.
Da dare sai ga Hajiya Babba ita da wannan sister din tata, amma babu Saghir babu alamarsa, su inna suka karbe su babu yabo babu fallasa sannan suka tambayesu jikin Alhaji. Sunce yana asibiti har lokacin amma yana samun sauki sosai. Suka kawo min maltina da fruits. Na gaishe su sai Hajiya Babba tace "Diyam, banji dadin abinda kika yi ba ko kadan wallahi, kinga abinda ya jawo ko? Garin kiyayyar Saghir an kusa a rasa rayuka har hudu" Mama da dama kamar jira take yi tace "me Diyam din tayi" Hajiya Babba tace "innarta bata gaya miki ba? Saboda bata son Saghir bata son haihuwa dashi shine ta shiga daki ta rufe kanta wai gwara ta mutu ita da yayan baki daya, gashi nan yanzu yaran da basu ji ba ba su gani ba sun rasa ransu, ga kakansu can kuma rai a hannun Allah. Dan ma Saghir mai taurin zuciya ne da har dashi zamu hada muyi jinya" naji raina yana min zafi, hawaye masu zafi suka kawo a idona, na yunkura zanyi magana Inna ta dakatar dani tace "kar kice komai" ta juya gurin Hajiya Babba tace "wannan magana ce da Saghir ya fada, ita kuma Diyam ba haka ta gaya mana ba tace a gaban Saghir ta haife yara guda biyu yana sheka uban bacci, babu irin tashin da bata yi masa ba amma ko motsawa baiyi ba" sai sukayi dariya duk su biyun, yar uwar Hajiya tace "kuma yanzu ku da hankalin ku sai kuka yadda da wannan maganar? Wanne irin bacci ne mutum zaiyi har a haihu a gabansa bai san anayi ba?" Mama tace "baccin wadanda suka sha suka bugu mana? Wadannan kam aiko yanka su zakayi sai dai su farka su gansu a lahira" sai kuma suka daina dariyar, Hajiya Babba tace "Hafsa? Wacce irin mummunar magana ce kike jifan dan dan'uwanki da ita?" Inna tace "ba mummunar magana bace ba, gaskiyar magana kenan. Saghir shayeshaye yake yi, kuma wannan shayeshayen shi yayi sanadiyar mutuwar wadannan yaran. Wannan shine gaskiyar magana" Hajiya Babba ta juyo kaina, fuskarta babu annuri ta nuna ni tace "Diyam sakayyar soyayyar mu gare ki kenan? Sharrin da zaki yiwa dan uwanki kenan?" Na girgiza kai na nace "ba sharri bane Hajiya, in baku yarda da magana ta ba ku je gidan ku bincika, ku duba dakinsa na tabbatar ba zaku rasa kayan maye ba, ku duba motarsa ba zaku rasa kwalbar giya ba, in still baku yarda ba ku tambayi uwani ta baku labarin yadda ta kwace ni rannan a hannunsa wanda shine dalilin fara nakuda ta ba tare da lokacin haihuwa yayi ba, in still baku yarda ba ku tambayi mai gadin gidan, ai yana ganin dawowarsa gida kullum a buge yake shigowa" sai suka hada baki suna tafa hannaye suna salati "kuji yarinyar nan yar karama da ita amma ta iya shirya magana irin wannan? Ku kuma iyayen ta kuka hau kai kuka zauna dan kun zama butulu ko? Duk kun manta irin alkhairin da Alhaji yayi muku amma shine yanzu saboda abinda ya same shi har zaku juya masa baya ku dorawa tilon dansa sharrin shayeshaye? Dan kunga Alhaji iftila'i ya fada masa shine zaku juya mana baya?"
Sai ta kama kuka yar uwarta tana rarrashinta. Mama da Inna duk suka tsaya suka saki baki suna kallonta. Sannan Mama tace "Hajiya saratu in kika ce haka baki kyauta mana ba, da Diyam da Saghir duk yayan mu ne amma dole a cikin su in wani ya kauce hanya zamu fada dan gyaransa ba wai dan bata masa suna ba. Bincike ya kamata ayi kamar yadda Diyam tace, wanda duk aka samu da laifi a cikin su sai ayi masa fada dan ya gyara laifukan sa" sai suka tashi cikin fushi suka fice daga dakin. Mama tazo ta zauna kusa dani ta goge min hawayen fuskata tace "kiyi hakuri Diyam, in dai shayeshaye halin Saghir ne wata rana zai yi ne a gaban jama'a yadda babu wanda zai musa". Ni kam zuciyata zafi take yi min, an jima ba'ayi min abinda ya kona min rai kamar wannan ba, ya Saghir zai kala min wannan sharrin? How can they accused me of killing my own babies?
Washegari da safe Hajiya Yalwati tazo itama, tayi ta bawa inna hakuri wai abubuwa ne suka sha kanta ga Alhaji a kwance ga yara ga gida babu kudi. Sai Inna ta bata labarin yadda mukayi dasu Hajiya Babba jiya, sai tace "dalla rabu dasu, waye baisan Saghir yana shaye shaye ba? Amma su kullum sai su ke nuna kamar ba'a sani ba. Yanzu shima uban da ace lafiyar sa kalau kuna gaya masa zai musa". Da daddare muna zaune Inna tana ta mitar cewa tunda muka zo asibitin Saghir bai ko kira waya ya tambayi jikina ba, bai bada ko kwandala ta magani ba bai kuma nemi yaji inda muka sami kudin maganin ba. Tace "wannan wanne irin aure ne?" Na dauke kaina dan bani da amsar da zan bata. Bayan mun kwanta na yi mata tambayar da take raina. "Inna Sadauki kuwa ko yasan bani da lafiya? Yanzu shi ko duba ni ba zai zo yayi ba ballantana yayi min gaisuwar wadannan yaran? In babu aure tsakanin mu ai akwai shakuwa ko? Shi din tamkar yaya yake a gare ni" sai tayi shiru kamar bata jini ba, sai can tace "Diyam bansan inda Sadauki yake ba. Yaya ladi ma da naje nemanta gidan Alhaji Bukar ance min ta tashi kuma basu gaya min inda ta koma ba" na mike zaune nace "nemanta kikaje yi inna?" Tace "eh, naje nemanta da niyyar in bata gadon zainabu na gidan ku kamar yadda kika bani shawara amma ban same ta ba. Bansan ya zanyi ba yanzu". Nayi ajjiyar zuciya kawai ina wondering what happened? Ina Sadauki? Ko yana bornon? Ya samu admission din kuwa ko bai samu ba? Is he doing well? Na lumshe idona ina hangen fuskarsa a cikin kaina.
Washegari bayan an gama duk tests din da za'a yi suka sallamemu, muna shirin tafiya sai ga mutanen gidan Alhaji Babba nan sunzo, har da saghir, a lokacin ne suka fada mana an sallami Alhajin shima jiya, Hajiya Babba tana ta wani yayyatsina tana bata fuska, shi ogan ma a bakin kofa ya tsaya ya gaishe da Inna sannan yace min "sannu" na tattara shi na bawa iska ajjiyarsa. Budar bakin Hajiya sai cewa tayi "amma Diyam gidan ta za'a mayar da ita ba ko?" Inna ta tsaya tana kallon ta tace "ban gane ba" Hajiya tace "ina ganin abinda yafi shine ta zauna a gidanta, sai a tura wata matar haka take kula da ita kafin jikinta yayi kwari saboda kinga shi Saghir kinga babu dadi a barshi shi kadai a gida ba mace" Inna tace "haka ne" sai ta yafa mayafinta ta kama hannuna muka mike, ranta ya baci sosai. Tace "shi Saghir din yasan yana da matar amma tunda ta kwanta kwana bakwai bai waiwayo inda take ba? Shi Saghir din shin anyi masa fada akan abinda tace yanayi ko kuwa haka za'a kuma daukanta a mayar masa in yaso ya karasa kashe ta? Ina son Diyam fa nima ba wai bana sonta bane ba, ina kawaici ne kawai saboda karfin zumuncin da nake hangowa a tsakanin mu amma kuma kunsan wallahi da mahaifinta yana da rai ko soma maganar nan ma ba za'ayi ba ballantana ayi ta" Aunty amarya tace "haba Amina, yanzu kiri kiri a gaban mu kike nuna Diyam taki ce ba tamu gabaki daya ba, yanzu zumuncin har yakai haka tabarbarewa?" Na juya ina kallon Saghir har yanzu yana tsaye da hannayensa a cikin aljihunsa yana bin kowa dai dai da kallo, naji a raina ni kam ko inna ta yarda da komawa ta gidansa ni ba zan koma ba, gwara in shiga duniya yafi min sauki. Na zame hannuna daga na inna na fice daga dakin.
A bakin gate din asibitin na tsaya ina sharar hawaye, sai ga Inna da saurinta ta rike ni, "Diyam ya akayi kika fito ke kadai? Ina zaki je?" Na sunkuyar da kaina bance mata komai ba. Muna tsaye a waje suka fito, Saghir shi kadai ne a motarsa sai Hajiya tace ya dauke mu, nasan a lokacin da inna tana da kudi da ba zamu shiga motar Saghir ba amma dai haka muka shiga muka zauna a baya mu biyu, yana ta wani bata rai irin shi ba haka yaso din nan ba.
Ina zama na kwantar da kaina na lumshe idanuwana ina tunanin ta inda zan fara neman Sadauki, I just want to see him koda bance masa komai ba. Naji ya tayar da motar, sai naji Inna tace "Yakasai zaka kai mu" nayi saurin bude ido na ina kallonta, a raina nace 'finally' Finally Inna ta yi breaking out of her shell zata yi flying, to kawai yace mata ya dauki hanyar gidan mu. Naji mun tsaya na kuma bude idona sai naga traffic light ce ta tsayar damu a gefen asibitin, na dan sauke glass din windown da nake saboda in sha iska tunda babu ac, kamar daga sama naji kamar an ambaci sunana da muryar da ba zan taba mantawa ba, nayi saurin dago kai amma sai naga su inna kamar basu ji kiran ba, and then I smelled him, wani unique smell wanda daga gurinsa kawai nake jin sa, nayi saurin kallon window na and there he was, Sadauki, yana tsaye da hannayensa cikin aljihunsa yana kallona da budaddun idanunsa. Yayi loosing weight sai naga kamar ya kara tsaho, fuskarsa da kansa suna bukatar aski. Na zauna kawai ina kallonsa as the time froze and my heart stopped. He just stood there looking at me, sai kuma na kwalla masa kira "Sadauki!!" Inna ta juyo a tsorace ta riko ni tana tambayata lafiya, na juyo na kalleta sannan na juya da niyyar nuna mata sadaukin dana gani but ge was gone, as if yayi vanishing.
Kuka nake iyakacin karfina ina kiran sunan Sadauki yayinda Inna ta rike ni take tofa min addu'a, Saghir kuma yana bala'i duk da bana jin abinda yake cewa nasan akan kiran sunan Sadauki da nake yi ne ni kuma ban daina ba.
Manage this please
[2/6, 10:06 PM] +234 818 247 0922: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Six: Mother's Tears
Har muka je gida ina kuka na, though na daina yi da karfi sai ajjiyar zuciya nake yi. Ina jin Saghir yana cewa "wannan Sadauki dama naji ance dangin mayu ne, tunda kin kwallafa shi a ranki ba dole yake yi miki gizo ba? In kuma da gaske shi din kika gani Allah ya bashi sa'ar yi miki magana in nuna masa shi karamin dan iska ne" daga ni har inna ba wanda ya kula shi wanda hakan ya bani mamaki dan nasan inna bata wuce tayi in dai akan zagin Sadauki ne. A raina nace "kaji Saghir din nan da son a sani gaida uwar saurayi a kasuwa".
A kofar gidan mu yayi packing muka fito, na tsaya ina kallon gidan da yake holding so much memories, good memories, Inna ta dauko key a jakarta ta bude gidan ni kuma na dauko mana jakar mu zan wuce ciki naji Saghir yana cewa "anan zan barku ne naga kuna daukan kaya?" Ban kula shi ba sai Inna tace "eh" daga haka itama bata kara komai ba muka shiga cikin gidan.
Na tsaya a tsakar gida na jingina da bishiya ina karewa gidan kallo, ko ina yayi datti dukun dukun. Inna ta bude dakin ta ta shiga sai ta dauko key din dakin baffa shima tazo ta bude. Cikin dakunan basu yi datti sosai ba. Na zauna akan kujera ina tambayarta "Inna anan zamu zauna ko? Ba zamu koma gidan Alhaji Babba ba ko?" Eh kawai tace min sai ta dauki kayan shara ta tafi ta fara share dakin baffa. Na taso na biyo ta zan taya ta tace "ke da baki da lfy kiyi zamanki kawai" amma sai naki, tana share yana ni kuma ina karkade kurar kan furnitures, a haka muka gama gara cikin daki da palon sa, muka wanke toilet dinsa na palo sannan sai gasu Mama sunzo ita da yammatan ta da yake ranar weekend ne babu school, su suka karasa aikin tsakar gida da kitchen da garage. Dakunan umma kuma aka rufo su muka zauna a palon Baffa muka ci abincin da Mama ta taho mana dashi sannan Mama da Inna suka fita su kace zasu je gidan Alhaji Babba.
Bayan sun tafi ne Rumaisa take tambayata "Diyam, bani labarin yadda haihuwa take, naji Mama tana cewa kinyi kokari kin haifi yara biyu ke kadai babu taimako, ya kika ji?" Na girgiza kaina kawai, ni kadai nasan yadda naji, babu wanda zai gane kuma yadda naji din sai wanda ya tsinci kansa a irin hakin dana tsinki kaina. Ba kuma nayi wa Rumaisa fatan shiga halin da na tsinci kaina.
Sai bayan magrib su Inna suka dawo, sun debo duk kayan Inna da na Asma'u, amma duk naga rayukansu a bace suke daga dukkan alamu ba rabuwar arziki akayi ba. Asma'u ta shigo tana ta tsallen murnar dawowa gida, tace "Adda ina son gidan nan wallahi, nafi son muyi zaman mu anan dani dake da inna".
Washegari muka yi breakfast da yan kudaden da Mama ta bamu da zata tafi, bayan nan kuma sai Inna ta fita can sai gata ta dawo da dillaliya, suka shiga dakinta suna ta cinikin kaya ni dai ban bisu ba, daga baya matar ta fita sai gata ta dawo da maza suna ta jidon kayan dakin inna. Set din gadonta, set din kujerunta, kayan kallon ta kai hatta labulayenta sai da aka fita dasu. Katifar dakin mu ce kawai aka kawo nan dakin Baffa sai sauran tarkace kuma ta saka almajirai suka tattara ta zuba su a dakin soro. Sai aka share dakin kuma aka rufe shi. Naje na leka dakin Ummah ta taga naga yana nan yadda yake ko kayanta ba'a kwashe ba. Da daddare naga Inna ta zauna tana ta lissafin kudi.
Kafin sati ya zagayo mun samu tenants a gidan mu, sai akayi yar karamar katanga a tsakanin mu for privacy. Mata da miji ne da kananan yayansu guda biyu Iman da Saudat, da zasu tare sai sukayi fenti suka hada harda gurin mu suka yi mana. Matar mai kirki, irin masu son shiga mutanen nan ce dan tun da suka zo data gama abinda taje yi zata zagayo gurin mu muyi ta hira, in mijin ya siyo wa yayansa wani abu kuwa sai kiga ta dibo ta bawa Asma'u.
Kudin kayan da inna ta siyar, sai ga Mama tazo ta dauke ta suka fita sai gasu sun dawo da lodin kaya, tun daga kan shinkafa har zuwa ashana, sabulan wanka dana wanki kala kala, har da biscuits da sweets da bobo na yara, ta saka aka buga mata runfa daga gefe ta jibge kayan ni na dauka kayan amfanin mune har ina lissafin watannin da zamuyi muna amfani dasu sai naji ta tura Asma'u duk makotan mu ta gaya musu tana siyar da kaya. Kwanon shinkafa kanon fulawa, har gwangwani daya in kana so zata auna maka, manja man gyada barkono babu abinda Inna bata siyarwa. Ta mayar da Asma'u kuma former school dinta, da yake tsohuwar dalibar suce ba'a siya mata form da uniform ba kawai books aka siya mata sai kudin makaranta wanda a take Inna ta biya, Asma'u tana ta murna. Sai naji dadi dana bata wannan shawarar, na kuma ji dadi data dauka.
A bangare na kuwa tunda muka koma gida kullum sai wata makociyar mu ta shigo tayi min wankan jego, wankan runhu take yi min inyi ta kuka wai zafi amma ni kaina nasan inajin dadin wankan. Sosai na warware na dawo haiyacina karfina ya dawo jikina. Inna kullum tana diban kudi ta siyo min nama ta dafa minmai romo ta saka in chinye in shanye romon, ga tuwo zatayi min da dare da safe ta dumama min. Har addu'a nake Allah kar ya kawo karshen wannan zaman nawa. Amma ina....
Tunda muka zo gida babu wanda ya kara bibiyar mu a cikin yan uwanmu, Saghir ko mai kama dashi ban gani ba, hatta aunty Fatima bata zo ba sai mama ce kadai take ziyartaru tana duba lafiya ta. Ta gaya mana itama duk sun daina kulata kuma suna ta surutun wai dan karayar arziki ta samu Alhaji Babba shi yasa muka juya masa baya, bayan mu abinda yayi mana bayan rasuwar Baffa ya dauko mu ya rike mu ya aurar dani ga dansa mafi soyuwa a gurinsa amma duk bamu gani ba saboda mun zama butulu. Inna tace "Allah ai shi yasan abinda zuciyar bayinsa".
Sai da mukayi wata uku a haka, har na gama wanka duk da cewa na wata biyu akayi min. Ranar nan muna zaune da maman iman muna cin wake da shinkafa sai najiyo Inna tana waya, daga jin sunan data ambata nasan kiran daga Kollere ne, ai kuwa tana gama wa naga jikinta yayi sanyi tace min "Hardo ne. Yace yana neman mu duk a Kollere ranar asabar" tun daga nan naji duk wutar jikina ta dauke. Washegari kuwa dai zazza蓳i. Ranar asabar da assuba Mama tazo tare da driver suka dauke mu ni da Inna muka bar Asma'u a gurin maman Iman. A hanya nayi kwanciya ta a mota trying so hard not to think about what the outcome of the meeting might be.
Muna zuwa muka tarar already su Alhaji Babba, kawu Isa, Aunty Fatima da kuma Saghir suna can. Tun kafin mu gama gaishe da Hardo ya fara fada. "Yanzu wato tun kafin in bar duniya har kanku ya rarrabu irin haka? Har zumuncin ku ya tarwatse har haka? Har son zuciya ta son yayanku ya rufe muku ido kun manta da yanuwantakar da take tsakanin ku? Kun manta da tarbiyyar da ni da inno muka baku?" Ni dai ina rakube dama daga can bakin kofar shiga dakinsa, na hango Saghir shima a can daya end din su kuma iyayen mu suna tsakiya. Sai daya gama fadansa sannan yace a tsara masa abinda ya faru, kawu Isa ne yayi bayanin haihuwata da rasuwar twins da kuma abinda ya sami Alhaji Babba na gobara, duk da cewa duk Hardo yasan wannan, sai kuma yayi bayanin shi Saghir abinda yace da kuma ni abinda nace, ya kara da cewa "mu abinda ya bamu haushi shine yadda Amina ta rufe idonta ta goyi bayan Diyam, bayan kowa yasan tsakanin mata da miji sai Allah babu ta yadda za'a gane mai gaskiya a cikin su. Kawai ta hana yarinyar komawa gidan mijinta ba tare da anyi bincike ba. Sannan kuma ta hada kayan ta ta bar gidan Alhaji Babba a lokacin da yake tsaka da bukatar kulawar yan uwansa, ta koma gidan marigayi ta bude ta kafa zaman kanta. Wannan ne yasa muma muka zare ta daga jikin mu".
Hardo ya hada su gaba-daya ya wanke su, yace da mai gaskiya da marar gaskiya duk a gurinsa masu laifi ne, sannan yace "ni yanzu zan yanke hukunci, sai kuma inga wanda a cikin ku zai nuna min cewa ya girma yanzu yayi ya'ya kuma ni bani da iko akan ya'yansa" ya fada yana kallon Inna data sunkuyar da kanta kasa. Ya nuna ni yace "Haleema" nace "na'am" yace "zaki koma gidan mijinki" na runtse ido hawayena yana zubo wa. Ya dora "uwani zata biku ku cigaba da zama tare kamar wancan karon. Zan gaya mata cewa ta saka ido sosai a kanka kai Saghir ko sau daya ta tabbatar da maganar Halima ni da kaina zan karbi takardar ta a hannunka. Sannan abu na gaba shine zaka saka ta a makaranta, zata karasa karatunta na secondary inta gama kuma in kun daidaita a tsakanin ku sai ta cigaba. Ka fahimta?" Saghir yayi gyaran murya yace "na fahimta Hardo, kuma ina godiya" Hardo ya juyo kaina yace "ke fa Halima? Kin fahimta?" Na gyada kaina, yace "ki bude baki kiyi magana mana?" Sai na bare baki na saka kuka. Nan take ya koreni daga dakin yace in tafi cikin gida.
Anan muka kwana, naga Inna ta dan shiga yan'uwanta suna magana sama sama. Ni kuwa babu wanda na kula ina kudundune ina zazza蓳i. Da daddare wai sai ga kira inje inji Saghir yana waje, na tashi naga duk suna kallona dan haka na saka hijab na fita, na dan tsaya a soro na bata lokaci sai na dawo gida nayi kwanciya ta.
Da safe kowa ya shirya zamu tafi, mukayi sallama da mutan gida ina fitowa waje na hango Saghir a tsaye a jikin motar dasuka zo da ita ya harde kafafu yana kada key, na dauke kaina zan wuce yace "babu gaisuwa?" Na juya baya naga kawu Isa yana kallon mu sai na gaishe shi ciki ciki, ya amsa yana murmushi yace "in kin koma gida ki shirya jibi zan zo mu tafi" na faki ido na jefa masa harara na wuce. A raina nace "munafiki".
Mun koma gida da kwana biyu kuwa sai gashi da safe wai in fito mu tafi. Na koma nayi kwanciya ta Inna tace "tashi ki dauki mayafinki ku tafi, sauran kayanki zan hado miki in aiko miki dasu" na fara kuka, sai ta zauna kusa dani ta jawo ni jikinta tace "kiyi hakuri Diyam, nasan wannan duk laifina ne dan tun farko ni na bada kofa har akayi miki auren nan, yanzu kuma babu yadda zanyi tunda igiyar auren ba a hannuna take ba. Kiyi hakuri kinji?" Sai naga kwalla a idonta, nayi saurin goge hawayena ina gyada kai, ta dauko sabuwar waya a cikin kwalinta da sim card ta miko min tace "tun ranar nan na siyo miki wata. Ki tafi da ita, duk halin da kike ciki ki kirani ko ki kira Hafsa ki gaya mana. Uwanin ma munyi waya da ita tace min itama yau zata je. Ki yi ta addu'a kina gaya wa Ubangiji kukan ki, shi kadai ne zai zaba miki abu mafi alkhairi a rayuwar ki".
A mota na tarar dashi a zaune yana jin kida, na kai hannu zan bude baya sai ya danna lock ya rufe, dole na na shiga gaba yaja motar ba tare daya ce min komai ba. Ina ta kuka na kasa kasa har mukayi nisa muka kusa unguwar sannan yace "wallahi ko kiyi shiru da kukan nan ko kuma in sauke ki a gurin nan" nayi shirun tunda nasan ba karamin aikinsa bane ya saukeni a wajen.
A bakin gate ya ajiye ni, ina fitowa ya ja motarsa yayi gaba. Na shiga gidan ni kadai kamar mayya. Maigadi ya taso ya muka gaisa na bude palo na ganshi kamar wanda akayi yakin badar a ciki, kaca kaca, ga used plates nan ko'ina duk sun bushe. Bedrooms ne kadai masu dan kyau suma bawai gyarawa akayi ba amma dai ba'a bata su ba. Na lura cewa abubuwa da yawa were missing a gidan, daga dukkan alamu kayan gidan su suka koma source of income na Saghir. Na kunna tv naga lafiyar ta kalau,na fara tattara gidan kenan naji a tv an sako wakar Westlife ta coast to coast "my Love"
An empty street, An empty house, A hole inside my heart, I'm all alone The rooms are getting smaller. I wonder how, I wonder why, I wonder where they are, The days we had, The songs we sang together Oh yeah
And all my love I'm holding on forever, Reaching for the love that seems so far, So I say a little prayer, And hope my dreams will take me there, Where the skies are blue To see you once again, my love, Over seas from coast to coast, To find the place I love the most Where the fields are green To see you once again, my love
To hold you in my arms, To promise you my love, To tell you from my heart You're all I'm thinking of. And reaching for the love that seems so far........
Sai naji kamar dani suke a wakar with Sadauki as my faraway love. Na zauna akan kujera na kama sana'ar tawa ta kuka. Ina cikin yi uwani tayi sallama ta shigo, sai na tashi da gudu naje na rungume ta.
Tare muka gyara gidan gaba-daya, sannan uwani ta fitar da kudi daga aljihunta ta bawa maigadi yayo mana cefane mukayi girki. Muna gamawa sai ga Saghir yazo ya zauna a palo suna gaisawa da uwani sannan ya ce min "kawo min abinci" Sai na juya ina mamakin karfin hali irin na Saghir, kai da baka bada kudin cefane ba ina kai ina neman abinci? Ina kallonsa ya dauki wayata ya duba, sai naga ya daddanna ya ajiye. Da dare na fito daga wanka ina shirin kwanciya waya ta tayi kara. Na dauka ina duba number din dan number inna da ta Mama kawai nsyi saving dazu a gurin uwani. Na dauka naji muryar Saghir "ki kawo min ruwa dakina" na ajiye wayar nayi tsaki. Har zan kwanta sai kuma na saka hijab dina na dauko ruwan naje na kai masa. Yana kwance ya kashe fitila ya rufa da bargo, na ajiye ruwan ba tare dana ce masa komai ba. Zan fita yace "Diyam" na juyo ina kallonsa ya nuna kusa dani a kan gado yace "come here" na watsa masa harara na juya yace "kin san dai hakkina ne ko?" Na juyo nace "kai wanne daga cikin hakkokin ka ka sauke?" Yace "ki bani chance ki gani. Kuma nasan so far I have been trying my best" na fara tunanin wanne ne best din nasa. Sai ji nayi yace "zanyi Allah ya isa in baki zo ba" na juya da sauri ina kallonsa nace cikin mamaki "are you for real?" Ya daga kafada yace "bani da wani choice ai, ina bukatar ki kin ki bani, bazan iya miki dole ba so my only choice is to do Allah ya isa, ta rago" na juyo kamar wadda aka saka wa remote ina tunanin yadda aljanna ta take kasan kafarsa amma a lokacin babu abinda nake so irin in shake kyakykyawan wuyansa har sai ya daina numfashi. Na zauna a bakin gado na juya masa baya ina jin hawayena yana zuba a cinyoyi na, ina jinsa ya matso ya zare rigata sannan ya jawo ni zuwa jikinsa, ina jinsa yayi duk abinda yake ganin zai iya yayin da ni kuma kukana yake kara tsananta har ya gama abinsa. Ya sake ni yana mayar da numfashi. Na mike zaune na jawo rigata na saka ba tare dana kalleshi ba na mike sai ji nayi yace "shikenan kuma? Ko dan curdle din nan ma, irin falling asleep together din nan na masu aure babu, na juyo ina kallonsa da kumburarrun idanuwana, yayi murmushi nace "shima in banzo ba Allah ya isan zaka yi?" Yace "well, yes" na juyo na dawo na kwanta. Ya matso da pillon sa kusa dani ya jawo ni jikinsa sannan ya jawo bargo ya rufe mu.
[2/7, 4:27 PM] +234 706 813 0709: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Seven : Abatcha Motors
Da assuba na tashi kamar kullum, na cire hannayensa daga kaina na mike ina kallonsa yana ta sharar baccinsa, ban tashe shi ba tunda ni dai dama ban taba jinsa ya fita masallaci ba, na tafi dakina na shiga toilet na kunna wa kaina shower wai ko zata sanyaya min zuciya, inna wanke jiki na sai in sake wanke wa in sake wanke gani nake kamar duk Saghir dinne a mammanne a jikina, ji nake ina ma ace zan iya cire fatar jikina in sake wata wadda Saghir bai taba ba? Nayo wanka na na fito na saka doguwar riga ta hijab nayi sallah ina addu'a Allah ya kawo min karshen auren nan, sai kuma na chanja nace idan auren shine mafi alkhairi a gare ni Allah ya cire min Sadauki daga zuciyata ya shiryar da Saghir ya saka min sonsa a raina. Ko da banso shi ba at least in rage tsanarsa hakan zai dan rage min zafin da nake ji a zuciyata.
Ina nan kan sallayata har gari yayi haske rana ta fito, sai naji an bude kofar dakin da nake, na juya ina kallon Saghir daya dau wanka yasa gayunsa kamar kullum sai kamshi yake, ya tako har tsakiyar dakin da takalmin sa a kafarsa yace min "ki zo ki bani breakfast zan fita" na dauke kaina gefe saboda wani takaici da ganinsa ya saka min nace "ka kawo abin breakfast din ne?" Yace "ki duba dakina akwai kayan tea sai ki hada min tea, akwai kuma kwai a kitchen sai ki soya min" daga haka ya fita, na tashi nayi abinda yace na kawo masa palon sama yana zaune yana kallo, na zauna ina kallonsa har ya gama ya karkade jikinsa zai tashi nace "mu kuma fa? Me zamu ci" ya tsaya yana kallona yace "babu abinci a store?" Nace "ka ajiye ne?" Yace "bana son maganar banza in babu kawai kice min babu" nace "ai ka fini sanin babun" yace "ku sha tean mana to, kafin lokacin abincin rana ai zan dawo" yayi hanyar waje nace "in baka dawo ba nima zanyi Allah ya isa" sai kawai ya juyo ya kalleni yayi murmushi ya fita.
Bai dawo ba din kuwa. Haka na samu wata guntuwar shinkafa a store muka dafa fara dama uwani tayo guzurin yaji muka ci da mai da yaji. Bai dawo ba sai dare, daren ma sai bayan mun kwanta kuma nasan maybe yayi hakan ne dan kar inyi masa mitar bai ciyar dani ba. Da safe ina kasa muna gyaran gida sai gashi ya sauko, ya leka wajeya kira mai gadi sai naga sun hau sama tare ya bashi akwati ya sauko dashi kuma daga ganin akwatin nasan da kaya a ciki, akwatin cikin kayan lefe nane. Nabi mai gadin da kallo har ya fita sannan na hau saman muka hadu dashi yana kokarin saukowa nace "wancan kamar kayana naga an fita dasu, ko dai ido na ne?" Bai kalle ni ba yace "aro na dauka, zan siya miki wasu idan wadansu kudina da nake jira sun zo" nace "ko aron ne ai ana tambayar mutum kafin a dauki aron kayansa, kuma ni ban bayar da aron ba a dawo min da abi na" yace "ta yaya zamu zauna da kaya cikin akwati alhalin store din abincin mu babu komai? Ai ba kyauta nace ki bani ba aro ne kuma zan biya ki kin dai san ni ba talaka ba ne ba ko?" Kafin in bashi amsa ya fice. Na shiga dakina na tarar duk ya hargitsa min kaya, kusan duk kayan lefe na masu tsadar ya dauke. Bakin ciki ya kama ni kawai sai na zauna ina kuka, sai na tambayi kaina, wai yaushe ne zanyi farin ciki ni kam, yaushe ne zanyi murmushi, irin geniun smile din nan mai zuwa har zuci.
Ya siyo mana kayan abinci sosai, ya kuma bani 10k ya ce kudin cefane "saura kuma a karar dasu da wuri ace min babu" sauran kudin kuma bansan me yayi dasu ba.
Kwana biyu bayan nan, tunda rana naga yana tayi min fara'a sai nasha jinin jikina, da dare ina kwance a daki sai gashi ya bude kofa ya shigo nayi sauri na rufe idona dama fitila a kashe take, yace "Diyam, Diyam" nayi banza na rabu dashi. Sai ya hawo kan gado na sai nayi juyi na fara munsharin karya, irin wannan munsharin mai kamar kakin majina, sai yayi tsaki ya tashi ya fita. Na gyara kwanciya ta a raina nace "sai dai kaje ka rungumi pillow bani ba" and that got me thinking, this is his second attempt a kaina a cikin sati daya da dawowa ta, amma wancan karon wata na bakwai a gidan sa tun randa yayi raping dina bai kuma kallata da wannan maganar ba, menene ya chanza yanzu? Sai nayi realising cewa da yana da kudi yanzu bashi dasu, meaning da yana iya siya a waje yanzu ba zai iya siya ba, wato wannan shine dalilinsa na yarda da dawowa ta irin ga banza ta fadi dinnan ko? Ni kuma indai haka ne bazan yarda ba sai nasan yadda nayi na karbar wa kaina yanci. Sai kuma nayi mamakin kaina yadda nayi realizing Saghir yana neman mata amma ko a jikina wai an tsikari kakkausa, ko kadan banji raina ya baci ba alhalin ko a yanzu da nake matar wani in nayi imagining Sadauki da budurwa ba karamin baci raina yake yi ba ballantana inyi imagining dinsa yayi aure. I can only imagine yadda Sadauki yake ji a ransa a yanzu da make matar wani, har na haihu dawani. Ko ya yake ji? Ko ya yake coping?
Washegari ya tashi yana ta fushi, ni ko kallo bai ishe ni ba. Zai fita yace "zanyi baki anjima, abokaina ne manyan mutane ne sun takura wai sai sunzo sun ganki. Please don't embarrass me, kiyi musu abinci kuma kiyi shiga mai kyau kisa kayan da zasu kara miki girma". Bai jima da tafiya ba dai sai gashi ya dawo da kaji wai duk ayi musu. Mukayi abinci ni da uwani muka jera a dining, muka gyara gida tsaf yana ta kamshi na tafi sama nayi wanka na saka wata doguwar riga ta atamfa, dama ba kwalliya nake yi ba, na saka hijab nayi sallah ina zaune akan sallaya ya shigo yace "gasu sunzo, kuma please ki cire wannan dogon abin" ya juya ya koma, na tsaya ina tunanin menene dogon abin, doguwar rigar ko kuma hijab din?
Na tashi na gyara hijab dina na bishi, suna zaune a palon kasa kusan su biyar duk irin sa, yayan masu kudi masu ji da kansu. Na zauna a hannun kujera na gaishe su suka amsa, suna tsokana ta wai amaryar da ake boyewa, ina kallon Saghir yana ta harara ta nayi kamar ban ganshi ba sai cewa yayi "kin zo kin zauna kin saka mutane a gaba, ba zaki tashi ki kawo musu ruwa ba?" Na fahimci lallai so yake ya dizga ni a gaban abokan sa ya nuna musu ba sona yake yi ba, ni kuwa bai san yadda nake jin haushinsa yafi yadda yake jin nawa ba. Na mike sai cewa yayi "au ina miki magana ba zaki tsaya ki gama ji ba sai ki wani tashi ko?" Na dawo da baya na tsaya a gabansa nace "wanne daga ciki kake so Saghir? In tsaya kayi min fadan ne sai in kawo musu ruwan ko kuma in tafi in kawo musu ruwan sai kayi min fadan which one will you like first". Kusan gaba-daya suka kwashe da dariya. Ya kasa cewa komai ya tsaya yana kallona, sai na daga kafada nace "abinci yana kan dining, you can serve them in ka gama fadan" na juya nayi hayewata sama. Ni kaina nasan na gama da Saghir, amma kuma shi ya jawo wa kansa, me yasa zaiyi tunanin bara ya wulakanta ni a gaban abokan sa? Ko yana ganin hakan zai kara masa class ne a cikin su.
Ina nan zaune naji fitarsu a motoci sai kuma naji yana hawowa, nasan zuwa zaiyi mu yita amma sai naji bana jin tsoronsa, ya shigo har dakina ya karaso gabana ya tsaya, kawai sai jin saukar mari nayi a fuskata, saboda karfin marin har saida na daina gani for some seconds sannan ya sauke min a daya side din. Sai da naji taste din jini a bakina. Ya nuna ni da dan yatsa "ke har kin isa ki ce zaki gaya min magana a gaban abokaina, me kika dauki kanki ne? Wallahi ki bini a hankali Diyam in ba haka ba watarana sai na kai gawarki gida" Ya juya ya fita.
Na rike fuskata na zauna a bakin gado, bazan iya tuna sanda aka taba marina ba, to ni waye ma mai dukana in banda inna itama kuma mostly a kafa take dukana. Hawaye ya fara bin kuncina ina lissafa irin abinda zai faru da ace da ne wani yayi min wannan marin a gaban Sadauki. Nice kuka har magrib ina tayi, daga yin Sallah kuma sai zazza蓳i mai zafi ya rufe ni. Uwani ta hawo taji ni shiru sai ta tarar bana jin dadi sai ta zauna a waje na har saida Saghir ya dawo sannan ta sauka.
Tun daga ranar ban kuma lafiya ba, yau zazza蓳i gobe amai jibi ciwon ciki. Saghir kam fushi yake yi dani sosai ni kuwa ta kaina nakeyi, bai ma kula cewa bani da lafiya ba ballantana yayi tunanin kaini asibiti. Bayan nayi kusan sati ina jinya rannan uwani tace min "Diyam anya kuwa ba zaki yiwa Saghir magana ya kaiki asibiti a gwada ki ba? Ni fa ina ganin kamar juna biyu ne dake" sai naji wani amai ya taso min, naje nayi na gama na dawo nace "ciki fa uwani? Wanne irin ciki kuma?" Tace "ni dai na fada miki, kuma kije a gwada ki gani" sai na hau sama da sauri ina jin kamar labarin mutuwa ta uwani ta fada min, na fada kan gado na kama kuka, na shiga uku ni Diyam, sai na fara addu'a "Allah ka dube ni Allah, Allah kasa kar maganar uwani ta zama gaskiya" amma kuma nasan rabo na da period tun ina gidan mu, ga kuma abinda ya faru ranar dana dawo.
Ina nan kwance Saghir ya hawo yana kwalla min kira, na tashi na same shi a tsaye a kofar dakinsa yace "ki shiga ki gyara min dakina" na wuce shi na shiga na fara harhada uban lodin kayansa duk daya barbaza a dakin, ga zazza蓳i gashi jikina babu kwari saboda amai. Shi kuma ya tsaya a kofar dakin ya harde hannayensa yana kallona. Na daga wata riga kenan naji kamshin turarensa ya doke ni sai amai, da kyar na karasa toilet na fara karara wa sai ya biyo ni ya tsaya a bakin toilet din yana kallona har na gama sannan yace "baki da lafiya?" Bance masa komai ba yace "me yake damunki?" Nace "zazza蓳i" yace "da amai?" Na girgiza kaina da sauri nace "warin turarenka ne ya saka ni aman" yace "amma ai kullum shi naje sakawa baki taba aman ba sai yanzu. Are you pregnant?" Nayi shiru bance masa komai ba sai yayi tsaki "ke bansan wacce irin mace ba ce ke, daga an taba ki kadan sai ciki" naji wani abu ya tsaya min a kirji na wuce shi na dawo daki ina cewa "tunda dai bani na hau kan kaina nayi wa kaina cikin ba ai da sauki. If you hate me that much ka sallameni mana in tafi" ya biyo ni yana cewa "and who says I hate you?" Na tsaya ina masa kallon kar ka raina min hankali, sai yace "idan da bana sonki Diyam da tuni kina gidan ku wallahi ko dan wannan rashin kunyar taki. Kuma yanzu ko dan wannan samun cikin da ake yi ai ya kamata ki fahimci cewa we are meant to be together. Ki kwantar da hankalin ki muyi rayuwar aure kinki, kin ki cire that Sadauki of a person daga zuriyar ki kuma... " Ban karasa jin abinda zai fada ba na fito daga dakin na koma nawa.
Washegari shi ya tashe ni da safe wai in shirya muje asibiti, muna zuwa ya samu doctorn dana lura kamar sun san juna yace "PT zaka mata Please" sai doctorn yayi dariya ya kira wata nurse ya hadamu muka je tayi min. And it came back positive. A ranar nayi kuka kamar idona zai fita.
Tunda muka koma gida ya tare a dakina yana jinya ta, shine bani magani shine yi min sannu da su hada min tea, ni duk na dauka jinyar Allah da annabi ce sai daya sauke bukatunsa a kaina sannan na fahimci inda jinyar ta dosa.
Kayan lefe dai mun cinye su, babu biya babu ranar biya. Sai kuma yazo ya dauki set din kayan kallo na palon sama ya siyar, daga nan sai set din gadon extra dakin da bama amfani dashi a sama, sai deep freezer. Duk abinda aka siyar daga an dan siyo kayan abinci an dan bani kudin cefane bana kuma sanin inda sauran kudin sukayi. A haka har cikina ya tasa yayi wata biyar.
Ranar nan na shiga kitchen na rasa me zan dafa mana na hawo sama na same shi akwance a gado yana daddanna waya. Nace "babu fa abinda za'a ci a gidan nan" sai ya saka hannu a aljihu ya zaro min yadin aljihun na karkade min ya cigaba da danna wayarsa. Sai na samu kaina da tambayar kaina menene role din Saghir a auren mu? Shi aikinsa kawai shine yayi min ciki? Na shigo ciki na zauna a kan bedside nace "Saghir idan ni da kai da uwani mun zauna da yunwa wannan" na nuna cikina, "bai san babu ba" ya kalli cikin nawa sai ya ajiye wayar yace "to wai me kike so inyi? Ni fa ko kudin man da zan zuba a mota in fita bani dashi, ko so kike a ganni a daidaita sahu ake nuna ni a gari? Ko kuma so kike in ke bin gidajen masu kudi ina cewa allazi wahidi? Ko kuma dako kike so in dauka ko lebura ko kuma aikin mechanic? Na fahimci abinda yasa ya fadi mechanic din, so yaje muyi fada inyi zuciya in rabu dashi amma sai nace "eh, so nake kayi duk abinda ka fada indai zaka samu halak dinka. Wai kai ba kayi karatu bane ba? Ina takardun ka, ka karkade su ka fita kane gurin abokan Alhaji su hada ka da connections din da zama samu aiki. At least if you can't be a good husband try to be a good father".
Bansan ya akayi ba kuma ina daki sai gashi da folder din takardu yace zai je gida ya kaiwa Alhaji, sai kuma yace "in na samo kudi a hannun Hajiya sai in taho mana da wani abun a hanya". Ni dai na rabu dashi a raina ina cewa lallai gata mugun abu. Na tuno Sadauki da rashin zamansa a guri daya, tun yana dan karamin sa Baffa ya nuna masa neman kudi. Sai nayi murmushi ina lissafin irin kudin da Sadauki zai tara in dai ya samu hanya.
Ban kuma tabbatar wa cewa Alhaji Babba ya fada kwata ba sai da muka je gidan few days after that. Mota daya ce a compound din, ita ma kuma daga ganin ta nasan an dade ba'a hau ta ba, komai babu, ni sai naga gidan kamar har wani duhu yayi. Shi kansa ya rame, kayan jikinsa sun tsufa, na gaishe shi ya amsa yana ta yake baki. Muka shiga cikin gida suna ta kallon cikina, Hajiya Babba har da yar min da magana wai da Inna ta hanani komawa bayan ni ina son mijina, ni dai bance mata komai ba. Itama naga dakinta yar aiki daya ce kawai kuma itama na tabbatar yan uwanta ne suka dauko mata. Hajiya Yalwati kam Allah ya taimake ta 拼a拼anta manya su uku sunyi nce sun fara teaching dan haka su suke daukan nauyinta da kannen su. Da zamu tafi su murja suka ce zasu bi mu amma Saghir ya rufe idonsa yace babu wadda zai dauka. Sai da muka dauki hanya ne yake cewa wai nauyi zasu dora masa in suka zo. Sai na tambayi kaina 'ba shine namiji ba, babban wa uba? Bashi ya kamata ya dauki nauyin kannensa ba amma shine mai gudun ciyar dasu na kwana biyu?"
Bayan munje gida yake gaya min "Alhaji ya hada ni da wani abokin sa shi kuma ya hada ni da wani mutum daya bude kamfanin siyar da motoci kwanan nan. Gobe zanje interview kiyi mana addu'a. Idan aikin nan ya fada ko? Hmmmm, ba karamin kudi suke dashi ba a gurin nan kuma kinsan accounting na karanta harkar kudin" ni dai nayi addu'a amma bansa ka rai ba saboda bansa ran zai samu aiki irin haka da wuri ba.
And to me surprise, sai gashi washegari da offer. "I nailed it. Diyam, I got it. Wato managern ne da kansa ya ganni, karamin yaro ne mai babbar harka. Kawai few personal questions yayi min shikenan yace 'you are hired' just like that fa, Diyam you are talking to the financial secretary of Abatcha Motors"
[2/8, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Eight : Subay'a
Na rike baki ina dariya, ko ba dan Saghir ba ko dan ni kaina da abinda yake cikina nayi murnar wannan aikin. Nace "Masha Allah. Alhamdulillah. Amma fa kayi sa'a, abinda mutane sai su dade suna neman aiki basu samu ba amma kai kaga lokaci daya ka samu" yayi dariya yana zama akan kujera yace "maybe mutanen da kike magana akan su basu san inda ya kamata su nemi aikin ba ko kuma basu dace da aikin ba. Kinsan appearance matters alot a gurin neman aiki, yanzu misali ni, kowa ya ganni yasan na chanchanta da post din dana samu" na zauna ina mamakin bragging irin na Saghir, nace "komai fa a rayuwa yana da lokaci, wadanda basu samu aiki ba lokacin samun su ne baiyi ba, kai kuma daka samu lokacin kane yayi, ita rayuwa....." Ya daga min hannu "don't spoil my mood please. Je ki kawo min ruwa" nayi ajjiyar zuciya na tashi.
Ranar daya fara zuwa office ne bayan ya dawo na tambaye shi "to an baka office? Da fatan sun fara baka aiki kanayi" yace "wanne irin aiki kuma?" Nace "rubuce rubuce mana, ba shine aikin secretaries ba?" Yayi tsaki yace "fin sec fa aka ce miki, ni harkar shiga da fitar kudi a companyn ne kawai part dina, besides, ina da mataimaki so shi zaike handling duk aiyuka" nace "so? Kai menene naka aikin?" Yace "who cares about aiki ne wai, what I care about is the salary kuma zasu ke bani mai kyau shikenan".
Tunda aiki ya samu kuma shikenan Saghir ya koma tsohuwar rayuwar sa, inya fita tun sassafe baya dawowa gida wani lokacin ma har sai nayi bacci. Baya zuwa gida a bige, amma hakan bawai yana nufin ya daina bane ba dan sau da yawa in ina gyaran kayansa nakan ji wannan warin a jiki, sai dai bani da wani kwakwkwaran hujja. Yana ciyar damu, duk da dai considering yadda yake kashewa jikinsa kudi baya yi mana yadda ya kamata amma dai muna cin abinci. Shi kuwa kullum cikin sababbin dinkuna yake yakance "gwara mutum yayi dressing sosai kar a raina masa hankali".
Cikina yana ta girma abinsa, ni kuwa babu komai a raina sai fargaba dan kuwa har yau ban manta da wahalar da nasha a waccan haihuwar ba, gashi wannan cikin duk da cewa daya ne a ciki amma tafi wancan cikin girma, wannan yasa tun cikin yana waya bakwai na tattaro kayana na dawo kasa kusa da uwani kuma kullum ways ta tana kusa dani dan am not looking forward to haihuwa ni kadai irin waccan.
Amma lokacin da muka je scanning tare da Saghir, bayan an gama mun zauna sai doctor yace "am afraid ba zaki haihu da kanki ba, dole za'a yi miki cs ne" duk muka bude baki da mamaki, Saghir yace "ta taba haihuwa fa doctor, twins ma" doctor ya dauko takardar scan din yace "tana da abinda a likitance muke kira da placenta previa. A ka'ida in aka tashi haihuwa 蓷a ne a farko sai an haife shi sannan sai mabiyya ta biyo baya. But in her case mabiyyar ce a farko sannan dan, meaning ko da ace ta fara labour to placenta ce zata yi blocking babyn yadda ba zai fito ba so babu yadda za'ayi sai dai ayi delivering through cs" na fara kuka, ni takaicina shine yanzu wai yanka cikina za'ayi a fito da babyn ni Diyam, kai mata munga ta kan mu. Saghir yayi tsaki yace "kuma menene abin kuka a ciki? Ke da ya kamata kiyi murna ma babu ke babu wahalar haihuwa. Sai ni aka bari da wahalar kudi".
Alayi fixing date, a week to my edd sai dai da sharadin in naji nakuda kafin lokacin muyi sauri mu tafi. Na dage kullum da addu'a, na kuma gayawa su inna suma suka tayani da addu'a har Allah ya nuna mana lokacin. Mama ce tazo gidan muka tafi tare, dama Inna tunda nayi aure bata taba zuwa gida na ba. Tun a day to aikin mukaje suka bamu gado muka kwana a can, sukayi duk gwaje gwajen da zasuyi sannan washegari sai ga Hajiya Yalwati tazo daga gidan Alhaji Babba, har aka zo aka gama shirya ni babu Saghir babu labarin sa. Naji duk jikina yayi sanyi. Anzo ance lokaci yayi na dauko waya ta and I found myself dialing number din Sadauki, hoping to hear his voice just once more amma naji a kashe na kashe wayar na ajiye feeling so lonely kanar ni kadai ce a duniyar. Mama da Hajiya Yalwati suna ta lallashina suna min addu'a a haka aka shiga dani.
Aikin mai bacci akayi min saboda jini na yaki karbar na ido biyun. Dan haka duk abinda akayi ban sani ba har aka gama aka fito dani dakin hutawa. Anan ne na dan farka kadan naga Inna a zaune kusa dani ta rike hannuna, gefe kuma Mama da baby a hannun ta "Sadauki" na fada cikin bacci, "inna ki kira Sadauki kice yazo ya duba ni" sai na kuma komawa bacci. Sanda na sake farkawa doctor na gani da nurse a kaina, suka yi min sannu daga nan na sake komawa.
Sanda nayi final farkawa kuma babu kowa a dakin sai ni kadai, na bude idona ina ta kalle kalle ina jin kaina yana ciwo sai na hango Saghir a can kusa da window da alama waya yakeyi. Irin yadda naga yana bada respect ga wanda suke wayar yasa ni son sanin ko wanene saboda ban taba ganin yana magana irin haka ba. Sai daya gama sannan ya juyo, muka hada ido yayi murmushi ya nuna wayar yace "my boss. Ya kira yaji ya jikin ki saboda na fada masa za'ayi miki aiki. Yana da kirki sosai. Can you believe he paid for everything hadda karin kudin ragon suna?" Na rufe idona na dauke kai ina jin haushinsa har cikin raina, wato abinda zai fara fadamin kenan bayan an yanka ni an fito da jaririn daya saka a ciki?
Sai yazo ya dafa kafada ta "am sorry banzo ba tun jiya, I am not good at all this emotional stuff ne shi yasa nayi zamana a gida kawai" sai kuma ya juya ya tafi gurin crib din baby ya dauko yana murmushi, na yi kokarin tashi amma na kasa nace "kawo min, menene?" Yayi dariya "au baki ganta ba? Baby girl ce, so beautiful like her mother" this is the first time daya kirani beautiful. Ya karaso ya sunkuyo yana nuna min ita, and he was right, she is so beautiful but tafi kama dashi because she looked just like twins dina, just ta fisu girma sosai.
Nayi murmushi ina jin attraction so much like wanda naji akan twins. Na daga hannu na shafa kanta ina murmushi, yace "inye, Diyam an zama uwa, sai ki daina yi min rashin kunya in ba haka ba zan saka take rama min" ya jima yana ta surutun sa shi kadai sannan ya mayar da babyn cikin crib dinta ya dauko waya yayi ta daukan ta pictures sannan yazo yayi kissing dina a goshi ya fita.
Four days nayi a asibitin. I was so in love with my daughter naji tamkar na samu another reason to live. Sau daya Saghir ya dawo ya tambayi Inna ko akwai abinda muke bukata, ya dauki daughter dinsa sannan yayi min sannu ya fita, and that was all, ko abinci ba'a taba kawo mana daga gidan Alhaji Babba ba. Wannan yasa ranar da aka sallame mu muka wuce gidan Inna, shi ogan ma baisan an sallame mu ba sai daya kira ni naki dauka sannan ya kira uwani tace ai an sallame mu sai kuma gashi a gidan Inna, wai ai ba'a gaya masa zan zo gida ba, ya gama rashin kunyar sa ya fita. Inna tana ta mitar abin, a raina nace "zabin ki ne dai". Tunda Hajiya Babba taje ta dubani a asibiti bata kuma zuwa ba, shima Alhaji Babba ko leke sai yace ace min baya jin dadi ni kuwa nasan dan mace na haifa ne da namiji ne da ko da rarrafe sai yazo.
Kullum in ana kallon yarinyar nan sai na tuno Sadauki, lissafin mu ni da shi shine mu haifi girl mu saka mata Subay'a, to ga girl din kuma na samu amma bata Sadauki ba, gashi ko sunanta ban sani ba duk da nasan yayi mata huduba gaya min ne kawai baiyi ba. Sai ranar suna da safe ya kirani "anyi radin suna a gidan Alhaji. An saka mata Saratu" sunan Hajiya Babba. Na runtse idona ina jin haushin sunan, nace "Allah ya raya, zamu sami wani sunan da zamu ke gaya mata" yace "already na riga na samu, Subay'a" na maimaita cikin mamaki "Subay'a?" Yace "yes, ko ba kya so?" Nace "no, ina so, a ina ka sami sunan?" Yace "my boss called, ya nemi alfarmar duk sunan da aka sawa baby a ce mata Subay'a, and I see no harm in honouring his wish. Besides, shi ya sayi ragon suna" ya karashe maganar yana dariya. Na kashe wayar ina mamakin me yasa boss dinsa zai ce a gaya wa babyn mu Subay'a? Inna ta tambayeni suna nace mata sunan Hajiya Babba ne za'a ke ce mata Subay'a, ta maimaita sunan tana kallona.
An dan taru a gidan sunan babu laifi, duk da cewa yan'uwa ne kadai kuma yanuwana da nasa duk daya ne, sannan ni ba kawaye ba ba makota ba, sai makotan mu na nan gidan da suka shishshigo mana. Abincin suna ma Saghir baiyi ba, cewa yayi ai ba shi yace in taho gida ba dan haka wanda ya kawo ni gidan sai yayi abincin sunan. Ragon sunan ma a gidan Alhaji Babba aka yanka aka soya aka kuma raba sai namu rabon aka kawo mana a kwano. Bayan suna Mama tazo ta dauke ni muka je asibiti, ni na dauka wani check up za'ayi min sai naga an saka min wani abu mai kamar allura a dantsen hannuna ashe abin family planning ne aka saka min na shekara biyar.
Satina biyu a gida Saghir yazo yace ai na warke haka, in shirya in koma. Haka ina kuka ina komai na hada kayana dana Subay'a, Allah ma yaso Asma'u tana hutu nace tazo mu tafi, itama kuma tana shiga mota yace da iznin wa zan tafi da ita? And that kept me wondering if I don't have a say in my own marriage. Shin miji shi kadai ne mai making every decision, ita mace bata da nata ra'ayin? Ko kuma ita mace bata da zuciya ne a kirjinta?
Bayan komawar mu gida ne nayi realizing something, Saghir's weakness lies in his daughter. Yana son Subay'a sosai da sosai dan zan iya cewa yana sonta fiye da komai a duniya. Kullum tana hannunsa sai dai in baya gida ko kuma in zanyi feeding dinta. A lokacin ne kuma aka fara daukan sabon session na makaranta, a lokacin yan set din mu zasu shiga ss3. Nayi wa Saghir maganar komawa ta school sai cewa yayi "ita kuma Subay'a fa? Yaya kike so ayi da ita? Sai dai ki bari sai wani session din kafin nan tayi kwari" sai ya kara da cewa "in kuma kafin nan kin kuma samun wani cikin shikenan" ban mayar masa da magana ba saboda bai san zancen implant dina ba, haka na hakura da zancen makaranta dan babu yadda zanyi, in nace zan kai kara ma bayan sa za'a bi ace in bari yarinya ta tayi kwari.
A lokacin ne kuma yake sanar dani cewa ogansa zai tafi kasar waje karatu "he will be managing the company from there, kin san komai yanzu an mayar dashi computerized ballantana manyan harkoki irin na wadannan mutanen" nayi kamar ban ji shi ba dan ni har na gaji da maganar ogan nan, kullum oga this oga that, oga yace kaza oga yayi kaza, I wonder me suke yi a office din bayan zaman hira.
Manage this please. Ina dan busy ne kwana biyu but I promise you a sweet episode tomorrow insha Allah.
[2/9, 9:39 PM] +234 706 813 0709: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Thirty Nine : The Boss
Bayan Shekara Biyar
Shekaru biyar suka zo suka wuce. A cikin su abubuwa da dama sun faru, na farko Hardo da Uwani duk sun rasu sati daya a tsakaninsu, Hardo ne ya fara rasuwa munje Kollere zaman makoki itama uwani ta kama jinya sannan ta rasu ranar sadakar bakwai dinsa. Naji mutuwar Uwani sosai kusan fiye da yadda naji ta Hardo.
Rayuwata a gidan Saghir babu abinda ya chanza sai abinda ya kara gaba, ya dawo da shaye shayensa, ya kuma mayar da neman matansa openly wanda da yana dan boyewa amma yanzu kiri kiri yake yi musamman tunda kudade suna shigo masa, har gida mata suke zuwa neman Saghir, tun yana yi min karyar cewa abokan aikin sa ne har ya daina. Lokuta da dama kuma yana dora min laifin neman matansa, yace nice na gaza sauke masa hakkin sa shi yasa yake zuwa yake nema a waje wanda ni kaina nasan ina da laifi ta wannan bangaren, nayi nayi in tursasa zuciyata ko yayane in saka Saghir a cikinta amma taki yarda, Sadauki ya riga ya chika duk wani lungu da sako na zuciyata yadda babu wani bugawar da zata yi wanda babu tunanin sa a ciki. It was so hard living with a man while my heart belongs to another. Another din da ban ma san inda yake ba, babu amo babu labarin sa daga shi har yaya ladi. Sometimes sai in samu kaina da tambayar ko wanne hali yake ciki? Ko ya samu admission din yayi karatun? Ko rayuwa tana tafiyar masa dai dai ko kuma akasin haka?
Amma kuma hausawa sunce idan bera da sata daddawa ma da warinta. Ina da laifi a zaman mu da Saghir na sani amma shima ai da laifinsa, at least da ace yana treating dina well da ko ban so shi ba bazan ki shi ba, da zan iya managing in faranta masa as long as nima yana faranta min amma Saghir was doing total opposite of faranta min. Tsawa, hantara, bakar magana and occational duka duk ina samu daga gurin Saghir. Yana ciyar dani, barely, dan duk ranar dana ganshi da leda a hannu ko kuma naga yana yi min murmushi to nasan wani abun yake nema a gurina ni kuma a lokacin zan tayar da tawa tsiyar har sai mun rabu baran baran.
Na koma makaranta bayan na yaye Subay'a, shima da kyar Saghir ya bari har saida na hada shi ta Hardo lokacin yana da rai sannan ya saka ni a wata government school anan bayan layin mu. Na fuskanci challenges da yawa a lokacin musamman saboda kasancewa ta matar aure a makarantar yan mata, kuma duk yan class din na girme musu dan ma bani da girman jiki dan haka da wahala ma ka gane shekaru ma, babu kuma wanda yake yarda nina haifi subay'a musamman saboda tana da girma sosai ita. Har nuna ni ake yi, ni kuwa sai naja kaina gefe nayi facing karatuna kadai wannan yasa har na kammala banyi wadansu kawaye ba sai dai gaisawa kadai.
Inna tana ci gaba da kasuwancin ta, dashi suke ci, sha da sutura ita da Asma'u kuma dashi take biya wa Asma'u kudin makaranta, ta gaya min cewa tunda ta bar gidan Alhaji Babba, kaf yanuwan Baffa babu wanda ya taba daukar kwandala ya bata yace ki siyawa Asma'u ruwa, komai ita take yi musu wani lokacin ma harni take dan dinkawa kaya ta aiko min dashi tunda nawa mijin ba mai yi bane ba. Zai dai dinkawa kansa suttura kamar banza, yayi ta shiga yana fita, mayukan shafawarsa da turarukansa ma kadai abin jinjinawa ne amma ni kayan kyalliya tun na lefe na, da suka kare da wahala yake siyamin wani abu dana yi maganar kayan lefe na ma sai cewa tayi "da uban waye ya siya miki kayan?".
A lokacin da nayi candy a lokacin nake da shekara ashirin da daya, Subay'a tana da shekaru biyar. Har lokacin kuma ina nan jiya iyau, babu abinda na kara a girman jiki sai ma kara motsewa da nayi wadda rannan da Inna take mita naji Mama tace yana da dangantaka da planning din da nake yi, maybe in ya barni zan yi kibar. Sometimes Saghir ma da kansa yana complain "Diyam kina da kyau sosai a fuska, mu maza kuma ba wannan kadai muke bukata ba muna son mace mai lady body parts" yana magana yana nuna irin parts din da yake nufi, nakan bashi amsa da "ai bani na halicci kaina ba, dan haka bani zakayi wa complain ba".
Ranar nan nayi bakuwa, Maman Iman, tazo ta wunar min ita da yaranta da Asma'u na wadda ta shiga ss2 yanzu. Sai Maman Iman ta dauko wasu kulle kulle a leda ta jani bedroom dina ta fara tsaramin
"kinga wannan garin da nono zaki ke sha ko da madara, kamar bayan la'asar haka yadda kafin dare ya fara aiki. Shi kuma wannan gumba ce ki adaba kina cin kayar ki a hankali tana da amfani sosai, wannan kuma na tsuguno ne, ki barbada shi a garwashin wuta sai ki tsugunna a kai ya shiga jikin ki sosai"
Nasan magungunan menene dan kusan duk sanda naje gida sai ta bani irinsu, wani lokacin ina fitowa nake zubawa a kwatar kofar gida inyi tafiya ta. Amma sai nace "maganin menene wannan maman iman? Maganin tajika ne ko kuma na mayu" ta harare ne "a'a maganin sihiri ne. Kar ki raina min hankali mana Diyam, kinsan nawa na saka na sayi maganin nan kuwa? Wannan na tsugunnon da kyar ma na same shi shine na raba biyu na kawo miki rabi amma zaki raina min hankali" nayi dariya nace "maida wukar yayata ta kaina. Amma ki tafi da kayanki kar inyi miki asarar kudi dan wallahi ba amfani zanyi dasu ba" na fada ina dora mata akan cinyarta, ta dawo min dasu kan tawa cinyar tace "wallahi ki gwada ki gani, matar data bani ta tabbatar min da cewa indai kika yi amfani da wannan yadda kika san cingam haka mijin ki zai manne miki" nayi dariya na sake mayar mata nace "bana son ya manne min kamar cingam, ki kara akan naki sai abban iman ya kara manne miki kamar superglue" kafin ta bani amsa aka budo kofar dakin da kallo, Saghir ya tsaya yana kallon mu sannan yace "dan wulakanci kinsan ma dawo amma kika yi zaman ki ba zaki zo ki bani abinci ba" Maman Iman ta gaishe shi, yayi mata kallo daya ya dauke kai fice. Na mike nabi bayansa idona blurry with tears, yaushe wannan zubar hawayen nawa zai kare? Indai har nayi baki, ko kuma shi yayi baki, to kuwa tabbas sai ya wulakanta ni a gabansu, shi yasa har banaso inyi baki indai tana gida.
Washegari muna kasa ina taya Subay'a yin homework dinta sai gashi ya dawo daga office. Ta tashi da gudu ta tafi gurinsa shi kuma ya daga ta sama yana juyata suna dariya. Na gaishe shi ya amsa ciki ciki sannan direct ya wuce dining ya zauna ya zaunar da Subay'a a kan table din ya fara zuba abinci suna hira. Na taso na karba ina zuba masa nace "Subay'a sauka ki zauna akan kujera, na hana ki zama akan table ko?" Ta kwabe fuska tana kallonsa yace "ita da gidan ubanta, table din ubanta kuma abincin ubanta" yana fada yana yi mata chakulkuli tana babbaka dariya, garin dariyar har ta zubar da abincin dana fara zuba masa. Nayi ajjiyar zuciya na zagaye su na wuce kitchen na dauko duster nayi clearing gurin, sannan na sake zuba masa wani. Ban mayi mata fada ba dan nasan indai yana gurin to ban isa ba, maybe a karshe ya kare da zagina a gabanta. Sai daya gama sannan ya kama hannunta suka yi sama sannan suka sake saukowa tare, ya chanza kaya, yace min "zan koma office, muna ta shirye shirye oga zai dawo office ranar monday" na gyada kai nace "a dawo lafiya" a raina ina cewa "gyara ya dawo din ai ko ka mayar da hankali gurin aikin" ni nayi mamaki ma da har yau basu kore shi ba saboda sai yayi sati baije ba, na kuma ji labarin cewa company basa yadda da irin wannan kailular.
Ranar Monday din da yamma, ina daki ina karatun novels a waya ina ta murmushi ni kadai ganin yadda mata suke soyewa a gidan mazajen su, sai naji shigowar sa, nayi sauri na boye wayar dan ya hana ni yace anan nake kara koyon rashin kunya. Ya shigo dakin babu sallama kamar kullum, ya karaso ya tsaya a gaban gado da leda a hannunsa yace "ga wannan ki tashi kiyi wanka ki saka, and please kiyi kwalliya mai kyau, in an jima da dare zamuje party" na zauna ina fito da kayan nace "party? Biki ake yi?" Ya zauna a kusa dani yana cire takalmi yace "no, wani surprise party ne muka shirya wa ogan mu a office, manyan ma'aikata duk kowa zai zo da familyn sa shi kuma za'a kira shi as far ana nemansa dinnan da gaggawa sai yazo zai gan mu" yayi tsaki "ni idea din sam bata yi min ba, tunda akace zai dawo kowa sai wani rawar kai yakeyi kowa yana neman gindin zama". Nayi murmushi kawai ina duba kayan. Doguwar riga ce mai dan karen kyau daga gani nasan an saka kudi masu yawa gurin siyan ta kuma ba dan ni aka siya ba sai dan a burge mutane. Nayi wani tunani, I had never been to a party before, what if naje na kwabsa mishi? What if yaje ya dizga ni a cikin mutane?
Kamar yasan tunanin da nake yi sai cewa yayi "but please Diyam, please don't embarrass me a cikin mutanen nan, my entire reputation depends on this, please don't do anything stupid" na mayar da rigar cikin ledarta nace "if it will make you feel better, ka tafi kai kadai kawai. Ni ba saba shiga cikin irin wadannan mutanen nayi ba" ya bude baki yace "salon a raina ni? Ace bani da iyali? Ki shirya kawai muje Allah dai ya kiyaye ni da jin kunya".
Shi ya dauko Subay'a daga islamiyya ya kaita makotan mu inda naje ajiyeta sanda ina school. Sannan ya dawo yace min in nayi sallar magrib in shirya shima zaije ya shirya. Na tashi na shiga wanka kawai naji jikina yayi wani irin sanyi zuciyata tana ta bugawa, ni duk ji nake yi bana son zuwa gurin taron nan nasu gani nake yi kamar wani abu ne zai faru idan naje amma babu yadda zanyi haka nayi wanka na fito, na shafa mai na saka rigar daya kawo min. Golden color ce da akayi mata agon stones na silver, sai veil silver da stones golden. Ina sakawa Saghir ya shigo yana fadan har yanzu ban gama shiryawa ba, sai kuma yayi shiru yana kare min kallo da sakakken baki. "You look really beautiful" na dauke kai ina kallon kaina a mirror, babu abinda na sakawa fuskata in banda kwalli amma ta fito fes tana kyalli, kayan jikina sun kara haskaka fatata, sai naga ya saka hannunsa a aljihu ya dauko wata sarkar gold ya karaso ya saka min a wuyana, sai kuma yayi kissing wuyan, nayi saurin matsawa ina wayencewa da saka yan kunnayen daya ajiye. Ya sake biyo ni ya dauki comb yana taje min gashin kaina zuwa baya sannan ya saka ribbon ya daure min shi a keya side din hagu ya zubo dashi ta kafada ta yana cewa "let's show them abinda matan su basu dashi" Na cire ribbon din ina girgiza kaina nace "babu kyau fito da gashi ga wadanda ba muharramai ba" yayi tsaki, "ke chafsi ne dake wallahi" a raina nace 'naji din' na daure gashina a tsakiya kamar kullum sannan na nannade shi sai nayi rolling veil din irin yadda naga su Rumaisa yammata suna yi. Sai kawai na tsaya ina kallon kaina a madubi, ban taba ganin nayi kyau irin na ranar nan ba. I looked like baby doll din da kullum ake kwatanta ni da ita. Na rike clutch silver sannan na saka silver hills masu tsinin da suka kara min tsaho. Ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin mirror yace "perfect, ina ma kin fi haka girma but hakan ma is okay. Am sure babu wanda zaizo da mata irin tawa".
A hankali muke tafiya, kowa da abinda yake zuciyarsa. Ni tawa zuciyar wani irin bugawa take yi wanka har daci naje ji a bakina, a tsorace nake sosai kamar in bude motar in fita a guje. Har muka je gurin, wannan shine karo na na farko da naje companyn Abatcha Motors. Dare ne kuma kusan duk fitulun gurin a kashe suke saboda basa son idan ogan yazo yayi tunanin wani abu, dan haka a lokacin bazan iya adar da komai dangane da yanayin gurin ba, baya muka zagaya mukayi packing, nan naga duk kowa yana packing ana ta fitowa kowa da matarsa ko budurwar sa. Saghir ya juyo ya kalle ni yaga yadda nake a tsorace yace "bafa cinye ki za'ayi ba, just do as i do. Duk wanda kika ga nayi wa magana sai ki gaishe shi, ba kuma cewa nayi ki durkusa har kasa kina gaishe da mutane ba" na gyada masa kai muka fita a tare, ya zagayo ya zura hannunsa cikin nawa muka shiga cikin mutane. Faran faran muke gaisawa da mutane kowa yana introducing matarsa, Saghir proudly yake nuna ni a matsayin matarsa, ina kuma lura da yadda idanuwa suke bina da kallon yabawa. Sai da aka gama gaggaisawa sannan muka zagaya muka shiga cikin building din gaba ki daya, nan ma babu fitulu sai guda daya dan haka dimly kowa ya samu guri ya zauna ana jiran wanda ya tafi tahowa da oga su dawo.una nan zaune ana dan hira kadan kadan suka shigo, sai aka yi saurin kashe fitila dayar da aka kunna gurin yayi duhu daga ki daya. Muna jinsu suka karaso suna yan maganganu. And my heart stopped at the sound of the voice I heard.
Sukayi unlocking kofar suka shigo cikin inda muke, and I heard one of them said "Mubarak let's hurry up and do this. I am kind of tired" clearly in Sadauki's voice. Na zare hannuna daga cikin na Saghir na mike tsaye da sauri "Sadauki!" Na fada under my breath. Sai kuma lokaci daya fitulun gurin suka kama gaba-daya yan gurin kuma suka hada baki wajan ambaton "surprise!!" Then I saw Sadauki a tsaye a gaba na, idanunsa cikin nawa.
Komai ya tsaya min. Numfashi na ya dauke, na saki jakar dana ke rike da ita a hannuna and ikon Allah ne kadai yasa nima ban bi jakar na fadi ba. Sadaukin ne dai a tsaye yana kallona, my Sadauki. But he has changed alot, he has grown more bigger and more muscular, his dark skin shining as brightly as his bright eyes. He looked more matured, more handsome, more confident and he looked rich. Very rich.
In a flash of second aka zagaye shi, kowa yana kokarin yi masa magana hakan yayi blocking view tsakanin mu, "what is Sadauki doing here?" Shine tambayar dana fara yiwa kaina a lokacin da numfashi na ya dawo jikina. Maganar Saghir da naji a kusa dani ita ta dawo dani hayyacina har na tuna me ya kawo mu gurin, but banji mai yaxe ba saboda voice dinsa sound so faraway kamar daga miles yake yi min maganar, the only sound da yayi filling kunnena shine na Sadauki yana gaisawa da mutane. Na girgiza kaina, trying to clear my head nace "me kace?" Tsaki kawai yayi, ya kama hannuna muma muka shiga mutanen da suka zagaye Sadauki suna gaishe shi tare dayi masa congratulations na kammala karatu. "karatu?" Na tambayi kaina. Menene hadin Sadauki da gurin nan wai? Mu ba zuwa mukayi mu taya ogan su Saghir murnar dawowa daga karatun sa ba? Ya naga kuma anayi wa Sadauki murna?
Ban samu amsar tambaya ta ba na ganmu tsaye a gaban Sadauki ni da Saghir, Saghir ya mika masa hannu yace "congratulations Mr Abatcha, and welcome back to Kano" sukayi shaking hands, nabi hannayen nasu da kallo sannan na sauke ido na akan Sadauki, trying to digest what I was beginning to understand.
Mintsini Saghir ya sakar min a hannu sannan cikin whisper yace min "for God's sake stop staring at him and greet him" sai kawai nabi Saghir din da kallo ba tare da nace komai ba, kamar daga sama naji muryar Sadauki yace "Hello Madam" na juya ina kallonsa, sai naga kamar ya saka wani mask ne yayi hiding Sadauki na, kamar this man is not the Sadauki I knew, this man is Mr Abatcha.
0 comments:
Post a Comment