"Hihhhhhhh, ya dahu?". Kanshi ya rausayar tare daci gaba da ɓare kwan saida ya ɓaresh tas ya fito subul gwannin ban sha'awa, sai turiri yaketayi, Junainah ya miƙa.
"Karɓi kici kiji mana, kwan ya nuna ne Ƙanwaliya".
Da sauri tasa hannu, zata amsa, cikin sanyi Aysha tace.
"Ke uwar kwaɗayi bazaki ciba".
Rau-rau tayi da idanu alamun zatayi kuka, shi kuwa Ba'ana fuskarshi ya haɗa tare da kafeta da ido, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana mai wasa da ƴan yatsun hannunta, dubanshi ya maida kan Junainah tare da cewa.
"Kici abinki Junainah". Fuskarshi ya ƙara haɗawa jin Aysha ta kuma cewa.
"Dan Allah Ya Ba'ana kada taci".
Ba tare daya kalleta ba, tace.
"Kema zakici ai bare ita". Da sauri ta ɗago kanta tare da girgiza kan tace.
"A a ni kam ngd bazanci abinda ban san da me aka dafashi ba".
juyowa yayi ya kalli Junainah da tuni ta fara cin kwanta, tana lumshe ido baki cike da kwan tace.
"Ya Ba'ana bari inje cikin gida in kawo mana yaji mai daɗi Addana bata cin kwai saida yaji".
To yace mata, tuni ta juya tayi cikin gida.
Kallonshi ya maida kan Shatu cikin haɗe fuska yace.
"Mata kina tunanin zan cutar da kene?".
A hankali ta jujjuya mishi kai alamun a'a, gyara zamanshi, yayi tare da cewa.
"To baki yarda dani bane?".
A hankali ta buɗi bakinta tace.
"A'a ni dai tsoron abun naji, ka toni rami mai danshi da sanyin yashin damina, ka binne ɗanyen kwai mai sanyi ka fito dashi da zafi a dafe ni kam ina tsoro ban san da wutan me ka dafashiba".
Fuskarta-ta yayi da kyau kana, ya fara magana.
"Ki yarda dani Mata, bazan taɓa cutar dakeba a rayuwa, duk abinda zakiga inayi, zanyine dan kare lfyarki da kuma baki kariyar. Jikin ki, kici kwannan, babu abinda zai miki".
A hankali tace,
"Ni bana cin kwai dama, kuma ai shi kariya Allah ke hadashi ga dukkan bayinsa".
hannu yasa ya amshi robar dakekken yaji da Junainah ta miƙo mishi, wacce yanzu ta dawo wurin.
Wani kwan ya kuma ɓare mata, ya miƙa mata, tanaci tana lumshe ido saida taci biyar, sannan tace.
"Ya Ba'ana na ƙoshi". Shatu ya ɗan kalla tare da cewa.
"Saura biyar kuma nakine, in kin shiga gida kicishi, sannan kuma akwai wani haɗin maganin da zan kawo miki kiyi amfani dashi. Ni yanzu zan tafi".
Kai ta gyaɗa mishi alamar to, kana kuma tace.
"Ina zakaje yanzu? Tunda naga lokacin tafiya kiwo dai ya wuce".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Zan shiga ƙauyen Bonon ne".
Da mmki a fuskarta tace.
"Ya Ba'ana me zakayi kuma a ƙauye Bonon garin masafa kafurai ƙabulun Ɓachama".
Ido ya zuba mata har saida taji tsoronshi a hankali yace.
"Kema watan watarana zakije, ki tuna da kyau Mamata ƙabilar ɓachama ce, ƴar garin Bonon kinga kuwa dole inje can tunda kawuneina ƙannen Mama da yayunta da iyayenta duk suna can".
Ya ƙarishe mgnar kamsr yaji zafin zancen ta,
ganin hakane yasa a hankali tace.
"Kayi haƙuri". Kai ya juya mata alamar babu damuwa.
Daga nan ya juya ya tafi, ita kuwa tacewa Junainah su shiga gida.
Suna shiga cikin gidan ta harari Junainah tare da kai mata bugu cikin faɗa tace.
"Hegiya kwaɗayayya maza ki zubar da sauran kwanan jakar yarinya ai sai ya ciyar dake guba tunda kince ke kwaɗayayya ce".
Ihu Junainah ta kurma tare da cewa.
"Wayyoooooooo Inna kin ganta ko tana cin zalina". a guje tayi gaba, ita kuwa Shatu tabi bayanta da sassarfa tana cewa.
"Wallahi sai kin zubda ƙoyayen nan".
A haka suka isa har gaban Ummey da inna da suketa tafasa nonon da aka tatsa a sanyin safiyar yau, wanda a ƙalla ya kai jarka goms sha uku, so masu gidajen fura da nono na cikin Shikan ɗin nema suke saya, dan matan gidan Bappa kab bai lamunce da zuwansu tallan nono ba.
Inna ce tayi saurin kare Junainah dan saura ƙiris ta abka cikin tafasasshen nono da yanzu aka sauƙeshi, cikin tsoro tace.
"Kai ya ilahi ku dai bazaku zauna lfy ba". Cikin nitsuwa Shatu ta zauna gefen Ummey nan ta labarta musu abinda ya faru da yadda ya dafa kwan ta ƙara da cewa.
"Amman da yake Junainah uwar kwaɗayi ce, a take a gabanshi taci kwai biyar cas tanaci tana lumshe ido".
Cikin tarin mamaki Inna da Ummey sukayi ta salati tare da tafa hannu, a tare sukace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, oh wannan yaron anya kuwa mutun ne ba shaiɗan ba?".
Cikin rau-rau da ido, Shatu tace.
"Ni ina jin tsoronshi, bana sonshi bazan aureshiba, mutumin da komai nashi na tsafine Inna ki cewa Bappa ya rabani dashi mana".
Cikin alhini, Inna tace.
"Rashin sani yasa Bappanki dama ke kanki kukayi mishi al'ƙawarin shine mijinki duk rintsi, gashi yanzu ya zame mana masifa.
Juyowa sukayi suka kalli Ummey da idonta ya ciki da hawaye a hankali tace.
"Dana sani wlh da ban bar haka ta faru ba".
Shiru sukayi cirko-cirko a wurin, saida suka jiyo ƙaurin nono na zuba cikin murhune suka dawo haiyacinsu.
Kana suka juya suka ci gaba da aikin su.
A birnin Jalaluddin kuwa ƙarfe tara na safiyar ranar, dai-dai jirginsu Sitti da jikanta Sheykh ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki da sauran taro al'ummar Annabi masu zuwa Umrah.
Soyayyar da Sitti keyiwa Sheykh soyayyace mai tarin yawa, wanda ko uwa iya son da zatayiwa ɗanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ƙil hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba'in da bakwai.
Bar jikoki da ƙanne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya ɗaura babban ɗanshi wanda yake ƙanin Sitti ne uwa ɗaya uba ɗaya a matsayin shi.
Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru ɗari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ƙuruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ƙasar Kautal na wancan ƙarnin yazo da babban ɗansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita ɗaya ba.
Tuni ita kam Allah ya mata rasuwa mahaifiyar Sittin kenan, yanzu mahaifinta ne kadai a raye, sai kuma ƙanninta da yake matsayin ɗaya daga cikin manyan limaman harami a yanzu sai sauran zuriyarta da yayu da kannenta.
Kowa na ahlinsu yasan Sheykh domin Sitti tana yawan zuwa dashi tun yana ƙarami, kana tana zuwa da sauran ma baki ɗaya, to shi Jabeer anan ƙasar saudia ya haɗa digiri ɗinshi na forko dana biyu. Shiyasa ya zama duk zuriyar an sanshi farin sani, ga kuma tarin kama da yakeyi da mutanen zuriyar wanda da zaran ka ganshi kasan jininsu ne.
Tafiya mai tsowo sukeyi cikin sararin samaniya suna keta gajumare, a ƙalla tsawon aha huɗu kenan suna tafiya.
Kafin suka sauƙa cikin babban Airport ɗin jidda, wanda yake tamkar zai fashe da jirage, ko wacce ƙasa ta duniya tanada jirginta cikin wannan babban Airport ɗin, tashin jirage da hawa da sauƙansu tamkar babu wani abun hawa a duniya sai jirgi.
Koda suka fito daga jirgin, wani jirgine na musamman suka shiga wanda yake daga fadar Mai Alfarma masarautar garin. Wanda ya turo a tarɓi ƴar uwar abokinshi da mahaifinsu keta begen gani.
A take suka shiga jirgin ya wuce dasu, asalin cikin garin makka, wanda pilot ɗin kuma ɗane ga Umaymah ƙanwar Mamansu Sheykh wato shima jikan Sitti ne ɗan Umaymah sai kuma Jannart wacce ta biyo Haroon Dan tarban kakar tasu wacce ita kuma ƴace ga babban ɗan Sitti wato ƙanwar Juwairiyya ce kuma anan take karatu.
Suna sauƙa a Airport ɗin,
suka fito, a jere, yana gaba yana rike da hannun Sitti tana biye dashi a hankali tana taka step ɗin Jannart kuwa tuni itace a gaba.
Haroon ne wanda yake biye dasu a baya yana kallon yadda kakar tasu ke taka step da kuma yadda ɗan uwan nashi ke rike da hannun ta, murmushi yayi tare da jingina a ƙofar bakin jirgin cikin harshen larabci yace.
"Ko dai zaka goyeta ne ka sauƙar da ita".
Sheykh bai kulashi ba, har saida suka sauƙo ya gyarawa Sitti tsayuwarta, kana ya miƙawa Jannart hannun Sitti alamun ta rike musu ita. Cikin jin daɗi Jannart ta riko hannunta tare da cewa.
"Ana Uhubbiki ya Sitti". Cikin jin daɗi da son jikokin nata tace.
"Ana". Sai kuma suka juyo suna kallon Sheykh dake tsaye cikin shiga ta al'farma shigar salihan bayi, wata dandatsetsiyar al'kyabbace mai masifar kyau ruwan ƙasace al'kyabbar sai surfani da aka sarrafa a jikinshi wanda yake da kalan gold, haka takalmanshi da hiraminshi duk masu ratsin Golding color ne, cikin tsananin jin daɗi Haroon ya fara sauƙowa daga step ɗin, yana kallon ɗan uwan nashi manda suke sa'anni, ruggume juna sukayi, cikin jin daɗi Haroon yace.
"Marhabin da zuwa Al'Sheykh, ya gida?, ina ƙannena? Yaya jikin Ya Jafar? Ya Hajja Mama da kowa da kowa."
Kwaɓe fuska ya ɗanyi tare da janye jikinshi daga na Haroon cikin sanyinshi yace.
"Duk in kana son ganinsu kaje Nigeria zaka gansu, kana nan kullum sai yawo a jirgi kamar turuwa a daji, duk ƙasashen duniya ka gama zagayesu".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"To ai dama na sani bakinka ɗaya da Umaymah'nka, zan koma ne in sha Allah, zan koma inyiwa ƙasarmu aiki, suma ai suna buƙata na".
Fuskarshi ya ɗan kauda tare da cewa.
"Da yafi kam". Juyowa sukayi jin Sitti na cewa.
"Kai Haroon ku taho mu tafi, ka tsareshi da surunka tun daga nan ko?".
murmushi Haroon yayi kana ya nufi inda take tare da cewa.
"Oyoyo My Sitti". Kai ta juya tare da cewa.
"Rabu dani ba kaga ɗan uwanka ka shareni ba".
Ruggumeta yayi ta baya tare da cewa.
"Na isa in share uwar gida ran gida a gidan Sarki Jalaluddin". Jannart ce tai dariya tare da cewa.
"Sitti karki yadda da daɗin bakinshi".
Hannunshin yasa ya ɗan dungure kan Jannart tare da cewa.
"Kishi ko dan kinga gani ga uwar gida".
murmushi Jannart tayi tare da jan hannun Sitti sukayi gaba, shi kuwa Haroon baya ya dawo ya saita da Sheykh suka fara tafiya a jere,
duk wanda yaga salo da tsarin tafiyar Sheykh zai gane cewa jini na sarauta na gudana a jikinshi, zai kuma gane nitsuwa ta addinin musulunci da kamala da haiba na hasken imanin ya game jiki da zuciyarshi.
A haka suka jera suna tafe, suna hira wacce ƙarfinta duk Haroon ke yinta.
Suna tafiya kaɗan.
Nan suka samu wasu irin zafafan tsala-tsalan motoci masu masifar kyau da tsada, suna jere a ƙalla sun kai goma sha biyu, motocine masu azabar kyau da sabunta da sheƙi da kyelli suna jere.
Kana ga kekkyawa fararen larabawa yan uwa da abokai
Da sauri suka rinka ɗan rusunawa suna, gaidasu Sitti da jikokinta, wani cikinsu ne da yake jikin wata dan datsetsiyar mota ƙirar Mercedes Benz maybach Exelero wacce kuɗinta zai kai kimanin $8 million dollars.
Motace mai masifar kyau da tsada, tana da inƙancin da ko bilet baya shigarta. Bisa dukkan alamu kuma sabuwa ce dal.
Direban dake jingine da ita ne yayi maza ya budewa Sitti bayan ta, a hankali suka ƙaraso gaban motar gaba ɗaya ma'akatan sunyi musu ƙawanya, cikin so da ƙaunar jikokin nata, ta yiwa Sheykh nuni daya fara shiga, ba musu kuwa ya shiga, motar, kana itama ta shiga sannan Haroon ya shiga, ya zamana sun sata a tsakiya,
Jannart kuma gaba ta shiga gefen drivern, suna gama shiga aka maida ƙofofin motar aka rufe.
Kana duk sauran hadiman suka shishiga motocin.
Kana suka fara tafiya a jere-a jere, tafiya sukeyi cikin salama da nitsuwa da bin doka da ƙa'idar tuƙi, kai tsaye suka wuce tushen ahlin nasu.
Wanda kafin su zoma, duk labarin zuwansu ya riski al'ummar family, kamar yadda aka saba, haka aka shirya musu tarba ta musamman an gyara sashin na musamman wanda nanne masaukin Sitti asali kuma sashin mahaifiyartace, anan cikin sashin kuma duk ahlinta da zaizo daga ƙasar Kautal nanne masauƙinshi, kuma kullum hadimai da bayin dake kula da wannan wurin suna nan suna tsabtace wurin. Suna isa fadar mai darar Sheikh Aliyu da kanshi ya fito tarbar babbar yayarshi wacce take a madadin uwa a gareshi a yanzu.
A wani falo da yafi dacewa da a kirashi al'jannar duniya, suka haɗu, a hankali Sheykh Aliyu ya ɗaga hannunshi alamun dakatar da ko wanne hadimi, a tare suka rusuna tare da komawa baya gaba ɗaya su.
Da sauri ya karaso gaban Sitti Ruggumeta yayi irin ruggumarsu ta jinin larabawa,
murmushi mai cike da jin daɗi ƙauna haɗida bege Sitti tayi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi tace.
"Masha Allah, ɗan uwana na sameku lfy?".
Saketa yayi tare da ruggume Sheykh yana murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah yar uwata, Barka da zuwa lfy".
Cikin kula da zaƙuwa tace.
"Yaya jikin Baba".
Murmushi ya kumayi still yana ruggume da Sheykh yana shafa bayanshi, yace.
"Alhamdulillah jikin baba da sauƙi kewarkice tafi damunshi".
Sai kuma ya kalli Sheykh bayan ya sakeshi yace.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero, barka da zuwa Doctor, ya gida ina Jafar da ƙannenka".
Cikin son dottijon Sheykh ya ɗanyi wani ɗan guntun murmushi wanda shima sai yayi tsawon lokaci bai yishiba, cikin sassanyan murya yace.
"Suna lfy, sun gaidaka".
Haroon ya tura baki tare da cewa.
"Wato mu ko ƴar ruggumar ma ta zumunci baza'ayi manaba, dan mu mun dade, nima zamu koma ƙasarmu mu rinƙa kawo muku ziyara jifa-jifa dan naga baƙi farinjini garesu a ahlinmu".
Dariya sukayi baki ɗayansu,. Yayinda duk mgnar da sukeyi da harshen larabci sukeyi.
Wani faffaɗan corridor mai girma suka ratsa, wanda suka riski wani babbanshi na musamman, inda gaba ɗaya yayan family suke nan zaune dan mahaifin nasu a tsakiyarsu.
Wanda yake tsakiyar gatan duniya, farin dattijone wanda tsabar tsufa har ya juye ya koma tamkar ƙaramin yaro, ya ƙanƙance, yana hango Sitti, ya rinƙa sakin murmushi tare da miƙa mata hannunshi alamun tazo.
Da sauri ta nufi inda yake su Sheykh na biye da ita a baya, yayinda duk sauran mutanen ketayi musu barka da zuwa.
A gaban tsohon ta rusuna, tare da sunkuyowa, hannunshi ya saka bisa kanta yana jero mata addu'o'in da sanya mata al'barka, ita kam sitti da sauran ƙannenenta wanda a ƙalla sun kai arba'in sai Amin Amin suke amsawa,
Koda ya gama da Sitti jawo Sheykh yayi ya manna kanshi da cinyarshi,
Shikuwa Sheykh. Motsoshi yayi da kyau Cikin wani irin mashahurin daɗin da sai in yana gaban tsohon nan yakejin daɗi yasa hannunshi biyu ya kamo hannun dattijon ya ɗaura tsakiyar kanshi kana ya ƙara manna kanshi da cinyar tsohon tasbihi yakeyiwa Allah mai rayawa mai kashewa.
Ya sani shi kanshi da macece shi da yanzu yanada ya budurwa amman gashi wai a gaban kakan mamanshi, ga kuma kakar tashi da sukewa kallon tsohuwa itama gata gaban mahaifinta wannan abu shine abu ɗaya da yake sashi kuka muddin yana gaban tsohonda kullum in yazo irin gaisuwar da sukeyi kenan.
Shi kuwa Sarki Abdulkareem cikin rawan jiki irin na tsoffi yake shafa kan Sheykh tare da kallon taron ahlin naahi cikin muryarsa da bata fita sosai yasa suke sanƙala mishi na'urar ɗaga sauti a jikin alkyabbarsa, shiru sukayi gaba ɗayansu suka dakata da ruggume-ruggumen da sukewa Sitti,
Cikin rawan muryan da alamu tsohon kuka yakeyi a hankali yace.
"Ku bashi dukkan kulawarku, domin yana cikin Magauta, yanada tarin ƙunci da ƙuna a rayuwarshi, matsalolin rayuwar duniya sun mishi ƙawanya, saukinshi ɗaya Allah yayi mushi dafa'i da hasken imani da riƙo da ibada, damuwar tana daƙushe duk wani farin cikin rayuwarsa rashin fara'a ba izza bace damuwace, yana cike da al'hinin kula da ahlinshi,".
Shiru ya ɗanyi tare da zubawa gaba ɗaya ahlin nashi idanu, sawon wasu daƙiƙu shiru falon babu sautin komai sai sassanyan sautin shessheƙan kuka da Sheykh a hankali, sai kuma sautin ƙaran A/C.
A hankali Dottijon yaci gaba da cewa.
"Kanshi akwai wani abu mai girma a tare dashi, yanada manyan baiwowi a jikinshi, sai dai kuma akwai tarin ƙalubale, zai ɗauki nauyi da yawa a kanshi".
Ya ƙarishe mgnar yana shafa tattausan suman Sheykh.
Shiru sukayi baki ɗayansu Sitti kuwa Hannu tasa bisa haɓar Sheykh tana share masa hawaye, Haroon kuwa Umaymah ya kira tun shigarsu tana jin duk kalaman kakan nasu haka yasa taketa kuka.
Sosai yayi jawabai masu ratsa zuciya kafin daga bisani, ma'aikatan gidan suka shigo suka rinƙa gabatar musu da abubuwan ci da sha a nan suka zauna ana ɗan ciye-ciye da taɓa hira,
Ganin lokacin salla yayine kab kowa ya miƙe dan yin al'wala su tafi harami.
Kamar koda yaushe Sashin Sitti suka wuce wanda yake a gyare, Jannart da Sitti side ɗaya suka shiga.
Haroon da Sheykh kuwa Side ɗaya suka shiga.
Ruwa suka ɗan watsa sannan duk sukayi al'wala suka fito suka kimtsa cikin manyan alkyebbars masu taushi da masifar kyau wanda sabbine dal akazo aka shirya musu a drower'n. Koda suka gama a tare duk mazan suku tafi Harami.
Haka dai rayuwa tai ta gudana a cikin kwanakin nan.
Randa suka cika kwana uku da zuwa a ranar ne Sitti ta samu mahaifinta da ƙaninta a kan batun tana son kafin tabar ƙasar nan ayiwa Sheykh aure, ta kuma bada zaɓin yaran yan uwa wanda suke larabawa, nan take kuma Sheykh Aliyu da kanshi yace ya bawa Sheykh Jabeer auren diyarsa Jazrah...
Rugar Bani Ɓadamaya state.
Yau kusan kwanan Shatu biyar da dawowa hutu, kuma kullum da salon da Ba'ana yake zuwar mata dashi, wannan abu shine abinda yafi tada hankalin Malam Liman Bappa kenan, wanda yana yawan tattauna matsalar da Ardo Bani kamar yadda yanzuma haka suke tare su daddatawa biyar,
Cikin kamala da harshen fillanci Arɗo Bani yayi gyaran murya tare da cewa.
"Koda Hashimu ya rasu, in sha Allahu bazamu zuba ido a aurawa Shatu wannan fasiƙi fajiri mushirkin yaron nanba, Salmanu zai fito zai nemi aurenta,in Allah ya yarda kuma zamu cire batun shaɗi tunda, mun sani cewa, bulalin da Ba'ana yake amfanin dasu wurin shaɗi da manema auren Shatu bulalin sihirine wanda duk wanda ya daka dasu ƙarshe mutuwa yakeyi ko ya haukace, to a karon nan zamuce babu shaɗi domin ai shi shaɗi al'adace ba shariya ba.
Zamu kuma bawa salmanu dakarun tsaro masu bibiyar lamuranshi a sirri dan gudun kada ayi mishi yankan rago kamar yadda akayiwa Hashimu duk da dai bamu da sanin shin Ba'ana ne koko kafuran Ɓachamawa ne".
Da sauri ɗaya daga cikin dottawan yace.
"Yo ai shima Ba'ana kusan kafurin ne, tunda baya salla kuma matsafine".
Bappa ne ya nisa tare da jan dogon numfashi mai tsawo sannan yace.
"Bazai yardaba duk yadda za'ayi sai yace dole ayi bulalin Shaɗi, kana kuma muddin akace baza'ayi Shaɗi ba to haƙƙun zai kashe Salmanu kisan da bazamu samu huja ko madafaba".
Shiru sukayi baki ɗayansu cikin kamala da nitsuwa da rauni Bappa yace.
"Kaɗan kenan daga illar riƙo da Al'adar daba addini ne ya tanadar dashi ba".
Ardonne yayi gyaran murya cikin sanyi yace.
"Ya Allah ka kawo mana mafita kan wannan bawa naka Ba'ana daya zame mana masifa a rayuwarmu".
Ɗaya daga cikinsu wanda tunda suka zauna baiyi mgna bane ya gyara zama tare da cewa.
"Gashi shi kamar ibilis yake, ya rigada ya gama dafa kanshi wuƙa ko bindiga basa shigarsa bare banzan abu shi bulalan Shaɗi shiyasa kullum shine da nasara a rayuwarsa".
Shiru sukayi suna kallon ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance malamin da suke sawa yana bincikar musu jikin Ba'ana wato Chubaɗo yana cewa.
"Akwai bulalin da zasu shigeshi su kuma karya duk wasu manyan sirrukan dake jikinshi, ta kuma sashi yayi kuka,cur-cur da hawayenshi, to amman bazasu taɓa samuwaba bamu da hanya ko damar samunsu, domin bulaline da a ƙalla sun shekara ɗari biyu a murde kuma suna cikin tsumin ma'jiya mai cikar tarihi da girma bulaline da tsawon shekara ɗari da ashirin da biyar kenan rabon da ayi amfani dasu, kuma an killacesu, killacewa mai tsauri, shi kanshi Ba'ana yana neman bulalin ruwa a jillo domin babban dodon tsafin Bonon ya sanar mishi saida bulalin zai samu nasarar da yake so, to amman bai san bulalin ina bane baisan a ina sukeba bai kuma san ta ina yake nemansuba an dai bashi yaƙini a hannun Fulani yake wannan dalilin ne yasa ya baza jakadunshi duk ƙasar da takeda Fulani."
Da sauri Suka zuba mushi idanu baki ɗayansu cikin zaƙuwa sukace.
"To Chuɓaɗo kai kasan inda bulalin suke e?".
Kanshi ya jinjina musu tare dayin ƙasa da murya yace.
"Eh na sani".
Cikin sauri sukace.
"Bulalin inane a wacce ƙasar suke?".
Cikin tsoro yace.
"Bazan fadaba bazaiyiwu in faɗaba".
Magiya suka fara yi mishi amman fir yaƙi yace mutanen jikinshi sun hanashi faɗa, dole haka suka haƙura suka tashi daga taron ganin dare ya raba tsakiya kowa ya koma gidanshi.
Washe gari da Asuban fari Rasuwar Chubaɗo ya zagaya garin Rugar Bani wanda akayi hira dashi lfy lau kawai washe gari aka riski ya rasu da alamun kuma ɗaure mishi wuya akayi ya rasu har lahira.
Wannan rasuwa ya jijjiga zuƙatan dottawan nan huɗu da suka rage Arɗo Yabani da Bappa, da kuma Alhaji Ja'eh da kuma Malam Umaru.
Sun shiga jimami mai yawa.
A haka dai akayi mishi sutura aka binneshi akayi zaman makoki na tsawon kwana uku, randa akayi sadan uku duk hankali mutane huɗun nan ya ɗan konta ganin ba'a sake kashe wani ba a cikinsu.
Yau tun da yamma Ba'ana ya matsa aka kira mishi Shatu wacce dolece tasa taje, inda yake har rugar shanunsu bata damuba sanin bai taɓa koda yunƙurin cewa zai taɓa koda ƴar yatsartace,
Cikin sanyin jiki ta sallami aminiyarta Bintu ƴar gidan malam Umaru, sannan ta tafi bakin rugagen.
Zaune ta sameshi cikin ƴar bukkarshi da yayi a cikin tsakiyar turken garken nasu,
A hankali ta ƙaraso wurin ta sunkuya zata zauna ne a saman farin yashin dake wurin yayi maza yace.
"Mata a ƙasa kuma? A a gskiya kada ki zauna a ƙasa.
Ga buzuna zauna a kai".
Kanta kawai ta jinjina shi kuwa shimfiɗa mata buzun yayi, a hankali ta zauna tana fuskantar cikin ƴar bukkar da yake zaune a cikinta ɗin.
Shima gyara zama yayi tare da fuskantarta,
Kwaryar dake gabanshi ta zubawa ido, shi kuwa. Cikin yin murmushi ya sa hannunshi yana gauraye magungunan dake ciki tare da cewa.
"Matar dafaki nakeso inyi, irin dafar da muddin mutun ya tuna zai miki sihiri, misali ya miƙa hannu zai amshi mgnanin da zai samiki to zai kuturce in kuma baki ya buɗe zaiyi mgna kan a miki sihiri to zai kuramce".
Cikin sanyi ta kwaɓe fuska tare da cewa.
"To ni kuma wa zaimin sihiri a duniya wayama damu dani?".
Murmushi mai kama da dariya yayi kana yace.
"In an nemi mijinki ba'a sameshiba dole kanki za'a dawo shiyasa nake shiryaki sabida kar Ni in an jefeni bai sameniba ya sauƙa kanki".
Ya ƙarishe mgnar da miƙo mata ɗan ƙaramin korya yace.
"Ingo ki fara shan wannan".
Kai ta gyaɗa ganin madarar shanuce da aka tatsa da ɗuminta.
Cikin takaicin halinsa tace.
"Me wannan kuma?". dariya yayi tare da cewa.
"Baki da yarda ki yarda dani wata rana zaki tuna nayi miki gata, wlh bazan taɓa cutar da keba mata, kisha madarace da zuma nasan kinaso".
Cikin sanyi tace.
"Sai dai in na koma gida zansha".
Murmushi yayi tare da zuba mata ido kana a hankali yace.
"Fulaku ko? Nasanku fulanin da kunya wato irin bazakici abu a gabana ba, to ai kafin ki koma gida zaiyi sanyi, bari in tafi can bayan bishiya in barki ke ɗaya kisha abunki da ɗuminshi".
Ido kawai ta zuba mishi domin tabbas badon halin banza da Ya Ba'ana yake dashiba ya cancanci ta soshi tabbas tasan ko ba yayi mata alherin da bazata taɓa mancewa ba a rayuwarta.
Ko komai nashi na duniya mara kyau ne to soyayyarta kekkyawace a zuciyarshi ya sota tun tana yar mitsitsiyarta kuma bai taɓa yunƙurin cutar da itaba ya kuma yi mata halacci.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Mata nayi miki kyau ne?".
Kanta ta gyaɗa mishi alamar eh, cikin jin daɗi ya juya ya tafi, can nesa ya ɓuya, ita kuwa a hankali ta fara shan madarar nonon da yaji zuma mai daɗi, kasan cewar nonon ɗan kaɗanne a take ta shanye.
Saida ta goge bakinta tace mishi.
"Na shanye kazo". Da sauri ya fito ya dawo gareta cikin bukkar ya koma ya zauna wani nonon ya ɗibo ya miƙa mata amsa tayi cikin sanyi yace.
"Me kika gani a ciki?".
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Nono fari ƙal mana".
Amsar ƙoryar yayi ya koma cikin bukkar dashi, jin kaɗan ya kuma fitowa ya miƙa mata tare da cewa.
"Me kika gani?". Tura baki tayi tace.
"Farin nono mana". Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Da kyau, yanzu kiyi kamar zakisha ki gani".
Ido ta zuba mishi tare da cewa.
"Sha kuma?".
Kai ya jijina mata kana yace.
"Eh amman ba shan zakiyiba kiyi dai kamar zaki kaishi bakinki da niyar sha zakiga wani abu".
Jim kaɗan tayi jin yana ce mata sha mana, yasa ta ɗan ɗago kwaryar ta nufi bakinda kamar zata sha.
Wani irin wawan zabura tayi jiki na tsuma da karkarwa cikin tsananin firgita da tarin tsoro ta sake kwaryar....!
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 8
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
Kada dai ku mance Free page ne, yana kuma gab da karewa.
*Ga mai buƙatar saya ga number ta, 09097853276 turo ɗari uku ko dubunki ɗaya kacal domin samun damar karantawa cikin salama, Ga Ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin biya sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in ba halin turawa ta ac bisa dole turo katin mtn.*
Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar.
Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba'ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?".
Gaba ɗaya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata.
Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin ɗaga murya yace.
"Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki".
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"Ban yardaba me ka shayar dani?".
Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam.
Kawai sai tasa mishi kuka.
Cikin tashin hankali yace.
"Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba.
Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba".
Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa.
"Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce".
Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai".
Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma.
A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haɗe tare da cewa.
"Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi.
A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama.
Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi?
ko dai wani kikeso ba niba?".
Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
"A a ni kam babu wanda nakeso."
Kanshi ya ɗan rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace.
"Dawo ki zauna".
A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna,
shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa.
"To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun Arɗo Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake".
Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa.
"A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani.
Makaranta kai kuma baka hanaba".
Cikin haɗe fuska yace.
"Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaɗi bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso".
Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace.
"Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba'ana kada ka yarda da ƙaryar mutane".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Uhum kinga nan cikin ranɗar nan, to bulaline wanda nake shaɗi dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaɗi basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe,
Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa'ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba".
Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa.
"Ya Ba'ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba".
A hankali yace.
"Eh ai yau kam zaki haɗu dashi".
Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa.
"Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla."
Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata.
"To Mata jirani inzo in rakaki Mana".
To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi.
Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta ɗan tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo,
cikin jin daɗi ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa.
"Bari inje wurinsu Ya Giɗi, in tayasu ɗaure shanun".
Murmushi yayi kana yace.
"To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba".
To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma.
Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa.
"Yaya sannunku da dawowa".
Da sauri Giɗi da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa.
"Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?".
Da ido ta nuna musu Ba'ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su.
Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi.
Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi.
Har saida Giɗi yace.
"Heyy Ya ba'ana Ubanka na kiranka".
Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa.
Shi kuwa Ba'ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo.
Cikin sakalci da gajiya Giɗi ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace.
"Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon ɗaure shanu ba, ga Shatu zata tayaku".
Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata ɗaure dabobbin suna ɗan dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu.
Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida.
Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa.
"Ya Giɗi tareni, na gaji ga damunku".
Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke.
Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya ɗauke kana ya buɗe kwaryar, ludeyi ɗaya ya sa musu a ciki.
Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa.
"Ya Giɗi kama ka bani". Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba.
Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata,
Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da ɗan uwanta tsokonta Giɗi abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace.
"Ya Seyo zauna ga fili."
To yace kana ya zauna suka fara sha,
Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace.
"To wai mu aka kawowa ko kune?".
Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi,
Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya ɗauki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace.
"To ni naci girma".
Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa.
"A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi". Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi,
Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi,
Cikin kula yace.
"Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin suka amsa baki ɗayansu,
Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace.
"Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla".
To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.
Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al'wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci.
Yayinda ko wanne garke an bar mutun ɗaya sabida tsaro...
Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.
Suna zaune, yaro yayi sallama, yace.
"Wai ana kiran Shatu a woje".
Ummey ce ta ɗan juyo ta kalli yaron tare da cewa.
"Wake kiranta?".
"Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne".
Yaron ya faɗi.
Da sauri Ummey tace.
"A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo".
To yaron yace kana ya juya ya fita.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa.
"Yace wai ince mata, ta fito woje".
"Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa".
Sai kuma Inna ta ɗan kalli Shatu tace.
"Tashi kije ai mun gama aikin ma".
Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma,
kwano ta ɗauko a konɗonsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu.
Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon.
A hankali ta ratsa gefen su Ya Giɗi ta wuce.
Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da Arɗo Yabani ya tabbata.
Suna fita suka sameshi zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasu.
Da sauri Junainah ta isa gareshi tare da cewa.
"Oyoyo yaya Salmanu".
Ajiye kwanon tayi a gefenshi.
Da sauri yasa hannunshin suka tafa da hannunta data miƙa mishi, cikin sakin fuska da nitsuwa yace.
"I miss you ƙanwali".
Dariya mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
"Miss you too my dear".
Dariya mai sauti sukayi a tare cikin jin daɗi wanda aka kira da Salmanu ya lakace hancin Junainah tare da cewa.
"Alhamdulillah alama ta nuna ƙanwaliya tana zuwa makaranta babu wasa".
Cikin jin daɗi tace.
"Sosai ma ya Salmanu yanzu ajiyana huɗu fa, yanzuma dan hutu mukeyi, kuma gashi ko a gidama Ina karatu".
Jinjina mata yayi da hannunshi kana, ya jawo kwanan data ajiye tare da cewa.
"Ƙanwaliya me kika kawo mim ne?".
Cikin murmushi tace.
"Gasheshen naman tattabarune Ya Salmanu barima in koma ciki inci rabona inci na Addana".
Kafin ya ankarama tuni ta juya da sauri tayi cikin gida.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da kallon Aysha dake jingini da bakin kofar zauren,
Cikin sanyi yace.
"Kamar bakiyi farin ciki da zuwana ba? Ko dai in komane?".
A hankali tace.
"A a Ya Salmanu nadai ga kamar kafi farin cikin ganin Junainah ne akai na".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Kin rama kena".
Murmushi sukayi dukansu, cikin sanyi yace.
"Ga wuri kizo ki zauna mana".
A hankali tace,
"A a Ya Salmanu mu shiga cikin gida mana".
"Kina tsoron kada saurayinki yazo ya ganmune?".
Salmanu ya faɗa a hankali.
Da sauri tace.
"Eh".
Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa.
"Babu abinda zai faru sai al'khairi zoki zauna, ki gayamin me kike tsoron?".
A hankali ta zauna gefenshi ɗan nesa dashi.
Shi kuwa juyowa yayi ya fuskanceta a hankali yace.
"Gaya min me kike tsoro?".
Kallonshi tayi cikin yin ƙasa da murya tace.
"Ina tsoron kada Ya Ba'ana ya cutar da kai, ina gudun kada sakaiyar alaƙarmu ya zama cutarwa, sabida Ni kamin rana a rayuwata, rana kuma ta al'khairi shiyasa bana son abinda zai cutar da kai".
Murmushi mai yelwa yayi kana a hankali yace.
"Ina sonki zan kuma aureki da izinin Ubangiji zan rabaki da wannan taƙadirin, domin baki cancanci zama matar mushurkiba".
Da sauri tace.
"Kada kace haka Ya Salmanu Wallahi zai cutar da kai, kada ka bari wani yaji, bare mgnar ta koma kunnenshi".
Murmushi yayi tare da jawo kwanon ya buɗe. Numfashin yaja jin ƙamshin naman a hankali ya fara ci, saida yaci ɗaya kab sannan ya rufe kwanon yace.
"Ga rabonki dan nasan Junainah ta cinye naki rabon".
Cikin yanayin nitsuwarta tace.
"A a kaci kawai Ya Salmanu".
Da sauri yace.
"No kada kimin musu".
Shiru tayi jin yaci gaba da cewa.
"Muddin dai ina raye in sha Allah.
wallahi Allah bazan bari Ba'ana ya aureki ya lalata miki rayuwaba, zan jure duk azabar da zai shayar dani na shaɗi in Sha Allah zan aureki".
Ido ta zuba mushi tana kallon shi cikin kamalarsa, ganin sam hankalinta ba'a kwance yakeba, yasashi ce mata ta shiga gida zasuyi mgna a waya, haka kuwa akayi, ta juya ta shiga gida shi kuma ya nufi hanyar gidansu.
A dandalin wurin da yake kamar kasuwar garin nasu ya samu abokanshi, kowa da budurwarshi suna ɗan hirarsu
Can gefe kuma ga yara nata wasansu, ga farin wata ya fito yayi ras, kana iya ganin komai.
Ita kuwa Shatu, bayan sun gama shirin baccinsu, ta kalli Ummey tare da cewa.
"Ummey".
"Na'am". Ta amsa mata cikin kula, sai kuma tayi shiru, ita kuwa Ummey ido ta zuba mata,
ganin hakane yasa a hankali tace.
"Ummey Ya Salmanu". Still kuma tayi shiru,
Cikin kulawa da shaƙuwa wanda ke tsakanin uwa da yarta Ummey tace.
"Gaya min mana, me Ya Salmanun yayi?".
Konciya tayi gefen Ummi dake bisa sallaya, kana a hankali tace.
"Wai yana sona, Ummey ina tsoro Ya Ba'ana zai illata mishi rayuwa, gashi kwanan nan Ya Hashimu ya rasu, kuma shima ance kasheshi akayi, Ummey ki cewa Bappa na, yacewa Baba Arɗo ya hana Ya Salmanu cewa yana sona, kinji ko Ummey?".
Kai Ummey ta jinjina mata tare da cewa.
"To zaki aureshi kenan duk da kinsan baya salla kuma yana tsafi".
Kai ta juya tare da cewa.
"Bazan aureshiba Ummey, amman ya Salmanu yayi shiru, bari in gama karatuna, in sha Allah akwai mafita in na gama karatuna, Ummey kin gane ai ko? Kin tuna ko".
Murmushi Ummey tayi kana tace.
"Eh na gane, yanzu konta kiyi baccinki".
da haka suka konta bacci.
Bayan kwanaki, sosai lamarin Ba'ana yake bawa mutane tsoro, mutun kamar ifiritu, dan yanzu yanayin sihirinshi ƙaruwa yakeyi sosai,
Wasu lokutan ba hawa ba sauƙa sai dai kawai ka ganshi a gabanka sabida yanzu layan ɓatarshi tama fi ta baya ƙarfi, ya dage wai zai bawa Shatu taƙi fir daya matsama kuka tasa mishi hakanne yasa ya hakura ya barta.
Ya Salmanu kuwa yanzu ya dage kan batun soyayyarsa da Aysha, ita kuwa tsoron abinda zai faru ya hana yarda da kowa, gaba ɗaya kuma yanzu Ƙabilar ɓachamawan nan masifa tuƙuru suke neman fulanin Bani dashi sabida baƙin ciki da hasadar ganin yadda shuke-shuken wurin fulanin yayi kyau, shinkafa, masara, dawa, gero, maiwa, wake, gyaɗa, gujjiya, riɗi, da dai sauransu.
Ga tarin bishiyoyi dorowa da suke zagaye da garin wanda kan ko wacce bishi akwai jingogin zuma, shiyasa garin suke da tarin zuma.
To waɗannan abubuwan sune suke ƙara tunzura kafuran, sabida gani suke aifa da filin nasune, sun mance kafin a saida wa fulani filin kufayine, fulaninne suke tafe da al'barkasu a jikinsu.
Zuwa yanzu kowa na Rugar Banin da kewaye yasan masoyan Shatu biyune, kuma za'ayi shaɗi, wanda tsawon shekaru biyu kenan ba'ayin ba.
Kowa in yaji da Salmanu za'ayi ana tausaya mishi domin shi mutunne mai laushin jiki shiyasa tun yana ƙaraminshi aka meda hankali kan karatun da yakeso, hakane yasa yayi karatun shi yanzu haka yana zama cikin Shikan ne inda yakeda shagunan kayan tireda sabida bazai iya noma da kiwo ba, kuma Alhamdulillah kasuwar ta amsheshi. Shiyasa shi zuwa yakeyi Rugar Bani ɗin.
A can ƙasa mai tsarki kuwa,
Yau kwanansu Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da Sittinshi goma da zuwa, to kasan cewar zasu gudanar da aikin Umarne yasa tun randa suka cika kwana uku da zuwa suka tafi, Madina,
Kuma sun bar mgnar batun Jazrah cewa sai sun gama gudanar da aikin Umararsu kafin su shaida mishi, kana in sun dai-dai ta da Jazrah sai su shaidawa Mai alfarma Sarki Jalaluddin, shi kuma yaje har Ɓadamaya ya shaidawa mai daraja sarki Nuruddeen Bubayero, da kuma Habeebullah, batun auren in yaso su shirya suzo ayi ɗaurin auren.
To yau kwanansu takwas a Madinah kuma yaune suke shirin dawowa makka.
Kullum sai sun gaisa dasu Hajia Mama dasu Jalal.
Kullum yakan kira Juwairiyya.
Da maraicin suka isa cikin Makka kai tsaye masarautar suka wuce.
Bayan sun gaggaisa, Sheikh Aliyu yace suje su huta, kafin su gaisa da Sheykh Abdulkareem domin yana tare da manyan baƙi.
Haka kuwa akayi, bayan duk sunyi wonka suka dawo falon Sitti.
Suna zaune cikin shiga ta al'farma a wuri na al'farma, an zagayesu da dukkan kayan jin daɗin rayuwar duniya,
Sitti na zaune bisa tsakiyar falon akan wani tattausan carpet, Jannart da Jazrah suna gefenta, cikin shiga ta al'farma,
Sheykh kuwa zaune yake bisa wata lumtsimemiyar kujera kana sawunshi na kan wasu tim-tim masu masifar kyau da taushi, wasu kyawawan larabawane guda biyu suke zaune a gaban Sitti sawunta dake bisa tim-tim ɗin sukeyiwa tausa.
Yayinda wasu hadiman kuma ke shirya musu ababen ci dasha dangin yayan itatuwa kamarsu, Inabi, tupa, ayaba, dabino, gabaruwa, sai zam-zam kana, saisu shawarma and pizza da kuma wasu irin manyan Foodflaks da aka cikasu da danƙawa-ɗanƙwal dajaja sai sauran abincinsu na larabawa.
Haroon kuwa gefe yake kusa da Jannart suna ɗan taɓa hira.
Wayarshi ce ta fara ringgin a hankali, idonshi ya ɗan juya ya kalli wayar ba tare daya juya kanshiba,
Da idonshi ya nunawa hadimin dake gefenshi wayar,
da sauri ya ɗauko wayar ya miƙa mishi, ganin Hajia Mamace ya sashi amsa kiran.
Kara wayar yayi a kunne cikin girmamawa yace.
"Barka da dare Hajia Mama".
A can gida kuwa cikin wani irin salo na musamman Hajia Mama ta rufe idanunta tare da cewa.
"Uhum ka manta Jabeer mu nan yammane".
Idonshi ya ɗan ɗago ya kalli agogon dake jikin ginin, a hankali yace.
"Haka nefa Hajia Mama. Ya gida yasu Jalal".
Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
"Suna lfy gasuma nan kusa dani, Jamil ne ya tsokano Jalal shine suka shigo sunata muzurai".
Kanshi ya jingina da jikin kujerar, a hankali yace.
"Hajia Mama kiyi musu faɗa kice su barifa sun girma".
Murmushi mai sanyi tayi tare da cewa.
"Na gaya musu sunma daina gasu nan sunata hira kuma".
Gyara zamanta tayi kana taci gaba da cewa.
"Ina Sitti na?". A taƙaice yace.
"Gata nan kusa dani".
Cikin yanayin jin daɗi tace.
"Bata waya". To yace kana ya miƙa Sitti daketa kallonshi wayar, da sauri ta amsa tare da karawa a kunne, murmushi tayi jin muryar Hajia Mama na cewa.
"(Allah beddu sabbugo Sitti), Allah ya ƙara nisan kwana Sitti". Amin Amin tace, kana suka gaisa cikin tsananin jin daɗi.
Bayan sun gama wayarne kuma Juwairiyya ta kira Jannart nan suka gaisa ta bawa Sitti wayar hirar tasu kab kan ya Jafar ne. Saida suka gama wayarne ta kalli Sheykh dake kishinƙiɗe ya lumshe ido a hankali tace.
"Juwairiyya tace , yau tun safe Jafar ya shiga sashinka yayi ta nemanka ɗaki ɗaki, da bai gankaba yaƙi fitowa sai kuka yake tayi, har saida yammane da Jalal ya dawo gida shine ya lallasheshi ya maidashi sashinsu.
Hannu tasa ta share hawayenta da ke kwaranyowa, Haroon ma hawayen ne ke zubo mishi,
Haka Jazrah da Jannart,
Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace.
"Lamiɗo ya gaya min ɗazu da mukayi waya".
Shiru sukayi baki ɗayansu, a hankali Haroon ya miƙe kwance tare da faɗawa nazari mai zurfi.
Nan kuma kiran Umaymah ya shigo wayar Sitti still hira sukayi sosai wanda ta kontar musu hankali kafin, sukayi sallama da juna.
Yau jumma'a ne gajeren lokacine basa kai yamma a wurin kiwo, kafin azahar suke dawowa, shiyasa yau Shatu tace da ita za'aje kiwo.
Dariya kawai sukayi mata dan sun san ba iya jurewa zatayiba amman tunda ta kafa ta tsare cewa dole zataje, sai aka barta.
Kasan cewar basu kai yamman bane yasa kuma suna tafiya da wuri.
Bayan duk an kunce dabobbin gaba ɗaya, hakama sauran makiyayan baki ɗaya, sahu- sahu shanayen keta wucewa.
Sun tafi tun shida da rabi na safe,
Kafin zuwa tara na safe sunyi nisa cikin wurin kiwonsu, inda nan kuma Aysha ta samu su Hindema sunzo kiwo, wanda su kullum dama suna zuwa.
Wani irin hadarine mai ƙarfi ya taso daga ƙasa, ganin hakane yasa, Gaini kwallawa Shatu kira wacce take can cikin ƴan uwanta mata makiyaya, jin shiru bata amsa bane ya nufi wurin da suke zaune,
Cikin kula yace.
"Aysha tashi keda Hinde dasu Mero duk ku tafi gida, kunga hadarine mai ƙarfi ke tasowa daga ƙasa da alamun za'ayi ruwa mai ƙarfi".
Cikin ƙarfin hali da son wasa cikin ruwan da taketa hari murya a sanyaye tace.
"Ba komai ya Gaini zamu jiraku ai lokacin tashi kuma ya kusa ko?".
Su Giɗi dasu Aro da sauran makiyayan ne sukace.
"Ya Gaini barsu mana ba kiwo zasuyi ba ai makiyayin shanu da tumaki baya gudun ruwa duk yawa shi".
Cikin jin daɗi sukace, eh mana,
Shi kuwa Ya Gaini murmushi kawai yayi tare da cewa.
"Shike nan yau zakusha dukan ruwa".
Murmushi sukayi sukace "Babu matsala". daga nan mazan duk suka koma wurin kula da dabobbin nasu da suka duƙufa cin koren ciyawa.
Su kuwa Shatu da Hinde a hankali sukaci gaba da tafiya, sosai tsarin wurin da yanayin shigar suturar dake jikinta yayi tsananin dacewa da ita.
Doguwar rigace irin tamu ta fulani, yadin farine, sai daga samanshi akayi mishi kolliya da zaron huɗu, mai color red white, blue, yellow, and green, wanda aka ƙawata saman rigar da kolliyar zanen ɗawisu, inda daga kafaɗunta har zuwa saman ƙirjinta, duk an shimfiɗa zaren, bisa wuyan rigar mai V.
sai kuma hannun rigar shima duk an zagayeshi da kolliyar,
Kana sai tsakiyar rigar dai-dai kan ƙugunta shima an ƙawatashi da wannan kolliyar ulu irin namu na fulanin daji,
Kana sai ƙasar rigar can itama an ƙawata da wannan zaren.
Sai dogon gashin kanta da yake zube a kafaɗunta, yayinda daga saman goshinta kuma tasa, bandana amman irin namu na fulani mai kalolin ƴaƴan tsakiya, ta zagaye kanta dashi, sai kolliyar da tayi a fuskarta irin ta asalin fulani, a goshinta zanen kan shanu tayi, shaidar cikekkiyar bafulatanace, sai kuma ƙasan lip ɗinta na ƙasa zuwa kan ɗan gemunta shi kuma taja zane da kuma yin ɗigo-ɗigo a gefenshi.
Sai wata kekkewar jakar sakan ulun mai kalolin kolliyar jikin rigarta data rataya a hannun damanta, wanda cikin jakar kuma ruwan shantane a ciki sai sassanyan kinɗirmo da goran zuma, sai ɗan sandar mu ta gado, takalman sawunta irin sau cikin nanne daku mutanen cikin birane kuke masa laƙabi da tashi kabi shanu.
Tayi masifar kyau a cikin wannan shigar tamu ta gado, kyau iya kyau farar fatarta ta baiyana tamkar balarabiya gashin girarta ya konta lib lib.
A hankali suke ɗan tattaki a cikin dogayen saunukan, da koriyar ciyawa da tayiwa ƙasanshi ƙawanya. suna ɗan tafe
Suna ɗan tsinkar ya'yan kanya da gwandar daji da suke cike da wurin Chaɓɓulle wato tsada.
Hadari kuwa sai gamgami yakeyi gabas da yamma kudu da arewa, ko ina yayi dib babu motsin komai sai nasu dana dabobbin su,
Iska ta tsaya cak koda ganye ɗaya baya kaɗawa duhu ya kareɗe illahirin yankin.
A hankali Hinde ta kalli sararin samaniya cikin tsoron ganin gaba ɗaya duniyar tayi baƙiƙƙirin ko ina yayi dib, hakanne yasata ɗan zaro ido tare da cewa.
"Kai Shatu, kalli sama, fa hadarin nan yayi duhu da yawa gsky mu tafi gida".
Da sauri ta ɗago kanta kana tasa hannunta na hagu ta ɗan kare saman goshinta kaɗan, ware idanunta tayi ta kalli sararin samaniya, wani irin azabebben firgita da tsorone ya rufeta wanda yasa ta juya da azaban ƙarfi ta ruggume Hinde dai-dai lokacin, sukaga wani irin tartsatsin azabebben igiyar...!
Dan Allah da Manzonsa in dai kin san zaki sayi littafinane ɗan ki fiddashi na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar su. Kada ki saya bana so, ki riƙe kudinki.
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 9
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘
*FREE PAGE*
*TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta wannan number 09097853276 DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA littafin GARKUWA, ba tare da haƙƙin kowa a kankiba. Akwai Special Group shi kuma na 1k rak, ki turoshi ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai ta WhatsApp 09097853276*
~Ga masu buƙatar kayan gyara na amare, akwai set-set masu kyau, a ƙananan robobi masu sauƙin kuɗi, akwai kuma na manyan robobi masu zafi, akwiasu dai-dai da tsarin al'jihun mai ƙarfi da mai rauni, ina araha ina hana bashi. Koda kuɗinka saida rabonka, kayan Kamfani daban dana shago.~
*Al'ummar Hausawa mazauna Saudiya wannan shafin nakune kyauta gareku, domin jiya da yau saida mai zaton babu wasu masu karanta littafi sama daku. Nasha mamaki da sanyin safiya naita cin karo da numbers ɗin ƙasa mai tsarki suna ta antayo min manyan kuɗi na ƙasa mai tsarki tun ina ƙidaya numbers ɗin +966 har dai abun yaci tura sabida yawansu, ashe daga zauren Umar Maisanyi sukayi ta antayowa gareni. Godiya mai tarin Yawa Umar maisanyi mai Tsakar gida You tube limamin tsakar gida*
Walƙiya mai tsananin haske da tartsatsi wanda saida ya haska gaba ɗaya, dajin ya zamana, har kana iya ganin inuwar dogayen bishiyoyin wurin da sukayi musu ƙawanys.
Wani irin tsoro da firgici da karkarwan ne ya bijirowa Aysha.
Cikin dauriya da sabo da ganin ire-iren irin waɗannan ababen a wurin kiwo, Hinde ta kamo hannun Shatu tare da cewa.
"Kai Aysha babu komai fa walƙiyace kawai fa kai".
Sai kuma tayi dariya tare da cewa,
"Uhum a hakan kike tunanin jurar taraddadin da muke gani cikin tsaunuka in muna kiwo".
Janye jikinta tayi daga jikin Hinde, hannun tasa ta tattare gashin kanta dake baje a kafaɗunta, tubkeshi tayi cikin, fidda numafashin tsoro take karisa addu'o'in datake tayi a bakinta, a hankali taja da baya ta jingina da jikin ƙatuwar bishiyar Gamji dake gefensu, jingina kanta tayi jikin bishiyar gamjin tana jin yadda zuciyarta ke harbawa, pat-pat da azaban ƙarfi domin tasan Hinde bata san me idonta ke shirin hango mataba,
ita kuwa Hinde, a gabanta take tsaye ya zamana sun fuskantar juna.
Su Ya Gaini kuwa sun duƙufa kiwonsu kamar dai yadda suka saba, ruwa ko iska ko zafin rana da ƙishi baya kora makiyaye daga kiwo a daji ya dawo gida.
So duk kowa yana yankin da yake bawa dabobbin tsaro, sam basuma hango su Aysha sosai.
Ita kuwa Shatu idonta dake lumshe ta fara ƙoƙarin buɗewa sabida wani irin tashi da taji tsikar jikinta nayi.
Hinde kuwa ido ta zuba mata tana ganin yadda ƙirjinta yake sama da ƙasa alamun tsananin firgita.
A hankali ta ware manyan kyawawan idanunta.
Wani ƙaton curi, dake can bayan Hinde ta zubawa ido sabida wani abu da take gani kamar hayaƙi yana fitowa ta ƙananan ƙofofin curin. Ita kuwa Hinde bata san meke wakana ba sabida, ita baya ta bawa curin, asalima yanzu kanta ta ɗaga sama tana shan ruwan dake cikin goranta.
Ita kuwa Shatu so take ta janye idanunta daga kan wannan CURIN amman sai taji ta kasa, bugun da zuciyarta keyine ya tsananta, lokaci ɗaya jikinta ya fara tsuma da karkarwa zufa mai azabar zafi ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.
Yayin da zuciyarta. Ke harba jini one litter. A Cikin ko wanne one second. Bakinta ta buɗe da nufun furta addu'o'in dake jere a zuciyarta amman sai taji ta kasa, zuru-zuru tayi da idanunta lokacin da taga wani dogon abu yana fitowa daga cikin babban ramin dake tsakiyar CURIN nan, a hankali ta ɗaga kwayar idanunta sama tana bin abin da kallo, wani irin dogon numfashi taja, ganin abun nan yana miƙewa yana yin sama, abun dogo kamar igiya sai dai kuma yanada zane kala-kala red, yellow, green, blue.
Kuma abun biyune ɗaya a sama ɗaya a ƙasa, cikin ranta take iya ammabaton sunan Allah ganin zahiri fitowar bakan Gizo daga cikin curi Allah ya nuna mata, ras zanen bakan Gizon nan yayi kama da kalolin kolliyar jikin rigarta,
Kanta ta ɗaga sama, tana bin Bakan Gizon da kwayar idanunta, tana gani har ya haura sama can ya konta a gicciye gabas da yamma kudu da arewa, kana kuma mai hasken ras yana sama mai ɗan dishi-dishin yana ƙasa. Wanda a falsafar al'ummar Duniya ake cewa suma mata da mijine, muddin kaga mai hasken in ka zuba ido zakaga mai dishi-dishin wanda akecewa, mijin shine dishi-dishin kuma shike goyo matarsa shiyasa sai ake ganin mai hasken shine a sama.
Wasu irin numfarfashi take ja da azaban ƙarfi da razana, kar-kar haka jikinta ke rawa.
Cikin tsoron halin da take ciki Hinde ta wurgar da goran dake hannunta, tare da cewa.
"Hande en boni, yau munga ta kanmu Shatu me haka meya sameki?". Ina babu mgna sai zamewa da ta farayi tanayin ƙasa alamun zata faɗi, ganin hakane yasa, Hinde juyowa da ƙarfi ta fara rabƙawa su Ya Gaini kira.
"Ya Gaini! Ya Seyo! Ya Lado, Wayyo Ya Giɗi kuzo kuga abinda Shatu keyi".
Maganarta ta karshece ta sasu, tasowa a guje gaba ɗayansu suka nufosu da gudu,
kafin su isoma Aysha ta faɗi ƙasa zaune, sai karkarwa da rawan sanyi takeyi.
Suna isa Ya Gaini yasa hannu ya tallabota ganin yadda taketa karkarwa, idanunta na rufewa,
Seyo ne ya kalli Hinde cikin kiɗima yace.
"Subahanallahi Hinde me ya sameta?".
Cikin kuka Hinde tace.
"Ban saniba wallahi haka kawai naga tana karkarwa".
Giɗi ne ya zauna kusa da yayan nashi kanshi ya sunkuyo kanta yana kiran sunanta a jere a jere.
"Aysha! Shatu. Ayshatu tashi buɗe idonki ki gaya min meya sameki meke miki ciwo".
Ina babu magana saima kara rumtse idanunta da tayi tare ƙara ƙaƙƙame jikin Ya Gainin nata.
Ya Lado ne da Seyo suka sunkuyo kanta addu'o'in suka rinka tofa mata, duk addu'ar da tazo bakinsu tofa mata sukeyi, Giɗi kuwa ruwa yasa a tafin hannunshi yana shafa mata a fuskarta.
Cikin al'hini sauran makiyayan duk suka iso kansu, ganin yadda suke birkice ne ɗaya daga cikin ƴaƴan Alhaji Haro da kuma Alhaji Umaru sukace.
"Gaini mu tafi gida da ita, tunda dama lokacin tashinmu yayi, an kusa fara tafiya masallacin juma'a."
Cikin damuwa Giɗi yace,
"To ai bazata iya tafiya ba".
Seyo ne ya miƙe cikin sauri yace.
"Bari inje in kawo doki sai mu ɗaurata a kai".
Da sauri Manu ɗan Alhaji Haro yace.
"Yauwa yi maza, kunga ku kuma Gidi kuje duk ku haɗo mana kan dabbobi ku fuskantar dasu hanyan gida".
Ai kuwa haka akayi sauran yaran duk suka kaɗa shanun.
Koda Seyo ya kawo dokin, shida kanshi ya hau baya sannan aka ɗaura mishi ita a gabanshi, a haka suka nufi gida.
Koda suka isa gida, da kanta ta taka har zuwa cikin gida, suna biye da ita a baya.
Kai tsaye ɗakin Ummey ta shige, bisa gado ta konta ta duƙunƙune tana rawan sanyi.
Da sauri Ummey da Inna da Junainah suka biyota a baya.
Cikin tsoro Inna tace.
"Subahanallahi Shatu meya faru".
Ummey kuwa gefenta ta zauna, tare da jawo borgo tana rufe mata jikinta.
Giɗi ne da yanzu ya shigo, shine ya basu lbrin iya abinda suka sani.
Seyo kuma cewa yayi a mata hayaƙi.
Haka kuwa akayi sukayi mata hayaƙin kana Ya Gaini ya zauna yayi mata rubutu nanma aka wonke aka bata.
Jin jikinta yayi zafi jau ne, alamun zazzaɓi ne ya rufeta yasa, Ya Lado yaje ya ɗauko mata mgnin a ɗakin Bappa, nan Ummey ta bata tasha, a take bacci ya ɗauketa.
Ummey kuwa da Inna woje suka fito sunata dariya dan su a zatonsu ko gajiyane yasata hakan tunda ita dai bata saba zuwa kiwoba tunda tanada yayu maza da yawa.
Koda akayi sallam Juma'a aka idar, su Bappa da yaranshi kab basu dawoba saida akayi sallan la'asar kafin suka dawo gida.
Ummey kuwa da Inna aikin abincin dare sukeyi wanda girkin ranar jumma'a na dabanne, zabbi biyar suke yankawa kullum jumma'a wata rana kuma tattabaru wani lokacin kuma jan nama Bappa ke saya to yauma hakanne.
Inna ce zaune tanayi musu wonke-wonke yayinda Junainah kuwa keyin shara, dama wonke-wonke aikintane to duk randa takeji tsiya sai tayi ta ƙorafi, shiyasa yau tana farawa Inna ta fara aikin.
Ummey kuwa tana cikin kitchin ɗinsu, wanda dama da Shatu lfyarta lau muddin tana gida ita keyi musu, girki domin Ummey ta horeta da iya girke-girken na ban mamaki.
A hankali Shatu ta bude idanunta daga baccin da takeyi,
Cin karfin jikinta ya ɗan dawo, a hankali ta tashi zaune, da sauri ta fito woje, sabida ganin ita ɗaya ne a ɗakin.
Da sauri ta fito, Inna ce ta ganta cikin kula tace.
"Shatu kin taso?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Cikin kula tace.
"To ya jikin naki?".
A hankali tace.
"Da sauƙi, Inna zanyi wonka".
Mikewa tayi dan dama ta gama wonke-wonken. Botiki ta ɗauka kitchin ta shiga, ruwan zafi ta ɗebo nan take cewa Ummey.
"Shatu ta farka".
Murmushi Ummey tai tare da cewa.
"Na jita ai wai zatayi wonka, ke kuma harda biye mata kamar ta shekara ba lfy, Shatu ba dai rakiba".
Dariya suka ɗanyi, ita kuwa a tsakiya gidan ta zauna kan dakalin da ke gindin bishiyar ceɗiya dake wurin.
Bayan inna ta kai mata ruwan ne ta kalli Junainah cikin sanyi tace "Junnu zoki rakani inyi wonka Mana."
Ido Inna ta zaro tare da cewa.
"Hahhh Shatu yau kuma ta rakaki wonkafa kikace".
Kanta ta gyaɗa cikin raunin fuska tace.
"Eh Inna tsoro nakeji shiyasa".
Ummey dake kitchin ne ta fito rike da aikoshn data zuba zabbin data soya a ciki, tace.
"Shatu ki rage tsorofa".
Kai ta gyaɗa kana taja hannun Junainah tare da ɗaukan kondon kayan wonkanta,
A bakin ƙofar mashiga bayan gidan tace.
"Yauwa Ƙanwaliya jirani a nan".
To Junainah tace,
haka ta tsaya tana jiranta,
Ita kuwa wonkanta tayi, a nitse kana, tana fitowa.
Tayi al'wala, ɗakin Ummey ta shiga, sallan azahar da la'asar ɗin tayi, sannan ta zira wata tattausar doguwar riga.
Turare ta ɗan fesa kana, ta fito,
Gefen katangar kitchin ɗinsu ta samu Ummey tana haɗa wuta a murhun dake wurin.
Inna kuwa zaune take a gefe, da turmi a gabanta, kana tana jajjaga tattasai da tumatur da kuma tarugu da al'basa.
Taburman data fito dashine ta shimfiɗa gefensu.
Inna ce ta kalli Junainah da itama yanzu ta fito wonka tace.
"Yauwa Junainah zoki kawowa Addanki abinci."
To tace kana tazo ta shiga ɗakin Inna.
Ta fito da tire a hannunta da wasu ƴan kananun robobi guda huɗu a kai masu marfi, sai kuma kula a tsakiyarsu.
A gaban Shatu ta ajiye kular.
Kana ta wuce ta nufi ɗakin Ummey.
Ita kuwa Aysha kular ta buɗe, dambun zogalenen a cikin wanda yaji, ganyen zogalen da kuma al'basa, sai tururi yakeyi.
Ƙananan robobin kuwa, ɗaya dakekken yajin ƙaragone wanda yaji magi da borkino da kuma tafarnuwa.
Kana ɗaya robar kuma, soyayyan man shanune a ciki.
Ɗaya kuma yankekken al'basane da kuma tumatur, sai dafeffe kwai duk a yayyanka,
Kana ɗayan kuma dambun namane mai laushi, a ciki,
ɗan karamin aikoshin dake gaban Ummey taja, ta zuba dambun, kana ta zuba sauran kayan hadin.
A hankali ta fara ci.
Junainah da ta fito yanzune ta kalla tare da cewa.
"Junainah bani ruwa".
To tace kana ta juya ta nufi gindin randunarsu inda suke jere a ƙalla sun kai shida ko dan ba manya bane dukansu na taɓone masu ɗan karen sanyi, ga kuma inuwar bishiyoyin ayaba da sukayiwa randunar ƙawanya,
Shiyasa ko yaushe ruwan zakajishi kamar na firiji,
A kofin silver ta ɗebo mata kana tazo ta zauna gefenta, sunaci a tare.
Ummey kuwa tukunyar ƙasa ta ɗaura a wuta tare da tsulala man shanu, a ciki.
Kayan miyan da inna ta kirɓa ta amsa ta zuba a cikin manda yayi zafin ta fara soya miyar, zabbin da zatayi musu.
Kana ɗaya murhun kuma ruwan tuwo ta aza a tukunyan ƙarfe.
Inna kuwa data gama kirɓa kayan miyar, shinkafar tuwon ta ɗebo tazo tana wonkewa.
Suna cikin haka su Bappa da yayunta maza suka dawo.
Nan suka shimfiɗa katuwar taburma a tsakar gidan.
kana Giɗi ya ajiyewa inna ledodin tsarabar jumma'a da Bappa kanyi duk ranar sati.
Tirirruka Ummey ta miko mata ta baza, juye kayayyakin a cikin.
Reke,Lemu, kwakwa, da Giginya, da kuma dafaffiyar gyaɗa, da ƙosai mai zafi da biredi da soyayyen doya da fulawa mai jawa.
kayan cimarmu kenan fulani
Zubawa maza nasu akayi, aka basu a tsakiyarsu suka ajiye sunaci da mahaifin nasu.
Shatu kuwa da Junainah aka basu nasu. Ummi da Inna kuwa sun ajiye nasu dan aiki sukeyi.
Ya Gaini ne ya ɗan danki ƙosai da bredy yasa a bakinshi,
tauwana yayi kana idanunshi na kan Aysha saida ya haɗiye kana yace.
"Shatu, ya jikin naki?".
Murmushi ta ɗanyi sai kuma ta ɗan harari Junainah dake cewa.
"Uhum ta worke ai dama kawai hegen tsorone da raki".
Dariya sukayi baki ɗayansu. Seyo ne wanda yakeda tarin jinƙai da nitsuwa,
ya ɗan afa geɗan daya ɓare a bakinshi tare da cewa.
"To Amman Shatu meya samekine lokaci ɗaya kika firgita?".
Giɗi ne da shi kuma doya yakeci yace.
"Kamar mai cutar al'janufa ta zama".
Bappa ne ya ɗan kalleta cikin kulawa yace.
"Shatu meya sameki ne?".
Murmushi ta ɗanyi tare da kallon Ummey dake cewa.
"Uhum tsorone da gajiya fa".
Kai ta jujjuya a hankali tace.
"Allah ko Ummey ba tsoro bane".
Sai ta kuma meda hankalinta kan Bappa cikin sanyinta tace.
"Bappa naga abinda ya firgitanine.
Shin Bappa dama bakan Gizon cikin curi yake fitowa ne?."
Cikin mamaki suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Bappa ne da kanshi yace.
"Ban fahimceki ba Shatu".
Bredy dake gefenta ta gutsura kana ta dandola da zuman data sa Junainah ta kawo musu, a baki ta ɗansa ta tauna kana a nitse ta basu labarin abinda ta gani da kuma yadda taji, ta ƙara da cewa.
"Bappa dama bakan Gizo a curi suke fitowa ne?".
Cikin mamaki da al'hini yace.
"Allahu al'alamu. Sai dai koma menene, lallai tabbas akwai abinda ke tunkarar rayuwarmu, fatana mu dage da addu'a koma menene Allah ya kawo mana shi kan al'khairi ya kuma sauƙaƙa manashi, zan kuma bincika in sha Allah.
Sannan kada ku gayawa kowa mgnar nan".
Ya karishe mgnar da kallon Junainah.
Wannan labari ya sasu cikin dogon nazari. haka dai sukaci gaba hira kamar yadda suka saba.
A can cikin yola kuwa, yau tunda Ya Jafar yaje sallan juma'a ya dawo baiga Ƙaninshi Sheykh ba, gaba ɗaya ya tashi hankalin ƙanenneshi da iyayenshi.
Domin kama hannun Jalal yayi yana kuka, yana jan Jalal zuwa sashin Sheykh koda suka shiga, Jamil kuwa sashin mahaifinsu ya nufa. Ba tare da ya saurari
Hadiman ba ya wuce.
A babban falon ya samu , Abba
Haurawa sama yayi yana shiga kuwa ya sameshi a falo shida jarabebboyar amaryar tasa cingom dinshi.
Sai dai tana konce bisa kujera,
Shi kuma yana zaune bisa sallayane ya fuskanci al'ƙibla, da ƙur'ani a gabanshi yana karatu cikin suratul Khafi.
cikin rauni Jamil ya ƙaraso gabansa.
Bai kulashiba har saida ya kai ƙarshen surar kana ya shafa addu'a.
Cikin haɗe fuska da alamun faɗa yace.
"Jamil lfy kuwa mehakan?".
ido na zubda hawaye yace.
"Abba Ya Jafa".
Rai a hade yace.
"To me zan mishi?".
Cikin zubda hawaye yace.
"Abba tunda aka dawo aka sauƙo sallan jumma'a fa yaketa kuka yana bin Jalal yana kuka alamun a kaishi wurin Hamma Jabeer, yau ko abinci baiciba, Aunty Juwairiyya ma sai kuka takeyi hakama su, Jiddah."
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"To ni zaka gayawa? Kaje ka gayawa Mamanku mana".
Wasu sabbin hawayene suka zubowa Jamil a hankali ya juya ya fita".
A can sashin Sheykh ya samesu, Juwairiyya da Jalal ɗin da Affan sun tasashi a gaba, Affan yanata kuma, shi kuwa Jalal sai tattaune laɓɓansa yakeyi, da sauri Jamil ya iso cikin sanyi yace.
"Affan je ka gayawa Mama".
Da sauri Affan ya juya har zai fita kuma ya dawo jin Juwairiyya na cewa.
"No Affan kada kaje, ka gaya mata, nasan yanzu tana bacci ne".
Shi kuwa Ya Jafar sai ya shiga ɗakin nan ya fito ya shiga wancan ya fito yana kuka kuma.
Shigowar Abbane ya sasu su Jalal duka fita.
A hankali Abba ya kamo hannunshi suma suka fito, da mamaki a fuskar Jamil ya bisu da ido.
Shi kuwa Abba yana riƙe da hannun babban ɗan nashi suka wuce har makoncinsa,
Gefen gado ya kontar da dashi, kana a hankali yake shafa kanshi cikin taushi da tausayawa yace.
"Jafar kayi haƙuri kayi baccinka kabar kuka, Sheykh yana lfy lau, ya tafi ƙasar Saudia ne shida kakarku Sitti."
Shiru yayi yana kallon mahaifin nashi.
Shi kuwa Abba, kanshi yake shafawa yana kontar mishi hankali a take yayi baccinsa.
Bayan sallan ishane Jamil yaje wurin Kakansun ya sanar mishi halin da ake ciki ya ƙafarsa cewa.
"Allah rene, magar gsky kace Hamma Jabeer ya dawo, sabida abin ya Jafar yana tsananta in bayanan".
Murmushi kakan nasu yayi tare da cewa.
"Uhum ai Allah ya sauƙaƙa abinda zai taso Sheykh ya dawo ba tare da an gama dai-dai-ta abinda ya kaishi ba Dole shi wannan mai saɓulellen mondon Jalaluddin shi zai dena yawon iskanci ya zauna ya kula dashi tunda yafi kallonshi a madadin Sheykh".
Cikin takaici Jamil yace.
"To ni zan kai Ya Jafar saudia wurin Sheykh ɗin suci gaba da zama a can in sun so, tunda dai kun san Sheykh shine GARKUWAnmu".
Cikin kontar da murya kakan nashi ya ɗan tausasashi kana yace in yaje ya turo mishi Jalal.
A can Saudia kuma, sosai aketa shirya yadda ɗaurin Auren Sheykh da Jazrah zai kasance, duk da basu sanar mishiba, sabida kashedin da Sarki Jalaluddin da Nuruddeen sukayi musu dan ko yaushe in dai ana shirya batun aurenshi muddin yaji sai yaƙi fir yayi ta kaucewa dole a ƙarshe aure ya fasu, to wannan abunne yasa ba'a sanar mishiba.
Sai dai yasan batun zuwan da Jazrah take sashinsu wai nune da ita suke zaɓa mishi in tayi mishi.
To shi kuwa bayan gaisuwa ko sannu bai taɓa haɗasu da itaba.
Haroon kuwa da Jannart sunata shirye-shiryen dawowa gida Nigeria.
A garin Bani kuwa,
Yau tun bayan sallan isha'i yaro ya shigo yace, Ya Salmanu yana sallama da Aysha,
haka kuwa ta fita taje,
Suka zauna a dakalin ƙofar gidan nasu suna hango yadda,
Yara keta wasa a dandali domin ranar jumma'a tafi ko wacce rana a garesu wurin shanawa.
Ya Gaini ne ya fito riƙe da hannun Junainah, a bakin ƙofar suka wuce Su Shatu
Bayan sun gaisane ya wuce riƙe da hannun ƙanwar tasa,
Murmushi Salmanu yayi tare da cewa.
"Shatu, inaga dai aurenmu dana babban yaya rana ɗaya za'ayi shi".
Murmushi itama tayi, tare da cewa.
"Tab shifa har an kai kayan aure".
Ido ya ɗan lumshe tare da cewa.
"To ai in kin bani dama nima gobe-goben nan sai a kawo kayan aurenmu ko?".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta, alamun jin kunya.
Su Ya Gaini kuwa kai tsaye ƙofar gidan Ahaji Haro sukaje,
A bakin ƙofar suka tsaya, sunkuyowa ya ɗanyi a hankali yace.
"Yauwa ƙanwaliya maza shiga cikin gidan kicewa Addanki Bintu tazo".
Cikin happy tace. To kana ta shiga cikin gidan da sallama.
Kamar yadda gidansu yake hakama gidan Ahaji Haro duk suna zaune a tsakiyar gida da yaranshi da matanshi sunata hira, bayan ta gaidasune taje gefen Binto cikin raɗa ta gaya mata saƙon ƴaƴansu.
Wani ɗan kekyawan matashi ɗan kimanin shekaru sha takwas mai sunan Junaidu ne ya kalli Junainah cikin tsananin so da ƙaunar yarinyar yayi murmushi tare da taɓa mamanshi cikin raɗa yace.
"Inno ga surkarki in Allah ya yarda".
dariya suka ɗan yi dan kowa yasan Junaidu yasan son da yakewa Junainah tun tana ƙaramar ta.
Ita kuwa Junainah hannun Binto ta riƙo suka fito tare,
Junaidu na biye dasu a baya,
Koda suka fita, Gaini ne ya kalle Junaidu tare da cewa.
"Yauwa Junaidu raka min Junainah gida ko".
To yace kana yabi bayanta suna tafe suna hira, sunzo dai-dai ƙofar gidansu Ahaji Umaru ne suka samu Ya Seyo da Hinde suna hirarsu.
Koda suka wuce, murmushi Junaidu yayi tare da cewa.
"Junainah sai yaushe zan fara zuwa muma muyi hira ne?".
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Sai na ƙara girma kafin nan Addana tayi aure".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ko dai bakya so nane".
Da sauri cikin yarinta tace.
"A a ina sonka mana".
Dariyar jin daɗi sukayi baki ɗayansu, sun zo kusa da ƙofar gidansu.
Ya Ba'ana ne sukayi kiciɓis dashi, murmushi yayi tare da cewa.
"Yauwa Ƙanwaliya kuzo mu shiga in baki aike ki kaiwa Shatu".
To sukace kana sukabi bayanshi, a tsakar gida suka samu, Iya Bultu majaifiyar Ya Ba'ana kena ƙatuwar mace baƙa ƙarin da ita, ga jajayen idanu, fuskarnan a haɗe ta kalli Junainah dake gaidata da fullanci cikin tsananin tsawa tace.
"Ke tafi daga nan ƴan iskan fulani masu jajayen kunnuwa, dan uwarki Ni ba fillatace da zaki gaidani da fullanci, hegu kwarkwasa fidda mai gida a gidanshi yan iska masu kama da al'janu, in sha Allah ƙarshen zamanku a wannan yanki yana nan tafe".
Da sauri Junainah ta koma bayan Junaidu, shi kuwa Junaidu wani irin tafasa zuciyarshi keyi akanme zata zagesu dan kawai sun gaidata da fullanci.
Bukar ne mijinta wanda yake babarbaree ya kalleta tare da cewa.
"Kuma dai al'barkacin fulanin kikeci".
Ba'ana ne ya ɗan harari mahaifin nashi tare da waskewa yace.
"Fulani kecin al'barkacin ta dai, tunda kowa ya sani wannan yankidai na Ɓachamawa ne, ba fulaninba".
Cikin ƙarfin hali Junaidu yace.
"Ato ai dai ba kyau aka bamuba da kuɗin mu aka bamu, kai kamma ya Ba'ana kaifa bawanmu ne tunda kai babarbarene".
Wani irin suka kalawan yaron suka mishi a ƙahon zuciyarshi amman sai ya dake,
ledan su ayaba da inabin ya bawa Junainah tare da cewa.
"Uhu Junaidu kenan aini ba bakanuri bane ni ba Bachamene, Dan da in zama bawan fulani gwara in zama bawan karnuka".
Haka nan kalamansu ke tafasa zuciyar Junainah da Junaidu, haka yasa fuska a hade suka juya suka tafi, har sunje bakin ƙofar fita Ba'ana yace musu.
"Yauwa kuce mata ina zuwa yanzu bari inyi wonka".
To sukace kawai suka fita suka tafi.
A ƙofar gidansu suka tsaya gaban Ya Salmanu da Aysha, ledan Junainah ta ajiye a tsakiyarsu cikin jin haushi tace.
"Addana gashi inji ya Ba'ana wai in kawo miki, yace kuma yanzu zaizo wai wonka kawai zaiyi".
Tana kaiwa nan tayi cikin gida shi ma Junaidu Binta yayi a baya, har gabansu Ummey ya tsuguna suka gaisa kana yace.
"To Ummey ga Ƙanwaliya na rakota Ya Ganin ne yace in rokata har cikin gida".
Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
"Mun kuwa gode, ka gaida min Innonka kace mata, in Allah ya kaimu gobe ta turo min Hari tazo tamin kitso".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"To saida Safe Bappa".
Allah ya bamu al'khairi sukace baki ɗayansu.
Daga nan ya fito, har ya wuce Ya Salmanu yace.
"A a Junaidu zoka amshi tsarabar mana".
Cikin girmamawa yace.
"A a Ya Salmanu ya isheni".
Cikin kula Salmanu yace.
"Ni kam yaushenene zaku koma school?".
Da sauri yace.
"Saura kwana biyar hutunmu zai ƙare".
"To Allah ya taimaka yanzu aji nawa kane".
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Ina SS 3 ne fa, Ya Salmanu na kusa gamawa ai".
"Masha Allah, Allah ya taimaka".
Amin Amin yace kana ya juya ya tafi.
Ita kuwa Shatu cikin tsoro ta kalli Ya Salmanu a hankali tace.
"Ya Salmanu tashi ka tafi kada yazo ya sameka".
Cikin harshen fillanci yace.
"To shi mala'ikan ɗaukan raine? Ko dai so kike in guje masane Shatu, kina son ragon mijine?".
A hankali tace.
"A a Ya Salmanu zai cutar da kaine nake tsoro".
Da sauri ya katseta da cewa.
"Babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ko yaya zaiyi bashi da ikon kasheni sai in kwana-nane ya ƙare. Ko ciwon kai bai isa ya samin ba".
Shiru tayi tana kallonshi.
Sai kuma tai maza ta miƙe tsaye ganin kamar daga sama aka jefo Ba'ana gabansu.
Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa.
"Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haɗa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaɗi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ƙasar nan gaba ɗaya zan koma ƙasar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki ɗayanta!".
Cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Shatu tace.
"A a fa Ya Ba'ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min".
Da sauri Salmanu ya katseta da cewa.
"Sonta nakeyi Ba'ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar Shaɗi da kai a ranar Litinin na amince".
Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace.
"Lallai gidan Arɗo Yabani na gab da rasa motsin ɗana miji".
Yana faɗin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya ɓaci.
Cikin ƙarfin hali Salmanu ya nufi gida.
Shi kuwa Ba'ana yana ɓacewa a tsakiyar dottawan Fadan Arɗo Yabani ya baiyana,.
Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi.
So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa.
"A a Ba'ana lfy kuwa?".
Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace.
"Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al'farma fagen shaɗi, nida Salmanu ɗan Arɗo zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki ɗaya".
Da sauri Bappa yace.
"A a".
Da sauri Arɗo Yabani yace.
"A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar Shaɗi mai nasara yaci gasar".
Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru.
Shi kuwa Ba'ana cikin tarin ƙeta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci.
"Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taɓa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu".
A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi.
Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda Shaɗin zai kasance.
Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar Shaɗi da za'ayi jibi litinin, da kuma, waɗanda zasuyi gasar da sunan wacce za'ayi dan ita.
Gaba ɗaya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici,
Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ƙarar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za'ayi gasar Shaɗi da mutun da sun san ba'a taɓa nasara a kansa a.,
Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da Arɗo Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu.
Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi.
Shi kuwa Ba'ana tun ranar ya ɗauki tunƙur ƙasar da yake tsuma bulalinshi, ya kaishi Ƙauyen Bonon, gaban dodon tsafinsu,
Anan tukunyar ta kwana bulali tamanin dake cikin tunkuyar nan aketa tsumawa da tsafi.
Kana an jikasu da ruwan gishiri sannan an juye kunamai sama da ɗari a ciki, irin baƙaƙen kunamun nanne masu mugun dafi, an sasu ciki sunata harbin bulalin nan suna sa dafinsu a jiki. ranar lahadi da yamma ya amso tukunyar,
Har zauren gidansu Shatu yaje yasa aka kira mishi ita bayan ta fitone yace ta leƙa cikin tukunyar, a hankali tace.
"Me zan gani a ciki?".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Nazo in nuna miki bulalin shaɗi nane, ki gansu da kyau, dan ki cewa wancan koɗeɗden ya shirya shan zabga".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni ba sai na ganiba".
Murmushi yayi tare da buɗe tukunyar kana ya karkatar mata shi gabanta.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"In......
Littafina na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ko karanta a nitse.
0 comments:
Post a Comment