Satin Abbu uku yana jinyar kafar shi kafin ya warke ya fara fita harkokin shi. Naje gida weekend muka je Malumfashi, Malam Inuwa kanin baban su Daddy ya rasu, kakanni na na ainihi sun jima da rasuwa ban yi wayo na ganni dasu ba, shi yasa su Hafsy suke burge ni ba kadan ba, suna da kakanni ta kowanne fanni abin su. Wato naji dadin zuwa Malumfashi wannan karon ba kadan ba, cousins dina duk sun dawo daga makaranta wasu hutu suka zo wasu kuwa sun zo wajen gaisuwa ne, nan muka hadu muka yi ta yawace-yawace da ziyara har ban so lahadi tayi ba, haka dai muka yi sallama da dangina muka wuce gida. Muna isowa na wuce Kano Saboda yamma tayi don haka a gajiye likis na isa gida, babu abinda na iya tsinanawa, ina gama sallah na bi lafiyar gado sai da gari ya waye.
Mun je lab Ramlah take bani labarin wata er ajinmu a Kasu zata yi aure wannan week din, er Kano ce, ta tambaye ni zan je nace ai dole ne, Sahiba mutuniyar mu ce ta sosai. Tun a ranar na kira daddy na fada mishi ba zan samu zuwa weekend wannan satin ba saboda bikin abokiyar karatun mu yace shi kenan Allah ya kaimu wani satin. Nayi shiru ban kashe wayar ba, tuni ya fahimci abinda nake nufi, "kudin anko koh?" naji ya tambaye ni, na saki murmushi mai sauti, wato Daddy ya karance ni kamar bayan hannunshi, yace "I will wire you the money in the next few minutes" nace "to Daddy nagode, Allah ya bar min kai!" yayi dariya tare da cewa "uwata kenan". A ranar muka shiga kasuwa muka sayo ashoben bikin, muka biya ta wajen telan Ramlah muka ajiye dinkin. Ranar juma'ah muka je saloon aka mana wankin kai da kitso, ni har kunshin hannu aka min, dama gani da son lalle kamar me. Ya kuwa yi min kyau sosai, sai da Ramlah taga na hannuna wai take cewa data sani da an mata itama, na kuwa dinga mata dariya. Daga nan muka yi shatar taxi muka wuce gida, sai da muka ajiye ta kafin muka wuce. Ina shiga falon naci karo da buhunan Irish, plantain ne, kayan marmari dasu doya, tunda na gani nasan cewa Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ibadan taron Doctors na fadin Nigeria, Allah ya taimaki rayuwata na mishi text na gaya mishi zamu biya ta saloon daga lab, yau da na shiga uku na ai. Na taimakawa Harira muka kai kayan kicin muka ajiye su a inda ya dace kafin na wuce dakina nayi sallah. Ina xaune Hafsy ta leko dakin tace in fita mu ci abinci, bana ma jin yunwa amma haka nan dai na fita don nasan bani da wani excuse din badawa. Na dauki gyale mai fadi na dora akan doguwar rigar jikina. Bana yarda in fita daga dakina ba tare da mayafi ba matukar nasan Abbu yana gari sai dai by mistake. Suna kan dinning table a zaune, Abbu na fara hangowa. Sanye yake da shirt din KC brown da bakin Jeans, ya kara wani irin kyau na musamman a kwanaki shida din da nayi ban gan shi ba. Na tafi da dokina na durkusa na gaida shi, shima cike da fara'ah ya amsa min, na gaida Anty Mubeenah kafin naja kujera na zauna muka fara cin abinci. Da muka gama Abbu ya fita, Anty ta wuce daki mu kuwa muka zauna a falo muna kallo har wajen karfe goma da rabi, har lokacin Abbu bai dawo ba. Na kashe kayan kallon kowannen mu ya nufi dakin shi ya kwanta.
[09:15, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*18*
_'Turn to Allaaah he's never far away......_
_'Put your trust in him, raise your hands and pray..... Ohhh Ya Allah! Guide my steps don't let me go astray..... You're the only One Who can show me the way..... Show me the way........ Show me the way...........'_
*In Shaa Allah by Maheer Zayn*
Da kyar na samu na sauka daga kan gadona ganin na gaji da juye-juye barci yaki zuwa misalin karfe tara kenan na washegarin ranar Assabar. Na fito daga dakina sanye da wandon Sports da rigar shi cotton ruwan madara, na dora hular beanie akaina wadda na nannade gashin kaina na saka a ciki. Wandering na fara yi a cikin falon hannuwana saye cikin aljihun wandon. Na tsaya a kasan staircase din dake falon, tunda nake a gidan ban taba Hawa saman ba, jifa-jifa dai na kan ga ko dai Abbu ya hau ko kuma yara sun sauko kuma ban taba tambayar me suke yi a wajen ba. Out of curiosity na fara takawa ina hawa saman, Tun kafin in karasa na saki baki galala ina kallo. Gym zan kira shi ko kuwa amusement park?? Kayan wasan yara kala-kala da different types of exercising machines ne birjik a wajen, wasu na san su saboda nima ina zuwa gym duk weekends lokacin da ina gida. Na fara zagaye wajen cike da mamaki, as in Abbu will never cease to amaze beings. Kan Dip station na hau na fara kokarin dagawa amma ko motsi, da alamun yafi karfina ne don haka na sauka. Daga bayana naji ance "hey! What are you doing here??" da sauri na juya, yana tsaye a jikin wata kofa sanye da sportys ya rataya dan karamin tawul a wuyanshi, na sadda kaina kasa cikin rashin abin cewa. Ya fara takowa a nutse har yazo gab dani, ya jingina da station machine din, jin yayi shiru nasan sauraren amsar da zan bashi ne yake yi, nace "umh! Dama kawai ina zagaye ne sai kuma naga na shigo nan" yace "this is your first time here I believe?" na gyada kaina. Yace I see. Are you interested in exercising?? Da sauri na dago ina kallon shi, "sosai ma Abbu! A gida ma ina zuwa gym duk sat...." wani irin kallo yake wata min babu shiri na kama bakina na bame, na sadda kaina kasa ina jin kafafuna suna dan shaking. Kokarin fita ya fara yi yana cewa "sai ki dan motsa jikinki ko? Ni zan sauka kasa..... By the way, I like your lalle!" nayi murmushi ina kara kallon hannuna, ni kaina nasan lallen yayi kyau sosai. Yana fita na fara wasa da karafa, sai wajen karfe goma da rabi na sauko falo, break nayi na koma dakina, sai lokacin naji gajiya da barci sun tarar min na kwanta. Kiran wayar Ramlah ne ya tashe ni daga barcin da nake yi, tace gata nan ta shigo layin mu daga amsar dinki in fito waje, na tashi da sauri na dora hijabi akan kayana na fita. Abbu da maigadi da wani makocin Abbu din suna kofar gida akan dan benci suna hira, na gaidasu. Ina tsayawa sai gata cikin napep, ta fito ta biya mai napep din, ta gaida su Abbu kafin muka shige cikin gida. Muna shiga ta fara jefo mun tambaya a rikice, "ke waccan giant gaye din waye? Anan gidan yake zaune?" cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace "wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??" dariya na kwashe da ita nace "wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?" tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, "Ya Allah! He's cool babe, dan dai yana da mata wallahi....!" duka na kai mata ina dariya, "da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya" ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, "sai dai rigar tayi show me da yawa" na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, "to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?" na turo baki kafin na daga kafada sama.
Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai'i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace "amma kinyi kyau sosai Nafee" nayi murmushi sosai har da fari, I'm a sucker for compliments. Yace "naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?" nace "y not?" na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *"Where are you now?"* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace "Abbu..... Gida. Gida zan tafi yanxu" tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan" nace "noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi" ta kalle ni sosai, "to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba" na girgiza kai, "baki san Abbu bane Ramlah..... Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan" na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, "muje koh?" na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace "to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride" yace "Kar ki damu.... Me za a cewa mutumin ne?" na danyi murmushi nace "kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba" yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu'ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, "wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?" jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba" yace "sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?" na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace "waye ya kawo ki yanzun?" nace "Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne" yace "dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?" nayi saurin cewa "ai abokin....." sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, "it's okay!" naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, "goodnight!" ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta.
*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] +233 50 348 1936: Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, "For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don't you think it's high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?" tsaki naji taja, "kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??" shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, "hakkina fa kuma Mubeenah?" "ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?" amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace "am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba....!" katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, ".... Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn't give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!" ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace "zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah" cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace "m looking forward to it" daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma'auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka??
Am sorry for the late update, jiya through out a kwance na yini ban jin dadin jikina ne sam. Yau din ma ta maza ce nayi shi yasa wallahi. Just kara hakuri dani pa!
*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*19*
Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.
[09:15, 12/4/2017] +233 50 348 1936: Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa'adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace "yah? Baki zuwa ne ke?" na kalli su Ni'ima kafin na kara kallon shi, "can I?" ya tabe baki, "that is idan kina son zuwa fa" na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni'ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni'ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai'i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi "Plss dafa mun shayi mana" nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, "lafiya Nafeesah?" na sadda kaina kasa nace "Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!" shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, "ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??" na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace "kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba" yace "dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka" nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace "tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?" na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace "Abbu nagode sosai, Goodnight!" na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu'ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani.
*♡Jeedderh♡*
[09:15, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*20*
*Sakon taya murna zuwa ga marubuciya MAIMUNA SANI BELI na lashe gasar HIKAYATA da BBC ta hada na gajerun labarai. Allah ya kara miki kaifin basira*
"I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?" cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace "yes ma'am" tace "bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?" nace "I'm not very sure ma, I'm thinking of filling D E form" tace "ina fata a nan BUK ne?" na girgiza kaina da sauri, "no ma'am, ABU Zaria ne" ta kalleni tana murmushi, "why?" na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace "maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida" ....ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace "am wishing you all the best Nafeesah" nace "thanks ma'am" na fita.
Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, "Soon.....!" na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, "ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?" na yamutsa fuska, "stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?" tace "ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma......" "For Heaven's sake Ramlah!!" na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, "this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!" cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, "am sorry babe, I shouldn't have said what I said earlier.... M sorry, really" ta kauce daga gabana, "me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!" nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, "look Ramlah! Wallahi I really didn't meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I'm trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah...." zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, "m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it's hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn't know, ki yafe min" rungumeta nayi ina tapping bayanta, "I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you" ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa "m sorry Nafeesah" nace "what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan" ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taron mu da Ramlah kenan.
[09:16, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*22*
_'Some nights I can hear you., Screaming on the phone over something that he did....., And I wonder what can I do to make you throw him out so you can let me in.....!'_
A song by *Shayne Ward* Titled *'Melt the Snow'*. I hope you will enjoy listening to it.
Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it's not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn't. God Forgive him but he's enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss.....! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, "Muneer you evil bastard!" yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!...." da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne.....!.
☆☆☆☆☆☆☆☆
A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar "Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?" sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata "idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne" ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da 'harara a duhu' saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, "Are you ok Nafeesah???!"
*♡Jeedderh♡*
[09:16, 12/4/2017] +233 50 348 1936: Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, "yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?" na zaro ido ina kallonta, "Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai" ta turo baki, "to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?" nace "dat's a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?" tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace "haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?" da sauri ta dago kanta ta kalleni, "da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai'i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da 'ya'yansu, Anty tace "Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?" nayi murmushi tare da gyada kai, tace "eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki" Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace "Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?" nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace "anan ma zata dinga mana weekend koh?" na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace "ehh" a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, "pretty ina zuwa?" ta juya tace "ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau" yace "a'ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata" aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, "babu komi Abbu, taho muje kinji?" ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace "Nafeesah!" na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, "are you sure Pretty ba zata takura miki ba?" na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace "umh.... Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?" nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace "good! I'm happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe" da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu'ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that was the worst moment I've regretted the most in my life!!!.
*♡Jeedderh♡*
[09:16, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*23*
Kalmar 'Are You Ok' kalma ce da nake matukar tsoro idan ina cikin halin damuwa. I am a very emotional person, shi yasa idan ina cikin halin damuwa bana son mutane a kusa dani saboda gudun su tambaye ni lafiya? Don zan iya fashewa da kuka, ni a gare ni tambayar are you ok kamar fama min gyambo ne. Yanzu ma sai da nayi iyaka kokarin da zanyi na danne kukan da yake kokarin barke min nace "m fine Abbu, kawai bana jin dadin jikina ne" ya kalleni kawai nasan bai yarda da abinda nace ba, ban ga laifin shi ba don yadda nake a hargitsen nan babu wanda zai yarda wai gajiya ce ta maida ni haka. Ya kalleni sosai kamar wanda yake so yayi magana sai kuma kawai ya maida kallonshi ga titi, a raina naji dadin hakan nasan tambaya daya zai kara jefo min zan fashe da kuka, kuka kuma ba abinda nayi niyar in ci gaba dayi bane saboda Muneer. Har yayi parking a parking lot din dept din Microbiology, na yunkura zan bude motar ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana, na Juya a hankali na kalleshi. Idanuwan shi fes a kaina suke, naji wani slight rawar jiki kafin in sadda kaina kasa, muryar shi a sanyaye yace "akwai abinda yake damunki Nafeesah wanda kika ki gaya min and I wouldn't force you to tell me, kawai ina so in gaya miki cewa komi na rayuwa sai da hakuri, koma menene yake damun ki kiyi hakuri ki dauke shi a ba komi. Idan ma wani abu ne kika rasa kike ganin kamar ba zaki iya hakuri da rashin ba kada ki manta Allah yana tare da Ke. Shi ya mana alkawarin canza mana abinda yake sharri ne a gare mu zuwa ga mafi alkhairin shi don haka ki roke shi game da abinda yafi alkhairi a gare ki ba kiyi holding into something wanda yake ba alkhairin ki bane kin gane?" na gyada kaina a hankali maganganun shi sun shige ni. Abinda ya kamata in tuna kenan a lokacin da naga hoton Muneer da amaryar shi jiya, abinda ya kamata inyi kenan ba wai in kira shi ba ina kara fallasa kaina da disappointing kaina, sai yanzu naga cewar hakika abinda nayi jiya ban kyauta ba, naji kunyar kaina ta kama ni har ma data Muneer din, ko da wane ido zan sake kallonshi kuma yanzu??. Nace "na gane Abbu nagode sosai, In shaa Allahu zan yi amfani da shawarar ka" yace "good" shiru ya biyo baya a cikin motar, can naji ya sake magana cikin whisper, kamar kuma wanda yake tsoron yin maganar, "anjima kuma sai gida koh?" na gyada kaina a sanyaye, barin rayuwar Abbu da iyalan shi!! Tunani ne mara dadi dake fadar min da gaba a duk lokacin da ya fado min a cikin raina don haka nake iyaka kokarina wajen ganin na kauda tunanin daga cikin raina. Na sake tsintar muryar shi yana tambayana, "da gaske zaki dinga zuwa kina mana weekend?" nace ehh, a cikin raina nasan fada kawai nake yi ba don zan dinga zuwa ba sai don kawai kada su dameni da tambaya. Kamar yasan abinda nake tunani, yace "da gaske kike ko kuma kina fada ne kawai?" shiru nayi wannan karon, yayi murmushi tare da kallona kawai yace na gane. Dash board ya bude ya ciro wata karamar jaka fara mai hannu ya miko min, na amsa fuskana dauke da alamun tambaya, yace "it's a small thank u gift, thank u for staying with us Nafeesah, we enjoyed having u in our life and we wish you will come back to us forever!" na dan rausayar da kaina cikin alamun rashin gane inda maganar tashi ta saka gaba, me yake nufi ne? Murmushi yayi ganin ya saka kwalwa na cikin rudani. Yayi murmushi yace "oya! Up you go! Naga abokan ki suna jiran ki tun dazu" sai lokacin idanuna suka koma ga inda muke zaune, su Ni'ima na hango tsaye a kofar shiga lab dinmu suna hirarsu da Ramlah, cikin sauri na jefa jakar daya bani cikin handbag dita na mishi godiya tare da bude murfin motar na fita. Gabadaya kallo suke bina dashi cike da alamun tambaya nasan bai wuce na mamakin abinda muka tsaya hirantawa da Abbu bane tun dazu, naja fuska tare da kara gyara zaman gilashi na a fuskana. Tun kafin in karasa wajen su suka iso gare ni, Saadiya da Ni'ima suka kamo hannuna Ramlah kuma ta dafa kafadata, cike da damuwa suke tambayana, "Nafeesah are you ok?" ni duk sai naji sun ma bani haushi, na cire gilashin idona ina kallonsu cike da takaici, "why?? Saboda crush dina zai yi aure sai kuke zaton karewar rayuwata ne yazo ko me?" gabadayan su were relieved da yadda suka ga nayi, Ramlah tace "yeah! I thought about more than that ma, nayi zaton zan ganki kamar sabuwar kamu ne wallahi sai kuma na ganki da hankalinki dai, but are you really ok?" na gyada kaina "yeah, I am Ramlah but that doesn't mean ban ji haushin abinda Muneer ya min ba" Ramlah ta rungume ni da sauri tana tapping bayana, "ohh my poor friend, Am really sorry. Don Allah kiyi hakuri, nasan in shaa Allah wanda yafi Muneer alkhairi a gare ki yana nan zuwa" na danyi murmushi, kwatankwacin abinda Abbu ya gama fada min. Na janye daga jikinta ina kallon su Ni'ima dake tsaye suna kallonmu nace "ba kuna da lectures ba wai me kuke yi anan?" Sa'adiya tace "wallahi Ramlah ce ta kira mu wai muzo mu tayata baki hakuri don tasan yau a hargitse zaki xo sai kuma muka ga akasin haka" ajiyar zuciya nayi nace "na hargitse kam Sady but Alhamdullillah na dawo cikin hayyaci na kuje kawai" suka mana sallama suka tafi mu kuma muka shiga lab. Ranar babu aikin da muka yi, sallama muka yi da staff da lab attendants na dept din don haka wajen karfe sha daya muka bar lab din cike da kewar mutanen da muka zauna dasu. Wajen su Ni'ima muka je na kara musu sallama, daga nan na wuce gida. Ita Ramlah tana Kano tukun.
Ina zuwa gida na kara hada kan kayana na zauna zaman jiran Daddy don yace shi zai zo ya dauke ni. Bayan an fito daga masallaci sai gashi har da Mommy, sai da muka yi Sallar La'asar sannan muka yi sallama da iyalan Ibrahim Galadanchi cike da kewa, kauna da zullumi. Zullumin ko zan sake ganin su a rayuwata ko kuwa? Zullumin ko zan iya da korar wadannan kananun feelings da nake ji game da Abbu? Zullumin ko zan iya yin normal rayuwa kamar da wadda nake yi a gaban Iyaye na? Magana ta gaskiya watanni shida da nayi tare da Iyalan Ibrahim Galadanchi watanni ne masu muhimmanci da tarihi a gare ni, sun koya min abubuwa da dama a rayuwata, sun kuma gaya min ainihin abinda ni, Zuciya, da gangar jikina suke so da Muradi.
Na daga idanu a hankali na kalli Hafsy dake hannun Babanta tana rusa kuka da iyakar karfinta tana ihun Ita sai ta bini, na kalli su Qaseem suma duk fuskokinsu cike suke da jimami har da kwalla a cikin idanunsu, hakika bahaushe yayi gaskiya da yace 'Sabo turken Wawa' dana kalli fuskar Abbu kuwa sai da naji kamar in balle murfin motar in fito ince na fasa komawa gidan. Damuwar dake fuskar shi was obvious, na karance ta kuru-kuru cikin idanunshi, kallona yake yi da dukka idanunshi, yanayin shi ya min kama da wani wanda yake tsoron rasa wani abu mai matukar muhimmanci a gare shi. Daddy ya bude murfin motar ya shigo ya mata key, Abbu da iyalan shi suka daga mana hannu bakinsu dauke da addu'ar Allah ya kiyaye hanyar yayin da naji kwalla ta cika min idanu, Daddy ya ja motar muka tafi. Nabi gidan da kallo idanuna cike da kwallah, Allah kenan! Kamar a ranar ne nazo gidan, na tuna sanda su Daddy zasu tafi kukan rabuwa dasu nayi, gashi yau kuma ina kukan rabuwa da iyalan Abbu. Tafi tafiya na fara bajewa daga kukan dana fara, su Daddy hirarsu suke tayi game da karamcin iyalan Abbu, ni kam kallon gefen hanya nake yi kawai. Barci ya dauke ni bani na tashi ba sai da muka isa gidanmu shima Mommy ce ta tashe ni, na fito daga motar fuskana a washe ina kallon gidanmu, Finally dai! I am back!. Muka dauki wasu kayan muka shiga dasu yayin da Maigadi ya shigo da sauran, Dakina a shirye na tarar dashi kamar ina gidan don haka ina shiga na ajiye jakar hannuna akan kujera daya dake dakin na zube akan gado ina ajiyar numfashi.
*♡Jeedderh♡*
[09:16, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*24*
_Follow me on wattpad *@Jeeedorhh*_
Ana kiran sallah Mommy ta leko dakina tace in fito Daddy zai ja mu sallah, sai lokacin na tashi daga kwanciyar da nayi na shiga bayi na dauro alwala na fito, dogon hijabi na dauka na tafi dakin Daddy. Wani dan karamin dakine a cikin dakin shi wanda yake aiwatar da ibadojin shi a ciki, dakin lullube yake da darduma sai tashin kamshi yake yi, shelves shelves na littafan addini a gefe a shirye gwanin ban sha'awa. Daddy ya ja mu sallah, muna gamawa ni da Mommy muka dauko littafin Arrijalu Wan-nisa'u fil Jannah Daddy ya ja mana karatu har aka kira sallar Ishai muka yi. Muka fita zamu yi dinner amma abinci fa yace sam bai ga wajen zama a cikina ba, Mommy ta kalli yadda nake ta juya cokali a cikin Irish Supper data mana wanda yana daya daga cikin favorites dina, na tabbata saboda ni tayi shi amma na kasa ci, tace "Baby lafiyan ki lau kuwa kin kasa cin abinci?" Daddy ya dago yana kallona, cikin sauri na girgiza kai nace "m fine Mom, cikina ne a cike kawai" Daddy ya tsiyayo Pineapple and coconut juice da Mommyn ta hada ya miko min, na amsa tare da kaiwa bakina na kur6a, aikuwa har da lumshe idanuna saboda gardi da sanyin daya ratsa ni, da taimakon lemun na dan samu na kara tura abincin haka nan kafin na musu sai da safe na tafi dakina. Ina shiga na fara kokarin kimtsa kayana cikin wardrobe duk a kokarina na kauda tunanikan dake dankare a cikin raina. Na janyo handbag dita ina kokarin rataye ta a bags rack naji nauyi a ciki, cike da mamaki na zura hannuna ciki na fito da karamar jakar da Abbu ya bani da safe, a hankali na zauna a gefen gado tare da janyo dan karamin purple akwatin dake ciki, cike da mamaki na fiddo shi ina jujjuya shi a hannuna. Ina budewa na zaro idanu sakamakon wata siririyar sarka dana gani a ciki da dankunnenta har da zobe, sarka doesn't look that out of ordinary but daga ganinta kasan ba karamar sarka bace. Hannuna rawa ya shiga yi na rasa abinda zanyi, tashi nayi da dan akwatin a hannuna na fita falo, su Daddy suna zaune suna kallo duk suka bini da kallo, na zauna a gefen Daddy tare da mika mishi akwatin nace Abbu ne ya bani dazu, da mamaki Daddy ya karbi akwatin yana jijjiga shi a hannunshi yace "Shi Ibrahim din ne ya baki wannan sarkar?" na gyada kai a hankali, ni kaina na kasa yarda da hakan gani nake kamar a mafarki, Daddy yace "amma me yasa?" na jijjiga kai "nima ban Sani ba Dad kawai bani yayi" Mommy ta karbi sarkar itama ta dudduba, ta kalli Daddy tace "da alamun sarkar Babba ce fa Habibiy, Anya zamu karba kuwa?" Daddy yace "abinda nake tunani kenan exactly..." yace min "ki je daki ki kwanta, da safe zan tuntube Ibrahim din inji" nace "toh" na musu sai da safe na wuce dakina. Ina kwanciya barci ya kwashe ni, after all it has been one exhausting and stressful day.
Washegari Daddy ya dawo min da sarkar da Abbu ya bani, ban tambayi abinda ya cewa Abbu ba ni dai yana bani na bude na zura zoben a cikin yatsa na. A ranar sai ga Anty Ameenah ta kira ni, korafi ta min akan na tafi ba tare dana musu sallama ba, hakuri nayi ta bata akan cewa Lokaci ne ban samu ba, bata hakura ba sai dana dauki alkawarin cewa zan je gidanta musamman sannan. Bayan mun gama wayar shiru nayi ina kallon wayar a raina ina tuhumar kaina akan ba mutane false hope na ganina da ziyartar su bayan nasan cewa ba haka bane a cikin raina.
Nayi shiru akan gado duk kadaici ya ishe ni, a raina na raya da ace a gidan Abbu nake da war haka ko dai muna hira dasu Hafsy, ina kicin ina girki ko kuma muna wasa a gym kamar yadda muka saba kwanan nan idan bama aikin komi. Wayata na janyo na latso lambar Abbu, sai kuma na kasa danna mishi kiran, a raina ina mamakin kaina me zan ce mishi ne idan ya dauka? Me zan ce mishi ne dalilin da yasa na kira shi?? Kawai sai na maida akalar wayar zuwa ga Anty Mubeenah, ta shiga tayi ta ringing amma ba a dauka ba, shiru na bata mintuna biyar ko zata kira amma bata kira ba sai na kira wayar Abdullahi, cikin ikon Allah ya dauka, cike da doki muka gaida dashi. Nace ya bani Hafsy mu gaisa yace ai tana gida yau bata je makaranta ba, nace me yasa? Yace ai Tun jiya take kukan Ita lallai sai an kawo ta wajena shine yau ta tashi da zazzabi, a raina naji ba dadi don haka nace idan sun koma gida ya kira ni yace toh. Yana kashe wayar na kira Ni'ima, muna gama gaisawa tace "yanzu kuwa Abbu ya bar nan" nayi jim ina kokarin yin maraba da sunan shi da naji ta ambata, haka kawai naji zuciyata ta dauki bugu da karfi, "umh ya su Mama?" nayi Kokari na kauda hirar Abbu da take kokarin sakowa amma duk da haka ban tsira ba, "next week ne bikin bude kamfanin shi a Beijing, how I wish zan samu zuwa" na hangame baki cikin mamaki nace "Da gaske?" tace wallahi kuwa. Nace "Masha Allah! Lallai zan kira shi in taya shi murna, na dade da jin labarin bude kamfanin wajen Bala Malam, ni nayi zaton ma an jima da budewa ashe har yanzu?" tace "kin san dama bude kamfani a kasar waje is not something easy musamman ga wanda yake ba dan kasar ba, don ma abokin aikin nashi haifaffen Beijing din ne shi yasa" na gyada kai. Tace "Hajiyar mu tayi mamakin tafiyar ki fa dazu da Babban Yaya yana gaya mata, tayi ta korafin baki masu bankwana ba" a raina naji babu dadi, sai lokacin naji ban kyauta ba, haka na baro Kano bayan Iyalan Abbu da Anty Haleemah babu wanda na wa sallama, nace "in shaa Allah duk ranar dana kara shigowa Kano zan zo in gaishe ta" tace better! Muka dan kara hira kafin muka yi sallama. Later in the evening Daddy ya dauke mu muka fita yawon gari, shiga nan fita nan har gidan Anty Uwani muka je acan ma muka yi sallar Magriba kafin muka juyo gida.
Sai dana gama shirin kwanciya barci misalin karfe tara na dare sannan na turawa Abbu text message, *"Abbu naji ance zaku bude kamfanin ku next week, Allah ya sanya Albarka da Alkhairi. And thank you for the necklace, it's beautiful, I like it!"*.
[09:16, 12/4/2017] +233 50 348 1936: Minti biyar tsakani naji Wayata tana vibrating, da sauri na janyo ta, as expected; Abbu ne. Sashe daya na zuciyata cike yake da murnar jin muryar Abbu yayin da a gefe daya nake jin wata er fargaba da tsoro dana rasa ko na menene a cikin raina. Na daga wayar da sallama cikin wata siririyar murya wadda ban san ina da Ita ba. A nashi bangaren sai da yaji wani yarr! Hakan ne ya haddasa mishi sanyin jiki da sanyin murya a lokaci guda, shima cikin sanyin muryar ya amsa min, yace "Why didn't you call early?" ban fahimci abinda yace ba nace "naga dare yayi ne shi yasa na maka text" wanda a hakikanin gaskiya ba haka bane ba, ina jin tsoron abinda jin muryar Abbu zai haddasa min a cikin jikina ne, yace "it's just nine fa, ya kike anyway?" nace "lafiya lau...... Naga sarkar daka bani, nagode sosai" ya dan yi er dariya, "shine Daddyn ki ya kira ni yau tun da safe yana interrogating dina kamar wani wanda yayi kyauta da abinda bai dace ba, sha ya bani dariya sosai ya kuma burge ni" naji na dan saki murmushi, ina so inji ana yabon iyayena, nace "sarkar ce Abbu naji Mommy tace babba ce, why would you give me such a precious thing?" na tambaye shi abinda nake ta tunani tun dazu, me yasa zai bani sarka babba haka ni ba diyar shi ba ni ba matar shi ba, in fact bamu hada ko wace irin alaka dashi ba sai ta Diyar Aboki da Abokin Uba? Ya katse ni ta hanyar cewa "Because I can ofcoure! So ya kika ga sarkar? Ina fata ta burge ki?" na kalli zoben hannuna naga yadda ta kayata hannun nawa sosai, nace "Sosai ma Abbu, zoben ya zauna a hannuna perfectly kamar don ni aka yi shi" yace "ai dama saboda Ke aka yi shi din" na danyi jim ina so kada in yiwa amsar tashi fahimtar da ba kenan ba, na maida akalar hirar tamu zuwa wata daban ta hanyar tambayar shi ina su Hafsy! Yace "pretty ta sha kuka tun jiya har dan zazzabi tayi saboda tafiyar ki" nace "Allah sarki Hafsy! I really miss her so much!" ba zato naji yace "ni fa?!" tsit nayi ina kifta idanu, maganar tazo min a bazata, ya sake cewa "ni fa? Didn't you miss me?" cikin wata irin seductive murya, Ya Allah! Me Abbu yake nufi da innocent rayuwata ne yake min magana cikin irin wannan muryar? Na tabbata da a kusa dashi nake babu abinda zai hana ni jefa jikina kan shi, cikin rawar murya numfashi na har daukewa yake nace "Abbu... Sai.... Da safe. I gotta go" daga can bangaren shi ya dan hade ran shi, a hankali yace "you are not enjoying having my company?" nayi saurin girgiza kaina, idan da mutumin da nafi jin dadin hira dashi duk duniyar nan wanda nake ganin ko kwana zamu yi akan waya muna hira ba zan gaji dashi ba to Abbu ne sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo, bana fata in sake dandana abinda naji daga Muneer a wajen ko wani namiji kenan ya zama dole in janye jikina daga Abbu tun kafin inyi ending up hurting my self. Nace "m just a bit sleepy ne Abbu" yace "ok, yakamata kiyi barci kam. Sweet dreams to you" "Thanks.... And same to you!" na karasa fada more like a whisper to myself, ban sani ba ko yaji ko bai ji ba? Bana ma so yaji din ni, nayi sauri na kashe wayar. Makale ta nayi a kirjina daidai saitin zuciyata ina ajiyar zuciya idanuna a lumshe, na kwashe Lokaci mai tsawo a haka kafin in silale kan gado in kwanta. Babu abinda ya dinga dawo min a cikin kaina irin fuskar Abbu, yanayin yadda yake gudanar da rayuwar shi very cool and impressive, murmushin shi, yanayin kallon shi, zubin halittar shi.... A takaice dai da tunanin Abbu nayi barci a ranar. Wasu irin mafarkai na dinga yi barkatai kala-kala kuma cikin su babu wanda ban ga Abbu a ciki ba. Muna zaune akan wani lilo ni dashi a wani hadadden lambu mai cike da ni'imah, hira muke yi dashi duk da bana sanin abinda yake fada amma murmushi nake tayi a mafarkin har ina hadawa da dariya, ya dauko strawberry da fork ya miko min, na daga bakina kenan zan karba naji an daka min duka a kafada ba shiri na tashi daga mafarkin da nake, hannuna dafe da kafadata inda yake min xugi na tashi zaune ina kallon wanda ya aikata wannan danyen aiki. Mommy ce tsaye a kaina tana hararata, tunda naga haka nasan abinda nayi. Da sauri na kai duba na zuwa jikina, as I expected; babu riga. Da sauri naja bargo na rufe zuwa wuyana tare da sadda kaina kasa, nasan cewa yau mai kwatana a hannun Mom sai Allah. Cikin hararar da take jifa na dashi tace "Yanzu saboda Allah Ummiey har yanzu baki daina wannan rashin hankalin da kike yi ba? Haka kika je gidan mutane dama kina musu tallar halittar jikin ki?" da sauri na girgiza mata kai, "A'ah wallahi Mom, bana yi a can" tace sai anan koh saboda kin raina ni ko" nayi saurin girgiza kai nan ma, "Allah Mommy ba haka bane, ni fa ban ma san lokacin dana cire rigar ba" tace "rufa min baki nan uwar en zagin baki tun yaushe nake miki fada game da haka Ummiey? Amma saboda taurin kai saboda kin maida ni abokiyar wasan ki baki ji koh?" tuni hawaye suka ciko min ido abinda nasan Mommy bata so kenan, cikin shagwaba nace "Allah Mommy da gaske nake. Nima fa ban san lokacin da nake cirewa ba, kawai ji nake yi kamar rigar ta na shake ni sai in kasa numfashi shi yasa nake cire rigar kuma fa na daina Allah da gaske, ban san ya aka yi na cire jiya ba" ta kalleni kafin ta kauda kai ta juya zata bar dakin, "sai ki tashi ai kiyi sallah koh? An kira tun dazu" na bita da kallo har ta bar dakin, sighing nayi a hankali tare da lalubo rigata da nayi jifa da Ita a kasan gado na zura, saukowa nayi daga kan gadon na fada bandaki.
[09:17, 12/4/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*26*
Anty Shafa ta fito daga dakin da aka mata masauki tana jan hannun Mukhlis, muna zaune a cikin falo Bayan mun gama cin abinci, ina gefen Mommy a zaune kawai muna hira da ita. Anty tace "Ummiey zo ki raka ni mana?" Na kalli Mommy kafin in maida kallona ga Antyn, Mommy tace "ni fa ba hana ki zan yi ba kike wani kallona, tashi ku tafi mana" murmushi nayi na tashi na shiga dakina, wandon jeans ne a jikina da shirt don haka na saka doguwar hijabi na fita muka wuce gidan su Anty. A Shagari road suke basu da nisa da inda muke don haka tricycle muka yi shata har kofar gidansu, gidan Babban gida ne da parts parts. Mahaifin su matan shi uku saboda haka gidan su gidan iyali ne sosai, Anty Shafa itace autar uwargidan Hajiya Maryam wadda ta rasu shekaru biyu da suka wuce. Muna shiga gidan gida ya dauki sowar murnar zuwanta, da kyar muka samu muka shiga part din Hajiya Talatu uwar gida a halin da ake ciki. Muka shiga har uwar dakanta inda muka sameta akan gado a hakimce, cike da girmamawa muka gaidata ta wani amsa da kyar kamar wadda aka takurawa, dana kalleta sosai sai naga kamanninsu da gayen nan na airport na tabe baki a raina nace ashe gado yayi. Bamu yi minti goma ba muka tashi muka wuce daya part din, Ita dayar da naji suna cewa Hajiya Amarya ba laifi tana da fara'a. Anan sashen nata en sannu da zuwa suka yi ta shigi da fici. Sai wajen karfe goma na dare muka musu sallama, na saba Mukhlis dake ta shakar barci a kafadata. Muna fita waje muka jiyo horn din mota a gefenmu, muka juya. Wata jar mota er karama da Ita mai kyau, Anty tace muje, Harith ne zai mika mu gida. Sai dana turo baki kafin na bi bayanta, haka kawai naji gayen bai kwanta min a rai ba. Na bude gidan baya na zauna a gefen Anty, Harith ya juyo ya kalli Antyn kafin ya kalleni ya sake kallonta, "amma dai ina fata ba Driver zaku maida ni ba ko Sis?" Anty tace min dan Allah tashi ki koma gaba diyata. Ba yanda na iya na fita na koma gaban, ya tashi motar muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikinmu har muka isa kofar gidanmu, yayi parking muka fita, Anty tace mishi "sai da safe koh?" bai amsa ba sai kallona da yayi, "enmata babu godiya ne?" ban san lokacin dana wurga mishi harara ba na juya na wuce abina, na kula he's very arrogant. Anty ta biyo bayana tana ce min wai kar in damu dashi, haka halinshi yake. Ban ma tanka mata ba don a tunanina ai sai ka damu da mutum ne sannan al'amuran shi suke damun ka. Sai da muka shimfidar da Mukhlis sannan na mata sai da safe na wuce dakina, cikin mintuna sha biyar na gama duk shirin da zan yi na kwanta barci.
Washegari aka fara bikin gidan su Anty Shafa, tun da safe ta tafi ni kam ko wajen bikin ban leka ba Mommy ce ma taje. Ina gida da yamma Malamin dake koya min karatu yazo ya kara min, lokacin Mommy ta dawo muka shiga kicin muka girka Jollof macaroni da fried chicken, muna girkin nake tambayarta Mama Sauda da yake kwana biyu ta sha rashin lafiya don haka suka maidata kauyen su tace ai taji sauki tuni, Daddy ne yace tayi zamanta a can kawai, na gyada kai.
Ni kadai ce a cikin falon lokacin da Anty Shafa ta dawo, na mata sannu da zuwa tace "tare muke da Harith wai yunwa yake ji, Allah sa akwai abincin?" na kalli dinning nace "akwai, sai dai ban tunanin zai ishe ku ku biyu" tace "nooo, ni nace abinci a gida, shine wai ba zai ci abincin biki ba, he can be picky about foods sometimes" na tabe baki nace shi ya sani ai. Anty tayi murmushi tare da juyawa don mishi iso ni kuma na leka dakin Mommy na fada mata. Ina dawowa falon yana zaune a daya daga cikin kujerun falon, Mukhlis yana cinyar shi, yaron yana ganina ya sauka daga kan cinyar shi ya rugo ya rungume ni, na tare shi ina dariya nace "mun shirya yanzu kenan?" Anty tace dama shi ai kwana daya ake Sabo dashi. Saboda idon Anty ne yasa na kalli sashen da Harith yake, "sannu" kawai nace, ban tsaya jiran amsawar shi ba na wuce dinning nayi serving dinshi abincin a plate na kai gaban shi na ajiye, kan kujera na koma na zauna na ja Mukhlis jikina ina jan shi da hira. Ya kalleni yace 'enmata baki bani ruwa ba" sai dana kalleshi kafin na tashi kicin naje na dauko ruwa mai sanyi a fridge na kawo na ajiye mishi, yace "sorry! Bana shan ruwa mai sanyi" na ciza lebe tare da dauke goran ruwan na je na canzo mishi da mara sanyi na kai mishi ya sake kallona yace "Baku da lemu ne haka kamar fanta ko peach?" zuwa lokacin nasan cewa he's doing it on purpose, ban ko kalleshi ba na koma na zauna abina, ya kalli Anty ya wani lankwashe murya, "Anty lemu nake so" tace Bari in dauko maka to, wanne kake so? Yayi saurin cewa "no no Anty, da girman ki ki dauko mun lemu haba! Bari yarinyar can ta dauko min mana" ban san lokacin da wani irin murmushin takaici ya subucewa fatar bakina ba, lallai ma Harith! Wai yarinya! Anty da bata kula da game din da yake bugawa ba ta tashi tsaye tace "Ummiey don Allah taimake shi da lemu, bari in rage kayan jikina" ta shige dakinta ni kuma naci gaba da wasana ni da Mukhlis, kallona yayi yace "baki ji abinda Sis tace ba? Ki bani lemu!" ban kalli sashen da yake ba nace "the kitchen door is over there...." na nuna mishi da yatsa ta, "zaka iya zuwa ka dauko da kanka, m not someone da u can be ordering around ni kuma in biye maka kamar wata er aikin ka" yayi wani irin smirking tare da dan shafa gefen wuyan shi, "seems like u r one Rude babe, I like it!" a xafafe na jefa mishi harara, "hey watch ur mouth!" ya tsuke baki yana jifana da wani irin kallo, "if not ki raba ni dashi?" tsaki kawai naja na kauda kaina gefe don na kula da neman magana ne kawai yake yi. Anty ta fito daga dakinta ta zauna a gefen Harith, ganin yadda nake jifan shi da harara ta dube shi cike da tuhuma tace "Me ka mata Harith?" ya kalleta kafin ya kalleni cikin dage gira, "Me na miki?" tashi kawai nayi na bar musu falon don na kula idan na zauna Harith zai iya sawa in zage shi a gaban Yayar shi abinda bana so kenan. Dakina na koma na fara chatting, a facebook na ga wani page da wani daga cikin friends dina yayi liking, *Hon. Ibrahim Galadanchi Official Fans Page* cikin mamaki na shiga page din, da gaske Abbu dinne. A Profile pic din da aka dora Abbu ne ya saka wata shadda Skye blue dinkin Abacha, shaddar ta matukar yi mishi kyau, kwarjinin shi da kyawun shi sun fito kamar ka kira shi a hoton ya amsa saboda yadda hoton ya dauku sosai. Na kura mishi ido na dan lokaci kafin na janye kaina, jikina yayi wani irin sanyi wanda ganin hoton Abbu da nayi yanzu ya haddasa min, sai kuma wani tunani daya darsu a raina, kenan Abbu har yanzu yana kan bakan shi akan fitowa siyasa? Ni dana ji shiru kwana biyu ban ji zancen ba nayi zaton ko ya hakura ne ashe bai hakura ba. Kenan idan har na aure shi sai dai in janye kiyayyar siyasa dana sawa raina, kenan zan zama matar dan siyasa? Murmushi nake yi kamar wata doluwa da nayi wannan tunanin, na sake janyo wayata nayi liking din page din. Ranar haka na bata Lokaci na wajen saving din pics din Abbu da suke cikin page din, sai wajen karfe sha biyu na kashe wayar na kwanta.
[truncated by WhatsApp]
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*28*
A hankali na juya na kalleshi, ya sake wanka yasa wani wandon jeans din Vogo da rigar CK mai V-neck, ya matso kusa dani ya tsaya gab dani yana kallon Muneer fuskar shi a cunkushe, sun dauki lokaci suna kallon-kallo shi da Muneer babu wanda yayi magana a cikin su, sai da naga shirun yayi yawa sannan na daga kafa na fara tafiya, na kalleshi nace "muje koh?" babu musu ya biyo bayana muka jera muka tafi, muna fara tafiyar ya tsaya cak tare da juyawa ya kalli Muneer da shima ya juyo yana kallonmu, yatsa ya nuna mishi cikin kashedi yace "and dude, stay out of my Fiancé side, if not....." ya juya ya cigaba da tafiya cikin takama har yana hadawa da wani bouncing, na bi bayan shi ina dan murmushin jin dadin shocked and horror expression din dana gani akan fuskar Muneer. Ramlah dake tsaye a gefe tana kallon dramar da muke bugawa ta kamo hannuna taja gefe tana tambayana wai da gaske na daina son Muneer? In ka kalli fuskarta a lokacin sai ta baka dariya, grinning take ear to ear kamar yaron da aka ba kyauta alewar bounty. Na sabule hannunta daga nawa nace mata "kinga jirana ake yi, anjima zamu yi magana" muka yi sallama na wuce na shiga motar Harith har ya tashe ta don haka ja kawai yayi muka wuce. Harara na jefa mishi, ya juyo ya kalleni "what??" nace "what was that for? That fiancé thing??" yayi rolling idanunshi, "baki gane bane? I was just trying to save you from him so that next time ba zai kara damun ki ba koda bana nan, by the way waye shi?" na danyi sighing softly kafin na kalleshi fuskana a dan hade don ya dauki maganar da zan mishi seriously nace "sanin waye Muneer ko rashin sa babu abinda zai tsinana maka don haka stay out of it, maganar fiancé kuma kada ka kara koda cikin wasa ne kuwa ko trying to help kamar yadda kace" ya kalleni yana murmushi cikin tsokana, "ko dai baki son inji cewa crush dinki ne yayi dumping dinki kuma ya dawo yace yana son ki?" kaina na kawar gefe naki kallonshi, naki jinin a tuna min da tarin yarinta da rashin hankalin da nayi akan Muneer. Amma Harith bai kyaleni ba cewa ya sake yi "tunda baya sonki me zai hana ki zo mu sasanta dake?" a fusace na kalleshi "stop messing with me fa Harith!!" ya tabe baki, "well, m not ai dama" nace "to ni nan da kake gani na I am taken ka gane?" ya juyo ya kura min ido na dan lokaci kafin ya maida hankalin shi ga tukin da yake yi yana chuckling, ban kula shi ba na janyo wayata ina latse-latse har muka isa gida. Yau ko godiya bai samu albarkacin jin ta ba, na fita daga motar har ina banging nayi cikin gida. Kai tsaye dakina na shige, nayi jifa da jakata akan gado kafin nabi bayanta nima na kwanta a rigingine ina tariyo abinda ya faru a makaranta ranar.
Vibrating din da wayata ya dauka daga cikin jakata ne ya dawo dani cikin hankalina, na danyi tsaki lokacin da nake laluben wayar, da kyar na iya bude idanuna da suka fara min nauyi saboda gajiya da barci na dora su akan fuskar wayar, sunan dana gani yana bouncing a jikin screen din wayar ne yasa naji zuciyata ta fara daka tsalle cikin wani irin farin ciki. Ya Allah! Yaushe rabona da inji muryar Abbu a rayuwa har na manta, Kun ganni nan kullum ina cikin page dinshi a facebook ina bibiyar rayuwar shi amma na kasa samun kwarin gwiwar kiran shi duk da cewa nayi kewar shi kuwa fiye da tsammanin mai karatu. Ganin kiran yana shirin katsewa yasa nayi saurin dagawa, sallama na mishi a nutse kuma cikin Karya murya, ya amsa cikin wannan muryar tashi cike da kasaita da wani irin huskiness daya kusa saka ni narkewa akan katifata saboda yadda naji wani electricity yana yawo a magudanar jini na. Daga can naji yana magana wadda tayi sanadiyar dawo dani duniyar Earth daga tafiyar da nayi zuwa Mars, cewa yayi "wato Nafeesah idan shekara zamu dauka ba tare da mun gaisa ba hakan bai dame ki ba koh? Ba kya neman mutane idan ba neman ki aka yi ba koh?" da sauri nace "Abbu ba haka bane ba fa!" yayi wata irin sassanyar dariya, "to ya ne Nafeesah?" na dan sosa wuyana tare da dan gyara muryata ina kokarin boye yadda dariyar Abbu ta kassara min gabbai, nace "Abbu muna karatu ne kuma dai bana so in kira ka ko kana aiki ko wani abu in takura ka" 'ina tsoron ka gaji dani, ina tsoron yin sabo da abinda zai zo yayi hurting dina daga baya" yace "that's not an excuse Nafeesah, when you feel like calling me just don't hesitate and call, zan amsa a duk inda nake no matter what m doing" na gyada kai kamar yana ganina nace "toh Abbu" ya sauya akalar hirar zuwa ta harkar karatuna, mun dauki lokaci muna hira kafin yace "Jiya muka dawo daga Beijing, nayo miki lodin tsarabar favorites chocolate crunch dinki, gabadaya na manta baki gidan ashe" nayi shiru kamar ba zanyi magana ba, wani irin dunkulallen abu ne naji ya makale min a kirji da kyar na iya danne shi na bude baki nace "Eyyah!! How I wish ina nan" yace "that's what m saying" nace "a ba Hafsy shi kawai, Allah ya nufa ba rabo na bane shi yasa" yace "um-uhm, abinda yake naki ne dole ki zaki ci shi Nafeesah. Pretty da kowa yaci nashi don haka kema dole naki zaki ce" na saki murmushi cikin jin dadin maganar shi, a hankali kuma cike da wani irin expectation nace "to ya za ayi yanzu?" shima yayi kasa da muryar shi har tafi tawa yin low, "ya za ayi? M thinking of coming to give it to you, Personally!" na karkada kunnena kamar ban ji sosai ba, sai dana dan yi hesitating kafin a hankali na maimaita "you?? Personally???!" sai dai can kasar zuciyata tsoro ne ya cikata, ina tsoron yace ba haka yace ba kila yace ba haka yake nufi ba.... Ya wanke min zargina ta hanyar cewa "yes, I'll come to you in baki tsarabar ki Nafeesah!!". Murnar dana ji ta cika min ciki ta ware a take lokacin da confusion ya dabaibaye ni, nace "amma why would you??" yace "because.... Because...... I.......!!" numfashi na ya dauke yayi sama yaki dawowa, na tabbata zuciyata ta buga sau dari cikin sakwannin da basu fi goma ba ina jiran inji karshen maganar shi, "..... Because I Can Of course Nafeesah!!" sai a lokacin numfashi na ya dawo kasa daga sama din da yayi, na fara yaki da zuciyata wajen ganin gudun da take yi marar adadi da numfashina da yake daidaituwa sun daidaita, a gefe guda wani irin disappointment ne ya lullube min zuciya. I'm such an idiot to think that Abbu zai fada min kalaman so! Yakamata in dawo daga duniyar Fantasy da Tunanin cewa wai Abbu zai so ni, Abbu yana da matar shi har da 'ya'ya abinsu and duk da cewa maimakon Happily, they are peacefully living together rather. Yace "besides Tu Me Manques!!" na dan yamutsa fuska, "Too mey Manqwe? Me kenan??" yayi er dariya, "just..... Sai anjima dai kawai. And please kiyi Kokari ki dinga kira na fa!" daga haka ya kashe wayar ya barni jiki a sanyaye kuma a sankame. Ajiyar zuciya na saki a hankali tare da saka kaina cikin tafukan hannuwana biyu ina jijjigawa, ji nayi xuciyata ta dauki wani irin zafi, na fara jefawa kaina tambayoyi da suka fara shirin tarwatsa min kwanya, Me ke damuna da Rayuwa ta ne? Me yasa nake son Mazan da basa sona ne? Me yasa zuciyata zata dinga jefa ni cikin damuwa ne a koda yaushe?? Bayan son Muneer da shi bashi ma da mata balle yaya, xuciyata tayi tsalle ta koma kan mutum mai iyali kamar Abbu, Abbu da yake Abokin Daddy na. Me zan fito in gayawa duniya? Anya Duniya ba zata zage ni ba kuwa?? Na dage kullum ina kara nutsa kaina cikin son kogin Abbu ba tare da nayi la'akari da halin da zan jefa kaina da iyayena a ciki ba..... Kafadata naji an dafa, an dago da sauri na kalli Anty Shafa wadda take zaune a gefen gado inda nake zaune, na riga nayi nisa a duniyar tunani ban ma san lokacin data shigo dakin ba.
Fuskarta dauke da damuwa tace min "lafiyan ki lau Nafeesah? Tun dazu nake magana a kanki amma ba kya jina" kai kawai na girgiza mata to ince mata me? 'Abokin Baba na nake so shi kuma baya so na?' nasan zagina kawai zata yi ko ta ce bani da hankali, don haka na bame bakina nayi shiru, it's better to deal with it on my own. Tace "you are lying Nafeesah! ga damuwa nan kwance akan fuskar ki ina gani, kar ki boye min komi kinji? Tell me, me ya faru?" kallonta nayi tare da sake girgiza mata kai ina jifanta da murmushin dani kaina nasan ko idanuna bai Kai ba balle xuciyata, nace "babu komi Anty, it's just a minor headache" ta kalleni cikin rashin yarda yayin da naci gaba da haske ta da murmushi kawai, sighing tayi tare da mikewa tsaye tace Mommynki ce take cigiyar ki dama shine nace bari in leko in gani ko lafiya? Na mike tsaye nace "bari inje in ganta lafiya na lau" Anty dai ta juya ta fita, na ajiye numfashi a hankali kafin na bi bayanta.
~Lots of Love and Hearts Ni Da Abokin Baba Na Fans 💕 💕
~Greetings to you #TeamAbbu....
[truncated by WhatsApp]
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*29*
Aunty Shafa tana ta shirye-shiryen komawa nan da kwana biyu don haka bata zama a gida, tana ta faman ziyarce-xiyarce da sallama gidan en uwa da abokan arziki. Ranar juma'ah karfe sha biyu muka gama lectures, muna fitowa ni da Ramlah daga lecture hall din na hango Harith jingine da motar shi hannunshi rike da lemun team yana sha, yana ganin fitowar mu ya dago mana hannu. Ramlah ta kalleshi ta kalleni tace "wai meke tsakanin ki da Harith ne?" na girgiza kai, "to wa ya sani Ramlah? Nima kin ganni nan ban sani ba wlh" ta tabe baki, "to Allah ya kyauta!" nace "ameeeeen". Daga nan muka yi sallama. Tun kafin in karasa ya bude min kofar motar, na shiga na zauna ya maida ya rufe. Yana shiga motar na fara jefa mishi korafi ko bari ya tashi motar ban yi ba, "Wai Harith ba nace na yafe zuwa dauka na da kake yi ba?" sai daya tashi motar muka fara tafiya kafin yace "I was just in the neighborhood ne, nayi dropping Sister gidan Amarya Murja ne, shine nace bari in biyo in dauke ki tunda nasan kin gama lectures dinki" nace "ni ban ga kana shirin komawa ba" ya juyo ya kalleni yana murmushi, "why?? Saboda kin gaji da ganina? To babu inda zan koma, na gama karatuna ai" na juya na kalleshi sosai, "woah! Da gaske?" yayi murmushi more like a grinning, "nayi kankanta koh?" kaina na gyada mishi ina kara kare mishi kallo, dariya ya saka har yana dukan sitiyari. Yayi parking a kofar gidanmu, na dauki handbag dina na rataya a kafada nace thanks fa! Ya gyada kai, "Anytime!". Kallona ya tsaya yana yi, har na saka kafa ta daya waje na juyo ina kallonshi, "meye kake kallona?" murmushi yayi ya kalleni fuskarshi na nuna yana shirin yin serious magana ne, yace "Nafeesah! How about We come together with a plan and help ourselves??" na kalleshi cike da mamaki, "mu taimaki juna? Me kake nufi??" ya daga kafada kamar maganar da zai yi ba mai amfani bace, "you see, there's this girl that I like....." yayi shiru yana kallona, ban ji mamaki ba haka babu shock din da naji saboda maganar shi, to ma akan me zan ji mamaki? Hankalina na mayar kan shi gabadaya ina sauraron shi, ya cigaba "she likes me too, sai dai bata son muyi aure nan kusa. Tana karatu a Turkish ne a Abuja and sai nan da shekara biyu zata gama, ni kuma na kosa... U know....!!" ya daga min gira ni kuma na Harare shi, ya kauda kai. Gyaran murya nayi a hankali bayan na gama digesting maganganun shi, nace "to daka gaya min mai kake tunanin zan yi ne??" ya juyo yana fuskanta ta sosai, "I want us to just play a game ta yadda zamu samu wadanda muke so Cikin sauki." nima na kara gyara zamana, "so??" yace "we will pretend to be lovers infront of them, I mean idan muka yi haka kishin mu zai sa su dawo kan hanya daga kaucewar da suka yi, zamu fara da Muneer ne ko menene? Tunda Ikhram 'Cara Mia' sai nan da two months zata zo gida" na hade fuska sosai, take naji raina ya wani baci, a xafafe na harare shi nace "idan har saboda Muneer kake zaton I'll be your partner in this game then you are wrong Harith, Muneer has become 'a past' ya daina existing a duniyata!" ya sadda kanshi kasa embarrassingly, nace "But we can play it with someone, not Muneer dai" ya dago yana kallona fuskarshi dauke da murmushi, "Really Nafeesah? Oh you're really going to save my life, thank you! But waye wanda zamu bugawa wasan?" nayi rolling idanuna, "just..... By the way meye ma'anar Cara Mia din da kace?" yayi murmushi sosai, "it means My Darling in Russia" na tabe baki nace "wani fi'ili!! Ni kam bari in shiga gida toh!" muka bude motar a tare muka fita yana cewa bari ya shiga ya gaida Mommy.
A hankali rayuwa tana tafiya tana juyawa, cikin Ikon Allah minti yake shudewa ya zama awowi, awowi su koma raneku, raneku su koma satika kamar yanda satika suke juyewa su koma Watanni. Kimanin watanni biyu suka zo suka shude, ni da Harith mun yi developing wani irin shakuwa a tsakaninmu, da yawan mutane suna cewa soyayya ce a tsakaninmu ciki har da su Mommy da Ramlah, mu kadai dai muka san menene Ainihin Akalar mu da juna.
A matukar gajiye muka shiga gidan ni da Daddy a safiyar ranar Sunday kenan muna ajiye numfashi daya bayan daya, Gym muka je wanda yake a cikin unguwar mu kamar yadda muke yi a cikin weekends. Muna shiga falon kicin na wuce na dauko mana ruwa mara sanyi na mikawa Daddy daya, nima na fara shan dayan. Sai da muka dan huta kafin muka wuce dakinmu, ruwa na watsa a jikina na saka kaya kawai na fita falo. Su Mommy har sun fara breakfast don haka nayi joining dinsu, a nutse muke cin abincin, ina jin Mommy tana gayawa Daddy bikin diyar wata Kawarta da za a fara cikin satin, tunda suka fara maganar na sha jinin jikina, a gaggauce na fara tura abincin ina so in tashi in bar musu wajen. Kamar daga sama naji Mommy ta jefo min tambayar da nake gudun tayi, "Ummiey Ke kam yaushe zaki gabatar da naki Mijin ne?" sau biyu kenan tana min maganar turo da wanda muke soyayya wanda nasan Harith take nufi, na turo baki tare da kara cusa fried plantain a cikin bakina, Mommy ta kalli Daddy tace "Habibty kana jin mu fa!" Daddy yayi dariya yace "ina jin ku, kina bukatar bakina ne?" Mommy cike da jin haushi tace "Allah Habibty hakan bai dace ba fa! Yarinya kamar Nafeesah saboda Allah ace har yanzu tana gabanmu babu zancen aure, ina mata zancen ta fitar da miji kuma wai ka wani dinga wani tambaya na ko bakin ka nake bukatar ji?? Anya Habibty kana ma so Nafeesah tayi aure ma kuwa?" Daddy ya kalleta a hankali, duk da cewa maganar Mommy ta taba ranshi amma bai nuna hakan ba, he was very calm. Yace "kema kin san ba abunda nake nufi ba kenan Habibty, naga shi auren nan nufin Allah ne. Duk iya kokarinmu da tursasawar mu a gare ta idan Allah bai nufa ba babu yadda zamu yi. Nima ina son in ga auren Uwata saboda nasan Martaba da Mutunci 'Ya Mace suna gidan auren ta ba gidan Iyayen ta ba sai dai kin san bana so in tursasawa Uwata ko kadan. Kema din you are just desperate ne, amma duka-duka nawa Nafeesahr take? She's just Twenty Two Habibty!!" Mommy ta dafe kanta, "Ya Allah meke damun ku ne Kun kasa gane abinda nake nufi?" Daddy ya dafa hannunta cikin sanyin murya yace "mun fahimta Habibty, sai dai muma ki fahimce mu mana. Na fada miki Auren nan...." tayi saurin cewa "naji, naji Habibty ba sai ka maimaita ba!" yayi murmushi, "ki dinga mata addu'ah kawai Habibty, amma tursasawar ki ba shine zai sa ko ya hana ba, only your prayers will" ta gyada kai gami da yin sighing cikin saddakarwa, "To Allah ya zaba mafi Alkhairi!" yace ameeen ko Ke fa Habibty? Na saki ajiyar zuciya a sace, muka ci gaba da cin abincin mu. Can kuma Mommy ta sake dagowa ta kalli sashin da nake, "amma meke tsakaninku ke da Harith ne?" na kalleta, "Mommy, sau dubu nawa kike so in gaya miki babu komi?" Mommy tace "to ku ne na rasa gane inda kuka sa gaba" ni dai na samu na lallaba na bar musu teburin kafin wata maganar ta sake bullowa. Wayata na cire a jikin Caji na shiga cikin whatsapp, dp din Abbu na daga, ya canza shi daga wani hoton shi daya dauka cikin suits bakake ya maida shi zuwa wanda suka dauka shi da 'ya'yan shi kamar a wani restaurant ne ma, na kura musu idanu ina kallo ina murmushi, precious memories dinmu dasu suka dabaibaye ni, take naji wasu irin kewar su ta cika min ciki, har na latso lambar shi zan buga sai kuma na fasa, na sake latsawa na fasa, a tunanina idan Abbu shi yana namiji ya iya kauda kanshi daga gareni why not ni mace? Tun ranar da muka yi waya dashi bamu sake wata wayar ba sai kimanin sati biyu da suka wuce, shima tambayana yayi wai ko ina da muradin zuwa BUK inyi D.E ni kuma nace mishi A'ah, daga ranar bamu sake waya ba sai dai muna exchanging din text messages dashi. A hankali nayi tsaki tare da ajiye wayar. Littafan makarantana na dauko na fara karatu ko na samu in daina tunanin Abbu. Gabadaya lamarin shi ya fara daure min rai, idan ya kira ni a waya ko ya min text, kulawar dake cikinsu sai su sa inyi zaton so ne yasa hakan, amma yanayin yadda mu'amalar mu take ko kadan bata yi mun kama da wani abu mai kama da so ba. Yatsun hannuna na nutsa a cikin gashina ina jan tsaki ganin har lokacin dai tunanin Abbu ne a cikin raina. Tashi nayi tsam na fara canza tsarin dakina gabadaya bayan na cika dakin da sautin music har sai da Mommy ta leko ta min magana sannan na rage.
Ranar Laraba a gajiye muka baro makaranta saboda Defense din IT da muka yi, da kyar na iya kai kaina bakin gate saboda gajiya inda nayi shatar tricycle zuwa gida, Harith baya Kaduna kwana biyu kenan, yaje New York wajen hado takardun shi saboda zai fara aiki. Na tura kofar gate din gidan na shiga, yamma tayi likis lokacin. Malam Idi maigadin gidanmu yana zaune a kan dan benci yana sauraron radio, na gaida shi ya amsa da fara'ar shi gami da min sannu da zuwa kafin na wuce falo. Ina shiga sallamar dana fara yi ta kakare a makogorona sakamakon Halittar da nayi ido hudu da ita..........
[truncated by WhatsApp]
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*31*
*So I made a mistake in the previous Chapter... TOI ET MOI TOU POUJOURS means 'You and Me Forever' in French. TU ME MANQUES ne I Miss You in French, Hope you guys wouldn't mind??*
☆☆☆☆☆
Abinci nake ci amma gabadaya hankalina baya kan abincin na dai san kawai ina kwaso abinci da spoon ina saka shi a cikin bakina, tunanina ya tafi ga yadda Mommy take acting weird tun zuwan Abbu, no tun zuwan Hafsy ma. Bayan su Abbu sun tafi jiya, mun gama dinner kenan na shiga daki Mommy ta biyo bayana, sam babu alamun wasa a fuskarta ta kalleni, "Ummiey me ke tsakanin ku da Baban Hafsat?" na kalleta da sauri kuma cike da mamaki, tambaya ce mai sauki, haka kuma amsar ta ba mai wahala bace, amma me yasa naji kamar ba'a taba tambayana tambaya mai wahala irin wannan ba? Saboda ni a karan kaina ban san me ke tsakanin mu ba. Kai na girgiza mata, "Mommy me kika gani ne?" ta Harare ni, "Ummiey ba cewa nayi ki tambaye ni ba, amsa nake bukatar ji; Me Ke Tsakanin Ku Ke Da Baban Hafsat?" na danyi shrugging kafadata ina kokarin nuna babu komi, "me ke tsakanin mu kuwa Mommy? He's just Daddy's Friend, and I stayed with them for a while I think that's all!" tace "That's all?!" na jinjina mata kai cikin tabbatarwa, "yes!" tayi shiru tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya, "ko ma dai Menene Ummiey, Ina fata zaki tsaya a iya inda Allah ya ajiye ki, and alakarku ta tsaya a haka Nafeesah, No more.... Bana son wani magana ya fita daga baya kina jina??" kallonta nake cike da mamaki, me ke damun Mom ne haka yau? Duk da hakan ban fasa daga mata kai ba, sai lokacin naga tayi murmushi. "good! Hurry up and go to bed then" nan ma Kai na sake gyada mata, "sure Mom, good night" tayi murmushi ta juya ta bar dakin tare da ja min kofa. Sosai maganganun Mom suka tsaya min a rai, ranar haka na kwanta ina nanata maganar ta, 'In tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ni?? Kada wata magana ta sake fita bayan alakar mu ta yanzu? Tana nufin kenan ba zata amshi Abbu a matsayin miji na ba? 'Miji??' naji na sake maimaita kalmar., wa yace Abbu zai zama mijina? Ni kadai nake imagining komi a cikin raina ba tare da tunanin shi Abbu din me yake tunani ba. Ni kadai nake tunanika na na manta da cin amanar da nake shirin yi, to cin amana mana! Na zauna lafiya qalau da iyalan Abbu cikin mutunci da girmamawa, daga karshe kuma kawai sai aji na aure mai gida? Anya na kyautawa kaina dasu kuwa? Me zan ce musu to? Me zasu daukeni, maciya Amana ko me? Su Qaseem.......... Shit!!! Me zasu dauke ni yanzu? Suddenly naji wata irin kunyar kaina ta kama ni, I wasn't thinking straight and smart. Ni da Abbu belongs to different worlds, I think it's time for me to let him go., let my dreams scattered just like how I did with my first love; Muneer!! Zuciyata tayi zafi sosai, m really an unlucky being!! Me yasa ban taba samun nasara akan soyayya ba a rayuwata? I mean me na rasa? I am a very beautiful and attractive young lady in my twenties, ina da kyau ina da diri ina da duk abinda namiji yake bukata a jikin mace but why?? Why???.......
Ramlah ta dawo da hankalina cikin restaurant din ta hanyar jijjiga ni, "hey babe!! Come back to your senses!!" na zabura ina kallonta a tsorace kafin in Harare ta, "What?!" na fada almost shouting, tace "Ke zan tambaya, you were deep in a thought and you suddenly became teary, me ke faruwa dake ne yau?" na kai yatsa na dan taba idanuna, da gaske kuwa I was about to cry ga ruwan hawaye nan ya fara taruwa a idanuna. Ta rungume hannayenta a kirji tana kallona cike da tuhuma, na sauke kaina kasa kawai ina wasa da cokalina a cikin plate, I wasn't ready to discuss the matter with anyone a lokacin, I wanted to dealt with anything on my own don haka na share Ramlah kamar ban san abinda take nufi da hakan ba har sai data kai ga yin magana, "ba zaki magantu bane har sai na matse bakin ki?" na kalleta, "Ramlah am sorry ok? When I'm really, zamu yi maganar please!!" na fada pleadingly don nasan halinta zata iya takura ni, hakan kuwa daidai yake da saka kuka na a cikin restaurant din makarantar mu. Tace "da gaske?" na gyada mata kai, tace "ok, kar ya dade fa kin san bana son jira koh?" na sake gyada mata kai. Na dauki lemun exotic na pineapple na kai bakina, kamar ruwa haka na dinga zugar shi sai kwalin kawai na ajiye kasa. A tare muka mike muka fita daga restaurant din, muna fita naji Ramlah tana xunguri na a bayana, na harareta, baki ta tabe cikin gulma ta rada min "mutumin ki is coming" na kalli inda ta nuna min da idanunta, Muneer ne tafe shi da abokanan shi suna tahowa inda muke da alamu restaurant din zasu zo. Naji ana zancen auren shi da aka daura last week, personally ya turo min Invitation Card na bikin nashi amma a take na aika aka maida mishi Ita don ban ga abinda zan je inyi a wajen bikin ba. Tsaki naja na fara tafiya abina, Ramlah ta biyo bayana, muka yi clashing dasu amma Muneer ko glancing at our side bai yi ba. Na kara jan tsaki a raina nace "banza dan akuya!" satika uku da suka wuce he was still following me around like crazy yana begging dina akan in bashi second chance shine yanzu daga yin aure Sati daya yana share ni irin yaji dadin Amarya dinnan, na kara jan tsaki. As if I give a damn! Kamata yayi inji da damuwata ba wai ta wani Muneer ba. Hostel muka wuce ni da Ramlah saboda bamu da lectures ranar, next week zamu fara exams already mun yi covering lectures dinmu. Muna kan gadonta muna solving din wata problem a Calculus wayar ta tayi kara ta daga, ta dauki wayar ta kalli caller ID din, "Ni'ima ce" ta daga kiran tare da sakata a hands-free, "Guess what guys??" muryar Ni'imah ta doki kunnenmu cikin farinciki, muka hada baki wajen cewa "ya ne? Bamu mu sha please!" tace "umh.... Dama......" ta fara kauce kauce, Ramlah taja tsaki, "malama aiki muke yi idan ba zaki fada ba ki kashe wayar kawai" sai data gama kauce-kaucenta sannan tace "aure aka sa mana.... Nan da one month!!" "WHAT??!" muka fada cikin karaji in Unison.
"What the f**k! Wannan ai rashin mutunci ne Ni'imah" inji Ramlah tana hararar wayar kamar Ni'imar tana gabanta ne, nima nace "Lallai mu da aka raina ne sai yanzu ake fada mana, ba zan zo ba don ma kiji" Ramlah ma ta cafe nan ma muka hau korafe-korafe har sai da muka rasa abin cewa sannan muka yi shiru, Ni'imah dai saurarenmu kawai take yi, ina jiyo dariyar Sa'adiya daga background din wayar. Tace "duka-duka jiya ne aka yi abin fa!" muka yi kus, ta cigaba, "muma bamu yi zaton abun will be so soon ba kawai jin su muka yi Kun gane? Now na isar da sakon da zan isar shikenan, Kun dai san you guys are needed one week before a fara bikin ko?" muka yi dariya ni da Ramlah, "yeah of course, ai dole ne. Thank God we're finishing our exams nan da sati biyu" muka yi sallama dasu, littafin da muke karantawa muka maida gefe muka fara hirar yadda zamu gudanar da bikin, wannan hirar ita ta dauke min tunanina gabadaya akan maganar Mom da sauran su.
*****
Daddy ya kalleni, "yanzu Har Sati daya kawai saboda biki Uwata?" na turo baki gaba, "haba Daddy, su Ni'imah ne fa, kuma lokacin muna free tunda mun gama exams dinmu fa!" ya rausayar da kai, "ai shikenan! Allah ya kaimu" nayi tsalle akan kujera daga zaunen da nake ina clapping hannu, "nagode Daddy! That's why you're always the best!" na mishi thumbs up da duka hannuwana, yayi dariya. Naci gaba da duba littafin hannuna shi kuma ya cigaba da kallon tashar Sports. Can na tambayeshi game da DE form din da yace zai sa a cika min, yace "ni na ma manta wallahi. Bari zan sake yiwa Ibrahim Magana inji yadda ake ciki" nace "Daddy Abbu kuma? Me yasa shi? Ni da ABU nake so in cike?" yace "ba kya son zuwa BUK din ne, me yasa?" na turo baki na, "ni nafi so ina kusa daku Daddy yadda kullum ba zan sha wahalar ganin ku ba!" yayi dariya yace "Uwata kenan! To in kika yi aure kuma fa? Kin san dai dole ki bar gidan nan koh?" na sake turo wani bakin, Mommy ta shigo dakin hannunta dauke da plate wanda aka yanka fruits a ciki. Ta kalleni kafin ta maida kallonta ga Daddy, "Habibty ina fata ba gulma ta kuke yi ba koh?" Daddy yace "mun isa! Diyar ki ce take zancen bata so ta rabu damu" Mommy ta ajiye plate din a tsakiyar dakin duk muka sauka kan carpet tace "Rabuwa kuwa ai ya zama dole tunda dai ke diya mace ce kuma Aure zaki yi" 'Ai fa an tabowa Mommy inda yake mata kaikayi' na fada a cikin raina, kwana biyun nan dama Mommy kamar mai jira, da an danyi magana zata hau zancen aure da waye da waye. Sai da muka cinye fruits din tas na dauke plate din tare da musu sai da safe, na kai plate din kicin kafin na wuce dakina nayi shirin kwanciya barci. Na budo hoton Abbu a cikin gallery dina ina kallo kamar yadda ya zama Al'adar rayuwata kowane dare, na janye idanuna daga kan hoton nashi na maida su kan frame din daya bani. Ban san meye dalilin da yasa ya bani frame din ba, ban san me yasa nake jin wani irin warmness da calmness a tare dani a duk lokacin dana kalli frame din ba. Koma dai menene na yanke shawarar janye Idanuna da Zuciyata daga kan Abbu. We didn't Deserve Each Other.
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*32*
Harith yayi parking motar shi a kofar gidanmu, da yake ya dawo tun last week. Yau tsokana muka fita, gidan su Ikram budurwar shi muka je da yake itama tazo hutu. Har kofar gidansu muka je aka mata sallama ta fito da saurinta ita ala dole masoyinta yazo, yadda tayi turus ganina akan motar shi ina wasa da keys din motar shi sai daya kusa bata mana budget, kaina na kawar gefe ina boye dariyar data kama ni. Haka ta daure ta karaso wajenmu muka gaisa Harith ya gabatar dani a matsayin sister dinshi, suka dan fara hira da ita, mintuna biyar basu cika ba na kalli Harith ina hamma nace "Hari, mu tafi gida!" da sauri ya mata sallama muka shige mota muka tafi, tana tsaye a inda take har muka bar layin. Dariyar abun muke yi har muka shiga gida kamar wasu sabbin mahaukata. Idanuna suka tsaya cak akan Abbu dake zaune akan fararen kujeru inda Daddy ya saba zama yana shan iska ko karatun jarida mostly on weekends. Kamar koda yaushe, babu abinda ya canza daga bugun da zuciyata take a duk lokacin dana ganshi, rawar da kafafuna suke da wani irin doki daya mamaye ni, makaman yakin dana tanada domin yakar zuciyar dake kayata min Abbu naji sun min nauyin dauka. Idanunshi fes akan mu suke, na kalli Harith a nutse nace "ina xuwa" ya gyada min kai. A hankali na fara tafiya zuwa inda yake zaune, kafafuna rawa suke yi saboda yadda nake jin idanun shi masu kaifi a kaina, da taimakon Allah dai na karasa inda yake. Na dan duka a hankali nace "Abbu barka da yamma" ya gyada kai, "barka dai Nafeesah. Daga ina haka?" na rasa abinda zan ce mishi saboda ba makaranta naje ba saboda ranar bamu yi exams ba, nace "mun dan fita ne" ya kalli kofar da Harith ya bi ya shiga falo ya kara kallona fuskar shi dauke da wani irin kallo daya kada min sassan jiki, "and who is he??" nima na kalli kofar, nasan da Harith yake, nace "Harith...." na rasa abin cewa saboda yadda idanunshi suke zagaye fuskata gabadaya sun dauke min kuzari, ganin nayi shiru babu amsa ya gyada kai, "well dama naso ganin Daddyn ki ne shi yasa na zauna jiran shi nayi zaton zai dawo da wuri don na biya ta ofishin shi baya nan, but bana tunanin zan cigaba da jira kam. Zan kira shi kawai" ya tashi yana gyara wuyan rigar shaddar daya saka, ya kalleni har zuwa lokacin normal kallonshi bai dawo ba, yace "Kano na nufa yanxu in shaa Allah. Nan da sati daya zaki zo bikin su Ni'imah koh?" na gyada mishi kaina a hankali, yace "good! Sai mun hadu kenan" ya fara tattaki xuwa inda ya ajiye motar shi, na samu kaina da take mishi baya har gaban motar. Ya saka makulli ya bude motar ya shiga ya kunna, sai lokacin ya juyo ya kalleni yana dan murmushi, Ya Allah! Da ba dan motar shi dana rike da hannuna ba da babu abinda zai hana ni faduwa a lokacin, na rasa irin effect din da Abbu yake dashi a tare dani. Yace "so??" nayi saurin kallonshi saboda gabadaya hankalina ya dauke daga gare shi, nayi saurin daidaita natsuwata nace "Allah ya sauke ka lafiya Abbu, a gaida su Anty Mubeenah da Hafsy" yayi murmushi wannan karon genuinely wanda tunda yaxo sai lokacin naga murmushin shi irin haka, yace "Ameen Nafeesah, zasu ji in shaa Allah!" yaja motar shi ya tafi nima na wuce cikin gida, a bakin kofa muka ci karo da Harith zai fito, yana gani na yace "sai anjima koh babe?" na harare shi ya danyi dariya saboda yasan na tsani sunan, ya wuce abinshi ni kuma na shige gida. Sai dana biya ta dakin Mommy na gaya mata na dawo, ta kalleni fuskarta babu yabo babu fallasa, "kin ga Baban Hafsat a waje kuwa?" gabana ya dan fadi, Allah dai yasa ba wani fadan zan sha ba. Nace "ehh, ya ma tafi ai" Mommy ta kalleni cikin tuhuma, na sadda kaina kasa ina wasa da jakar hannuna, tace "na tambaye ki abinda ke tsakaninku kin ce babu komi, yanzu kuma me ya kawo shi wajen ki?" na kalleta da sauri, "ni fa ba wajena yazo ba wajen Daddy yazo, ya gaji da jiran dawowar shi ne shi yasa ya tafi" tace "haka ya gaya miki?" nace "ehhh, ba haka bane?" ta dan harare ni na kauda kaina, tace "shi kenan je ki" kamar jira nake yi dama, da sauri na bar mata dakin na wuce nawa ina ajiye numfashi a hankali. Duk yadda Tunanin Abinda Mommy take nufi da Tunanin makomar rayuwata da Abbu suka so dabaibaye ni haka naki basu dama, na dage da karatun exams sosai. Cikin ikon Allah cikin sati daya muka gama exams dinmu, cikin lokacin mun kara zuwa gidan su Ikram sau biyu. Wato idan na tuno diramar da muka buga a zuwanmu na karshe gidansu dariyar dake kama ni koh??
Sai ana washegari a fara harkokin bikin su Ni'imah sannan na tafi Kano. Gidan Anty Ameenah muka sauka directly saboda a can amaren suke zaman biki, su Hafsy suka fito suka min oyoyo yaran sun wani kara girma, ban taba sanin nayi kewar su sosai ba sai dana dora idanuna a kansu. Qaseem ne ya dauki jakar hannuna na kama hannun Hafsy Abdullahi ya biyo mu a baya muka shiga gidan. Tarbar dana samu daga Anty Ameenah ta bani mamaki, har uwar dakinta ta kaini inda na samu su Anty Raliya da wasu abokan su, na gaida su suka amsa Anty Raliya na min korafin na tafi babu sallama ni dai nawa bada hakuri ne kawai don nasan cewa m at fault. Na shiga bandakin ta na watsa ruwa na fito nayi sallar Laasar, kafin in gama har an shirya min abinci a tsakiyar dakin ina gamawa na zauna na fara ci. Sai dana gama sannan aka kaini inda amaren suke. Dakine guda aka ware musu inda ake musu gyaran jiki, ina shiga hayaniya ta barke kamar me. Sai a lokacin aka min kitso da kunshi Allah ma yasa na je wankin kai a Kaduna.
Washegari aka yi kamu a Triple Crown Reception Masha Allah wajen ya tsaru iya tsaruwa, mata ne zallah a wajen mun yi shiga ta gargajiya haka ma kide-kiden da aka sa na gargajiya ne zallah. A wajen kamun ne muka hadu da Anty Mubeenah, tana nan yadda take babu abinda ya ragu a yanda take. Kibar nan tata marar fasali ta karu, table daya suka ja ita da kanwar ta Anty Shakira, ta hakimce tana ta hure-huren hanci yayin da su Anty Ameenah suke ta kai kawo suna kokarin entertaining din baki. Na ja hannun Ramlah muka nufi teburin da suke zaune, tun kafin mu karasa nake yago hakora ina murmushi har muka gaban su na musu sallama tare da gaida su, I didn't expected her to look at me with a smile on her face, tace "Nafeesah sai a haka ake ganin ku ko?" ko babu komi naji dadin yadda tayi, nayi zaton wulakanci zan sha a wajenta kam. Nayi er dariya kawai na zauna a gefen Anty Shakira ina kara gaishe su, nan muka dan yi hirar yaushe gamo kafin na musu sallama na tashi muka cigaba da gudanar da sha'anin bikin mu. Bayan mun koma gida da dare na shiga dakin Anty Ameenah zan dauko kayan barcina da yake tunda naxo kayana suna dakinta, ina yin sallama muryar Abbu ta amsa min, sai dana yi kamar in koma da baya don dai kawai nasan yaji murya ta ne shi yasa. Na shiga cikin falon a hankali kaina a kasa kamar tsohuwar munafuka, daga can gefen shi na durkusa nace "Abbu sannu da zuwa!" muryar shi tayi kasa sosai akwai alamun gajiya sosai a tattare dashi, yace "yauwa Nafeesah, bani ruwa please!" nace toh. Na fita zuwa kicin naje na dauko mishi ruwa mai dan sanyi, har zan fito na kula da farfesun kayan cikin dake cikin warmer, na koma na dauko plate na zuba a ciki na cicciba. Na dire kayan a gaban shi, ya kalleni ya Kalli abincin, fuskar shi ta nuna alamun relaxing and amusement. Ya kalleni cikin lumsassun idanunshi, "Nafeesah!!" ya kira sunana cikin muryar rada, na kalleshi a hankali ba tare dana amsa ba, it's not that ban amsa ba, nayi niyar amsawa sai dai muryata bata fita ne balle har yaji, yace "Nafeesah!! Zaki iya....." maganar shi ta katse lokacin da Anty Ameenah ta shigo falon, na kalleshi da sauri cikin mamakin dalilin tsayawar maganar shi. Anty Ameenah ta zauna a gefen shi cike da tsokana tace "ya aka yi Ibu??" na sadda kaina kasa ina kokarin boye dariyar data taso min da jin sunan da Anty Ameenah ta kira shi dashi, ya dan ja tsaki kawai ya fara cin abinda na ajiye mishi. Ganin haka na tashi na shiga dakin na dauko kayana na fito na musu sai da safe na fita, idanun su suna kaina har na fita. Na kai gadon bayana akan katifar da aka shimfida mana a tsakiyar dakin na kwanta, tunanina a lokacin me Abbu yaso fada min dazu??
Washegari aka yi Walimah anan farfajiyar gidan Anty Ameenah. Washegari kuma aka daura aure da dare muka tafi wajen dinner. Kamar da wasa ina juyawa daga seat din da nake zaune na hango Harith da Ikram a zaune, na zaro idanuna ina kallonsu daidai lokacin da shima ya juyo, na mishi alama da hannuna alamun "ya aka yi haka?" ya danyi shrugging kafadar shi. Wayata tayi kara a daidai lokacin da sauri na daga naga Ramlah ce take kira, na daga da sauri, tace in same ta a parking lot Fiancé dinta zai tafi mu gaisa. Nayi excusing kaina wajen wasu daga cikin abokan su Niimah da muke zaune a seat daya dasu na fita. A can parking lot na same su, muka gaisa da Ayan saurayin Ramlah, (Ban fa ce na Ummu Maryam da Ihsan ba... Don kar kusa Husna tayi daidai da naman jikina, tamm). Anan na baro su su gama sallamar su. A hankali nake tafiya saboda heel din dake kafa ta, gashi dinkin skirt din dake jikina ya dan matse ni somehow don haka bana iya daga kafata sosai inyi tafiya. Kawai ji nayi an ja hannuna anyi gefe dani, na daga baki tun karfina zan kwala ihu, aka sa wani tattausan hannu akan bakin nawa ta yadda babu yadda za ayi ihun da nayi niyar yi ya fita......
0 comments:
Post a Comment