*11*
"Kai ma haka."
A hankali ya zauna bakin gadon ya aje ledojin hannun shi, kallonta ya yi ya d'anyi shiru, dama dai fuskarta a rufe take, dan haka ita ma ta yi shiru, kowa da abin da yake sak'awa a ran shi, kusan minti sha biyar su ka d'auka a haka kafin ya sake kallonta ya d'anyi gyaran murya yace "Ko za ki iya bud'e fuskar ki."
Shiru ta yi kamar ba ta ji ba kuma bata bud'e ba, numfashi ya sauke cike da nuna kasala ya zuro hannayenshi ya yaye mayafin, fad'uwar gabanta ne ya nunku, shi kuma ya kafe fuskarta da babu ko d'igon kwalli da ido, sai dai lumshe ido ya yi saboda matsowar da ya yi kusanta k'amshin turaruka ne suka bigi hancin shi, ajiyar zuciya ya sauke yace "Ya kamata muje mu yi alwala ko?"
Ba tare da tace komai ba ta fito da k'afafun ta daga tank'warewar da ta mu su ta sauka daga kan gadon, bin bayanta ya yi su ka samu buta su ka yi alwala su ka dawo, hijab ta saka ta shinfid'a sallaya ya shiga gaba ya kabbara sallah, raka'a biyu su ka yi su ka sallame, juyowa ya yi ya na fuskantarta ya zuro hannunshi zai dafa kanta dan yin addu'a, zabura ta yi taja baya sosai, da sauri ya janye hannun shi yace "Lafiya?"
Girgiza kai ta yi alamar ba komai, shima girgiza kan ya yi yace "Kar ki damu, ba abinda zan miki, addu'a zan mana."
Gyara zamanta ta yi shi kuma ya rik'e kanta ya yi addu'a kamar haka _"Allahuma inni as'aluka khairuha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi."_ Sakin ta ya yi ya juya ya janyo ledar gabanshi ya bud'e, har zata tashi yace "Zauna."
Yanda ta ji muryar shi ya sa ta zauna ba musu, gasassar kazar ya d'auka yakalle ta yace "Bismillah, ki ci."
Murya na rawa tace "Na k'oshi."
Da mamaki ya kalle ta yace "Kamar ya kin k'oshi? Nasan ki na jin yunwa, ga cikin ki nan ma ya nuna."
Da sauri ta k'ara k'udundune cikinta cikin hijabi ta na kallon k'asa, juyin duniya Usman ya yi amma tace ba ta cita k'oshi, abu d'aya ya fahimta shine tsoron shi take, sai dai tsoron me bai sani ba, saboda yanda had'uwar su ta kasance ne ko kuma tunanin zai mata wani abu a daren nan? Idan har hakane zaifi ta kwantar da hankalinta, ba ya da tunanin tauye hakk'in ta ko d'aya, sai dai ba zai kusance ta da wuri ba, dan haka ya mik'e yace "Zan fita waje, ki samu ki ci ko kad'an ne, idan kin gama za ki iya kwanciyar ki, ni zan kwanta a falo."
Ko d'agowa ba ta yi ba bare ta kalle shi, ta na ganin ya fita ta mik'e ta tura k'ofar d'akin ta rufe ba tare da ta saka makulli ba, rufe ledar kazar ta yi sannanta canza kayan jikin ta ta kashe fitila ta kwanta, ba tare da ta cire gilashinta ba ta shiga duniyar tunanin irin zaman da za ta yi da mutumin da ba ta so, da wannan tunanin bacci ya d'auke ta ba tare da ta cire gilashin ba, shi ma a falo ya zauna tunani iri-iri a zuciyar shi, daga bisani ya gaji ya kwanta bacci ya d'auke shi.
*Kiran sallah farko* Khadija ta farka, bayan ta yi salati tare da addu'ar tashi daga bacci _"Alhamdulillahi-lazi ahayana, ba'ada ma amatana, wa'ilaihi-nushur."_
Gefen damanta ta lalaba dan d'aukar gilashinta amma sai ta ji ba komai, da sauri ta gyara zama zamanta ta ci gaba da lalabawa kowace kusurwa, Usman da ya gama saka kaya a falo ne ya shigo da niyyar d'aukar sallaya ya fice, ta sauko daga kan gadon kenan dan ta lalaba akan coiffeuse (dressing miror), da sauri ya k'arasa gaban madubin inda ya cire ya aje mata, d'auka ya yi ya mik'o mata yace "Karb'i gashi nan."
Hannu ta zura dan dama ga duhun d'aki ga kuma matsalar idon ta, a k'irjin shi ta d'ora hannu da tunnin ta kai hannunta daidai, rik'e hannunta ya yi ya d'ora mata gilashin ta bud'e shi ta saka, kallon shi ta yi tace "Nagode."
Ba wata fara'a yace "Ba komai, laifi na ne da na mi ki nesa da shi."
Jin kiran sallah ya sa yace "Na tafi masallaci, sai na dawo."
Murya k'asa k'asa yace "A dawo lafiya."
"Allah ya sa." Ya fad'a ya na ficewa daga d'akin, fita ta yi ita ma ta d'auro alwala a tsakar gidan ta dawo ta yi sallah ita ma, ta na kammalawa ta koma d'akin ta d'an gyara in da ta kwanta sannan ta shiga wanka, ta na shigowa falon da d'aurin k'irji da hijab ta samu Usman zaune a falon, sinne kai ta yi ta shige ciki dan ta shirya, doguwar rigar shadda ta saka da d'an kwalinta ta fito da tunanin d'ora mu su abin kari, har k'asa ta durk'usa ba ta had'a ido da shi ba tace "Me za'a dafa?"
Kallon ta ya yi yace "Ina kwana?"
K'ara k'asa da kai ta yi saboda kunya, dan ta san gatse ne ya mata saboda ba ta gaishe shi ba, cikin rawar murya tace "I...na, kwa...na."
Tab'e baki ya yi yace "Ba sai kin damu kan ki ba, yanzun nan za'a aiko da abin karin kumallo wa ke inji Hajia."
"Nagode." Tace ta na mik'ewa ta koma d'aki, ba jimawa Mannir ya kawo mu su abinci, sai da ya gama zubawa in da ya dace ya shiga d'akin ya same ta zaune bakin gado yace "Ki zo ki ci abincin."
Tashi ta yi ta sake d'aukar hijabinta ta fita, a tsakiyar falon ta samu ya aje abincin, juyawa ta yi ta kalli teburin da aka siya mata mai kukera shida, matsawa ta yi ta zaune daga gefen shi yanda basa fuskantar junansu, har ta d'auki cokali ta ji yace "Ki ci da hannu yafi."
Kallon shi ta yi sai kawai ta aje cokalin tasa hannu, haka dukansu suke cin abincin a hankali babu mai magana har Khadija ta cire hannu za ta mik'e yace "Zauna."
Zaunawa ta yi ta na kallon shi da sauraren shi, kallonta ya yi sosai ya matsa kusa da ita ya deb'o lomar abincin da hannun shi ya nufi bakin ta, kawar da kai ta yi tace "Na k'oshi fa."
Wani iska ya fuszar yace "Nana Khadija."
Yanda sunanta ya fita daga bakinshi ya tilasta mata kallon fuskarshi ita ma, da sauri ta d'auke nata idon saboda kallon da ya ke mata, d'orawa ya yi da "Ke amana ce a gare ni, ba zanyi duba da yanda auren mu ya kasance ba, dole na sauke duk wani hakk'in ki da ke kai na, jiya ba ki ci komai ba, yau ma gashi ba kici mai yawa ba, anjima aka fara shagalin damu zai iya saka ki jin jiri, dan haka bud'a bakin ki na ba ki abinci, ba wani abu bane a gare ni, ina da burin bawa duk matar na aura abinci da kai na, kuma ke ce wannan matar."
Sake d'aga ido ta yi ta kalle shi, a hankali ta kai bakinta ga hannunshi da ya mik'o mata abincin, sosai Usman ya dinga d'irka mata abincin nan ta na amsa, ta k'oshi sosai, amma ta kasa fad'a masa saboda yanda fuskar shi ke had'e ko kallonta bayayi, lomar da ya saka mata a baki k'in had'e ta tayi, wata ya d'ibo zai saka mata a baki ta k'i bud'a bakin, d'an k'aramin tsaki yaja yace "Karb'i mana, sai na ga cikin ki ya taso, ko ki na so yan biyar su fara jin haushi na tun ba aje ko ina ba?"
Da k'yar ta tura lomar zuwa mak'ogwaro ta amshi wacce ya mik'o mata, ta na fara taunawa sai kawai ta ji amai ya taho mata, da gudu ta mik'e ta fita farfajiyar gidan ta amaye kaf abincin da ta ci, da sauri Usman ya bi bayanta cike da tausayi, dan tunanin shi ba ta cika cikinta irin haka shi ya sa, ruwa ya bata ta kurkure baki ya na jera mata sannu, da kan shi ya had'a mata ruwan shayi tasha, har zai tattare kwanukan ta tashi ta hana shi da kanta ta d'auke, ganin dai ba wata matsala ya sa ya mata sallama ya fita dga gidan, kamar kuma fitarshi ake jira dama sai ga Kaltume da Barira sun zo, dan mama ce tace su zo kafin rana mutane su zo, tun da ba ta da yer uwa mace da za ta iya zuwa kafin zuwan mutane.
*Yau* ma haka aka yi shagalin damu aka gama, da dare kuma Rahama matar Ashir da *Aisha* matar Bashir su ka mata kwalliya kafin su ka bar gidan, har *11* dare ba Usman ba labarin shi, sai kawai bacci ya suri Khadija ba tare da ta shirya masa ba, ta na nan har sai da ya shigo, yanda ya same ta saita bashi tausayi, mayafin jikin ta ya fara cire mata a hankali kafin ya cire mata takalmin k'afar ta, a hankali ya tallabo k'afafun da nufin d'ora su akan gadon sai ta farka, da k'arfi taja baya ta had'e da gadon har tana neman fad'uwa, yanda ta ke kallonshi a tsora ce ya sa yace "Khadija, tsoro ki ke ji?"
Girgiza kai ta yi alamar a'a, tab'e baki ya yi yace "Shikenan, ki tashi ki cire kayan jikin ki sai ki zo ki kwanta."
Ganin ya juya zai fita ya sa tace "Kai fa?"
Juyowa ya yi yace "Ni fa me?"
"Ina nufin ina za ka kwanta kai?"
Murmushin mugunta ya saki ya kalli gefen ta yace "Anan mana, ko ki na so na sake kwana a falo ne?"
Shiru ta yi ba za iya cewa eh ba, saboda kar ya ji ba dad'i, kayan bacci ya d'auka ya fita falo dan canzawa, ita kuma k'in sauya kayan ta yi har ya sake samunta a haka, kashe wutar d'akin ya yi ya kwanta gefe ya na satar kallon ta, ba ta kwanta ba sai ma k'ara rakub'ewa da ta ke, kallonta ya yi yace "Ki kwanta Khadija, daga ni sai ke ne fa a gidan nan, kuma a cikin d'akin da babu wanda zai iya taimakonki, idan na so ai zan iya yin komai a d'an k'ank'anin lokaci, amma ba yanzu ba kinji, ki kwanta ki yi bacci kawai."
Ya na fad'a ya juya mata baya ya na ci gaba da murmushin gefen labb'a, bacci ne kad'ai ya fizgi Khadija yasa ta kwanta ba tare da ta sani ba, sai dai baccin bai je ko ina ba Usmn ya tashe ta yin sallah.
Ko da ta yi sallah ya fita a runfar nan ta samu akwai kayan abinci sosai, sassauk'an girki ta yi har ta gama bai shigo ba, akan teburi ta aje ta shiga wanka, ta na fitowa yau ma kamar jiya zaune ta same shi, d'aki ta wuce ta shirya cikin riga da siket na shadda sun mata kyau, ta gama shafe jikinta da turare za ta fito Usman ya shigo, cak ta tsaya dan ya tare k'ofar fitar, k'asa take kallo shi kuma ya na kallon fuskarta, kamar daga sama ta ji yace "Ki je ki yi kwalliya, ko da ba kya ra'ayinta ni ina so."
Galala ta bishi da kallo kafin ta zauna gaban madubi, da k'yar ta iya shafa hoda (powder) da d'an jan baki ta tashi ta bar d'akin, ta na zaune akan kujera taga fitowar shi, da sauri ta mik'e ta fara zuba abincin a k'aramin farantin da zai wadaci mutum d'aya, zan kujera ya yi ya zauna ya na kallon ta har ta gama zuba mi shi, wani farantin ta d'auka za ta zubawa kan ta yace "Ba buk'atar ki zuba na ki, mu fara cinye wannan."
Ta gilashi ta d'aga manyan idon ta ta kalle shi ta buntsuro faffad'an labb'an ta, zaunawa ta yi ta d'auko cokali za ta saka yace "Na fad'a mi ki ai, ba na cin abinci da cokali, zan so ki saba da hakan, dan ci da hannu ma sunna ce."
Mayarwa ta yi ta aje ta na kallon k'asa, hannu ya sa ya fara ci tare da bismillah ya kalle ta yace "Sa hannun ki mana."
Kamar wacce zai cinye haka ta saka hannu ta na tsakuro abincin tana sakawa a baki, ganin haka ya sa yace "Ki na so sai na baki da kai na kenan?"
"A'a." Ta fad'a da sauri ta na kai wata lomar bakin ta, d'an gyaran murya ya yi ya cire hannun shi ya na kallon ta yace "Nana Khadijatul Kubra."
Kallon shi ta yi jin wani cikakken suna da ya kira ta da shi, a hankali tace "Na'am."
Cikin nutsuwa yace "Kinga wani ikon Allah ko? Auren mu za mu iya kiran shi a bagtatan, domin kuwa babu wanda ya tsammani hakan daga mu har iyayen mu, amma Allah ya sa mun zama miji da mata sanadiyar had'arin da ku ka samu ke da mahaifi na, zan iya kiran haka da k'arfin da ke cikin rubutun *alk'alamin k'addara*, Khadija, tunanin hakan kad'ai ya isa ya samu mu rumgumi wannan k'addarar, dan ina da tabbacin wani babban al'amari zai faru tsakanin mu, sannan iyayen mu sun bimu da addu'ar mu da fatan alkairi, da wannan na ke rok'on ki da ki kwantar da hankali mu yi zaman aure, ina so mu yi zaman da iyayen mu za su yi farin ciki da mu, idan mu ka yi haka insha Allah Allah ba zai barmu mu wulak'anta ba, sannan maganar karatunki wannan ba matsala bane, za ki ci gaba insha Allah, sai dai kamar yanda ki ka sani ni ba mazauni bane, ba lallai na dinga sati d'aya ko biyu a cikin gidan nan ba."
Cikin ladabi tace "Na yarda na yi auren nan saboda yan uwa na, dan haka zaman ba zai gagare ni ba insha Allah."
"Alhamdulillah, hakan ya yi kyau, Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya azurtamu da zuri'a ta gari."
Da sauri ta kalle shi wanda shi ma ita ya ke kallo, da azama ta sauke nata idon ta na murmushi, shi ma murmushin ya yi ya lek'a fuskarta yace "Ya dai Hajia, ko ki na mamaki ne?"
Girgiza kai kawai ta yi, loma ya yanko ya nufi bakinta da fad'in "Maza bud'a bakin."
Amsa ta yi cike da kunya kafin yace "Wai ni ne ba'a lele kenan?"
Kallon shi ta yi cikin rashin fahimtar maganar shi, d'orawa ya yi da "Eh mana, har yanzu ke ba ki saka min a baki ba, ko kunya ta ki ke ji?"
Ai kuwa kunyar ce ta rufe ta ta mik'e da sauri za ta bar wajen ya rik'o hannunta, ba tare da ta juyo ba yace "Zo zauna to na hak'ura."
Janyo hannunta ya yi bai direta ko ina ba sai a kan cinyarshi, wani numfashi ta saune ta rufe idon ta ruf ta kasa ko numfashi bare motsi, shi kan shi wani sabon al'amari ne ya ziyarce shi, amma sai ya share saboda ya na so ta saki jiki da shi, dan ya lura har yarinta ma na damunta, cikin zolaya yace "Kinga ki bud'a idon nan, ko kuma dai..."
Shiru ya yi ya juya bayan ta ya saka bakinshi a zip d'in rigarta ya jashi k'asa, jin ya na zame mata zip ya sa tayi wni dogon numfashi ta bud'a ido, ta so ta d'aga daga jikinshi sai ya k'i bata dama, jin ya na ci gaba da zame shi ita kuma a ganinta abun kunya ne ya ga rigar nonon da take sakawa sai kawai ta fashe da kuka, jin yanda ta b'arke baki ne ya sa ya tsaya ya na kallon fuskar ta, da sauri ya mayar mata ya fara goge mata hawayen yana fad'in "Dan Allah ki yi hak'uri Khadija, banyi haka da wata manufa ba, ki yi hak'uri ki daina kukan to, na daina, shikenan?"
Share hawayen ta yi ta tashi daga jikin shi ta koma d'aya kujerar ta na ci gaba da share hawaye shi kuma yace "Ki rufa min asiri Khadija, yanzu me ki ke tunanin zai faru idan yan biyar d'in ki su ka shigo su ka same ki kina kukan nan? Ina tabbatar mi ki rataye ni za su yi a jikin pankar nan." Ya fad'a ya na nuna pankar sama da ke falon.
Kallon shi ta yi tace "Ka yi hak'uri to." Yanda ta yi magana cikin shagwab'a ba k'aramin birge shi ta yi ba, murmushi ya yi yace "Ai ni ne da baki hak'uri, tun da na fahimci ba kya so mu k'ara samun kusanci."
Haka dai suka kammala ya mik'e zai fita ya fito da jikka uku ya bata, kallon shi ta yi tace "Na miye wannan?"
Murmushi ya yi yace "Da taimakon Ashir ni ma yau gashi ina bayar da kud'in cefane."
Dariya ta yi tace "Ai ba sai ka bayar ba, akwai duk abubuwan buk'ata."
Sunkuyowa ya yi yace "Sai abin da ba'a rasa ba ko?"
Shiru ta yi ya janyo hannun ta ya d'ora mata kud'in yace "Kar ki rage min darajata mana."
Murmushi ta yi tace "Angode, Allah ya saka da alkairi."
D'agota ya yi tsaye ya rumgume ta, yarrrrr, dukansu suka ji saboda dukansu shine karo na farko, shiru su ka yi kowa da abin da ya ke ji a game da d'an uwan shi, kamar ba za su rabu ba sai kuma suka raba jikin su, ba su yarda sun kalli juna ba sai Usman ne yace "Wannan ranar ita ce iyaye na ke min burin shiga, su na yawan fad'a min idan na yi aure ko kud'in cefanai na bayar idan har na yi sa'ar samu mace ta gari, to tabbas za ta gode min akan hakan tare da min addu'a."
Shiru ta yi ita dai har yace "Ni zan tafi, sai na dawo."
"Allah ya kiyaye, Allah ya tsare ka ya bada abin da aka je nema."
"Ameen ameen, nagode sosai." Har ya juya zai fita ya sake juyowa ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta, ficewa ya yi ya bar ta tsaye ta na tunanin sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a cikin k'ank'anin lokaci, kayan da suka b'ata ta fito da su ta wanke ta gyara wurin sannan ta d'an zauna ta huta, ba jimawa sosai ta d'ora girkin rana, ita kad'ai ta gama aikinta ta yi wanka ta shirya, ta na zaune ita kad'ai yaran mak'otansu suka shigo su ka tayata hira, har la'asar ba Usman ba labarin shi, ta idar da sallah ta d'ora girkin dare kenan Hassana da Husseina su ka zo tare da Aziza lokacin ba ta fi shekara uku ba a duniya, wannan abincin ta juye mu su suka ci suna ta hira, zuwa k'arfe *biyar* na yamma su ka tashi tafiya, turaren wuta da na jiki da kud'i ta basu su shiga taxi, haka suka fita su na fad'an ta da alkairi cike da k'aunar ta dukansu, har suna mamakin yanda ta so su bar Aziza wajen ta, aikinta ta ci gaba da yi har ta na daf da k'arasa miya, kamar jiran fitarsu ya ke sai gashi ya shigo gidan, cike da gajiya da kasala ya zauna akan kujera kusa da ita ya na sauke numfarfashi ya na cire hular kan shi yace "Wallahi na gaji sosai."
Cike da kulawa ta kalle shi tace "Sannu, aiki ka yi sosai?"
Ido rufe yace "Wallahi ina fita *Murtala* ya fizge ni mu ka tafi wani k'auye, na d'auka zamu dawo da wuri amma Allah bai nufa ba."
"Ayyah! Sannu." Kallon ta ya yi yace "Ko zaki had'a min ruwan wanka?"
"To, to." Ta fad'a ta na tashi kamar za ta ruga a guje, ta na kai mi shi ruwan ta d'auki kwandon sabulu ta kai mi shi da towel, dawowa ta yi ta d'ibo ruwan sha ma su sanyi ta durk'usa gaban shi tace "Ga ruwa ka fara sha to."
Karb'a ya yi yace "To zan sha saboda daga hannunki su ka fito, amma bayan wanka na fi buk'atar abinci gaskiya."
Sororo ta kalleshi ta had'e yawu, rarraba ido ta fara yi gabanta na fad'uwa, dan ba ta saune miya ba ma bare ta d'ora macca, ko da yasha ruwan ya mik'e zai wuce tace "Ka fad'a min me za ka iya ci yanzu na dafa maka?" Ta fad'i hakane ko da zai ci wani abu mai sauk'in sarrafawa.
Juyowa ya yi da mamaki yace "Ban gane ba, ki na nufin ba ki d'ora komai ba tun da na fita?"
Cikin nutsuwa tace "Wallahi na d'ora, na yita jiran shigowar ka amma shiru, sai kuma su aunty Hassana su ka zo kawai sai na juye mu su abincin."
Murmushi ya yi yace "Wai su aunty, Hassana fa k'annai na ne su, ba sai kin kira su da aunty ba."
Cikin jin kunya tace "Amma ai ni sun girme ni."
"Duk da haka, dan na tabbata da zasu fita da ke aka tambaye su wacece ke? Za su ce matar yayan su ce, ke ma kuma dole ki kirasu da hakan."
"To na ji, yanzu dai ka shiga ka fito."
Dariya ya yi ya wuce, ta na ganin shigarshi ta gaggauta k'arasa miyar ta, da sauri ta d'ora ruwan macca, ya na fitowa ruwan sun taso ta zuba maccar, cikin sauri ya shirya ya fito zai fita, rik'e shi ta yi da hira tace ya koma ya zauna za ta bashi wani abun mamaki, zaune ya yi ya na kallo yana jiranta, baifi minti sha biyar ba ta shigo da kwanuka masu kyau da gani ta aje gaban shi ta d'auko ruwa da lemo da faranti ta aje masa, sai da ta zauna gaban shi zata zuba mi shi yace "Amma ina ki ka samu wannan?"
Ba tare da ta kalleshi ba tace "Abincin dare ne za ka ci tun yanzu."
Dariya ya yi yace "To idan daren ya yi kuma ya zanyi?"
"Sai na girka maka na safiyar gobe ka ci."
Dariya ya yi sosai yace "Da alama zan cinye abinci na kafin kwana na ya k'are."
Dariya ta yi sosai har hak'oran ta na fitowa waje sosai, duk da ba ta jin yunwa sai da ya takura ta ta ci abincin tare da shi, daga lokacin kam ta yarda cewa ba zai iya cin abinci ba tare da ita ba, ya na gamawa hira su ka dinga yi kamar dama sun saba har saida magrib ta gabato kad'ai ya fita.
*Allah ka mana kyakyawan k'arshe.*
18/01/2020 à 17:42 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*12*
Da dare ma tare su ka ci abinci su ka ida su ka tab'a kallo, ko da dare ya k'ara yi Khadija ta fara tashi ta yi shirin kwanciya, ta na gamawa ta kwanta ta rufe ruf dan ta nuna ta yi bacci, sai da aka d'auki lokaci kafin ya shiga d'akin shi ma ya shirya, kashe wuta ya yi ya kwanta gefen ta, daga yanda Usman ya ji canzawar numfashinta ya tabbatar mi shi ba bacci ta ke ba, dan ya tsoratar da ita ya yaye zanin rufar daga fuskar ta cikin taushi murya yace "Allah yasa matsoraciyar nan ta yi bacci, sai na samu yanda na ke so."
Zunbur ta mik'e zaune ta kafe shi da ido duk da ba ganin shi takeda kyau ba, zaune ya yi ya janyo hannun ta ya na fad'in "Ashe ba bacci ki ke ba, to matso kusa da ni."
Girgiza kai ta yi alamar a'a, k'in matsawa ta yi sai da shi ya matsa daf da ita ya rumgumea jikin shi, shafata ya ke ya na fad'in "Khadija, kinsan me ye aure?"
D'an tureshi ta yi daga jikin ta tana so ya rabuda ita, matseta ya yi sosai yace "Ki nutsu mana, me ya sa ki ka cika tsoro ne? Ni fa mijin ki ne."
Kamar za ta fashe da kuka tace "Ni dai dan Allah ka sake ni, ba na jin dad'i."
Kallon fuskarta ya yi yace "Khadija ba na da tunanin tauye mi ki hakk'in ki, kar ki ga kamar ina takura ki, ina so ne kema ki shaida kinyi aure, sannan ki zama babbar mace, ba zan so ace kin wuce kwana uku a gidan nan ba tare da kinsan a wane matsayi ki ke ba, kumada safe na fad'a mi ki ni matafiyi ne, gobe ko jibi tafiya za ta iya taso min, kuma ba na dawowa k'asa da sati biyu, kinga kenan idan banyi abin da ya dace ba na zama kamar lusari kenan."
Khadija dai shiru ta yi ba tace komai ba sai sauraren shi, daga nan kuma sai ya samu dama ya kuma yi anfani da ita wajen mayar da Khadija babbar macen kamar yanda yace, dukansu sun san bak'on al'amari ne a gare su, shi farin ciki tare da jin wani sanyi a zuciyar shi, Khadija kuma kuka na rad'ad'i da zafin da take ji da ya zama sabon abu a wajen ta, da taimakon shi ya taimaka mata ta gyara kan ta ta tsarkake jikinta, har bacci ya fara d'aukar ta tajiya k'wak'ume ta kamar zai mayar da ita ciki, haka bacci ya rideta amma banda Usman da ya kwana ya na kallon fuskarta ya na shek'a mata sawar albarka da tunanin yanda rayuwarshi ta canza sanadiyarta cikin k'ank'anin lokaci, har aka kira sallah idon shi biyu, sai da ya yi alwala sannan ya zo ya tashe ta a hankali, masallaci ya nufa ita ta yi sallahnta a gida, tun akan sallaya ta kwanta saboda zafin da har yanzu take ji a k'asan ta da kuma bacci, ko da ya same ta bai tashe ta sai da ya tabbatar ya had'a mata ruwan shayi da soyayyen k'wai, tashin ta ya yi da kan shi ya mata wanka duk da ta cije akan bata so amma bai barta ba, haka ya saka mata kaya suka karya, yinin ranar babu inda ya je duk da yaran mak'wabta na shigowa, ya na zaune ya na kallon matar shi na kai da kawo ya na jin dad'i da sabon abu a game da ita.
*Muje da sauri fan's*, sati biyu kad'ai da auren su, amma shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanin su sosai, a cikin k'ank'anin lokaci suka saba da junan su, dan sosai Usman ke sakin jiki da Khadija ya na janta a jikinshi, *sabo tirken wawa*, sai gashi ita kanta Khadija ta saba da shi sosai ta yanda ba ta kl cin abinci in ba tare da shi ba, dan ji take kamar ya zamar mata yan uwan ta biyar, cikin wannan rayuwar farin ciki Usman ya shirya tafiya *zinder*, matuk'a Khadija taji ba dad'i, tunanin ta ya za ta yi rayuwa a gidan ita kad'ai babu shi, ya yi k'ok'ari sosai ya kwantar mata da hankali, amma hakan bai mata ba har sai da tace ya d'auko Aziza ya kawota nan, ya ji dad'in tunanin ta sosai, kuma haka akayi kam, a ranar da zai tafi a ranar aka kawo Aziza da kayan ta, haka ya tafi suka rabu cike da kewar juna.
Ta ji dad'in zaman ta tare da Aziza duk da yarinya ce, ita ke kula da duk d'awainiyar ta, haka ma yan uwan Usman d'in na yawon kawo mata ziyara, haka ma jefi jefi yan yan uwan ta su kan lek'o dan su ga halin da take ciki, a haka har aka kwashe *kwana goma sha biyu*, a kwana na sha uku Usman yace ya na nan tafe, duk da ba ta san ainahin abin da ta ke ji a ran ta ba a game da shi, amma haka ta ji farin ciki ya mamaye ta sosai, a ranar Kaltume ta zo gidan, kuma Kaltume yarinya ce da Allah ya bawa basirar sanin kan tsiyar maza😂, idan ta fad'i wata magana sai ka d'auka babbar mace ce, haka ta samu ta had'awa Khadija wani had'add'en lemun kayan marmari sannan ta zuba mata madara a ciki da *garin raihan*, wuni ta yi ta na shan shi bayan tasha lalle da kitso na tarban miji, bayan nan kuma da kan ta ta taimaka mata suka canza zaman duka kayan d'akin, kuma duk su na aikin ne ta na k'ara fad'a mata irin shiri da kwalliyar da za ta yi, duk Khadija na sauraren ta har ta gama, girki ta d'ora su ka ci kafin ta tafi gida.
Kasancewar shigowar rana zaiyi ya sa tun k'arfe *d'aya* na rana Khadija ta kammala girki ta aje in da ya dace, dama tun da safe Hajia ta aiko Mannir ya d'auki Aziza, hakan ya bata damar sakewa sosai ta yi aikin ta, wanka ta yi ta jima ta na shafawa ta na zanawa da dangwalawa, k'ananan kaya ta saka riga da siket na kanti masu kyau da suka dace da ita, turaren tsintsiya ta kunna sannan ta turara na wuta mai dad'in k'amshi, sai kuma na ruwa (airfreshner) shi ma mai k'amshin lemon tsami ta fesa, ko ina ya d'au harama mai gidan kawai ake jira, k'arfe *uku* cip-cip ta na zaune ta ji sallama, shaida muryar ya sa ta ja dogon numfashi lokacin da ta tuna hud'ubar Kaltume, mik'ewa ta yi ta fice da gudu ta yaye laluben, ba ta tsaya tunanin komai ba ta fad'a jikin shi ta rumgume shi k'yam, cikin farin ciki take fad'in "Sannu da zuwa miji na, sannu da dawowa, na yi farin ciki da dawowar ka gare ni."
Ajiyar zuciya Usman ya sauke ya d'an juya ya kalli *Kabir* k'annan shi da ya d'auko shi daga gidan mota, karb'ar jakar hannun shi ya yi yace "Nagode ko, ka gaishe da su Hajia sai na shigo."
Baki bud'e ta d'ago a hankali dan ganin waye, ta na ganin Kabir ta sake saurin sunne kan ta cikin k'irjin shi ta cakumo rigar shi ta rufe fuska da ita, dariya su ka mata Kabir yace "Matar yaya wai ba dai sati biyu da ya yi baya nan ne ya saki wannan farin cikin ba kamar ya yi shekara?"
Ita kam kunya ce ta sake rufeta ta kuma tusa kan ta cikin k'irjin shi dan ba za ta iya d'agowa su had'a ido ba, murmushi Usman ya yi ya na shafa bayanta yace "Dallah malam ka wuce ka yi abin da na saka ka, sai ka takura min yar..."
Shirun da ya yi ya sa Khadija d'agowa ta kalle shi, had'a goshinsu ya yi wuri d'aya yace "Yar yarinya ta na ke nufi."
Cikin dariya Kabir yace "To sai anjiman ku amare, sai ka shigo d'in, amma ni banga alamar za ta barka ka fito ba."
"Saboda me?" Cewar Usman ya na kallonshi, shafa kan shi ya yi yace "Ai na ga ta yi kewarka ne sosai."
Wannan maganar ce ta sa Khadija juyawa da k'arfi za ta koma d'aki Usman ya fizgota ta fad'a kan shi, dariya su ka saka Usman ya juyo ya kalli Kabir yace "Kai wai za ka fice min ko sai na raka ka ne?"
Sosa k'eya ya yi yace "To ai ba ka ban tsaraba ta bane, ko ka manta yanda mu ka yi da kai kafin ka tafi?"
Sakin Khadija ya yi ya aje jakunkunan hannun shi ya tunkari Kabir ya na fad'in "Ina zuwa, bara ka gani d'an hancin uwa kai."
Maimakon ya fita daga gidan sai ya daka da gudu ya yi hanyar ban d'aki ya na dariya ya na fad'in "Amma fa sai da na fad'a maka banda mai a moto na, kace idan mu ka zo za ka ban kud'i na saka, ka bani kawai sai na tafiya ta na barku ku soyewar ku."
Dawowa ya yi ya kama hannun Khadija ya sunkuya zai d'auki jakunkunan ta tu saurin karb'a ta na fad'in "Bara na shigar ma ka da su."
Kabir ne ya sake fad'in "Dan Allah ka fito ka sallame ni kafin ka shiga d'akin nan, dan bansan me zai faru ba idan ka shiga."
Juyowa ya yi ya kanne shi Khadija kuma k'arasa shiga ta yi saboda kunya, suna shiga Usman ya tsaya ya na k'arewa d'akin kallo, komai a d'akin kalar kayan d'akin ta ne ma'ana fari da maron, sai telebijin da k'aramin teburin tsakar d'aki ne kad'ai bak'ak'e, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta yace "Duk wannan shirin na zuwa na ne?"
Cike da kunya tace "Eh mana, sati biyu ba ka gidan ka, ya na da kyau ka tarar da sabon abu dama."
Hannunshi ta kama tace "Muje ka cire wannan kayan ka yi wanka, idan ka fito sai ka zo ka ci abinci."
"Na ci abinci ko ki ba ni abinci?" Ya fad'a ya na tsare ta da ido, murmushi ta yi ta kalle shi tace "Duk yanda ka ke so ai girman ka ne, ka cancanci fiye da haka ma."
Wani basaraken murmushi ya yi ya nufi d'aki yace "Godiya na ke Nana Khadija."
Zasu shiga d'akin Kabir ya d'aga murya daga waje yace "Kai fa na ke jira, wallahi yah Fodio kar ka manta da ni anan waje ka shiga harkar gaban ka, kasan dai nima matar ce da ni ko."
Shima d'ago muryar ya yi yace "Naji me mata, amma aljihunka ba ka da kud'in da zaka saka mai a moto, to waye zai ciyar maka da matar kenan, ko dai hak'uri take ci?"
K'arasa shiga d'akin su ka yi, k'amshin da ya daki hancin shi ne yasa shi lumshe ido, a hankali ya bud'a ido ya sauke akan gadon da shi ma zanin da aka shinfid'a sama fari da maron ne, kallon ta ya yi yace "Khadija kin wahalar min da kan ki dayawa fa."
Murmushi kawai ta yi ba tace komai ba, zai fara cire kaya Khadija ta nufi wajen wata k'aramar jakar ta ta hannu ta d'auko ta fito, a tsakar gida ta samu Kabir ya na ta shawagi shi kad'ai, bud'a jakar ta yi ta ta ciro yan jikka jikka har guda biyar mik'akk'u ta mik'o mi shi tace "Gashi wai a baka."
Da mamaki ya kalli hannunta yace "Inji shi?"
"Eh." Ta fad'a da murmushi, jim ya d'anyi kafin ya karb'a, dan shi dai a iya saninshi Usman na k'ok'ari da su sosai wajen yi mu su buk'atunsu, amma kyauta irin haka dai ta shiga tsakanin shi da su gaskiya da wahala, saboda shi kan shi ma ai ba k'arfi bane da shi, da wannan mamaki yace "Ki masa godiya matar yaya, nagode sosai, ni na wuce."
"Amma ai da ka jira shi sai ku ci abinci ko."
Cike da zolaya yace "Me ki ka dafa ne? Kinsan ni fa ina son abu mai dad'i."
Dariya ta yi tace "To ka tafi tafi kawai, dan nasan abin da na dafa ba lallai ya birge ka ba."
"Da alama dai ba kya so na ci ne, to na hak'ura ma bana ci."
Jin motsin Usman ya sa ta dawo ciki, da sauri ta karb'i abun tsane ruwan hannun shi ta d'auki kwandon sabulu ta kai ban d'akin ta dawo ta cika bokiti da ruwa ta kai mi shi, kallonta ya yi yace "To na shiga na yi ne? Ko kuma madam ce ke da wannan alhakin?"
Dariya ta yi kawai ta kama hannun shi su ka nufi ban d'akin, shine ya fara shiga ita kuma ta tsaya baya tana tunanin ta mi shi wankan kamar yanda k'awar ta tace? Ko kuma dai ta bar shi ya yi da kan shi, wata zuciyar ce tace ma ta to ai mijin ki ne, ya sanki kin san shi, dan haka babu kunya a wannan fanni tsakanin ma'aurata, shiga kawai ta yi ta fara gurza shi soso da sabulu, haka su ka fito ta gama shirya shi cikin k'ananan kaya na kanti, sai dai la'asar ta matso ya sa shi yin alwala ya nufi masallaci ya fara sallah, ya na dawowa su ka ci abinci tare kamar yanda su ka saba, daga kan teburin ya kashe ta da wani kallo yace "Khadija."
"Na'am." Ta d'ago ta na kallon shi, cikin taushin murya da nuna buk'atar shi yace "Kinyi kewata kuwa?"
Da idon ta nan masu kama da na mai jin bacci ta kalle shi tace "Dan ba ka gan ka akan gado na bane ka fad'i haka?"
Sai da ya d'an lashe baki yace "Da gaske? Kenan kema yanzu haka ki na jin abin da na ke ji?"
Da gangan ta d'auki kofin (cup) lemun shinkafar da ta yi ta zuba a rigarta a tsakiyar maman ta tana kallon shi tace "Ya ma fi wanda ka ke ji."
Taso da ita ya yi tsaye ya d'aga kan shi ya na kallon ta ya soma cire mata mab'allan rigar ta har sai da ya rabata da ita, rigar nonon da ta kamata ya cire ita maya jefar kafin ya sa harshe ya na lashe jikinta in da lemun ya zuba... *gyara kimtsi*.
*Misalin* 05:54, su na kwance akan gado ya kalleta yace "Khadija, kin mayar da ni babban mutum, ina godiya ga Allah da ya k'addara had'uwa ta da ke a lokacin da babu wanda ya yi tsammanin faruwar wani abu tsakani na da ke, sannan ina godiya a gare ki da ki ka zama yarinya mai hak'uri da zab'in iyayen ta da kuma tawwakali da hukuncin ubangiji, ina kuma godewa Ashir da ya yi tunanin had'a ni da ke har yanzu mu ke kwance akan gado d'aya a matsayin mata da miji, sannan ba zan manta da k'ok'arin iyaye na a kai na wanda su ka jajirce har sai da su ka ga kin zama mallaki na, tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayen shi ba ya tab'ewa, ni shaida ne kuma na gani a zahiri, Khadija, zuwan nan da na yi na taho mi ki da tsaraba mai yawa, amma babbar tsarabar da na ke so na ga ta k'ayatar da ke ita ce *kyautar zuciya ta*."
Tashi ta yi daga kxance ta na kallon shi tace "Ka na nufin ka mallaka min zuciyar ka gaba d'aya?"
Sai da ya jinjina kai alamar tabbatarwa kafin yace "Hakane, kin cancanci fiye da wannan ma, dan da akwai abin da ya fi zuciya ta mahimmaci a gare ni, to da shi zan ba ki, dan a gaskiya ba zan iya ba ki rayuwa ta ba."
Da sauri ta kalle shi tace "Ka na nufin ba zaka iya sadaukar da kan ka ba wa ni?"
Da fuskar tausayi yace "A gaskiya ba zan iya ba."
Cikin rashin jin dad'i tace "Kenan akwai wata da ka ke so?"
"Akwai mana." Ya fadada murmushi, sai lokacin ta rarumo gilashin ta ta saka ta kalle shi da kyau, ganin idonta sun kawo ruwa ya sa ya saki dariya ya rumgume ta yace "Ina da wacce na ke so mana, ga ta a gaba na, Nana Khadija *baiwar Allah*, Khadija ke ce na ke so, ba zan iya sadaukar da rayuwa ta ba wa ke saboda da ke kad'ai na ke so na yi rayuwa, ina so na na k'are rayuwa ta tare da ke cikin farin ciki."
D'agowa ta yi daga jikinshi ta kai mi shi duka a k'irji ta na fad'in "Har ka tsorata ni."
Dariya ya yk yace "Hakan na nufin nima na samu shiga kenan a cikin wannan tattausar zuciyar?"
Sai da ta rumgume shi tace "Sosai ma, kai ne farko da ka fara shigar ta, kuma insha Allah kai ne za ka zama na k'arshe, saboda ka na shiga na rufe ta na kuma jefa makullin a cikin tekun maliya."
Sumbatar ta ya fara yi daga nan dai aka sake juyewa ni kuma na sake juyowa na fito😎,haka su ka dinga gudanar da rayuwar su abar sha'awa, sun manta da yanda ma aka yi su ka had'u, soyayyar su suke barjewa kawai, zan iya cewa daga cikin biyayyar da Usman ya wa iyayensa akan auren Khadija ce ta sa k'ofofin arzik'i su ka fara bud'e masa ta ko ina, ga kuma addu'a da kullum ya ke samu daga matar shi da iyaye da yan uwa akan k'ok'arin da ya ke da kowa, sosai ya ke samun ci gaba ta fannin kasuwancin da ya saka a gaba, duk da su na d'an samun k'arancin lokacin juna hakan bai hana Khadija taya shi murnar samun ci gaban ba, dan ta lura mutum ne mai son samun na kan shi ba ya kuma buk'atar taimakon kowa, dan ita kan ta yawan kyautar da take wa yan uwan shi da iyayen shi lokuta da dama ya na nuna rashin jin dad'in shi, musamman idan Kabir ko Mannir ko Nura da ke k'arami su ka zo ya ga ta d'auki kud'i masu yawa ta basu wasu lokuta ma har da sabulan wanka da turaruka, sai yai ta fad'a wai ta lalata su har Kabir da ke da aure, ita kam tausayin shi take ganin koyarwa ce ya ke sai wata a baka, duk da ya na fad'a ba ta daina ba saboda a ganinta ita ta na da halin da za ta yi mu su tun da yan uwan mijin ta ne, sannan duk wata ita ma yan uwan ta su kan turo mata kud'i daga cikin ribar da ake samu na kud'in ta da suke juya mata, haka dai har lokacin hutunta ya k'are ta ci gaba da zuwa makarantar ta cikin kwanciyar hankali, duk da mijinta ba mazauni bane, amma ta na gamsuwa da kulawar da ya ke nuna mata.
*Wata biyu* da komawa makaranta Khadija ta kwanta rashin lafiyar da ta jijjigata sosai, dan sai da ta kwana hud'u asibiti ba ta cikin hayyacin ta, ta galabaita da mugun zazzab'i da ciwon kai, ga kuma ciwon ciki da ya murd'ata dole ta yi amai, allura kam tasha ta har ba adadi, haka K'arin ruwa har sai da hannayenta su ka kumbura saboda sukar da ya sha, duk da jikin ya yi dama amma sai da ta cika sati d'aya a asibiti kafin aka sallame ta, cikin ikon Allah kuma sai jiki ya yi kyau sosai, tun daga ranar kuma Khadija ba za tace ga ranar da ta sake kwantawa rashin lafiya ba, sai dai kawai abin da ba'a rasa ba irin su ciwon k'ugu, ciwon baya da d'aurewar mara, kullum Usman godiya ya ke wa Allah da Khadija da ta zama silar sauyawar rayuwar shi, bai tab'a tsammanin auren shi da ita abu neda zai kallo ba, duba da babu maganar soyayya tsakaninsu, sannan ita mai kud'i ce kuma matashiyar yarinya mai ji da kyau, amma ta aure shi babu kud'i babu kyau, kuma duk da haka ta zauna da shi da kyautatawa, wannan ya sa lokuta da dama ya kan fi kiran ta da Nana Khadija baiwar Allah, lokacin kuma arzik'i ya hab'ako sosai, sai kawai ya fara da iyayen shi ta hanyar canza mu su fasalin gida, in da ya gwangwaje su da bila (villa) mai kyau yar zamani, ya d'aukarwa mahaifiyar shi wacce za ta dinga girka mu su abinci sai dai su ci kawai, lokacin da cikin Khadija ya girma ne ya samu wani babban aiki, wata kwangila da aka mallaka mi shi milyoyin kud'i, a lokacin ne ya fara mu su sabon gini su ma, ginin da a lokacin ya amsa sunan gini, ta wani fannin kuma dije na zuwa makarantar ta hankali kwance.
Lokavin dacikin ta ya isa haihuwa ne wata tafiya ta taso mi shi zuwa Dubaï, shine karo na farko da zai fara zuwa, hakan ya sa a ranar Khadija ta wuni ta na kukan ba zai tafi ba, rarrashin duniya ya yi amma ta toshe kunne ta k'i fahimtar shi, a k'arshe dai dole ya yanke shawarar kaita gida ta zauna tare da su mama har ya dawo, ita kuma bud'ar bakin ta cewa ta yi "Aiko sai dai ka tarar na haihu wallahi, dan ba zan jira ka ni."
Dariya ya yi yace "Ba za ki haihu ba insha Allah har sai na dawo."
Haka ya kaita gida ya aje shi kuma ya wuce, tun a mota Murtala ya lura yanayin abokin shi ya canza sosai, cike da kulawa yace "Aboki na lafiya dai? Ya na ga ka yi wani iri ne?"
A hankali ya kalleshi ido sunyi jawur kamar zaiyi kuka yace "Khadija, ita na ke tausayi, sai ta haihu kafin na dawo, ba na jin za ta wuce sati ba ta haihu ba, dan duk alamu sun nuna haka, kwana hud'u ko bacci ba ta iya yi saboda ciwon baya da mara, mtss." Ya k'arashe da d'an guntun tsaki.
Murtala ne yace "To ya za ayi sai hak'uri? Kuma gashi ba ka fad'a mata gaskiyar magana ba cewa tafiyar nan za ta iya d'aukar ka wata d'aya ko fiye da haka."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Sati d'aya ma na fad'a mata amma ta damu sosai, ina ga na fad'a mata wata d'aya zanyi? Shi ya sa ma na riga na barwa Hajia komai su kula idan ta haihu, kuma na gode Allah da na iya fad'awa yan uwan ta adadin lokacin da zan iya yi."
"Hakan ma da ka yi ya yi daidai, kaga za su dinga kwantar mata da hankali."
A haka su ka isa kuma su ka rabu suma cike da kewar juna, a daren wannan ranar Khadija nak'uda ta taso mata, da su ka tafi asibi har sai da gari ya waye rana ta yi fatsal-fatsal kafin ta haihu, duk abin da ake Usman na da labari, lokacin da Husseina ta bawa Khadija waya ya mata magana da ta kasa, wata k'ara tare da kuka had'i da salati da ta yi sai da ya ji kamar ya bud'a ido ya ganshi gabanta, a k'arshe dai *bayan wuya* sai dad'i, ta haihu lafiya haka ma yaro, lokacin wani mugun bacci ne ke d'ibar Khadija amma sai Usman yace Hajia ta bata waya su yi magana, daga kwance ta karb'i wayar ta d'ora a kunne, shiru ta yi sai shine yace "Barka baiwar Allah, daga k'arshe dai Gashi kin haifo min yaro, Khadija ina cikin farin ciki sosai, godiya ko dukiya ba za su iya biyan ki ba, amma ina so ki fad'a min duk abin da ki ke so? Ni kuma zan baki shi a matsayin tukuicin wannan kyautar."
Cikin muryar jin bacci tace "Ina hushi da kai kafin minti ashirin da su ka gabata, saboda ka k'i zama tare da ni a lokacin da na ke buk'atar ta, da ka k'ara kwana d'aya tak da na haihu a gaban idon ka, amma bayan minti ashirin da ya wuce, lokacin da na d'ora ido na akan yaron ka, sai na ji komai ya yaye a zuciya ta, dan haka ka d'auka yaron nan shine tukuicinka gare ni."
Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi hak'uri Khadija, haka Allah ya so, kuma duk da kin ce ba jya buk'atar komai, amma akwai wani abu da zan ba ki, kinsan me ye?"
Cikin lumshe ido tace "A'a."
"Khadija, nine ya cancanci na yi wa yaron nan hud'uba, kuma gashi bana nan, dan haka babu wanda yafi cancanta sai ke, na d'ora mi ki wannan nauyin a kan ki, idan kin ma sa hud'uba sai ki rad'a masa sunan da ki ka ga ya dace kuma ki ke so."
"Da gaske ka yarda na saka mi shi suna da kai na?" Ta tambaya da fara'a.
"Sosai ma, wannan hukuncin na jima da yanke shi ai, ba kawai dan bana nan bane."
Shiru ta yi kamar mai bacci kafin tace " *Abban Bilal*., hakan ya yi?"
Da farin cikin jin sunan da ta sakawa yaron ya sa yace "Masha Allah, Bilal, sunan da ke birge ni, sunan da ya nake da burin sakawa yaro na shi, hakan fa ya na nuna k'arfin soyayyar da ke tsakanin mu ne."
Jin bcci na son surarta ya sa tace "Ka gafarce ni Abban Bilal, bacci na ke ji sosai a ido na, za mu yi magana anjima."
"Ayyah sannu momyn Bilal, zan barki haka to, amma anjima za mu yi magana, kin yarda?"
Cikin hamma tace "Na yi alk'awari."
Da haka su ka yi sallama, kamar yanda ya bar komai hannun Hajia haka ta dage sosai ta yi takamata, dan mawasu lokutan maman Khadija da yan biyar ba sa tsayawa komai da an nemi abu za su siyo su kawo, haka dai aka yi shagalin biki babu uban yaro, a lokacin Khadija ta fara damuwa da rashin dawowar Usman, da k'yar yan uwanta da mama suke kwantar mata da hankali, tun suna waya ya na cewa zai zo aiki ne ya rik'e shi har ya kai ya rasa me zai ce mata, sai kawai zuciyar shi ta bashi ya daina kiranta, ita kuma idan ta kira jar ya d'aga sai an kwana biyu, wannan dubarar ce ta jefa Khadija a wani hali na daban, da ta kwashe kwanaki ta na kira bai d'aga ba, damuwar ta ta nunku sosai, mama kuma sai take cewa tayi hak'uri mana da yanda Allah ya hukunta mata, hakan ya sa Khadija tunanin ko Usman ya mutu ne dai, kawai sai ta yanki jiki ta fad'i, sai da ta kwana asibiti, a ranr Usman bai shirya tahowa ba amma dole ya taho, dan cewa ya yi neman kud'i ba zai ja mi shi rasa matar shi ba wacce ya ke da yak'inin ba zai samu kamar ta ba a wannn k'arnin, sai lokacin kad'ai Khadija ta samu sauk'i ta kuma huce.
*Allah ka k'ara mana lafiya mai anfani.*
20/01/2020 à 12:38 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
💕💕💕 *My Heenat, My BK, My Meelat*💞💞💞
_Alkhairin Allah ya lullub'e min ku, ina k'aunar ku._😘
```Fatan alkairi masoya```
*MOMYN DADY, KI JI DAD'IN KI WANNAN PAGE TA KI CE KYAUTA.* 😉
_Bismillahir rahamanir rahim_
*13*
Kullum taresu ke idan dare ya yi har ba ya son rabuwa da iyalin shi, kuma bai sake wani tafiya ba har sai da ta yi arba'in, sabon gidan da ya gina mu su matsakaici daidai da rayuwar su suka tare, haka suke rainon Bilal cikin kulawa da so da k'auna, ta b'angare d'aya kuma ta na ci gaba da zuwa makarantar ta, kasancewar babu nisa da gidan su da makarantar ya sa take aje Bilal nan kafinta wuce, idan ta sauko ta biyo ta d'auko shi, a haka dai har ta kammala karatunta lafiya, haka ma Usman ya na k'ara samun hab'aka a kasuwancin shi, a lokacin da ya ke tunanin nemawa Khadija aikin karatun da ta yi, sai kawai ta shawarce shi kan ta na son fara kasuwanci, ta na so Ashir ya fara kawo mata kwanuka da karap (jug) da sauran kayan anfanin mata ta na siyarwa, ya ji dad'in haka kuma yace nauyi ne a kan shi ya mata hakan, Ashir ya nema su ka yi magana sannan ya fara bashi *million d'aya* dan a fara da ita, cikin ikon ubangiji kuma sai Allah ya sawa kasuwar albarka, duk da komai bashi ne, amma dai ana samu sosai, lokaci na tafiya kamar walk'iya in da abubuwa ke faruwa, ta na taimakon danginshi da danginta da ita kan ta ma da kasuwancinta, in da Aziza kuma ta zama kamar ba k'anwar Usman ba, dan ya zama Khadija ita ce komai na ta, har tafi son zama gidan nan akan gidan su, a lokacin kuma Khadija su na ta sake zuba ido akan samun wata haihuwar amma shiru, abu d'aya shine kasuwancin ta ya na d'aukar hankalin ta sosai.
*Shekarar Bilal takwas* sai kasuwar ma ta durk'ushe, sakamakon wata mata da ta shigo rayuwar ta da sunan kasuwanci, da farko sai da ta sa Khadija ta yarda da ita ta hanyar yi mata ciniki na milyoyin kud'i sau ba adadi, sun saba sosai ta na bata kaya za ta biyata kud'i a take, daga k'arshe sai ta nemi ta bata kayan milyoyin kud'i, ba fargaba Khadija ta kwashe duka kud'in ta ta bayar aka siyo mata kaya, wannan karan matar cakin (check) kud'i ta bata da nufin ta je banki ta cira, sai da ta d'auki kayan sannan Khadija taje cirar kud'i, cakin k'arya ne na bogi, hakan ne ya jefa Khadija matsala har aka mata taro ana neman mik'a ta hannun kwalawa🤣, sai da Usman da Ashir su ka zo kad'ai aka samu matsalar ta mutu anan su ka dawo gida, ba girgiza ko damuwa a tare da ita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Ta ci kad'an wallahi, ita da Allah, ya na sama ya na gani, dan haka na barta da shi."
Usman ya si bata wasu kud'in amma tace kawai ta hak'ura da kasuwanci, tun da dama ta na yawan samun irin wannan matsalar, wannan karan dai ne abun ya girmama, tunda ba ta rasa ci da sha ba da duk abun buk'ata, dan haka ta hak'ura tun da akwai wanda ba sa son ta da arzik'i, ya nuna mata wannan ba shine maslaha ba amma ta rufe ido tace ba ta so, dole ya rabu da ita kawai ba dan ya so ba, a lokacin ta rage hada hada da jama'a Aziza kuma ta k'ara girma an zama yan mata, lokacin ne ta fara sakawa rayuwar su ido saboda yanda ta ga d'an uwan ta na rawar k'afa akan Khadija da d'an ta Bilal, in dai har yayi tafiya ya dawo to na tsawon kwana biyu ko uku Khadija ba ta girki in ka cire ranar da zai dawo, saboda Usman na da buk'ata sosai, idan ya dawo sai ya yi kwana uku bai lek'a waje ba idan ba masallaci ba, hakan ne ya sa yace ba ita ba shiga madafa sai dai in ruwan zafi za ta d'ora mu su na wanka, a cikin kwanakin da zaiyi kusan kullum sai sun fita cin abinci ko shan ice crime ko ya mu su siyayya ko kuma sada zumunta gidan yan uwan shi da yan uwan ta, yayin da su ke jin dad'in rayuwar su sai Aziza ta fara zargin akwai wani abu a k'asa, yanda ya ke komai dai matar shi da d'an shi abun na bata mamaki, musamman idan Kaltume ta zo ta ga sun shige d'aki ana ta dariya da ba ta yan k'unshe k'unshe, sai kawai tace sun mallake shi ne, (d'an adam butulu), a hankali sai ta fara fad'awa yan uwan ta su Hassana, su kuma ba tunanin komai su ka yarda, dan suma sun fahimci hakan, musamman idan ya zo daga tafiya ba ya fita wani lokacin gidan su ma sai ya kwana ya hantse baije ba, su kuma iyayen da yake su na da hankali sai suke ganin wata buk'atar ce ta sa haka, a hankali sai suka fara canza mata fuska, ko alheri ta musu sai su k'i karb'a, ana haka wata rana k'anwar shi *Rabi'a* ta zo neman jari wajen shi za ta fad'ad'a kasuwancin ta, rashin sa'ar da ta yi Usman kwanan shi biyu da dawowa, sai yace mata ba ya da kud'i yanzu, amma ta yi hak'uri ta dawo nan da kwana uku, ita kam a ganinta wannan k'aton gidan da suka sake ta kalli Khadija ta ganta mulmul cikin rantsetsen leshe, sai taga ai k'arya ne ma ace babu kud'i a gidan nan (🤣🤣🤣), sai kawai ta tashi rai b'ace ta na gunguni, Khadija ce ta dawo da ita ta zauna ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko kud'in da yan uwan ta ke bata ta mik'a mata, sai da ta kalle ta sama da k'asa ta kalli Usman tace "Dama akwai kud'in kawai tsoron bani ka ke saboda ba ta yarda ba, to ki bar shi nagode."
Ta na fad'ata mik'e ta bar gidan, Usman kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "Waya saki? Keta tambaya ko ni? Yanzu gashi kin ja k'aramar yarinya za ta fad'a mana magana."
Murmushi ta yi baiwar Allah ta b'oye abin da ke ran ta tace "Allah huci zuciyar ka, ba na fatan ganin b'acin ran ka a lokacin da ka ke cikin yanayin farin ciki."
Tun fa daga ranar su ka sake kafawa Khadija k'ahon zuk'a, sai dai ba su tab'a yarda sun bari iyayen su sun sani ba, dan sun san iyayen su yan a mutun Khadija, za su iya b'ata mu su fiye da tunani Saboda ita, amma kullum buri da addu'ar su Allah ya kawo wata gidan wacce za ta fanso d'an uwan su daga sharrin Khadija, babban abun haushi shine lokaci da su ka had'u da Usman gida su ka saka Kabir da ke bi mi shi a cikin maza ya mi shi magana ya k'ara aure, murmushi ya yi ya kalle shi yace "Me ya sa zan k'ara aure?"
Shi dai Kabir ya fad'a ne ba da wata manufa ba, dan shi ba ya manta alkairi kuma ya na k'aunar Khadija, cewa ya yi "Ko ba komai ai ka k'ara saboda ka samu zuri'a dayawa."
Cikin bacin rai Usman yace "Wallahi, da ace wani ne ba kai ba ya fad'i wannan maganar, da sai na fad'a maka kalmar da har ka mutu ba ka manta ba, kai ba dan ma butulu bane har Khadija ce za ka yi fatan a k'arawa kishiya? To jini da kyau, kar ka sake min wannan maganar, sannan duk wani mai wannan banzan tunanin a gidan nan ma ya daina, dan za mu iya samun matsala da mutum."
Hussei na ce tace "Yanzu yah Fodio saboda an ma ka maganar aure shine ka ke wannan kumburin? Na ga dai da ba'a aure ai da ba ka aure ta ba, kuma k'ara aure sunna ce ta *ma'aiki*, bugu da k'ari za ka k'ara samun ya'yan da za su gaje ka."
Murya kasa k'asa yanda ba zaiji ba Rabi'a tace "To ba sai ta ba shi damar yin hakan ba, shi fa a d'aure ya ke ba ya da katab'us sai yanda ta yi da shi."
Duk da ba duka Usman ya ji ba, amma dai ya ji kalmar k'arshe ta sai yanda ta yi da shi, cikinjin zafi ya juyo ya kife ta da mari, zai k'ara mata wani marin Hajia ta d'aga mi shi hannu, huci ya dinga yi kafin yace "Wallahi dukanku butulu, kun manta alkairi kuma kun manta hallaci, Khadija bata cancanci wannan daga gare ku ba, ko ba komai ita uwar d'ana ce, ita da Bilal sun fiye min komai a duniyar nan, ita kad'ai ta bani farin cikin da ku ma da ke yan uwana ba ku ba ni shi ba kafin zuwan ta rayuwa ta, dan haka in dai har ku na son zama da ni to dole harshenku ya san me zai dinga fad'a akan mata ta."
Ya na fita Hajia ma ta mu su fad'a sosai tare da tuna mu su baya, daga ranar kuma ba su sake yarda sun b'ata Khadija ba a gaban iyayen su bare kuma Usman, amma abin takaicin shine k'iyayyar da su ke ma Khadija sai ta shafi har Bilal, dan yanda su ke ganin Bilal na wahalar da mahaifin shi, yaro ya zama saurayi amma kamar k'aramin yaro, ba ma in sun had'u da shi gidansu Hajia, ya kan zo da kayan ciye ciye ma su tsada da kyau da dad'i, duk abincin da za'a mi shi tayi ba zai ci ba, haka mahaifin su malam Ali zai dinga biyewa yaron ya na siyo mi shi duk abin da ya ke son ci, to fa ana hakane har Allah ya had'a Usman da Haseenah, lokacin ya na yawan zuwa wajen wani shago da ke can wajen filin kokawa saboda wasu kaya da ya ke kawowa mai shagon, a nan ya had'u da Haseenah wacce a lokacin ta samu exam (brève) d'in ta ta na zaune gida, baban ta ne ya tilasta mata komawa makarntar islamiyya dan ta k'ara samun ilimin addini, a lokacin har nik'abi take sakawa da dogon hijab, wannan nutsuwa da hankalin na tane su ka sa Usman jin kamar ya samu wata Khadija, fatan shi shine ta zama kamar yanda ya ke tunani, bayan ya yi tambaya a kan ta an fad'a mi shi yarinyar kirki ce daga gidan mutanen k'warai, sai kawai ya gabatar da kan shi a matsayin yana son auren ta, duk da bai cika magana akan matar shi ba, amma ya fad'a mata ya na da mata d'aya da yaro d'aya, kuma ya na matuk'ar son su, a lokacin da su ka fara soyayya Usman na bata lokaci wajen waya da Haseenah har dare, sannan duk abin da ta yi ya kan yaba hakan kamar d'abi'ar shi ce, amma a tunanin Haseenah matar shi ba ta da kulawa ne shi ya sa har za ta yarda ya na waya da ita tsawon dare ko ya na gari, abin da kuma ba ta sani ba shine duk lokacin da ya ke wayar da ita to ba ya gida, Khadija kuma ba ta damuwa saboda ta san in baya gida yana tare da su Murtala, ta na ba shi lokaci sosai da ya ke jin dad'in rayuwar shi shima kamar yanda ya ke wuni tare da ita da safe har zuwa yamma, ko kwalliya ta yi taji yana kod'ata sai tace wai uwar gidan shi ba ta yi shi ya sa idan ya ganta da kwalliya kamar ya ga matar aljanna, hakan ya sa ta sawa ranta ta na zuwa gidan za ta cinye yak'in ba tare da tasha wahala ba, amma kuma gashi Mariya ta kawo mata wani labari da ya sa har ta fara had'awa da malamai.
_Toh, ko tunanin Usman ya fad'a mi shi daidai? Shin Haseenah za ta zama kamar yanda ya d'auka? Ko kuma dai *kallon kitse ne ya ma rogo*?_
*Mu koma labari*
Ko da ya dawo daga kan Bilal kai tsaye falon shi ya wuce, sak'o ya turowa Khadija ta same shi falo haka ma Haseenah da ke d'akin ta, hakimcewa ya yi ya na jiran zuwan su, (da alama Usmanu yan mulkin sun motsa, yau kam duk wacce ta yi wasa za ta gane shayi ruwa ne 😉), kusan a tare su ka shigo falon sai Khadija da ta k'ara da sallama, zaune su ka yi su na fuskantar shi su na kallon shi, d'ago kan shi ya yi ya kalli Haseenah ya kalli Khadija kafin yace "Kun gaisa ne da safen nan?"
Khadija da tasan waye mijinta ne ta yi saurin cewa "Sosai ma, har falo ta same ni ai, mun gaisa da ita."
"Da kyau." Ya fad'a ba annuri kafin ya d'ora da "Ku zuba mana abinci mu ci."
Satar kallon shi Khadija ta yi dan tasan ya same ta tana karin kummalon ta, amma jin haka daga bakin shi da kuma ganin yanayin shi ya sa tasan yau ba ya yanayin wasa, dan haka ta mik'e tare da Haseenah da ke ta wani yauk'i kamar za ta karye, murmushi ta mata tace "Kinga amarya zauna, ki zauna zan zuba."
Ci gaba ta yi da zuba ma kowa har ta gama ta aje farantin a gaban shi kafin ta matso kujerar ta kusa da shi, sai da ya fara saka hannu tare da bismillah sannan su ma suka saka, Haseenah dama haushi ne kamar ya kashe ta, Khadija kuma a k'oshe take neman agaji take, a tare su ka cire hannun su suna kallon shi, shi ma kallon su ya yi yace "Me ku ke nufi?"
Cikin wata shegiyar shagwab'a Khadija tace "Mun k'oshi."
Duk daba kuzari a tare da shi sai da ya murmusa yace "Ku na nufin ni kad'ai za ku bari? Ai ba ku isa ba, dan haka ku mayar da hannuwan ku."
Kamar za ta fashe da kuka ta shafa cikin ta tace "Ciki na fa zai fashe, ka ci kawai sai ka had'a da nawa ka ci."
Sama da k'asa ya harare ta yace "Sannu mai wayo, kenan ni na cika cikin nawa? To na k'i wayon."
Mik'ewa ta yi tace "To bari na je na amaye wanda na ci sai na dawo mu ci gaba ko?"
Da gayya Khadija ta dinga tafiya ta na wani juya k'ugunta, mazaunan ta na kad'awa yanda su ke so, sai da ta kai k'ofar fita ta juyo ta kalle shi dan dama a sanin da tawa mijinta ba ta ba da baya bai bita da kallo ba, su na had'a ta ga ya wani saki baki ya na kallon ta, cije leb'e ta yi ta kashe ma sa ido d'aya ta fice da murmushi, Haseenah Usman ta bi da kallo ganin ya wani wagale baki har da rumgume hannaye ya na kallon ta, sai da yaga ficewar Khadija ya sauke wata sayayyar ajiyar zuciya da murmushi a fuskar shi wanda shi kad'ai ya san ma'anar shi, a hankali ya zuro hannun shi cikin farantin da nufin ci gaba da cin abincin shi sai ya lura da Haseenah da ta kafe shi da ido, saita nutsuwar sa ya yi yace "Ya dai?"
Ita ma had'e abin da ke ran ta tayi tace "Ranka shi dad'e, wai me ya sa aunty Khadija ke jin dad'in anfani da gilashi a kowane lokaci? Ba ta tsoron ta samu matsala a idon ta."
Kallon ta ya yi ya na tunani, bayan gamsuwa da zuciyar shi sai kawai yace "Haseenah kema yanzu iyalin gidan nan ce, ba wani abu da za'a b'oye mi ki, Umman Bilal na fama da larurar ido ne, kuma anyi neman maganin amma har yanzu shiru ba labari, sai dai har yanzu ba mu cire rai da rahamar ubangiji ba, mu na sa rai wata rana za ta samu lafiya da yardar Allah."
D'auke idon ta ta yi daga kan shi ta kalli k'asa da murmushin jin dad'i a ran ta kuma ta furta "Ashe ma makauniya ce, gilashi shine idon ta, hum."
D'agowa ta yi tace "Allah sarki, Allah bata lafiya."
"Ameen." Ya fad'a ya na cire hannun shi ya wanke cikin wata k'aramar roba mai d'auke da ruwa, mik'ewa ya yi ya kalle ta yace "Zan d'an shiga d'akina na kwanta, misalin *11:00* sai ki tashe ni."
Mik'ewa ta yi cikin kwarkwasa tace "Ni kad'ai kenan zan zauna? Gaskiya a'a sai dai na bika mu je tare."
Kallon ta ya yi ya na sauke ajiyar zuciya yace "Haseenah kenan, kedai kawai ki na so ki hana ni bacci ne, amma idan ba haka ba me zai hana ki je wajen yayar ki."
Cikin sanyin jiki tace "A'a gaskiya, gwara na zauna d'aki na ni kad'ai."
Da mamaki sosai ya kalle ta yace "Me ki ke nufi? Haseenah akwai wani abu da ake mi ki a gidan nan da ba kya jin dad'i ne?"
Wani murmushi ta yi da bai kai zuci ba tace "Ba komai fa, kawai ka je ka kwanta abin ka."
Rumgumo ta ya yi jikin shi su ka nufi d'akin na shi ya na fad'in "Ai sai kin taimaka min kafin na yi baccin ko?"
Su na shiga d'akin ya cire doguwar rigar shi ya kwanta, hijabin ta ta cire k'ananan kayan ta su ka bayyana, bayan shi ta kwanta ita ma ta na shafa kan shi har zuwa kunne, ba tare da magana sai kuwa bacci ya d'auke shi, a hankali ita ma sai bacci ya yi awon gaba da ita, daga nan fa su ka shiga baccin su hankali kwance.
Khadija kuma na falo ita da Uwani su na ta hira su na kallo, har ita ma Khadija ta kwanta a kan kujera bacci ya soma d'aukar ta, *12:15* Uwani ta daddab'a k'afar Khadija ta farka, agogo ta kalla tace "Aunty, na ga sha biyu har ta wuce amma Bilal bai dawo ba."
Da sauri ta zabura ta mik'e zaune ta na fad'in "Abban shi ya fita ne?"
"Gaskiya ban ga fitar shi ba, dan har yanzu motar shi na waje."
Wayar ta ta d'auka ta kira shi amma ta na silent, dan haka ba ta sake na biyu ba kawai ta kira lambar Naseer, ya na d'auka ya fara da "Autar Hajia ya ake ciki ne?"
Cikin shagwab'a tace "Yaya na, Bilal ya na makaranta har yanzu ba'a d'auko shi ba, kuma na kira wayar Abban shi ba ya d'agawa, shine na ce ko za ka saka cikin yaran shagonka su d'auko min shi?"
Daga in da ya ke ya mik'e yace "Abu mai sauk'i, dama zaune na ke ina kallon titi, bara na isa da kai na na d'auko shi."
"Yawwa yah Naseer nagode."
"Uhum! Kar ki damu."
Aje wayar ta yi ta na mamakin abin da ya sa Usman mantawa da gudan jinin shi a makaranta, sharewa kawai ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani, ki duba madafa ki ga idan babu kowa sai ki d'orawa Bilal indomie kafin ya dawo, dan kinsan abinci ya ke fara nema da ya sauko."
"To aunty." Ta fad'a ta na tashi ta nufi madafar, ba kowa a ciki dan haka ta fara abin da ya kai ta, sallama ta ji tun daga tsakar gidan, lek'owa ta yi dan madafar a bakin k'ofar shiga duka b'angarorin take, su Rabi'a ne da kuma matar Kabir *Jauza'u*, amsawa ta yi ta na fad'in "Aunty Rabi'a sannun ku da zuwa."
"Yawwa Uwani sannu, aiki ake?" Cewar Rabi'a, k'ofar Haseenah su ka nufa Rabi'a ta sa hannu ta bud'e sai ta jita a rufe gam, kallon Uwani ta yi tace "Amaryar ba ta nan ne?"
"Ta na nan, amma ina jin kamar ta na d'akin Abban Bilal." Ta fad'a da nuna mu su falon na shi, Jauza'u ce tace "Shikenan bara mu shiga wajen aunty Khadija to."
Da sallama su ka shigo a bakin su, Khadija da ke zaune ta na danna waya ne ta d'ago ta kalle su, sharrin shaid'an da zafin kishi ya sa Khadija tuna irin k'iyayyar da yanzun su ke mata, a ganin ta suna matuk'ar farin ciki da k'ara auren Usman, su na jin dad'i saboda an mata kishiya, sai kawai ta ji ba ta buk'atar sakar mu su fuska kamar baya, fuska ba fara'a ta amsa da "Wa'alaikum salam."
Suma k'asa su ka zauna Jauza'u na fad'in "Aunty Khadija ke kad'ai zaune?"
Kallon ta ta yi tace "Umm."
"Ina kwana aunty Khadija?" Cewar Jauza'u, ta na ci gaba da danna wayar ta tace "Lafiya k'alau, ya ki ke?"
Duk da Jauza'u ba haka ta saba gani ba ammata dake tace "Lafiya lau, ina Bilal?"
Ba tare da ta d'ago ba tace "Bilal ya na zuwa yanzu daga makaranta."
Sai lokacin Rabi'a tace "Ina kwana?"
D'agowa ta yi ta jefe ta da wani banzan kallo kafin ta yi k'asa da kan ta tace "Lafiya, ya gida?"
Sai da ta harare ta ta wutsiyar ido kafin tace "Lafiya lau."
Shiru ne ya d'an ratsa wajen kowa da abin da ke sak'awa a ran shi, Jauza'u kam duk ta ji ba dad'i dan har ga Allah ta na k'aunar Khadija, saboda ta mata abin da ko mijin ta bai iya yi mata ba a lokacin da baya da k'arfi, su na haka babu mai magana shiru kamar ba gidan wannan Khadija ka zo ba wacce ke washe baki idan ta yi bak'o har ya tafi ta na rawar jiki, amma yau gashi sai wani shan k'amshi take.
Usman ne ya zabura ya tashi ya na rarraba ido, da sauri ya kalli agogon da ke fuskantar shi, " *12:45*." Shine abin da ya fad'a da k'arfi har ya sa Haseenah tashi zaune ita ma, da hanzari ya sauka daga kan gadon ya na d'aukar doguwar rigar shi ya zura, makulin mota ya wawura a gefen gadon ya juya zai fita Haseenah tace "Wai saurin me ka ke ne haka?"
Ba tare da ya juyo ba yace "Yarima zan d'auko, lokacin tashin su ya wuce sosai."
Da sauri ta duro daga kan gadon ta tari gaban shi tace "Amma haka za ka fita ko wanka ba ka yi ba?"
Ture ta ya yi daga gaban shi yace "Wani wanka dallah, yaro na can tsaye ya na jira na, ban san a wane hali ya ke ba."
Fita ya yi daga d'akin ta bishi da kallo, k'wafa ta yi ta fita daga d'akin ita ma kai tsaye madafa ta nufa da tunanin d'ora silalar nama sai ta yi wanka, ta na bud'a k'ofar ya yi daidai da Uwani ma za ta fito, hakan ya sa Uwani bige ta ba ta sani ba, rik'e hannun ta tayi da ta bugu ta na ma Uwani kallon tsana, cikin jin zafi da b'acin rai ta kife Uwani da marin da ya sa farantin indomien zubewa k'asa saboda yanda ya zo a bazata , dafe kunci ta yi ita kuma ta na fad'in "Dan uban ki ni za ki bige? Wacece ke a gidan nan? Me ma ya kawo ki madafar nan? Ko kin manta yanzu ni ke aiki a ciki ko wacce ta aje ki sai na yarda za ta shigo? To ki saurare ni da kyau, daga yau ba na son sake ganin k'afar a madafar nan in har aiki na ne, in ba haka ba kuma zan ci uwar ki a gidan nan sannan na sa mai gida ya yi waje da ke, kinji ni ko?"
Kai Uwani ta d'aga alamar ta ji, da hannu ta mata alama tace "Fitar min daga nan, k'azama kawai 'yar matsiyata."
Kasancewar Uwan irin mutanen nan ne masu jin zafin magana, wanda da ka zage su yafi sauk'i ka yanke su da wuk'a, hakanne ya sa ta fito tana kuka tana jin k'una na kalmar 'yar matsiyata da ta yi da cewa za ta ci uwa ta, ta na nufowa falon Khadija ta tsinkaye ta, dan haka ta tashi da sauri ta nufe ta, sai da ta rumgume ta a jikin ta ta fara tambayar ta lafiya? Cikin kuka ta ke fad'in "Aunty amarya ce tace wai kar na sake shiga madafa in ta na aiki."
Shiru Khadija ta yi tana sauke huci kafin ta d'ago Uwani daga jikin ta tace "Haka ta fad'a mi ki?"
Kai kawai ta d'aga mata, d'orawa ta yi da "Shikenan Uwani yi hak'uri, yanzu ina indomien da na saki dafawa?"
"Ta na can ta zube." Ta fad'a tana share hawaye da hijabin ta, da k'arfi tace "Ta zube kamar ya?"
"Lokacin da ta mareni ne faranti ya sub'uce a hannu na ta zube."
Da k'arfi ta dafe k'irji tace "Mari kuma? Ta mare ki fa ki ka ce?"
Kai Uwani ta d'aga alamar eh, share mata hawayen fuskar ta ta yi tace "Wuce d'aki Uwani ina zuwa, zanji dalilin marin ki, in ba ta san darajar mutane ba ni na sani."
Za ta wuce madafar Uwani ta rik'o hannun ta tace "Dan Allah aunty Khadija ki yi hak'uri, na yafe mata wallahi, ba na so saboda ni ku samu matsala."
Fincike hannunta ta yi tace "Uwani kin tab'a ganin b'acin rai na?"
"A'a." Ta fad'a har da girgiza kai, "To ki wuce d'aki kamar yanda na ce." Ta na fad'a ta nufi madafar a matuk'ar hassale, daidai lokacin kuma mai gadi ya bud'e k'ofa da motar Usman da ta motar Ashir ta danno ciki, Ashir na kusa da gidan ya ga motar usman, dan haka ya kira shi ya fad'a mi shi ya na tare da Bilal dan haka ya juyo su ka dawo.
Khadija kam na shiga ta samu Haseenah ta wanke naman zabbi ta zuba a tukunya za ta kunna wuta, sai da ta tsallaka indomie da ke zube k'asa kafin ta isa gare ta, cikin gadara ta tsaya bayan ta tace "...
_Wata yau za ta gane kuren ta fa._😉
*Allah ka sa mufi k'arfin zuciyar mu.*
21/01/2020 à 13:34 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*14*
"Haseenah, Uwani ta fad'a min abin da ya faru, kuma har ta fad'a min ma wai kin mare ta, shin hakane?"
Juyowa Haseenah ta yi cike da rainin wayo tace "Ki cire wai, gaskiya ne abin da ta fad'a, ko za ki rama mata ne? Sai ki tabbatar min yar aikin gida tafi matar gida."
Wani murmushin gefen labb'a Khadija ta yi kafin tace "Ko kinsan kin mana b'arin abincin da yarima zai ci?"
Ba tare da ta juyo ba tace "Ban san wani yarima ba a gidan nan, sai Bilal kawai, wanda na ke da tabbatacin ba shi kad'ai bane yaron da zai rayu a gidan nan, k'annan shi na nan zuwa duniya nan gaba kad'an."
Wata dariya Khadija ta saki har da rik'e ciki kafin tace "Nagode Allah da ki ka iya tuna Bilal shine babban yaron da ya fara zuwa duniya kuma a gidan nan, hakan ya tabbatar min da mai hankali na ke zaune."
Kallon ta ta yi sosai tace "Kasancewar Bilal d'an farko a gidan nan ba shi ke nuna zaifi sauran yaran da za su zo daraja ba, kamar yanda jimawar mahaifiyar shi a gidan bai sa matsayinta yafi nawa ba, dukan mu mata ne kuma matan Usman a gidan nan, aljanna ki ke nema haka nima ita na ke nema."
Juyawa ta yi ta d'auki wuk'a hakan ya sa Khadija fizgo wuyan rigar ta da ko hijabi babu a jikin ta, sosai ta shak'e ta tace "Dama abu d'aya na zo fad'a mi ki, Uwani ba wai yar aiki ba ce a gidan nan kamar yanda ki ka d'auka, kuma mai gidan ma yasan da haka, ko shi bai isa ya mata abin da ki ka mata ba, dan haka ya zama na k'arshe da kalma marar dad'i za ta shiga tsakanin ki da ita bare duka, na yarda ki mata fad'a idan har ta yi ba daidai ba, amma banda cin zarafi a ciki, ki kiyaye nan gaba."
Sakin rigar ta ta yi za ta fita kawai Haseenah ta ja tsaki tace "Idan shi tsoronki ya hana ya mata magana, ni nan Haseenah zan iya, kuma ki sani shigowa ta gidan kamar shigowar rahama ne da sauyi."
Murmushi Khadija ta yi tace "Ina fatan dai ki na da kud'in biyan bokan na ki, dan in ba ki shirya ba za ki sha wahala wajen karb'ar gidan nan a hannu na."
Juyawa ta sake za ta fita Haseenah ta kuma cewa"Aikin banza, ai ba boka ba malam wallahi zan karb'i gidan nan, makauniyar banza makauniyar wofi, ai ba a banza Allah ya hana ki idon gani ba."
Wannan maganar ta makauniya ita ce ta tsayawa Khadija a rai, da k'arfi ta juyo ta matso daf da ita tace "Me ki ka ce?"
Yanda taga idon Khadija sunyi ne ya sa ta kasa cewa uffan, lumshe ido ta yi ta bud'e ta sauke su a kan ta tace "Haseenah ina da yak'inin ban tab'a yin fad'a ba tun da k'uruciya ta har zuwa girma na, sai dai ina ji a jiki na cewa fad'a na zai yi matuk'ar muni, dan haka ina so ki kiyaye, ba na so na yi abin da zai b'ata min suna ko kuma zuri'a ta."
Cikin rashin gamsuwa da abin da ta fad'a tace "Wai ke Khadija me ki ke d'aukar kan ki? Mummuna ko me? Akan komai sai kin nuna ke dabance, to ba zan d'auka ba wallahi, kar ki k'ara cewa za ki nuna min izzar ki dan ba ta shafe ni ba."
Matsowa Khadija ta yi ta sa hannu ta ture ta baya ta na fad'in "So ki ke kisan me na d'auki kai na? Na ce ki na so ki sani ne?"
Hankad'ar da ta mata ce ta sa ta yi baya sosai har ta bige tukunyar da ke kan wuta ruwa da naman ciki ya watse, lokacin da hannun Haseenah ya bugi tukunyar ta ji zafi, hakanne ya tilasta mata sakin razananniyar k'ara har duk gidan na amsawa, Usman, Naseer da su Rabi'a da ke zaune su ka hanzarto su ka nufo madafar, ganin Khadija tsaye ta na kallon Haseenah da ke rik'e da hannu ta na kuka ne ya sa Usman saurin k'arasawa, rik'o hannun Haseenahr ya yi yana kallon abin da ya zube ya kalli Khadija yace "Lafiya? Me ya faru ne?"
Cikin tafasar zuci tace "Kallon me ka ke min? Ka tambaye ta mana, ni ce za ka tambaya?"
Rabi'a ma matsawa ta yi kusan Haseenah tace "Haseenah me ya faru ne wai? K'onewa ki kai?"
Girgiza kai ta yi cikin zubar da hawaye tace "A'a, ba k'onewa na yi ba."
Usman ne ya d'ora da "To me ya faru?"
Fashewa ta yi da wani kukan, hakan ya sa Usman mayar da kallon shi ga Khadija yace "Khadija me ya faru, naga ai daga ke sai ita ne a madafar ko? Me ki ka mata haka?"
Kallon shi ta yi cikin ido da niyyar fad'in abin da ya faru, amma ta na kallon shi sai wannan kwarjinin da haiba da rashin sabo na rashin samun matsala da ba su tab'a yi ba ta yi k'asa da kan ta, cire gilashin ta tayi ta fashe da kukan da babu sauti, ai tuni sai hankalin Naseer ya tashi, da gaggawa ya matso kusanta shima ya kalli Haseenah yace "Wai me ya faru ne? Ke ki fad'a mana."
Cikin kuka Haseenah ta kalli Naseer d'in tace "Ni ban san me ya faru ba, na dai san na yiwa mai aikin nan magana kan cewa kar ta sake shigowa madafar nan in ina aiki, banji shigowar aunty Khadija sai ji na yi ta tura ni gaba kawai, shi ne na..." Sai kumata fashe da kuka.
Da tsantsar mamaki Khadija ta kalle ta, kallon ta Usman ya yi yace "Gaskiya ne abin da ya faru kenan?"
Mayar da gilashin ta yi ta kalli Usman tace "Babu abin da zan fad'a ma ka, ka d'auki mataki kawai."
Kallon Haseenah ta yi tace "Ba zan ce ki ji tsoron Allah ba, amma zan mi ki kashedi da kar ki sake kira na da makauniya, in ba haka ba kuma wallahi zan mugun sab'a mi ki fiye da tunanin ki."
Juyawa ta yi ta kama hannun Bilal da na Naseer da nufin fita, k'yam Naseer ya tsaya ya kalli Haseenah yace "Kamar k'anwa na ke kallon ki, dan Allah kar ki bari wani abu na rashin kyautatawa ya shiga tsakanin ki da yer uwa ta, ita d'in kamar rayuwar mu ce, ban tab'a jin wanda ya yi k'ok'arin kiranta da makauniya sai yau, dan haka ki kiyaye dan Allah, ku zauna lafiya sai mijinku ya yi farin ciki da ku."
Juyawa ya yi su ka fita, a daidai k'ofar shiga falon Khadijar su ka tsaya, dafa kan ta ya yi yace "Ki yi hak'uri kinji yar autar mu, ina tabbatar mi ki hakan ba zai sake faruwa ba, ki daina kuka kinji ko."
Cikin shashek'ar kuka tace "Shikenan yaya na, kar ka damu na dain, ka tafi gida kawai, amma dan Allah kar ka bari kowa ya ji a gida, wannan matsalar gidan nan ce."
"Shikenan zanyi, amma ki min alk'awarin hakan ba zai sake faruwa ba."
"Nayi." Ta fad'a da murmushi, shafa kan Bilal ya yi yace "Yaro na sai anjima ko, yaushe za ka shigo wajen matar?"
Ba walwala a tare da shi yace "Tonton (uncle) da Momy za ta yarda da na bika gida, gaba d'aya yanzu gidan nan ba dad'i, Abba ma ya daina cin abinci da mu kuma ba ya..."
"Bilaaaal." Khadija ta kira sunanshi, wucewa kawai Naseer ya yi su ma suka koma ciki, d'akin Bial su ka nufa dan ta taimaka masa ya canza kaya Uwani ta yi sallama, juyowa ta yi ta kalle tace "Uwani ki je gida kawai, ki bari sai gobe ki dawo."
"To aunty, amma Abban Bilal yace wai ki same shi a d'akin shi yanzu."
Sai da ta d'an kawar da kai kafin tace "Shikenan, ina zuwa."
Kallon Bilal ta yi tace "Ka je ka cire wannan kayan sai ka watsa ruwa ka canza wasu, ina zuwa yanzu ka ji."
Ciki ya shiga ita kuma ta wuce d'akin Usman, a falon shi su ka ci karo da su Rabi'a za su tafiya, amma ko kallon ta Rabi'a ba ta yi ba saboda a tattaunarwa da su ka fara da Usman sai kare Khadijar ya ke, Jauza'u ce tace "Sai anjima aunty Khadija."
"Ki gaida gida Jauza'u." Cewar ta ta na shiga d'akin, zaune ya ke akan kujera da ke gaban madubi in da Haseenah ke zaune bakin gado, ita ma bakin gadon ta zauna kamar yanda ya nuna mata, ya na kallon fuskokin su ya gyara zama yace "Baiwar Allah, a gaskiya yau d'in nan na ji kunyar abin da ya faru a gidan nan, sai da zuciyata ta wahala kafin na yarda Khadijata ce ta aika abin da ta aika ta, saboda ni dai nasan tawa Khadijar mai hak'uri ce da kawar da kai, amma ban san ya akayi wannan karan hak'urin ta ya gaza ba, ni da na ke mata fatan ta kai k'adamin da za ta dafa dutse har ma ta shanye romonsa, amma gashi shaid'an na san min yawo da hankalin ta wajen tilasta ta yin abin da bai dace ba, Khadija, ya haka? Ya akayi ki ka bari haka ta faru? Me ya tunzura ki haka?"
Tabbas a kowane lokaci kalaman mijinta su na tasiri a kan ta fiye da yankan wuk'a, hakanne ma ya sa ta kalle shi a ladabce tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ni ma sai yanzu na ke jin kunyar abin da na aikata, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, wannan alk'awari ne."
Sai da Usman ya lumshe ido saboda tsabar jin dad'i, ji ya yi kamar ya rumgumota jikin shi, sai dai a yanayin da ake ciki hakan bai kamata ba saboda tsaro, murmushi ya yi yace "Hakan ya yi kyau, Allah ya ba ki ikon cika alk'awarin nan da ki ka d'auka, kuma sai a ci gaba da kiyaye saboda gudun b'acin rana, wata rana ba'a san me zai faru ba a irin haka."
"Insha Allahu za'a kiyaye." Ta sake fad'a a ladabce, mayar da kallon shi ya yi ga Haseenah yace "Ke kuma Haseenah, ba wai zan tambaye ki me ya faru ko kuma waye mai laifi ba, a'a, zan fad'a mi ki wani abu ne da na ke ganin ya kamata ace tun farko kin san shi kafin ki shigo gidan nan, Haseenah."
Yanda ya kira sunan ta yasa ba ta da zab'in da ya wuce d'agowa tace "Na'am."
D'orawa ya yi da "Khadija dai matata ce tsawon shekara goma sha uku, shekara sha uku ba kwana goma sha uku bane Haseenah, kinga kenan k'arshen sanin juna munyiwa kan mu shi ni da ita, a wannan shekarun da mu ka d'auka Haseenah, wallahi, wallahi na rantse mi ki da Allah ba zan iya tuna ranar da zan ce mi ki wannan baiwar Allahr ta min ko da kallon raini ne bare tsaki ko bak'ar magana, Haseenah, kin ganta nan ki tambaye ta kiji yanda auren mu ya kasance, amma sau d'aya ba ta tab'a nuna min k'iyayya ko tsana ba, idan har na ce eh, to eh ne a wurin ta ko da a'a ne, idan na ce a'a haka ita ma za tace a'a, a iya zama na da ita ban tab'a ji ko a labarin ta ba cewa ta na da abokin fad'a ba, d'azu ma na tambayi me ya faru ne saboda shine adalcin da zan iya yi, amma a gaskiya ni nasan Khadija ba ta da tashin hankali ko kad'an, dan haka Haseenah ki kiyaye dan Allah, Khadija dai ita ce gaba da ke a shekaru da ma zuwa gidan nan, kuma nasan kinsan karin maganan da ake cewa *duk wanda ya rigaka bacci dole zai rigaka tashi*, ba na so ki sawa zuciyarki irin tunanin matan yanzu cewa, wai ko shekara d'ari ka samu mata a gidan mijin ta, to wata na shigowa gidan kuma tasan mijin sun zama d'aya, eh tabbas dukan ku matana ne kuma d'aya ku ke, amma ki sani Khadija ta riga kwana a gidan nan har da ma tashi, duk da Allah bai bamu 'ya'ya dayawa ba, amma dai ita ce uwar d'an da ni a yanzu na ke kallo kuma ina jin dad'i, sannan Haseenah duk da ki na ganin kamar kinsan komai a kai na har yanzu da saura, sani na a namiji ba shine sanin da ya kamata kuyi alfahari da shi ba, me na ke so?Me ye ba na so? Me ke sani farin ciki? Me ya ke b'ata min rai? Me yafi saka ni nishad'i da akasin haka? Wannan shine ya kamata ki zage damtse wajen sani, sai maganar makauniya da ki ka kira ta da shi, a gaskiya ba zan b'oye mi ki ba Haseenah rai na ya b'ace fiye da yanda ki ke tunani, me ya sa ba ki yi tunanin larura ce da Allah ya d'ora mata ba, wacce ke ma ba ki wuce ya jarabce ki da ita ba? To wannan ya zama na k'arshe da ko a mafarki za ki sake kiran da makauniya, kin fahimta?"
Haseenah da zuciyar ta ke tafasa ta ke jin kamar ta fashe da ihu, saboda ganin duk ya tattara laifin ya d'ora mata, hakanne ya sa hawaye su ka zubo mata ta d'ago kai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri, insha Allah za'a kiyaye."
Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, sai ki bata hak'uri, da fatan hakan ba zai sake faruwa tsakanin ku ba."
A hankali ta kalli Khadija tace "Ki yi hak'uri aunty Khadija, insha Allah ba zan k'ara ba."
Hannun ta Khadija ta rik'o tace "Ba komai yer uwa, ki gafarce ni nima kinji, sharrin zuciya ne da b'acin rai, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."
Cire doguwar rigar shi ya yi ya fad'a ban d'aki dan yin wanka, mik'ewa Khadija ta yi tare da hannun Haseenah tace "Ki je ki taya shi wanka, zai iya wuni bai saki maganar nan ba, amma da kin mi shi abin da ya dace sai komai ya wuce."
Tura ta tayi ban d'akin ita kuma ta fita, ta na rufo k'ofar ta jingina a jikin k'ofar ta lumshe ido, a hankali ta ji zuciyar ta na hasko mata mijin ta da Haseenah a ban d'akin, yanda ta san mijin ta da sauk'in kai da raha da barkwanci ta san yanzu har sun fara juyewa, da sauri ta bud'e ido har sun cika da hawaye, "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim." Ta furta ta bar wajen, ta na zuwa ta samu Bilal har ya shirya cikin gajeran wando da riga, *cornflakess* ta d'auko da kofi da madara ta yamutsa mi shi, ba dan ran shi na so ba ya karb'a ya na turo baki, shafa kan shi ta yi tace "Yi hak'uri mana yarima, yau ne fa kawai, kuma yanzu za'a kammala abinci."
Cikin turo baki yace "Mummy ni da wannan abun gwara ki bani ayaba na ci."
"Shikenan to." Ta fad'a ta na mik'ewa, friji (fridge) ta nufa yar k'arama da ke d'akin na ta wacce ita ta siyi abar ta, ta d'auko ayaba biyu da gwanda da ke yanke a faranti ta dire gaban shi tace "To maza ka ci."
Da sauri Bilal ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai, kuma a k'a'ida ya na zuwa gida zai samu maman shi har ta kammala abincin, fita Khadija ta yi ta bar shi ta nufi madafa, sai da ta gyara ko ina kamar babu abin da akayi b'ari a ciki sannan ta d'ora ruwan zafi, cikin sauri ta ke komai in da ta b'areye doya ta zuba sannan ta fara had'a sauce d'in.
_Tukunya ta d'ora ta zuba mai, bayan ya yi zafi ta zuba silalallan naman ragon da ke fridge wanda ya ji albasa attarugu da maggi, soya shi ta yi sosai ya soyu kafin ta kwashe, albasar da ta yanka mai yawan gaske ta zuba a cikin man, haka ma tumatiri d'anye da ta yanka da fad'i ta zuba a ciki, rufewa ta yi ta fara b'are tafarnuwa, zuwa lokacin albasa da tumatir sun rusuna sosai, kayan k'amshi da gishiri ta zuba kafin ta jajjaga ataru da tafarnuwa da poivron kafin ta jujuya sosai, maggi ta saka da yan ruwa kad'an sannan ta sake rufewa, a lokacin kuma doyar ta ta silala ta juye ta a mataci kafin ta zuba ta in da ya dace, komawa ta yi kan miyar nan ma komai ya yi daidai, k'wai ta d'auko guda uku d'anye ta fasa shi cikin wata k'aramar roba ta kad'a shi sosai, cikin miyar ta zuba ta na motsawa saboda kar ya yi gudaji-gudaji, ta na zubawa kuma ta kawo soyayyen namanta ta zuba sai ta rage wuta dan ta k'arasa dahuwa, doyar ta d'auka ta kai kan teburin d'akin Usman ta dawo ta juye miyar bayan ta fitarwa da mai gadi na shi, tsaf ta jera su akan teburin._
Ta juyo za ta fita dan yin wanka ta ji fitowar su daga d'akin, juyawa ta yi ta kalle su da murmushi tace "Barka da fitowa."
Sai da ya kalli teburin yace "Barka baiwar Allah."
Haseenah ta kalla tace "Amarya ki yi hak'uri na yi karambani, na kammala mi ki girki amma fa mai sauk'i ne, ban san ko zai birge ki ba."
Ta wutsiyar ido ta harare ta amma sai ta yi murmushi tace "Haba aunty Khadija ya ki ka wahalar da kan ki? Gashi kuma da fitar da zaiyi yanzun abinci ne zai siyo mana."
Da mamaki Khadija ta kalle ta tace "Siyowa kuma, haba dai amarya, gidan nan cike da abinci Allah ya hore, ga kuma mata ma su rai da lafiya, amma ya fita siyo abinci, a'a gaskiya sai dai in da wata larura."
Usman da ke kallon ta da murmushi ne ya taka ya isa ga kujera ya ja ya zauna, tangale hab'a ya yi ya kalli dukan su yace "Ku taimaka ni ku zuba min abincin to na ci."
Haseenah da ranta ya gama b'acewa saboda abin da Khadijar ta fad'a d'akin ta ta nufa tace "Aunty kawai ta zuba, tun da dama ita ta yi girkin, ni wanka zanyi."
Da sauri Khadija tace "Ni ma fa wankan zan yi." Amma ina Haseenah har ta fita ta shiga k'ofar da za ta sadata da na ta falon, abu d'aya da Khadija ta fahimta shine Haseenah ba ta ji dad'in abin da ta yi ba, ita kuma ta yi ne saboda ita ce silar zubar mata da girkin da ta d'ora, juyawa ta yi ita ma za ta tafi sai kuma ta juyo, idon su ne suka had'u da na Usman da ke kallonta, kamar yanda tasan ba ya iya shirya kansa da kyau in ba ita ta taimaka masa ba, hakan ta ke da yak'inin ba zai iya zuba abincin nan ba in ba wani ya zuba masa ba, dawowa ta yi ta zuba mi shi ta zauna nesa da shi tace "To maza ka bada himma."
Kwab'e fuska ya yi yace "In dai ba za ki ci ba ni ma haka."
Kallon shi ta yi tace "Gaskiya sai dai ka jira Haseenah ta zo ku ci, wanka yanzu kawai na ke son yi."
Rumgume hannaye ya yi a k'irji yace "Da alamar maganar ki ke so."
Wata dubara ce ta fad'o mata dan haka ta mik'e tace "Shikenan to ina zuwa, bara na kira Bilal."
Ta na fita ta samu Bilal a falo tace "Bilal, tashi mahaifin ka na jiran ka ku ci abinci, ina zuwa yanzu ka ji."
"To Mummy." Ya fad'a yana nufa falon, wanka ta shiga shi kuma ya na zuwa Usman ya rumgumo shi jikin shi ya na fad'in "Yarima na ya ka ke?"
Baice komai ba ya kalli Usman d'in ya na turo baki, lab'e baki Usman ya yi yace "Ko dai yaro hushi ya ke da baban sa ne saboda bai je d'aukar shi ba?"
Sai lokacin ya saki fuska yace "A'a Abba, bacci na ke ji."
Duk da girman yaron amma haka ya zaunar da shi akan cinyar shi yace "To idan mun ci abinci sai ka yi baccin ko?" A tare suka saka hannu su na cin abincin su na hira, har sun ida su na nan zaune suna ci gaba da hirar su irin ta d'a da uba Haseenah ta shigo, kallon ta Bilal ya yi yace "Sannu aunty."
Da murmushi har kunne ta amsa da "Sannu yarima, ya ka ke?"
"Lafiya lau." Ya fad'a ya na saukowa daga k'afafun Usman, fita ya yi daga d'akin Usman bai hana shu saboda ya na so ya yi magana da ita, ya na ganin fitar shi ya kalle ta da kyau lokacin da take shirin zaunawa, riga da siket ne na kanti wanda su ka kama jikin ta sosai, siket d'in ko k'asa bai gama sauka ba, sannan babu d'an kwali a kan ta, sai da ta zauna yace "Haseenah, yanzu ki na ji a jikin ki wannan kayan sun dace ki saka su a yanzu kuma har ki fito da su?"
Da mamaki tace "Ban gane ba? Me wannan kayan su ka yi?"
Murmushi ya yi yace "Ba fa mu kad'ai bane a gidan nan, wannan kayan da ya dace ki saka ne da dare lokacin da mu ka rage daga ni sai ke."
Cike da tsiwa irin ta yan zamani tace "Matsala, wannan ita ce matsalar da ake magana in dai har ka auri me mata, ba ka isa ka sake ka wataya yanda ka ke so ba, yanzu dan Allah me wannan kayan su ka yi? Na ga kai miji na ne, me ye dan na saka wannan kayan a gida na?"
Har kas'an zuciya maganar ta ta tsaya mi shi a rai, amma sai ya kawar da kai kawai ya mik'e yace "Zan fita ni sai anjima."
Binshi kawai ta yi da harara, dan yau ita zuciyar ta fal take da tarin k'unci, wani faranti ta janyo gaban ta ta bud'a kwanukan, sai da taja numfashi saboda k'amshin da ya daki hancin ta, ai kuwa zubawa ta yi sosai ta kuma ci ta k'oshi ta ma manta waya girka, dan har ga Allah abincin ya mata bala'in dad'i, ko dan ta na jin yunwa ne oho.
Khadija ma na gama shiryawa sai da ta yi sallah kafin ta cika cikin ta da kayan marmari da yan dubaru, daga nan kuma bacci ta shiga dan a huta ma rai.
Kiran sallah ne ya tashe su duka gidan, Bilal masallaci ya nufa kafin ya dawo ya shirya zuwa makaranta, Usman da kan shi ya zo ya d'auke shi su ka tafi lokacin Haseenah har ta shiga girkin dare.
*Mummyn Sultan*
*Mamienmu*
*My sweet Hawwer*
*My lovely Hawwer*
*Mummyn Ameer & Khairat*
*Sis Alawiyya*
*Sis Fusseina*
*Momyn Rasil*
_Da duk wanda baiji sunan sa ba, zaiji anan gaba insha Allah._
23/01/2020 à 13:43 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*15*
Haseenah dai a shirye take da samu zuciyar mijinta ita ma, hakan ya sa yau ma abinci ware mu su na su ta yi ta kai falon ta, sannan ta zuba maganin saboda ta na so yau ya ci na uku kenan, Bilal ta k'walawa kira tun daga madafar, hankalin shi ya tafi kan kallon da ya ke a *mbc action*, Khadija da ta fito daga d'aki cikin doguwar riga ta shadda ne tace "Bilal ba ka ji auntyn ka na kiran ka ne?"
Da sauri ya mik'e ya nufi k'ofar ya na fad'in "Banji ba Mummy." Ganin ya nufi k'ofar falon ta ya sa tace "Ta na madafa ina jin."
Da sauri ya nufi can, ya na zuwa ta mik'o mi shi kular abinci tace "Abincin ku kai da maman ka."
Jiki a sanyaye ya karb'a ya na kallon ta da mamaki, haka ya juyo ya fito ya kawo abincin maman shi na zaune, aje kwanan ya yi gaban ta ya d'ago ya fad'a kusan k'afafun ta yace "Mummy abincin mu ne wai inji aunty."
"Abinci kuma?" Cewar Khadija ta na yamutsa fuska, "Eh." Cewar shima Bilal d'in, gyara zamanta ta yi kamar wata hamshak'iya matar shugaba akan kujerar tace "Ka kaiwa mai gadi shi."
Ba musu ya d'auki kwanon ya fita da shi, ya na zuwa ma har ya samu ya na cin na shi abincin, cike da ladabi ya aje kwanon gaban shi yace "Baba *Garba* ga abincin ka."
Da mamaki ya kalle shi yace "Abinci na kuma d'an Alhaji? Ai gashi nan har na kusan kai shi k'arshe ma, ko dai makuwa ka yi."
Da dariya Bilal yace "A'a Baba, wannan Mummy e tace na kawo ma ka."
Jim ya d'anyi kafin ya janyo kwanon gaban shi ya na fad'in "Allah sarki, Hajia ta d'auka ba a aiko min da shi bane ina ga? To ka ce angode ka ji ko, ai ba'a maida abinci ba, ko almajirai na bawa tun da na koshi ma."
Juyawa Bilal ya yi Garba ya bi shi da "Sai da safe d'an Alhaji." Duk abin da ya faru akan idon Haseenah wacce ke shirin rufe madafar, k'wafa ta yi tare da mirmushi ta rufe kafin ta wuce d'akin ta, sai da ta gama shirinta tsaf cikin riga da wando masu shegen kyau kafin ta zauna zaman jiran shi.
Kamar yanda ya zamar masa jiki haka yau ma, ya na dawowa da matsananciyar yunwa kai tsaye falon Khadija ya nufa, da sallama d'auke a bakin shi, da gudu Bilal ya tare shi ya na fad'in "Sannu da zuwa Abba."
Cike da rangaji ya d'an rumgume shi yace "Sannu yarima, ya ka ke?"
Mik'ewa Khadija ta yi ta d'auko ruwa da kofi lokacin ya zauna in da ta tashi ya cire hular kan shi, durk'usawa ta yi gwiwarta d'aya a k'asa ta fara tsiyaya ma sa ruwan ta na fad'in "Ko ba ka fad'a ba alamun sun nuna a gajiye ka ke, sannan ka na tare da matsananciyar yunwa wacce ke neman jigata min kai, amma yanzu ka fara da ruwa ma su sanyi." Ta fad'a hakane lokacin da ta mik'o masa kofin ruwan.
Da tattausan murmushi a fuskar shi ya karb'a ya kafa a baki, sai da ya shanye duka ruwan kafin ya sauke numfashi mai k'arfi ya mik'a mata ta karb'a, aje wa ta yi gefe ta janyo k'afar shi ta soma cire masa takalman sa k'afa ciki, zaunawa ta yi kusan shi ta na kallon shi, ido lumshe ya ke kallonta yace "Uwar gida na sarautar mata."
Da wani tsadadden murmushi ta amsa da "Labbaika."
Cike da kasala yace "Wanka na ke so na yi, amma kuma yunwa ba za ta barni ba, yanzu ki zab'a min wanda zai fara yi."
Sai da ta d'an saci kallon Bilal da ya ke tsaye gaban telebijin ya na kallo sannan ta kalle shi tace "Ka k'arasa shiga mana wajen amaryarka, ita ce za ta zab'a ma ka, ko ka manta har yanzu kwananta ka ke?"
Wata doguwar hamma ya yi kafin ya kalle ta yace "Wai ni ban tambaye ki ba ma, yaushe ne kwananki zai zo ne?"
"Me ya sa ka tambaya?" Ta fad'a ta na shafa wuyanta, saida ya rufe ido yace "Ina so na san ranar da zan dawo hannunki ne kawai."
Shiru ta yi ba tace komai ba shi kuma ya mik'e yace "Zan shiga ciki na yi wanka, amma ki tabbatar kun shigo akan lokaci dan mu ci abinci."
Da kallo kawai ta bishi har ya shige ciki, takalman shi ta d'auka ta shiga da su d'akin ta, ya na shiga can ma wata tarairayar ya samu wajen Haseenah har sai da ya yi wanka ya canza kaya kafin su ka zo kan teburi, kallon ta ya yi yace "Ki saka hijab sai ki kirasu su zo mu ci abinci."
D'an jim ta yi kafin ta zagayo kujerar shi ta zauna akan k'afar shi ta na shafa d'an gajeran gemunshi tace "Hubbi na, ban san ko tunanin da na yi zai gamsar da kai ba, amma ina fatan ba zai zama kuskure a gare ka ba, ka ga ni amarya ce, kuma kowace amarya ta na so taga ta more amarcinta babu takura da matsi, wallahi har zuciya ta ba na jin aunty Khadija da Bilal a matsayin takura a gareni, sai dai ina so na sati d'ayan nan mu dinga cin abinci tare da kai, amma kuma na san hakan ba zai yiwu ba saboda ka saba cin abinci da iyalinka, amma gaskiya idan ba ka min wannan alfarmar ba zai sa na ji kamar ba ka d'auke ni a matsayin..."
Da sauri ya rufe mata baki yace "Wa ya fad'a mi ki ke ba iyali na bace? Ai tun ranar da aka d'aura mana aure mu ka zama iyali ni da ke, dan haka kar ki sake fad'in haka, yanzu ba dai maganar cin abinci tare bane?"
Kai ta d'aga cike da shagwab'a alamar eh, d'orawa ya yi da "Angama da wannan buk'atar, sai kuma wata idan akwai, zan wa Ummyn Bilal magana za ta fahimta, sai dai yanzu ki zuba mu su na su abincin sai ki kai mu su, ko ya ki ka gani? Tun da ai ba sa zauna da yunwa ba."
Shiru ta yi kamar za ta fashe da kuka ta kalle shi tace "Ban san me ya sa ba, amma dai da ido na naga Bilal ya kaiwa mai gadi abincin da na ba shi su ci, watak'ila bai mu su dad'i bane."
Shiru ya d'anyi kafin ya kalle ta yace "Shikenan, zuba mana abincin."
Zubwa ta yi amma kuma sam ta k'i yarda ta ci wai ita ta k'oshi, ba dan ran shi na so ba ya ci sai dan kar ta ji ba dad'i, amma har ga Allah abincin bai masa ba, domin kuwa yau ma dai shinkafa ce da jar miya, shi kuma bai fiya cin shinkafa ba da dare, sannan kuma ga ya ji da abincin ma ya yi, da k'yar ya d'an tuttura ba tare da ya nuna mata ba, su na kammalawa yace su je falon Khadija, cikin shagwab'a tace "Wanka fa zan shiga yanzu na yi shirin bacci."
Murmushi ya mata yace "To a shirya da kyau kafin na dawo."
Cikin kwarkwasa tace "To amma fa kar ka jima sosai, wallahi idan ka jima ni bacci na zanyi."
Sai da ya janyota jikin shi yace "To ki ba ni minti talatin, ya isa?"
Waro ido ta yi tace "Talatin? Ai na d'auka saida safe za ka musu, ashe wajen aunty Khadija za ka je ku sha soyayyar ku."
Yanda ta yi maganar da shagwab'a ya sa shi darawa, rusunawa ya yi yace "To ki ban minti ashirin, hakan ya yi?"
Turo baki ta yi tace "Gaskiya sai dai in ka amince da minti sha biyar, shi ma fa daurewa ne na yi wallahi, dan ban cika son yin nesa da kai ba."
Haka kawai ya tsinci kansa da kasa yi mata musu, a cewar shi kam "Angama ranki shi dad'e."
D'aki ta nufa shi kuma ya nufi falon, ya na shiga ya same su a d'akin Bilal ya yi shirin kwanciyar shi, amma da littafi a hannun shi na addu'o'i Khadija na karanta masa ya na maimaitawa, Bilal na ganin shi ya yi saurin daka tsalle ya mak'ale a wuyanshi, cike da zolaya Usman ya fad'a kan gadon ya na fad'in "Wai wai wai, wannan yaron me ka ci hakane da ka yi nauyi? Kaga ka na shirin karya ni."
Tsaye Bilal ya yi ya d'aga rigar shi ya na shafa cikin sa yace "Sarauniya ta cika min ciki na da kayan dad'i."
Tashi ya yi zaune ya na ma Khadija wani kallo yace "Me ki ka ba shi ya ci?"
Bilal ta kalla tace "Ka tambaye shi mana ga ka gashi."
Jayo Bilal ya yi ya kwantar da shi ya ja zanin rufa ya rufe shi, da kan shi ya tofa addu'a a hannu ya shafa mi shi kafin ya sumbaci kan shi yace "Yi baccinka yariman mahaifin shi, safe lafiya."
Kallon shi Bilal ya yi ya sumbaci hannun shi yace "Saida safe Abba."
Murmushi ya masa ya mik'e, zagayawa ya yi wajen da Khadija ke zaune ya kamo hannunta yace "Muje ko kema na shinfid'e ki."
Da sauri Bilal ya juyo ya kalle shi yace "Abba, yau ma ba za ka kwanta tare da mu ba?"
Dukansu ne su ka kafe shi da ido, cikin rashin kuzari yace "Zan kwanta mana, me ka gani?"
"Ka fad'a masa gaskiya, ka ce wajen amaryarka za ka koma, ba na so ka fara sawa yarona wani tunani na daban." Khadija ce ta yi maganar fuska a had'e, juyawa ta yi ta fita daga d'akin, kallon Bilal ya yi yace "Ka kwanta kaji ko, banda tambaya akan abin da bai shafe ka."
"Ka yi hak'uri Abba." Ya fad'a ya na k'ara jan zanin rufarsa.
Ya na shiga ya samu Khadija har ta cire rigar ta za ta shiga ta watsa ruwa, ta na ganin shi ta sa kai za ta wuce ban d'akin, da sauri ya rik'ota ta fad'a jikin shi ya na kallon fuskar ta yace "Me ye haka wai? Me ya ke damunki ne?"
Da k'arfi ta ture shi daga jikinta ta na fad'in "Dallah ni rabu da ni, ka koma wajen amaryarka mana, nasan ai ta na can ta na jiranka, me ka zo yi mana anan? Saida safe? To mun gode Allah tashe mu lafiya."
Ta na fad'a ta juya dan shiga ban d'akin ya sake rik'o ta, had'e fuska ya yi yace "Haseenah ta aiko mu ku da abinci, amma ba ku ci ba kin bawa mai gadi, ko me ya sa?"
Cikin k'unar zuci da wani zafi da ke cikin zuciya tace "Eh, ba zan ci ba, kuma d'ana ma ba zai ci ba, sannan ka fad'a mata karta sake aiko min da abinci dan ba zan ci ba, tun da ai bata ga yunwa a tare da mu ba."
Cike da mamaki yace "Khadijaaa, me ya sa ba za ki ci ba?"
Rik'e k'ugu ta yi tace "Kai me ya sa ka daina cin abinci tare da mu? Ita ce ta buk'aci hakan ko? To ya yi kyau, amma ka sani ni ba sakarya bace da za'a rainawa hankali, kai da ita ku ci na ku tare, ni da d'ana kuma ta ware mana na mu, ma'ana mu kad'ai ne ake son bala'in ya samemu, to ba zai yiwu ba wallahi, abincinta har abada ba zan ci ba."
A hankali ya zauna bakin gadonta dafe da kanshi ya kalle ta yace "Khadija a haka ki ka fahimci abun? Haba dan Allah, me ya sa ki ke haka? Karfa ina yabonki sallah kuma alwala ta gagare ki."
"Sai me?" Ta fad'a har da hararan shi, zunbur ya mik'e ya had'a da jikinshi da k'arfi ya had'e ta da bango ya na kallon k'wayar idonta, k'asa tayi da idon dan haka yace "Kalle ni nan."
Kallon shi ta yi kai tsaye kuma ta sake k'asa da idon ta, cikin daka tsawa yace "Kalle ni nan nace."
A hankali ta d'ago ta kalle shi, hawayen da suka taho mata ne yasa shi cire mata gilashinta ya wurgar da shi akan gado, duk da ta na ganinshi tsaye a gabanta, amma ba ta iya ganin shi da kyau, sassauta murya ya yi yace "Khadija, tun da muke da ke kin tab'a ko da hararan baya na bare kuma gaba na?"
Girgiza kai ta yi alamar a'a, k'ara tausasa murya ya yi yace "To me ya sa zuwan Haseenah gidan nan zai zama sanadin da raini zai shiga tsakanina da ke?"
Shiru ta yi sai hawayen da suka sake bulbulo mata, ganin shirun ya sa yace "Me ya sa idan dare ya yi b'acin ranki ke nunkuwa ne? Wani abu na ke mi ki da ba kya so?"
Da k'arfi tace "Eh, dubi can." Ta fad'a da nuna mi shi makeken gadonta da yatsa, kallo ya yi ita kuma tace "Na yi rashinka akan shinfid'a ta Abban Bilal, kwana hud'u ne kawai mu ka yi nesa da juna, amma jinsu nake tamkar shekara hud'u ne, Abban Bilal na..."
Had'e bakin shi ya yi da nata, dan gaskiyar magana akan abin da take magana baida kalaman da zai iya tausarta da su, tun da bai isa yace bai kusanci Haseenah ba, bai kuma isa yace ba zai k'ara ba, kamar yanda ba zai iya cewa ya datse kwanan Haseenahr ba, tsayuwar ce ya ji ta gagare shi hakan ya sa ya gangara zai kwantar da ita, da k'arfi ta ture shi daga jikin ta ta kalle shi tace "Kar ka sake had'a jikinka da nawa, ba na buk'atar ka."
Ban d'aki ta nufa tana goge bakin ta, shi kam fad'awa ya yi akan gado ido lumshe, ya yi iya k'ok'arin shi wajen gayyato nutsuwar shi amma ya kasa, haka ya mik'e ya fita daga d'akin amma har zuciyar shi ya na sha'awar kasancewa da Khadija, dan ita kad'ai ce ta iyashi yanda take samar mi shi da nutsuwa, ta na jin fitar shi ta fito ta zura farar doguwar riga mai kauri ta kwanta, kuka sai da ta ci ta k'oshi har ta godewa Allah, a k'arshe dai mik'ewa ta yi ta d'auki Qur'ani ta fara karatu, cikin k'ank'anin lokaci sai zuciyarta ta washe ta yi wasai da ita babu ko d'igon damuwa a tare da ita.
Usman kam na shiga dama a rikice ya ke, har d'aki ya samu Haseenah ta shirya cikin arniyar rigar bacci, ta na jin an bud'a k'ofa ta juya, amma abin da ya fito shine ya d'auki hankalinta, a tsaye ya ke k'yam abun har ya bata tsoro saboda ba ta tab'a ganin irin haka ba a rayuwarta, kafin ta ankara ya cakumota jikin shi ya manne bakinta da na shi ha haura da ita kan gado, dama dai rigar wata d'ogal ce, dan haka baisha wahalar cire ta ba, ya na shirin kaiwa ga gaci Haseenah ta dakatar da shi ta hanyar sauka daga kan gadon, kallonta ya yi a raunane yace "L...afi..y.a?"
Kayan ta ta bud'a ta d'auko riga ta zura, da sauri ya sauko daga kan gadon ya rumgumota ya sumbatar wuyanta, dan ba zai iya magana ba, d'an ture shi ta yi taja baya ta na kallon shi tace "Ka je kawai ka kwanta ka yi bacci."
Kamar wanda ya sha kuka haka idon shi su ka yi jawur, girgiza mata kai ya yi da k'yar ya had'a kalmar "B...ba ...zan iya ba."
Ba tare da shakka ko tunani ba tace "To ka je wajen wacce ta d'ora ka sai ta sauke ka."
Banza ya yi da ita ya kumo janyota jikin shi, ture shi ta kuma yi ta kalli idon shi tace "Wallahi kaji na rantse ko ba za ka samu abin da ka ke so ba, a gaskiya ba zan iya d'aukar wannan wulak'ancin ba, haka kawai ranar kwana na amma kaje wajen wata har ka bari ta ribace ka, shine sai ka dawo min kamar kasha wani abu, to ba zai yiwu ba gaskiya."
Ta na fad'a ta kwanta kan gadon ta ja zani ta rufa, kan gadon ya haura ya dinga shafarta ya na rarrashi, amma ko kallo bai isheta ba bare ta kalli idonshi ta tausayawa halin da yake ciki, duk da ranshi ya b'ace haka ya danne ya rumgume ta har baccin wahala marar dad'i ya d'auke shi.
😂😂😂 *Surukin sis Chappa fa yau ba kanta*
Washe gari da safe haka Khadija ta gaggauta had'a sassauk'an abin karyawa, Haseenah ma haka shayi kawai ta had'a da k'wai sannan ta yi wanka, a tak'aice dai safiyar babu mai farin ciki ko karsashi, haka Bilal ya tafi makaranta Khadija kuma ta zauna kafin Uwani ta zo.
Bayan Uwai ta zo yau Khadija ta ji bata buk'atar raini a wajen Haseenah, hakanne ya sa ta d'auko tsohuwar ajiyar gas d'in ta mai d'aukar tukunya d'aya ta sa Uwani ta d'ora silalar nama dan suyi na su girkin, su na cikin aikin kam sai ga Kaltume ta sallamo, da farin ciki Khadija ta tarbi k'awar ta, sun jima suna hira anan wajen kafin aikin ya yi nisa Khadija ta barwa Uwani ta k'arasa kula da shi, d'aki su ka koma suka dinga hira har Khadija ta tsegunta mata abinda ya faru daga zuwan amarya har zuwa jiya, nan Kaltume ta jinjina al'amarin kafin ta d'ora da "Kinsan me na ke so dake k'awata?"
A raunane Khadija tace "Sai kin fad'a k'awata, wallahi kaina ya kulle."
Gyara zama Kaltume ta yi tace "Da alama yarinyar da fitsara ta shigo, amma ki bita ta bayan gida, ki nuna mata na gaba ya yi gaba, na baya kuma sai tsinkaye, ki nuna ke ba wai shekaru ku ka yi tare da shi ba, ki nuna mata ke goggagiyace a fannin sanin mijinki, ki nuna mata na ku ba irin na su bane, sannan *wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa*, kissa, k'awata yanzu kishi ma cikin kissa ake yin shi, kada ki kuskura ki bari yarinyar nan ta gane kina kishi da ita, bare harta fahimci kuna samun matsala da mijinki, k'awata abun ya na da wuya sosai, saboda ya na buk'atar k'arfin zuciya, amma ni nasan za ki iya, saboda kin jure fiye da wannan ma, yanzu ki fad'a min yaushe ne Usman zai dawo hannunki."
"Na yarda Hajiata, amma ai ko ban fad'a mi ki ba ai kin sani"
"Hakane kuma fa." Cewar Kaltume, matsowa ta yi ta rad'a mata abu a kunne, a tare suka bushe da dariya harda tafawa da hannu, Khadija ce tace "Banda mastala dake k'awata, nasan za ki gyara ni."
Bayan fitar Usman kam gida ya nufa, ya samu mahaifinshi ma na shirin fita, saida ya duk'a k'asa ya gaishe su kafin ya zauna kan tabarmar da Hajia ke zaune, fita malam ya yi Usman ya bishi da "A dawo lafiya."
"Allah ya sa." Ya fad'a fita, kallon Hajia ya yi yace "Su Nura har sun fita ne?"
"Sun fita tun safe." Cewar Hajia, d'orawa ya yi da "Ba wani abu da ku ke buk'ata?"
Ba tare da ta d'ago ba tace "Babu komai Fodio, Allah ya yi albarka."
"Ameen Hajia."
Shiru ne ya d'an ratsa kafin Hajia ta kalle shi da kyau tace "Jiya su Rabi'a sun zo nan su ke fad'a min wani abu da ban ji dad'in sa ba ko kad'an, sai dai kuma na yi mamaki da hakan ta faru a gidan ka, duba da tsayawarka akan iyalinka da kuma hak'urin ita Khadijar."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Hakane Hajia, nima abun ya ban mamaki, sai dai koma miye ni nafi ganin laifin Haseenah, tun da Khadija ai ba yau mu ke tare ba, ko tsakani na da ita bamu tab'a samun matsalar da za ta saka mu d'agawa juna murya ba."
"Toh, haka kai ka ke gani, amma yan uwanka ba haka su ke gani ba, sunfi ganin laifin Khadija."
Murmushi ya yi yace "To Hajia koma me su ke gani ai wannan matsalar su ce, tun da dai ni ga yanda nake gani kuma na sani."
"Hakane, Allah dai ya kyauta, amma dan Allah a saka ido sosai saboda gudun abin da zaije ya dawo."
"Insha Allahu Hajia."
Mik'ewa ya yi ya zura takalmin shi yace "Hajia ni zan wuce, amma anjima da dare zan dawo, dan mun kwana biyu bamu had'u da yan rigamar nawa ba (k'annan shi)."
Daroya ta yi tace "Gaskiya kam, dan tuni ma su ka fara k'orafin amarya ta b'oye ka."
"Na sani dama ayi hakan." Ya fad'a ya na dariya, har ya juya Hajia tace "Yawwa har na sha'ada ban fad'a ma ka ba."
Juyowa ya yi ya dawo ya sunkuya, d'orawa ta yi da "Jiya matar *Issoufou* (d'an k'anin baban shi) ta haihu, an samu 'ya, idan ka samu dama sai ka je, su ma kuma matan sai ka fad'a mu su."
"Ah masha Allah, insha Allah kam Hajia zanje, amma na yi mamaki da bai kira ni ba."
"Watak'ila ya manta ne."
"Ba shakka kam."
Da haka ya bar gidan kuma ya na shiga mota ya kira Issoufou, take yace mi shi su had'u gidan yanzu zai je, haka ko akayi, ka zuwan nashi alkairi ne, domin kuwa kud'i ya bashi ma su yawa ayi hidima, bayan tafiyar shi kuma sai ya ya sa aka kawo mi shi kayan abinci, daga nan kuma makaranta ya wuce d'aukar Bilal.
Suna ta hirar su cikin farin ciki sai ga Usman tare da Bilal, sannu da zuwa suka ma sa in da ya dinga tsokanar Kaltume su na wasa da dariya, da haka ya lek'a wajen Haseenah, ya samu ta na girki ba ta gama ba, dan haka ya fita yace sai ya dawo, saida ya dawo su ka yi sallama da Kaltume, sai dai mamaki ya kama shi ganin su na cin abinci har da Bilal ma, dan shigowar shi ya ga gas a waje da tukunya, sam bai kawo a ran shi abinci su ka girka ba, haka ya fita da tunani iri iri da kuma niyyar tsayar da wannan abun, dan ba zai yarda tun yanzu su raba mi shi kan gida ba ta hanyar raba abinci.
_Ah to banga laifinka ba._🤷♀
*Luv u guy's*
24/01/2020 à 21:19 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
_*ALLAH GATAN BAWA*_
*16*
Farar miya Haseenah ta yi da shinkafa, ba wai miyar ba ta yi bane a wajen Usman, sai dai ji ya yi cin shinkafar ta gundure shi, kuma hakan baya rasa nasaba da sabon da Khadija ta mi shi na girka abinci kala kala, musamman da tasan ba ya san shinkafa sosai, sai ta yi wata d'aya ba ta girka ta ba, yanzun ma bai wani ci mai yawa ba ya bar shi, ko da ya yi wanka ya shirya falon Khadija ya shigo, Uwani na ganin haka ta mik'e ta fita, Bilal kuma dama ya na ciki ya na shiri, Kaltume kam ta na sallah la'asar ta wuce gida, zaune ya yi kalle ta ta na fad'in "Har ka fito?"
"Um." Ya fad'a ya na sake kafe ta da ido, ita kam gyara gilashinta ta yi ta kalle shi tace "Ya dai? Da magana ne? Wannan kallon haka."
K'asa ya kalla kafin ya kalle ta yace "D'azu da na shigo sai na ga kamar girki ku ka yi ko?"
Ba tare da shakka ba tace "Eh, girki na yi, da matsala ne?"
Gyara zama ya yi kamar zai had'e ta yace "Sosai ma, Khadija kar ki ce min ba ki hango matsalar da ni na hango ba, hakan bai dace ba, kuma gaskiya ba na so, idan har zai yiwu, to cikin d'aya dole ku yi d'aya, ko dai ku had'a kanku ku dinga girki tare, ko kuma dai duk ranar girkin d'aya to d'aya ba za ta tab'a d'ora min tukunya ba da sunan girki ba, wannan hukuncin yankakke ne, kuma umarni."
Mik'ewa ya yi ya juya ya kalli d'akin Bilal ya kalli agogon hannun shi, mik'ewa ta yi ta kalle shi tace "Ban k'i ta taka ba, amma kafin ka yanke wannan hukucin ya kamata ka fara fad'awa amaryarka cewa ba'a raba abinci a gidan nan, in dai har za ta ci gaba da ware mana abinci ni da yarona, to wallahi ba zan ci ba haka ma d'ana, kuma ko kaga ai bama zauna da yunwa ba alhalin Allah ya hore abinci ta ko ina, wannan shine."
Ta gaban shi ta rab'a za ta wuce ya rik'o hannunta, kallon ta ya yi yace "Na fad'a mi ki ba na so, raba abinci kuma na yan kwanaki ne da ba su taka kara sun karya ba, idan ki ka duba tsawon lokacin da mu ka d'auka tare hakan bai tab'a faruwa ba, me ya sa yanzu za ki gagara fahimta Khadija? D'an lokaci fa kawai tace a bata ita ma ta san ta na da miji, me ya sa za ki zama mai son kan ki dayawa, me zai rage ki idan ki ka hak'ura ki ka ci abincin, nan da lokacin da kwananta zai k'are fa shikenan komai ya wuce."
Rik'e k'ugu ta yi da hannu d'aya tace "Uhum! Anzo gurin, yau kuma sai gashi ka na fad'in wai ni ce mai son kai na, ni ce mai son kai na yau? To na ji kuma nagode, amma ka sani in dai wannan ne son kai to tabbas ni mai son kai na ce, wallahi ba zai tab'a yiwuwa ba ta barbarad'a min iskanci a abinci sannan ta bani na ci, wallahi ka ji na rantse ko ba zai yiwu ba, rai a baran mai shine, lafiya kuma uwar jiki, daidai da ciwon hannu wannan idan ya same ni akwai abin da za ka iya yi min ne? Ni fa zan ji zafin kuma na yi jinyata, hasalima duk soyayyar da ka ke sauki burutsun cewa kana min wallahi babu abin da za ka iya tsinana min, haka kawai kuma sai na jefa kai na a motar da na tabbatar ba ta da birki, rai fa guda d'aya ne."
Yanda take masifa sai abun ya ba shi dariya da mamaki, a zaman shi da ita bai tab'a ganin ta na fad'a haka ba sai yau, b'ata rai ya yi yace "Wallahi ba da wasa nake ba, kar ki sake d'ora min tukunya indai har ana girki a gidan nan, kinji na fad'a mi ki."
Za ta yi magana Bilal ya fito daga d'akin, sai kawai ta yi murmushi ta sa hannu ta shafo d'an gemunshi ta kashe masa ido tace "Ban ji da kyau, d'an sake maimaita min."
Dariya ce ta so sub'uce mi shi sai ya dake ya matsa kusan ta ya rad'a mata a kunne "Wallahi karki sake na sake ganin kin aza girkin ki, in ba haka ba rai zai b'ace fa."
Bilal ne ya shiga tsakansu ya na fad'in "Idan na bi taku sai na makara islamiyya, muje Abba."
Hannun shi ya kama ya na juyowa ya na kallon Khadija, ita kam wani shegen murgud'a baki ta yi irin ai ba ka ma isa d'in nan ba, daga yanda ya motsa bakin shi ya tabbatar mata da k'wafa ce ya yi, gwalo ta masa tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki wayar ta, su na fita ta ci gaba da latsa wayar ta hankali kwance, kamar daga sama ta ke jin k'amshin daddawar kalwa na bad'e ko ina na gidan, tashi ta yi ta fito farfajiyar gidan sai ta fahimci daga madafar su ne ya ke fitowa, kai tsaye ta shiga ta samu Haseenah ta zage ta na tuk'a tuwon shinkafa, da murmushi Khadija tace "Amarya sannu da aiki, yau kuma tuwo ake mana?"
Wani takaici ne ya taso ma Haseenah wacce ke wahalar tuk'a tuwon, k'ala ba tace mata ba sai Khadija ce ta sake cewa "Sai dai kuma mijinki baya cin tuwo da dare, ko bai tab'a fad'a mi ki ba? Musamman ma na ga wake ne ki ke miyar da shi, kuma ba ya cin wake ko kad'an, amma za ki iya had'a ma sa wani sassauk'an abun, mu sai mu ci tuwon dan munyi kewar shi."
Ran Haseenah ne ya yi mugun b'aci tace "Kutumar uba, baiwar Allah na fad'a mi ki ina neman taimakon ki ne? Kinga Khadija, gaskiya ba na son haka, mijin ki ba ya cin tuwo a lokacin da ke kad'ai ce cikin gidan, yanzu kuma Haseenah ta shigo, dan haka ki barni na yi rayuwa ta mana, ki barni ni ma na kafa salon nawa tarihin a gidan nan kuma a zuciyar miji na, amma ba ki dinga min shishigi ba, ba lallai dan kin saba mi shi da saka kalar fari ba ki ce nima wannan kalar ki ke so na saka mi shi, ki barni na yi abin da ya dace, nan gidan miji na ne."
Wani warrr Khadija ta yi da manyan idon ta kafin ta sa hannun ta tana fifita da shi tana fad'in "Wash Allah, zafi."
Kallon Haseenah ta yi da murmushi tace "Sannu mai miji, Allah ya bar k'auna."
"Ameen." Ta fad'a har da zaburowa, fita Khadija ta yi, tsaf Haseenah ta gama tuwonta ta mulmule, da kan ta ta kawowa Khadija na su tuwon, ko k'ala ita ma ba tace da ita ba har ta fita, Uwani ce ta tashi tafiya tace "Uwani d'auko wani kwano a d'akin can ki tafi da abincin nan."
D'aya d'akin ta shiga da ke da tarkacai abubuwan buk'ata ta fito, juye tuwon ta yi ta tafi da shi bayan sun yi sallama, Bilal ne ya shigo gida shi kad'ai da takarda a hannun shi, rumgume maman shi ya yi ita kuma tace "Wa ya dawo da kai ne?"
" *Bilyaminu* ne Abba ya tura ya d'auko ni, Mummy karb'i wannan." Ya fad'a bata takardar, ta na dubawa tace "Har wata ya k'are kenan?"
Kai kaxai ya d'aga mata, ba shi ta yi tace "To ka aje wurinka idan Abbanka ya dawo sai ka ba shi, amma ni zan iya mantawa."
A tare su ka tashi ita ta shiga d'akin ta saboda magriba ta gabato sosai, kaya kawai Bilal ya canza ya wuce masallaci, Khadija ma na idar da sallah ta shiga wanka, shiryawa ta yi sosai kafin ta lalabi gilashin ta na jiya da Usman ya cilla kan gadon, dan tun jiya bata waiwaye shi, shi ta saka dan ya fi mata kyau sannan ta fito, zaune suke ita da Bilal su na kallo su na hirar su, bayan sallah isha'i ko da su ka yi sallah abincin ranar da Uwani ta kwashe mata a kula ta d'auko ta zuba, tare su ka ci hankali kwance su ka k'oshi, hamdala su ka yi kafin su ka tashi kamar ba su ci ba.
Kamar yanda ya yi alk'awarin komawa gida haka ya wuce, ya kuma samu su Kabir Mannir da Nura, hakan ya sa suka bud'a babin hira su ka dinga yi, Haseenah da ke jiran shigowar shi taga shiru sai da ta kai ga kira, amma sai ya d'aga yace ya na gida zai zo ba da jimawa ba, amma fa bai zo d'in ba saboda suna tattaunawa da ahalin shi, sai wajen *22:20* ya baro gidan ya nufi gida, Khadija har sun kwanta ita da Bilal ya shigo, ko da ya ga babu wuta a falon sai ya wuce falon shi kai tsaye, Haseenah na ganin shi ta d'ago kai ta kalle shi, ba fara'a ko sakin fuska tace "Sannu da zuwa."
Sai da ya kamo hannun ta tayi tsaye ya rumgume ta yace "Sannu da gida."
Kamar ba ta son magana ta amsa da "Yawwa."
Kallon fuskarta ya yi yace "Ki yi hak'uri na barki ke kad'ai ko? Ina can gida tare da yaran nan su na ta min shirme."
Cikin shagwab'a tace "Na ji to, yanzu dai mu je ka yi wanka sai ka zo ka ci abinci."
Rimgume ta ya yi yace "Wallahi kamar kinsan kam na d'ebo yunwa, muje ki kintsani yanda ya kamata."
D'akin shi su ka nufa, bayan ta taya shi wanka ya canza kaya su ka fito, ya na jan kujera ya kalle ta yace "Da alama su Bilal har sun kwanta ko?"
Kallon shi ta yi tace "Eh to ban sani ba dai, amma tun da na ji shiru babu hayaniyar tv na ke tunanin haka."
Ba tare da ya kalle ta ba yace "Haseenah me zai hana idan ba na nan ki dinga zuwa wajen su ki na zama ku na hira? Ina ga hakan ai zaifi ko? Tunda daga ke sai sune a gidan, kuma sune abokan rayuwar ki a yanzun."
Ta na aza marar tuwo a farantin ya kalle ta, bai kai ga jin amsarta ba yace "Haseenah tuwo ki ka dafa?"
Kallon shi ta yi tace "Eh, da matsala ne?"
Ya na ci gaba da kallonta yace "Khadija ta ga ki na aikin nan?"
Sam Haseenah ta ma manta da abin da Khadija ta fad'a mata, sai kawai tace "Eh, me ya faru?"
Da wani irin kallo yace "Kuma ba ta fad'a mi ki komai a game da hakan?"
"A'a, wai me ya faru ne?" Ta fad'a cike da k'aguwa, a hankali yace "Shikenan kawai, zo zauna nan."
Janyota ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi ya na kallon fuskarta yace "Haseenah, ki yi hak'uri kinji, ina ganin laifi na ne da har mu ka yi soyayya da kai ba tare da kinsan abubuwa da dama a kai na ba, kuma hakan ya samo asaline saboda ba mu jima tare ba, sannan ni mutum ne da bai cika fad'an abin da ya shafe shi ba, amma a gaskiya ni ba na cin tuwo da dare, ba kuma shi kad'ai ba, akwai abin da ma kwata-kwata ba na cinsu kamar wake da nasan sa, sannan kinga shinkafa ma ban cika son ta ba haka, sannan kifi ma ba na cin shi da dare, wannan shine."
Bushewa ta yi da dariya ta sauka daga cinyar shi taja kujera mai fuskantar shi, da k'yar ta tsayar da dariyar tace "Miji na, ka na d'an africa, a africar ma a niger, kuma ka ce ba ka son shinkafa, lallai ka na jin dad'in ka."
Ganin ta mayar da abun kamar wasa ya sa ya d'an gimtse fuska yace "Ni dai ban son ta, na fad'a mi ki ne dan ki kiyaye."
Ita ma had'e fuska ta yi tace "To yanzu tuwon nan fa ya zanyi da shi?"
Shima dariya ya yi yace "Ku ba kun ci ba? Kawai ki samar min wani abu na ci."
Cike da kasala tace "Kamar me fa?"
"Ko taliyarku ta yara ki d'ora min." Yanda ya yi maganar da zolaya ya sa ta taso ta na dariya ta rumgume shi ta baya ta na fad'in "Yanzu ni yarinya ce a wurin ka?"
"Sosai ma." Ya fad'a ya na dariya, cikin kunne ta rad'a ma sa "Ni kam banyi tsammanin za ka iya kira na da yarinya ba."
D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Shekarar ki nawa ne wai dan Allah?"
Saida ta waina idon ta tace "Sha takwas."
Da sauri ya mik'e tsaye ya na k'are mata kallo, har zagayata ya ke ya na kallonta, tab'e baki ya yi yace "Lallai ina da sa'a, gani tsoho amma sai Allah ya dinga had'a ni da yara yan sha takwas shakaf."
Juyawa ta yi ta nufi madafar, d'ora tukunya ta yi duk da ba wani sanin kan indomie ta yi ba, amma dai wani lokaci ta d'an dafawa yayan ta *Mubarak*, yanzun ma yanda take yi a gida haka ta dafa, sai dai da ta zuba a faranti sai ta ga abun bai birge ta ba, dan indomien duk ta dahu sosai kamar za ta narke, to amma ya ta iya haka ta d'auko ta kawo mi shi, dakewa kawai ya yi tamaza ya d'ura indomien nan, amma bai ci sosai ba, ya na gamawa ya mik'e yace "Zan lek'a na ga su Bilal."
Kallon shi ta hi ta kalli farantin indomien, k'ala ba tace masa ba ta tashi ita ma ta wuce d'akin ta dan shirin bacci, shi ma ficewa ya yi bai kula ta ba, d'akin Bilal ya fara shiga, sai da ya k'arewa yaron kallo ya shafi kansa kafin ya fito, da sallama ya shiga d'akin amma shiru, kujerar gaban madubi ya janyo ya zauna bayan ta ya daddab'a ta, bud'a ido ta yi ta tashi zaune ta janyo gilashin ta ta sanya, kallon shi ta yi shi kuma yace "Hajia Khadija ki na lokaci, yanzu har an daina sona ta yanda ba'a jira aga na shigo lafiya ko akasin haka."
Murmushi ta yi tace "Abban Bilal ma ya na lokaci, tun da har zai shigo gidan nan amma ya kasa neman mu."
Da mamaki ya bita da kallo ita kuma tace "K'warai, na ji shigowarka ai."
"Hum." Ya fad'a ya yi shiru, ita kuma tace "Ka daina mantawa, yanzu mu biyu ne da hakk'in kula da kai, in da lokacin kwana na ne zan iya jiran ka har gari ya waye."
"Amma in ba kwananki bane kuma ko oho ko?"
"Kai ma kasan dole zan damu da kai, sai dai ba na son shiga hurumin da ba nawa bane."
Mik'ewa ya yi ya nufi frije d'in ta ya bud'a, wani k'aton cake ya d'auko mai suffar zuciya tare da yagourt mai kauri da sanyi, komawa ya yi ya zauna ya fara ci ya na shan madarar, Khadija dai kallon shi take har ya sai da ya cinye duka kafin ya mik'e, ban d'akin ta ya shiga ya wanko bakin shi ya dawo, kallon ta ya yi yace "Umman Bilal ya yarinyar can ta fad'a min kinga lokacin da take tuwo ko?"
Gyara zama ta yi akan gadon tace "Eh, na gani."
"To amma me ya sa ba ki fad'a mata ba na cin tuwo ba? Tunda ke kin sani."
Da mamaki ta kalle shi tace "Au! Wai dama duk soyayyar da ku ka yi ba ka tab'a fad'a mata abin da ka ke so ba da wanda ba ka so? Dole sai ni ce zan dinga fad'a mata?"
Matsowa ya yi kusanta yace "A gani na ya zama dole tunda ke ce gaba da ita, me ya sa ba za ki d'ora ta a hanya ba a matsayinki na babba?"
Da k'arfi ta zaburo daga kan gadon ta sauko ta na fad'in "Oho, wato babba juji ko? Komai tunda ke ce babba ke ce babba, to daga yau na bar mata girman ta d'auka, kuma ka je ka tambaya ta idan ban fad'a mata ba ka cin tuwo ba, amma sai tace a dole ita ma sai ta d'ora ka a tsarin da ya mata, saboda ita ma matarka ce, haka kawai za ka zo ka d'ora min laifi ka cika ni da surutu."
Komawa ta yi kan gadon ta kwanta ta ja zani ta rufa, shi kam baki bud'e ya ke kallonta har ta kwanta, sunkuyawa ya yi ya sumbaci kumatun ta ya d'ago yace "Saida safe masifata."
Zunbur ta tashi tace "Masifar ka kuma? Abban Bilal ni ce ma masifar yanzu? Lallai ka kyauta."
Gimtse dariyar shi ya yi yace "To in ba tawa ba ta wacece? Ai Khadija sai Usman, Usman kuma sai Khadija, kinga dole na kiraki da masifa ta tunda na ga kin fara koyon masifar."
Cinno baki ta yi gaba ta bishi da kallo har ya kai k'ofa, sai da ya bud'e ya fita ya juyo yace "Allahya huci zuciyar Umman Bilal, ta Usman bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad'i, na Khadija ba ni shan furataba nono, hakan ya yi ko? Saida safe, ina son ki."
Dariya ce ta kubce mata, sumba ta aika masa tare da fad'in "Ina son ka ni ma, saida safe."
_Ni ma dai saida safen nan gaskiya._😉
*Washe gari* ta kama alhamis, hakan kuma ya sa duk yan islamiyya na hutu ba karatu, k'awayen Haseenah na su ka zo gidan tun misalin *11:00* bayan fitar Usman ba jimawa, in da Bilal ma ke gida ya na wasan shi, dan ya so ya je gidan su maman Khadija amma ta hana, a madafa suka tare su na ta hira abinsu, kasancewar *Zeinab* na da k'ok'arin aiki ya sa yau ita taja ragamar girkin gidan, abinci su ka had'a kala har uku da kuma abin sha, bayan sun gama su ka dawo falon Haseenah dan cin abinci, kiran Usman ta yi ya aiko a d'aukar mi shi abinci ta na da bak'i a gida, ba d'aukar lokaci ya aiko da yaron shi Bilyamin ya d'auka, su na ci su na kwamtsa hirarsu sai ga Mariya, sai da suka gama ta shiga da ita ciki inda ta kwashe komai ta fad'a mata, bud'ar bakin Mariya cewa ta yi "Lallai Haseenah ina tausaya miki, dan wallahi kishiyar nan ta ki ba k'aramar muguwa bace, kawai ki hak'ura ki bita sau da k'afa, domin kuwa ita da d'an ta ne da gidan nan wallahi."
Cike da damuwa Hassenah tace "Ni ma na fahimci hakan, kar ki tona raina ki ji me na ji ranar, ita ce da laifi amma ya rufe ido ya d'ora min laifin, wai shi ya san matan shi."
"Ai kad'an ma ki ka gani in dai ba ki tashi tsaye ba, yanzu dai ina magani da na baki? Kinyi aiki da shi?"
"Duka na yi, kuma ya ci abincin? Amma ni banga wani sabon abu ba."
Gyara zama ta d'anyi tace "Kinsan me zai faru, ki sake kawo kud'i a kaiwa malam ya sake mi ki wani maganin, ko da na bakali ne da kuma samun soyayyar shi."
"Kamar nawa?" Ta fad'a ta na kallonta, ita ma kallonta ta yi tace "Eh to, iya kud'in ki ai iya shagalinki."
Da alamar tambaya Haseenah tace "Ki na nufin idan na bayar da kud'i dayawa zaifi kyau aikin?"
"Sosai ma."
Mik'ewa ta yi ta bud'a jakarta da take zuba kud'in da yake bata tun da ta zo, yan biyar biyar ko karyawa babu guda hud'u ta bata, aifa baki har waje ta karb'a suka fito daga d'akin, sallama su ka yi ta tafi ta barta da k'awayen ta, yamma ta yi suka sake tashi kama mata aiki, sai dai suna buk'atar bredi dan soya shi da k'wai, babu yaron da za'a bawa ya siyo sai Bilal ta kira dake farfajiyar gida tare da mai gadi, kud'i ta bashi ya siyo mata bredi, cikin sanyin jiki yace "Aunty nan ba'a siyar da bredi sai can nesa tsallaken titi, kuma Abba ya hana ni fita har can wajen."
A gadarance tace "Kenan ba ka da wani anfani cikin gidan? Sai dai a dafa a baka ka ci? To k'arya ka ke, maza wuce ka d'auko wannan shegen moton na ka da baida anfani sai dai ka yi yawo da shi cikin gida ko k'ofar gida ka je ka siyo ka kawo min yanzun nan."
Cikin sanyi ya juyo ya nufo wajen uwatai, d'akin da ya ke aje moton ya fito da shi, Khadija na gani tace "To, to ina kuma zuwa da wannan tuk'a-tuk'ar?"
Sai da ya zo gabanta cikin turo baki yace "Ba aunty amarya ce ta aike ni siyan bredi ba."
Da mamaki ta kalle shi tace "Bredi fa? Amma ba ka fad'a mata ba ka tab'a zuwa ko bakin titi kai kad'ai ba bare gaban shi?"
"Na fad'a mata, amma tace wai ni ban da anfani a gidan sai dai na ci abinci, kuma wai dole na je na siyo."
Wata shegiyar dariya Khadija ta bushe da ita ta kalle shi ta kalli Uwani, mik'ewa ta yi tace "Ku biyo ni har da ke Uwani."
Fita su ka yi har madafar ta same su, sai shewa da hira su ke, suna ganin ta kowa ya yi shiru sai wani kallo ake mata, ko ta kan su bata bi ba ta kalli Haseenah tace "...
*Ku yi hak'uri da wannan.*
29/01/2020 à 13:36 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Littatafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_INA K'ARA TAYA 'YAR UWARMU KUMA D'AYA DAGA CIKIN 'YAR GIDAN AMANA WATO MEMBER'S D'IN K'UNGIYAR *🇸🇦ZAMAN AMANA* MAI SUNA *MARYARHMAH UMMISIDDIQUE* MARUBUCIYAR *MINTI KARU'NYI YE* DA KUMA *NAGA TA KAINA* TA'AZIYYAR RASHIN UWA MAHAIFIYA DA TAYI, INA ADDU'A GA UWAR KIRKI HAR KULLUM ALLAH YAKAI RAHMA K'ABARINTA, ALLAH YA K'ARA MANA HAK'URIN RASHINTA, MUNYI RASHIN UWAR K'WARAI😰_
_Bismillahir rahamanir rahim_
*17*
"Haseenah, ga Uwani ki bata kud'in ta siyo mi ki bredin, amma Bilal mahaifin shi ya hana a aike shi ko kusa da titi."
Sai lokacin ta juyo ta kalle ta tace "Yanzu kamar Bilal ne za ace ba'a aikin shi, shi kad'ai ne yaro cikin gidan nan, kuma ace ba'a aikin shi, to me ya sa? Me ye anfanin haihuwar shi kena..."
Ba ta sauka daga abin da za ta fad'a ba Khadija ta ji ba za ta iya d'auka ba, zuciya ce kawai ta d'ebe ta ta kife ta da mari, kafin ta ankara ta shak'o wuyan rigar ta cikin d'aga murya tace "In ke ba ki san zafin haihuwa ba ni na sani, in ba ki san darajar 'yaya' ba ni na sani tunda na haifa, idan ba ki san anfanin haihuwa ba, to ki bari har ki bari ki haifi na ki sai ki zuba cikin shara, dama ya fad'a min kin ce wai sai dai a dafa a bashi ya ci, to ki sani Bilal ba jinin matsiyata bane, ko gidan uban shi babu abinci ba zai rasa abincin da zai ci ba daga dangin uwar shi, ki kiyaye ni, sannan ki fita ido na."
Sakin ta tayi ta juya ta fice, Zeinab ce ta yi saurin kallon Haseenah tace "Wai k'yale ta za ki yi? Jar uban nan, ai wallahi babu macen da ta isa."
Wannan magana ce ta sa Haseenah d'aukar k'aramar tab'aryar da ke madafar ta fita, su na ganin haka su ka tashi da sauri su ka bi bayan ta, Khadija na daf da shiga falon ta Haseenah ta sauke mata tab'aryar nan a kai, dafe kai ta yi ta juyo ta na fad'in "Kai kai kai kai."
Ta na ganin Haseenah ce sai kuwa ta cakume ta da kokawa,😂 (Allah ya kyauta, mata mu na bawa kan mu wahala wallahi, wata sai ki ga ma mijin da su ke fad'a akai kamar kalangu, amma haka za su yi ta bala'i a kan shi maimakon kwantar mi shi da hankali), k'awayen Haseenah na ganin haka su ka shigarwa k'awar su saboda tuni aka aza Haseenah ga k'asa ana shirgarta, Uwani na ganin haka ta fita da gudu zuwa gidan mak'wabtan da Khadija ke abun arzik'i da su, Bilal kam wayar shi ya d'auka k'arama ya kira mahaifin shi ya fad'a mi shi, mai gadi na daga gefe ya na dan Allah ayi hak'uri amma ko jin shi ba su yi, jin zafin dukan da k'awayen ta ke mata ne ya sa Khadija finciko wata daga cikin k'awayen ta had'a su ta taushe, wuri fa ya kaure ana ta bawa hammata iska sai ga mak'wabtan sun shigo, da gudu su ka k'arasa su ka d'aga Khadija daga kan Haseenah da *Farida*, anyi jina jina sosai kamar filin yak'i, cecekuce aka shiga yi tare da aikawa juna ashar, Khadija na k'ok'arin k'wacewa ta koma ga Haseenah amma an rik'e ta, su na haka fa gida ya kaure Usman ya baro mota waje ya kutso ciki, ganin su duk a yamutse ya sa ya tsaya ya sa hannu ya rufe fuskar shi, ya d'an jima a haka kafin ya k'araso wajen, k'awayen Haseenah ya fara kallo yace "Yamma ta yi, za ku iya tafiya."
Cikin sanyin jiki duka aka watse aka bar shi da matan shi, har Uwani ma ba ta tsaya ba tafiyar ta ta yi gida, falon shi ya nufa ya na fad'in "Ku same ni a falo na."
😂 *Aiki ya samu Usmanu, yanzu ma ka fara cewa a biyo ka falo ai*
Su na shiga daga zaman da Khadija ta yi zai tabbatar maka ba arzik'i, cikin b'acin rai ya yi tsaye yace "Me ku ka zama? Me ku ke son mayar min da gida? Wannan wane irin dabbanci ne?"
Tsaye Khadija ta mik'e tace "Dakata malam, dakata min, a sani na irin haka ba ta tab'a faruwa ba, to akan me sai yanzu haka za ta faru? Akan me ye amaryar ka za ta nemi ta raina ni? Ni sa'ar ta ce? Ko kai ka ce ta raina ni? Saboda rashin sanin darajar mutane har ta bud'e baki tace min wai mi ye anfanin Bilal a gidan nan, bayan kin fad'a ma sa bai da anfanin komai sai dai a dafa a ba shi ya ci, to uwar ki ce ke dafa mi shi ya na ci? To ki kama bakin ki ki dinga sanin me za ki fad'a."
Mayar da kallon ta ta yi ga Usman tace "Kai kuma dan Allah idan kun shiga ciki ka yi k'ok'ari ka sanar da ita mahimmancin d'an ka gare ka da anfanin shi gare ka, ni ba buk'atar sai na fad'a mata anfanin d'ana gare ni, amma ka fad'a mata shi kad'ai gare ni, dan haka bana had'a yaro na da kowa da kuma komai a duniya, a matsayi na na uwa kuma zan iya yin komai saboda shi."
Ta na gama fad'a ta fice ta bar su, juyowa Usman ya yi ya na kallon Haseenah, a hankali ya furta "Haseenah, ki na tambayar anfanin haihuwar Bilal a gidan nan? Ni fa uban sa ne, duk fafutukar da na ke yi saboda shine na ke yi, amma ki bud'e baki ki ce me ye anfanin haihuwar shi."
Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya dafe k'ugu da hannu d'aya yace "Maganar gaskiya Haseenah ba na so na nuna mi ki b'acin rai na, amma ki sani ko Khadija ba na buran b'acin ran ta bare kuma Bilal da ya fito daga tsatso na, ina k'aunar iyalin nan nawa matuk'a, su ne ni, su suka mayar da ni mutum da har ki ka so ni a haka, ki kiyaye furta abin da zai iya ja mi ki matsala, sannan k'awayen nan naki in har kinsan zuwan su gidan nan ba alkairi bane, to zaifi kyau ki fad'awa kowace ba na son sake ganin k'afar su a gidan nan."
Ya na gama fad'a shima ya fita ya barta, kallon shi ta yi a matuk'ar hassale ta mik'e ta nufi madafa, kashe wutar ta yi ta gyara abin da ya sawak'a ta koma d'akin ta, wayar ta ta d'auka ta kira Mariya ta fad'a mata duk abin da ya faru, nan dai ta girmama abin tare da k'ara tunzurata sannan tace ta bar komai a hannun ta, da haka su ka yi sallama ta yi wanka ta shirya, sai dai ba wata kwalliya ta yi ba dan duk jikin ta ma ciwo ya ke na tsinannan dukan da ta sha.
***************
Bayan sallah isha'i Khadija na zaune tare da Bilal a falo Nura ya shigo gidan da rahar shi kamar yanda ya saba, tun daga bakin k'ofa ya ke fad'in "Dije, Dije ba ta jina ne? Na shigo amma ki kasa tarba ta tun daga k'ofar gida."
Ganin Khadija zaune ta yi shiru sai kallon shi take ya sa yace "Ah lallai ma matar nan, ashe ki na jina na ke ta kwaroronton nan amma ki ka share ni? Ko dan yau ban baki kud'in cefanai ba?"
Khadija da har yanzu ran ta a b'ace ya ke k'ala ba tace mi shi ba, Bilal ne ya tarbe shi da murna sosai, tare su ka zauna ya na kallon Khadija ya kalli Bilal yace "Yaro waya tab'a min maman ka ne haka ta ke ta kumbura?"
Shiru Bilal ya yi ya na kallon ta, a hankali ta maido kallon ta gare shi tace "Sannu ko."
"Ai na ba za ki yi magana ba, da na tabbatar mi ki mijin gaske ne ni."
"Ya su Hajia?" Ta fad'a ba yabo ba fallasa, saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Lafiyar su k'alau, kai kawo min lemu mai sanyi na sha." Ya k'arashe da kallon Bilal.
D'auko masa ya yi ya kawo ya ba shi ya amsa, sai da ya fara sha ya kalli Bilal yace "Ina auntyn ka take?"
"Ta na d'akin ta." Cewar Bilal ya na kallon k'ofar falon mahaifin shi, tura shi Nura ya yi yace "Je ka ce ina kiran ta, ka ce ta fito ta kwashi gaisuwa tare da albarka mai gida ya dawo."
Da dariya Bilal ya nufi k'ofar falon mahaifin shi, cikin daka tsawa Khadija tace "Kai Bilal, ka na da hankali kuwa? Dallah malam dawo ka zauna min nan."
Da mamaki duka su ka kalle ta, in da ta nuna masa da hannu ya zauna hakan ya bata damar kama kunnensa tace "Wallahi ka sake zuwa in da matar can take sai na b'ata ma ka rai, kaji ko?"
Yanda ta d'aga murya tare da k'ara murd'e kunnen shi ya sa yace "Na ji Mummy, ki yi hak'uri ba zan k'ara ba."
Nura da ke kallon ikon Allah ne yace "Khadija me ya sa za ki ma sa haka? Naga da ke da ita ai duk d'aya ne, iyayen shi ne ku."
Tsaye khadija ta mik'e tace "Dakata min Nura, ni daban ita daban, wallahi duk yanda za ta kyautata mi shi ba za ta tab'a zama kamar ni uwar shi ba, dan haka kar ka sake had'a min yaro da wata banzar mata da ba ta san darajar shi ba, idan ka zo gani na ne na gode, idan wajen ta ka zo ka shiga ta na ciki."
Juyawa ta yi ta shige uwar d'akin ta, mamaki ne ya kusa kashe Nura, dan shi dai a sanin shi wani ma ba su tab'a samun matsala da Khadija ba bare kuma dangin mijin ta, cikin sanyin jiki ya aje robar lemun hannun shi ya mik'e zuciyar shi na tunanin wane irin kishi ne da Khadija haka? Bilal ne ya mik'e yace "Tonton (uncle) Nura zan bika wajen Hajia."
Shafa kan shi ya yi yace "To ka fara fad'awa Maman ka, idan ta amince sai ka d'auko kayan ka mu tafi."
"To." Ya fad'a ya juya da k'arfi ya shiga d'akin, zaune ya same ta yace "Mummy, tonton Nura yace na d'auko kaya na mu tafi gida wajen Hajia."
Cikin jin haushi tace "Babu in da za ka je, ka wuce d'akin ka ka kwanta ko kuma ka yi karatu."
Hawaye ne su ka cika idon shi saboda shi dai haka ba ta tab'a faruwa tsakanin shi da maman shi ba sai yau, juyawa ya yi zai fita sai taji ya bata tausayi, amma kuma hushin ta da duk dangin Usman da suke murnar an mata kishiya, a hankali tace "Bilal."
Juyowa ya yi ya dawo ya tsaya, hannun shi ta kama tace "Ka had'a kayan ka zan kira tonton Naseer ya zo yanzu ya d'auke ka, hakan ya yi?"
Ba tare da sakin fuska ba ya d'aga kai alamar eh, fita ya yi Nura na tsaye yace "To ya? Za mu wuce ne?"
Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy ta hana."
Ji ya yi kafin yace "Shikenan kar ka damu, ai gobe juma'a, watak'ila ku tafi gidan tare da Abban ka."
Shiru bai ce komai ba har ya fita daga gidan ba tare da ma ya shiga wajen Haseenah ba, ta na kiran Naseer kam dama bai shiga gida ba, dan haka ya taho d'aukar shi, sai dai lokacin Usman ya shigo gidan, sun gaisa kamar yanda su ka saba tare da wasa da dariya, amma har Khadija ta had'awa Bilal kayan shi su ka tafi babu fara'a a tare da ita bare ta yi magana, a tak'aice dai haka duka gidan su ka gudanar da daren su babu armashi a ciki, dan Usman ya nunawa Haseenah kuskuren ta ma ko abincin ta bai ci ba, haka ma a d'aki da suka kwanta juya mata baya ya yi, dan in har za ta iya cin zarafin d'an shi har haka to fa akwai yiwuwar ya nuna mata ba'a mi shi wasa da gudan jini.
Washe gari da safe ma haka abin ya ke, kasancewar Khadija ta san a wannan lokacin ya na d'akin shi ya na karatu ya sa ta shiga har can ta gaishe shi, bai wani yi karin kummalo ba ya yi shirin masallaci, *11:00* cif ya fita ya bar gidan zuwa masallaci kamar yanda ya saba, bai dawo cin abinci da rana ba sai aikowa da ya yi aka d'aukar ma sa, da yamma kuma ya kira Khadija yace su shirya dukan su za su je su yi barka gidan Issoufou, tunda magriba Khadija ta gama shirin ta tana jiran shi, Haseenah ma ba ta b'ata lokaci ba wajen shirin duk da fitar ta ta farko kenan, watak'ila ta na zumud'i ne saboda yace zai aje ta har gidan su ma su gaisa da mutane, ana idar da sallah isha'i ya shigo gidan, shi ma sai da ya sake shiri kafin su ka fita gaba d'aya, Haseenah ce baya tare da kwanukan abincin da zata kai gidan su.
Babu mai magana a motar dan kowa da abin da ke ran shi, sai Khadija da ke latsa wayar ta hankali kwance, gidan su Haseenah su ka fara tsayawa dan ya fi kusa da gidan Issoufou, Usman da Haseenah ne su ka fita, amma ganin Khadija ba ta da niyyar fitowa ya sa ya kalle ta yace "Uwar gida sarautar ta motsa ne? Ko sai na fito da ke?"
Ko kallon shi ba ta yi ba tace "Ku shiga kawai zan jira ku."
Wani murmushi ya yi yace "Ke ma kinsan ba zan lamunci haka ba ai, fito mu wuce dallah."
Cike da damuwa tace "Ba na cikin yanayin dad'i, ba na so kowa ya fahimci hakan har a dasa min hak'ora, dan ina fitowa za ace ba na da mutumci na fiya kishi da yawa."
Bud'e murfin motar ya yi ya kamo hannun ta ta fito, bai saki hannun ta ba har sai da su ka shiga cikin gidan, sakin ta ya yi ya saci kallon ta yace "In dai ina da mahimmanci a wajen ki, to ki kankaro min mutunci na a gurin mutanen nan, kar ki bari laifin 'yar su ya shafe su."
Kallon shi ta yi da farko turo baki ta yi, amma da ya marairaice sai ta saki fuskar ta na murmushi, Haseenah da tuni ta shiga gidan su ba ta ma san tsiyar da ke faruwa ba, sallamar su ce ta sa ta mik'e ta d'auko mu su kujeru su ka zauna, mahaifin ta na daga gefe zaune akan kujera, sai mahaifiyar ta na cikin sange zaune akan katifa da alama sunyi shirin bacci kenan, sosai su ka gaisa cike da mutunci da girmamawa, jim kad'an su ka mik'e Khadija na fad'in "Mama mu za mu wuce, saida safen ku."
"To Allah ya bamu alkairi, Allah fisheku dare." Cewar maman.
Da "Ameen." Su ka amsa, Haseenah kamar kar ta tafi take ji haka dai ta taso su ka fito, su na d'aukar hanya Usman ya kalli Haseenah ta madubi yace "Ke Hajia haka ake harkar duniya, daga kawo ki ku gaisa sai ki yi ta wani mak'alewa ba kya so ki tafi."
Cikin turo baki tace "Ni wallahi da ka bar ni na kwana anan ma da zanji dad'i, gidan mu ne fa."
"Wai ki na nufin har kinyi kewar gidan da har ki ke so a bar ki ki kwana anan?"
"Sosai ma, ai tun ranar da aka kaini gidan ka na fara kewar gidan mu."
Kallon Khadija ya yi yace "Hajia ki na jin ta fa, yanzu ke dan Allah za ki yarda ace ki je gidan ku ki kwana?"
Fuska ba annuri tace "Saboda ni banyi shak'uwar da zan iya kewar 'yan uwa na ba kenan? Ai ko yanzu ka ce tafi to sai dai ka aje ni na d'auki adaidaita, dan gani zanyi kamar motar nan ba ta gudu sosai."
Maida hankalin shi ya yi kan tuk'i yace "Kenan idan na fahimce ku duk cikin lamarin ni ne bare, kun nuna min har yanzu ba ku d'auka ta kamar yanda na ke d'aukar ku, kun nuna min har yanau babu wacce ta ke jin za ta iya k'arar da rayuwar ta a tare da ni."
Wata shegiyar harara Khadija ta masa tace "To me za mu zauna mu yi da tsoho, ka na so ne mu kai lokacin da za mu fara goge ma ka majina a hanci."
Hannu ya kai ya damk'o wuyan ta ya na dariya ya na fad'in "Ni ne ma tsohon? Yanzu ke mijin na ki ne tsoho? Lallai ma yarinyar."
Gwalo ta mi shi ta na fad'in "Gashi kai ma ka fad'a da bakin ka, har yanzu ni yarinya ce, tunda sai nan shekara biyu zan cika *talatin da biyar*."
Juyowa ya yi ya kalli Haseenah yace "Ke kin yarda mijin ki tsoho ne?"
Haseenah da haushi ya fara kashe ta ne tace " A zahiri wanda bai san ka ba zai iya kiran ka da tsoho, amma ni a wuri na ba tsoho bane, dan ni nasan k'arkon miji na."
Dariya Usman ya yi ya juyo ya bata hannu alamar su bige ✋ tare da fad'in "Ban biyar amarya ta." Bashi ta yi su ka bige su na dariya.
Kallon Khadija ya yi yace "Sai yanzu ai na fahimta, ashe ke ce ki ka tsufa ba ni ba."
Dariya ita ma ta yi tace "Amarya kam dole ta fad'i haka, amma da tasan waye kai lokacin da ka ke ji da k'uruciya, to fa da za ta gasgatani d'ari bisa d'ari, amma da ya ke zuwan shekaranjiya ce ita ba za ta gane komai ba, ko ba haka ba?"
Ta fad'a ta na kashe masa ido d'aya, turo baki ya yi gaba yace "Za ki yi magana ne idan ki ka shigo hannu na."
Bushewa ta yi da dariya tace "Yanzun haka ina matakin shekarun cikakkiyar mace ne da ke jin jini a jika, dan haka ba za ka tab'a tsorata ni ba malam Manu."
Wani mayan kallo ya mata ya na d'an cije labb'an shi na k'asa, sake tsinkewa ta yi da dariya har da kai mi shi duka a hannu ta na kwantar da kan ta a kafad'ar shi ta na fad'in "Ka tuna? Ka tuna wannan ranar da ka fad'a min haka? To nima na rama, yanzu ina kan shekaru na ne, dan ni yanzu ma ji na ke kamar yanzu ne na balaga, dan haka ka zama tsoho a wuri na."
Shi ma dariyar ya ke sosai yace "A ranar kam sai da na k'ara gyara tsayuwa ta sannan na ce mi ki, yanzu fa sai kinyi hak'uri da ni, dan ina ganiyar shekara talatin da biyar ne, shekarun hura wutar..."
Da sauri ta rufe ma sa baki su na ci gaba da dariya, d'an k'aramin tsaki Haseenah taja da ya sa su ka kalle ta, saita nutsuwar su su ka yi Khadija tace "Yi hak'uri amarya."
Take ta kalli Usman ta saisaita murya tace "Abban Bilal, munga shekaran jiya tare da kai, haka ma munga jiya da yau, insha Allahu da izinin ubangiji za mu ga gobe."
Wani fari ya mata da ido alamar wai ta sumbace shi, ita ma mayar masa ta yi da idon alamar a'a, Haseenah da abin duniya ya isheta ne tace "Wai har yanzu ba'a kawo gidan ba ne?"
Babu wanda ya kalle ta sai Usman da yace "Halan bacci ki ke ji?"
Banza ta yi da shi daga haka har su ka isa gidan, nan ma da suka shiga wata sabuwar hira aka dasa Khadija da Usman da Issoufou da mai jego kasancewar babu kowa a gidan sai yaran su da kula mai tayata kwana, da ganin yanda suke hira kasan akwai shak'uwa da fahimtar juna da kuma mutunta juna, saida dare ya yi su ka taso su ka dawo gida, kowa d'akin shi ya nufa ya yi shirin kwanciya, sai da Usman ya zo ya wa Khadija saida safe kafin ya koma, duk da Haseenah ba ta bashi hak'uri ba akan abin da ya faru, amma da ya neme ta sai ya sa ta sake jin girman kai, hakan ya nuna mata ko ka wa namiji laifi ran shi ya b'ace dole shi zai neme ka ko dan biyan buk'atar shi, da haka gari ya waye.
*Yau kuma da wacce aka wayi gari? Sai kun biyo ni.*
0 comments:
Post a Comment