TSOHON kakakin ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP a zaɓen 2019, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wato Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya takalo magana da shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), da kuma fitaccen jarumi Tijjani Asase.   



Tun da farko, Alhaji Sanusi ne ya yi kira ga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da ta dakatar da haska wasannin kwaikwayo ɗin nan guda biyu masu dogon zango waɗanda Asase ke shiryawa, wato ‘A Duniya’ da kuma ‘Haram’.

A wani saƙo da ya wallafa cikin harshen Ingilishi a shafin sa na Facebook a safiyar Lahadi da ta gabata, hadimin na Kwankwaso ya ce: “Idan har da gaske Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ke yi a kan ayyukan ta, to ya kamata ta dakatar da shirin wasan kwaikwayo na ‘A Duniya’ da kuma ‘Haram’, domin su na matuƙar kawo illa a cikin al’ummar mu.”

Ya ƙara da cewa wasannin ba sa koyar da komai illa miyagun halaye da yanzu haka al’umma ke fama da su daga ɓatagarin matasa.

“Waɗannan finafinan ba sa koyar da komai sai ƙara koyar da mugayen halayen da mu ke fama da su, da su ka haɗa da daba da ƙwacen waya da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma safarar yara ƙanana wanda hakan ke cutar da al’umma.”

Haka kuma ɗan siyasar ya zargi Hukumar Tace finafinan da yin bi-ta-da-ƙulli ga waɗanda su ke adawa da gwamnatin Ganduje, ta na huce fushin ta a kan su.

“Ina mamakin yadda Hukumar Tace Finafinan ta fi mayar da hankali ido rufe a kan masu adawa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ke cikin masana’antar Kanywood,” inji shi.

To sai dai da mujallar Fim ta waiwayi Isma’il Afakallah a kan maganar, sai ya yi watsi da ita da cewa batu ne na son rai ƙarara.

Ya ce hukumar sa ba za ta saurara wa duk wani ɗan fim ko mawaƙi ba matukar ya saɓa wa dokar da ta kafa hukumar.

Ya ce, “Ba za mu taɓa bari wani abu ya zo ya a taɓa tarbiyya, al’ada da addinin ‘yan Jihar Kano wannan hukuma ta zuba ido ta na kallo ba. To ka ga inda ya ke so ya dira sai ya dira kan cewa ana yi wa wasu ba a yi wa wasu, don haka da sai ya ce an yi wa wane saboda ko ya ce Kwankwaso ko ya ce PDP ko ya ce kaza, an kuma yi wa wane saboda ya ce Ganduje ko ya ce APC.

“Da a ce maganar da ya faɗa ta farko cewa fim ‘A Duniya’ kaza ne ko kuma an yi kaza, da wannan sai a ce an karɓa an kalli abin, amma ka ga ya shigo da siyasa, don haka babu wani abu.”

Afakallah ya ƙara da cewa, “Duk fim ɗin da ake sai an kawo mun tace sannan kuma idan ya je ya kalla zai ga ana nuna akwai mutanen kirki akwai mutanen da ba na kirki ba, kuma duk rayuwar duniya akwai mai kyau akwai mara kyau, akwai baƙi akwai fari, don haka ba yadda za a yi ka fito ka yi ta nuna mutane cewa farare ne, amma ba za a rasa cewa ko idan an yi kuskure ba.

“Duk wani fim da zai fita a Jihar Kano, dole sai Hukumar Tace Finafinai ta tace shi, mun kuma tabbatar da shi. Don haka duk wanda ya yi riga ta rangwaɗa ko ya shigo da siyasa ba za mu ƙyale shi ba, don haka wannan shi ne gaskiyar magana.”

Bugu da ƙari, shugaban ya ce, “Kowa ya san abin da Hukumar Tace Finafinai ta ke yi wanda kullum ana jin ta a kotu, ana jin ta da mutane waɗanda ba ma wai masu harkar fim ba har da wanda ya yi abu ya shafi hukumar ana jin ta da shi. Hasali ma, mutanen gari ma shaida ne. Wannan ita ce gaskiyar magana.”

Shi kuma a nasa ɓangaren, jarumi, marubuci kuma furodusan shirin na ‘A Duniya’, Tijjani Abdullahi Asase, ya ƙaryata batun Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa tare da bayyana shi a matsayin hassada da rashin son cigaban ‘yan fim irin sa da wasu mutane su ke yi. 

Asase ya faɗa wa mujallar Fim cewa wasu daga cikin ɗaiɗaikun mutane ne ke danganta fim ɗin da ɗaukar wata hanya da ake ganin za ta jawo cigaban ayyukan daba a sassan Jihar Kano.

Ya ce a da kafin a dawo da ci gaba da haska wannan fim na ‘A Duniya’, ya ɗauki tsawon lokakaci wanda har ta kai ga sa ran hukumomin tsaro ne su ka shiga tsakani domin hana nuna fim ɗin.

Asase ya ce, “Kamar yadda al’adar finafinai masu dogon zango ta ke a ko’ina, a kan ɗauki tsawon lokaci idan an gama da ɗaukar farko kafin a shiga ta biyu, wato ‘season’ kenan. To wannan ma hakan ne ya faru.

“Duk wani aiki mai wahala ya kan ɗauki lokaci kamar yadda mu ma mu ka yi.”

Da wakilin mu ya tamabayi Asase batun raɗe-raɗin da ake yi na dakatar da nuna fim ɗin sakamakon ana zargin su da tallata harkokin daba da ƙwacen waya, sai ya ce, “Wai makaho ne ya ce a yi wasan jifa, ka san ai akwai abin da ya taka! In dai ba akwai abin da ya taka ba, ya za a yi ya yi? Don haka duk mutumin da ka ji ya na cewa kaza-kaza, idan ba ka son abu ba ka son sa, idan ka na son abu ka na son sa, saboda abu ne a buɗe; wanda da man ba ya son sa dole ne ya kawo kushewa a kai. 

“Finafinai nawa aka yin akasin fim ga suna na wanda kuma tun tuni ake yin su kamar irin su ‘Basaja’, ga kuma finafinan Indiya nan wanda ake tace su ake yi da Hausa, duk ga sunan. Sannan idan finafinan ‘yan daba ake magana, me ma aka yi a fim ɗin ‘A Duniya’?

“Duk cikin fim ɗin babu inda aka nuna an sari wani, babu inda aka nuna an ɗauki wuƙa aka buga wa mutum. To menene abin da ake a ciki? 

“Kawai dai abu ne da Allah ya sa masa albarka kuma surutun mutane ba zai ƙare ba.

“Mu ‘yan Kano ne ‘yan birni, mu na da iyaye mu na da surukai mu na da ‘yan’uwa. In ka yi abin da ya dace, ka sani, in ba ka yi ba ma ka sani. Duk kuma wani abu da za ka samu a gidan duniya ne, sannan duk wani abu da za ka yi ka yi ƙoƙari ka gyara lahirar ka.”

Ya ƙara da cewa, “Na ƙirƙiri fim ɗi na ne ba a kan daba ba, sai a kan son zuciya irin na ɗan’adam, a nuna wa mutane cewa da kowanne zai cire son zuciyar da ya ke ran sa da duniya ta zauna lafiya, da kai kan ka za ka cire naka son zuciyar ni ma na cire nawa, wancan ya cire nasa, to da mun zauna lafiya.

“A ko da yaushe mutane su dinga fatan alkhairi a kan mutane mana. Na farko dai yanzu abin da ake so a nuna wa mutane shi ne mutum ya dogara da kan sa, ba wai ya yi tunanin sai ya yi aikin gwamnati ba. Idan ka duba za ka ga ɗimbin mutanen da su ke cin abinci ta cikin wannan fim nawa kuwa? 

“Ya kamata mutane su dinga ba wa mutum ƙwarin gwiwa idan ya sama wa kan sa aikin yi, ba wai a dinga daƙile shi ba. Don haka yanzu mu yi ƙoƙari mu koya wa samarin mu yadda za su samu abin da za su ci su sha, ba wai yadda za su zama maƙiyan mu ba a rayuwa.”

Shirin ‘A Duniya’ dai shiri ne da ake nunawa a tashar YouTube mai suna Zinariya wadda ta ke mallakin Tijjani Asase.

Shirin ya na nuna wasu daga cikin halayen son zuciya da matasa su ke nunawa ta hanyar kashe zuciyar su tare da yin sace-sace wanda har ya kai su ga da-na-sani.

‘A Duniya’ wanda aka ɗauki tsawon shekara ɗaya da fara yin sa, za a ci gaba da haska kashi na huɗu bayan da aka gama kashi na ɗaya da na biyu da na uku.