Ƙungiyar Matan Kannywood (Kannywood Women’s Association of Nigeria, K-WAN) ita ce ta shirya taron, wanda aka yi da misalin ƙarfe 4 na yamma a filin Social Welfare da ke unguwar Court Road.
Taron, wanda ya samu halartar wasu daga cikin dattawa maza kuma malamai da ke masana’antar Kannywood domin jagorantar taron addu’ar.
Malaman da su ka gabatar da addu’o’i na musamman a taron sun haɗa da Kabiru Nakwango, Hussaini Sule Ƙoƙi, Khalid Musa da Malam Inuwa.
Da ya ke jawabi gabanin fara addu’o’in, Malam Inuwa ya yi nasihohi masu ratsa zukata inda ya bayyana cewa marigayiya Zainab mutuniyar kirki ce kuma mai ƙarfafa zumunci tsakanin ta da abokan sana’ar ta da sauran al’umma.
Ya ce: “Ba na mantawa, a duk lokacin da mu ka haɗu da wannan baiwar Allah sai ta tunasar da ni a kan cewa ta ba ni wasiyya da in yi mata addu’a tare da dangin ta da ma bayan rasuwar ta. Ba na mantawa da wannan abu; ga shi yau Allah ya karɓi rayuwar ta ta na mai samun kyakkyawan zato kamar yadda aka ji daga bakin mutane da dama.
“Ina jan hankalin ku da iyalan ta tare da sauran jama’a da su yi koyi da kyawawan ma’amalar ta tagari.
Marigayiya Zainab Booth
“Mu yi amfani da damar da mu ke da ita wajen yin ayyukan da za su kai mu zuwa ga Aljanna. Wannan masana’anta idan mutum ya yi aikin daidai a cikin ta zai samu Aljanna, idan kuma aka samu akasin haka to fa sai dai addu’ar Allah ya kiyaye.”
A nasa bayanin, jarumi Malam Hussaini Sule Ƙoƙi ya maida hankali ne wajen tunasar da jaruman Kannywood da su bai wa batun addini muhimmanci domin kauce wa kallon da mutane su ke yi wa ‘yan masana’antar na yin burus da abubuwan da su ka shafi addini.
Shi kuma Kabiru Nakwango, ya yi bayani ne kan irin kyawawan halayen marigayiyar. Ya bayyana rashin Zainab Booth a matsayin wani babban rashi na jajirtacciyar mace.
Nakwango ya ce, “Hajiya Zainab na da kaffa-kaffa da duniya tare da gudun zuciya. Ba ta bari ko da wasa zargi ya ɗarsu a zuciyar wani, ba ma ita ba, duk yadda za ta yi sai ta yi domin ganin ta samar maka da farin ciki.
“Zainab mai yawan addu’a ce tare da a duk lokacin da mu ka haɗu sai ta tambaye ni cewa ‘Ka na yi wa ‘ya’yan ka addu’a kuwa?’
“Wata rana ta kira ni, mu na karatu da ɗalibai, sai ta ji karatun yaran. Ta ce, ‘Na kira a kan gaɓa kenan?’ Sai kawai ta gaya min wata kalma guda ɗaya ta na sa ta a addu’a. Daga wannan magana, sai ta kashe wayar.
“Haƙiƙanin gaskiya, mun yi rashin mutuniyar kirki a cikin wannan masana’atar. Ya kamata a ce mata matasa su yi koyi da irin ɗabi’un ta da mutane su ke yabawa ko da yaushe. Mu bar bayan da za su yi mana addu’a tare da yin alfahari na alkairi wanda za mu gani, ba wai mu bar wa ‘ya’yan mu abin da za mu yi da-na-sani ba.”
Malam Kabiru Nakwango ya na jawabi
Jarumin ya kuma ja hankalin iyalan marigayiyar da su riƙe zumunci hannu biyu-biyu kamar yadda kowa ke shaidar Hajiya Zainab da shi.
Da ta ke jawabi a madadin shugabar ƙungiyar ta K-WAN, jami’a mai kula da tsare-tsaren ƙungiyar, Hajiya Rasheeda Adamu (Maisa’a) ta bayyana farin cikin da ta yi dangane da yadda ‘ya’yan wannan ƙungiya su ka amsa kiran yi wa marigayiyar addu’a.
Rasheeda ta ce, “Wannan shi ne karon farko da mu ka fara yin wannan taro na addu’a a tsakanin ‘yan wannan ƙungiya domin kuwa ita ce mace ta farko da ta fara komawa ga Mahaliccin ta tun bayan kafa ƙungiyar.”
Haka kuma ta bayyana cewa wannan taro ba zai zama na ƙarshe ba domin kuwa za su ci gaba da shirya addu’o’i da dama, ba wai sai dole an yi rasuwa ba.
“Mu na addu’ar Allah ya gafarta wa Mama, ya yi mata Rahama.”
Da ya ke maida jawabi a madadin iyalan su, Shehu Abdullahi, babban ɗan Hajiya Zainab, ya bayyana farin ciki kan wannan taro da K-WAN ta shirya wa mahaifiyar su.
Ya ce, “Wannan ya nuna yadda mahaifiyar mu ta yi zama da mutane lafiya da ƙaunar juna. Ba mu da abin da za mu ce sai dai Allah ya yi mata rahama, ya kuma saka wa kowa da alkairi.”
A ƙarshe, ya buƙaci jama’ar da ke wannan masana’anta da cewa duk wanda su ka san su na bin mahaifiyar tasu bashi ko ta ke bi da su taimaka su yi magana domin a sauke mata nauyi.
Taron addu’ar ya samu halartar Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad, wadda ta yi nasiha ga mata da su kula da irin suturar da za su saka wanda ya dace tare da guje wa abubuwan da su ka san sun saɓa wa addini da al’adar mu.
Dandazon mahalarta
Ɗimbin dattawa da matan Kannywood da kuma ‘yan’uwan marigayiyar da su ka zo daga sassan ƙasar nan da dama sun halarci taron.
Cikin jaruman da mujallar Fim ta gani akwai Maryam Dodo, Fati Bararoji, Maryam CTV, Safiya Kishiya, Fati Al-Amin, Jamila Nagudu, Teema Yola, Hadiza Kabara, Hauwa Waraka, Siddiqa Jibril, Aina’u Ade, Hajara Usman, Momee Gombe, Rasheeda Maisa’a, Sadiya Shehu da Batula Hussain.
Mazan kuwa sun haɗa da Kabiru Maikaba, Malam Inuwa, Ahmad Alkanawy, Yusuf Haruna Funtuwa (Baban Chinedu), Rabi’u Lawan, Hussaini Ali Ƙoƙi, Baballe Hayatu, Yakubu Furodusa da sauran su.
An gudanar da taron tare da ɗaukacin ‘ya’yan marigayiyar su huɗu, wato Shehu, Sadiya, Maryam da kuma Ahmad (Amude).
Allah ya jiƙan Hajiya Zainab Booth, amin
Malam Khalid da Malam Inuwa su na gabatar da jawabi
Kwamishinar Al’amuran Mata, Dakta Zara’u Muhammad, a wajen taron
Rasheeda Adamu Maisa’a (a hagu) tare da Kwamishinar Al’amuran Mata, Dakta Zara’u Muhammad (a tsakiya) da wata bayan an kammala taron
0 comments:
Post a Comment