Jarumin, wanda wasu ke kira Abale ko Ojo, ya faɗi haka ne a tattaunawar sa da mujallar Fim kan kyautar mota da fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi masa.
Ya ce, “Ni na san cewa ina tare da nasara ta a kowane lokaci saboda ina tare da mahaifiya ta, ina alfahari da ita.
“Na san kuma in Allah ya yarda duk wani abu na rayuwa da ake yi zan iya yi, zan kuma shige haka in Allah ya yarda.”
Kazalika ya ce addu’o’in mahaifiyar tasa su ne abin da ke yi masa garkuwa a dukkan wani abu da ya saka a gaba na rayuwa.
Rarara ya ba Daddy Hikima kyautar motar ne lokacin da kamfanin Zinariya ke karrama Rarara a ofishin sa saboda yadda ya ke bada gudunmawa ga ci-gaban masana’antar finafinan Hausa.
A yayin da ya ke bayyana farin cikin sa dangane da wannan kyauta, Daddy Hikima ya faɗa wa mujallar Fim cewa ko a mafarki bai kawo kyautar ba.
Ya labarta wa wakilin mu cewa sun haɗu da Rarara ne ta hanyar furodusa Bashir Maishadda, sakamakon yadda Rarara ya ke ƙaunar sa.
A kan yadda aka yi har Rarara ya yi masa wannan kyauta, jarumin ya ce, “Komai na Allah ne. Ba a daɗe ba a satin da ya gabata na yi hatsari a mashin ɗi na, sai ga irin wannan kyautar da ban taɓa tsammanin ta ba na samu.
“A jiya mun je taro na fim ɗin da na ke jarumi a ciki na ‘A Duniya’, za a karrama Rarara saboda an yi bikin cikar fim ɗin shekara ɗaya da fara shirya fim ɗin.
“To ranar da aka yi bikin cikar fara nuna fim ɗin bayan Sallah da sati ɗaya ni ba na nan, ban samu damar zuwa ba, na je Abuja wasan Sallah, shi ma kuma Rararan wani uzuri ya hana shi halartar taron. To sai ya bada lokacin da za a zo a karrama shi. Da ya ke kuma an ware mutanen da za a karrama saboda wata gudunmawa da su ke bayarwa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, ciki kuma har da shi Rarara, to sai ya bada lokaci ya ce a je jiya Lahadi, kuma a cikin jaruman da aka zaɓa waɗanda za su wakilci sauran har da ni.
“Bayan an zauna an gaisa haka, ana ta abubuwa kamar wasa ya ke ta dariya, sai ya ce ai shi akwai wani jarumin sa a cikin wannan fim na ‘A Duniya’ da ya ke so. Sai ya ce ni ne.
“Sai kuwa aka ce masa, ‘Ai jarumin naka ba a fi sati ba ya na tafiya wani mai Adaidaita Sahu ya kaɗe shi a kan titi.’ Sai ya ce, ‘To in Allah ya yarda daga yau Adaidaita Sahu ba zai sake kaɗe shi ba, sai dai shi ya kaɗe shi.’
“To amma ni ban fahimci me ya ke cewa ba. Kwatsam, sai na ji ya ce, ‘Abale, na ba ka mota.’ Kamar a mafarki na ke ji maganar.”
Matashin jarumin ya ƙara da cewa, “A gaskiya na ji daɗi sosai matuƙa mara misaltuwa, kuma ina yi masa addu’ar fatan alkairi. Allah ya ci gaba da buɗa masa, sannan ni ma Allah ya kawo lokacin da zan ba wa waɗansu.”
Daddy Hikima ya kuma bayyana kyautar motar a matsayin wani abu da zai ƙara zaburar da shi wajen ganin ya dage da addu’o’i kamar yadda ya ke ganin soyayya a gun jama’a ta ko’ina, “ba ga maza ba, ba ga mata ba.”
Ya ce, “Yanzu zamani ya sauya, a duk inda ka shiga sai ka ga mutane su na nuna sun san ka, tsofaffi da yara kowa mararin gani na ya ke. To gaskiya hakan ya sa ni dole na ƙara zage dantse wajen gode wa Allah tare da yin addu’a.”
Tawagar masu shirya fim ɗin ‘A Duniya’ lokacin da su ka karrama Rarara a ofishin sa
Ya shawarci ‘yan’uwan sa jarumai da su maida hankali wajen riƙe sana’ar su ta fim da muhimmanci ta yadda za su amfanar da wasu da iyayen su da ma yara na ƙasa masu tasowa a duk lokacin da su ka samu ɗaukaka.
‘Yan’uwa da abokan arziki sun yi ta taya shi murna tare da yi masa addu’ar Allah ya tsare.
Rarara dai ya saba yin irin wannan kyautar lokaci zuwa lokaci ga ‘yan fim. Haka kuma ba a iya mota kyautar sa ta tsaya ba, har kuɗi da sauran abubuwa ya na ba su.
An ƙiyasta cewa Rarara ya raba aƙalla sama da mota 20 a Kannywood.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka samu kyautar mota a wurin sa sun haɗa da Aminu Mai Dawayya, Tijjani Asase, Jamila Nagudu, Maryam Yahaya, Aminu S. Bono, Teema Yola, Aminu Dumbulun, Ummi Ibro, da Isah Bawa Doro.
0 comments:
Post a Comment