An gudanar da sallar jana’izar marigayiyar, wadda ‘yan fim kan kira da laƙabin Mama Zee, a gidan ta da ke unguwar Court Road, Kano, da ƙarfe 8:15 na safe.
Marigayiyar mai shekaru 63 a duniya ta rasu bayan ta sha fama da rashin lafiya, kuma ta bar ‘ya’ya huɗu waɗanda su ka haɗa da maza biyu mata biyu, waro Shehu, Ahmad (Amude), Sadiya da kuma Maryam Booth.
Ɗimbin jama’a waɗanda su ka haɗa da ‘yan’uwa da abokan sana’ar ta ne su ka raka ta zuwa makwancin ta a maƙabartar unguwar Gyaɗi-Gyaɗi.
Jim kaɗan bayan an kammala binne Zainab Booth, mujallar Fim ta ji ta bakin wasu daga cikin ‘yan Kannywood kan wannan babban rashi da aka yi.
Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba wai ga iya Kannywood ba. Ya ce: “Ba abin da za mu ce sai dai mu ce duk abin da Allah ya karɓa nasa ne, kuma duk gaba ɗayan mu mu ma masu tafiya ne.
Lokacin da za a yi wa Hajiya Zainab Booth sallah
“Lallai Hajiya Zainab mace ce mai girmama mutane ba wai don ka fi ta shekaru ko ka na ƙasa da ita ba. Ta san mutuncin mutane. Ta na girmama mutane, don haka kuma ga zumunci kamar yadda sauran jama’a su ke faɗa. Mu na yi mata addu’ar Allah ya jiƙan ta; wannan jinyar da ta yi ya sa kankarar zunubi ne.”
Alhassan Kwalle, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Jaruman Hausa ta Nijeriya (Hausa Actors Guild of Nigeria), reshen Jihar Kano, ya bayyana wannan rashin a matsayin wani babban giɓi wanda zai yi wuya a cike shi.
Alhassan ya ce, “Mama Zee ba ta da wani laifi. Duk wanda ya ke cikin wannan masana’anta tamu ta ɗauke shi tamkar wanda ta haifa a cikin ta. Tsakanin mu da ita sai nasiha da addu’a.
Karanta kuma Yadda Hadiza Gabon ta zama Uwar Marayu
“Mu na fatan irin nasihohi da addu’o’in da ta dinga yi mana da kuma kyawawan mu’amaloli da ta ma’amalence mu da mu da ‘yan’uwan ta Ubangiji ya dubi wannan lamari ya sada ta da Manzon Allah (s.a.w.). A masana’antar mu ta Kannywood zai yi wuya a maida wannan gurbin nata tsakani da Allah. Sai mu yi mata addu’ar Allah ya yi mata rahama.”
Shi ma a nasa ɓangaren, darakta Hassan Giggs ya bayyana matuƙar kaɗuwar sa dangane da wannan rashi. Ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai ƙoƙari ganin wannan masan’anta ta zauna lafiya haɗi da ƙaunar juna.
Giggs ya ce, “A gaskiya mun yi babban rashi a Kannywood, saboda Mama Zainab ta zauna da kowa lafiya. A duk inda ta gan ka – ko ka san ta ko ba ka san ta ba – za ta gaishe da kai.
“Kuma ta na bada gudunmawa wajen dawo da mu kan turba. Da zarar mutum ya yi ba daidai ba ta kira mutum ta ba shi shawara cewa wanna rayuwar fa ba matabbaciya ba ce, babu komai a cikin ta, don haka mu bi rayuwa a sannu. Ni dai addu’a ta a gare ta shi ne Allah ya jiƙan ta da rahama.”
Jarumi Ali Nuhu shi ma ya shaida wa mujallar Fim yadda ya ji wannan rashi kamar haka: “Wannan ba ƙaramin rashi aka yi a masana’antar Kannywood ba. Gaba ɗaya da ilahirin mutanen da ta ke mu’amala da su domin kuwa Mama Zainab Booth ta na da zumunci. Ga duk wanda ya san ta, mace ce mai jajircewa a kan al’amuran mutane da kuma damuwa da damuwar jama’a.”
Ali ya kuma bayyana wasu daga cikin halayen marigayiyar da ba za a manta da su ba, ya ce, “A cikin halayyar ta akwai girmama mutane da karamta su da kuma zumuncin nan dai kamar yadda na faɗa maka. Ta na da zumunci sosai.”
Karanta kuma Halacci ne ya sa na auri Hassana - Sahabi na cikin 'Kwana Casa'in'
Fitaccen jarumi kuma mawaƙi Yakubu Muhammad ya zamto suriki ga marigayiyar a da saboda ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta, wato Sadiya, har sun haifi ‘ya da ita. A tasa ta’aziyyar ya faɗa wa wakilin ni cewa: “Kamar ni ba wai iya masana’antar shirya finafinai aka yi wa wannan rashi kaɗai ba, saboda ita sirika ta ce domin kuwa kaka ta ke a gurin ‘ya ta. Don haka babban rashi ne a wajen mu sosai. Sai dai mu ce Allah ya gafarta mata, ya jiƙan ta, ya sa kuma ƙarshen wahalar kenan, domin kuwa ta sha wahala sosai; ta yi jinya, don haka Allah ya sa ƙarshen ta kenan.”
Ana rufe Hajiya Zainab Booth a kushewar ta
Kazalika ya kuma bayyana marigayiyar a matsayin mai zumunci wacce ba ta da abokin faɗa tare da bayyana gaskiya ko kai waye.
Shi ma jarumi Mustapha Musty ya bayyana Hajiya Zainab a matsayin mace mai addini kuma mutuniyar kirki. Ya ce, “Mace ce wadda a duk lokacin da ku ka gamu da ita za ta yi maka nasiha a matsayin ka ji tsoron Allah.
“Kuma kirkin ta ma ba zai iya misaltuwa ba don dukkanin wanda ya ke cikin wannan masana’anatar babu wanda kuma bai san irin kirkin da ta ke da shi ba. Don haka a ko da yaushe ta gan ka ba ta da aiki sai ‘bi Allah da manzon Allah’. Wallahi abin da ta ke faɗa kenan a ko da yaushe ta gan ka.
“Ta na ce mana mu dinga yin addu’o’i, a bi iyaye, da sauran su.
“Mu na addu’ar Allah ya jiƙan ta, Manzon Allah ya yi mata makwanci.”
Karanta kuma Ko a Aljanna ina so Muhibbat ta zama mata ta, inji Hassan Giggs
A nasa jimamin,Ado Gwanja, wanda ya na ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa kuma jarumi a wannan masana’anata, addu’a ya yi wa Hajiya Zainab tare da bayyana ta a matsayin uwa tagari.
Su ma matan industiri ba a bar su a baya ba wajen bayyana alhinin wannan rashi da aka yi.
Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso) ta bayyana wa mujallar Fim alhinin ta kamar haka: “Zainab Booth mace ce mai kirki, kuma kowa ta gani ta ce ‘ɗa na ne’. Ga addu’a.
Ali Nuhu (a hagu) tare da Isma’il Na’abba (Afakallah) a wajen rufe gawar Zainab Booth
“Ba ta da wani abokin rigima a wannan masana’anta ta fim. Tun da mu ke ba mu taɓa yi mata sulhu da wani ba na faɗa ko na wani abu. Gaskiya halin ta ya na da kyau. Mun yi zaman lafiya a aikin mu, ga shi kuma Allah ya sa an rabu lafiya. Irin zaman mutuncin da mu ka yi ne ma ya sa yau na zo tun safe aka haɗa ta; komai da ni aka yi mata.
“Wannan masana’anta ba za ta taɓa mantawa da ita ba duba da cewa mace ce wadda ta ɗauki fim a matsayin sana’a ƙwarai da gaske ba wasa ba, domin kan haka ne ma ya sanya ta sako ‘ya’yan ta na cikin ta a ciki. Saboda haka ba za mu manta da ita ba. Ta na ƙaunar harkar fim, ta na son ci-gaban masana’antar. Wannan shi ne ya ƙara burge ni da ita.”
Wasu daga cikin jarumai da mujallar Fim ta yi tozali da su a gun wannan jana’iza sun haɗa da Baballe Hayatu, Ali Nuhu, Alhassan Kwalle, Yakubu Muhammad, Mustapha Musty, Bashir Nayaya, Lawan Garba Taura, Nazifi Asnanic, Isah A. Isah, Mudassir Haladu, Falalu A. Ɗorayi, Aminu A. Sharif (Momo), Hajara Usman, Adama Daɗin Kowa da kuma Rasheeda Adamu (Maisa’a).
Mu na addu’ar Allah ya jiƙan Mama Zee, ya yi mata rahama.
Su Mudassir Haladu da Mustapha Musty a wajen jana’izar Hajiya Zainab Booth
Allah yajikanta yakumasa aljannace makomarta
ReplyDelete