Sai dai a wannan karon ba wani sabon mutum ta aura ba, ta koma gidan tsohon mijin ta ne, Alhaji Mu’azu Yusuf, wanda lauya ne a Kano.
Mu’azu dai shi ne mijin ta na biyu, kuma su na da ‘ya’ya biyu, Ahmad da Yasmin.
A auren ta na farko, wanda ta yi a Birnin Kebbi bayan an ɗaura shi a ranar 1 ga Nuwamba, 2014, ta haifi ‘yar ta ta fari, wato Hafsat, wadda ake wa laƙabi da Preety.
Mujallar Fim ta fahimci cewar Fati KK ta saba ɓoye duk wani aure da aka ɗaura mata, sai dai daga baya a ji labari. Haka ta yi a auren ta na farko da na biyu.
A lokacin waɗancan aurarrakin, yawancin mutane sun samu labarin ne ta wata hanya, amma wakilan mujallar Fim sun samu halartar ɗaurin aure, wanda daga baya mun buga cikakkun bayanai.
A wannan karon, sai dai kawai gani aka yi jiya da yamma jarumar ta Kannywood ta ɗora wasu hotuna inda ta yi shigar amarya kamar a wurin taron bikin nata.
Haka kuma ta rubuta kalaman godiya ga Allah, ta ce: “Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah… Allah ka ba mu zaman lafiya ni da miji na. Ya Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu.”
Sai dai kuma ba ta faɗi wanda aka ɗaura auren nata da shi ba, illa dai ta kira kan ta da “Mrs M.”, wanda hakan dai na nufin “matar Mu’azu” kamar yadda wannan mujallar ta gano.
Wata majiya ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa har Fati ta tare a gidan mijin ta a Kano.
Amarya Fati KK wajen walimar sabon auren ta da aka ɗaura jiya
Amarya Fati KK wajen walimar sabon auren ta da aka ɗaura jiya
Wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin tsohuwar jarumar, amma hakan bai yiwu ba domin a duk lokacin da ya kira ta sai ta danna ƙin amsa kiran nasa a waya.
Karanta kuma Ko a Aljanna ina so Muhibbat ta zama mata ta, inji Hassan Giggs
Wakilin namu ya so ya samu ƙarin bayani game da auren daga gare ta da kuma makomar shagon sayar da kayan amfani a cikin gida da ta buɗe kwanan baya a Kaduna.
Fati da Mu’azu a wani tsohon hoto nasu
Idan masu karatu za su iya tunawa, a lokacin da auren ta da Alhaji Mu’azu ya mutu a cikin 2018, tsohuwar jarumar ta faɗa wa mujallar Fim a wata hira da mu ka buga cewa dangin sa ne su ka kafa mata ƙahon zuƙa da damuwa kala-kala, har su na yi mata gori.
Shi ma Mu’azu, a wancan lokacin ya faɗa wa mujallar Fim cewa Fatin ce ta bijire masa saboda zai yi mata kishiya.
Amma a hirar ta da Fim a lokacin, Fati KK ta ƙaryata zargin da dangin nasa da shi su ka yi mata, ta ce don me za ta hana shi ƙara aure bayan lokacin da ya aure ta ɗin ita ma ta samu uwargidan sa tare da shi? Ta ce ya faɗi haka ne domin ya ɓata mata suna a idon duniya.
To, yanzu dai komai ya wuce, sun sasanta kan su.
‘Yan fim da dama sun taya Fati murnar wannan aure da ta sake yi.
Mu ma mu na addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, ya kasance mutu-ka-raba.
Amarya Fati KK tare da tsohuwar jaruma Wasila Isma’il a wajen bikin
Amarya Fati da ango Mu’azu a ranar maida auren su
0 comments:
Post a Comment