Malam Muhammad Adamu ya rasu ne a safiyar yau Asabar a asibiti a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Shekarun sa 86 a duniya.
Marigayin dai ɗan asalin Jihar Adamawa ne wanda ya dawo unguwar Sabuwar Gandu, Kano, da zama a shekarun baya.
An gudanar da jana’izar sa kamar yadda Musulunci ya tanada, aka kai shi maƙabartar da ke Kwanar Barka, Sabuwar Gandu, da misalin ƙarfe 1 na rana.
Aisha Muhammad, wadda ita ce babbar ‘yar marigayin, ta shaida wa mujallar Fim cewa mahaifin ta ya bar ‘ya’ya takwas, maza 4 mata 4, da kuma matar sa ɗaya.
Ta ƙara da cewa ta ƙadu matuƙa saboda rashin mahaifin nata wanda da man shi kaɗai ya rage mata bayan rasuwar mahaifiyar ta.
Ta ce, “Babu abin da zan ce da Allah sai godiya, domin ina gida aka kira ni aka ce ya faɗi kamar yadda matar sa ta sanar da ni yau da asuba, kuma da man na san ya na da lalura.
Malam Muhammad Adamu ya rasu ya na da shekara 86 a duniya.
“Nan da nan na zo mu ka kai shi asibiti, har ta kai ga an sa masa abin shaƙar iska (oxygen). Ana haka kuma Allah ya yi masa cikawa.
“Da man shi Allah da ya halicce mu mu ka zo duniya dole zai jarabce mu, amma na ji ɗaci domin yau na rasa kowa, ɗan idon da na ke gani ba ni da shi. Ba ni da kowa, ba ni da uwa ba ni da uba. Allah ya jiƙan su da rahama.” Da faɗin haka sai ta soma kuka.
Tuni dai abokan sana’ar Aisha na fim su ka fara aika mata da saƙon ta’aziyya, yayin da wasu su ka je har gida su ka yi mata gaisuwa.
Allah ya jiƙan Malam Muhammadu, ya ba iyalan sa jimirin jure wannan babban rashi, amin.
Cewar Aisha a cikin alhini: “Yau na rasa kowa, ɗan idon da na ke gani ba ni da shi. Ba ni da kowa, ba ni da uwa ba ni da uba.”
0 comments:
Post a Comment