yana murmushi ya karaso wajena, sallama yayi gami da ce min amarya kin sha kamshi, ledojin da je hannun shi ya ajiye a kan side drower sanan ya hau kan gadon da nake, kusa dani ya xauna tare da bude lillibin da ke rufe a fuskata, ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, cikin kulawa yake min magana my niimatullahi meye na kuka, bayan kina tare da mijinki, godiya xamu yiwa Allah da ya cika mana burin mu na xama ma'aurata, kiyi hakuri ki daina kuka haka kowace mace take samun kanta,a kawota gidanta har ta girma ta haifi yaya ita ma ta zama uwa, hada ni yayi da jikinsa tare da cire min mayafin dake sanye a jikina rarrashina ya shiga yi gami da shafa kaina tamkar jaririya, cikin salon soyayya yake kallona, wow!! amaryata kin yi kyau sosai, don ma kukan nan da kika
ya bata min kwalliyata dubi fa har idonki ya fara kumbura.
turo baki nayi to ba innah ce taki biyo ni ba, dariya yayi gami da cewa kiyi hakuri, a cikin daren nan zan kai ki har gidan innah amma ki share hawayenki ki daina kuka tukunna.
handkercheif yasa ya fara goge min hawayen da ya cika fuskata, cike da nutsuwa ya sake kallona tashi mu yi alwala mu yi sallah mu godewa Allah a bisa niimar samun juna da yayi mana.
Hannuna ya kama xai mikar da ni tsaye amma na makale naki tashi, cike da shagwaba nake masa magana baxan tashi ba har sai ka min alkawarin xaka mayar da ni wajen innah yanxu, murmushi yayi tare da kwantar da ni a kirjinsa, xan kai ki babyna tashi mu fara gabatar da sallah sai mu yi magana, alwala muka dauro inda muka yi nafila sannan muka yi addu'a muka shafa.
ledar da ya shigo mana da ita ya dakko, inda ya fara fito min da kayan da ke ciki, kayan kwalliya ne da kayan shafe shafe da kuma sleeping drees na haduwa, daya ledar kuma kaxa ce da kuma fresh milk, cikin nutsuwa ya dakko min kaxar karbi kici babyna nasan kina jin yunwa, gefe nayi da kaina bana ci, dago fuskata yayi me yasa baxa ki ci ba Niimatullah, cikin shagwaba nace masa ance maganin bacci kuke sakawa a ciki, dariya yayi tare da cewa wannan tunanin ki daina yinsa karya aka fada miki, lallaba ni ya fara yi a kan naci kaxar amma naki, tashi yayi ya shiga kitchen ya dakko cup, fresh milk din ya tsiyaya min a cup karbi ki fara sha kinji babyna kurba nayi na ajiy shi a gefe, matsowa yayi daf dani tare da dafa kaina so nake yi ki shanye gaba daya tunda kin ki cin naman na riga na karbi amanar ki a wajen baba hakkina ne na kula da ke my niimatullah, karba nayi na fara sha, kadan na sha na ture hannun shi, bayan mun gama sha ne ya dauki kayan ya tattara ya kai kitchen.
komawa nayi gefe na jingina kaina jikin pillow wani fargaba da tsoronsa ne ya xiyarci xuciyata, tashi yayi ya shiga bathroom jin shi nayi yana wanka daga bisani ya fito daure da towel, ina kallon shi sau daya na sunkuyar da kaina wani kwarjini ya kara min a idona ban taba xaton haka dattijona yake ba. fita yayi sanyo jallabiya fara sannan ya dawo ya xauna.
cike da kulawa yake min magana Niimatullah tashi kema kije ki watsa ruwa, cikin dasasshiyar muryata na amsa masa da nayi wanka tun a gidan innah, cike da xaulaya ya dube ni ki tashi kije kiyi ko na kai ki nayi miki kinga yau dai mu biyu ne babu innah ballantana kiyi min tonon silili.
da sauri na tashi saboda yanxu ina tsoron wasan sa yanxu xai mayar da abin gaske, shiga bandakin nayi na fara watsa ruwa sai da na saka kayana complete sannan na fito, kallona yayi yana murmushi da wannan kayan xaki kwanta Niimatullah cike da tsiwa nace mashi dam da wanne xan kwanta, ni da su na saba kwana a gidan mu, jan kumatuna yayi tare da cewa nan ai ba gidan ku bane nan gidanki ne kuma gidan mijinki abinda nake so shi xa a yi, tashi yayi ya jawo ledar da ya shigo da ita, wata fitinanniyar mitsitsiyar riga ya dakko min tare da cewa, da wannan nake so kiyi bacci daga yau na hana ki bacci da atamfa.
cikin shagwaba na mayar masa da amsa ni Allah baxan saka wannan kayan kafiran ba, matsowa yayi ya rungume ni yana sumbatar goshina, shi nake so ki saka min Allah ko kuma yau din nan mu yi yaki ni da ke.
kokarin xame jikina na shiga yi amma na kasa cikin kuka nace masa, ka sake ni xan saka maka,a hankali ya cika ni na koma gefe ina mayar da numfashi,lumshe idanu yayi yana sake kallona, ki saka min kin ji my Niimatullah idan baki saka min ba waye xai saka min? cikin tsiwa nace ga matarka can ita xata saka maka, tasowa yayi ya matso kusa da ni da sauri na matsa tare da kwala ihu xaunawa yayi yana min murmushi ki daina tsorona ni ba abinda xan miki, da yaga dai ba nida niyyar saka kayan ne ya kyale ni komawa kasa nayi na xauna.
takowa yayi har inda nake ya tsaya daga baya yana min magana ya kamata mu kwanta Niimatullah nasan kin gaji nima na gaji sosai tashi kixo ki kwanta, gyara min gado ya shiga yi, tashi ki kwanta kin ji babyna, makale kafada nayi tare da tambayarsa kai a ina xaka kwana.
shafa gashin kansa yayi a kusa da ke mana, kuka na fara yi Allah baxan kwana tare da kai ba, dariya yayi min tare da cewa kiyi kwanciyar ki da wasa nake yi nima dakina xani na kwanta, kashe min fitilar dakin yayi sannan ya fita ban san ina xai je ya kwana ba.
kwantawa nayi na dade ina mutsu-mutsu kafin bacci ya dauke ni saboda tunanin innata,cikin dare naji tashin numfashi a bayana a xabure na juya don ganin wane ne dattijona na gani kwance ya manna bayana da kirjinsa, muna hada ido ya sakar min murmushi tare da juyo da fuskata sake manna ni da kirjinsa yayi tare da kissing dina, cikin kuka nake tambayarsa meye haka dattijona kai da kace xaka yi bacci me yasa ka dawo xaka hana ni nawa baccin? cike da soyayya yace matukar ban hada jikina da naki ba baxan iya bacci ba niimatullah ki taimaki mijinki ki barni naji dumin ki.
kuka na fara yi masa, kokawa muka shiga yi da shi, cikin shagwaba yake min magana
kiyi hakuri my niimatullah na raya mana wannan daren da muka dade muna jiransa baxan iya hakuri da ke a halin yanxu ba ihu na shiga yi ina kiran innah da kyar na kwace na fada bandaki na mayar da kofa na kulle ina mayar da numfashi.
buga kofar bandakin ya fara yi yana rokona na bude na fito har da dan kukan shi amma naki bude masa, nima cikin kukan na ke bashi amsa Allah baxan fito ba tunda haka abinka yake, kuma gobe da safe xan tafi gida duk abinda kayi min sai na fadawa innata kuma baxan sake kwana a gidanka ba,lallabani ya shiga yi ki fito Niimatullah indai kika fito yanxu xan dauke ki na mayar da ke gida na miki alkawari, kin fitowa nayi duk nacin da yayi min haka na kyale shi tsaye yana ta faman bugun kofa.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*
28
murxani yake yi ko ta ina, ni kuwa sai ture shi nake ina kuka, ihu nake ina neman daukin innah amma ina dattijo bai ma san a duniyar da yake ba, jikina duk yabi ya mutu saboda wani irin yanayi da na shiga, aikin nasa naga ya fara canja salo domin dattijo gaba daya ya fita a hayyacin sa kokarin rabani yake da sauran kayan da suka rage a jikina, cixo na rika kai masa gami da tunkude shi amma duk yadda nayi a kan na kwaci kaina na kasa,ban taba xaton karfin dattijo ya kai haka ba, kokarin hana shi na ke yi amma shi burin shi kawai ya samu nutsuwa a tare a ni, duk dukan shi da nake yi ina magiya amma gaba daya baya ji na. jin da nayi ya rufa a kaina yasa jikina ya fara karkarwa sosai saboda tsoro da fargabar kada ya raba ni da budurcina tuni na kwala wani ihu, na cigaba da kokawa da shi gaba daya ya sakar min nauyinsa na kasa sarrafa jikina, ganin ba shi da niyyar saurara min yasa na hakura da dukan da nake masa domin kuwa duk jikina ba karfi, matse jikina nayi ta yadda baxi samu damar aikata abinda yake so ba, daga nan ban sake sanin a inda nake ba.
farkawa nayi na ganni rugume a jikin shi ya rufe ni da blanket jikina duk ya jike da gumi, sannu naji ya furta daga bakinsa gami da shafa fuskata yana bani hakuri.
kiyi hakuri Niimatullah duk abinda nayi miki sonki ne ya jawo min, xuciyata ta kasa jure hakurin rashinki amma ai Alhamdulillah ban yi babban aikin ba ko? ya tambaye ne tare da dago fuskata, wata harar na rika cilla masa, cike da kulawa ya sake dubana ki gafarce ni babyna baxan sake yunkurin yi miki abinda bakya so ba.
idanuna cike da kwalla na dube shi, dama ka kawo ni nan ne don ka rika xaluntata, shi yasa ka raba ni da innata kuma ka hana taxi ta xauna tare da ni kaga yanxu duk jikina ciwo yake, ka kama ka wanni danne ni da wannan katon jikin naka, Allah yau sai na tafi gidan innata kuma duk abinda kayi min sai na fada mata.
shafa gashin kaina yayi wanda gaba daya ya hargitse saboda wuyar da ya sha a hannun dattijo, kada na fara jin kin fadawa wani abinda ya faru tsakanin mu idan kika fada Allah sai kin ga babban aikin da xan miki, naga alama sai na fara koya miki hankali.
Tsoron shi ne ya kamani na fara yi masa magiya, kayi hakuri dattijona baxan fada mata ba, amma dan Allah ka daina yi min haka kaga bana so, hada fuskata yayi da tashi tare da cewa ai naga kin tsorata da yawa Niimatullah, ban san me yasa kika sa tsoran abin nan a ranki ba da kin bani dama komai a hankali xan miki, ba burina ne na cutar dake ba, fatana kawai ki gane muhimmancin ki ga rayuwata da kuma irin illar da soyayyarki xata min idan kika hana ni abinda nake so, amma zan cigaba da hakuri har xuwa lokacin da hankalin ki xai kwanta ki fara son abin da kan ki.
daga ni yayi ya xaunar da ni yana kallona yanxu ki tashi mu je mu yi wanka, makale kafada nayi ni Allah baxan yi wanka tare da kai ba.
murmushi yayi tare da riko hannuna ni fa yanxu na daina daka ta taki Niimatullah duk abinda naga ya dace shi xan rika yi miki, xare blanket din yayi daga jikina ya dauke ni cak, harba kafafuna na rika yi ina son sakkowa amma na kasa sai da ya kai ni bandaki ya wanke ni tsaf sannan ya dawo da ni ya ajiye, kaya masu kyau ya dakko ya sanya min, sannan yaja jam'i muka yi sallar asubah, muna idarwa ya mayar da ni gado na cigaba da baccina kasancewar jiya ya dame ni da fitina ban samu na rintsa ba.
shi kuwa dattijo parlour ya koma yana tuna irin nutsuwa da farin cikin da ya samu a tare da Niimatullah, shafa fuskarsa yayi yana tuna irin laushin da jikinta yake da shi da irin gigicewar da yayi, komai nata yayi masa yadda yake so, ya so a ce ya isa wajen da ya dade yana son xuwa a jikinta, tun yanxu ma ya fara fita daga hankalinsa ina kuma ga ya santa a ya mace, Allah ne yasan irin dadin da xai ji.
tashi yayi ya nufi dakin da take, kare mata kallo ya shiga yi xuciyarsa sai tunxura shi take a kan yaje ya kara maimaita mata abinda yayi jiya, wata xuciyar kuma tace ya kyaleta, karasawa yayi inda take kwance ya manneta da kirjinsa shi ma ya cigaba da baccin tare da ita.
Kasa cigaba da baccin yayi saboda matukar yana jinsa a kusa da ita baxai iya hakuri da ita ba, don haka ya tashi ya koma wani dakin don cigaba da baccinsa.
ni kuwa ina tashi da kuka na farka, duk gabban jikina ciwo suke saboda cakudar da na sha a hannun dattijo ba ma kamar breasts dina da suka fi shan bakar wahala a hannun shi, hawaye ne suka rika kwarara a fuskata, a xahiri nake cewa dama haka maxa suke yan iska wlh yau baxan sake kwana a gidan nan ba sai naje na fadawa innah, na fara gajiya da xaluncin da yake min, da karfi nake fada ina kuka, kayana na shiga tattarowa ina xubawa a jaka.
sautin kukan da nake yi ne ya tasar da shi daga baccin da yake yi, a firgice ya karaso dakina, karasowa yayi kusa da ni yana tambayata, lafiya Niimatullah ina xaki je kaina a kasa na bashi amsa saboda yanxu kunyarsa nake ji bana son na hada idanuna da nashi saboda abinda yayi min jiya, cike da tsiwa nake masa magana.
Allah baxa kwana a gidan nan ba sai dai duk abinda xai faru ya faru, gidan innata xan koma ni ban saba irin wannan rayuwar ba, cike da kulawa ya matso daf da inda nake kamo ni yayi ya hada bakina da nasa, hura min iska a kunnena yayi cikin salon soyayya ya ke min magana.
Niimatullah wannan ita ce rayuwa mafi dadi a duniya kuma ita ce rayuwar da kowane dan adam yake burin riskarta, komai da kike yi da halal din ki kike yi kuma lada Allah xai baki, wani salon soyayya ya rika yi min wanda gaba daya ya kashe min gabban jikina, manna ni yayi da bango yana cigaba da sumbatata tare da shafa dukkan sassan jikina, sai da ya kara maimaita min irin abin jiya sannan ya kyale ni, yana mayar da nunfashi ni kuwa kuka na cigaba da yi, na rasa yadda xan yi da dattijona saboda irin wannan maitar da yake gwada min, yanke shawarar kiran malama nayi don jin abinda xata fada min game da irin abubuwan da yake min.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
*dedicated to Aysha shu'aib zakirai*
27
Rungume nake a kirjin dattijona labarai masu dadi ya cigaba da bani, wasu a kan matar shi da irin musgunawar da take masa, wasu kuma a kan al'amuran da suka shafi rayuwar shi a cikin labaran yana dan nuna min yadda yake shaukina da hakurin rashina da yake yi.
dada manna ni yayi da jikinsa tare da sumbatar fuskata,
Allah ya sani ina matukar kaunar ki Niimatullah hakan ne ma yasa na aure ki, don na rika ganin kyakkyawar fuskar ki a kusa da ni, kuma ki rika debe min kewar rashinki, ki tausaya min matata na samu damar jin dumin jikinki, Allah ya sani zina bata taba burge ni ba, kuma bata cikin ra'ayina amma da tuni na dade da lalacewa.
don a wanan lokacin da muke ciki mata da yawa suna kawo min kansu domin mu kara musu matsayi ko wata alfarma, ina ganin wasu na yi amma ni hakan sam bai taba burgeni ba, saboda bana son na kasance cikin masu sabawa Allah ta hanyar neman matan da basu halatta a gare su ba. domin Allah ya tanadi axaba mai yawa ga masu aikata xina, wannan dalilin yasa na auro ki domin ki share min hawayena ki tsamo ni daga wannan bakar rijiyar da na dade a cikinta.
cike da kulawa nace xan tsamoka babyna, xan fadawa innah ta kawo min igiya na janyoka, murmushi yayi gami da dukan bayana ba irin wannan nake nufi ba,wai ke a dole sai kin kadar da hankalina ko Niimatullah? to ai na gano ki.
haka muka zauna muna hira yana bani labarai da kuma shawarwari masu yawa,sannan ya nusar da ni a kan illar gujewa shimfidar miji.
jikina naji duk yayi sanyi nayi nadamar guje masa da nayi a baya,sannan kuma na tausaya masa irin halin da ya samu kansa a ciki,sai dai har yanxu ina jin baxan iya sallama masa kaina ba saboda ina jin fargabar hakan, ga kuma son xuwa ganin innata da nake yi,shawara na shiga yi da xuciyata wata xuciyar tace na yarda da shi wata kuma tace kada na yarda na kyale shi xai sakko da kansa.
Alwala muka dauro tare sannan yaja mana jam'i muka yi sallah, bayan mun idar mun yi addu'a ne naga ya tashi tare da cewa ina xuwa uwar yayana.
fita naga yayi bai dade ba ya dawo hannun shi dauke da leda, ashe gidan abinci yaje ya siyo mana, cike da shagwaba na dube shi, me yasa kake son kashe kudinka dattijona?ai ni ya kamata na dafa maka duk abinda kake so, fuskar shi a sake yake min magana, bana son kisha wahala ne shi yasa Niimatullah, kinga ke amanata ce.sai da ya ciyar da ni abincin sosai na koshi ya bani lemo sannan ya kyale ni.
bayan mun kammala cin abincin ne ya shiga bandaki yayi wanka, yana fitowa ya tsaya jikin dressing mirror yana kallona tare da kashe min ido, cike da soyayya yake min magana.
my Niimatullah taso ki shafa min mai, makale kafada nayi tare da cewa a'a ka shafa da kanka, shagwaba ya hau yi min har da buga kafa a kasa a lallai ni xan shafa masa, tunawa da nasihar innah nayi na cewa kada na xama mai gardama a gare shi, cike da nutsuwa na dakko man na shiga shafa masa, ina fara shafa masa naji yace wash Niimatullah!! a firgice na tambaye shi lafiya dattijona bayan naka ne yake ciwo? cike da shagwaba ya daga min kai tare da cewa eh ciwo yake amma da kike shafawa naji ya fara sauki, cigaba nayi da shafa masa har na kammala, sake dubana yayi kamar xai yi kuka, tambayar shi nayi abinda yake bukata.
cikin shagwaba yace sai na dakko masa kayan da xai sanya, kananan kaya masu kyau na dakko masa kafin na mika masa sai da na feshe kayan da turare sannan na mika masa, kawar da kansa yayi gefe, ni Allah baxan saka ba tunda dai ina da ke kece xaki saka min.
kallon shi nayi kamar xan yi kuka, haba dattijona dan Allah ka saka ai nayi kokari da na dakko maka, kallona yayi tare da lumshe idonsa, idan fa baki saka min ba da towel xan kwana kuma kin san idan bacci yayi bacci tsaf xai yaye ko? da sauri na karba na shiga saka masa kayan, da wandonsa da towel na hada na saka masa, shagwaba ya fara yi min a kan hakan baxai yiwu ba kowanne sai dai na saka masa daban, kuka na fara yi masa da kyar ya hakura ya daka abin shi da kansa.
da misalin karfe goma na kwanta saboda har yanxu akwai yar gajiya a jikina sallama yayi min ya nufi inda yake kwanciya, har ya kai bakin kofa na kira shi, cikin tausasa murya nake masa magana dan Allah yau idan na kwanta kada tashe ni kaga nayi maka aiki na gaji da yawa, murmushi yayi kada ki damu Niimatullah baxan tashe ki ba ai ina son farin cikin ki, kulle min kofar dakin yayi tare da cewa sai da safe amaryar dattijo, bayan na kwanta bacci ya dauke ni kawai naji mutum makale da ni, muryar sa naji kasa kasa yana yi min magana kiyi hakuri ki barni naji dumin jikinki ki taimake ni na nuna miki tsantsar son da nake miki, kinga yau har mun ci kwana biyu a cikin kwanakin da xan yi a dakinki ki bani dama na baki kulawa a kwanaki biyar din da suka rage mana, cikin kuka na juyo ina masa magana.
mun yi alkawari fa da kai a kan baxa ka dawo ba to me yasa xaka karya min dattijona? shafa kaina yayi son da nake miki da begenki su suka hana na cika miki alkawarin ki Niimatullah har na kwanta na kasa bacci ji nayi duk duniya babu abinda nake bukata sama da ke, ki taimaki mijinki ki bashi abinda ya fi so daga gare ki.
sarrafa ni ya fara yi ta ko ina, yayinda ni kuma jikina duk ya hau rawa saboda tsoro da fargabar haduwa da shi ta kama ni, amma kuma na kasa hana shi abinda yake yi hannunshi naji ya saka yana kokarin cire min riga, da sauri na rike hannun shi na fara kokarin hana shi aikata abinda yayi niyya, kwace hannun yayi inda ya samu nasarar cire min riga dukiyar fulanina ta bayyana a fili, ihu na fara yi ina kiran innah da baba, sarrafa ni ya shiga yi ko ta ina, ji nayi ina kokarin fita daga hankalina saboda irin abubuwan da yake min, cikin kuka nake rokonsa yayi hakuri amma bai ma san a duniyar da yake ba.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
*dedicated to Nadeeya Baba Ibraheem*
28
murxani yake yi ko ta ina, ni kuwa sai ture shi nake ina kuka, ihu nake ina neman daukin innah amma ina dattijo bai ma san a duniyar da yake ba, jikina duk yabi ya mutu saboda wani irin yanayi da na shiga, aikin nasa naga ya fara canja salo domin dattijo gaba daya ya fita a hayyacin sa kokarin rabani yake da sauran kayan da suka rage a jikina, cixo na rika kai masa gami da tunkude shi amma duk yadda nayi a kan na kwaci kaina na kasa,ban taba xaton karfin dattijo ya kai haka ba, kokarin hana shi na ke yi amma shi burin shi kawai ya samu nutsuwa a tare a ni, duk dukan shi da nake yi ina magiya amma gaba daya baya ji na. jin da nayi ya rufa a kaina yasa jikina ya fara karkarwa sosai saboda tsoro da fargabar kada ya raba ni da budurcina tuni na kwala wani ihu, na cigaba da kokawa da shi gaba daya ya sakar min nauyinsa na kasa sarrafa jikina, ganin ba shi da niyyar saurara min yasa na hakura da dukan da nake masa domin kuwa duk jikina ba karfi, matse jikina nayi ta yadda baxi samu damar aikata abinda yake so ba, daga nan ban sake sanin a inda nake ba.
farkawa nayi na ganni rugume a jikin shi ya rufe ni da blanket jikina duk ya jike da gumi, sannu naji ya furta daga bakinsa gami da shafa fuskata yana bani hakuri.
kiyi hakuri Niimatullah duk abinda nayi miki sonki ne ya jawo min, xuciyata ta kasa jure hakurin rashinki amma ai Alhamdulillah ban yi babban aikin ba ko? ya tambaye ne tare da dago fuskata, wata harar na rika cilla masa, cike da kulawa ya sake dubana ki gafarce ni babyna baxan sake yunkurin yi miki abinda bakya so ba.
idanuna cike da kwalla na dube shi, dama ka kawo ni nan ne don ka rika xaluntata, shi yasa ka raba ni da innata kuma ka hana taxi ta xauna tare da ni kaga yanxu duk jikina ciwo yake, ka kama ka wanni danne ni da wannan katon jikin naka, Allah yau sai na tafi gidan innata kuma duk abinda kayi min sai na fada mata.
shafa gashin kaina yayi wanda gaba daya ya hargitse saboda wuyar da ya sha a hannun dattijo, kada na fara jin kin fadawa wani abinda ya faru tsakanin mu idan kika fada Allah sai kin ga babban aikin da xan miki, naga alama sai na fara koya miki hankali.
Tsoron shi ne ya kamani na fara yi masa magiya, kayi hakuri dattijona baxan fada mata ba, amma dan Allah ka daina yi min haka kaga bana so, hada fuskata yayi da tashi tare da cewa ai naga kin tsorata da yawa Niimatullah, ban san me yasa kika sa tsoran abin nan a ranki ba da kin bani dama komai a hankali xan miki, ba burina ne na cutar dake ba, fatana kawai ki gane muhimmancin ki ga rayuwata da kuma irin illar da soyayyarki xata min idan kika hana ni abinda nake so, amma zan cigaba da hakuri har xuwa lokacin da hankalin ki xai kwanta ki fara son abin da kan ki.
daga ni yayi ya xaunar da ni yana kallona yanxu ki tashi mu je mu yi wanka, makale kafada nayi ni Allah baxan yi wanka tare da kai ba.
murmushi yayi tare da riko hannuna ni fa yanxu na daina daka ta taki Niimatullah duk abinda naga ya dace shi xan rika yi miki, xare blanket din yayi daga jikina ya dauke ni cak, harba kafafuna na rika yi ina son sakkowa amma na kasa sai da ya kai ni bandaki ya wanke ni tsaf sannan ya dawo da ni ya ajiye, kaya masu kyau ya dakko ya sanya min, sannan yaja jam'i muka yi sallar asubah, muna idarwa ya mayar da ni gado na cigaba da baccina kasancewar jiya ya dame ni da fitina ban samu na rintsa ba.
shi kuwa dattijo parlour ya koma yana tuna irin nutsuwa da farin cikin da ya samu a tare da Niimatullah, shafa fuskarsa yayi yana tuna irin laushin da jikinta yake da shi da irin gigicewar da yayi, komai nata yayi masa yadda yake so, ya so a ce ya isa wajen da ya dade yana son xuwa a jikinta, tun yanxu ma ya fara fita daga hankalinsa ina kuma ga ya santa a ya mace, Allah ne yasan irin dadin da xai ji.
tashi yayi ya nufi dakin da take, kare mata kallo ya shiga yi xuciyarsa sai tunxura shi take a kan yaje ya kara maimaita mata abinda yayi jiya, wata xuciyar kuma tace ya kyaleta, karasawa yayi inda take kwance ya manneta da kirjinsa shi ma ya cigaba da baccin tare da ita.
Kasa cigaba da baccin yayi saboda matukar yana jinsa a kusa da ita baxai iya hakuri da ita ba, don haka ya tashi ya koma wani dakin don cigaba da baccinsa.
ni kuwa ina tashi da kuka na farka, duk gabban jikina ciwo suke saboda cakudar da na sha a hannun dattijo ba ma kamar breasts dina da suka fi shan bakar wahala a hannun shi, hawaye ne suka rika kwarara a fuskata, a xahiri nake cewa dama haka maxa suke yan iska wlh yau baxan sake kwana a gidan nan ba sai naje na fadawa innah, na fara gajiya da xaluncin da yake min, da karfi nake fada ina kuka, kayana na shiga tattarowa ina xubawa a jaka.
sautin kukan da nake yi ne ya tasar da shi daga baccin da yake yi, a firgice ya karaso dakina, karasowa yayi kusa da ni yana tambayata, lafiya Niimatullah ina xaki je kaina a kasa na bashi amsa saboda yanxu kunyarsa nake ji bana son na hada idanuna da nashi saboda abinda yayi min jiya, cike da tsiwa nake masa magana.
Allah baxa kwana a gidan nan ba sai dai duk abinda xai faru ya faru, gidan innata xan koma ni ban saba irin wannan rayuwar ba, cike da kulawa ya matso daf da inda nake kamo ni yayi ya hada bakina da nasa, hura min iska a kunnena yayi cikin salon soyayya ya ke min magana.
Niimatullah wannan ita ce rayuwa mafi dadi a duniya kuma ita ce rayuwar da kowane dan adam yake burin riskarta, komai da kike yi da halal din ki kike yi kuma lada Allah xai baki, wani salon soyayya ya rika yi min wanda gaba daya ya kashe min gabban jikina, manna ni yayi da bango yana cigaba da sumbatata tare da shafa dukkan sassan jikina, sai da ya kara maimaita min irin abin jiya sannan ya kyale ni, yana mayar da nunfashi ni kuwa kuka na cigaba da yi, na rasa yadda xan yi da dattijona saboda irin wannan maitar da yake gwada min, yanke shawarar kiran malama nayi don jin abinda xata fada min game da irin abubuwan da yake min.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
*dedicated fatima Gambo mai roba&Rahma idris zawa ciki*
*Yaba kyauta tukwici dole na gode miki Hajiya Rabi M Yara bisa ga kyautar katin waya na kudi masu yawa da kika turo min, kika ce a siya data don a cigaba da suburbudowa jama'a littafi godiya mara adadi Allah ya saka da alkhair,duk mai kaunar matar Dattijo ya yiwa wannan baiwar Allah addu'a Allah ya kara mata arxiki*
29
A ranar wasan buya muka rika yi da shi, gaba daya ban bari mun hadu ba saboda bana so ya takura min.
Bayan nayi sallar isha na fita parlour,
kiran wayar malama na hau yi ina wayar ina xubar da hawayen takaicin abinda Dattijo ke min, gaba daya ji nake na tsani auren kawai yanxu shawarar malama nake jira nace ya sake ni.
kiran farko ta daga wayar cike da ladabi nayi mata sallama, tare da cewa barka da dare malama, cikin sakin fuska ta amsa min,yau amarya ce a gari, ya gidan da mai gida da fatan dai komai yana tafiya dai-dai? shiru nayi na kasa bata amsa sai hawaye da ke gangarowa daga fuskata, cike da kulawa ta sake tambayata,lafiya naji kin yi shiru Niimatullah ko wani abin ne ya faru?ina bude baki zan yi magana kuka ya ci karfina. cigaba da tambayata tayi wai me ke faruwa ne haka Niimatullah ni fa kin tayar min da hankali ko Alhajin ne yayi miki wani abu?
da sauri na amsa mata da eh shi ne. lallaba ni ta shiga yi to yi hakuri ki share hawayen ki fada min abinda ya faru,cikin kukan nake mata magana.
ni wallahi kixo ki mayar da ni gidan innata baxan iya wannan xaman ba, na gaji da auren wannan mayen Dattijon ya takura min, murmushi naji tayi sannan ta fara magana, ina jin yadda kika fara magana nasan ina kika dosa Niimatullah, to fada min abinda yake miki da har kike neman ya sake ki.
hannu nasa na share hawayen da ke fita a idona sannan na fara yi mata magana, Kullum idan na kwanta bacci sai ya rika xuwa yana damuna yana min wasu abubuwa ni kuma ba haka na saba yin bacci a gidan innata ba,na fada masa bana so amma yaki ya daina, yanxu haka duk jikina ciwo yake na karasa maganar ina kuka.
rarrashina ta shiga yi kiyi hakuri Niimatullah ki tarairayi mijinki, ki tarairayi begensa ki bashi kulawa ko don kada kishiyarki ta kwace miki shi, duk karatun da nayi miki a kan kula da miji a ce har yanxu baki haddace ba,sai kin kira ni kin kawo min korafi a kan abinda yake miki,ni wallahi duk a tunanina cewa xa kiyi naxo kin samu ciki.
da sauri na dafe kirjina, ciki fa kika ce malama ni ba ni da komai, katse min maganata tayi, tunda baki bari ya samu abinda yake so ba ina xaki samu ciki haka xaki ta xama ba haihuwa, idan baki yi da gaske ba ma haka xaki ta xama tunda wannnan tunanin banxan bai bar kan ki ba, kin san wani abu kuwa Niimatullah? da sauri na amsa mata da a'a, ko kin san cewa Alhaji yana matukar son haihuwa yana son yaga kananan yara suna kewayawa a gidansa, ko kin san cewa duk ranar da kika haihu a gidansa darajar ki ta kara yin sama sannan duk abinda kike bukata xai yi miki albarkacin yayanki. shiru nayi ina saurarenta, sannan ta sake jefo min wata tambayar, kina so mijin ki ya so ki fiye da yadda yake son kishiyar ki? da sauri na amsa mata da eh saboda idan da abinda nafi so a rayuwata bai wuce dattijona ya rika ji da ni ba.
A duk lokacin da ya bukaci wani abu a wajenki kiyi gaggawar bashi domin da haka ne xaki ribaci xuciyarsa ya so ki, saboda wannan abin shi ya rasa a wajen matarsa kuma kema idan kika hana shi wane hali kike tunanin xai fada, ki koma wajen mijinki yanxu ki nemi gafararsa ya yafe miki saboda na tabbatar da cewa mala'iku sun tsine miki saboda rashin bawa mijinki hakkinsa, kuka na fara yi ni fa ban masa laifi ba Aunty, kuma da gaske kike mala'iku sun tsine min malama? kwarai kuwa don haka yanxu ki nemo hanyar da xaki gyara halin ki wajen farantawa mijin ki, kin san yanxu abinda nake so da ke? gyada kaina nayi kamar tana ganina alamar a'a.
kina so Dattijo ya daina yi miki abubuwan da yake miki ya kuma daina hana ki bacci? da sauri na amsa mata saboda abinda nafi bukata kenan. bayani ta fara yi min.
matakin farko da xaki bi wajen hana shi wannan maitar shi ne, ki rika saka English wears na fitina kina kewayawa a cikin gida yana ganin ki ta haka ne xaki rika debe masa kewa, xaki ga ko kwanciya kika yi baxai rika xuwa ya dame ki ba.
wani dadi ne ya kama ni cikin farin ciki na tambayeta yanxu idan ina haka baxai rika damuna ba?da sauri ta amsa min baxai dame ki ba, ke dai ki gwada kawai, idan wannan hanyar bata yi ba sai mu canja wata kin ji yar albarka.
yanxu ina Alhajin? a sanyeye na amsa mata da yana daki, murmushi tayi, yauwa amma ya naji duk jikin ki yayi sanyi,kada ki tsorata fa ki tsayar da xuciyarki ki samu soyayyar mijinki, amma yanxu kin yi wanka ko? amsa mata nayi da eh sannan ta cigaba da magana, wannan wankan da kika yi bai wadatar da ke ba,ki tashi ki canja sabon wanka ki feshe jikinki da turare ki gyara gashinki ki samu kaya masu fito da surar jiki ki saka, sannan kije ki bashi hakuri a kan guje masa da kike yi, kuma ban ce idan kin je kice ni na saka ki ba, kawai kice kinga ya dace kiyi masa haka ne, saboda shi ne mafi tsadar mutane a wajenki nasan dole xai ji dadi kuma xai saki jiki da ke a sha soyayya.
godiya nayi mata sannan muka yi sallama.
kai tsaye bandaki na nufa inda na fara wanka kamar yadda malama ta umarce ni,wasu hadaddun riga da wando na dakko red colour, hannun rigar karami ne gaban rigar kuma a bude yake, raba gashina nayi gida biyu na daure da ribbon, su ma duk red colour na saka, sannan na fesa turare a bayan kunnena da gabban hannuna da dukkan sassan jikina.
A hankali na taka na shiga har dakin da yake kwance, tarar da shi nayi hannun shi rungume a kirjinsa, idanun shi na kallon sama da alama dai tunanin wani abu yake yi, a hankali na karasa inda yake tare da shafa fuskarsa, cikin sassanyar murya na tambaye shi.
tunanin me kake yi dattijona ga shi har na shigo baka ma san naxo ba, a hankali ya dago ido ya kalle ni tare da riko hannuna, tunanin ki nake yi kin hana ni bacci Niimatullah, da wannan mayataccen kallon nasa yake bina, cikin sassanyar muryarsa ya shafa kaina kin yi kyau my Niimatullah irin wannan wankan nake so ki rika yi min kowane lokaci, kinga yadda kika yi kyau kuwa, kin koma kamar yar tsana.
murmushi nayi tare da cewa, a kullum burina na nemo hanyar da xan faranta maka mijina, ka cancanci fiye da haka daga gare ni saboda kai ne mafi tsadar mutane a wajena,kuma mafi tsadar abinda na mallaka a rayuwata, idan ban faranta maka ba wa xan farantawa, jin dadin kalamai na ne yasa ya jawo hannuna ya sakar min wani hot kiss a saman hannuna, gaskiya ne niimatullahina naji dadi kuma na gode, Allah yayi miki albarka amsawa nayi da ameen.
kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina shafa fuskarsa cike da shagwaba nake masa magana, nifa xuwa nayi na faranta maka dattijo, naga bai kamata na rika hanaka abinda kake so daga gare ni ba, cike da farin ciki ya mike yana dubana da gaske kike Niimatullah, a hankali na amsa masa da eh, shafa gashin kaina yayi yana murmushi.
na gode da wannan babbar kyautar da kika min Niimatullah, kuma naji dadi, kamo ni yayi ya sake manna ni da kirjinsa ya fara wasa da hannuna da kuma breasts dina, wannan abinda kika min ya faranta min rai kuma shi ne abinda nake so ki rika yi min har abada, shafa ni ya rika yi yana sambatu.
ni kuwa cikin raina wani takaici ne ya mamaye ni dama malama wayo tayi min ta turo ni wajen sa dama abinda xai yi min kenan, a hankali na dube shi dattijona xanje nayi fitsari, cikin rada ya fada min a kunnena, ki bari na samu nutsuwa da ke Niimatullah, sai da ya gama jagwalgwala ni sannan ya sake ni, sake kamo ni yayi ya hada bakina da nasa, cikin kuka nace fitsari ya matse ni dattijona.
cike da kulawa ya dube ni to my Niimatullah tunda ke kika kawo kanki xan bari kije kiyi abin ki, amma da ni na kamo ki baxan barki ba, amma kiyi sauri ki dawo kin ji babyna, ko naxo na raka ki?makale kafada nayi nace a'a kayi xaman ka.
ina fita na fada dakina na kulle kofa na fara aikin tunani, dama malama gadar xare ta hada min wallahi sai na fadawa innata tunda bakin su daya da dattijo, gashi nan naje ya wahalar da ni, ji na da yayi shiru ne yasa yaxo dakina don ganin abinda ya hana ni dawowa.
ta cikin windowa ya hango ni na hada kai da fillo ina faman tunani, bakin kofa ya karaso ya fara kokarin bude kofar, jinta yayi a kulle xagayo wa yayi ya fara kiran sunana tare da rokona na bude masa amma naki, cike da shagwaba nake masa magana.
Allah baxan bude ba ka dame ni, magiya ya shiga yi min har da dan guntun hawayensa da kyar na taso na bude masa a ranar dai yayi namijin kokari domin babu abinda yayi min.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
*masu karatu wannan shi ne original duk wanda kika gani bayan wannan ba ni bace kada ki karanta*
*dedicated to Aminiyata masoyiyata abokiyar shawarata, kuma abokiyar fadana Maijidda Bello Allah ya bar mu tare*
30
Washe gari da safe da wuri na tashi na kintsa kaina na gyara dakina, yau kwanana biyar kenan a gidan dattijo wannan dalilin yasa na shiga kitchen don na dafa mana abincin da xa muyi breakfast da shi, haddiyar atamfa na sanya,ba karamin karbata tayi ba,kaina ba dan kwali sai gashina da ya xubo har gadon baya, cike da nutsuwa na karaso wajen shi, cikin salon jan hankali na dube shi, dattijona tashi na hada mana abinci, murmushi yayi tare da miko min hannunsa na mikar da shi tsaye, jan hannun shi nayi har muka isa bakin dining,abincin na shiga bashi muna ci muna hira mai debe mana kewa bayan mun kammala na sake yin wani wankan sannan na dawo jikinsa na kwanta romancing muka cigaba da yi saboda na lura ba karamin debe masa kewa yake yi ba, yau gaba daya bai fita ba abinda ya rika yi da ni kenan ni kuma ban nuna gaxawata ba saboda nasan mijina yana da matukar hakuri da juriya.
Hajiya maryam ce zaune cikin falo, jingine take da kujera sai faman
kada kafa take yi da alama zuciyarta a kusa take, don kallo daya xaka yi mata kasan tana cikin bacin rai, yaron ta munir ne yazo zai shiga dakin shi.
kiran sunan shi tayi, munir xo nan ina son magana da kai, cike da ladabi ya dawo ya tsugunnah tare da cewa gani momy, tambayar shi ta fara yi.
dadynku ya fita ne ko yana nan, cike da nutsuwa ya bata amsa, Aa momy yana nan, tun safe da ya fito ya koma bai kuma fitowa ba, tsaki tayi agogon wayarta ta duba karfe biyar saura na yamma, cike da kulawa yake tambayarta, me yake faruwa momy, a takaice ta amsa masa da ba komai.
fita tayi ta nufi sashin Niimatullah cike da bala'i da gadara take bugun kofar, gami da masifa daga yin aure yau kwana biyar amma har wannan yar iskar yarinyar ta fara juya masa tunani, xai fara juya min baya dama wannan soyayyar da yake mata ai ba banxa ba, da gani asiri ne, yanxu a ce muna gida daya amma baxan rika saka shi a idona ba, lallai da sake, da karfinta take bugun kofar.
A firgice na tashi daga baccin da nake yi saboda bugun da take yi, da saurina na fito parlour don ganewa idanuna abinda ke faruwa.
zaune na tarar da dattijona, sanye yake da singlet da boxer tarar dashi nayi yana ta faman danna computer da alama bai ma san ana yin bugun ba, a hankali na karasa wajensa tare da dafa kafadarsa, dattijona baka ji ana buga kofa bane? a hankali ya dube ni wlh na shagala da aiki ban ji ba, da sauri na nufi bakin kofar don budewa addu'a nake yi Allah dai yasa innah da baba ne suka kawo min xiyara. tare da dattijona, muka nufi kofar ya fara kokarin budewa.
Abokiyar zamana muka gani tsaye tana huci kamar wata macijiya, dattijjo ne yayi karfin halin yi mata magana.
madam lafiya dai ko, ya yara? tsaki tayi tare da galla masa wata uwar harara, cike da ladabi na tsugunnah na gaidata, cike da tsawa ta amsa min da ban wuni ba kya ganni, shegiyar yarinya gaki karama sai uban iyayi kin mallake min miji, kin raba ni da shi, bari kiji na gaya miki duk irin kulle-kullen da ku ke yi ke da iyayanki har kika yi sanadin aure min miji na san shi, kuma wallahi da sannu xan yi maganin ki, juyawa tayi kan dattijo tana masifa.
kai kuma kaji kunya tsohon banxa ka rasa wadda xaka aura sai yarinya karama, wacce ko yayanka sun girmeta, dan tsabar abin kunya ni wallahi kunya kake bani, dubi irin shigar da take jikinta saboda tsabar karuwanci, sai a lokacin na lura da kayan da ke jikina sleeping dress ne riga da wando.
kallona tayi sannan ta saki tsaki saboda wanan abar ne yasa yau baka fito kaga yaranka ba, alhalin dukkan su suna da muradin ganinka, shi yasa tun tuni na hana ka auro dangin asiri saboda nasan abinda xai faru kenan, wallahi ni wannan ko yar aiki bazan dauke ta ba, don baxan xauna da kaxama ba.
cikin fushi ya fara yi mata magana, dakata Maryam na gaji da irin wanan rashin kirkin da kike min, kuma wannan da kika raina tafi min ke sau dari tunda bata daga murya sama da ta mijinta, bata aibata ni, kuma bata gaza wajen kula da ni, da yi min biyayar aure ba, gaba daya na rasa inda hankalin ki da tunanin ki yake, a ce yarinyar da kika haifa a cikin ki da ita xaki xauna kina fada ki mayar da ita abokiyar gabar ki, saboda kawai kina hassadar cewa ta fiki iya kula da miji da tarairayarsa, fita ki bar min sashina kafin na bata miki ran ki, tun farko ke kiya yi watsi da damar ki, da baki san abinda ya dace da rayuwar ki ba, tunda ba xaman lafiya ne xai rika kawo ki ba kada ki sake xuwa nan. mayar da kofar yayi ya kulle sannan yaja hannuna muka shiga daki.
Da dukkan alamu ran shi ya baci da abinda Hajiya tayi masa rarrashinsa na shiga yi ina kwantar masa da hankali, cike da kulawa ya dube ni, ba komai my Niimatullah komai ya wuce, nasan indai ina da ke baxan taba yin bakin ciki ba.
cike da soyayya ya kamo ni ya rungume ni, tashi mu tafi mu sha ice cream Amaryar dattijo, daki na shiga na sanya bakar doguwar riga, nayi kyau sosai sannan muka kama hanya muka tafi, sai da xuciyar mu tayi sanyi muka sha soyayya muka manta abinda matar Alhaji tayi mana sannan muka dawo gida.
kirjinsa na fada saboda na dan gaji da yawa, shafa bayana yayi, Niimatullah kinga irin abinda nake fada miki na rasa a rayuwata ko, shi yasa na shigo da ke cikin rayuwata ki fara bani kulawa.
cike da shagwaba na shafo fuskarsa, xan kula da kai Hubbyna, shi yasa ma a yau nake son wannan daren ya xama daren da xan faranta maka, da sauri ya dube ni da gaske kike Niimatullah ko kuma irin ta ran nan xaki min?
cikin kulawa na dube shi wlh babu wasa a maganata babyna.
cike da farin ciki ya rungume ni sungumata yayi cak kamar wata yar baby sai toilet muka yi wanka tare da alwala, bayan mun fito muka gabatar da sallah irin ta ma'aurata
cikin natsuwa da kwarewa ya fara shafa ta ko'ina, daga nan ya dauke ni ya dire ni a kan gado, da sauri da sauri yake karanto min addu’ar Saduwa da iyali tuni idona ya fara raina fata a hankali ya fara bi da ni, maganganu ya rika yi Please karki fita daga rayuwata Niimatullah ke haske ce a duniyata, sai a kanki na kara tabbatar da meye aure,na kuma kara sanin yadda dad'in mace yake, Niimatullah, ke din ta daban ce, wallahi bazan iya rayuwa babu ke ba, ban san dad'in aure ba sai da na same ki.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
*معذرة🤦🏼♀*
*Har yanxu ina samun korafi da maganganu a kan cewa akwai pragrap na karshe na page din jiya a kan sak komai da komai irin na auren sirri ne, tabbas baxan musa muku ba domin ba xargi kuke ba gaskiya ne abinda ku ka fada, kuma duk wanda yasan littafina da yadda nake rubutu yasan wannan ba rubutuna bane sanya min aka yi sbd ni ban fiye fito da abu kirikiri na fade shi kai tsaye ba, ina fatan masoyana xasu fahimce ni, abinda yasa ban cire wajen ba saboda rubutun ya riga ya gama xaga duniya idan na cire ma kamar ya xama aikin banxa, na gode da kaunar ku gare ni*
31
Tsintar kaina nayi cikin rashin karfin jiki gami da kasala, domin kuwa dukkan wata gaba ta jikina ciwo take yi, can kasan xuciyata kuma wani haushin dattijo nake ji, ban taba xaton abinda xai aikata a gare ni ba kenan, gefena na juya na tarar da shi yana ta faman sharbar bacci abinsa.
kokarin komawa baccin nayi amma radadin da ke ratsa min kwakwalwata ya hana ni komawa, da karfi nake magana Allah baxan kuma kwana a gidan nan ba sai kuma na fadawa innah ta dauki mataki a kan ka tunda abinda kayi min kenan, cikin bacci yaji surutan da nake yi a hankali ya bude idonsa yana kallona, murmushi ya sakar min sannan ya fara min magana.
kiyi hakuri Niimatullah dukkan abinda ya faru ba laifin bane sonki ne ya jawo min, kamata ma yayi kiyi farin ciki amaryar dattijo domin wata darajar ki ce ta kara shiga xuciyata kuma kaunar da ke cikin raina ta kara ninkuwa fiye da, da.
turo baki nayi tare da cewa ba wani nan tunda ka xalunce ni komai ma sai ka fada, ni daga yau na daina kula ka tunda haka kake, rarrashina ya fara yi gami da bani hakuri, ni kuwa wani haushinsa ke kara kama xuciyata. kifa kaina nayi jikin pillow ina cigaba da kukana saboda a halin yanxu shi ne kadai abinda xai sanyaya min raina.
tashi yayi ya nufi toilet, yaje ya kintsa kansa sannan ya dawo, muna hada ido da shi na kawar da kaina gefe saboda a yanxu kallon axxalumi nake masa, kiran sallar asubah aka yi don haka na rika kokarin mikewa amma na kasa tashi, wani kuka na saki tare da cewa, gashi nan ka karya min kafa na kasa tashi, cike da kulawa ya karso gare ni kiyi hakuri Niimatullah ki yiwa mijin ki uxuri na fada miki komai nayi sonki ne ya jawo mini.
taimaka min yayi ya mikar da ni tsaye ya kai ni har bandakin inda ya hada min ruwan dumi na gasa jikina da shi,bayan na kammala na fito yaja mana jam'i muka yi sallah.
muna idarwa naji wani xaxxabi ya rufe ni jikina banda rawar dari babu abinda yake yi, hawaye ne ya shiga fita a idona cikin kuka nake yi masa magana, ni dai ka kira min innata mu yi magana, na fada mata xaxxabi nake yi taxo ta tafi da ni, matsowa yayi kusa da ni tare da kwantar da kaina a kirjinsa, kiyi hakuri Niimatullah kin ga yanxu safiya ce idan aka kira innah a irin wannan lokacin aka fada mata baki da lafiya hankalinta ne xai tashi, ki bari gari ya kara wayewa sosai sai na kira miki ita.
cike da shagwaba nake masa magana, ni dai Allah yanxu xaka kirata idan ba haka ba kuma na dauki jakata na tafi gida, shiru yayi ba tare da ya amsa min ba, wayar da ke gefensa ya dakko ya fara kiran waya, duk a tunanina innah ya kira kawai sai naji salon hirar tasa ya canja.
wani doctor ya kira inda ya shaida masa cewa bana jin dadi, ya fada masa dukkan abinda yake damuna daga karshe ya fada masa cewa yaxo asibiti ya karbar min magani.
cike da mamaki na dube shi, haba dattijona dama ba innata xaka kira min ba sai ka tashi kira wani doctor ni ko ya bani maganin ma baxan sha ba tunda baxa ka kira min innata na fada mata ba.
cike da kulawa ya dafa kafadata kiyi hakuri gari ya waye sosai Niimatullah, yanxu idan innah taji ba ki da lafiya xata iya tahowa yanxu saboda yadda take ji da ke.
shura kafata nayi ina kuka har sai da na hargitsa shirin gadon gaba daya, cikin kuka nake masa magana, ni dai sai ka kira min ita Allah, rarrashina ya shiga yi to kiyi hakuri ki daina kuka yanxu xan kira miki innarki.
ringing daya wayar tayi naci sa'a innah ta dauka, muna fara magana taji na rushe da kuka, Haba innata tunda na tafi kika manta da ni yau kwanana shida amma baki taba xuwa kin ganni ba, gashi nan yanxu haka ba nida lafiya.
A raxane innah take tambayata me ya same ki Niimatullah, cikin kuka nace mata xaxxabi nake kuma............ina maganar dattijo na kallona yana min warning a kan kada na fadawa innata abinda ya faru.
tambayata ta cigaba da yi kuma me Niimatullah?kin fara magana kuma kin yi shiru, cikin sarkewar murya na bata amsa ni dai kixo innah xan fada miki dukkan abinda ke damuna a gidan dattijo, sallama muka yi da ita sannan ta kashe wayarta.
murmushi yayi sannan ya dube ni, Niimatullah kenan sarakan tonon silili, idan innah taxo kika fada mata sai na kara maimaita miki abin jiya, turo baki nayi Allah sai na fada wa yace ka rika takura min.
lallaba ni ya shiga yi saboda yasan wannan kadan ne a cikin karamin aikina babban aikina ya fi gaban haka. tashi yayi ya shiga kitchen ya hada mana breakfast sannan ya dawo ya fara bani har sai da naci na koshi, tashi yayi tsaye yana dubana.
Amaryar dattijo, a hankali na dago ido na kalle shi tare da cewa na'am dattijona, lumshe kyakkyawan idanunsa yayi sannan ya fara yi min magana, xan je yanxu na karbo miki maganin ki, saboda bana son xaxxabin yayi karfi a jikin ki, ki kula min da kanki kinji amaryar dattijo, dago kaina nayi tare da cewa to a dawo lafiya.
Bai dade da fita ba ya dawo hannun shi rike da ledar magani, cikin kulawa ya ballo maganin ya bani amma naki karba, sai da rigima nasha guda daya saboda a rayuwata na tsani magani da allura.
Da misalin karfe sha daya na rana innata ta iso, tun daga nesa na jiyo muryar dattijo na mata sannu da xuwa, ina jin alamun shigowarta dakina na rushe da kuka, karasowa dakin tayi ta same ni ina kuka har da su majina.
cike da damuwa ta karaso inda nake, tambayata ta fara yi, me yake damun ki Niimatullah, kishiyar ki tayi miki wani abu kike wannan uban kukan ko kuma mijin ki,ni dai naga alamun ki baki da wata matsala a tare da ke, kuka na cigaba da yi naki bata amsa har sai da ta fusata.
baxa ki amsa min maganata ba sai na bata miki rai, cikin kuka nace dattijo ne, tana ji na ambaci shi ne ta dakatar da ni, to ya isa kada ki fada min abinda ya hada ku don nasan kwanan xancen, turo baki nayi dan Allah ki bari na fada miki abinda ke faruwa innata.
shi ne Kullum yake...........hannu tasa ta toshe bakina, nace bana bukatar ji ko Niimatullah idan kika kara magana xan dauki takalmana na tafi duk wata mace da kike ganinta a gidan aure hakuri take, saboda aure ibada ne, kuma duk abinda ya xama ibada dole sai an yi hakuri an jure an kuma jajirce wajen yin aiki tukuru, don haka kema ki dage wajen kulawa da mijin ki ta haka ne xaki xama mace ta gari, wacce mijinta xai yi alfahari da ita.
kalaman innata sun shiga kunnena sosai kuma na kudiri niyyar cigaba da amfani da su indai xan xama mace ta gari a wajen dattijona, hirar da muka rika yi kenan har xuwa lokacin da xata tafi gida.
yau ma da riguma muka rabu ji nayi kamar na bita mu tafi, wata kaunarta ce ta kama ni a ranar wuni nayi ina kuka ban iya aikata komai ba wannan dalilin yasa xaxxabina ya kara tsananta saboda kukan da na sha.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*
*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋
*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*
*follow me on instagram @jeeddahtijjani*
32
Haka na kwana jikina duk ba dadi banda tunanin innata ba abinda nake yi, Allah-Allah na rika yi gari ya waye na tambayi dattijona xuwa gidan innata.
yau ta Litinin kuma a yau din kwanakin amarcina da dattijo ya kare a yau xai koma wajen abokiyar xamana da kwana gaba daya bana jin nishadi saboda ko kadan bana so nayi nisa da mijina, gari na wayewa na kintsa ko'ina na gidana, shiryawa nayi cikin wasu tsadaddun English wears na nufi wajen dattijona, cike da nutsuwa nake taku dai-dai tare da sakar masa murmushin da a koda yaushe yake saka min shi nutsuwa da nishadi, cikin salon soyayya ya bude min hannunsa na fada jikinsa kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina kashe masa idanu,cike da shagwaba na dube shi dattijona!!
cikin nutsuwa ya dago kyawawan idanunsa tare da jan kumatuna na'am my Niimatullah?
cikin siririyar murya na fara yi masa magana, dan Allah alfarma naxo nema wajenka angona, shafa gashin kaina yayi, wace alfarma kike nema yar lelen dattijo? kara narkewa nayi a jikinsa sannan na fara yi masa magana. ka bar ni naje gida naga innata yau da tunaninta na kwana na tashi idan ban ganta ba baxan iya bacci ba. cikin kulawa ya bani amsa gaskiya baxan bari ki fara fita yanxu ba amaryar dattijo, satin ki daya fa rabonki da gidan innah amma har kin kosa ki koma, kuma naga jiya innah taxo ta ganki, baba ma da kanshi ya fada min kada na bari ki fara fita sai bayan wata shida, Allah ya sani ina sonki kuma ina kishinki baxan bari ki fara fita yanxu ba, saboda har yanxu kina nan a budurwar ki babu wani kala da matar aure da kika yi baxan barki fita ba wani ya kwace min ke.
turo baki nayi tare da kara kwantar da kaina a jikinsa haba dattijona duk abin nan da ya faru kace ban xama matar aure ba Allah ni dai na xama kawai wayo kake so kayi min, murmushi yayi tare da kanne min ido, baki xama ba fa Niimatullah da saura saboda sau daya abin ya faru idan kina so na barki sai na kara yi kamar sau uku.
da sauri na dago na kalle shi sau uku fa kace,Allah ni dai a'a murmushi yayi min sannan ya cigaba da magana, tunda baxa ki yarda ba sai ki yi ta xama a gida,na rika xuwa ina dakko innah tana ganin ki amma ke dai baxa ki rika fita waje ba har sai kin xama matar aure sosai. kuka na fara yi masa ina masa magiya amma yayi shiru yaki bani amsa, na lura dattijo mutum ne mai kulle, magiya dai nake masa amma har yanxu yana nan a kan bakansa na mayar da ni matar aure.
cike da kulawa ya dube ni my Niimatullah bari na tashi na tafi wajen maman munir tunda yau a dakinta nake, amma gaskiya kafin na tafi ki bani kulawa saboda nasan xan yi missing din ki kafin na dawo, hawaye naji ya fara xubo min daga idona, yanxu tafiya xa kayi ka bar ni dattijona sai da ka bari na saba da kai sannan xaka tafi ka kyale ni, ni gaskiya baxan iya kwana ni kadai ba sai dai ka mayar da ni wajen innata, hannu yasa ya shiga share min hawayen.
kiyi hakuri my Niimatullah kwana uku kwai xan yi a wajenta sai na dawo gare ki,ina son kwatanta adalci a tsakanin ku ne shi yasa bana son na dannewa kowa hakkinsa, banda wannan dalilin babu abinda xai sa nayi nisa da ke, amma har cikin xuciyata nafi son xama a dakin ki domin shi ne aljannar duniyata, kina min duk abinda nake so kina bani kulawa shi yasa bana son na bar ki ko da na minti daya ne.
cike da shagwaba nace to don yau a dakinta kake sai ka tafi da wuri haka, ai bari xa kayi sai dare xaka je, shafa fuskata yayi ya kara manna ni a kirjinsa, haka ne ka'ida Niimatullah yanxu ya kamata na tafi wajenta naga ya ta kwana ita da yaran mu, tunda dai lokacinta ya shiga kada ki damu xan rika xuwa wajen ki ina ganin ki, Niimatullah ki sani ko da kin yi nisa da jikina soyayyar ki na nan a cikin xuciyata, duk inda naje a duk inda na kasance ina tare da tunanin ki.
rarrashina ya shiga yi tare da romancing dina har sai da na manta dukkan damuwata, kwanciya nayi a wuyan shi ina jin radadin barina da xai yi, don a yanxu na fara sabawa da soyayyar dattijona, ban jin xan iya jurewa rashin shi.
A dai-dai lokacin muka ji an bude kofa an shigo, da sauri muka daga kai don ganin wane ne, matar dattijo ce rike da kugu take kare mana kallo, cikin fushi ta fara masa magana, yau fa xaka dawo dakina amma gashi har kusan karfe goma ban ga keyarka ba saboda tsabar rashin adalci me kake nufi da hakan? saboda ka auro wannan kaxamar yarinya karuwa xaka samu damar wulakanta ni.
shiru dattijona yayi yana naxarin maganganunta, ba karamin xafi kalamanta suka yi min ba, ganin ba shi da niyyar cewa komai yasa nima na mike, cike da tsiwa na bata amsar maganarta, kada ki sake ce min karuwa domin kula da mijinki kika kasa naxo na taya ki kula da shi, kaxawar ki ita ta janyo har ya ganni yaga na dace da rayuwarsa sannan ya aure ni, da kin cika cikakkiyar mace da baki yi sake an yi miki kishiya ba, ki dube shi ki gani da lokacin baya da yanxu daya yake?daga xuwana gidan nan ya canja yayi kiba hankalin sa ya kwanta saboda yana samun abinda yake so. juyawa nayi na koma jikin dattijona na kwantar da kai bisa kirjinsa.
Dattijo yayi mamakin maganganun da Niimatullah ta fadawa Hajiya Maryam, a cikin xuciyarsa kuma yayi nadamar kwancewa uwar yayansa xani da yayi a wajen Niimatullah da har ya fada mata cewa rashin kulawa da shi da bata yi ne yasa ya aureta,(don haka ya kamata maxa su hankalta idan sun je neman aure su daina fadar aibun iyayen gidan su ko don kaucewa samun raini tsakanin uwar gida da amarya).
A fusace ta karaso wajena ta dalla min mari, wata kara mai firgitarwa na saki, cikin masifa take min magana, ni xaki fadawa wannan maganar dan uban ki yaushe kika xo duniya har kika yi wayon da xaki fada min bakar magana, da sauri dattijo yaja hannunta ya fitar da ita,ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi.
har falo ya kai ta ya ajiye ta, rarrashinta ya shiga yi kiyi hakuri momyn munir ban auri Niimatullah don na toxarta ki ba, kina da matukar muhimmanci a wajena saboda kece uwar yayana, na auri Niimatullah ne don ta taimaka miki ki gyara rayuwar auren ki da kika bari a baya, idan kika yi kokarin raba ni da yarinyar nan xan iya shiga matsala,ko kina so na fada halaka ne, na rika bin matan banxa? kuma dan Allah ina rokonki ki daina kokarin xagin yarinyar nan kinga tun yanxu ta fara ramawa, sannan ga marinta da kika yi wanda hakan babban kuskure ne tunda dai ba yarki bace, ba kuma kanwarki bace, shawara nake baki ki nisanci yin hakan ko don gudun wata rana kada ku yi doke-doke da ita domin na lura hakurinta ya fara karewa.
shiru tayi tana saurarensa daga bisa ni kuma ta sauke ajiyar xuciya tare da cewa, gaskiya ne abinda ka fada dadyn munir kuma nima naga kuskuren da nayi a baya kuma xan yi kokarin gyarawa, amma ni wannan tsinanniyar yarinyar ce baxan taba kauna ba, kuma wlh mu xuba ni da ita a gidan nan sai ta gudu saboda tsabar wahalar da xan bata.
Godiya yayi mata sannan suka cigaba da hira cikin farin ciki.
Har bayan sallar magariba banga dattijona ba babu shi babu alamar shi, ga shi ba ni da wayar da xan kira shi, kukana ne ya tsananta, a fili nake magana tun yanxu dattijona ya fara wulakanta ni saboda wannan tsohuwar matar tasa wallahi baxan sake kwana a gidan nan ba, bakin kofa na fita inda na tarar da ita a kulle don haka na hakura na dawo, kan gado na fada na rika aikin kuka, a fili na rika fadar da nasan haka aure yake da ban yi shi ba, ji nake kamar na haura katanga na gudu saboda xafin da gidan yayi min, tunanin nasihar da innata take min nayi inda take fada min cewa aure ibada ne dole akwai jarrabawa a ciki, kuma duk inda ibada take tana bukatar hakuri da juriya, wanda idan aka yi hakuri aka jure sai Allah ya bawa mutum dukkan abinda yake nema, wannan nasihar da na tuna ita ta kwantar min da hankali, nayi bacci mai dadi.
gari na wayewa na xuba ido ko xan ga dattijona ya shigo amma shiru bai leko ni ba, don haka na shiga hada kayana ina cigaba da kuka, duk na hargitsa dakin, a dai-dai lokacin naji an turo kofar dakin da nake. muna hada ido nayi gefe da kaina,
cike da nutsuwa ya karaso wajena tambayata ya fara yi, lafiya Niimatullah ina xaki je kike hada kaya?cikin kuka nake masa magana baka sona dattijona gida xan tafi,Allah kuma sai ka sake ni a kan wannan tsohuwar matar taka ka tafi ka barni na kwana ni kadai, Allah sai na koma gidan innata.
rarrashina ya fara yi, kiyi hakuri my Niimatullah wlh ina sonki, kuma aurena da ke mutu ka raba, idan kinga kin fita daga gidan nan sai dai idan ni ne na mutu ko ke kika mutu, amma a auren mu babu saki na riga da na yiwa kaina wannan alkawarin. kuma ban tafi na barki don na wulakanta ki ba sai dan na bata hakkinta kuma na tsayar da adalci a tsakanin ku, kuma jiya ma kin min laifi, me yasa kika cewa matata don bata kula da ni na auro ki, shin yanxu baxan iya yin sirri da ke ba xabina, kina so ki rika tona sirrina ba a wajen innah kawai ba har a wajen mutane, ki sani ina daraja matata saboda uwar yayana ce, baxan bari wulakanci ya shiga tsakanin ku ba, yanxu kina ganin akwai wadda xan bari taxo ta wulakanta ki? ba auren ki kadai ne abinda nayi ba Niimatullah har tarbiyyar ki a hannuna take, baxan bari ki dore a haka ba Niimatullah saboda xan iya mutuwa na barki ko kuma wani abin daban, kuma ina so na hada kan ku ne ku xama tsintsiya madaurin ki daya. gaskiya guda daya ce baxan iya bari ki rika yin abinda bai kamata ba.
jikina ne yayi sanyi da maganganun da dattijona ya fada min, cikin kuka nace baka ga ita taxo ta fara yi min wulakanci ba har dakina kuma ta mare ni.
na sani Niimatullah amma duk inda babba yake babba ne ya kamata ki girmamata ko don yayan da ta haifa, kuma maganar mari duk nayi mata fada a kan haka kema kuma ki rika girmamata kin ji amaryar dattijo.
gyada kaina nayi alamar eh, cike da xaulaya ya fara min magana kin san ma wani abu ne, ni fa xuwa nayi ki bani kulawa don jiyan nan nayi missing din ki sosai, dago ido nayi ina hararasa Allah baka isa ba sai dai ka koma wajenta ai ba kwana na bane, da sauri ya mika hannu ya damko ni, kokawa muka shiga yi banda aikin kuka babu abinda nake yi har sai da yayi abinda ransa ke so sannan ya kyale ni.
*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*
33
Bai wani dade a dakina sosai ba ta rika kiransa a waya ya dawo gareta, fuskarsa cike da damuwa ya dube ni, xan koma wajen momyn munir tana kirana, bata fuska nayi tare da yin gefe da kaina, ba tare da na bashi amsa ba na cigaba da tunanina.
matsowa yayi daf da ni tare da dago fuskata kiyi hakuri nima ba a son raina xan tafi na bar ki ba, daga yau saura kwana daya na dawo gare ki da fatan xaki shirya min tarba mai kyau, don kin san ke din ta daban ce komai naki na musamman ne, fuskata a kasa na amsa masa da to.
A sanyaye ya tashi ya fita, bin sa nayi da kallo ina tunanin irin matsalar da xan shiga idan baya kusa da ni, ji nayi kamar nasa masa kuka ya dawo dakina, xafi xuciyata ta rika yi, wani kishi ne ya taso min ji nayi kamar na rusa ihu da sauri na rika karanto innalillahi wa inna ilaihi raji'un ban taba tsammanin haka xafin kishi yake ba, kwantar da kaina nayi tare da lumshe idanuna ina tunanin mijina, na saba kwana a kan kirjinsa da jin harbawar numfashinsa yau kuma da pillow xan yi matashi, hawaye naji na shirin xubo min, a ranar cikin damuwa na wuni tun daga xuwan da yayi min da safe bata kara barinsa ya leko wajena ba.
Da misalin karfe tara nayi wanka na fara shirin kwanciya bacci, sallama naji an yi min a falo cikin hanxari na fito don ganin mai sallamar, daya daga cikin yayan dattijona na gani, cike da ladabi ya gaida ni tare da cewa dadynsa na kirana,cikin sakin fuska na amsa masa da ina xuwa.
Hijabi na saka har kasa, kasancewar kayan bacci ne a jikina, kulle kofa ta nayi sannan na nufi wajen dattijona, a bakin motarsa na tarar da shi yanayin sa kawai na kalla nasan yana cikin damuwa.
cike da nutsuwa na karasa wajensa, a hankali ya dago ido yana kallona tare da cewa ai na xaci baxa ki xo ba Amaryar dattijo, murmushi nayi me xai hana ni amsa kiran mijina sai dai idan ko ba ni da lafiya ne.
Daga min hannu yayi tare da cewa matso nan xa mu yi wata magana, A hankali naja jikina na karasa gare shi tare da kwantar da kaina a wuyan shi, farin gashin da ke kewaye a fuskar shi na shafa kasancewar nayi missing din shi, cike da soyayya ya fara min magana.
Ina cikin wani yanayi Niimatullah,matar nan ta kasa kulawa da ni kuma ta hana ki kula da ni na rasa yadda xan yi da rayuwata, shi ne nace ki taimaka kixo ki taya ni hira a nan ko xan samu sauki da sauraren muryar ki.
cike da shagwaba na bashi amsa, ni dai baxan iya ba tunda ba lokacina bane dakina xan koma nayi baccina, ka koma wajenta ka lallabata nasan xa tayi maka duk abinda kake so.
ina kammala fada masa na kama hanyar komawa bangarena, jawo ni yayi ya hada fuskata da tasa da alama yana cikin yanayi, kamar xai yi kuka yake min magana.
Baxa ki tallafi mijinki ki tsamo shi daga fadawa halaka ba ko, da kika ce na koma wajenta yanxu haka kofar dakinta a kulle yake ina kike so naje naji dadin rayuwata,ke da kike sona kuma xaki juya min baya Niimatullah wane yanayi kike tunanin xan fada idan kika bar ni, na dade da fada miki kice nutsuwata kece farin cikina.
kaina a sunkuye na bashi amsa, kayi hakuri dattijona baxan iya danne hakkin wata ba,tunda lokacinta ne kaje ka sameta idan bata baka kulawa ba, ka dawo xan kula da kai.
fuskarsa cike da fara'a ya dube ni da gaske kike amaryar dattijo? cikin kulawa nace masa eh, rungume ni yayi yana kissing dina, na gode Allah yayi miki albarka Niimatullah, dole ta rika bakin ciki da ke kin fita biyyaya kin fita komai, na gode amaryata, cikin rada nake masa magana kaje yanxu ina jiranka a cikin gida.
cikin rawar jiki ya tashi ya nufi bangaren Hajiya maryam, sallama ya yi amma shiru ba a amsa masa ba, dudduba dakin ya shiga yi ko xai ganta, a bakin brander ya hangota tsaye, jikinsa a sanyaye ya karaso wajenta.
fuskar sa cike da murmushi ya bude baki xai mata magana, hannu ta daga masa, kai malam dakata tsohon munafuki duk abinda kake yi a kan idona, ka koma wajen kaxamar matarka tayi maka duk abinda kake ganin na gaxa yi maka, ni baxan iya da wannan jarabar taka ba da nacin tsiya, ka koma maybe ita xata iya jurewa, tunda ita jaka ce amma ni baxa ka xo ka takura min ba.
sakin baki yayi yana kallonta ya rasa bakin magana masifar dai ta cigaba da yi masa a fusace ya bata amsa, idan na danne miki hakki kice yarinya ta yi miki asiri bayan komai ke kike jawowa kan ki, wlh xan tafi baxa ki kara ganina ba xaki gane ba nida xuciya.
da sauri ya bar wajenta ya nufi sashin Niimatullah, A kulle ya tarar da kofarta, A hankali ya rika kankwasawa tare da kiran sunanta.
cikin bacci naji alamun ana buga kofar dakina a hankali na bude ido na fito parlour ta window na hango dattijona, yana ta faman bugu leka kaina nayi, muna hada ido ya fara min magana, ki taimaka ki bude min na shigo Niimatullah kada na shiga wani hali.
makale kafada nayi, baxan bude ba Allah sai dai ka koma wajenta, na fada maka baxan taba shiga hakkinta ba, magiya ya rika yi yana ta bugawa komawa kan kujera nayi ina kallon shi ina masa dariya, gaba daya ya fita daga hankalinsa ina mamakin yadda yake da jaraba duk da kasancewarsa dattijo ya kamata a ce yayi sanyi amma abin nasa ya wuce gona da iri.
Buga kofar yake ba sassautawa yana ta magiya, ni kuwa sai dariya nake masa cike da tsokana nake masa magana, baxan fa bude maka ba sai dai ka koma inda ka fito kuka yake min sosai, a xuciyata naji tausayin sa amma baxan bude masa ba sai na gama ja masa Aji.
*
34
Ganin yadda yake min naci ne yasa na taso don bude masa, cikin nutsuwa na leka kaina ta window na fara yi masa magana, kiran sunan shi nayi tare da kashe masa ido, dattijona xan bude maka yanxu amma sai ka yi min wani alkawari, kuma ka tabbatar min da baxa ka saba min ba. da sauri ya karaso tare da cewa, nayi alkawarin xan cika miki alkawarin ki matukar xan iya.
gyara tsayuwa nayi tare sa sakar masa murmushi xaka iya ma ai abin ba mai wahala bane, cikin siririyar murya na cigaba da fada masa, kayi min alkawari idan ka shigo babu abinda xa kayi min saboda wallahi duk jikina ciwo yake har yanxu ban warkewa daga abin nan da kayi min ba, cikin marairacewa ya amsa min, nayi alkawarin baxan miki komai ba ai ina son farin cikin ki amaryar dattijo.
karasawa nayi na bude masa kofar, yana shigowa na bude masa hannu ya fada kirjina na rungume kayana, kissing din shi na shiga yi sannan na fara bashi hakuri a kan abinda matarsa tayi masa saboda ina so hankalinsa ya kwanta.
kayi hakuri dattijona kada kasa damuwar komai a ranka indai kana da ni baxa ka taba yin kuka ba, duk inda farin cikin ka yake xan nemo shi,domin ba nida wani aikin da ya wuce kulawa da kai.
cike da soyayya ya kara hada fuskata da tashi na gode sosai Niimatullah, na dade da sanin kece rayuwata kuma abar alfaharina, Allah ya taimake ni kin shigo rayuwata ne,don nayi dariya nasan duk wani bakin cikina xaki share min, murmushi nayi tare da matsa masa hannun shi insha Allah xan maka komai dattijona.
daga kanshi yayi sama tare da lumshe idanunsa tunani naga yana yi, fuskata cike da damuwa nake tambayarsa, tunanin me kake yi mijina dan Allah ka manta da komai ka saki jiki mu sha soyayyar mu.
dagowa yayi ya dube ni yunwa nake ji my Niimatullah tun safen nan da na fita daga dakin ki ban ci komai ba har yanxu da muke wannan maganar, girgixa kaina nayi cikin damuwa nace masa,yanxu kana nufin kace tun daxu baka ci abinci ba? gyada min kai yayi kwarai kuwa ke dai tashi ki hada min yar aljannata, da sauri na tashi na shiga kitchen na fara girkin kenan na ji shi rungume a bayana yana sakar min numfashin sa a kunnena, cikin marairacewa nace masa dattijona ka kyale ni nayi maka girkin kada ya kone.
rada yayi min baxan iya bari kiyi aiki ke kadai ba amaryata, taya ni yayi na fara
hada masa abinci mai rai da lafiya sannan na hada masa lemo mai dadi, a baki na bashi sai da ya ci ya koshi sannan na kyale shi, albarka ya rika saka min yana min fatan alkhairi.
Bayan ya kammala na kwashe kayan na kai kitchen, sannan na raka shi bandaki yayi wanka, ni kuma na fito na dakko masa kayan da nake son ya sanya, yana fitowa na shafe masa jikinsa da wani cream mai kamshi sannan na sanya masa kaya masu kyau parlour muka fito muka fara hira, a cikin hirar tamu yake bani labarin irin wulakancin da matarsa tayi masa ya kuma roke ni da kada nayi koyi da irin abubuwan da take yi masa.
cikin marairacewa ya sake mayar da kallon shi gare ni tare da cewa, Niimatullah kiyi min wani taimako amaryar dattijo, sunkuyar da kaina nayi tare da cewa wane taimako kake bukata daga gare ni babyna, hannunsa ya dora bisa wuyana sannan ya fara yi min magana cikin rada.
ki taimaki mijinki ki bashi kan ki, shi ne abinda nafi bukata daga gare ki, saboda ina cikin wani hali ki share min hawaye kiyi min sadaukarwar da yar uwarki baxa ta taba iya wa ba.
jikina naji ya fara karkarwa saboda ina tuna irin axaba da wahalar da nasha a hannunsa, cikin rawar murya na fara yi masa magana, dan Allah kayi hakuri dattijona wlh jikina ciwo yake.
rarrashina ya fara yi ki taimaki rayuwar mijinki wlh idan kika hana ni ban san irin halin da xan shiga ba, Kuka na fara yi ina rokonsa yayi min hakuri xuwa gobe, shi ma kukan yake yana fada min baxai iya jurewa ba sbd xai iya samun matsala.
Hakuri na bawa xuciyata na amince da shi yayi dukkan abinda yake so, bayan muna kammala ya dawo da ni ya kwantar da ni bisa gado, wani kallon soyayya yake bi na da shi duk inda na juya idanun shi a kaina, ni kuwa saboda kunya na saka kaina a cikin pillow bana son hada ido da shi saboda irin rashin ta idon da yake aikata min.
Tasowa yayi daga inda yake ya dawo kusa da ni, bude blanket din da na rufa da shi yayi, ya shigar da jikinsa ciki, riko hannuna yayi ya shigar da tafin hannunsa cikin nawa, cike da soyayya ya fara min magana, my Niimatullah kin hadu baxan iya barin ki ba har abada, kina da baiwar da ni kadai ne xan gane hakan,dan Allah ki cigaba da rike ni amana wallahi ina sonki kuma a kullum na kasance tare da ke sai naji soyayyar ki ta kara ninkuwa a xuciyata fiye da da.
Dan Allah kada ki hukunta ni da hana ni jikin ki,duk girman laifin da nayi miki ki fada min ni kuma nayi alkawarin xan baki hakuri na kuma karbi kuskurena, amma dan Allah kada ki taba kauracewa shimfidata domin baxan iya rayuwa babu soyayyar ki ba.
kaina a kasa na amsa masa da xan so ka dattijona.
sake rungume ni yayi ya cigaba romancing dina, kokarin kara kusantata yayi nayi masa magiya ya kyale ni saboda na gaji, ya hakura ne kawai ba don ransa ya so ba.
Bayan ya dawo cikin nutsuwarsa ya dube ni, my Niimatullah saboda faranta min ran da kika yi na baki dama gobe kije gidan innah ki gaida su, rappers din yan dari biyar ya xaro ya bani, idan kin je sai ki bawa su innah.
rungume shi nayi ina murna har da dan guntun hawaye na, na gode maka dattijona ka faranta min raina wlh, dole nima na rika faranta maka Allah yayi maka albarka yasa kafi haka, dago fuskata yayi kin cancanci fiye da haka daga gare ni amaryar dattijo fatana dai ki cigaba da faranta min.
kwanciya nayi a kirjinsa wani farin ciki da dadin abinda yayi min na ratsa xuciyata, a lokacin ma bamu kwanta ba sai da ya kara yi min wani aikin.
0 comments:
Post a Comment