Misbahu ya yi gargaɗin ne bayan ya lura da yadda wasu mawaƙa su ka ɗauki waɗansu tsofaffin waƙoƙi irin na da su ka juya su zuwa wani salo na daban, ya ce shi kam zai ɗauki matakin shari’a kan duk mawaƙin da ya kama ya yi masa haka.
Juya fitattun waƙoƙin finafinan Hausa da su ka yi tashe a da wanda matasan mawaƙa ke yi a yanzu ya zama ruwan dare.
Misbahu ya ɗora laifin barin matasan mawaƙan su na cin karen su ba babbaka kan shugabannin industiri.
A wani saƙon murya da ya tura cikin wani guruf na shugabannin masana’antar a jiya Litinin, wanda mujallar Fim ta samu, shahararren mawaƙin ya bayyana cewa abubuwa da dama su na faruwa a Kannywood waɗanda ya kamata a ce mahukunta sun tsawatar a kan su, to amma sun shafa wa idon su kwalli tare da kauda kai daga abin da ke faruwa.
Misbahu, wanda kuma babban jarumi ne, ya ce, “Alal haƙiƙa, mu na da shuwagabanni, amma a baka. Shugabanci kullum ya na da’awar shugabanci ne shi ko kuma shuwagabanni ne, amma da yawa akwai abubuwan da su ka kamata a ce akwai jagoranci, a ce akwai tsawatarwa, akwai doka, amma ba a tafiyar da su, ba a san da su ba.
“Yanzu mu na raye a matsayin mu na mawaƙa waɗanda an san irin waƙoƙin da mu ka yi kuma waƙoƙin nan an san irin tasirin da su ka yi a cikin masana’antar nan, an san cigaban da su ka kawo, an san irin arzikin da aka samu da su, ba ma mu kankin kan mu ba, ‘ya’yan mu ma da mu ke gadara za su yi alfahari da su, to sai ga shi tun da ran mu ma yanzu mu na ji mu na gani yaro ya taso, bai san hawa ba bai san sauka ba, bai san ya aka yi aka yi waƙa ba, idan ka tambaye shi waye mawaƙin bai sani ba, kawai saboda ya na situdiyo a zaune tare da wani furodusa ko ya na tare da wani mawaƙi, kawai sai ya zo ya ɗauki waƙa ya je ya zauna a gida ya sa ta a kaset ya na ji, ya na bin ta baiti bayan baiti, ɗango bayan ɗango, ya rubuta ta a takarda ya zo ya biya kuɗi dubu biyu ko dubu uku, ya zauna a situdiyo a sake mata kiɗa ya ɗora muryar sa, ya nemo yarinya ta ɗora muryar ta. Kawai sai ya zo ya sake ta a YouTube ko ya sake ta a duniya, kawai ya na samun kuɗi.”
Cikin ɓacin rai, Misbahu ya ƙara da faɗin, “Da ran mu mu na ji mu na gani waƙoƙin nan mu mu ka ƙirƙire su, ba ma waƙa ce irin ta nanaye ko ahayye ko irin ayye mama ayye mama da za a ce waƙa ce ta dandali ba, a’a, wasu waƙoƙin kai ka ƙirƙiri abin ka da karin da rubutun da komai, ka na ji ka na gani ka na raye wani yaro ya ɗauka!”
Mawaƙin ya faɗi abin da ka iya faruwa idan fasihai irin sa su ka yanke hukuncin bin haƙƙin su a kan masu satar basirar su, ya ce, “Abin da ya sa na ke magana, daga lokacin da ka yunƙuro ka ce za ka nemi haƙƙin ka ko ba ka yarda ba, ko ka nuna ba ka amince ba ko ka nemi bahasi, sai ka ji a cikin masana’antar za a dawo ana zagin ka, ana cewa kai mafaɗaci ne, ba ka da mutunci, ko ka yi rashin mutunci ko ka na yi wa yaro hassada don zai ci gaba, da kaza da kaza. Wannan abin fa ba daidai ba ne!”
Ya ƙara da cewa, “Babu yadda za a yi mutum ya shiga ɗakin ka ya ɗaukar maka kaya, ka kama shi ka na raye da ikon ka, ka yi da’awar ka kama ɓarawo a ce don me za ka kama shi? Ya kamata a samu shugabanci ya kalli waɗannan abubuwan.
“Yanzu ta wuce ma a ɗau baiti ko ka ƙirƙiro wata kalma ka sa a waƙar wani mawaƙi ya ɗauka ko wani baiti a ɗauka, a’a, ta wuce wannan; ka yi waƙa da yarinya, ta koma ta ɗauki waƙar ta tafi situdiyo ta rera ta ga baki ɗaya saboda ka ɗaga ta da waƙar, ta ɗaukaka, ta ɗauke waƙar ta na bada tarihi. In ta zo tarihin ma ko sunan ka ba za ta ambata ba! Duk wannan mun haƙura da shi.”
Misbahu ya kira lamarin da hannun-ka-mai-sanda ga shugabannin Kannywood domin su farka su ɗauki matakin da ya kamata.
A ƙarshe, ya yi rantsuwar cewa zai sa ƙafar wando ɗaya da duk wani mawaƙi da ya ɗaukar masa waƙa ya juya ta ba tare da izinin sa ba.
Ya ce, “Wallahil azim, duk wanda ya taɓa waƙa ta ko ya hau waƙa ta, idan na samu labarin inda ya ke sai na kamo shi mun yi shari’a da shi, kuma sai an biya ni haƙƙi na.”
Ba Misbahu M. Ahmad kaɗai ba, mawaƙa da dama, musamman ma dai tsofaffin, su na nuna takaicin su kan yadda wannan abu na satar basirar su da sababbin mawaƙa ke yi ya zame musu ƙarfen ƙafa, wato salon maganar nan ta kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa sakamakon wannan koken da Misbahu ya tura, shugaban ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Kannywood na ƙasa (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari, ya gayyace shi zuwa ofishin sa domin su tattauna matsalar saboda a yi wa tufka hanci.
Misbahu dai shi ne yayan fitattun ‘yan Kannywood ɗin nan biyu, darakta Aminu Saira da mawaƙi Naziru M. Ahmad.
0 comments:
Post a Comment