************
Tana shiga d'akin ta tarar dasu Mamanta suna cin abinci harda naman kaji an karramasu ta bangaren girki se duk taji kunya take cewa lemon baqinta ta siyo dazasuzo yanzu....tana nan khadeeja tazo kiranta akan ga angon da abokanan sa sunzo maganar kudin bikin dazasu bayar, tazo suje taso ta tirje mamanta tace lallai taje dole ta sauya kaya tare da d'ora niqafi saman firkarta kanta fice daga dakin zuwa inda en matan ke jiran ta ai zancen kudade!!!
Tunda ta shigo idan Maheer ke kanta so barkatai suke had'a ido, girjin dukkansu se tsananta dukawa yake hafsat kuwa duk yayin data tunano yanayin data shiga sanda ya furta mata muggan kalamai setaji tamkar ma taje ta shaqesa a wuce wurin kowama ya huta wani haushin sa da takaicin sa suke mata dirar mikiya arayuwa yanda takejin Maheer aranta bata zata akwai ranar dazata zo a rayuwarta da har zataji tsanar sa irin hakan ba, yanda ya kalli tsabar idan ta ya aibata ta da kalmar karuwanci abin yana mata ciwo matuqa!! Beji kunyar kallon mafificiyar Fuskar dake asaman tata ba ya kalleta kanshi tsaye yake kira mata wannan mugun abun datake ganin data aikata gwara mata mutuwar quruciya!! Miyar da dubanta tae zuwa ga Mahal wannan karon bazata iya jure kallon Maheer ba, shi kuwa dayasan itace se nacewa kallon ta yake wannan ya sanya ta tsargu ta miyarda kanta a qasa a haka a haka dai sukaita surutun su da en matan dake wurin akan programs da zasuyi amma hafsat batace kanzil ba....... Ummul ta kula sam Ameenu bashida niyyan barin su sui wani fitaccen bikin dazeje tarasa dalilinsa nasab zuwa programe ko d'aya ne...amma dai acikin mutane seka gagara cewa komai illah kallon su kawai kamar yanda Nancy tae haka itama tae!! Maheer ne yace
"Yanzu dai Nine zan dauki nauyin dinner da komai daya shafeta seku tsayar da matsaya d'aya akan kudad'en da ake bayarwa na al'adarku nawa kuke ganin ze isheku" kallon Mahal Ummul keyi tasani tana qaunar sa soosai kurun dai tarasa gane inda zuciyarta keta wurgi da ita! Wanj zubin idan ta tuna mahal har kuka takeyi yau kam tafi ko yaushe rikicewa ganinsa tare da Ameen, amma bata nuna ba sam ga alama shidin qani ne cox bataji bakinsa tunda aka zauna.....khadeeja ce tace
"To Ku fad'i dai nawa zaku bayar semu ji idan zeyi mana karmu fad'i abinda ze baku wuya" murmushi su Ameen sukai har Mahal ma dake wurin, shi tausayi ummul ke bashi kuma yanzu, sabida yana jin qananun maganganu gameda Ameen d'in akan rashin sanin sana'ar sa gashi bashida mata yanata girma, yayi mamakin ma dasuke abota da Maheer sabida ya masa zarra har a shekaru sedai kuma Business men ne dukansu ba lallai bane ace se shekaru yazo d'aya zasuyi abota...Muryar Maheer ne ya qatse masa masa tinaninsa
"Waccen me Fuskar a niqafi ta bamu acc details ku saka kudin acikin acc nata, idan tace ya wadatar shikenan na kula ita zataji tausayin mu ita kad'aine bata magana" Dariya suka sanya dukkansu banda Nancy dataji bala'in takaicin sa kamar ta shaqesa seda Ummul tace
"Nanuwa ki bayar mana"
*"NANUWA"* ya qara nanata sunan a ranshi ita kuwa bataso akaji bakinta ba sam, da qyar tace
"Ka shirya in fad'a maka?" Tana bude bakinta yasoma tunanin yasan muryan amma seya kawarda wannan tunanin,Bayaso ya yaudari kansa.........Kallon ta yae kafin ya miyarda dubansa zuwaga Ummul
"Ya kuke da wannan qawar kice?" Murmushi tae tace
"Qanwa tace sedai ba sosai na girmeta ba, kanmu d'aya dai Babanmu d'aya" murmushi yae
"Barin Baki Number wayana, ki turamun Text message na acc details naki, yanzu idan muka tafi zan miki transfer idan akwai damuwa seki kirani ko kuwa?" Batace komai ba dai se Godiya da en matan suka hauyi yayinda wasu duk sukaji haushin Maheer abinda yae...ya kula wata acikin su tafi kowa jin haushin hakan yace da ita
"En mata kefa ya sunanki" wani sanyi taji a ranta
"Sunana zulaiha"jinjina kansa yae
" zoto ga wannan ki riqe muku, idan zaku tafi kwa hau abin hawa" tana wani rangwad'a taje ta karb'e rafar d'ari biyar biyar da aka basun tana godiya godiyar sukai banda Nancy dakejin takaicin maheer ko a ina seya nuna cewar shid'in wanine ta tsani wannan show up d'in nasa......haka suka shige gida har yamma yana jiran acc details amma babu alamar sa seya tsinci kansa da damuwar daya rasa dalilinsa...
************
Nancy Amma dai kinsan baki kyauta ba ko, har yanzu tura acc details ya gagara idan bazaki yiba niki bani number dinsa dake wayarki na tura naga alamar ke er baqin ciki ce wlhy, yanzu ina xega bank after 5 kuma kin sani sarai ina buqatar kudin nan ko me decor half kurin na bata" murmushi tae
"Kiyi hakuri wlhy shap na manta, yanzu zan tura" juyawa tae batare datayi magana ita kuwa ta lalubo Number tada rubutawa suna "Show up" ta tura masa acc details nata na GTbnk tana mamakin dagewar sa akan lallai se acc number nata yake so.....
***********
Maheer kwance asaman kujerar dake parlor sa yana kallon wani korean series me suna Rebels film din yana masa dadi...jin qarar shigowar saqo a wayansa ya sanya ya tsayar da kallon ya duba wayarsa, kai tsaye transfer na 2.m yayi ya ci gaba da kallon dayake cikin nishad'i......
Ta jima sosai tana nanata karatun zirurrukan dake gaban 2 d'in bayanda alert d'in ya shigo mata kanta miqe da saurinta zuwa part d'in su Ummul....
Zama tai kusa da ita
"Ummul kalli wannan alert daya shigo da sunan wannan abokin na Yaa Ameenu.... Wak kaman fa 200k nake gani 2.M ne?" Da sauri Ummul ta karb'i wayar ta duba ta miyar da dubanta zuwaga Hafsat
"hafsat 2.m wlhy yanada kai kuwa?"
"Oho dai nima dai nace ko kusjure yae ne" gyaran zamanta tae
"Nasaka subamu 500k gaskia shine ma budget dina amma wlhy ban sakaran ko 1. Ba,kinga kirashi a waya kiji ko kuskure yae, ni Ameen dama yamun gargadi akan kiran ko daya daga cikin abokanansa,beside ni ban tab'a ganin abokansa bama se Maheer da wani Salah" gyaran zamanta tae ta soma dialing number sa
"En mata yaya dai" ya fad'a daga bangarensa
"Barka da yamma" murmushi yae kamae tana gabansa yace
"Barka dai en mata ya kike ya komai, ina fatan kun samu saqona"
"Ea saqonka yazo mana, amma munga kamar kayi kuskurene kudin yayi yawa" gyaran kwanciyarsa yae yace
"Ina Amaryar tamu?"
"Gata a kusa dani" ta basa amsa a taqaice
"Ok ki sanar mata nace 1.m shine kudin dana bata na shagalin bukukuwa 1.m kuma tawa gudummawarce kyauta na bata kinji" Godiya tayi masa sosai sannan sukai sallama ta gayawa ummul yanda sukai ummul uwar er san kudi se murna ake tace
"Ki dauki 100k ki turamun 1.5 m dama Baba ze nemo kudin abincin da season 7 zasu mana ki bashi 400k din data rage ni zanyi sauran abubuwa ke kuma kya karbi din kunanki ko?" Godiya ta mata tace
"Amma kinsan fa acc din nawa,bazan iya cire kudi da yawa haka ba, amma goben zan baje bank nayi withrawing nasu duka" murna suke susu biyu a abinsu,ummul ta gayawa Ameen shima ya kirasa ya masa godiya yace ai yiwa kaine.....
*Menene alaqar dake tsakanin Maheer Ameen?*
Maheer yarone me tsananin qwazon neman na kansa, mahaifinsa kuma baya hanashi shiga sabgogin neman kudin sa da kasuwan cinsa, ko sanda yake zaune a turai sam be zauna a banza ba, acen ne ya had'u da Ameen a wani zuwa da yae china sarar wasu kayan decoration da bama samu a Niger shi kuwa Ameen yakanji yaran na qasar shangan dake china shiya taimaka yake saka baki inda rashin iya turanci ya shiga tsakainin Maheer da abokanan kasuwan cinsa wannan ne ya sanya alaqa me kyau tashige tsananin su, har yau Maheer besan gidansu Ameen ba amma shi yakanje har gidansu a runaninsa ma auren farko ne zeyi, jin yana sokoto ne ya sanya Ameen ya janyo Maheer ajiki ya san sa da matuqar san kyauta !! Dama ya gaji da kashewa Su Ummul kudaden sa beko saniba ko zata haifa masa yara da yawa, sabida biyar yakeso ya siyar a miliyan dari biyar biyar yasan zeja kaya..wannan kenan.
***********
Washe gari Nancy tai shirinta tsaf na zuwa banka domin withdrawing kud'in dake bank d'in daya turo dama tana san qarin lace na sakawa ranar dinner tana ganin rashin dacewar shiga cikin en anko gashi ta samu 100k na 50 zata siya ta cancare abinta acikin qawayenta, ga kayan jikin mamanta ganinsa ya bata takaici ta kula har qaninta tanada wata er dubu 40 dayike tanashan kyauta awurin Aminu tace bara itama ta siyanmata kona 25k ne da atamfofi qanana guda biyu takai a d'inka mata kan wednesday ta siyawa qanin ta maza qananun kaya bazata iya ganin mamanta kamar jaka ba...bayan ta cira se kuma period ya mata dirar bazata wannan ya sanya ta sauya akalar zuwanta kasuwa ta juya gida takai kudin Ummul idan ta kimtsa seta fita zuwa kasuwar.
***********
Bayan kammala shirinta tsaf tabaiwa ummul kud'd'enta seta juya zuwa kasuwa sabida tau takeso ta kaiwa suhailu tela din kunan kozata dace, dazata samu sarari ne data dinka da kanta amma ba halin yin hakan.....kai tsaye gate ta nufa domin ta nemi adaidaitan daze kaita kasuwa..... A qofar gidan taci karo da Maheer zaune a saman motar sa ko yau din batada zab'in daya wuce ta gaidashi dole ta matsa daf dashi ta qaqaro murmushin dole wanda baya ma ganin fuskar tata sabida niqafin data adana fuskarta aciki
"Sannu yaa Maheer ina wuni"
"Lapia qalau Hafsat ya gida ya shirin biki?" Murmushi ta sakar masa a karo na barkatai
"Alhamdulillah"
"Dama saqo na kawo miki, atamfofin yayin bikine zaki rabawa qawayenku Ameen ne yace na kawowa Ummul inata kiranki baki daukaba, qwaya d'arine na en mata ne, se kuma ni tawa gudummawar takice gaba d'aya" shiru tae ya bude but bayan ya diro ya zaro wata qatuwar jaka, ya dire ya kira wasu yara susu uku suka kinkima zuwa ciki,ya zaro wata madaidaiciyar jaka me kyau yace
"Ungo wannan nakine tawa kyautar aje a dinka aci bikin sister" kasa karba tae ya b'ata rai
" Da Ameen ne yamiki kyauta zakiqi karb'a ne? Gaskia banason hakan idan baso kike raina ya baci ba ki karba kawai, kuma banaso nama kyauta wani ya sani dagani sekai se Allah" hannu tasaka ta karba ta dinga godiya seda ya tsayar da ita ta juya se part dinta acen ta bude dakinta ta saka ta rufe ta nufi wurin ummul tamata bayanin atamfofin ta zari nata dana Islam da wata qawar su farida sannan ta koma d'akin dan ganin meke cikin jakar.
Mom Nu'aiym.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
12
Yafi mintuna talatin yana nazarin maganganun islam se cen ya dawo ya zauna ya muskuta da kyau yae gyaran zamansa yace
"Amma islam kina cikakkiyar sallah biyar awuni kuwa" dukda bataji dad'in maganar ba amma seta tsinci kanta da bashi amsa kamar haka
"Ina yi mana Maheer, meze hana nayi saah na taso agidanmu an koyar dani tsare sallah akowane hali" jinjina kanshi yae alamar gamsuwa
"Amma kuma bakyayi akan lokaci islam" shiru ta d'anyi kan tace
"Ea to anan bazanyi qaryaba wani zubin se magrib nake yin azahar da la'asar dinma gaba daya senai maja" kalonta ya qarayi
"Amma aka gayan miko cewa haka ake sallah? Idan fa kabari lokacin sallah ya wuceka da gangan kashiga uku islma, mesa zaki miyar da rayuwarki kamar ta marasa ilmi? Kina ganin ko wannan rashin kiyaye sllah akan lokaci baze jefaki ajikin ibtila'in rayuwa ba? Ya dace ace kisan cewa ba'awa sllah hakan ai, wanda ma yake hada salloli yaushe zega time din yin adu'a tukunna ma yaushe rabonki dayin azkhar? Kokuma ki zauna kiyi karatun alqur'ani me girma tayaya zakiga haske islam?" Shiru tae tana tunani ita wlhy tun quraninta na islmaiyya bazatace ma ga inda yake ba, ko na app da ake turowa a waya bata taba ajiyewa ba kuma ita abinda yasa bata ajiyewa shine sabida yanayin abubuwan dake kan wayarta, soda yawa idan taje wurin gardawan bariki setayi kallon fina finan batsa takejin sha'awa, sannan wani zubin idan taje wurinau sesu shagala da zancen sallah ta kula dan zaman nan datae agida sosai take sallah sam bata wuceta to kenan duk musababbin shigarta wannan halin hadda mugun abun nan datakeyi....seda ya qara cewa "kinaji kinyi shiru islam nace yaushe rabonki dayin karatun alqur'ani ko Azkhar? Hawayen dake kan fuskarta ne ya sauka tace..
" bazan iya tuna tuna tun yaushe ba Maheer" nisawa yae yace
" Manta wa da Allah tamkar qulla qawancene da sheda islam, baze taba barinki ki mori tsufanki ba, zega yanda duk zeyi ki lalata quruciyar da hannunki ta yanda tsufanki baze miki kyau ba, kazalika koda kin mutu kafin tsufan ki shige wutar Allah, banji dad'in yanda rayuwarki ta kasance hakan ba, dukda kome kika aikata a rayuwa tare da Suraj za'a raba a baki naki kason shima yaja nashi, ga kuma haqqin ki na cutarwar daya miki gashi shine mutumin farko da kika nemi ya aureki sanda nace kiyi hakan, ki kasance acikin istigfari ako da yaushe kije gida yanzu sena qara neman ki kuma" sakkowa tai tabi gwiwowinta tana kuka tace
"Ka taimakeni Maheer ka rufa asirina, ka aureni wlhy idan baka banida amfani" murmushi ya sakar mata yace
"Kije gida karki damu My Islam zanzo gidan idan na dawo kinji" godiya ta masa ta miqe yace
"Zoki karba ki riqe a hannunki banaso wata buqatar ta taso dazaki nemi wani abu awurin wani" sadda kanta a qasa tae ta kasa koda motsin kirki bare ta karbi kudin seda ya mike ya saqala mata a hannu sannan ta juya Kamala ya dauki hanyar gidansu da ita!!!!
************
Yau auren Ummul saura sati d'aya wannan ne dalilin dayisa gidan nasu ya qara kaurewa da hayaniya da ihun mutanen qauyensu da en uwa dakuma abokanan arziqi!! Ummul na zaune tana d'aye selotop dake tafin qafarta bayan ta gama cire lallin gargajiyar data saka, farar qafarnan ta d'akko jan lalli se sheqi takeyi! Ata gefenta qawar Ummul ce Khadeeja ke mata zuba
"Yanzu ke Nancy meya alaqanta ki da lallin gargajiya za'ai biki a gidanku? Bakya jin kunyama kizo muje gun zarah uwar zane mana ranar laraba ta zane mana hannayen mu da qafafuwa dubu uku ce kun rabu lapia" Kallon sosai ta mata tana murmushi
"Zanjene ai kurun dai dama dole wannan nake farawa dashi, shisa ma nakeyi da wuri danna cire a tare" murmushi tama tai ta sunkuya sosai tace
"Wai nikam Hafsat Anya ke ba balarabiya bace? Wlhy danice ke da duniya seta gama ganin wannan surar tawa, sumar kanki kawai seta b'ata wa mutum lokaci wurin kallon ta nifa aduk cikin jikinki banga inda Allah ya kuskure miki ba dama kuma shiba me kuskure bane yasan daidai...ummul ita muke zuzuta kyawun ta amma wlhy Nancy bawai buzuwa ba babu wanda baze yarda cewar keba balarabiya bace idan ya ganki" sakin lallausan murmushi tae .
"Khadeejahh abeg jeki kiyi sallah abinki" ta qarashe maganar tana dariya......itama khadeejan juyawa tae tana fad'ar
"Anyi baqi daga Niger naga wata mata me kamarki ga alaama maman kice" murmushi tae ta zata wasa ne yasa bata kulata ba seda ta gama tae alwahala ta nufi d'akin Baba Azumi.....
Acen ta tarar mamanta da qannin ta sunzo mata...Baba iro ne ya aika suzo dan ya bata haushi sabida taga yayi kudi data gujesa, acewar sa dan bashida kudine taqi zaman aure dashi yayanshi dayakeda abin hannunsa ai basui haka ba ta zauna..... Murna a wurinta ba'a magana sam, mamanta ma taji dadin ganin ta se yare sukeyi na Buzayen Niger Baba Azumi se harare harare takeyi tana yatsina fuska!!.....
**********
Duk saurin datake ya hanata d'aukar niqafin ta ayau dinnan, dama wasu lokutan takan fita acikin unguwarsu hakan......murna sosai takeyi tanaso taje ta siyawa mamanta Lemu tasani akwai lemuka agidan taga ko abinci ba'a baiwa har qannin taba, bazata jira yaran su mutu ba da yunwa murnan ganinsu ya hanata shiga b'acin ran an hanasu abinci.....a qofar gidansu tae karo da Mahal da Maheer a tare suna hira sun haye saman motarsu ta baya sunata tafa hannu suna murna qirjinta ne yae mugun dokawa ganin yanda dukkaninsu suka zuba mata ido tamkar wacce qwai ya fashewa a ciki haka ta dinga wurgo qafarta tana kusanto gate din gidan dauke da ledar lemo a hannunta...kanta qaraso Ameen yayi parking zuqeqiyar motarsa ya fito ga mamakin ta wata qara suka saka shida Maheer ya diro daga motarsa yana ihun "MAZAJE!!!!!" Suka tungume juna bayan sun tafa yace
"Ango kasha mai" dariya Amin yae "Tunkan akai Amaryar kake cewa nasha mai ya akai ka gane gidan harka rigani qarasowa" kallon Mahal yae yace
"Wannan yaron ne qani nane dan wurin qanwar mahaifina ne anan suke zama shine muna tare dayaji kana kwatantamun yace ya gane wurin" murmushi yae shima
"Ohk sannunka shima semuje dashi ai, wannan al'adar ta sakkwatawa dame tae kama ace se an maka taron en mata sun fadi adadin kudaden dasuke so ka basu" dariya Maheer yae yace
"Tunda al'adar suce aisemu hakura, namata waya tace suna masaukin baqi na waje muje kawai" wucewar Nancy ne ya dakatar dasu duka ukun suka bita da kallo, dukse ta tsargu aciki Mahal ne kurun yasan fuskarta amma Maheer da Amin basu santa ba bata fata su santa ma se idanta da suke gani..... Maheer da qirjinsa ya ninka dukawa ganij cikin idon daya taba sani yace da Amin
"Aboki ko wannan ce amaryar?" Dukan bayansa yae
"Ko alama tawa matar taci uwar wannan a kyau da komai, baka ganin wannan da yanayin qauyawa" dariya sukai dukkansu ya sake cewa
"Qanwar matana ce fa, nasha ganinta da wannan kayan na jikinta so am sure itace ma" kallon sa Maheer yae
"Kayan kawai fuskar fa?" Be kulasaba sukai ciki ita kuwa se d'aga qafa takeyi zuwa cikin gidan kamar zata kifa.
Mom Nu'aiym.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
11
Kallon Mahal take cikeda mamakin sauyawar halayensa, yanda yake roqarta akan ta daure ta auresa, cikin sanyin murya tace
"Kayi hakuri Mahal wlhy bawai sanka ne bana yiba ko kuma na rainaka, ko d'aya wlhy ka sani bazan iyaba, na sani auren huce haushi kake shirin yi dani bawai soba, hakan kuma na sani cewar bakada labarin azabar da zansha a hannun su Ummul idan sukaji wannan maganar, ina roqon alfarma agareka daka janye wannan qudurin naka" nisawa yae yace
"Amma menene zesa ki damu da abinda zasu mikin keda bawai dad'ewa zakiyi a gidan ba, auren danakeso nanda sati biyu ayi, dan Allah ki dubi maraici na" Nisawa tae
"Banida wani gata a duniyar nan sesu mahal, bazan lamunci watsar da dangina akan ka ba, ka sani ni marainiya ce sabida su Baba iro sune iya yena, mahaifina ya rasu bayan nini kadai suka haifa a duniya!! Ya rasu ya barni inada qananun shekaru mahaifiyata er jamhoriyar Niger ce haka bayan rasuwar mahaifina ta auri mahaifin su ummul babu kalar qiyayyar daban ganiba nida ita qarshe ya saketa kuma taso tafiya dani ya hanata, a yanzu haka tana aurenta acen Niger da yaranta uku, ina shiga a Nigeria idan nae rashin su Baba iro? Bayan sune gatana gaskia ka sani wlhy bazan iyaba dan Allah kai hakuri" murmushi ya sakar mata yace
"Bazan takuraki ba Nancy amma dai zan baki lokaci zuwa wani satin kiyi nazari akai" shiru ne ya rataa wurin kanta nisa tace
"Banaso ka wahalar da kanka wurin neman aurena Mahal, sabida ni bazan tab'a iya aurenka ba har abada" Tana gama fadar hakan tae ciki abinta shi kuwa ya dafe kansa dukda haka bata tsiraba seda sukaci mutuncin ta sosai!
************
Sosai Maheer ya tattare nutsuwar sa yana kallon islam!! Duk ta masa fari tamkar batada jini, tayi baqi da komai.....gyaran zamanta tae kantace
"Da farko dai ni sunana Salahatul islam Idris me walda, mahaifina da mahaifiyata haifaffun en sokoto ne acikin qaramar hukumar silame dake cikin jihar ta sokoto, wannan kyawun halittata ta bahaushe ce kawai dani sabida iyayena duka hausawa ne, haka na ganni ina kamada mahaifiyata sosai komai nawa natane, mun taso a unguwarmu dake tudun wada mahaifina walda yakeyi itace ta kawoshi zaman sokoto ma, wannan dalilin ne ya sanya ake ce masa idi me walda, ya taso da matuqar son yaga yaranshi suna karatu sedai bashida qarfi ina da yayyu guda hudu duka maza, biyu uwarmu d'aya ubanmu d'aya biyu kuma yaran kishiyar Mahaifiyatane amma ubanmu d'aya, dukkansu suna fara karatu har matakin jami'a amma da qyar biyu suka qarasa kuma suna nan har yanzu cikin gidan ba aikin ayi tun daga bautar qasa, biyun kuma sune muke uwa d'aya uba d'aya wanda khamis yanzu yake aji hudu shi kuwa Asheer yana gun bautar qasa dalilin dayisa se yanzu suka kai nan shine sabida kosun fara rashin transport kawai seya tsayar dasu, so biyu khamis yana fara zuwa coe rashin transport yana daqushe karatun harya watsar wannan ma dasuka kammala da taimakona ne!!! Nice na taso me nutsuwa acikinsu amma se Allah ya mayar dani haka tunda na soma karatun gaba da secondry school....so da dama nikan tashi agidan mu babu abinda zamuci wani zubin haka zamu wuni ina kallon yaran kishiyar Babarmu suna cin abinci amma bazasu bamu ba... Haka sabida ita en uwanta sunada rufin asiri mukuma bamuda kowa se Allah, bayan dana samu admission a jami'ar usman d'an fodii na soma zuwa school sena soma had'uwa da ibtila'in rayuwa... Wani zubin inaji ina gani lecture zata wuceni sabida rashin transport.. Idan zanje makaranta na dinga kame kame kenan na rashin suturar zuwa makaranta wannan abin yana damuna bame qawance dani sabida hatta turaren sakawa banida shi wani lokacin ma sekaga vaselin dazan shafa ya gagaremu senaje a hakan ta fata duk furfuri!! Haka idan nawa mahaifina zancen siyen handout baya kulawa seyace babu har wani zubin nakanji tamkar indena zuwa makarantar!! Haka dai naketa daurewa har muka qarashe zangon karatunmu na farko,nida Nanuwa ajinmu d'aya kuma mumu kad'aine yaran bayin Allah, abinda na kula dashi shine Ita nanuwa bata sakin fuskarta nima muna qawancene kawai amma befi naga face dibta so biyar ba, wani zubin tare da ita muke soleta har gida qasa, idan mun fita bama rabuwa se munkai dandima se kowa ya dauki hanyar gidansu da qafa, ganin inashan wahala ya sanya mahaiyta tace in dawo hostel da zama na daure haka nan na dawo tare da neman Nancy akan ta dawo amma se Baban ta yaqi yarda, sedai takanzo duk sanda takeda test ta kwana karatu......zamana a hostel ya sanya na had'u da qawaye iri iri kala kala, dana gari dakuma b'ata gari ganin banida gata ya sanya wata qawata danai a hostel me suna jameela ta dinga nunamun hanyar yin zina amatsayin sana'a amma fir senaqi yarda haka ya sanya ta soma rarrashina harna soma kaucewa hanya, wani zubin takanzo da maza muje hira a mota kuma takan bani kyautar sututu da kud'ad'e jamcy na yawan nunamun cewar ina cikin musiba na talauci gashi handout ma ya soma gagarana siya, Namcy ta soma ankaewa da yanayin dana soma shiga na wani sauyi ta matsamun na bata labari ta hau wa'azi da ban baki, harta mun magiya, a haka dai ta saisai toni tayi sa'an rabani da jamcy!!!
Bayan nan kuma se Allah ya had'ani da wani saurayi me suna suraj haka na daddage ina qaunar suraj, suraj ya yaudareni har gidan mu yaje ya gayar da iyayena ya kuma tura neman aurena, komai suraj yana mun nafita a qangin talauci har ina samu in taimaki iyayena da qawata Nancy dake shan wahala matuqa agun Qanin mahaifinta dake riqon ta da matar sa, Suraj ya sabarmun da kud'i seya kashemun dubu hamsin a rana qarshen wata yana bani dubu dari yace nai laluran school suraj dan kasuwane kuma d'an siyasa ne riqaqqe!! Katsam rana d'aya suraj ya bijiro mun daneman hadin kaina akan mui zina, na nuna masa muda zamuyi aure menene abin rushing yayi yayi nace harammun bazan ba musamman shida yakeda matansa biyu yaje ya rage zafin sa anan, daganan ya nunamun gini yakeyi kuma yanada kwadayina, dayaga bazan yiba seya dawo rarrashin akan nai hakuri koda wasanni yana tattab'ani munayi tunda ba komai bane, haka na saki jikina dashi ganin kamar a hostel mafi akasarin mata suna yi, inajin suna hira mukanyi wasanni ta hanyar tabawa juna sassan jikinmu...wannan shine babban kuskuren dana tafka!!!! Na saba sosai da wasannin da suraj kemun ganin na fara sabawa ya sanya suran ya qara tadamun maganar zina, nace bazanyiba bece komai ba ya tafi tun daga ranar suraj seda yae watanni uku baya waiwayata ko wayana baya d'auka na shiga damuwa sosai, abubuwa ukune suke neman zautar dani na farko dai Ina matuqar son suraj a rashinsa har rama nai da kuma ciwo, na biyu kuma shine tsantsar talaucin dayamun dirar mikiya nasoma sabawa da kudi a wannan lokacin ina aji biyu kuma tun a zango na biyu na hadu da sura farkonsa kusan shekara munyi rayuwa me ma'ana sosai na shaqu dashi....haka kuma abu na uku shine tsantsar sha'awa na saba da wannan wasannin banzar, sena kasa sukuni inji ina son kasancewa da suraj harna soma jin koma waye zan iya wasannin dashi, adu'a naketayi haja dai har Allah ya karkato da suraj awurina, koda yadawo ko wasanin baya mun yace dani harammune nai hakuri koda wancem yaji wa'azi ya tuba, haka muka qara watanni biyu bama komai daya danganci wannan ko riqen ahnnu bayayi kuma duk abinda yakemun ya linka!! Ranar mukaje shopping akan kayana ya qare yace muje na rakashi yaudai na gayar da mamansa haka mukaje gidan ba komai a raina......"😭😭😭😭😭 shiru tayi tana sharar qwallah kantace cikin raunin murya
"Maheer bayan mun shiga gidan har parlor muka zauna wata yarinya dagani er aikin gidance ta wadatani da abubuwan sha shi kuwa ya shiga ciki, nasha lemo da cake da aka ajiyemun dama na kwaso qishiruwa kuma naga alamar ba kowa tunkan suzo naji kunya....haka ta kasance Maheer daganan se farkawa nai na ganni cikin jini da wahala ko yatsana bana iya d'agawa, alamu duk suka nunamun fyad'e suraj yamun tun daga yanayin zogin danaji jiki na yanayi aciki, ina nan kwance ina tunanin meya faru se ganin suraj nai ya shigo dagashi se boxers yana murmushi ina hawaye nace
" suraj mekamun mesa zaka cutar dani?" Dariya yae yace
"Soyayyace ta sanya haka Islam kiyi hakuri" kukana ya qaru jinya tabbatarmun na qarasa rufe jikina da bargon dake wurin nace
"Wlhy senayi qararka a kotu azzalumi kawai" kallon cikin idona yae yana wani shu'umin murmushi yace
"Waye ubanki islam? Me waldar? Me zaku iyayi dani? Aganin bansan darajar kudi na dakuke taci bane islam? Inada hankalina wlhy nasan me nakeyi ki sani ba'a cin kud'ina haka kawai kuma kije kotun qoli shari'a zan iya kune zaku wahala tunda kune talakawa, ina zamana kika zo har gidana kuma waye shedarki? Banza jaka" kukana na tsananta haka na barwa Allah ban gayawa kowaba se kawai na hakura, tsawon watanni biyu suraj ya dena kulani kuma tun daga lokacin da abin ya faru har akai watannin biyu na nemi al'adata na rasa!!! Shiru tai na some seconds tana sharar qwallah kan taci gaba... Koda na ankara na gayawa jamcy setace muje asibiti gwajin farko aka tabbatar inada ciki, da taimakon Allah fad'uwar gaban jin inada ciki shine yayi sanadiyar soma bleading dina har cikin ya b'are nasha wahala seda akamun wankin mara banji ba ban gani ba!!! Daga wannan lokacin kuma se jamcy ta fara tsora tani akan nazo mui karuwanci kota nunawa kowa takartar miscarriage din dan shegen dana samu ya fadi har akamun wankin mara, sabida bazata rufamun asiri haka kawai ba ita idan ta kaini gun manya zata samu kudi, nayi nayi jamcy ta rufan asiri taqi haka na yarda akan zanje so biyu tace itama ta yrda, mutumin farko dana fra had'uwa dashi shine ya bani kyautar miliyan daya, ya baiwa jamcy dubu dari uku, na biyu kamma daya tashi seya 1.5m wannan ya qara bud'e idona tunda nasan dad'in kud'i shi kenan sena manta batun yi so biyu haka na manta haramcin aikata abin,Nancy har kuka takemun akan ma tuba na dena amma Allah be sanya nayi nadama se zuwanka, babu memun fada agidanmu mahaifina be taba bincikar inda na samo kudi ba" .....jin tayi shiru na mintuna biyu ya bashi damar miqewa tsaye ya miyar da hannayensa guda biyu baya yana zagayen parlor d'in yarasa mezece laifin waye to? Iyayen ta ko suraj ko kuma ita kanta?
Mom Nu'aiym.
Zan shiga hidima kwana biyu wataqil kujini shiru sedai yanda ta yiyu.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
15
Tare da Ameenu yauma sukaje gidan su Ummul, wayar gafsat Ameenu ya kira ta fito suka gaisa sannan yace da ita
"Nancy en mata, an dinga b'oye fuskar nan acikin niqafi, keda ummul halinku ne ko ita seda nasha daga ta dena nace fuska aiba al'aura bane,kin dinga qudundune fuska kenan a qyalle haba qanwata" Jin ankira hafsat da suna Nancy ya ankarar da Maheer akan Hafsat, tabbas ya gaskata zarginsa akanta itace qawar Islam, tun ranar daya ganta awurin karb'ar kud'in nan ya ga kamar yasan qwayar idanta,yanayin tafiyarta ma ya hadda ce ya soma zargin Nancy ce tun ranar gashi yanzu ma ya qara tabbatar da zargin sa...
"Yaa Ameen zan riqa rage sakawa inshaa Allah" murmushi yae
"Enhen kokefa lil sis, yafiye miki ai, kuma ranar dinner da kamu plus arabi'an night dazamuyi karna ganki da wannan hijabin idan ma bakida mayafai zan bada kudi aje asiya wannan alfarmar kawai kiyi kwalli kamar wayayyiyar mace nace buqata kiyi ranar shagulgulan bikin nan" Dariya tayi sosai seda gaba bakinta ya washe acikin niqafin har suna hango hasken fararen haqwarenta kanta ce
"Na siya wasu ai, inshaa Allah zanyi gayen an decently" dariya suka saka har Maheer.....
"Dama saqon d'inkunan tane na karb'o mata danaje abj tace ana mata dilke shine tace nakira layinki ki karb'a so ki bude bayan mota ki dauka" da murmushi ta amsa da "to" sannan ta juya bayan ta dauko tazo zata musu sallam Maheer ya kasa hakuri yace
"Wainikam Nancy bake bace qawar Islam?" Murmushi ta masa
"Au dama baka ganeni ba? Nice kuwa qawarku" fad'ad'a fara'ar sa yae ya kalli Ameen yace
"Dama wannan dakake ganinta ai d'alibata ce, ka barni da ita kurun akan niqafin nan, a class tafi kowa iya kawo points amma iya muryanta kawai muka sani, muryan ma kaga tamu dabance da en gida dan wlhy ban shaidata ba se yanzu danaji ka kirata da suna Nancy dan haka frnds nasu ke kiranta dukda yake tun ganin farko qwayar idon yazomun da alamar sani"
"Kai haba kace mun zatasha carry over idn bata dena zuwa muku da niqafi ba" dariya yae yace
"Auu qanwar taka kakewa fata, qawar islam d'inace fa sosai kullum suna tare" da mamaki ya kallesa
"Wannan mara jin?" ga mamakin Namcy lokaci d'aya maheer ya had'a rai
"Yanzu sabida Allah seka kalli tsabar idona kace zaka gayamun koriya akan islam? Nazata kowani kaji ze zagarmun ita zaka tare, fiancee na be dace ace kaida kanka zaka zageta ba" murmushi ya wadata fuskarsa dashi yace..
"Allah huci zuciyar Abokina wasa nake, yanzu mu tafi kenan?" Be qara bi ta Nancy ba ya zaga ya shige gaban mota suka wuce, itakam dama tace wannan Maheer din be shaidata da kyau ba, daya ganeta sam dabaze sake mata ba yanda suka rabu ba arziqi a gidan sa zuwansu tare da Islam......
*************
Durqushe agaban mahaifiyrasa yake ya qasqantar da kansa sosai yana sauraren abinda zatace bayan da yagama zayyana mata bayani gameda son auren islam kuma lokaci d'aya ya sanar masa rayuwar da islam tayi mara kyau da kuma tuban datayi sabida Allah, abubuwan dabe dace ta sani bane kurun be sanar mata ba.....d'akin nata ya d'auki tsawon mintuna goma bakajin qarar komai se bugawar zuciyoyin mutanen biyu secen ta nisa sannan tace
"Tabbas Maheer Zaka samu d'inbin lada idan kayi hakan musamman idan kayine da zuciya d'aya badan ka wulaqantar da ita ko tozarta da ita ba, kakumayine domin ceton al'ummar annabi ka rage yawan b'ara gurbi acikin al'umma, sedai fa ka sani akwai qalubale babba agaban ka, kaga da farko dai akance yara sukan tsotsi ire iren abubuwan nan awurin iyayen su mata kaga matsala ta farko shine yaranka, na biyu kuma irin wa d'an nan matan sun saba da kashe kud'ad'e kamar ba gobe kakuma sani dukiyarka ta kasuwan cice bata siya sa ba, karkayi tunanin ana cewa aduk africa mahaifinka ne na daya a dukiya kakuma yi tunanin shine na uku a duniya ka sani komai yawan dukiyarka zata iya qarewa yau ko gobe kuma kud'i ayi amfani dasu ta tsafta tacciyar hanya, sabida haka nasan dole tazama me yawan buqatar kudi wa dan nan matsalolin sune abin damuwar dazaka duba amma ni bandaja ga hukuncin Allah, 'ya'yayen mu da muka gansu a shirye shirin Allah ne ba namu bane, idan Allah ya qaddari aure ka kasance me yawaita yin adu'a shiriyar wa 'ya'yayen dazaka haifa tunda kaga ita mahaifanta bawai sunyi yawon tazubar bane qaddarace ta haye kan ersu badon sunso ba, amma sakaci da addu'a yakan janyo hakan sabida haka ka dage ka kuma kula da er mutane, dan Allah idan kasan cewar zaka kawo er mutane ne ka wulaqantar da ita karka aureta , mahafinka kuma ka rigada kasan bawai zama yakeyiba seyafi 3 month bezoba be kuma dad'e da juyawa ba sabida haka zan masa waya tare da adane abubuwan dabe dace yajiba na kuma san ze amince inshaa Allah" Dama beyi tsammanin suyi masa gaddamaba sabida kasancewar sa masu sauqin kai da fahimta da wannan yabar komai awurin mahaifiyarsa ya zabga godiya ya miqe...
***************
Bayan kwana biyu dayin maganar su ranar data fado ranar talata ana i gobe wankan amaryar matar Ameen mahaifiyarsa ta sanar masa amincewar mahaifinsa akan auren, tare da wakilta en uwansa akan zuwa neman auren tare da sanya qalilan lokaci acewarta washe garin yace aje.........
*******
Kamar daga sama kuwa Ummul taji wannan labarin bakin mahaifinta wanda Maheer ne da kansa yazo ya sameshi ya masa bayanin komai kuma a washe garin sukazo akai komai aka sanya ranar auren nanda watanni biyu kacal!!!!! Wannan kenan.
***************
Yauce ranar wankin matar Ameen kuma an cashe daidai gwargwado,kamar yanda sakkwatawa keyi da safe sukai salalli da magrib akai wankan na amarya se kuma washe gari akai bikin kamu
Ba kadan ba Ummul tae kyau kuma ta tilastawa Nancy yin makeup ma ko islam tazo musu bikin, haka suka tasa islam agaba da zolaya suka kuma manna mata sirinrin mayafi shisa duk a wurin bikin a takure take ga maza sunzo ciki kuwa harda Maheer!! Ga wacce ta wadata wurin da abinci madam season 7 batasan kowa ba se Nancy so ita takewa nacin waza a kaiwa duk yayinda data miqe setakejin tamkar duk ita kae kallo.....tunda Maheer yaga wannan halittar hankalinsa ya tashi tunda yake be tab'a ganim mace me kyawun daya gani a fuskar Nancy ba, kai bama nan ba be yarda da love @ first sight ba se yau din nan, shibama kyawun ba yanayin murmushin datake zubawa ne ke dulmiyar dashi gefe d'aya kurin na kuncinta ke lob'awa haka kuwa ba qaramin kyau yayiwa fuskar tata ba, ga wushirya madaidaiciya dake tsakanin kyawawan haqwaranta!!! Wnnan murmushin yake bi da kallo ba fuskata ba, jin Ana kiranta da Nancy ya sanya ya ankare dacewar bega waccen ba kenan wannan itace Nancy?!!!!! Ya tambayi kanshi
Mom Nu'aium
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
14
Dogayen riguna ne guda biyu da mayafansu ja se kuma me black and dark purple sunyi matuqar kyau, se wani riga data kasa gane na material ne kona shadda me laushi dinkin ready made ne me asalin kyau yasha aiki ata gaban rigar shima guda biyu ne red and black ne kuma Emerald green se takalmi dako shakka batayi sun mata yawa wata kyakyawar sarqa data gani tafi komai burgeta acikin kayan, tana mamakin Maheer shidai ba tab'a ganinta yae ba mesa yake mata kyaututtuka ta tabbatar babu wanda ze iya shaidata acikin su se Mahal ranar dasuka ganta ba niqafi, menene alaqar sa da zuciyarta? Mesa yake mata kyaututtuka?" Nisawa tayi kanta janyo wayarta ta rubuta masa saqon godiya da adu'a.....murmushi ya sake bayan ganin message d'in nata ya mata reply Kamar haka
"Ameen ya nikeda godiya Hafsat" murmushi kurun itama tayi batae rply ba a sarari ta furta
"Wannan man din ya fiya nacin tsiya, narasa menene alaqar dake tsakaninsa da ruhi na ya ta'azzaramun" daganan ta miqe taje kasuwar da tae niyar zuwa.....yau kawai Hafst taga dacewan siyawa kayayyakin da Maheer ya bata mayafai wa ennan Rigunan qwaya biyu ko wacce ta siyan mata abinda ze dace da ita sannan ta siya fashion jewelries ta siya abubuwan datake buqata ta wuce shagon masu d'inki takai tukunna ta koma gida.
***********
Yau gaba d'aya Islam acikin damuwa take tunda Maheer ya tafi baya d'aukan call nata kuma shibe kirata ba, tashiga tsananin damuwa duk tayi rama, da wannan ta yanke shawarar ziyartar gidansa ko Allab zesa ta dace, har cikin parlor gidan kamala ya kaita ya gabatar mata da ruwa kafin yaje ya gayawa me gidansa yayi baquwa!!!
Kai tsaye kujerar dake fuskantar tata ya nufa ya zauna yana murmushi yace
"Manyan baqine yau agidan namu?" Kasa yin koda murmushi tae se yan tsunta datake murzawa a hankali cikeda qaguwa sekace me jiran wani abu....murya a dishe alamar tasha kuka
"Ina wuni Sir" kallonta yae yana murmushi yace
"Zaki kirani sir mana kinga hutunku yazo qarshe zamu koma muita gumurzu a class" Nanma batai magana ba yaci gaba
"Issy Baby yaya akayi ne? Na ganki da tsakar ranar nan" qwallan datake qoqarin tarewa ne ya silalo mata ta furta cikin raunin murya
"Maheer ka sani acikin dukkanin zagayen rayuwar d'an Adam akwai qaddarori iri biyu dake dabaibaye da akalar rayuwarsa, duk yayinda d'an adam yaso kaucewa wata qaddarar datazo masa da qarfin tsiya se reshe ya juye da mujiya, dukkanin abubuwan dake acikin qaddarar rayuwar mutum baya iya shallake su, na tabbatar kana sane da ingantaccen hadisin dayake nuni da yarda da qaddara ta alkhairi data sharri, kana kwai hadisin dayazo mana acikin arba'una hadith sahihin hadisin manzon rahma da bukhari da muslim suka ruwaito me bayanin ya da halittar d'an adam take tun daga mafarin samuwar sa har makomar sa ka, koda mutum shaqiyine kome ariziqi da abinsa ake haifarsa, hadisin be gushe ba seda ya tabbatar mana da acikin al'umma akan samu wanda ze kasance yana aikata aiki irin na en aljanna, harse ya kasance tsakanin sa da aljannar be wuce kamu d'aya ba sekuma ya aikata aiki irin ma en uwata kuma yashiga wutar, haka zalika d'ayanmu acikin al'umma ze kasance yana aikata aiki irin na en wuta harse ya kasance takaninsa da wutar be wuce kamu d'aya ba seya aikata aiki irin na en aljanna kuma yashigeta....ka sani Maheer dukkanin mutanen dake duniyar nan babu wanda baya kuskure koya aikata laifi kawai dai na wani yafi na wani munine, kuma Allah da kanshi yana yafe wa bayinsa bare kuma mu mu yafi juna? Na sani Ba duka maza bane zasu iya daurewa auren mace irina bama nida, amma ka sani auren na irina ma jahadi ne nayi tsarkakken tuba mezai hana ka tallafi maraicina ka aure na wlhy Maheer badan kai na tuba ba sedon tsoron Allah da kuma tunanin mezance masa idan ya karb'i raina ina mazinaciya sedai kuma maheer ina maka son daban taba yiwa wata halitta a doron qasa ba har kaina kuwa....Maheer ina maka *SON SO!!* ka kalleni da kyau ka gani wlhy banida *WATA FUSKAR* a qarqashin wannan ka dubi maraicina ka tallafi jihadina Maheer... Ka sanya Fuska ta tayi fice!!!! Tawa mazan bariki zarrah, ka taimaki salahatul Eslam ta sake *WATA FUSKAR* wacce tafi gaban mari awurin qadan garun bariki...dan Allah maheer" ta qarashe maganar a durqushe tana gunshshen kuka....nisawa yae gabaki d'aya maganganun islam gaskia ne ta ankarar dashi abinda ya gagara ganewa wanda addininsa ya sanar masa!! Cikeda tausayi yace
"Yanzu Islam me kikeso na miki?" Kallonsa tae
"Aurena zakai Maheer kayiwa Allah ka miyar dani macen danace in zama tun a baya" jinjina kanshi yae yace
"Kije inshaa Allah zan aureki cikin qanqanin lokaci, amma sekinyi bara'a kije ki tsarkake kanki namiki alqawarin aure inshaa Allahu" wani farin ciki ya mamaye ruhin Islam ta saki wani murmushi me qayatarwa kan tace
"Nagode maka Allah, na gode Maheer,Allah ubangji ya saka maka da mafificin alkhairin sa ya biya maka dukkanin buqatunka ya kuma tallafi bayan ka Maheer" gida ya sanya aka mayar da ita ya kwanta tunani shi sam baya sab'a alqawari kuma inshaa Allah ze gwada wannan wataqila auren na islam itace qaddarar sa shikuma yana ganin wata jarabawace yake gani akanta...yana roqon Allah ya bashi ikon cinyewa.
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
16
Sosai yasha mamakin yarinyar to ita kuwa menene da riqa ninke wannan fuskar ta d'aura *Wata Fuskar* akan kyakyawar fuska irin wannan? Dukda ya kula akwai makeup a kan fuskar amma ya tabbatar da cewar itace tawa makeup d'in kyau bawai makeup d'inne ya mata kyau ba, tana sanye da rantsattsen lace maroon color ta yafa mayafi fari dayake ratsin fari ne ajikin lace din, mayafinta asaman kafad'unta duka biyu ta zagoshi be sauka ba bare ya rufe mata jikinta wannan ya sanya duk a takure take, yakuma kula sosai da hakan murmushi ya sakarwa kanshi ya kula ya shagala sosai da kallon Nancy yana qoqarin kawarda dubanshi gareta ta juya masa baya nan take doguwar sumar kanta da aka linke kusan hudu aka mata daurin zara buhari ya bayyana, kafe idanshi yae akan sumar kanta ko shakka bayayi yanayin Nancy ya masa shi duk wannan qaton qugun nata be dameshi ba sam hankalinsa yatafine akan murmushin ta me qayatarwa daya tabbatar murmushin ne yake sada zuciyar sa da tata wuri d'aya suke tattakin had'ewa su tarwatse masa!!! Gyaran zaman sa ganin dayae ta tinkarosa gaba d'aya, runtse idan sa yae haka halittar tafiyarta take ya gano hakan sanda take nufar sa ko a hijan haka tafiyar ke nunawa qafafuwanta ba tsaye suke ba miqe sundan bole aqasansu irin bow legs din nan sedai ba sosai ba kamarma heeps din dasuke shirin mata yawane suka miyar da qafafuwan haka, miyarda kallonsa yae zuwa ga fuskarta Allah ya mata arziqin goshi kam qatoto ma kuwa bazece yawa fuskar kyauba muniba amma bako shakka be wani yi mata kyau ba sedai yarasa ata ina kyawun ke fitowa to? Lumshe idon sa yae ya furta a sarari "Daga cikin ruhin mamammalakiyar fuskar ne bako shakka" Zuhair ya miqa masa kyakyawan kallo yace
"Kaima kana kallon wacce yarinyar ne ko, ban taba ganin bow legs sunyi kyau ba se nata dukda ba sosai suka bole ba amma kam ana gani tangaram, sedai kalli fuskar tsarki ya tabbatarwa ubangijin daya qera wannan halittar" kan Maheer ya lalubo wata kalma harta qaraso da yaron masu rarraba abinci a bayanta dauke da tray tana murmushi ta nuna ma yaron table tace
" yaa Maheer ga abinci kui hakuri se yanzu yake isowa ina wuni" yau kawai Maheer yaji kalmomin bakinsa sun masa nauyi ya kasa furta koda qwaqwaran kalma dayace se murmushi yake zuba mata itama haka aka gama jere abincin tace
"Yaa Maheer idan kana buqatar wani abun call me plss, islam fa banan na ganku atare ba" kallon wurin datake yae bema san yaushe ta tashi a wurin ba, murmushin sa kawai yake narka mata,kanma yace wani abun islam ta dawo, harara ta wurga mata
"Danla ni muje ki tayani nuna wa masu rabon abincin nan baqin mu na musamman Allah a tsauwale nake da mayafin nan, tamkar zan runtuma ihu" Dariya tayi
"To ai kuma wlhy kinyi kyau qawata kamar bake ba, babu ma wanda ze yadda kece Nanuwan Baba iro" dariya suka kwashe dashi dukkansu kan su juya a tare yanayin tafiyar Nancy yake kallo ata baya yana murmushi........
Mintsilinta lslam tai tace "ke mazari a hijabi yau banga kina rawar ba" Murmushi tae
"A wannan taron zanyi rawa Islam? Kumama babu sutura ajikina fa dan wannan mayafin wlhh gwara na wurgar ma nake gani nikam"
"Amma kinsan beyiba kice bazakiwa ummul lik'i ba, koda na 2 mns kiyi, kina sani sarai mutanen nan kallon maqiya suke muku, plss ki nuna musu kin fisu murnar bikin kije kiyi rawa abinki, bafa komai bane ba yanzu an wuce wannan abubuwan dakike Nancy" murmushi ta sake yi a karo na barkatai
"Zanyi liqin mana rawar cedai bazan yiba" haka suka wuce suna wannan zancen,tayi likin amma batai rawar ba sam har aka tashi a wurin bikin......
***********
Yayar Maheer sam ta kasa aminta da aurensa da islam yayinda mahaifiyarsu tace sam baza'a takura masa ba, idan bazasu tayashi da addu'a ba tokuwa su bari kawai sabida ita bataga dalilin fasa yin auren ba dan kawai ana taqamar yarinya bataji, a bincikenta kaf bataji inda akace yarinyar ta tab'a barin gidansu zuwa wani wurin domin yin zaman kanta ba, in ko hakane meye nasu na dirza rashin mutunci har suce bazasu bari ya aureta ba, qaddarace ta rayuwa kuma wlhy kowa ze iya afka mata" Badan sunso ba suka hakura tare da sanyawa abun albarka....Anty Nasara itace babba kuma itace fitinanniya acikinsu sam ita bawai dan ance yarinyar tayi yawon tazubar ba kawai batason talakawa, yanda friends dinta ke bata girna ace auren Maheer dataci buri zasuyi da er matsiyata qyaure kofar gidansu yarinyar ance basuda shi se fatar buhu a irin wannan gidan zasukai baqin su ko en rakiyar daukan amarya da en kai lefe? Gaskia da sake wai an baiwa me kaza qafa.....bari yaje amma taga maheer din!
A parlor shi ta sameshi zaune ya d'aura k'afarsa d'aya kan d'aya ta kalleshi da kyau ta murtuqe fuska alamar ba wasa...shi d'inma tashi fuskar ya had'e sosai
"Maheer mesa zaka mana haka?" Kallonta ya qarayi
"Name fa?"
"Kamar yaya name? Ita muna danace kaje ku shirya meta maka dazaka d'akko mata er gidan matsiyata kuma tsohuwar karuwa kace mana ita zaka aura, banda kake mara tunani ma menene alaqarka da er talakawa?" Takaici sosai ya kama sa harya gaza furta mata komai ganin haka taci gaba
"Gaskia maheer da sake, ka janye wannan zancen auren idan auren kakeso kaje mana ga muna tun yaushe take dauke sa sanka aranta, yarinyar er masu dashi wannan ma ai ko kayan gida sesu gagara yi" yanzu kam mutumina ya sosu, ko ita da kanta daya d'ago ya kalleta seda taji wani iri cikin takaici yace
"Danke zaki zaunamun da matar zaki gayamun wacce ta dace dani? Haba anty Nasara yaya da iliminki da komai zaki gagara gane cewar da arziqi da talauci duk na Allah ne? Da Allah ya had'aki da miji me arziqi mahaifinki ma me arziqi se akace miki wayonkine ko dabararki ya baki? Kokuma aa sabida kawai Allah yafisanki da sune ya barki ajikin daula su kuma akasin haka, ki sani wlhy bazan taba auren muna ba sabida ba zab'ina bace zab'inki ce islam nace inaso kuma inshaa Allahu kodan tsarkakkiyar niyyar danake da ita akan islam Allah ze bani aurenta, magana ta qarshe kuma gaskia karki qara kiranta da sunan karuwa cox ni banga wannan sunan a tattare da ita ba, salihatul Islam shine asalin sunanta incase baki san sunan ba" Harara ta wurga masa
"Au tunkan yarinyar tashigo ma harka soma mun rashin kunya Maheer abinda baka tab'a yiba lallai wannan yarinyar ga alama da bokaye ta had'aka" Miqewa yae
"Anty nasara zanje kano ne yanzu nikam, akwai bikin friend dina yau ake dinner friday kuma kinga goma ta gota" be jira cewarta ba yabar gidan ita kuwa tashiga neman yanda za'ayi tayi maganin d'an banza.....
**************
D'aya daga cikin jallabiyoyin da Maheer ya baiwa Nancy ta saka me ja din, tayi masifar karb'ar ta ta sanya takalminta ja mayafin abayar ma jane, tayi asalin kyau dukda kwalli ne kurin a fuskar nan se powder da red lips stick...... Sha biyun na ranar akai walima sabida suna so suje makeup din dinner da wuri yasan ya suka saka walimar da safe da wannan rigar taci walimar ta, ganin rigar ba wata me matsewa bace ya sanya tafita zuwa karb'o d'inkinta na dinner da ita, A daidaita take nema gashi so take tayi taje ta dawo kar su tafi gun makeup su barta amma shiru babu alamar adaidai tan tamkar anyi ruwa an d'auke ma gaba d'aya........motar data sha gaban tane yasa tadanja baya tana yamutsa fuska har dimple nata seda ya lob'a loda glass yaje qasa setaga islam da Maheer
"Banza da kin zata saurayine kimai halin ko, to nice ina zaki?" Murmushi tayi daya sanya Maheer lumshe idanuwan sa ya saukesu a kanta a hankali...
"Bauchi road zanje shagon su Munir, kayan dazan saka dinner suna cen kuma 4 zamuje makeup kinsan wannan" Sauke ajiyar zuciya tae
" kinsan me dama gidanku Maheer ze saukeni mu tafi makeup d'in a tare, amma nifa wanka nakeso inyi, abinda ze faru bari na sauka na qarasa da qafa tunda ga gidan cen ke kuma sekuje yakaiki ki karb'o ku dawo, kannan kinga nayi wanka semuje makeup d'in atare" Bataso hakan ba amma tasan Islam da wanka tamkar er agwagwa bazata yarda wai ta bisun ba dole ta fito ita kuma ta zauna agaban motar, shidai banda islam datace dashi
"Honey bye" ya sake mata murmushi tare da d'aga mata hannunsa bece kanzil ba, seda suka lula kan titi yace
"Ina wuni?" Wata iriyar kunya ce ta lullub'e ta taji tamkar ta nutse da qyar tace dashi
"Kayi hakuri Yaa Maheer senaga kamar mun gaisa" be kula taba jin yayi shiru ya sanya ta d'ago ta kalleshi sosai ya qura mata ido sekace ba tuqi yakeyiba ita yake kallo....kallon nashi ya nayar kan titin batare dare dayace qala ba itama shiru tae ya mata qwarjini a takure take jinta matuqa
"Rigar nan tamiki kyau fiyeda tunaninki" ta tsinkayi muryar sa yana fad'a.... Murmushi tayi
"Nagode yaa Maheer, yaya nane ya siyamun ita dama yasan zatamun kyau" Be zaci tanada barkwanci haka ba amna beyi magana ba se murmushi dayakeyi......har suka isa shagon Babu wanda ya qarayin magana acikinsu,fita tae bayan ya tsaya data nuna mai wurin tace tana zuwa........koda taje telan ya fita yakuma rufe durowarsa dayake ajiye kayan daya karba, abokin aikknsa kuma ya tabbatar mata indai kayan data kawone ta karbi wani ranar alhamis to kuwa be qara d'inka ko d'aya ba aciki, seda taji kanta ya sara mata ga wayansa a kashe, koda taje motar kuka takeyi juyin duniya kuwa Maheer yayi ta gaya masa menene amma se kukan take tamkar wata yarinya qarama.....head ma ta siya kalar lace d'in takalmi haka, har yalolon mayafin dazata yafa dukta siya d'ankunnayenta ma haka gashi uku saura. Shidai ficewa yae daga cikin motar ya nufi shagon bayan daya tambaya suka mai bayanin komai bece komai ba se godiya daya musu ya juya.....Da qarfinsa ya figi motar
"Ki dena kukan nan haka, sekace wata jinjira tela seya sanyaki kuka, bari muje da akwai lace danake da a gida na siyane dama in sanya a lefe amma zan baki, nasan inda zasu miki d'inki cikin awanni biyu"
"Nibase ka bani ba, ka barni kawai nafasa zuwa bikin, harfa head da takalmi da komai na siya kalar lace din shine zasumin baqin ciki" murmush yae sekace wata jinjira ji yanda take shagwab'a ya fada a ranshi, a fili kuma be kula taba yaje gidan nasa ya shiga ya d'akko, ya dawo ya tuqa motar suka dauki hanyar zabira mall ....Appareal sukaje ya kira babba acikin telolin yace dashi
"Dinkin riga da skirt nakeso acikin awanni biyu zan samu?" Kallonsa telan yae
"Yallab'ai sedai idan zakayi doubling kud'in"
"Nawa kukeyine?" Ya buqaci sani
"Dubu shida muke dinka set, kaga 12k zaka bayar amaka express kenan" zaro kud'i yae a aljihunsa ya miqa masa sunkai 15k yace maza ka aunata ga 15k nan, kuma yae kyau d'inkin nanda qarfe biyar da rabi zanzo na karba" murmushi telan yae ya hau godiya kana suka shiga daga ciki macen dake shagon ta aunata, ya karbo guntun lace din ya dawo mota suka tayar
"Ki kaini kasuwan da kuke siyan Ashoeken zan siya miki da komai kinji" kallon sa tae
"Ka bari wancen sena hadasu a haka kawai d'awainiyan seyae yawa" B'ata fuska yae ganin haka ta nuna mai, laylac purple ne touch up din dake jikin farin lace din haka suka siya komai suka biya MR.BIGS sukai take away, tawa Islam waya take sanar mata komai inda tace su hafu gun makeup sukam sun wuce abinsu.....
Se after 6 d'inkin ya kammala, har lokacin suna nan atare, bayan angama taje gidan ta tarar na kowa, yace ta komatsa tazo haka tafito sanye da dinkin daya matuqar karbeta ya kaita wurin makeup daban yace tajira ya shirya yazo d'aukarta ........
********
Shida kansa data fito be gama shaida ita bace ba, tayi asalin kyau na musamman makeup d'in babu wani hayaniya amma tayi kyau sosai, bud'e motar tae tashigo qamshin turaren daya siya mata d'azu ya daki hancin sa seda ya lumshe ido....beyi magana ba wayanshi ya soma ruri d'agawa yae
"Baby" shine abinda ya furta a d'aya b'angaren
"Kiyi hakuri gashima na d'akko qanwata zamuzo" shagwab'e fuska tayi
"Honey kowa ya gama kallemun kwalliyana baka zoba ga angon ma naji yana tambayarka"
"Kiyi hakuri Babyna, ina hanya yanzu zanzo naga kwalliyan zanma bada kudin wankan tunkan nagani na siya naira goma ina zuwa zam baki goman ki lakadan" dariya ta bushe dashi sosai yabata dariya ainun......Lokaci d'aya Nancy taji ba dad'i amma bata nuna ba sabida batasan dalilin jin hakan ba
"Kinyi kyau Hafsat" kallonsa tae tana murmushi
"Kaima kayi kyau yaa Maheer sosssai kuma banma ganekaba" Kallon ta ya qarayi,ita d'inma shi take kallo dukkansu suna murmushi ya d'age mata girarsa d'aya abinda ya sanya ta kwashe da dariya sosai har wushiryarta ta bayyana, shima qasa qasa yake dariyar yaja suka lula...
Tun a qofar shiga wurin daze sadaka da hall d'in suka had'u dame d'aukar hoto nan take ya soma d'aukarsu hoto....tun suna kaucewa har suka tsaya ya musu haka suka doshi hall d'in bamewa wani magana amma murmushi ya kasa d'aukewa a fuskokinsu haka suka tunkari hall d'in aiko suna shiga kallo ya koma sama sabida d'aukacin mutanen dake wurin kallon su suke acikin dakakkiyar farar shadda maheer yake dinkin babbar riga yasha kyau ita kuwa farin lace ne me ratsin laylack purple tasha kyau, se haskawa suke tamkar wasu amarya da nagon me hoton da kanshi ya zata wasu ango da amaryar ne aiko ya soma danna musu pics hatta mutane da wayoyinsu se pics suke musu wasu basumasan dasu ba......islam qirjinta se dokawa yakeyi ganin shigowar su kasa hakuri tae tazo da sauri ta riqe hannun maheer murmushi ya sakar mata yace
"Na matsu azo tamu dinner nanda jibi baby, duk naji tamkar ace nidakene, tajiyoshi sosai dukda waqar dake tashi ta saki murmushi
"Allah ko?" Ta fada ya dage mata gira suka sanya dariya Hafsat kuwa harta sulale wurin Ummul dataga tana mata aamar tazo da hannunta......
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
17
Yaune karon farko na had'uwar hannayensu wuri d'aya, zame hannunsa yae ya kalleta yace
"Ba kyau kina had'e hannunki da nawa, tukunna dai" hannayenta ta had'e wuri d'aya
"Am so sorry honey rud'ewa ne nayi dana ga kyawun dakayi" bece komai ta jagoran ceshi zama wurin da aka keb'e don abokanan ango da qawayen Amarya,kusa dashi ta zauna yayinda Nancy tazo itada khadeeja ita kuma ta zauna kujerar dake fuskantar tasa batare dama ta lura da shi ba, har kad'a kanta take sabida waqar na ratsa ta soosai😍😍😍 shi kuwa gogan ya shagala da kallonta har seda islam ta kula da hakan, deejah ce ta zungureta
"Banza da zaran kinji kid'a se rawa, ikon Allah gaki saliha har saliha inda Allah ya rageki d'aya duk inda kikaji kid'a sekin raya" Dariya tayi ta dauki samosa dake gabansu acikin small chops da aka ajiye musu ta kai baki ta gutsura ta soma taunawa a hankali
"Karkace kansa yae yana kallon yanda gefen kuncin ta na dama ke lob'awa idan tana chewing ramin is do deep gashi da tsawo shisa koba murmushi take ba sekaga kamar tana murmushin......islam kuwa kasa hakuri tae tace da Maheer
" Honey mu koma sit na baya am not confortable anan" kallonta yae ya matso daf da kunnen ta ya rad'a mata
"Kishine kawai kinga en mata se kallo na suke, karki damu duk kin fisu kyau kuma babu wacce nakeso seke, ko gani kikai idona ya sauka kan wata ni kece a idona,kuma kece a raina kinji?" Murmushi ya sub'uce mata ta saki murmushin tana wani mammaqale masa...
Hafsat kuwa ta kaiwa moctail daya cafka ta soma tsotsa seda ta zuqi yafi rabi sannan ta dire ta miyarda kallonta ga khadeeja
"Ina islam ke?" Dariya tae
"Banza kinzo kina kwad'ayi ba gata a gaban ki ba" kallon gabantan tayi tana murmushi tace
"Kai lallai ma wlhy islam ke er Air ce tunda kikaga yaa Maheer niko oho ko, zaki nutsune idan ma miki fushi" Dariya tai tana qoqarin yiwa Nancy magana aka qara muryan waqa dole tai shiru cox bazata iya ihu ba....
Waqar hausa ke tashi me taken Hasashena ya tabbata...sosai Nancy ke qaunar waqar wannan ya sanya ta kasa hakuri ta zari hannun khadeeja sukai cikin filin rawar a tare, wannan ne ya d'auke hankalin Maheer zuwaga islam bebi takan masu rawar ba sabida an cika.....suna hira aka sauya waqar zuwa waqar Arashi naso aikam se sowa suka jiyo, islam ce ta miqe Honey bari naga meke afkuwa acen wurin yasin dukda kake ganin nancy haka nan ne kawai Allah ya rageta yanda kasan me aljanai inda taji kida tokoda d'an yatsane seta taka rawa" murmushi yae
"A sauka lapia to" juyawa kawai tayi taje ta shige cikin sahun gaba dayike duka a zaune ake masu rawar ne kawai a tsaye, to sekuma masu video dake gefe wasu har a wayoyin su......maheer ma juyawa yayi bil haqq Nancy da khadeeja se step dance skeyi duk inda aka sare ko aka karya a waqar ta arashi se sunyi murmushi ya sub'uce masa aranshi yace wannan ustazancin na Nancy yazo da wani salo irin na raini ma, kalli yanda take rawa har tana wani fari da ido wakar ma akanta yake, tsintar kansa yae dasoma yin video step dance da suke acikin wayar sa daga wurin dayake ya juyo gaba daya ya, dama sune a jerin gaba amma sit din dayake yana da nisa shisa islam ta koma gaban sosai ita kanta video take na rawar dasuke seda aka tsayar da waqar tukunna suka sarara wa kansu sukaje suka zauna,yanzu kam bata zauna da Maheer dan ita harga Allah ta manta dashi ma a wurin seshi da duk motsi yana kanta, aka qara kiran ango da amarya da abokanan ango da abaokanan amarya sui rawa haka suka jeru mata layi daya mazan ma haka, akwai wani gasa da ake na dance for the groom and dance for the bride qawayen amarya su mata na ango su masa aga wayafi iyawa,akan bada kyauta wa wanda yaci idan ango abokanan sa sukaci shi za'a baiwa in kuma qawayen amarya sukaci to....anyi anyi islam taqi ta shiga ita dai wai kunyar Maheer takeji ita kuwa Nancy ba ruwanta tunda ta soma rawar setaji ba kamar ranar kamu ba duk tadena jin kunyar beside acewarta ingaka fuskarta zuwa sunday anyi final....... Shida kanshi Maheer Bason yin rawar yake ba amma ya zeyi? Ameen shi ya saka a gaba akan lallai seyayi bashida zab'i mc ke zab'ar wa koea partner dazasuyi gasar anyi yakai mutane bakwai se a na 8 MC ya nuna maheer da kuma Nancy......tafi wurin ya d'auka har suna sowa akan zab'in na mc wasu daga ciki na ihun basu yarda ba a qarshe dai dukkaninsu kasa rawar sukai, shidai Maheer ya kasa rawar ne ganin yanda Islam tae kici kicin ita kuwa kunyar mutanen dake wurin dana Maheer ya hanata rawar, haka aka tashi a gasar maza suka cinye
Bikin ba qaramun qayatarwa yayi ba zan iya cewa yafi sauran duka events da akayi.....Maheer da kanshi ya ebi su islam zuwa gida tare da khadeejah da Nancy, juyin duniya da shagawb'a Islam tayi amma Maheer ya kafe akan ita ze fara direwa gida tukunna sabida unguwarsuce cikin gari Nancy kuwa basuda nisa, badan tasoba ta hakura da haka ko sallama batawa Nancy ba ta shige ita kamma vata kulaba ta mance se dannan wayanta take....bayan fitar islam a motar ta dawo gaba ta zauna haka yaja suka tafi jugum jugum dama khadeeja gidansu take kwana wannan ya sanya suka d'auki hanyar gidan kai tsaye ya tsaya Flamingo ya siyan musu kaza da chips daganan suka lula hanyar gida, haka kawai daduka tsaya se khadeejah ta fita Nancy bata ko motsa ba deejah dai ciki ta wuce abinta,kallon ta ta miyar zuwaga Maheer
"Yaa Maheer thank u so very much for everything i reallg Appreciate it, Allahu yabar zumunci ya qara bud'i ya kuma jiqan iyaye, Allah ya share maka hawayenka kamar yanda ka share nawa hawayen" Murmushi ya sakar mta dukda babu watacciyar haske yace
"Ba komai ai yiwa kaine, yanzu se gobe kenan?" Murmushi itama tame kan tayi magana call yashigo wayarta tana dagawa islam tace
"Frienf d'an bami deejah mana na tambayeta wani abin" bata kawo komai a ranta ba tace
"Ki kira wayarta ta shiga cikin ni ina waje" qirjin islam ne ya doka tace
"Waje kuma, after 11 fa keda wa?" Murmushi tae tamkar tana ganin ta
"Nida yaa Maheer ne, na tsayane na masa godiyar d'awainiyar dayamun yau" tsaki Islam taja ta kashe wayarta kallon wayar Nancy tae da mamaki amma batace da Maheer komai ba, sallama ta masa ta fice a motar, taje tayita kiran islam bata dagawa tarasa dalilin wannan iskancin amma ba komai ruwanta.
***********
Maherr dayaje gida ya kintsa wuraren sha biyu ta gota seya kira Islam so biyu bata d'aga ba, haka kawai yaji yanason yaji muryar Nancy kai tsaye ya juya akalar ntwrk dinsa zuwaga lambobin wayarta, ringin biyu ta d'auka
"Yaa Maheer ka isa gida lapia?, kayi hakuri ban kirakaba na gajine wlhy" murmushi yae
"Lapia lau ni gashi nakira ai, ya gajiya yaukin gaji ko?" Murmushi tayi me sauti
"Na gaji wlhy duk jikina se tsami yakemun"
"Ayya sannu kinji dear Allah ya baki lapia, dama nacene barin tab'oki,yanzu kin yi shirin kwanciya?" Gyaran kwanciyarta tae
"Ea na kwanta amma na gagara bacci ko motsinsa banaji".... Hira suka hauyi sosai ita kuwa islam ganin call din Maherr ya sanya ta kira back amma shiru be dagaba se dogon call waiting haka ta juya tana kiran Nancy nanma call waiting, lokaci d'aya ta shaqa sosai wani azababben kishi ya bijiro mata na bazata ta gigice tana neman haukacewa
Jin alamar kira nashiga wayar Nancy ya sanya Maheer yace
" Hafsat wake miki waya cikin daren nan inajin qarar shigowar waya" tayi mamakin shi amma setace
"Islam ce dayime nakirata bata daga ba shine take ta kirana ko zakamun uzuri injita" ya gano bincike take masa amma seya basar
"Ba damuwa muyi waya da safe, promise that u'll call me early in d morning 2mrw" da murmushi tace
"Allah ya kaimu goben zan kira" koda takira islam bata d'aga ba.
A wannan daren islam ta gama shirin yaya zatayi da Nancy bazata bari wannan yarinyar tamata qwacen Maheer ba zata iya yin komai akansa!!!!
**************
Washe gari asabar akayi wuni dakuma kai Amarya agidanta dake sama road en daukar amarya sun watse en mata sun dawo gidansu amarya amma babu Nancy babu labarin wayarta.....ankira layin har an gaji, kowa seyace rabon daya ganta tunkan isha!!! Wasa farin girki haka aka dinga neman Nancy har safe babu ko labarin inda take!!!.
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
19
Kai tsaye fareedah gidanta ta nufa tae wanka tae salla ta zauna ta qurawa wannan pic d'in ido ita sam ta kasa nutsuwa akan wannan maganar, yaya zaka dauki rayuwar d'an uwanka musulmi ba komai ba? Ko rayuwar arne babu wanda yace ka dauka ka kashe kace kaci bulus maganr nan da daddy keyi akan qyamatar talakan da Anty Nasara keyi har yaje wannan wurin!! Yasha yin fad'a akan korar mutanen datake yi idan sunzo masa, yakance mata yana tausayin ta kar wata rana wannan qiyayyar datakewa talaka ya janyo mata wata musibar, gashi yanzu ta fara gani tunkan aje ko ina, sabida tsabaragen iskanci da sonkai gashi nan ta soma safarar mutane....."Bazan iyaba!!!" Ta furta a sarari da d'an qarfi ladiyo me mata aiki tace
"Na'am hajiya, Magana kike ne?" Murmushi ta sakar mata na yaqe tace....a gayawa d'an liti ya shirya zan fita, wayarta ta d'auka tawa Maheer waya yana d'agawa suka gaisa tace
"Kana ina ne zamui magana dakai ne"
"Shirin zuwa sokoto nakeyi ko ince nama kammala sokoton zani"
"Idan na roqi aron awa daya zamui magana ban takuraka ba maganar tanada muhimmanci ne" murmushi ya sakar mata tamkar tana gabansa
"Ba komai anty Reedah bari nazo"
"Ka zauna kawai ni ganinan tahowa gidan naku" sallamah sukai ya zauna a parlor part dinshi yana nazarin dalilin reedah nasan ganin shi cikin gaggawa haka, yaga dai dazu dazun nan suka rabu, shikamma zewa sokoti shigar dare dan yanzu qarfe biyu ta kusa haka ya zauna wurin 30mns kanta iso........ Quryar dakinsa taja shi mahaifiyarsu nata murmushin ganin ana gudunta da zanje ta wuce dakinta abinta..... Zama sukai sannan ta kalleshi
"Sorry lele na b'ata maka lokacin ka ko?" Kallonta yae bece komai ba ta zaro wayar ta, ta lalubo hoton dayake tare da Nancy sunsha kyau kamar ango da amarya an dauki hoton daidai lokacin da dukkansu suka daga qafarsu daya da zummar takawa suci gaba da tafiya kana ko wannensu dauke yake da murmushi a fuskarsa se glowing sukeyi........ A hankali ya karb'i wayar ya qurawa hoton ido hoton ya masa kyau ainun ya burgeshi hanun shi yakai ya miqa dan ya tsarsa d'aya ya tab'a saitin dimple nata d'aya daya lob'a besan yaushe hawaye ya zubo masa ba harga Allah wani tausayin ta yaji ya kamashi sabo fili, farkon b'atanta yakansa hotunanta da videon rwarta agaba ya dinga kalla amma yanayin azabar dayakeji a zuci game da ita ya sanya ya dena amfani da wannan wayar zuwa wata, akwai wani waya dasukai da dare shida ita sanda ya mata hidima a gun finner take mai godiya mistkenly ya danna record sanda suke wayar bemasan ya shiga ba se daga baya dayake duba wayanshi yaji shima yakan kunna ya dinga sauraro gwanin tausayi😭😭....... Kallon sa Anty Fareedah keyi cikeda mamaki ya shagala da kallon hoton amma ya gagara ce mata cikanki!!! Matsawa tayi kusa dashi ta riqe hannunsa d'aya ya d'ago ya kalleta tace
"Wacece wannan Mahi?" Ta kirashi da sunan dasuke masa wani zubin ko ince yakusa ya zama sabon en gidan wato mahi......
"Anty qanwa tace, kuma kusan watanni biyu yanzu kenan da b'atan ta, ko bekai biyu saura kad'an....ta b'ata b'at anty wlhy, an nemeta an rasa sama da qasa" qura masa ido tae na wasu en daqiqu bilhaq kuka yakeyi kuwa lallai ta b'aci sabida tun suna yara maheer yakeda qarfin hali wani zubin komai girman dukan dazasu masa baya kuka harya girma kuwa baka ganin kukansa sabida dauriya har wani zubin sukan ce masa Biggest soldier.....hannu takai ta share masa qwallan sa akwai shaquwa me tarin yawa tsakanin sa da Fareedah tare suka tashi shekaru biyu ne a tsakanin su Twin brother take kiranshi shima yace mata twin sister har a waya haka sukai saving number's na juna.....
"Twin kuka kuma, menene tsakanin ka da wannan yarinyar da kakewa b'atanta kuka, am pretty sure cewan she's not d first person daka samu labarin b'atan ta"
"Anty Reedah wlhy mutunci yaufa muna tare gobe aka ce dani ta b'ata kuma shikenan fa anty ko labarinta babu, gwanda ace ta mutu ai ko" tausayin sa taji
"Qawar kace?" Qwallan shi ya sanya yatsa ya d'auke
"Qawar islam ce, kuma student d'inane, beside munada shaquwar wuni d'aya a tare, bama wannan ba kallon sister na nake mata tamkar ke da sauran en uwana ina qaunar yarinyar nan" shirune ya ratsa d'akin na wasu en daqiqu ya nutsu sosai yana kallon fuskar ta....muryan reedah ya tsinkaya tana magana
"Twin akwai damuwa fa" kallonta yae
"Mecece damuwar Twin sis?" Sadda kanta tae a qasa
"Anty nasarace tasanya aka........."daga nan ta kwashe komai ta gaya masa tun yana gane zancen ta har ya zamana meji amma kurma sam baya ganewa, babu dalilin aikata hakan agun anty Nasara sabida selfish interest nata kawai seta b'atar da d'an adam qwaya d'aya jal!! Jejin Amanawa!!! Ya nanata hakan a zuci se kuma ya miqe kamar wanda aka tsikara ya kalli reedah
" Anty fareedah wannan yana nufin kenan tuni Hafsat ta mutu aljanai ko namun jeji sun cinye ta ko?" Riqo hannun sa tae
"Calm down twin pls, inshaa Allahu Allah baze bariba wanda suka kaita cen ai muta nene, suba sun dawo ba? Inshaa Allah yanda suka dawo haka zamu nemota ta dawo itama kaji" duk da AC dake bayarda ni'imtacciyar iska me dad'in qamshi hakan be hana shi had'a gumiba, ya kalleta a karo na barkatai yace a yamutse
"Anty Reedah da tana raye aida an ganta tuni kusan watanni biyu fa cur?" Tausayi ya bata ta kula cewar akwai shaquwa sosai a tsakanin su kasa magana tae ya sake cewa
"Barinje in gayawa umma wlhy Anty Nasara seta gane kuskurenta har daddy zan kira yaji wannan rashin imanin da ta yi" miqewa tae ta riqeshi
"Karka soma zo muje gidanta kabi komai a hankali kaji" haka sukaje gidan a hanya se rarrashin sa takeyi har suka isa....
****************
"Amma anty binta hakan yayi kenan, da islam d'ince se ki mun asarar ta,kina nufin kenan dan abinda nakeso yana talaka bazaki tayani sonsa ba matsayina na d'an uwan ki" harara ta wurga masa
"Dan ubanka ninace maka abinda akayi laifi nane? Na samar da reedah dataje ta d'akko ka y'ar akuri ce ta aikata waidan yarinyar taganta karta tona azaci mudin masu garkuwa da mutanene, cewa fa kurun a tsoratar da ita ta fasa auren ka ni meye laifi na sema dana dawo ake gayamun" kallon ta yae cikeda takaici da baqin ciki mara misaltuwa yace
"Ba wannan ba yanzu ha d'amu da qawar taki ta nuna mana yaran da inda suka kaita nida kaina zan shiga neman ta da police" da dauri ta d'ago ta kalleshi
"Da police kuma kanada hankali kuwa sekaje a riqa cewa wai yayarka me en ta'adda wlhy kayi kadan tunkan ba qanwar uwarka bace ba seka qyaleta ai" kallonta yae har idanshi ya kad'a yae jajir se zare mata su yakeyi ita kanta ta tsorata da yanayinsa ya dauke qafarsa d'aya ya d'aura kan d'aya yace
"Anty Nasara ki sani wlhy baki kaimun cenba, na rantse da wanda rayuwata take hannun sa akan Hafsat zan iya yanke jinin dake yawo nawa acikin naki, zan yanke alaqa dake ta har abada, zan rabu dake rabuwa me girma zan nisanceki nisan ci me tsanani wlhy summa tallahi zan tsaneki tsana mafi muni a rayuwa!!! har a wurin Allah banida laifi idan nayi hakan sabida baki d'auki rayuwar d'an adam a bakin komai ba, zan kuma gayawa Daddy zan sanar masa cewar bakida imani yanzu kin sauya daga Fatima Bintar daya haifa kin zamo me kisan kai me gardawa,gwara miki tun wuri ki dawo hayyacinki zan rufa miki asiri na hana en sandan dogo bincike na binne sunanki kimun bayanin su dan naje nemanta da kaina" Mamakin kalaman sa ya sanya ta gaza furta koda kalma d'aya ta hango haqiqancewa a kalamansa iyakar gaskiyar sa kenan fa!! Reedah ce ta tare
*look twin beje cenba abin sam ko kad'an beyi nisan daze cenba, ke kuma Anty dan Allah ki had'a mu dasu waike ko haqqi bakya tsoro" nisawa nasaran tae tace ba damuwa zan hadaku dasu yanzun nan amma dai kaikam ka bani mamaki ta yanda zaka fifita wata bare akaina har kana rantsewa akan datse zumuncin mu akanta lallai da mugun abinda ta maka" bece mata kanzil ba harta had'asa dasu.
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
18
Maheer besan meke faruwa yana zaune a parlor gidansa babu abinda zuciyar sa ke masa se azalzalarsa akan yaje yaga Islam beson fushin ta ko b'acin ranta ko kadan, yayita kiran layinta a kashe gashi gaba d'aya ya damu, Maheer yana qaunar Islam sosai baso na wasa ba......breakfast kurun yake jira ya tafi ya qakara, whatsapp nashi ya shiga yaje gun status kai tsaye.....acen yaga wani friend dinsu ya saka rawan dasu Hafsat sukayi jiya beso hakan ba ze mata fad'a sosai akan rawa, tanada kamun kai koyaya takeson rawa tasan inda ya dace tayi rawar shine yafi,acikin maza bayaso yanzu gashi video din yana yawo hakan aibe kyautuba tsaki yaja a ranshi yace
"Nikuma awa?" Wuce status d'in yayi sekuma ya miqe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya qara qurawa picture din ido, hoton sane shida ita anja arror akusa da ita wai ana cigiyarta tun jiya da dare daga kai amarya kowa ya mata shedar batada yawo an jajje gidajen en uwa ba'a same taba.......da jallabiyar jikinsa ya fita daga gidan jikinsa har rawa yakeyi b'ata fa, jiya ya ganta wurin kai Amarya to ina tashiga? Shida kanshi ya kula da rashin ganin dabe mata ba sanda ake qoqarin barin gidan amaryar akai en mata gida har layinta ya nema be shiga ba...... Kai tsaye gidansu islam yaje anan yakejin wai tana kwance babu lapia tun shekaranjia.....har ciki ya shiga suka gaisa yake gaya mata aikuwa ta nemi cutar dake damunta ta rasa, se kuka tare sukaje gidan su Nancy islam se kuka take masa amma hankalinsa baya gunta, koda suka je khadeeja ce me musu bayanin
"A tare muka fito daga cikin gidan Amaryar fitsarine ya mayar dani da gudu inyi kafin mu dawo, na barta aharabar gidan...mune farkon fita gaba daya amma sena samu matsala danaje fitsarin nashiga toilet setai locking ga d'akin dana shiga babu kowa acikinsa haka nayita kici kicin na bude ga wayana na bata riqo yana jakarta qaramun wayana dake hannuna ba kati haka naita jiran tsammani da qyar na bude qofar koda nazo ba kowa shisa ban nemetaba na hau adaidaita kawai na dawo, neman wayana dana bata riqo ne ya ankarar da mutanen cewar ba'a gantaba a wurin sam!!!! Ta qarashe maganar tana kuka hadr da toshe bakinta da hijabin ta
" tundaga lokacin wayanta da nawa aketa kira basa tafiya ko nan da cen, Mamanta sumanta biyu muna zargin kidnerpers dinnan dasukai yawa ne a gari" Shiru Maheer yae yana nazarin kalamanta kanshi yayi zafi yarasa ma mezeje ga islam se qara d'aga masa hankali take tana faman kuka...
**************
Nancy se zare iso takeyi tarasa gane inda take bayan ta farka, hankalinta ya matuqar tashi ganin kanta datae acikin qungurmin daji ita kad'i kuma a d'aure jikin icce, takasa gane shin mafarki takeyi ko Gaske ne......innalillahi wa innah ilaihirraji'un itace kalmar dataketa nanatawa a bakin ta, bilhaq dai ta gano tana cikin musiba bazata iya tuna komai ba se ganin wasu maza suna tambayarta ko nane gidan Amaryar Aminu tace e shikenan seta wayi gari ta ganta a wani d'akin tare da wata mace kantae wani yunqurin kuma tarasa ina take se yanzu, waiga wa tae gabas da yamma kudu da arewa bataga alamar ko kadangare a jejin ba, babu alamar gari a gaba bare a baya, wurin yayi tsit se ita kadai runtse idanta tae ta soma rero duk wata addu'a datazo bakinta haka ta wuni har yamma ga jakarta a kusa da ita an ajiye mata amma bataza iya kunce kantaba bare ta dauki jakar ko zataga wayarta!!! Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.....wata irin razananniyar qara ta saka sabida ta gaji ga yunwa ga qishiruwa, ta qosa ta ganta a kunce, babban abinda yafi daga mata hankali shine rashin yin salloli idan zata irga da kyau tunjiya da aka d'akkota rabon datae salla yo batamasan inda kanta yakeba bare tace zatayi salla.... Adu'ar taci gaba dayi ganin ihun ba abinda ze fitar da ita bane......duhu ya sauka se wannan lokacin tasoma jin kukan tsuntsaye alamun sun dawo daga inda suka tafi qishiruwa takeji sosai tamkar zata mutu, yawun bakinta ya gama qafewa wani duhu ta gani tsaye agabanta abinda , a hankali ta d'aga kanta sama domin kallon meye anan ta sume bayan ganin abin....
*************
Maheer ya rasa dalilin damuwar sa akan Mancy, ko Ummul bata cikin nutsuwa kullum setayiwa Ameen kuka, ango ya kasa gane kanta, mahaifiyar Nancy tana nan an miyarda yaranta Niger amma tana nan, gashi an koma skul amma Nancy bata nan yanzu tsawon wata d'aya kenan da b'atan Nancy amma bako wanda yaga sanda wani abu ya sameta, Islam kam an gama ramewa an lalacewa akan rashin Nancy indai ka santa to kallo d'aya zaka mata ka gano cewar tana cikin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa na rashin Aminiyarta school d'inma tana zuwane kawai sabida babu yanda zatayi, auren ta kuma saura sati uku gaba d'aya ji takeyi batason auren nan kwata kwata, indai Nancy bata nan gani take auren ma gwara babu, da farko ta dauka kidnappers ne har tana shirin kudaden data tara na yawon duniya take shirin siyan kayan daki ta bayar a hada a karbo ta amma segashi shisu basu kiraba...tafi qaunar yau ace gawar Nancy aka gani tasan mutuwace akan hakan.....
Maheer kam acikin ranshi yakejin azabar daya kasa bayyana ta sabida babu wata alaqa ta jiji a tsakaninsa da nancy dazata sanya ya kasa mancewa da lamarin ta ya bita da addu'a kawai, wani zubin har abinci yake kasa ci,abu mafi bashi mamaki shine yanda yake mata kuka duk sanda ya tunata seyayi kuka kenan kuka ya zame masa d'abi'a kullum sabida da ita yake kwana yake kuma tashi baya manta ta wanda ya sanshi ma yasani walwalarsa ta ragu sosai...
Yauma kamar kullum kwance yake acikin bahon wanka an zuba flowers masu tsananin qamshi acikin ruwan dayake wanka dasu, ya kasa koda mosti bare yae wanka hawaye yakeyi yana tunanin Hafsat metawa mutane? Dawa take fad'a?, police sunyj shiru da binciken inda ta shiga to yaya hakane?.."..
Kallon Anty reeda anty nasara tae tace "Wai matar tasa tana nan ne? Kike zancen an bugo IV?" Kallon ta tae
"To anty ina zataje tana nan mana?" Biki fa saura sati biyu ko d'inkuna bamui ba, Umma kuma tayi zancen kayan lefe" Zaro wayarta tae jikinta har rawa yakeyi, ta nunawa Reeda wani hoto
"Wannan dake tare dashi wacce suke ajikin wannan hoton atare wacece ita to? Nasha itace amaryar ai?" D'an murmushi tae
."Ba wannan nasani ba bari kiga wacce ze aura damukaje gidansu kina dubai" nan take ta nuna mata hoton islam jikin ta kuwa har rawa ya somayi ita anty nasaran ta kalli fareeda cikeda tsoro tace
"Nashiga uku sis, wlhy nayi hauka da shirme kuwa?" Qura mata ido tayi tana mamakin kalamanta kantace
"Ban fahimcekiba sis?"
"Kinsan na sanar dake banason auren nan,nakuma kira Maheer namasa magana akan ya janye yaqi, shine danaga wannan pic a social media nace to lallai itace, senawa er akuri sending lokacin zanje umra daganan na wuce dubai, tofa shine dana tura mata nace a sace yarinyar a tsoratar da ita sosai akan maheer, ni tunda tace ansace yarinyar ban qarawa hajiya maganar ba, jin anyi shiru ya sanya nayi tunanin yarinyar ta janye ne shisa banbi ta kaiba, amma bawai sace yarinyar dawowar danai shekaranjiya hajiya azumi ke gaya mun wai taga fuskarta ta farka musu bisa kuskure shisa ta sanya aka kaita jejin amanawa wannan mugun jejin aka manna mata igiya suka jibge mata kayanta anan, wai idan ta mutu ko oho basu suka kashe taba, to nima banji dadin hakan ba amma senace bani nayiba ko lahira banida laifi" Mamakinta ne ya sanya Reedah miqewa tace
"Anty Binta yaushe kika canja? Wannan wane irin mugun tane fisabilillah? Koda islam dince yanzu keba ruwanki kenan? Idan da ace Meerah ce zakiji kwanciyar hankali tana wannan jejin? Karfa ki manta ko masu shiga ciki seda tsafe tsafe haba anty Nasara wlhy baki kyauta ba, qyamar dakikewa talaka hartakai kiga kamar idan ya mutu ruwansa shisa kiyashi duk d'ayane a gunki? Lallai ma Anty" shiru ta danyi kantace
"Karkimun raini wayau Fareedah kinaji ba" zama tayi ta dauki wayarta tawa kanta sending pic din ta wtsapp sannan batama mata sallama ba ta fita..........
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
20
Maheer da police ne suka zagaye kwalawan bayan sunyi nasaran kame su ta hanyar wayau, babban cikine yake jawabin abinda ya faru tirtan tiryan ya qara da cewar
"Cewa akayi ma mu kashe ta tomu a qa'idar aikin mu bama kisa ko bindiga ma bama amfani da ita qarqari yanki mutum inda mukasan baze mutu ba, shine mukace bama kisa se matar tace mukaita wannan jejin muda kanmu munajin storo seda aka qara dubu dari uku sannan muka kaita bama wani da nisa mukaje da ita ba muka daureta wurin kawai dan mukanmu a tsorace muke, sannan wlhy muba en fashi bane area boys ne kawai mabiya en siyasar sokoton nan" nisawa maheer yae yace
"Yanzu kune zaku mana jagoranci zuwa jejin, tunda naji ku kunada dama dama inshaa Allah bazan bari a tsare kuba kuma zan daukeku ayyuka a company d'ina me zaman kaina zan kuma baku jari wanda zaku ja a dayan bangaren ku qara nidai kawai so nake na ganta ne" kallonshi ogan yayi yace
"Malam tsakani da Allah zaka sama mana aikin nan ka rabamu da zaman banza, wani zubin abinshan koko ne seya fagaremu ka ganni nan NCE ce dani amma ba aikin yi idan har haka ne zan gaya maka gaskia" dan sandan ne yace
"Au kai dama dan qaniyarka qarya kakeyi ba hakan bane"
"Bafa qarya nayiba yallab'ai kawai dai wani abu yabiyo bayan mun ajiyeta ne" Riqe hannunshi maheer yae
"Wlhy summa tallahi zan cika dukkanin alqawarin dana d'auka kurun dai ka gaya mun gaskia kai harma da qari zan maka wlhy"
"Yallab'ai bayan munkai yarinyar nan abu biyu ne ya dawomun a zuciya, na farko dai nayi tunanin idan ta mutu mune da haqqinta na biyu kuma da akwai wani mutum dake so akai masa en mata ya bamu kud'i bansa me suke masa ba amma dai nasan ba kashesu yake ba wani zubin ma mu yake baiwa yaran muje mu mayar dasu inda muka dakko su, wasu bayan wata tara wasu shekara wasu har shekaru biyu suke kan mu maidashi, tose nayi tunanin na kai masa ita amma kuma nayita kiran wayarsa a kashe, ban taba sanin inane gidan saba kullum a hanya muke had'uwa....dukda haka senaje na dauketa koda naje ta suma a wurin amma haka na d'akko ta na kaita wani gidan mu na daureta kullum ko bayan kwana biyu nikanje sedai shekaranjiya naje batada lapia sosai, kamar ulcer ne da ita kwana biyu babu aiki ba kudi banida abun siyan mata abinci banjeba, inaso in sake ta ta tafi amma ina tsoron sena saketa oga me en mata ya dawo"
Cakumo rigar sa maheer yar "kanada hankali kuwa yaya zaka daure mutum ka kwana biyu bakaje ka bashi abinci ba, to waima tukunna ita kadaice kenan a gidan koda me kula da ita?" Riqewa maheer hannu yae yaji maqura yace
"Kayi hakuri yanzu muje cetonta shine yafi" sakeshi yae tare da tunkudashi yace ku tashi mutafi wlhy idan wani abu ya sameta duk sekun gane wlhy" haka suka d'unguma dukkansu har anty Reedah dake biye dashi kamar jela har sokoto ta bishi sanida en iskan a sokoto suke...... Da kanshi ya bude gidan ya kasa hakuri ya warce key d'in a tare suka shiga dukkansu wasu nabin wasu haka ya miqawa ogan key ya bude d'akin ya shiga shima yabi bayansa wasu police suka tsaya da wasu yaran a waje.......d'akin duhu sosai, Maheer jikinsa har rawa yake garin laluben fitilar wayarsa haka Anty Fareedah ma,hasken fitilar d'akin ya soma mamaye d'akin wannan ya baiwa Ilahirin mutanen d'akin damar fuskantar gabansu, Seda maheer yae baya sannan ya sake wayar hannunsa Nancy ce kam amma kamar ba itaba tayi baqi abin baqin ciki da takaici ma a tsaye aka d'aure ta kashi da komai anan takeyi kuma doguwar rigar dake jikinta dukta nannade a jikinta d'akin se tashin wari yakeyi na kashinta da fitsarin da takeyi...Maheer beko kalli kashin ba yae kanta da taimakon ogan suka kunce ta amma seta biyosu lago tana shirin fad'uwa riqeta maheer yae ya janyeta daga wurin najasar amma bega alamun akwai numfashi a tattare da ita ba, Se tsakar gida ogan ya kama masa suka kaita Maheer tamkar nagoye yake kuka hatta fareedah kuka takeyi police uku ma acikinsu kuka suke, lokaci daya nadama me tsanani ta saukarwa oga, ya kalli Maheer yace da kun shigar da ita bayin nan an dauraye mata jikinta bazamu iya fita da ita a haka ba, jikinta duk kashi" harara maheer ya wurga masa ya kalli fareeda yace
"Twin tayani duba pulse d'inta dan Allah" Dayake dama fareedah medical doctor ce wannan ne ya basu damar dubawa tabbas akwai sauran numfashi ajikinta sedai she's too weak....kallan shi tae tace "tana buqatar taimakon gaggawa amma dole seda wanka babu asibitin dazamu nufa da ita haka, gashi bazata iya yiwa kanta ba harga Allah ni bazan iya taimakontaba, tunda gidansu anan yake mukaita gida kawai" kallonta yae
"Banason sunan gidanmu ya b'aci twin, bazan kaita gida a haka ba dole seda wani plan, kinga police suje station da azzaluman nan ke kuma muje gidana ki gani...
Hakan kuwa akayi islam yawa waya yana nemanta a gidansa da gaggawa dolenta ta hau adaidai ta rigasu gidan suna zuwa yaja hannunta ciki " ki nutsu babu lokacin dazan miki bayanin wani abu a yanzu maza jeki ciki zan kawo miki Hafsat tana buqatar wanka k mata mu kaita asibiti tana buqatar taimakon gaggawa" kallonshi ta qarayi
"Wace hafsan? Tsawa ya mata
" Nace bamuda lokaci salaha!!!" Bata qara magana ba, wlhy dataga hafsat bata gane taba seda yace Nancyn kice a haka fa Salaha, wlhy an cutar damu" tsayawa tae yace "haba salaha ki mata wankan nan wlhy bamuda lokaci sannan kuma kinga bata numfashi da kyau" A haka islam na kuka tawa Hafsat sab'i yakai bakwai seda taga ta soma haske sannan ta barta haka anty Fareeda ta kira suka dawo da ita dakin suka saka mata kaya wanda yauma da ake neman kayan da qyar aka samu doguwar riga abinda kullum akwai kayan kyauta yau aka rasa se rigar maheer aka sanya mata, aka shafa mata mai da komai sannan fareedah tasa akai rushin nata zuwa asibitin uduth, a gaggawa suka karbe ta sannan suka samu nutsuwa kad'an mota Maheer ya kira islam yace
"Islam ki nustu kiji abinda zan fad'a miki, kuma ki sani wannan sirrine bana buqatar koa gidanku ki fad'a, sannan kuma ki sani abinda zan fad'a miki ya shafeki ne dakema bazan sanar miki ba" kallonshi tae amma batace komai ba yaci gaba
"Duk kanin abinda ya faru da Hafsat ta dalilin kine" da sauri ta kalleshi alamun bata gane ba....atake ya bayyane mata komai har qarshe yace.
"Bani buqatar sunan yayata ya fito sabida haka zan adana wannan maganar se Nancy taji sauqi gaba d'aya, sena nemo wani plan dazan fada kina jina ko?" Nisawa tae har tana qwallah tace
"Amma wlhy an cuci Hafsat wai kasan na kula da qafarta d'aya daga qasanta kamar a karye take😭😭 karaya tsohuwa kuma dan hargun yayi baqi, dukda batasan inda kanta yake ba wlhy na kula cewar tana yamutsa fuska duk sanda na taba wurin kuma, duka qafafun guda biyu sun kumbura suntum se qyalli sukeyi wataqik dukanta sukayi a qafar" kallonta yae shima qwallan dayake tarewa seda ya zubo sannan yace
"Islam a tsaye suka d'aureta kusan watanni biyu dole qafafunta suyi hakan ai, wataqil inaga ba karaya bace ba dai wani abinne karki damu kinji?" Gyada masa kai tayi tanata kuka, yau kad'ai maheer ya kamo kafad'un islam yana ganin wannan ne kawai ze sanyaya masa zuciyar sa gani yakeyi tamkar haqqin Hafsat ze dinga bibiyar zuri'arsu ne har qarshen ta .
**************
Seda doctor yaja numfashi sannan kalli Maheer yace cikeda tausayawa "kaine mijinta?" Kallonsa Maheer yae ya kalli islam da fareeda sannan yace
"Ea nine mijinta" doctor yace
"Babu damuwa in fad'i abinda zan fad'a agaban wa ennan?" Daga masa kai kurun yae alamar e baze iya magana ba jikinsa har rawa yake yi sosai akan hakan, doctor yaci gaba
"Ranka ya dad'e nayi mamakin yanayin abubuwan dake damun matarka har haka kanada arziqinka amma baka d'auki wani matakin ba, da farko dai yunwa tayi mata illa me tsananin wahalar magan cewa har indorscopy se an mata domun gano menene matsalar cikinta idan ta farfado, na biyu kuma tanada tsohuwar karayar da zance tafi wata daya ba'a dorata ba harma ta soma rube k'afarta ta dama, wanda ko shakka banayi dole se an yanke qafar, abu na uku kuma bata cikin hayyacinta jininta yayi mugun hawa, pcv dinta kuma is very low, yanzu zaka saka mana hannu ne a takardar cire qafar tata sabida a gaske bamason aikin ya wuce sati sabida qafar tanata ci karta qara sama tunda a qasane kawai, qarayar wurin ankle d'inta ne" kasa magana maheer yae ganin komai yake tamkar a mafarki yanzu kam har fareeda kuka takeyi sun gagara cewa da likitan komai se kuka har maheer din, mijin fareeda ne ya kira dama yace zezo sokoto shima dayake babban likitane, ta fice ta daga wayar tana kuka take sanar masa...... Haka Maheer be baiwa doctor amsa ba kuka yaci qarfinsa yaje mota yafi 30 mns yanayi, daga baya yaje dakin da aka ajiye Hafsat anan ya tarar da islam na kukan ta riqe hannun Nancy, shi dinma ya gagara rarrashinta zama yae ya qurawa fuskar nansi ido,se yamutsa fuska nancy keyi harse dimple nata ya lob'a, shafa fuskarta yae yace
"Ki yafemun Hafsat, duk ta dalilina kika shiga wannan halin" haka ya dinga surutai yana kuka islam ta kasa magana se kuka take qwalawa harna tashin hankali shima maheer haka......
0 comments:
Post a Comment