"Honey dama cewa zan maka ko za'a d'auke lokacin bikin nanne naga saura kwana bakwai ko IV ba'a kawo ba gidan ma harsun soma mgana" Sajen fuskarsa ya kaiwa laluba kanya qara kame staring yace
"Afwan Babyna, wlhy rashin lapiyan hafsat ne ya sanya na shafa gaba d'aya da zancen iv d'in nan amm kuma kinsan abba daddy baze tab'a sauya date d'in aurena ba sabida commitment nasa yagama schedulling da komai akan hakan,so yanzu inaga zan miki transfer seki nemi wani buga iv a garin naku ya buga muku naku na mata, na daurin auren ma daddy ya aiko nine zan aiko dashi but na manta wlhy" Bataji dad'in kalaman saba koda yike itama tanada damuwa sosai akan ciwon hafsat amma tana ganin be cancanci ya shaagala da sha'anin auren ba akan shi ace saura sati d'aya,cikin kasala ta furta
"Amma Honey hakan ai ba daidai bane, daga wurinku ake aiko da kati da alawa a al'adar sokoto fa" Haka kawai ya saka mata fad'a
"Haba Islam!! Ke bakya ganin ina cikin tashin hankali ne inada patient? Agidan mu wayakeda lokacin zuwa sokoto yin wannan abin, kinga dire al'ada gefe zanwa Ameena transfer koma namai magana asiya komai akai muku ina idan friend dina yazo babu damuwa?" Sekuma ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, hakuri ta bashi sukai sallama akan gobe za'aje akai....
***************
Tunda yaje asibitin ya kasa sukuni cox ana kan aikin qafar basu fito ba, tunawa da yae agidan sa na kano daza'a kawo islam akwai wuraren da babu funiture ya manta ba'a saka ba, tsaki yaja ya kira islam
"Honey ina wuni yaya anfito aikin ne?" Ga alama tunkan su fara magana harya qosa da maganar
"Ammm cewa nayi kin iya tuqi kuwa?" Bataji dad'in yanda yae ba amma jiki a sanyaye tace
"Ea na iya amma automatic kawai ban iya manual ba" jinjina kansa yae kamar tana ganinsa
"Kije gidan cen tunda key yana hannun ki ki shiga bed room d'ina ki duba a drower mirror akwai key's na motocin gidan farar jeeb dinda ke gidan kawai ce auto seki dauketa, idan ackin qannenki maza wanda ya iya tuqi seki bashi benz black sabida hidin dimun gida ke kuna ga naki hidima, sannan kuma gobe zan aiko kamala dukkanin abu nawa dayakeda muhimmanci agidan nan ze kwashemun shi zuwa sabon gidanki na sokoto, ku koma wannan gidan keda en gidanku da kowa ma, amm sannan kuma akwai d'akuna biyu acikin gidanki na kano dava komai aciki yaya kikeso ayi dasu, a zuba wane color zan kira company tun ban manta ba, amma se kuma nangidan shima daki biyune da furniture sauran tile ne kawai me za'a saka zanwa wani company magana a sokoto yazo yae wannan gyaran" Godiya taita masa kantace
"Dan Allah Maheer hidimar nan tayi yawa ka taimaka kabarshi a hakan zamu saka anan din, Allah ya saka da alkhairi yabar qauna na kanon ma inda aka gyara ya wadatar" Shiru kamar bazeyi magana cen se kuma yace..
"Amm dan Allah salaha karkice zakiyi bidi'o in nan wlhy samun lapiyar hafsa ce a gabana, ki taqaita zanzo iya dinne kinji babyna, idan zakiyi jmahagulgulanki kiyi amma karkice ban zoba" Numfashi ta fesar
."Dinner da walima kawai zanyi karka damu, se magaana ta gaba yaya zancen tariya sokoto ne ko kano" gyaran zamansa yae
"Kano za'a kawoki Mana ai nanne garinmu, abu na biyu sokoto sabida nan nakeyin aiki dole mu koma sannan na sanar dake bazaki ci gaba da karatu bako? Zan miyar dake wani skull daban bansan wannan yawon" haka taita binsa da toh har sukai sllam, annan ta durqushe taita kukan wahalar data daukarwa kanta...
Lapia lau aka wa hafsat aikin qafar anyi nasarar daurin sedai fa dawuya be karkace ba se wani hukuncin na Allah.
***************
Yau Ameen da ummul suna zaune a parlor ya hade girar sama data qasa, tamkar be taba dariya ba ummul ta kallesa tace
"Yaa Ameen banida lapia ciwon mara nake da yawan tashin zuciya gashi daga zaran na zauna kome nake se bacci" wani annashuwa da annuri ya bayyana a fuskar sa na lokaci d'aya ya kalleta
"Auu haba, barin kira miki Familu Dr. Dinmu ko" kallon mamaki take masa yanda ya sauya to ciwon nata ne abun murna, haka Dr. Yazo ya duba ta ya tabbatar cikine da ita 2 months mamaki ya kama Ameen shida yake da saurin gane ciki, kodan tayi period se biyune ya sanya yake tunanin babu, ya kalli Dr. Din
"Takan yi period fa yallabai yazace ciki har 2 months?" Murmushi Dr din yae
"Zata dena ne wasu matan sukanyi hakan, so kawai ta dena aikace aikace cikinta baya so shisa take ciwon mara" ranar murna awurin Ameen ba'a magana aikam hafsat har abinda ba'aso seda aka mata!! Kanta ya d'aure ta soma tunanin anya nrman haihuwabaure da watanni biyu hankaline kuwa? Amma dai dukda haka zataga qarshen abin.
Mom Nua'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
*Assalamu Alaikum...masoya kuma makaranta wannan novel din ina me baku hakurin abinda zan fada, dan Allah kuyi hakuri daga page 20 na jiya nadena baiwa kowa daga farko, inasha wahala wurin turawa gaskia, dan Allah dukmeso ta nema a group kotaje wattpad nagode sosai da qauna.*
*Maman Ramly wannan shafin nakine kyaita, ina godiya sosai da comment*
21
Haka Anty Reedah da mijinta Dr. Muheeb suka shigo suka samesu, ya kasa ya tsare tamkar ya rungume ta yakeji ita kuwa islam ta kifa kanta jikin gadon tanata kukanta a hankali.......Hannun Maheer d'aya tsaqale acikin na patient d'in yanzu kam qwallan ma ya gagara yi se numfarfashi yake saukewa da sauri da sauri itakam Hafsat batasan ina kanta yake ba oxygn mane aka sanya mata, kallon muheeb yae ya saketa da sauri yaje wurin shi ya riqe masa hannu
"Ka taimaki baiwar Allah nan muheeb banaso acire mata qafa qaramar yarinya ce muheeb, dan Allah ka dubi maraicinta ko aure batayiba ace a gundule mata qafarta waze aureta?" Rungumeshi Muheeb yae
"Calm down Twin kaji, komai zezo da sauqi na nemi transfer ma zuwa asibitin frnd dina me zaman kanta ta qashi dake kano, ni kasan ba ainahin wurin qashi nake ba amma nasan sosai akan bangare, zan duba qafar kuma yanzu da condition dinnan idan muka dauketa komai ze iya faruwa se dole an ciwo kan numfashin ta, abu na gaba shine ka sanar wa iyayenta cewar ka kama mutanen dasuka saceta sedai ka boye sunan yayarka dana qawar ta kakuma ce zaka dauki mataki akansu karka fadi wani dalili se bakasan komai ba faqat" binshi yae da kallo shikuwa ya sakeshi yaje ya duba qafar.....tabbas karaya ce ta wurin Ankle dinta sedai wannan karayar bazata wuce sati uku ba, kuma a yanda yaga hoton babu wani nama dataci sosai sedai fa tabbas koda zasu gyara qafar har abada bazata tab'a dawowa normal ba seta dan karkace idan akayi sa'a karkacewar bazata nuna ba amma idan akai rashin sa'a sedai yazamana qafar ta karkace yanda ze nuna sosai kamar me dingishi ko kurkuwa ma dan idan daya tafi daya tsyi dole seda sanda.....dafe kanshi yae cikin bacin rai anty Nasara tayi aiki irin na jahilai kuma jakai, talakan data raina yafita har a wurin Allah indai ze fita jin tsoron Allah......waigowa yae ya bayyanawa Maheer abinda yake hange ya qara da cewar
"Abari amma Dr. Sunusi yazo muji nashi tunda a wannan gefen guru ne yafini sani, sabida haka ka shirya muje gidansu hafsat a gaya musu abinda ya dace su sani sannan aga yanda zamui mu koma kano da ita amma gaskia dole se anyi amfani da private jet na Abba wurin daukarta" Hakan kuwa akayi Baba azumi se gwatsina takeyi akan qaryane seda sukaje taga yanayin hafsat itama seda tae qwallah jin an daureta a tsaye kusan watanni biyu ga kuma yanda jan buzu ya dawo kala kala ajiki, Mahaifiyar hafsat kasa kuka tae se zare ido takeyi dukta rikice........
*****************
Maheer ga mahaifiyar hafsat a asibiti amma ya kasa ya tsare yaje ya riqe hannunta yanata mata addu'a yana tofa mata yana ganin kota farka a firgice zata tashi dukda likitan ya sanar masa abincin dasuka bata ta hanci ya taimaka mata zata farfad'o anytime soon.....amma cire ox da aka daura mata,ganin haka ya sanya ta koma qaramin dakin dake farkon shigowa cikin dakin....
Hannunta ta motsa kad'an dayake yana riqe da hannun seya kaiwa wurin kallo ya dawo da dubanshi zuwa gareta a hankali ta bud'e idanta qura masa idanta tae na wasu en daqiqu batare data qifta ba shi dinma kallon ta yake har yana washe baki ya matsa daf da ita ya tallafi kanta
"Sannu Hafsat ya jikinki kin farka, inane yake miki ciwo sannu kinji yanzu kin dawo gida komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki" kallon sa tae alamun bata fahimtar komai ya kalleta sosai ya fara sunsuno wani abin, saketa yae yaje ya kira Babarta itama tazo tayi maganar harta gaji amma shiru hafsat ba amsa se kallon su takeyi tamkar wasu wawaye.......Ana haka ummul ta shigo itada Ameen, sukai kanta amma ga alama ba wanda ta gane se kallon mutane takeyi, fareedah ma da Muheeb dasuka gama kaiwa qarshen neman hanyar kaita kano suka shigo......da kanshi muheeb ya dubata yanda yaga kowa ya zagayeta har islam itama tazo amma batawa kowa magana ba se kallon su takeyi
"Lost of memory!" Ya furta a hankali bayan ya gama tab'a kanta dako ina amma bata ko damuba se binshi takeyi da ido, wannan yarinyar taga rayuwa ya furta a sarari, cikin gaggawa ya nemi hoton qwalwa batare daya musu bayani ba kiran wani dr. Kurun yae ya qara dubata sukazo aka tafi da ita hoton Kai....
Tunda aka gayawa maheer da sauran mutane cewar a kai ake hangen matsalar se suka rikice, abin ya daurewa kowa kai ga ummul dama tana cikin damuwa, Ameen kullum sesunyi fad'a yana cewa ya auretane danyaci riba da yaran dazata haifa amma wata biyu shiru babu ciki, tana mamakin sa ko shekaru biyu tayi batai ciki ba aibata cancanci hakan daga gareshi ba zaman su yaqi dad'i, har yana cewa dole tasan yanda zatai da samu ciki inba haka ba akwai damuwa cox bazeyi asaran kudinsa a banza ba...... Maheer ko yanzu mota ya koma yarasa meyasa yakeji kamar ana cewa za'a kashe shi duk sanda akace ga abinda ke damun hafsat, kwana biyu ma beje lecture ba, yanzu baya iya koda qwalla ne akan Hafsat tun ranar dasuka baro gidan nasara take kiransa baya d'auka sam!! Har dakanta taje ta gayawa ummansu abinda tae tare da yin qarairayi ta kare kanta umman tamata fada amma ta yarda bada hannunta akawa er mutane hakan ba....Abba ne kawai besan miyan da ake shaba sabida baya garin.
*************
Bincike ya nuna qwalwar hafsa babu inda ya tab'u amma fa tayi lossing memory dinta gaba d'aya wanda suke saka ran ya dawo bada jimawa ba, a wannan ranar suka wuce kano domin yiwa hafsat aikin na qafar.......
Mom Nu'aiym
*mu hadu a page na gaba anjima da yardar Allah.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
23
Bayan sun kammala wayar ne kuma tana tsakiya da kukanta mahaifiyarta ta shigo ta zauna gefen gadon ta kalleta
"Salaha lapiya dai? Kukan me kikeyi ne haka?" Share hawayentabtae tace tana murmushin yaqe
"Dad'i nakeji zakuji dad'in rayuwa ta dalilina akan auren da zanyi Inna, Maheer ne ya bamu gidansa daya tashi yace mu zauna anan garin, be furta yace kyauta bane amma dai yace mui mooving ciki Inna bakiga gidan ba ya had'u wlhy gidan masu kud'i ne fa" murna innar ta shigayi tana rarrashi akan abin farin cikine ta dena kuka kantace da ita
"Dama Nikuwa salaha cewa nai zancen kawo kayan lefe naji shiru har yanzu, en uwa sun soma tambaya kinsan mutane" Murmushi tayi
"Bam masa magana ba tukunna amma barin masa waya" Yana wurin Hafsat ya kasa ya tsare seda yaga farfad'owarta yana tsakiyan mata sannu yaji qarar wayansa.....Ganin islam ce ya sanya ya fita waje
"Baby" shine abindabya furta bayan d'aga wayar
"Ina wuni honey?" Yana murmushi yace
"Lapia lau my baby, hafsat fa ta farfad'o" se yanzu ta gane dalilin dinga fadan shi d'azu akan bega hafsan ta farfad'o bane, farin cikinsa yanzu kuma akan ta farfad'o ne
"Alhamdulillah Allah ya qara mata lapia" shine abinda ta furta tana murmushi
"To Babyna how far meye a qasa" sakon barkwancin da yae ne ya sanya ta saki jikinta takumaji sanyi a ranta, itadai tana matuqar qaunar maheer...
"Honey dama cewa nai zancen kayan lefe najiku shiru kasan a nan kafin biki ake kawo wa" Dafe kansa yae shap yama manta
"Dan Allah baby kuyi hakuri, kinsan Allah wlhy na manta ana lefe a aure ma, kumafa umma na kullum setayi maganar ranar da twin tamun magana ranar aka samu labarin hafsat duk wannan abun ne ya mantar dani yanzu kinsan meze faru,barin wa umma waya inyaso kinga sena kiraki back yanda mukai" Bataso jin hakan daga gareshi amma setace.
"Ba komai dear, sena jika" haka ta ajiye wayar ta kalli mamanta
"Ammm Inna wai akwai shirin dasukeyi amma ze kira mamanshi yaji inyaso seya kirani muji yaushe zasu kawo" murmushi uwar tayi
"To kuma zancen kud'in saka lalle da wankan amarya shifa yaya za'ayi? Ko kaya zasu kawo ne?" Nanma yaqe tayi tace
"Na manta dubu dari ne ya bayar suna nan acikin jakana" Gud'a uwar tayi ta karb'i kud'in tafita waje tana murnar an musu qoqari ta samu kudin yin kayan tuya na gara!!...
****************
"Ummana yaya maganar kayan lefen nan ne wai, kinga ni na shafa wlhy" Dariya tae har yana jiyo sautin muryanta tace
"Mahi auren nan sekace dole aka maka, waya tab'a manta kayan lefen matarsa? Kaga nifa enkai lefe nakan hanyar sokoto yanzu ma haka sun mun waya akan suna kan hanyar shiga layin su a unguwar....dama Fareedah bata sanar maka ba tare fa suka tafi, itada qawata da qanwar mahaifinku" Daria yae
"Nayita neman layinta beje ba kuwa, to Allah ya qara girma ummana nagode sosai"..
Kallon kayan aketayi ana mamakin had'uwarsa da uwar dukiyar da aka narka zani babu na qasa da dubu 25 komai yaji, tsayawa fad'ar dukiyar dake cikin kayan lefen ma bata baki ne, Islam tasha mamakinsa har taji kunyar hakurin data kasayi tayi kiranshi sabida kamma su gama wayar aka soma sallama ana shigo da kayan.
Agurguje plss
Auren Maheer da Islam dai Babu wasu bidi'o i da akai se dinner se kuwa gagarumar walimar data daddage ta shirya me qayatarwa, Maheer yai qoqarin zuwa gun Dinner wacce ta haska bilhaq anja dala an cuci naira kuma manya manyan en kasuwa sunzo anci ansha an wakita, islam kam tayi kyau na nunawa sa'a Maheer duk yanda ka kalleshi zaka tabbatar yana cikin kwanciyar hankali,nutsuwa da ni'imtaccen farin ciki mara misaltuwa shida kanshi shaidane akan tabbacin son dayakewa islam, dukkanin abubuwan dayaji yakuma gani akanta babu daya da yae tasiri akansa ya manta dasu tamkar yanda ka manta rayuwarka ta quruciya ko kuma tamkar wanda bema tuna komai ba na dangane da rayuwarsa ta jarin taka, yayi murna matuqa da aurensa, yanzu damuwarsa d'aya hafsat dabata magana har yanzu inda yake cikeda tsoron akan bayanin da aka masa kan cewar idan basui hankali ba maganar ma se an dawo fresh cox ko kashi takeji bata fadan zatayi da susuce ta lalace ta zama wata kala wata iri abin tausayi Yana ganin cewar duk abinda ya sameta ta dalilin sane domin akansa aka mata, shisa yake ganin haqqinta yana rataye ne a wuyansa, zuwansa sokoto ma be barota da kowa ba mahaifiyarta ta koma Niger sabida mujinta ya matsa en uwanta na sokoto anyi anyi Baba azumi taqi zuwa ita acewarta ummul ma batada lapia.... So Wata er aikin gidansuce larai kurun tare da ita hankalinsa duk kashi 30 yana gunta dukda murnar dayake ciki a qauyan su aka daura auren inda manya manyan en kasuwar duniya sukazo aka daura auren islam da Maheer amarya ta samu kyautar mota kusan 5 awurin daurin auren daga wurin abokanan mahaifin maheer se murna mahaifinta keyi haka washe garin d'aurin aka wuce da amarya agidanta dake kano.
*******************
Amarya duk inda hankalinta yake baya kwance kasancewar rashin adanar budurcinta zuwa gidan mijinta, a tsorace take da abinda zeje yazo fad'uwar gaba ya sanyata ramar wuni uku kacal shigowarsu gidanta na sunna ya qara gigitar da ita ainun!!! Haka en rakiyar amarya suka watse zuwa masaukin da aka ware musu aka barta ita kad'ai qwallin qwal!! Girjinta be dena bugawa dukda gyaran data samu daga Anty billy... Batasan yaya mijinta ze kalletaba ba akan wannan abin..tana nan zaune har Allah mad'aukakin sarki ya kawo Maheer da tawagarsa amma sesuka tarar ba qawayen amarya ko d'aya wannan ya basu dama baiwa amaryar kudin siyan baki 500k suka juya... A wannan daren sukai alwala da sallar nafila, sosai darajar islam ta qaru agun maheer ganin cewar tasani sosai akan addinintabya mata nasiha sannan ya bata wuri domin ta kintsa amma abinda ya bashi mamaki haryaje ya dawo bata sauya kayan ba tana takure a hijabin da tae sallah dashi, zama yae ya kamo hannun ta yaji wani asalin laushi me d'aukar hankali da sanya nutsuwa, murza hannun ya somayi a hankali hannun acikin tafinsa gumi yakeyi
"Babyna yaya, bazaki sauya kayan jikinki zuwa na bacci ba mu kwanta?" Kallanshi tae se ta kawar da kanta, jikinta rawa yakeyi ya kula da hakan sabida hannunta dayake riqeda se karkawa yakeyi,ya kula hankalinta baya jikinta kuma ga dukkan alamu bata cikin nutsuwarta ko kad'an,alamu ma sun nuna cewan a tsorace take....bayaso ya saka a ransa cewan wai dalilin yawon datai ne takejin tsoro wannan ya sanya ta tattaro nustsuwarsa shima ya janyota jikinsa, mamakin yanda jikinta ke rawa gabaki d'ayansa yakeyi, amma seya kawar
"Yau ina tsiwar ne eee matana? Ina tsokanar ina bakin duk sun tafi kema kinsan bawai sassauta miki zan ba, barin lalubo miki kayan baccin ki ko?" Runtse idanta tae, yaje ya bude jerin akwatunan daya gani ya nemo wata riga me tsantsi ya dawo.... Tanaji tana gani ya cire dukkanin kayan jikinta ya zura mata wannan, yauce ranar farko data somajin kunyar wani namiji arayuwa, sanda aka qwace mata budurcinta batasan ya akaiba, sanda ta fada bariki babu tsoro ko kunya a tattare da ita!!! Kashe fitilar dakin yae ya zare jallabiyar jikinsa ya dare gadon sannan ya janyota jikinsa hannunsa ya shinfid'ar ya d'aura mata kanta a saman hannun nasa suna fuskantar juna, hannunsa daya ya sanya ya zagaye bayanta a hankali ya shafi bayanta wanda wlhy babu qarya acikin ni'imtaccen dad'in dayaji da had'uwar jikinsu da shafar dayawa bayanta...runtse idanta tae jikinta se rawa yakeyi tana sauraren yanda yake sarrafa jikinta san ranshi, Maheer sam ya manta a wacce duniyar yake baya tunanin ya tab'a kasancewa akan ni'ima me kwantar da hankali sama da wannan, Murzarta yakeyi tako ina baji ba gani, Kasa hakuri yae sabida beso fara yin wani abu da ita ba yau, amma tunda ya had'a jikinsa da nata ya tabbatarwa kansa Islam d'insa ta daban ce, lalubo bakinta yae ya kai masa cafka, yau kawai duk jarumtar islam seta gagara aiwatar da komai tayi lago se yanda yae da ita, haka ya kaiwa dukiyar fulaninta cafka!! Ya dinga murzanshi a takaice dai seda ya yae mata jiga jiga ita kuwa ta kasa komai banda rawa da jikinta keyi babu abinda take iyawa, koda yazo domin gaabatar da aiwatar da shirin bayan gabatarwa seta sanya masa kuka sabida anan take ganin tagama wulaqanta, yauce ranar farko da islam ta tabbatar wa kanta ta wulaqanta rayuwarta na wofintar da Kanta awurin mazajen bariki, dama ace sanda akai mata fyad'e ta barwa Allah wataqil dabata tsinci kanta acikin wannan halin ba......
Kwanciya yae ya janyota ajikin sa
"My islam karki mun haka mana, ki barni in karbi haqqina idan kikamun rowa wurin wa kikeso inje? Ke kadai gareni islam na jima ina jiran ranar nan,ranar dazaki samto mallakina inyi yanda nakeso dake" Shiru ta masa ya kai harshensa a kuncinta ya lashe qwallan datakeyi sannan ya koma ruwa duk yanda taso ta kame kanta seda ya cimma burinsa da manufarsa akanta, a wannan lokacin daya samu nutsuwa jiyakeyi tamkar ya miyar da ita ciki, Ya kansance cikin farin ciki mara misaltuwa, haka ya dinga mata sambatu yana saka mata albarka me tarin yawa....nauyi da kunyar sa suka dirar mata ta kasa koda motsi haka suka kwana yanata daukinta yayi abu d'aya yakai so biyar, da asuba da kanshi ya mata wanka yana mata fi'ili akan bakinta da ya mutu ita kuma se mamakinsa takeyi bata tab'a koda mafarki tunanin zata samu tarairaya haka daga wurin gwarzon mazajen taba, shuya yane bed sheet ya turashi cikin ingin wanki ya sauya wani, kuma ya hanata aikin komai daga gidansu aka kawo break fasat da kanshi ma ya bata taci....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
24
Se yamma ya qara yin waya gidan nasu aka kawo abinci, sukaci sannan suka nufi asibiti wurin Hafsat.... Bayan sun tsaya yamata umarni da taje ciki yana zuwa, kifa kanshi yayi saman Staring motar tasa ya runtse idansa, yana da damuwa sosai akan yanayin daya riski Islam, ya sani ya shiryawa hakan kuma ya tabbatar wa kanshi ya samu gamsuwa me tsanani a tattare da islam to amma ya rasa dalilin damuwar sa akan riskarta matsayin cikakkiyar budurwa, yana ganin hakan baya rasa nasaba ne da kasancewar sa me tsananin kamun kai da kame jikinsa ga matan banza, ya sani Fasiqi se fasiqa amma a wannan lokacin yana kyautata zaton banda wacce ta tuba! Yana kallon islam a matsayin mace mafi tsarki aduniya baya jeranta ta a matsayin fasiqan mata, kasancewarta kamilalliya a yanzu Allah ne ya masa zab'inta kuma shine yawa alqawarin bazata tab'a ganin wani wulaqanci daga wurin saba danwai be sameta a matsayin budurwa ba, yawa kanshi alqawarin har abada indai ta wannan b'angaren ne bazata tab'a ganin wata alama daga gun saba ta rashin jin dad'i koya wulaqanta tata ba har abada......cikin damuwa yace
"Allah ka sanya islam ta shiryu kenan har abada, dazan samu wannan dana riqe islam har abada,idan zan iya bada shaida a lahira dasena bayar da ita acikin mata mafi salihanci na duniya"...... Kashe motar yae ya fita waje ya nufi d'aki, acen ya tarar da islam zaune tayi tagumi ita kuwa Nancy ta qurawa tv dake d'akin ido tana kallon wani film...gashinan an sato wani yaro yanata tattalin qwacewa shima seya raja'a da kallon cen kuma se aka qwalawa yaron kwalba akai nan take ta qwalla qara me tsanani ta had'e da dafe kanta, atare sukai wurinta suka ririqeta se ihu takeyi, Islam kuwa itace tae qarfin halin fita waje neman Dr., a d'aya b'angaren kuwa likitan dayake wani dakin duba patient qaran dayaji ya gayyato sa zuwa d'akin, seda sukai karo da islam da sauri yanufi kan Nancy ta gagara nutsuwa ta kwantar da hankalinta se ihu take, cikin gaggawa ya sanya aka kawo masa allurar bacci ya danna mata kana ya nemi ba'asin yanda abin ya faru....Bayani Maheer ya masa, yae murmushi ya dafa kafad'ar sa
" karka damu inaga mun soma samun nasara zata samu memory d'inta, hopefully ma yadawo gaba d'aya" Nisawa Maheer yayi
"Allah yasa hakan, daka duba qafanta naga tayita jijjiga" Nanma murmushi yae
"Lapia lau qafan take karka damu kaji" bece komai ba ya miyarda dubansa zuwa gareta yana nazarin yanayinta,se yamutsa fuska takeyi dukda bata cikin hankalinta alamun akwai abinda ke damun ta.....
*Bayan sati hud'u*
Acikin wa en nan satitiitkan Hafsat ta samu sauqi sosai, kuma tana magana sedai abinda muke tsammani na dawowar memory d'inta abin ya faskara ci gaba d'aya ne ta soma yin magana, kullum Maheer da islam wurinta suke wuni zamu iya cewa rayuwar amarcin Islam ya k'arene awurin sintirin asibiti da jinyar Nancy, Baba azumi dai taqi zuwa haka Ummul laulayi takeyi me matuqar bata wahala yayinda take samun tsananin kulawa awurin Ameen....Batada kowa se islam da Maheer su kad'ai ta sani su kad'ai take gani, acikin satin nan d'aya jal gaba d'aya islam bata zuwa asibitin sabida zazzab'in datakeyi, damuwa sosai take ciki akan yanayin yanda Aunty Nasara ke mata wulaqanci da nunin wariyar launin fata, a shekaranjiya ta sanar mata karta yadda tayi ciki ta haife musu dan tsohuwar karuwa tayi kukan wannan maganar harta godewa Allah amma sam bata gayawa Maheer ba, wannan dalilin ne ya sanyata jin zazzafan zazzab'in daya kwantar da ita, tayi dana sani me tsanani na halin rayuwar data aikata a baya, ta kuma kasa sanarwa kowa dama ace Hafsat d'inta nada lapia dama ace 'yar uwace bata rasa tunanin taba data gaya mata ko zata samu sassaucin abin da takeji......
***************
Maheer yayi wata shaquwa me tsanani da hafsat da har bayason zuwa sokoto kullum idan zeje seyasha fama, ganin tana masa rigima ya sanya yau yace baze ma sanar mata ba ya shirya ta tafi abunshi ya barta da islam, se dare ita kuma ta barta da Inna wacce dama hayarta sukayo domin tana kwana tare Hafsat d'in.....kwana biyu hafsat bataga maheer ba ta soma yiwa islam rigima akan yaa maheer kamar yanda taji qannin sa na fad'a idan sunzo mata dubiya... Da q'yar islam ta shawo kanta ta dena rigimar hadda kukan ta kuwa, abun ya matuk'ar dami islam, ta kasa gane alaqar zuciyoyin biyu, shima a b'angarensa hakanne ko waya ya kira Hafsat ze fara tambaya' yauma kamar kullum tana tsakiya da tunanin nan wayarta ya shiga ruri ko bata duba ba tasani Maheer ne ko daga yanayin waqar dake tashi....karawa tayi a kunne bayan data d'aga kiran a hankali ta furta
"Assalamu Alaikum Honey" murmushi
"Amin wa Alaikissalam Baby na ya gida"? Murmushin tayi itama
" Alhamdulillah"
"Ina Hafsat da jikinta?" Kallon Hafsat d'in tayi a ranta tace "Ni bazece ya nake ba se hafsat? A sarari kuma seta furta
" Taji sauqi Alhamdulillah" washe baki yayi
"Ki bani ita muyi magana" bataso hakan ba dama kenan ba ita ya kira ba? Badan ita ya kira wayar ba kallon hafsat din tayi ta mik'a mata wayar tana murmushin k'arfin hali....Bata karb'a ba kuma bata kula taba wannan ya sanya tace
"Yaa Maheer ne zaku gaisa ki karb'a mana" kallon ta tayi ita ma
"Bazan yi magana dashiba bayan ya tafi wani wurin ya barni kuma yace muyi magana bazan yiba nidai" Haushine ya ishi islam na sosan ma ta kalli wayar kanta daqile kiran tasoma k'osawa da wannan iskancin itakam ma gani takeyi tamkar memory d'in Nancy ya dawo rainine kawai dacin zarafi koda ya k'ara kira bata d'aga ba tamai banza Hafsat kuwa ta sanya kuka sekace wata jinjira baqin cikine ya sanyata barij asibitin batamawa hafsat sallama bama, ta barta da inna cena gwamatse masu bazata iyaba salon wulaqanci kawai.
****************
Washe gari ma Islam bataje asibitin ba da Maheer ya kira tace masa batajin dad'i shikuwa ya rasa dalilin daya sanya zuciyar sa take azalzalar sa akan yaje gun Hafsat wataqil hakan baya rasa nasaba da cewar da aka masa Hafsat ta soma yin tafiya da kanta kuma Dr. Ya tabbatar masa ta soma samun memory d'inta dan an sanar masa tasoma tambayar en uwanta su Baba azumi dasuke en iska basu zauna jinyar taba Ummul ce kad'ai me yawan kiran waya gashi batada lapia sosai laulayi takeyi kamar me.....Jikinsa har mazari yakeyi akan yaje ya ganta.....kai tsaye asibitin ya wuce daga zuwan sa garin na kano, yaji dad'in ganin ta tana tafiya da qafarta kuma lapia lau ba laifi tayi daidaito da y'ar uwarta sedai tak'i sake masa fuska gaba d'aya ta b'ata ranta...zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta
"Lil sis menene kuma na fushi? Na kikkira kinqi ki karb'i wayan mu gaisa" kallon sa tayi
"Ba komai" ta furta a taqaice da murmushi d'auke a fuskarsa yace
"Kinsan Ni lecturer ne a makarantar ku udus dake sokoto, baze yiyu na dinga jeka ka kawoba kano zuwa sokoto akwai nisa sosai"
"Udus kuma?" Ta nanata a sarari se kuma ta lula a duniyar dunani...kamar kuma wacce aka tsikara seta warce hannun ta ajikinsa
"Innalillahi yaa Maheer dama kaine ka sanya aka satoni ko, dan Allh ka kaini gun su Baba azumi mena maka a rayuwa" Wasa wasa dai da k'yar da sid'in goshi Dr. Ya kwantar da ita da alluran bacci se hamdala sukeyi ta samu memory d'inta back...sedai Beji dad'in hakan data zata ba amma ba komai ze jira farkawar ta seya mata bayani.
************
*Bayan kwana d'aya*
Islam da Maheer atare suka shigo d'akin, ga maheer ranshi a b'ace yake da islam akan rashin zuwanta asibiti kwana biyu, sarai ya sani lapiyan ta qalau yakula kishi ne ke d'awainiya da ita dukda yasan akwai kishi amma be dace tayi tunanin kishi akan Nancy ba sabida shi ba komai aranshi akanta se alkhairi kuma kwanaki da yawa tayi tana aikin lada, sadaukarwar data qara mata k'ima da daraja agunsa kwana biyu kuma se wani banzan kishi ya sanya ta b'arar da ladar ta na jinya....Babu wata walwala a tattare da islam amma ganin Nancy na kallonta ya sanya lokaci d'aya ta sake fuskarta tana fara'a taje ta rik'e hannunta sannu Nancy yaya jikin naki?
Murmushi Nancy tayi
"Lapia na qalau naji sauqi sedai inata ganin jiri, me kikeyi anan tare da Maheer" kallon Maheer ta juya tayi sannan tace
"Waya ce dake Maheer ne ya sanya aka saceki ne wai, kinga yayanki beji dad'in maganar ki ba, bakida lapiya kusan watanni uku kina kwance har loosing memory d'inki kikayi shisa kike ganin komai a haka ki kwantar da hankalinki zakiji bayanin komai idan kika k'ara samun sauqi, amma kan nan ki dinga yiwa Maheer adu'a shine sanadin samuwar sauqin ki da taimakon Allah" Batai magana ba, se shine ya kalli Islam
"Baby ungo key jeki mota nabar wayana d'akko mun" karb'a tayi da hannu biyu ta juya ya zauna a kujerar dake fuskantar inda take kwance
"Hafsat yaya jikin naki?" A maimakon tayi magana seta d'auke masa kanta gefe d'aya, be qara cewa da ita komai ba ya zauna kurin yana nazarin ta har Islam ta shigo da sallama a bakin ta, miqewa yae ya karb'i wayanshi sannan yace
"Baby barinje gun Dr. Zamuyi wata magana ne, da wuta na biyo tanan din idan na gama dashi idan kika gama zaman asibitin sekimun waya na turo miki driver yazo ya d'aukeki" kwanciya tayi asaman faffad'an qirjinsa
"Mesa yau kawai zakace bazaka dawo duba qanwar kaba" murmushi yayi
"Daddy yazone dole na ganshi yau bansan se yaushe zamu zauna ba, idan yana gari koke dakike matana bakida guarantee xaki ganni bare kuma k'awarki" Bataji dad'in maganar daya fad'a ba kanshi tsaye agaban Nancy amma setayi yak'e
"Idan dai zan kwana a saman qirjin kan nan toba damuwa, Allah ya tsare" Be qara kallon Hafsat ba ya fice abinsa.....
Ko kalma qwaya d'aya tak bata rage ba daga cikin abinda ya faru ta sanarwa Nancy, kuskuren ta d'aya shine Maheer be sakata aikata aikata hakan ba na biyu kuma bashida niyyan sanar mata cewan Antyn sa Nasara ce ta sanya amata wannan aikin, acikin labarin ta sanar mata zancen aurensu da maheer da dakatawar karatun ta itama....Nancy tayi kuka tamkar ba gobe, ta godewa Allah daya kub'utar da ita amma taji storon jin wai 'yan uwan Maheer suka kuskureta da islam suka mata abinda aka mata tunawa da abinda ta gani a jejin ne ya sanyata soma karanto adu'a tare da rufe idanta.
*Dan Allah kuyi hakuri, ina fama da students ne masu koyon girki shisa kwana biyu kuka jini shiru, kuma banida lapiya mura ce ta sakoni a gaba*
Mom Nu'aiym
[2/16, 11:35 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
[3/3, 5:54 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
25
A hankali ya gangara ya yae parking d'in motanshi, harga Allah baya cikin nutsuwar sa gameda Hafsat, yarasa dalilinsa najin haushin ta akan abinda ta masa abin ban mamaki kuma shine ya rasa meya sanyashi damuwa akan hakan? Ko gun Dr. D'in dayace zeje be biba, ranshine kurin yaji yana matuqar b'aci akan yanda be kula da Nancy ba yau...... Da k'yar ya iya saisaita kansa ya nufi guess house d'in daddyn sa cikin qunan rai,yayi matuqar mamakin jin cewar Mahaifiyar sa ta sanar masa dukkanin abinda Nasara ta aikatawa baiwar Allah yayi fushi me tsanani da har Maheer d'in dayazo d'aurin aure be gaya masa ba daya sani da tuni yarinyar tana waje ana kulawa da ita na mussaman....
"Yanzu sanar dani wane ci gaba aka samu ajikin yarinyar?" Kanshi aqasa yace anyi nasaran gyaran k'afar harma ta miqe kuma memory d'inta ya dawo normal idan ta k'arajin sauk'i ma aka sallameta zan miyar da ita sokoto" Jinjina kanshi yae ya miyar da dubanshi kan jaridar Daily trust dake hannun shi kamar bazeyi magana ba se kuma yace
"Akace baku sanar da iyayenta daga nan gidan aka aikata wa 'yarsu hakan ba,ko miye dalili?"
"Ea dama Abba rashin dacewar hakan kurin nagani, bazanso wannan maganar ta fita ba, tunda Allah ya kub'utar da yarinyar, kuma iyayenta ma ba wasu bane basu ma damu ba,ko mahaifinta tunda tazo nan garin basu zo dubata ba, kuma acikin watanni biyun datayi bekira waya so biyar ba yaji ya take ba, hasalima babu wanda yanemi ba'asin sanin inda aka ganta acikin su" kallonshi ya miyar akan Maheer yace
"Yace Mahee kai wanine kenan kake gani ko?" Da sauri ya kalli mahaifin nashi ya sani wannan kad'ai ya isa sanyashi ya dinga rigima,muryan shi na rawa yace
"Ba haka bane Abba rainane ya b'aci dasu mutane idan basu suka haifi yara ba sekaga ko mutuwa yaran zasuyi ko oho" Gyaran zaman shi yayi
"Su waye iyayen nata to?" Kallon Abban shi yayi
"A yanda naji dai wai mahaifinta ne ya rasu yabar dukiya me yawa, to ita kad'aice dashi shine se qanin mahaifinta ya auri maman nata ya kuma karb'i dukiyan azuwan ze riqewa yarinya shine fa zaman yaqi dad'i harya saki maman ta ta koma k'asarsu Niger to yarinyar se wahala takesha, yanzu gashi karatun nata ma data gama cin wuyar shi ya lalace sanadiyan haka nazata sunje sun mata defring ashe basuje ba....school d'inda take zuwa wani zubin da k'afa tun daga low cost har D'an fodio" wara ido yae ya jinjina nisan wurin kan yace
"Sanda naje sokoto nace zanje naga jami'ar d'an fodio nayi mamakin nisan ta, batada banbanci da jeji ai akwai nisa sosai, harna qosa naga isarmu bazakacemun mutum ze iya zuwa gun da k'afa ba tun daga gwiwa lowcost sabida nasan Gwiwa lowcost ai na sanar maka inada gida acen cen nake sauka idan naje sokoto, da nisa sosai fa"
"Allah abba ni shaidane takanje gida da qafa ko tazo da qafa ma, ai wasu mutanen basuda imani" kishingid'a yae kan kujerar dayake kai
"Kaima meya hana kaje kamata, ina kace d'alibar kace k'awar iyalanka kuma"
"Allah ko abba nazata iyayenta sunje" D'an guntun tsaki yaja
"Wanda be baka tranport kaje skul ba kaga alamun ze damune dan bakaje ba, kaida kace basa ma zuwa dubata kuma kace ko a waya basa kira, yaya zakayi wannan tunanin, yanzu abunyi mu had'e ta dasu sha'awa sedai iyayenta suna haqqin sanin me muke shirin yi, sabida haka ka shirya zamuje gobe sokoto" Be isa yayi musu ba dukda ba hakan yaso ba, had'e ta dasu sha'awa na nufin komawar ta london kenan gaba d'aya da zama da karatu toshi yaya ze rayu babu ita a rayuwarsa?....seda abban yace
"Ka tashi ka tafi mana",tukunna ya miqe,yana godiya yabar parlor d'in.
***************
*Bayan kwana biyu*
Har akayi discharging na hafsat maheer be k'ara komawa asibitin ba, abun duk ya dameta Islam da kanta tayi mamakin hakan duk sanda tace asibiti driver ke kaita tayi tambayar harta gaji amma be kulata ba, yau da akayi sallamar Reedah tana wurin kasancewar me gidanta ya sanar mata za'ayi sallamar, da suka gayawa maheer ma se cewa yayi akaita gidan umman shi, sunsha mamakin bece gidan islam ba, amma haka suka d'unguma har islam d'in.
Hannu bibbiyu umma ta tarbesu aka kai hafsat b'angaren da aka ware mata kusa dana su Shauty da sophie har ta k'ara jin sauk'i su kuma sukayi k'awanya a parlor suna zuba zance Umma se washewa islam baki tabke tana sakota a hira ita kuwa kunyarta sosai takeji ta kasa sakin jikinta, su sophie se yatsina suke an kai musu ita kusa dasu sufa basuga dalilin nanuk'e musu datayi ba yarinya se san abun duniya sun tsaneta wlhy.....
Maheer se bayan isha ya shigo gidan, bayan sun gaisa dasu Reedah ya buk'aci sanin inda take aka gaya masa tana can sama...kai tsaye saman ya haura ya k'wank'wasa d'akin a hankali, cen k'asan muryanta tace
"Bismillah, wanda seda ta fad'a so uku tukunna ya jiyota, ya turo k'ofar a hankali ya shiga, kallon sa tayi dan batayi tsammanin ganin saba ta sare akan ya tafi abunshi kenan
" Sannu da zuwa yaa maheer" shine abunda ta fad'a kanta a k'asa...Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
"Yauwa ya jikin ki?"
"Da sauk'i Alhamdulillah" zama yayi akan gadon cen nesa da ita
"Ga sabuwar waya na siya miki dan taki ko labari, nayi k'ok'arin miki welcome back na layukanki duka biyu sedai d'ayan na Airtel dole sekinje da kanki wannan na mtn gashi nan banma gwadaba amma bari na gwada akan wayan yanzu" murmushi tayi
"Allah ya k'ara girma na gode sosai" Be kulata ba har messages suka fara dira akan wayar daga kunnawa kai idanshi yae akan wata number data turo message yafi so 20 se shigowa sukeyi ba adadi ya tsaya cak!! Akan lambar ya soma bud'awa
("Nayi kewar rashin ki nayi kukan nisan dakika mun nayi dana sanin rashin zame miki dan sandan ciki domin baiwa lapiyarki kariya, nayi sake dakika zamto acikin halin rashin tuna komai gaki kwance k'afa a karye Allah ya baki lapiya...Naki me k'aunarki Mahal")
Wannan shine saqo na farko dayayi tozali dashi a wayar
("Babu a duniya me iya sanya na nisanceki ki warke ki dawo gareni muyi auren mu na soyayya...Naki Mahal")
("Ina kukan rashin ki, ina keawarki abar sona, Allah ya tashi kafad'unki") haka messagea suka dinga shigowa sama da kasa na Mahal ya zauna harya manta da wanzuwarta agun seda ya gama karanta su tsaf!! NA K'ARSHEN ne yafi tsorata shi
("Labarin samuwar lafiyar ki ya riske ni daga gun Mahal!! Naji ance kin warke ina nan zuwa gareki soon tawan, bazan rayuba idan baki abar sona, ina fatan kiga saqon nina") wato dama Mahal shiya miyar wani sha ka tafi? Lallai ma wannan yaron yazo da salon raini, mik'ewa yayi yana kallonta, ta tabbatar ba haka idanshi yake sanda ya shigo ba to meye damuwar?
"Bana son wannan sim card d'in bazakiyi amfani dashi ba, zan siyo wani da safe, ki rik'e wayar a gunki" kai tsaye yacire layin a wayan ya ajiye mata wayar, cikin rauni tace
"Amma yaa Maheer naga layin ya hau lapiya, kuma komai nawa na school da bank da komai dashi nake using" wata muguwar harara ya wurga mata, cikin d'aga murya yace
"To nace bazaki yi amfani dashi ba ko kinada ja ne!" Nan da nan idanta ya kawo ruwa
"Kayi hakuri ba haka nake nufi ba, abari da safe akawo sabon" seyaji kuma duk beji dad'in hakan ba daya mata amma bece komai ba ya fice daga d'akin...
************
Bayan ya tafi kuma dukse ya kasa nutsuwar sa, ya gigice ya d'imauce ya rasa meke masa dad'i yafa kasa gane inda zuciyar sa ta dosa gameda Hafsat, abu k'alilan ya fusata sa akanta, abu kad'an indai ya shafeta yake susutar dashi wani zubin, yau kam be tab'ajin kwatan kwacin azabar radad'i da zafin zuciyaba kamar irin wanda yaji yau ganin saqon nin nan, yana mamakin wanann dama Mahal son ta yakeyi yake masa wayau? Lallai ma yaron nan....
Islam ma bata ganewa komai ba yau din dasuka je, sabida yasha mur baya ko magana,beko kwana a d'aki d'aya da ita ba.
Mom Nu'aiym ce
Inshaa Allah na dawo kenan daily update💃💃💃💃💃
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
28
Washe gari tayi mamakin ganin an tasheta tun asuban fari kuma ance tayi wanka, 6:30am suka fita susu biyu, mamakinta yanda Maheer da kanshi ke tuk'i agarin kuma babu inda ya b'ata yasan kan garin kamar cikin gidansu.... Wata Makaranta taga sun shiga me d'an karen kyau da tsari, kai tsaye wurin shugaban makarantar sukaje yamai bayanin komai da harshen turanci inda yace sesun mata interview...Ba jinawa aka kammala komai kuma kai tsaye ta lula level 1 a b'angare low a makarantar me sunan Brilliant university makarantar su d'aya dasu Sophie kenan su suna level 3 inda sophie ke bibiyar medicine ita kuma sha'awa ke karantar b'angaren zane zane........
***************
A waya yake sanarwa Abba k'udirinshi nason dawowa Uk din shima, seda yayi wani dogon nazari kanya amince masa da hakan, yana jiyewa yaron fadawa business irin nashi na rashin lokacin iyali kwata kwata amma yana masa fatan alkhairi.
Kwance yake akan kujerar dake parlor d'in yana kallon tv duka tunanin shi da hankalinshi yana gun islam, d'azu dasukayi waya yaji muryan ta cen k'asa alamun tanajin jiki b'oye masa kurun takeyi, baya ga hakan ma yanaso ya kasance tare da matarsa sabida yana missing nata.....Lumshe idanshi yayi ya k'ara budesu a hankali acen k'asan zuciyarsa kuwa yana wani tunanin ne na daban sam ya gagara dena tunanin daya zamto masa tamkar numfashin sa, idan Abin da yakeji gameda islam so ne to lallai ko yana sonta so bana wasa, amma inhar ya kasance abinda yakeji gameda Hafsat shine So to kuwa da banbanci tsakanin so dakuma k'auna sabida ita har cikin jijiyoyin jikinsa yakejinta, tana masa zagaye acikin jini da b'argon sa, takasance itace numfashinaa dayake shaqa yana mata *Son so* wanda babu irin shi, yana mata k'auna wacce mizani yayi kad'an ya aunata sabida duk girmansa ta masa nauyi, yana jin dad'in sauti da amon muryarta tamkar itace ta farko ta kuma k'arshe acikin halittun a irin jinsinta a duniya, tafiyarta tana burgeshi takan d'auke hankalinsa xuwa wata duniyar daban yakanji tamkar bow legs d'inta sunfi na kowa masu irin nata kyau, seyaga kamar kyau ma suka k'arawa tafiyar ta, idan yana kallon d'an siririn hancin ta seyake ji tamkar ya dinga jansa a hankali yana wasa dashi, idanta masu ruwan zaiba aciki yake k'ara narkar masa da duk wani kuzari ya rasa katab'us idan beyi tunanin taba, k'wayar b'akin idanta ke d'auke hankalinsa yayinda ya kalleshi ya hango kanshi aciki, seyaji inama zata bashi aronsu su zame masa madubi dan harga Allah yafi ganin kyawun kanshi acikin d'igon bak'in idan nata, Duk sanda kumatunta ya lob'a kuwa idan tana cin abinci ko dariya kota yamutsa fuska, jiyake yi tamkar yaje ya sanya dan manuninsa acikin ramin yana mata wasa dashi, sumar kanta ke k'ara hura wutar abubuwan dake damunsa akanta, yakanji inama ace ze samu damar shinshinar sumar kan nata, ya shak'i k'amshin kan nata yanayin kwanciyar sumar nata yana nuni sosai da tsantsar tsafta kota yanda yake zuba sheqi......yarasa makama ya rasa madafa, ya ayyanewa ranshi komai nata burgeshi yakeyi daidai da yatsun hannayenta dake zara zara da nails masu kyau farare masu d'igon ruwan zuma a k'asan su, lumshe idanshi ya k'arayi a karo na barkatai, wannan yarinyar tana shirin wargaza masa lissafi,tanaso ta rikita tunaninsa ta tarwatsa masa kansa......da wannan ya miqe domin barin gidan kwata kwata, sabida harga Allah yana so ya yakice ta a ranshi, tasan sirrin islam!! Tasan wacece islam koda yayi nasarar auren ta baze tab'a nasarar zaman lapiyar su, ita islam bazata ji dad'in rayuwarta kishiyarta tasan seda ta gama yawon duniya aka aureta kuma sanin na sosai ba rumours ba, ita kuwa Hafsat zata dinga goranta mata hakan koda wane lokaci kuma yasani a wurin yara ma se ansamu haka ga Islam na shrin soma zazzaga masa yara agida......
******************
Matashiyar dake tare da ummul ce tace da ita cikin fusata
"Baiwar Allah kinfa isheni da tambayoyi marasa kan gado!! Bake bace mace ta farko data fara zama anan gidan tare dani, kece ta biyar idan ma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar dan bakida hanyar fita daga nan gidan, nida kaina na gudu yakai so bakwai amma da k'afana nake dawowa sabida wannan gidan dakika gani duk kyawun shi a jeji ne muke rayuwa, wanda bashida farko bashi k'arshe dubin duniya idan zakiyi bazaki gane komai ba ta inda ze sadaki da wani gari ko k'auye..... Idan kika kwantar da hankalinki kina haihuwa zasu maidaki inda kika fito, dama kwad'ayi ne ya kawoki kuma nasan kinci naki rabon da duk wacce bataci ba bata zuwa nan, sabida haka dan Allah da manzansa ki rufawa kanki asiri ki nutsu ki haife musu yaron cikinki ki huta da rigima" kallon rashin fahimta ta mata, ta rud'e sosai dajin wai yaron cikin ta zata haife musu!! Suwa?... Ta tambayi kanta, bak'in ciki tamkar ze kasheta da rud'u ta kuma durk'usa mata
"Ki taimakeni Naja'atu ki fayyacemun buri har wutsiya wlhy tallahi bansan komai ba game da zuwa nan gidan, hasalima wlhy tallahi ni matar Ameen ce, ba abinda naci nasa......
" Da haka yake yaudarar ku, nidai kuna bani mamaki wlhy, iyayen dayake kai muku kawai na bugi ne, dukkanin wani abu daze muku bana alkhairi bane ba, kukuma mata da iyayenku dazaran kunga me kud'i to ba wani dogon me bincike se aure, yanzu wa gari ya waya? Ki sabi tunda kikazo ta hanyar aure bakida odar barin nan gidan d'in sedai kiyita adu'a....yara kuma dazaran kin haife bakya ganin su kam ko labari sedai kamma kiyi arba'in suke k'ara danna miki wani cikin a huta gaba d'aya" ta karashe maganar tana d'age kafad'unta duka biyu....damuwa sosai ta nuna a fuskar ummul ta soma k'ok'arin kawo ruwan idanta k'asa...."Naja'atu mu kashe Ameen idan yazo semu gudu mana mu taimaki juna, na iya mota semubi duk sawun da tayoyin motar sa suka bi suka shigo" Dariya najan tayi
"Bari kiji Ummul kowama kike da suna, wlhy keda ganin Ameen seyazo sake yi miki ciki, abuncin gidan nan ma bansan da yanda yake shigowa ba nida na shekara biyar acikin gidan, sedai nikanga me gadine yake kawo abincin shima da bundigarsa yake yawo sannan duk wata idan za'a kawo kayan abunci me gadin dake kawowa daban, shi kamma bansan wayake bashi abinci ba,kina dai gani daidai da sylinder wannan guda bakwai ne agidan cike da gas, idan na fitar da wanda ta kare bansan yaushe ake daukewa sedai naga an miyar,gulma har bacci nake hana idona ina zuwa leqe amma bani ganin komai, gen din da ake kunna mana da solar bansan yaushe ake saka masa mai ba, hasalima bana ganinsa banjin kukan sa, ba'a tab'a hanani yiwa wata mace bayanin kan gidan ba, nidai kurun abinda na sani zaman iyayena nake a gidan nan" Shiru Ummul ta kasa magana tabbas ta d'akko ruwan dafa kanta, ta kashe kanta da kanta, ta tsoma kanta a uku da kanta....
************
Islam na kwance a d'akin Umma tun bayan da yayi tafiya agidan take kwana wurin Umma babu tsangwama ba kyara, sema wani tattali na musamman datake samu awurin ta koda wane lokaci.....yau Umma taje meeting bata gidan wannan ne ya baiwa Hajiya Nasara daman shigowa gidan tana wani yauk'i da uban k'aton kai da cikin dasuka mata yawa babu d'uwawu gatanan sekaje wani mayunwacin zaki......taunat cingam takeyi tana yatsina fuska sanda ta shigo d'akin...kallon wulak'anci da raini tawa Islam dake k'ok'arin gaisheta sannan tace
"Ke ina Umma?" Sadda kanta tayi k'asa
"Tajee meeting ne" ta bata amsa a tak'aice
"Kwanciyar me kike mana akan gado magajiya?" Kalmar ta daki k'irjin ta ba kad'an ba wannan ya sanya ta d'ago jajayen idanta daya riked'e mata zuwa ja ta kalli Nasara ido cikin ido amma batace komai ba....
"Dena kallona karuwa!!!" Ta furta mata cikin d'aga murya wanda yayi daidai da shigowa umma d'akin bata san da zuwan umman ba taci gaba
"Naji ance kinada ciki wato baki d'auki magana taba ko? Kina gani kamar wasane bazan iya kashe kiba akan wannan cikin? Kina tunanin bazan iya kassaraki ba bazan iya lahantaki ba kenan ko?" "Innalillahi wa inna ilahiraji'un" Itace kalmar da Umma ta furta a sarari
"Nasara dama haka kika juya? Dama zaman cikin daula haka kika dawo Nasara? Ganin kinada dukiya kike ganin tamkar ki sab'awa mahaliccinki ba komai bane ba? Lallai kin shayar dani zumar mad'aci, kin kunyatar dani kin tarwatsa tarbiyar damuka baki, yaushe kika koma haka Nasara? Matar d'an uwan naki tome ta miki? Meta kashe miki a rayuwa? Kuma koba itaba wannan kalaman basuyi tsauri ba kuwa? Anya Nasara? Anya bakya gudun sauyin rayuwa?" Shiru batayi nagana ba uwar taci gaba
"Fice mun agida, karki kuma dawowa sekinyi hankali, ko a waya karki k'ara kirana sekin yi hankali tukunna kinaji ba" Shiru tad'anyi nad'an k'ank'anin lokaci kanta ce
."ki Gafarceni Umma inshaa Allahu zan kiyaye" hararanta umman tayi
"Ki ficemun agida nace ko kuwa?" Sumsum ta fita ta k'udurta aranta seta ciwa islam zarafi acikin ruwan sanyi ........
*****************
Yau dai gaba d'aya Nancy ta tashine cikeda kasala kasancewar tayi mugwayen mafarkai game da ummul, a daddafe tayi shirin school taje ta gayawa su sophie zata wuce abinta tana sauri, Batabi school Bus nasu ba Maheer ne yace ze direta, ya kula sosai da rashin kuzarinta da walwala....kallon ta yayi yana murmushi
"Longon beb how far? Menene damuwarki kinyi wani shiru yau ko dimple din ma banga yana magana ba" tamkar yasani kuwa magana takeso tamasa amma ta rasa ina zata soma
"Yaa Mahii dan Allah number ummul zaka nemomun awurin Baba iro inaso nayi magana da ita" kallonta yayi adaidai sanda yake lankwasa sitiyarin motarsa don shiga kwana yace
"Kanki dawo skul inshaa Allah, zan masa waya sena bani in baki"
"Ni A a yanzu nakeso" na furta maganat tamkar zatayi kuka cikin shagwab'a, harga Allah Nancy ko a Nik'afi duk tadowar ta cikin rashin gata tanada shagwab'a, abune dai kawai wanda bakasan kanayi ba, gata da saurin kuka abu kadan kuka abu kadan kuka.....har wani zubin takan bashi takaicin kukan nan shi bayason kuka ya tsaneshi sosai.....kallon ta yayi fuskar nan tamau
"Bakida Number d'in Baba iro ke? Idan yanzu yanzu kikeso ki kirashi da kanki danni bazan nemo yanzu yanzu ba tunda ba fad'ar Allah bane ba" shiru tayi nad'an lokaci kan tacr
"Kayi hakuri" bece komai ba har suka isa, babu me magana yana direta ta sauka batako kalleshi ba..
************
Tunda taji bayanin haukan Baba iro taji hankalinta be kwanta da zancen ba, abinda ta tuna ta tab'a gani a motar sane ya fad'o mata aranta, cikin takaici tace da Baba iro
"Baba yanzu kunada yak'inin ummul tana k'asar waje? Niba gani k'asar wajen ba amma ana samun nunber na, gaskia da sake wai an baiwa me kaza k'afa ku bincika gidansu yarin mana" k'irjin Baba ne ya doka se'a sannan ya tuna da betab'a tambayar Ameen gidan suba, amma yaga k'anin Baban sa sananne ne shisa be damuba, duk da ya shiga damuwa
"To zan bincika gidan nasu Ameenu karki damu, yanda akayi na sanar miki" sallama sukayi ya dire kiran gwawar sa ba k'wari.
*Bayan watanni Biyu*
Tuni Maheer ya dawo Niger yayinda suke zaman ba laifi itada su fiyya, har mamakin yanayin kudad'en da ake basu takeyi, itama ta acc ake saka mata every month.....Basa shiri da shauty amma da sophie suke mugun shiri itane taketa wayar da ita amma shauty kulljm cikin zaginta wai kwadayine da ita.
Yau cikin ummul watanshi Bakwai, amma segashi tana ciwon mara da baya mara misaltuwa, tun tana iya daurewa harta kasa...Naja ce taketa kulawa da ita ashe Nak'udacr haka ta haifi yarinya susu kad'ai ke dumui niyar su, babu sanin kowa tunda ba kowa agidan, haka yarinya tazo Bakwaini, me tsananin kamanni da mahaifinta tayi kyau seda gatanan er mitsila tamkar lomar kishiya, haka Naja tayita tattalinta dama ita ke karbar haihuwa idan aka haihu amma bata taba karbar Bakwaini ba!!! Ko yaya zata rayu? Ko yaya Ameen zeji idan yaji tasha nono, a ka'idar yaran dasuke d'auka sam ba'a bari susha nonon uwarsu tasan kuma shida gidan se nan da watanni biyu idan yasan EDD na Islam ya cika!! Akwai matsala kenan!!!
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
27
Ummul dai yau ta shirya zuwa yawon zaga garin dabatasan wane garin bane, dan haka ta fito da hijabin ta sanye tana neman hanyar daze sadata da gate d'in gidan tayi hanyar waje abinta kan Ameen ya dawo.... Tana k'arasawa taga gate d'in a k'ulle ta ciki mamaki ya kamata ta shiga waige waige, idan har aciki aka rufe toko tabbas da akwai wanda ya rufe d'in tunda Ameen baya nan me hakan yake nufi kenan? Tasoma shiga ko kwanto game da al'arin Ameen, ga alama ma babu wani gida a kusa dasu bata hango roof ata saman gidan ganin tunanin ta baze k'areta da komai ba ya sanya ta juya kawai zuwa cikin gidan kanta yana matuk'ar sara mata tana cikin k'unci da bak'in ciki da takaicin kalar rayuwar datakeyi.....
***************
Islam tanaso tace zataje gun Hafsat amma bataga fuska ba agun maheer, hasalima tun daga ranar bata k'ara ji yayi maganar hafsat ba, takula yaji haushin abinda ta masa......Haka ta daure ta kirasa a awaya
"Honey dama zancene dan Allah kozanje na duba hafsat?"
"Ok kamala yana zuwa nanda 30 mns" shine abinda ya fad'a tare da katse kiran... Bata wasu en damu ba dai tace "Nagode honey" Bece k'ala ba ya datse kiran...ranshi a matuk'ar b'ace yake dukkanin abinda Anty Nasara ta aikatawa Hafsat a kunnen sa yana ji, kasa tsayawa jin sauran yayi islam ma ya d'auki wayar tane sabida ya kula rashin walwalarsa ya sanyata acikin damuwa, ita kuwa Anty wlhy dashi take zancen!!
*************
Be nemi Hafsat ba yabar gidan gaba d'aya koda islam tazo shi yabar gidan, A d'aki ta samu Nanuwa tana kukan ta juyin duniya tayi amma tak'i sanar mata me aka mata, sema daga baya takewa islam magana ta roki a karb'o mata kayanta daga kano gaba d'aya.....
****************
Bayan isha ya shigo part d'in nasu,kai tsaye d'akinsu ya nufa su yaran su sophie, bayan sun gayar dashi ya kallesu fuska a had'e
"Zuwa nayi in gayamuku naji dukkanin abinda Nasara ta sakaku kukayi ina tsaye jikin k'ofar d'akin kuma ke shauty na tabbatar kin ganni ko? Toku sani wlhy dama kunsan halina, kuskure daya naji kunwa yarinyar cen Allah ne kadai ze rabani daku, danjin zataje london tare daku bashi zesha a kitsa muku mugun abu kuma ku dauka ba, ina gargadin ku akan fita harkar ta idan ba hakaba zan muku mummunan hukunci kuma zan gayawa Abba ya miyar daku Bayero university duk a huta" Am batar za'a maidasu nan yafi komai d'aga musu hankali suka hau ban baki da ban hakuri....daganan d'akin Nancy ya wuce ya tarar islam na ciki suna tare, bayan sun gaisa yace da islam
"Zamuje gida ki sauka k'asa kiwa Umma sallama" Ba musu tawa hafsa sallama ta sauka ya fuskance ta sosai
"Na sanarwa Baba iro ya bayarda kayan ki dake kano duka, credentials dinki kadai nace ya turo a motan haya gobe, to ma driver daya kaishi ze dawo dasu,koda wani matsalar ne?
" Ni a gaskiya da akwai sababbin kayana fa danakeso acikinsu, kayana na bikin ummu da komai fa yanacen, hijab dayane anan kuma babu Niqafi" kallon mamamki ya mata yace
"To Nancy ba anan sena siya miki wani kayan ba" mik'ewa tayi ta soma doddoka k'afanta a k'asa
"Wlhy Allah ni inason kayana, dan annbi kace a kawomun" shiru yayi nad'an lokaci kanya zaro waya ya kira Baba iro akan a hado da wasu daga cikin sababbin kayanta da kuma takardun sannan nikafanta amma banda hijabai.....Ba msu yace to ya kalleta
"Ya isa,hijaban ki shirya gobe zakuje da islam kasuwa seku siyo ko kuwa?" Shiru tayi secen tace
"Yaa Maheer inason inga ummana dake Niger kan in tafi inda kukace" Dariya ta bashi wai inda kukace😀 .....
"Nanda kwanaki uku ki shirya nizan kaiki da kaina" murna tashigayi har ya hango hakan zataje Niger, Sophy ce ta rugo d'akin
"Yaa Maheer wai kazo inji umma, anty islam daga tasha agwaluma taketa kelaya amai harta kasa tashi ma" Yariga ta fice a d'akin da gudinshi yaje k'asa, be damu da umman dake kusa da islam ba ya d'ago ta zuwa jikinsa, kallon umma yayi sabida neman k'arin bayani tace
"Kaga waifa agwaluma yaran nan kesha shine tana ganinshi tayi zallo abata, anan gidan ko girkinmu batasanci sabida kunya har nayi mamakin agabana take cewa a samma ta abu nasan islam da kunya, shine fa tanashn biyu se naga ta ruga tun tana zuwa ta dawo harta gagara yanzu na share wanda tayi anan acikin minti biyar tayi yakai so hudu fa" kansu karayin magana se wanin aman, duk ajikin maheer tayishi be kulaba yakira fareedah, kai tsaye asibitin su aka kaita, gwajin farko ya nuna zaman ciki daram na wata d'aya da satuka uku harda kwanaki.....Murna a wurin Maheer ba'a ko maganar ta, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, ita uwar rakiyar wato Nancy ma har mamaki yake bata yanda ya sake yau se nisha di yake yi Islam se nan2 ake yi da ita tamkar ze maidata cikin sa....an samu nasarar tsayar da aman ma har ta samu bacci abinta.
**************
Yaso suje tare da islam Niger amma umma ta hana azuwan ta dawo gunta tunda batada lapiya, sophie da sha'awa su musu rakiya tunda kwana uku ne kurin zasuyi......
***************
Sokoto suka fara zuwa, tasha mamakin hakan a gidansu suka kwana d'aya, se washe gari suka doshi hanyar niger anan tasamu damar daukar abubuwan ta masu muhimmanci datake buk'ata bata kuma samu matsala dasu fiyya ba tun zuwansu washe gari suka wuce Niger......
A hanya se Bacci Nancy keyi gashi itane agaba, kamala kejan motar yayinda maheer da kannensa ke bayan motar a zaune, haka har suka isa garin Niger atare.....Mahaifiyarta taji dad'in ganin ta takumayi farin cikin jin tabar hannun azzaluman cen, tayiwa maheer godiya sosai, seda sukayi adadin kwana kin su sannan suka juyo zuwa kanon dabo inda koda suka karasu Nancy ta samu visa na zuwa london karatu inda tare da Maheer d'in zasuje se yaga yanda za'ayi ta samu komai cox ko maganar admission ba'ayi ba sesunje sabida k'urewar lokaci!
*******************
*London*
A babban birnin london sukawa kansu masauki a wani k'ayataccen gida me kyau tsarin ginin turawa yayi kyau sosai, 3 bedroom flat ne se wani cute parlor dake hade da kitchen da dining d'insa, Har yanzu dai Maheer baya sakewa Nancy, yayinda su kuwa su sophie suke matuk'ar jin haushin ta akan niqafin datake mannawa, sun tabbatar a london tayi kad'an tayi yawo acikin sa shisa ma suka gayawa maheer ya mata magana.
Kallon sosai ya mata bayan daya kirata yace da ita cikin isa
"Niqafan nan dakika zo dasu dole ki ajiyesu, bazasu lamunta ba anan kam, su komai da camera sukeyi kar wani ya aikata wani abu zargi ya tabbata akanki tunda face dinki a rufe yake, ya kamata ki sani nanba gida bane, tunda yake dama fuskar ki ba al'aura bace ba seki hakura da wannan aqidar" shiru batace masa komai ba yaci gaba
"Kin fara pure English yanzu wanne zakiyi anan?" Kallonshi tayi idansu suka gauraya lokaci d'aya k'irjin dukkansu ya buga, ta kasa d'auke idanta akan nasa, shi d'inma ya rasa dabarun yi ayau idanshi akanta baya ko k'iftawa, murmushin dabasuda niyyan yiwa juna suka sakarwa juna kan daga bisani yace
"Yaya dai sefa ince sekin biya kud'in wannan kallon, kinga fine boi kin wani kafeni da ido" shagwab'e fuska tayi
"Allah ni yaa maheer ban kalle ba, kaine ma kake kallona shisa har kaga ina kallon naka" dariya ya d'anyi
"Kin sani dai matana batada k'aton goshi ni banason mace me qaton goshi" tabare fuska tayi ta tunzuro baki
"Ni yanzu kawai se a rik'a cemun wai me goshi,bayan nasan wlhy ni nafika kyau so dubu" Besan dalilin jin yanason ci gaba da wasan ba, seya tsinci kansa cikin nisha d'i yana k'ara fad'ad'a fara'ar sa yace
"Oho dai nidai banason k'aton goshi da wani k'aton kanta a wurin" dariya itama tayi ta zauna da kyau
"Yaa Maheer yanzu wane course zanyi wai?" Murmushi ya mata
"Ke kika zab'i English dacen?" Girgiza kanta tayi alamar aa tace
"Noo Law na saka ban samu bane" gyaran zaman sa yae
"Kijewa law d'in mana ko kuwa?" Haka dai yayi convincing nata ta yadda zata yi law din....
A wannan daren kasa bacci Maheer yayi ya gama k'udurcewa kansa cewar lallai seya mallaki Hafsat!!! Ya fahimvi ba wani zagaye santa yakeyi sona hak'ika bawai na wasa ba, to Amma ta yaya? A yanda yakeji ze koma Niger ya ajiye aikin lecturing ya dawo ya rik'awa Abba wasu harkokinsa na nan, daga nan ya dakko islam tazo itama taci gaba da karatunta, babu sassaucin daze samu a nesanta kanshi da Nancy face siyan fashewar zuciyar sa!!!!
Tayaya zaman nan ze yiyu? Anya ba yanzu muka fara wasan ba kuwa? Da alama akwai sauran rina a kaba.
Mom Nu'aiym ce.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
29
Islam ta k'urawa babynta ido cikeda so da k'auna da kuma tausayi me tsanani!! Bata tab'a kawowa aranta duniya zata mata atishawar tsaki haka ba, bata tab'a kawowa ranta akwai ranar dazata haihu babu dangi a tare da ita, bata tab'a kawowa ranta zata haifi 'ya ba uba ba, ko a mafarki bata zata zata haihu ba asibiti ba, ta samu rauni amma bame kulawa da ita, Bata tab'a zata zata haihu ta rasa romon dataga ana yiwa masu jego ba, tasha ji Baba Azumi na fad'en idan ta haihu kunu zata dinga mata me kyau jikinta yayi k'wari da wuri, tasha ji Baba Azumi na fad'ar zata mata wankan iccen Dogon yaro na ruwa me shegen zafi, Baba Azumi taci burin sanyata a kujerar mata ta dinga turara mata kasanta ance yana maganin tusar gaban da mata keyi bayan sun haihu.....Bata tab'a zata, zata a haihu. Babu uba ko wani jigon dazewa abinda ta haifa Hud'uba da kiran salla ba, Bata tab'a koda a mafarki tunanin cewar zatafi haifi abinda ze rasa sunan da za'a kirasa dashi Ashe Ameenu ninketa yayi baibai ta hanyar sanyawa ainahin fuskar sa *WATA FUSKAR!!* ya danne wata salahar Fuskar da Mummunan *WATA FUSKAR!!* sa lallai tana cikin B'akin ciki, tasha ji yana fad'a cewan Duk sanda ya haifi Namiji ze bashi sunan mahaifinsa na ainahi wato Musa idan kuma Macece ze sanya mata sunan mahaifiyarsa wato *NANA KHADEEJAH* da wannan ta dauki jinjirar ta mata huduba da kanta tana sharar k'wallah lokaci d'aya kuma tana mata kiran sallah ta mata hudu ba da sunan Nana khadeeja....tausayi sosai ta baiwa Naja daya sanya ta kasa daurewa ta sanya kuka.
********************
Abubuwa sun soma yiwa Baba Azumi yawa sosai, ta soma neman sukunin ta ta rasa, bashi ya mata dabaibayi wanda taketa ci da sunan ummul zatazo amma shiru kakeji tamkar an shuka dusa kwanakin cen gwal d'inta ta eba ta siyar babu yanda ta iya akan zata rage bashi yanzu gashi marasa mutuncin mutane sun taso ta agaba, har yanzu a k'asan ranta ummul take jira ta tabbatar ummul tanacen abunta k'asar waje tana hutawa, bata raba d'aya biyu cikin ummul ya kusa zuwa duniya da wannan take ganin dole su dawo gida.....yau dai kam rana ta b'acewa Baba Azumi sabida tanaji tana kuma gani aka zo aka wuce da ita station akan bashi belinta an gagara karbowa sabida yayan ummul yace shiba ruwanshi yayita gargadin su akan hakan wata er sandar mace har duka ta tik'a mata tsabat haushin datake bata sabida had'e kai masu binta bashin sukayi suka kai k'ararta, taci azaba kan abada belinta, se fad'i takeyi suyi hakuri 'yarta ummjl tazo wai me kudi take aure dansunje yawon shan iskane turai amma dasunzo zata bada, wasu kam kallon mahaukaciya tuquru suke mata.
*****
Maheer ya dawo Niger ansha love shida islam se narkewa take wai ita adole me ciki, shi kuwa ko motsin kirki tayi seyaji a ranshi bayan zuwansa da one month suka juya zuwa London inda itama tunda jikinta yae kwari aka soma nemar mata gurbin karatu a turai din inda ta samu nasarar shiga level one a bangaren turancin data faro....dayake su cen abinsu akwai tsari sanda kayi joining college sannan semester ka ze fara....
Tir k'ashi!!!
Yau a parlor islam ce kwance tana narka shagwab'a tayi matashin kai da cinyar Maheer dayake biye mata ya sanya hannunsa yana wasa da sumar kanta dake a kwance, ita lallai yau chicken byte takeso, kuma anje siya sunce seda safe gashi 8 yayi, kiran Sophie yayi tazo tace gata
"Kin iya chicken byte ne?" Ya tambayeta kanshi tsaye kallon shi tayi ta dan saci kallon islam, a ranta tace wato matarnan tunda tazo muke cikin takura indai tana ganin yaa mahee durun uwa iri iri ko,
"Ea bazance ban iyaba amma muma Nancy ke mana, tafi kowa iyawa" jinjina kansa yae
"Jeki ki kiramun Hafsatun" juyawa tayi aranta tace so daya mukayi a gaban Nancyn Allah yasa ya kwab'e" tana zuwa ta turo ta, k'irjinta na dokawa ta iso parlor d'in tunda sukazo da islam batada sukuni, tarasa mesa takejinta a takure sannan kuma batason ganinsu kullum.manne da juna tarasa dalilin jin hakan, ada tasan taso maheer amma yanzu ta sani koda a k'afa zasu d'aura mata shi bazata jasa ba sabida sam ita bazata iyaba, tanada wasu dalilai data barwa kanta sani..
"Yaa Maheer sannu da gida"
"Yauwa sannu Hafsat, am chicken bytes zakiwa baby, shi takejin ci kuma near by shops dinnan babu wai seda safe suke ta cewa" wani k'ututun bak'in ciki ne ya tasowa Hafsat amma seta kanne tace
"E babu damuwa, munada kayan hadin barinje na hada mata" Bece komai ba ta juya tana had'awa tana mita harta kammala ta kawo, agabansu ta ajiye tana kallon islam da wasa irin na ftnds dinnan tace
"Maman biyu ga wannan karki cinyemu" murmushi islam tayi sannan cikin isa tace da ita
"Kekuwa ina d'an drink dazan had'a da? " miyarda dubanta tayi zuwaga maheer ta shagwab'e fuska
"Ni honey kace da ita ta had'amun ko smoothie ne dabashi da wuya nafison Banana smoothie yafi rik'e ciki" kallon mamaki hafsat ta mata shi kuwa Maheer yace
"Kinji me tace kije ki had'o kin wani tsayawa mutane akai" zuwa wannan lokacin seda tayi kuka a kitchen tana mamakin sauyawa halin qawarta.....
**********
A wannan daren Nancy ta kwana tana bak'in cikin faruwar wannan abin,tasani Maheer baya mata wulakanci shida sophie amma shauty da islam suna yawan kaita mak'ura aciki islam tafi bata mamaki, ita bazata fito ta mata wulakanci ba amma sedai tana mata abubuwan datake so taga sun k'ureta tayi wani abin daze ja mata raini!!! Mamakin wannan halin na islam na cikin damuwar ta......Bazatace Komai ba akan wannan abin tayi alkawari zata jure amma tasan wuyace zata shata ta hango wulakanci tsantsa acikin take taken da islam keyi tun zuwanta, ta dinga mata abubuwa tamkar wata 'yar aiki tana tunzurata zuwa bango, amma ba komai zata jure!!!
**********
Duk wani juyin da maheer zeyi tunanin Nancy ne danqal acikin kansa, yana cikin tsantsar damuwa mara adadi, yana kula sosai da yanayin islam da yanayin d'abi'un datake nunawa agaban na Nancy, bayaso ya mata magana ne tazo tana mar wani kallo na daban,yasan mata seya sanya wani abu aranta daze k'ara dagula zaman, yana hango yanayin Nancy da kuma b'acin ran datake shiga duk sanda ta mata irin wannan abun, ya kula ma tun dawowar da yae da islam Nancy walwalarta ta ragu sosai, ya kula kuma takan zauna skul ko bata komai har yamma sabida batason ganin abubuwan da islam keyi sam ya kula tana cikkn damuwa abun yana damunsa!!!
Mom Nua'iym ce
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
31
A hankali ya soma laluben inda ze qarajin kukan amma shiru be jiyo komai ba, yayi bincikensa sosai amma ba abinda ya gani a kitchen d'in juyawa yayi da zummar komawa d'akin har yakai k'ofar yajiyo k'arar jinjirai da k'arfin Gaske sekace wacce aka tsikara da sauri ya juyo ya kalli k'ofar store d'in kukan taci gaba dayi bil haq da iya kacin k'arfinta tamkar wacce ake ciza dukda yake kana ciwo sautin kukanne alamar bakin a toshe yake da wani abin, da sauri ya juya zuwa store ya soma binciken shi besha wahalar neman taba sabida kukan dataketa k'arayi da sauri ya zaro ta a kwalin yana huci ya kuma haska kwalin da fitilar wayarshi cinnakune a saman zanin datake kai sunkai biyar warwareta daga cikin d'ankwalin datake yayi nanma wani cinnakan ne alamar shi yake cizon ta, riqeta yayi ya soma sosa wurin a hankali yana shhhhhh alamar tayi shiru cikeda tausayawa a kafad'arsa ya d'aurata ya soma sosa mata bayan a hankali be koma d'akin ba yafi 15 mns yana sosa mata wurin a hankali hartayi bacci juyawa da ita yayi d'akin dayabar Ummul ya shiga a hankali, tana zaune tana kuka me ban tausayi....rungume yarinyar yayi ajikinsa yana mata murmushi me k'ayatarwa dabema san yana yiba sosai ya k'urawa yarinyar ido baya ko k'iftawa ba k'aramun kamanni takeyi da late mahaifiyar saba, har acikin baccin yamutsa fuska takeyi alamar tanajin zafin cizon da cinnaka ya mata, har cikin ranshi yakejin wani azababben rad'ad'i akan cizon da cinnaka ya manna wa 'yarsa....tunda yake a duniya be tab'a jin yana son wani abu ko mutum ko aljan sama dayanda yaji yanason wannan abar ta hannun shiba!!! Ko Ummul dayake so bata kai kwatankwacin san dayakewa wannan babyn ba, kallon ummul yayi yace
"Ki Nutsu kimun bayani niba abinda zan miki, yaushe kika haihu naga yarinyar tayi kwar'i sumar kanta kurin ya nuna hakan" d'ago jajayen idanuwanta tayi tace
"Watannin Nana khadeeja biyu kenan a duniya, bakwaini aka haifeta kamar yanda na fad'a maka, nafi sati ina b'oyonta akan ance kana raba iyaye da yaransu tunda take bata tab'a yin kuka ba idan na b'oyeta yau, na barwa Allah akan Nana nikam, tunda yake ubangiji ya bayyana maka ita cikin sauk'i shiyasan me yake nufi da Nana, ni bazance maka komai ba illa kurin kaji tsoron Allah mad'aukaki dukkanin abinda kakeyi yana kallonka" Wata iriyar zufa ce take tsatsafowa Ameenu babu wannan shirmen aranshi waishi ya mik'a 'yarshi shi kenan kuma idan ya bayar baze k'ara ganintaba har abada gashi Alhj Baba ya sanar masa ana kaisu wasu garuruwanne masu kud'in dabasa haihuwa ne ke siyan yara da tsadar dayaga suna siya suna adopting nasu, dukda an sanar masa basa shan wahala ko kad'an amma seyaji a ranshi ko Nawa za'a bashi akan Nana baze iya bada itaba gashi Har Alhj Baba ya gama cinikin kome aka haifa mace ko Namiji kallonta yayi
"Ummul Sunan Mamana kika baiwa wannan jinjirar? D'aga masa kanta tayi tace
"Wannan shine sunan danaji kace zaka sakawa yarinya idan macece shine nacika maka burin ka" nisawa yayi yace cikin takaici
"Da hannuna nake siyar da yarana ummul, bakuma siyar dasu nake dan komai ba sedan ina ganin ina tara uwar dukiya akansu, an sanar mun turawa ke siyan yaran musamman wanda basa haihuwa suna adopting d'insu suna basu gatan daya dace dasu.....yarana sunkai goma sha biyar dana zubar na bada kyauta wasu duk iyayensu aure mukayi wasu matan banza ne wasu hayarsu nakeyi, yanzu dakikace naji tsoron Allah wani tunani yazomun shin idan anje dasu qasashen turwa wane addini ake koyar dasu? Wa danne irin sunaye ake kiransu dashi shin anya zanga annabi kuwa, wani zubin idan akamun haihuwa banako kallon jinjirayrn nake badasu amma akan Nana Khadeeja bazan iyaba ummul, bazan kara siyar da yarana akan wannan abin duniyar ba inada dukiyar dazan rayu acikinta har abada inada gidajen mai iri iri inada kampanin silipas bazan iya qayyademiki adadin abubuwan dana mallaka ba, na dad'e ina tunain cewan had'uwana dake alkhairi ne na jima ina miki kallon ke alherice ashe hakan, Allah na tuba ka yafemun laifuffukana na baya"
Dubansa ya miyar zuwaga ummul kan yace
"Alhj Baba mutum ne me tsananin san abun duniya, shine ya d'aurani akan wannan mummunan turbar ta banza, yanzu nasan ze iyayin komai akan zan hanashi wannan jinjirar, koda yake dama bayason wanda suka sha nonon uwarsu bare ma wanan watanninta biyu" kallonshi tayi
"Sekace abun tsafi Ameen, anya kuwa wasu ke siyan yaran nan kodai tsafi ake dasu?" Kallonta yayi amma beyi magana ba yana nazarin kalamanta ne kurun secen yace
"Tunda nake mik'a jinjiraye ban tab'a sanin me akeyi dasuba face abinda na gaya miki Allah ne shaidana, amma kuma ummul maganar kin nan ta zomun da wani tunani, bana mantawa akwai wani yaronmu da yarinyarshi ta haihu da kwana biyu daya kawo jaririn mayar masa akayi akan yasha nonon uwar sa baida wani amfani....wani zubin nikanyi mamakin dalilin sato matan da ake masu tsohon ciki idan sun haihu a kaisu kan hanya a wurgar a dauke jinjirayen duk akan abu d'aya waishi neman duniya kuma bama wannan ba idan suna son jinjiraye babu a k'asarsune? Wlhy ummul nikan jima ina nazqrin abubuwan nan amma yaya zanyi da Alhaj Baba shine gatana banida kowa" shiru sukayi dukkansu suna kallon juna k'arar wayarshi ne ya miyar dasu duniyar dasuke a tare suka kalli screen na wayar *ALHJI BABA* shine rubuce ajikin fuskar wayar...miyarda duban su sukayi akan fuskokin juna bayan da kuran ya yanke lokaci d'aya zuciyoyin dukansu suna lugud'e!!! Murya na rawa yace
"Mesa Yake duk wanda ke qoqarin guduwa daganan gidan seyace baya ganin gabansa bare bayan sa, abubuwa da dama dasuka shafi nan gidan ban saniba ummul!!! Wannan tsafin da kika ambata ya rikirkitani koda kuma kinzo da waya ke naki baze shigaba amma ni zan samu wanda nakeso kuma zasu krani, anya babu zancrn ki kuwa anya babu tsafin to amma tayaya? Ni komai na Alhj Baba nasani ki taimakeni ummul ina cikin tsananin rud'u wlhy" shiru sukayi sanda kiran ya k'ara shigowa se gumi yake had'awa tamkar wanda ya had'iyi kunama"......
**************
Koda wasa Nancy bata zata Maheer zezo mata da wannan zancen ba!! Bata burin aurar sa, tunani ya mata waya wannan ya bata damar kiran Mahal ta tbayeshi gameda labarin soyayyar sa akan ta tada, yana amince mata tace yaje yawa Baba iro magana a shirya komai, indai ze aureta karatunta ma zata ajiye, dad'i ya kamashi yace da ita zema barta ta dawo kuma yamata alqawarin farin ciki na har abada.....
*Bayan sati d'aya*
Maheer yana kwance a parlor wayan Daddh ya shigo masa, d'agawa yayi yana murmushi suka gaisa yace dashi
"K'anwar ka tayi muji fa, malam iro ya kirani a waya yana neman izini kozan bada ita, nace duk yanda nace nikam nace a tsarina seta kammala karatunta amma zamu iya tsyar dashi matsayin manemin auren nata" gyaran zaman shi yayi sabida harya dawo zaune yace
"Abba wacce daga ciki?"
"Kanajin nace malam iro ai kasan Hafsat nake magana ko!!! " k'irjinsa me yayi wani irin mugun dokawa da tunda yake a ranshi be tab'a jin fad'uwar gaba irin wannan ba, lokaci d'aya ya tsarke ya soma tari sosai
"Sannu idan ya fad'a maka ka kirani nanda awanni uku zan shiga meeting yanzu.......
Tunda Maheer yake be tab'a shiga wannan tashin hankalin ba, ya jima bega tashin hankali ba irin wannan, se yanzu ya yarjewa kanshi yanawa Hafsat *son so* wanda be tab'a yiwa wani ko wataba yana cikin tashin hankali, yaya Hafsat zata masa haka?? Anya tayi masa adalci kuwa tasan me yakeji kuwa?...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
30
Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma sosai bazakace bakwaini bace, tayi kamar mahaifinta yamkar an tsaga kara, ita kuwa uwar se rama takeyi tamkar kud'in guzuri a tsorace take kwana sabida labarin dataji a bakin Naja akan kwace jarirai da ake a wurin iyayensu bata kuma san ina kaisu ba, shak'uwa me tsananin yawa ta shiga tsakaninta da Naja, taji labarin iyayenta aka dauka akan zaman dole takeyi anan kusan shrkaru biyar rabonta da gidansu, da iyayenta da dangi, tayita kokarin gusuwa amma ba hanya......
Hankalin Ummul baya jikinta EDD da aka bata kan azo da ita nan sauran shi sati biyu kacal, hakan yana nufin kenan zasu rabata Da NaNan ta zasu k'wace ta daga hannunta tosu kaita ina? In hakane tun yanzu ya dace ta keci jejin kota nemi dabarar yi sabida akwai matsala, ga mikin ta na haihuwa har yanzu da saura sabida rashin magani koda na hausa ne tana cikin tsananin damuwa me yawa ba er kad'an ba.
***************
A parlor su sophie ne ke zaune suna hirarsu har Nancy wani zubin zakaga suna raha gaba d'ayansu tamkar basa gallaza mata, yauma hakan ce en matan uku se hira suke suna shewa dukkansu acikin kayan bacci masu wando iya gwiwa da riga me gajeran hannu amma tanada tsayi har socks suka sanya sabida ana tab'a sanyi a garin babu me d'ankwali acikin su, ita nancy ma tsawon sumar kanta daya sauka har cen bayanta ta tattaro zuwa gefen kafad'arta ya sauka ta gaban qirjinta, tana sanye da madubi sabida matsala da idanta ke bata akan yawan duba takarda suna hiran tana dannan wayanta.....zuwa wannan lakacin ta zama 'yar gida sun gama sakin jiki da Maheer ta cire shi aranta babu abinda take mai kallo se yayanta uwa d'aya uba d'aya, gidansu ne anan suke zaman hira musamman idan yaa Maheer baya nan.....islam ce ta shigo tana yamutsa fuska su sophie suka kalleta atare suka hada banda Nancy
"Sannu anty kin fito" murmushi ta musu
"Nafito en uwa ya kuke?" Murmushi sukayi shauty tace
"Qalau muke anty" kallonta Nancy tayi da murmushi a fuskarta
"Isy baby how body" ta furta tana gyaran zaman madubin idanta, yamutsa fuska islam tayi
"Yadai kamata kisan banbancin da dakuma yanzu, matsayin yayarki nake inda kikazo agolanci fa yayan su nake aure, ai ya dace ki ajiye qawancen mu nada ki gayar dani yanda kikaji kowa yayi bawai ki kirani da sunan raini ba tsabar izgili, amma bari yayan yazo zance ya miki magana ki san yanda zakimun magana, kina b'atamun rai gako Dr. Yace adena b'ata raina" sophie ma yau taji haushin wannan wulaqancin da islam kewa Nancy ita kuwa Nancy batace komai ba ta tattare yanata yanata tayi hanyar d'aki,tsaki ta bita dashi ta zauna wurin data tashi, ta tabbatar maganar da Anty Nasara ta fad'a Gaskia ne, wato dai Nancy ta manta halacci auren mijinta takeso tayi ko, itako kozatayi yawo tsirara bazata tab'a bari mijinta ya auti vergine ba gwara ya auro magajiyar karuwai, ko Umma ta gano bata santa arayuwa duk sunfison Nancy da ita tunda suke shirin auramai ita dabadan anty Nasara ba dabazama tasan miyan da ake yiba, amma ba komai wuya zata sanya ta gudu da k'afanta tabar gidan!!!
Suma duksu sophie se suka bi bayan Nancy, a d'akinta suka sameta sophie tace
"Mesa wai ke adinga miki abu bazaki yi magana ba, me anty islam ke nufi dake zata rik'a kiranki agolar, ko agolancin kike aiba gidan ubanta bane itama" Murmushi tayi tace tana kallon sophir
"Ku manta da ita sophir duniya taga ta samu shiyasa, a turan nan Allah sa yaa Mahii ya samu wata matar ya aura" ta qarashe maganar tana dariyar mugunta , sha'awa d'aka mata duka tayi a cinya
"Ke Banza ce wlhy, duk abinda ta miki ke dariya ma kike, ni wlhy duk abinda na miki ada sharrin shedan ne dakuma zuga kiyi hak'uri na fahimci kinada hak'uri da girmama mutane, uwa uba gashi kina koya mana karatun Allah harma mun gayawa Umma wlhy kuma tana jin dadi, mukace dama kece matar wancen se ikon tsiya" Tana murmushin ta tace..
"To meye duniyar shauty? Duk idan ka kwantar da hankalinka dudu kwana nawa ya rage maka a duniyar? Ko yanzu seka iya mutuwa wlhy ku barta duniyar ce akanta ita har yanzu ni bazan tab'a kulata ba wlhy" haka duka zauna sunata mita haushin Islam fal aransu basuda labarin Anty Nasara ce ta ingizota take wannan izgilancin takuma tabbatar mata su Abba sunce ita zasu aurawa Maheer.......
****************
Mahal se yanzu ya gano yanason Nancy da kanshi yaje gun Baba iro ya karb'o lambar wayarta, Yau ma kamar kullum aikin ne da aka saba sakata na wahala takewa islam wai kunu zatasha dama an aiko garin kunu daga gida sabida tanaso, tana kawowa ta ajiye akan centre table islam ta soma rigima
"Ni Honey nace kadena sanya Hafsat tanamun abu,bansan meya shiga tsakaninmu ba ta tsaneni yanzu sabida Allah kunu haka da ruwa yaushe ze riqen ciki gashi taga bana iya cin komai" kallonta Maheer yayi ya sani neman fitinane kurin
"Adama me kaurin ne?" D'auke kanta tayi
"Nafasa shan kunun abari kawai na kwana da yunwar" tasani baze lamunci barin ta da yunwa ba yanda yake tattalin cikin nan tamkar ranshi,tallafota yayi
"Noo Baby karmuyi haka dake plss, ki bari yanzu taje ta dama me kaurin sekisha kinji" yamutsa fuska tayi
"Nise naji dama ace peppersoup ne na kaza danasha romon inci naman"
"To yanzu ayi peppersoup d'in?" Gyad'a masa kanta tayi, akwai house girl agidan har biyu ita ya kwallawa kira har yanzu nancy tana a tsaye , wayanta ne ya soma ringing bata san Number ba, juyawa tayi tana daukar kiran
"Yaa Mahal dama kana nan? Lallai ma ai nayi maka fushi wlhy" shine kalmomin daya miyar da duban Maheer zuwaga Nancy k'irjinsa yana dokawa
"Ba waninan yaa Mahal wlhy Allah nayi fushi, amma ina abu yanzu barin gama zan kiraka" Bata k'ara kallon subama tawuce d'akin su sophie yanzu kamma har zama d'akinta ta dena yi sesu kwana a tare suna zuba shagalin su tama rage damuwarta akan Islam takula batada hankali.
***************
Bayan sati biyu
Yauce ranar cikan EDD na Ummul kuma yarinyarta ta cika watanninta biyu a duniya tayi kyau abinta tayi qiba ta murje sedai abin tausayi bata da ko rigar sakawa a duniya ko pant batada sabida ba'a tanada ba, kullum acini. D'ankwalin ummul take har ciwon mura tayi sosai amma babu maganin bata da taimkon Allab taji sauk'i tunda aka soma tab'a k'ofar shigowa gida suke a rud'e da kanta taje ta neki kwali ta shinfid'a d'an kwalaye aciki takuma saka Nana ta sanya wani kyalle tanaji dana gani ta d'aure bakin 'yarta ta d'auki kwalin ta sanyashi ackkin store dake gidan na kayana abinci cen bayan buhun hunan shin kafa, kullum haka sukewa jinjirar har yau Allah yasa yazo ita ta bud'e masa k'ofar gidan tana ganin shine ta fad'a jikinsa tana ta kuka,dama haka suka shirya.
"Yaa Ameen wani laifin namaka ne? Menamaka a rayuwa? Ka gudu kabarni anan dabansan ko ina bane, na rasa inda zan dosa arayuwa, har k'addara ta sameni bakazoba yaa Ameen" d'agota yayi ya kalleta daga samanta har k'asan ya yamutsa fuska "me kike nufi? Ina kika kaimun yaron cikinki...kuka ta k'ara fashewa dashi
" ka zauna zan maka bayanin komai, mana da waccen muguwar abinda tamun datana kulani daban shiga tashin hankali irin wannan ba yaa Ameen" Lokaci guda ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, ya zauna yana kallon ta tace
"Bayan daka tafi ka barni anan bako sallama ya Ameen, ranar da dare kasan ciki da kwadayi na tashi ina neman yoghurt babu agidan nan ga wannan Najar batako kulawa dani yanda kace.....shine fa na fad'i a kitchen lokacin cikina watanninsa bakwai kacal*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
30
Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma sosai bazakace bakwaini bace, tayi kamar mahaifinta yamkar an tsaga kara, ita kuwa uwar se rama takeyi tamkar kud'in guzuri a tsorace take kwana sabida labarin dataji a bakin Naja akan kwace jarirai da ake a wurin iyayensu bata kuma san ina kaisu ba, shak'uwa me tsananin yawa ta shiga tsakaninta da Naja, taji labarin iyayenta aka dauka akan zaman dole takeyi anan kusan shrkaru biyar rabonta da gidansu, da iyayenta da dangi, tayita kokarin gusuwa amma ba hanya......
Hankalin Ummul baya jikinta EDD da aka bata kan azo da ita nan sauran shi sati biyu kacal, hakan yana nufin kenan zasu rabata Da NaNan ta zasu k'wace ta daga hannunta tosu kaita ina? In hakane tun yanzu ya dace ta keci jejin kota nemi dabarar yi sabida akwai matsala, ga mikin ta na haihuwa har yanzu da saura sabida rashin magani koda na hausa ne tana cikin tsananin damuwa me yawa ba er kad'an ba.
***************
A parlor su sophie ne ke zaune suna hirarsu har Nancy wani zubin zakaga suna raha gaba d'ayansu tamkar basa gallaza mata, yauma hakan ce en matan uku se hira suke suna shewa dukkansu acikin kayan bacci masu wando iya gwiwa da riga me gajeran hannu amma tanada tsayi har socks suka sanya sabida ana tab'a sanyi a garin babu me d'ankwali acikin su, ita nancy ma tsawon sumar kanta daya sauka har cen bayanta ta tattaro zuwa gefen kafad'arta ya sauka ta gaban qirjinta, tana sanye da madubi sabida matsala da idanta ke bata akan yawan duba takarda suna hiran tana dannan wayanta.....zuwa wannan lakacin ta zama 'yar gida sun gama sakin jiki da Maheer ta cire shi aranta babu abinda take mai kallo se yayanta uwa d'aya uba d'aya, gidansu ne anan suke zaman hira musamman idan yaa Maheer baya nan.....islam ce ta shigo tana yamutsa fuska su sophie suka kalleta atare suka hada banda Nancy
"Sannu anty kin fito" murmushi ta musu
"Nafito en uwa ya kuke?" Murmushi sukayi shauty tace
"Qalau muke anty" kallonta Nancy tayi da murmushi a fuskarta
"Isy baby how body" ta furta tana gyaran zaman madubin idanta, yamutsa fuska islam tayi
"Yadai kamata kisan banbancin da dakuma yanzu, matsayin yayarki nake inda kikazo agolanci fa yayan su nake aure, ai ya dace ki ajiye qawancen mu nada ki gayar dani yanda kikaji kowa yayi bawai ki kirani da sunan raini ba tsabar izgili, amma bari yayan yazo zance ya miki magana ki san yanda zakimun magana, kina b'atamun rai gako Dr. Yace adena b'ata raina" sophie ma yau taji haushin wannan wulaqancin da islam kewa Nancy ita kuwa Nancy batace komai ba ta tattare yanata yanata tayi hanyar d'aki,tsaki ta bita dashi ta zauna wurin data tashi, ta tabbatar maganar da Anty Nasara ta fad'a Gaskia ne, wato dai Nancy ta manta halacci auren mijinta takeso tayi ko, itako kozatayi yawo tsirara bazata tab'a bari mijinta ya auti vergine ba gwara ya auro magajiyar karuwai, ko Umma ta gano bata santa arayuwa duk sunfison Nancy da ita tunda suke shirin auramai ita dabadan anty Nasara ba dabazama tasan miyan da ake yiba, amma ba komai wuya zata sanya ta gudu da k'afanta tabar gidan!!!
Suma duksu sophie se suka bi bayan Nancy, a d'akinta suka sameta sophie tace
"Mesa wai ke adinga miki abu bazaki yi magana ba, me anty islam ke nufi dake zata rik'a kiranki agolar, ko agolancin kike aiba gidan ubanta bane itama" Murmushi tayi tace tana kallon sophir
"Ku manta da ita sophir duniya taga ta samu shiyasa, a turan nan Allah sa yaa Mahii ya samu wata matar ya aura" ta qarashe maganar tana dariyar mugunta , sha'awa d'aka mata duka tayi a cinya
"Ke Banza ce wlhy, duk abinda ta miki ke dariya ma kike, ni wlhy duk abinda na miki ada sharrin shedan ne dakuma zuga kiyi hak'uri na fahimci kinada hak'uri da girmama mutane, uwa uba gashi kina koya mana karatun Allah harma mun gayawa Umma wlhy kuma tana jin dadi, mukace dama kece matar wancen se ikon tsiya" Tana murmushin ta tace..
"To meye duniyar shauty? Duk idan ka kwantar da hankalinka dudu kwana nawa ya rage maka a duniyar? Ko yanzu seka iya mutuwa wlhy ku barta duniyar ce akanta ita har yanzu ni bazan tab'a kulata ba wlhy" haka duka zauna sunata mita haushin Islam fal aransu basuda labarin Anty Nasara ce ta ingizota take wannan izgilancin takuma tabbatar mata su Abba sunce ita zasu aurawa Maheer.......
****************
Mahal se yanzu ya gano yanason Nancy da kanshi yaje gun Baba iro ya karb'o lambar wayarta, Yau ma kamar kullum aikin ne da aka saba sakata na wahala takewa islam wai kunu zatasha dama an aiko garin kunu daga gida sabida tanaso, tana kawowa ta ajiye akan centre table islam ta soma rigima
"Ni Honey nace kadena sanya Hafsat tanamun abu,bansan meya shiga tsakaninmu ba ta tsaneni yanzu sabida Allah kunu haka da ruwa yaushe ze riqen ciki gashi taga bana iya cin komai" kallonta Maheer yayi ya sani neman fitinane kurin
"Adama me kaurin ne?" D'auke kanta tayi
"Nafasa shan kunun abari kawai na kwana da yunwar" tasani baze lamunci barin ta da yunwa ba yanda yake tattalin cikin nan tamkar ranshi,tallafota yayi
"Noo Baby karmuyi haka dake plss, ki bari yanzu taje ta dama me kaurin sekisha kinji" yamutsa fuska tayi
"Nise naji dama ace peppersoup ne na kaza danasha romon inci naman"
"To yanzu ayi peppersoup d'in?" Gyad'a masa kanta tayi, akwai house girl agidan har biyu ita ya kwallawa kira har yanzu nancy tana a tsaye , wayanta ne ya soma ringing bata san Number ba, juyawa tayi tana daukar kiran
"Yaa Mahal dama kana nan? Lallai ma ai nayi maka fushi wlhy" shine kalmomin daya miyar da duban Maheer zuwaga Nancy k'irjinsa yana dokawa
"Ba waninan yaa Mahal wlhy Allah nayi fushi, amma ina abu yanzu barin gama zan kiraka" Bata k'ara kallon subama tawuce d'akin su sophie yanzu kamma har zama d'akinta ta dena yi sesu kwana a tare suna zuba shagalin su tama rage damuwarta akan Islam takula batada hankali.
***************
Bayan sati biyu
Yauce ranar cikan EDD na Ummul kuma yarinyarta ta cika watanninta biyu a duniya tayi kyau abinta tayi qiba ta murje sedai abin tausayi bata da ko rigar sakawa a duniya ko pant batada sabida ba'a tanada ba, kullum acini. D'ankwalin ummul take har ciwon mura tayi sosai amma babu maganin bata da taimkon Allab taji sauk'i tunda aka soma tab'a k'ofar shigowa gida suke a rud'e da kanta taje ta neki kwali ta shinfid'a d'an kwalaye aciki takuma saka Nana ta sanya wani kyalle tanaji dana gani ta d'aure bakin 'yarta ta d'auki kwalin ta sanyashi ackkin store dake gidan na kayana abinci cen bayan buhun hunan shin kafa, kullum haka sukewa jinjirar har yau Allah yasa yazo ita ta bud'e masa k'ofar gidan tana ganin shine ta fad'a jikinsa tana ta kuka,dama haka suka shirya.
"Yaa Ameen wani laifin namaka ne? Menamaka a rayuwa? Ka gudu kabarni anan dabansan ko ina bane, na rasa inda zan dosa arayuwa, har k'addara ta sameni bakazoba yaa Ameen" d'agota yayi ya kalleta daga samanta har k'asan ya yamutsa fuska "me kike nufi? Ina kika kaimun yaron cikinki...kuka ta k'ara fashewa dashi
" ka zauna zan maka bayanin komai, mana da waccen muguwar abinda tamun datana kulani daban shiga tashin hankali irin wannan ba yaa Ameen" Lokaci guda ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, ya zauna yana kallon ta tace
"Bayan daka tafi ka barni anan bako sallama ya Ameen, ranar da dare kasan ciki da kwadayi na tashi ina neman yoghurt babu agidan nan ga wannan Najar batako kulawa dani yanda kace.....shine fa na fad'i a kitchen lokacin cikina watanninsa bakwai kacal, shiru tayi yana kuka yace cikin tsawa
" ina jinki mana kinyi wani shiru seme dan cikinki wata bakwai" tana sharar k'wallah tace
"To shine sena soma nakuda me tsanani nikadai a d'akin sedaga baya tazo koda tazo yaro ya gama wahala, ana haifarshi ya mutu, neman duniya na maka har gidan naso in bari amma banga hanyaba, haka muka hak'a rami muka binne gawar yaron yanzu kusan watanni biyu kenan" wata iriyar shak'a ya kai mata ya cafko wuyan rigarta seda ta yage ma, idanshi duk yayi waje yace
"K'arya kikeyi wlhy sekin fitomun da cikin jikinki, watak'ila ma yanzu kika haihi muje in gani" yajata giri riri zuwa d'aki se rantse rantse take akan wlhy bakwainin ta haifa!!!
***********
Mahal da Nancy kam kullum suna maqale a waya kowama ya fahimci hakan har su sophie ke tsokanar ta akan NaHal 2k19, bata kulasu dai ita kurin yana d'ebe mata kewar er uwarta ne yasa take kulashi ma, kuma dai ina laifin me sanka...
Yauma kamar kullum zaune take a saman matattalar benen dake cikin sabon gidan dasuka koma a london din, tana wayarta da Mahal se raha suke abinsu, Maherr dake bayanta yana sauraren wayar dasuke lokaci daya ta bashi takaici me tsanani, ya kalleta tana zaune tana wasa da sumar kanta tamkar ya rufeta da duka yakeji, yayi tsammanin daya sakko ta ganshi ta dena wayan amma ko gezau batayi ba, ta kurin ce
"Sannu da fitowa yaa mahii" ko kallonta beyi ba, dama ace tasan yanda yakejin sonta a ranshi data masa adalci, da ace tasan yanda take da matsayi a zuciyarsa data rufawa kanta asiri ta dena sauraran kowa, dama ace tasan bashida niyyan yafewa waninsa ita data dena baiwa kanta wahalar sauraran wasun shi..... Harya wuce ya dawo yace
"Ke ajiye wayar ki sameni garden yanzu" Mik'ewa kurin tayi taje ta sanya hijab har lokacin tanakan wayar seda ta kusa isa garden d'in sannan ta ajiye wayan...sosai ya kalleta kallo me tattare da tarin ma'anoni yace cikeda kasala
"Menene tsakaninki da Mahal ne, kullum kuna maqale a waya" murmushi tayi
"Bafa komai yaa mahee wlhy, kurin dai muna gaisawane he's just a friend nothing more nothing less" Shiru yayi kafin yace
"Hafsat inason ki, so nakeyi in aureki kuma ba wasa nake ba da gaske nake, har raina ina k'aunar ki sosai, ina miki son so daban tab'a yiwa wata 'ya mace a duniya ba, dan Allah ki amince dani ki aureni" wani kallon tuhuma ta bishi dashi bata tab'a kawowa zezo da wannan haukan ba, kowace k'addarar zata had'ata kishi da Islam oho? Har abada bazata tab'a aurar Maheer ba har duniya ta ninke kuwa, ko da ta kula ba wani so aranta se zallan burgeta da yanayinshi keyi yanzu kuwa kallon yaya kurun take masa,sewani haushi dayake bata yanda islam ta mayar dashi wani soko agabnshi take cin zarafinta, batace dashi komai ba ta wuce ciki da gudu batada amsar bashi ita kam....
*************
Har sunkai ciki ya dawo yana k'wallawa naja kira anan yajiyo kamar kukan jarirai kallonshi ya miyar daidai kofar kitchen din inda yakeda yaqinin nan ne yaji kukan juya akalar tafiyarshi yayi zuwa cikin kitchen d'in.....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
32
Gumice ke tsatsafowa su ummul tako ina, yasan halin Alhj Baba yasan meze iya akan wannan jinjirar yasani zega laifin sane amma bari ya gwada d'aukar wayar tasa,jikinsa ba k'wari ya d'auki wayar ya danna lambar ya kara a kunne
"BAKA KUSA DA WAYAR NE?" aka buk'aci sani daga d'ayan bangaren....
"Ea Baba bana kusa nashiga bayi gudawa nake tunda nazo gidan, akwai matsala fa Baba" Gyaran zaman hular kansa yayi
"Mecece damuwar?" Ya tambaya cikin isa
"Baba wai bakwaini ta haifa ashe tun bayan watanni biyu, kaga kuma ni banzoba gashi yarinya har tayi k'wari a hannunta" Tsaki yaja kan yace
"Wannan wane irin mugun sakarcine? Bakwaini kuma? kana da labarin cewan na karbi fiyeda rabin kudin wannan jinjiran kuma ka sani ni bana asara sedai idan kai zakayi, kuma a kawomun Uwar zan had'ata da shap shooter ya mata wani cikin shap shap ta haihu a ta maye mana gurbin asarar mu sannan kuma ita jinjirar yaya zakayi da ita? Karka zomun da ita nan kaji na gaya maka wlhy" Muryanshi na rawa yace ze kawotan, kallon Ummul yayi Baze tab'a iya bari wani namiji ya rab'i matar saba, wato shikenan Alhj Baba sabida ya renesa seya hanashi walwala yana nufin iyalansa ma baze bari suyi k'wai ba? Mik'ewa yayi yace
"Tashi muje Ummul tashi mubar gidan nan akwai matsala, bazan k'ara cutar miki da rayuwarki ba, bazan yarda wani ya rab'eki da sunan zinaba wai dan ze miki wani cikin, gwandamun in mutu da inganki a wannan halin Alhj Baba bashida imani ko kad'an" koda Bata fahimci kala mansa ba amma ta gano da matsala Naja ma agaba suka sanyata sunsha mamakin gate a wangale suka fad'a motar kuma acikin qalilan lokaci dabefi 50 mns ba suka hau titi da kyau, suna shiga gari Mamaki ya kama ummul ganin ko wane sighn boad zata gani setaga an rubuta masa jos nigeria wato jos ma suke kenan? Lallai ma Ameen namiji munafuki, kai tsaye kano suma nufa acen ya nemi gidan ajiyesu wanda Alhj Baba bemasan yana dashi a kano ba....
Bashida wani wanda ze gayawa damuwarsa amma mutumin farko daya fad'o masa shine Maheer....sun kwana biyu basuyi wayaba kasancewar ya dena amfani da layin da Maheer ya sanshi dashi, lalubar layin yayi ya saka shi ya dannawa Number d'in Maheer kira, yana ganin tak'i shiga ya gano yana london wata iriyar zufa ce ta keto masa, lalubar lambar maheer ta london yayi yae sa'a kuwa ya samu, a wannan lokacin Maheer yana cikin tsananin damuwa akan Nancy, koda yaga Ameen ne yayi mamaki, yafi watanni yana kiram wayansa baya tafiya sam!! Da sallamar sa ya d'aga kiran suka gaisa yace dashi
"Kwana biyu Ameenu bana samun wayarka yaya wurin su ummul hope dai lapiya?" Susa kanshi yayi cikeda jin nauyi kan yace
"Abubuwa da dama sun faru abokina, dogon labari ne dabazan iya bakashi ba yanzu, naso ace kana gari ne mu hadu gani gaka amma yanzu yaushe zaka dawo?"
"Eeeh to akwai abinda zanzo yi Nigeria nanda 3 weeks idan beyi nisa ba, semu hadu daga na dawo idan Allah yasa muna cikin masu numfashi a lokacin" Nisawa yayi
"Babu damuwa Maheer amma dai ka sani ina tsananin buk'atarka a yanxu hakan, idan da hali karka wuce sati ukun da kace, bayan wannan idan akwai gidan dakakeda shi a nan kano ina son aron key zanje da ummul gidan akwai damuwa fa" Shiru kan yace
"Akwai gidaje ma abokina, zanwa kamala waya seka nemeshi ko, naga kaman hakan yafi kaima zan bashi wayarka"
"E hakan ma yayi amma dai a bani motoci guda biyu suma, zan bashi tawa ya ajiyeta a gidan ku kan ka dawo" Maheer be wani tsaurara tambayoyi ba, ya kawai masa fatan Alkhairi....har zasuyi sallama yace
"Kanada labarin en uwan ummul kuwa?" Yana murmushi yace
"Ea ai yanzu haka Hafsat tana hannun mu, mun sakata skul anan london, tana yawan damuna akan zancen ummul"
"Ka gaya mata ummul tana nan cikin k'oshin lapiya harta haifa mata 'ya sunan ta Nana khadeeja amma ina kiranta da suna mamina" murna ya masa kan nan sukayi sallama......
*************
Yau dai Islam tana school wannan ne ya baiwa Nancy damar fitowa parlor domin yin kallo sabida da a farko sam sam tadena fitowa sabida wulaqancin da ake mata, wayanta take daddanawa tana chat da Mahal lokaci zuwa lokaci takan saki murmushi zuwa wannan lokacin zuciyarta ta soma shiryawa da Mahal ta aminta dashi matuk'a....Maheer se kallon yanayinta yake wani irin burgeshi takeyi aduk takun dazata yi a wurin shi....zama yayi kusa da ita ta mik'e zaune daga kishin giden da take
"Sannu yaa Maheer barka da zuwa" wani irin zuba mata manya manyan idanuwanshi yayi baya ko k'iftawa,ita d'inma shi take kallo basako k'iftawa acikin idansa ta hango k'auna zallah tata, ta hango son fiye da kai, ta hango tausayinta, ta hango d'igon k'aunar ta a had'e da wata zaiba dake cikin k'wayar idansa!! Ta hango Son so acikin idansa, fuskarsa ta bayyanar da yanayin yanda yake matuk'ar k'aunarta ya marairace mata fuskarsa me kyau har hakan yana shirin yin tasiri azuciyar ta kawar da idanta tayi daga dubansa tana yunk'urin mik'ewa ya rik'e hannunta gagam juyowa tayi suka k'ara yin ido biyu dashi ga mamakinta k'walla ta gani a idanshi har yana shirin sauka, lokaci d'aya ta jirkito gaba d'aya zuwaga dubansa tana me wara idanta......."Bakada lapiya ne yaa Maheer na shiga uku na" muryanshi har rwa yake yace
"Kece hafsat, dan Allah ki tausayamun wlhy bazan rayuba idan baki a tawa rayuwar....macewa zanyi matuk'ar kikace zakimun hakan, Naji hukuncin dakika yanke dukdan k'iyayyar dakikemun, na yarda da kiyita k'ina amma ki rayu dani ki taimaki maraicina ki aureni kinji" Kallon ta ta miyar jikin k'ofa ta warce hannunta daga nasa tace
"Yaa Maeer kayi hak'uri wlhy bazan iya aurar kaba har abada!! Banason koda rab'ar ka inayi da inada wani iko da nabar muku nan gidan kaida islam d'inka!!! Da inada ikon dena sanyaku biyun nan a ido dana dena, ina rok'on ka yanda kaga nabarka kaima ka barni, ka cireni a ranka kaje cen ku qarata kaida islam, wlhy yaa Maheer Baso a raina, in dai aure ka, ina maka kallon Babban yayana me girman daraja da k'ima ina sonka fiyeda tunanin me tunani a bangaren zamtowarka yaya na, acikin jinina kake yawo yanda kasan dan uwa nayi acikin jinin d'an uwansa, a numfashina kaine nake ja nake fesarwa amma na matsayinka na yaya na, a idonane kurun kake kala biyu wanda hakan bazema maka wani tasiri ba ko kadan!!!! Ka fitar dani a ranta kamun kallon danake maka dan bazan aureka ba".... Tana kammala fad'ar hakan ta mike
" ummul ta haifi Nana khadeeja inji Ameenu daya mun waya d'azu" da sauri ta dawo ya mata bayanin komai sannan suka rabu zuciyoyin su babu dadi sam...
**************
*Bayan sati biyu*
Shirin tafiya America yake gun mahaifinsa ze had'ashi da wasu muhimman abubuwa nasa tukunna su wuce Nigeria tare zancen auren Hafsat...tamkar me wani mugun ciwo haka Maheer ya dawo duk ya yamutse sosai kuma.....yana dira tun a airport Abba ya diririce ganin Maheer a rud'e ya yamutse a daddafe sukayi kwana biyar suka juya Nigeria.....kai tsaye gidan su Hafsat suka dira akan maganar auren kai tsaye Maheer agaban Abban shi ya yanki tikitin rashin kunyar shigar da Buk'atarsa tason auren hafsa....mahaifinsa ya nuna rashin dacewar neman aure cikin aure, amma Baba iro ya zak'alk'ale yace sam dama be baiwa Mahal Hafsat Ba be kuma ce dasu komai ba illa su bari se marik'anta sunzo yanzu kuwa tunda sunzo zece dasu sun baiwa wani, Babu yanda Abba beso a nemi izinin yarinyar a tuntub'eta aji ra'ayin taba, tunda ita ta kawo wannan tace tanaso amma k'ememe Baba iro harda kukan munafurci daga k'arshe ma kafewa yayi akan lallai a d'aura auren su yanzu tunda ba wani abin bane kar wata maganar ta k'ara tasowa..... Da Abba da umma ma'auratane masu tsananin girmama junansu...komai zasuyi sesun nemi sha'awar juna anan take y koma mota ya mata waya akan abin da ke wakana, amma ita seta Rok'a akan abari se juma'a idan an sakko masallaci tunda yake yau laraba, haka suka bashi hakuri suka koma kano..... Sosai Abban Maheer suka rok'eshi akan ya janye amma ya kafe su a ganinsu baze iya da mata biyu ba musamman kasancewar su k'awaye kuma duka yara shidai ya kafe kuma ya hana a kira Hafsat akan bazata amintaba sabida kawaicin islam.....mahaifinsa ya kafe akan lallai seya kirata a k'alla ta sani mahaifiyarshi batason d'anta ya gagara samun me yakeso amma ina seda Abba ya kira hafsat, cikin girmamawa suka gaisa yace
"Hafsat dama na kirane in shaida miki ranar juma'a zan d'aura aurenki da yayanki Maheer, kasancewar hakanne daidai ina fatan a matsayina na uba zakimun biyayya" Batare datasan me tace ba ta amsa da
"Duk hukuncin daka yanke akaina daidai ne abba, fatana zab'in iyaye ya zamto Alkhairi agareni" sosai ya saka mata albarka ya k'ara dacewar
"Banason koda su safiyya su sani ko bayan daurin auren se sanda zan baku umarni, sabida haka aci gaba da zama matsayin da ake kai amma aure zan daura idan inacikin masu numfashi jibi juma'a" Tana k'wallah tace
"Inshaa Allahu Abba zan kiyaye nagode Allah ya k'ara girma" yaji dad'in adu'arta ya dinga mata godiya seda taji nauyin sama!!!!!!
Sake wayarta tayi ta zube a wurin tana sharb'ar uban kakan kuka, wlhy batason auren Maheer, mutumin dayafi son islam akan kansa ma agabansa islam din ke mata cin kashi bazeyi magana, ashe ko yanzu seta duka, wato yayi tafiyane sabida yasan iyayenta sunada kwadayi yayi amfani da kargin ikon dukiyarsa ya tursasa aka bashi ita ko, bayan ga zabin ta...koda ta kira Baba irk tasha zagi sosai bana wasa ba .....yace er b'akin cikice bataso yaci gaba kuma idan ta kuskura tace batason auren Allah ya isa kuma Allah ya tsine mata albarka....badan tasoba ta hakura ta kira maman ta itama kai tsaye ta goyi bayan su baba iro kuka kam ta shashi....
*Ranar juma'a*
A babban masallacin juma'a dake jihar sokoto aka d'aura auren Maheer da Hafsat bayan idarda sallan juma'a Bazamu iya fad'ar d'umbin al'ummar dasuka shaida auren ba.....
Tun bayan da aka d'aura auren yake cikin fad'uwar gaba, ya hango iyakar gaskiyar Nancy na bazata auresaba kamar yanda ta fad'a!!!!! Ya gagara kiranta, ga farin ciki a qasan ranshi ga kuma tashin hankali a ckin ran nasa, ko yaya zata kallesa? .......Hafsat kuwa tasha kuka su sophie sunyi sunyi sedai tace dasu zazzab'i takeji suka dinga mata sannu....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
33
Alhj Baba ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, neman Ameenu yake hankalinsa a tashe, duk garuruwan dayake tsammanin ganinsa yaje amma ba labarin sa....a gaba ya sanya Babban yaron Ameenu da izgilanchi iri iri dakuma treatening nashi akan hallakar da iyayen sa...dolensa yakaishi gidan Ameenu na kano inda suka tarar baya nan, tsammanin Alhaj Baba zuwa yanzu shine Ameen yabar k'asar kwata kwata don haka ya kud'irta aranshi idan ma ya kamashi har 'yar tashi ze yanka agabanshi besan haka bane dabe nuna masa ze karbi matar tasaba, kuma matarsa seya wulak'antata ya sanya dukkanin samarin dake masa aiki sun hauta agabansa, duk gatan daya masa ya d'aurasa akan hanyar samun kud'i zema iya cewa gabaki d'aya yafishi samun kud'in gefen wannan harkar yaya ze masa haka?! Duk wani hanyar daze sanya ya ganeshi ya gujeta danko ko kud'ad'e ya dena cirewa ta banking sa to a ina ze samu kud'i? Hankalin Alhj Baba fa ba karamun tashi yayi ba......
*******************
Ameenu kuwa dabara ya masa, sabida yasan yanda sun tab'a samun yaron dayak'i bada yarinyar sa da matarsa ta hanyar inda yacire kud'ad'e banki ya gano shi, wannan ya sanya yawa abokin shi dasuke huld'ar fata waya wanda dama akwai kud'insa a hannunsa ya tura masa 3 million d'insa acikin acc d'in Ummul dako ATM nata batasan inda yake ba seda yasha wahala ma tukunna ya samu aka mata ATM d'in yake zarar kud'ad'en suna lalurarsu har yanka yawa Nana khadeejah aketa ji da iya, ankuma kaisu asibiti itada uwarta an duba lafiyar su da komai Alhamdulillah.....
***************
Tun faruwar wannan lamarin Nancy bata cikin nutsuwar ta, ta rasa dalilinta najin hakan game da Maheer, bazatace ta tsaneshi ba amma sam batajin sansa aranta kamar da, kodan tana jin tsananin takaicin islam ne yasa ko meye dalilin ta oho? Tasani ada ta bautawa san Maheer takuma sha d'awainiyar begenshi amma zuwa yanzu tunani take kaman zallan burgewa ne kawai baso a ranta, ta misibar shak'a da wannan izgilancin daya mata, shime dala kenan ko? Masu kud'i kenan ko? An had'u da kwad'ayayyun iyayenta anje basu abun duniya sun bada aurenta batare da izinin taba sam! Bata masan anayiba, banda Abba ma daya nemi amincewarta Baba iro ko gaya mata beyi ba sanda ta kirashi ma seya nemi tsinemata akan hakk'inta....haka mamanta ma data kirata seta ce ta amince mesa basu ko duba kawaici ba? Kodan islam ai sace noo ko? Wannan auren ta kudiri niyyan wahalar da Maheer akanshi kuma ze ganene.....
***************
Sosai suka zanta da Ameenu gameda abubuwan dayake aikatawa da wanda ke gudana a yanzu, Ran Maheer ya b'aci da shashamcin Ameen....ze dinga rayuwa kenan acikin tsoro da b'oyo se kace d'an fashi, sun jima suna meman mafita, basuda dabarar dayafi ya kwashe 'en kud'ad'ensa ya koma wata k'asar xuwa wani lokaci shida iyalansa wannan kuwa ze d'auki lokaci dan haka gwara su zauna da shiri....Ameenu ya sanya kamala harkan visa dinsu da komai daya shafi barin k'asar.
**************
London
Koda Jirgin su maheer ya dira a london seda k'irjin sa ya doka yana tunanin yanda ze kalli Hafsat, yana tunanin abubuwa da yawa masu dama....haka ya isa gidan jikin sa ba k'wari ko kad'an da sallamar sa ya shiga cikin parlor d'in inda ya tarar sophie ce zaune tare da Nancy suna kallo sunashan Banana smoothie...a tare suka mik'a suka gayar dashi inda Sophie ta k'arb'i jakar hannunsa Nancy kuma ta k'arbi wacce ya ciro daga bayan shi adaidai lokacin da Islam ke dannowa parlor d'in kai, da sauri har tana had'awa da gudu tazo ta sanya hannu ta tureta ta karb'e jakar hannun shi
"Kajimun yarinya da iskanci fa, kina agola dan er masu gida ta karb'i jakar hannun yayanta kekuma asuwa da wani salon karuwan cin zakizo kice sekin karb'a" kalaman na islam ba k'aramun dakarwa Hafsat k'irji sukayi ba gashi turin data mata seda ta fad'i...k'ura mata ido Hafsat tayi ta kasa furta komai yayinda sophie iyayen fitina ta gagara hak'uri tace cikeda tsiwa
"Haba Anty Islam, wannan wane irin mugun furucine kalmar karuwanci ai batada dad'in ji ko karuwar gaske bataso ace mata karuwa bare kuma kowa yasan waye karuwa waye ta k'warai anan, agolanci kuma mu a iya sanin mu Hafsat Abba shine ubanta abinda ya tara mu ya gaya mana kenan cewar er uwarmu ce kuma ershi ce ta jini, kin kama kin matsawa yarinya to kece agola danmu bece damu ke ershi bace kuma kece Tsohuwar karuwa ai kowa ma ya sani" Dire mata lafiyayyen mari Maheer yayi
"Ke kinada hankali kuwa? Kina hauka ne? Zaki zauna dan babu cikakken ilmi akanki kina gayawa matana wai itace karuwa" Dafe wurin tayi tana kuka
"To yaa Mahii kamata magana mana itama ai tana wuce gona da iri,Ai Abba yace Hafsat k'anwarkace mesa zatace mata karuwa kaki cewa komai kumama har tana tureta ta fad'i Allah ya gank daddy zan gayawa wlhy" ya gaza kalmar daze furta seya kalli islam yace
"Karna k'arajin kin matsawa yarinyar nan Salaha, banaso meta miki? Yaya zaki tureta dan zata karb'i jaka a hannuna? Itama ta isa duk abinda su sophie zasumin ita ma ta isa tamun, kinsani batun yauba nasha zaunar dake a d'aki ina miki magana akan abubuwan dakike mata bakyajin magana ne yanzu kinga su gan suke kamar bana tsawatar miki, ki sani wannan karon bazan lamunta ba wlhy, karna k'araji kin tsauwalawa yarinyar mutane sabida ba zamanki takeyi a nan garin ba, matsayin gidan ubanta ne anan banine na kawota nanba me gidan ne ya kawota sannan idan daddy yaji kina mata haka zaku b'ata ne sosai dashi, lastly kalmar karuwanci karna k'ara jinta acikin gidan nan daga yau, baze yiyu ki kalli yarinya acikin gidan suba ki jefeta da muggan kalamai ba, a iya zamana dake da yaran nan bana tunanin sun tab'a yi miki rashin kunya amma yanzu kinjwa kanki sabida haka ki kiyaye.....juyawa tayi tanata kuka sekace wata jinjira ya rik'o hannun Sophie
" Am so sorry sis kinji bazan kara ba" murmushi tamasa taji sanyi daya wanke islam
"Yaa Maheer ka isa kamun fiyeda haka, ba komai kayi hakuri abinda nawa Adda islam" rungumeta yayi sannan ya mik'awa Nancy hannunshi wacce tun faruwar abun bata mik'eba daga kishingidar datayi ta fadi, batayi musuba ta mika nata ya mik'ar da ita, kai tsaye cikin faffad'an k'irjinsa ya mannata yace
"Am so sorry sister kinji, bazata k'ara ba, zan k'ara tsawatar mata" wani sanyine ya ziyarci hafsat, bazata fad'i iyakar adadin dad'in datajiba daya rungumeta kwantar da kanta tayi saman k'irjinsa haka kurun taji tana buk'atar wadataccen lokaci asaman k'irjin masa, sun kusa 1mn a haka seda Sophie ta gaji da tsayuwa tace "yaa Mahii nakai wannan kayan d'akin ku" sakinshi Nancy tayi tana mejin kunyar sa da sophie gaba daya..karbar kayan yae
"Noo bari na k'arisa dasu ciki karki damu" jan hannun Nancy tayi sukai cikin d'akin su
"Ke Nan kinga yanda kukai matching da yaa Maheer sanda yae hugging naki, wlhy kun had'u inama zan iya gayamai ince dan Allah ka aureta" dariya sukayi ta d'aka mata duka
"Ba wani matching kema ai yayi hugging naki ko? Nima hakanne ko kinaso tun yanzu ki k'aryata kanki da kike cewa ni daku uwarmu d'aya ubanmu d'aya" rungumeta sophie tayi
"Ki gama zagayenki yaa Maheer seya aureki,ni danake nice ai ko second d'aya beyi ba ya sakeni kuma beji komai b, amma ke har idanshi ya canja dan yana sankine na sani" Earp ta zare ta tsala mata take suka fara zagaye suna gudu akan seta daketa, nanma maheer da islam sunzo parlor yanata faman rarrashi sabida tana fushi shisa ma ta fito tabaro masa dakin, kallon mamaki suke musu har suka juya zuwa dakin da gudunsa murmushine ya sub'uce masa ganin sunata afka wawta sekace yara.....
*******************
Da kanshi yaje ya d'akkota school kai tsaye wani hotel ya wuce da ita itadai batace dashi cikanka ba, bata kuma musa masaba da suka shiga cikin hotel room din daya buk'ata, zama yayi itama ta zauna ta had'e rai sosai da sosai batako murmushi...yafi minti uku beyi magana ba kan daga bisani yace
"Hafsat inaso ki nutsu kiji abinda zan gaya miki, da kuma dalilina na kawoki nan" kallon shi tayi amma batayi magana ba yaci gaba
"Nasani ban kyauta miki ba, nakuma sani kinada daman zaman mijin dakikeso, amma na tauye miki hakk'in ki dan Allah kiyi hakuri, ki d'auki wannan a matsayin k'addarar mu dama cen ke anrubuta matata ce" Wani kallo ta wurga masa kan tace
"Yaa Maheer kaifa me kud'ine koka manta? Me kake tunani daya kaika bani hakuri, yanda ka sanya kud'inka ka siyo igiyoyin aurena haka nakeso kayi amfani da kud'inka da isarka ka siyo hakuri nan dakake bani bawai kayi amfani da bakin ka ba" kallonta yayi ya gagara gare inda kalamanta suka dosa ko kadan
"Me kalamanki suke nufi Hafsat?" K'ank'ance idanuwanta tayi
"Kai yayane agareni yaa Maheer sabida haka ba rashin kunya a tsakanina dakai, kai mijine agareni yaa maheer sabida haka banida wanda zan girmama sama dakai a duk fad'in duniyar nan, abu d'aya zan sanar maka shine yanda ka sanya kud'i ka siya igiyoyin aurena, to kud'inka baze iya siya maka soyayya naba, da gangar jikina da ruhina bazan mallaka maka ba koda zaka bani dukiya malali gashi tinkiya, kadena tunanin rab'ata yanzu se sanda Abba yayi umarni da asan da zaman aurenmu.....daga ranar daya bada umarnin namaka alk'awarin zan mallaka maka jikina sabida girman Abba, ruhina kuwa baya tare dakai ko kad'an yaa Maheer ka sani kuma idan matarka tana mun izgilanci kana k'yalewa zan mayar da abunne akan kai sabida ya dace tasan meye kalmar halacci" Nisawa yayi zuwa yanzu ya fahimci kalamanta, wato gani take tamkar kud'i yaje ya nunawa iyayenta suka bashi aurenta, in hakane bazata fahimce saba se zuwa gaba, ya gagara furta wata kalma dan kanta ta gaji da zaman ta mike
"Ka.miyar dani gida yamma nayi" shi d'inma mik'ewa yayi suka bar wurin gaba daya....
*********
Tana bayansa suka shiga parlor d'in ranshi baya masa dad'i besan wane irin mahaukacin sone yakewa hafsat ba, yana matuk'ar san islam amma bekai haka ba, ko kad'an bayajin wannan zafin zuciyar idan yana tunano ta, bata tayar masa da wani abu dayakeji tun daga kan dan yatsansa har saman kansa duk sanda ya ganta......Islam ce zaune a parlor miyarda dubanta tayi zuwa garesu lokaci d'aya ta murtuk'e fuskar nan...hafsat ko kallon inda take batayiba ta nufi hanyar d'akinsu shi kuwa yayi wurin islam, da tulelen cikinta ta mik'e
"Tsohuwar kilaki daga ina kika fito keda mijina?" Juyowa Hafsat tayi sannan ta dawo cikin parlor d'in gaba d'aya tazo daf da ita ta tsaya tace cikin d'acin murya
"Da zanyi karuwanci islam kinsan da nayi tun sanda nake taka k'afana daga jami'a zuwa lowcost a k'asa....da zanyi karuwanci da islam da nayi shi tun sanda nake zuwa jami'a tun 7 na safe har shidan yamma batare danaci komai ba ko nasha ko ruwa ba, da zanyi karuwanci islam damayishi sanda nake rasa Naira goma na siyan handout sena zauna da takarda da biro na ari na wasu na kwafa, da zanyi karuwanci islam da nayishi tun sanda nake rayuwar hostel tare da lalatattu irin ku, da zanyi karuwanci islam wlhy danayishi tun sanda kike neman d'aurani a hanyar yinshi, sanda kike hawan jirgi kina zaga duniya, dq zanyi karuwanci dana biyewa Babbar k'awata aminiyata dakowa ya sanni da ita mun tambad'e a tare....Ashe talauci be saka naki karuwanci ba se wadata islam? Ashe wuya da a zaba da rashin sanin madafa be sanyani nayi karuwanci ba se yanzu da Allah ya 'yantani daga tsananin bauta ya rabani da ita? Ashe tursasasawa be sanyani nayi karuwanci ba se yanzu danake kwanciya in tashi a inda naso babu me tursasamun? Kije makaranta ki koyo ilmin zama da mutane bakisan meye hakk'in d'an adam ba, ke d'in nan bakida mijin dazan nema muyi harkar banza yaa Maheer kuma yaya nane, ko bayan wannan ma nan zuwa gaba kad'an zaki gane cewar inada matsayi har guda biyu awurin shi wanda d'aya kurin kika mallaka...wlhh summa tallahi kika k'ara alak'antani da wannan kalmar sena nuna miki acikin karuwan ma akwai na gida, kuma sekinyi kuka da idanuwan ki wlhy, keda kanki kin sani sam ni Hafsat bana d'aukan raini inadai da hak'uri amma raini kam bana d'aukar shi ko nan dacen" Kuka islam ta saka ta juya gun maheer dayake tsaye tamkar wani statue yana kallon su tace
"Honey kanajifa cin mutuncin da wannan banzar kemun amma ka k'yaleta" k'ara murtuk'e fuska yayi
"Matsalar baki kenan, kasan me zaka fad'a abinda za'a miyar maka ne baka sani ba, ban miki maganr dena gaya mata wannan kalmar ba? Inaso ma na sani shin yanzu mi kike zargi ko ita?" Shiru babu amsa juyawa yayi zuwa d'akinsu itama Hafsat ta juya aranta tace "wlhy sekunci ubanku, na dena barin kina wulakantani mijin nan ina nima inada hakki akanshi? Wlhy sekinsha azaba awurina akan yaa Maheer muzuba mu gani kuma!!!!!!!!!!!!!"
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
34
Da k'yar maheer ya shawo kanta ta dawo masa normal, yana fita a gidan tawa anty Nasara waya akan wai taci mata mutunci, sabida taga sun dawo tare, qwafa tayi tace
"Kinga islam wlhy sekin tashi tsaye akan wannan shegiyar, har fa Abban mu bata bari ba, gaki da tsohon ciki yanzu ai yakai 7 month, ki zauna kina ganin azaba akan wata banza, ki rik'a zubarda hawayenki, k'wacen muji kuma bazamu bari tayiba indai muna numfashi, sannan shima ki dinga cin mutuncin sa kina zaginsa idan har kikaga yana shiga lamarinta, shifa namiji dazaran ka nuna kana tsoron sa shi kenan se raini" Share hawayen ta tayi
"Kuma fa anty kosu sophie sun gama d'inkewa da ita, bakiga ba tamkar uwarsu d'aya ubansu d'aya amma nifa koda ace mukad'ai ne agdan basa kulani, ko magana na musu se hantara" murmushin mugunta anty Nasara tayi
"Had'asu zaki rik'ayi da yayasu, dazaran sun kuskure miki abu d'aya ki saka masa kuka kr har sharri kina mak'ala musu ya musu d'an banzan duka zakiga sun soma tsoron ki" dad'i ne ya kamata ta dinga godiya ita ga mahaukaciya....
***************
Ameen da ummul suna cikin damuwa, rayuwa a b'oye rayuwa ce wacce bazata tab'a yiyuwa agaresu ba, sun shiga takura da matsin rayuwa ita harga Allah ma so takeyi ta gana da iyayenta, gashi kwata kwata Ameen yaki ya yarda suje sokoto akan yana jin tsoro kar Alhj Baba ya kamasu, yaudai kukan sosai ta sakawa Ameen daya sanya bab shiri ya shirya kaita gidan su ya barota cen itada Khadeeja, amma da sharadin bazasu fitoba bare wani ya gansu har se sanda ya nemesu, shi kuwa ya shiryawa kanshi tinkarar Alhj Baba indai ya adana iyalanshi, hakan kuwa akayi sukawa sokoto saukar dare ya kaisu gida, be b'oyewa iyayen ta komai ba dangane da abunda ya faru ya basu kudi masu tarin yawa yae umarni akan lallai karsuje ko ina, Baba iro da akayi tsammanin zeyi masifa tunda yaga kud'i yake washe baki yace ba komai k'addarace Allah ya kiyaye su dana gaba, ansha hiran yaushe gamo Ummul har waya tayi da Nancy sun jima suna hira, koda dare seda sukayi waya babu abinda ta b'oyewa er uwata inda hankalinta ya tashi ta bata shawarwari da adu'o in tsari kala kala kan suyi sallama.
*****************
Sabon tane yanzu data waye a turai shan yoghurt duk dare kasancewar batacin abu me nauyi, wannan ne ya sanya ta baje a parlor tana duba laptop tanayin wani assighnment tana kuma kurb'ar shi a hankali, Islam ce tazo tana wani yatsina da wani qaton cikinta a wurin ta kalleta
"Mujina yana kan hanya kuma anan zamu zauna, tinda ba gidan uban mutum bane seya b'acemun da gani da wannan shigar" mudubin idanta kurun ta gyarawa zama amma ko d'agowa batayi ta kalleta ba
"Ke banza bakyaji dake nake magana, nace nunawa mijina tsiraici da ake tunda be k'yasa ba dakin hakura kin dena kuma yanzun ma ki bashi wuri sabida zezone yaci abinci ya huta" Ko kallonta batayi ba bare ta saka ran zata tanka ta madubin idanta kurun ta zare ta ajiye, warce cup d'in hannunta tayi ta watsa mata yoghurt d'in a fuska da jiki baki d'aya wanda wannan yayi daidai da shigowan sophie da Maheer, da sauri sukayo kanta Maheer yana furta kalmar
"Subhanallah Islam kina haukane" mik'ewa Namcy tayi tana yarfe hannaye
"Nashiga uku yaa Maheer idona" ta furta tana yarfe hannaye tamkar wacce aka watsawa garin barkono a ido, da sauri yayo kanta ya rik'e kafad'unta, se zabari takeyi tana ihu
"Dan Allah ka lashen wannan na idona yanamun zafi" seda ya kalli islam da sophie sannan ya rik'e fuskarta da duka tafukan hannayensa guda biyu ya sanya harshe ya lashe na idanuwanta duka biyu sannan ya zaro hanky ya goge mata fuskarta..k'in bud'e idanta tayi tana meci gaba dayin kukan
"Yaa Maheer har yanzu idona zafi nashiga uku zan dena gani" rik'o hannunta ya kumayi
"Muje gun wash hand base ki wanke Fuskan ki, da kanshi ya wanke mata fuskar amma fir tace ita zafi takeji, kuma tak'i ta bud'e motan, se sannu sophie ke mata
" ke safiyya jeki ki d'akko mayafinta ko abaya haka mu had'u dake mota, gwara muje asibiti kurun" rik'e masa hannu islam tayi
"Wlhy k'arya takeyi yoghurt aiba attaruhu bane babu inda zakaje" warce hannun sa yayi
"Danla cen ni banson hauka, kinzo kin takurawa yarinya ina agaban idona kika watsa mata kofin yoghurt d'aya a fiskar ta, har a ido kinsan me takeji? Wawiya ma dake bakisan hakk'in d'an adam ba" Kan tayi magana safiyya ta iso da abaya ta zura mata,islam kuka ta saka ta shige d'akinsu su kuwa sukayi hanyar waje yana rik'e da ita har suka isa jikin motar
"Yaa ko zaku tafi bani, zanyi bakine wlhy" d'aga mata kurun yayi ya sanyata a baya shima ya zauna a baya driver ne yajasu, seda suka hau hanya da kyau sannan yace
"Mesa zakiyi k'arya ki bud'e idanki sabida nasan ba wani zafi dayake miki" A hankali ta bud'e idan nata ta saukesu a kanshi ta shagwab'e fuska, idan kam yayi ja sosai tace cikin muryan kuka
"Toni meye laifina da ake wulak'anta ni, ni wlhy hostel zan koma abuna tunda ana kallo take mun wulakanci amma ba'a mata magana" rik'o hannunta yayi
"Yaushene tayi ban mata magana ba hafsat? Lallai ne idan zan mata fad'a sekin sani, bata daiji ne amma ina mata fad'a sosai kiyi hakuri, zancen zuwa hostel kuma kema kinsan wannan kina fad'ane kawai" Turo baki tayi
"Ai bana ganin ko fushi kana mata, sedai kaje cen ka dinga rarrashin ta, wlhy sena dinga sakata kuka wlhy seta gane shayi ruwane" kallon bakinta yayi yanda take zuba masifa yace
"Kinga karki soma tashin fitina kiyi hakuri dan Allah"
"Auuu nicema zan tashi fitina ba ita ba? Tab lallai ma" be kara kulataba seda suka zaga gari tukunna suka koma gida, har lokacin fushi takeyi...suna shigowa Islam tazo ta rungume Maheer tana kukan munafunci, ita kuwa ta k'udiri niyyan seta gasawa islam aya a hannun ta....tana sani ta fadi k'asa har tana k'walla k'ara tace
"Wayyo Allah na k'afana" har tana rike k'afarta..... Da sauri ya sake Islam yazo ya duk'a
"Menene meya samu k'afar?" Tana kuka tace
"K'afanane ya bige dana fad'i zogi sosai yakemun" rik'e wurin yayi harga Allah ta bashi tausayi yace
"Sannu tashi kije ciki to se sha'awa ko sophie su saka miki man zafi" yunk'urawa tayi kamar zata tashi sekuma ta k'ara k'wallah k'ara tana ihu takoma ta zauna
"Wlhy bazan iya tafiya ba ka kiramun sophie ta d'agani" cak ya d'agata zuwa d'akin su sophie har saman gadon ya direta yace sophie ta gasa mata sannan ta saka mata man zafi....
Tun daga parlor suke jiyo ihunta ana k'ok'arin gasa k'afar amma tak'i se dariya suke mata, baro parlor d'in yayi yazo d'akin ita kuwa ta biyo bayansa tana ta faman mita akan iskancine kurun ba wani zafi data keji, shi kuwa ko kallonta beyiba ya shige dama fad'a sukeyi tunda abin ya faru
"D'are kan gadon yayi ya karb'i towel d'in hannunta ya kalli Hafsat
" ki nutsu kinji Hafsy, da kaina zan miki kuma zan miki a hankali bazan miki da zafi ba ko kad'an a hankali zan miki, haka sukayi cirko cirko suna kallon su yana danna mata towel me ruwan dimi tana ihu sekace wacce za'a cirewa ido....koda akazo dirza man zafi ba k'aramun kuka tayi ba kaikace da gasken taji ciwo, kowama ya gama yarda cewan ciwon taji...takaicine ya sanya islam barin dakin duk yanda taso daurewa seda tayi, shi kuwa ya kasa ya tsare seda tayi bacci tukunna yabar d'akin....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham..
35
Ranar kam islam fushi tayi me zafi,tama dena kula Maheer, shima d'in shareta yayi har washe gari yayi babu mewa wani magana, haka Nancy ta fito da shirin zuwa skul tana d'ingishi ita adole waiga wacce taji rauni, Sophie se sannu take mata suka fita zuwa gate d'in gidan sabida normally sunada skul bus ita ke wucewa dasu to idan kayi late tana barinka sedai wata tazo, dayake yanayin karatun turawa ba irin namune babu ruwansu da d'an wane su kowa yana hawan bus ko taxi.....driver ya d'akko su Maheer shida Islam se cin magani sukeyi dukkansu, tsayar dashi maheer yayi akan su wuce dasu Hafsat, a gaba Sophie ta zauna yayinda Hafsat ta zaga gefen da maheer yake ta bud'e tana ta faman d'ingishi ta shige, Matsawa yayi tana zaunawa ta rik'o hannun shi
"Aauucchh yaa Maheer k'afara zafi" kallonta yayi zuwa yanzu ya soma fahimtar hadda raki acikin lamarin na Nancy hannunshi dake tsak'ale a nata ya kalla yace cikeda kasala
"Sannu ze dena ne" k'ara matse hannunshi tayi ta kwantar da kanta saman kafad'arshi
"Inama ace yau banida test daba inda zani wlhy" murmushi yayi amma shi kanshi beji nutsuwar hakan datayi ba, d'an matsawa yayi kanta ya goce ta d'ago suka had'a ido sunfi 20 secons suna kallon juna ta had'e fuskar nan alamun yaya zakamun haka bece komai ba se k'ara matsawa kusa da ita da yayi ya kasa koda kwakwaran motsi mayar da kanta tayi saman kafad'an nashi ta kwanta tana wani basarwa, islam yi tayi tamkar bata gansu ba, yanzu ta gama hak'ik'an cewa kanta cewar lallai Maheer neman Hafsat yakeyi, idan hakane sun cucesta kuma basu kyautaba ko kad'an.....sannan kuma bazata tab'a yafewa dukansu ba musamman ma ita Hafsat, seta tozartar da ita.......
*************
Durk'ushe yake agaban Alhj Baba yana bashi hakuri amma k'ememe mutumin nan ya had'e rai
"Kai kana gani kamar kafini wayau ne? Yaushe ma ka taso akan harkar? Wanene kai? Nizaka guda akan matar ka? Dole ka kawomun ita in baiwa maza masu iyawa su mata ciki in biya bashin danaci danni kasan bana asara, mutane da yawa nake huld'an cinikayya na dasu sauran masu cikin na siyar danasu"
"Kayi hakuri Alhaj nabaka yarana sunfi 10 wannan iyalin tawa ita nake fatan qarasa rayuwata da ita har abada, nima inaso in samu magazai kamar yanda ka sameni kayi hakuri, zanyi wani auren semu haifa maka adadin dakake buqata kayi yanda kaso dasu" mari ya danna masa seda yaga wutar lahira
"Da Ummul nakeso, yaranta nakeso na siyar bana kowaba dan ubanka kai harkayi girman dazaka gayamun wai iyali dan kutirin uba" dafe wurin yayi ya mik'e tsaye
"Nagaji da kashe yarana, inaji ajikina bawani adopting nasu da akeyi tsafi kakeyimun da yarana,kaima namijine kaje kayita haifar yaran mana kana yanda kaso dasu,koda ba tsafin akeyiba ai turawa kake siyarwa kace, shikenan mu muna musulmai su sutashi a yahudu mucewa Allah me, wlhy nagaji da bauta maka tunda bakai bane Allah, bazan kuma k'ara b'oye maka ba kaji na gaya maka, ka cutar dani ka gurb'ata tarbiyata Allah ya isa" mamakine ya sanya Alhj Baba yin sororo yana kallonshi har yabar gidan ya kasa koda qwaqwarab motsi...
*****************
Kai tsaye gidansu Ummul ya nufa, yaje har huci yakeyi yana rarrashinta akan bakin cikin dayake ciki seda yayi mata kuka, ita kuwa Allah Allah takeyi ta fad'a masa tanada shigar sabon ciki, har asibiti taje ma satin cikinta 7, koda ta fad'a masa murna awurinsa ba'a cewa komai sunsha murnarsu susu kad'ai sambarka.
***************
Maheer yana cikin damuwa sosai, bayason yanayin islam gata da uban ciki, ta d'auki fushi dashi me zafi kusan kwanaki biyu kenan bata kula sa, gashi batacin abinci yana ganin kamar yanayin yanda Hafsat keyin abubuwa ya dace ace Abba ya bari a sanar wa islam zancen auren nan, besan dalilin Abba na yanke wannan hukuncin ba ace ko yayyunsa babu wanda ya sani, abun yayi yawa amma yazeyi shi awa yace Abba beyi daidai ba haka yayita zarya acikin d'akin shi kad'ai yana neman mafita, daga k'arshe ya kira Umma, itace ta buk'aci ya d'auke islam daga gidan zuwa wani gidan tunda ko rent ne yana halin yin hakan, tunda yake a London gidanne kurun dasu...sosai yayi Na'am da shawarar ta, batare da b'ata lokaciba yasoma shirin neman gidan gadan gadan...ba b'ata lokaci ya samu wani gidan babu nisa da unguwar tasu ak'afa ma sekaje baka sha wahala ba, a parlor ya tadda islam ta had'e rai sosai ko kallonshi batayi ba zama yayi kusa da ita yace
"Haba uwar gida sarautar mata, menene haka na fushi da mijinki har bakya mai magana, yakamata kiyi hakuri, ki kuma fahimci ni Maheer mijin Islam, ina k'aunar matana fiyeda kowa da komai a duniya, ki taimaka ki sassauta mun wannan fushin dan Allah" kallonshi tayi lokaci d'aya ya narkar mata da zuciyarta ta langwab'e masa kanta tana me yimasa k'uri da idanta amma batayi magana ba
"Ki shirya kayanki gobe zamu koma sabon gidan mu inda zamu kasance mumu biyu kacal, muci karenmu babu babbaka cox banso ake yawan bata miki ranki" Mik'ewa tayi
"Da Gaske zamu bar nan gidan mumu kad'ai mu tafi abunmu" Rik'o hannunta yayi
"E mana babyna, banaso aketa b'ata miki ranki ne, gwaramun in d'auki matana mu tafi abunmu" murmushi ta mishi
"To yanzu zamu tafi?" Murmushi yayi shima
"Gobe da safe zamu tafi babyna inshaa Allahu" Kissing juna suka fara alamun dukkansu suna buk'atar junansu, Sha'awa sarakan gulma dake lab'e sum sum ta wuce d'akinsu tana sand'a.....komai seda ta feshewa su Nancy tanata murna zasu rabu da k'aya , rayuwar hafsat ne ya mugun b'aci wanda har suka fahimci hakan, sophie ta tab'a ta
"Baby sis menene, kin b'ata rai" harara ta wurga mata da wasa tace
"Kece kanwata fa" bata kulata ba
"Mesa kika b'ata rai?" Ta k'ara tambayar ta wayancewa tae
"Kurun dai kinsan sabo" tafawa sukayi sophie da sha'awa suka had'a baki wurin cewa
"Soyayya" kallon mamaki ta baisu dashi
"Kaman yaya ban gane ba?" Harara shauty ta aika mata
"Ko makaho yasan keda yaa Mahii soyayya kukeyi, batun yauba muka gano hakan, mu fatanmu ma kuyi aure mu huta da waccen muguwar bafullatanar" murmushi tamusu
"Kanku dai akeji, muba wata soyayya damuke, yaa Maheer soyayyar en uwantaka ce a tsakaninmu ta jini, kamar yanda nake daku haka nake dashi" Dariya suka k'arayi
"Idan tayi wari maji" sophie ta furta tana me barin d'akin zuwa toilet dake ciki......
************
Wayan ta ta d'auka takira yaa Mahala be d'aga ba har kiran ya yanke gaba d'aya kusan so biyu, abinda ya faru be hanasu yin waya suyi zumunci ba sedai sukan rarrashi junansu, akan hakan k'addararsu ce basuda yanda suka iya se hak'uri.......kitchen taje ta nemi youghurt ta tsiyaya a cup seda tacikashi fam sannan ta juya wayanta ne yae k'ara adaidai sanda take k'ok'arin danna kanta cikin parlor d'in...cikeda shagwab'a tamkar zatayi kuka ta kara wayan a kunne
"Nika rabu dani tun jiya nake kiran wayanka baka d'auka" a d'aya bangaren yace
"Haba Hafsat nasani kema kinsan cewar be halatta muke yawan keb'ewa da junaba musamman dakikeda igiyar auren wani akanki, idan wata shawarar kike nema kimun message zan kiraki na baki shawara da kaina" kuka tasoma masa
"Haba yaa Mahal, wanake dashi aduk duniya dazan sanarwa damuwana idan bakai ba, ni shikenan kowama ya tsaneni, sekaga kirana ka shareni mena maka" ta karashe maganar tana sharar k'wallah...
"Ba haka bane Hafsat, ki fahimci magana na, mijinki bazeji dad'i ba yaga ina waya da matarsa, da ace wata alaqa ta soyayya bata tab'a had'amu ba tokuwa da babu abinda ze dameni, amma yanzu zargi seya shiga kinga seki b'ata aurenki ko" Tanameci gaba da kukan tace
"Dukda haka tunda na matsa maka da kira aikasan da wata a k'asa, ni wlhy ka dena sona ko kad'an" shiru yayi sam ta kasa fahimtar sa
"Kiyi hakuri kinji, inasu sophie sufa ba wani sanina sukayi ba, ina matsayin d'an uwansu amma basu sanni ba" murmushi ta d'anyi, suna ganinka mana a hoto, abinda har kama ma kakemun da Sophie" murmushi yayi
"Allah ko?" Bata amsa shiba yaci gaba
"Menene damuwarki Hafsat?"
"Ya wuce kawai karka wasu en damu" beso ya takurata seyace. Kurun
"Zan kiraki anjima yanzu ina tuk'i ne"
"To Yaa Mahal thanks alot bye" sukayi sallama, kallonta sosai Maheer keyi baya ko k'iftawa.......mik'a mata hannun sa yayi tabi tafin hannunsa da kallo
"Wayar zaki bani?" Ya furta cikin dakakkiyar murya
"Akan me?" Itama ta furta cikeda tsiwa" bece komai ba ya juya abinshi itama tana mita ta juya zuwa cikin d'akinsu...abinda ya mugun k'onawa Maheer rai, yanaji take cewa wani wai baya santa yanzu tana matar auren takewa wani irin wannan maganar lallai ma sosai Hafsat ta rainashi amma zata ganene wlhy dan baze d'aukar mata ba.....kai tsaye mahal yawa waya .... Bayan sun gaisa yake tambayar sa
"Menene yake sanyawa kake waya da Hafsat har yanzu? Zancen haskia mahal banaso ka den plss" Murmushi mahal yayi
"Kayi hakuri, koba komai Hafsat k'anwatace, naso Ummul ma ina kallo abokinka yamun k'wace banbita ba, yanzu kuma ka kwace mun Hafsat bance komai seka kirani kace na dena waya da ita, niba jahili bane Maheer ko budurwar dabata aure banbi ba bare kuma matar aure, matar auren ma matar d'an uwana, kasani matsayin duk dasu sophie sukeda a wurina irinshi ne takedashi awurina, hanyar gaskiya kurun nake d'aurata akai bawai muguwar hanya ba ya kamata kasan wannan" Nisawa yayi jikinsa yai sanyi da maganganun mahal
"Kasan matane masuda Hankali Mahal amma idan bakaji dadin magana naba kayi hak'uri ba wani abun nake nufi ba" gyaran murya Mahal yayi
"Koda baka kurani bama nizan kiraka ayau nayi niyyan hakan, inaso kasani Hafsat shekarunta kusan 20 yanzu ta mallaki hankalin kanta, baze yiyu ace kana tauye mata hakkinta ba matsayinta na matar aure, koda umarnin Abba ne rufe maganar amma ka duba lamarin, aure ba abin wasa bane, nasani Abba shi gudun fitina yake agarin daba kowa amma fa kayi kokarin koda a b'oye ne ka nuna mata itad'in matar aurece, na tabbatar ka fahimceni sarai...abu na gaba kuma dama inason namaka waya akan sophie, yarinyar tamun inaso zan aureta ina fatan zaka tayani yak'in neman zab'e" Dariya Maheer yayi
"Kai mashaa Allah amma naji dad'in wannan maganar taka sosai, zanma sanarwa daddy" murmushi shima yayi
"London d'in zanzo zuwa nxt week nida ummy na fa, kabari na soma kafa gwamnati tukunna tunda ka kwacemun budurwa dama dole ka bani kanwarka" Sosai suka dara kansuyi sallama ran Maheer yayi fes...message daya shiga wayanshi ne ya mayar da hankalinshi kan wayan
"Inaso zamuyi magana by 1:am mu had'u a wurin motsa jiki" Hafsat ce tamasa wannan sak'on seda yaje d'aki wurin matarsa duka soye yayi wanka ya tabbatar tayi bacci sannan ya rufo dakin yama rufeshi ta waje ya nufi wurin, da k'arfe 12:56 am ya isa wurin ga mamakinshi tarigashi wurin.....a hankali ta tako tamatso daf dashi har suna jiyo numfashin juna da bugun zuciyar junansu, suka k'urawa juna ido na kusan mintuna biyu batare da waninsu ya gajiya da kallon d'an uwan saba, kowa da abinda yake sak'awa a ranshi mamakin ta sosai yakeyi yanda ta k'ware a iya kafe mutane da ido batako k'iftawa watak'ila hakan baya rasa nasabane da yawan sanya nik'afi ta kuma rufe idanta da gilashi... Anata b'angaren kuwa idanuwan sane ke hana nata motsawa duk sanda taso yin hakan, duk lokacin da idanuwansu suka gauraya tokuwa tabbas bazata iya janye nataba seya janye nasa, wani uban magnet ne ke manne su wuri d'aya da idan har yaci gaba da kallon ta tokuwa ita sam bazata iya d'auke nata idanba.....shine ya soma magana batare daya janye idanshi anata ba, cikin sanyin murya ya furta
"Hafsat lafiya dai kira cikin daren nan?" Tattaro duk wani courage nata tayi tace har lokacin idanta na cikin nasa
"Sabida niba mace bace, kokuma aurena yanada banbanci dana sauran mutane ne?" Be fahimci kalamanta ba
"Subhanallah Hafsa, meya kawo wannan maganar me kika gani? Ban fahimce kiba" k'ank'ance idanuwan ta tayi sosai
"Bazan kiraka acikin dare ba sabida ni banida kwana ko?" Se yanzu ya gane inda zancenta na farko ya dosa amma seya gaza furta wata kalmar se bakinsa dake motsi alamar da akwai abinda yake so yace...taci gaba da magana
"Dolene ya zamar mun idan har inasan nayi magana dakai mijina sena b'oye, idan ba ahaka ba matarka bazata bari ba, dole ne nabi dare sabida in ari halin b'arayi in rufawa tsufana asiri kar a cimun mutunci in gaza ramawa bakuma nida me ramamun" yasani sarai dashi take cen cikin mk'oshin daya bushe masa qayau ya lalubor kalmar
"Haba hafsat wannan wace irin magana ce?" Gyaram tsayuwarta tayi ta hard'e hannayenta asaman k'irjin ta tace
"Banida iko da hurumin sanin cewar zaku bar gida kaida matar ka awurinka sedai a bakin shanun tallah, niba mace bace yaa Maheer, banida wani buri kenan arayuwa? Dan ban aureka asan rainaba bashi ke nuni dacewar banason aurena ba, bashi ke nuni da cewar na shiryawa kaina rayuwar zawarci ba, bashi ke nuna cewar zab'in iyaye ba Alkhairi bane ba, dan Allah be bani auren wanda naso aura ba bashi ze nuna cewar wai zab'in Allah kuskure bane, watakila wanda nakeson ba kuskure bane arayuwata, dan daddy yacr aurenmu ya zama sirri har zuwa wani lokaci sekuma yace dakai dukkanin hakk'okina ka wofintar dasu?" Gaza furta koda kalma d'aya yayi k'ara taku biyu tayi izuwa daf dashi ta kunce hannayenta data hard'e ta rik'o hanshi biyu
"Ashe banida hakk'in tab'a jikinka kamar yanda islam keyi agaban kowa, ace ban cancanci a bani shinfid'a asaman k'irjin kaba, ni banida damar da za'a waremun lokaci na aci abinci atare dani,ajani salla, amun hira koda a waya matsayina na matarka ban cancanci ko d'aya ya maheer, ashe ayanayin yanda aurena dakai yazo ban cancanci rarrashi ba.....Ashe ban cancanci kulawaba yaa maheer kasani nima macece dukkanin abubuwan dana fad'a dama wanda ban fad'a ba suna raina nima inaso ina buk'atar tattalin nan danaga kanawa islam koma fiye, kana fad'ar soyayyar nan tawa a baki komenene yake kashe maka jiki kake kasa nunamun ita a sarari" shiru yayi ya kasa magana se janyota da yayi zuwa faffad'an k'irjinsa ya kwantar da ita...yana patting bayanta a hankali, besan dalilin saba na zama dolo wawa agaban Hafsat seya kasa yin magana ko wace irice agabanta, seya zamto mara wayau idan suna tare yakan kasance cikin, tsananin shauk'in ta idan suna tare....daidai sautin kunnenta ya rad'a mata
"Kiyi hakuri, wlhy kinada dukkanin matsayin dababu wata macen dake dashi awurina, banida burin daya wuce in faranta miki, Allah ne shaidana idan farin cikin islam shine babban dalilin dayasanya zan d'auketa agidan to kekuma kwanciyar hankalinki shine abu mafi soyuwa agareni, wanda shine babban dalilin d'auketa agidan, abubuwan da idanuwanki ke gane miki na tabbatar kina daurewa ne kurun badan kin soba bakya cikin kwanciyar hankali, nasani k'azantar dukda baka ganiba tsaftace wannan ne ya sanya na yanke shawarar sauya mata wuri sabida ku nesanta da juna dan Allah kiyi hak'uri" matseshi tayi sosai ta hanyar zagaye hannayenta a bayansa tace
"Babu komai na fahimceka mijina, hukuncin ka daidai ne, amma fa ka sani ina buk'atar kulawarka,kuma idan ka tafi ka rik'a kawo mun ziyara zanfi kowa farin cikin hakan" matseta shima yayi
Inshaa Allah sekin gaji dani, kin sakani a farin ciki Hafsat, dole kema ma saka miki da fin abinda kikamun, ki sani wannan kulawar da kika bani ya wanzar da farin ciki me yawa a rayuwata Allah ya miki albarka kinji" sunfi 10mns rungume da juna sedaga baya ya d'agota ta fuskancesa ya sanya hannu a hab'arta ya sumbace bakinta sosai ya tsotse sa, har suka kusan fad'uwa bazatace bataji daban ba to waye ita da maheer ze sarrafata ta kasa zama garin tuwo!! Zama sukayi suna hira se wuraren asuba suka rabu da juna...
Washe gari suka bar gidan shida islam komai nasu suka kwashe, ita kuwa ta kira anty fareeda ta gaya mata tayi yanda yace gama abinda yace, dama anty fareedah tasan da maganar auren, Umma da kanta ta gaya mata kuma takula da shigewar da nasara kewa islam ko a waya, shisa itama take tattalin Hafsat.
0 comments:
Post a Comment