BA GIRIN GIRIN BA.....
Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin.
Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa.
Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne.
Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta.
Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba.
Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji.
arabs desperation fikraw
abdoul
Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin.
Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa.
Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne.
Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta.
Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba.
Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji.
Aure ibada ce, sunna ce mai girma amma kuma rashin sa bai rage komai na daga Darajan bawa a idon mahallicinsa, matukar mutum zai tsare kansa daga kowanne nau'i na zina, zai kasance abin so a wajen Allah har zuwa lokacin aurensa, anan Allah zai saka masa da abokin rayuwa nagari wanda zai sa a manta da kuncin jinkiri, in kuma bai da rabo zai samu babban rabo ranar gobe kiyama.
Babu jinkirin da ba Alkhairi ba, matukar an yi hakuri, in kuwa ba'a yi ba tsaf ze zama azaba...
***
Zaune take a ofishin ta na sashin kere-keren magudanar ruwa ( water resources engineering department) a bangaren kere-kere (faculty of engineering) da ke jami'ar kimiyya da fasaha ta Safiyyah Jibril (Safiyyah jibril University of science and technology) da ke daular Qahɗanie.
Kacokan hankalin ta na kan zanen Dam ɗin da jami'ar ke shirin kaddamarwa wanda musamman aka zaɓe ta cikin ma'aikatan wannan sashi na su don ta zana ta gabatar ma shugabannin makarantar don a samu a sa shi cikin kasafin shekara mai zuwa.
"Miss Fatima ki ɗauki abin sannu a hankali mana, ke ba miji ba balle a ce zai hutar miki da gajiya a gaba" faɗin wani magidanci wanda kallo ɗaya zaka masa ka san in bai yi jika da wacce ya kira da Miss Fatima ba toh tabbas zai haife ta. Aikinta ta dukufa ta cigaba da yi ba tare da ta dago kai ta kalle shi ba.
" Ankara ɗin nan ya fito da ke, kin ga yanda kwalliyar ki ke gayyata na zuwa gare ki, don Allah ki aminta da ni zan shayar da ke daɗin da ba ki taɓa tsammani ba, sannan hakan ne zai kara min mararin aurenki, wallahi ina son ki" Ya sake faɗi yana mai kai fuskansa saitin nata fuskan har suna shakan numfashin junansu.
"Au'uzu Billahi Minka" Ta ce tana mai mikewa
"Zan ba ka mamaki Prof. Ka bar ganin kai ne shugaban ɓangaren nan (Dean) Wallahi zan maka abin da ba ka taɓa zato ba, Banza tsohon Bunsuru" Ta ce tana ficewa da ga ofishin sanin da ta yi kofar jam lock ne.
"Ai ko da karfin tsiya sai na sha romonki, Ace yarinya se shegen fuska biyu, mace za ta kai shekarun ta ne ba tare da neman namiji ba, duk kuɗin da na ba ta ba zai tashi a banza ba" Ya fadi yana buga kofar da karfi.
Da kyar ta iya jan kanta zuwa gidansu da ke unguwar da ake kira Madina saboda kasancewar sa sabuwar anguwa da ya kunshi sabbin gine-gine da abubuwan kawata waje. Ba kowane dan Qahɗanie ke mallakan gida a wajen ba sai wane da wance musamman yan jinin sarauta da hamshakan yan kasuwa kamar Mahaifin Fatima Alhaji Bello Yahuza.
***
Daular Qahɗanie na tsakanin Kasar Nijeriya da Ghana masarauta ce da fataken Larabawa su ka kafa yayin da su ke yaɗa zango in za su je kasuwanci a wannan yankin. Sannu a hankali sai ya zama duk wani wanda ya ratsa daga yankunan Sahara da arewacin Nigeria a nan su ke yada zango har sai da zuwan wasu ayarin Karauka karkashin shugabancin Madugu Imam Jibril da ya ke yawon yaɗa musulunci a shekara na ɗari uku da hamsin bayan Hijira.
Tun da ya yaɗa zango ya ga wajen sai ya yi ra'ayin kafa daular musulunci a wajen. Ba tare da ɓata lokaci ba yayi Shawara da ayarin sa nan su wasu su ka aminta da haka, yayin da wasu su ka ki amincewa. Cikin shekara ɗaya aka kafa daular sannan su ka sanya masa suna Qahɗanie kasancewar su Larabawa. Sun ɗauko iyalansu sannan sun bar kofa a buɗe ga duk wani mai bukatar zama a daulan bisa ga amana.
Kafin a ankara Hausawa sun rinjayi Larabawa masu zaman wajen saboda kasancewar sun fi Larabawa kusa da nan. A lokacin mulkin Imam Abdulhamid Bn Jibril watau shekara ashirin bayan kafa daular ne aka fara auratayya tsakanin Hausawa da Larabawa a daular Qahɗanie, sannan a shekaran ne aka kafa makarantun boko a daulan wanda fa taimakon yayar Imam Abdulhamid Safiyyah bnt Jibril ne aka kafa su.
Tun daga nan aka fara samun cigaba ta fuskan kimiyya da fasaha, har ma da shari'a sannan akwai yalwan ilimin addini a daulan. Bayan tsawon shekarun daulan sannu a hankali Al'adun Larabawa ya gushe da ga jikin su, yaren su da Al'adun su ya zama na Hausawa amma duk da haka ba za'a ce sak na Hausawa ne ba kamar yan Nijeriya, Cameron da Nijar da Chadi da sauransu ba...
How do you see our shimfiɗa?
How do you see our main protagonist?
Others are yet to come
Get set for twined twists, all you have to do is to invite extra patience coz more update may b after my exams
Insha'Allah. But if am opportuned I will publish one or two Insha'Allah.
Invite ur family and friends,family of friends, friends of the family, friends of friends, friends of friends of friends, friends of family of friends.
I love you and I will forever do
Vote, comment and share please
Kamar yadda al'adan gidan ya ke, duk bayan sallah da zikirin asuba kananan gidan kan bi manyan har mazauninsu domin su isar da gaisuwa. Hakan na da ga cikin abin da ya kara soyayya da kauna tsakanin ahlin gidan.
Fatima ce ta fara da ɗakin mahaifinta kuma shugaba ga duk wani mai rai a gidan. Ta same shi zaune Saman sallaya hisnul Muslim a hannunshi, Qur'ani ajiye a gaban shi. Hannu ta sa ta ɗaga Kur'anin ta na
"Abbie kai ma ka saba da Al'adun mutane na aje Kur'ani a kasa, Darajan Kur'ani ya fi karfin a dinga ajiye shi a kasa fa" Ta karasa tana mai zumburo baki, in har da sabo toh ya saba da halin yar tasa, ba ruwanta da girma ko izzan mutum in dai zai wulakanta wani abu da ya danganci musulunci cikin sani ko rashin sa, sai ta furta sai dai duk abin da ya fanjama fanjam.
"Assha ba fa ina kin gyaran ki bane, kin san an saba ajiye Kur'ani a Saman darduma in za'a yi sallah alhali a sa shi sama da abin da duk rashin ganin mai tafiya ba zai buge shi ba ko taka shi. Ina alfahari da ke fatima, Allah miki albarka. Kin tashi lafiya"
"Laa Abbie ni zan gaida ka, ina kwana" Ta karasa tana murmushi cike da kauna
"Ai kin gaida ni, akwai gaisuwan da yafi sallama alkhairi? Ai a matsayin mu na musulmi gaisuwan mu shine sallama sai dai mu ɗaura al'ada a sama" Ya ce yana shafa kanta
"Abba ka sani a addu'a, ni ma dai in yi auren nan in huta, na gaji jiya fa Farfesa Jabir har da sa mu musayar numfashi saboda yanda ya tunkaro ni, ga ɗan waziri Abdul-Barr ya fa alwashin mallakata yayi ko ina so ko banso, na gaji Abbie"
"Ka da ki gaji, sannan ka da ki saida mutuncin ki, ke ce babba a gidan nan, kanen ki biyu sun yi aure, ba hakan na nufin Allah ya fi son su da ke bane. Wanda Allah ya fi so shi ya fi jarabta. Kada ki kuskura ki yi gaggawa don in dai latti ne a daular nan da ake aure shekara goma sha huɗu, sha da sha shida toh ke mai ashirin da takwas ai kin yi latti. Amma a musulunci ba wani garaje ba jinkiri kowa na tafiya daidai da lokacin sa ne, kin gane" yace fuskanshi yalwace da murmushi.
"Yauwa! Jiya ina ji amminku na faɗin kina shiga irin ta matan aure kina wani ɗaure fuska yaushe za'a aure ki, manta da ita fa, in kin yi yawo tsirara ko kina tafe kina washe ma maza hakora ai kam za ki samu kasuwa amma ba za ki yi daraja ba. A hakan ma an yi yunkurin lalata ki ballantana kin kyautar masu da rabin jikin. Ki cigaba da tsare mutuncin ki sannan banda wasa da addu'a RABBI INNIE LIMA ANZALTA MIN KHAIRIN
FAQEER ka da ya fita daga bakin ki. Tashi ki je kafin iyayenki su tsargu" Nan su ka sa dariya, don halin iyayen ne tsarguwa duk sanda aka iske Fatimah da mahaifinta saboda sun san itace sirrin shi.
Da ga nan ɗakin Hajiya Hafsa mahaifiyarta da su ke kira Ummi ta shiga, nan ma gaishe ta tayi, itama nasiha ta yi mata akan tare mutunci tare da shi mata albarka, daga nan ta wuce bangaren Hajiya Sadiya da su ke ce ma Mamie, sun gaisa babu yabo ba fallasa don ita kishin da Fatima take yi, tsakanin ta da Hajiya Hafsa babu matsala amma bakin cikinta yanda Alhaji kan fifita fatima akansu har ta zama aminiyar sa alhali su ya kamata su zama aminansa. Har ta mike za ta fita sai ta tsakayi hajiya sadiya na faɗin
" Ki sa baki alhaji ya bani Dubu hamsin, kwana uku kenan ina bin sa ya hana min" Ta ce cikin jin zafi da takaici
"Mamie zan baki, amma Alhaji ya samu asaran fiye dollars dubu ashirin, in aka juya shi zuwa Nutud (sunan kuɗin daula) za ki ga ba karamin asara yayi ba, mu cigaba da addu'a ya fita kawai. Laa ya ce kar na faɗi fa" tace tana rufe da har hakan ya sa ba ta kula da harararta da Mamien nasu ke yi ba. Nan ta cika da murna don ta samu abin kushe Fatima a idon mahaifinta.
A ɗakin Amminsu Hajiya Amina ba ta ko zauna ba, don ta san in ta yi abin da ya wuce gaisuwa toh karshen abin ita za'a yaɓa ma magana. Wajen mahaifinta ta koma ta faɗa masa kuskuren harshen da ta samu har ta faɗi ma Mamie abin da ya same shi, nan ya ji haushi amma kuma ya yafe saboda ta tsaida gaskiya.
Kalaci su ke yi, Alhaji Bello Yahuza ne da matansa, da su ka kammala ne ya saurare su in da mai matsala a cikin su, hakan ya kasance al'adansa sai ya ji matsalar matansa kafin ya tafi harkokin kasuwancinsa.
"Alhaji ashe abin da ya faru kenan, ɗazu na tsinkayo muryar Fatima tana magana a waya, nace mu dai wannan karfa-karfa na Fatima karfi da yaji ta fi mu mahimmanci a gidan nan" Ta karasa zancen tana dariya. Nan matan su ka fara tambayar abin da ya faru tana maida masu zancen har da karin gishiri.
"Af, tun da ta ki aure kawai sai a raba kwana da ita" cewar hajiya Amina kai tsaye ba tare da tunanin mai zai je ya dawo ba. Take Hajiya sadiya ta yi Dana sanin abin da ta faɗi don ta san in hukunci zai yi toh tabbas ita ma ba za ta tsira ba..
"Toh ai ni a sani na tafi ko uwar ta daraja a gidan nan don duk in da za ta je nan ya fiye mata ko ina, in na so zan chanza ku amma ita ko na kore ta ba zai chanza mata sunan ya ta ba. Ina ga dai yau babu mai matsala cikin ku, na bar ku lafiya" yana kaiwa nan ya sa kai ya fice daga gidan.
Nan fa cecekuce ya tashi tsakanin matan suna masu nuna ma hajiya Amina kuskurenta na faɗin maganar nan ita kuma tayi fir ta ki amincewa don a cewarta an shiga huruminta ne shi ya sa ta yi magana.
***
Fadar mai martaba sarkin Qahɗaniee cike ya ke da farin ciki saboda dawowar yaran mai martaba wa'inda ake sa ran samun sarki daga cikin su.
Biki aka yi mai kayatarwa don har hutun kwana biyu aka ba da saboda dawowar mahimman mutane guda biyu da su ka fi kowani mahaluqi daraja a daular. Dukkansu sun yi karatu ne a ɗaya daga cikin jami'o'i masu daraja a duniya wato Massachusetts Institute of technology da ke birnin Cambridge na Kasar USA.
Babban watau AbdulHalim ne ya karanta Nuclear Science and Engineering yayin da karamin AbdulHaseeb ya karanta Military science duk a wannan jami'ar. Tun da su ka tafi ba su dawo ba se yanzu da suka kammala digirgir (PhD).
Bayan dogon jawabi da sarki yayi a fada, ya faɗi ma fada nan da wata takwas zai fitar da sarki mai jiran gado a cikin su biyu. Sannan ya ce zai zaɓi amintattu daga fada wa'inda za su sa ido akan su wajen gane wanda ya cancanta a cikin su biyu.
Daga fada sun shiga cikin gida in da su ka iske ana kwarya-kwaryan biki na tarbo ga yan Mata hadaddu an kawo Su duba su zaɓi wacce ta musu don a fara shirin biki. Yan mata ne da sarki da kansa ya tura masarautu masu daraja daga Kasar Hausa da Larabawa har ma da kanuri don ya'yan sa maza biyu rak da ya mallaka su samu mata daga tsatson sarauta ba a gauraye da wa'inda ba su da jinin sarauta a ransu.
"Ni fa ban ki a bani yan matan nan duka ba suna rotation har na gama dandana romonsu ba, ni ban ga matar aure ba duk na holewa ne" AbdukHalim ya ce yana mai kallon AbdulHaseeb.
"Dan uwa kai de ka hole, ban san da kai da AbdulBarr wa ya fi wani ba, ni matar aure na ke nema amma mai aji ba wa'inda aka turo su yi tallan kansu ba" yace yana fuskewa, dariya AbdulHalim yayi har da buga kafa.
"Wato ba ka son haja kenan" Ya ce yana mai cigaba da dariya
"Ai ko hajar ne gara na je na siyo mai daraja wanda kafafu na zai kaini ba wai in ga tallan raguwan kuda ba in siya" Ya kara fadi yana yamutsa fuska don kwarai abin takaici ya ba shi.
***
Bayan sun yi wanka sun shirya cikin kaftani da wando haɗe da hula duk mai ruwan sararin samaniya. Hakan ya fito da hasken su na jinin Larabawa, sannan kayan ya bayyana tsawon su da kyau fuskokinsu
"Takawanku lafiya Allah ja zamanin tagwaye hasken idaniya Qahɗanie sarauta gadonsa ku ka yi sannan abadan ba za ku bar shi ba" cewan maroka sanda su ka fito. Za su ce kewaye gari.
Marsandi su ka shiga suna tafe suna jin wakar Humood Alkhudher suna kallon yanda daular su ta kara habbaka da Sabbin gine-gine da ya dace da lokacin da mu ke ciki.
Sun shiga har cikin jami'a in da su ka iske ɗai-daikun mutane kasancewar ana hutun da aka bada na bikin dawowarsu sannan maraice ne don haka wa'inda su ka shiga makarantar ma sun tafi gidajen su. Bayan sun gama kewaye a makaranta ne su ka baro don su koma gida, a nan bakin gate ɗin fita aka ce su buɗe booth don a duba kamar yanda ake ma kowa.
"Kana da hankali, motar sarkin ku a gobe ne za ka duba ko ya yi sata, baka san mu bane, banza talaka, bawa da kai" cewar Abdulhalim yana mai shirin marin mai gadin wanda a shekaru zai iya haifan su ko ya zama babban yaya na chan nesa
"Ayi min hakuri ranka shi daɗe Allah ja zamanin mai jiran gado" yace yana mai kwanciya a kasa. Shi bai san su bane don shi aikin shi yake tsakanin sa da Allah ba wai yana duba ido ko kyautan da ake ba dawa ba.
"Kada ka taɓa ni la shafa min warin talauci, wallahi ka sake sai na sa an ɓatar da kai" Ya ce yana mai buga tsaki shi kuma mai gadi sai gyada kai yake kamar kadangare.
"Ka same ni a fada yanzun nan in ka bari muka riga ka isa, hmmmmn! Ya ce yana kaɗa hannu" Nan cikin baba tsoho ya kaɗa jin kalaman AbdulHaseeb da tun da aka fara bai fito ba balle ya tofa albarkacin bakin sa, yanzu ma da su ka fita gate ne ya yafito shi da hannu ya faɗa masa.
"Wato kai ka fi ni mugunta, ni fa kawai kyamar talaka gareni mutum matukar ba jinin sarauta ba toh bawa ne, sannan bayan jinin sarauta duk wanda ya yi karatu a MIT ai sunansa wuyan faɗi ya ke a cikin tsararsa, one of the world's most prestigious University na gama fa, sannan ni ne ɗan fari a wajen mai martaba dole kowa ya so ni, dole kowa ya daraja ni don na cancanta" Ya karasa yana mai buga sitiyari.
Dariya sosai AbdulHaseeb ya yi, yana yi yana taɓa Abdulhalim da ya gama kuranta kan shi.
"Ai shi wanda ya gama MIT ilimin da yake da shi ya ke sa ya fita zakka har a ga bai da lamba biyu a cikin tsaransa. Ni ban cancanci soyayya da girmamawa daga talakawa ba, zan dai siya hakan daga garesu yanda ba za su san lokacin da za su bani shi ba" Ya ce bayan ya gama dariya
"Ashe dai za ka wahala da yawa don kuwa talaka ko naman jikinka kake ba shi sai ya tsine maka, sun fi son mai cin ubansu, shi tsohon nan me za ka masa?"
"koransa zan yi daga aiki, don bai cancanci zama a wajen ba" Ya ce yana mai fuskewa. Haka su ka cigaba da hirar duniya har su ka isa fada. Nan su ka iske maigadi har ya isa yana jiransu a kofar fada.
" ga wannan Nutud dubu ɗari kuma bashi ka ja jari zan nemi kuɗi na nan da shekara ɗaya, sannan gobe ka rubuta wasikar ajiye aiki, tsohon ka da kai ka tsaya aikin gadi, nawa ne albashin na ka? Maza ka je ka san abin da zaka fara don rana ita yau shekara mai zuwa in ba ka biya bashi ba, sannan baka ɗauki akalla mutum biyar aiki karkashin ka ba za'a neme ka a rasa" Ya karasa cikin izza da isa. Bai jira yayi godiya ba ya wuce abin shi ya bar tsoho cikin farin ciki.
One word for the first chapter
Guess our main male protagonist
Guess where this story is heading to
Thnx alot for the votes and comments pls don't get tired I love u
ol. mention a usermention a user
Una don start ba, Haba ghosties, pls now, ga ni akan guiwa, pls vote and comment
Gabas da Qahɗaanie akwai wata karamar yanki da ake kira Zango. Wanda Amir Al'ansarie ke shugabantar Zangon.
Duk wani nau'i na ta'addanci da alkba'ir za ka samu ana aikata shi kai tsaye a wannan yankin amma hakan bai sa a ci zarafin ahlin wannan yanki ko kuma a musguna masu ba.
***
Asalin Al'ansarie mutumin Qahɗaanie ne don tare da iyayensa na hamsin da bakwai Sheik jibril ya kafa daular Qahɗaanie. Hakan ya sa ya ga shi ya fi kowa cancantar rike sarautar Daular a wannan lokacin har ya fito takara da sarkin wannan zamani duk da ba'a kallon gidansu a matsayin gidan sarauta. Tun a zagaye na farko aka watsar da shi daga jerin wa'inda kwamitin za su zaɓa, a karshe aka zaɓi sarki AbdulJaleel wanda akasarin al'ummar daula suka aminta ya zama shugaba gare su, ku ma shi ne jinin sarki kwaya ɗaya tilo da yayi saura har mutuwar sarki.
wannan zaɓe ne ya tunzura Amir wanda asalin sunansa Saifullahi Alhamzie kafa na shi yankin ya sanya masa Zango saboda wannan yankin ne duk wani wanda zai tsallake Qahɗaanie zuwa fatauci kan tsaya don ya huta.
Abu na farko da ya fara yi shine bai wa yan fashi masauki a wannan yankin. Ya basu hannun amana su ka amince su ka amsa sannan ya musu alkawarin kariya, a dalilin haka Larabawa daga cikinsu suka fara kiran sa da Ameer..
Daga nan ya ba dukkan fatake masu yaɗa Zangon hannun aminci tare da alkawari ga duk wanda ya yi rajista da shi cewar babu shi ba wahalar yan fashi don ko ina aka musu a bisa kuskure yayi alkawarin maida musu da dukiyarsu da aka sace, hakan ya sa Larabawa daga cikin su sanya masa Al'ansarie..
Kafin shekara ya zagayo Al'ansarie ya samu cigaba don yankin sa ya habbaka sosai sai kuma aka fara damun al'ummar daula da sata, fashi har ma akan taɓa fyade.
"Mai girma Ranka shi daɗe, ranmu fansa a gare ka, binciken da mu ka yi ya nuna mana da sa hannun Saifullahi Alhamzie ake duk Wa'innan miyagun ayyukan.. Ka bamu izini mu zubar da jinin sa kafin ya fi karfin mu" cewar sarki yaki kuma kwamandar sojojin Daular Qahɗaanie.
"Ku gayyato mana shi ne, mu ji daga gare shi" cewar sarki a wancan lokacin. Bisa ga yin biyayya ga sarki aka gayyato saifullahi har fada, bayan an karanto masa abin da ake tuhumar sa da shi ne ya ce
"Ba ni na sa su sana'ar nan ba, sannan ba na cin ko digo daga haramun, suna min biyayya dai saboda adalci na gare su, zan yi biyayya ga umurninku amma bisa sharadin babu ruwan hukumar daular nan da su, in an kama su da yin laifi a sanar da ni, karkashi na su ke ni na fi kowa cancantar hukunta su" nan take fada ta kaure da hayaniya dogarai da sojoji na jiran umurni don zartar masa da hukuncin da ya dace da shi na yi ma sarki tsaurin ido, amma ga mamakin su sai sarki ya ce
"Shi ke nan abin da kake bukata? Ko da wani sharadin, in shike nan ni kuma ina so ka sani duk ranar da ka saɓa alkawari za mu ci ka da yaki, ko kuda aka taɓa a Qahɗaanie zan turo dakarun da za su taho min da kanka ko da gangar jikinka zai cigaba da aiki ko ba zai cigaba ba, babu abin da ya shafe ni. Kada ka yi tunanin zan dubi zumunci kasancewar ka ɗan kawun mahaifiyata, na sallame ka"
"Godiya nake" yace yana mai ficewa. Sarki bai ba kowa fuskan korafi akai ba. Kuma tun daga lokacin har yanzu shekaru talatin da biyu kenan ko kaza ba'a ake sata ba a Qahɗaanie haka ko tsakar dare mace ta fita babu wanda zai tunkare ta balle ya cutar da ita.
***
Gagarumin Sata aka yi a kasar Ghana inda aka yi fashi a babban bankin Kasar (central bank of Ghana) kuɗi aka sace da in aka juya zuwa dollar zai iya kai dollar biliyan talatin, hankalin gwamnatin Kasar ya tashi ainun nan aka sa bincike ana neman wa'inda su ka yi fashin ta hanyar na'ororin ɗaukan hotuna da ke maqale a bankin.
Add Vote
Dukkansu sanye su ke da lullubin fuska, dauke su ke da na'ororin buɗe kofofi wanda da gani ba karamin. Masanin fasaha ne ya qera Shi ba. Ba sa magana sai dai yin alamu da idanun su da ke buɗe. Har sifeto janar din yan sandan Kasar zai ce a kashe faifain da aka samo daga bankin sai fuska ta bayyana na shugaban tawagar, nan take ya sa aka tsayar aka dauki fuskan hoto haɗe da tsayar da faifan bidiyon.
Binciken farko da su ka yi nan su ka gano mammalakin fuskan ta hanyar yanar gizo "Adjetey Tetteh" shine sunan da ya fito da duk wani shafi da ya bayyana sunansa. Bincike ya nuna ɗan unguwar Zango ne da ke Kasar Ghana (zango community). Nan take a ka baza hotunan sa a ko ina da sunan a kawo ma gwamnati shi ko a mace ko a raye.
"Nii Adjetey ka ga hotunan ka a ko ina ana nema a mace ko a raye, ya kamata ka aiwatar da wani abu in ba haka ba za'a kashe ka ne a banza" cewar ɗaya daga cikin yan tawagar sa, duk da ya san ba wai zai tsorata bane don duk duniya Adjetey ya kasance mara tsoron komi da kowa. Sai dai abin da ba su sani ba duniya ba wanda yake so da kauna sai Amir Al'ansarie.
"Babu damuwa Armah, zuwa gobe maganar zai zama tarihi, yanzu dai ku tabbata kun bar yankin nan, zan kula da kaina, abu ɗaya za ku sa a ranki shi ne Amana, sannan abokantaka na da hakki fiye da jini, in dai kuna tare da ni, babu abin da za'a mana" da haka ya juya baya alamun ya sallami Armah.
Bayan fitar Armah, wayar sa ya ɗauka ya latsa wasu lambobi, kara na biyu aka ɗaga daga wancan ɓangaren.
"Yau ɗa na ya ni me ni, ina fatan bai yi girman da ya fi karfin taimakon uban sa ba" suka sauka a kan kunnen sa
"ina neman afuwa Amir, ba zan taba yin girman da zan fi karfin albarkan uba ba, yanzu haka rai na ake nema ido rufe a Ghana, kuma na san ba ka shirya birne ɗan ka ba" Ya fadi yana mai cike da imanin matsalar sa ta kawo karshe.
"Gobe da safe ka shirya wani zai zo ka sammasu wani abu cikin abin da kuka samu, da yamma kuma duk runtsi ka iso nan waje na" Ya ce masa kai tsaye ba tare da ya ja zancen da tsawo ba. Godiya Adjetey yayi ya ajiye wayar.
Amir na ajiye wayar Adjetey ya nemi sifeto a waya bayan doguwar gaisuwa da ke nuna alamar sanayya ya ce
"Wannan aiki na kasan rai ne shi ya sa na neme ka in ba haka ba gobe iwar haka Kasar Ghana za ta kasance cikin kunci da tashin hankali, na ji yaranka na neman raina" Ya faɗi kai tsaye
"Ranka kuma Amir, da taimakon ka na dane kujerar nan, ka taimaka ka min bayani yanda zan gane"
"Adjetey yarona ne na kasan rai, ka je gidansa ka amshi abin da za mu iya baka a ciki maganar nan ya zama tarihi. In kuma ka ki, toh tabbas ran Adjetey daidai yake da na kusan duk wanda Ajali yayi kiran sa. Adjetey na gidansa na zango community, kana iya zuwa yanzu" Amir ya karasa yana mai katse wayar.
Hankalin sifeto ya tashi, ga koshi ga kwanar yunwa. Bayan ya zauna yayi tunani mai zurfi can dai ya yanke shawarar karɓan rabon sa ya kara gaba. A cikin daren ya shirya fita ofireshon inda yayi nasaran kashe wani mashayi, aka ɗauke hotunan sa cikin jini da sunan shi ne Adjetey. Sannan ba'a samu kuɗin ba don a inda aka same shi bindiga kawai aka Samu sai kwalaban giya.
Wannan labari ya kara ma sifeto daraja a idon al'ummar Kasar Ghana don ganin da shi aka fita ofireshon. Shi kuma Adjetey ya isa Zangon Qahɗaanie kamar Yanda Amir ya umurce shi.
***
Wanka ta fito cikin sauri kasancewar ta yi latti, tana yi tana kallon agogo hakan ya sa ta zira doguwar riga baki mai filawowi a jikinsa. Karamin hijab ta sa wanda iyakarsa hannunta ruwan ganye wanda ya shiga da wasu daga cikin filawowin jikin rigar. Tsaraban Mahaifin ta ne daga zaria ɗinkin hazikin ma ɗinkin hijabi baban sadiya mijin sadiya. Duk ta sanya hijabin nan sai an faɗa mata yanda hijabin ya fito da ita ya bayyana kyawunta, hakan ya sa ta aika masa da kuɗi ya ɗin ko mata kaloli daban daban har guda goma.
Bayan ta gama ne ta tsaya gaban doguwar Madubin ta da ya kai tsawon ta, duk da kasancewar ta doguwa, doguwa da ta kasance doguwa don ita mace ce. Fara ce tas, saboda jinin Fulani da Larabawa da ke yawo jikinta, kirjinta a cike yake sannan tumbin ta a shafe yake, tana da mazauna daidai misali duk da cewa siririya ce sosai.
Gashin kanta a dunkule yake yayi tuntu, hakan ya sa hijabin ya ɗan dage ta keyarta ya zama wani nau'i ma. Kwalliya.
"Abie na shirya ka min addu'a" Ta faɗi yayin da ta iske iyayenta na yin kalaci
"Kin yi kyau sosai yar albarka, Allah shiga tsakanin ki da magauta, ki dawo cike da aminci kinji" yace yana mai yin musabaha da ita.
"Ummie! Mamie!! Ammie!!! Na wuce, se na dawo" Ta ce tana mai shirin fita
"Yaya Fatima ki dawo da wuri don Allah, za a zo gaisuwa daga gidan su Sufyan, ba zan so a zo ba ki ba" cewar zubaida kanwar ta na wajen biyar sannan babban yar Ammie.
"MaashaAllah, ana gama meeting zan dawo Insha'Allah. Ki ce za mu sha biki" tace tana mai cike da murna.
"Ai kam de, tun da manya su yafe girman su gara kanne su yi su yi, kannenki uku na ɗakunan su amma ke ko kunya ba kyaji" cewar Mamie kai tsaye, fatima ba ta tanka ba ta sa kai ta wuce makaranta abin ta.
Assalamu Alaikum warahmatullah
Da fatan kuna lafiya. Exams time table is out, 2 more posts before the date Insha'Allah. Se kuma 13th December da zan gama Insha'Allah from then daily updates if my thesis permit.
Don't forget to vote, comment and share
ﺃﺣﺒﻜﻢ ﻳﺠﺮﻱ ﻓﻲ ﺩﻣﻲ 😘😍💞💕
Bin ta su ka yi da kallo har ta ɓace ma ganin su. Nan su ka ji karan tashin motar ta kirar vibe, sannan Alhaji Yahuza ya maida kallon shi ga matansa
"Duk wata wacce ta sake goranta ma ɗaya daga cikin ya'ya na gorin aure toh a bakin aurenta da ni, ko da kuwa ita ta haifi yar, ko da kuwa a bayan ido na ne, in ta rufe ta kwashi zunubin zaman zina ita kaɗai.
Rawa ake ma Allah ya sa mutum yayi aure? Na tabbata da rawa ake da dukkanku na gidajen iyayenku ba aure. Kun fi ta son taga tayi aure ne? Ba Za ku sa ma yata damuwa ba, in ba zaku bi ta da addu'a da fatan alkhairi ba toh ku kyale min ita" yace rai a ɓace
"Amma Alhaji haka za'a sa mata ido tana haɗa kafadu da mu" mahaifiyarta tace tana mai jin haushin yanda yake ɗaure ba karya kugu
"A'a, sa ta zamu yi a gaba ta bi duk samari da mazan aure da suka bata sha'awa tana rokon su arzikin zuwa neman aurenta. Ko so kuke in ɗauki hoton ta ina yawo masallaci mai so ya zo ya ɗauka.
Ko yau ta rasu bata ci baya ba, ba haka aka so ba amma kuma alkhairi ne gareta don ina da tabbacin ba ta taɓa zina ba. Wasu ma sun haifa sun yar an kuma aure su balle nawa kintsatssa" Ya ce yana mikewa haɗe da kakkabe riga
"Alhaji toh wa ye yayi haihuwan gaba da Fatiha, ni dai na san duk a ledan mu ka auro mu balle ka saki magana" waigowa yayi duk da ya san ita kaɗai ce zata iya maida masa amsa ta kwana lafiya shi ya sa a hali irin haka take shigar ma abokan zamanta fada ko da kuwa ita aka cuta.
Sai da ya kare ma dukkansu kallo sannan yace;
"Ke dai kin san kan ki, ko da yake kila ma ba ki san kanki ba bare saura" Nan ya fita ya barsu duka kamar ruwa ya cinye su. Kowannensu da abin da yake sakawa a rai.
Makarantar su fatima ya isa nan ya iske sun shiga taron,jira yayi har su ka kammala.
Tana fitowa tayi arba da shi, nan ta nemi duk wani damuwa ta rasa, fuska yalawace da fara'a ta iske shi
"Abie Allah ya bar min kai" Ta faɗi cikin farin ciki.
"Aminin kwarai ke saurin isa ga amini lokacin da wata damuwa ta samu amininsa, a ina zamu zauna ko mu karasa wajen cin abinci ne" Ya ce yana daga mata gira
"A'a mu je lambun fada" tace tana jin farin ciki na wanke bakin cikin da ta fito gida dashi.
Tafiyar minti ashirin ya sada su da lambun fada, suna yi suna tsere tsakanin su don kowannensu a cikin motarsa yake.
Lambun fada babban waje ne da ya kunshi ababen shakatawa tun daga furanni, tsuntsaye da saiwa kala kala. Lambun ya kasance daya daga cikin abin da Daular ke samun kuɗin shiga don in zaka shiga wajen sau ɗari a rana duk shiga sai ka yanki tikiti na nutud hamsin.
Sannan duk wani abin lashe baki da ake siyarwa a waje daga aljihun masarauta ne don haka riban na amfanin al'umma ne.
Bayan sun zauna aka kawo musu abin taɓa ka lashe ne ya kalle ta yace
Add
" Faɗa min damuwar ki, na san kina ta tunanin wacce za ki kai m kukan ki ne ko" Ya faɗi yana dariya
"Abbie aure nake so, babu wanda ya ke so na yanzu, duk masu zuwa min da an kwana biyu sai su nemi yin zina da ni, Abbie kallon wata mai nakasa ake min saboda rashin aure" Ta ce tana hawaye
"Toh fatima kina da karfin chanza kaddaranki ne, ko masu miki magana da habaici suna da ikon chanza kaddaranki ne? Damuwa ba abin da yake sawa sai cuta ba ya biyan bukata.
Ina so ki sa a ranki duk abin da yake rabon ki ba zai wuce ki ba, abin da ba rabon ki ba ko kinyi zina ko kinyi tsafi ko me za kiyi in dai ba rabon ki bane ba zai zo miki ba. Ki yi hakuri" Ya ce yana lallashin ta
"Abbie shi ne aka ce ko zan samu masu ruqya ne su min ko a amso min rubutu saboda aljanu na hana aure" Ta sake faɗin haka cikin marairaicewa
"Subhanallah! Fatima kada ki ɓa ta imaninki, su za su sa Allah ya aurar da ke in bai so ba? Shi faFA'ALLUN LIMA YURID ne, kada ki yarda a maida ki hanyar yin kuɗi, garin haka a yayimo miki muguwar fata.
Ba kya yin azkar ɗinki ne?
" Abbie ina yi kullum,safe, maraice, bayan sallah farali, na barci, na tashi daga barci duk ina yi"
"Toh kenan kina yi ne ma fashion ba wai da imani ba, don in kina yi da imani kin san kin fi karfin duk wani mai sharri don kariyan Allah ke tattare da ke, in haka ne babu wani dan 419 da zai ci kuɗin ki. Kwantar da hankalinki babu jinkirin da ba alkhairi ba, kuma ana yin auren masu gulman kin ki aure za su fara hassadan jin daɗin da kika iske a gidan auren. Almuhim ki tsare mutuncin ki, wanda bai aure ki ba don baki ba shi jikinki ba toh ko kin bashi ba auren ki zai ba" yace yana mai kara mata kuzari
"Abin ne yana damu na, tun ba in naga yara da ya'yan su ba" tace cikin karaya
"su kuma suna sha'awar ki ba, abin da baki sani ba wasu sun yi Dana sanin aurensu sau Bila adadi, ke dai kawai ki roki Alkhairi Insha'Allah zaki manta anyi wannan. Ki kara hakuri kinji, Allah ya miki albarka ya sa ki dace kin ji" yace nan su ka zauna jugum
"kin san kafin na auri Ummie sai da na yi soyayyar shekara biyar da Ammie. Soyayyar in ba ke ba sai rijiya ɗin nan" Ya faɗi yana dariya. Itama dariyan ta yi tare da maida hankali gare shi cike da son jin labarin
"zan iya cewa ita ce masoyiyar farko, in kika ganta lokacin kamar kada kuda ya taɓa. Hakan ya sa mu ka buga gasa da manyan mutane ciki har da Saifullahi Alhamze"
"wanene Saifullahi ɗin"
"Au Amir Alnasarie, kwatsam sai ya aiko ma Marigayi alhaji da sakon in har yana son ya sake haihuwan wani Yahuza toh in cigaba da neman Amina. Nayi kunci kamar ba zan rayu ba can dai na hakura don dole, hakan ya sa ido na ya gano ummi, cikin ikon Allah a cikin wata uku mu ka yi aure.
In kika sa ma ranki dole-dole sai miji iri kaza, toh ba za ki buɗe zuciya ki karbi zaɓin Allah ba, ki maida zuciyar ki ba kowa se abin da Allah ya azurta ki dashi" haka ya cigaba da mata nasiha har sai sai da aka kira azahar. Sannan su ka shirya su ka tafi gida zukatansu fal da farin ciki.
***
Sai bayan isha'i sannan Adjetey ya isa Zangon Qahɗanie. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ganshi gaban Amir. Tsugunawa yayi ya gaida Amir cike da ladabi. Maimakon ya amsa sai dagewa yayi ya kwashe shi da mari, bai farfado ya sake jin saukan wani marin, sai da yayi masa sau biyar sannan ya ɗago ya rungume shi.
"Ba ka jin magana, ɗa na, me ya kaika? Yaushe rabon ka da ganin shugaba a wajen sana'a? Sanda na so ka da aikin lawyer ki kayi. Shi lawyer in de yana rike da bakin jakarsa zai yi fashin kuɗin da yan fashi ɗari da bindigogi ba zasu iya samu ba, lokacin ka tsallake ni kace kaji ka gani. Zan ba ka uzuri, amma dole ka bi umurni na a karo na karshe, za ka zauna anan har ka yi aure kuma za ka koma makaranta.
"Abin da ka zartar Shine daidai gare ni, ba zan musa maka ba., zan ci gaba maka Biyayya matukar ina da sauran rai a jiki na" yace yana mai kara rusunawa. Take soyayyar sa ya cika masa da yana son mutum mai biyayya kamar yanda yake son mai gaskiya.
A titi ya tsinci Adjetey lokacin bai wuce shekara takwas ba, kishiyar uwa ta sako shi gaba da duka duk ta farfasa masa jiki da igiyar rediyo. Tausayin sa kwarai ya shige shi lokacin da ya samu labarin rasuwan mahaifiyarsa da kuma ukuban da ya ke sha hannun kishiyar uwar. Hakan ya sa ya sallama ma mahaifinsa ya ce da shi cikin ɓacin rai
"Ai duk kiyayyar da ke tsakanin ka da uwar yaron nan, tun da ta mutu ya ci a birne ta da kiyayyar amma wannan ba ka tsoron ya girma ya zama ajalinka" shiru yayi yana kallon karfin halin Amir, mutumin da bai sani ba har yake da karfin halin bin sa da muguwar fata.
"Ka bani shi in baka so, yanzu in kai ma matata shi dama zaman garin nan kewa na damunta" Ya kara yana sakin fuskarsa.
Malam kofi Mahaifin Adjetey bai amsa ba iya ya koma cikin gida sai ganin sa yayi da kayan Adjetey su ka yi ya watso musu
"Ban taɓa ganin ɗan da zai tona asirin uban sa ba se tsinanne, ka tafi da shi la'ana biye da ku" Ya faɗi a tsiyace
"Alhamdulillah! Amma sai ka zo da kukanka kana neman ya dawo gidanka nan ne kuma baka isa ba" Ya fadi yana rike hannun yaron da kaunarsa ke shiga zuciyar sa kaɗan kaɗan.
Maimakon ya kai shi gidansa kamar yanda ya alkawura sai ya kai shi makarantar kwana a jihar iko na Nijeriya, nan kuma ya sa masu kula da shi cikin wa'inda hurdan arziki ya haɗa su. Hakan bai hana masa zuwa duba shi ba duk bayan wata uku kuma duk su ka haɗu sai ya tuna masa da mahaifinsa da ce masa
"ka dinga sa mahaifiyarka a addu'a ta rasu lokacin da ta fi sonka, sannan mahaifinka Allah kare shi daga sharrin asiri don farraqu aka muku" tun baya iya gane mai kalmomin su ke nufi har ya fahimta.
Bayan ya kammala karatun sakandire ya nema masa jami'a anan ne ya ki karatun ya ce sana'a zai yi, Aamir yayi yayi amma Sam bai bi ta kansa ba, wajen neman sana'ar ne ya zaɓi sata don a cewarsa yafi komai kawo kuɗi sannan ya fi komai sauki. Za'a iya cewa ya faɗa harkan a sa'a don ba'a daɗe ba ya gina gida mai kyau a kasar sa na gado a kuma shiyar da aka birne mahaifansa, uban sa kuwa ya zama bai da bukatar komai don dan sa ya kudanye.
"Zan tura ka Kasar Masar ka karanto shari'a, don ina ji a jiki na saura Kiris daula ta dawo hannun mu. Sannan zan nema maka aure tare da matar ka za ka wuce" Aamir ya ce kai tsaye bayan ya gama tuna haɗuwar su
"Allah kara girma, ina godiya" faɗin Adjetey, a haka ya bar Amir da tunanin yanda zai fara abin.
***
Tun bayan dawowarsu yau kwana goma kenan ba su samu damar kebancewa da uwayensu ba sai daren yau, shima ba su shigo gidan a tare bane kamar yanda su ka saba sai kowannensu ya fara da ɗakin mahaifiyarsa.
Ummou Hafsah (suna kiran su da Ummou ne don matan shugaba uwaye ne ga al'umma) ta hakince zaune ko da ya shiga, da ido ta yi ma masu mata hidima alamun su ba ta waje don ta daɗe tana so ta kebe da ɗan ta.
"Kai na rasa gane maka, Sam ba ka da wayau, shi ya sa mai martaba ke kokonton ɗaura ka a matsayin mai jiran gado duk da kasancewar kai ne jinin sarauta gaba da baya" tace tana aika masa da harara ganin ya fara canza fuska
"Ummou kin san dai AbdoulHalim bai da amini sama da ni, son da ya ke min ya sa bai taɓa yafe abin da aka min na ɓacin rai, ni ma ina son ɗan uwa na" yace yana zumburo baki
"Toh tunda haka ne ka je wajen Mai girma ka ce ka yafe ma AbdoulHalim sarautan" tace tana gyara zama tana mai jingina a jikin filo da aka sa mata.
"Ai ni na fi cancanta in zama Sarki, ke ce fa uwargida, kawai dai ya riga ni zuwa ne amma ai ni ya kamata na zama babba, kuma.. Kai! Ba ma zai iya mulki ba, ni na san rauninsa" yace yana jan tsaki,
"Ai naji labarin kyautan kuɗi kake don talakawa su so ka, abin da baka sani ba, babu butulu azzalumi kamar talaka kana masa arziki ne yana neman nakasa ka. Zan tura ka wajen Baffanmu, kawu mahaifi na ne kamar yanda yake ɗan uwar mahaifiyar mai girma. Can yankin zango ka nemi Aamir Al'ansarie shi kaɗai zai cika maka buri AbdoulHaseeb.
Ina sane na ce ka karanta military science, don na san za ka koyo dabarun mulki da yaki, shi ma wannan din shawarar Aamir ne. Kuma bakinka alaikum, tun ba shegen nan dan mabarata AbdulBari, wallahi shima kujerar yake hari" a haka ta cigaba da kintsa masa son mulki tare da cusa masa kalolin makirci da zai iya amfani ya ci nasara.
***
A gajiye AbdoulHalim ya karasa wajen mahaifiyarsa Ummou Maryam. Tana karatun Kur'ani ko da ya shiga, sai da ta kai aya sannan ta tsaya ta yi addua su ka shafa sannan ta Kalle shi.
"Kayi girma sosai Yaro na, duk na Kalle ka sai na kara gode ma Allah da bai bani kai ba da wayau na ko dabara ta ba" nan ya fara wangale baki kan shi na kara girma
"Sai naga baka zaɓi ɗaya daga cikin zaɓin mai martaba ba" Ta ce tana kallon idonsa
"Toh ni da bayi aka ce an kawo min da na zaɓi goma su ta min hidima..." saukan carbi ya sa shi yin shiru .
"Allah Ina son yar gidan sarautan da duk duniya aka san da su ba wai kasashen kewaye da mu da yan siyasa su ka fi sarakunan su daraja ba. Zan iya samun bugun zuciya in aka ce da ni wani gwamna ya tsige baban matata daga kujerar sarauta" Ya ce yana kwanciya a gefenta.
"Wai Halim kana da aiki, ni fa mahaifi na yantaccen bawa ne, kuma yancin sa ne sadaki na, ka ga tun wuri ka rufa min asiri ka cire duk wani ji da kai da ka aro, ka cigaba da addu'a Allah baka tagari, ya zaɓa maka abin da ya fi alkhairi, bana ma sonka da sarauta wallahi"
"waiyazubillah Kina neman kashe ni da raina wallahi, na ma fasa hiran da I Allah karanki zan kai wajen Allah kada ya amsa miki" Ya faɗi, iya gaskiyarsa. Taɓ yana babban ɗan mai martaba sannan ta ce wani ba zai yi mulki ba. Gsky hakan ba mai yiwuwa bane.
"Au wai abin har da kai kara ne, daga son ka da alkhairi. Toh yi hakuri sarki mai jiran gado. Allah ya ida nufi, oh ni maman sarki" ba shiri ta ji ya sure ta sama yana zagaye ɗaki da ita.
Dariya su ke cike da farin ciki. Duk suka shiga wannan dakin su kan manta da wani sarauta su ji daɗin rayuwar su don duniya basu da kamar su biyu.
Hira sosai su ka yi ya buɗe mata abubuwan da ya siyo mata wanda mafi yawansu zinariya ne da lu'ulu'u. Sannan ta shiga bashi labari cikin siyasa tana sako masa illar girman kai ga musulmi amma jin ta kawai yake a rana yana faɗin "wanda ba jinin sarauta ba beyi ba, kawai mutum yayi ta rayuwar kaskanci"
Haba Haba Haba ghosties, kun kyauta kenan Ace ratio din readers and votes is 5:1,wallahi duk na gani se inji sanyin jikin typing duk yanda na so na muku kuwa. Any way, in tafiya yai tafiya a hakan I will quitely unpublish the story.
Ummu-Abdoul
Sun iso gida ana kiran la'asar, farali kawai su ka sauke aka cigaba da kiciniyar tarbon baki masu zuwa neman aure.
yana da ga cikin al'ada in za'a je tambayar neman aure a daular qahɗanie yin gagarumin biki, dangin amarya kan yanka dabba a bankare ayi balango da shi yayin da su kuma dangin miji za su taho da abinci nau'i nau'i, haka aka yi a gidan Alhaji Bello Yahuza.
Rakumi ya ba masu sana'ar nama aka soke aka gasa shi, su dai a gida an kawo musu shi a gashe ne. Amarya ta ci kwalliya, dangin mahaifiyarta duk sun hallaro na nesa da na kusa kowannensu sai murna su ke.
Fatima ba ta ɓata lokaci ba, tana idar da sallah ta fito sanye cikin doguwar riga yadin yan India (Indian material) ruwan yara (baby color) da ratsin ruwan coffee. Kayan ya fito da ita, ba za ka Kalle ta kace yar shekara ashirin da takwas ba ce don fuskanta sheki yake kamar wata a daren goma sha uku.
An fara taron cikin kwanciyar hankali, masu bincike sun ba da shaida akan Dukkansu nagartattu ne kuma sun dace da juna a matsayin mata da miji kamar yanda akan yi wajen tambaya.
"Tun da an dace, nan da wata bakwai za'a ɗaura aure, zuwa lokacin ta shiga ajin karshe na sakandire" faɗin Alhaji Mus'ab Yahuza waliyin amarya.
Nan duk aka dinga addu'a da fatan alkhairi ga maauratan har ma da iyayensu.
"wai Ke Amina an ce miki ana biye ma binciken kwamitin aure ne, in sun yi na su ku a matsayin iyaye ai ya kamata ku yi na ku, amma kun bar musu su kaɗai, su suka haifa miki. Ko kishiyoyin ki ka biye mawa in har su suka zuga ki" cewa yayan Amina da ke aure a Nijar.
"A'a yaya kada ki musu sharri, ni ce dai na ki yarda zancen su don gani nake bakin ciki su ke min, faɗin farko ita Hajiya Sadiya ta ce wai ai zubaida ta yi kankanta shekara goma sha biyar, ita kuma uwargida Hajiya Hafsa ta bincike ta bullo kin san duk su na da yayyin zubaida a gaban su, ita Hafsa akwai fatima da take babban yar Alhaji sannan da wasu" Ta faɗi tana zumburo baki.
"Toh Allah sa Abdullahin kwarai ne, amma yanda zamani ya canza sai da bincike in ba haka ba ka ɗauki yarka ka kai gidan da za'a kuɗi da ita"
"A'a yaya ayi zato mai kyau, in an yi tunanin alkhairi sai kika ga alkhairi ya tabbata in anyi tunanin sharri kuma se ya bi ka" Ta ce a kufule tana mai jin haushi, a zuciyar ta kuwa mamakin yanda jininta ke mata bakin ciki take.
"Allah baki hakuri ya sanya Alkhairi". Haka dai su ka rabu kowa da abin da yake sakawa a ransa.
***
Farin cikin da zubaida ke ciki baya misaltuwa, don har mamaki dattawa su ka dinga yi yanda yarinya karama ta kosa ta yi aure, wasu ba su ga laifin ta ba don a cewar su zamani ne, da yawa kuma gani su ke akan me za ta bayyana farin cikinta, abin ta shiga zulumin abin da za ta tarar ne.
Tun da aka kamalla take manne da Fatima kasancewar jinin su ya haɗu sosai. Tare su ka yi sallah, bayan magriba su ka yi azkar dinsu har aka kira isha'i, nan su ka gabatar da farali sannan su ka zauna. Take wayar zubaida ya ɗauki kara, cikin mamaki Fatima ke kallonta, don ba ta taɓa sanin tana da waya ba.
"Shine Kaki zuwa, ni fa na matsu in ga fuskan mijina uban ya'yana. Ace har ayi wannan gagarumin taron da ya shafe mu baka zo ba" faɗin zubaida wanda hakan ya sanya ta sakin baki tana kallonta, ba sun ce yaron kawar Ammi ba ne da yake karatu a Ghana, ko da yake kila tana nufin ta daɗe ba ta ganshi ba ne, amma kuma ko shekaran jiya na gansu tare. Duk fatima ke wannan tunanin don kawai sai jikinta bai bata ba. Ba Ta gama farfadowa ba ta ji tana faɗin
Add Vote
"Don Allah ka turo min hotunan ka don in ga da waye yayanmu za su yi kama, ka ce min kana kama da mutan Ghana da Nijeriya, ance a duk bakake babu wa'inda su ka kai yan Nijeriya kyau, ka ga kenan black beauties zamu haifa" Tayi shiru tana saurare, sai tayi dariya abin ta sannan ta ce
"wallahi na kosa in ji wannan nauyin naka da kullum kake faɗi" ai kam take a wajen Fatima tayi mutuwar zaune, zubaida da a cikin set ɗin su don su uku aka haifa, ita ce karamar su sannan kuma ita ce mara wayau a cikinsu ashe dai kallon kitse ake ma rogo. haka su ka cigaba da kalamai wasu ma sun girmi kunnuwan Fatima amma ta d'aure don ita da girmanta ba ta san da su ba.
"Zuby ban gane wayar nan da kika gama ba, kamar na ji kina fad'in ba ki ta6a ganin Abdullah ba, ka da fa ki yi saurin yanke abin da za ki zo kina da na sani, shi aure da kike gani duk ya fi karfin tunanin wanda bai shiga ba, karance-karance da kallace-kallace da jin dukkan labarin aure bai isa ya ba mutum muk'amin zama mai aure ba. Saboda haka yanda aka shimfid'a miki aure ba lallai ki iske shi a hakan ba, za6in miji ko mata shine za6in da mutane ya kamata su fi maida hankali akai don za6i ne da in mutum ya kuskure toh kamar ya d'auki almakashi ne ya yanka rayuwarsu zuwa kashi biyu. Ki kara bud'e ido ki farka da ga magagin da kike yi" tace mata , yayin da Zubaida ta turo bakinta kamar na shamuwa, zuciyarta na tafasa don gani kawai ta ke hassada ce kawai ke d'iban yayarta tun da ta kasa auruwa. Haka ta fita ta bar Fatima da doguwar nazari. Tana cikin haka ne wayarta ta d'auki kara, ganin ba'kuwar lamba ya sat a yi saurin d'agawa don tana tsammanin kira daga wata kamfani da ke shirya magudanar ruwa don ta yi musu tsarin zamani.
Da sallama ta amsa wayar ga mamakinta sai ta iske muryar da ta sani ne, amma ta kasa gane wanene mamallakin muryar.
"Don Allah wa ke Magana?" ta fad'i bayan doguwar gaisuwa
"Lallai ne ma Batula, watau kin ma manta ni kenan, ba ma ki da lamba ta, na gode daman a ji an ce ana bikin tambaya a gidan ku ne na kira na taya ki murna" ya ce yana dariya
"Ayya ai kuwa na gode , a gaida iyali duka" t ace tana ajiye wayar. Ko da ta hau shafinta na whatsapp nan ta iske sallamar sa tare da hotonsa ya turo, nan din ma dariya kawai tayi ba tare da ta tsawaita zance da shi ba. Da ga haka kuma ta sauka ta cigaba da abin da ke gabanta.
***
Washe gari tun da safe ta kama hanyar zuwa wajen aiki, hatta abinci bat a wani natsu ta ci ba saboda tunaninta gaba d'aya na ga aikin da za ta yi. Ta dukufa tana aikinta kira ya sake shigowa wayarta, kallo d'aya ta yi ma kiran ta kad'a kanta don bat a san mai ya ke nema daga gareta ba. Hakan ya sa ta kira abokinsa da yake d'a ga baffanta ta ce mace masa Khuder ya kira ta, amma ga yanda su ka yi da khuder d'in, nan ya fara dariya y ace
"Lallai mutumin nan da gaske ya ke, don satin da ya wuce ya ke ce min yana so ya k'ara aure, kuma masoyiyar asali zai aura ba wai wata sabuwa zai nema ba, ki bashi dama mu ga inda ruwansa zai tsaya" haka ya cigaba da bata baki har ta fara jin burbushin sonsa na dawo mata a cikin zuciya. Ba ta tashi daga aiki ba sai da ya su ka yi waya mai tsawo, duk da bai furta mata kalman so ba ya bat a alamun da su ka fad'I son ta yake ko aurenta ya ke shirin yi.
Da farinciki ta isa gida, Allah Allah ta ke ta ga mahaifinta don ta fad'a masa cigaban da aka samu adduar su ta kar6u amma sai ta iske ya je taro da mai martaba sarki, ko da ya dawo kuma ta riga ta kwanta saboda gajiyan da ke tare da ita.
***
Cikin sati biyu sun shaqu sosai, duk da ba wani zancen soyayya ce tsakaninsu ba, amma suna nuna tsantsan kulawa ga junansu, da anyi sallar isha'I su ke sallama saboda gudun shiga hakkin matarsa don ita Fatima ba ta son abin da zai ja ma'aurata yin rigima ko samun matsala saboda ita. Shima kasancewarsa mai daraja iyalinsa ya sa shi ganin dacewar abin da ta tsara.
Add Vote
Yau ma kamar yanda su ka saba sun yi sallama da Khuder gaf da zai shiga gida daga sallan isha'i. Sun dade su na hira a falon su yayin da su ke kallon shirin da ake a gidan talabijin d'in Qahd'aanie ta jiyo wayarta na kuka, hakan ya sat a shiga d'akinta don agaza ma wayar , nan ta iske Khuder ne mai kiran tayi mamaki sai kuma ta yi tunanin ko ya fita ne, maimakon ta maida kiran sai ta neme tayi tunanin nemansa a whatsapp, hawanta ke da wuya ta iske sallamansa.
Bayan sun gaisa take tambayar me ya hana masa barci kuma mai ya kaishi nemanta da dare bayan ya san baya cikin yarjejeniyar da su ka kulla
"Wallahi na kasa barci ne sai tunaninki nake" aka aiko mata, nan dai ta yi dariya kawai. Daga haka ya cigaba da turo mata sakwanin soyayya da kalamai da har sai da ta maida martini don a yan kwanakin da su ke Magana sosai ta ke jin sa a rai don ko a da ba wai bas a son juna ne ya sa su ka rabu ba, dalili dai da kuma barin halas don kunya a wanan lokacin ya sa, yanzu kuma da komai ya zama tarihi sai ta ke ganin in anyi ai ba wani abu bane.
"Sweet yaushe za mu had'u ne, mu tsaida Magana" ya turo mata
"ko yaushe ka ce ni ina gida" ta maida amsa
"A'a ni dai mu fara haduwa gobe a lambu, karfe goma mu yi maganar daganan sai a zo ayi maganar da zaa yi akan mu ko ya kika ce" ya turo
"Allah ya kaimu" da haka su ka yi sallama ya na mai cikata da daddadan kalamai da ta so ace a waya ne aka fada mata don za su fi shigan ta jinni da 6argo.
***
Washe gari kwalliya na musamman ta yi, ita kanta ta san ta yi kyau, leshi ta sa mara nauyi da ya sha d'inkin doguwar riga irin na zamani ruwan gwal, sai ta yafa mayafi kalan maroon, takalminta ma hakan jakar ta kuma dan posa ta rike ruwan gwal . nan ta firo kamar wata amarya, bata fadi ma kowa in da za ta ba duk a tunaninsu wajen aiki za ta je kamar kullum saboda sanin da su ka yi ita d'in ba mai yawan yawoce yawoce bane.
"Kin yi kyau sosai Ya ta" cewar Ammi da ta gani a haraban gidan, dariya kawai tayi don tana mamakin kirkin da Ammi ke mata yanzu ba tare da tsangwama ko cin fuska ba.
Ta isa Lambu saura minti uku, nan ta sa waya ta kira Khuder, bayan sun gaisa ta ke tambayar sa y a aka yi ta riga shi isa, amsar sa ya sata mutuwar tsaye, cikin motarta ta shiga ta ce
"Ban gane ina ba? Ka sa ni zuwa Lambu kuma ka ce min ina?" ta ce cikin alamun fushi fushi
"Au toh ban sani ba ko ba ni za ki kira ba, Khuder ne fa nan" y ace yana mai mamaki don bai iya tuna an yi hakan ba.
"Ok , hau online in nuna maka" ta ce ranta duk a 6ace. Ba tare da 6ata lokaci bat a tura masa duk zancen da su ka yi da dadare, karkade kai yake kamar kadangare don ya san aikin matarsa ne, nan y ace, afuwan ga ni nan zuwa dama tsokanar ki zanyi, a ransa yana tunanin me zai ma matar ya huce, haba shi yasa ta nemi izinin zuwa gida yau .
Fatima na ajiye wayar ta ji an kwankwasa mata gilashin mota, ganin macece ya sa ta bud'e gilashin motar yanda za su iya Magana.
"Fitowa za ki yi Fatima" ta ce mata tana murmushi, ganin haka Fatima ta fito kan ta tsaye ba tare da wani dogon tunani ba.
"Shegiya Karuwa mai bin mazan aure, dama so nake ki fito duniya ta ganki, wato ke jiya kin wani bi min miji kin kalailaye ko , toh da ni nan kika yi chatting kuma wallahi sai na wulakanta ki don ki san illar karuwanci" ta fadi bayan Fatima ta fito, nan ta cika da mamaki don kuwa ita ba ma iya tuna wani chatting ta ke Magana ba.
"Kin tsaya kina kallo na ne , wallahi yanda kika shigo min rayuwar aure na yi bakin ciki ke ma sai na sa miki bakinciki, shegiya mai bin mazan aure, karuwa, mazinaciya yar iska barauniyar miji kawai, ni na hana ki aure da za ki bi min miji, wallahi tsirara zan miki anan yar iska" tana fadin haka wasu matan su ka fito su ka janye gyalen Fatima, wata ta janye mata d'an kwali yayin da wasu ke jan rigarta da sunan yagawa. Ko motsi Fatima ba tayi ba sai rufe ido tayi tana addua a ranta, tana mai jin zafi a zuciyarta.
Saukan marin da ta ji ne ya sa tayi saurin bud'e ido, Abdul Bari ne da wani wanda bata sanshi ba amma akwai d'an kamanni na jinni a tsakaninsu.
"Zan ci mutuncinki kuwa yanzun nan, Yar iska, har ke kin isa ki d'auki hukunci a hannu? Me ta yi miki da za ku dauki hukunci a hannu?"
"A'a yarima da ka bari ta min maganin yarinyar nan it ace n ace maka ina so ka sa a sato min ita" nan ya mai kallonsa ga AbdulBari da ke maganar ba tare da ya ji wani bakincikin abin da aka aikata ba.
"Mijina fa take soyayya da shi, shine na dau wayarsa mu ka yi chatting har mu ka ce mu had'u anan, ni miji na ni kadai zai yi soyayya, ku bar ni na kasha shegiya" ta fadi ido rufe tana matsawa kusa da AbdulBari
"Ke! Ko Ubanki waziri bai isa in yi Magana ya maida min da martini ba balle kina ganin d'an uwanki zai kwace ki, nan ya sa aka rufe gate d'in lambu aka hana kowa fita sannan ya kira ma'aikatar ba da iskar netwrk ya sa su janye netwrk gaba d'aya don yana son ya fara kaddamar da mulki tun a lokacin. Tsallan kwado ya sa Yan matan da ita kanta har sai da ya ga dagaske sun jigata ga su dai yan hutu tun da suka diro duniya ba su taba fuskantar ko wani irin horo ba balle a ce, sanna ya sa aka kawo masa yan sanda su ka tafi da su don a kulle masa su, sannan ita kuma Fatima ya yafa mata mayafinta ya ce ta shiga dayan barayin zama ya shiga gefen direba ya ja ta su ka tafi sai kuka take tana mai gode ma Allah.
"Ni fa bana son kuka, ina son mahaifiyata kamar rain a shi yasa na ke da tausayin mace, zan kai ki gidan kakata da ta haifi mahaifiyata saboda ki samu natsuwa kafin ki isa gida, zan tabbatar da an bi miki hakkinki kinji" ya ce yana mai tausayin ta.
"Ka kaini office dina kawai , ba matsala Allah ya saka da alkhairi" ta fadi cikin hawaye. Sai da ya kaita har office d'inta sannan ya fito ya gangara zuwa ofishishin shugaban sashin su ya sa aka maida shi fada.
DIN DIN DIN!!!
0 comments:
Post a Comment