Ko da su AbdulBarr su ka isa fada, sun iske shi cike da masu madafun iko, da gani su ake jira saboda daukewar network da aka samu ya kara hargitsa fada da tun bayan fitowar su yake a hargitse.
Karfe tara na safe Yarima AbdulHaseeb da yarima AbdulHaleem su ka iske AbdulBaari har gida don su fita rangadi da shakatawa, suna shirin shiga mota wayar AbdulHaseeb yayi kara duba ɗaya yayi ya ga mahaifiyarsa ce mai kiran. Bai ɓata lokaci ba ya ɗaga cike da sallama da isar da aminci
"Duk inda kake ka zo ina son ganin ka, yau babu inda za ka je" Ta ce a tausashe. Hakan ya sa ya musu sallama akan mahaifiyarsa ba lafiya zai koma, duk yanda su ka so su bishi ciki ya ki tare da faɗin
"kun san dai tun da na dawo sau ɗaya na ke ɓace da ita, ba ku sani ba kila zaman yau ne na karshe duk da ciwo ba mutuwa bane" take zuciyar AbdulHaleem yayi baki, da Ace wani ne yayi ma Ummu wannan fatar da babu abin da zai hana ya sa a aika masa shi lahira, amma abin takaici ba cin kasancewarsa abin da ya fi so bayan mahaifiyarsa, sai kuma ya kasance ɗan wacce yayi ma fata, hakan ya sa bai sake gardama ba ya shige mota, AbdulBaari ma ya shiga ya ja suka fice.
"Ba na so ka fita a yi zargin ka, ka san cikin dare ka sami Baffa, toh ɗazu ya kira ni akan in saurari abin da zai faru a fada, ko ma menene ni da kai kada wanda ya bada goyon baya, mu nuna muna tare da fada sannan mu dinga sanar masa da duk wani motsi na sarki cikin sirri" Ta tare shi bayan ya iske ta a ɗakinta.
"wannan mai sauki ne, Allah ya kara girma da lafiya, in har na tabbata sarki, zan gina miki daula cikin daular Qahɗaanie, zan shayar da ke daɗin da duk duniya babu kamar sa sannan duk wani makiyinki sai na ɓatar da shi a doron kasa" Ya faɗi cikin sanyin murya mai cike da farin ciki.
"za ka fara da wancan kenan" Ta ce tana dariya, haɗe da nuna masa setin ɗakin Ummou Maryam.
"A'a Ummou wannan ba wajen zuwa bane, matar nan tana so na fiye da tunanin ki haka ɗan ta, saboda haka duk abin da zai faru toh kada a nemi kuntata musu, hakan zai bamu nasara in ba haka ba alhakin su zai kama mu" yace yana kallon idonta don ya ga reaction ɗin ta.
Haka su ka zauna su na hira har karfe goma sha ɗaya da minti talatin nan sai ga sakon kiran sarki. Gaban su na faɗi suka isa falon da ke manne da turakar sa inda ya ke ganawa da iyalinsa.
"Ya na ganka kai kaɗai babu ɗan uwanka, maza sa waya ka kira shi" sarki ya ce ma AbdoulHaseeb bayan duk sun mika gaisuwansu. Nan ya iske babu network akan wayar sa,
"Babu network, mai girma" Ya ce yana sunkuyar da kansa. Hakan ya sa sarki ciro wayar sa ta musamman don yin kira, nan ma ya iske wayam. Ba tare da ɓata lokaci ba ya sa jakadiya ta sauka ga sarkin gida ta ce ya isa helkwatan sadarwa ya ji dalili.
Bayan kamar minti talatin aka sanar da sarki ai AbdoulHaleem ne ya ba da umurnin a janye. Hankalin sarki ya tashi amma wani sashi na zuciyar sa na faɗi masa ya kada ya shiga umurnin nan. Take ya sallami jakadiya sannan ya kalli iyalinsa
"Wasika ne daga ɗan uwa na, baffan mahaifiyar Hafsa, sannan baffa na ne saboda da mahaifina da shi ya'ya maza su ke, kuma mun yi takarar kujeran nan da shi.
Ga wasikar nan AbdoulHaseeb ya karanta mana, sannan ya zama wakili ga sauran ya'yan gidan nan.
Aminci ya tabbata a gare ka mai Qahdaanie, na rubuto maka wannan wasika ne a matsayina na Baffanka, ba a matsayin ɗan kasa ba. Labari ya isko ni akan ka ba da kwamiti su zaɓi yarima mai jiran gado, ni kuma ina mai umurtanka da ka tsaida AbdoulHaseeb ya zama mai jira, saboda abubuwa guda uku
Start from the beginning
1. Ya kasance masoyin talakawa mai kyauta da son cigaban su.
2. Ya kasance mai kamala da ibada, ba wancan da ya ma baturiya ciki aka markade ba.
3. Jinin sarauta ne gaba da baya, da fatan baka manta wanda ya haifi Mahaifin Hafsa shine ɗan fari nine na auta ba sannan shi ya rike ni har ya aurar dani.
Saboda haka ka fara kallon Mahimmancin daga lamba na uku zuwa ɗaya saboda hakan na nufin mafi mahimmanci a ciki.
Wannan umurni ne kuma shawara ce amma rashin ɗauka na nufin maida Qahdaanie tarihi tare da maida ahlinta yan gudun Hijira a wasu kasashe
Saifullahi Alhamze
Aameer Al-ansarie
Ba sarki kaɗai ba hatta wa'inda aka yi don su sun kadu da kalaman wasikar, sarki dai bai nuna ba don tun da mai kawo wasika ya ce masa takardar don shi da iyalinsa ne kawai ya san da wuya in zai ga alkhairi a ciki.
"Ai wannan duk ba abin tashin hankali bane, shi AbdoulHaleem ya faɗa min baya son sarauta, shi ya sa ma ya zaɓi karanta Nuclear science and Engineering, don jiya maganar da mu ka yi shine tun da Haseeb dama military science ya karanta kuma shi ke koyar da dabarun mulki da yaki da komai, na ɗaura shi amai jiran gado ya fi dacewa akan a sa shi wanda kere-kere kawai ya fi ba da himma. Kawai abin da za'a yi kada ka amsa sannan kada ka sanar da kowa ga abin da aka yanke, hakan zai sa shi Ansari yayi ta tunane tunane. Sannan ya da wasikar take na kai da iyali kada majalisa su san da shi don makashin ka na tare da kai" Ummou Maryam ta faɗi hankalinta kwance, babu ko damuwa a tattare da ita.
"Ba Za ayi haka ba, shi Haleem shi ne babba, kuma ko da yaushe babban ɗa shi ne ke gadon mulki, ban ga abin razana a cikin wasikar da har za'a yi saurin mika wuya ba" Ummou Hafsa ta ce tana mai yamutsa fuska.
"Ka bani izini in je in sami Baffa, ya kamata a ajiye duk wani adawa a haɗa kai. Ni dai a bari mai rabo ya dauka, banga abin karaya da wuri ba kamar yanda Ummou ta ce" AbdulHaseeb ya faɗi har da hawayensa. Sarki dai bai ce uffan ba, har su ka gama gardamansu sannan ya ce
"idan ɗan uwanka ya dawo ka ce ya kawo min hujjan da zai hana in hukunta shi na sa a ɗauke mana network"
"Ranka shi daɗe ka yarda bai cancanta ba ko" faɗin Ummou Maryam. Murmushi kawai yayi sannan ya sallame su.
***
Sai bayan la'asar sannan ya gurfana a gaban majalisa, bayan ya mika gaisuwa ga sarki ya sunkuye da kansa yana jiran abin da zai ce.
"Kai mu ke jira, saraki" faɗin waziri ganin yayi shiru
"Cin zarafin wata baiwar Allah na iske a nayi a lambun fada, wacce na iske tana yi kuma takama da karfin mulkin mahaifinta take da kuma kusancinta da masarauta, gudun kada a hana min yanke hukunci ya sa na sa a janye network, yanzu haka tana tare da yan da ayi min afuwa ranka shi daɗe" Ya faɗi cike da biyayya.
"Wacece ita, wajibi a hukunta ta matukar ta tabbata mai laifi" jin waziri ya faɗi haka ya sa ya zauna ya feshe musu duk abin da ya faru da hukuncin da ya ɗauka. Nan su ka sanya salati tare da Allah wadai da kishi irin na wasu matan don kuwa ba kishi bane rashin hankali ne.
Bayan sarki ya sallame shi ya karasa cikin gida don duba lafiyar Ummou Hafsa, nan ya same ta kwance ana mata tausa, da fara'a ta amsa gaisuwar sa sannan ya karasa wajen mahaifiyarsa. Nan ya bata labarin abin da aka ma fatima ya karkare da faɗin
"wallahi na tausaya mata, haka nake jin kukanta har cikin raina, karantarwa take a jami'a, sannan da gani ba tayi aure ba. Ta birge ni ta kuma bani tausayi" Ya ce yana mai nuna alhini.
"Allah sarki, har ka sa min sha'awarta, ko za mu cusa masu haushi ne mu aure ta kawai, dama ni bana son ka yi aure gidan sarauta" Ta ce masa ganin yana ta nanata maganar cikin tausayawa da jin haushi
"Kai Ummou har yanzu kin kasa fara tunanin masu sarauta, mijin ki fa shi ne mutum mafi ɗaukaka a duk faɗin Qahdaanie ki sa na auri baiwa. Duk wanda ba jinin sarauta ba bawa ne a waje na kin sani" Ya ce yana kara kwanciya akan shimfiɗar da ta ke zaune.
"haka fa, karshen duniya dama baiwa zata haifi uwargijiyarta ko"ta ce tana murmushin jin haushi
" Yaa salam, wallahi ba nufi na kenan ba, Ummou kin kasa fahimtar inda na dosa, ni fa yanda nake ɗan fari kujerar nan fa ba zai wuce ni ba" Ya ce yana wasa da hannunta suna er tafawa
"Toh ina so ka zaɓa ko ni ko sarauta, kuma ba zan taɓa janye ɗaya ba, dole ka zaɓa kowanne ka ɗauka zan mara maka baya har ka kai ga nasara"
"Toh Ummou in dai haka ne, ba zan sake maganar ba, Allah sa haka ne Alkhairi" Ya ce yana mai share kwallan da ya zo masa. Take ta tausaya masa amma tana son sa da alkhairi ne shi ya sa.
"ka san kafin na auri mai martaba wa na so?" tace tana son ta dauke hankalinsa. A hankali y girgiza mata kai hakan ya sa ta cigaba
"mus'ab bn Abbas na so kamar rai, duk aka ce min Allah tabbatar da Alkhairi sai in ce ai shine alkhairi saboda ido na sun rufe akan lallai sai shi. Addu'a ta kullum Allah sa ni ce mace ta farko da zai aura amma inaa kullum kamar kara nesanta mu ake, har dai na hakura.
Wata rana ina zaune a shago sai ga yan gidansu sun shigo suna hiransa, anan na gano a she ɗan karya ne, ba abin da ya sa a gaba sai cin bashi. Albashin sa kusan nutud dubu ɗari huɗu ne don wajen karɓan haraji ya ke amma bai da gida, bai da ko keken hawa sai abokantaka da manyan masu kuɗi.
Ana haka sai na ga ai soyayyar asali shine in gyara shi y shiryu sai kawai na koma ruwa a sonshi, in faɗa maka na ji jiki sosai wallahi kuma ba nasara. Kwatsam rannan na hango shi, sai na fara auno wahalar da zan sha in har na amince na aure shi, kawai sai na koma da dukkan lamurana zuwa ga Allah, ba'a yi wata uku ba sai ga mijin da dukkan mata ke Mafarkin samu, shekara biyu da aurenmu ya hau karagan mulki.
Kenan abin da Allah ya tanada maka yafi alkhairi akan abin da ka so ma kanka. Yi tunani akan Fatima, ban ce ka nemi shawara ba. Duk abin da ka yanke shike nan" Ta karasa tana ɗaga masa gira. Nan ya sa dariya. Cikin barkwanci ta bashi lbrn wasikar da k aiko ma mai martaba. Dariya kawai yayi ya ce
"Ai ke na zaɓa, kuma ke zan zaɓa ko menene kuwa aka haɗa zaɓin sa da ke" Ya ce yana mai kara Mike kafa. A haka su ka cigaba da hira har aka kira magriba.
***
Fatima tun bayan fitan AbdulHaleem ta zauna akan kujera ta shiga rera kuka har sai da ta gaji don kanta. A duk lokacin da aka ɓata mata rai ba ta da abin da ke saukar mata shine ta zauna mahaifinta ya karanto mata tarihin su, tun daga tushe su. Hakan ya sa ta yi tunanin yin abin da ba ta taɓa yi ba ita kaɗai watau to.
Stop being angry at your mom just because she says stuff that no one else does. Remember that she does things for you that no one else ever will. That’s what I’ve learnt when I’ve looked back at my childhood.
Thanks ma, happy birthday.
A shekarar da aka kafa makarantar koyor da boko na farko wato shekara ashirin da tara bayan an kafa daular Qahɗaanie, a shekaran ne aka samu wasu baki yan Hijira daga yankin Adamawa. Mai gida ne da zuri'arsa nan suka nemi iso wajen sarki imam Abdulhamid.
"Marhabanbikum" Ya faɗi ganin su farare kirar Larabawa
"Shukran Yaa Aamir" dattijon cikinsu ya faɗi
"Sunana Muhammad Sambo, Mun taso daga yankin Gongola ne, na kasance limami ga tsohon Lamido ya rasu wata bakwai da suka wuce sai aka naɗa ɗan shi, yana hawa ya sauke ni a matsayin liman kuma alkali ya naɗa wani, hakan ne dalilin da ya sa na yo kaura, na yaɗa zango wurare da dama kafin mu ka iso nan, ina rokon sarki da ya bamu wajen zama ni da iyali na har ma da dabbobinmu da su ka mana saura" Ya faɗi cikin ladabi duk da kallo ɗaya za ka masa ka san zai haifi sarkin.
"mu na muku barka da zuwa Qahɗaanie, mun ba ku yankin arewa da fada ka tare da zuri'arka da dukiyar ka sannan na sanya ma wajen Hilaalu Sambo. Gobe za ku fara gini kafin nan zan baku wajen zama na wucin gadi, da fatan za ku kammala wajen zaman ku kafin wata biyu ma su zuwa" da haka sarki ya sallame su, washe gari da sassafe maza daga cikinsu tare da wasu mazauna Qahɗaanie su ka taru wajen gini. Cikin ikon Allah sati daya bai shige ba aka kamala gidan, babban gida mai dakuna da sassa daban daban na shi da iyalinsa har da yaransa maza da iyalinsu.
A haka rayuwar mutanen Hilaalu Sambo ke ta tafiya ana mutuwa ana haihuwa, duk wani Fulani da zai yaɗa zango a Qahɗaanie toh a Hilaal yake sauka.
A mutu a haihu ayi aure a rabu haka dai har duk wa'inda aka kafa Hilaal da su suka rasu, ya'yansu ma haka har dai aka ai ga zuri'arsu ta ashirin da takwas a nan ne aka haifi Muhammad Yahuza, ya taso cikin gata da yan uwansa mata bakwai cur. Dalilin haka ya sa ya taso cikin gata duk da rasuwan iyayensa hakan bai sa ya san maraici saboda rashi ba.
Yana da shekara takwas a duniya ya yi saukan alkur'ani hakan ya sa su kayi tunanin tura shi makarantar koyon kimiyya. Ganin shi ke ci a Qahɗaanie kowa na son zama kwaro a kimiyya.
Muhammad Yahuza bai ba Yan uwansa kunya ba yayi karatu cikin nasara, bayan ya kammala kwaleji suka tura sa Kasar Turai ya karo ilimi, dawowarsa ya sa babu wanda ya kai shi ilimi a bangangaren kimiyya. A shekaran ne aka kafa jami'ar kimiyya da fasaha na tunawa da Safiyyah bnt Jibril, kuma take aka bashi mukamin shugaban jami'ar.
Duk da zaman sa shugaba hakan bai hana masa shiga aji sai kafin shekara ya zagayo an samu nasara sosai a jami'ar amma kuma cecekuce ya fara yawo akan shugaban da ya kasa ajiye iyali ta ina zai shugabanci al'umma. Hankalin sa da na yan uwansa ya tashi don shi bai da abin so sama da littafan sa da yan uwansa, hakan ya sa bai taba soyayya ba.
Bayan sun yi zama ne suka yanke shawaran haɗa shi aure da kanwar mijin yayarsa marikiyarsa Surayya. Ba'a ɗauki lokaci ba yayi aure ya tare da amaryar sa a cikin makaranta.
Shekara daya da aurensa su ka wayi gari da tashin hankali, don kuwa mahaya suka shigo har cikin jami'a suka iske shi a gida su ka raba gida biyu. Daukacin al'ummar Qahɗaanie sun shiga tashin hankali don wannan shine taaddanci na farko da aka fara tun bayan kafa daular shekaru aru-aru da su ka wuce.
Bayan rasuwan sa da wata uku matarsa ta haifi da namiji nan aka sa masa Muhammad Bello, wasu sun so a maida masa da Yahuza amma Surayya ta kasa ta tsare tace "kafin kanina ya rasu ya sha faɗa min Bello zai haifa"
Bello na da shekara ɗaya Allah yayi ma mahaifiyarsa rasuwa anan kula da shi ya koma hannun Hajiya Surayya, bai rasa komai ba haka ta haɗa shi da nata ya'yan ta raina ba tare da nuna gajiyawa ko bambanci ba.
Bello na da shekara biyar Allah yayi ma Hajiya Surayya rasuwa, anan rikon sa ya koma gun mabi da ita Aisha, nan ma shekara biyu kawai yayi hannunta ta rasa ranta a dalilin haihuwa. Tun daga nan Bello ya san me ake kira da maraici don sauran yan uwa da su ka rage mazajensu na kallon dukiyar da Bello ya gada ne, nan su ka yi kasafi a tsakaninsu kowannensu ya kwashi rabon sa. Shi kuma su ka barshi da gallafiri a tsakanin su yau yana gidan wannan gobe yana gidan wancan har dai ya samfe ya koma fadan sarki da zama. Nan ɗin ma ba wani abin arziki yake samu ba sai dai yakan ci ya sha sannan yana zama cikin ya'yan sarki da su ke sa'oinsa.
Da rarrafe ya kammala kwaleji anan ya fara siyar da dabino da riɗi, sannu a hankali ya koma safaran fata daga Nijeriya zuwa Qahɗaanie. In zai tafi sai ya kai musu man riɗi da riɗi da dabino. Tun yan tsallakawa ya dawo babu wani riba har ya kai ga ribansa kan ninka kuɗin da yaje da shi. Daga haka ya buɗe masanaartan sarrafa riɗi zuwa biskit da wasu ababen kwalama. Hakan Allah ya ɗaukaka shi yana da shekaru ashirin da takwas a duniya.
"Bello ya kamata ka yi karatu mai nisa,ka bar min amanar kamfanin ka zan kula muka da shi ka je Kasar waje ka you ilimi ka dawo" faɗin amininsa AbdoulGaffar ɗan sarki mai ci a lokacin. Bai Musa masa ba ya nema kuma ya samu tare da taimakon AbdoulGaffar ɗin. Kasar Spain ya je yayo ilimi akan kasuwanci, shekara uku ya ɗauka ya dawo ya iske ya samu riba fiye da tunani.
Bayan ya dawo ne ya haɗu da Amina, budurwar da ke tashe a Qahɗaanie don duk samarin ta dafa sarakai sai ya'yan su amma Bello ya kasa ya tsare shi sonta ya ke.
"Ba fa za ta aure ka ba, yarinyar da su saifullahi su ka gama kwakwala za ka aura, sannan ai kai ba ajinta bane" faɗin AbdoulGaffar cikin jin haushi bayan sun je gidan su Amina zance sun iske maza na layi.
"ina sonta ne Amini" Bello ya ce yana jin zafi
"In rabon ka ce zaka aure ta a gaba, yanzu ka je ka nemi Abokiyar tagwaitar matata ka aura, samun abokiyar zama ta gari kuma uwargida ta gari zai sa duk Fitinar wa'inda zaka auro daga baya ba zai taɓa damunka ba, je ka neme ta" a ranar da haka su ka rabu kowannensu da abin da yake sakawa a ransa.
A daren ranar kuma Allah yayi ma adalin sarki rasuwa. Sarki Abdoulwahabb ya rasu sanadiyar ciwon cikin da ta turknuke shi. Haka aka yi kwanan jimami Bello na faman rarrashin amininsa AbdoulGaffar saboda Shakuwar da ke tsakanin sa da mahaifinsa ya fi na kowanne don sarkin ya sha faɗin bashi da Magaji sai AbdoulGaffar duk da kasancewarsa ƙkarami cikin ya'yan sa maza uku.
Washe gari aka sallaci marigayi aka kai shi gidan sa na gaskiya, da yamma lis sai ga labarin rasuwan AbdoulGaffar da matarsa ta sanadiyar ruwan da su ka sha. Hankali ya tashi a fada nan aka fara bincike don ganin wa zai ba su ruwan guba da har za su rasu. Ana cikin bincike kuma aka sake samun labarin rasuwan amintaccen hadimin sarki wanda shi ke bashi abinci, kuma mutane da dama sun ganshi da AbdoulGaffar bayan sallan la'asar.
Nan bincike ya sauya salo don take aka gano cewa sarki da AbdoulGaffar duk Alu amintaccen hadimin sarki ne ya kashe su. Amma abin tambaya a zuciyar kowa Shine wanene ya sa shi kashe su?
***
An ɗauki kwana bakwai ana makokinsu uku da aka birne a jere, sannan an kafa kwamitin bincike da ke bincike akan wanda ya sa ayi kisan. Sannan an ba da Daman fitar da masu takara saboda wanda ke jiran gado ma babu shi. Nan duk wasu masu kwaɗayin sarauta kuma su ke tunanin sun cancanta su ka fito. Da fari babu ɗa ko guda daga cikin ya'yan sarki mai rasuwa da ya fito, sannan duk. Kannensa da su ke Raye sun yafe sarautan ya sa aka saka sunan Abdoulajabbar ba tare da ya sani ba.
Bayan bincike da duba cancanta sai kwamitin suka tsaida Abdoulajabbar a matsayin sarki kuma Alkali mai iko na karshe a Daular Qahɗaanie.
Tsaida Abdoulajabbar ya kawo cecekuce a masarauta ganin in ba'a yi wasa b sarautan zai fita daga gidansu ganin bai da ɗa namiji ko ɗaya sai mata biyar da uwargida Ummou Hafsa ta haifa masa.
A cikin bayin sarki akwai wanda jinin su ya haɗu da Abdoulajabbar, dattijo ne shi yake kula da shanayen masarauta hakan yasa da yawa basu san Ammou Yusuf a matsayin bawa ba. Yana da ya'ya goma sha huɗu da matarsa Zainab wanda sha uku daga ciki maza ne sai mace ɗaya tilo.
Not much sha
Vote share and share after commenting evry line
Thnx 4ur love
Ummu-Abdoul
Add Vote
Do you know that...?
BGGB was sopos to b the title for
Silar Ajali..
I only know two things about BGGB that is the disguised blessings in delay of marriage when one is patient and decent and the problem of desperation.
I only know what to write when I pick up my system to type😂 or sometimes some thin will come to my mind and I will quickly type It so that I won't forget..
Qahɗaanie doesn't exist its just an Arabic name for some clans of Arabs
But the culture of the Qahɗaanies is
nt Arab its theirs 😂😂😂 so don't compare them with any body.
Nutud is from nuqud
Hilaalu Sambo meaning
Sambo'quarters or crescent
Qahɗaanie's settings is from my imagination and that of Ghana or Nigeria are 80% real.
If u realize any kwafsi pls quickly draw my attention, but pls the words should be💞💕
ﺃﺣﺒﻜﻢ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ 😍😘💞💕
ﺻﻔﻴﻴﺔ ﺑﻨﺖ ﺟﺒﺮﻳﻞ ( ﺃﻡ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ )
💞💞💞
Musamman Mai martaba ya iske Ammou Yusuf a gidansa da ya sama masa a can wajen gari, a cewarsa shi mahaifi ne kuma mahaifa ba sa zama cikin fada don kuwa ya'ya ke bin iyaye ba iyaye ke bin Ya'yan su masarauta ba.
"Ranka shi daɗe da aikowa ka yi aka kira ni" faɗin Ammou Yusuf yana mai gurfanawa kamar zai masa sujjada
"Ai kai uba ne, na tuna lokutan da mukan kebe mu yi sirri a cikin shanaye ne nayi sha'awar yin hakan. Ko za mu je ran gadi ne Ammou" sarki ya faɗi yana zama kusa da Ammou Yusuf. Dukkansu tunawa su ka yi da lokutan sirrin su, in Abdouljabbar na da wata damuwa Ammou Yusuf ne kaɗai wanda ya kan iske kai tsaye ya faɗa masa sannan shi ne kaɗai ya ke fahimtar sa ya bashi shawaran da amfani da shi cin riba ne.
Shiryawa Ammou yayi ya fito su ka gangara, su na tafe su na hira, har su ka shiga gonar masarauta da ke daga bayan gari, cikin shanaye inda su ka saba zama nan suka zauna, take sarki ya umurci ma'aikatan wajen da su basu waje. Sun fita suna mamakin ganin sarki shi ɗaya kamar yanda dukkan wa'inda su ka wuce ke mamakin ganin shi da tafiya a kasa kuma shi kaɗai.
"Ammou ina son ɗa namiji, in ka yi la'akari da mu huɗu ne kawai maza cikin ya'ya arba'in da huɗu da marigayi ya haifa, sai in ce kila nine nayi gado. Bani shawara me ya kamata inyi kada sarauta ya fita daga gidanmu" sarki ya faɗi cike da damuwa
"Abdouljabbar haihuwan mace, namiji, ko rashin sa ma gaba daya ba yin mutum bane. Allah da kansa ya faɗi yana azurta wasu da da wasu da maza wasu da duka biyu sannan yakan hana ma wasu amma dai ka kara aure, in rabon na jikinta ne sai ta haifa maka" Ya ce yana mai tausaya masa.
"Ammou ka bani auren Maryam, ka yanke min sadaki ko nawa ne zan biya" Ya ce cikin hawaye, don damar da yake so Ammou ya bashi kenan kuma ya bashi.
"Maryam baiwa ce a masarautarku, ka manta ni bawa ne? Ya'ya na ma duka bayi ne don ɗaya daga ciki ma a wajen bauta ya iske ajalinsa" Ya faɗi kai tsaye.
Add Vot
"in dai haka ne, daga yau na yanta ka, sannan duk wani jini naka ya tashi da ga bawa, kai ba ma ku ba na soke bauta a daular Qahɗaanie." Ya faɗi cikin isa da mulki, rungume sa yayi yana kuka nan tausayin tsohon ya kara kama shi.
Basu bar gona ba sai da aka tara shaidu aka ɗaura auren Sarki Abdouljabbar da Maryam. Sannan a wajen sarki yayi shelar yanta duk wani bawa da ke Qahɗaanie sannan aka sa haddin zaman shekara ashirin ga duk wanda aka kama da bautar da ɗan Adam.
Duk wani hadimanci na gida aka sanya albashin da za'a sa musu saboda ba bauta su ke ba aiki ne kamar ya'ya.
Labarin na isa fada tsofaffin bayi su ka shiga murna suna roka ma sarki Aljanna da kuma biyan bukatun duniya da lahira.
***
Sai da aka yi kwana bakwai ana bikin Sarki wanda ya haɗa har da bikin Yanci da kuma naɗa Ammou a matsayin uban masarauta. Anan ne kura ya tashi sosai amma masu hankali sun yarda ya cancanci a bashi wannan sarautan.
Sati ɗaya bayan biki amarya ta tare a sashinta, a ranar ne Bello ya kai ziyarar sa ta farko wajen Hafsa, abokiyar tagwaitar Abdoulgaffar. Sanin da ta masa ta hannun marigayi ya sa ba ta wani ja zancen da tsawo ba. Ta amince masa nan su ka kulla alkawarin hana komai shiga tsakaninsu.
Bai bar gidansu ba sai da son ta ya samu waje ya zauna a zuciyar sa, sannan ya yi na'am da ɗan ɗabi'un da ta nuna masa. Bai yi kasa a guiwa ba ya iske mijin yayar mahaifinsa ya nema masa auren Hafsat
"Ka taɓa ganin wani cikin zuri'ar Sambo ya auri bare? Toh ka zo ga ikilima ka aura an riga an gama magana kai kaɗai muke jira" Ya ce da shi bayan ya gama saurarensa.
"Ni fa ba izini na zo nema wajenka ba baffa, alfarma nake nema ka jagoranci neman aure na don kada ku ji a gari ku ga ban muku adalci ba" Bello ya faɗi kansa tsaye.
"Au! Au!! Au!!! Toh an ki a je, in kana da wa'inda su ka fi mu sai su je maka, shashshasha wanda bai iya rike maraicinsa ba" Ya faɗi yana shura takalmansa da yin gaba.
Haka ya bi yan uwansa duk wanda ya je sai ya iske inda ya fito ya fi na gaba sassauci, don gori kala-kala da cin mutunci sun sauke masa a cewarsu yayi kuɗi ya manta da su.
Ganin haka ya sa ya bi ta fada, nan sarki Abdul-Jabbar ya sa aka je aka yi komai na auren, haɗe da sanya rana wata goma sha biyar.
***
Kwanci tashi ba wuya, wata goma da auren sarki da Maryam ta haifa masa yan biyu duka maza, anyi shagali sosai sarki ya yanta yan kurkuku sannan ya bada Sadaka na kuɗi da abinci ga mabukata. Wannan murna da ya nuna ya kara dasa ma uwargida ummou Hafsa tsanar Ummou Maryam da yaranta. Nan ta bazama neman magani duk inda ta ji ana bada maganin haihuwa ta ke zuwa don a bata na haihuwar ɗa namiji.
Cikin ikon Allah yaran na da wata uku ta samu ciki, kuma a watan babban AbdoulHaseeb ya ce ga garinku ya bar husaininsa AbdoulHaleem, Sarki da duk wani masoyin fada yayi bakin cikin wannan rashi da aka yi.
***
Anyi bikin Bello da Hafsa cikin kwanciyar hankali ta tare a gidanta da ke bayan fada. Gini ne wanda zai ci mace daya da ya'ya don dakuna uku ne sai falon a tsakiya. Yan uwa sun mata murna suna masu roka mata zaman lafiya da zuri'a dayyaba.
Cikin Ummou Hafsa na cika ta haifi ɗan ta mai kama da marigayi AbdoulHaseeb hakan ya sa sarki ya maimaita masa sunan.
***
Tun bayan haihuwan AbdoulHaseeb ba'a sake haihuwa a fada ba, duk yanda sarki ya so Ummou maryam da ta nemi taimako ta ki don a cewarta "Haihuwa, mutuwa da aure duk na Allah ne, in lokacin yi bai zo ba duk wayon mutum da dabaransa ba zai yi ba" da kalaman da take kwantar ma sarki rai kenan ya hakura duk da yana ji a jikin sa asiri aka mata akan haihuwa.
Bello da Hafsa na zaune cikin zaman lafiya amma ganin shekara takwas ya wuce ba tare da ta yi ko ɓatan wata ba, ya sa suka dukufa addu'a, azumi da sadaka.
In suna zaune ko tafiye ba abin da suke ambata daga istigfari sai RABBI LAA TAZARNI FARDAN WA ANTA KHAIRUL WAARITHEEN saboda addu'ar da annabi zakariyya ya yi kenan Allah azurta shi da Yahya.
A shekaran su na tara ne ciki ya ɓullo a jikin and murna a wajensu ba'a magana, sun yi godiya ga Allah sannan sun maida hankali wajen ci gaba da rokon sa akan ya sauke ta lafiya sannan ya albarkaci abin da za ta haifa.
"Kin san buri na Hafsa, in haifi ya mace mai kama da ke, in ba ta daɗin da babu wanda zai taɓa ba ta a duniya" Ya zama wakan da Hafsa ta hardace daga bakin mijinta.
"Allah dai ya bamu masu albarka" kan zama amsar ta.
Cikin ikon Allah lokacin haihuwarta na isa ta haife ya mace mai matukar kama da mahaifinta. Farin ciki a wajen sa ba'a magana nan ya saka mata suna Fatima.
Tun bayan dawowarsu daga gida wankan jego ya maida shi jiki yi ma Fatima wanka. Wani lokaci har goyata yake har barci ya kwashe ta. Hakan ya jawo Shakuwa mai karfi da soyayya tsakaninsu.
Fatima na da shekaru uku aka haifi Surayya, daga ita sai Aahil. Bayan haihuwan Aahil ne Alhaji Bello ya auro sadiya, ita yar asalin Kasar Nijeriya ce karatu ya kawo ta Qahɗaanie su ka haɗu su ka yi aure.
Zaman lafiya sosai su ke yi don tun da ta gano soyayyar da ke tsakanin Fatima da mahaifinta ta daura mata ninkin sa. Hakan ya sa Alhaji Bello ke girmama ta haka za lika Hafsa.
***
Amina na jin labarin kuɗin da Alhaji Bello ya tara nan ta kasa ta tsare har sai da ta shigo gidan, lokacin ne zaman lafiya ya fara karanci a tsakanin su don Amina bata kyashin karta ma kowa rashin mutunci a gidan sannan ta yi amfani da kissa ta rufe ba tare da Alhaji ya san anyi ba.
Fatima na da shekaru goma sha shida ta kammala karatunta na kwaleji, cikin nasara da hazaka nan Hajiya sadiya ta bada shawaran tura ta jami'ar Ahmadu Bello don yin karatun digiri amma Sam Alh Bello ya ki.
Fatima ta taso shiru-shiru mara hayaniya, ba ta da abin da ta sa a gaba sama da littafanta na boko da islamiyya. Ta taso ba ta da kawa ko ɗaya sai dai a haɗu a aji a rabu cikin aminci. Mahaifinta ne kawai ya san sirrin ta, shi kaɗai ta ke isa ga don neman shawara sannan shi kadai ke iya fassara maganar ta ko bata furta ba.
"Ni a zan tura ya ta gari garara har wata kasa ba, ki sake shawara ko zan iya dauka wannan dai kiyi hakuri" Ya ce da ita lokacin da ta masa maganar.
"Aure dai za'a mata, wani irin jami'a ko yawon karuwanci" hajiya Amina ta faɗi son ita babu wacce ta tsana sama da fatima don ganin yan matan ta uku ba wani kulawa suke daga mahaifinsu ba.
"Ke dai baki da magana sai na namiji, kada ki maida min ya'ya jarababbu don Allah. Fatima ko za tayi aure sai ta fara karatu. Zan nema mata a Safiyyah jibril, ta fara in miji ya zo in aurar da ita" da haka ya rufe taron da yake da matansa akan Fatima.
Add Vote
Afuwan Afuwan pls, da kyar na iya yin wannan, ku min addu'a. Manage this pls.
Cikin ikon Allah ya sama mata gurbin karatu a jami'ar kimiyya da fasaha wato Safiyyah jibril University of science and technology a sashin kere-keren magudanar ruwa ( water resources engineering adepartment). Sannan ya siya mata mota kirar civic don zirga-zirgan ta na makaranta. Siyan motar da yayi ya kara tayar da hankalin Hajiya Amina don ko su matansa da a tunanin ta yake karuwa da su bai siya musu ba. Nan kishin Fatima da tsanar ta ya cika mata kirji har take ganin ai kawai ta kawar da ita shi ne mafita.
Ranar da Fatima za ta fara zuwa makaranta, ta shirya cike da ɗoki kamar kowane sabon ɗalibi. Bayan ta bi iyayenta mata ta yi musu sallama ne ta karasa wajen Abbie.
" Fatimatu-zahra an shirya kenan, ubangiji Allah ya sa kin fara kenan a sa'a, ya miki albarka. Ina so ki sani cewa jami'a waje ne na koyon darasi. Ko in ce duniya ce mai zaman kanta, wasu kan shiga a tambade su fita a shirye, haka wasu kan shiga a shirye su tambade kafin su gama wasu su kan shiga a shirye su fita a hakan wasu a tambade su fita a hakan. Saboda haka ina so ki kasance mai tunawa da inda kika fito a duk wani mataki na rayuwa. Ki tuna ke ɗin musulma ce wane dokoki ne Allah ya sharɗanta miki.
Ban rage ki da komai ba, duk abin da kike bukata ki same ni zan miki, sannan ki sani kina da babban Aboki kuma amini wanda ba kunya ko tsoro tsakanin ku, sannan wanda duk duniya babu wanda zai kai shi ɓoye miki sirri don kuwa ba zai so a ce ga yar sa tayi kaza ba " ya faɗi yana nuna kansa. Hawayen da ta gani a idon ta ya sa shi yin dariya da faɗin
" oooo Yar jami'a da kuka? Ba ki san kin zama yan mata ba, maza share hawayenki Allah ya miki albarka" ya karasa yana mika mata hankici. A karshe ma tashi yayi don ya kaita makarantar suna tafe yana kara mata kwarin gwuiwa tare da nuna mata ai zata iya kwas din da aka bata kuma za ta yi nasara. Hakan ya sa ta isa makaranta da karfinta, ta shiga Darussan da aka ce tana da su a ranar kuma ta fahimce su duka.
A ajin ne ta haɗu da wata wacce ta zauna kusa da ita mai suna Salma, a tsakanin darussan ne su ka gaisa har suka gabatar da junansu.
Salma yar asalin Qahɗaanie ce don balarabiya ce da ma ba su watsar da al'adan su ba. Amma tana jin hausa kamar kowane ɗan Qahɗaanie.
Bayan an tashi makaranta ne yayan salma ya zo ya ɗauke ta, ita kuma Abbie ya zo ya ɗauke ta. Tun a cikin mota ta ke bashi labarin darussan da aka musu da maluman su har da sabuwar kawarta salma.
"Aahh MaashaAllah, kada ki yi saurin sake mata jiki sai kin tabbatar da cewa tarbiyyan ku ya zo ɗaya, kin san masu iya magana na cewa gwada min abokinka ya ishe ni
sanin ko kai w aye. Banda rashin karatu banda rashin tarbiyya in dai ba shi ba kina iya kawncen aji da ita in kuma hali ya zo ɗaya sai ku zama kawayen har abada"
"Abbie har wani kawar aji ne akwai?" Ta tambaya cikin dariya
"Sosai ma kuwa, kawar da a aji zaku gaisa a ɗan yi hiran duniya amma in za'a sa mata wuka bata san komai game da ke ba" ya faɗi shima yana dariya. A haka su ka isa gida, ta gaida iyayen ta mata sannan ta karasa ɗakin ta don chanza kaya.
***
A wata ɗaya da yan kwanaki da Fatima ta yi a jami'a ta saba da karatun sannan sun shaqu da kawarta Salma Babikir saboda yarda da tayi da tarbiyyan ta. Sai ya zama in Fatima ta fito gida take biyawa Salma su wuce a motar ta. A ɗan wannan lokacin duk yan gidan su fatima sun san Salma haka yan gidan su salma sun san Fatima.
A nan cikin ajin nasu kuma akwai saudah, ita ma balarabiya ce amma b su daɗe da tarewa a Qahɗaanie ba. Ta kan zauna a cikinsu amma ba kasafai ba, amma in ba'a ganta ba akan tambaye su ina Saudah.
Tun da kanin mahaifin saudah mai suna Sufyan ya kyalla ido ya ga Fatima ya ce da wa Allah ya haɗa shi. Nan ya shiga mata aike ta waya da wasika, katukan gaisuwa na bege (greeting card) da wasu ababen.
Kafin a ankara ta faɗa tarkon soyayyar sa, saboda kirkin da ya ke mata da kulawarsa gareta. Bata ɓoye ma Abbie ba shi kuma yana bata shawara don baya so yayi gaggawa ya fi so ya ga gudun ruwansu.
***
"Habibty kin san irin son da na ke miki kuwa, don Allah ki so ni kuma kada ki yarda wani ya shiga tsakanin mu" su ne kalaman sufyan kullum har Fatima ta haddace. Hakan ya sa ta tabbatar da lallai ta sa mu miji, kuma zata ji daɗin aurenta don gwani ne wajen tsara kalamai na soyayya da kulawa.
Shekaransu ɗaya tare kenan kasancewa tana aji biyu, soyayyar sufyan bai taɓa hana mata karatu ba don ita ke jagoranci a ajin nasu.
Zaune su ke ita da Salma suna karatu, wayarta tayi kara nan ta ɗaga cike da shauqi ta ce
"Habibie Sufyan, na yi kewan ka wallahi ba ko kaɗan ba, kana ina" Ta ce cikin shagwaba
"Gani na shigo makarantarku, ki fito mu yi hira daga nan mu karasa lambun fada" yace mata yana kwantar da murya
"Gani nan tafe, Insha'Allah" tace tana sauke waya haɗe da ajiye littafan da take karantawa a gefe. Fauda ta dauko ta shafa ta kara gyara fuskanta nan ta fito fes abin ta.
"Kin san Allah babu inda zaki, in yana so ku yi hira ya je gida mana" salma ta ce a fusace
"Toh wakikiyar Abbie ai ko shi ya san da shi" Ta ce tana murguda baki, bata ankara ba Salma ta ɗauke takalmanta da wayarta ta zauna akai
"ba zan san kina cikin majununai ba sai kin tafi a haka, kin bari soyayya na neman rufe miki ido wallahi ba aurenki zai yi ba. Dalilin me ya baki na rashin zuwan sa gida? Kullum shi kenan sai dai ku haɗu a wani waje ba dai ya je gidanku ba kuma kina laqe da shi" Ta ce mata kai tsaye duk da sanin da tayi ranta zai ɓace.
"Alo tace ka yi hakuri kazo gida anjima karfe uku za mu kammala" salma ta faɗi bayan ta ansa wayar da ya kira.
Duk inda ran Fatima ya kai ya ɓaci don gani take kamar bakin ciki Salma take mata, hakan ya sa ta quduri cema sufyan ya turo ayi aurensu ta huta da masu faɗi mata ba aurenta zai yi ba. A haka su ka tashi kowannensu ya isa gida a gajiye saboda karatun da su ka sha.
Na Kanji ana cewa makaranta ke son
marubuta, amma gare ni ba haka bane don ni ina son makaranta
littafai na don jin su nake kamar
wasu jinina. Allah ya bar zumunci har
gaban abada. Keep on voting, keep on commenting, and I will keep you updated
Tun da ta isa gida ta ke tsumayen kiran Sufyan amma shiru take ji, haka ta zauna sukuku kamar wacce kwai ya fashe mawa a ciki. Tsaki take tana zagin salma a ranta don ta san duk ita ta ja mata fushi masoyi.
Ganin anyi sallan isha'i bai kira ba ya sa ta danna masa kira, bugu biyu ya ɗaga
"idan na ce miki Salmah ba kawar arziki ba ce ki ce na cika kishi, gashi nan ta zuga ki yau kin ki gani na" ya ce bayan ya ɗaga kiran. Take zuciyar Fatima ta kara cika da jin haushin Salmah
"Kawai a zo a sa mana rana mu wuce wajen don Allah,ka ga masu bakin ciki sai cikin su ya kara baki" Ta ce cikin shagwaɓe murya
"Ayi aure mutum bai san kalan matar da ai aura ba, ɗan zancen kwantar da zuciya da mace za ta yi mutum ya san aurensa zai cika da romansiyya kawarki ta hana, yanzu haɗuwar ma tana neman ta hana balle mu ji ɗumin juna. In kina so ayi auren nan ki bani dama sau ɗaya Kawai habibty" ya faɗi yana mai sumbatar iska zuwa ga kunnenta.
"toh" Ta ce a sanyaye zuciyar ta na karyata bakinta
" kuma ki sani wannan sirri ne tsakanin mata da miji, saura ki je ki faɗi ma kunne na uku" ya faɗi da muryar umurni.
"wai har yanzu baka hakura bane, wallahi kwace wayar tayi a hannu na ban ma sani ba, sannan ta ɗauke takalma na ka san ba zan iya tafiya haka ba, kai ma ba za ka so ba aiko" tace masa cikin muryar kuka don duk in da hankalin ta yake ya tashi saboda fushi da ya nuna mata yana yi da ita.
"ai ba abin da so baya sawa se ki taho a hakan, nan zan tabbatar da son da kike ikirarin kina min" ya ce yana mai katse wayar. Nan ta zauna tana kallon wayar a hannunta, zuciyar ta na faɗi ma ta " ai da yana son ki da ya zo gidan yanda kika ce " amma mayaudariyar zuciyar ta cewa take " ya za ki ce haka, bayan kin san yana
makaranta ta wulakanta shi" haka ta yi ta sakawa da warwarewa har barci ɓarawo ya sace ta.
***
Washe gari da matsanancin ciwon kai ta tashi da shi, sannan ga karuwan son Sufyan da ya kara mamaye mata Zuci, haka dai ta cigaba da abu kamar mai cuta.
"Fatima me ke damunki ne tun jiya na lura kina wani shiru shiru" mahaifiyarta tace lokacin da ta shiga gaida ta
" Ummie kaina ke ciwo, ki mun addu'a" Ta ce tana mai hawaye
"ciwon kai sai ki kama kuka Fatima se kace wata karamar yarinya, sa'o'inki nawa ke dakunan mazajensu haka za su zauna su na ma ciwon kai kuka, kar ki nemi magani ki sha ki tsaya kina wauta" Ta ce tana juyawa tana ma kanwar fatima surayya tana mata bayanin wani kaya da ta siyo mata don an sa ranar aurenta daga ta kammala shekarar farko na jami'a inda take karanta Technical education.
Sumsum Fatima ta fita ta isa ga hajiya Sadiya, nan ma bayan gaisuwa tambayar ta tayi me ke damun ta, amsa ɗaya ta bayar,
"Kar ki ce don an sa ranar surayya za ki tada hankali, kowa da lokacin sa, shi wannan mai kiran ki a waya ba zai fito bane? Ni ban san mai sa Abbie ke yin shiru bane, nan ya matsa ma Anisa kwatakwata guda nawa ta ke, daga ya kamata tana waya yace ya zo. Kin ga tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu, in son ki dagaske yaron yake ya fito a wuce wurin in kuma ba dagaske yake ba ya baki wuri masu son ki su fito" Ta ce cikin faɗa, haka ta cigaba da faɗan ta kai tsaye wanda Fatima a zuciyar ta faɗi take " don an takura yar ki sai ki
takura ni"
Add Vote
Haka ta baro ɗakin ranta a ɓace, san inda ta yi kila zuciyar ta ya buga matukar ta kai kanta ɗakin hajiya Amina ya sa ta wuce wajen Abbie, nan ta take sa'a yana barci ta juya ta yi shirin makaranta.
A makaranta ba ta ko bi takan Salmah ba, waje daya su ka zauna amma ba wanda ya ce da wani kanzil. Bayan darasin da su kayi karfe 12 zuwa 2 ne Saudah ta Kalle su tace
" Ni kuwa Ammie Fatima kun rabu da ammou nane? Naji ana za'a je tambayar sa Anjima, momma take ce min ba kawata na ce yana so ba nace eh, sai ta yi shiru" ba Fatima ba hatta Salmah sai da ta ji karayar zuciya. Nan Fatima ta tattaro duk wani Karfin hali ta ce
"Ya faɗa min, dama abokantaka kawai mu ke yi" Ta faɗi tana dariya
"Haba wallahi na yi mamaki da yace ma su momma haka, wai shi fa dama can ba budurwar sa bane kawarsa ce, ai ko gidanku bai taɓa zuwa ba, ni ko na ce ammou aji tsoron Allah, ya biyo ni zai kwade, amma Ammie kin yi babban wauta, saboda aboki ki kori wa'inda ke son ki da aure" Ta ce tana karkada kai
"Sai kiyi, Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zama lafiya" Fatima ta ce tana murmushi. Salma bata ce kala ba sai wayarta da tayi ta latsawa, sunyi shiru duka kafin su ga ta kara wayar a kunne
"Ubangiji Allah ya azurta ka da ya mace a farko, ya sa a mata abin da kayi ma yar wasu nan zaka ji in da Daɗi" salma tace tana mai katse wayar.
"Haba Salmah Ido da kunya fa, ko mai zai yi ai yaci albarkaci na, ita wacce kika shigar mawa ma cewa tayi su abokai ne, kin ga kenan babu abin da ya'yansa za su gani sai alkhairi" Ta ce tana mai mikewa da barin wajen. Sai a lokacin Fatima ta samu damar yin kuka, tana mai gode ma Allah da bata kai ga amincewa ba, niyyarta yau in ta tashi ta neme shi duk abin abin da zai faru ya faru su yi aurensu su huta.
"Share hawayenki, ba karamin asara yayi ba, ke kuma Allah na sonki shi ya sa har kika ga hakan ya faru, miji nagari na nan zuwa miki. Ki cigaba da addu'a da tsare mutuncinki kamar yanda Abbie ke faɗa mana" Ta ce tana share mata hawaye tana mai matse nata hawayen. Nan Fatima ta ɓata labarin yanda su kayi da kuma niyyarta a da.
"Alhamdulillah, Kinga yana cikin rahman Allah dabaran dauke miki waya da takalma, don na tabbatar da kun haɗu jiya da kin zama fanko. Ai duk namijin da ya ce zai aure ka bayan ya sanka ɗiya mace to dama ba aurenka zai yi ba" haka ta cigaba da ba ta baki har su ka isa gida. Tare su ka isa har ga Abbie, Salmah ta ba shi labarin abin da saudah ta ce musu.
" Kun ga kenan ya zama maku darasi ku duka, namijin da ke son ku gidan Mahaifin ku zai biyo ku amma duk wani mai haɗa wajen haɗuwa toh ba aurenku zai yi ba. Sannan duk wani disappointment alkhairi ne, abin da ake bukatar mumini da shi a wannan lokacin shine hakuri.
Akwai wani sarki yana da amintaccen
bawa, duk abin da ya faru sai bawan nan ya ce "alkhairi ne daga rahman Allah" hakan da ya ke faɗi sai yayi ta
ba sarki haushi don gani yake kawai
rainin wayau ne. Wata rana sarki sai ya rasa yatsa ɗaya, sai bawan nan
yace "Alkhairi ne daga rahaman Allah" Sai sarki ya ji haushi ya sa aka
kulle shi a gidan yari. Bayan shekaru
sarki ya ma manta da wannan bawa
na sa, sai wata rana yana rangadi se
yayi sha'awar yin farauta, a cikin daji ya ci karo da masu cin mutane. Nan
suka ɗaure shi suka hura wutan da za su gasa shi sannan su ka kamo shi don su yanka. Nan su ka lura da
rashin yatsan nan na shi su ka sake shi a matsayin shi ba cikakken
mutum bane.
Add Vote
Yana dawowa sai ya tuna da
amintaccen bawansa da kalamansa
na cewa rashin yatsan sa alkhairi ne
daga Rahman Allah, sai ya sa aka
kawo masa shi, nan ya bashi labari ya kuma kara ba shi hakuri. Bawan nan ya sake gurfanawa ya ce "Kulle
ni ai alkhairi ne daga rahman Allah"
Sai sarki ya ce masa "Ta ya zaka kira
zaman gidan yari alkhairi bayan ba akan laifin ka aka kulle ka ba"
Sai bawa ya ce "Da ace baka kulle ni
ba, babu yanda za'a yi in barka ka je
farauta kai kaɗai, Kaga kenan da tare
zasu kama mu, kai za'a sake ka ni
kuma da nake cikakken mutum a
wajensu tsaf zasu cinye ni.
Kun ga labarin nan kaɗai ya ishe ku gode ma Allah a duk wani abin da ka so kuma Allah bai ba ku ba.
Kin san kanwar sarki Safiyyah, ita ma
lokacin nan akwai wani da ta so
kamar ranta zai fita, bata da abokan
shawara daga ni sai marigayi
Abdoulgaffar, shi ya sa kika ga har
gobe zumuncinmu da ita bai yanke
ba.
Taso bawan Allah ɗin nan amma
kwatsam yace shi Sam ba zai aureta
ba wayonta yayi yawa kuma ta fito
gidan sarauta. Tayi kuka tayi karamar
hauka in faɗa muku amma ba'a yi
wata ba take ce min "ashe gara da ban aure wane ba, Allah ya tanadar min wannan ne" , saboda shi wanda ya ki ta ɗin nan zina abin ado ne a
wajen sa, ya nemi matan aure,
zaurawa har ma da yan mata. Ga
caca sannan matarsa wuya take ji.
Anan na kara gaskata kissar sama"
Shiru yayi yana kallon su yanda jikin su yayi sanyi, ruwa ya dauko ya ba su daga firij ɗinsa sannan ya cigaba da faɗin
"Saboda haka, ku kwantar da hankali, banda gaggawa banda wulakanci duk wanda ya zo kuma dagaske yake sai ku faɗi a binciki halinsa da asalinsa, ku natsu ku yi karatun ku yanda ya kamata saboda shine ginshikin zama mai nasara" haka ya cigaba da mu su nasiha har zuwa la'asar sannan su ka je yin sallah su ka maida Salmah gida.
***
Duk yanda Fatima ta so ta kwantar da hankali damuwa bai gagara ziyartar ta ba lokaci zuwa lokaci, haka ta dage da karatu har suka kammala aji uku na jami'a, a shekaran ne aka yi auren Surayya kanwar ta da ke bi mata da Anisa babban yar hajiya sadiya.
Biki aka yi na yan gata, Fatima ta shiga ta fita ta tabbatar da bikin ya tafi yanda ake so, Salmah ma ba'a barta a baya ba don zama tayi yar gida aka shagale da ita duk da ita ma bikin ta saura watanni ne.
Add Vote
Tribute to Zainab Muhammad @xiesobamention a user
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
Some hours ago I called Sharhabil Yahaya Musa to confirm something concerning my soil physical measurement report, from the background I heard a frnd of ours saying "kace mata taji mutuwar zee soba" I freezed upon hearing that, even though death has no notice but Urs is one of the least expected death.
I asked him more than 3x "zee soba fa" coz my mind was busy telling he is just joking even though I knw he don't joke on serious issues like death.
I knew zainab since my 200lvl at abu but we became close during AMSA's (Association of Muslim students Agriculturalist) Agro-trip to Sokoto cement, from then onwards we became sisters. I so much respect her because of her straightforwardness and kind heart.
Earlier this year we met at faculty of Agric ABU, her words were "Sophie zamu dawo masters dinnan next year Insha'Allah, tunda kun wuce mu" not knowing u will only sit for the aptitude test before leaving us for ever..
U messaged me everytime u r coming to zaria but the meetings we r destined to have ended April 2017.
Zee I wish u d best of best of the hereafter, may ur grave be part of Raudha min riyaadil Janna, may we meet in jannatul firdaus, may Allah make ur pains a purification for ur sins and may he bless us the fortitude to bear the pain of ur loss coz My heart is seriously aching as am writing this.
Allah amshi bakoncin ki zainab😭😭😭😭
Add Vote
Assalamu Alaikum warahmatullah
Dafatan na same ku lafiya, Nagode
kwarai da addu'o'inku akan yar uwa
zainab @xiesoba, faɗin irin kaɗuwar da nayi ma ɓata lokaci ne, har yau na
kasa dawowa daidai, practical report
ɗin da na ke yi labarin mutuwar ta ya
iske ni wallahi se yau na iya
karasawa kuma last experiment ya rage min.
Kullum da zainab nake kwana nake
farkawa, d moments we had together, da na san zaman mu
kalilan ne da zumuncin da zamu yi se ya fi wanda aka yi a baya.
Rasuwar zainab ya kara tabbatar min da ɗan Adam zai mutu da burikansa. Allah bai yi zainab ta cika mafi yawan
burikanta ba. Muna fatan Allah ya
musanya mata su da lada mai girma
don burikanta mafi yawa akan neman
yardan Allah ne.
Last time da muka haɗu ta iske ni a
skul, duk yanda tayi mu haɗu
washegari mu je bikin wata a Kaduna
na ki akan bata gayyace ni ba, faɗi take ai zaman tare ya wuce a yi
gayyata ina ma lokaci zai dawo baya da kafata kafarki zainab 😢😢😢.
Add Vote.
A ranar nake mata tsiya "xiesoba bani kaso na na Npower" Ta siya min
eggrol da team tana ai wani jin daɗi
se aikin federal government ya fito. Mun rabu muna kewan juna da
alkawuran zamu haɗu akai akai not knowing it was our last.
Ta ci burin dawowa msc, muna kara
zuga ta akan ta dawo ashe ba ta da
rabo, ta so tayi entrance exams not knowing sauran ta kwana goma sha
uku a duniya.
Ta ci burin tayi aure ta nemi Aljanna ta nan, disappointments kala-kala ta
samu sai da bikin ta ya rage saura
wata biyu Allah ya amshi abarsa , a
iya sani na xiesoba ba ta taɓa Zina
ba, ina sa ran tana cikin wa'inda
annabi SAW ya kira da shahidai.
Duk na ɗauko Wattpad msgs ɗin xiesoba ke fin karfi na,
in na tashi typing tunawa da ita ma some weeks ago Haka take typing se
na ji rubutu ya fice min a rai. Amma ya muka iya, haka Allah ya tsara, haka yaso kuma haka ne daidai. Allah ya rahamshe ta ya sa jinyar da ta yi kaffara ne agareta , ya sa tana
cikin dausayin aljanna. Mu kuma in
tamu ta zo ya sa mu cika da imani.
***
Anyi bikin su surayya cikin kwanciyar hankali kowaccensu an mika ta ɗakunan mazajensu, a nan kewa ya cika Fatima don Ahlam da ya ke abokin hiranta ya cilla Kasar Masar don karanta shari'ar musulunci a jami'ar Al'azhar.
A haka ta shiga aji huɗu nan kuma aka sanya ranar auren Salmah da masoyinta Muhammad Suraj. A wajen shirye-shirye ne ta haɗu da amininsa Muhammad Khuder, tun da ya ga Fatima ya fara bibiyar ta, tun ba ta amince masa ba har dai ta bashi fuska. Murna wajen aminan biyu ba'a magana saboda ganin amintansu zai kai ga ba yanda miji zai shiga tsakani.
Sun yi soyayya mai tsafta har ya fara shirin turo iyayensa ayi tambaya, murna a wajen Fatima ba'a magana burin ta ya kusa cika itama tayi auren nan, kullum zancen su da Salmah bai wuce "aure daɗi gareshi" hakan ya sa ta matsu tayi auren ta ji daɗin da Salmah ke kira mata.
Yau ma kamar kullum Khuder ya zo gidansu su na hira a falon Abbie sai wayar ta tayi kara, ganin bakon lamba ne ya sa ta dagawa tana mai cika sallama.
"Waalaikumus salam warahmatullah, Hajiya Fatima kin kusa haɗa digiri shi ya sa ba'a ko ta kanmu ko?" aka ce daga ɗayan ɓangaren
" Allah sarki ban ma gane mai magana ba" tace tana dariya
"Sufyan ne, lallai Fatima kin koshi da yawa" yace daga jin sautin muryarsa ta san ya ji haushi
"Allah sarki, Ammou Sufyan ai ko ka kira a sa'a, ga surikinka ku gaisa, ai nayi aure ne" tace sanin da tayi saudah ta yi aure tana Kuwait, kuma ba waya su ke ba balle ta san abin da ke faruwa tsakanin su. Ta mika ma Khuder wayar su ka gaisa ya kashe wayar.
"Wane Sufyan ne kuma wannan har da Kalen Ammou"
"Allahus Samad Rafeeq, wallahi baffa kawata ne, kwanaki ya so ni amma Allah bai nufa ba" tace saboda ta san babu ɓoye ɓoye tsakanin su.
"Ai na sanshi, aboki na ne tare mukai karatu lokacin ba su dawo Qahɗaanie ba, ba wani abu zamu yi waya" yace yana mikewa. Ita mamaki ya cika ta mai Sufyan ya faɗi da ya ke kumbure-kumbure.
Khuder na fita bai tsaya ko ina ba se gidan Salmah. Bayan sun gaisa ne ya kalli idonta ya ce "yanzu kin san kawarki ba ta da kamun kai kika rufa min, ni ban taɓa zina ba kuma soyayya ba zai sa na samar ma yayana mazinaciyar uwa ba." takaici ya cika Salmah don ji take da ma ita ya zaga akan ya aibata baiwar Allah Fatimah
"Au wai baka da labari, yara uku ta haifa gaban Fatiha fa, ai soyayya ba ruwan shi da aibu in kana son mutum yanda yake za'a so shi, Allah kaɗai ya san yawan kwan da kayi asarar su gara ita ta haife" Ta na kaiwa aya ta wuce ɗaki ta barshi nan tsaye. Muhammad na masa magana amma inaa duhu kawai yake gani haka ya juya a fusace ya bar gidan. A ranar ya yanke shawarar auren Aisha budurwar da ta mace a son sa yayin da su ke jami'a.
***
Ganin anyi sati babu labarin Khuder ne ta tuntuɓe Salmah, nan ta fishe mata abin da ya haɗa su da ce ma Muhammad da yayi "Ai duk wanda ya san Sufyan ya san kura ne a kan mace, akan me zai sa in auri raguwarsa" Nan Bakin ciki ya mamaye zuciyar ta, hawaye ke zuba daga idonta zuciyar ta na quna
"ki gode ma Allah da yanzu ya miki hakan, da sai da aka yi auren ne ya sake ki fa? Ko kuma a ce se bayan an saka rana ne ya miki wannan tijarar, ai ki kwanta ki more Allah ne ya kwace ki daga mugun miji" haka salma ta cigaba da bata baki har ta samu kanta.
***
A kwana a tashi ba wuya su ka kammala karatunsu cikin nasara sannan aka ɗauke ta aiki kasancewar ita ta buɗe ajinsu a maki. Anan ne kuma sabon tashin hankali ya zo mata saboda damuwa da mahaifiyarta tayi akan rashin aurenta da kuma sauran matan mahaifinta, tun bata damuwa har ta kai ga damuwa. Samari da mazan aure ma su zuwa mata su kan zo ne da sunan za su aure ta amma da magana ya dan kwana biyu sai su fara neman jikinta.
Wasu kuma tun a zuwan farko da neman biyan bukata su ke zuwa ciki kuwa har da AbdoulBaar da farfesa Jabir da wasu da duk su ka ɗauki aniyar sai sun bi hanyar da ta tanadar ma mijin aurenta kawai.
***
Hawayen da ya zubo mata ta goge bayan ta gama tuna rayuwar ta.
"Ya Allah don rahamanka da tausayinka, kai ne sarki, buwayi gagara misali wanda in ya so aukuwar abu ya kwance kun fa ya kun. Ya rabbi kai kaɗai nake bautawa kuma gareka kaɗai nake neman Taimako ka gafarta min, ka yafe min ka zaɓa min abokin zama zaɓin ka ba nawa ba. Yaa hayyu ya qayyum bi rahmatika astagithu" Ta maimaita ya fi a kirga kana ta rufe da salatin annabi.
"tab in ba don bawan Allahn nan da ya zo ba da yanzu an min tsirara a bainar jama'a" Ta faɗi a bayyane tana kara hamdala tana mai mike wa. Salmah ta kira a waya ta bata labari
"Amma ke ma Fatima abin duka kike, yanzu har kina da zuciyar kula khuder, ni wallahi ba ni ya mawa ba amma tsakanin mu sallama" Ta ce tana tsaki.
"Salmah auren nan nake so na yi in huta da rigiman su Mamie" tace tana hawaye
"Toh za ki yi ma kanki abin da Allah bai miki ba? Ko kuwa don kina son ki yi aure shike nan kowane kare da doki za ki aura, ki cigaba da hakuri ki yi imani da Allah ki yarda dashi zai baki mijin da kullum sai kin gode ma Allah" Salmah ta faɗi cikin rarrashi.
A haka su ka rabu Fatima ta isa gida zuciyar ta na sanyi saboda kalaman Salmah a gareta.
Ku yi hakuri gobe Insha'Allah zan
turo wani mai yawa. Gaba daya komi ya tsaya min ne chak daz y nai saurin summarizing fb ɗin. Thank you ol
Love
Ummu-Abdoul
Adjetey Tetteh ne zaune a filin jirgin Kasar Habasha in da jirgin su ya tsaya shi kuma yana jiran cikan lokacin da jirgin su zai ɗaga Kasar Masar in da ya samu gurbin karatu a jami'ar Ain Shams University in da zai karanci Shari'a. Karfe huɗu jirgin su ya tashi daga Habasha, ya zauna jigum yana nazari, tunano babban aikin da ke gaban shi da auren da Ubangidansa ke shirin k'ak'aba masa, ga labarin kashe yan uwansa na fashi da ya ji sifeto janar ɗin ya jagoranci yi da wasu ababen su ka dinga masa yawo a kwakwalwa.
" Ina so ka dawo da shiri, in mulkin
Qahɗaanie ya dawo gefenmu tabbas babu yanda za'a yi a ce wani bare ne
zai zama babban Alkalin Kasar nan, shi ya sa na maida maka suna
Abdullah Saifullahi, in ka zama akwai
wa'inda za mu tura gidan yari kawai
mu manta da lamarin su " ya tuno maganganun Aamir a daren da zai baro Zangon Qahɗaanie.
" Kaga hakan na nufin kila wata rana
kayi sarki ko kuma ka zama fiye da
Aamir a mulki" zuciyar sa mai son qawa ta ayyana masa, bai san lokacin da ya saki murmushi ba wanda yayi daidai da isar su Kasar Masar.
***
Ko da Fatima ta isa gida da niyyar ba Abbie labari, hatsaniyar da ta iske a gidan ne ya sa ta jan bakin ta tayi shiru.
"Ai wallahi se dai ka sake ni, aure za'a yi shi nan da sati biyu babu fashi, akan wani dalili za'a bar min 'ya ta yi kwantai, miji ya fito ka ce baka yarda da shi ba, ohhh ruwan idon er gaban goshi kake son rufe wa da ya ta, sanda kannenta da sa'o'inta ke aure uban wa ya hana mata yi, sai an taɓo ku yanzu ku fara tauhidin karya lokacin ta ne bai yi ba" faɗin Ammi Hajiya Amina cikin ɗaga murya, hawaye na zuba mata
zai mare ta Fatima tayi sauri tarewa, cilla ta yayi gefe ya nuna ta da yatsa
"Ke don baki da hankali kaifin halshenki bai tsaya a kaina ba sai ya kai ga Mahalicci, in ma ruwan idon ne ta yi ina ruwanki, kenan akwai tauhidin karya da gaskiya, musulunci dama in ka so yai na karya in kaso kayi na gaskiya ne da kike ba da wannan fatawa.
Mutun kan zama sanadi ne, naji tayi ruwan ido ya zama mata sanadin rashin aure da wuri ko? Amma dai Allah babu mai sa shi babu mai hana shi, ashe zubar da madara da kika yi kika ce min qaddara ce ashe tauhidin karya ne ko yanzu aka baki dama yi zaki yi.
Na gode Allah Fatima tayi ruwan ido amma kuma ba'a kama ta da badala ba, kuma ina da yakini kamun kan da tayi Zai sa Allah ya bata mijin da ya fi na dubu, aure ne nace ba zan ba da ya ta ga wanda ban sani ba" ya ce yana shirin barin wajen don hawayen da ya zubo masa, faɗi yake a ransa "ashe ba Yan matan da su ka daɗe ba aure kaɗai ke jin jiki da damuwa har iyayensu" don tun da ta fara babu abin da ɓata masa rai sama da wannan. Karaf se ya ji tace
"in dai zancen Yan Hilaalu ba gaskiya bane na zaman ka shege toh ka aurar da ita ga masoyinta, amma in Kaki Kaga ka tabbatar da zancen su don shege ne kawai bai son raya sunna." tace tana shigewa ɗaki da rufe kofa.
Duk wani mai hankali yaro da babba ya ji zancen kamar dirar aradu. Hajiya sadiya da kan biyeta tafi kowa shiga damuwa don faɗi take
" Haba Amina wannan diban albarka har ina? Wai baki san tausasa halshe ga makiyi ma aikin lada ne balle kuma ga wanda yake wajibi a gare ki, Abbie don Allah kayi musu yanda su ke so, ni ban son fitina" ko kallon su bi ba ya juya, babu wanda yayi yunkurin bisa sai fatima da ke kuka kamar ranta zai fita. Hawayen da ta gani a idonsa ta fara sharewa, cewa take
Add Vote
"Abbie ka aura min duk wanda ka so, zan zauna zan yi biyayya ba zan jure ganinka cikin damuwa ba" shafa mata kai yayi ya Mike ya faɗa makewayi, nan ma alwala yayi ya tada sallah duk da kasancewar maraice ne lis ba'a nafila amma abin da yake bukata kawai shine ya samu ganawa da Mahaliccinsa cikin soyayyar da babu kamarta (sujjada). Ya fi minti talatin a sujjada yana kuka yana mai fadawa Allah damuwar sa, Fatima nana zaune tausayin mahaifinta na kara mamaye zuciyarta, tana mai kara gode Allah da mahaifin da ya azurta ta da shi.
"Abbie ka yafe min, na bar maka. Zaɓi ka zaɓa min duk wanda ka so ka aurar da ni ka huta da gori, kayi min rai" Ta ce sanda ya kammala addu'a ya shafa. Murmushi yayi ya ce
"Allah ne mai azurtawa walau arziki na kuɗi, ya'ya ko abokin zama. Duk wanda aka ma gorin arziki sai Allah ya azurta shi da wanda yafi na mai Gorin albarka. Za ki yi aure Fatima kuma kowa sai ya so ace shi ya samu mijin da zaki samu. Zubaida kuma ranar Juma'a zan ɗaura mata aure kuma a ranar za ta tare a gidanta " ya ce yana murmushi, ganin hawayen ta yaki tsayawa ne ya fara tsokanar ta har su ka dara, nan su ka fito dakinsa suna dariya abin da ya ba mutanen gida mamaki.
" Zubaida " ya kira ta yana mai ɗaga murya, jiki na rawa ta fito ita ma idanunta sun bayyana alamun ta sha kuka ba ko kaɗan ba.
"shi Abdullahin yana ina kika ce?" Ya tambaye ta murya a sanyaye kamar ba shi ya tashi dukanta ba
"Abbie ya je karatu ne Kasar Masar toh shine ake so in je chan dan na cigaba da karatu nima" Ta maimaita cikin tsoro.
"in kun yi waya toh ki ce ranar Jumma'a za'a ɗaura aurenku a fada, gobe zan je in sami mai martaba" ya ce yana ficewa daga gidan zuwa masallaci.
"Aaa lallai mun yarda Fatima er Abbie ce, wato kun Shige ɗaka kun kimtsa tsakanin ku, Allah sa hakan ne Alkhairi" cewar Mamie haj sadiya. Nan duk suka sa dariya haɗe da fara shirya ma bikin.
Ko da ya dawo bayan sallar isha'i ba abin da ya nuna na ɓacin rai, tare da matan su duka ya ci abinci daga nan su kayi hirar duniya.
***
A fada kuwa bayan sarki ya shiga ɗaki ya nemi ganawa da iyalinsa a karo na biyu duk a dalilin Wasikar Ansari. Bayan sun zauna da matansa da yarana maza da ya mallaka ne ya buɗe taron da addu'a sannan yace
" Nayi tunanin fitowa in bayyana AbdulHaleem a matsayin yarima mai jiran gado. Dalili na kuwa shine tsoro ba namu bane, kuma shi saifullahi ya kamata ya san matsayin sa ba zai ci gaba da zama barazana a garemu ba. Kuma na baku sati ku samo matan aure" ya yi shiru yana kallon su duka da kuma yanda su ke tafiyar da fuskokin su a dalilin waswasin da su ke a zukatansu.
"Allah qara girma Zaki, ka bani izini in kawar maka da shi daga doron kasa, ba zai cigaba da zama barazana ga masarauta ba" AbdulHaleem ya faɗi yana mai tsanar Ansari
"Hakan bashi a cikin tsarin mulki, in kace da an maka abu ka yi kisa wata rana zaka nemi wanda za ka so ka kashe baka samu ba, wanda ya kashe barci kuma ai ya gama barci" sarki ya faɗi yana dariya
"Kaga kenan bai cika zama sarki ba, ɗazu yake ce dani in da hali a nema masa auren yarinyar nan da ya taimaka amma bai sani ba ko za ka yarda ya aureta don kamar Fulani ce, Kaga kenan ba jinin masarauta bace" Ummu Maryam ta faɗi. Bakin ciki ya taso ma AbdulHaleem, akan me zata sa shi yin abin da bai iyawa, auren baiwa, duk karatunta ya kamata Ace jinin sarauta na yawo a jikinta ko yaya ne. Hawayen da ya ji ne yasa yayi saurin sauke kansa qasa hakan ya sa mai martaba tunanin kunya ce tasa shi hakan.
"MaashaAllahu Barakallah, zan aika a bincika min asalin ta gobe, kuma za'a yi nan ba da jimawa ba. .
AbdulHaseeb da Ummu Hafsa na zaune takaicin duniya ya cika su, yanzu duk abin su zai tashi a banza kenan.
" Allah taimaki zaki, abu na gaba don Allah a AbdulHaseeb sarautan, Allah barshi kar a faɗi, ka gina min katon gida can waje da fada don zama da matata" AbdulHaleem ya faɗi bayan tunanin irin horon da zai mata don kuwa itace sanadin rashin samun sarautar.
Sarki dariya kawai yayi ya sallame su sai Ummu Maryam da ke da kwana ta tsaya. Suna fita AbdulHaseeb ya mata nuni da su kebe. Anan su ka shawarta zuwa wajen Ansari a wannan daren.
****
Satar hanya su ka yi cikin daren nan suka samu Ansari, sun feshe masa duk abin da ya faru, nan shi kuma ya shiga nazari.
"yauwa, abu ya zo cikin sauki ma. Kin gane Abdoulgaffar ai kanin mijinki, toh akwai amininsa in za ki gane shi Yahuza Bello kuma matarsa abokiyar tagwaitar matar Abdoulgaffar ɗin, sarki na son mutumin nan saboda dan uwansa, yana da ɗiya Fatima abin da za'a yi ka ce da mai martaba Fatima kake so, ina mai tabbatar maka babu yanda za'a ayi sarki ya hana ya ba jinin Yahuza zama matar sarki " dariya duk su ka yi nan su Abdoul haseeb su ka koma.
Asubahin fari Ummu Hafsa ta sami sarki ta faɗa masa wacce Abdoul haseeb ke so, sai da yayi Jim sannan ya ce
"tun yaushe su ka haɗu, bana son aikin gaggawa fa" ya ce yana kallonta, take ya karanci firgicin da ta shiga amma ya basar yana jiran amsar da zata bashi.
"eh! Toh gaskiya bai riga ya mata magana ba, amma dai ya san ba za ta ki shi ba" tace ta na yake.
"Toh zan bincika in ji in har ba ta da wani, don ba zan yi nema akan nema ba. Allah ya tabbatar da Alkhairi" ya ce yana mai kauda kai alamun ya gama da ita don shi jikin shi ya gagara yarda da ita duk da bai son ya yanke hukunci akan zato. Ta fita tana roqon Allah ya sa yanda baffanta ya shaida mata cewa babu wani a tare da ita ya tabbata a hakan. Nan dai ta isa ɗaki ta iske mai kula da kayan sawarta ta fito mata da shi, masu hidimar wankanta suna haɗa mata ruwan wanka, nan ta shiga ta yi wanka ta fito, aka shafe ta da mai kana ta sa kaya. Sannan ta kwanta don komawa barci kamar yadda ta saba.
***
Sarki na isa fada ya fara sa a binciko masa wacece AbdulHaleem ya taimakawa sannan a binciko shin tana da wani in babu ya bada izini a nemi mahaifinta a ce ana neman iri ya basu lokacin da za su zo bikin tambaya.
Dan sako wanda ya kasance babban ɗan yayan mai martaba. Shi kuma yana fita daga fada AbdulBaar ya nema ya tambaye shi wacece yarinyar shi kuma sanin da yayi Alhaji Muhammad yafi kowa tsanar talaka ko wanda yake ba jinin sarauta ba ya sa shi faɗa masa wacece a tunaninsa rashin mutunci zai karta mata don shi yaya yake a wajen mahaifiyarsu. Duk da yaya yake a wajensu in aka bi gefen mahaifinsu ne.
Jin sunan wanda aka kira ya sa shi dariya, tare duk su ka taso da Alhaji Yahuza a fada sai dai tun bayan rasuwan Abdoulgaffar zumuncinsu yayi nisa don shi bai faye harka da wanda ba jinin sarauta ba duk kuɗin sa, kuma shi ya sa ma AbdulHaleem wannan ɗabi'a don rayuwar da su kayi da shi a kasar America.
Bai qara ce da AbdulBaar komai ba ya ja mota ya fice, hakan ya kara faranta ran sa don ya san daga ita har ubanta a gidan yari za su kwana in kuwa hakan ya faru ko fyade ne sai ya mata a cikin sel dinnan abu ne da ya ba gandirobobin kuɗi ya samu shiga. Da wannan farin cikin ya shiga cikin gidansu ko ya samu ya kwanta don ya sha alwashin raya daren yana horar da Fatima ta hanyar da har abada ba zata taɓa mantawa ba.
***
Ko da Alhaji Muhammadu ya isa gidan su Fatima ya iske Alhaji Yahuza ya fito zai shiga motarsa da aka fitar wajen gate.
"wa nake gani ne haka amma dai ɗan nan namu ɓatan hanya yayi ko" yace da shi bayan ya ɗan rungume shi.
"Kai Ammou, ka san dai bana zama ne shi ya sa" yace yana dariya, duk izzarsa yana girmama Alhaji Yahuza duk da ya ɗan girme su kaɗan amma kasancewa Abdoulgaffar kanen mahaifinsa ne ya sa yake kiran su da Ammou
"Ko da yake saraki ake bi amma ka san dai shi ke bin iyayensa, ai ina shirin isa fada ne akwai auren da nake so ayi ranar Jumma'a ne, toh abin ya zo ba notice ne shi yasa" ya ce yayin da suka karasa cikin falon tarbon bakin sa. Kayan shayi aka kawo masa bayan ya yi waya cikin gida mahaifiyar fatima ta shigo da su.
"Hajiya Hafsa kuna lafiya, ya muka kara ji da hakuri" ya faɗi yana share kwallan da ya zo masa, yana daga cikin abin da ya sa baya neman Alhaji Yahuza don duk ya gansa sai mutuwar amininsa kuma baffansa ya dawo masa sabo, haka duk suka haɗu sai ya sake musu ta'aziyya shekaru talatin da huɗu kenan amma kamar minti talatin da huɗu.
"Sai hakuri Alhaji, muna musu kyakkyawar fata, in da suke yafi nan da su ka bari. Allah ya mu dace" tace tana mai jin zugi ita ma.
"Mai martaba ya aiko ni, AbdulHaleem ya ga Fatima yana so, shi ne aka ce in zo ka ba mu lokacin bikin tambaya"
Add Vote
Sujjadan godiya kawai Alhaji Yahuza ya yi don bai taɓa ganin ijaba cikin gaggawa kamar wannan ba. Yana dagowa ya rungume Alhaji Muhammadu sannan ya ce
"Fatima ta yi hakuri, Fatima ta ga jarabawa iri-iri, na san Allah ba ya barci kuma maji roko ne, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
"Ai na san ba wanda zai kai mai martaba murna, ba shi kaɗai ba duk wani ahli na gidan nan zai farin ciki don kuwa kamar an dawo da Ammou Abdoulgaffar ne" ya ce shima cike da farin ciki. Ganin Alhaji Yahuza bai kawo zancen abin da ya faru ba ya sa shi ma bai dago maganar ba. Anan su ka tsaida sati uku masu zuwa a matsayin ranar bikin tambaya.
***
Bayan tafiyar Alhaji Muhammadu, tafiya wajen aiki alhaji Yahuza yayi ba tare da ya koma cikin gida ba balle ya faɗa musu abin da ya faru. Nan ya kula a rana ba zai faɗi ba sai ana gobe bikin, duk wani shirye-shirye zai bada kwangilar yi ne don kuwa a Hilaalu Sambo za'a yi ko don bakin cikin masu bakin ciki ya kashe su.
Shi kuma Alhaji Muhammadu ko da ya isa fada nan ya faɗa ma Mai martaba wanene Mahaifin Fatima da kuma yanda su ka kwashe. Take ya ciko Nutud dubu ɗari uku da zinari dirhami arba'in ya ce ga sadakin AbdulHaleem nan ya bada gudunmuwa. Nan yan majalisa su ka masa godiya da jinjina akan kokarin da yayi.
Sarki dai ya shiga ruɗani don baya son abin da zai kawo masa matsala a cikin gida, da Ace Muhammad bai furta ma su AbdulHaleem ba da babu abin da zai hana ya juya shi ga AbdulHaseeb don ya san ya fi nagarta sannan AbdulHaleem ya fi hakuri da juriya yayin da ya rasa abu.
Haka ya zauna shiru yana neman taimakon mai duka, ba zai ɓoye musu ba amma ba zai faɗi ma su wa za'a ba ma wa ba.
"ina so zancen kada ya fita bangon majalisan nan, in Allah ya kaimu sati uku ma su zuwa Daula za ta san wanene mijin Fatima. Allah ya nuna mana, Muhammadu ka san ana babban wa uba, toh ka jagoranci komai na neman auren nan. Allah ya maka albarka" ya ce yana mai rufe zama.
***
Duk yanda Alhaji Yahuza ya so ya ɓoye murnarsa ya gagara don haka ya dinga sadaka da kyaututtuka yana gode ma Mai duka.
Ko a gida sai da aka fahimci farin cikin sa, duk yanda aka so a ji dalilin ya ki ya faɗi sai cewa yake
"Addu'a nayi jiya kuma Allah ya amsa min ita nagani a yau" nan dai su ka dinga masa tsiya ba tare da sun hasaso komai ba.
Sarki kuwa sai da dare ya sake ganawa da iyalinsa. Tare su ka ci abincin dare su duka sannan su ka taba hira.
"wai kun san wani abin mamaki, Fatima Yahuza Bello ita ce yarinyar da AbdulHaleem ya ke so, haka itace yarinyar da kanensa AbdulHaseeb ya gani yace yana so. Toh abin da ban sani ba shine yaushe kuka fara ɓoye ma junanku sirri da har aka samu wannan akasin, ko kuma duk ku biyun wani abin kuke nema da kuka ɗauko min ta hanyar da yake rauni a gare ni" ya ce yana karantar dukkansu, so yake ya fahimci mai gaskiya a tare da su.
" Ni dai na san sunanta Fatima, AbdulBaar ne ma ya nuna min ya Santa, kuma ni in bacin Qalbi da na ce ma ina sonta har ta faɗi maka ba wanda ya san ina sonta, amma in shi yana sonta da gaske ne na hakura" AbdulHaleem ya faɗi yana ciccijewa don kuwa shi dama ba kalarsa bace duk da ya yini tana masa gizo amma zai yi ne don farin cikin ummansa
"Ni dai ina sonta kuma ba zan taɓa hakura da ita ba, haka kawai don na ce ina sonta saboda wani buri da ake son a cika a ce shima yana sonta" AbdulHaseeb ya faɗi har da hawayensa don burinsa ya zama sarki kuma duk hanyar da ya dauko sai ta rushe
"Ni kuwa mamaki kuke bani, tun kuna shekara goma a duniya mu ka tafi Kasar Amerika tare, nice uwar ku nice makwafin ubanku, na rike ku tamkar AbdulHaleem da AbdulHaseeb ɗin da na haifa AbdulHaseeb ya rasu. Na baku tarbiyya ba tarbiyyan son mulki ba, ban dawo ga miji na ba sai da kuka kammala jami'a kuka mallaki hankula.
Add Vote
Dawowarku bayan kun yi digirgir na fahimci AbdulHaseeb ya fi hankali da daraja dan adam, na fahimci cewa kun watsar da kusan rabin abin da na ɗaura ku akai ban furta muku ba ban damu ba amma yau kun tabbatar min da cewa na faɗi a matsayin uwa, tun da zaku kalli idon Zaki ku yi rashin kunya.
In ma wani abin kuke sha toh ku dawo da hankalin ku waje ɗaya, Fatima ba rabon ko guda bace a cikin ku. Don mace ba za ta shiga tsakanin ku, ba zata rusa ginin da na sadaukar da son mijina wajen gina shi ba" Ummu Maryam tace hankali a tashe. Don ta na iya hango kiyayyar da ke kwance a idanunsu.
"wai duk za ku barni in ji sanyi ko kuwa za ku karasa ni da tsufa na" mai martaba yace yana mai ɗaga murya. Nan duk suka yi shiru suna sauraronshi.
"Fatima dai ya ta ce, sannan zan nema ma AbdulBaar aurenta haka zalika shi zan naɗa Yarima mai jiran gado. In kun ga dama ku kashe shi, kafin ku an kashe min uba, an kashe min Kane. Kun ga kenan ba akanshi za'a fara mutuwa ba sannan zan sa muku idanu don na fara shakku akan ku duka, son sarauta ai ba hauka bane" da haka ya bar su kowanne da abin da yake saqawa a ransa. Haka su ka rabu babu annashuwa a tare da su.
***
A cikin Sati uku duk yanda su AbdulHaseeb da mahaifiyarsa su ka so tarwatsa auren sun gagara, ga sarki ya tsaurara musu don duk wani motsi na su yana sane da shi hakan ya hana musu isa ga Aamir Ansari.
A ɓangaren su Alhaji Yahuza kuwa bai faɗi m kowa ba, Jumma'a na zuwa aka ɗaura auren Zubaida da Abdullah Saifullahi, sai a lokacin Alhaji Yahuza ke jin labarin ɗan Saifullahi alhamzee ne, sannan a lokacin ya sa ranar bikin tambayar Ramla kanwar Zubaid kuma autar Hajiya Amina daidai da ranar na Fatima.
Nan fa su ka fara shirye-shirye da jefar da maganganu ga Fatima wacce hankalin ta yayi dubu ya tashi don gani take tana daga cikin wa'inda Allah ya qaddaro ba su da rabon aure a duniya.
Ranar bikin fili guda Ya ware a Hilaalu Sambo ya sa rumfa da kujeru ya shirya don yin bikin a wajen. Mutane sun yi mamakin yawan mutanen da ya gayyata don ciki da wajen Qahɗaanie ya gayyato abokan hurɗa da yan uwa.
Ganin tawagar masarauta ya sa sauran dangin sa da su ka yi saura shiga taitaiyinsu, nan tsofaffin ciki wa'inda su ka watsar da shi ciki ya fara murdawa don bakin ciki da hassada.
An fara taro da addu'a kafin Alhaji Muhammadu ya mike ya nemi auren Fatima ga Dan uwansa AbdulHaleem Abdul-Jabbar.
Nan su hajiya Amina su ka tsure don sam ba su san da wannan ba, Fatima na zaune da su Salmah sanarwan ya daki kunnuwanta amma bata yarda ita ɗin bace sai da ta ji mahaifinta na faɗin ya bada, sannan ya tsayar da ranar bikin ta a saba'u ga wata mai kamawa. Nan maroka su ka fara sana'ar yayin da yan bakin ciki suka yi mutuwar zaune da tsaye. Shi kuma mai shaila ya fara yayin da kafafen yaɗa labarai da kafafen internet su ka ɗauki labarin tambayar auren yarima AbdulHaleem da Fatima Yahuza.
Tambayar Fatima ya sa alhaji Yahuza bai yi bakin cikin rashin ganin dangin manemin Ramla ba, da ya bincika sai ce masa hajiya Amina tayi ai tun da yana zuwa zancen an san da shi a sa rana kawai da na Fatima. Don kuwa ba za'a yi bikin Fatima ba tare da na Ramla ba.
***
Ko da labari ya isa Fada nan sarki ya bayyana AbdulHaleem a matsayin Yarima mai jiran gado, wannan sanarwan ya sa aka fara bikin a take duk da ba'a shirya ma bikin ba, amma dogarai haka su ka ciccibo shi ba su dire ba sai kujeran mai jiran gado. Mamaki ya cika shi son shi ya cire rai da samun komai tun da mahaifiyarsa ta zaunar da shi ta yi masa nasiha. Tun a lokacin ya fara shirin zuwa karatun gaba da digirgir (post doctorates) a chan jami'ar da su ka gama.
"Allah ja zamanin Sarkin gobe, mai hakuri bawan mai hakuri, AbdulHaleem mai daraja da daraja mutum, masoyi talakawa zaɓin su. Allah yayi jagora angon Fatima Allah ya nuna mana mu zuba ruwa a kasa mu lashe" haka su ka dinga kwazaza shi bai iya cewa komai ba sai hawaye. Lallai Allah maji rokon bawan sa ne. Don tun da mahaifiyarsa ta ce ya dinga faɗin YAA RABBI INNIE LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FAQEER bai taɓa gajiya da ambata ba, yin sa yake cike da imani da tsoron Allah sai gashi Allah ya masa arziki ta inda ya ke zato da inda bai zata ba.
Duk yanda AbdulHaseeb ya so ya ɓoye bakin cikinsa ya gagara, don kasa zuwa wajen yayi balle ya taya shi murna.
Labarin na iske Amir Ansari hankalinsa ya tashi don bai taɓa saɓa alkawari ba sannan bai taɓa nema ya rasa ba amma Qahɗaanie na neman ya gagare shi da duk wani da ya haɗa jini da shi a kusa.
"Zan nuna maka kalata" ya faɗi a bayyane sannan ya juya ya shige ɗaki. Tun bayan da ya tura Zubaida Kasar Masar in da ta iske Adjetey a matsayin miji ya kira su a waya ya tabbatar da ta isa lafiya bai sake ɗaga waya ya kira su ba, don yana son su saba da junansu sannan soyayya ta shiga tsakaninsu yanda duk runtsi babu mai iya raba su.
"Aikin nan Adjetey kaɗai zai iya min shi a tsanake ba tare da an samu akasi ba" ya faɗi a bayyane yana mai kiran adjetey.
***
0 comments:
Post a Comment