"Ai sama jinkiri alkhairi ne matukar mutum yayi hakuri, don gashi nan da yan shekaru za ta zama sarauniyar Qahɗaanie" cewar sashin da ke mata fatan alkhairi.
"Ap ayi dai mu gani, dama abin da su ke jira kenan shi ya sa ta ki auren talakawa. Ai kam dai babu auren da zai yiwu tsakaninsu." inji hasidin iza hasadin.
An tashi daular Qahɗaanie cike da tashin hankali, don an tashi duk dawakan fada an kashe su, sara daga bayan wuya. Dogarai masu gadin dawakan kuma an iske su kwance suna sharban barci wanda daga gani an san wani abin su ka sha ko aka fesa musu.
Faɗin bakin cikin da sarki ya shiga ba zai misaltu ba don ganin da yayi ma dawakai hamsin ɗin da masarauta ta mallaka na sarki da yayansa duk kwance a mace ya tayar masa da hankali, don ya san tabbas wannan sheda ko kuma alamu ne da ke faɗin rayuwar al'ummar Qahɗaanie na cikin hatsari.
Add Vote
Wacce ta yi ta yi mail akan nayi hkr ba zata sake ba. And from comments se na ga tun da mun fara gara mu kammala don kaunar ku na daban ne tunda ghosties sun fi kowa comments a post ɗin. but Insha'Allah 60hours after my last post am taking it down.
In da corrections ko shawara kindly send to safiyyahjibril@gmail.com
Thnx alot
Love
Ummu-Abdoul (Safiyyah)
Ban yarda a copying kowane lbr na
zuwa wani kafa ba, in an ga gyara a min bance a sarrafa min lbr ba.
Hotunan da nayi amfani da su sato
su nayi a Instagram, ban san masu shi ba ban kuma ce su ne ba, sun min kyau ne naga za su fi bayyana
abin da na rubuta...
Kun san ina son ku kuwa😍😘. Ina son
ku wujiga-wujiga..
Da na samu sarari zan muku, amma
daga post na biyu bayan wannan ku zama cikin shiri, komai zai iya
faruwa. Kar ku ce ban faɗi ba.
Ummu-Abdoul
***
Duk yanda yan majalisa su ka so su ji daga bakin Sarki ya gagara, shiru yayi akan batun mutuwar dawakan sannan a ranar ya sa aka je Kasar Poland a jirgin masarauta don a shigo da wasu dawakan. Babu abin da ya tsaya masa a rai sama da irin kisan wulakanci da aka yi ma dokinsa da ya ke na hawansa. Wannan kaɗai wata wasika ce mai zaman kanta.
Bayan an tashi majalisa ne yayyin sarki da su kai saura da kannensa su ka iske shi a ɗakin sa.
"Abdul-Jabbar me ke faruwa ne? Wa ke neman ganin bayan ka, na san haka kawai ba za'a tunkare ka ba sai an yar da alamun da tabbas za ka gani, sarauta da kake gani ba'a ganin hatsari a yi shiru, me ke faruwa ne" Babban su dattijo Mahaifin Alhaji Muhammadu wanda tun bayan rasuwan mahaifinsu ya zama uba ga dukkansu ya faɗi cike da damuwa.
"Yaya Abdulhameed, wannan aikin ba kowa bane sai Saifullahi Alhamzee, don shi bai yarda ya rasa sarauta ba hakan ya sa ya ce lallai a tilas AbdulHaseeb za'a ba yarima mai jiran gado saboda Hafsa."
"Don Hafsa yar yayansa ce sai ya zama dole jininta zai yi sarauta ko ba AbdulHaleem bane babba" cewar hajiya Aisha kanwar mai martaba kuma matar kanen Alhamzee. Wacce duniya in da wanda ta tsana suka tsane ta toh dangin mijinta ne don a cewarsu bai kamata ta qi taya Ummu hafsa kishi ba, me zai sa ta dinga magana da Ummu Maryam har ta taimaka mata wajen haihuwa.
"A bani dama in dau mataki akan wannan abin,don ni babu wanda ya isa ya taɓa min mahaifi ya kwana lafiya" AbdulHaleem ya faɗi yayin da yake shigowa ɗakin. Nan su ka maida kallo gareshi. Duk da saɓa ma dokar masarauta ya shigo lokacin da sarki ke ganawa da yan uwansa amma ya birge su don duk haushin Alhamzee su ke.
Add Vo
"Wani irin hukunci za ka yanke da ka san ba zai taɓa lafiyar mabiya ba, don ni tun ɗazu na kasa samun mafita" cewa sarki yana kallon sa.
"A matso da bikinmu tukuna, sannan kada zaki ya furta komai a kan maganar, zan yi tafiya ranar tara ga watan gobe, a can wajen tafiyar zan ɗauki hukuncin da yayi daidai, in Allah ya taikamaka komai zai zama labari don har fansan jinin kakana da baffa na zan ɗauka " ya faɗi cikin izza da birge wa.
" dawo da bikin ka ba zai yiwu ba don tun da ga haka kamar magana akai ne, biki saba'a ga wata za'a yi, sannan biki za ayi da ba'a taba irin sa ba. Saura kuma mun amince da shi" cewa dattijo Alhaji Abdulhameed.
"Godiya nake Allah ya kara girma" ya ce ya na ficewa. Nan sai zancen su ya koma akan AbdulHaleem
"Maryam ta yi kokari akan yaran nan, AbdulHaleem ka barshi dai da halin Muhammadu AbdulHaleem mutum ne da ya cancanci zama sarki, wancan halin kuma shi ma zai daina da yardan Allah" cewar Hajiya Rumaisa yayar mai martaba.
"Ga kyauta ga biyayya ki dai barshi da mulki, kuma ai saraki sai da mulki" haka dai su ka dinga hira har aka kawo musu gasasshen cinyar sa suka zauna akai. Su na ci suna hira har sai da aka kira la'asar sannan su ka tafi zuwa gidajensu
***
Rashin jin wani magana daga bakin mai martaba ya sa kowa ya fita batun kisan da akai wa dabbobi, kowa ya maida hankali wajen al'amuransa na yau da kullum.
"Ummuna kin ga dai karfi da yaji sarautan nan na neman fin karfinmu, jiya AbdulBaar ke fada min AbdulHaleem ya ci alwashin wulakanta ni matukar ya tabbata sarki, ashe dai zulwajhaini ne kullum ina kwana da Tsoron ranar da zai gano makirci da muke" Ummu hafsa ta cika da murna, ta ji daɗi yanda AbdulBaar ya goya mata baya ya kuma yi mata aiki yanda ta sa shi.
Maraicen jiya ta aika a kira mata
AbdulBaar inda ya same ta babu ɓata
lokaci.
"Ya banga ka yi wani abu ba akan
matar da Yarima zai aura, bincike ya
tabbatar min da cewa tsohuwar
budurwar kace, haka za ku sa ido kai da auta ya tashi da sarauta da kuma mata ajin farko" Ta ce masa tana
karantar yanda fuskar sa ke sauyawa
zuwa ga damuwa.
"Ummu ya za mu yi, mai martaba ya
riga ya gama yanke magana, yin wani
abin zai sa ayi tunanin muna da
hannu a kisan Dawaki, shi ya sa na
zaqe ina ba da goyon baya, jiya muka
amso akwatuna da zinarin da ya
Kwaso mata wanda za'a kai na aure" ya ce yana mai jin ciwo, ya so ya
mori Fatima amma duk yanda ya bi
don cutar da ita sai ya ga Allah ya
buda mata wani hanyar da ya fi inda ya so rufe wa.
"Akwai hanya ɗaya, da ta nan za'a ci
nasara. Shiga tsakanin sa da
AbdulHaseeb don kuwa shi ne karfin
sa, raba su zai sa ayi saurin samun
nasara a kansa. Ka ga shegiyar can
ɗiyar bayi babu abin da ta musu sai
cusa ma junansu kauna mai tsanani a tsakanin su" haka ta cigaba da faɗa
masa irin maganganu da zai faɗi ma
AbdulHaseeb akan shine shirin
AbdulHaleem in ya zama sarki .
Add Vote
"Ummu! Ummu!!" ya kira ta ganin ta yi nisa a cikin tunani. Kiran ne ya dawo da ita duniyar tunanin abin da suka shirya da AbdulBaar.
"Nayi mamaki ne ai, amma mutum ba abin sheda bane, kada ka damu, ka nuna babu damuwa a yi bikin nan lafiya, da yardan Allah zamu kai ga nasara. Ka cigaba da hakuri, nima ba zan zauna ba" tace tana shafa masa kai. Haka su ka cigaba da hira har aka kira sallah.
***
Shi kuwa AbdulHaleem yaji yayi gaba ɗaya daga masarauta,, fushi yake da kowa musamman mahaifiyarsa don gani yake ita ta laqa masa auren da bai shirya ba. Zuciyar sa ta cika da kewan mahaifiyarsa hakan ya sa ya shiga ɗakin yana wani ciccijewa. Zaune ya iske ta, Qur'ani take karantawa tun da ta dago ta kalle shi bata sake kallon shi ba ita ma ta cigaba da karatun na ta. Ganin ba ta da niyyar idarwa ne ya mike ya isa gareta ya zauna manne da ita kamar zai maida ta jikinshi. Yana yi yana leqa Kur'anin da take karantawa. Nan ma ta yi banza da shi kuma ta cigaba da karatunta. Kawai sai ya fara bin karatun tare da ita, nan ne ta sakar masa dundu a baya.
"Wayyo Qalbi ciwo baya ya ɓurma" yace yana sosa wajen. Bata kula shi ba tayi addu'a ta mike don ajiye Kur'ani a wajen da ta ke shirya su.
"Wai ba ka tabbatar ban mutu ba, ai sai ka tafi ba ka tsaya min tsegege ba, ni Maryam za ka watsa ma kasa a ido ko, don na maka gata na baka mace son kowa" tace tana karkada kai
"Subhanallah! Ummu wa ne mutum, ai da hakan ne da yanzu bani don ba yanda za'a yi in tsira ina mai saɓa miki" Tayi banza da shi
"Anti a'azzu nasi alayya" yace yana rungumarta
"Da dagaske nice mafi daraja a gareka da baka wulakanta ni ba, don duk wulakancin da ka yi ma Fatima ni kayi ma wa. Ina da labarin baka taɓa zuwa ba. Hakan za'a yi aure? Yanzu ina so ka shirya kaje, ka kai mata wannan
sakon gaisuwa da soyayya daga gare ni kenan." bai iya musa mata ba ya wuce yana sake sake.
Motarsa ya shiga Lexus, ya kure wakar Humood Alkhudher ta Ha'anazah. Tafe yake yana bin baitocin ɗaya bayan ɗayan kamar shi ya rera ba Humood ba.
Sai da ya isa kofar gidan ya sake kallon kansa ta madubin motar ya ga yanda bakin kaftanin ya fito da shi, duba bayan motar yayi ya tsinto hula ya kifa, kayan mai martaba ya ba da odar su daga zaria shi kuma Allah ya ɗaura masa son bakin.
Kiran lambar da aka bashi a sunan nata yayi, nan ya karaci tsuwa ya katse ba tare da ta ɗaga ba, nan ya ji ransa ya ɓaci don in akwai abin da ya tsana toh ya kira a ki ɗauka. Ya saka makulli zai tayar da motar kenan ya ji an kira nan ya ɗaga ya ce
"kin raina arziki na ne da za ki jira ya tsinke ki biyo" yace a fusace
"Yi hakuri bana kusa ne, ina yini" tace masa don tun da ya amshi numbar ya tura mata sako.
"ki zo ki shigar dani kin shanya ni a kofar gida" ya ce haɗe da kashe wayar, nan ta cika da mamaki, ita irin nata jarabawar kenan. Gayle ta ɗaura mai ruwan ganye a Saman doguwar rigar ta ruwan hoda. Da ratsin bula da duwatsu. Bata tsaya wani kwalliya ba ta fita zuwa gareshi.
"Tabarakallahu ahsanil khaliqeen" ya ce sanda ta fito, wato a ranar da abin ya faru firgici ya ɓoye kashi saba'in na kyawun da Allah ya ɗora mata. Nan ya gode ma Allah da ya azurta shi da uwa ta gari don in ba don ita ba da yayi babban asara.
Bai nuna mata komai ba ko da ta karaso, ya amsa sallamanta kamar yana da ciwo a baki. Bata damu ba don ta daɗe da sanin halinsa daga bakin Salmah don ta feshe mata abin da ta jiyo kansa.
***
Ruwa da inabi ta kawo masa bayan sun shiga falon Alhaji Yahuza. Sake gaishe shi ta yi sai ta yi shiru abin ta. Ganin bai da niyyar magana ya sa tace
"Nagode da rannan fa, Allah kara ɗaukaka"
Kallon ta yayi, har cikin ransa ya ji daɗin addu'ar, ya ce Aameen kai tsaye tare da murmushi. Ina Aljanna Fatima ta jefa kanta don daɗi don murmushin da yayi ya kara haska mata kyawun mijin da zata aura. Haba shi ya sa Salma tace mata za su haifi ya'ya kyawawa.
"Ya su ummu, da fatan duk su na lafiya" Ta sake cewa a darare.
"Qalbie na nan lafiya kin tuna min ga shi ta ce na kawo miki, ita kaɗai za ki tambaya" ya ce yana kallon idonta
"Ita kaɗai na sani, a sannu zan Sam saura" tace iyakar gaskiyarta kenan. Take ya ji wani irin ni'ima don tsoron sa Ace dagaske budurwar AbdulHaseeb ne.
"Amma kin Sam AbdulBaar ko, ni ina da kishi, kuma duk abin da yake mallaki na bana tarayya da wani akansa. Ki kiyaye ki kula, sannan in kina da zuciyar saurin yarda da mutane ki aje shi tun anan. Gidan da zaki ko miji ba kya bashi dukkan yardanki don babu abin da giyar mulki bai sawa. In kika rike wannan zaki zauna da kowa lafiya. Ke dai kar ki cutar kar kuma kiyi Sakaci a cutar da ke.
Bana son gardama, sannan ban son mita, in kin iya karanta sakonnin da idanuna za su aika miki kin huta don ba kasafai nake magana ba.
Ina son uwata, in kin taya ni son ta toh inaga kin gama samun AbdulHaleem amma in kika bari taga abin qi a tattare dake toh ban san ya zan kwatanta miki irin kuncin da zaki samu ba" ya na kaiwa nan yayi shiru daga gani ya takura kansa ne wajen yin dogon magana. Ita kuma bata ce kala ba tana nazarin kalamansa ɗaya bayan ɗaya.
Har ya tashi zai tafi ya zauna kusa da ita ya dauke su hotuna, don har ga Allah ta masa kyau ta birge shi ainun.
Kinga zan kai ma Ummuna in nuna mata yarta. Da haka su ka yi sallama ya tafi a cewar zai dawo kafin a fara biki.
Add Vote
I dedicate this to Meenahassan for sharing her best quotes from BGGB, Thanx dear.
My lovely mumcy @aminabello thanks for sharing too.
Ps
Sharing doesn't mean copy and paste ooo, don't quote me wrong 😛😊
Ghosties 😢😎😎😎
Voters 💞💕😍😘
And above ol those that always give me the courage to type by their comments, I love u to d moon and back, I don't knw what to pay u with but I think u will ol feature in my next novel... A dalilin rubutu if time permits 😘😍
💕💞💞💞💞💞
Da kyar ta iya tashi daga falon zuwa cikin gida, gani take kamar barci ta ke yi za ta farka ta ga ba hakan bane, ko kuma ta shiga ta jiyo labarin an fasa. Kara zama tayi daɓas a kasa, saboda wani murɗawa da hanjin cikinta yayi.
"YAA ILAHI YA RABBI AGITHNIE" Ta faɗi da karfi. Shigowar mahaifinta ne ya sa ta mikewa da azamanta.
"Me ke faruwa ne, yanzu na iske Yarima zaune cikin mota, yace waya ya amsa amma daga ji wayancewa yayi" ya ce shima cikin tsoron abin da zata ce, rokon Allah yake a ransa akan ya tabbatar da Alkhairi don duk son su na su ga tayi aure ya fi son ta auri nagari mai alkhairi a gare ta.
"Abbie ya ce ya fasa ko" Ta ce se hawaye sharr ya fara zubo mata.
"shike nan dama na san bani da rabon aure a duniya" Ta ce cikin kuka da yankar kauna.
"Aaah! Wa ya ce miki zai fasa, ki zama mai yi ma Allah kyakkyawar zato. Shi ɗin mai yalwan Rahma ne, in ko kika ga ya fasa toh fasawa ne Alkhairi. Ki toshe kunnuwa daga faɗin mutane, ki kalli ni'imomin da Allah ya miki sai ki gode masa. Wannan shine sirrin rayuwa mai inganci " ya ce yana mai goge mata hawaye, sai kuma ta fara dariya, tunawa da abin da tayi kuma sai ta rufe fuska.
" Lallai Fatytyn Abbie ta shiga kogin soyayya,kar dai ki shiga gaba daya ki tsaya ki ga zurfin kogin tukuna " yace yana dariya, itama dariyan tayi sai ta nuna masa kyautan da Ummu Maryam ta aiko mata da shi. Nan ya yaba ya kuma kwaɓa mata akan kada ta nuna ma kowa don yanzu mutane abin tsoro ne. Da wannan shawaran ta shiga cikin gida, dakin Mamie haj Sadiya ta shiga don dama sun fi shiri rashin jituwar su a dalilin shawara da Alhaji ke yi da fatima ne.
"Har ya tafi kenan? Dafatan dai ya miki" Hajiya sadiya ta faɗi kai tsaye da murnar ta bayan ta amsa sallaman da Fatima ta yi.
"Ya tafi Mamie, addu'ar ku da albarkanku kawai na ke bukata" tace tana sunkuyar da kai.
"Ai ko da yaushe addu'ar mu ba ta wuce akan ku, ba yanda za'a yi mu yi addu'a ba mu sako ku a ciki ba" tace tana dariya. Haka su ka cigaba da hira tana faɗa mata wasu sirrikan zama da miji. Ki samu ki karanta littafin Gidan Aurena, nan za ki samu dabarun kawar da kai da ga fadawa matsalolin Gidan Aure. Sau da yawa akan kira miji mugun miji ne a dalilin na sa ɗaukan mataki daga wani laifi da matar sa ke aikatawa. Kin san maza sun fi yin abu a aikace ba wai su dinga magantawa ba. Ki natsu ki karanta, duk abin da kika kasa fahimta ki same ni zan miki bayani, babu kunya a tsakanin mu kin sani" Ta karasa tana mai mika mata littafin.
"Insha'Allah, Mamie na gode Allah kara girma" Fatima ta faɗi ta na murna.
***
A ɓangaren Yarima kuwa tun da ya fita daga falon ya samu waje ya zauna a motarsa yake kallon hoton da su ka ɗauka. Jin son ta yake tun daga tafin kafarsa har kwanyarsa, zuciyar sa na masa zugi kamar vibration din waya. Shiru yayi yana kallon hoton yana kara gode ma Allah akan arzikin da ya bashi ne ya jiyo sallaman Mahaifin Fatima. Abin da tun da yake bai taɓa ma wani in ba sarki ba shi ya tsinci kansa da aikatawa wato duqawa yayi cikin girmamawa ya gaishe da shi..
Add Vote
"har ka fito?" Alhaji Yahuza ya ce da shi bayan ya amsa gaisuwansa
"Eh Abbie! Na tsaya amsa waya ne" ya ce masa yana kara sunkuyar da kai. Godiya ga Allah Alhaji Yahuza ya sa ke yi saboda yanda ya ji labarin AbdulHaleem bai taɓa tunanin yana da ladabi ba.
"toh toh Allah huta gajiya" Abbie ya ce yana mai masa musabaha, da haka su ka yi sallama ya shiga ciki shi kuma AbdulHaleem ya tayar da motar zuwa gida. Wakar krish 3 ya kunna wanda aka yi na You are my love you are my joy. Yana tafe yana auno ai shi da Fatimansa ne su ke wakar shaukin so na shigansa, tun da yake bai taɓa tunanin zai so wata ba, dama an ce babu soyayyar gaskiya sama da soyayyar da ka fara a lokacin da baka taba tunanin zaka fara ba.
Dakin Ummu Maryam ya wuce cikin kosawa da son yin mata albishir. Har ya sa kafa zai shiga ɗakin sai ya tuna da ashe ya ce ba ya son ta, nan take ya fuske ya mayar da duk wani farin ciki da yake ciki ya maida fuskar sa ba yabo ba fallasa.
"A'a tilona ka dawo, da wuri haka na sha ai sai kayi magrib a can" tace bayan ta sallami ma su mata hidima da su ke mata aiki a ɗakin.
"Kawai sai in zauna ina kallonta, mun gaisa na bata sakonki, don ki tabbatar da na je ɗin na ɗauki hoto da ita" ya ce yana mai mika mata wayar daidai inda hotonsu ke haskowa a fuskar wayar
"Kai! MaashaAllah! Kun yi kyau sosai, Allah ya sa rayuwar aurenku yayi kyau kamar yanda hoton nan yayi kyau" tace tana wangale baki, "kai ku ma se ka kai mata mene." tace tana kallonsa ganin ya kara ɗaure fuska bayan addu'ar da ta yi masu.
"Ban kai mata komai ba, kawai sai in kai mata wani abin bayan ga dukiya kin bayar a kai ma ta" yace yana zumburo baki.
A zuciyar sa kuwa bayan Aameen din da ya dinga ambata ma addu'ar da ta yi masa, takaicin rashin ba ta wani abin yayi, ko ba komai za ta ji daɗi kila hakan zai sa ta so shi.
"Kar ka damu, mutane kan ɗauka ana soyayya kafin aure a dena son juna bayan aure, wannan duk ba haka bane, mutane ma su hankali kan faɗa soyayya kafin aure sai aurensu ya tayar da son da suka faɗa ya ginu a jikin su, sai su zama masoya, aminai kuma jinin da ke gudana a jikin su.
Kar ka damu wai don ba ku yi soyayya ba za ku yi aure, ku natsu ku fahimci junanku sannan ku kyautata ma junanku hakan zai sa ku fara son juna cikin mutuntawa ba tare da kun sani ba" tace ganin ya yi nisa a tunani.
"Ko ba ta maka bane?" Ta qara jifansa da tambaya
"Wallahi ta yi, na gode ma Allah da ya bani ke a matsayin uwa, ina ganin ta fa na fara sonta, har kamanin Abbie yayi ina shauki ina kallon hoton nan" yace yana murmushi. Dariya tayi cikin jin daɗi da gode ma Allah.
****
Ana shiga sabuwar wata aka fara shirye-shiryen bikin Yarima AbdulHaleem da Fatima, sai Ramlat da Suraj wanda har yanzu Alhaji Yahuza bai gama tantance za'a yi ko ba za'a yi ba don babu Suraj ba danginsa.
"Ina ga za'a ɗaga auren Ramla har zuwa lokacin da da shi ma nemin nata zai turo mutanen ta, kuma kwatakwata guda nawa ta ke da za'a yi gaggawa akan zancen aurenta" Alhaji Yahuza ya faɗi suna zaune da iyalinsa
"Abbie ya ce ranar daurin auren za su zo ayi komai a ranar shi ya sa bai zo ba, amma ko ɗazu ya kira ni a waya" Ramlat ta katse shi don ba ta son ya samu goyon bayan kowa.
"Wai ni Alhaji mai na tsare maka ne, bakin cikin auren ya'ya na kawai ka keyi. Ita Fatima ba sai a filin bikin tambaya aka san da zancen bikin ta ba? Ka ce a'a ko kayi masa gurguwan tunani. Ga zubaida can hankali kwance a Masar duk da bakin fatan da kuka bi ta da shi, ni ko ba su zo ba a ɗaura kawai, Allah barshi na bada sadakin in ya zo ya biya ni" hajiya Amina tace hankalinta a tashe.
Add Vo
"Ba sai kin biya ba, ana bada aure a bashi duk ranar da ya samu sai ya biya, shike nan ko" Alhaji Yahuza ya ce yana karkada kai.
"Ban numbar sa in masa magana" ya ce yana kallon Ramla, ta karanto masa ya kira, bugu biyu ya ɗaga
"Yaa" ya ce daga ɗayan ɓarin wanda hakan saransa ne akan in an kira shi ya amsa da Yaa.
"Yahuza ne Mahaifin Ramla" Alhaji ya amsa kai tsaye
"Au toh ya aka yi? Ina Yini" Suraj ya amsa daga ɗaya gefen.
"Kana da ra'ayin auren ko yanzu ka fasa?" Ya sake tambaya duk da kokarin sa na son ya kwantar da kansa da fushin da ya ji yana taso masa.
"ina son baby amma gaskiya kuɗin sadaki na bai cika ba" ya amsa masa yana layi kamar wanda ya sha wani abin kawar da hankali.
"Ba matsala ka zo za'a baka bashi in ka samu ka biya, ranar Jumma'a fa biki don Allah kada ku saɓa alkawari" ya sake faɗi, ba tare da godiya ba kawai ya katse daga ɗayan gefe. Nan ya bar su duka da sakin baki don duk suna jin sa don a sifika Alhaji yasa.
"Alhaji ni kuwa sai in ga kamar kada ka biye ma su, Son zuciya kullum fa ga ɓacin zuciya ya ke kai mutum. Aure ba'a masa gaggawa in aka yi hakuri sai a kai ga auren mijin da zaa ce gara da aka jira" inji Hajiya Hafsa tace
"kwarai kuwa, za ki ce haka da yar ki ta kusa ga rashin iya haihuwa sannan aka iya kiranyo mata miji dole ki ce haka. Yanzu wannan tsohuwar wani soyayya za ta samu wajen miji duk lokacin da ya ci tayi shagwaba ta shanye shi a gidan uba. Ni dai yata za ta yi aure ba gudu ba ja da baya" tace tana karasawa da tsaki. Nan ta cigaba da jefa magana a cewarta na suna masu hassada.
Tun daga ranar aka cigaba da shirin bikin mutum biyu a gidan Alhaji Yahuza Bello da kuma fadar sarkin Qahɗaanie. Ana sauran kwana biyar daurin aure aka kawo lehe kamar yanda yan Hilaalu Sambo ke yi don ba su watsar Al'adun su na Yola ba.
Babu abin da ya dauki hankalin mutane kamar zinarin da aka zuba wanda musamman masarauta ta yi odar sa daga wajen ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺟﺐ Wato Abdullah M. R gold aka siya jaka guda aka sa mata, hakan ya sa mutane ba su maida hankali a sauran kayan ba sai a gwalagwalen.
STORY CONTINUES BELOW
"MaashaAllah! Fatima ta yi goshi, Allah ya sa a miki fiye da hakan bayan aure" kawai yan fatan alkhairi ke faɗi. Yayin da yan ciki baki ke faɗin
"BA GIRIN-GIRIN BA ta yi mai" a zukatan su kuma suna bi da mugun addu'a.
***
Faɗin yawan mutanen da su ka halarci ɗaurin auren ɓata lokaci ne ma. Sarakuna daga sassan duniya, yan siyasa da kuma manyan masu kuɗi duk sun halarta. Bayan an ɗaura ne aka shirya gagarimin Walima,
amarya tayi kyau sosai lallen ta kaɗai abin a kalla ne yayi jaa yayi kyau sosai.
STORY CONTINUES BE
Wasu na ganin ai ta fi kyau duk da ba wani kwaliya ta yi a bikin da aka yi jiya ba, nan ɗin ɗan karamin liyafa ne ango da amarya da abokan su su ka yi a filin gidan su Fatima.
Ramla ma ta yi kyau sosai, sai a wajen walima labari ke zuwa cewa ba'a ɗaura auren Ramla ba saboda angwayen ba su zo ba sannan babu wakilansa ko ɗaya. Nan Hajiya Amina ta rufe bakin mutane da faɗin in sun zo ba sai an yi wani biki ba, kawai a ɗaura aure ne a kaita ɗakinta.
Nan fa surutai su ka dinga tashi, mutanena ta kus kus wasu na faɗin ba'a daura ba wasu na faɗin an daura ba dangin ango ko ɗaya.
Sai cikin dare aka mika amarya fada, ɗakin ta kusa da na Ummu Maryam, kafin a yi budan kai a kaita gidanta da ke can gaba da fada.
***
Washegari wajen buden kai amarya da ango sun ci kaya kalar shuɗi,
musamman Alhaji Muhammadu ya je jihar Kaduna na Kasar Nijeriya ya ɗauko fitattun mawaka sha'irai masu daɗin murya wato Saadatu Isa vocal, Jamil Nafseen da MD Asnanic. Tun bayan da ya ci karo da wakar aure da su ka yi ya yaba da aikin su,lambarsu kawai ya kira. Nan su ka turo masa sakon tallansu kamar haka;
<<AREWA sound RECORD>>
Qungiya ce ta zaratan mawaqa
samari masu kaifin qwaqwalwa gami da jini a jika, a shirye suke don
sadaukar da lokutansu wajen yin
amfani da baiwar da Allah ya ba su
domin sanya ku nishad'i da
dad'ad'an waqoqinsu cikin dad'ad'an
muryoyinsu.
Add Vote
Wannan qungiya d'auke take da
qwararrun mawaqa a fanoni da ban da ban, kamar :-
Waqar Biki,
Waqar Suna,
Waqar Sarauta,
Wakar Siyasa,
Waqar Candy,
Waqar Taya Murna,
Waqar Passing Out,
Waqar Masoya Biyu
Waqar Film,
Kai, har ma kai da kanka za mu iya
waqewa idan kana buqata. Duk irin
waqar da kuke buqata daga cikin
wad'anda muka zayyano muna da
mawaqin da za mu had'a ku da shi
daga cikin 'ya'yan wannan qungiya ta
AREWA sound RECORD, sannan za
mu iya bin ku har gida mu gabatar da
wasanni bayan mun buga waqar (Life performance), duka wannan muna yi
ne Cikin RAHUSA matuqa.
Don yin Booking za a iya tuntu6ar
mu a lambobin waya kamar haka :-
08037191788
08032125326
Email:-arewasound@gmail.com
WhatsApp :-07063828558
Facebook :- Arewa Sound Record
Instagram:-md_asnanic
Tsara talla : MD Asnanic .
Saboda ya tura ma wa'inda su ka ji daɗin aikin su kuma su ka yi sha'awar gayyatar su.
Bayan an zauna an gabatar da abubuwa da yake al'adan gidan sarautan Qahɗaanie aka ba sha'irai Daman baje basirarsu don gabatar da basiransu. Nan su ka fara
Amshi:- Auren soyayya dadi ne da shi, Yarima Abdulhaleem ka kula da Fatima
Zama mai daďi zama na aure,
Aljannar masoya a gansu a tare,
Ďadi ko wuya kam dukansu su jure,
Suna a tare masoyan juna babu faďa
balle ka ji kokawa.
Fati mai karamci, mai babban suna,
Inai miki nuni ki zam mai amana,
Gwanar iya girki na saki da kaina,
Kalamai na soyayya ki yi mai, hakan
yana qara danqo na qauna.
Abdulhaleem kaima, ba zan barka ba.
Fatima yau taka ce, haqqinta ka
duba,
Tabar danginta duk, uwa har da uba,
Ta yarda da kai za tai rayuwa, ka riqe
amana banda kyara.
Iyaye na ango ina gaishe ku,
Iyayen amarya kuma na sa ku,
Anties sai ku jiya ku yo rawa da
taku,
Qannai da yayye suna cikin tsare dole ne na sa ku cikin waqata.
Kiɗan kaɗai ya ɗauki hankalin mai saurare, yan uwa sunyi rawa sun yi ɓarna kuɗi kamar ba gobe. Anan wajen budan kai ne Khuder da matarsa su ka san wa AbdulHaleem ya aura don tun da sarki ya ba da umurni a sallame ta daga tsare ta da aka yi suka je Dubai ita da Khuder bikin ya dawo da su. Nan duk su ka cika da bakin ciki don kuwa sun san ta zarce ma tunanin su.
Sarki ya mata marhabin da mata kyautan sarka mai kyau da tsada.
Nan aka ci aka sha, yan uwa su ka yi hotuna, kannenta da kawayen ta ma duk aka kyalla su.
Kanen amarya Surayya da Najaatu
Assalamu Alaikum warahmatullah
Da fatan kuna lafiya, ya kuka ji da
hakuri da Safiyyah, ku dai cigaba da
hakuri har zuwa lokacin da uzurorin
zasu daidaita, ku sa ka ni a addu'a
kuma don shine kawai kaunarku gare
ni bayan kun gama voting da commenting su kuma ghosties 👊👊👊 a
idanun kanne daga cikin su 😢😢😢 yayyi da iyaye a tausaya kafin hawaye na ya shanye garin Kano.
Yan uwa kun kula da yanda mutuwa
ke ɗaukan mutane ba notice, mu
gyara halayenmu musamman ga yan
uwa musulmi har ga wanda ba
musulmi ba, Ahlaq zai kai mutum
wuta/Aljanna depending on yanda
mu ka yi amfani da shi duk kuwa da
yawan ibadanka.. Mu kiyaye kalaman
ɓatanci ga duk wane kunne mai
saurare ko idanu mai karantawa. Mu
kyautata kalamanmu akan mutane
sannan mu kiyaye zaqulo aibunsu.
Khalifa Aliyu bn Abie ɗalib ya ce duk
wanda ya fara tunanin ya fi wani mai
ɓarna (alfasha) a wajen Allah toh
tabbas ya ɗauko hanyar ɓata.
Matukar mutum musulmi ne, ba
mushriki ba ina ruwanka da zunubin
sa da ke tsakanin sa da Allah, in dai
ba tunkarar sa za kayi ka gyara
ɓarnar da hannayenka ko bakinka ba, in kuwa yaɗa shi ne hanyar gyara to ka sani shi Allah mai yalwan Gafara
ne kuma mai jin kai ne.
Yan uwa muna da sauran lokacin tuba kafin kofofin tuban mu su kulle,
mu gyara tsakanin mu da mutane,
mu mu'amalance mutane ba tare da
cutar da su da halshen mu ba ko
idanunmu. Sannan mu yawaita
istigfari, ibada kaɗai ba zai tsiratar da
mu gobe qiyama ba.
Safiyyah Ummu-Abdoul
16/01/2018
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Ummie da kannen Fatima
Sai da aka kwashi sati ana bukukuwa da shagali har abin ya gunduri Fatima, Sam ba ta taɓa son budaddan biki ba don yawan shagali a biki in shagali ya haɗa da saɓon Allah ya kan kai ga raguwa a albarkan da ke cikin aure. Amma ya ta iya, sai hakuri. Duk da shagulgula aka yi mai tsafta, talakawa sun ci sun sha, don duk wani mabukaci ya samu wadata a wannan kwanakin.
Bayan kwana bakwai ɗin ne aka sada ta da gidan ta da aka keɓe ma su. Ta yaba kwarai da zubin gidan. An zuba kaya ta alfarma sannan ga kuyangi da ma'aikata da aka zuba mata bayan na'urori na zamani da ke saukaka aiki. Ta bayan gidansu kuma dawakai ne guda biyar da suka samu kyauta daga fada. An sakaye gidan da furanni don samun ingantacciyar rayuwar aure.
***
A kwana a tashi satin su biyu ba tare da sun fito ko kofar gida ba. Rayuwa su ke gudanarwa cikin kauna da girmama juna, in sun zauna baya gajiya da bata labarin Kasar Amerika inda ya yi rayuwar kuruciyarsa a can, yakan nuna mata hotuna ya mata bayani. Anan ta fahimci shi mutum ne mai saukin hali amma mai wuyan gane hali.
"Rayuwa babu abin darajawa kamar mace don uwata macece kuma ita ce gatana. Amma kuma babu abin da nake kyama kamar mace duk da ina son su. Ni ba wani kyau ba amma mata sun zubar da kimar su a gare ni har ya sa na dauke su kawai abin da su ka bayyana min su ɗin ne" ya ce da ita suna zaune a wajen dawakai. Kallon shi take zuciya na ayyana mata abubuwa marasa daɗi, nan ta hango darussan da ya koyar da ita a Yan zaman su ya riga ya koyar da wasunta, wasunma kazamai tambadaddu. Take zuciyar ta tayi kunci murmushin fuskar ta ya ɓace. Shi kuwa ido ya sa mata yana ganin yanda Yanayin ta ya canza kamar a shirin fim. Daga ta yayi ya ɗaura Saman doki sanin da yayi tsoron su ta ke, aiko take ta kamkame shi tana ihu, shi kuma ya sauko da ita. Rungume ta yayi su na jin saukar numfashin junansu, sai da ta samu daidaito sannan ya riko hannunta yana kallon ta cikin ido ya ce.
"matsoraciya! Kin san kuwa kin fi kyau in kaka firgita" ya ce yana kyafta mata idanu. Duka ta kai masa duka a qirji nan take ya gauce yana dariya yace
"Ke! Sarkin gobe za ki duka. Hmmmn ba ruwa na in hannunki ya kumbura" nan duk su ka sa dariya. Kamo ta yayi bai sauke ba sai gefen da korama ke gudana, an samar da matakala da mutum zai bi ya kai ga koraman, a nan su ka zauna, ya kunna wayarsa su na kallon video da aka turo masa ta hanyar WhatsApp.
"Wow Sauti safiril bulbuli kenan, wani soja ɗan asalin Nijeriya da ya zo jami'ar mu ɗaukan kwas ne ya turo min, kuma ina son wakar" yace mata bayan ta buɗe wani video ta na kallon sa alamun neman karin bayani.
"Ina son yan Nijeriya ance mutane ne masu son addini, Kaga duk kusan hijabai na a zaria Abbie ke siyo min su" tace tana murmushi
"Major Abubakar Abdullahi kenan, bawan Allah mai kiyaye dokokin sa, in faɗa miki shima dai haka, in na faɗa miki tarihin wakar sai kin ci dariya" yace yana kara jinjina maganar ta na son addinin yan Nijeriya
"Haba Azeezie sai na ce ka bani yanzu" Ta ce tana kashe shi da ido.
" A kasar larabawa ne aka yi wani
sarki lokacin jahiliyya, sannan suke ji da maaurar fasaha.
To shi wannan Sarkin marowaci ne
na gaske. Idan ya ji abu sau d'aya
duk yawansa zai haddace, shi kuma
wazirinsa idan Ya ji abu sau biyu duk
yawansa zai haddace, yana da wata
kuyanga a bayan lalube ita kuma duk
abinda ta j i sau uku duk yawansa za ta haddace.Hakan ya ba shi dama
duk mawaqin da yazo Ya biya masa
waqa da sunan shi ya rera wa, sai Ya
ce ai wannan waqar na santa tun
tuni, bari ma ka ji in rera maka. Sai ya
rera waqar, saboda dama yana da
baiwar hadda in ya ji abu sau d'aya, in ya gama sai ya ce, in ma baka
yarda ba ga wazirinsa nan ya san
wakar, bari ka ji ya rera maka, shi
kuma waziri dama ya ji sau biyu
kenan sai ya rera.
Sai sarkin Ya kara cewa, ai hatta
kuyangina ma a cikin gida sun iya, bari in kira kuyanga ďaya ta yi maka ka ji, sai Ya kira wannan kuyangar
tashi ta bayan lalube, ita ta ji sau uku
Kenan, sai ta rera.
STORY CONTINUES BELOW
Sai kiga mawaqi yana dabur-dabur, yana tunanin anya kuwa aljanu ba su
shafe shi ba, Ya akai haka.
Daga nan sai sarkin Ya ce "ku amshi
takardar ku auna ta a sikeli, ku ba shi
zinari iya nauyin awon Takardar.
Wata rana da mai Safirul Bulbuli ya ji
labari, sai ya je wa da wannan Sarkin da wakar Safirul bulbuli, ai kuwa sarki Ya rasa ta ina aka fara balle Ya
maimaita, shi kuma waziri dama sai ya ji sau biyu ne zai iya, ballantana
kuyanga dai sai ta ji sau uku.
A ranar dai aka qure Sarki, sai Ya ce to kawo takardar da ka rubuta wakar a ba ka kyauta iya nauyinta, sai mai
Safirul bulbuli ya ce "ranka Ya dade
sanda na rubuta ta ina daji ne ba
takarda kusa da ni"
Sai Ya ce "to kawo ganyen da ka yi
rubutu a kai"
Sai Ya ce "ranka Ya dade ba ganye
ba ne"
Sai Sarki ya ce kawo ko ma meye za a auna maka da shi.
Ashe ďan malaminka a jikin 6angori Ya rubuta. Yana sauke mangalar
jakinsa sai aka ga manyanyan 6angorai na tukunyar qasa a jiki ya
yi, a ranar dai sarki sai da ya yi
kyautar zinari mai nauyin gaske.
Ai yana karewa ta sa dariya har da kwanto masa, rabon da ita kanta tayi dariya irin haka har ta manta.
'ashe dai yana magana sosai, amma duk haɗuwar mu kafin aure ba ya ko yarda mu yi hira balle ta ga fara'arsa' ta ce a zuciyar ta, ganin ta yi nisa a duniyar tunani ne ya ce da ita
"Ba ki ji ba" Sai ta ɗaga kai tana kallon sa hi kuma ya yi amfani da wannan damar ya aika mata da sakonni da ta gagara ɗauka. Ganin ta na neman yin yaushi sai kawai ya sa mata dariya.
A nan su ka yini, sai yamma su ka koma gida shi kuma ya shirya ya je Fada don ganawa da sarki. Ta raka shi har inda zai shiga motarsa, bakinta na masa addu'ar dawowa lafiya da samun nasara duk kuwa da ba ya faɗa mata abin da zai je yi fada bane.
Yana tafiya ta dauki waya ta kira Abbie wanda kullum sai ta kira shi don su gaisa amma yau so take su yi hira.
"Abbie, am in love" tace masa bayan sun gaisa
Add Vote
"Ahhhh lallai Er Abbie aure daɗi ko" yace yana dariya, ya san halin da take ciki neman wanda za ta faɗa mawa take kuma kasancewar sa amininta ya sa ta tunkare shi da zancen.
"Abbie zamu ɗaure a haka ko, kar ya yi disappointing ɗina, ya zanyi? Yana da kirki kuma ga sanyin hali a ɗan iya fahimtar da na masa" Ta ce kai tsaye.
"Amarsu har yanzu ba ki san mijinki ba, addu'a ce kawai babban ingredient ɗin da kike bukata, daga nan se ki rike biyayya. Banda gardama kin san maza ba sa son gardama ballantana jinin sarauta, jinin sarautar ma sarki mai jiran gado. Ki rike Allah fiye da yanda kike yi a gida, sannan kada ki dinga kallon laifi ki kalli alkhairi, hakan zai kara muku zaman lafiya."
" Insha'Allah Abbie zan kiyaye, ina Ramla ne ni kuwa, na ga da ita aka yi dukkan bukukuwan da aka yi mana na fada, an kai ta kuwa "
" Hmmmn! Mijin bai zo ba kuma bai turo ba, ni dai ban ɗaura mata aure ba, gata nan daga ita har uwarta fita na gagarar su" yace yana mai jin daci a ransa, don duk ya tuna sai ya ji haushi.
"Amma abu bai yi daɗi ba, sai ta koma makaranta kawai don zamanta haka ba zai yiwu ba Abbie" tace tana tausayin mahaifinta.
"Fatima ta ki zuwa tace za'a mata dariya don duk ta ce musu aure za ta yi" ya ce yana tsaki
"Abbie ka sa mata ido, ai gara ta koma, darasi ne gareta da mu kanmu, wanda yacce ruwan wani ba zai tafasa ba Abbie na shi ko zafi ba zai yi ba, ban ga abin gaggawa a aure ba kwata kwata shekarunta nawa ne, bana take sha biyar fa, Abbie ka yi hakuri amma in har ɗaukan mataki zai sanyaya maka rai Abbie ka ɗauka kawai, na san kana cikin damuwa" Ta faɗi cikin shagwaba.
"Mataki kuwa ai za ɗauka, lokacin zartarwa kawai na ke jira, kar ki damu ki kula da kanki ga Mamie ta zo ta tsare ni da ido ta ji me muke faɗi" ya ce yana dariya, mikawa Mamie wayar yayi su ka gaisa da fatima sannan su ka yi sallama.
***
AbdulHaleem yana isa Fada AbdulHaseeb ya fara nema don yana cikin kewar ɗan uwansa. Tare da AbdulBaar ya gansu duk da yayi mamakin ganin su tare bai nuna ba
" Haba yan uwa, kun barni cikin kewa, don Allah inji duminku" yace yana buɗe musu hannu. Ba musu su ka rungume shi zukatan su na quna.
"Haseeb ka dawo sashi na don Allah, rashin ka na taɓa ni" ya sake faɗi yana rungume ɗan uwansa. Ganin hawaye idanun AbdulHaseeb ya tayar masa hankali.
"Na sani, ba sai ka faɗi ba. Ka dawo mu cigaba da zaman mu tare, kai ma in ka yi aure mu zauna dukkanmu kamar yanda Ummu ta tarbiyyantar da mu" AbdulHaleem ya faɗi yana share kwalla. Zuciyar sa cike da kewan ɗan uwansa, yana tunano rayuwar da su ka yi tare.
"AbdulBaar bamu waje don Allah" AbdulHaleem ya faɗi ganin ɗan uwansa ya gagara magana yana share hawaye. Bayan ya fita ne ya ja AbdulHaseeb quryar ðaki ya ce
"Son mulki wai hauka ne? Na san duk abin da ke faruwa, da kuma shirin da kuke yi akan kujerar nan. Ka sani duk wani tarbiyya da zaka samo bayan na Ummu Maryam to ba zai ɓulla ba, ka tattaro ka dawo gida na mu cigaba da rayuwar mu hankali kwance, but in ka ce za ka zama matsala ba zan duba alakarta jini da ke tsakanin mu zan hukunta ka. Babu wanda zai so ka sama da AbdulHaleem Abdul-Jabbar" yana cewa ya fice ta kofar da ya shigar da su cikin gida ya je dakunan iyayensu.
Dakin ummansa ya shiga karshe, kamar yanda Ummu hafsa tayi bakin cikin kiban da yayi haka Ummu Maryam ta yi farin ciki sosai, har ta kasa ɓoyewa, sun yi hira sosai su ka yi anan ya ke faɗa mata abubuwan da ya lura dangane da AbdulHaseeb da Ummu Hafsa
"A'a tilona bana son ka sa zargi a zuciyar ka, don bai zo gidan ka ba shi ne wani abu ko don ya ganka yana hawaye shine na bakin ciki, kai ɗin ba hawayen ka ce kayi ba" Ta faɗi tana shashantar da sauran abubuwa da ya faɗi wanda ya ke daga bincikensa ya samo.
STORY CONTINUES BELOW
"shike nan nayi shiru, bari in je wajen mai Qahɗaanie" yace yana mai Mike wa don babu abin da zai faɗi ta yarda da shi sai m in ya nace ta ce shi ke son su da rigima.
***
Bayan ya isa Fada, nan ya nemi izini sarki da yan majalisa su ka masa iso, fadawa su ka mika gaisuwa shi kuma ya gaida manyansa. Bayan gaisuwa ya nemi a bashi izini zai yi magana babu gardama aka bashi ya mike yana godiya.
"A wannan qarni da muke ciki qarni ta ashirin da ɗaya, an samu cigaba da dama a duniya musamman duniyar kimiyya. Ina bakin ciki idan na kalli daular mu na ga muna can baya ta wannan fannin duk samun matasa masu jini jiki da ke da ilimin fasaha da kere-kere
Ina so a bani dama, mu maida komai ta masarautar mu da yanar gizo, a sanya kyamarori a ko ina a cikin masarauta wacce za'a alakanta shi da rundunar sojin Qahɗaanie, a tura sojojin da su ke ɓangaren yanar gizo da satellite wato (signals) su ko you kwas da dabarun amfani da wannan na'ura. Sannan a sauya kofofin da su ke sadar da mutane ga maɓuyar bango na cikin masarauta a saka mai lambobin sirri wanda ahlin masarauta kaɗai zai mallaka." Ya ce yana mai dukar da kansa alamun godiya tare da zama. Gaba ɗaya majalisa ta yi na'am da tunaninsa, har su ka kai ga jinjina masa tare da yaba ma sarki na zaɓansa a matsayin mai jiran gado.
" ka faɗa mana abin da kake so a yi ba ka faɗi tanadin da ka ma shirin" sarki ya faɗi yana gyara zama. Take ya sa aka haɗa kwamfutar majalisa ya haɗa da wayar sa nan komai ya bayyana (projector)
"Nan za'a sa na'ura, kun ga ai a ɗan ɓoye ta ke, nan ma za'a saka kyamara wacce za ta dinga ɗauko abin da aka yi a nan da chan, ba za'a sa a dakunan barci da bandaki ba saboda sirri ne amma ko wace taga da kofa za ta ɗauko mai shiga da fita dakunan.
Nan zai dinga ɗaukan na fada, tun daga wanda ya shigo kofar har zuwa nan, daga nan wannan zai ɗauko na daga wannan kusurwa zuwa nan" haka ya dinga nuna musu tsarin ɗin da ya zauna ya haɗa akan wannan shiri.
"Muna bukatar kuɗi, don kamfanin da za su yi aikin a cikin kwanaki biyu za'a yi gudun samun matsala, ni zan ɗauko su toh in aka ji matsala ni za'a tunkara" Nan ya kammala ya rufe kwamfutar ya koma ya zauna. Daɗi ya ma sarki yawa yana qara jinjina ma AbdulHaleem don bai taba tunanin zai kawo wannan tunanin ba.
"Akwai mai qalubalantar wannan shiri da hujja" sarki ya tambaya don ya ba kowa hakkinsa, ganin sun yi na'am da shirin ya ce a fara aikin a lokacin da AbdulHaleem ya shirya.
Tun daga majalisa babu inda maganar ta fita har se bayan sati da ma'aikata su ka zo su ka yi duk wani haɗe-haɗe na kayan mafi yawa a bango su ke birnewa sai su saka kofa da ta haɗe da sauran fentin, sai kuma wasu a kasa aka yi, daga gefe kuma ginin fada na karkashin kasa aka sanya abubuwan tsaro da ya yi daidai da zamani.
***
"Wai baffa haka za ka sa mu ido? Ka ga yanzu duk wani shiri na mu an tarwatsa shi, ni dai bana son yaron nan ya sha balle har sarautar ta zo kan shi" Ummu Hafsa ce ta faɗi gaban Alhamzie bayan ta faɗa masa matakan tsaron da aka sa fada.
"Ki barni da su, fadan zan zo da kaina in masa tijara cikin mabiyansa, in shi bai da kunya toh zan nuna masa shi qaramin mara kunya ne" yace yana mai sallamanta don kuwa ranshi ya riga ya ɓaci. Ashe tun bai shekara da zama yarima mai jiran gado ba yana neman ya zama masu matsala.
"Baffa kuma an ce matarsa ciki ne da ita, satin da ya wuce ta zo inaga zai kai wata huɗu kenan. Ka san wata su takwas da aure kenan" Ta faɗi cikin ɓacin rai tana mai mikewa don ta san ba zai saurare ta ba kenan.
Tun bayan da aka kafa matakan tsaro a fada Ummu Hafsa ba ta samu fita ba saboda ciwon hawan jini da ya kwantar da ita, AbdulHaseeb kuma da gangan AbdulHaleem ya sanya sunansa a cikin sunayen ma su zuwa kwas don ya tsiratar da shi daga sharrin da ya ke shirin jefa kansa. Hakan ya qara dafa Ummu Hafsa don Sam an rusa mata duk wani shirin ta.
A ɓangaren sa da Fatima kuwa zama lafiya sai san barka, mafi yawan lokutta shi ya ke kaita makaranta wajen aiki kuma ya je ya ɗauke ta, don ba ya son a tura da masu gadin masarauta wa'inda sojoji ne maza da mata.
Sanda su ka gane ciki ne da ita kuwa shi da kansa ya rubuta mata ɗaukan hutu na shekara ba tare da a biyan albashi ba (leave without pay) ya kai tun daga nan ya ke kara shagwaba shi don burinsa ta hayayyafa da yawa zuri'ar Ummu Maryam su yi yawa su ma.
***
Tun bayan da Ummu Hafsa ta bar zango, Alhamzie ya rasa in da zai sa kansa, bakin ciki ya masa yawa, can dai ya figi mota bai tsaya ko ina ba sai majalisar sarki inda su ke ganawa da yan majalisa.
"Kai Abdul-Jabbar! Tsohon banza wanda bai cika ɗa ba. Wai me kake nufi da mutane ne" ya faɗi ya na nuna sarki da ɗan yatsa, nan yan sanda da sojojin da ke wajen su ka tashi ɗauke shi, amma sarki ya dakatar da su. AbdulHaleem ne ya Mike ba tare da ya ji umurnin sarki ba ya same shi gaba da gaba. Kallon sa Yayi tun daga kasa har sama sannan ya ce
"Duk cikin dangin ubanka babu wani tsohon da zai tunkare ni ne sai kai karamin Alhaki?" Ya ce yana harararsa bai ankare ba ya ji an kwashe shi da mari, wanda ya gigita shi har ya tsuguna. Yana tasowa ya sake dauke shi da mari anan ne sarki ya daka ma AbdulHaleem tsawa. Hakan ya sa ya ɗauke rawanin Alhamzie ya fita da shi.
Bai zame ko ina ba sai madafa nan ya nemi a bashi bussashen kifi ya nade ya ce a kai ma Alhamzie gidansa kafin ya isa.
"Ina umurtan AbdulHaleem da ya sauke rawaninsa, sannan na bashi kwana uku ya fita daga daular Qahɗaanie, wannan hukunci ne akan duk wani wanda aka kama da laifin ɗaga mukami sama da na sarki, wanda hakan ne abin da AbdulHaleem yayi yanzu" ya faɗi bayan yan sanda sun janye Alhamzie zuwa wajen fada kamar yanda nai martaba ya ba da umurni.
Daga kitchen ɗakin da shi kaɗai ke da hurumin shiga ya isa cikin sauri, na'urar kwamfutar da ke maqale jikin bango ya kunna nan take fuskar kwamfutar ta hasko masa kofar fadan Qahɗaanie, yana kallon yanda komai ya ke tafiya har fito da Alhamzie da yan sanda su ka yi har ya shiga motarsa, sannan ya kashe ya fice daga gidan. Motarsa ya shiga ya fige ta kamar zai tashi sama, hanyar gidan sa yayi don ya san lallai da akwai yan gulma, sai da ya fice ma idon mutan fada sannan ya juya kan motar ya nufi hanyar Zangon Qahɗaanie. Yana cikin tafiyar Fatima ta faɗo masa a rai, kamar zai juya amma dai yana so ya ida nufin sa. Ya kai inda ba zai kai mile goma zuwa ga zango ya hango motar Alhamzie tafe, take ya ja burki ya tsaya a tsakiyar titin yanda babu yanda za'a yi Alhamzie ya iya wucewa. Shima ɗin tsayawa yayi ya na kallon sa rai a ɓace
"Kaga karamin kwaro, bani waje in wuce tun kafin Yar bayin nan ta sake naquda" ya faɗi yana hura hanci
Bai yi aune ba ya ji saukan harsashi a jikin sa, bai yi tsammanin haka ba, take ya zube a wajen yana zubar jini. AbdulHaleem na gama sakin harsashin ya ɓalla bindigar ya aje kusa da Alhamzie sannan ya juya. Tashin motarsa yayi daidai da isowar mutane zuwa wajen don sun ji karar saukar bindiga wanda abu ne da aka daɗe ba'a ji shi ba.
***
Wasikar kora daga Fada ya iske a gidan, bai yi mamaki ba amma kuma abin ya taɓa shi. Wanka yayi ya wanke kayan jikin sa son ya ga alamun jini a hannun rigar sa, sannan ya fito ya sami Fatimah da ta shiga damuwa saboda Yanayin da ya zo mata da shi.
"Azeezatie ki yi hakuri, muna cikin wani jarabawa wanda sai da taimakon ki kawai za mu iya ci. Mai martaba ya kore ni daga daular qahdaanie saboda laifin yin hukunci sama da nashi a fada, haka dokar take, za ki bini ko kuma za ki zauna ki haifi ya'yanki a cikin dangin su. Ban san in da zamu nufa ba, saboda haka na bar ki zuwa gobe ki yi shawara da zuciyar ki" ya faɗi kai tsaye yana mai mikewa.
Sai a lokacin ta fara tsanar kasancewar sa mai abu kai tsaye ba tare da ɓoye-ɓoye ba ko lallashi ba, takaicin ta ya karu duk ta tuna da faɗin sa na wai zata bi shi ne? Tunanin sa za ta bar shi ya tafi ba tare da ta kasance makale da shi ba.
"toh aikin ki fa" wata sashi ta zuciyar ta ta tuna mata da kasancewar ta mai aiki. Nan ta kara shiga ruɗu don har ga Allah tana son aikinta burinta da mahaifinta shine ta taka matakin farfesa. Kuma bata ga dalilin da zai sa ta rusa musu wannan buri na su ba. Haka zuciyar ta taci gaba da raya mata abubuwa, nan ta gama rudewa kawai sai ta ja jiki zuwa ɗaki.
***
Tun da AbdulHaleem ya shiga ɗki ya ke tunanin ina zai nufa, ga matarsa ga ciki ga kuma kewan gida, ya san barin sa Qahɗaanie kamar bayyana mahaifinsa ga abin da zai cutar da shi ne. Yana cikin wannan tunanin ya tuna da abokin sa da su ka yi karatu tare mai suna Stefano Angelo wanda yake ɗan yankin romaniyawa ne wato Kasar Italiya. Stefano abokin AbdulHaleem ne kuma ya sha faɗa masa irin dabarun mulki da su ke da shi a yankin su da kuma yanda Kasar Italiya ta zama cikin kasashe da su ka samu nasara lokacin yaqin duniya na ɗaya.
Hakan ya sa ya tura masa sako ta akwatin email akan ya na so ya zo Kasar su ya yi shekara saboda koyon dabarun mulki da yaki, yana so ya sama masa gida a kusa da yan tawaye matukar hakan ba zai cutar da shi ba. Daga nan ya masa godiya bayan Stefano ya tabbatar masa da samun duk wani abin da ya bukata, daga nan ya fara neman hanyar fita saboda fasfo da bisa ɗinsa na masarauta ce ta bashi damar shiga dukkan Kasar da ta ke da jakadanci da a Qahɗaanie ciki kuwa har da Italiya.
***
Mutanen wajen na qarasowa su ka tsinci Alhamzie kwance cikin jini. Ganin ya ɗaga hannunsa ya sa ya tabbatar masu cewa yana da sauran rai a jikinsa. Cikin azama wani ya ɗaga shi sai a lokacin su ka kula da Aamir Al Ansari ne. Ba su ɓata lokaci ba su ka ɗauke shi sai babban asibitin Zangon Qahɗaanie inda likitocin su ka tare shi cikin gaggawa.
"Aamir Al Ansari ya rasu a sanadiyar harbin bindiga" ya kasance taken Labaran gidajen radiyon Qahɗaanie, haka gidajen talabijin ga hotonsa da kuma hotunan da aka ɗauka bayan fitowarsa daga fadan mai martaba.
Nan mutane su ka fara samun bambancin ra'ayi, wasu gani su ke hukumomin tsaro ke da alhakin kisan yayin da wasu ke ganin cikin yan tawayen da ya hana musu wajen zama ne a zango aka samu wanda ya masa wannan kisan gillar.
"Majiya ta musamman ta sanar mana da yan tawaye yan aqidar ISMAAALIE ke da alhakin mutuwar Alhamzie, su dai Wa'innan sun zo ne daga yankin gabas in da su ka nemi da ya basu matsuguni don yaɗa aqidar su tare da yaqar duk wata aqida da ba tasu ba, amma Alhamzie ya kasa ya tsare ya hana, kakakin wannan akidar ya sanar a wani faifai na bidiyo da su ka saki akan sun kashe shi ne saboda ganin sa ya fito daga fadar daular Qahɗaanie, sun yi amanna akan yana so ya haɗa kai da sarki ne don yakar su" kashe talabijin ɗin AbdulHaleem yayi don ya san karya ce kawai, duk da yana sane da ISMAALIE ya san ba su da makamai a hannun shi kuma ya sani sarai Alhamzie na da hannu a cikin kafuwar qungiyar.
Tashi yayi ya shirya kayansu don ba zai kara awa 24 a cikin Qahɗaanie ba, in Fatima za ta bi shi toh in kuma ta fi son zaman Qahɗaanie toh ruwan ta don shi a shirye yake da ya ya qi Alhamzie don yana da yaqini bai mutu ba yana nan da rana.
Manage this
Love u all
A Zangon Qahɗaanie kuwa tun da aka kai Alhamzie asibiti labari ya iske iyalinsa akan ya rasu. Nan yan uwansa da yake zumunci da suna kusa suka hallara a gidansa don tarbon gawar sa yayin da yan maza su ka isa asibiti don tahowa da shi.
Da isar su ne suka iske labarin yana Raye sai dai ya jikkata sosai saboda asarar jini da yayi.
"A cinya aka harbe shi" faɗin mijin er sa ta fari. Don ya riga isa wajen kasancewar yana cikin wa'inda su ka fara isa inda abin ya faru.
"Wai waye wannan ya aikata wannan aika-aika" wani matashi ya tambaya, kallo ɗaya zaka masa ka san malami ne zaahidi. Don kuwa yakan jikin sa kaɗai ya isa ya nuna tsantsan talaucin da yake fama dashi.
"ga dai abin da aka kawo ma matansa cikin rawani sa, ganin kifin a bushe yana nufin Aamir na cikin hatsari, in bai niyyar kashe shi ba yanzu toh ana rantsar da shi sarki zai gama da Aamir" Yusuf kanen Aamir ya faɗi wanda shi matan su ka mika ma sakon ganin ai rawanin da yayi amfani da shi a ranar kenan.
"Ai yanzu lokacin bayyana kanmu ne yayi, zamu ce mu muka harbi Alhamzie don mushen can da ke mulkin zalunci ya saki jiki da shi, daga haka sai mu ba ɗaukacin al'umman qahɗaanie shiriya su tuba su bi hanyar gaskiya" wannan zaahidin ya faɗi yana zazzare idanu.
"Amma kuma ai bamu san shirin da ya ke ba, kada mu yi sauri mu ga abin da ba hakan ba" Yusuf ya faɗi yana mai jin tsoro. Amma shi zaahidin nan ya tsaya kai da fata akan gara a nuna musu akwai shiri na musamman, sannan a yi ma fada shigo shigo ba zurfi. Hakan ya sa su bada sanarwan su suka harbi Amir al Ansari.
***
Tun da Zubaida ta isa Kasar Masar ta haɗu da wanda ya kira kansa Abdullah ta mace masa, baki ne mai tsawo da kyan sura, sannan yana da wani irin zaiba a idanunsa da ke tafiya da zukatan yan mata. Ta iske shi a namiji da ya iya sarrafa mace, ita kuma karatun da ta taso da shi kenan a aure, hakan ya sa gaba ɗaya ta ke ganin ta a Aljanna.
Tun da ta isa bata taba jin haushi ba sai da mahaifiyarsu take faɗa mata wa Fatima ta aura sannan auren ramla bai yiwu ba nan ta zauna da mahaifiyar nata su na tsine ma Fatima da mahaifinsu don Zubaida faɗi tayi
"Ammie kin tabbata da ba so yake ya dinga haura mata ba kamar fatima shi ya sa yake cewa shi ba zai ɗaura mata aure ba" tace kanta tsaye ba tare da da la'akari da girman ɓatancin da take faɗi akan mahaifinta ba. Nan uwar ta shiga waswasi don sheɗan ya sha raya mata wannan shakuwa da ke tsakanin Fatima da Alhaji yahuza babu Allah a ciki.
"ke dai ki iya bakinki, ita Ramla yanzu zan san yanda za'a yi na turo miki ita ko kuma in shi Abdullah na da wani a kasa da zai aureta ya taimaka ya zo a ɗaura" haka su ka tsaida magana akan haka su ka yi sallama suna cike da begen juna.
Abdullah na dawowa kuwa ta zauna ta feshe masa komi tana karfafa mahaifinta ba ya so Ramla ta yi aure ne don ya samu ya dinga haure mata kamar yanda yake yi da Fatima. Nan su ka haɗu suna tsine ma Fatima da fatan dukkan wani bala'i ya sauka a gareta da mijinta, shi yana yi ne saboda ubangidan sa mafi ma uba a wajen sa Aamir Al Ansari, sannan yana yi don ya kara samun yardanta yayin da su ka tashi shuka ma su Fatima wani bala'in.
"Yauwa akwai ɗan uwa na, yaron kawu na ne, kin san na ce miki mahaifiyata er Ghana ce toh shi yana chan amma mutumin Allah ne, don kuwa zan iya rantsuwa akan shi waliyyi ne, zan masa magana sai ya je su daidaita da Ramla ayi auren a wuce wajen" yace bayan ya lissafa ya ga hakan ne zai kara ba su damar mallakar fada in su biyu suna auren mafi soyuwa a wajen sarki. Ba su tashi a wajen ba sai da suka kira Hajiya Amina a daular Qahɗaanie suka mata albishir sannan ya kira wanda ya laqa ma Nasiruddeen ya faɗa masa ya masa mata yana so ya shirya ya je Qahɗaanie ayi komai cikin wata biyu zuwa uku. A bangaren Nasiruddeen bai ko Musa ba don Abdullah ya bashi labarin dace da yayi da mata ruwan Fulani da Larabawa.
Add
Nkrumah Kojo ɗan asalin qasar Ghana ne gaba da baya, shine yaro na ta a wajen malam Kojo malike da ya ke zaune a Zango ghana, hakan ya sa aka faɗa masa Nkrumah. Ya taso a sake babu kwabo babu tarbiyya har Allah ya sa ya girma Hak ya taso sagagaga. Bayan kammala karatun sa na sakandire ne jinin su ya haɗu da Adjetey har su ka zama aminai kum shugabanni ga kungiyoyin yan fashi guda biyu da su ke gagarumin ɓarna a qasar Ghana baki ɗaya.
Bayan tarwatsewar kungiyar adjetey da tafiyarsa Kasar Masar ne Nkrumah ya ɗan ja baya da fashi don shi burin sa ya samfe daga Kasar kafin ya haɗu da bakar rana, shi dai bai da ubangida mai harkoki kamar adjetey saboda haka kawai ya dira ta kai ya shiga wata kungiyar asiri wanda ta kunshi manya daga cikin kusoshi a kasashen da ke kewaye da Ghana da ita kanta Ghana ɗin.
***
Cikin wata biyu Nkrumah ya shirya kamar yanda su ka tsara da amininsa Adjetey ya je a matsayin Nasiruddeen tubashin Abdullah ya amso matarsa wacce ba musu aka bashi. Bayan ya kira adjetey ya faɗa masa abin ya tabbata ne su ka kira ammie
"Maman Amarya" Zubaida ta faɗi bayan ammie ta ɗaga ita kuma ta bayyana sautin yanda Abdullah zai iya jiyo abin da Ammie ke faɗi.
"Ai kam dai fa uwar Amarya, Ramlatie na can uwa duniya ɗazu muka gama waya, ai in faɗa miki ranar da Nasiruddeen ya zo ranar na saka borin ya kira shaidu a waje a ɗaura auren, Allah cikin ikonsa sai ya sa er ayin na gidan ta zo. Budan bakin ta wai a ɗaura aure ba bincike ko ba don komai ba wai ai ba'a daula za ta yi aure ba, in gaya miki mijinta na zaune na gwaɓe mata baki, wai se cewa yayi Nisfie taso mu je, ban iya masa tijara ba don na san yana iya sa wa a kulle ni don ba mutunci ne da shi ba. Amma naji daɗi don duk basu so abin da nai mata ba" du suka sa dariya suna mai ganin Ammie ta burge. Haka su ka cigaba da hiran su har su ka mata sallama.
***
A bangaren Ramlat kuwa sun sha amarci na sati biyu ba tare da ya fita ba, amma daga sati biyun nan ba ta sake gane mijin da take aure ba, ya amshe wayar hannunta sannan su kan yini tun safe har ayi sallar isha'i tare ba tare da taga ya yi alwala ba, zai yi sallah duka don shi ke jan su limanci kuma Allah ya ɗaura mata son kira'arsa. Amma tana bin sa jam'i ne cikin waswasi don bata ganin sa yana alwala.
Sannan da ance karfe tara ta yi zai shiga wanka ya sauya kaya zuwa ja da ruwan bula da baki, ya fice ta kofar baya ba tare da yace mata uffan ba.
Duk ta yunkura za ta masa korafi sai ya chanza akalar labarin ya fara shayar da ita kalan na shi salon hakan ke rufe mata baki don jin ta take a wata duniya ta musamman.
A cikin watanni biyu da su ka yi tare, ta tabbatar ma kanta lallai ko menene hanyar samun kuɗin Abdullah toh ba hanya ce mai tsafta ba, don ta sha kama shi da jini a hannu ko kuma ya dawo idon ta biyu ta ga jikin sa duk shatin jini kamar ya feso masa. Anan ta shiga damuwa da danasani fiye da akirga don kuwa ta sha gani finafinan da ake cewa ana kuɗi ta shan jini sannan uwa da mata ake mikawa ko ya'ya. Tsoro da firgici ya shige ta sosai nan duk ta lalace ta yi baki ta shiga damuwa.
Tana cikin wannan damuwar ne Nasiruddeen ya dauke ta zuwa gaida ubangidanshi. Nan ta ke fadama matar damuwar ta don tun da aka yi aure itace mace ta farko da ta fara haɗuwa da ita, shi ya sa tana ganinta bata ɓata lokaci ba ta fara gaya mata matsalar ta.
"Ai kam tun da anyi gara ki yi hakuri, kina so a fara kiran ki bazawara ne? Ai komai munin halin namiji zama ake da shi a rufa masa asiri don hakan ne zai sada mutum ga Aljanna. Yanzu ki yi shiru kuma duk ranar da ya neme ki ta baya ki amince, Aljanna kike nema sai an sha wuya, don in kin hana zai koma kunnama ne yayi ta harbin ki" tace mata kai tsaye, haka ta cigaba da lallashin ta tana faɗa mata abin data ke yi hanyar neman Aljanna ne kuma sai an dage. Ba musu ta amince amma zuciyar ta taqi amincewa don ba laifi Mahaifin su ya yi kokari wajen inganta musu ilimin addini kuma ta san babu biyayya ga miji wa wajen saɓon Allah. Nan ta tuna da iyayenta da yan uwanta, nan ta fara zargin mahaifiyarta da yayarta wajen jefa ta wannan bala'i. Gashi addu'a kanta gagarar ta yake yi. Tunanin da ya faɗo mata ya sa ta washewa ta saki jiki tana ta gode ma matar don kawai ta cinma burinta.
Ko da aka tashi sallan la'asar nan ta ga duk sun Mike sun tada sallah ba tare da sabonta alwala ba, itace dai ta sake sannan su ka shiga yin sallah. Bayan sun idar ne ta samu ta sace wayar matar gidan ta aika ma Fatima da sako. Sannan ta goge shi da lambar gaba ɗaya.
***
Harbin da aka ma Alhamzie ya ɗaga hankalin adjetey ba ko kaɗan ba, don a ranar zubaida ta ga sabon Abdullah ba iri ɗaya da nata da ta sani ba. Masifa yake yana sakin ashar akan masarauta yana ɗauka alwashi. Hankalin sa bai kwanta ba don so yake ya ga Aamir din shi ya ji ya kalan cutar da aka masa duk da rahoto ya zo masa kan cewa a cinya ne aka masa sai dai jini da ya zubar.
"Baba kar ka damu, sai mun gama da daular nan, ni ɗin nan zan jagoranci wannan shiri, sai na zo in Allah ya kaimu sati mai zuwa zan diro. Da kaina zan taho maka kanshi" alwashin da Adjetey ke ma Alhamzie kenan da su ka yi waya safiyar washegarin ranar da aka harbe shi.
***
A qahɗaanie kuwa tun da garin Allah ya waye aka baza jami'an tsaro a lunguna da sakon Qahɗaanie. AbdulHaleem kuma ya tashi cikin shiri don jirgin sama na sojojin sama ne za su wuce da su. Wanda duk cikin dare ya gama shirya wa, ba tare da ya nemi ra'ayin Fatima ba.
"Haba tawan, farin cikin zuciya ta, matar sarkin gobe uwargida na a Aljanna" ya ce yana shafo cikin ta, kamar abin da ke ciki ya sani kuwa ya motsa, da sauri ya janye hannu yana kallonta, dariya ta sa masa kawai.
"ki shirya mu je kiyi ma Abbie sallama, don karfe goma sha biyu zamu wuce" yace kai tsaye
"Aiki na fa? Karatu na fa? Saura kaɗan in haɗa doktora na fa amma ka ce mu tafi?" tace tana mai jin haushi don ita gaba ɗaya ta tsara zata koma gaban iyayenta ne har ya dawo.
"kiyi hakuri, aikin ki za mu dau hutu, karatun ki za ki dinga turo musu ta akwatin sako, azizatie an samu cigaba, ranar gabatar da aikin kuma zaki zo kiyi alkawari ne, kiyi hakuri kece karfi na, ina son ki sosai kinji" ya karasa yana marairaice mata.
"muje amma in Abbie ya ce a'a se kayi hakuri, don mun riga mun tsara zan zama farfesa ne kafin na cika 35" tace tana juya idsnu
"WA MAKARU WAMAKRAL ALLAH, WALLAHU KHAIRUL MAAKIREEN" yace mata cikin kira'arsa mai laushi. Mintsilin shi tayi, shi kuma ya sa mata dariya. Dauko wayar ta tayi nan ta ga sako na yawo buɗewar da tayi se ta ga lambar wata kasa ce don ya fara da +233, buɗewa tayi ta karanta shi kuma ya tsare ta da ido ganin firgicin da ta shiga. Jin tayi shiru yasa ya share suka fita zuwa gidansu.
Tafiyar mintuna goma ya sada su da gidan Abbie, sun iske shi suna hira da matansa alamun sun gama cin abinci. Wayar ta ta mika masa ya karanta sakon bai ce uffan ba ya mika ma Ammie
' Assalamu Alaikum warahmatullah, yaya Fatima Ramla ce ki taimaka min, miji na ɗan luwaɗi ne kuma yana kisa sosai, kusan kullum da jini yake dawowa. Ya kwace wayata, bana fita, banda ko sisi yau ne ya kaini gidan ubangidanshi shine na sace wayar matar na miki text, kar ki kira, ki taimaka min ne don Allah, kar ki faɗi ma Abbie zai shiga tashin hankali, kice ma Ammie ita ta ja min' ta karanta tana zare idanu.
'oh ni Aminatu, bakin ciki har ya kai ga haka, ni za ki ma haka Fatima, yata na cikin kwanciyar hankali kuma da yardan Allah Kinga ɗn luwaɗin nan gefenki" tace cikin borin kunya amma kan cikin ta ya duri ruwa don wata biyu kenan bata ji daga ramla ba. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta shiga ba Abbie ya mika mata farar embilob, yace
"takardar nan tun da kika sheganta ni na rubuta ta amma na aje se kina cikin kwanciyar hankali, ba'a kai ga haka ba na gano irin mazajen da kika haɗa min ya'ya da su.
AbdulHaleem mai martaba ya min bayani, kuje Allah ya muku albarka ya tsare mana ku, zan kula da komai fatima kada ki damu kin ji, maza ku je ku cigaba da shiri" ya karasa yana mai sallaman su fatima wacce ba haka ta so ba, ta so ta rungume mahaifinta ta bashi hakuri su yi nafila tare su roki Allah tare kamar yanda suka saba. Kawai sai ta fashe da kuka tare da fita, kowa ya tausaya musu don matan sun san kukan da take ba na rabuwa bane, na tafiya ta bar mahaifinta cikin kunci ne.
Add Vote
Haka su ka isa gida hawaye kwance a fuskarta, a tunanin ta za su isa Fada ne amma sai ta ga yayi hanyar gidansu.
"ya kamata mu je wajen Ummu ko" tace cikin kuka tana share hawaye, shi takaicin kukanta ya cika shi don bai ga abin kuka ba, sai kace wacce za'a yanka in aka tafi da ita.
"Nace miki an kore ni daga Fada, duk wanda ke son gani na shi zai biyo ni, in kuma za ki je sai ki aje min ɗa na ki je ke kaɗai" ya faɗi a fusace duk da ba hakan ya so ba. Bai kara ce mata komai ba sai figar motar da yayi har ta tsorata. Kallon sa tayi sai ta maida kallon ta ga tagar motar tana kallon titi. Ko da su ka isa gida basu ce da juna uffan ba. Ita wajen kayanta ta je ta haɗa, kayan jariran da su ka fara siya da gadon ta kalla sai hawaye.
' yanzu Shike nan duk shirin mutum
ba tabbas akai, lallai WA MAKARU WA
MAKRA ALLAH, WALLAHU KHAIRUL
MAKIREEN' tace a ranta tana tausayin kanta tana tausaya ma sauran yan Adam yanda mutum yake cike da kashi amma ya zauna yana tsara ma kansa ko wanda ke karkashin sa rayuwa cike da son rai alhali shi ɗin ba komai bane sai digon maniyyi da karshe zai zama abincin tsutsotsi. Ta gama shirya kayan kenan ta jiyo sallamar kuyangin da ke mata hidima nan su ka sanar mata da zuwan mahaifinta. Sam ta manta halin da take ciki na juna biyu ta fita da gudu. Tsaye ta isko shi da AbdulHaleem wani tsalle tayi ta rungume mahaifinta. Haba nan ta saki sabon kuka. Murna take mahaifinta ya shigo gidanta don bai taɓa zuwa ba sai wannan, bakin ciki take saura awanni kaɗan tayi masa nisa.
"Toh Aminiya zan koma tun da kuka za ki yi" yace yana share mata hawaye. "Na sha faɗa miki kuka bai miki kyau ki dena yi" ya kara faɗi yana dariya, itama dariya ta fara tare da jawo hannun sa zuwa kujera,
"Abbie kana lafiya? kayi hakuri kaji, addu'a ce magani, kayi nafilan? Me ke damun ka?" haka ta bi shi da tambayoyi tana rike gam da hannunsa kamar za'a kwace mata shi. Sai a lokacin AbdulHaleem ya fahimci shakuwar da ke tsakanin su nan kuma ya ji takaicin kansa na ihun da ya mata a lokacin da tafi bukatar ya lallashe ta.
" Fatimatuz Zahra! Duk nayi! Ni yanzu yanda zan kuɓuto da Ramla na ke tunani, sanda na so su fahimta sun ki, gani su ke aure ne bana so ta yi, yanzu ga inda gaggawa ya ke neman kaisu ko ince ya kaisu nan." Ya ce yana girgiza kai. Duk sun yi shiru kowa da abin da zuciyar sa ke kintsa masa.
Ganin shirun yai tsawo ne Abbie ya sake katse shirun
" AbdulHaleem ga amanar Fatima nan na baka a karo na biyu, tarbiyyanta, farincikinta, koshinta, suturarta, ilimin ta duk na wuyan ka. Kai ne miji Kaine aboki don ban yarda ka kwace min amintakan ba" Nan duk su ka dara gaba ɗaya.
"Abbie ni de na kwace mata gurbin ta, ka ga aminci tsakanin namiji da namiji yafi, nine amini itace matar amini dukkanmu kuma ya'ya in bata yarda ba ta zama matar ɗa" AbdulHaleem yace cikin dariya, ita kuma ta zumburo baki. Haka Abbie ya musu nasiha sosai akan rayuwar aure da kuma hakkokin da ke kasu. Ya musu addu'a sannan ya sallame su ya tafi su na kewa. Ya tafi ba da jimawa ba tawaga daga fada su ka zo, mai martaba ne da Ummu Maryam. Shimfidar jan kafet ne ya sanar musu da shigowar mai martaba. Cikin ɗaki su ka shige don Fatima ta sauya kayan ta shi kuma AbdulHaleem bai san irin tarbon da zai samu daga mai martaba ba.
Tare suka fito cikin shirin tafiya, sun mika gaisuwa ga iyayen da ke zaune a kan kujera, yayin da masu take musu baya da masu tsaronsu suka tsaya daga waje.
"Yanzu wane kasa kuka shirya tafiya?" mai martaba ya tambaya bayan sun gama gaisawa.
"Italiya" yace kai tsaye
"ina aka samo muku muhalli a Italiyan" ya sake tambaya
" lardin Milan (Milan province)" ya sake amsawa yana sunkuyar kai.
"Allah ya cigaba da tsare ku, ya baka ikon ɗaukan darasin da ya kamata ka ɗauka" ya ce yana zaune ba tare da ya sake cewa komai ba.
"Aameen ya rabbi" su ka ce suna godiya. Ummu kuwa ba abin da tace sai Fatima da ta ke ma nasiha akan hakuri da kuma kula da kai a matsayin mai juna biyu. Daga nan mai martaba ya cire kuɗi ya ba Fatima ya ce ta rike zai mata amfani. Da haka ya su ka tashi su ka juya, Fatima da AbdulHaleem na musu rakiya jikin kowannensu a sanyaye.
***
0 comments:
Post a Comment