BABBAN furodusa a Kannywood, Usman Mu’azu, ya bayyana cewa ana cikin shirin tafiya da fitaccen mawaƙin siyasar nan Isiyaku Forest asibiti a ƙasar waje ne Allah ya yi masa rasuwa.
A cewar sa, ciwon daji ne ya kama mawaƙin, wanda har ya yi sanadiyyar yanke masa ƙafa a cikin shekarar da ta gabata, kuma daga baya ya bazu ya dagargaza masa huhu.
Da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a jiya Asabar, 4 ga Satumba, 2021 Allah ya ɗauki ran Alhaji Isiyaku Muhammad Forest a wani asibitin kuɗi da ke Titin Karkasara a Kano.
Marigayin, mai kimanin shekara 41 a duniya, ya rasu ya bar mahaifiyar sa da matan sa uku da kuma ‘ya’ya 10.
An yi masa sallah da misalin ƙarfe 9:00 na safe a yau a gidan sa da ke unguwar Maidile, a Kano.
Manyan mawaƙa, jarumai, daraktoci, furodusoshi da sauran ‘yan Kannywood da su ka halarci jana’izar sa sun haɗa da Isma’il Na’abba (Afakallah), Dauda Kahutu (Rarara), Aminu Ala, Yusuf Baban Chinedu, Sadiq Mafiya da Sanusi Oscar442.
Da ya ke yi wa mujallar Fim bayani game da wannan abin baƙin ciki da ya faru, Alhaji Usman Mu’azu, wanda aminin marigayin ne na kuskusa, ya bada labari mai ban-tausayi na jinyar da Forest ya yi.
Ya ce, “Da farko mun fita ƙasar waje za a yanke masa ƙafa, sai kuma ba a yanke ba, aka ce an yi masa ‘total treatment’. Daga nan mu ka dawo Nijeriya a kan cewa idan mu ka yi wata shida sai mu ƙara komawa a duba shi.
“Mu na shirin komawa sai korona ta zo, da ta zo aka hana zirga-zirga. Ana cikin haka, sai gwiwar sa ta fara ciwo, sai aka ce idan ba a yanke ƙafar nan ba za a samu matsala, saboda ciwon zai iya ‘transforming’ ya tafi jikin sa. To, mu abin da mu ke zargi, ya yi ‘transforming’ ɗin, mu ba mu sani ba.
“An yi azumi, bayan Sallah sai mu ka je aka yanke ƙafar.
“Bayan an yanke ƙafar, ya dawo ya ci gaba da rayuwa kamar yadda ya saba, ya na harkokin sa, kawai sai ya fara haki. Aka kai shi asibiti aka gwada shi, sai aka ce ruwa ya taru a cikin sa, sai a fitar da shi.
“Da aka fitar da ruwan, aka je aka gwada ruwa, sai aka ce kansar ta taɓa huhun sa ɗaya. Sai su ka ce shawarar da za a yi shi ne a fitar da shi.
“Mun je Abuja mun nemi biza, yanzu haka fasfo ɗin ya na can. Mu na tunanin mu tafi Indiya ko Egypt.
“Wannan makon mu ka yi magana da shi a kan zan je in karɓo mana fasfo ɗin. Kawai sai shekaranjiya ya ce haki ya na ta damun sa. Mu ka ɗauke shi mu ka maida shi Asibitin Aminu Kano. Asibitin Aminu Kano na yajin aiki, sai wani likita ya ce mana akwai wani abokin aikin sa ya na da asibiti a kan Titin Karkasara.
“Da mu ka je, aka yi masa gwaje-gwaje. Bayan an yi, sai su ka ce mana ai huhun shi na gefe guda ya lalace gaba ɗaya, na ɗaya gefen ma ya fara taɓuwa.
“A nan mu ka ce menene abin yi? Aka yi masa allurai, aka ba shi magunguna, aka sa masa ‘oxygen’. Daga nan su ka ce babu abin da za su iya yi masa bayan wannan, mu dai ci gaba da addu’a.
“Wannan abin da su ka yi masa, ɗaya huhun ya ɗauka. A ƙarshe dai ya ce in sa a yi masa allurar bacci domin ya na jin jiki.
“Sai mu ka samu likita mu ka sanar da shi. Sai ya ce a halin da ya ke ciki ba za a iya yi masa allurar bacci ba.
“Ya tashi hankalin sa dai sai an yi masa allurar. A ƙarshe dai likitan ya ce akwai hikimar da zai yi, a je a zuƙi ‘drip’ sai a yi masa a matsayin allurar bacci. Aka je aka yi masa.
“Sai ya kalle ni ya yi dariya, ya ce, ‘Usman, wallahi ba allurar nan aka yi min ba!
“Sai na je na samu likitan, na ce masa, ‘Ya gane ba allurar bacci aka yi masa ba.’
“Ko da na koma sama, na je na samu ana ta ba shi kalmar shahada ya na yi. Nan mu ka ci gaba da yi, mu na ta yi masa. Daga ƙarshe mu ka daina jin muryar sa. Shi kenan, likita ya zo ya tabbatar mana da rasuwar sa.
“Kuma da ma da mahaifiyar sa ta zo ya ce mata, ‘Yadda ku ka rasa yayye na, Adamu da Sule, ni ma yau zan bar duniya.’
“Sai na ce masa, ‘Kai don zuciyar ka ta karye kada ka karyar mana da zuciya. In-sha Allah za ka warke. Ai ka yi wanda ya fi haka.’
“Sai ya yi dariya ya ce, ‘Ba ku san me na ke ji ba ne, amma ni ba zan wuce ba.’
“Duk abin da aka yi tare da Baban Chinedu aka yi. Allah ya jiƙan Isiyaku da rahama.”
Rasuwar Forest ta girgiza Kannywood domin tun da aka bada sanarwar rasuwar sa, masana’antar ta cika da alhini.
Isiyaku ya samu yabo na arziki daga wurin abokan sana’ar sa.
Allah ya rahamshe shi, amin.
0 comments:
Post a Comment