Naziru Sarkin Waƙa
WASU ‘yan jarida sun mayar da martani ga kalaman da fitaccen mawaƙi kuma Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) ya furta a kan ‘yan jarida a cikin dirama mai dogon zango ta ‘Labari Na’.
Ana haska shirin ne a tashar talabijin ta Arewa24 a duk mako.
A cikin mako na 11 na shirin, wanda aka haska a jiya Juma’a, an nuno wani matashin ɗan jarida ya je ofishin Sarkin Waƙa don neman ƙarin haske a kan sabuwar waƙar da ɗaya daga cikin ma’aikatan sa, Sumayya (Nafisat Abdullahi), ta fitar mai taken ‘Dawo-Dawo’.
A ƙoƙarin ɗan jaridar na samun labarai tare da samun bayanin wanene Mahmud ɗin da aka fitar da waƙar a kan sa, ya yi wa Sarkin Waƙa ‘yan tambayoyi, shi kuma ya ce masa ba shi ne ya ke da hurumin bayar da amsa ba, sai dai ya tuntuɓi Sumayya ɗin.
Da za su rabu, sai Sarkin Waƙa ya yi umarnin da a nema wa ɗan jaridar kuɗin mota, bai ko yi sallama da shi ba ya haye motar sa, direba ya ja su ka tafi.
Ƙalubalen Hidaya Ahmed ga ‘yan jarida
Wannan maganar ce ta fusata wasu daga cikin ‘yan jarida a soshiyal midiya, musamman a Facebook, inda su ka bayyana rashin jin daɗin su da kalaman na jarumin ya furta a fim ɗin.
Karanta kuma Ali Nuhu: Yadda zan gudanar da aikin jakadanci da Jami'ar Skyline ta ba ni
Mujallar Fim ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin da ‘yan jarudar su ka wallafa.
Shugabar sashen labarai da al’amuran yau da kullum na gidan rediyon Aminci FM da ke Kano, Hidaya Salisu Ahmed, ta buɗe muhawarar da cewa: “Kamar ‘yan jarida ba ku ji an ce wa ɗan’uwan ku a nema masa kuɗin mota ba a wani wasan Hausa? Menene matsayar ku kan wannan kalamin da Naziru mai waƙar nan ya yi?”
Ita kuma wata mai fafutikar kare haƙƙin mata a Jihar Kano, Zainab Nasir Ahmad, cewa ta yi: “Ko mu da ba ‘yan jarida ba abin bai mana daɗi ba. Akwai raini da ƙasƙanci a abin da su ka yi. Wani mawaƙi da ba a da shaidar kwalin sa na difloma bai kamata ya raina ma’aikacin jarida ba.”
Shi kuwa Auwal Mahmoud Durumin Iya cewa ya yi, “Shirmen banza ne kawai. Ai duk lalacewar ‘yan jarida ba su kai matakin lalacewar da Naziru ya kwatanta su ba a jiya. Babu shakka mu na Allah-wadai da wannan ‘scene’ ɗin da aka gabatar cikin shirin ‘Labari Na’ na jiya. Babban mai laifi kuma shi ne Aminu Saira, tunda shi ne ya bada umarni.”
Karanta kuma Sabbin hotuna masu zafi na Rahama Sadau da ƙannen ta
Saƙon Auwal Mahmud Durumin Iya
Aminu Ibrahim Rimin Keɓe kuma ya ce: “A matsayi na na ɗan jarida, na yi Allah-wadai gami da tir da waɗancan kalaman na Naziru Mai Waƙa. Duk lalacewar ɗan jarida ya wuce a yi masa waccan rashin darajar.”
A ra’ayin Nazifi Dawud kuwa, wanda tsohon ma’aikacin jaridar Daily Trust ne kuma mawallafin jaridar Daily Focus, “Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Ai da ‘yan jaridan ba su wulaƙanta kan su ba, da babu wani mahaluƙin da ya isa ya raina su.
“Mu ‘yan jarida mun san yadda wasu daga cikin mu su ka ƙasƙantar da darajar aikin su, su ka maida kan su almajirai. Kullum su ke nan bin ofis-ofis na ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da sunan neman labari.
“Da yawa daga cikin mu ba su iya yin labarai na bin diddigi (investigative journalism) saboda kada su ɓata wa wasu manya rai a daina ba su abin da ake ba su. Idan waɗannan ‘yan jarida su ka halarci taro, sai su tsaya bayan an gama don a ba su kuɗin da bai taka kara ya karya ba. Wasu ma har faɗa su ke yi a kan wannan kuɗi. Kuma mutane na kallon su.
Karanta kuma 'Yan Kannywood sun yi tir da kalaman Ummah Shehu
“Saboda haka ai maimakon mu zo mu na ɓacin ran banza a kan abin da mu ka san mu na aikatawa, ai gwara mu yi amfani da wannan damar mu gyara aikin mu, mu guji kwaɗayi. Da ba su ga mu na wulaƙanta kan mu ba, wallahi da ba su isa su yi mana wannan cin zarafi ba. Allah ya ganar da mu, ya ba mu ikon gyara wa.”
Abin da Ibrahim Aminu Rimin Keɓe ya ce
To sai dai mujallar Fim ta lura da cewa abin dubawa shi ne rashin albashi mai kyau, da rashin cikakkiyar kula da walwala, da kare haƙƙoƙin ‘yan jarida a Nijeriya na daga cikin manyan ƙalubalen da ma’aikatan aikin yaɗa labarai ke fuskanta a ƙasar nan.
Duk da cewa masu ruwa da tsaki a ɓangaren kamar majalisar kula da ayyukan ‘yan jarida ta ƙasa, da ƙungiyar editoci, da kuma ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ, har ma da masu sharhi da rajin cigaban aikin jarida a Nijeriya sun daɗe su na gwagwarmayar wayar da kan hukumomi game da muhimmancin samar da tsarin da ya dace ga ‘yan jarida, amma har yanzu a iya cewa kwalliya ba ta kai ga biyan kuɗin sabulu ba.
0 comments:
Post a Comment