Ya shiga masana’antar ta Kannywood tun a shekarar 1999 kuma tun daga lokacin ake damawa da shi a masana’aantar har ya zuwa yanzu, kimanin shekaru 22 kenan da doriya.
A wata ‘yar matsakaiciyar hira da aka yi da jarumin, wanda shafin Official Kannywood suka wallafa a shafin su ya bayyana yadda ake yiwa jarumin tambayoyi yana amsawa, inda a cikin amsoshin da yake bayarwa ya sanar da cewa yanzu sun barwa ‘ya’yan da suka haifa da kannen su harkar rawa tunda yanzu su girma ya riske su.
A cikin tambayoyin anyi masa tambaya kan wani tsohon suna da ake kiranshi da shi wato ‘Yaro Mai Tashe’, sai dai a karshe dai ya kare da tabbatar da cewa yanzu ya dai na rawa a fim, ma’ana ya yi ritaya baki daya.
Ga dai magana daga bakin shi jarumi Ali Nuhu:
Ko da yake dai an dade ana yiwa Ali Nuhu maganganu irin wadannan akan ya dai na rawa da ‘yan mata sa’annin ‘yarsa a fim, tun bayan tasowar ‘ya’yansa, da kuma shi kan shi jarumin da ya haura shekaru arba’in ya doshi hamsin.
Sai dai kuma jarumin ya sha bayyanawa masoyansa cewa idan lokacin barin ya yi zai bari, inda muke ganin wala’Allah lokacin ne ya yi yanzu.
0 comments:
Post a Comment