Wata sabuwar jaruma ta caccaki Saratu Daso kan rawa da take yi da kananan kaya a tiktok
Share this content
Lamarin dandalin sada zumunta na tiktok ya zama tamkar wani guri da duk wanda ya sa kansa ciki tamkar kwashe masa nutsuwa yake ya zama tamkar garma-garma, sai mutum ya yi ta abu tamkar marar hankali.
Sai dai a hankali abubuwan na canjawa a shafin na tiktok, tunda an samu wasu ‘yan tsirarun mutane da suke sanya karatukan Malamai da abubuwa na a yaba a shafin na tiktok.
Mafi akasari ana kuka ne da yara ‘yanmata da wasu kadan daga samari dake raye-raye da abubuwa marasa dacewa, sai dai a wannan karon jaruma mai fitowa a matsayin uwa a fina-finan Kannywood wato Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta shiga wannan kafa, inda ta bude shafi take kuma wallafa abubuwa kamar yadda ‘yanmata suke yi.
Wata jaruma mai suna Nafisa Isahq dake fitowa a cikin shiri mai dogon zanfo na “Izzar So” ta kasa hakuri, inda ta yi tsokaci kan abin da Saratu Daso ke yi da ta kira da zubar da mutunci a matsayinta na babba.
Jarumar tayi kira ga manyan masana’antar su taka mata burki a wasu bidiyo guda biyu da ta wallafa sanye da kananan kaya tana tikar rawa.
Wadannan bidiyo na rawa da tayi sanye da kananan kaya ya dauki hankali, inda masoyanta suka dinga yi mata tsokaci da nuna rashin dacewar abin da ta yi.
Ita kuwa sabuwar jarumar bidiyo ta yi, inda ta bayyana rashin jin dadin ta kan wannan abu da Daso ke yi, sai dai ita ma tasha zagi daga masoyan Daso da masu ganin shishshigin jarumar tayi, ga dai abinda jarumar ta ce:
Daso ba ta tanka ba, amma ta wallafa wani bidiyo
Bayan ta yi wannan jawabi na ta Daso ba ta tanka mata ba, sai dai ta wallafa wani bidiyo rai a bace tana sauraron wani jawabi na Sheikh Daurawa, inda yake magana cewa idan rayuwa da matuwa ko wuta da aljannah a hannun mutum suke ya hana mu.
Ita kuwa a na ta bangaren jaruma Nafisa martani tayi ga masu zaginta ta hanyar yi musu bidiyo ta mai da martani da cewa:
Wannan lamari na ‘yan tiktok na cigaba da zama abin jan magana da Allah wadai duk da irin jan hankalin da Malamai ke yi, sai dai tamkar tunzura masu yi ake.
Shin a wannan lamari dake faruwa tsakanin Daso da jaruma Nafisa waye mai laifi, Daso da tayi rawa da kananan kaya duk da shekarun ta da zummar nishadi, ko ita Nafisa da ake zargin tayi shishshigi da shiga abinda babu ruwanta.