ranta a murtuke… bata zame ko ina ba sai kofar gidan su
kawun deeny wato dai wajan mamar deeny ta zo. Tafito
ta nufi cikin gidan ganin bata da niyar bashi kudin sa ne
yace hjy kudin fa. Jirani haka tace mai ba tare da ta juyo
bama. Suna zaune Suna zaune suna jimami sai ji sukayi.
Murya kamar daga sama ku fiddo min ya'ta tana hawaye
dan allah ku taimaka min ku bani yarinya ta ita kadai na
mallaka sai hawaye suka fara zarya gaba daya hankalin
su ya tashi bama kamar maman deeny tace ga kujerq
zauna mana aa ba zama nazo yi ba nidai kawai ku
taimaka min ku fiddo min da di'yata mamar deeny kasa
cewa komai tayi daga haka kawai kuka take abubuwa
sun mata yawa ko abinci kwanan nan biyu bata iya ci
duk ta rame. Aliyu naga ya fito daga dakin sa wanda yana
jin duk abunda ke faruwa yazo gaban maman halima ya
kalli maman deeny yace wannan ita ce mahaifiyar
yarinyar? Kai kawai ta iya daga mai alamun eh ya maida
hankalin sa ga matar wacce kuka yaci karfin ta sai sharar
hawaye take da hijab dinta ya yi kasa da murya sannan
yace inaso ki kwantar da hankalin ki ki saurari abunda
zan gaya miki pls ki natsu ya dauko wata kujera ta katako
wa ajiye sannan yace zauna ba gardama ta zauna ita da
farko da niyar masifa taxo amma harga allah yanda ta
iske su suma gidan gaba daya ba wani walwala shi yasa
taji duk jikinta yayi sanyi. aliyu yace to da farko inaso ki
natsu kiyi tunani sannan zan gaya miki wannan
maganganun ne bawai dan baki sani ba aa kawai dan
tunatarwa yace ki san cewa komai mukaddari ne daga
allah duk abunda ya faru da mutum to daga gare sane
alkhari ko makaman cin sa saidai abunda wasun mu
basu gane ba shine a lokacin da allah ya sauko da
alkhairi ga mutum sai yay ta jin dadi wani ma baya
godewa allah domin gani yake kamar wayansa ne ya
kawo mai wannan alherin. gaba daya maman deeny da
maman halima da kuma ita kanta amina wato maman sa
duk sunyi shiru shi kawai suke sauraro. yace to idan
kuma allah ya jarabci mutum da wata masifar kuma sai
mutu kaga duk ya rikice a nan ne ma zai tuna da allah
hmm shi kuma allah zaima wannan abun ne dan ya
gwada iya imanin ka..... nandai yata mata nasiha itadai
tayi shiru sauraran sa kawai take.yace to ina so ki dauki
wannan abun a matsayin kaddara sannan ki dage da
addu'a domin addu'a itace maka min mumuni yace ke
naki mai sauki ne ma domin ke kin fara cire rai ga yarki
domin ance ta mutu ya nuna maman deeny yace kinga
maman sa nan itama da shi din da kuma maryam wato
kanwarsa duk ba daya daga ciki domin ita maryam tun
ranar da abun ya faru ta tafi islamiya bata dawo ba har
yau shi ma dini kuma haka domin suma basu dawo ba
daga binciken da suka tafi mamar deeny wasu zafafan
hawayan ne suka kubuto mata wanda ita kanta hjy
khadija wato mamar halima saida ta tausaya mata
sannane ma ta san wai maryam bata dawo ba yace ynz
abunda za'ayi shine kiyi hakuri ki koma gida kici gaba da
addu'a domin lamarin nan sai addu'a dai. jiki ba kwari ta
tashi ta musu salama duk a kunyace domin yanda ta
shigo musu da fari tana fita da tarar da dan adaidai tar
nan inda ta barsa ya fiddo waya sai chat yake abunsa shi
kam yama manta da wata yake jira chat yayi dadi ta hau
tace mayar dani inda ka dauko ni. yayi mamaki shima
yanda yaga matar da farko cike da damuwa ynz kuma
gashi ta fito ba kmr dazu ba ya tuka ya maida ita tana
sauka bata tsaya tambyar ko nawa ne kudin ba ta zaro
1000 sabuwa dall ta mika mai domin tasan kudin sa
baikai hk ba ta wuce zata shiga gida yace hajiya chanjin
fa tace ka rike ba tare da ta waiwayo ba dadi ne ya cika
shi shi kuma domin riba biyu ga ya huta kuma ga kudin
da ko lokacin aiki yake bai isa ace dubu ta shigo ba yaja
adaidaitar sa yayi gaba tana shiga gidan sai wayarta
tadau kara tana dubawa taga hjy saratu ce take kira ta
dauka suka gaisa nan take tmbyar ya lbrn halima tace
abundai gashinan sai addu'a nan hjj saratu take gaya
mata suyi hkr da basu sama zuwa ba amma ga yazeed
nan zuwa yau yau.... ...........
A CAN BANGARAN SU DEENY KUWA.........
ISAHN ♥ KUNE
π«π« BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng π«π«
Na π king boyπNa π king boyπ
Part 21
.
CIKIN gidan suka nufa suna waige waige yana yin gidan
ya fara furgita su domin ko motsin basuji ba wata kofa
ce katuwa wacce akayi da zinary a sukazo kofar dakin
sukayi curus kowa yaki yarda ya fara taba kofar ogan ya
kalli deeny da jikin sa ke rawa yace kai zo ka bude mana
kofar nan dan uban ka. Haka ya taho yana makyarkyata
kamar ya kama kamar kuma yaki saidai yasan ba yanda
ya iya
Wata zuciyar tace mai kai koma fa kun kubuta daga
gidan nan to ba makawa kashe ka za'a yi domin banda
wannan hujar ba wata tunda anzo ba'aga ko ramin ba
kaga kuwa ba makawa kashe ka za'ayi sai yaji duk tsoro
ma ya fita a ranshi. Ya rufe ido yayi yan addu'o'i sannan
ya sa hannu biyu ya tura kofar da yake kofar mai hannu
biyu ce kamar get gani sukayi kofar ta bude kai tsaye
Suka nufin parllo suka fara salama shiru basuji ko motsi
ba hakan yasa suka kutsa kai sukayi cikn. Katan farllo ne
tan gameme yasha ado kujeru ne jere birjik a parllan ga
kuma can wasu dakuna ba adadi a jere sai kalle kalle
sukeyi domin dakin ya hadu sosai durum wuta sukaga ta
dauke hade da wata shu'umar dariya hahahaha muna
maraba da ku yau abinci har gida hhhhhhh dadai zuwa
mukeyi mu kamo da karfin mu ko musa sihirin mu mu
kama amma yau muna maraba da sauyin da yaxo mana
cikin wannan masarauta hahahahaa kuma sai sukaji tsik
dariyar ta dauke wuta kuma ta dawo a kame na gansu
waje daya ko wanne cikin su sai karkarwa yake deeny
kuwa da yake baya wasa da addu'a tun da yaga wannan
al'amari ya dukufa karanta →ayyatul kursiyu← ( yan
uwa mu bar wasa da addu'a duk a binda kaga zai firgita
ka saka allah a ranka ka fara addu'a zakaga dace sannan
tsoranka zai fita allah kasa mu dace ameen) can kuma
sai hasken ya fara ya kawo ya dauke can kuma sai gaba
daya dakin ya zama ja jawur wata kofa sukaga ta bude
wasu karti ne ke futuwa daga ka gansu kasan ba imani ko
kadan a ransu gasu bakake duk ba riga sai Ja jayan
wandu na a jikin su da kuma jan kyalle a kansu sun
dadaura.kowa ta kansa yayi dukan su kofa suka nufa da
gudun su kowa na ta kansa wutar dakin ta dauke dub..
can jimawa kadan sai wutar dakin ta kawo kowa ganin sa
yayi a hannun kato guda hankalin su tashe kowa sai fizge
fizge yake deeny ne kawai baya fizge fizge kasan cewar
shi tuni ya sadaukar da rayuwar sa a zuciyar sa kuwa
addu'a kawai yake wani tsoho ne ya fito kanaa duk
furfura cikin fararan kaya idanunsa jawur da alamun
dai shine shugaba a wannan gidan hahahaja haka ya
taho yana dariyar mugunta yaxo gaban su daya bayan
daya yana kare musu kallo sai fizge fizge suke deeny
kadai ya gani a nutse yaje gaban sa ya tsuguna tsayin su
yazo daidai yace yaro nan fa gidan mutuwa ne nan gidan
shan jini a ci nama ne nan gidan a tarihin sa ba wani
mahaluki da yake shigowa ya fita da rai in ba dan
kungiya ba amma kai me yasa naga kamar baka damu
ba alhalin kasan mutuwa zakayi
deeny ya dago kai wanda har lokacin gabansa faduwa
kawai yake da ya hada ido da mutumin nan duk sai yaji
tsoro ya fita a jikin sa ya samu kwarin gwewa. yace
hmmm me kake tunani ne da kake fadar wannan mgnr
ko dan banyi mamaki ba domin kai ba imani a zuciyarka
bana tunanin kana da ilimin sanin allah da har zakasan
shine mai kashewa mai rayawa ba kuba. hakika maganar
deeny ta bata masa rai. ya daka masa tsawa kai yaro ni
kake gayawa wannan bakaken maganganun ya kama
habar deeny ya zaro wata wuka ya dora mai a wuya yace
sake fada mgn daya in baka sheqa lahara ynz ba kuma
jinin ka zamu sadaukar da shi ga gunkin mu sanan
namanka yan kungiya ne zasu cinye hahahahah mgnr da
deeny ya fada itace ta tsaida shi daga dariyar hade da jin
wani mugun bacin rai kamar xuciyar sa zata kone. kai
jahiki ne wannan mgnr ce ta fito daga bakin deeny
wanda har ynz wukar ce a wuyansa. can kuma sai ya
tuntsire da dariya hahahah i like this boie ina san marar
tsoro irinka da zaka shigo kungiya mu da ka huta yaro da
ka more dadin duniya kuma kaci arziki ka barsa hatta
jikokin ka ma bazasu yi talauci ba. tirr tirr da wannan
muguwar kungiya taku da zaka gane alherin lahira shine
yafi dacewa da ka nema jindadin duniya aikin banxa
ne....... waya tayi ringing wani kato ya mikowa ogan
wayar sir bad boy calling ya amsa wayar ya kara a kunne
yana kallan deeny hello bad boy daga can kuma hw ar u
dady 5yn dad i will come 2 kano 2day wow am hppy
bad son kafin kazo kuwa zan tana dar maka baban abun
tarya. tnx dad bye. ok bad. tashi yayi daga wajan deeny
yake fadawa wannan kartan bad boy na hanya dan haka
dole a tanadar masa muhimmin abu ya kalli yan sanda
wanda duk a tsure suke yace waye oga a cikin ku waye
babba? kowa ya nuna dan uwansa ogan ma na gefan sa
ya nuna suka kama bararabi. tsawa ya daka musu nace
waye babba yana karkarwa ya daga hannu yallabai nine
ku kawo min shi nan. saida akazo gaban deeny dashi
sannan yasa wasu kartai suka danne wannan ogan yan
sandan yasa wuka wuluk sai ga kai a kasa............ king
boyn kune
π«π« BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng π«π«.
Na big boy isah
Part 22
Gaba daya sauran yan sanda sun kidime sakamakwan
basu saba ganin kisa irin wanan ba deeny kuwa ido ya
lumshe hade da cewa ya allah. Ya daga kai sama.
Hahahahaha tshon ya fara dariya suma kartin nan gaba
daya sai suka kama dariya can kuma sai yayi shiru kamar
hadin baki suma kuma duk sai sukayi tsit sannan ya
nuna wasu karti hudu yace ku dauki wannan naman ya
nuna ogan yan sandan nan kuje ku gyarama oga domin
yana nan tafe cikin yan secondna tuni sun dauke sa ya
dubi su deeny yace kuma duk waka zamu muku domin
ba mai shiga gidan nan ya kubuta kuma baza'a fara a
kanku ba dan haka sai ku shirya yana gama maganar ya
juya ya nufi wani dakin har zai shiga ya juyo ya kalli wani
kato daga cikin kartan nan yace ku kaisu dakin ajiya ya
juya ya shige dakin .....
su anne ne zaune gidan inna sai tadi suke su ukun kmar
dama kawaye ne gwaggo tace ai gwara ku tashi ku tafi
can gidan ku ta kalli anne tunda kinga yamma tayi anne
kuwa cijewa tayi wai ai ita bata so a rabasu da halima
duk dadai tare da maryam zasu koma tace inna me xai
hana mu kwana a nan ynz inje in kawo mana abincin
rana da dadare ma haka inje in kawo ina tace to kwantar
da hankalin ki tare da halimar zaku tafi can ku kwana
uwar iyayi har zaki fara kawo mana kabli da ba'a di ba
yanzu kuka sha fura ba har wani abinci rana kuma za'a ci
da sauri su maryam suka kalli kaka. kaka fura ce abinci
rana kuma cewar maryam. kaka ta rike baki ohh ni ya'su
yanzu bayan furar nan har wani abinci kuma za'aci.
anney tace hmm kunga ku kyale ta ai tsohuwa ce ita ta
kusan margayawa shi yasa bata iya cin abinci da yawa
amma ko ni nan ai cikina ba komai nake jinsa. su duka
suka hau dariya halima tace ai ni fura dan marmari
kawai nake shanta ba dan koshi ba. kaka tace kundai
hade baki ko to ai sai ku tashi ku tafi can gidan kuci
abinci ni dai na koshi furar na ta ishe ni har gobe da safe
duk suka zaro ido gobe fa. Anne ce ta tashi oya standup
following me tayi gaba su kuwa dariya sukayi turancin
yar rugga....
tafiya suke su kunya suke ji duk jikin su ko gyale babu
duk ba wacce ke da gyali a gunta ga mutane sai kallan su
ake ita kuwa anney sai wani bun kasa take ita wai with
yan bunni haka sukata tafiya duk garin ba mai kyau
anney saka makwan gata fara da kyan diri hadee fuskar
ta yar doguwa ma daidai ciya duk da yake ba duguwq
bace sosai amma kuma ba gajera ce ba duk da su
maryam yan burni ne basu saba da wahala ba ba
abunda zasu nunawa anney saidai ma ta nuna musu da
yake yar fulani ce
Tafiya suke suna ta shiririta sun biye wa anne ta saya
musu wannan ta saya musu wannan sai washe baki take
tana tare da yan bunni. A haka har suka karasa suka iske
maman anne tuni ta dafa abinci su kawai take jira da
yake tanada yar sauran shinkafa itace ta idasa dafewa
suka shigo da salamar su ko wacce da murmushi a
fuskarta haka anne taje ta dauko musu tabarma roba
wai a cewar tayan burnine ba tabar mar kaba za'a basu
ba. Suka zauna a ka zubo musu a tran silva suna ci suna
hira salama sukaji. Gabaki daya suka amsa hade da
kallan kofar shigowa da sauri maryam ta kauda kai
ganin mai salamar ba wani bane isah ne rike da zoman
daji dayan hannunshi kuwa ya riko kwari da gwafan
shi...................oooppppps
King ne ♥
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng π«π«.
Na big boy isah
Part 23
Maman anney ta fito da mamaki a fuskarta dannan
sannanka da zuwa yau kuma kane a gida da rana haka
abunda bakayi.ya sunkuyar da kai wanda ya kara bayana
kyan fuskar sa tare da cewa uhm uhm..... Yama rasa me
zaice ya kama in ina gaba daya suka kama kallan sa
maryam ce kawai taki dagowa domin in suka hada ido
wani abu take ji na daban da ta rasa minene. Cansai yace
ummana dama wannan na kawo muku ya daga xomo
tare da nunashi.tace hmm dama kana kawo mana xomo
a haka ne ai sanin da nayi saika babake ka gyara kake
kawo mana
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 22 Na
Isah Bigboy
Gaba daya sauran yan sanda sun kidime
sakamakwan basu saba ganin kisa irin
wanan ba, deeni kuwa ido ya lumshe
hade da cewa “ya Allah”, ya daga kai
sama. Hahahahaha tsohon ya fara dariya
suma kartin nan gaba daya sai suka
kama dariya can kuma sai yayi shiru
kamar hadin baki suma duk sai sukayi
tsit sannan ya nuna wasu karti hudu
yace ku dauki wannan naman, ya nuna
ogan yan sandan nan kuje ku gyarama
oga domin yana nan tafe. Cikin yan
sakanni tuni sun dauke shi, ya dubi su
deeni yace kuma duk haka zamu muku
domin ba mai shiga gidan nan ya kubuta
kuma baza'a fara a kanku ba dan haka
sai ku shirya, yana gama maganar ya
juya ya nufi wani dakin har zai shiga ya
juyo ya kalli wani kato daga cikin kartin
nan yace ku kaisu dakin ajiya ya juya
ya shige dakin.
************************
Su anne ne zaune gidan inna sai tadi
suke su ukun kamar dama kawaye ne,
gwaggo tace ai gwara ku tashi ku tafi
can gidan ku ta kalli anne, tunda kinga
yamma tayi, anne kuwa cijewa tayi wai
ai ita bata so a rabasu da Halima duk
dadai tare da maryam zasu koma tace
inna me xai hana mu kwana a nan yanzu
inje in kawo mana abincin rana da da
dare, inna tace to kwantar da hankalin ki
tare da halimar zaku tafi can ku kwana
uwar iyayi har zaki fara kawo mana
kabli da ba'a di, ba yanzu kuka sha fura
ba har wani abinci rana kuma za'a ci, da
sauri su maryam suka kalli kaka, kaka
fura ce abinci rana kuma cewar maryam,
kaka ta rike baki ohh ni ya'su yanzu
bayan furar nan har wani abinci kuma
za'aci, anne tace hmm kunga ku kyale ta
ai tsohuwa ce ita ta kusan margayawa
shi yasa bata iya cin abinci da yawa,
amma ko ni nan ai cikina ba komai nake
jinsa, su duka suka hau dariya halima
tace ai ni fura dan marmari kawai nake
shanta ba dan koshi ba, kaka tace kundai
hade baki ko to ai sai ku tashi ku tafi can
gidan kuci abinci ni dai na koshi, furar
nan ta ishe ni har gobe da safe duk suka
zaro ido gobe fa.
Tafiya suke sai kunya suke ji duk jikin
su ko gyale babu duk ba wacce ke da
gyale a gunta ga mutane sai kallan su
ake ita kuwa anney sai wani bun kasa
take ita wai tare da yan bunni, haka
sukaita tafiya duk garin ba mai kyawun
anney saka makwan gata fara da kyan
diri, fuskar ta doguwa ma daidai ciya
duk da yake ba duguwa bace sossai
amma kuma ba gajera ce ba, duk da su
maryam yan burni ne basu saba da
wahala ba, ba abinda zasu nunawa anne
saidai ma ta nuna musu da yake yar
fulani ce. Tafiya suke suna ta shiririta
sun biye wa anne ta saya musu wannan
ta saya musu wannan sai washe baki
take tana tare da yan bunni. A haka har
suka karasa suka iske maman anne tuni
ta dafa abinci su kawai take jira da yake
tanada yar sauran shinkafa, suka shigo
da sallamar su ko wacce da murmushi a
fuskarta haka anne taje ta dauko musu
tabarmar roba wai a cewar ta yan
burnice ba tabar mar kaba za'a basu ba.
Suka zauna a ka zubo musu a tiran silba
suna ci suna hira, sallama sukaji, gabaki
daya suka amsa hade da kallan kofar
shigowa da sauri maryam ta kauda kai
ganin mai salamar ba wani bane face
isah ne rike da zoman daji, a dayan
hannunshi kuwa ya riko kwari da bakan
shi...................Maman anne ta fito da mamaki a
fuskarta “dannan sannunka da zuwa,
yau kuma kaine a gida da rana haka
abinda bakayi”, ya sunkuyar da kai
wanda ya kara bayyana kyan fuskar sa
tare da cewa uhm uhm..... Yama rasa me
zaice ya kama in ina gaba daya suka
kama kallan sa maryam ce kawai taki
dagowa domin in suka hada ido wani
abu take ji na daban da ta rasa menene.
Can sai yace ummana dama wannan na
kawo muku ya daga zomo tare da
nunashi, tace hmm dama kana kawo
mana zomo a haka ne, ai sanin da nayi
saika babake ka gyara kake kawo mana
yadan sosa kyeya “kuma dama inajin
yunwa ya kalli gurin tukunya an gama?
Maman nashi ita duk mamaki ya cikata
tace nemi waje ka zauna bari in kawo
ma. Haka ya samu wani dan turmi ya
zauna.
Yanayi yana satar kallan maryam a
zuciyarsa yace shin wai yarinyar nan ko
dai yar fillo ce, ji tsabar kunya taki kallo
na ma hmm yarinya kenan ai wllh tunda
kika riga kika harbo kibiyar so ta caki
zuciyata ba yanda za'ayi in barki wata
zuciyar tace sbd me? Kana santa
mana..... Duk zancan zucin da yake idan
sa na kan maryam suma da suke gefe
suna cin abincin su. “Kai kai dan na”
maman sa ce a tsaye ta kawo mai
abincin, firgigit ya xabura ya karba. Me
kake tunani haka, meke damunka,
tabbas ta gane me yake kallo domin tun
sanda ta kawo mai abincin taga idansa
na a kan maryam. Yace umma ba komai
wllh kawai ina dan nazari ne, ta juya
tare da cewa to Allah ya kiyaye, anne
kuwa da hankalin ta yana kan su isah
tuni ta gane abinda ke faruwa tayi
murmushi a zuciya tace wato yaya isah
anga yar burni......
Yazeed ne ya shigo da motar sa mai gadi
yayi saurin budewa da yake ya gane ko
waye. Gadan gadan gunda aka tanada
domin faka mota ya ajiye ta, karamar
mota ce kirar 407 ya tsaya tare da fitowa
ya ya nufi cikin gida, maman halima na
falo taji shigowar sa ai kuwa cikin far'a
ta tare shi, tare da kirawo yan aiki suje
su dauko mai kayansa a mota. Haka suka
zauna falo suka gaggaisa sosai sannan
ya tashi ya nufi dakinsa wanda dama an
tanadar masa idan yazo nan yake zama,
yan aiki ma sun sani domin can suka kai
mai akwatin sa da sauran kayansa.
Maman halimar tayi mamaki mutuka da
yazeed bai tambaye ta ko ince jajanta
mata a kan haleemar ba, sai dai kuma
kawai ta basar tace amma kuwa indai
rikicin da sukayi da haleema ne har
yanzu abun ya tsaya mai a rai har ya
gagara yimin maganar ta gaskiya bai
dai-dai ba, haka dai taita sake sake
Abunda ya hada su fada wancan zuwa
da yazeed yayi………….
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
hudu dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 23
Share This:
Yazeed dai ya kasance baya san surutu
idan ya shiga dakin da yake sauka a
gidan su haleema, ba ya bari kowa ya
shigar mai daki, kuma sai yayi shiru ko
motsinsa ba'a ji. Wata rana waje jan
karfe goma na safe duk anyi karin
kumallo kowa ya watse ya kama harkar
gaban sa, ba sauran abinci sai na yazeed
gashi kuma yaki zuwa ya dauka, halima
abun ya bata mamaki ganin 10:30
shayin zaiyi sanyi da sauran kayan bai
fito ba, ita dai tana nan tana ta danne
danne a waya ta leka can ta leka can nan
har ta kira deeni suka fara waya. Bayan
sun gama ta duba agogo taga 10:40 har
zataje ta dauko filas ta juye mai kuma
saidai ta fasa, a zuciyar ta tace ba'a shiga
dakin ka ko to wallahi ni yau sai na
shiga saidai in kashe ni zakayi kayi ta
dauki kayan break din ta nufi dakin da
yazeed yake.
Ta yi nufin kwankwasawa, dafa
hannunta keda wuya taji kofa ta bude, a
sanyaye ta saka kafa kamar marar
gaskiya tsakar dakin ta tsaya tana yan
dube dube, ganin yana ban daki ta ajiye
mai kayan karin a tsakar daki, can wajan
waige waige ta hango wani abu kamar
kwaran gwal sai dai a lullube yake, tashi
tayi a hankula ta nufi wajan, mika hannu
tayi da niyar ta cire abunda ya lullube
wannan abun, wata irin tsawa taji an
daka mata da sauri ta juyo, yazeed ne ya
fito daga bandaki daure da tawul ga
dukkan alamu ma bai gama wankan ba,
haka ya fito sakamakon jin an shigo
dakin, domin ruwa kawai ke disa a jikin
sa, ita kuma abunne ya burgeta ta tsaya
tana kallan sa yanda ruwa ke bin ta
yalwacin kirginsa ga gashi lip lip abin
gwanin sha'awa ji take kamar taje ta
rungume shi. Saukar marin da taji shi ya
dawo da ita hayyacinta, “baki da hankali
ne, ke wawuyar ina ce, uban wa ya kawo
ki nan bana hana kowa ya shigo min
daki ba kuma you know shine zaki shigo
min daki get out, ita kuwa duk ta saka
hannuwa ta rufe kumatun ta biyu,
sakamakon marin da ya sakar mata,
uban ihu ta saka! radadin zafin mari
ganin batada alamun tafiya yasa shi
kama hannunta da karfi yaja ta ya kaita
waje, tukun ya dawo ya saka key ya
kulle dakin.
Sa kuka take sossai hakan yasa mamanta
taji ta taho da sauri “lafiya lafiya kuwa,
haleema subuhanallah me akai miki kike
kuka, bata iya cewa komai ba domin
kuka yaci karfin ta haka ta fara zage
zage tana kuka tana Allah ya isamin wai
momy daga na kaimai kayan kari cikin
kuka take maganan, mum din ta shiga
lalashin ta tana cewa kiyi hakuri mana
keda ba yarinya ba kuma kinsan cewa
ba'a shigar mai daki me ya kaiki shiga.
Ta kalli umman nata ido duk hawaye,
mum abincin sa fa naga zai huce na
kaimai, to me yakai ki, yanzu dai ai
gashi kinjawa kanki, mum din tayi gaba.
Kare fashe wa tayi da wani sabon kukan
me hade da shagwaba mum bazaki ce
mai komai ba tana bubuga kafa, to ni me
zance mai ai ke ce kika jawa kanki.
Kofar dakin taje ta fara mai Allah ya isa.
Hakika yaji haushi, hakan yasa ya zare
belt ya bude kofa ya nufota a
guje...................
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
biyar dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 24
Yazeed dai ya kasance baya san surutu
idan ya shiga dakin da yake sauka a
gidan su haleema, ba ya bari kowa ya
shigar mai daki, kuma sai yayi shiru ko
motsinsa ba'a ji. Wata rana waje jan
karfe goma na safe duk anyi karin
kumallo kowa ya watse ya kama harkar
gaban sa, ba sauran abinci sai na yazeed
gashi kuma yaki zuwa ya dauka, halima
abun ya bata mamaki ganin 10:30
shayin zaiyi sanyi da sauran kayan bai
fito ba, ita dai tana nan tana ta danne
danne a waya ta leka can ta leka can nan
har ta kira deeni suka fara waya. Bayan
sun gama ta duba agogo taga 10:40 har
zataje ta dauko filas ta juye mai kuma
saidai ta fasa, a zuciyar ta tace ba'a shiga
dakin ka ko to wallahi ni yau sai na
shiga saidai in kashe ni zakayi kayi ta
dauki kayan break din ta nufi dakin da
yazeed yake.
Ta yi nufin kwankwasawa, dafa
hannunta keda wuya taji kofa ta bude, a
sanyaye ta saka kafa kamar marar
gaskiya tsakar dakin ta tsaya tana yan
dube dube, ganin yana ban daki ta ajiye
mai kayan karin a tsakar daki, can wajan
waige waige ta hango wani abu kamar
kwaran gwal sai dai a lullube yake, tashi
tayi a hankula ta nufi wajan, mika hannu
tayi da niyar ta cire abunda ya lullube
wannan abun, wata irin tsawa taji an
daka mata da sauri ta juyo, yazeed ne ya
fito daga bandaki daure da tawul ga
dukkan alamu ma bai gama wankan ba,
haka ya fito sakamakon jin an shigo
dakin, domin ruwa kawai ke disa a jikin
sa, ita kuma abunne ya burgeta ta tsaya
tana kallan sa yanda ruwa ke bin ta
yalwacin kirginsa ga gashi lip lip abin
gwanin sha'awa ji take kamar taje ta
rungume shi. Saukar marin da taji shi ya
dawo da ita hayyacinta, “baki da hankali
ne, ke wawuyar ina ce, uban wa ya kawo
ki nan bana hana kowa ya shigo min
daki ba kuma you know shine zaki shigo
min daki get out, ita kuwa duk ta saka
hannuwa ta rufe kumatun ta biyu,
sakamakon marin da ya sakar mata,
uban ihu ta saka! radadin zafin mari
ganin batada alamun tafiya yasa shi
kama hannunta da karfi yaja ta ya kaita
waje, tukun ya dawo ya saka key ya
kulle dakin.
Sa kuka take sossai hakan yasa mamanta
taji ta taho da sauri “lafiya lafiya kuwa,
haleema subuhanallah me akai miki kike
kuka, bata iya cewa komai ba domin
kuka yaci karfin ta haka ta fara zage
zage tana kuka tana Allah ya isamin wai
momy daga na kaimai kayan kari cikin
kuka take maganan, mum din ta shiga
lalashin ta tana cewa kiyi hakuri mana
keda ba yarinya ba kuma kinsan cewa
ba'a shigar mai daki me ya kaiki shiga.
Ta kalli umman nata ido duk hawaye,
mum abincin sa fa naga zai huce na
kaimai, to me yakai ki, yanzu dai ai
gashi kinjawa kanki, mum din tayi gaba.
Kare fashe wa tayi da wani sabon kukan
me hade da shagwaba mum bazaki ce
mai komai ba tana bubuga kafa, to ni me
zance mai ai ke ce kika jawa kanki.
Kofar dakin taje ta fara mai Allah ya isa.
Hakika yaji haushi, hakan yasa ya zare
belt ya bude kofa ya nufota a
guje...................
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
biyar dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 24
Share This:
RECOMMENDED ARTICLESBANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng .
Na big boy isah
.
Part 25
.
Note..
A zancen gaskiya dole inyi jinjina a gare ku masu bibiyar
novel dina Dubun godiya a gare ku da bibiyar BANI NA
KASHE TABA duk da nasan ba wani dade gare sa ba amma
a haka kuke hkr dani kuke bibiyar sa ina jin dadin
haka amma ku san cewa mai hakuri wata ran xai dara
domin wannan shine first novel dina kunga kuwa sai slow
but da sannu sannu yaro ke girma dan haka ku kara hkr
inda nayi ba daidai ba luv u oll
.
.
.
Haka sukaita zagaye parllon yana ta zane tana kuka da ihu
sai hajiya ce ta raba to tunda ga wannan ranar kuma ba
maiwa wani mgn tsakanin ta da yazeed but tasha duka....
Wannan kenan
... Yana shiga dakin ya cire kayan jikinsa ya shiga toilet ya
hada ruwa sannan yayi wanka ya fito ya feshe ko'ina na
jikin sa da turare sannan ya kama shafa wani abu wanda
bansan ko me nene ba ga alamu dai abun nada wari
domin turaran ne ke hana jin warin jeans yasa tare da
wata black shirt ya taje gashin kansa sannan ya dau
wayoyin tare da car key dinsa ya fito hjy ya iske a parllo
mum har ynz dad din bai dawo ba? Yace yana dan
murmushi eh wllh kadai ga har ynz gashi yamma ta fara
yi ok mum zan danje nan wato maman hallema da yake
mum yake ce mata. Haba yazeed kaima kasan hakan
bazata faru ba ga abincinka can fa a dinner an hada maka
kuma kace zaka fita ko abinci baka ci ba shin wai inama
zaka? Inda yaji kansa ya daure haushin kansa ma yaji da
ya tambaye ta can kuma ya dago kai au wllh zanje gun
friends dina ne domin tun kafin ynz suna ta called dina
naki dagawa shine nake sauri in fita kuma bana jin yunwa
ynz wllh....
To shikenan a dawo lfy in ka dawo kaci.
Fita yayi yaja motarsa a guje ya dau hanya ko ina zasa
oho......
Haba mum deeny kamar yarinya ki dinga kuka haka
addu'a ne ya kamace mu b kuka ba dan allah kiyi hkr
aliyu ne yake bata hkr ita kuwa sai sharara kuka take mai
matukar cin rai da ban tausayi ga wanda duk ya gani
haba aliyu taya ta wace hanya ce zan iyayin shiru ai ko
nayi niyar hakan bazai yuyuba zuciyata kuna take a ko
wane lokaci idan ba kukn nayi ba bana ma jin dadi. Sanan
ta hau wani saban kukan wanda saida ta cika dan
karamin parllo. Cikin kuka take cewa miye amfanin
rayuwa ta in ba wannan yaran me amfanin tama. Ya
salam yace hb mum da girma ki fa kuma kinsan kaddara.
Wqce irin kaddara ce wannan da zta rabani da yarana
iyee wace kala ce... Nan dai na barsu tana kuka abun
tausayi ana rarashinta....
Hanyar wani kasurgumin jeji ya nufa gudu yake kamar
me baya da niyar tsayawa haka yata lumawa cikin daji da
motar sa wajajan 6:00 ya isa kofar wannan kata faran
gida wato inda su deeny suke bisa mamaki yn zuwq kofa
ta bude ya kutsa kai ya sama waje yayi park. Wani sashe
da ban ya nufa a cikin gidan ya shiga wani room sai gani
nayi yazeed ya canja shiga wato ya cire kayansa ya saka
wasu jajaye ne riga doguwa tare da wani jan wando..........
...
By
Bigboy isah
Sannan ya daura wani jan kyalle a
goshin sa saidai nasa ya banbanta da na
sauran wancan kartin, shi zai tabbatar
maka cewa shima babba ne a kungiyar
sannan ya dawo ya nufi wannan kofar
dakin, ai kuwa yana nufar kofar ta bude
sannan ya shiga.
Duk wannan kartan sun jeru layi layi
sunyi sahu sahu, ta tsakanin su ya wuce,
duk wanda yazeed yazo saitin sa sai ya
durkusa kasa dan kwasar gaisuwa.
Wannan tsohun na can kan wata kujera
ya hakimce ga wani dining table a gaban
sa duk kujeru ne a zagaye da table din,
sannan sai wata kujerar mai kama da
tasa a kusa dashi, kai tsaye yazeed ya
wuce dayar kujerar ya zauna.
Sannan ne suma manyan cikin kungiyar
sun zo duk an zazauna kowa da plate a
gaban sa, abun dake cikine zaisa idan ka
kalla sau daya baza ka kara ba, sasan
jikin mutum ne kala kala a ko wane
plate ba kyan gani, “welcome my son”
inji tsohon juyawa yayi ya kalleshi hade
da cewa :thank you” sannan tsohon ya
tashi yana wasu gwalan gwalantun
tsafinsa sannan yace muna maraba da
babban yaro na kuma shugaba magajin
wannan kungiya wato yazeed (bad man)
ya dora da cewa kun sani cewa a cikin
mu ko jikokin dan kungiya bazasu yi
talauci ba, bazasu taba sanin miye babu
ba kuma baza mu yi sasauci ba ga duk
wanda ya bujirewa umarnin mu, sannan
ku sani dole ku kula da dokokin kungiya
sannan ya juya ga yazeed yace dodon
mu yana bukatar jini kuma daga gareka
wato a cikin dangin ka, dole ka bamu
jininn ka domin tun farko kayi alkawari
cewa a wannan shekarar ne zaka bayar.
Chan kuma cikin dakin ajiya wato inda
aka saka su deeni sun matukar gala baita
yunwa ma ta ishe su gashi anki kawo
musu abinci, wadannan yan sandan biyu
sun sha kuka kamar ransu zai fita
sannan suka hakura sukayi shiru, domin
ba maganin da kukan ke yi musu ba.
Deeni ne ya tashi ya nufi kofar fita
sakamakwon magana da yake ji sama
sama, lekawa yayi ta wata yar kofa, da
sauri ya dago ya dan kama baki alamun
yana so ya tuna wani abu, a ina yasan
waccan fuskar kamar ya taba ganin ta,
kunne ya kafa yana saurare me suke
cewa.. ..
Yazeed ne ya mike yayi gyaran murya,
“a matsayina na mataimakin shugaban
mu kuma babana gashi a zaune ya nuna
wannan tsohon. Inaso in muku bayani
wato dan takaitacan tarihina domin
kusan cewa a harkar nan ba imani idan
kanada imani bazaka ci muriyar mu ba...
Ni dai na kasance fuska biyu ne domin
idan ka ganni a gari bazaka taba cewa ni
mugu bane, yanda nake al'amura na
sakin fuska, kyauta da sauran halaye
masu kyau. Ina so ku sani yan matan da
na kawo nan aka hallaka sun fi a kirga
kuma duk a matsayin saurayi nake gare
su, abinda baku sani ba shine duka ba
wacce mahaifanta suka sanni, hatta
unguwa sai naje nesa da tamu sannan
nake yin budurwa, ku sani cewa yan
matan yanzu ba ruwansu da
SOYAYYAR GASKIYA kawai sudai
abin hannunka suke bukata, laifin iyaye
kuwa da suke barin yaran su wato mata
suna fitowa zance alhalin basu san
saurayin ba.
Ya danyi shiru tukun yace karfa ku zata
wannan nasiha ce, no ni da kuke gani ba
alamun imani ko tausayi tare dani, ni na
hallaka haleema ya fada tare da kawarta
maryam sakamakwan tona min asiri da
suka so suyi.....
Gaban deeni ne yayi mumunar faduwa
sai yanzu ya gane yazeed din
sakamakwon sau daya ya taba ganin sa,
ya dafe kai da yake sara mai da karfi,
“yanzu yana nufin ya hallaka min
maryam dina, no no no, haleema na da
gaske kin mutu kai ban yarda ba karya
kake karya kake” ganin zasuji yayi
saurin control din kansa ya natsu sai
hawaye sharrrr!
Can ya sake kafa kunne dan jin me
yazeed ke cewa...
Sannan ina so in fadawa kungiya cewa
lallai ni mai cika alkawari ne dan haka
naba kungiya babana (mahaifina) ranar
Friday zan kawo shi domin baya garin
nan amma tabbas nasan yanda zanyi in
kawo shi, wannan babbar kyauta ce
nawa kungiya... Gaba daya suka fara
tafi.........................
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
bakwai dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 26
Share This:Shi kuwa deeni gaban sa ne yaci gaba da
faduwa wato kawun haleema kenan aka
bawa dodo, hawaye keta kwaranya a
idaniyar deeni, wai an kashe haleeman
shi da kuma kanwarshi shi maryam da
yake matukar ji da ita, bashida burin da
ya wuce ya farantawa ummansa da kuma
yar kanwarsa wato maryam tunda
babansu baya raye, wani xazzabi ne ya
rufe deeni.
Maryam ce zaune kan wani gado na kara
ta dafe kumatu wato tayi tagumi, tunanin
ummanta kawai take, wasu yan siriran
hawaye ne suka kwaranyo, haka
haleema ma da take kwance
kwakwalwarta sai juyawa take cike da
tunani iri iri tama rasa wanne zatayi shin
waye mai neman hallaka mu, shin wane
hali deeni na ke ciki, shin umma da abba
ya zasu ji na rashina bayan basa san yin
nesa dani ko kadan, idanun ta cike da
kwalla ta tashi zaune ganin maryam a
gefan gado ta zuba uban tagumi,
“maryam maryam” inji haleema tunanin
me kike. Tuni maryam ta dago tare da sa
zani tana goge hawayan fuskarta, nan
haleema ta fahimta cewa duk ashe daya
ne halin da suke ciki. Ta dafa kafadar ta
haba my sis ki saka dangana a zuciyar ki
mana mu barwa Allah komai shi zai yi
mana maganin wannan al'amari ba kuka
ne abunyi ba...
Aneesat ce ta shigo, ganin su a wannan
yanayi ta fahimta tunanin gida suke yi,
duk da sun so su boye wa anne amma
saida ta fahimta, “haba yan uwana, nan
fa kamar gidan ku ne ku kwantar da
hankalin ku, dama yanzu daga wajan
maman mu nake shawara muke yi yanda
za'a maida ku gida, ku kwantar da
hankalin ku”...
Tabbas sunji dadi sosai da jin kalaman
anne gaba daya suka ce “hmm anne
kenan haba ba komai amma gaskiya
muna so muga iyayan mu domin basu
san ko wane hali muke ciki ba, kinga in
sun gammu hankalin su zai kwanta.
Yaro ya shigo da salamar sa “anne wai
ana kiran maryam, bata tsaya ko jin
waye ba tace “je kace gata nan”, domin
anne tuni ta kyaro su wato tana lura da
abunda ke faruwa tsakanin maryam da
kuma isa. Ya zaki ce gani nan bayan
baki san kowa ke sallama ba, shin waima
cikin gari nan waya san ni da har zai
aiko kuma wai ace maryam tazo ma.
Anne tayi murmushi ai sai kije ki gano
mana. cikin zolaya haleema tace
“kanwar mu ah gaskiya kinzo kauyan
nan a sa'a kinga shikenan sai mu barki
anan”. Suka sa dariya gaba daya. Bari
inga ko waye tunda kun matsa ta ce,
anne ara min hijab dinki. Ya mata daidai
kuwa kamar dama nata ne..
A tsaye ta iske shi ya harde kafafu da
kara da ya rike a hannun hagu yana
wasa da shi, hannun daman kuma yasa
shi cikin aljihun wando.
“Assalamu alaika” ta fada, wani irin
sauti mai dadi yaji a zuciyarsa yace
dama haka muryar yarinyar nan take
ashe.
Amin wa'alaiki Salam warahmatul lahi
ta’alah wa barakatuhu: sanda ya cika
amsa sallamar cif cif.
Gefe daya ta samu ta tsaya nesa da shi
kadan, ita kam ta kasa dagowa da kanta
domin wannan ne karo na farko nata na
tsayawa da wani da namiji ..
Maryam kenan sarkin kunya shin ko dai
kema yar fulani ce kamar mu, amma ai
ke kunyar taki tayi yawa ma.
Murmushi kawai tayi domin ta gane
yaya Isah ne shi isa taki ma dago kanta
domin tsoran abinda take ji in ta hada
ido da shi wato faduwar gaba.
Ki daure ki dago kanki, ki kalle ni ya
fada yayin da ya dan kara matsowa
kadan kusa da ita.
A hankali ta dago kai “wow” dama haka
wannan bawan allah yake da kyau, ashe
duk ganin da nake mai zaije farauta ne,
amma duk da haka yana da kyau saidai
kayan da yasa sun kara fito da zallan
kyawun sa wanda haka yasa ta kafe shi
da ido shima dai abun ya daure mai kai
ta tsaya sai kallan sa take...
Um dama so nake in gaya miki……
Kuma sai yayi shiru, ka fada mana a
zuciyarta ta fadi hakan, gani tayi ya
kalle ta, tayi saurin sunkuyar da kai ashe
yaji abinda tace...
Maryam ba wani abu bane dama ina so
in gaya miki ina sonki, ina kaunar ki,
tunanin ki ya hanani sukuni ko ina naje
bana jindadi in ban ganki a gunba, idan
na rufe ido ke nake gani, nayi tunanin
cire haka a zuciyata sakama kwan ni dan
kauye ne ke yar birni ce kinga kuwa
auran mu bazai yiwu ba amma dai yanda
sanki ya addabi raina yasa ni dole in
gaya miki ko naji dan sauki...
Farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta hakika
taji dadin kala man sa, wannan ne na
farko da namiji ya taba cewa yana santa
abinda ko da wasa ba'a taba gaya mata
ba, kalmar so kenan yayin fadarta sai
bakin ka ya fara bari duk jarumtakar ka,
bama kamar karo na farko haka duk
macen da aka furtawa a take a waje sai
taji chanji, lalai so halitar Allah ne,
juyawa kawai tayi da niyar tafiya ita
duk kunya ta dabai baye ta..
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
Salam Alaikum masu bibiyar wannnan
labari, muna baku hakuri sakamakon
rashin kawo muku cigaban labarin har
na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo
bayan wasu kalubale da muka fuskanta
amma yanzu insha Allahu zamuci gaba
daga inda muka tsaya.
**************
A baya mun tsaya ne inda
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
***************
Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida
yana ta tunane tunane shin me yarinyar
nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata
so na ba saita fada ba kawai a wuce gun,
Isah ne shi kadai yana tafiya yana
zancan zuci....
Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka
gyara zama wato haleema da anne wai
sai ta fada musu waye yazo gunta, ai
kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi
anma tace kawai bata sanshi ba. Anne
tace to ai nasan dole ya fada miki
sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane
saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi
min suna ba... Suka hau dariya wai bata
da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar
maryam wacce ita kuwa tunani ne duk
ya addabe ta..
************
“Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a
cewar mamar tasa, sannan ya juya ga
maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har
yanzu ba batun ko daya daga cikin su
ne? Wllh mama babu wani labari a
cewar aliyu haka makarantar su maryam
ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni
ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a
idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara
sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana
inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta
fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime
suka kwasa sai asbiti akayi Emergency
da ita, duk a gigice suke sun ma kasa
zama da kyar aka lallashe su da cewa
jinin tane ya hau yanzu tana bukatar
hutu anjima zasu iya shiga domin ganin
ta ....
Bangaran yazeed kuwa
*******************
Naman suka hau ci kallo daya zaka
musu ka fahimci ba imani a tattare da su
gaba daya yanda suke cin abinci da
sassan dan adam a ciki amma su ko a
kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya
badman kayi mana asara kasan fa
dodanmu yafi bukatar jinin yan mata
amma ka bari su mugu suka kashe su.
Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba
wanda su mugu suka samu damar
kubutar da su, a inda suka iske su a nan
suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah
ne ya kawo mana dakwale har hudu
police 3 da kuma wani 1 dan karamim
cikin su. Dad kace naman police ne shi
isa na ganshi da baki baki. Hahaha
sukayi wata irin dariya tasu ta marasa
imani wacce suka saba. Tashi muje ka
gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu
dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan
can naman abinci mana, ko so kuke sai
sun rame sun zama kashi ne.
Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya
wato inda su deeni suke, kallan deeni
yake kamar yasan shi saidai ya rasa a
inane, gaba daya kan yazeed ya daure to
shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi
gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna
wani abu amma ya kasa kai kamar na
sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake,
“a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed
yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu
da abinci, plate uku ne aka bawa deeni
daya suma sauran aka jiye musu nasu,
kamar jira suke dama suka fara aika
abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da
katar da su “kudaina cin abincin nan” ya
fada. Wata irin harara dan sandan ya
dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni
kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff
sai ya ga akwai nama mutum da sauri
yasa kafa ya hankadar da abincin ya
zube ..
*************
Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba
ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi
bangaran abokinsa da wato salmanu ya
zauna kan dan guntun iccan da yake a
zaune, abokina waya tabo ka ne naga
duk ka wani canja fuska, ya tambayi
isah. hmm abokina zo muja gefe ina san
magana dakai, salmanu ba gardama
kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya
kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa
da maryam tun daga farko har karshe,
yace to amma naga alamun yarinyar ba
sona take ba jifa yanda na dame ka a
kanta ko da yaushe tunanina gareta ne
amma kaga fa abinda ta saka min da shi
kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da
ita harda su rike ciki, “bana san haka fa
kai wato nazo na fadama damuwata,
wato abinda zaka min kenan ko kasan fa
na tsani dariya” isah ne ke fadan haka.
Salmanu ya dafa kafadar sa yace
kwantar da hankainka abokina nasan
baka fahimta bane kawai, amma a
hakikanin gaskiya ina tayaka murna
abokina domin na tabbata ta amshi
soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan
ma lokacin da ya rungume salmanu ba
dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana
domin kuwa murmushi ta shine tabbacin
haka sannan ba yanda za'ayi in mace
bata sanka ta maka murmushi a lokacin
da ka furta mata so saidai ma ta bata rai.
“Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani
yaro ne dan makwabtan su aka aiko,
“Wake kirana” isah ya tambayi yaran,
“abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan
zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin
wannan gagarumin albishir naka sannan
yanzu taya zan gane haka gaskiya ne
idan naje gidan. Kawai abinda zakayi
shine ka mata murmushi in kuka hada
ido sai kaga kalan martanin da zata
dawo maka dashi inji salmanu. Nan
sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan
nasu.
Assalami alaikum ya maimaita har sau
uku amma shiru kake ji gidan kamar ba
mutane. Saida ya zo wucewa ta
matattakala sannan ya fahimci akwai
mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu,
Haba hajara miye haka ne yasa zaki
dorawa kanki damuwa da yawa bayan
haka allah ya kadarta, haka yayi niyya
ya faru gare mu, kisawa ranki dangana
mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago
alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan
fuskar ta. Haba maman deeni yanzu
dama duk wannan kugin da nake faman
yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi
tausayi domin yanda take ji da yar ta,
rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu.
Rungumota yayi a jikinsa yana share
mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa
sai shesheka take tana cewa yanzu
shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta
kara kakame alhaji tare da kuka mai
tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da
lallaban ta yana lallashin ta...........
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
Tara dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 28
Share This:Salam Alaikum masu bibiyar wannnan
labari, muna baku hakuri sakamakon
rashin kawo muku cigaban labarin har
na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo
bayan wasu kalubale da muka fuskanta
amma yanzu insha Allahu zamuci gaba
daga inda muka tsaya.
**************
A baya mun tsaya ne inda
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
***************
Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida
yana ta tunane tunane shin me yarinyar
nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata
so na ba saita fada ba kawai a wuce gun,
Isah ne shi kadai yana tafiya yana
zancan zuci....
Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka
gyara zama wato haleema da anne wai
sai ta fada musu waye yazo gunta, ai
kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi
anma tace kawai bata sanshi ba. Anne
tace to ai nasan dole ya fada miki
sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane
saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi
min suna ba... Suka hau dariya wai bata
da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar
maryam wacce ita kuwa tunani ne duk
ya addabe ta..
************
“Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a
cewar mamar tasa, sannan ya juya ga
maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har
yanzu ba batun ko daya daga cikin su
ne? Wllh mama babu wani labari a
cewar aliyu haka makarantar su maryam
ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni
ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a
idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara
sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana
inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta
fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime
suka kwasa sai asbiti akayi Emergency
da ita, duk a gigice suke sun ma kasa
zama da kyar aka lallashe su da cewa
jinin tane ya hau yanzu tana bukatar
hutu anjima zasu iya shiga domin ganin
ta ....
Bangaran yazeed kuwa
*******************
Naman suka hau ci kallo daya zaka
musu ka fahimci ba imani a tattare da su
gaba daya yanda suke cin abinci da
sassan dan adam a ciki amma su ko a
kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya
badman kayi mana asara kasan fa
dodanmu yafi bukatar jinin yan mata
amma ka bari su mugu suka kashe su.
Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba
wanda su mugu suka samu damar
kubutar da su, a inda suka iske su a nan
suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah
ne ya kawo mana dakwale har hudu
police 3 da kuma wani 1 dan karamim
cikin su. Dad kace naman police ne shi
isa na ganshi da baki baki. Hahaha
sukayi wata irin dariya tasu ta marasa
imani wacce suka saba. Tashi muje ka
gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu
dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan
can naman abinci mana, ko so kuke sai
sun rame sun zama kashi ne.
Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya
wato inda su deeni suke, kallan deeni
yake kamar yasan shi saidai ya rasa a
inane, gaba daya kan yazeed ya daure to
shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi
gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna
wani abu amma ya kasa kai kamar na
sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake,
“a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed
yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu
da abinci, plate uku ne aka bawa deeni
daya suma sauran aka jiye musu nasu,
kamar jira suke dama suka fara aika
abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da
katar da su “kudaina cin abincin nan” ya
fada. Wata irin harara dan sandan ya
dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni
kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff
sai ya ga akwai nama mutum da sauri
yasa kafa ya hankadar da abincin ya
zube ..
*************
Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba
ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi
bangaran abokinsa da wato salmanu ya
zauna kan dan guntun iccan da yake a
zaune, abokina waya tabo ka ne naga
duk ka wani canja fuska, ya tambayi
isah. hmm abokina zo muja gefe ina san
magana dakai, salmanu ba gardama
kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya
kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa
da maryam tun daga farko har karshe,
yace to amma naga alamun yarinyar ba
sona take ba jifa yanda na dame ka a
kanta ko da yaushe tunanina gareta ne
amma kaga fa abinda ta saka min da shi
kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da
ita harda su rike ciki, “bana san haka fa
kai wato nazo na fadama damuwata,
wato abinda zaka min kenan ko kasan fa
na tsani dariya” isah ne ke fadan haka.
Salmanu ya dafa kafadar sa yace
kwantar da hankainka abokina nasan
baka fahimta bane kawai, amma a
hakikanin gaskiya ina tayaka murna
abokina domin na tabbata ta amshi
soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan
ma lokacin da ya rungume salmanu ba
dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana
domin kuwa murmushi ta shine tabbacin
haka sannan ba yanda za'ayi in mace
bata sanka ta maka murmushi a lokacin
da ka furta mata so saidai ma ta bata rai.
“Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani
yaro ne dan makwabtan su aka aiko,
“Wake kirana” isah ya tambayi yaran,
“abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan
zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin
wannan gagarumin albishir naka sannan
yanzu taya zan gane haka gaskiya ne
idan naje gidan. Kawai abinda zakayi
shine ka mata murmushi in kuka hada
ido sai kaga kalan martanin da zata
dawo maka dashi inji salmanu. Nan
sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan
nasu.
Assalami alaikum ya maimaita har sau
uku amma shiru kake ji gidan kamar ba
mutane. Saida ya zo wucewa ta
matattakala sannan ya fahimci akwai
mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu,
Haba hajara miye haka ne yasa zaki
dorawa kanki damuwa da yawa bayan
haka allah ya kadarta, haka yayi niyya
ya faru gare mu, kisawa ranki dangana
mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago
alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan
fuskar ta. Haba maman deeni yanzu
dama duk wannan kugin da nake faman
yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi
tausayi domin yanda take ji da yar ta,
rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu.
Rungumota yayi a jikinsa yana share
mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa
sai shesheka take tana cewa yanzu
shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta
kara kakame alhaji tare da kuka mai
tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da
lallaban ta yana lallashin ta...........
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
Tara dan jin cigaba
adsAliyu ne ya shigo dauke da ledoji guda
biyu a hunnunsa, ya ajiye ledojin tare
da dagowa yace mama ya jikin maman
deeni, da sauki ai, Alhmdulilah saidai
doctor yace ta rage tunani domin duk shi
yake kara zafin ciwan .
Yaja nunfashi tare da cewa to Allah ya
bada lafiya ga abinci nan ai sai ki bata
ko, kema ga naki ya mika mata ledojin
sannan ya mike ya fita, maman deeni
kuwa duk ta wani rame tana jin su duk
abinda suke kuma idan ta a bude amma
bata iya cewa komai ba...
******************
Deeni kuwa tunanin tserewa yake domin
kuwa yaji yazeed yace zai kawo baban
sa. Yace a ransa ai gwara in fita ko ba
komai da zan taimakawa kawun haleema
kuma zan sake ganin ummina ko sau
daya ne kafin a zartar da hukunci a
kaina. Juyawa yayi ya kalli yan sandan
nan yaga sai barci suke abinsu, shi kam
kwana 2 da yayi a gun ko gyan gyan di
baiyi ba.. .
***********************
0 comments:
Post a Comment