wata jaka ya dauko wata Pistol ya bude
ta ya zube harsashi sannan ya sakata a
tsakanin belt din sa na wand, ya sake
fitowa a fusace sannan cikin hanzari
yazo ya wuce, har ya kama kofa zai
bude sai abbansa yace: “yazeed mene
haka ina zaka kake sauri haka ko gaida
abbanka bakayi ba” daddy ina zuwa
abinda kawai ya fada kenan bai jira
wata amsa ba ya bude kofa ya fita. Gurin
motoci yaje yasa makullin motar ya
warce ta kamar wanda zai tashi sama....
Deeni kuwa cikin cell kake hango sa
yayi tagumi duk an bubuge masa kafa,
tunani yake tayi kala-kala a zuciyarsa, a
gaskiya idan ya makara fa yazeed zai
kai kawun haleema gidan gunkin su, shi
isa duk ya matsu da su sallame sa amma
ina sunki wai shi mugu ne sai sunyi
bincike a kansa. DPO suke jira kuma
wai shi sai 9:30 yake zuwa.
Wani makeken gida yazeed ya faka tare
da yin hoon, mai gadi ya leko yana
ganin yazeed ne da sauri ya bude gate
din dake shima yasan yazeed, a millon
ya shiga gidan motar ma bata gama
tsayawa ba ya bude murfin motar ya fito
a fusace ya nufi cikin falon. Ko
kwankwasawa bai tsaya yi ba ya tura
kofar ai kuwa ta bude. A dinner ya iske
su mugu suna breakfast shayi da biredi
ne da wainar kwai sai indomei, ko
sallama baiyi ba, tsaye cik yayi yana
kallan su, a zuciya yana cewa wato na
baku aiki bakuyi ba kun min karya kuma
gashi sai holewa kuke abinku. Oga ne
ya dago kai, Yazeed ya gani a tsaye ya
zuba musu na mujiya fuska a murtuke
ba ko walwala a fuskarsa..
Ah mai gida yazeed barka da zuwa kana
tafe ashe kuma shine ko kira babu ai da
mun tanadar maka special break da
munsan zaka zo, sai a lokacin ne su
mugu suka lura ma da yazeed din take
duk suka tsare shi da kallo suna mai
wani dan murmushi...
Shi kuwa maganar ce ta ogan ta bata mai
rai yaji wani tiririn bakin ciki yake ji a
zuciyar sa, wata zuciyar tace ya harbe su
kawai, me yake jira da su wata kuwa
zuciyar tace, ya tambaye su yaji me zasu
ce karya zasuyi ko kuwa..
Karku min karya, kunce min kun kashe
maryam da haleeema?
Dukkan nunsu saida hantar cikin su ta
kada domin duk sanda suka firgice
domin kuwa sun san tambayar nan ba’a
banza ba, ruwa baya tsami banza kuma
sun san yazeed ba imani a tare da shi,
duk shiru sukayi suka kasa cewa komai,
duk sun shiga tunani, ogan cikin sune ya
katse tunanin da yin wani dan
murmushi, Hmm oga yazeed kenan kaga
ya daga hannu, Ni na kasheta Halima....
Harbi uku kawai akaji sai gasu duk a
kasa, ya juya da bindiga a hannunsa
tana wani tiriri.
Fita yayi da waya a makale a kunnan sa,
barka da safiya shi ne abinda ya fara
furtawa dake mu Journalisms in zamani
ne har mgnr wancan in naji. Morning hw
ur day shine abunda yce: im 5yn: dad
haleema an maryam they ar living. Me
kake cewa kasan me kake fada kuwa.yes
srry dad wllh nayi da nasani sa su mugu
aikin da ni na aikata da duk hkn bata
faru ba amma saukin abu ba alamun
cewa sun fadi abunda suka gani.gud ka
take care of ur self. Ok dad bye. Ya
kashe wayan sannan yi shiga motan sa
yazo gate yayi oda da nufin mai gardi
yaxo ya bude mai gate amma ina yaji
shiru.
Abinda bai sani ba shine mai gadi yana
jin harbi yayi waje da gudu, dole ce tasa
sai shi yazeed ne ya fito a motan yaje ya
bude gate in.
Can gidan su haleema tuni an gama
breakfast kowa ya kama harkokin gaban
sa su alhaji bangaran su daya su uku,
yau dai kawu an kashe mai zuwa kasuwa
du da yaso ya fita amma haka bai samu
ba, su alhaji sanusi sun hanashi dole
tasa shi hakura, yanayi yana surutu a
zuciya “hmm wato ku masu kudi ko?
kun tara! ku bar bawan Allah ya fita ya
nemo na kansa amma kunki ku barni...
Haka shima isa yayi niyar jan yar
kanwar sa su nufi gida in yaso sai ya
dawo batun maganar auran maryam
amma alhaji ya hana yace dole ya bari
sai gobe domin akwai kyauta ta
musamman da zaiyi mai na ban mamaki.
Haka ya hakura gashi aliyu ma ya fita ya
barsa shi kadai ne a wajan yayi zuru sai
kale-kalle yake dake a lambu ne. Ji yayi
an rufe mai ido daga baya da wasu
tatausan hannaye, wani sanyi ne yaji ya
ratsa duk kannin jikinsa, baiji anyi
magana ba murmushi kawai yayi tare da
cewa hmm anne, to na gano ki. Shiru
yaji ba'a tanka ba kuma sai yaji abin
zobe a hannun nan ya tabbatar da ba
anne bace domin yasan ita bata da
zobe............
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 37
Share This:A GAFARCE MU NA RASHIN KAWO
MUKU CIGABA DA WURI
Wata zazakar murya ce yaji ta daki
dodan kunnansa, ta shiga cikin
kwakwalwarsa ta dinga yimar yawo.
Tabbas bazai taba mantawa da zazzakar
muryar maryam ba, “Hmm maryam”
yace, Hmm taya ka gane nice lokacin da
ta sake shi tana zagayowa ta zauna a
kusa dashi, haba tayaya ne zan ji muryar
abar sona in kasa gane wa ai da bakiyi
magana bane shine sai in kasa ganewa.
Murmushi tayi tare da cewa ya isah baka
gayawa su umma abinda ke tsakanin mu
ba kuma dazu kake cewa wai zaka tafi,
dan marairai cewa yayi tare da cewa ai
ko na tafi ma to annesah zan kai in dawo
gare ki sahibata, idan ka aure ni a wane
gari zamu zauna? Tabbas ta debo
babbar magana, shin yanzu shi mema
zaice mata ne, shima kansa ba san
zaman a wancan kauyen yake ba balle
ita da take dama yar birni, kai gaskiya
da sake, to yanzu me zaka ce mata. Yana
cikin yan sake-sake ne tace “yaya isah
ina sanka, so na gaskiya kasani cewa ko
a kauyenku zamu zauna zan aure ka.
Wani murmushi yayi wanda ya kara
bayyano kyawunsa, baice komai ba,
hada ido sukayi, sun dade a haka suna
kallan juna.
Yazeed ne ya shigo ya faka motar sa
kafin ya fito, da murmushin sa ya fito ya
nufi inda su abban suke ya gaida su da
kawu wato baban aliyu sannan yake
gayawa abban sa ya shirya yanzu zasu
je domin yaga gun aikinsa da kuma mai
gidansa. Alhaji bashir ya kalle sa yace
to ai a shirye ma nake, yi sauri ka zo mu
tafi, amma ina kaje ne naga kana
hanzari haka ko karyawa kuma bakayi
ba ka fita inji abban nasa.
Daddy naje wajansa ne domin ya kira ni
namai wani dan aiki ne, ok to allah yama
albarka tashi jeka. Tashi yayi ya nufi
falo, Haleema da Maryam da Anne su
duk ukun suna zaune a falo sun kunna
kallo sunayi hade da hira sama-sama.
Baima bi ta kansu ba kai tsaye dakinsa
ya nufa, “ina kwana Ya yazeed”, Yaji
ance. Juyowa yayi bisa mamaki yaga ai
haleema ce, lfy lau yace har ya juwa zai
bude dakin ya karaji an gaida shi da
murya biyu, Maryam da Anne ne, suma
haka dai ya cije lebe ya amsa sannan ya
wuce dakin nasa. Kan gadonsa ya haye
yana jin wani tiriri da zafi a zuciyar sa.
Wanni bangaran kuma tunani yake taya
zai hallaka su tun kafin su tona mai asiri
domin tunani yake sun san ko shi waye,
amma yayi mamaki da basu fadawa
kowa ba, yaji kamar ya kyale su
hallarcin da suka mai na kin tona masa
asiri, saidai kash!! Lokaci ya kore dole
ya kashe su domin kuwa a duniya banda
su ba wanda ya san ko shi waye sai yan
kungiyar su.
Mutanan gari a yaro mai ladabi mai
girmama na gaba da shi, mai kyauta, san
addini, kyakykyawar tarbiya kawai suka
sanshi, ba wanda yasan mugun abinda
yake aikatawa, kuma ya shafe sama da
shekaru 4 a cikin wannan kungiya.
Tashi kawai yayi rai a bace, ya fito da
wayarsa yayi kira wata number “da fatan
ashirye kuke domin ina zuwa da
mahaifina”. Eh a shirye muke kawai a
ka fada ya katse wayar ya shiga
bandakin dake cikin daki, yayi brush
tukwanan ya dan watsa ruwa ya fito ya
chanza kaya, Jeans baki yasa sai wata
riga T-shirt mai layika shudi da fari, ya
taje gashinsa, yayi kyau sosai tukwanan
ya fiton daga dakin.
Su haleema da ke zaune a falo suna
shiriritar su. Tun kafin ya karaso gunsu
kanshi ya cika su,gaba daya kamar
hadin baki suka juya suna kallan sa shi
kam ko damuwa baiyi da su ba ya wuce
waje abinsa. Haleema kam yayi mata
kyau yau, tace wa maryam kinga
mutumin yau anci gayu ko dai zance
zashi, kinga ba ruwana kinsan dai halin
sa ... Hhhhh dariya halima tayi au ashe
baki manta ranar ba, Maryam ta kama
baki tare da cewa hmm wane ni in
manta, Anney kuwa tambaya ta shiga yi
wai me akayi wancan ranar, suka share
ta. Can halima ta dago ta kalli anney
"ohh yi hakuri anneesat, bari in gaya
miki abin da ya faru wancan rana."
Kamar kullum duk weekends maryam na
kawo min ziyara ko ni in kai
mata............
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 38
Share This:HALIMA TACI GABA DA BAWA
ANNE LBR: Ranar wata lahadi maryam
ta kawo min ziyara kamar yanda kika
ganmu yanzu to haka muka zo falo
muka kuna kallo sai hira muke abun mu,
yazeed yana gidan wato ya kawo ziyara.
Maryam ta tambaye ni miye tsakani na
da yazeed da muke faman fada da shi
haka, nace mata wai kawai dan na shiga
dakin sane kinsan ya hana, “to miye a
dakin nashi da yake hana shiga, naga dai
ba komai ne a dakin gauro ba daga kati
fa sai jakar kaya” inji maryam. Nace
mata to shi wannan ba haka yake ba
domin shi abubuwa sunyi yawa a dakim
nasa domin harda wani abu na gani ma a
rufe da wani zane, haka nake gayawa
maryam a lokacin, ita kuwa kin ganta
nan da karan bani tana jin haka naga ta
mike.
Nake tambaya ina zata tace wai dakin ya
yazeed, wai in taso muje tunda baya
gida nace mata wallahi ni bazan je ba
kuma kema ban goyi bayan kije ba idan
kika je duk abinda ya same ki toh ni ba
ruwa na, tace ita dai wai yasin sai taje ta
bincike dakin taga wai miye da yazeed
baya san a shiga.
Ai kuwa kamar wasa maryam ta nufi
dakin ya yazeed ni kuwa kallo ya dauke
min hankali ban kula ba har ta bude
dakin ta shige ba tare da fargabar komai
ba domin nace da ita baya nan. Nidai ina
nan sai kallo na nake nama manta da
maryam ta shiga dakin, ita kuwa
bincike-bincike ta hau yi chan ta hango
laptop dinsa, ai kuwa taci sa'a ba
password a jiki, haka ta haye mai kan
gado tana ta danne-danne abinta.
Ganin shiru-shiru maryam bata fito ba
yasani tashi na bita, abin mamaki a kan
katifa na ganta da kwamfuta sai wangale
baki take bata ma ko kula da na shigo
ba, hakan yasa naje da sauri ke maryam
wai me kike yi ne haka, kinzo kin wani
zauna a dakin mutum bayan kinsan idan
ya dawo ya tarar dake sai ya wulakanta
ki gashi kuma kinsan mama bata nan
wallahi duka zai miki. Yayin da nake
karasa wa wajanta ta dago min wani
hoto dake jikin laptop din, yazeed ne
cikin wasu jajayen kaya, fuskan sa duk
ya shafe ta da wasu zanuka.
Nan muka yada zango a kan gadonsa
muke ta kallan hotunansu shida wadan
su abokan sa, mun kusan share minti 30
muna kallan hotunan amma bamuga
karshen su ba haka yasa muka koma
wani bangaran. Da nace aje videos
amma Maryam taki yadda, haka yasa na
kyale ta badan naso ba ta kamo games
nan ma mukata bugawa, ni dai na nace a
kan sai an shiga videos nashi, “ kin cika
naci da yawa wallahi ke da almajira ce
da masu masu sun shiga uku wallahi,
bari a shiga videos din"
Mu kam sai shagalin mu muke yi ba
ruwan mu mun ma manta da a dakin wa
muke. Nan maryam ta nufi kan videos ni
kam nayi mamakin yanda ta iya
computer haka ma domin nasan bata da
ita, hakan yasa na tambaye ta a ina ta
koya tace a laptop din yaya deeni mana,
ta shiga bude videos, video farko ya
ruda mu gaba daya jikin mu ya fara
rawa a tare tuni muka kankame juna
domin kuwa abinda muka gani ne yafi
karfin tunanin mu.
Anne tayi zugum ta saki baki sai
sauraren labari take yi, gani tayi halema
na waige-waige saida taga ba kowa
sannan ta yi kasa kasa da murya sosai
sannan take cewa “anny wallahi in gaya
miki annesah yazeed ne a videon ya rike
wuka yana yanka mutum, kuma dan yaro
gashi nan jage-jage duk jini shi kuwa
sai yanka sasan jikin wannan yaran
yake, yaro ne fa dan shekara baifi 7 ba.
Ganin haka ya firgita mu da gudu muka
tashi a tare ni da maryam da niyar muyo
waje ko laptop din bamu wani tsaya
kashewa ba, abin mamaki ina kama
kofar yazeed shima ya turo da niyar zai
shigo.
Karki so kiga yanda mukayi baya a wani
firgice ni kam bansan lokacin da na
shiga basa hakuri bama, maryam kam
tuni ta fara kuka, shi kam da ya shigo
tsayawa yayi chak ya kare wa dakin
kallo yaga duk an bincike mar daki can
ya hango laptop dinsa a kunne tana
kallo. Daga jin sautin video ya gane ko
wannene, haka yasa shi kulle dakin da
mukulli ya koma can gefan katifarsa ya
jawo computer ya kashe tukun,ya hada
hannuwa biyu ya dora a goshi alamun
yana tunani kenan..
Anne in takaice miki labari wallahi ranar
mun daku domin samun mu yayi kamar
yayan sa ya dinga lafta yana fadin zaku
kara, muna kuka muna a’a, saida yayi
mana dukan tsiya sannan yace muyi
shiru, ya zazzare mana ido tare da cewa
wallahi muka sake muka kuskura
wannan maganar ta fita duk sai ya kashe
mu. Hakika mun tsorata ba yanda muka
iya haka ya bude mana kofar muka dawo
falo muka sha kukan mu. Kinga zancen
nan dana fada miki ko to wallahi ba
wanda na fadawa ko ummana da abbana
basu sani ba domin nasan wannan
mugun zai iya aikata komai, Halima da
tazo nan ta juya ga maryam, “ke ko kin
taba gaya wa wani”, “ni nama isa” inji
maryam. Ai tun lokacin na kama baki na
nayi shiru gidama da naje mama tayi
kokarin gane miye ya same ni amma
naki fada mata nace ba komai. Anne ta
rike baki tare da girgiza kai chabb!!
Wallahi idan nice sai na tona asirin sa a
kan me, ke rufawa kanki asiri idan kika
fada akaje kuma ba'a kama sa da hujja
ba ya zaki ce? Jikin anne yadan yi sanyi,
kinga ba muda mafita ne, kawai kedai ki
bari rana dubu ta barawo rana daya ta
mai kaya ko ba haka bane? Haka ne inji
anne sannan ta mike “matar yaya zo ki
dan rakani mana” inji anne take fada
mawa maryam, maryam ta mike tare da
cewa ina? “Dakin yazeed mana da sauri
maryam ta koma ta zauna tare da cewa
ba dani ba, ai kuwa duk suka kyalkyace
da dariya.
*******************
Deeni kuwa yana can sai fargaba yake,
shi kam yama rasa me ke mai dadi
domin yasan jinkirinsa nada mummunan
hatsari indai har yazeed ya samu damar
tafiya da abban sa wancan gidan tabbas
akwai matsala, domin kuwa dodansu
za'a bawa shi, gashi yayiwa yan sandan
nan bayani amma ina sunki sauraran sa
wai kawai basu yarda dashi ba muna fiki
ne. Shigowar DPO ce ta dansa zuciyar sa
ta danyi sanyi........
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 39
Share ThCan yaji shigowar DPO hakan tasa ya
sami yar natsuwa, saida suka yiwa DPO
din bayani tukwanan ya nufi wajan
deeni, shi kuwa dama kamar shi yake
jira, yana isa deeni ya gaida shi ya amsa
tare da karewa deeni kallo, “kai gaskiya
wannan ba mugu bane” haka ya fada a
zuciyar sa tare da zuwa gab da deeni ya
tsuguna a cikin cell din, " kalle ni nan
ina so ka fada min gaskiya who ar u?
Deeni da hawaye tuni sun cika mar ido
ya fara bayani sunana zahradeen kaza
da kaza dai ya fada mai kaff labarin sa
har mutuwan halima, dama tserowar sa.
DPO ya yi wani ajiyar zuciya sannan
yayiwa deeni wani kalan kallo yace “ka
tabbata?” eh na tabbata, ban maka
karya ba, ok yanzu kace yazeed ya
bayar da mahaifin sa? kwarai da gaske
kuma yallabai jinkirin mu ma ba
karamin hatsari bane ya kamata muje ka
tabbata da kanka.
Bai gardama ba yace a kunce deeni,
wani kurtun dan sanda ne yaje ya cire
mai ankwar dake sanye a hannunsa,
sannan DPO din ya dauki mutum 4 daga
cikin yaransa tare da shi da kuma deeni
suka hau mota kai tsaye suka nufi gidan
su haleema, shikam deeni godewa Allah
yake yayi da DPO nan ya fahimce shi, a
zuciyar sa da yana tunanin ko DPO in
mugune amma yanzu kam yaga sabanin
haka..
***************
Yazeeed kuwa yana fita daga falo ya
nufi gun da su abbansa suke a zaune, su
uku ne suna hira, da baban sa da kuma
wan babansa sai kuma baban aliyu wato
kawu. haka yaje cikin ladabi (kunsan
ance mai san kayan ka yafika dabara)
yaje ya sami abbansa yace dad na
shirya, “ok mu tafi kenan” a cewar
abban nasa, yauwa ai kuwa ina ganin
gwara kawai mu tafi mu duka tunda
kaga wadannan suma iyayan ka ne ya
nuna su kawu, lokaci daya yazeed ya
bata fuska yaji ana shirin bata mai shiri,
a’a dady kawai gwara dai mu tafi mu
biyun kasan mai gidan nawa bai cika san
hayaniya da yawa ba, abban haleema ne
ya kalle sa tare da yimai dakuwa uku
“nace wato mune zamu mai hayaniyan
ko, to dai mu nan duk iyayan kane kaji
na gaya maka” sunkuyar dakai kawai
yayi. Wayar alhaji sanusi ce tayi kara
ganin wanda yakira ne yace to ni ga ma
kira ya shigo wayana kuje kawai domin
wani abokin kasuwanci nane kuma zamu
dade muna waya, alhaji bashir ya tashi
yana murmushi to ai shikenan bari muje
yanzu zamu dawo insha Allah, suka nufi
motar yazeed ya hau sannan aka bude
musu gate suka fita.
****************
Can bangaran kuma isah ne shida aliyu a
zaune da yake gidan fadede ne kowa
harkan gaban sa yake yi, suma haka
zaune suke suna hira, nan aliyu yake
tambaya ko an zabawa anneesat miji ne,
isah kuwa yayi farin ciki da wannan
zancen domin kuwa yasan ba a banza
aliyun zai mai wannan tambayar ba. "a’a
ba wani tsayayye ko a can kauyen ma"
“gud” aliyu yace yayi shiru kuma “ko da
wani abune isah ya tambaya, a’a ba
komai kawai na tambaya ne, “hmm to
shikenan tunda kaki fada.
Jiniyar motar police suka ji a kofar gida
nan take DPO ya fito ya sako deeni a
gaba sukayi sallama suka shigo gidan
mai gadi kam da yaga police ne kuma ga
deeni a gabansa yayi mamaki sossai na
ganin deenin, haka shima kawu ya mike
yana kallan deeni. Maman deeni kuwa
suman tsaye tayi dan farin ciki na ganin
yaran nata, amina ce tayi kanta a kidime.
Ba tare da bata lokaci ba DPO yaje ya
bawa alhaji sanusi hannu suka gaisa
sannan yabawa kawu ma, deeni kuwa
idan sa a kan mahaifiyar sa yake wanda
yana gani ta zube.
Kwayar idansa ce ta kai ga masoyiyar sa
wato halima, al'amarin da yayi matukar
bashi mamaki kenan, shin wai wannan
halima tace ko dai idona ne yake min
gizo, saida ya sa hannu ya murza idon
dan ya tabbatar da hakan.
Alhaji da fatan dai kasan wannan yaran
a gagauce, kwarai kuwa wannan deeni
kenan shi muke ta faman nema ma a
halin yanzu, alhmdulilah inji DPO a
halin yanzu ba lokacin batawa ina
yazeed da kuma abbansa, yazeed ai
yanzu suka fita.
“Inalilahhi wa'ina ilaihi raji'un” su deeni
suka kama fadi ba'ayi wata-wata ba suka
juya tare da cewa alhaji ya biyo su
yanzu ba lokacin yi masa wani bayani.
Cikin sauri suka hau motar DPO……..
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 40
Innalilahhi wa'ina ilaihi ra'jiu, abinda ke
fitowa daga bakin su deeny kenan,
officer yace alhaji zamu iya tafiya yi
sauri biyo mu ba lokacin batawa, da
sauri alhaji yabi bayan su, wannan
karan ma DPO ne ke tuki deeni kuma na
nuna mar hanya.
Can sunyi nisa sun kusa fita daga gari
sai suka hangi motar yazeed sai uban
gudu yake ba saurarawa da DPO yayi
niyar suje su taresu amma deeni yace
kar ayi haka, gwara dai aje har gidan
nasu in yaso dama akwai yan sandanku
da aka hadani dasu biyu amma dayan
wato ogan su tuni an yankasa.
“innalillahi kawai DPO ya fada tare da
cewa Allah ya gafarta masa, a nan ne
alhaji ya dan fahimce su yake tambaya
su fada mai me ke faruwa ne.
"DPO ne yace yayi hakuri a yanzu ba
halin yin hakan, a hankali suke bin
bayan motar yazeed shi kam baima lura
da wata motar police ba da yake ya dan
basu tazara. Abbansa kuwa gani yayi
ana ta tafiya dashi har za'a bar cikin gari
a yanki daji amma ba'a zo ba, kai yazeed
wai ina ne nan zaka kaimu, dad ai mun
kusan karaso wa ba nisa. Can bayan sun
sake yin wata tafiya mai dan nisa daddy
ya kara tambaya domin guraran shi
baiga alamar gari bama, daddy nace ka
kwantar da hankalin ka mun kosa zuwa.
Kai bana san shirme wannan wace kalar
shiririta ce, tun minti 20 baya kace min
ankusa zuwa sai yanzu ka kara cewa an
kusa. Kaga ni bansaka dole ba in dama
karya kake min baka da wani uban gida
to gwara ka fada sannan ka juya mu
koma domin ni zaman motar nan ba
wani kaunarsa nake ba na gaji. Ganin
baban nasa zai kawo mar matsala ne
yasa shi fito da wata yar kwalba ya fesa
mai. Ba'afi sakan 30sec ba abban nasa
ya hau barci harda munshari.
Su kuwa su deeni a baya suke suna biye
da su, deeni ne yake bawa DPO shawara
a kan a karo ma'aikata in so samu ne har
sojoji ma a kirawo domin na tsorata da
kalan kartin gidan, DPO yace hmm deeni
ke nan zaka nuna mana aikin mune, a’a
yallabai ni kawai shawara na bada, kafin
deeni ya rufe baki ne suka hangi motan
yazeed can zata gangare daga kan titi ta
nufi wani daji.
Nan ne fa DPO ya fara gaskata maganar
deeni nan take kuwa yasa a kira babban
office dinsu dake cikin garin kano ya
bayyana musu abinda ke faruwa tare da
fada musu address din gun da suke a
yanzu, saida suka bari yazeed ya mika
tukun suma suka gangaro motar tasu
suka bi bayan sa, shi kam duk abinda
ake bai ma san akwai mota na biye da
shi ba, abbansa kuwa nan ya kwanta ya
dinga barci na fitar hankali..
Bangaran maman deeni kuwa da aka
dauke ta aka kaita daki bayan tafiyan su
deeni kadan ta farfado ba abinda take
kira sai deeni-deeni ashe dama kana
raye ina ka tafi ka barni, duk wanda ya
ganta a wannan halin tilas ya tausaya
mata. Maryam ce ta ruko hannunta itama
hawaye take, itama sai lokacin ta
fahimci ashe yaya deeni baya gida boye
musu ne kawai akayi, mama kiyi hakuri
sunje su dawo tabbas deeni ki ne, nan
dai suka shiga lallashin ta. Haleema
kuwa wani farin ciki take na ganin
sahibin nata, hakan yasa ta tashi ta tafi
dakinta ta fada kan gado sai wani kukan
dadi take.
Aliyu da kawu kuwa duk hankalin sune
ya tashi sun rasa abunyi, ba'a musu
bayanin abinda ke faruwa ba.
*********** A can Kauye kuwa
“malam nifa ina jin kamar ba lafiya fa
ace har yanzu su anne basu dawo ba”,
“haba ke kuwa zuwaira me yasa kin cika
garaje ne, kuma ke da zaki dinga musu
addu'a, ai addu'a zaki yi ba ki tsaya ki
dinga zarge-zarge ba kinsan dai isah
yaro ne mai natsuwa bazaiyi abinda zai
saka mu a damuwa ko ya bata mana rai,
ni banyi tunanin zai kwana a can bama
to amma kika sani ko lokacin da sukaje
dare yayi ne kuma iyayan yarinyar suce
sai sun tsaya sun kwana.” to allah dai
yasa a dace kuma Allah ya kare mana su,
ameen kinga da tun farko ma haka kika
ce, to ai malam abin ne da ban tsoro
yanzu fa kaga karfe 10 da wani abu
amma yaran nan basu dawo ba, ki
kwantar da hankalin ki zasu dawo
isha'allahu ya fada lokacin da yake
mikewa, to ni zan fita kuma sai na dawo
zan biya wajan kaka daga nan in bata
sako domin kinga jiya an barta ita kadai
a gida, to malam Allah yasa a dace a
gayar min da kakar, to zata ji
isha'allahu...
**************
Yazeed na gaba suna binsa a baya can
da suka hangi gidan kuma suka lura nan
ya dosa sai suka kara gudu wato dan su
isko sa amma ina tuni ya riga ya karasa
domin ya musu nisa, a guje suka karasa
tun kafin motar ta tsaya yan sanda suka
fito kowa da bindiga a hannunsa suka
nufi gidan, nan deeni kuwa ya shiga
gayawa abban halima abunda ke
faruwa...............
Abba yayi mamaki sosai ya jinjina kai
zuciyarsa cike da tunanin irin wannan
yaro wato yazeed duk biyayar da yake
wa abban nasa, kenan dama duk kudin
da yake da su ta hanyar da ya tara su
kenan, banyi tunanin yazeed zai iya
yiwa ‘yaya haka ba, ban ma taba tunanin
yazeed zai iya kashe ko kwaro ba balle
ma ace wai mutu. “Abba to ai shine yayi
yunkurin kashe su haleema ma da
bakinsa naji yana fada lokacin da nake a
tsare a gidan” inji deeni, “Ya allah”
abban halleema ya fada tare da dafe
kansa da yaji yana irin wata juyawa,
dama yazeed fadan da suke da halima ba
iya nan ya tsayaba, yanzu ita daya tal da
nake da ita yayi niyar hallaka min, kai!!
amma da ya cuce mu gaskiya, baza mu
taba yafe wa yazeed abinda ya aikata
mana ba, Allah ya isa tsakanin mu da kai
yazeed.
Direct gate din gidan suka nufa cikin
irin sallan su na ma'aikata wanda suka
san aikin su bibiyu suka kasu inda shi
kuma DPO ya bi bangare daya, a hankali
suka tura gate din, guda daya ne ya fara
kutsa kai can ya hangi motar amma ba
kowa a cikin ta, nan ya daga wa na waje
hannu alamun su shigo bayan ya leka ko
ina baiga kowa ba, haka suka shiga a
hankali suke tafiya irin tasu ta ma'aikata
, wani daga cikin sune ya tura dakin, sa
kafarsa keda wuya sai sukaji anyi harbi
ba dan yayi gaggawar dukewa ba da sai
ta same shi da sauri yayo baya, sunyi
mamaki matuka ta yanda akayi yazeed
ya san da zuwan su shin dama ya gansu
ne ko kuwa
BAYA.......
Yazeed tunda yaga abbansa ya fara
barci ya fara tukinsa a hankali kwance,
can ya lura da motar police amma kawai
sai ya basar a cewarsa ai shi ba wani
laifi yayi ba me ruwansa da su, kuma ma
dan yaga tabbas din hakan sai ya dinka
rage sauri domin wai suzo su wuce, can
nesa da shi suke abun mamaki kuma duk
sanda ya rage gudu suma sai yaga sun
rage haka dai ake ta tafiya, ana cikin
hakan ne yaji wayarsa na kara yana
dubawa yaga dad wato wancan dad din
nasa matsafinan yake fadamar cewa
daya daga cikin wa yanda muka kamafa
ya gudu, yazeed yace garin ya bayan ba
wanda ya taba guduwa daga cikin gidan
nan ya haka ta faru, dad din yake gaya
masa cewa ko ka manta ne sai wanda
yaci abincin gidan ne bazai iya fita ba to
yaran taurin kai ne da shi ba yanda
bamuyi da shi ba a kan yaci amma yaki,
ok yanzu miye abunyi domin ga wata
motar police nan ina kyautata zatan
kuma ni suke bi to amma ni bansa ya
akayi ba domin ni kam ban karya dokan
titi ba tun tahowata, ok kadai kara kula
kuma ka lura sosai yanzu kuna tare da
dad din naka? tsohon ya tamabya, eh
muna tare gashi nan ma wallah saida na
sa mar hodar barci tukuna domin naga
ya fara ganowa, ohhh saboda me kasa
mar ai da baka sa mai ba domin kasan
dokar gunki mu bazai karba kyautan nan
ba ko kuma zai raina ne anma da ka
kawo shi a hk kasan fa muna da kartai
ko da karfi ne da sai mu turasa ga ogan.
srry dad ai ina tunanin ma kafin in
karaso ya tashi domin bamai karfi bace
sosai. ok sai kazo be carefull " ok dad.
Yazeed bai tabbatar da su deeni shi suke
bi ba saida ya shiga dajin nan, can yayi
nisa ya hango su suma sun biyo sa
lokacin da har zai waske yayi wani gun
kuma sai ya fasa ya sake kiran dad nasa
ya sanar da shi cewa police din shifa
suke bi, dad yace ba damuwa zasu
shirya kafin karaso warsa kawai yazo ba
damuwa, haka kuwa yaje ya shiga gidan
ya faka motarsa sannan ya kira wasu
suka taimaka masa aka dauki abbansa da
yake faman barci kamar na mutuwa aka
sashi daga ciki.
Tuni karti gidan kowa yayi shiri tare da
mugayan bindigun su a hannu, amma
suna ciki, wato a falo ba su fito ba
saboda tsaro, can su kuwa yazeed da
ogan tsafin sa kokari kawai suke na su
tada abbannasa wato alhaji bashir
domin su bawa gunki sa domin kar
lokacin ya kure, dan idan lokaci ya kure
basu bawa dodan nan abinda yake
bukata ba duk sai sun mutu, a wannan
ranar ba wanda zai tsira, shi yasa ma
basa wasa da du umarnin da ya basu,
nan dai suke ta iya kokarin su amma ina
yaki ya farka, sun kwara mar ruwa sunyi
yaki ya farka balle su jefa sa cikin dakin
dodan, suna cikin hakan ne suka ji anyi
harbi hakan ya dada tabbatar musu da
cewa yan sandan ne suka karaso, nan
suka kara azama na tashin alhaji bashir
daga baccin.
CI GABAN LBR...
Su DPO kam da sukaga haka komawa
sukayi da baya suna tunanin taya zasu
jewa wannan mutanan, gasu su biyar ne,
kawai hakan tasa ya sake kiran lambar
shugaban su a kan suna bukatar
taimakon gaggawa. deeni da sirikinsa da
aka bari a cikin mota ba abinda suke sai
addu'ar Allah ya fito musu da alhaji
basher lafiya ba kamar alhaji sanusi
yanda ya damu shi kam kamar ma ya
shiga da kansa dan cetan dan uwan nasa.
Su DPO kam jinkirtawa sukayi anan
suna tunanin wane tsari zasuyi dan shiga
gidan nan, saidai fa kuma mu biyar ne
gashi bamu san ko su nawa bane a ciki
sannan bamu san yanayin makaman su
ba dole dai mu jira, wani police ne daga
ciki yake cewa oga baka tunanin zasu
iya cutar da alhaji kuwa idan mukayi
jinkira, to yanzu ya kake tunanin
zamuyi kasan fa cewa duk wanda ya
shiga ciki sunan sa shekakke domin
kaga fa yanda akayi harbi, karan
bindigar ma na daban ne ya kamata mu
kula.
Al'amarin baccin abban yazeed fa zuwa
yanzu ya fara basu haushi, to shi wai
wane irin maganin bacci ne wannan
domin sunyi yan dubarun su na ya tashi
amma ina har ruwa mai sanyi suka dinga
kwarara mai amma ko motsi yakiyi
hakan yasa suka shiga yimai allurai
masu kashe wannan ta barcin amma ina
shiru yaki ya farka hakan ya fusata
wannan tshon shi isa yata dura masa
allurai iri-iri ba sassauci, su abinda ba
su sani ba tuni ya suma domin sinadaran
da suka hada mai sun yi yawa. Yazeed
kam tashi yayi ya jigina kai jikin bango
bakin ciki ya cika shi, kamar ya karasa
kashe abban nasa yake ji sai dai ba halin
yin haka, dole suka kyale sa suka nema
gu suka zauna a cewar su saiya fardado.
Su DPO ne hade da sauran yaransa sun
tsaya sai zurga zurga suke domin su rasa
abunyi, haka shima abban haleema
addu'a kawai yake shi baima iya
daurewa ba saida ya shigo gidan ya
tambaya wane hali ake ciki yanzu, shi
duk a firgice yake kar a hallaka mar dan
uwa wanda shine ya rage mai dan uwa
na jini a duniya, aka sanar dashi cewa
ya kwantar da hankalin sa ba abinda zai
faru amma yanzu akwai ma'aikata da aka
turo mana da su sun kusan karasowa,
sannan DPO yace dashi ya koma mota
domin bamu san irin shirinsu dinsu ba.
Suna cikin maganar ne sai sukaji karan
motoci hakan ya tabbatar musu cewa
ma'ikatan ne suka karaso, gabaki daya
sukayi waje, sojoji ne da police cikin
shirin yaki. Suka fara dira daga saman
motar tun kafin a tsaya nan take duk
suka zazagaye gidan inda su kuma
sojojin da zasu kai kimanin 12 suka
nufi cikin gidan, saida DPO ya musu
bayani tukunna suka tsaya suna tunanin
yanda zasu bullowa al'amarin, ciki kuwa
karti ne sama da 50 ko wanne rike da
mahaukaciyar bindiga ya saiti kofa,
lallai kam duk wanda yayi gangancin
shigowa dakin nan zai zama sheqaqqe
domin duk a lallabe suke a cikin dakin.
Umarni aka bawa mutum 3 su shiga,
suna shiga suka ga lokaci daya mutun
sama da goma sun fito kafin suyi wani
yunkuri tuni an hallaka su duk da rigar
harsashin dake jikin su, tabbas suma
kartin nan ba'a banza suke ba sunyi
training mai kyau.
Suna waje sukaji karan fitar harsashin
can kuma sai sukaji shiru ko motsi basu
kara ji ba, hakan yasa aka kara umartar
mutum biyu da su shiga, ba gardama
kuwa suma suka kutsa kai, akwance
suka is iske abokan aikin nasu, wannan
yasa sukayo baya saidai a lokacin ne
kuma sukaji kartin nan sun fara
harbinsu, nan dai suma suka fara
kokarin mayarda martani hade da
gocewa, sun ci nasarar harbin mutum
daya daga cikin kartan. A tsiyace suka
fito da gudu nan suke sanarwa da
shugaban nasu irin shirin mutanan, ogan
nasu yayi ajiyan nunfashi yana tunanin
ta wace hanya kuma za'a shiga gidan
nan..
DPO ne ya kawo shawara cewa hanya
biyu ne kawai dole a turo mana da
kartafila ko kuma tanka domin gidan
nan saidai a shige sa ta hanyar rusawa
haka ne kawai mafita, no ba sai anyi
haka ba inada abinyi.....
***************
Maman deeni kam tuni an rarrasheta ta
hakura ta dawo hayyacin ta sai dada
godewa Allah take yi na bayyana mata
duk ya'yan' ta bayan da har tama hakura
da su kaddara kenan. Maryam kuwa
saida taga hankalin umman nasu ya
kwanta tukun ta fito domin tana kewar
ganin isah tare da yaya ali ta gansu
zaune sai hira suke. Suna ganin ta suka
fara tambaya ya jikin umma, da fara'arta
ta basu amsa umma kam jiki yayi sauki,
ya aliyu ashe kuna nan, eh wallahi
maryam muna nan muna dan hutawa
bakwan naku ne ya takura a kan wai shi
tafiya zaiyi. Maryam kuwa bata fuska
tayi jin ance wai ya isah shirin tafiya
yake, to ya zaimin haka saida ya sace
min zuciya tunanin sa ya hanani sukuni
zai tafi ya barni to in ya tafi ma yaushe
zai dawo, maryam data sunkuyar dakai
tana ta zancen zuci. Ya ali yace yadai
naga kin dan bata rai dan ance zai tafi
ko dai bakwan sirikin mune ya fada
cikin tsokana, dago kai tayi ta kakaro
murmushi kai ya aliyu ka cika zolaya ni
ina ruwana da shi ya tashi yata tafiya
mana idan har zai bar mana annisat din
mu, isah da baice komai ba har a lokacin
kallanta kawai yakeyi yace “ok haka
kika ce ko to ai shikenan indai anne ce
gata nan ai sai kucinye an bar muku”, ya
kalli ya aliyu lokacin da ya mike tashi
ka rakani in hau mota mana tunda kaga
dai korar mu ake a garin naku, “aa ba'ayi
haka ba gaskiya mu kam mun isa mu
kori sirikin mu ai bamu isa ba” aliyu ya
fada yana dariya. Maryam kuwa ganin
aliyu ya gano komai yasa ta rugawa ciki
cike da kunya tana dariya...
“Ohh kace kazo zaka dauke mana
kanwarmu ko” aliyu yake zolayar isah,
ai wannan abun baza mu yarda ba kuwa
sai dai ayi chanje, isah murmushi kawai
yayi baice komai ba amma kamar ya so
ya gane wani abu a cikin zancen aliyu
haka shima aliyu yaso yayi mai magana
domin ya tabbatar mai da cewa shi fa
yana san kanwarsa amma sai yayi shiru,
baiji dadin shirun ba.
*****************
Shugaban sojojin nan kuwa wasu ya
aika mota domin su kwaso taigas.....
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 43
Suna isa asibiti aka yi saurin karban
abban yazeed, akayi emergency da shi
domin bashi taimakon gagawa, abba da
deeni kasa zaune sukayi tsayuwar ma
gagara tayi sai zirga zirga da suka hau
yi. A can kuma cikin gidan alhaji tsit
kake ji ba wani mai kuzari a cikin su
domin alhaji sanusi ya kira ya shaida
musu halin da ake ciki shi yasa duk suka
damu wasu na kuka wasu na jimami,
hajiya saratu kam kuka take yi sosai
bata taba tunanin wai danta zai iya
kashe ko kaza ba balle mutum, uwa uba
ma wai yau abbansa zai bayar, cike take
da takaici iri iri. Su haleema kuwa dake
sun san komai dama basu wani ji
mamaki ba, annee kuwa lokacin ta
tabbatar da labari da suka bata gaskiya
ne, haka dai gidan ya kasance har
yamma shiru kake ji ba wani mai
walwala a ciki.
Su abba kuwa suna asibiti jikin alhaji
yayi sauki sosai domin sun hadu da
kwararun likitoci, tuni suka magance
matsalar. Shidai kawai tsintar kansa yayi
a gadan asibiti a kwance gashi baiji
wani gu a jikin sa na mai ko alamun
ciwo ba, hakan yasa da abban haleema
suka shigo ya fara aika musu da
tambayoyin cewa wai me ke faruwa da
shi, me ya kawo shi hospital ina yazeed
nan suka shiga kwantar mai da hankali a
kan ya natsu bayada lfy yana bukatar
hutu, amna shi ina shifa lfy sa lau yake
gaya musu, lokacin ne wani likita ya
shigo hannun sa dauke da wasu takardu,
nan yake sanar musu cewa an sallame sa
zasu iya tafiya dama ba wani abu ke
damunsa ba kawai alluran da aka mar ne
abun ya wuce ka'ida, nan dai sukayi duk
abinda ya dace suka taho gida, duk
abinda akeyi DPO na tare da su...
Bangaran su yazeed kuwa ranar sunsha
azaba iri iri wacce ma basu taba tunanin
kalarta ba domin sojojin nan kalan
abinda suke musu sun gwammaci
mutuwa ma a kan haka. Lokaci daya duk
aka canza musu Kamanni, gaba daya ba
zaka iya gane yazeed ba, haka suka sako
shi a mota suka nufo gida da shi.
Su abba kuwa a babban falo gida suka
hadu, DPO ya mike yake musu jawabi a
kan duk abinda yake faruwa tun daga
lokacin da suka kama deeni har zuwa
yanzu. Sannan deeni ya mike shima yayi
sallama, farinciki cike a ransa, nan ya
fara basu labarin duk abinda ya faru,
duk yan wajen saida suka tausayawa
deeni, mahaifiyar sa kuwa sai kuka take
tana dada tausayawa yaran nata, haka
itama haleema abin ya kasance. Nan
deeny yake fada musu duk abunda yaji
a bakin yazeed na cewa shine ya sa a
kashe su haleema da kuma kyautar
abbansa da yayi ga dodo. Alhaji yayi
mamaki sossai da jin wannan zance
wato yanzu dama yazeed duk tarbiyar da
muka mai a banza kenan ta tashi, dama
kudin da suke shigo mai yna fakewa da
kasuwanci ashe dama ta wannan hanyar
yake samun su, haka dai yaci gaba da
tunane tunane, nan shima isah ya mike
ya bayyana komai dangane da tsintar
halima da yayi haka kuma abin da deeni
ya fada shima daidai ya fade shi bai ko
saba ba. Nan dai kowa yaci gaba da bada
labarin sa duk aka cika da mamaki sai
dai har yanzu an rasa wane laifi ne su
haleeman suka wa yazeed har da ya
kudarci daukan fansa da ransu. Haleema
kam tsoro taji ya kara shigan ta, ta kasa
fadar gaskiya lokacin da aka tambaye ta
meye suka mai, maryam ce tayi bayanin
komai cewa dakinsa suka shiga alhalin
ya hana kuma suka dauko laptop dinsa
to anan ne suka gane cewa ba mutumin
kirki bane, taci gaba da cewa kafin mu
fito ya ritsemu a daki sannan ya mana
duka hade da kashedi karmu kuskura mu
bayyana idan ba haka ba kuma duk zai
hallaka mu shiyasa duk muka tsorata
muka ki fada.
Kowa ya cika da mamaki a gun, ba'a fi
minti uku ba sai ga yazeed sojoji sun
shigo da shi, kallo daya zaka masa ka
gane cewa ya lakadu, durkusar dashi
sukayi a gaban jama'a, a cewar su wai
suyi bankwana da shi. Maman sa kuka ta
shiga yi ganin halin da dan nata ke ciki
sabanin abban sa da yake jin wata
tsanarsa kamar yaje yasa bindiga ya
harbe shi a gun, jama'ar wajen kowa
yayi Allah wadai da halin yazeed, shima
yazeed sai a lokacin yake nadamar shiga
wannan kungiyar bayan bai rasa ci ba
bai rasa sha ba, kudi suna shigo mai ba
laifi amma san zuciya da san tara
makudan kudi sun kaishi ga halaka.
A lokacin duk wanda ya kalli yazeed zai
gane yana cikin nadama, ko bakayi
niyar tausaya mai ba sai ka tausaya mai,
cikin kuka da wata murya ciki ciki yake
cewa ku yafe min dan Allah ku yafe min
nasan na jefa rayuwarku ku duka cikin
wani hali amma sai yanzu nake cike da
nadama wanda nasan ko kun yafe min
ba lalai ne in sami rahamar Allah ba,
amma yafiyar kawai nake nema a gare
ku. Wajen tsit yayi, kowa ya tausaya wa
yazeed domin yayi nadama.
Halima ce ta fara kada baki tace ni dai
na yafe maka duk abinda kamin ya
yazeed, Allah ya yafe mana ga baki
daya, saida hawaye suka kwaranyo
mata, kowa yayi mamaki a gun shi kansa
baiyi tunanin halima ce zata fara yafe
masa ba, daga jin haka maryam itama ta
kada baki tace ta yafe duniya da lahira,
wannan ya faranta ran yazeed sossai.
Haka yasa kowa ya ta yafe masa, duk
kowa ya yafe har ummansa itama,
abbansa ne kawai yayi shiru bai ce uffan
ba.
Abba idan baka yafe min ba bansan
halin da zan kasance ba, bana so in tafi
ba tare da yafiyar ka ba, abba ni nasani
cewa tawa ta kare domin kuwa koda ace
basu kashe ni ba ni nasan cewa yau
bazan kwana ba domin ka'idar kungiyar
mu kenan, mun karya alkawari dan haka
bazai kyale ni ba duk wani dan kungiya
dole ne yau ya bakunci
lahira.......................
TAMBAYA IDAN KAINE ABBANSA
ZAKA YAFE KO KUWA?
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 45
Hakika yabawa abbansa matukar tausayi
baisan lokacin da idanunsa suka ciko
taff da kwalla ba, nan ya dinga tuna
abubuwan da yazeed yake musu na
alkhairi, wannan kawai sharrin shaidan
ne, “na yafe maka yazeed Allah ya yafe
maka” haka ya furta yayin da tuni
hawaye sun gangaro fuskarsa sanda
yake kallan yaran nasa cike da tausayi.
Cikin wata irin murya mai karkarwa
yake cewa na gode abbansa sannan ya
fashe da kuka a wajen ba wanda bai
tausayawa yazeed ba. Nan wani soja
yace kana da magana ko kuwa ka gama,
na gama yallabai yanzu abinda zance
shine ya kalli abbansa sannan yace a
kwashe kaf kayan dakin can ya nuna
dakinsa yace gaba daya a kona, haka ma
dakina na can abuja shima a kwashe
kayan kaf a kona, yana gama fadin haka
caf wasu sojoji biyu sukayi sama da shi
suka fara tafiya, yana kuka ake tafiya da
shi, haka itama mahaifiyar sa kuka take
sossai tana yiwa dan nata kallan karshe.
Gaba ki daya dai gidan haka ya wuni
ranar nan ko abincin kirki ba wani
wanda ya samu damar ci saidai
tattabawa.
Aliyu kam zaune yake shi kadai ya rasa
meke mai dadi shifa a gaskiya san anne
yake gashi ya kasa gaya mata karfa yayi
zurfin ciki, nan ya dafe kai yana tunanin
shi ya zaiyi ya bayyanawa wannan
yarinyar yana sonta domin kuwa idan ta
koma kauyan su baya tunanin zai sake
ganin ta, gashi yana ji yayan ta ya
takura shi gida yake so ya koma. Tashi
yayi da sauri ya nemo takarda da bairo
ya rubuta wasika, yar aikin gidan
yabawa ta kai mata sannan ya kwatanta
mata anne yace ta bata a sirrance kar ta
bari wani ya gani.
Deeni ma fa haka al'amarin shi duk
wannan al'amarin baya damunsa tun
dazu bayan sun hadu da maryam da
mamansa yaji wani fayau ba abinda ke
damunsa yanzu masoyiyarsa kawai yake
san gani saidai ya rasa ta hanyar da zai
kirawo ta domin su hadu da juna, itama
haka taji ba abinda take so yanzu sai
ganin deeninta cikin falo suke zazzaune
sun kunna tv amma ba wanda hankalinsa
ke kan tv kowa ta tasa yake yi. Halima
sai yan kifce kifce take hakan yasa
ummanta ta gano ta, tace uhm wato
gurinsa kike so kije shine kika kasa fada
ko to ai ni na ganoki tashi kije wa zai
hanaki ganin deeni. Fuska ta rufe ciki da
kunya tana murmushi ta yo waje bisa
mamaki a kan wani dan dakali ta tarar da
deeni inda dama sun saba haduwa a
gurin, nan fa aka sha hira irin ta masoya,
an dade ba'a hadu kuwa yana nuna kalan
damuwar da ya shiga dalilin rabuwa.
karfe 10 sukayi bankwana kowa yayi
bangaransa.
Isah kam yaso ya koma gida yau amma
ganin halin da gidan yake yasa ya
hakura amma yasan cewa iyayansa
bazasu ji dadi ba kawai dai yasan idan
ya fada musu abinda ya faru zasu yi mai
uziri, kwance yake yana wannan tunanin
a cikin dakin da suke shi da aliyu da
kuma deeni, sai yanzu yama tuna da ya
hardace lambar salmanu cikin hanzari
ya tashi aliyu yace ya ara masa waya,
shima aliyun bai yi barci ba tukun yana
nan sai tunanin sahibar sa yake, nan ya
miko masa wayar ya kira lambar
salmanu amma a kashe. haka ya hakura
yabawa aliyu wayarsa shima ya kwanta.
Anne kuwa har ta kwanta kuma sai ta
tuna da wasikan da aka kawo mata cikin
hanzari ta tashi ta dakko tazo ta tashi su
halima wai su karanta mata, “kai anne
wallahi bakya jin magana yanzu bazaki
barmu muyi barci ba mu hutawa ranmu”
inji maryam, sannu matar yaya kwanta
kiyi barci ni nama isa in hana aunty na
barci. Pillow din dake wajen ta dauka ta
wurga wa anne hade da cewa wannan
kanwar tawa bata jin magana, suka yi
dariya gaba daya. Anne ta mika wa
haleema takardar, karanta min wannan,
haleema ta karba takardar “mene
wannan?” lokacin da take warwarewa,
“kedai kawai ki karanta” hmm tace
sannan ta fara karantawa kamar haka.
(( Assalamu alaiki bayan gaisuwa mai
tarin yawa tare da fatan kin wuni cikin
koshin lafiya gimbiya aneesat, farar
mace alkyabbar mata, yar mutunci da
kima. Halima ce ta dan tsaya da karatun
ta kalli anne tana mata murmushi, ita ma
martani ta mayar mata, maryam ma haka
ta matsokurkusa dan jin waye ya aiko
wannan wasikar sannan halima taci gaba
da karanta musu, a hakikanin gaskiya na
fada kogin kaunarki tun kallan farko da
na miki nake, tunanin ni dake mun dace,
tarbiyarki da natsuwarki da sanin ya
kamatar ki sun mini aneesat. Saidai
bansan ko zan sami masauki wato gurbi
a zuciyarki ba, ki bani dama in nuna
miki so da kauna da kulawa, ina san ki
zama mallaki na uwar yayana, ki zamo
mai share min hawaye, karki sa su zubo
aneesat. Nasan zakiyi mamakin jin nine
na aiko da wannan wasika amna ta wani
bangaran ba abin mamaki bane domin
shi so baya buya kuma so makaho ne.
Daga karshe dai ina kuma jadada miki
so da kaunar da nake miki i love u
aneesat. Daga Aliyu zuwa gareki.... ina
jiran amsa daga gareki sai anjima...
Nan fa anne kunya duk ta cika, zolaya
dai ba irin wacce basu mata ba daga
baya suka natsu, maryam tace to yanzu
fada mana, kina san sa ko kuwa.
Haleema ce tasa hannu ta dan bigi
maryam tare da cewa ke ina ruwanki,
maryam tabe baki tayi sannan tace to
miye laifi na ai gwara a fada mana
domin musan matsayin mu, haka dai
sukaita surutan su ita kam anee bata sa
baki ba, bata ce musu ko uffan ba. Nan
suka gaji har suka kwanta bata basu
amsar eh ko a’a ba.
Washe gari tunda sassafe bayan anyi
breakfast wajen karfe 8 kowa ya taru a
katan falo kawu ake jira kawai ya
karaso................
Ayi min afuwa ban sama damar post ba
jiya da shekaran jiya ba
Shi kuwa deeni gaban sa ne yaci gaba da
faduwa wato kawun haleema kenan aka
bawa dodo, hawaye keta kwaranya a
idaniyar deeni, wai an kashe haleeman
shi da kuma kanwarshi shi maryam da
yake matukar ji da ita, bashida burin da
ya wuce ya farantawa ummansa da kuma
yar kanwarsa wato maryam tunda
babansu baya raye, wani xazzabi ne ya
rufe deeni.
Maryam ce zaune kan wani gado na kara
ta dafe kumatu wato tayi tagumi, tunanin
ummanta kawai take, wasu yan siriran
hawaye ne suka kwaranyo, haka
haleema ma da take kwance
kwakwalwarta sai juyawa take cike da
tunani iri iri tama rasa wanne zatayi shin
waye mai neman hallaka mu, shin wane
hali deeni na ke ciki, shin umma da abba
ya zasu ji na rashina bayan basa san yin
nesa dani ko kadan, idanun ta cike da
kwalla ta tashi zaune ganin maryam a
gefan gado ta zuba uban tagumi,
“maryam maryam” inji haleema tunanin
me kike. Tuni maryam ta dago tare da sa
zani tana goge hawayan fuskarta, nan
haleema ta fahimta cewa duk ashe daya
ne halin da suke ciki. Ta dafa kafadar ta
haba my sis ki saka dangana a zuciyar ki
mana mu barwa Allah komai shi zai yi
mana maganin wannan al'amari ba kuka
ne abunyi ba...
Aneesat ce ta shigo, ganin su a wannan
yanayi ta fahimta tunanin gida suke yi,
duk da sun so su boye wa anne amma
saida ta fahimta, “haba yan uwana, nan
fa kamar gidan ku ne ku kwantar da
hankalin ku, dama yanzu daga wajan
maman mu nake shawara muke yi yanda
za'a maida ku gida, ku kwantar da
hankalin ku”...
Tabbas sunji dadi sosai da jin kalaman
anne gaba daya suka ce “hmm anne
kenan haba ba komai amma gaskiya
muna so muga iyayan mu domin basu
san ko wane hali muke ciki ba, kinga in
sun gammu hankalin su zai kwanta.
Yaro ya shigo da salamar sa “anne wai
ana kiran maryam, bata tsaya ko jin
waye ba tace “je kace gata nan”, domin
anne tuni ta kyaro su wato tana lura da
abunda ke faruwa tsakanin maryam da
kuma isa. Ya zaki ce gani nan bayan
baki san kowa ke sallama ba, shin waima
cikin gari nan waya san ni da har zai
aiko kuma wai ace maryam tazo ma.
Anne tayi murmushi ai sai kije ki gano
mana. cikin zolaya haleema tace
“kanwar mu ah gaskiya kinzo kauyan
nan a sa'a kinga shikenan sai mu barki
anan”. Suka sa dariya gaba daya. Bari
inga ko waye tunda kun matsa ta ce,
anne ara min hijab dinki. Ya mata daidai
kuwa kamar dama nata ne..
A tsaye ta iske shi ya harde kafafu da
kara da ya rike a hannun hagu yana
wasa da shi, hannun daman kuma yasa
shi cikin aljihun wando.
“Assalamu alaika” ta fada, wani irin
sauti mai dadi yaji a zuciyarsa yace
dama haka muryar yarinyar nan take
ashe.
Amin wa'alaiki Salam warahmatul lahi
ta’alah wa barakatuhu: sanda ya cika
amsa sallamar cif cif.
Gefe daya ta samu ta tsaya nesa da shi
kadan, ita kam ta kasa dagowa da kanta
domin wannan ne karo na farko nata na
tsayawa da wani da namiji ..
Maryam kenan sarkin kunya shin ko dai
kema yar fulani ce kamar mu, amma ai
ke kunyar taki tayi yawa ma.
Murmushi kawai tayi domin ta gane
yaya Isah ne shi isa taki ma dago kanta
domin tsoran abinda take ji in ta hada
ido da shi wato faduwar gaba.
Ki daure ki dago kanki, ki kalle ni ya
fada yayin da ya dan kara matsowa
kadan kusa da ita.
A hankali ta dago kai “wow” dama haka
wannan bawan allah yake da kyau, ashe
duk ganin da nake mai zaije farauta ne,
amma duk da haka yana da kyau saidai
kayan da yasa sun kara fito da zallan
kyawun sa wanda haka yasa ta kafe shi
da ido shima dai abun ya daure mai kai
ta tsaya sai kallan sa take...
Um dama so nake in gaya miki……
Kuma sai yayi shiru, ka fada mana a
zuciyarta ta fadi hakan, gani tayi ya
kalle ta, tayi saurin sunkuyar da kai ashe
yaji abinda tace...
Maryam ba wani abu bane dama ina so
in gaya miki ina sonki, ina kaunar ki,
tunanin ki ya hanani sukuni ko ina naje
bana jindadi in ban ganki a gunba, idan
na rufe ido ke nake gani, nayi tunanin
cire haka a zuciyata sakama kwan ni dan
kauye ne ke yar birni ce kinga kuwa
auran mu bazai yiwu ba amma dai yanda
sanki ya addabi raina yasa ni dole in
gaya miki ko naji dan sauki...
Farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta hakika
taji dadin kala man sa, wannan ne na
farko da namiji ya taba cewa yana santa
abinda ko da wasa ba'a taba gaya mata
ba, kalmar so kenan yayin fadarta sai
bakin ka ya fara bari duk jarumtakar ka,
bama kamar karo na farko haka duk
macen da aka furtawa a take a waje sai
taji chanji, lalai so halitar Allah ne,
juyawa kawai tayi da niyar tafiya ita
duk kunya ta dabai baye ta..
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
KU KARANTA :- An kama wani Fasto
dumu-dumu yana yayyaga Qur`ani
yana konawa a jihar Kogi
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
Takwas dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 27
Share This:
Batun yazeed kuwa da aka tafi dashi
dake dare yayi cikin wani daki aka saka
shi wanda ake saka masu laifi da safe da
suka zo suka duba tarar da shi sukayi ya
mutu, bakin sa na zubar da wani abu
bakikkirin kamar an daka tawwada haka
kuma ya wani kun bura kamar zai fashe,
shugaban sojojin DPO ya kira ya
sanarwa da hakan cikin gaggawa ya nufi
gidan alhaji sanusi, ganin yanda gidan
ya cika da farin ciki da murna yasa bai
fada musu halin da ake ciki ba, suna
gaisawa ya juya zai koma nan alhaji ya
kira sa ya mai kyaututtuka, nan ya
fahimci su tuni sun ma manta da dan
nasu shi yasa ma bai fada musu abinda
ke faruwa ba dan karya tayar musu da
hankali.
Washe gari bayan isah yaje ya bayyana
wa iyayansa duk abinda ya faru, sannan
ya bayyana musu maganar auren sa da
kyaututtuka da abba ya mishi da ma
batun anne sannan kuma ya nemi su da
su koma birni tunda ba abinda suke yi a
kauyen har kaka zasu tafi. Iyayan isah
sun amince da zasu dawo birnin,
ummansa ce ma taki yarda daga baya
kuma da suka bata baki saita amince, a
gidan da abba ya basu suka sauka, gida
ne isasshe ba laifi ya isa suyi iya
rayuwarsu, nan suma suka gode wa
abba, bayan sunyi wanka sun huta ne
isah ya dauke su a mota da yake dama
ya iya da ita yaje dauko su ma a kauye,
yan kauyan sun taya shi murna sosai
suma, nan ya kaisu gidan alhaji ya
gabatar da su, anne tayi murna sossai
ganin mahaifiyar tata da kuma kaka, nan
isah yake bayyana wa abba cewa iyayan
nasa sun amince sun dawo nan domin
yanzu na kwaso kayan su ma mun dawo
nan, kowa yayi farin ciki sosai da jin
haka, nan aka tashi yaran wajen ya
koma sai iyayen aka cigaba da tattauna
maganar aure yaushe za'asa shi, kawu
yace tunda dai yara nasan junan su
kuma iyaye duk mun amince dan haka
ba sai an dauki wani tsawan lokaci ba
kawai asa auran nan sati daya kafin nan
kowa yayi abinda ya dace, kowa ya
amince da maganar kawu nan aka shiga
shirye-shiryen aure, amare kuwa sai
gyara ake musu.
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah
yaune sati ya cika kuma yau ta kama
asabar daurin aure, anyi taro sosai anyi
sha gul gula wanda lokaci bazai bada
damar bayyana muku irin abubuwan da
akayi a cikin wannan sati ba, anyi komai
anyi taro iya taro an daura aure amare
uku su duka ukun kaya kala daya suka
saka, ba abinda zai burgeka sai ma kaga
gidajen da abba ya basu a jere, fenti da
komai da tsare-tsaren gidajen duk kala
daya ne. Haka ko wacce kawayen ta
suka rakata gidan ta, gida dai ya kara
girma ya cika da farinciki zaman lafiya
suke su duka ukun suna shan soyyaya
abinsu.
ALHAMDULILLAH!!!!!
A nan wannan labarin yazo karshe ina
fatan masu karatun kun samu darussa da
nishadi a ciki.
Muna muku albishir da cewa a yanzu
haka akwai wani littafi da zamu fara
saka muku shi, kuma muna sa ran zaku
ji dadinsa sossai, Musamman ganin
yadda wannan littafin na namiji ne
kuma shine littafin sa na farko, shi
kuma wanda zamu fara kawo muku na
mace ne kuma ta dade tana rubutu.
Daga karshe muna godiya ta
musamman ga wadanda suka bamu
lokacinsu wajana binmu har muka
gama wannan littafin.
BISSALAM
0 comments:
Post a Comment