dalilin kiran ki ba komai bane
illa ina son na san ko ke
wacece, ba don komai ba sai
don mugun kama da kike yi da
ummi na, maganan ki, nd a lot
of things" cikin tashin hankali
ta dago fuskar ta, caraf suka
hada ido, dan dama ita din
yake kallo, sai da ta tattara
natsuwar ta, sannan ta fara
magana "ni kam ba kowa bace,
ba kuma komai bace, asali ma,
marainiya ce ni, ina zaune da
goggo na, wadda ta kasance
kanwar mahaifina, iyayena sun
rasu tun ina shekara 5 a
dunia" tana kai wa nan, taja
bakin ta tayi shiru. Shiru na
yan dakiku ya ratsa wurin,
sannan ya saki ajiyar zuciya,
yace "ehnn ina sauraren ki" ba
tare da ta kalle shi ba, tace
"shikenan ai" ya kura wa
kyakkaywar fuskar ta ido,
tabbas ya ga damuwa a tattare
da yarinyar, amma ya rasa
dalilin da yasa a lokaci daya
yaji ta shiga ran shi, ya rasa
dalilin da yasa yaji yana son ya
san wani abu dangane da
damuwar da ya gani bayyane a
saman fuskar ta. Ya dan gyara
zaman shi, sannan yace "a
matsayina na psychologist, na
karanci wani abu a tare da ke,
wanda baki son ki sanar dani"
ta dan firgita, sannan tace
"bakomai fa" ya shafi tarin
sumar da take saman kanshi,
sannan yace "alright then, zaki
iya tafia" bata kai ga mikewa
ba principal ya dawo office din,
a haka tayi musu sallama, tasa
kai ta fita ta bar office din.
Hally ta gani zaune a gefe ta
karasa kusa da ita, tace "muje
ko" ta mike suka jera,ta fara
tambayar "me ya faru ne
Deedo?" Ba tare da ta boye
mata komai ba, ta fada mata
abinda ya faru tsakanin ta da
wanda taji an kira da Dr.
NAWAP KHAMIS..
BA’A SHAN
ZUMA… 21, 22
& 23
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
A haka suka kawo layin su
Deedo, inda suka yi sallama
kowa ya kama gaban shi. Tana
shiga gidan da murnar ta,
sallama tayi, a lokacin goggo
tana kofar daki, ta dago ta
watsa mata wani kallo mai
tattare da tsana da tsangwama,
da sauri ta karasa gaban ta,
tana "sannu goggo" ta dago
fuskar ta a murtuke tace "uban
mi zanyi da sannunki? Shine
sai yanzu zaki dawo mun gidan
nan ko? Kina can kina yawon
naki na iskanci da kika saba"
tayi kasa da kanta, tace "kiyi
hakuri goggo, wlh a makaranta
ne aka tsaida mu" tayi kwafa,
sannan tace "uban miyye nan a
hannun ki?" Tace "kyautar da
aka bamu ce" goggo ta warce,
ta farka wrapping sheet din,
sannan ta fara fito da text
books da math set, da note
books da sabbin uniform gal,
da sauran tarkace dai na
students, ta kwashi uniform
din tare da text books ta watsa
mata, tace "wannan kadai zaki
samu shegiya, wannan sauran
kuma duk su shehu zan ba su"
ta tattara ta tura su bayan ta, ta
kara da cewar "wai ke nan a
wannan shegen kan naki har
wani kallon mai kokari suke
maki, tashi wuce ki bani wuri,
kin zura mun ido kamar na
mujiya, kuma ga kayana nan, ki
tattare su ki wanke tass" ta
kwashe yan kayan da ta bata,
ta shige daki, ita murna ma
take yi, dan bata yi zaton zata
samu wani abu daga cikin
kyautar da aka bata ba.
Dr. NAWAP KHAMIS, matashi
ne mai kimanin shekarun da
basu wuce 28 ba a dunia.
Dogo ne sosai dan har ya dan
rankwafa saboda tsabar
tsawon shi, yana da kirji mai
fadi wanda a kallo daya zaka
ga bayyanannun 6-packs din
shi. Yana da muscles a
damtsen hannun shi,
kasancewar shi masoyin gym
ne na bala'i, yana da doguwar
fuska wadda ke dauke da dara
daran idanu tare da dogon
hancin da ya dace da
kyawawan lips din shi. In fact,
Nawap namiji ne wanda ya
ansa sunan shi namiji, yayi
degree din shi na daya dana
biyu a jami'ar Bayero da ke
garin kano, inda daga bisani ya
wuce England inda ya hada
PhD din shi akan psychology.
Shine da na farko a wurin
mahaifiyar shi haj. Fatima
wadda yake kira da ummi,
mahaifin shi Alh. Khamis
shaharraren dan kasuwa ne a
garin kaduna, wanda Allah yai
mashi rasuwa shekara biyu da
suka gabata, kanwar shi kwaya
daya Hafsat wadda take aure a
garin Abuja. Yanzu haka yana
aiki da federal ministry of
education, wannan ne dalilin
da ya bashi damar zuwa
kauyen su Deedo, kasancewar
su masu inganta ilimin matasa
yan secondary skool.
BA'A
SHAN ZUMA… 2⃣2⃣
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tun ranan da Nawap ya bar
kauyen su Deedo bashi da abin
tunani wanda ya wuce ta,
babban tashin hankalin shi
shine damuwar da ya gani
shimfIda saman fuskar ta,
gashi ya rasa gane menene
ainahin dalilin damuwar ta a
matsayin ta na yarinyar da
duka duka bata wuce shekara
15 ba a dunia, idan zai iya
tunawa principal din su yace
suna 3rd term ne yanzu a ss2.
Babu abinda ke mashi yawo a
kan shi irin kalaman principal
na karshe da yace "Deedo ta
kasance yarinya hazika wadda
zan iya cewa babu kamar ta
kaf cikin makarantar nan, sai
dai kuma yarinya ce wadda
take bukatar taimako cikin
gaggawa!" Dam! Gaban shi ya
Kara bugawa, to wane irin
taimako ne take bukata? Shine
abinda bai tsaya ya samu
cikakken labari ba. Mikewa
yayi daga kan kujeran da yake
zaune, ya tattara laptop din
dake saman cinyan shi ya dora
kan center table, sannan ya
fara zagaya palon a hankali.
Tunani ya fara yi shin me yasa
ya damu da yarinyar bayan
kuma ya kan hadu da cases
sosai irin nata a yawancin
makarantun da suke zuwa, a
fili ya furta "nata is different! I
saw the sorrow in ha, she's
desperately in need of my
help!" Ya sa hannu ya ciro
wayan shi da ke ta faman
ringing cikin aljihu, ya zaro
wayan ya kaima screen din
kallo, lokaci daya yayi wurgi da
ita saman kujera har ta katse
bai daga ba. Aka sake kiran
wayan, a karo na biyu shima
kaman ba zai dauka ba, can
dai ya daga cikin muryar nan
tashi mai kwantar da hankali,
yace "Aysha ya akayi ne?" Ba
tare da mun jiyo ansar da aka
bashi ba, yace "I'm kinda busy
yanzu gaskia, May be I'll call
back later" bai jira ansar ta ba
ya katse wayar yaja tsaki, tare
da komawa kan kujeran ya
lumshe idon shi, Deedo ya
gani cikin kodaddun uniform
dinta, fuskar nan ta ta cikin
yanayi na damuwa da bukatar
tallafin gaggawa, firgit ya bude
idon, amma bai ganta ba,
hakan ya sa ya cika bakin shi
da iska sannan ya fitar, yace
"I'll come 4 yu Deedo nd I
promise I'll help yu" ya mike ya
shige bathroom ya sakan ma
kanshi shower…
Katon bahon ruwan ta, ta
doro a kai tana ta bunguza
sauri kasancewar maghriba ta
gabato, kayan jikin ta duk sun
jike sai rawar sanyi take yi,
kafar nan ta ta firi firi kaman
tayi birgima cikin kasa, shehu
ne tare da wasu yara suke
binta a baya suna mata daria,
bata ko damu da su ba, dan ta
san idan ta tsaya yau kashin ta
ya bushe wurin goggo. Hango
shi tayi rungume da hannayen
shi, ya zuba mata idanu kamar
mai nazarin wani abu a tattare
da ita. Kanshin turaren shi da
ta shako daga inda take shi ya
tabbatar mata da abin da take
tunani! Cikin jin kunyar yanayin
da take ciki tazo, ta raba ta
gefen shi zata wuce ba tare da
ta sake kallon inda yake ba,
bai tanka mata ba, ta shige
cikin gidan da saurin ta dan
har an kwalla kiran sallah.
Shehu ne ya shigo da sauri
yana kwala wa goggo kira, ta
fito daga daki zanin ta a
hannu, tace "Shehu na Allah,
yau kuma da waccen ka
shigo?" Yace "wani mai mota
ne wai a kira mai Deedo" ta
zaro ido tace "mai mota da
neman Deedo? Kai shehu ko
dai dijangala yace?" Yace "wlh
Deedo yace, har ma yace wai
wadda ta shigo yanzu" goggo
ta rafka salati tace "na shiga
ukku, ubanwa kuma kika jawo?
Wlh in masifa ce yau a kanki
zata kare, dan ni dai ina zaman
zama na baki isa ki jawo mun
bala'i ba" ta dafe kanta tace
"oh ni Batula! Wannan
tsintacciyar mage na neman
jefa ni cikin masifun ta" ta
damko kunnen ta, ta wurga ta,
tace "wuce kije ki san yadda
zakiyi da bala'in da kika
tattago, idan ma tafiya zasuyi
dake wlh ko kofar zaure bazan
je ba, tunda ban san sadda
kika je yawon iskancin ki ba
har kika jawo bala'in" Deedo
tasa kara, tace "wlh goggo
banje wani yawon iskanci ba,
wlh ban ja kowa ba" goggo ta
hankada ta, tace "ki wuce ki
fita wlh jar ki ja tsinannun su
shigo mun cikin gida, dan wlh
duk wanda ya shigo sai na
fasa mai kai da tabarya" Deedo
ta share yan hawayen ta, taja
lamusassun silifas dinta da
suka ji wahalar dunia ta bi
hanyar zauren zata fita, shehu
kuma ya sa ihu yace "bari muje
muga irin dukan da za a
nakadawa shegiya, dama su
tafi da ita mu huta" goggo tace
"ka tsaya daga bakin zaure dai,
dan kar su hada mun da dakai"
bai bi ta kanta ba ya juya da
gudu ya fita kofar gidan.
BA’A SHAN
ZUMA… 24, 25
& 26
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Koda ta fita baya kofar gidan,
sai dai motan shi kawai, har ta
juya zata koma ciki ta jiyo ana
kwala mata kira, waigowa tayi,
ta hango shi yana tahowa, da
alama daga masallaci ya fito.
Da sallama ya iso, ita kuma
tana tsaye tana matse kwallan
da suka taran mata, kallon ta
yake cike da tausayin rawar
sanyin da take yi, gata dai
yarinya karama amma alamun
damuwar da take tattare dasu
sun bayyana karara akan
fuskar ta, ba tare da yace
komai ba. Dukawa tayi har
kasa sannan tace "ina wuni" ya
ansa a taqaice, sannan yace
"kin gane ni kuwa?" Ta daga
kai alaman eh, ya gyara
tsayuwar shi, sannan yace "na
tambaye ki labarin ki, amma
baki fada mun komai, a yanzu
kam, ba sai kince dani komai
ba, domin yanayi da kike ciki
ya sanar dani irin matsalar da
kike fuskan ta a gidan nan" ta
dago jajayen idanun ta da suka
rine da kuka, tace "ni bana tare
da matsalan komai" kallon ta
yake yana nazarin yadda tayi
maganar, murmushi yayi, ya
juyar da kanshi ya ce "well,
tunda baza ki fada mun
matsalar ki ba, bara na shiga
gidan sai inji dalilin da yasa
kike daukan wannan katon
bahon na ruwa a kanki, a
matsayin ki na yarinya mai
karancin shekaru" ya sa kanshi
alamar zai shiga zauren, shehu
na ganin ya nufo inda yake ya
tashi ya runtuma da gudu cikin
gidan, itama tayi sauri tasha
gaban shi tace "kayi mun rai
dan Allah, ba dan ni ba, yau
muddin kaje ma goggo da
maganar nan wlh sai ta kusan
kashe ni" murmusawa yayi,
sannan yace "zaki fada man ko
ke wacece ko kuwa?" Ta
girgiza kanta, "zan fada maka"
ya ja da baya ya jingine jikin
kofan zauren, yace "ina
sauraren ki" ba tare da bata
lokaci ba Deedo ta warware
mashi komai, ta fada mashi
duk halin da take ciki a gidan
goggo, hatta da mutuwar mal.
Ilu bata boye ma Nawap ba, ji
yayi kafafun shi na neman
kasa daukar shi, bai taba
tunanin mutane marassa imani
irin goggo suna rayuwa ba har
yanzu a doron kasa, ya zata
irin su sun gama karewa tun
zamanin jahiliyya. Tausayin
yarinyar ya kara shigar shi, ga
wani irin kuka da take yi marar
sauti, kallon ta yake a matsayin
tilon kanwar shi Hafsat, har
yana imagining idan ita ce
wane irin mataki zai dauka.
Kallon ta yayi, yace "kukan nan
ya isa, ki shiga gida kinji, zan
karasa cikin bauchi na kwana,
zuwa gobe zan dawo in sha
Allah" ta mike jiki ba kwari ta
shige ciki, shi kuma ya shiga
motan shi yai mata key ya
kama gaban shi.
Tana shiga ta tarar goggo da
Hadiza da shehu sun jera sun
zuba ma kofar ido suna jiran
suga mei zai faru, damko ta
goggo tayi tace "uban wanene
wancan?" Deedo tasa kara tace
"wani ne" goggo tace "wani
wa?" Ta fara kame kame dan
bata san ya za tai ma goggo
bayani ba, ta daka mata tsawa
tace "baza ki fada ba?" Tace
"daga makarantan mu ne"
goggo tace "naga alamar yau
yan iskan ne a kanki, yanzu
zanyi maganin ki idan baza kiyi
magana ba" cikin tsoro da
fargaba ta fada ma goggo
yadda ta san Nawap, ta kara da
cewar "yazo garin ne shine ya
biyo ta nan" goggo ta sa salati,
tace "ke Deedo ki fita a ido na
wlh, yanzu ke yawon iskancin
naki ya kai har da yan birni
kike yi? Yau zaki gaya wa yan
garin ku" ta damki yarinyar nan
ta fara bugu, Hadiza ma ta
mike ta debo ruwa a randa ta
watsa mata, suka ci gaba da
jibgar ta, shehu kam sai tsalleh
yake yana jin dadi, dan duk
dunia ba abinda ya ke so irin
yaga goggo na kwalfar Deedo,
saida sukai mata liiis,sannan
suka shige daki suka barta a
wurin. Dakyar ta lallaba ta
shige dan akurkin dakin ta,
kuka take yi sosai, ita kanta
tausayin kanta take yi, wannan
azaba ta ishe ta, neman hanyar
da zata kubutar da kanta kawai
take yi, ta lallaba tayi alwala
tazo ta fara sallah ta gama, ta
jawo littafin ta Geography
tasha karatu sosai, abinka da
mai sharp brain, dandanan ta
kwashe komai da take bukata,
ga yunwa ta addabe ta, ga
kuma wani mugun bacci da
yake figan ta, nan inda take ta
dan shingida, kafin kace wani
abu tuni bacci yayi gaba da ita,
abin ka da ansha bauta da
rana an gaji.
Yau Allah ya taimaka ta kiran
sallar farko a kan kunnen ta
dan haka tayi zumbur ta mike,
tashin ta keda wuya, goggo ta
shigo da robar ruwan ta, tana
haska fitila ta ganta a tsaye,
tace "la'ananniya, da kar ki
tashi mana" tayi kwafa tace,
"kin wuce kin wanke kayan
fitsarin can na shehu ko sai
nasa kafa na hanbare ki?" Sum
sum Deedo ta fito tana rawar
sanyi, kayan fitsarin ta kwashe
ta wanke, sannan ta doro
alwala tazo ta gabatar da sallar
asuba, sannan ta dauki bahon
nan, ta wuce borehole.
Bayan ta dawo tayi duk wani
aiki da tasan nata ne, ta gama
ta jawo uniform dinta, ta saka
sannan ta fito ta karasa kofar
dakin goggo. Ita daya ce zaune
a bakin gado, dan su Hadiza
sun dade da tafia makaranta.
Tace "goggo zan tafi" ta watsa
mata harara tace "na rike miki
kafa ne? Ko wata tsiyar zan
miki ne? Eyee?" Ta girgiza
kanta, sannan ta mike ta fito
daga dakin ta nufi makarantar.
Tana isa har an fara exam,
malamin ya kalle ta kaman
wadda aka koro, yace "Firdausi
Kabeer" dam taji gaban ta ya
fadi, ta tsaya cak a inda take,
yace "mei sa tunda aka fara
exam kullun sai kinzo late?" Ta
rasa abin cewa, sai can ta tuna
da goggo ta fasa mata baki
jiya wurin dukan ta har ma ya
kunbura, tayi saurin cewa "I'm
sorry sir, na taho ne na fadi a
hanya saida na tsaya chemist
na ansa magani" ya kare mata
kallo, tabbas ga alama nan a
tattare da ita, dan haka ya bata
question paper yace ta wuce ta
zauna, ta ansa da sauri ta
wuce seat dinta ta zauna.
Nawap kasa bacci yayi a daren
jiya, yana tunanin ta ena zai
biyo ma mace mai mugun hali
da rashin imani irin goggo; shi
dai yayi alkawarin taimakon
yarinyar nan no matter what;
amma ya rasa ta wane hanya
zai bi dan ya kubutar da ita
daga hannun azzalumar matar
nan. Tunani ya fara yi ko court
zai mika ta, sai kuma wata
zuciyar tace "a matsayin ka na
wa? In kaje gaban alkali kace
me?" Yaja tsaki, ya watsar da
wannan tunanin can kuma
wata dabarar ta fado mashi,
murmushi ya saki wanda ya
kara mashi kwarjini, da sauri
ya canja akalar motar shi yabi
wani titi, ba tare da yasan ko
ina cikin garin Bauchi ba, haka
ya bi main road na cikin garin,
nan ya samu wani katon mall,
ya karasa yayi parking ya fito
ya shige ciki. Duk wani abu da
dan adam zai bukata akwai shi,
haka ya zage yayi kyakkyawan
shopping na dangin kayan
abinci masu uban yawa,
tarkacen man shafawa,
sabulun wanka dana wanki, ya
koma bangaren kayan sawa
nan ma ya kwasa son ran shi,
har da kayan yara maza ya
kwaso, akai mashi total kudi
wurin 150, 000, credit card din
shi ya ciro ya basu suka cire,
sannan aka kwashi kayan aka
sa mashi a pickup ta shopping
mall din, dan motar shi baza ta
iya daukar lodin ba, ya shiga
yana gaba masu motan na bin
shi har cikin garin Ningi.
A kofar gidan Hajia goggo
suka tsaya, ya kira wasu
almajirai suka taimaka ma
masu motan suka shiga da
kayan ciki. Goggo dake kofar
daki tana sakacen hakori taga
mutane da kaya niki niki, ta yi
zumbur ta mike tace "kai
malam daga ina wannan
kayan?" Wani cikin su yace
"wani ne yace mu shigo dasu
yana nan waje" tana tambayar
wanene amma bai bi ta kanta
ba, suka juya suka fita. Saida
aka gama shigo da kayan tsab,
sannan Nawap ya shigo ya
tsaya bakin zaure yayi sallama,
goggo data kagara taga wanda
ya kawo wannan kantin guda
(inji ta tace wannan ai kanti ne
guda ya kwaso) tayi saurin
cewa "shigo mana" ganin
tsayayyen namiji, jarumi,
matashi, dan boko, wanda ya ji
hutu, ya kuma ji bugun A.C,
mai asalin zati da kwar jini!
Yasa goggo tayi saurin ja da
baya kamar wadda tayi karya,
ta samu gefe ta rakube, bakin
ta na rawa tace "yaro daga
ena?" Yanayin da goggo ta
shiga ya bala'in bama Nawap
daria; haka dai ya gintse, yace
"bari mu gaisa mana goggo
ta"..
BA’A SHAN
ZUMA… 27, 28
& 29
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Goggo tana zara idanu ta mike
da sauri ta dauko sabuwar
tabarma daga daki ta shimfida
mashi, ya zauna, ya gaishe da
ita cikin ladabi, ta ansa bakin
ta na kyarma, tace "ni fa har
yanzu ban dau haske ba, daga
ina kazo ne samari?" Ya saki
lallausan murmushi, sannan
yace "Sunana Nawap, dan
asalin garin kaduna ne ni,
yanayin aiki na ne ya kawo ni
Bauchi state, daga nan kuma
aka turo ni wannan gari" goggo
tace "Ayyya, to wannan tulin
kayan fa na menene?" Ya kara
murmusawa, yace "naki ne Haj.
Goggo" goggo ta zaro ido ta
dafe kirji, tace "wannan uban
kaya haka? To wai kai a ena ka
sanni ma?" Nawap cikin
zuciyar shi daria kawai yake,
ya san hakon shi ya kusan
cimma ruwa kasancewar
yanayin da goggo ta shiga, ya
san dama baza ta rasa son
abin dunia ba. Yace "ina zaune
da mahaifiya ta, ina kuma da
kanwa kwaya daya, amma tayi
aure, to mu kan samu masu
aiki da dama, sai dai da yawan
su basu zama sai su gudu,
saboda aikin gidan yana da
yawa. To jiya sai naga wata
yarinya da katon baho na ruwa
ta shigo gidan nan, hakan ya
tabbatar mun da zata iya ko
wane irin aikin wahala, shi
yasa nace bara nazo naji ta
bakin ki, ko zaki taimaka ki
bani ita? Ke kuma ina turo miki
da kudin aikin nata a ko wane
karshen wata" goggo ta gyara
zaman dankwalin ta, tace "ba
dai wannan tambadaddiyar
yarinyar kake nufi ba?" Yace
"wa kenan?" Tace "Deedo
mana, tsintacciyar mage,
shegia mai mugun hali" har
cikin zuciyan Nawap baya jin
dadin zagin da goggo take ma
marainiyar yarinyar nan, haka
dai ya daure yace "ina ga ita
din ce, ban dai san sunan ta
ba" goggo ta dan matso da
kanta dab dashi, kamar wani
zaiji abinda zata ce, a hankali
tace "nawa zaka na biya na duk
wata idan na baka ita?" A
takaice, yace "naira dubu
hamsin" dan tsabar tsorata har
sai da goggo ta hantsila baya
daga kan yar kujerar tsugunnin
da take kai, tace "dubu
hansin?" Ya gintse dariyar shi
yace "ko sunyi kadan ne
goggo?" Tace "haba ina fa, ai
ban taba kama ko rabin su ba,
bari tsinanniyar tazo, ko zata
mutu sai ta bika, kuma ko
wahala zata kashe ta, kar ta
sake ta dawo mun gidan nan,
kai ni in ka tafi da ita ma ko
ganin gida kar ta sake tazo"
Nawap kallon ikon Allah kawai
yake, tare da tsantsarar rashin
imani na matar nan, ya
muskuta, yace "ena yarinyar
take ne?" Tace "ta tafi
makaranta, ai tana dawowa ba
abinda za a jira wucewa kawai
zakuyi, daman ba wata kwalwar
fahimtar karatun ne da ita ba,
haka nan dai take zuwa
makarantar" Nawap yace "bari
dai muji ta bakin ta ko goggo"
goggo tace "in dai ta bakin
wannan shegiyar zamu tsaya ji
ai ba yarda zata yi ta bika ba,
dan haka kawai ba sai an mata
wani bayani ba" Nawap wani
irin kallo mai tattare da tsana
yake watsa ma goggo, yanzu
shi inda ace ba manufar alkairi
gare shi akan yarinyar ba, da
haka zata dauke ta ta bashi, ba
tare da tunanin shi din ko
wanene ba. A zuciyar shi yayi
Allah wadaran hali irin na
wannan matar, ya kuma yi mata
addu'ar Allah ya sa ta
dandanin kuncin rayuwa koda
rabin wanda Deedo ta dandana
ne.
Sai da ya tattaro natsuwar shi,
sannan ya saki murmushin
yake, yace "to shikenan goggo,
bara na dan zaga cikin gari zan
dawo zuwa anjima" yasa hannu
a aljihu ya ciro bandir na yan
500 ya mika mata, goggo
hannu na bari, tayi saurin
warcewa, sai da ta adana su
cikin zanin ta, sannan tace
"bayan wannan kantin guda
daka kwaso, abin kuma har da
wahala" yana tsaye yana kallon
karfin hali da munafurci irin na
goggo, ya girgiza kanshi, yayi
murmushi, yace "wannan ai
kadan ne goggo, kar ki damu"
ta wangale bakin ta, tace "to
shikenan Nawab, sai ka dawo
din" yadda ta kira sunan nashi
yasa ya kasa gintse dariyar
shi, dan haka ya dan dara,
sannan ya wuce ya fita.
Yana fita skool din su Deedo
ya zarce, direct office din
principal ya nufa, bayan sun
gaisa yake tambayar "Dr. Kaine
a garin namu" Nawap ya shafi
kyakkyawan sajen shi da ya
kwanta luf saman fuskar shi,
yace "wlh fa, ya students?"
Yace "Lafia fa" nan suka cigaba
da fira, inda yawancin firan
nasu duk akan tabarbarewar
ilimin yaran karkara ne, nan ya
samu labarin su Deedo suna
zana waec ne, wadda zasu
gama sati mai zuwa, sannan
kuma su fara neco. A haka yai
ma principal din sallama,
sannan ya fito.
A kofar gidan goggo ya tarar
da Deedo tare da hally, tana
mika mata magani da ta ciro
daga jakar ta, tace "wlh Deedo
ki natsu, yanzu kinyi girman da
za ace kin wuce duka, har ana
kumbura miki baki, wlh idan
nice ke tuni zan ture goggon
gefe, sai dai ko mai zai faru ya
faru" Deedo ta murmusa tace
"hally ke dai ki gode ma Allah
da yasa iyayen ki suna raye,
amma baki san menene
maraici ba, ni ina naga karfin
halin da zan iya taba koda
yatsan goggo ballantana kuma
in samu halin ture ta, ke dai ki
taya ni da addu'a kawai har
Allah ya kawo karshen zamana
a gidan nan" hally tace "Allah
ya taimaka, bara na wuce" suka
juyo a tare, nan suka ga Nawap
jingine jikin mota, fuskan ba
yabo ba fallasa, duk suka duka
suka gaishe shi, sannan suka
yi gaba ta dan taka ma hally,
nan take fada mata yadda suka
yi jiya, hally tace "Allah yasa ya
zamo silar fitar ki daga kangin
da kike ciki" Deedo tace
"kaman ya? Ke ni ko ganin shi
bana son yi wlh" hally tace "Ke
dai yanzu je kiji da wacce yazo
tukunna" sukai sallama ta wuce
ita kuma ta dawo, amma bata
ganshi ba dan haka tayi saurin
shigewa cikin gidan, nan ta jiyo
muryar goggo tana cewa "kaga
gantalalliyar yarinyar nan har
yanzu bata iso ba" jiki ba kwari
tayi sallama cikin gidan ta
shiga, ganin shi tayi zaune
saman tabarma, dan da nan ta
shiga tashin hankali, tasan yau
karyar ta ta kare, Allah ne
kawai zai raba ta da goggo da
bala'in ta..
Dakyar ta karaso cikin gidan, a
dai dai lokacin kuma goggo ta
fito daga daki inda suke shiga
da kayan da Nawap ya kawo
masu. Harara ta watsa mata,
sannan tace "ke dai Allah
wadaran hali irin naki, shegiyar
'ya gantalalliya, ina kika je kika
zauna kuma" ta karaso gaban
ta, ta duka tace "kiyi hakuri
goggo wlh ban tsaya ko ina ba"
tasa kafa ta wurgar da ita, tace
"daga yau dai gantalin ki ya
kare, naga gidan uban da zaki
kara yawon iskancin ki, dubi
nan" ta nuna mata Nawap da
yake zaune yana kallon goggo,
Deedo ta dago ta kalle shi,
sannan goggo taci gaba "to da
shi zaku tafi, zaki je can kina
masu aikatau, sauran kuma inji
abinda ba shikenan ba, wlh na
lahira sai ya fiki jin dadi" wani
irin kuka ta saki, duk wanda ya
kalle ta sai ya tausaya mata,
kafar goggo ta rike tana "kiyi
mun rai goggo, ki taimaki
rayuwa ta dan Allah, wlh ban
san shi ba, bazan bi shi ba,
kila ma dan yankan kai ne, wlh
zan yi miki ko mai kike so,
amma kiyi mun rai kada ki
kaini wurin yan yankan kai"
saida goggo ta tattaro karfin ta
gaba daya, sannan ta wancakar
da Deedo, har saida ta bige da
dogon karfe na baranda,
sannan tace "kinsan Allah ko
gawar ki ce sai bawan Allahn
nan ya tafi da ita, kinji dai na
rantse, baki isa ki sani kaffara
ba kuma" tayi hanyar dakin
Deedo da niyyar watso mata
tsummokaran ta, Nawap dake
gefe yana kallon abinda ke
faruwa, cikin kunan zuciya
wanda bai bari goggo ta gane
ba, yace "ehnmm goggo" tayi
saurin dawowa ta duka gaban
shi tace "ya akayi ne Nawabu?"
Saida yaja dogon numfashi,
sannan ya tuna principal din
su Deedo ya fada mashi suna
exams, sannan ya tuno da
ummin shi, at least ya kamata
ya sanar da ita kafin ya kai
mata Deedo, wata dabara ta
fado mashi, ya dan gyara
zama, sannan yace "naga
alamar yarinyar nan tana da
yan matsaloli, ga kuma yanayin
jikin ta ba wani gyaran kirki,
dan haka ina son a aje mun ita
a nan zuwa nan da kamar wata
guda, amma ina so duk wata
wahala da take yi a da ta daina
yin ta, ba don komai ba sai
don idan na kaita can ta samu
karfin yin aiyukan da muke
dasu, irin dibar ruwan nan da
sauran su, in yaso ko kofar
gida kada a rinka barin ta tana
fita, makaranta kawai na
amince taje, wannan shima
wani aiki ne, wanda zan biya
kudin shi yanzu yanzun nan"
goggo da taji maganar kudi,
tayi sauri tace "to ai shikenan
tunda dai kai ka bukaci hakan,
amma dai naso ka tafi da ita
yau din" yace "bakomai, zan
dawo nan da wata 1" yasa
hannun shi aljihu ya kara
kwaso wasu kudin ya mika wa
goggo, sannan ya mike yayi
hanyar zaure, sai da ya kare
ma Deedo kallo tsab, sannan
ya sa kai ya wuce abin shi.
Shehu ne ya rugo daga daki da
sabbin kaya jikin shi, sai da
yasa kafa ya hanbari Deedo
sannan yabi Nawap har kofar
gida yana cewa "Allah ya
kiyaye hanya" Nawap wanda
yake jin haushin su shi da
uwar su, ko kallon shi bai ba,
ya shige motar shi ya tada.
BA’A SHAN
ZUMA… 30, 31&
32
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Acikin Gida kuwa goggo takalli
deedo sannan tace "kinji
abunda yace!, tsintacciyar
mage wacce bata gaji arziki ba,
albarkacinki daya karna miki
dukan tsiya kisamu illa yafasa
daukanki, donhaka kije kina
hutawa," takamo kunnenta
sannan tace "saura kuma da
gigin wasa kice bazakijeba,
kokuma inkinje su koroki, wlh
saina hallakaki" deedo dai
shiru tayi, tana ganin goggo ta
shige daki, itama ta mike ta
shige akurkin ta, ta cire
uniform dinta sannan ta fito
tayi alwala ta koma ciki.
Zuwan nawap gidan goggo ba
karamin alkhairi bane yajawo a
rayuwar kuncin da Deedo take
ciki, domin kuwa tadenaa
aiki,harta kai ko tsintsiya ta
dauka, goggo ta fara zagin ta
tana cewa zata janyo musu
asaran arziki, hakan yabata
daman yin karatu, hatta a
makaranta sukansu sun lura da
zuwa dawuri datakeyi, hally har
zolayen ta takeyi, tana cewa "
Allah ya yi abin, inji mafadin
aure. kekuma aidole kidawo
shalele, kudi saan kowa,
mutuncin kowa, mu dai muna
godewa Allah daya taimakemu
yakawo karshen wahala duk da
bauta zakijeyi" itadai Deedo ta
kan rasa abin cewa, duk da
tana son ta rabu da azabar
goggo, amma kuma bata son
bin mutumen da bata san daga
ina yake ba.
* **Nawap kuwa koda ya fito
gidan goggo, gudu ya rinka yi
sosai, har ya isa garin kaduna.
Ta Alkali road ya bi, sannan ya
shiga cikin Isah Kaita road,
gida mai No. 55 ya danna horn
mai gadin cikin uniform ya
rugo da gudu ya bude mashi,
bai jira komai ba ya kunna kan
motar ciki. Parking yayi ya
shiga gidan a gajiye, saida yayi
wanka yayi sallah sannan
yafito. Mahaifiyar tasa na
zaune a falo yazauna yana
sosa kai, kallon shi tayi, ta dan
yi murmushi sannan tace
"meya faru?" Ya dan gyara
zama, ya dukarda kanshi kasa
yace "Wlh ummi wata nasamu
a wani kauye da aka taba kaini
aiki, taban tausauyi sosai,
yarinyar tana cikin wani hali,
inason nataimaka mata, don
Allah inason kawota nan, ko
aiki tana dan tabawa" ummi
tayi murmushi ganin cewan
halin nan nashi na taimakon
mutane da tausayi, bai canja
ba, tace "bakomi, ai shi da' ai
na kowa ne, kakawota mana"
yasan daman ba zai taba
samun matsala da ummin shi
ba, kasancewar ita ta dora shi
akan wannan kyakkaywar
tarbiyya ta tausayi da jin kai.
Dan haka cikin farin ciki ya
wuce dinning ya ci abincin shi
yayi kat, sannan ya koma side
din shi dan ya dan huta..
BAYAN GAMA WAEC ND
NECO….. Ranana da Deedo
tagama exams dayamma tana
zaune, wani murna takeyi
tamkar zata shiga aljanna, ta
godewa Allah sannan tanemi
albarkan karatun agunsa,
sallama taji saiga shehu ya
rugo da gudu yana kiran
goggo, da sauri tafito tana
cewa "mei kuma ka samo mana
yau?" Ya wangale baki yana
cewa "Goggo nawabu ne yazo"
Idonta ta zaro sannan tace
"yana ina?" Yace"yana waje," da
gudu gudu goggo ta koma
tacanja zanin jikinta, ta jawo
wani sabon mayafi ta buga
sannan ta fito, yara ta gani
sunata shigowa da carton
carton da buhhuna da manyan
ledoji, ta washe baki tana cewa
"Nawabu sarkin kokari, baya
gajiya da hidima, ku aje nan"
tace da yaran, sannan dasauri
goggo ta shige daki taciro wata
atamfa sabuwa kal, dakin
Deedo ta shiga tabata tare da
cewa "ungo wannan, yi sauri
kisa, yaganki fes fes abunki,
kozamu samu da tsoka" ita dai
ansa kawai tayi tasa ba tare da
ta fahimci abinda goggo ke
nufi ba. Da sallama ya shigo
cikin gidan, goggo na jin shi
tayi saurin fita suka gaysa, sai
a sannan Deedo ta fahimci
abinda ke faruwa, Dam taji
gaban ta ya fadi lokacin data
jiyo shi yana cewa yazo tafiya
da ita ne. Goggota gyara
zaman mayafin ta, tace "Ah
itakam dasauki ai, kaga kuma
yau tagama jarabawa sai farin
ciki take" bai ce komai ba, dan
bai yadda da goggo ba, burin
shi dai yaga Deedo sannan ya
tabbatar da abinda take fada,
jin da tayi yayi shiru yasa ta
kwala mata kira, Deedo ta fito
jiki ba kwari, fuskan ta ba yabo
ba fallasa, gashi kuma ta dan
yi kumari, ga wani dan haske
da tayi abin ta. Juyawa yayi ya
kalla goggo, sannan yace "ai
babu wata matsala ko?" Goggo
ta wangale baki, tace "babu
komai Nawabu, tafiya kawai ya
rage muku" yasa hannun shi
aljihu ya fito da kudi masu
yawa ya mika mata, sannan ya
mike tsaye yace "idan ta gama
ta same ni a mota" yasa kai ya
fice kofar gidan
Goggo na ganin fitar shi, ta
kwashe kudin da ya bata, ta
kama bakin zanin ta ta daure
su tam, sannan ta juyo inda
Deedo take tsugunne bata da
niyyar tashi. Kunnen ta ta
damka, tayi daki da ita, tace
"kinsan Allah, idan kika yi
abinda mutumen nan yasa
yace ya fasa tafiya dake, sai
dai uwar ki ta dawo daga lahira
ta haifa wata, dan wlh sai na
hallaka ki, shegia wadda bata
gaji arziki ba" ta wurga ta, ta
ce "maza hada inaki inaki ki
wuce ku tafi, kuma ko da ganin
gida kar ki sake ki dawo mun
nan" Deedo ta dan matse
kwalla, ta shiga tattara yan
kayan ta, ta daure a dankwali,
ta matse a hammata, sannan ta
fito. Shehu da goggo suna
kofan dakin suna jiran ta,
Hadiza kuwa tunda Nawap ya
fita ta bi bayan shi tana
karairaya wai ita dole don ya
ganta ya kyasa, wanda shi bai
ma taba tunanin Allah yayi
halittan ta ba a wurin. Shehu
ya buga ihu yace "yau zamu
yar da dajar mangwaro mu
huta da kuda" goggo tace "kai
dai bari mana kar ya jiyo ka"
haka suka tasa keyar Deedo
gaba suna binta a baya, shehu
har dan jawo mata kullin kayan
ta yake yana cewa "tsintacciyar
mage bata mage" sai ya
kyalkyale da daria, a haka har
suka iso gaban motar. Deedo
ta bude gidan baya ta shiga,
goggo kuma ta koma ta side
din Nawap tana cewa "Allah ya
tsare Nawabu, sai na ji sako
na" wani kallo mai tattare da
tsana ya watsa mata, sannan a
zuciyan shi yace "zaki ga sako
ganin idon ki" a fili kuma ya
dan daga mata kai, alaman sai
ta ji shi din, sannan yai ma
motar key suka dau hanya.
Suna fitowa layin gidan goggo,
Deedo dake matse yan kwalla
daga bayan mota, tace "dan
Allah ina son in yima hally
sallama" ba tare da ya kalle ta
ba yace "ina me gidan?"
Kwanar ta gwada mashi ya
shiga, suka so har kofar gidan,
sannan ta fita ta shige gidan
su hally. Ta gaishe da maman
su, sannan ta wuce dakin hally,
ta same ta zaune ta gama
sallan la'asar, ta zauna a gefen
gado tace "nazo yi maki
sallama ne, yanzu zan tafi"
hally ta mike suka rungume
juna suna dan kuka, a haka
suka fito har bakin motan,
suka yi sallama, tare da
alkawarin baza su taba manta
juna ba har abada. Tana shiga
ko, ya ja motan sai garin
kaduna..
BA’A SHAN
ZUMA… 33, 34
& 35
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gudu ya cigaba da yi, babu
wanda ya ke ma wani magana,
Deedo dai adduo'in matafiya
take ta faman nanatawa cikin
zuciyar ta. Shirun ya ji yayi
yawa dan haka ya danna
Suratul Room cikin qira'ar
Sheikh Ahmad Sulaiman, ita
kuma ta tattara hankalin ta baki
daya, banda kallon titi ba
abinda take yi, dan yau ne rana
ta farko data fara barin kauyen
Ningi. A sannu a hankali har
suka shigo garin kaduna,
Deedo idon ta kyar, ko alamar
bacci babu, gashi lokacin
kusan karfe 8 na dare, idanuwa
ta baje ta fara kallon street
light da yawan hold up, da
kyawawan motocin da suke ta
rafsa uban gudu a manyan
titinan garin. Wani dadi taji ya
ratsa mata zuciya, a hankali
kuma ta fara samun natsuwa,
dan tunda suka taho hankalin
ta a tashe yake, hamdala ta
yima Allah, sannan cikin
zuciyar ta tace "ko bakomai
ganin wannan kyawawan
abubuwan ma wani abu ne a
rayuwa" daga karshe tayi
addu'ar Allah ya sada ta da
dangin mahaifiyar ta, tunda dai
ta san a garin nan suke. A
haka taga sun shigo wata
hadaddiyar unguwa wadda
babu kowa sai kukan karnuka
da yan tsiraran motoci da suke
wucewa jefi jefi. A bakin wani
makeken gida taga yayi horn,
mai gadin ya fito da sauri ya
bude tafkeken gate din, Nawap
kuma ya tura kan motar shi
hankali kwance. Ido ta cigaba
da zarawa tana kallon flowers
din da suka kayatar da
tsararren ginin gidan. Wuri ya
samu kusa da wasu jerin
motoci ya parka, sannan yace
mata ta fito suje ciki. Haka ta
fito tana ta kalle kalle, yana
gaba tana bin shi a baya, har
suka iso kofar palon, ya tura
kanshi da sallamar shi, babu
kowa sai karan T.V an kunno
tashar BBC WORLD. Deedo ma
bata yi kasa a gwiwa ba ta
biyo shi a baya ta shigo,
sanyin A.C ne ya dake ta,
sannan ta taka wani lafiyayyen
carpet mai asalin taushi, gefe
guda ta samu ta rakube ta
zuba ma screen din tafkekiyar
LED plasma idanuwan ta, yayin
da shi kuma ya haura sama, ba
tare da ta san abinda zai yi
ba…
* **Wata kyakkawar dattijuwa
mai cikar kamala da kwarjini, ta
gani tana saukowa a hankali
daga stairs din yayin da shi
kuma yake biye da ita a baya.
Ido Deedo ta tsura masu, ganin
asalin kamar da suke ne ya
tabbatar mata da cewa matar
jinin shi ce. A tare suka zauna
a kujerun da suka yima palon
ado, sannan matar ta gyara
muryar ta, tace "ta so ki dawo
nan mana yan mata" a hankali
deedo ta mike, tana matse da
dan kullin ta kamar wani zai
kwace mata ta karasa tsakiyar
palon ta zauna kasan carpet, ta
dago domin ta gaishe da matar
sai taga ashe tun da ta taso
idon matar a kanta yake! Nuna
ta matar ta fara yi da hannun
ta, kamar zata ce wani abu, sai
kuma ta fasa tace "ki saki jikin
ki, kinji" ta dukar da kanta, ta
gaishe ta, ita kuma ta ansa
cikin fara'a da jin dadi, sannan
kuma a hankali ta fara
tambayar ta labarin ta, dana
garin su da labarin karatun ta,
da duk wani abu da ya shafi
rayuwar ta. Hankali kwance
Deedo ta rattaba mata tarihin
ta, dana goggon ta, da irin
rayuwar kaskancin da ta yi a
kauyen Ningi! Dam gaban
ummi ya fadi, mikewa tayi ta
karasa gaban Deedo ta mikar
da ita tsaye, kallon ta take
kamar ta samu T.V daga bisani
kuma ta rungume ta, wasu
kwalla masu zafi suka gangaro
mata, Deedo da bata fahimci
komai ba, ta fara zara idanu,
Nawap ma da yake gefe a
zaune mikewa yayi, yazo gaban
su yana cewa "ummi lafia?"
Kuka sosai ummi ke yi, tace
"Nawap ita ce wlh, yarinyar da
nake kwana da tunanin ta nake
tashi da shi a ko wace rana"
tasa hannu ta kara rungume
Deedo, tace "Firdausi dama
kina raye? Ashe da rabon zamu
gana dake" Nawap yace "ummi
ban fahimce ki ba fa" sakin
Deedo ta yi, sannan ta kamo
hannun ta suka zauna a kan 3
seater, ta juya tana facing
Nawap, tace "ita ce yarinyar da
kanwa ta Rukayya ta rasu ta
bari, wadda har naje dauko ta
amma goggon ta ta hana, ashe
dama don ta azabtar da
marainiyar Allah ne" ta karasa
maganar tana matse kwalla,
Nawap kan shi sai da kafafun
shi suka kasa daukan shi,
karasawa yayi ya zauna sannan
ya fara tunanin ashe dama
yarinyar nan jinin shi ce, no
wonder ya ji tausayin da yake
mata ya banbanta da na sauran
mutanen da yake taimakawa,
Allah mai iko! Shine kawai
abinda Nawap ya iya fada a
bayyane..
* *Ummi ta kama hannun Deedo
ta rike gam, kallon ta take
tamkar marigayiyar yar uwar ta
Rukayya, yarinya tubarkallah
amma wahala ta kashe ta, cikin
zuciyan ta take cewa zan kula
dake Deedo, in maki gatan da
banyi ma diyar dana Haifa ba,
zan mayar da ke abin
kwatance, in inganta rayuwar
ki, sannan in tallafa maki har
sai kin cika burin ki na zama
kwararriyar likita. Deedo banda
kuka babu abinda take yi, yau
itace ta samu matar da ke
consoling din ta, har ta yarda
ta zauna kusa da ita! Ashe
dangi ma wata rahama ce a
rayuwar dan adam, Nawap ya
katse su ta hanyar saukar da
ajiyar zuciya, sannan yace
"well, faduwa tazo dai dai da
zama kenan, tunda dai yau ga
diyar ki ta dawo hannun ki ai
shikenan, ita kuma goggo
akwai Allah, zai yi ma Deedo
sakayya" ya mike, ya kara da
cewar "bara na shiga ciki, ko
sallan maghriba ba mu yi ba"
ummi kai kawai ta daga mashi,
dan yau wani farin ciki take ji,
gata ga diyar ta. Kallon ta tayi,
sannan tace "da izinin Allah,
wahalar ki tazo karshe Deedo,
ki saki jikin ki, dan baki da
mahaifiyar da ta wuce ni, idan
kin kwana biyu kin huta, zan
kaiki kiga dangi su ma su
ganki, zan baki duk wani farin
ciki wanda ya kamata uwa ta
bai wa diyar ta, kinji? Tashi
muje in kaiki dakin ki, kiyi
wanka kiyi sallah, sannan ki
sauko muci abinci" dagowa tayi
da jajayen idanun ta, tace
"nagode ma Allah da ya nuna
mun wannan rana a rayuwa ta,
nagode ma Yaa Nawap wanda
yayi silar sada ni da ku ummi,
Allah ya yi maku sakayya da
mafificin alkairi" hannu ummi
tasa ta rufe bakin ta, tace
"kyautata maki ya zama dole a
gare mu, saboda mune dolen
ki a rayuwar nan, kar na kara
ganin hawaye a idanun nan
kina jina?" Ta daga mata kai,
sannan ta mike ta dauko kullin
kayan ta, ummi na gaba tana
binta a baya har suka haye
sama, dakin da ke opposit na
ummin ta bude mata, anyi
painting dakin da pink nd
purple, yayin da komai da yake
cikin dakin ma pink nd purple
ne, baki Deedo ta sake tana
kallon haduwar wurin, hannun
ta ummi ta ja ta gwada mata
komai, haka ma toilet ta gwada
mata, da yadda za tayi amfani
da komai, ta dauko towel mai
mugun taushi ta bata, tace ta
daura ta shiga tayi wanka.
Yayin da ita kuma ta juya ta
fita, ta rufe mata kofan dakin.
A bakin gado Deedo ta zauna
tana kare ma dakin kallo, bata
taba tunanin akwai irin jin
dadin nan a wannan duniyar
ba, hawaye suka yayyafo mata,
tasa hannu ta share, sannan ta
mike ta cire kayan ta, ta daura
towel din ta shige wanka…
BA’A SHAN
ZUMA… 36, 37
& 38
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tana shiga wankan takurawa
bandakin kallo shima kansa
wani duniya aka zuba, tadauko
shampoo da sabulu ta ajiye
akasa tazauna dirsham akan
tiles din don yanda taganshi
tsaftsaf tasan zata iyacin
abinci aciki, takaranta jiki
sannan tadauko soso tanufi
cikin shower, murdawa
taringayi harya kunnu taji
ruwan sanyi dasauri takashe,
takara kunna dayan saitaji
ruwan zafi, murmishi yafito
mata, tasanya tafara wanka,
tafi awa biyu tana dirje jikinta,
kafin ta wanke kanta ma, duk
da Allah ya hore mata gashinta
daidai gwargwado baya samun
gyra, tafito tana goge kanta,
itakanta wani iska takeji yana
buso mata, tazauna gaban
dressing mirror. Shafa wancan
mulka wancan, dakarshe
tashafa powder sannan ta leka
wardrobe taga kaya azube ,
lalle yanzu duk wannan kayan
ita zatasa?, set 4 takedashi a
kauye, nan kuwa tanaga yafi
dari, ga gun gyale daban, hijab
daban, atamfa daban less da
shadda ma haka, gefe kuma
dogayen rigunane a tsaye.
Taciro riga daya, ta maida ta
rufe, sannan ta bude ta kasa
nan taga inners, ta ciro shima
tasaka sannan tadaure kanta ta
tattara kayan da ta cire, ta zuba
su aciki sannan tadauki sallaya
tabiya sallahn dake kanta, tana
nannadewa wata ta shigo tana
murmushi daga gani saar
Deedo ce, tace "inji ummi
kisauko abincinki is ready"
itama murmushin tayi sannan
tabita suka sauka, Nawap na
zaune yana mikawa cikinsa
abinci takaraso, itama zama
tayi sannan tafara kallon
coolers din gabanta, Nawap
yayi murmushi sannan ya
kwala kiran saude, wacce
takirata a sama sannan yace
"zo ki diba mata abincin ko" ta
amsa da "toh" Nan tafara zuba
mata, ferfesun kayan cikin,
agefe kuma jollof din shinkafa
ne yaji busheshen kifi, tun
tana kunyan ci anma tazage
taci abunta, Nawap kuwa ganin
zai takura mata yasa yamike
yabar mata gun, itakuwa taci
tayi nak, sunadan tadi sama
sama da saude wacce take
kimtsa gun, suna gamawa tai
masu saida safe, ta haye
sama, saboda wani bacci da
yake figan ta.
Haka Deedo ta kwana cikin
farin ciki da jin dadin sauyin
rayuwan data samu cikin dan
kankanin lokaci. Da safe bayan
ta tashi tayi wanka ta shirya
tsab cikin wata royal blue din
abaya, palon ta sauko domin
taimaka ma Saude da aiyukan
gida, amma abin mamaki har
ta gama komai ta jera abinci a
dining, suna cikin magana
Ummi ce tashigo palon
fuskarta kaman gonan auduga,
Deedo ta karasa gaban ta da
sauri, ta duka har kasa ta
gaisheta. Cikin jin dadi ta
ansa, sannan tace "Masha
Allah, kinga yadda kikayi
kuwa?, kuyi ku gama cin
abincin nan na aike ku da
Nawap ko kema zakiga gari,"
Jikinta narawa tamike don
yanzu gani take kamar a
aljanna take, Allah sa dai ba
mafarki takeyi ba balle ta tashi,
da sauri ta tuttura abincin,
sannan ta koma sama, gyalen
abayan ta dauko sannan ta
fito, yana jingine ajikin mota,
yasha brown shadda da hular
zanna, kullum kwarjini yake
kara mata, ta isa gareshi
sannan tashiga.
A hankali ta gaishe da shi, ya
ansa ba tare da ya kalla inda
take ba, ya cigaba da tukin shi
har suka bar unguwan. Ido ta
ware sosai ganin yadda
mutane ke shawaginsu ba
ruwan wani da wani, babban
abinda ke kara sanya ta
nishadi shine yadda take ganin
kyawawan motoci suna rafsa
gudu a titi hankali kwance. Ta
cikin Malali suka shiga, sannan
suka bi wani layi inda taga an
rubuta Raba Road, ita dai bin
ko ina take da kallo, ba tare da
wata damuwa ba. Ba suyi wata
tafiya mai nisa ba taga sun
kawo gaban wata katuwar
supermarket, wuri ya samu yayi
parking mai kyau, sannan ya
juyo yace mata "muje ko?"
Fitowa tayi har tana dan
tuntube, ta daga kanta sama
wani tafkeken sign board ta
gani mai dauke da manyan
haruffa, an sa STOP AND
SHOP! Jinjina kanta tayi, ganin
haduwar wurin, ba tare da bata
lokaci ba Nawap ya ja basket
suka wuce ciki. Shopping ya
cigaba da yi ba tare da ya bi ta
kanta ba, kuma most of
abubuwan da yake kwasa duk
na mata ne, dangin cosmetics,
native wears, handbags,
takalma, jewelries da dai
sauran su, sai da ya cika
basket din dam, sannan ya tura
zuwa inda zaiyi payment, ya
biya kudin aka kwashi kayan
aka sanya a boot din shi,
sannan suka shige suka dau
hanya. A tunanin ta hanyar da
suka bi zasu koma, amma sai
taga ya dau wata sabuwar
hanyar. Emirate plaza ya nufa,
inda ya shige ciki kai tsaye;
sannan yayi parking a wurin da
aka tanadarwa motoci. Ya fito
yana bada fadi, a tunanin shi
tana biye dashi, amma sai da
ya juyo ya ganta zaune cikin
motan sai kalle kalle take.
Girgiza kan shi yayi, ya kara
gaba inda ya shige wani katon
shop mai kofa hudu, kuma
babu komai a ciki dai zallan
electronics. Gefen wayoyi yayi,
inda ya zabo mata Samsung
Galaxy s3, ya karasa ya biya
kudin, sannan ya fito, yadda ya
hango ta kura ma wasu
kyawawan yan mata da suke ta
kilbibi ido, sai abin ya bashi
daria, inda cikin zuciyan shi
yake cewa "kema very soon
zaki zama abin kallo Deedo" da
sauri ya karasa ya shige
motan, yana shirin tadawa ne
wayan shi dake aje a tsakanin
seat din shi da na Deedo tayi
ringing, ita ta dawo da Deedo
daga duniyar da take, inda a
tare suka kai kallon su kan
screen din wayar…
BA’A SHAN
ZUMA… 39, 40
& 41
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Aysha shine sunan dake
rubuce a saman screen din,
sai da ya ja dan siririn tsaki,
sannan ya maida hankalinshi
ga tukinshi. Reverse yayi, ya
fita daga wurin, yayin da wayar
ta cigaba da rera waka alamar
kira yana kara shigowa. Deedo
ganin bashi da niyyar dauka,
tace "Yaa Nawap ana kiran ka"
cikin halin ko in kula yace "ina
ji ai" ganin bai damu da kiran
ba yasa itama ta juya ta cigaba
da kalle kallen ta har suka iso
gida.
Direct ya shige yayi parking
kanshi tsaye, a gefe suka ga
wata sabuwar Audi V10 baka,
ba tare da tunanin komai ba ya
fito, ya bude boot din ya
cigaba da ciro kayan da suka
siyo, yayin da Saude wadda ta
fito tun lokacin da taji shigowa
su ta cigaba da kwasa tana
kaiwa ciki.
Sauran da suka rage Deedo ta
kwasa ta yi gaba yana binta a
baya, da sallama suka shiga
palon, inda suka tarar da Ummi
da wata bakuwa a zaune. Sai
da Deedo ta gaishe da su,
sannan ta haye upstairs da
kayan hannunta.
Karasawa Nawap yayi ya zube
a kujera yana kiran wash.
Ummi tace
"ya dai? Ko ka gaji ne?" Yace
"Wlh yarinyar ki din can ta bani
wahala Ummi"
Ummi ta murmusa, sannan ta
kara da
"Ai sai hakuri dama, tunda dai
ka riga ka zama babban yaya"
ba tare da yace komai ba ya
mike da niyyar barin palon,
Ummi ta dakatar dashi ta
hanyar cewa "wai baka kula da
bakuwar mu bane?" Sai a
sannan ya kai duban shi ga
kyakkaywar budurwar da ke
zaune, wadda tunda ya shigo
ta tattara duk wata natsuwa,
tare da hankalin ta, ta mika
mashi.
A kasalance ya juyo ya kare
mata kallo, sannan ya shafi
sumar shi mai tarin yawa, yace
"Yaushe a gari?"
Wani lallausan murmushi ta
saki, sannan tace "inji maki'
bako kenan" cikin halin ko in
kula, yace "sorry naga call
dinki, I was driving" ta gyara
zaman ta, tace "no p" a dai dai
nan, ta ja handbag dinta,
sannan tayi ma Ummi sallama,
ta mike da niyyar barin palon.
Ita ma Ummi mikewa tayi, ta
nufin wurin Deedo wadda
hankalin ta ke wurin ta tunda
suka shigo gidan.
Shima juyawa yayi, ya bi
hanyar da zata sada shi da
part din shi, ba tare da ya kara
bi ta kanta ba. Aysha ta juya ta
bi bayanshi da kallo, tace
"Nawap"
Ya juyo hankali kwance, yana
mata kallon fadi matsalarki.. Ta
gyara tsayunwanta, tace "amma
kasan saboda kai nazo gidan
nan ko?"
"Ban fahimce ki ba" ya fada,
sannan ya jingine da bango ya
nade hannayen shi yana
kallonta. Takowa tayi a hankali
zuwa gaban shi; tace "har
yaushe ne ranar da zaka
fahimci yadda zuciyata ke
tafarfasa saboda sonka?
Nawap yaushe ne ranar da zan
samu farin ciki daga gare ka?
Shin wai mei yasa baka
tausaya ma zuciyar da ta dade
tana azabtuwa da so da
kaunarka ba? Plz Nawap kaji
tausayi na mana" ta karasa
maganar tana mai marairaice
fuska kaman zata yi kuka.
Kayataccen murmushinsa ya
saki, sannan yace "look Aysha,
ya kamata ace maganar nan ta
wuce tsakanin mu, ya kamata
ace a matsayin ki na mace
kinyi facing reality yanzu, ki
gane abinda kike so ba zai
taba kasancewa tsakanin mu
ba, in fact, kiyi hakuri ki bama
masoyanki dama har a cikin su
Allah yasa ki samu wanda zai
kwanta maki, I'm sorry" yana
gama fadin haka ya juya, ya
cigaba da tafiyar shi..
Hawaye ne kawai Aysha bata yi
ba, sai kukan zuci da take ta
faman yi, zuciyanta yayi baki,
ta rasa menene yake mata
dadi. Juyawa tayi zata fita, a
dai dai lokacin Deedo ta sauko
daga sama, kujeran da Aysha
ta tashi Deedo ta kaiwa kallo,
nan taga iPhone6 dinta a
yashe, da alama ta manta da
ita ne, dan haka tayi saurin
karasawa ta dauka wayan,
sannan ta bi bayanta…
Har ta shiga motan ta zauna, ta
hada kanta da steering, wani
irin zugi take ji a zuciyanta.
Deedo ta karasa tayi knocking
glass din, ta dago ta kare mata
kallo, sannan ta zuge glass din
ta watsa mata kallon raini, tace
"ya akayi ne?" wayan Deedo ta
mika mata, sannan tace "kin
manta wayan ki ne" fisgan
wayan tayi, sannan ta maida
glass dinta ta zuge, ta fara
kokarin tada motan. Ita kam
Deedo da bata fahimci halin da
take ciki ba, ta juya ta shige
ciki abinta.
WACECE AYSHA?
Aysha Sabe Musa, 'ya kwaya
daya tal a wurin iyayenta
wanda suka kasance yan asalin
garin Katsina, amma yanayin
aiki ya dawo dasu garin kaduna
da zama. Suna zaune a
Galadima road inda ya kasance
basu da nisa tsakanin su da su
Nawap. Sunyi karatu tare da
kanwar shi Hafsat a A.B.U
zaria, inda daga bisani ta wuce
Jordan inda ta kammala
masters dinta, ta dawo gida
yanzu.
A kalla Aysha tayi shekara
biyar tana dakon soyayyar
Nawap, wanda son da take
mashi ne ya kara kusancinsu
da Hafsat har zuwa lokacin da
tayi aure, amma saboda shi ta
kan wanke kafa taje gidan su
duk don ta ganshi, sai ta fake
da cewar taje gaishe da Ummi
ne. Sai dai tayi rashin sa'a, har
inda yau take, Aysha bata
samu karbuwa ba a zuciyar
Nawap, asali ma bata jerin
matan da Nawap zai iya so a
rayuwanshi!
BA’A SHAN
ZUMA… 42, 43
& 44
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cigaban Labari
Cikin gida Deedo ta koma inda
ta tarar da Saude tana jera
abinci a dinning, taimaka mata
tayi har suka gama, sannan ta
wuce tayi sallah, ta gama ta
shiga dakin Ummi ta sameta
zaune saman sallaya, gefe
guda ta samu ta zauna har ta
gama, sannan ta juyo da
murmushin ta, tace "auta ta ya
aka yi ne?" Ta murmusa tace
"lafia lau Ummi, abinci ne ya
zama ready" ta kara fadada
murmushinta, tace "kuma autar
Ummi na jin yunwa ko?" Ta
dukar da kanta tana 'yar daria,
sannan tace "a'a nazo na fada
maki ne kawai" daria Ummi
tayi, tace "to tashi muje kasan"
a tare suka mike, inda Deedo
ta tattara hijab da sallayan da
Ummi ta gama sallah ta ninke,
ta mayar da su wurin su,
sannan ta bi bayan ta suka
sauka kasan.
Nawap suka gani zaune da
jallabiya a dinning area yana ta
kwasan girki ba ji ba gani,
Ummi ce tayi gyaran murya, sai
a sannan ya lura da zuwan su.
Daria suka sanya shi da
Ummin, inda ita kuma Deedo ta
dukar da kanta tana tata
dariyar a boye.
Karasawa sukai suka zauna,
Ummi ce ta umarci Deedo da
tayi serving dinsu, dan ta lura
akwai abubuwa da dama da ya
kamata ace Deedon ta iya, dan
haka ma ta kalleta, ta kara da
cewar "yau fa da girkinki zamu
yi dinner, dan haka sai ki
shirya" murmushi tayi, yayin da
ta cigaba da zuba abincin, tace
"to shikenan Ummi"
Kallon ta Ummi ta cigaba da yi,
tana mai tunano 'yaruwarta,
wani so da tausayin yarinyar
taji ya kara tsirga zuciyarta,
wasu yan kwalla suka feso
mata, inda tasa hannu ta share
ba tare da ta bari sun lura da
ita ba.
Kallonta, ta mayar kan Nawap
wanda ya tada plate din fried
couscous yana korawa da
kunun aya mai gardi, tace "wai
kai yaushe zaka koma office
ne? Ko har yanzu hutun bai
kare ba?" Yayi gyatsa tare da
hamdala, sannan ya dan shafi
sumarshi yace "Jibi zan wuce
in sha Allah" tace "ai gara kazo
ka tafi dan ka kusa cinye mana
abincin gida" yace "kin dai gaji
da ni tunda kin samu diya
yanzu" tace "har ma da hakan"
yace "yawwa yanzu naji batu
Ummi" haka suka cigaba da
firan su cikin jin dadi, Deedo
da bata cika saka baki a firan
ba, sai dai tayi dan murmushi
kawai. Jin ta take a wata
duniya ta daban, yay ita ce ta
samu 'yanci. Hamdala tayi
sannan ta yima Allah godia da
ya nuna mata wannan
kyakkaywar rana…
A tare suka mike bayan sun
kammala con abincin, inda
Deedo ta tattara wurin ta
kimtsa komai, sannan ta wuce
da kwanukan kitchen.
Tana kokarin shigowa palon
taji Ummi na cewa "yanzu
Nawap kana ganin rayuwa zata
yi a haka? Ka tuna kai fa ba
yaro bane, ya kamata ace
yanzu ka aje iyali fa, kuma ni
ita yarinyar can Aysha ban ga
abinda ta rasa ba da baza ka
so ta ba, ko dai kana da wata
matsala ne?"
A hankali ya fara magana, "wlh
bata da komai Ummi, kawai dai
ba zan iya rayuwa tare da ita
bane, amma kar ki damu in
sha Allah zan nemo mata in
dai hakan zai faranta maki rai"
tace "shikenan, Allah ya
taimaka" ya ansa da amen,
sannan ya mike ya bar palon.
Karasawa Deedo tayi, ta zauna
a kasan carpet tana dan matsa
kafan Ummi.
Kanta Ummi ta dafa tace "auta
ya akayi ne?" "Lafia lau" ta fada
tana dan murmushi, ita ma
Ummi murmushin tayi, tace
"gobe dai in sha Allah zamu je
kiga danginki, kiga yar
tsohuwar kakarki da kowa da
kowa" dadi ne ya ratsa ta, ta
rasa abinda zata ce ma Ummi,
nan da nan hawaye suka fara
bin fuskarta, a hankali ta fara
magana "Ummi kinyi mun
komai a rayuwa, kin mayar da
ni mutum a lokacin da kowa ya
ke kyamata, bani da bakin yi
maki godia, sai dai ina addu'ar
Allah yayi maki sakayya da
mafificin alkairi, ya sa ki gama
da dunia lafia"
Nan take itama Ummi hawayen
suka gangaro mata, mikar da
ita tayi ta rungume ta sosai,
tana shafa bayanta alaman
rarrashi. A sannu a hankali ta
daina kukan, mikewa duk suka
yi zuwa sama domin gabatar
da sallan la'asar.
Suna gamawa suka wuce
kitchen, inda Ummi tare da
Saude suka cigaba da taimaka
ma Deedo har ta gane yadda
zata yi amfani da abubuwan
kitchen din, cikin raha da
annashuwa suka gama komai
suka jera a dinning, sannan
suka wuce domin bada farali..
Misalin karfe sha daya na safe
Deedo ta fito daure da towel a
jikinta, a hannunta dan karamin
towel ne tana tsane
yalwataccen gashinta. Gaban
mirror ta zauna, ta shafa mai
tare da Dan simple makeup. Ta
gyara gashinta sannan ta mike
zuwa wardrobe domin ta samu
kayan sakawa.
Daya bayan daya take bin lodin
kayan da kallo har ta rasa
wanne zata saka a ciki. A
karshe ta jawo wata super
peach nd coffee brown dinkin
skirt and blouse ta saka, ta
buda kallabin tayi mashi wani
mugun dauri kamar ta kifa
turmi. Kallon kanta tayi a
mirrorn dake jikin wardrobe din
taga kaman ba ita ba, a fili ta
furta "lallai sutura ita ce
mutum" murmushi tayi, sannan
ta jawo bakin gyale ta buga
abinta.
Wurin takalma ta matsa taga
duk high hill ne, ita kam ta san
ko za a sa mata wuka ba zata
iya tafia da su ba. Wani
maroon ta gani shine mai dan
tudu kuma bai cika tsawo ba
dan haka ta jawo abinta, ta
dora ta sauka zuwa palo inda
Ummi ke jiranta.
Nawap ne ya fara kallonta,
daria taso kwace mashi, amma
ya fuske yace "Ummi ga fa
autar ki ta faso"
Juyawa Ummi tayi ta kare mata
kallo, gata dai tubarkallah, kaya
sun ansheta sai dai wani
bahagon daurin kallabi da tayi
da kuma color riot din da ta
buga. Murmushi tayi sannan ta
mike tace "eyyeh! Lallai auta ta
tayi kyau, sai dai matsala daya"
taja hannun ta suka koma
sama.
Wardrobe din ta bude ta dauko
mata peach din gyale, ta bata
peach din takalmi, sannan ta
dauko mata handbag coffee
brown, ta zaunar da ita ta
gyara mata daurin kallabin
sannan tace "tashi ki gan ki"
mikewa tayi ta kare ma kanta
kallo, lallai gyara shine mace,
ta dan rufe fuskanta alaman
kunya, Ummi tace "tashi muje
kar muyi rana" ta mike ta bi
bayanta, a hankali take takawa
kasancewar bata iya tafia da
high hill ba, amma abin sai ya
bada wani style na daban…
Dagowan da Nawap zaiyi, tsab
suka hada ido, da sauri ta
dukar da kanta, inda shi kuma
ya kasa dauke idonshi a kanta,
Tubarakallah Masha Allah ya
dinga furtawa a zuciyanshi,
lallai yarinyar mai kyau ce.
Ummi ce ta katseshi da cewa
"muje mana" cikin jin kunya ya
dan sosa kai, sannan ya mike
suka wuce, amma hankalin shi
kaf yana gun yadda Deedo ke
takawa a kasaitance..
0 comments:
Post a Comment