tafiyan ma Deedo hankalinta
kwance, bata da sauran
matsala, gashi kuma ta kan
kira Hally su sha labarin
duniya amma ko ta tambayi ya
su Goggo, Hally zata
shashantar da maganar bata
ma son ko kadan Deedo na
tunawa da Goggo, yau ma
kwance take a daki suna waya
da Hally take ce mata ta samu
admission a ATBU, har ma ta
fara registration, Deedo ta mata
murna sosai, inda take
tambayar "ya maganan naku
admission din?" "Muna kan jira
muma, in sha Allah" "Allah ya
taimaka" ta fada, haka suka
cigaba da tadinsu cikin jin
dadi, daga karshe tai mata
sallama ta mike, domin gabatar
da sallahn azahar.
Bayan ta gama sallah tana
zaune kan sallaya taji wayanta
yayi kara, ta dauko ta duba,
email ne ya shigo daga KASU,
sun bata admission a faculty
of Medicine and Surgery.
Murna sosai take yi, da gudu
ta mike da niyyar zuwa dakin
Ummi, wayan Yaa Nawap ce ta
katse mata hanzari, cikin sauri
ta daga wayan tare da gaishe
shi cikin zakuwa, shiru yayi
yana imagining farin cikin da
take ciki, nan da nan ya ji
inama yana da iko da sai dai
su ganshi a gida kawai.
Murmushi yayi yayin da ta
katse mashi tunani ta hanyar
cewa "Yaa Nawap dama yanzu
zamu kira ka" "ni da na fi
damuwa daku ai gashi na riga
ku kira, kuma da babban
albishir na zo"
Cikin zakuwa tace "nima
albishir ne zan maka, amma ka
fara fada mun naka 1st"
murmusawa yayi, yadda take
maganar duk ta tafi mashi da
wata kasala da yake tare da ita,
idonshi a lumshe, yana juyawa
a kujerar office dinshi, yace
"yanzu Dr. Kashim yai mun text
sun baki admission" murmushi
ta saki mai taushi, kaman yana
gabanta, tace "shine albishir
din da zan maka nima, yanzu
email ya shigo mun"
"congratulations, sai ki shirya
on monday, kuje tare da driver,
zan hada ki da Dr. Kashim ki
fara registration ko" "nagode
Yaa Nawap Allah ya saka da
alkairi" "issokay" ya fada, inda
a lokaci guda yai mata sallama
ya koma bakin aikinshi.
Dakin Ummi ta wuce da
murnarta ta shaida mata yadda
sukai da Nawap, Ummi ta
rungume ta suna ta jin
dadinsu, tace "tashi mu wuce
kasuwa, ai zama bai ganni ba
auta zata tafi jami'a" murmushi
tare da hawayen farin ciki ne
suka gangaro a fuskar Deedo,
ta share, sannan ta mike ta
wuce daki ta fara shiri.
Siyayya sosai Ummi tayi ma
Deedo, dangin kayan sawa,
takalma, jakunkuna da sauran
tarkace na 'yan matan jami'a. A
gajiye liss suka dawo gidan
wurin karfe biyar na yamma,
wanka tayi, tayi sallah, sannan
ta gangaro palon don ta samu
damar hutawa, Ummi ta tadda
tana bude kayan da suka siyo,
inda ta zauna itama suka
cigaba da budawa tare, daga
karshe Ummi tayi ma tailansu
waya, domin yazo ya anshi
kayan dinki.
* **
A daddafe Nawap yake rayuwa
a garin Abuja don wani
matsanancin kewar Deedo da
ke damunshi, wadda ya rasa
tantance ko menene dalilin.
Pictures dinta kawai yake kallo
ya samu natsuwa cikin ranshi.
Ga aiki ya sakashi gaba sosai,
bashi da wani lokaci balle yayi
tunanin samun damar zuwa ya
ganta.
Da misalin karfe biyar na
asubar ranar litinin, wadda tayi
dai dai da daya ga watan
February, 2016 (1st Feb, 2016)
Deedo ta tashi, wanka tayi,
sannan ta doro alwala ta fito.
Sallah tayi, ta zauna a wurin ta
cigaba da azkar har wurin karfe
bakwai na safe, daga bisani
tayi addu'ar neman sa'a a
karatunta, da kuma rayuwarta,
ta kara da neman tsari daga
dukkan wani sharri na rayuwa.
Daga karshe tai ma Ummi
addu'ar da ta saba, sannan ta
nema ma iyayenta gafara a
wurin mai kowa mai komai.
Gaban dressing mirror ta isa ta
shafa mai tare da designers
din turarukan da suke zube a
wurin, simple make up tayi,
sannan ta matsa gaban
wardrobe din ta buda tana
tunanin wane kaya ya dace ta
saka a wannan farar rana.
Wata super java ta dauko, mai
kalar light orange nd purple,
dinkin skirt nd blouse ta saka,
wasu round dankunnen ta
sanya masu kalar gold, ta
daure hannunta da agogon
Vintage, itama dai kalar gold
din ce, bracelets ta sanya a
dayan hannunta na hagu,
sannan ta dora zobuna na
isassun yan mata, wanda duk a
cikin siyayyar da Ummi tayi
mata suka siyo da su.
Lafiyayyan daurin yan zamani
tayi, sannan ta jawo gyalenta
purple, takalmanta da handbag
dinta kirar Jimmy Choo wanda
suka kasance reddish brown,
ta sanya, ta dauko handbag
din, ta kara feshe jikinta da
turaruka na alfarma, sannan ta
fito. Karfe tara lokacin har da
minti biyar, dakin Ummi ta
shige, inda ta same ta tana
breakfast. Dukawa tayi har
kasa ta gaisheta, Ummi kam
binta tayi da kallon mamaki,
anya wannan autarta ce? Da
murmushinta ta ansa, tace
"wannan duk kyau ne Deedo?"
Kanta a kasa tana dan
murmushi, ta zauna kusa da
Ummi ta fara hada tea.
A gurguje tayi breakfast din ta
gama, Ummi dai sai yaba kyau
da gayun Deedo take, bayan ta
gama fitar da kwanukan, ta
dawo tayi ma Ummi sallama,
inda tayi mata nasiha mai ratsa
jiki kan ta kula da mutuncinta,
ta kuma tsare martabar
gidansu. A haka suka sauko
palon tare da Ummi, ta dauka
kudi ta bata, sannan tayi kiran
driver, tace ya kaita skool, idan
ta gama sai tayi waya, yaje ya
daukota. Cikin zakuwa ta
rungume Ummi, tayi mata bye,
ta wuce ta shige motan.
Tana shiga wayan Nawap ya
shigo, da murnarta ta daga ta
gaishe da shi, sai da yaja
numfashi, sannan ya ansa,
tambayarta ya fara "kin shirya
ne?" Tace "gamu zamu tafi
ma" yace "ina fatan dai bakiyi
wani kwalliya ba, dan karatu
zakije ba fashion parade ba"
murmusawa tayi, sannan ta
kalla mirrorn gaban motan,
tace "ban yi ba fa Yaa Nawap"
yace "idan kina son na yadda
ki mun snapping kanki, ki tura
mun ta whatsapp yanzu" "to"
kawai ta fada, yai mata bayanin
yadda zata ga Dr. Kashim, dan
shine zai mata komai ya kuma
hada ta da wannan zai taimaka
mata wurin registration. Daga
karshe cikin wata irin murya
mai sanyi yace "I wish ina tare
dake a irin wannan ranar lil
sis" kasa magana tayi, saboda
yanayin da yayi maganan bata
san ya zata fassara shi ba,
murmushi kawai tayi, tace
"thanks for everything Yaa
Nawap, sai na kira idan naje
skool din" ta kashe wayan
lokaci guda, sannan ta dauka
selfie ta kunna datan ta tura
mashi, tayi bala'in kyau kamar
aljana, ta kashe datan ta jefa
wayan cikin jaka.
Suna shiga office din Dr
Kashim ta nufa direct, ko da
bata fada mashi ba ya san ita
ce sister Dr. Nawap, saboda
asalin kamar da yaga suna yi.
Gaishe dashi tayi, sannan ta
samu wuri ta zauna, bayan ya
ansa, yace "Firdausi, ryt?" "Yes
Sir" ta fada, yace "ina fatan
kinzo da credentials dinki baki
daya?" "Eh na zo da komai" "ok,
lemme call someone who will
assist yu" "Ok Sir" ta fada,
yayin da ta dukar da kanta, ta
cigaba da wasa da 'yan yatsun
hannunta.
Wayanshi ya dauka ya kira
wani, yace ya sameshi a office
yanzu. Cikin mintunan da basu
wuce sha biyar ba, aka turo
kofar office din aka shigo,
kanshin wani lafiyayyan turare
ya daki hancin Deedo inda a
lokaci guda taji zuciyarta ta
buga da karfi, kafarshi ta fara
kallo ta ganta lullube cikin
lafiyayyun sneakers black nd
white kirar Tommy Takkies, a
hankali take dago kanta, sanye
yake da bakin pencil jeans, da
white t-shirt ta Ralph Lauren,
hannunshi daure da agogon
fata baka kirar Orlando, kasa
dauke idonta tayi lokacin da ta
yi arba da kyakkyawar
fuskarshi, gashin kanshi ya
kwanta luf, sai kyalli yake
kaman na jarirai, kallonshi take
kaman yau ne rana ta farko da
ta fara ganin bil adama.
Kallonta yake shima, inda cikin
zuciyarshi yake nanata "tsarki
ya tabbata ga Allah, ubangijin
da ya tsara wannan kyakkyawar
halitta!" Murmushi ne ya
subuce mashi, inda itama a
lokaci guda ta sakan mashi
nata kayataccen murmushin…
BA’A SHAN
ZUMA… 70-72
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Dr. Kashim ne ya katse su da
cewa "yawwa Affan ka zo ne?
Karaso ciki mana" cikin jin
kunya ya dan shafi sumarshi
ya karasa cikin office din ya
mika gaisuwarshi ga Dr.
Kashim, inda shi kuma a
hankali kwance ya ansa, ba
tare da ya dago ba, ya cigaba
da typing din da yake akan
laptop dinshi.
Kujeran da ke kallon ta Deedo
ya zauna, kura mata ido yayi,
inda a bangarenta itama ta
kasa tantance dalilin da yasa
take jin dadin kallon da yake
mata.
Dr. Kashim ya dago daga
kallon laptop din gabanshi,
yace "yawwa, Affan plz, wani
taimako za kai mun dan Allah"
ya maida dubanshi ga Dr. Yace
"na me fa? Hope dai ba aike
bane, cuz ina da class karfe
sha biyu" ya fada yana duban
kayataccen agogon hannunshi.
Dr. Yace "kai fa problem dina
da kai kenan, ka cika laziness
kaman, mace" murmushi Affan
yayi, ba tare da yace komai ba,
inda Dr. ya cigaba da magana..
"Wannan sister phrnd dina ce,
tazo registration ne, nd as yu
can see bani da time da zanyi
guiding dinta, kuma ba zai
yiwu na hada ta da Secretary
dina ba, plz ka taimaka mata
komai da za'a bukata tana
dashi, zaku je kuyi clearance
ku ansa admission, then sai ku
fara reg, plz my Lil bro" ya fada
yana kallonshi, inda shi kuma
ya dan dage giranshi tare da
kafada irin na big boys, yace
"alright then, I'll try my best"
sannan ya mike, ya cigaba da
kallon Deedo, yace "let's go
beautiful" murmushi tayi kawai,
ta mike ta yi wa Dr. godiya,
sannan ta fita.
Dr. Kashim ne ya kwala ma
Affan kira a yayin da yake
kokarin bin bayan Deedo, yace
"plz, ka kula da yarinyar nan,
amanan Dr. Nawap ne kana ji
na?" Juyawa yayi yana dan
bouncing yace "have no probz
bro.." yana dariya ya bar office
din, Dr. Ya girgiza kanshi,
sannan cikin zuciyarshi yace
"Affan the trouble maker"
Tare da taimakon Affan Deedo
ta kammala clearance dinta
tsab, ta anshi admission letter
dinta. Bayan sun fito ne tayi
deciding kiran Nawap ta fada
mashi, nan ta ci karo da 3
missed calls dinshi, sai da ta
duba taga ashe wayan silent ta
shiga lokacin da ta jefa ta cikin
jaka. Da sauri ta fara kiran
number har kuma ta katse bai
dauka ba, ta kara kira a karo na
biyu, nan ma shiru kake ji. Ba
tare da wata damuwa ba ta
maida wayan cikin jaka,
sannan ta cigaba da yan kalle
kallen yadda students suke
shawaginsu hankali kwance.
"Hey beautiful" taji an fada
cikin muryar nan tashi mai
dadin sauraro. Juyowa tayi
dauke da murmushi ba tare da
tace komai ba. Ya karaso ya
zuba mata idanu, sannan yace
"zamu je inyi lecture, idan na
fito sai muyi wani abun, zuwa
gobe kuma sai mu karasa ko?"
Ya fada yana mai cigaba da
kallon kyakkyawar fuskarta.
Bata iya yi mashi gardama ba,
dan haka suka mika zuwa
wurin da yayi parking suka
shige motan, sannan ya fara
k'ok'arin tadawa.
Bayan sun shiga motan sun
zauna ne, har ya tada, amma
sai bai tafi ba, kallonshi tayi
tare da alamar tambaya, nan ta
ci karo da shanyayyun
idanuwanshi na aiko mata wani
sako wanda har sai da
zuciyarta ta buga lokaci guda.
Dakyar ta daure tace "muje
mana" cikin wata irin murya ya
langab'ar da kanshi yace
"Feedo I can't hold it, to be
honest, you're beautiful nd
you've a beautiful smile too"
murmushi ne ya kwace mata,
inda tasa gyalenta ta dan rufe
fuskanta, a hankali ya furta
"OMG look at ha dimples, I love
them" ya dan ciji leb'enshi,
sannan ya daure yayi ma
motan key suka bar wurin.
Zaune take a gefenshi, inda ya
tattara hankalinshi gaba daya
yana kallonta ba tare da sanin
ta ba, kasancewar hankalinta
na kan game din da take yi a
wayanta. Wasu phrnds dinshi
ke ta tambayar inda ya samo
ta, amma yana ta basarwa, shi
a dole kada su samu fuskan yi
mata magana.
WANENE AFFAN?
Affan Taufiq, matashi ne mai
shekaru ashirin da biyar a
duniya, namiji dan gayu wanda
ya saba da hutu mai asalin zati
da kwarjini a wurin jama'a.
Kyakkyawa ne dai dai misali,
sai dai yana da wasu idanuwa
masu haske da walk'iya wanda
sune suke rikita duk wata
mace da tayi arba da kallonshi.
Iyayenshi Alh. Taufiq, da Haj.
Maryam yan asalin garin
mak'arfi ne ta jihar Kaduna,
amma Allah yayi masu rasuwa
tun Affan yana shekara goma a
duniya, wannan yasa rik'onshi
ya dawo hannun yayan
mahaifinshi, wato Daddyn su
Dr. Kashim.
Affan ya kasance masoyin
karatun likitanci kamar Deedo
tun daga k'uruciyarshi, wannan
yasa ya zama zakaran gwajin
dafi a gaba daya department
dinsu, tun ranar da ya fara har
izuwa yanzu da yake a final
year dinshi.
* *
Misalin karfe biyar na yamma a
gajiye liss Deedo ta koma gida,
a palo ta zube inda ta tarar da
Ummi, nan ta gaisheta, cikin
yanayi na tausayawa Ummi ta
ansa, sannan tace "makaranta
ba dadi ko auta?" Murmushi
Deedo tayi tace "a hankali zan
saba Ummi" ta mike saman 2
seater, can kuma tace "Ummi
ko Yaa Nawap ya kiraki?" "A'a
bai kira ba, ya akayi ne?"
"Munyi magana kafin na isa
skool, to na manta waya na
silent ashe ya kira, na kira
kuma bai dauka ba"
Ummi tace "may be aiki yake,
idan ya gani zai kira" bata kara
cewa komai ba, ta koma ta
kwanta luf, fuskan Affan ce ke
dawo mata, yadda yake
tsokananta da yadda yake
magana, abin na bala'in birgeta
murmushi ta saki, a dai dai
lokacin kuma wayanta ya fara
ruri,hakan yayi sanadiyyar
yankewar tunaninta.
Yaa Nawap ta gani, dan haka
tayi saurin dagawa, tana
kokarin gaishe da shi, taji yace
"haka muka yi dake? Wane irin
abu ne ban fada maki ba kafin
na tafi? Haka nace ki rink'a
dressing idan zaki je skool?
Wato kin raina ni ko? Ni ban
isa ince ga yadda zakiyi ba, kin
tashi kinyi uban kwalliya kin
tafi skool, a haka zaki
karatun?"
Kyarma hannunta ya fara yi, a
karon farko kuma ta saci kallon
kujeran da Ummi ke zaune
amma bata ganta ba, cikin
murya mai alaman ta kuka tace
"I'm sorry Yaa Nawap, wallahi
banyi dan na b'ata maka ba,
bazan sake ba in sha Allah"
wata muguwar tsawa ya daka
mata wadda ta sa yan hanjinta
motsawa lokaci guda, nan da
nan hawayen da suka mak'ale
suka gangaro saman fuskarta,
ba tare da ya jira me zata ce
ba ya datse wayan, sannan
yayi wurgi da ita saman kujerar
dake gefenshi..
BA’A SHAN
ZUMA… 73-75
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Zubewa shima yayi a kujeran,
ya rasa dalilin rasa
natsuwarshi tun lokacin da ya
ci karo da pic d'in da Deedo ta
tura mashi ta whatsapp.
Zuciyarshi da take wani
tuk'uk'i yake dan bugawa a
hankali yana fadin, "why! Why
this for my lil sis?" Ya dad'e
yana k'aryata zuciyarshi akan
abinda take fada mashi, amma
ina, ya riga ya gama yardan ma
kanshi cewa yana cikin yanayi
na soyayya! Soyayyar ma mai
mugun tsanani, wadda take
tattare da wani mugun kishi
wanda har ya kan rasa inda zai
tsoma ranshi a duk lokacin da
ta taso mashi.
Cikin k'unar zuciya ya furta "I
love yu Deedo, why can't yu
understand? Me sa baza ki
kulan mun da kanki ba? Me sa
kike neman halaka ni da
soyayyarki" ba tare da ya
tantance ba ya ji wata zufa ta
karyo mashi duk kuwa da A.C
dake palon, babu abinda yake
tunani sai hanyar da zai je
Kaduna, tunanin Deedo tare da
son ganinta yana bala'in
azabtar da shi da rayuwarshi.
Kuka sosai Deedo ta cigaba da
yi, ta rasa wannan wace irin
rayuwa ce, ace a matsayinta na
mace kuma 'yar jami'a amma
bata da wani 'yanci nata na
kanta? Tana tunanin tun da ta
bar gidan Goggo tayi
bankwana da bak'in ciki, ashe
ba haka abun yake ba, mutum
baya nan ma amma ya sama
rayuwarta ido, shin wai ya yake
so tayi ne? Jin alamar mutum
na tunkaro palon daga hanyar
kitchen yasa tayi saurin
mikewa ta haye sama, Jan
gado ta fada ta cigaba da rera
kukanta inda a zuciyarta tana
fadin baza ta k'ara bashi
hak'uri ba, tunda dai ba wani
abu tayi ba.
Ta k'ara da cewar "kuma
abinda nake in ba mai kyau
bane ai Ummi baza ta barni
nayi ba, dan haka taje can ta
matse mashi mutum sai fad'an
tsiya" a haka har aka kira
maghriba, sannan ta mik'e ta
shige toilet ta d'oro alwala.
Tana gama sallan taji text ya
shigo wayanta, sai da ta gama
duk abinda take sannan ta
dauko wayan, ga mamakinta
taga ashe Yaa Nawap ne,
gwiwa sake ta bud'a text din
"text me the registration fees"
taga ya turo, shiru tayi tana
k'ara kallon wayan, inda take
tambayar kanta "wai shi wane
irin mutum ne?"
Wurgar da wayan tayi ta mik'e
ta sauka k'asa ba tare da ta
mashi text din kud'in
registration din ba, nan suka ci
abinci, sannan suka cigaba da
firarsu da Ummi. Jin shirun da
Nawap yayi yasa ya kira
number ta har sau biyu amma
shiru, dan haka ya kira Ummi
yana tambayar ko ina Deedon
take. Bayan sun gama gaisawa
da Ummi ta mik'a mata wayan,
sannan ta wuce sama domin
gabatar da sallan isha'i.
Gaisheshi tayi ciki-ciki, haka
shima ya ansa mata yace "baki
ga text dina bane"
"Ban gani ba na bar wayan a
daki"
"Oya kije ki duba, ki mun reply
yanzu, ok?"
"Ok zan duba"
Ba tare da ya kara cewa komai
ba ya kashe wayan, inda
zuciyarshi ta cigaba da jin
haushi da kuma son yarinyar
da bata san ma yana yi ba.
Mik'ewa tayi ta koma d'akin, ta
d'auko wayan, nan tayi arba da
missed calls dinshi, shiru tayi
tana tunanin rashin kyautawar
da tayi wa yayanta mai burin
faranta mata a koda yaushe.
Admission letter dinta ta
d'auko ta duba kud'in
registration din, ta rubuta,
sannan daga k'arshe ta sa "I'm
so sorry big bro, bazan k'ara
ba" ta tura mashi.
Yana kwance ya ji alamar text,
da sauri ya duba wayan, nan
ya ci karo da text din Deedo,
wani lausassan murmushi ya
saki, nan da nan kuma ya nemi
damuwar da yake tare da ita ya
rasa. Bai b'ata lokaci ba yayi
mata mobile transfer ta kud'in
registration din, sannan ya
k'ara mata da 20k, yayi mata
text cewar "in case idan kina
da buk'atar wani abu"
Washe gari ma da wuri ta
shirya cikin turquoise blue din
abaya ta yafa gyalen abayar ya
zauna mata d'as, ta zaro
handbag dinta mai tarkacen
takardunta, ta sanya takalminta
sannan ta k'arasa dakin Ummi.
Ta zauna a gefe ta gaishe da
ita, ta ansa tana mai sanya
mata albarka, tayi mata
sallama, suka wuce tare da
driver.
Ko da suka shiga skool
tunanin abinda zata yi ta fara,
bata san kowa ba bata san ko
ina ba kuma, gashi bata da
number Affan, dan haka ta
wuce office din Dr. Kashim ba
tare da wata damuwa ba. Abin
mamaki tana isa kofan office
din ta jiyo k'anshin turaren nan
da ta ji jiya, ba tare da saninta
ba ta lumshe idanu ta, sannan
ta saki wani kyakkyawan
murmushi, a dai dai lokacin
shi kuma ya bude kofan ya
fito.
Kallonta yayi, ya tabbatar tana
cikin nishadi, dan haka yayi
saurin fadin "Hey beautiful"
kaman daga sama taji
muryanshi, hakan yasa ta kara
sakin wadataccen murmushi,
sannan ta gaisheshi, sai da ya
k'are mata kallo sannan ya
ansa yace "me kika zo yi nan?"
"Neman wanda zai raka ni
registration" ta fada kanta
tsaye. Murmushi yayi, yace "ga
wani kin samu, muje ko?" Ba
tare da tace komai ba, tabi
bayanshi suka fara tafiya. Suna
yi suna dan fira jefi-jefi.
A haka dai da taimakon Affan
da kuma sanayyarshi da
mutane ta samu ta kammala
registration dinta, sai dai 'yan
abubuwan da baza a rasa ba,
wanda koda tana cikin lectures
ne zata iya k'arasa su. Affan
ne yayi mata rakiya zuwa bakin
mota lokacin da driver ya zo
d'aukanta, sai a sannan kuma
ya anshi wayanta, yayi dialling
number shi, sai da ya tabbatar
ta shiga sannan ya mik'a mata,
cikin wani salo yace "I'll miss
you for a while" ba tare da tace
komai ba, ta d'an saki
murmushi, dan ta san itama
har zuciyarta zata missing
dinshi, saboda yan kwanakin
nan da suke yawan kasancewa
tare ta shak'u dashi da yawan
zolayarshi.
BA’A SHAN
ZUMA… 76-78
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kwanakin da tayi tana fita
zuwa makaranta registration
yasa tafara jin kad'aici da bata
fita yau ba, zaune take tana
karyawa da dankali soyayye da
k'wai, wanda ta lafta ketchup
akai, wayanta a hannunta tana
game d'in candy crush,
message ne ya shigo mata,
cikin hanzari ta fita sannan ta
duba, Affan ne ya turo mata
"hey, ya gajiya?, sannan ya
shirin fara lectures?" Tayi
murmushi sannan ta ajiye fork
d'in ta masa reply da "ga
munan, munata shiri"
Message taji ya k'ara shigowa,
da sauri ta d'auka zata duba a
zatonta Affan ne sai kuma taga
sunan Ya Nawap, cikin sanyin
jiki ta bud'e ta karanta "kin
gama registration d'in ko da
saura?" Ta mayar masa da
"nagama Yaya, Allah bada lada"
Murna yake ji da walwala idan
yana musayar txt da ita, don
haka sai yafara tunanin me zai
kara ce mata, don yanzu so
yake ya jata ajiki kasancewar
yasan inda zata je, jami"a ba
gidan wasa da dama bane, kar
wani yaje ya hure mata kunne
duk shukan da yayi wani k'ato
ya girbe, ita kuwa tattara
abincin tayi sannan takai
kitchen ta nufi d'aki ta fara
gyran wardrope d'inta wanda
bata samu tayi ba saboda fita
data keyi kwana biyu.
Affan na k'ok'arin jan
hankalinta wanda itama ta
tattara hankalinta ta mayar
gunsa, k'arshe yaga message
d'in bazai yiwu ba don haka
kawai ya kirata, murmushi tayi
ta jawo earpiece ta saka
sannan ta saka wayan a
aljihun riganta ta cigaba da
gyaran yayin da suke magana.
Shikuwa Nawap ya mata text
yana jira ta mayar masa da
martani yaji shiru, ya fara
tunani me yarinyan nan take yi
tana gida yau kuma babu wani
aiki da takeyi, baya son kiranta
akan message d'in don haka
ya kira Ummi ya fake da
gaisheta yake yi sannan ya
tambaya ina Deedo?, tace "tana
d'aki"
Sallama yai ma Ummi, sannan
ya kira numbanta, sai kuma ya
kashe, sai da ya samo abin
cewa sannan ya kirata, number
busy yaji, domin bata sa
wayanta a call waiting ba balle
ta san yana kira, tuni yaji
gabanshi ya fad'i ganin sai kira
yake yi amma bai shiga ba, har
lokacin wayan take yi, tuni yaji
zuciyarsa ta tokare,
numfashinsa na neman
guduwa gagara zama yayi yana
jan tsaki, a kalla yakai minti
talatin yana kira yana jin busy,
bai san Affan da Deedo sunyi
nisa a tad'insu na duniya ba.
Wanda muka rasa gane shin
soyayya ce ko kuma tsabar
shak'uwa ce?
Deedo da Affan suna cikin
nishad'i domin kuwa wayan da
sukeyi kowanne acikinsu najin
kamar kada su rabu, sai taji
tana Allah Alah afara lectures
ko zasu na had'uwa da Affan
sosai, siffarsa na mata gizo,
tana tunanin halittarsa, duk da
cewa bai manyanta sosai ba,
anma namiji ne wanda ko
wacce mace zata so ya kulata,
don haka har ta gama aikinta,
ta wanke toilet duk suna
wayan, ta kunna ruwan wanka,
sannan ta zauna akan gado,
tanason cemasa zata shiga
wanka tanajin kunya, don haka
kawai sukayi ta tad'in
makaranta yana bata labarin
abubuwan dariya da al'ajabi
dake faruwa acikin makarantan,
Can dai ya dan nisa, yace "bari
naje na karb'i aiki, zan kiraki
anjima" suna sallama ta ajiye
wayan, bata lura da text din
daya shigo ba kai tsaye toilet
ta shiga tafara wanka, tana
shiga taji wayan na kara,
Nawap ne yake kira akalla awa
daya da minti sha biyar suna
waya, jin wayan ta shiga yasa
shi jan numfashi yana jira ta
d'auka ya sauke mata kwandon
masifa, sai kuma ikon Allah
yana ta kira shiru, feedo kuwa
jin kukan wayan ya tsananta
tafara tunanin waye, don dai
ita tasan Affan bazai kira yanzu
ba, toh ko ma waye ya jira ta
ta gama kammalawa.
Sai da ta gama wankanta tafito,
har lokacin wayan na kara, ta
duba kawai ta d'auka gabanta
na fad'i ganin sunan Yaa
Nawap, a hankali ta saka a
kunnenta sannan tace "ina
wuni Yaya?" "Dawa kike waya
for more than one hour?" Shiru
tayi bata bashi amsa ba, wanda
hakan ya kara kular dashi "Me
kike so ki mayar da kanki?,
daga fara makaranta tun kafin
muje ko ina har kin fara tara
maza?, ba na hanaki ba?, ko so
kike na kwace wayan?, ki
kiyayeni fa!, ki gaya mun da wa
kike waya kuma!" Duk fad'an
da yake yi bata bashi amsa ba,
sai ma kukan da ta saka, a
duniya babu abunda ya tsana ji
kaman kukanta, a take ya rud'e
sannan yace "Ji fa, fisabililah
daga miki magana kin fara min
kuka ke kinfi kowa yawan
ruwan hawaye ne?"
Bata amsa shi ba sannan ba ta
daina kukan ba, zuciyanta na
kunci, ta rasa meke mata dad'i,
kashe wayan tayi alokacin ta
ga missed call 42, ga
messages guda hudu, duk
nashi ne, sai taji wani iri ta
tabbata yayi ta kirane yaji shiru
yasa yake fad'a, batason taji
yana mita ko fad'a , don haka
saida ta ida hawayenta a
lokacin text d'in affan ya shigo
"Yh, how far r u done?" Saitayi
shiru tana tunani, ta tabbata ita
bata ce masa zata yi wani abu
ba, shi yace bari yayi abu
anma sai gashi yana
tambayanta, murmushi tayi
ganin cewa ya gane akwai
uzuri agabanta har ya saurara
mata, tuni ta manta da batun
Nawap, yayinda shikuwa gogan
yana zaune yana jira yaga text
d'in ban hakuri,
Ba tare da bata lokaci ba ta yi
reply wa Affan da "ae am
done" Aikuwa sai gashi ya kira,
aka cigaba daga inda aka
tsaya, Nawap ganin bata turo
masa komai ba yasa yayi
tunanin ko kuka take har
lokacin don haka sai ya kara
kiran numban don yaji ko
lafiya, number busy da ya ji
yasa ya daki teburin dake
gabanshi, sannan yaja wani
mugun tsaki! Wanda muma sai
da muka tsorata..
Wayansu suke hankalinsu
kwance, domin kuwa yadda
Affan ke fada mata kalamai
masu kwantar da hankalin mai
sauraro yasa ta manta da
batun fad'an da Nawap ke
mata kwata kwata, cikin wani
irin salo na karya murya yace
"Feedo na yaushe zan ganki
dan Allah?" Wani irin abu taji
har cikin zuciyarta, dak'yar ta
gyara murya tace "ni ba sunana
Feedo ba, ka kira ni Deedo
yadda kowa ke kira na" kaman
yana gabanta ya mak'ale
kafad'anshi yace "no, ni ba
kowa bane so zan na kiranki
Feedo cuz ya fi mun dadi"
Bata k'ara cewa komai ba sai
wani farin ciki da take ji yana
ziyartanta, haka suka yini suna
wayan nan inda ta b'angaren
Nawap kuwa, fashewa ne
kawai bai yi ba saboda bak'in
ciki. Ana gab da kiran azahar
sannan Affan yayi mata
sallama, ba wai dan sun gaji
da juna ba, kawai dan ya bata
daman aiwatar da abubuwan
da suke gabanta hankali
kwance. Suna gama wayan ta
d'an mik'e rigingine a gado
sannan ta rungume wayan a
k'irjinta, ta rasa me sa take
jinshi har cikin jininta, saboda
ita dai bata tab'a shiga irin
yanayin nan ba.
Mik'ewa tayi da niyyar ta d'oro
alwalla, amma taga wayanta
yana blinking alaman tana da
sak'o murmushi ta saki, inda
cikin zuciyarta tace "Affan baya
gajiya shi kam" toilet din ta
zarce tayi alwalanta ta fito ta
tada sallah ta gama, ta shirya
tsab, sannan ta dauka wayan
ta sauka k'asa. Dinning ta
wuce ta zuba abinci, sai da ta
fara cin abincin sannan ta
duba wayan, gabanta ne ya
fad'i dam! Kasancewar karo da
tayi da text din Ya Nawap
kamar haka "are yu insane? Kin
maida ni k'aramin yaro ko? Shi
yasa ina maki magana kika
share kika cigaba da wayanki.
Ki shiga hankalinki tun kafin
na iso garin nan"
Ture plate din tayi a gefe ta
dafe kanta, "wai shi meye
nashi da yake neman matsa
ma rayuwata?"
BA’A SHAN
ZUMA… 79&80
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Wani fanni na zuciyarta ne
yake fada mata "ya damu da ke
ne da kuma al'amurranki, kuma
ko bakomai Yayanki ne wanda
ya cancanci kiyi mashi biyayya
a kowane irin hali" girgiza
kanta tayi, alaman ta gamsu, a
karo guda kuma ta fara kiran
numbershi amma shiru. Saida
ta kira har sau hudu, amma bai
dauka ba, hakan ya tabbatar
mata cewar lallai Nawap yayi
fushi da ita, daga k'arshe da
taga zaman ba zai kaita ba,
dan haka ta yanke hukuncin
tura mashi text na ban hak'uri,
inda take bayyana mashi cewar
ba wai abinda yake tunani
bane.
* ****
Wasa wasa har ta suka fara
lectures, amma Nawap bai
k'ara bi ta kan Deedo ba, dan
ko waya suke da Ummi da ta
bata wayar yake kashewa. Bata
damu da irin abinda yake yi ba,
dan a tunanin ta ko ya bata
freedom dinta ne, dan haka ta
ba Affan dama suka fara
shimfid'a nagartacciyar
soyayya mai asalin dad'i da
kuma tsafta, hakan yasa har
aka fara sheda su a cikin
makaranta, dimin ko da yaushe
suna manne da juna, idan
bashi da lecture haka yake
rakata har sai ta gama
lectures, yayin da itama hakan
yake a wurinta, basa iya
rabuwa ko kadan sai abinda ya
zama dole.
Yau ma kamar kullun zaune
suke gaban faculty suna
tad'insu na masoyan da suka
zurfafa a cikin son junansu,
wata bak'ar mota k'irar Corolla
S ce tayi parking daga gefen
da suke. Kamar ance ma
Deedo ta kalla wurin, cikin
firgici tayi arba da fuskar
k'awar nan ta Aysha wadda
suka nad'a mata duka a
saloon. Cikin yanayi na
mamaki matar take kallon
Deedo, bata gaskata abinda
take gani ba saida tayo tattaki
har zuwa inda suje, a dai dai
lokacin ita kuma Deedo tace
ma Affan ya tashi su bar
wurin.
Mik'ewar da zasuyi taji caraf
matar ta damk'e hannunta gam,
cikin fargaba ta zare ido tana
kallonta, can murya dashe tace
"ina wuni aunty" wani
malalacin murmushi matar ta
saki, sannan ta matso daf da
kunneta tace "hey you lil bitch!
Nan kika dawo kenan? Kin bar
mu muna shan wuyan
nemanki. Ina mai yi maki
albishir da ki shirya taranmu
nida k'awata, domin muna nan
zuwan miki, domin ke baki kai
matsayin fa za'a ci mana
mutunci saboda ke ba" tayi
wurgi da hannun sannan ta
dafa kafadarta tana murmushi
tace "see you 'yan mata" ta
juya ta cigaba da tafiyan ta.
Sai a lokacin Affan ya kula shi
kadai yake tafiya, bai wani
b'ata lokaci ba ya dawo, yace
"meke faruwa ne? Kin bar ni
ina tafiya ni daya"
Murmushin yak'e ta k'ak'alo,
tace "I'm sorry, ina gaisawa da
mutane ne, muje mu tafi" a dai
dai nan drivernta ya iso, dan
haka sukai sallama ta wuce
gida, zuciyanta fal da tsoro da
tunanin abinda zai biyo baya.
Lokaci na tafiya, yayin da
abubuwa da dama suke
shud'ewa, rayuwar Deedo ta
zama sabuwa, ta inda in ba
wanda yayi mata cikakken sani
ba, ba lallai ya gane ta ba, ta
zama cikakkiyar budurwa mai
madaidaitan shekaru kusan
goma sha bakwai, (17) kenan,
ta waye ta goge, tayi clean
abin sai dai wanda ya gani. Da
sauri take ta shiri dan tana da
exams k'arfe biyun rana,
kasancewar sun fara exams
d'in first semester, gashi kuma
tana son ganin burin ziciyarta
kafin ta shiga exams din.
Duk wannan abu da ake, har
yau Nawap bai shigo Kd ba, ta
inda ya daina kiran ta kwata
kwata, ya kuma daina chatting
da ita ta ko ina. Wannan ya
bata damar sakankancewa ta
cigaba da b'arje gumin
soyayyarta, ita da Affan.
Hakan bai k'ara komai ba, sai
asalin so da kuma k'aunar
Deedo wanda suka cigaba da
wanzuwa a cikin zuciyarshi,
suke kuma azabtar dashi.
Kasancewar yau Juma'a, da
wuri ya tashi ya fara shiri,
jakunkunanshi guda biyu
babba da k'arama ya jawo ya
cika su dam, da kayanshi, ya
tattara takalmanshi, da duk
wani abu mai muhimmanci,
sannan ya wuce toilet yayi
wanka, ya fito. Fuskarshi babu
yabo, babu fallasa, haka ya
fara shiri, ya gama tsab, ya fito
cikin shaddar Gezna fara k'al,
ya d'ora hularshi zanna mai
kwalliya bak'i da ash, ya sanya
bak'in takalmin ALDO, sannan
ya d'aure hannunshi da
lafiyayyar b'akar agogon fata,
ta Promado Royal.
Dan da nan ya fito tass dashi
kamar sabon ango, ya feshe
jikinshi da turaruka, sannan ya
fara kwasar kayan shi yana
sanyawa a boot din motarshi.
Gudu yake yi sosai, domin
baya son ya tsaya ko ina sai a
cikin garin Kaduna.
BA’A SHAN
ZUMA… 81&82
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cikin ikon Allah Nawap ya iso
Kaduna k'arfe d'aya da yan
mintuna, bai b'ata lokaci ba ya
wuce massallacin Juma'a yabi
jam'i, sannan ya wuce gida.
Ummi tana zaune ta ganshi
kamar wanda aka jefo daga
sama, da murnanarta, ta tarbe
shi tana mashi lale marhabun
da mutanen Abuja. Cikin jin
dad'i ya zauna suka gaisa,
sannan suka cigaba da
tad"insu na d'a da mahaifiyar
da suka dad'e basu ga juna ba.
Ido ya ware yana ta jiran
saukowar Deedo, amma shiru
kake ji, Ummi ce ta so ta
fahimci halin da yake ciki,
kasancewar yadda yake yawan
kallon stairs din benen, dan
haka tace "wai baka ce ina
auta ta ba"
Yace "ina niyyan tambayarta
inda take ai Ummi" "tana skool,
kasan har sun fara exams"
nunawa yayi kaman bai sani
ba, yace "eyya, abin ba wuya
kenan, to Allah ya taimaka"
Ummi tace "amin." Har ya mik'e
zai wuce side dinshi, ya juyo
yace "k'arfe nawa zata gama
exams din na yau?" "K'arfe
biyar" Ummi ta bashi ansa, bai
k'ara cewa komai ba, ya wuce
domin ya samu damar hutawa.
* **
K'arfe hud'u da kamar minti
ashirin, Aysha tare da k'awarta
mai suna Baby Labo, suka yi
parking motarsu gaban faculty
of medicine & surgery. Baby ce
ta fara fitowa kasancewar ita ta
san kan makarantar, saboda
anan take masters dinta, itace
kuma ta binciko cewar Deedo
tana da exams yau, da misalin
k'arfe biyu zuwa biyar na
yamma.
Bayan Nawap ya dan huta, ya
tashi yayi sallan la'asar,
sannan ya shirya, ya zari key
din motarshi, ya fito. Wurin
Ummi ya k'arasa yace zai je ya
d'auko Deedo ba sai driver ya
je ba. Allah ya kiyaye Ummi tai
mashi, sannan ya sa kai ya
wuce, zuciyarshi duk a dagule,
ya rasa abinda yake mashi
dadi..
Kasancewar basu da nisa
sosai yasa ya isa wurin da
misalin k'arfe biyar saura
kwata. Gefe guda yayi parking
ta inda zai iya hango duk wani
mai shiga da mai fita a harabar
wurin.
Cikin jin dad'i Deedo ta fito
daga exam hall tana ta faman
fara'a, kasancewar ta rubuta
komai da aka tambayeta,
murmushi ta saki a lokacin da
ta hango abar k'aunarta
rungume da hannayen shi, a
gaban hall din yana jiran
k'arasowanta.
Wayarta dake cikin jakar
hannunta ta fara ruri, ta fito da
ita ta duba, Hally ce ta kira ta,
da sauri ta d'auka suka fara
gaisawa, tayi mata ya exams,
ta ansa da "lafia lau 'yan mata,
ya skool" "ina gida ma wlh,
kinsan an sa ranan bikina"
"amma baki da kirki, shine baki
fadi mun ba" "jiya ne fa aka sa,
kuma naga kina da exam yau,
shi yasa nace idan kin fito zan
kira na fada miki" murmushin
jin dadi Deedo tayi, tace
"Bauchi dai ta aureki kenan, ai
nasan dama baza ki bar
Mubarak din nan ya wuce ki
ba" duk suka sa dariya, tayi
mata fatan alkairi, sannan tace
"say hi to my boo" ta mik'awa
Affan wayar, ya ansa suka
gaisa, kasancewar ya san
labarinta tsab a bakin Deedo.
Ansar wayar tayi bayan sun
gama gaisawar, tace "zamuyi
waya anjima" "ke ban gane ba,
ina Ya Nawap din?" Hally ta
tambaya, "ke ki share, bakomai
fa tsakanin mu" "ni dai nafi son
ki da shi Deedo, wannan daga
ji ma dan yaro ne, irin chewing
gum guys din nan wallahi"
murmushi tayi, tace "zamuyi
waya anjima" ta kashe wayar ta
jefa a jaka, suka jera da Romeo
dinta, suna tafe suna firansu
abin gwanin ban sha'awa, sai
dai wanda ya gani.
Gaban faculty suka isa, saman
wasu kujeru suka zauna suna
ta zabga soyayyarsu, su Aysha
da suke gefe suna jiran
fitowarta ne suka hango kamar
ita, dan haka duk suka fito a
motar, a dai dai lokacin wani
abu yazo zai fada idon Deedo,
Affan yace ta rufe idonta ya
cire mata, hannunshi da ya sa
zai cire abun, yayi dai dai da
d'agowar Dr. Nawap ya kawo
kallonshi kan kujerun da suke.
Daaaaaaam! Yaji zuciyarshi ta
buga a lokaci guda, wani
bak'in kishi ne ya ya kai mashi
ziyara, yayin da a karon farko
yaji k'wanyarshi na shirin
d'inkewa! Da sauri ya fito, a
dai dai lokacin kuma su Aysha
suka k'arasa wurin inda Baby
tasa hannu ta finciko gashin
kan Deedo wanda ta daureshi a
baya, gyalen kanta ta fara
k'ok'arin warewa, amma Allah
ya bata sa'a ta rik'e shi gamda
hannunta. Affan yayi saurin
mik'awa yana fadin "what the
hell are you doing? Ke
wacece?" Isowar Nawap yayi
dai dai da shiga hankalin kowa
da yake wurin in banda Affan
wanda bai taba ganinshi ba,
bai kuma san daga ina yake
ba.
Deedo dake lab'e bayan Affan
tana raba idanuwa tuni tayi
saurin fitowa, ganin Idanun
Nawap sun sauya kala daga
fari zuwa jaa, ta san cewar yau
k'aryarta ta gama k'arewa.
Hannunta ya finciko tun
k'arfinshi ba tare da ya cewa
kowa komai ba, shima Affan
bai yi k'asa a gwiwa ba yasa
hannu cikin izza yana jawota
daga hannun Dr. Nawap!…
BA’A SHAN
ZUMA… 83&84
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Nan da nan hankalin mutanen
da suke wurin ya dawo kansu,
kafin kace wani abu wuri ya
cika mak'il da mutane iyayen
son jin k'wak'waf. Juyowa
Nawap yayi idon shi ya
k'ank'ance, kallon Deedo yayi
cikin wani irin yanayi yace "I'm
disappointed in you, abinda
kika koma yi kenan? Irin
tarbiyyar da aka baki kenan?
Who's this guy?" Ya fada da
wata irin tsawa, wadda tasa
'yan cikin Deedo kadawa a
lokaci guda. Cikin muguwar
tsawar da tafi ta dazu yace
"I'm talking to you, kin tsaya
kina mun shirme, me sa kika
zubar da k'ima da darajarki ta
'ya mace? Me sa kika yi watsi
da hudubar da na dade ina yi
miki? Me sa baki fahimci
abinda nake ji game dake ba?
Me sa baki kulan mun da kanki
ba? Me sa kika kasa gane
cewar duk abin da nake ina yin
shi ne sabo da SO da
K'AUNAR da nake miki? I LOVE
YOU DEEDO y can't you
understand!?"
Numfashin Deedo ne ya fara
k'ok'arin sark'ewa, cikin tashin
hankali ta d'aga kai ta kalle
shi, sai a sannan abinda ya
fad'a ya fara yawo a kanshi,
"damn it" ya fad'a tun
k'arfinshi, sai kuma a lokacin
Affan ya samu bakin magana,
ya k'araso gabanshi, ya kalle
shi ido cikin ido, yace "malam
kai kuma daga ina? Me
hadinka da matar da zan aura?"
Wani mugun kallo Nawap ya
watsa mashi, a yayin da ya
dunk'ule hannunshi yana shirin
kai wa bakinshi naushi, ko me
kuma ya tuna, kawai ya saki
hannun ya juya, a fusace ya
fara tafiya.
Aysha da kuka ya k'wace mata,
ta bi bayan shi, da sauri ta tari
gabanshi tace "Nawap nice mai
sonka, wadda take k'aunarka,
zan iya jure ko wane irin cin
fuska in dai daga gare ka ne,
me sa baza ka bani dama na
nuna maka irin yadda nake son
ka ba? Ka taimaki rayuwa ta
Nawap!" Gefenta ya bi, ba tare
da yace mata uffan ba, ya
shige motarshiya tada da wani
irin k'arfi, ya wuce ya bar
wurin..
Kuka sosai Deedo ta saki
ganin Nawap ya ja motarshi ya
tafi, Affan ya matsa gabanta ya
fara lallashinta, yana fad'a
mata kalamai masu dad'i
wanda suke tafiya da ita da
imaninta. A sannu a hankali ta
samu natsuwarta, ta kalleshi
tace "ka fitar dani bakin gate
na samu abin hawa, nasan
driver ba zai zo ba" "no, bazan
iya barinki ki tafi ke daya ba,
muje na kaiki gida" dak'yar ya
lallabata, ta tashi, inda yayi
parking motar shi suka isa, ya
bude mata gaba ta shiga,
sannan ya maida murfin ya
rufe, ya zagaya ta mazaunin
driver ya shiga ya tada suka
tafi.
Baby Labo da akaje da niyyar
dambe, can na hange ta, taja
k'afafun nan nata masu kama
da na sauro ta k'arasa gaban
k'awarta, tana bata baki,
dak'yar Aysha ta mik'e saboda
kukan da take, haka dai ta
kamata suka shige motarsu
suma suka kama gabansu, ta
inda suka fara tunanin canja
shiri akan na dukan Deedo da
suka zo dashi.
Har sai da Nawap ya kawo
gida, sannan ya fara tunanin
halin da ya baro Deedo, amma
dakewa yayi, ta inda yake
ganin koma me yayi mata,
itace ta ja wa kanta, dan haka
bai shiga gidan ba, yayi
parking nesa kadan da
gidansu, yana jiran yaga yadda
za ai ta dawo gida.
Kusan mintuna ashirin ya
share yana jiran zuwanta
amma shiru, dan haka ya tada
motar da niyyar ya shige gida,
sai kuma ya hango wata ash
din Toyota Supra na k'ok'arin
danna kanta a gate din gidan
su.
Dakatawa yayi, har motar ta
shige, sannan ya bi bayan ta
shima ya shigar da tashi, nan
ya ci karo da Affan ya fito, ya
bude wa Deedo k'ofa yana aika
mata da wani sak'on kallo mai
tattare da so da kuma k'aunar
juna..
BA’A SHAN
ZUMA… 85&86
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Fitowa yayi zai shige kaman
bai san da halittar mutane
agun ba, a zahiri kuma
zuciyarsa tafasa takeyi, tana
ingizashi da yaje ya kama
Affan da duka, can kuma har
zai shiga daga ciki wanda
Affan jikinsa yayi sanyi ganin
cewa cikin d'aya ko yayanta ko
dan'uwanta bai ankara ba yaji
Nawap na cewa maigadi
"yaushe ka fara barin samari
suna shigo mana cikin gida?"
Dasauri mai gadin ya nufi inda
Affan yake tare da cewa "mai
gida don Allah kad'anyi hakuri"
Wani k'ullutun bak'in ciki yaji a
zuciyarsa yana kallon Nawap
anma rashin sanin wayeshi yafi
komi 6ata mishi rai, ya kalli
Deedo wacce duk ta rikice tana
neman madafa yace "ki shiga
zamuyi waya" tayi shiru kaman
zatayi magana saikuma ta
shige, motarsa yaja yafice
yayinda shikuma Nawap
yashige palo ya zauna, yana
ajiyar zuciyar kamar wanda
yafito daga filin daga.
A hankali take tafiya zata wuce
yace "zo nan" jikinta na bari ta
zo ta tsuguna kanta a kasa,
cikin mugun gushi yace
"Inaso kigayamun wanda
yabaki izini kiyi saurayi" shiru
bata amsa ba illa hawaye da
yake kokarin zubowa, ganin
hawayenta yafi komi cimasa rai
anma haka yarufe ido ya fara
zuba mata yayyafin masifa ta
inda yake shiga ba ta nan yake
fita.
Muryarsa Ummi tajiyo tafito, a
yadda yake masifan kaman uba
ya kama 'yarsa tana zina, abin
ya matuk'ar bata mamaki sanin
cewa bata taba ganinshi
awannan yanayin ba, idonsa
yayi jajur ya cicciko, ya kalli
Ummi sannan yace "Ummi da
wani fa na ganta"
Sai da ta nemi wuri ta zauna
sannan tace "toh daka ganta
da wani shi ne yazama laifin
me? Wayeshi kekuma?"
Kuka take sosai yayinda ta
goge hawayenta tace "wanda
ya tayani registration ne"
Nawap ya katseta da cewa
"ohhhh shine kuka hau
soyayya, Ummi can u imagine
har yana ce mun ni waye meya
had'ani da matar da zai aura"
Abun yabawa Umma dariya
ganin yadda Nawap karara
yake nuna kishinsa.
Anan tace wa Deedo ta tashi ta
shiga ciki, shikuma tace "
kamata yayi in sonta kakeyi ka
fad'a mata, baka fito kana
takura mata ba, zata tsaneka,
mu mata bama son takuri
munfi gane lallab'i inka bincika
lallab'ata yakeyi shima wancen
din" fuskarshi cike yace "Ummi
yaro ne fa, irin chewing gum
boys din jami'a"
Dariya tayi sannan tace "ahaka
kuma ya take ka agun nema
ba, dole ka koyi sassauci ka
koyi danne zuciyarka idan
mace kakeso, kacire maganan
dizgi da takuri karka kara yiwa
y'ata tsawa haka, ji yadda ka
sata zubar da hawaye" tana
gama fad'in haka ta mike ta bi
sawun Deedo wacce ko da taje
d'akin ma fad'awa tayi akan
gado tana kuka, har ranta
bataji dadin yadda Nawap ya
mata ba, sai dai ta wani fannin
kuma ji tayi kaman ansauke
mata dutse a ranta ganin yau
ya furta mata da kanshi cewa
yana sonta..
BA’A SHAN
ZUMA… 87, 88
& 89
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Da murmushi Ummi ta shiga
d'akin, wuri ta samu a bakin
gado ta zauna, sannan ta kai
dubanta ga Deedo wadda take
kuka bil hak'k'i da gaskiya. A
hankali ta furta "oh, auta ba
dai abinda wancen yayi miki
bane kike kuka?" Sai a sannan
Deedo ta san da shigowarta,
kasancewar kanta na kasa tayi
ruf da ciki. Ba tare da ta jira
ansarta ba ta cigaba "ke manta
mun da shi auta, babu wanda
zai miki dole kinji 'yar albarka,
dan haka tashi maza, ki wanke
fuskar nan taki bana son ganin
bacin ranki 'yar auta ta" cikin
jin kunya, Deedo tana sum
sum da kai ta mik'e ta shige
toilet, wanka tayi sosai, sannan
ta fito, amma bata tarar da
Ummi ba.
Shiryawa ta cigaba da yi dan
lokacin maghriba ta gabato,
kasancewar tana hutun sallah,
ga wani yunwa da yake
addabar cikinta yasa tayi
gaggawan sauka kasa domin
ta samu abinda zata ci. Zaune
ta tarar dashi a kujerar da ta
barsa ya k'ura wa halittar t.v
ido, amma daga dukkan alamu,
bai san abinda ke faruwa cikin
t.v din ba. Sad'af-sad'af tayi ta
shige kitchen, shi kam jin
kanshin turarenta yasa yayi
zumbur, ya dawo daga dogon
tunanin da yake.
Mik'ewa yayi yabi hanyar
kitchen din, can ya hango ta
tana faman daga manya
manyan food flask din da su
kan zuba abinci. A kofan
kitchen din ya harde
hannayrnsa, ya zuba mata
idanu wanda bata ma san
Allah yayi ajiyarsa a wurin ba.
Ta gama dibar abincinta, tana
k'ok'arin fitowa, amma ya kare
hanyar ta yadda baza ta iya
wucewa ba matuk'ar bai bata
hanya ba.
Ido ya k'ura mata sosai ta
yadda ba wani motsi da zata
iya yi. Take ta daburce, ta
nema natsuwarta ta rasa, bata
ta6a tunanin Nawap na da
kyau haka ba, ga wasu irin
idanunshi masu kamar yana jin
bacci, dak'yar ta sauke idonta
a kansa, cikin k'arfin hali tace
"zan wuce Yaa Nawap" bai ce
komai ba, sai ma gyara
tsayuwarsa da yayi, ya
fuskance ta sosai. Har ya daga
baki zai fara masifa, sai kuma
ya tuno da kalaman Ummi
wanda tace "mu mata mun fi
son lallami" sumarsa ya shafa,
cikin boron kunya ya daure
yace "Lil sis, yanzu haka kike
ganin ya dace ace munyi
dake?"
Bata ansashi ba, dan haka ya
cigaba "ban son yadda akai na
kamu da soyayyarki ba, haka
na tashi na tsinci kaina a
cikinta, amma a tunanina, baza
ki ta6a gujewa duk wani abu
da ya shafe ni ba, matuk'ar ba
sa6on Allah bane." Ya ja
gauron numfashi sannan ya
cigaba "soyayyarki ta riga ta yi
mani mugun kamu, wanda in
har ban samu goyon bayanki
ba, komai zai iya faruwa,
amma idan kina ganin zan
takura ki, fine, kina da 'yancin
da zaki zabar ma kanki dukkan
abinda kike so, amma kafin
kiyi saurin yanke hukunci, ina
son kiyi nazari, duk shawarar
da kika yanke, zan aminta da
ita, matuk'ar abin zai zama
farin ciki a gare ki."
Ya gyara mata hanya, yace
"zaki iya wucewa" bata ce
uffan ba, ta bi gefensa ta wuce
palon, yayin da shi kuma ya
fito ya kwashe wayoyinsa,
sannan ya wuce part dinshi.
Juyawa spoon din hannunta
kawai ta cigaba da yi, ita dai ta
san bata k'in Yaa Nawap, dan
shine mutun na farko da ya
daga darajarta a lokacin da
bata da wani gata balle kuma
'yanci, shine wanda ya inganta
rayuwarta da farin cikin da ta
dade tana mafarkin samu. To
amma ya zata yi da Affan
wanda ko wane bugun
zuciyarta yake fita da son shi
da k'aunarshi? Ya za ta yi da
shak'uwa da karamcin da ya
nuna mata a cikin dan
k'ank'anin lokacin da ta san
shi? "Ya Allah ga ni gare ka"
shine abinda ta furta, tare da
ture plate din da yake gabanta
zuwa gefe.
Wayanta ne ya fara ruri alamar
text yana shigo mata, hannu ta
sa ta ciro shi a aljihun dake
jikin rigarta, text din ta fara
dubawa kamar haka "Hope
you're fine Feedo na?"
Murmushin k'arfin hali ta saki,
sannan ta fara typing mashi
ansa "I'm good, kayi hak'uri da
abinda ya faru dazu fa"
Take ta ji ansar shi ta dawo
mata, "never mind dear, but
wanene shi a wurin ki?"
"Cousin dina ne" ta maida
mashi ansa itama.
Dam! Zuciyar Affan ta buga, ba
don komai ba sai don jin
dangantakar dake tsakanin
Nawap da Deedo, shi dai yana
son ta, har cikin ransa, amma
ya san aure tsakanin su abu ne
mai matuk'ar wahala, domin ko
ga Dr. Kashim nan har yanzu
bai yi aure ba, ya san da kunya
ya kai batun nashi auren daga
gama skool dinshi, sannan
yanayin da Nawap ya shiga a
yau, ya tabbatar mashi da
cewar yana k'aunar Feedo fiye
da yadda yake son ta, kuma ko
bakomai zai so mata abinda
yake mafi alkairi ne a gare ta,
dan haka yana jin zai iya
sadaukarwa Nawap da
soyayyar da yake wa Feedo ba
don komai ba sai dan
cancantar shi da ya gani.
Jin shiru bai dawo mata da
ansa ba yasa ta k'ara tura
mashi "are you there?"
Shigowar message din ne ya
katse tunanin shi, a hankali ya
share zufanda ta karyo mashi,
sannan ya fara rubuta mata
ansa "ki fada mun gaskia kina
son shi ko?"
Kamar daga sama ta ji
tambayar, haka dai ta daure
tace "I can't say Affan, but,
shine mutumin da ya 'yanta ni,
ya mayar da ni abinda nake a
yau"
"Ok, na fahimce ki, ki kwantar
da hankalinki, zamu yi magana
anjima kinji?"
"Alright, take care" ta tura
masa, sannan ta mik'e a
3seater ta cigaba da tunanin
halin da take ciki.
Number Hally ta fara kira
amma har ta katse shiru bata
daga ba, dan haka ta shafa
mata lafia, don ta san indai ta
gani, to zata kira ta.
BA’A SHAN
ZUMA… 90&91
NALUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Tunani kam tayishi harta gaji,
ta rasa me zatayi, don tasan ba
karamin butulci bane tace taki
jinin ummi,
Shikuwa acikin kwanakin
yakara daburcewa yadawo wani
iri har Ummi tagane saidai bata
ce masa komi yadawo baya ko
kulata ayayinda shikuma Affan
yariga da ya cire abun aransa
yasawa kansa cewa ya hakura
kawai, tunda tamishi bayanin
komi na rayuwanta da nawap,
randa taje makaranta lectures
ma sun zauna anan yace mata
"ina ga zan baki zabi ne, kije
kiduba kiga wa kika fi so,
zanzama mai farin ciki da
bayaninki, zan kuma yarda da
kaddara, saidai kisani cewa
inasonki ba kuma zan hadaki
da wata ba, niyyata na aureki"
Har ya idar da bayaninsa
batace komi ba, ita dai ta shiga
rudani gashi shareta da nawap
keyi yakara sata awani
damuwan.
Nawap a gida yasamu ummi ya
ce yana son magana da ita, ta
ce "toh" sannan ta zauna
yafara sosa keya sannan yace
"Ummi na zauna nayi tunani
ne, wlh inason Feedo ba kadan
ba, don Allah ummi ki mana
aure" tunda ya fadi kalmomin
sa tasan cewa tabbas dagaske
yanason feedo din tunda tasan
shi mutum ne mai balain
kunya, bai taba tunkararta da
magana shige irin wannan ba
tayi murmushi sannan tace
"Ai dole sai yar tawa ta
Amince, zan mata auren dole
ne aka gaya ma?"
Yayi shiru don bai tabbatar
tana sonshi ba yace " zata
cemiki tanason wani ne, wlh
ummi kar ki yarda, yaro ne
yaudaranta zaiyi" itadai ta zura
mishi ido aranta kuwa kaman
ta juye ruwa a kasa tasha don
murna, tadade tana adduan
Allah yanuna mata wannan
rana da zata hadasu aure,
shikenan tuwonta maiyanta,
Feedo kuwa bayan tagama
tunaninta duk ansa daya ta
kare dashi, wato nawap takeso,
takira Affan tace inta gama
lectures suhadu nan ya
amince, ko da yazo yazauna
akan kujera a dept dinsu
datake jiranshi, ta ce "ni dai
nasan randa nafara soyayya
dakai, bantaba yi don ranka
yabaci ba, banyi don na
yaudareka ko na rabu dakai
daga baya ba, ban yi da zuciya
biyu ba, anma kasan dan adam
ajizi yau an wayi gari bakai din
zancigaba da so ba, maganan
gaskiya yaa nawap nafara so
arayuwata, shi ya maidani
mutum har ka ganni kakeso,
shi ya taimakamin kuma yana
kai, mahaifiyarsa ita tarikeni da
zuciya daya, ban mata adalci
ba ace dan cikinta guda yace
yana sona naki yarda, ba zata
ji dadiba duk da zata nunamin
ba komi anma danka naka ne,
kayi hakuri ka gafarceni" tana
fada ta share hawayenta,
shima kallonta yake har ransa
tausayinta yake ji, yace
"bakomi wallahi, na fahimceki
sosai ubangiji Allah ya sa
hakan shiyafi alheri, nima Allah
hadani da wata" nan suka
danyi tadi sannan ta mike don
komawa aji
0 comments:
Post a Comment