tana jin tamkar ta sauke wani
gagarumin nauyin dake kanta.
Bayan sun gaisa da Ummi ta
wuce sama, don ta shirya ma
wannan rana, domin alkawari
ta yi yau zata fada ma Yaa
Nawap ta ansa tayin
soyayyarsa, don haka take son
tayi surprising dinshi ta hanyar
kawata mashi kanta da ado na
ban mamaki da daukar hankali.
Number sa ta laluba ta kira
amma a kashe, ba tare da wata
damuwa ba tai mashi text "I
need to see my big bro" ta tura,
amma bai yi delivery ba,
hankali kwance ta gama
shirinta tsab, ta sauko kasa
amma ba kowa a palon, ga
wani shaukin son Yaa Nawap
da yake fisgarta, bata da buri a
lokacin wanda ya wuce mata
ganin fuskar shi. Ko ina ta
dudduba amma babu kowa a
cikin gidan, ba tare da wata
fargaba ba ta zarce part dinshi,
a hankali ta tura kofar palon,
amma ga mamakinta ta jita a
datse gam.
Cikin natsuwa take
kwankwasa kofar amma shiru,
dukawa ta yi ta dan leka ta
inda ake sanya key, nan taga
jam lock, cikin rashin jin dadi
ta juyo ta dawo cikin gidan, a
palo tayi arba da Ummi, nan ta
fara kame-kame, amma Ummi
ta basar tace "ina kika shiga
ina ta kwala kiranki?" "Na dan
zagaya nan baya ne in sha iska
Ummi" tace "to, wuce ga abinci
can" dining area ta nufa ta
zuba abincin ta ci gaba da juya
spoon din tana tunanin inda
Yaa Nawap ya nufa, domin shi
dai yawo ba al'adarshi bace
matsawar yana gari to fa kullun
yana gida kaman mace.
Ummi tana hankalce da
yanayinta amma ta basar, don
bata son ta takura mata sai
taga kamar don ba ita ta
haifeta bane. Spoon biyu kawai
tayi a abincin ta taso ta dawo
gefen Ummi ta zauna ta kurawa
wayanta ido tana jiran taga
delivery na sakon da tayi wa
Yaa Nawap.
Can dai zuciyarta ta kasa
daurewa, tace "Ummi ni kam
ina Yaa Nawap ya shiga?
Rabon da na ganshi tun
shekaran jiya" murmushin jin
dadi Ummi tayi a fakaice, ta
san ko bakomai d'an nata ya
fara samun kar6uwa a zuciyar
Deedo. Ta kalleta tace "jiya tun
kafin ki tashi bacci ya koma
Abuja an mashi kiran gaggawa"
ta dan saci kallon ta taga
yadda hankalinta ya tashi
lokaci guda, sannan ta cigaba
da magana…
BA'A SHAN ZUMA… 94
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Bayan ya isa kuma wurin karfe
shidda na yamma ya kira ni
yake sheda mun cewar yau da
misalin karfe biyar na asuba
zasu tashi zuwa London, an
tura su yin wani course na
shekara ukku" tana kawowa
nan taja bakinta tayi shiru, tana
mai cigaba da kallon akwatin
t.v.
Mikewar da Deedo zata yi taji
wani mugun jiri ya kwashe ta,
kukan da take makalewa a take
ya subce mata tagal tagal tayi,
tana me kokarin faduwa, nan
Ummi ta kwashi salati tana
kwalawa Saude mai aiki kira,
cigaba da jijjigata tayi tana
fadin "lafiya Deedo? Menene
abin kukan?" Cikin rashin sani
Deedo take magana "Yaa
Nawap me sa kai mun haka,
bayan kasan kaine buri na,
kaine farin cikin rayuwa ta"
kuka ta kuma fashewa da shi
ta koma kaman zararriya, ta
kalli Ummi da tausayin Deedo
ya cika ta, tare da jin dadin
kalamanta, tace "Ummi da
gaske Yaya ya tafi ya barni?
Ummi ya zan yi da DAKON SO
(Na KAUSAR LUV) na Yaa
Nawap da nake fama dashi?"
Ta k'ara fashewa da wani
kukan mai ban tausayi..
Dak'yar Ummi ta lallaba
Deedo a wannan rana, banda
kuka ba abinda take yi, haka
dai Ummi ke kwantar mata da
hankali, yayin da wutar
soyayyar Nawap take faman
kara ruruwa cikin zuciyarta
tamkar ana watsa mata fetur.
* ***–******
Da sallama suka shigo palon
ba kowa sai Deedo da ta
kurawa wani makeken hoton
Yaa Nawap dake mak'ale a
palon ido, wanda ya kasance
sana'arta kullun da ta dawo
daga makaranta bata da sauran
aikin da ya wuce ta zauna
gaban wannan hoto tayi ta
kallonshi, wani lokacin har da
yan sambatun da baza a rasa
ba.
Aysha ta karasa ta dafa
kafadar Deedo, sai a sannan ta
dago a razane dan ko alama
bata ji shigowar mutun ba.
Kallonta tayi a tsorace, inda ita
kuma ta sakar mata murmushi
tace "Ina Ummi fa?" Murmushin
k'arfin hali ta mayar mata, tace
"ku zauna mana, taje unguwa
ta dawo" su Baby Labo aka ja
yan kafafuna aka karasa cikin
palon aka zauna a kujera ana
aika ma Deedo sakon
murmushi.
Ita kam abin ya bata
mamaki, mutanen da suke
neman ta su daketa sune suka
dawo kamar ba su ba, anya
babu wani kulli a kasa? Ta dai
daure ta kwala kiran Saude ta
kawo masu dan abin motsa
baki, yayin da Aysha ta fito da
I.V na guda ukku ta mik'awa
Deedo, tace "da naki, da na
Ummi, wannan kuma na daurin
aure ne ki bama Nawap"
[18/04 23:41] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 95
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Ansa tayi idonta waje ta duba
da kyau, tabbas bikin Aysha za
ayi, cikin zuciyarta tace "har ta
hakura da Nawap din kenan"
tunani ta fara itama ko hakura
za tayi dashi, tunda bai damu
da ita ba, gashi yau kusan wata
daya da tafiyarsa amma ko a
waya bata jishi ba, Ummi ma in
zai kira ta sai yayi hiding
number sannan, tasan kuma
duk don saboda ita yake
hakan. Aysha ce ta katse mata
tunani ta hanyar cewa "ya dai?
Naji kinyi shiru ko congrats
babu" murmushin dole tayi,
tace "I'm so happy 4 yu, sai
dai kuma Yaa Nawap baya nan,
yaje yin wani course London,
amma in sha Allah zaki ganmu
ni da Ummi" "Allah ya sa"ta
fada, sannan suka mike a tare,
ta d'an taka masu zuwa inda
sukai parking sannan ta dawo
ciki, tana me cike da mamakin
sauyawan da Aysha tayi lokaci
guda.
* *–****
Cikin yarda da hukunci irin
na ubangiji, aka yi bikin Aysha
da angonta Saifullahi, wanda
dak'yar Ummi ta lallaba Deedo
ta leka wurin dinner. Haka ma
aka sha bikin Hally, aka kaita
Bauchin Yuguda, amma Allah
bai ba Deedo ikon zuwa ba,
kasancewar rashin Yaa Nawap
wanda ya kasance wani jigo na
rayuwarta, tafiyarsa ta zama
wani gi6i a rayuwar Deedo,
domin tana jin tamkar ta rasa
shi ne har abada, ga wani irin
son shi da ya bi ya addabi
zuciyarta, gani take ashe son
da tayi wa Affan ba soyayya
bane shak'uwa ce kawai, amma
asalin so na zahiri Nawap take
yiwa shi, sai dai bata gane
hakan ba, sai yanzu.
Idan tana tunanin shi ta kan
zubar da hawaye domin shine
kawai abinda take yi ta samu
sassauci a cikin birnin
zuciyarta. Ummi ce ma take
dora ta akan yawan addu'oi
domin kuwa addu'a takobin
mumini ce kuma ta kan
taimaka ma bawa a kowane irin
yanayi.
Shawarar Ummin dai ta bi,
idan abun ya dameta ta kan yi
salloli tare da addu'oi, sannu a
hankali ta fara samun natsuwa,
ba wai don ta daina jin DAFIN
SO (coming soon) na harbin
zuciyarta ba, sai don
fawwalawa Allah dukkan
lamurranta da tayi, ta maida
hankalinta ga karatun ta,
wanda take ganin shine kawai
abinda zata yi ta farantawa Yaa
Nawap dinta.
BA’A SHAN
ZUMA…
96,97&98
BA'A SHAN ZUMA… 96
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
BAYAN SHEKARA UKKU
A hankali yake saukowa daga
matattakalar jirgin janye da dan
madaidaicin trolley, yana
shakar iskar da take busawa
mai cike da ni'ima tamkar za'a
saki ruwan sama a dai dai
lokacin. Waige-waige yake
alamar yana neman wanda ya
zo daukarshi, can ya hango ta
sanye da wata light purple d'in
abaya, ta yafa gyalen, ta nade
hannayenta duk biyun ta zuba
mashi idanu tana murmushi.
Sosai ya wara idonshi yana
kare mata kallo, tabbas
Deedonshi ce, ta canja sosai,
ta zama cikakkiyar budurwa,
fatar jikinta ta goge sosai, ga
wani annuri mai haske tattare
da ita. Wani mugun dadi ne ya
tsirga zuciyarsa, nan take
soyayyarta ta dawo masa
sabuwa fil, tayi masa famin
ciwon da yake fama da shi
shekara da shekaru, sai dai
kuma ya san ta riga ta mashi
nisa, ya san son da take ma
Affan ba irin wanda zata yi
fatali da shi ne ba, ya san ba
zai taba samun kar6uwa a
wurin zuciyar da ya hallakar da
tashi zuciyar domin ta ba, dan
haka dole ya kama mutuncinshi
tun kafin ya zube a idonta.
Gintsewa yayi, ya karasa gaban
ta, dariya take mai cike da
wani salo, tana kallonshi, a
lokaci guda tace "sannu da
zuwa Yaa Nawap"
Kaman ya nitse a wurin,
kasancewar muryarta da ya ji,
shekara ukku cif cif rabon da
ya ji wannan zakakkar muryar.
Dakyar ya dawo daga duniyar
da yake, yace "na sameku
lafiya lil sis?" "Lafia lau" ta
fada, yayin da ta anshi trolleyn
da ke hannunsa tayi gaba, shi
kuma ya bita a baya.
Inda tayi parking suka
k'arasa, fuskanta lullu6e da
wani farin ciki wanda ba zai
iya 6oyuwa ba, bayan motan ta
buda ta jefa jakan hannunta,
sannan ta zagaya driver seat ta
zauna ta daura seat belt, duk
idanun Nawap na kanta,
mamakin ta yake yi sosai,
yadda take abu komai a waye,
kanta ya gama fashewa kamar
ba Deedon Goggo ba, kallonshi
tayi ta saki murmushi wanda ya
rasa ko na menene sai dai ya
kawar da kanshi, ita kam ta yi
ma mota key suka kara gaba.
BA'A SHAN ZUMA… 97
NALUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka je gida ba wanda ya
tanka ma wani, illa Deedo da
lokaci zuwa lokaci ta kan kai
dubanta gareshi sannan ta saki
murmushi, wanda ya rasa gane
ko na menene, daga k'arshe
tasa ya tsargu da kanshi, har
yana tunanin kodai wani abu
ne a jikinsa wanda yake sanya
ta dariya? Nan da nan ya hade
rai, ya juyar da kanshi yana ta
faman shan kanshi, har suka
isa.
Wucewa ciki yayi bayan tayi
parking, inda ita kuma ta fito
da jakarsa, ta ja zuwa cikin
gidan.
Da murna Ummi ta tare shi
tana mashi barka da zuwa,
cikin jin dadi da girmamawa ya
isa suka gaisa, sannan suka
mike gaba dayan su zuwa
dining table, kamar sun san da
yunwa ya iso.
A haka suka gama cin
abincinsu hankali kwance,
suna yi suna yar fira jefi-jefi ta
yaushe gamo.
* **—-******
Tun bayan da Nawap ya dawo
kwata-kwata Deedo ta rasa
gane kanshi, baya shiga
harkan ta ko kadan, haka zalika
ko shigowa yayi ya tarar da ita,
to fa baya zama zai bar wurin,
inda a bangarenta take fama
da so da kuma k'aunar shi
wanda su kan tunzura
zuciyarta. Hanyar da zata sanar
dashi yadda soyayyar shi ke
azabtar da ita take nema,
amma ina, babu fuska ta
bangarensa, domin kuwa ya
dade da sallamawa da ita, ya
shafa ma zuciyar sa ruwan
sanyi, ya daukan ma kanshi
alkawarin ba zai taba takurata
ta so shi ba.
Ganin halin ko in kula da
Nawap yake gwada ma Deedo,
yasa Ummi ta kira shi, tana
tambayar "ni kam Nawap ina
maganar ku ta kwana kai da
auta ta?" Ba tare da ya kalleta
ba yace "Ummi wannan
magana ai ta wuce, ita da take
da wanda take so" murmushi
Ummi tayi, ganin yadda yayi
kicin-kicin da ido, tace "me zai
hana ka kara jarraba sa'ar ka,
ka sani ko ka samu kar6uwa
yanzu" bai ce komai ba, sai ma
mikewa da yayi ya wuce part
dinsa…
BA'A SHAN ZUMA… 98
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Yana shiga ya mike a kujera
yana jin wani tiririn son Deedo
na tokarar zuciyar sa, anya zai
iya jure rashinta? Ko dai
shawarar da Ummi ta bashi zai
yi amfani da? Cikin azama ya
mike ya jawo wayarsa, ya cire
screen lock din, nan da nan
hotonsu shida ita da suka
dauka wata rana dazai koma
Abuja ya bayyana, sosai ya
kura ma hoton ido yana ganin
yadda take dariya, ga dukkan
alamu bata da wata damuwa a
wancan lokacin. A fili ya furta
"i can't let yu go Deedo, cuz yu
belongs to me" ya shafa
fuskan wayan, sannan ya
lalubo number ta a sabon layin
mtn din da yake amfani da shi.
Sai da ya kira har ta katse
bata daga ba, inda ya k'ara kira
a karo na biyu, nan ma shiru
kake ji. Text ya tura mata "Ina
fatan lokaci yayi da zan samu
ansar tambayar da na maki
shekaru ukku da suka wuce" ya
tura ba tare da ya sanar da ita
ko wanene ba.
Kwance take tana sana'ar
tata, wato tunanin halin da zata
shiga in ta rasa Nawap, tana
kallo aka kira har ta katse
amma bata ko motsa yatsanta
ba, shigowar text din ne yasa
ta gane mai kiran yana bukatar
wani abu daga gare ta. Hannu
tasa ta janyo wayan ta buda
text din, sai da ta gama
karantawa sannan ta duba
number, amma bata san mai
ita ba, tunani sosai ya cika
kwanyar ta, daga k'arshe
dabara ta fado mata, inda ta
sanya number a TrueCaller,
nan ta ci karo da sunan DR.
NAWAP KHAMIS har ma da pic
dinshi..
Yadda kasan an mata albishir
da gidan aljanna, haka Deedo
ta tsinci kanta cikin farin ciki.
Zumbur ta mike daga
kwanciyar da take ta kara
murza idonta, tabbas ba gizau
sunan yake mata ba, cikin
zazzodi ta fara rubuta mashi
ansa "I'm just waiting for this
day to come" can kuma wata
zuciyar ta bata shawaran ta
dan jaa class mana, tunda dai
har yanzu yana son ta.
Murmushi ta saki sannan ta
goge text din, ta rubuta wani
"nd who's this?" Ta tura masa
ba wai don zuciyarta ta so ba.
Jin shigowar text yasa yayi
saurin duba wayar, bayan ya
karanta, yayi murmushin
takaici, sannan ya rubuta
"someone who can't live
without yu" ya senda mata…
Ganin text din yasa ta taka
rawar disco, domin ta gama
sarewa Nawap ya guje mata,
ashe ba haka abin yake ba,
ashe kallon kitse ne su ke wa
rogo. Wasu hawayen jin dadi
suka gangaro ga bakinta
kunshe da murmushi, ta shafa
idonta taji tabbas hawaye ne,
nan ta kara fadada
murmushinta, domin duk
duniya ba yanayin da ya kai
wannan dadi, kana hawaye a
lokaci guda kuma kana
murmushi, wannan ya nuna
farin cikin ya kai k'arshe
BA’A SHAN
ZUMA… 99&100
BA'A SHAN ZUMA… 99
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Cikin sigar shagwaba kamar
wanda yake kallon ta ta turo
dan bakinta, sannan ta fara
rubuta ansar da zata bashi "if
yu really mean ur words, me
zai hana ka bayyana kanka?"
Ta tura, yayin da ta rungume
wayar tana jin sabon yanayi na
daban a cikin jikinta.
Murmushi yayi wanda har sai
da kyawawan hakoransa suka
bayyana, a lokacin da yayi arba
da sakonta, ba tare da wata
fargaba ba, ya mayar mata da
ansar "ok, ki shirya gani na da
misalin karfe bakwai na daren
yau."
Ihun murna ta saki, inda ta
fada da baya ta kwanta, ta
k'ank'ame wayan tana tunanin
abinda ya dace tayi kafin
lokacin haduwarsu. Da sauri ta
mike ta wangame wardrobe
dinta, sannu a hankali take bin
kayan ciki da kallo, amma bata
ga wanda ya dace da ita a rana
irin ta yau ba, rufewa tayi,
sannan ta bude dayan gefen
wanda yake dogayen riguna ne
zallah jere a cikin wardrobe
d'in, a hankali take duba su
daya bayan daya, inda a
k'arshe ta sauke idonta akan
wata English gown kalar lemon
green, murmushi ta saki
sannan ta zaro rigar, wuyanta
irin rufaffen nan ne (tuttle
neck) yayin da hannun rigar
yake dogo, sai dai ya matse
daga k'arshe, doguwa ce har
k'asa, in banda kyakkaywan
(shape) da aka yi mata daga
sama.
A samar gado ta aje rigar,
sannan ta bude inda
gyaluluwanta suke, ta samo
wani madaidaicin jan gyale
wanda ta san tabbas zai hau
da rigarta, haka ta gama hada
duk wani abu da zata sa,
sannan ta sauka kasa zuwa
kitchen.
Saude ta tarar tana aiki, ta
kalleta tace "je ki huta Saude,
bar ni da aikin kitchen din nan
yau" godiya Saude tayi ta
wuce, duk da ta fuskancin
yanayin farin cikin da uwar
dakin nata take ciki.
Tana tsaka da aiki, ta juya
bayan ta Nawap ya shigo
kitchen din, ya buda fridge ba
tare da ya san ita ke aiki wurin
ba. A hankali ta dago idanunta,
inda ta sauke su a kan nasa,
amma yayi kicin-kicin da fuska
shi dole ga big bro, baya son
ta gane da shi tayi musayar
text dazu.
Murmusawa tayi, sannan
tace "har ka tsorata ni wlh, me
zaka dauka na kawo maka?"
Basarwa yayi, yace "eyya, ban
san kina nan bama ai, ruwa ne,
na riga na dauka ma, kiyi aikin
ki kedai" tana kallonshi tana
dariyar yadda yake faman
bonewa, tace "ok, ehnmm" ya
juyo yace "ya dai?" "Daman zan
ce ne anjima ina da bako, yace
zai zo nan dan kada kace ban
fada maka ba" ta karashe
maganan tana mai karantar
yanayin da yake ciki. Cikin
borin kunya ya shafi kanshi,
"lokacin da kika fara
soyayyanki dama kin nema
izinina ne?" Ya fada yana fita a
kitchen din, biyo shi tayi tana
fad'an "ni fa ba wani soyayya
Yaa Nawap, aboki ne kawai" da
murmushi ya juyo, sai kuma ya
daure yace "naji, kije kiyi
aikinki"
"to bakon nawa fa? Baka ce
komai ba"
Ido ya kura mata, yana mata
kallon kece rayuwa ta, nan da
nan yake neman sanya ta a
wani hali, domin bugun zuciyar
ta taji ya karu, ba tare da tace
komai ba, ta juya ta koma
kitchen din zuciyarta fal da so
da k'aunar Yaa Nawap.
[20/04 20:56] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 100
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Lokacin da ta gama girkinta har
karfe shida saura kwata, a
gurguje ta jera komai a dining
table, lokacin Ummi na
saukowa ta kalleta sai zuwa
take tana dawowa tsakanin
kitchen da dining area, ga
fuskanta a sake da alama tana
cikin farin ciki sabanin
kwanakin baya da ko kasan ta
daina saukowa, kullun tana
daki kaman bokanya.
"Ba dai ke kika yi girkin yau
ba auta" Ummi ta fada dai dai
lokacin da ta karaso gabanta.
Da murmushi ta kalla Ummi
tace "yau special na hada
mana Ummi, har sai kunne yayi
motsi idan aka ci" bubbuda
coolers din Ummi take yi, inda
wani kanshi ya daki hancinta,
tace "lallai naga alama, amma
menene sirrin?" Ta fada da
sigar tsokana.
"Ba komai fa Ummi" Deedo ta
fada tana rufe fuskanta da
hannu, "sai dai ehnmmm"
"mene?" Ta tambaya tana
kallon ta. "Ina da babban bako
anjima Ummi, idan ya zo zai zo
ya gaishe ki ma" ta fada tana
dariya. "Bako Deedo?" Ummi ta
fada cikin karaji,
girgiza kai Deedo tayi, "zaki
ganshi Ummi, kuma in sha
Allah zaki yaba dashi" "Allah
yasa" ta fada yayin da take
wucewa zuwa palo ba tare da
ta ji dadin maganar Deedon ba.
"Yanzu shikenan yaron nan
yana gani zai yi rashin mace
kamar Deedo? Duk dan saboda
dan banzan kishi irin nasa,
kuma yana son ta ba wai baya
son ta ba." Sababin da Ummi
ke ta faman yi kenan a cikin
zuciyarta, har aka kira
maghriba, ta mike ta haye
sama domin bada farali.
A bangaren Deedo ko bayan
ta fito wanka ta bada sallar
maghriba, sannan ta cigaba da
yan shafe-shafenta, sassaukar
kwalliya tayi kasancewarta ba
ma'abociyar dam6are-dam6are
ba, sannan ta ja rigarta ta
sanya, ta gyara gashinta ta
faka shi a tsakiya, inda tayi
amfani da jajayen kananan yan
kunne, ta daura bracelet ja,
tana kokarin feshe jikin ta da
turare, taji alaman message ya
shigo mata, da sauri ta duba
"Ina cikin gidan ku, zaune a
palon baki, just waiting for my
princess" shine abinda ta gani
rubuce a message din.
BA’A SHAN
ZUMA…
101-103
BA'A SHAN ZUMA… 101
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Dariya mai sauti ta saki, a fili
ta furta "Yaa Nawap kenan"
sannan ta rubuta mashi ansa
"hmmmm, ina zuwa yanzu" ta
tura masa, sai da ta karasa duk
abinda zata yi, ta janyo wasu
red plat shoes ta saka, ta yafa
gyalenta sannan ta fita. Dakin
Ummi ta fada, ta tarar da ita
zaune tana jan casbaha, ta
zauna gefen gado tana wasa
da hannunta. Har sai da tayi
addu'a duk suka shafa a tare
sannan Ummi tace "har ya iso
ne?" Kanta a kasa ta girgiza
kai alaman "eh"
"To ki tashi kije, ki dai kula
da kanki da mutuncinki" "in sha
Allah Ummi" Deedo ta fada
lokacin da take mikewa, a
zuciyarta tana mai cewa "Ummi
da ta san ko waye da ba
wanda zai kaita jin dadi, shaaa,
zanyi surprising dinta ne" ta
wuce hankalinta kwance,
domin yadda take jin son
Nawap yasa ta rage fargaban
haduwa dashi.
Zaune yake ya bama kofa
baya, in banda kanshin
turarensa na Tom Ford Velvet
Orchid, babu komai da yake
tashi a wurin sai fa sautin T.V
inda ake nuna labaran kasa a
tashar TVC. Da sallama ta
shigo, kanta a kasa ba tare da
fargaba ko mamakin ganinsa
ba, haka ya dago kansa yana
kallon yanayinta, me sa bata yi
mamakin ganin shine ba? Anya
babu wani abu da ta sani
tuntuni? Kawar da tunanin da
yake yayi, sannan ya ansa
sallamar yayin da take
karasowa tsakiyar palon.
Kallonta yake tamkar yau
ce rana ta farko da ya fara
ganinta, tayi mashi kyau sosai
wanda bai taba tunanin tana
da shi ba. Nesa dashi ta
zauna, ta dago a hankali tace
"Ina wuni Yaa Nawap"
Cikin rashin kuzari ya ansa ta,
nan wani dogon shiru ya ratsa
tsakaninsu, muskutawa Nawap
ya yi, cikin k'arfin hali, sannan
yayi gyaran murya yace "ke
haka ake taran bako ko ruwan
sha babu?" Shiru tayi kaman
baza ta ansa ba, can dai ta
nisa tace "bakon nazo nema,
but unfortunately sai na ganka,
kunya ce ta hana ni tambayar
ko ka kasan inda yake?"
Ido ya tsare ta dashi har
saida ta gama maganarta, inda
ya cika bakinsa da iska, a karo
guda ya furzar dashi, ya rasa
ta ina zai fara mata bayani, ga
so da k'aunarta na matuk'ar
azabtar dashi, amma yana
tunanin halin da zai tsinci
kanshi matuk'ar bata ansa
tayin soyayyar shi a karo na
biyu ba.
Fuskantarta yayi, yayin da ya
dawo daga duniyar tunanin da
yake, cikin wata irin murya ya
kira sunanta "Firdausi" ta dago
a hankali ta yadda taga
fuskarsa ta san he's damn
ready nd serious. Domin tunda
take dashi sau daya ya taba
kiran ta da ainahin sunanta,
ranar da ta fara ganinsa a
duniya.
Kwantar da kai yayi, sannan
ya fara magana "Bazan so na
zama mai son kai ba, haka
zalika kada kiyi tunanin
dangantar dake tsakaninmu,
ina son ki dauka baki taba sani
na ba, ta yadda baza ki sha
wahala wurin yanke hukunci a
kaina ba. Shekaru ukku da
suka wuce na nemi sanin
takamaiman abinda ke
zuciyarki dangane da ni, amma
Allah bai nufa zan samu ansa
ta, ta inda tafiyar gaggawa ta
same ni, gashi kuma nayi
alkawarin bazan neme ki ba,
har sai ke da kanki kin neme ni
da ansar tambayar da na miki"
sai da ya dan tsagaita, yana
mai cigaba da kallon yadda ta
dukarda kanta, tana wasa da
yatsun hannunta, sannan ya
cigaba…
BA'A SHAN ZUMA… 102
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Ina mai rokon Allah yasa yau
ta kasance rana ta k'arshe da
zan san matsayina a wurin ki"
yayi shiru yana mai cigaba da
kallon ta yana kuma rokon
Allah yasa ya dace a wannan
rana.
Shirun da tayi har na tsawon
mintuna kusan bakwai yasa ya
cigaba da magana "idan har na
saka ki a rudani, ina son ki
gafarci zuciya ta wadda take
bugawa a ko wacce sa'a da so
da k'aunar ki, wadda take
azalzala ta, ta ke kuma hana ni
sukuni a duk tsawon shekarun
dana sanki, ba laifi na bane
Deedo, ba kuma ni na dorawa
kaina ba, Allah ne ya jarabce ni
da son ki, me sa baza ki
taimaki yayanki ba? Me sa
baza ki gane farin cikin da zan
samar maki ba, matuk'ar kika
yarda da ni a matsayin uban
ya'yanki, ina son ki sosai,
wanda bazan iya dainawa ba,
domin kuwa kece mace ta
farko da na fara so, haka kuma
kece ta karshen da zan tafi ga
mahaliccina da k'aunarta koda
baki yarda kin so ni ba."
Yana gama fadar haka ya
mike da niyyar fita, domin
zuciyarsa ta gama karyewa,
gashi Deedo ta ki tace komai,
asali ma ko kallon yanayin da
yake ciki bata yi.
Har sai da ya kai bakin kofa
sannan ta samu damar dago
da jajayen idanunta, wanda
suka rine da ruwan hawaye
tace "Yaa Nawap" juyowa yayi
da sauri jin raunanniyar
muryarta na kiran shi, ganin
hawaye na zuba daga
kyakkyawar fuskarta yasa yayi
saurin dawowa da baya yace
"no please lil sis, don't be like
this kinji, na fahimci kina son
Affan ko? Me sa zan shiga
rayuwarku, na hakura zan
danne son da nake maki,
amma bazan iya jurar ganin
hawayenki ba, it's ok kinji"
yayin da yasa hannu ya zaro
handkerchief ya mika mata.
Ansa tayi ta toshe bakinta
dashi, sannan ta saki kuka mai
sautin, wanda ya gigita Nawap,
har ma ya rasa ta ina zai
lallasheta, da ya san haka ne
da bai zo mata da maganar
nan ba.
Katse mashi tunani tayi ta
hanyar cewa "Yaa Nawap kaine
mutun na farko wanda ya kalle
ni a matsayin mutun kamar
kowa, kai ka daga darajata, ya
cika mani gurin rayuwa ta,
sannan kaine mutun na farko
wanda zuciya ta ta mace
saboda son shi, ban taba son
wani kwatankwacin son da
nake maka ba, amma na rasa
me sa baka fahimci hakan ba,
har kayi fushi da ni, tsawon
shekaru ka barni ina dakon
sonka ka manta da ni, me sa
Yaa Nawap? Kasan halin tashin
hankalin da na shiga?" Ta k'ara
fashewa da kuka mai tsuma
zuciyar masoyi, wanda yasa
Nawap dafe kanshi da duk
hannayensa biyu.
Ya ma rasa menene
yanayin da yake ciki, shin farin
ciki ne ko kuma haushin
kanshi yake ji yadda bai
fahimce ta ba tun asali. Kasan
carpet din ya zauna shima ya
dago fuskanta ya share mata
hawayen, sannan yace "I'm so
sorry lil sis, azaban kishi ne ya
hana ni fuskanta inda kika sa
gaba, I promise baza ki taba da
na sanin kasancewa tare da ni
ba, zan faranta maki dai dai
gwargwadon iko, zan kula
dake, in tarairaye ki fiye da
yadda ARCH. SADDIQ ya
tarairayi LAILA (Rabon ka ko
yana bakin kura na Chuchun
Gaye) zan shayar dake
madarar farin ciki fiye da
yadda FU'AD ya shayar da
MEELA (WATA RAYUWA) ki
yarda da ni my lil sis, ki bani
aron zuciyarki, ni kuma na
maki alkawarin I'll never ever
let yu down…."
BA'A SHAN ZUMA… 103
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Murmushi ta sakan mashi
yayin da hawayen suka cigaba
da zarya akan kuncinta,
"shhhh.." ta fada lokacin da
take dora dan yatsanta akan
bakinta, nan take yayi tsit, tare
da aika mata sakon kallo mai
alamar nayi missing dinki,
langabar da kai tayi, itama tana
kallonsa, sannan a tare suka
sa dariya kamar ba ita ce
wadda tasha kuka yanzu yanzu
ba.
Cikin dan k'ank'anin lokaci
suka dinga aika ma juna da
kalamai masu dadi da kwantar
da hankalin masoyi, har sai da
suka gama aminta da junansu,
inda daga k'arshe Nawap ke
tambayar ya akai bata yi
mamakin ganin shi yake aika
mata sakon text ba, nan ta fada
mashi tayi amfani da
TrueCaller ta gane shine.
Dariya yayi, sannan yace
"Ooops, na manta akwai
wannan fa" dariyan tayi itama,
gani take kaman ba Yaa Nawap
din da ta sani ba, ashe dama
ya iya soyayya?
"Tashi muje ka nema izini
wurin Ummi, dan idan ba kai
mata ba nima zan hakura da
kai" wara idanunsa yayi "da
zaki hakura ai da yanzu kin
mance dani, yarinya ko Ummi
bata yadda ba ni ba yadda za
ayi dani, dole a so ni,"
Sannan ya mike ya bi bayanta
tana dariya suka fito, suka
k'arasa cikin gidan.
Ummi zaune saman dining
table suka shigo fuskokinsu
dauke da murmushi, kallon
Nawap tayi tace "Kai kam ina
ka shige ina nemanka ka taya
ni cin abinci?" Sosa kai yayi,
yace "naje neman aure ne"
Ummi sake da baki tace "to fa!
Babbar magana"
Ganin Deedo na bin shi a
baya tace "ke kuma ina bakon?
Ko har ya tafi?" Dariya ta
kwace mata, ta karasa kujerar
da take kusa da ta Ummi ta
zauna, yayin da shi kuma ya
zauna a wadda take kallonsu,
tana kallon Ummi tace "ga
bakon na kawo ya gaisheki"
tana yi tana nuna Nawap da
yatsa.
Shiru Ummi tayi, yayin da
take k'are masu kallo duk
kowannensu da fara'a dauke a
fuskarsa, tace "kai ku dakata,
ban fa gane ba" duk suka sa
dariya, inda Nawap yace
"Ummi zaki bani autar taki ko
na nema wata?" Duk da kanta
ya kulle da sha'anin yaran
zamani, amma matuka tayi
farin ciki, taji dadi fiye da
misali, inda ta kai kallonta ga
Nawap tace "akwai sharudda
dai, wanda matuk'ar ka kiyaye
su to zan baka ita"
Ya buda ido yana kallon
Ummi, yace "tohm a jero su ina
ji" ya fada lokacin da yake sai
ta kunnensa garesu.
Dariya ya basu, dan haka suka
kyakyale gaba dayansu,
sannan Ummi tace "banda
yawan takuri, sannan bana son
yawan la6e, ana kiraye mun
auta, kuma idan ka shirya ka
turo da magabatanka dan dama
na gaji da ciyar da gauro a
gidan nan"
Sosai ya ji dadin
maganganunta, "zanyi yadda
kike so Ummin mu" ya fada
yana kallon Deedo da ta dukar
da kanta tana murmusawa…
BA’A SHAN
ZUMA…
104-106
BA'A SHAN ZUMA… 104
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda tunda aka fara
maganar kanta yake kasa, tana
jin wani sabon canji a jikinta,
domin yanayinta na yau, yasha
ban ban dana kullun. Mik'ewa
tayi ta zuzzuba masu abincin
cikin jin kunyar mugun kallon
da Nawap ya tsare ta dashi.
Bayan sun gama Ummi taga
abin nasu ba mai k'arewa
bane, dan haka ta wuce sama,
inda a zuciyarta take cewa "oh
ni Fatima, yaran zamani sai a
bar su, ko dan kunyar idona
ba'a ji, uhunmm" ta haura
sama, ta haye dan gadonta
tana tunanin yadda zata aurar
da ya'ya har biyu.
Deedo da Nawap wanda
soyayya tasa suka manta ko
sallar isha'i basuyi ba ne suka
ankare da lokaci, yayin da ta
sauke idanunta kan tafkekiyar
agogon bangon dake manne a
palon, k'arfe goma har da minti
ashirin da biyu (10:22pm).
Mik'ewa tayi ba wai dan ta so
ba, ta kalli Nawap wanda ya
marairaice fuska kaman zai
saki hawaye yana mata kallon
ban gaji da ganin ki ba. Alama
ta mashi da ido, abin nufin ya
kalla agogo. Wadda ke daure a
hannunsa ya duba, bai ma san
lokaci ya ja haka ba, dan haka
ya dan wara idanunsa, sannan
ya mike, hannuwansa duk
biyun cikin aljihu, ya kalli
Deedo yace "it's ok yan mata
na, ki shiga ciki, I'll call kafin ki
bacci"
Murmushin itama ta sakan
mashi, sannan ta juya tana
tafiya, sai da ta hau stairs din,
kafin ta juyo tace "don't keep
me waiting plz" cikin shagwaba
mai narkar da zuciya tayi
maganar, dan haka Nawap ya
sandare a wurin, ya kasa
motsa koda yatsan k'afarshi,
har ta haye tana mai dariya.
Girgiza kansa yayi, sannan
ya juya ya wuce side dinsa,
inda a zuciyarsa yake cewa
"tabbas ka so a so ka ma wani
babban abu ne mai tattare da
farin ciki a duniyar masoya"
* ***—-******
Soyayyar Nawap da Deedonsa
soyayya ce wadda suka
shimfid'a a kan gaskiya da
amana, soyayya mai cike da
so, tattali, da kuma kula da
junansu, wanda hakan ya basu
damar sanar da magabatansu
domin cika burin masoya.
A ranar yau, wadda tayi dai
dai da juma'a ishirin da ukku
ga watan ifirilu (23 Apr,) aka
sanya ranar auren Deedo da
Nawap dinta, wata ukku cif cif,
wanda ya kama sati daya dai
dai gama jarabawarta ta aji
hud'u (400L). Bayyana farin
cikin da masoyan suke ciki,
b'ata baki ne, domin ko suna
cikin tsananin farin cikin da ni
Lubiee ba zan iya fasalta shi
ba, lokaci kawai muke jira mu
sakata mu wala, sannan kuma
mu 6arje guminmu.
BA'A SHAN ZUMA… 105
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
BAYAN WANI LOKACI
A gajiye liss ta shigo gidan, ta
zube akan kujera tana kwala
kiran Saude wadda ta rugo da
dan saurinta tana cewa "sannu
da zuwa uwar dakina, ya
jarabawar?" Idonta a lumshe
tace "Alhamdulillah, taimaka
mun da abu mai sanyi, baki ji
ranar da na kwaso ba" "to, to
bari inzo" Saude ta fada,
sannan ta mik'e ta koma
kitchen din, ta dawo hannunta
dauke da dan tray, da jug, da
kuma cup a sama.
A gaban Deedo ta dire shi,
tace "kinyi sa'a ko, dazun nan
muka hada zo6on nan ni da
Hajiya, kinga har ya dau ra6a
kuwa" tsiyayawa Deedo tayi, ta
kai bakinta yayin da taji wata
nutsuwa ta sauko mata, ga
wani gard'i da dad'i da zo6on
ke da shi, sai da ta kara cika
wani cup din, ta sha kaman
rabi, sannan tace "lallai zo6on
nan yayi dad'i Saude, wai ina
Ummin take ma?"
"Tana ciki, ga dukkan alamu
sallah take"
"Ok, bara na shiga, nagode
Saude"
Yayin da ta mik'e ta haye
saman, ta wuce dakin Ummin
straight.
A zaune ta tarar da ita tana
duba wani littafi mai sunan
(You can be the Happiest
Woman in the world) na Dr.
A'id al-Qarni. Saida ta gama
karanta bayan littafin, sannan
tayi murmushi, ta zauna gefen
ta.
"Sannu da gida Ummi"
Da fara'arta ta dago, ta cire
medical glass din da yake
idonta, sannan ta kalle ta,
"Yawwa auta, ya exams din?"
"Alhamdulillah Ummi, amma fa
ta yau sai hamdala, ku dai taya
mu da addu'a"
"Ana ta yi ai, Allah dai ya baku
sa'a"
Tace "amin" sannan ta dukar
da kanta bakinta na motsi, da
alama akwai abinda take son
fada.
"Ya akayi ne amarya?" Ummi
ta tambaya, tana kallon ta da
alamar tsokana.
Rufe idonta tayi da duk
hannunta, tana dariya, sannan
tace "ehnmm, Ummi dama zan
ce ne dan Allah idan na gama
exams ina son zuwa ganin
Goggo, in masu bankwana"
Murmushin jin dadi Ummi tayi,
tace
"Ahaf, kin hutar da ni kenan,
dan ni ina nan na shirya irin
lallashin da zan maki akan kije
kuyi bankwana, dan ba dadi
haka kawai suji an miki aure,
ashe 'yar tawa mai hankali ce
da hakuri da kuma maida
komai ba komai ba, amma naji
dadin kasancewarki haka,
domin haka ake son dan Adam
ya kasance, duk wanda yayi
maka sharri, kai kuma ka saka
mashi da alkairi, sai kiga kai
kuma Allah yayi maka sakayya
ta wani 6angaren"
Hannunta ta rike, "Allah yayi
maki albarka Deedo, ya kuma
kare ki daga ko wane irin
sharri kinji"
Da murmushinta, ta ansa da
"amin Ummi, Allah yayi maku
sakayya da gidan aljanna
kuma"
"Amin, kinga next week zanyi
tafiya, kuma Hafsat (kanwar
Nawap) tace mun jibi zasu zo,
sai ku zauna dasu, ga Saude
kuma, idan kin gama exams, ke
kuma sai kuje da driver, nasan
kafin nan na dawo, zan zo sai
mu dawo tare, da su din ma,
tunda na san zasu zo bikin
suma"
"To shikenan, Ummi, duk
yadda kika ce haka za'ayi"
"yawwa autalle, tashi kije ki
danyi wanka ki huta kinji" ta
mik'e ta wuce dakin ta, sannan
Ummi ta maida tabaranta ta
cigaba da karatun ta.
BA'A SHAN ZUMA… 106
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga, kiran Nawap ya
shigo mata, da murmushi ta
ansa wayar, suna firarsu ta
masoya, nan take shaida masa
zata je ganin su Goggo, yace
"yaushe kuma keda kike
exams"
"Sai na gama fa, kuma Ummi
ma tace naje ai" ta fada tana
tura bakinta gaba, kamar yana
kallon ta.
"To ke banda abinki, Ummi ce
mijinki ko ni? Idan nace a'a fa,
ya zakiyi?"
"Tafiya zanyi mana, tunda dai
Ummi ta barni, kai kuma sai ka
bari idan na zo gidanka ka juya
ni yadda ka so"
Dariya mai sauti ya saki, yace
"Yarinya kina da aiki, ai tun
yanzu zan fara ba sai kin zo
ba"
Ba tace komai ba, tayi shiru
tana saurarensa. Sai da ya
gama tsokanarta sannan yace
"I'm just kidding kinji, na san
by then na samu hutu, kinga
idan na zo sai muje tare kawai.
"Thanks hun" ta fada, bakinta
kunshe da murmushi, nan suka
cigaba da firan su har suka
gama, sannan ta mike ta fada
toilet.
* —****
Ranar da Ummi tare da
kanwarta zasu wuce Dubai,
domin hado lefen Deedo, da
kuma siyayyar wasu abubuwa
daga cikin kayan dakin ta, kiran
ta tayi, sukai sallama, inda ta
kara da cewar "duk in mun
dade, to sati guda ne, ke kam
ai jibi kike gama jarabawan
ko?"
Deedo ta girgiza kai, Ummi
tace "yawwa, kinga washegari
sai ku wuce da driver, idan na
dawo na dan huta, zan zo sai
mu dawo tare"
"Ya Nawap yace zai zo sai
muje tare wai"
"To ai shikenan ma, amma
abinda za ayi shine, to ku tafi
da Hafsat da yaranta, su sai su
dawo tare da shi, ke kuma su
baro ki can"
"To shikenan Ummi, Allah ya
tsare, ya kuma dawo daku
lafia"
Tace "amin" yayin da ta mika
mata kudi, tace "kya yi masu
tsaraba."
Gaba dayansu suka fito
domin yi masu rakiya, yayin da
driver ya dauki su Ummi zuwa
Abuja, kasancewar ta can zasu
tashi.
Bayan sun shiga Abuja,
waya sukai ma Nawap, yaje ya
samesu, nan sukai bankwana,
yayin da shi kuma ya dauko
hanyar Kd, tare da driver,
zuciyarsa fari kal yana ta
faman sharta gudu kaman zai
tashi sama.
Deedo wadda tuni suka saba
da Hafsat, tare suka shiga
kitchen suka cigaba da tanadar
mashi dad'ad'an abincin kala
kala.
0 comments:
Post a Comment