Babalalo ya kalli fuskan Malam Arabi a ragowar farin watan da ya haske sararin samaniya,yaga yadda k'ullu ya b'ata masa fuska tamkar Wanda watan Ramadan ya shigo yayi shirin tafiya tashe,k'iris ya rage ya kwashe da dariya sai dai yayi ta maza ya waske da tambayar Malam Arabi cikin haki.
"Wai Malam biyo ka tayi ne naga ka fito da gudu?
Malam Arabi yaji kamar ya shak'e Babalalo Dan k'ufula,ya kuwa dank'ara masa muguwar Harara ya zarce da bashi amsa a fusace.
" Ban sani ba,nace maka ban sani ba,banda wulak'anci daman ka san matarka mahaukaciyace kuma Y'ar iska ce ka kawo ni da sunan cire mata aljanu,yanzu ba Dan Allah ya kiyaye nayi ta maza ba Cibiyata fa taso cire min,kai wannan mata anyi tsinanniya,billahil azimu na zata kaca aka watsa min a Cibiyar,wai Ashe hak'oran ta ta kafta min,in banda Y'ar iska ce tana matar aure amma ta cafki Cibiyar k'aton mutum irina?Haka kawai da gemuna na sunnah ta keta min haddi?a yanzu ji nake Cibiyar na rawa tamkar zata fad'o k'asa,Allah dai ya tsareni kar in je ta zuba min virus da dafin bakinta"
Babalalo Abu biyu ya had'e masa,ga takaici ga shi yana son yayi dariya,tilas ya k'unshe dariyar ya dinga bawa Malam Arabi hak'uri,har da cewa.
"Malam mu koma cikin gidan na baka kaya ka sauya,kaga na jikinka duk sun b'aci da mark'aden gero, kar kaje gida a ganka haka babu dad'i"
Kallon da Malam Arabi yayi masa ko bai tanka ba ya isheshi amsa,amma Duk da hakan saida ya tanka cikin fusata da b'acin rai.
"Babalalo ka san tsirara?to gara na tafi tsirara akan na sake shiga gidanka domin annobar da take ciki,matarka kuwa kada Allah ya k'ara had'a fuskata da tata ko a hanya,domin naga bala'i da masifa a tare da ita yau,haka kurum daga zuwa taimako ta had'ani da jinyar Cibiya,Wallahi Allah ya isa ban yafe ba,Y'ar banza me hak'ora irin na karya"
Yana gama magana ya saita hanya yayi gaba zugudun zugudun kamar zai kifa,da yaga malum malum d'insa na hard'eshi ma tsayawa yayi ya cire ya soketa a hammatarsa,sannan yayi gaba yana ta masifa yana Jan Allah ya isa,Dan ji yake yi kamar Cibiyarsa ta tashi daga aiki.
Har ya k'ule Babalalo na tsaye yana kallonsa,sai da ya dena ganinsa sannan ya kwashe da dariya har da rik'e ciki,yayi dariya me isarsa har da hawayen mugunta,sannan yaji a zuciyarsa ya fara fargabar shiga gidan shi kad'ai saboda tsoro.
Yafi rabin awa a tsaye yana tararrabin shiga,gari yayi tsit dare yayi nisa kowa ya nemi makwanci amma shi yana tsaye ya rasa madafar kamawa,tilas haka ya daure ya fara sand'a ya shiga Dan ba zai iya kwana a waje ba..
D'aga labulen falon yayi,sai ya hangeta daga gefe tana ta shirgar bacci har da Munshari,yayi ajiyar zuciya a hankali yana godewa Allah,a hankali ya fara sand'a zai tsallaketa ya wuce d'aki,bai kula ba saboda babu haske sosai k'afarsa ta dunguri tata k'afar,a tare suka razana,k'iris ya rage Babalalo ya saki fitsari a wando tsabar tsoron da yaji,ita kam Habiba k'unshe dariyarta tayi,domin tun bayan fitar Malam Arabi da yayi cilli da ita take dariya,sai da taji motsin shigowar Babalalo sannan ta fara baccin k'arya da munshari,kamar irin wadda bata san abin da ya faru ba ta fara murtsika idanu da Hammar k'arya,sannan ta juya ta kalli bokitin gasararta da ya b'are a gefe,sannan ta waiwayo ta dubi Babalalo da ke tsaye yana zare idanu,saura kad'an ta saki dariya amma ta gimtse,tayi mik'a tana kallon Babalalo tace.
"Me ya sameni ne naji jikina da bakina na ciwo?ga kuma k'ullu na ya b'are?
Babalalo ya fara in ina jikinsa na mazari.
" um...um..dama..daman fad'uwa ki kayi...shine kika b'arar da gasarar ..kuma kika bige bakinki"
Ya fad'a yana kallon leb'enta na k'asa da ya zama sharb'eb'e kamar ganda,saboda bulalar da yasha.
Ta mik'e tsaye tana bank'arewa Dan Duk jikinta ciwo yake mata saboda bige bigen da tayi,Babalalo ya d'an matsa Dan har lokacin a tsorace yake sosai,ta kalleshi tana k'unshe dariya tace.
"To taimaka ka gyara gurin nan da ya b'aci,zan je na kwanta saboda jikina ciwo yake min ko ina,k'ila fad'uwar da nayi ne yasa hakan,idan nayi bacci k'ila na samu sauk'in ciwon da nakeji".
Da sauri ya amsa da .
" to!to!jeki ki kwanta abinki zan gyara"
"Idan ka kammala abincika yana kitchen sai ka d'auka"
Ta fad'a tana shigewa d'aki.
Tana shigewa ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya fara gyaran wajen da ya b'aci,ya kauda bulalar da Malam Arabi ya gudu ya bari,ko abincin kasa ci yayi,ya d'auro alwala yayi salla yayi addu'o'i sannan yabi lafiyar ledar dake shimfid'e a falon ya kwanta,domin ba zai Iya zuwa d'aki kusa da Habiba ya kwanta ba,yana ta tunani a ransa a haka har bacci yayi nasarar kwasheshi.
Ita kam Habiba tun da ta kwanta a gado take dariya,ta san yadda Babalalo ya tsorata ba zai sake yi mata maganar kishiya ba,Malam Arabi kam ta tsine masa yafi sau shurin masak'i,domin ya d'and'ana mata azabar da ta jima bata ji irinta ba,ji take tamkar harshenta da leb'enta zasu zazzago,duk da dai tayi masa abin da gobe idan an masa tayin zuwa Ruk'iyya sai ya zunduma a guje,saboda mikin da ta asassa masa a bisa Cibiyarsa,da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.
******************
Washegari a gidan Zahra'u aka baje,domin ranar dutin ta ne, a gidanta za a yini a na washshagare walle,Suna baje a falonta su Uku ana shan rake,Zaha'u da Shafa'atu sai Harira da take basu labarin zuwan Maman Samiha gun Sunusi da kashedin da ta bayar,suna ta dariya har Zahra'u ta mik'e ta Shiga d'aki ta d'akko wani turare na tsuguno da Miski ta mik'awa Harira,Ta karb'a tana ajiye raken hannunta sannan tace.
"Wannan fa na menene?
Zahra'u ta zauna ta kalleta tace.
" Harira shawarar da zan baki kidinga gyara jikinki,kin San Allah tunda aka fara da haka wataran zaki nemi masu zuwa kitso ki rasa,kuma dai kin san ba k'aramin rufin asiri kike samu a cikin sana'ar ba,wannan turaren dubu d'aya kenan,ki daure ki siya ki dinga turara k'asanki kina shafa miskin,ina tabbatar miki duk wani wari da d'oyi da kike yi zaki dena,wajen zai dinga k'amshi ko fitsari kika yi sai yayi k'amshi,ko ba don masu zuwa kitso ba kya gyara ko don mijinki yaji dad'i,ke ko Dan kiji dad'in jikinki kya gyara Harira"
Da kyar Harira ta amince zata siya sai da Shafa'atu tasa baki tukun,Zahra'u tana ta cusa musu ak'idar amfani da magungunan mata na mallaka da na jin dad'i,domin a wannan b'angaren tayi zarra,shiyasa k'asimu yake ji da ita,kuma bata b'ata masa rai biyayya take masa kamar ta kwanta ya takata,ta wannan b'angaren kam tafi su Harira wayo saboda bata raina mijinta ba, kuma ta iya siyasa.
Suna nan zaune sai ga Habiba ta shigo kamar an jeho ta,duk suka bita da kallo hankalinsu a tashe ganin yadda leb'enta ya zama lafcece yayi tsawo yana reto,kamar sun had'a baki wajen tambayarta.
"Habiba Had'ari kika yi ne?
Ta zauna tana girgiza kai leb'en na rawa saboda suntumar da yayi,sosai tayi muni kamar wata horuwa,cikin takaici tace.
" ina fa Had'ari!wannan dukan Malam Arabi ne kawai"
"Wane Malam Arabin?ke kuwa wane laifi kika yi masa tashi d'aya ya sauya miki halitta?Habiba kin duba mudubi kinga yadda bakinki ya zama kuwa?sai kace gandar da taji dahuwa a cikin tukunya"
Inji Harira ta ambata tana kallon bakin Habiba da yake k'yalli saboda basilin d'in da ta lafta.
Shafa'atu ta karb'e maganar da cewa.
"Lura dai Harira!ai wannan bakin yafi kama da ragadadar da aka gama dafata aka bajeta a faranti,gaskiya Habiba duk Wanda yayi miki wannan abin yayi miki k'arshen cuta,nifa ba don na sanki sosai ba da wuya na shaida fuskarki,wai!sunan wani gari!wai shi Kumbotso"
Suka k'yalk'yale da dariya.
Habiba ta hararesu tace.
"To!marasa mutunci,idan kun gama yankata sai Ku tsaya na Baku labarin abin da ya faru"
Nan ta Shiga basu labarin komai da komai da ya faru a Daren jiyan,Subhanallahi!dariya dai me suna dariya ranar sun shata har da birgima,shakiyanci iri iri,Zahra'u har da cewa idan K'asimu ya dawo zata sa ya siyo lemo da Ayaba suje su dubo Cibiyar Malam Arabi.
Da sun dubi leb'en Habiba kuma su shek'e da dariya,Shafa'atu ta saita wayarta ta d'auki bakin Habiba hoto wai zata sa a status d'in ta,haka suka addabi Habiba da tsokana kala kala,kuma a ranar ma Saratu bata fito ba saboda gargad'in da Salisu ya gindaya mata,tilas ta hak'ura saboda bata manta da gittar da Salisu yayi mata a muk'amuk'inta ba.
***************
Tana tsaye a soron gidanta daga ita sai zani da k'aramar Riga Duk k'irjinta a waje,babu d'ankwali a kanta,ta d'an sakayo k'ofar ta zuro kanta tana ta lek'en waje da masu wucewa,daga gefen layin nasu wasu yara ne suke ta wasanni suna buga ball,tana ta kallonsu suna kokaye kokaye tana musu dariya,duk da Salisu ya hanata fita ta shiga cikin k'awayenta hakan ma yana d'ebe mata kewa,can yaro d'aya ya hard'e d'ayan da k'afarsa garin buga ball har ya tuntsira ya fasa baki ,nan yaron ya fara kuka,ta tuntsire da dariya ganin jini a bakin yaron tana fad'in "Allah ya k'ara,shegu kun baro Layin Ku kunzo kun addabemu da ball a namu layin"
D'aya yaron ya kama dariya ganin ya FASA masa baki,a fusace wancan ya mik'e ya d'auki wani rank'walelen dutse yana kuka ya saita yaron da ya tureshi ya cillo masa dutsen da nufin jifansa,da sauri yaron ya falla da gudu ya kauce,cikin ikon Allah dutsen bai sauka a ko ina ba sai a goshin Saratu dake lek'e,ji kake Dammmmm!
Bala'in da ya ratsa kan Saratu bashi da misali,har ga Allah ta zaci rodi aka maka mata saboda tsananin yadda dukan ya ratsa ta,a razane ta saki k'ofar soron tayi cikin gida da gudu tana ihun azaba,jini tuni ya wanke mata fuska saboda yadda goshinta ya fashe,tashi d'aya kuma ya kumbura suntum kamar an dasa mulmulallen lemon zak'i,haka ta dinga safa da marwa a tsakargida tana kuka tana tallafe goshi jin yana shirin zazzagowa ya fad'o k'asa Dan har wani zillo yake,ganin jini yana sharara da gudu ta nufi famfo ta Tara fuskar tana wankewa,da k'yar jinin ya tsaya ya dena zuba,amma hawaye bai dena sharara a idanuwanta ba, Dan zafin da take ji kamar wadda a ke dafa k'wak'walwar kanta a kurfoti,haka ta lallab'a ta shige falonta ta ware fanka ta kwanta shame shame ta Shanya k'aton goshinta domin yasha iska......!
*A K'ARA YAWAN COMMENTS FAN'S*🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
08080049548.
[7/28, 10:51] Hassana D'an Larabawa🥰: *TYPING*📲
🏘️ *BAHAGON LAYI* 🏘️
(CHEMIST)
*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR*👇
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*👇
BAHAGON LAYI
*BABI NA SHA D'AYA DA NA SHA BIYU*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*SABODA YARDA KUKA K'AGU SHIYASA NA K'ARA MUKU WANNAN SHAFIN,INA JIN DAD'IN YADDA KUKE SON LITTAFIN,HAR WASU SUNA CEWA WAI DA MA SUNAN LITTAFIN MAGANIN HAWAN JINI😂😂😂JINJINA GAREKU MASOYANA,DAGA YAU SAI BAYAN SALLAH IDAN DA RAI DA LAFIYA🙋🏻♀️🙋🏻♀️🙋🏻♀️MATAN BAHAGON LAYI SUNA JIRAN KU AIKO MUSU DA NAMAN SALLARSU😜😜😜*
Har Yamma da Salisu ya dawo gida Saratu na fama da rad'ad'in goshi da ciwon kai,haka tayi ta b'oye b'oye Dan kar ya gani amma sai da idanuwansa suka gane masa. Ya zuba mata idanu yana tambayarta.
"Me ya samu goshinki haka yayi tulele yayi tsini?
Ta fara inda inda har ta samo amsar da zata bashi.
" Daman fad'uwa nayi a band'aki,santsin sabulu ne ya kwasheni da zanyi wanka shine na buge goshi da bango"
Yayi kasak'e yana kallonta zuciyarsa bata amince da abin da tace ba,saboda ya san ta muguwar mak'aryaciya ce,amma duk da hakan sai ya share ya bita a yadda ta fad'a.
Magriba tayi ya d'aura alwala ya fice masallaci,bai dawo ba sai da ya sallaci isha'i sannan,yana shigowa ya tarar da Saratu tana zagaye a tsakargida,goshinta ya addabeta da ciwo kamar tayi hauka,sai k'ara hawa yake yana kumburi kamar Wanda aka zubawa yeast,ga hawaye yana sharara a idanuwanta,kawai sai yaji tausayinta duk da iskancin da take masa,tsakanin miji da mata sai Allah,ya kalleta sosai yace.
"Wai goshin har yanzu bai sace ba?
Ta gyad'a kai hawaye na k'ara zuba,da k'yar tayi magana.
" K'ara kumbura ma fa yake,ni dai Allah ya tak'aitamin wahala kar na zama mai kawuna biyu"
Yayi d'an murmushi sannan yace.
"D'akko mayafinki muje gun D'ahiru me chemist, ko akwai maganin da zai taimaka ya baki don goshin ya sace kuma ya rage zugin da yake"
Da hanzari ta shige d'aki ta yayimo hijab ta saka suka fita, Salisu ya kulle gidan suka fice daga layin zuwa bakin titin unguwar,Da yake Salisu yana da jiki kuma yana da sauri sai ya shige gabanta ya barta a baya,duk taku d'aya idan zaiyi sai mazaunansa sun juya,Saratu duk da ciwon da take ji hakan bai hanata dariya ba,ganin sai sukutur sukutur mazaunansa keyi,nan da nan ta fara wak'a da Y'ar k'aramar murya tana fad'in.
"Sittin, saba'in,sittin,saba'in,sittin,saba'in"
Salisu yaji kamar magana take yi shiyasa ya juyo yace.
"Magana kike yi ne?
Ta k'unshe dariyarta tace.
" Eh!cewa nayi dama a gaba ka sakani,wallahi kayi min d'irmeme a gaba ko hangoni ba a yi"
Ya zabga tsaki ya juya ya cigaba da tafiyarsa,domin yayi zaton wata magana ce mai muhimmanci,Ashe iskancin da ta saba ne,tana fama da goshi amma ba ta bar shakiyanci ba,Saratu ta k'unshe baki tana dariya har da yi masa gwalo.
Suna isa shagon D'ahiru basu samu jama'a ba sai shi kad'ai,Bayan sun gaisa,Salisu yayi masa bayani,sai ya buk'aci Saratu ta matso ya duba goshin.
Ta matsa kusa da shi ya bata kujera ta zauna,yayin da Salisu ya zauna a wani benci da ke gefe,D'ahiru ya d'akko wata( torchlight) me haske ya haske goshin Saratu,ta runtse idanu saboda hasken fitilar,ba zato ba tsammani Saratu taji D'ahiru ya kai Hannu ya latsa goshin da d'an k'arfi,wani shahararren ihu ta saki tare da bud'e idanuwanta ta mik'e a gigice saboda zafin da ya ziyarci k'wak'walwar kanta,ba tayi wata wata ba ta fidda Hannu ta zabgawa D'ahiru wani bahagon mari har sai da hular kansa ta fad'i shi kuma ya tuntsira k'asa hajijiya na d'ibarsa.
Salisu ya mik'e a firgice yana dafe kunci kamar shi aka Mara,cikin tsananin tashin hankali ya dubi Saratu dake maida numfashi yace.
"Saratu baki da hankali ne?kin san abin da kika yi kuwa?ko kin sha kayan maye ne?
" Eh!Burkutu nasha,wadda ka sha ka rage min a matsayin karin kumallon safe ba,banda shi mugu ne azzalumi ta k'ak'a ina fama da goshi na zai k'arasa b'urma min shi,Ashe ba k'arya bane da ake cewa likitoci azzalumai ne,to in yayi wa wasu mugunta ya kwana lafiya ni yayi kad'an in k'yale shi, wallahi daddala masa mari zanyi, in sace masa k'aton kumatunsa mai kama da naka"
Salisu Haushi da takaici ya kamashi ya nufota kamar zai dake ta,wai me yasa komai a ka had'a da jaki sai yaci kara?Da sauri D'ahiru ya mik'e jikinsa a sanyaye saboda Marin ya shige shi ba kad'an ba,Dan shi a zatonsa ma ya makance Dan tsinin D'an yatsanta saida ya tab'a idon sa,amma da yake mutum ne mai yawan Hak'uri sai ya fara bawa Salisu hak'uri,ya d'ora laifin a kansa a matsayin hannunsa ne ya kufce har ya danna mata goshin da k'arfi.
Tilas Salisu ya koma ya zauna yana ta numfarfashi,ba k'aramin b'ata masa rai Saratu tayi ba,ji yake kamar ya sake yi mata gittar da yayi mata randa ta ambato Mahaifiyarsa,in yaso ya bajeta a chemist d'in kowa ya huta.
Shi dai D'ahiru dole ya hak'ura da tab'a goshin Saratu ,kawai ya harhad'a mata magani da na sha da na shafawa,sannan ya juya ya dubi Salisu yace.
"A bayaninka da kuka zo kace min fad'uwa tayi a band'aki ko?to gaskiya abin da nagani wannan goshin nata ba fad'uwa bace,Marmara ce ta kawo masa ziyara,da alamun wani muk'ek'en dutse ya sauka a gurin"
Hankalin Saratu ya tashi jin maganar D'ahiru,haka kawai zai tona mata asiri,shiyasa ta figi ledar maganinta ta zabga tsaki ta kalli Salisu tace.
"Idan ka gama sauraron k'aryar da yake shirga maka ka biyoni ,ni dai nayi gaba"
Ta fice daga shagon tai tafiyarta,sai da taje k'ofar gidan ta Ganshi a kulle sannan ta tuna Ashe mukullin na hannun Salisu,tilas ta tsaya tana tsaki ku san minti goma sannan ya k'araso,kallon banza yayi mata yasa mukullin ya bud'e gidan,ita kam k'eya ta juya masa,tana ganin ya shiga ta bishi a baya ta na yiwa k'eyarsa gwalo.
Da suka shiga sosai ya dinga yi mata fad'a akan Marin da tayi wa D'ahiru me chemist,sannan ya fara tuhumarta ya akayi aka jefeta a goshi?amma Saratu ta gaddame akan D'ahiru k'arya yake yi kawai fad'uwa tayi.
Tilas ba don ya yarda ba ya k'yaleta ya shiga sabgar gabansa.
**************
Sati d'aya bayan hakan leb'en Habiba da goshin Saratu ya warke,haka nan babu abin da ya sauya a hallayarsu ta tumasanci da akuyanci,sunk'i hankali su gane hanyar dai dai.
Zahra'u ce ma ta d'an fisu hankali,domin ko ranar dutin ta da zarar yamma tayi take korarsu gidajensu,saboda bata son b'atawa K'asimu rai ko kad'an,ta yarda suyi shargallensu amma bata amince a Shiga hakkin mijinta ba.
Ranar ta kasance Lahadi,suna zaune gabad'ayansu a gidan Safa'atu,har da Saratu da ta samu fitowa saboda Salisu baya nan ya tafi d'aurin auren wani Abokinsa a Katsina,Hira suke sha suna gulmar yadda suka ga ana shigowa da kaya na garari da za a jerawa amaryar da zata tare a d'aya gidan,a labarin da suka samu mijinne bai k'arasa gininsa ba,shi kuma mahaifin amarya yana so ya had'a bikinta da na yayarta,shine dalilin da mijin yazo ya kama haya su zauna na wani d'an lokaci kafin ya kammala NASA ginin,daga ganin kayan da ake shigowa da su Jere sun san yarinyar Y'ar gata ce,kuma ance mijin yana da abun hannunsa sosai,da alamu zasu dinga sharb'ar romon dimukrad'iyya kenan,musamman idan suka yi nasarar janyota cikinsu.
Harira ce ta shiga kitchen d'in Shafa'atu da niyyar d'ora musu girki,garin tab'e tab'enta ta hango bak'ar Leda da kifi a cikinta,ta k'walawa Shafa kira tana cewa.
"Au Shafa wasa tare ci bambam ko?da ban shigo kitchen d'in ba ba zamu San kina da kifi ba balle ki bamu rabon mu,to Allah ya toni asirinki"
Shafa'atu ta taso tana k'ok'arin fizge ledar tace.
"Rufamin asiri Harira!wannan kifin da kika gani Kamilu ne ya siyo wai in yiwa Goggo Zulai farfesu da daddare za mu je dubata bata jin dad'i,Dan haka bani nan ba nawa bane na Uwar masu gida ne"
Harira ta danna mata Harara tace.
"Kutri!Ai ba Goggo Zulai ba wallahi ko Zulailaya me kan tantabara ce sai munci kifin nan,ke kin san ko mage ta saramin wajen k'aunar kifi, Dan haka ja jiki Malama wannan kifin haramiyar uwar masu gida wallahi"
Ba irin magiyar da Shafa'atu bata yi ba amma suka hanata,tana ji tana gani suka sarrafa kifin nan aka saka a dafadukan taliya me manja da romo,kan kifin kuma Zahra'u taje ta d'akko k'uli k'uli suka daka kafikaza suka sa a ciki,Shafa'atu dai tunanin k'aryar da zata yiwa Kamilu kawai take yi,ya siyo Abu Dan mahaifiyarsa amma sun cinye.
Basu bar gidan ba sai da suka ga dawowar Kamilu yamma lik'is,kowacce ta shuri silifanta tayi gaba,suka bar Shafa da susar k'eya da Neman abin da zata kare kanta.
Har Kamilu ya shirya bayan dawowa daga sallar isha'i,ya nemi Shafa'atu ta d'akko mayafinta su wuce tuni ya karb'o Aron mashin d'in abokinsa,ta tsaya nuk'u nuk'u,ya nufi kitchen yana cewa.
"A wane flask kika zuba farfesun ne?zo kibani in saka a Boot saboda kar ki rik'e a Hannu romon ya Zube"
Jiki a sanyaye tace.
"Nifa ba wani farfesu da nayi"
Ya juyo a hanzarce yana dubanta yace.
"Kamar ya ya ba wani farfesu da kika yi?ban gane ba"
Ta d'an zumb'ura baki ta Sosa k'eya tace.
"To ba muna ciki muna hira ba bamu sani ba Ashe magunan bayan layi sun shigo sun shiga kitchen d'ina sun cinye kifin"
"Kan uban can!kifin mahaifiyar tawa ne maguna suka cinye?magunan bayan layi ko magunan k'awayenki,amma Shafa kin mugun rainamin ajawali,ki Tara d'ima d'iman mata Ku cinye kifi kizo ki ce min wai maguna sun cinye?ni sa'an wasanki ne da zaki kawo min d'ibar albarka?
Shafa ta cono baki ta fara maganganu.
" Kaga Kamilu kar ka nemi ka zageni akan kifin da bai wuce na d'ari uku ba,ka jirani zuwa gobe zan biyaka d'ari ukun ka Dan kar ka kaini gaba"
Ta saki mugun tsaki ta shige k'uryar d'aki ta barshi da Baki a sake,tsananin mamakin k'arfin halin Shafa'atu ya kid'ima Kamilu.
********"****
Akuyar d'aure ta samu sake!
Tun bayan da suka fito daga gidan Shafa kowacce ta shige Gidanta amma banda Saratu,kawai sai ta shige gidan Amarya da ta tarar ana dandazon Shiga duk dangin amarya da Ango sun cika layin,ta nemi guri ta rashe har aka kawo amarya,ita a ganinta tunda Salisu Katsina ya tafi sai Can dare zai dawo,bata san cewa tuni ya dawo ba kuma ya tarar bata nan,hakan ya harzuk'ashi ya tafi gidansu Saratun ya fad'awa Mahaifinta duk irin wulak'anci da rashin mutuncin da take yi,Sosai ran Malam Munzali me almajirai ya b'aci,ya umarci Salisu ya tashi su tawo gidan tare.
Har suka zo Saratu bata dawo ba,Malam yace su tsaya k'ofar gida suga ta inda zata b'ullo.
Saratu kam Sai wajen taran dare sannan ta Ankara, da sauri ta mik'e ta yiwa mutanen sallama ta fito Dan Shiga gidanta.
Gabanta ya buga dammm!ganin Salisu da Mahaifinta a k'ofar gidanta a tsaye sun zubo mata idanu......!
*GODIYA GAREKU MASOYANA*🌹💃😍😘🥰
0 comments:
Post a Comment