Jikinta ya kama karkarwa k'afarta na rawa,tuni idanuwanta suka ciko da hawaye saboda ta san Mahaifinta ba yayi mata da wasa,kallon da yake mata kawai a yanzu haka ya isa yasa hantar cikinta kad'awa.
Malam Ya maida kallonsa kan Salisu yace.
"Idan akwai mukulli a hannunka bud'e mu shiga"
Salisu cikin sunkuyar da kai ya amsa da "To Malam" Sannan yasa makullinsa ya bud'e gidan.
Malam ya kalleta fuska a d'aure yace.
"Zo ki shige mutuniyar Banza,kina yawo k'afa kamar kwarkwaro"
Jikinta na rawa ta rab'a ta shige tana Hararar Salisu ta k'asan idanuwanta.
Suka bita a baya har zuwa cikin gidan,tana niyyar bud'e d'akin nata Malam ya daka mata tsawa da cewa.
"Dawo nan Dan ba shiga d'akinki zan yi ba,Mara kunya fitsararriya"
Ta dawo tana sosa kai ta tsuguna,yayin da Salisu ke tsugune shima kansa a sunkuye,cikin matuk'ar b'acin rai Malam ya soma yi mata fad'a.
"Ba k'aramin mamaki kike bani ba Saratu,Mamakin bai wuce na watsar da kyakkyawar tarbiyyarki da kika yi ba kika aro mummuna kika yab'awa kanki,Allah shine shaidata na baki tarbiyya ta gari na baki ilimi na addini Wanda zai miki jagora zuwa bautar ubangijinki da bautar aure,amma a yanzu duk kin watsar babu abin da kike yi sai zaluntar mijinki da munana masa,tun yana hak'uri dake har kin kaishi mak'ura yazo ya sanar dani komai,Saratu kin san yawan zunubin da mace ta ke samu idan ta sake ta fita ba tare da izinin mijinta ba kuwa?kin san yawan zunubin da mace take d'auka akan wulak'anta miji da lek'e idan baya nan?Saratu idan baki yi tunanin ta nutsu ba zaki kai kanki wutar jahannama,mace tayi biyayyar aure tabi Allah da manzonsa ma amma Allah yana jarrabarta balle ta k'etare dokokin sa,kiyi duba ga mahaifiyarki ta zame miki izna a rayuwarki,tabi Allah da manzonsa ta tsare hak'k'ok'in aure yadda ya kamata,ta kasance mace mai bin umarnina da yi min biyayya da kaucewa b'acin raina,amma duk da hakan Allah ya d'ora mata lalurar da ko tashi zata yi sai an d'agata,to ke da kike k'etare iyakokin Allah da na aure idan Allah ya tashi jarrabarki kin san wace irin jarrabawa zai miki?Ba yau na fara yi miki nasiha da fad'a akan munanan halayen da kike ba,amma inason in shaida miki wannan ne na k'arshe,Annabi (S A W)ma ya umarci d'iyarsa Fad'ima (R A)tayi wa mijinta sayyidina Ali (R A)Biyayya,duk da kasancewarta mai girma d'iyar masu girma,ba ke ba karankad'a miya tasono dake,Annabi (S A W)yace"Da Allah zai umarci wani yayi wa wani sujjada,to da ya umarci mace ta yiwa mijinta sujjada"Saboda tsananin girman miji a wajen matarsa,Dan haka ki maida hankalinki Saratu,wannan ita ce hanyar aljannarki,domin aljannar taki tana k'ark'ashin k'afar mijinki,wallahi tallahi idan kinga kin shigeta to sai dai idan ya d'aga miki,to ta ya ya zai d'aga miki kina cutar dashi kina zaluntarsa?ita zuciya ai an halicceta ne ga son Wanda yake kyautata mata,haka nan ga k'in Wanda yake munana mata,duk randa kika yi sake ragowar k'imarki ta zube a idanuwan mijinki kin kad'e Saratu,domin ba zaki tsira da komai ba,kuma ko a lahira ni kaina mahaifinki ba ruwana dake,Dan haka ina yi miki nasiha da kiji tsoran Allah,ki sani Allah yana kallon dukkan abin da kike aikatawa,maganata dake ta k'arshe ita ce, Muddin kika sake Salisu ya gaji da halayyarki ya koroki gida ya sake ki to fa tabbas zaki d'and'ana kud'arki,ba zan koreki a gidana ba saboda ni Mahaifinki ne,amma wallahi zaki gwammace zaman kurkuku da zaman da za kiyi a gidana,wannan ce maganata dake ta k'arshe,ya rage ruwanki ki gyara ko ki cigaba da aikata munanan halayenki,(Imma shakiran,wa imma kafura).
Malam yana kammala maganarsa ya dubi Salisu yace.
"Kai kuma ka cigaba da hak'uri,Sannan ka cigaba da nuna kai namiji ne mai cikakken iko a kanta,kai Allah ya bawa kiwonta,kuma ka tabbata kaima Allah zai tambayeka akan kiwon da ya baka,ka lura da wannan,Ni zan wuce,Allah ya sadamu da alkairinsa"
Saratu tuni jikinta yayi sanyi akan nasihar mahaifinta,har k'walla ta ciko idanuwanta,da sauri ta mik'e ganin mahaifin nata ya nufi k'ofar fita, Salisu ya mik'e ya bishi a baya Dan ya rakashi,da k'yar ta fizgo magana a bakinta da sauri tace.
"Baba nagode, a sauka Lafiya a gaida Umma"
"Madalla" Kalmar da malam ya Amsawa Saratu kenan suka fice a gidan suka barta da sanyayyun k'afafuwa ta na muzurai.
***************
Kwana biyu da hakan har Saratu ta fara nutsuwa ta dena wad'ansu Abubuwan,kuma ba laifi tana jin maganar Salisu,sai dai fa tana jinta a takure sosai,ba lek'e ba zuwa gidan k'awaye shan shafta.
Su ma k'awayen suka ji shirun yayi yawa basa ganinta,gashi sun shirya shiga gidan Amarya domin su gabatar mata da Kansu,tun washegari suka so shiga amma suka d'aga k'afa,su kuma basa son Shiga ba tare da Saratu ba,burinsu su Shiga gabad'ayan su,hakan yasa suka had'u a gidan Habiba suka tattauna akan gara suje su gano ko lafiya Saratu shirun yayi yawa,ko wayarta aka kira ba a samunta,sun san dai a wannan lokacin Salisu baya gidan ya tafi kasuwa balle suyi Arangama da shi.
Suna fitowa suka hangi Malam Arabi zai wuce ta layinsu,da sauri Harira ta tab'o Habiba tana dariya tace.
"Habiba ga mutuminki fa"
Duk suka kalleshi ganin yadda yake sauri gemunsa yana tsalle suka tuntsire da dariya,Malam Arabi ya saci kallonsu jin dariyarsu ya k'ara sauri yana d'aga k'afafu yana zungura k'eya,gudun ma kar su kulashi,domin ya san magana ta bazu a unguwar akan Cizon da Habiba ta gallara masa a Al'aura,amma ina!bai samu nasarar Hakan ba,domin kuwa Zahra'u ce da azamarta ta fara k'wala masa kira.
"Malam Arabi,Malam Arabi,Malam Arabi...!
Yayi musu banza kamar bai jisu ba yana k'ara sauri,amma sai da suka had'a da sassarfa suka cimmasa suna shan gabansa.
Ya d'ago yana harare harare yana satar kallon Habiba,matar da ta haifar masa da jinyar Cibiya yana zaman zamansa,Zahra'u ce ta fara zubewa tana gaisheshi,da k'yar ya amsa yana basarwa yana kau da kai yace.
" Ya akayi..?Lafiya dai ko..?
"Lafiya k'alau Malam,Daman muna ta shirin zuwa mu dubaka,Ashe abin da ya faru kenan Malam?to Allah ya tsare gaba ya kad'e tsautsayi da Asara"
Zahra'u ta ambata tana k'unshe dariyar ta.
Malam Arabi ya k'ara had'e rai ya karkata hularsa gefe yana muzurai kamar bai gane me take nufi ba yace.
"Me fa? Me kuma ya faru?ko ance muku bani da lafiya ne?
Harira ta kama hab'a tace.
" Yo Malam muna magana ne akan Aljanun Habiba da suka so tsige ma Cibiya fa,bamu ji dad'in abin ba Malam,Gashi k'anwata ma tana fama da Aljanu muna shirin kawota gurinka a taimaka ayi mata Ruk'iyya Malam,kuma wall...
"Ku bana son d'ibar albarka...
Malam Arabi ya katse Harira cikin sababi yana zare idanuwa da makyarkyata,sannan ya d'ora da cewa.
"Da man labarin da nake ji a kanku gaskiya ne ba k'arya ba? Wato rashin mutuncinku da iskancinku yazo kaina kenan?ni zaku kawowa shakiyanci?na fi ku iya shakiyanci da iskanci,nan da kuka ganni D'an iska ne Lamba d'aya,ni k'olo ne a fagen iskanci,gardi ne a rashin mutunci,Dan haka Ku saita kanku ku kama kanku,in ba haka ba yau idan na hau buzu na billahillazi huwar rahmanu a kanku zan kwana,Girman Allah Yaseen mai dabaibayi da waraddallahu zan ta ja muku,,Allah ya dandab'en min ku,Aradun Allah washegari daga wadda zata tashi a makance,sai wadda zata tashi a lauye,sai wadda zata tashi a k'andare,sai wadda zata tashi a mokad'e,kushiga Hankalinku dani ba a yi min irin wannan,Yanzu sai na maida mutum abin kwatance,Y'an iska kawai gafalallu marasa daraja,Ku jira Ku gani k'arshenku ba zaiyi kyau ba indai Baku sauya hali ba,lalatattun banza lalatattun wofi masu cin Amanar mazajen su"
Ya juya ya kalli Habiba duk da a tsorace yake,yace.
"Ke Kuma tsinanniya matsiyaciya haddina da kika keta min kika cafkar min Al'aura na barki da Allah,yadda kika sa min jinyar Cibiya banji ba ban gani ba insha Allah sai Cikinki ya kumbura Yayi bindiga yace Tushhhhhh....!Lalatacciyar wofi kawai.
Yana fad'in hakan ya wuce fuuuu!yana ta sababi yana cilla hannaye,nan kuwa tsabar kunya ce ta rufeshi,ga Shakkar Habiba da yake ji,don kallon da take masa a lokacin zata iya cafko mak'wallaton wuyansa ma ba Cibiyarsa ba.
Yana wucewa suka kwashe da dariya har da tafawa.
Harira tace.
" Tsinanne mai kama da alade borin kunya fa yake,Gaskiya Habiba kin gurji mutuminnan da yawa,ku dubi gingimemen tumbi irin na Malam Arabi, amma Cizo yasa cikin ya koma Yayi lak'wam"
Suka kuma bushewa da dariya suka nufi Gidan Saratu,Habiba na fad'in.
"Duk gurzar da nayi masa ai bata kai wadda Yayi min ba,kai mutuminnan baida imani ko kad'an Harira,iya k'arfinsa ya zage ya dinga laftar bakina,sanda ya sakar min bulalar nan wallahi na zaci bom aka tayar a bakina,saboda shine shugaban mak'aryata na duniya har da cewa Babalalo wai yaga aljanu a bakina suna rawa da juyi,Allah ne ya taimakeshi ya tunkud'eni amma da niyyata yadda na cafki Cibiyar nan wallahi sai na tsigota,da man gata doguwa Allah yai masa Cibi"
"Shaharani kenan" Shafa'atu ta ambata lokacin da suka shiga gidan Saratu suna k'wala sallama.
Zahra'u ta d'aga murya ta na fad'in.
"Kina ina ne Mace me lek'e,Ko nace Y'ar Malam tak'i halin Malam,fito gamu munzo biko"
Saratu da ke d'aki ta na had'a kayan wanki ta jiyo muryar manyan Aminanta,da sauri ta cillar da kayan ta fito tsakargida da gudunta har zaninta na shirin fad'uwa.
Comments
Share
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
[8/6, 09:42] Hassana D'an Larabawaπ₯°: *TYPING*π²
π️ *BAHAGON LAYI* π️
(GIDAN AMARYA)
*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR*π
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*π
BAHAGON LAYI
*BABI NA SHA BIYAR DA NA SHA SHIDA*
Follow me on watpad Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
π *PEN WRITERS ASSOCIATION*π️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
SADAUKARWA GA:
*HASSANA D'AN LARABAWA FANS,WANNAN SHAFIN KU NE KYAUTA A GAREKU MASOYANA*πΉπΉπΉ
Ta na zuwa ta fad'a jikinsu ta na dariyar ganinsu,suka rungumeta suna dariya suna kallonta,Harira ta nufi ktcheen tana bud'e kwanuka ta na fad'in.
"Me zan samu ne?nifa kwad'ayi nake ji yau tunda safe wallahi na rasa abin tab'awa"
Ta bud'e tukunyar da ke kan risho ta lek'a,da sauri ta d'ago tana b'ata fuska tace.
"Wannan gardin fa Saratu?bak'ik'k'irin da shi kamar d'uwaiwan mijinki....
Saratu ta waigo ta harareta tace.
" Harira shugabar y'an iska ta duniya,d'umamen tuwon ne me kama da mazaunan mijina?to babu kyau dai wulak'anta abinci domin wani yana nan yana nema"
Ta rufe tukunyar ta na tab'e baki ta fito rik'e da k'ugu,sannan ta kalli Saratu ta shek'e da dariya tace.
"Au Saratu wai nan kece maiwa mutane wa'azin babu kyau wulak'anta abinci?yau Saratu kece kika dafa tuwo a tukunyarki?kamar ba kece Y'ar malam tak'i halin malam ba?kamar ba kece kwanaki da Salisu ya siyo dawa kika bayar aka nik'o kika kwab'a garin kika juye shi a Masai ba?a k'ok'arin ki na ki tabbatar masa bakin ki ba zai ci tuwo ba sai shinkafa da taliya?ni yau sai naga duk kin canza Saratu,da alamun idanuwanki sunyi Arangama da Malam kunnuwanki sun sha wa'azi ko?
Saratu ta sauke ajiyar zuciya ta shige falonta,duk suka bita a baya suka samu waje suka zauna,amma Harira na tsaye k'ik'am,idanuwansu akan Saratu suna jiran jin maganarta domin alamu sun nuna bakin nata akwai magana.Ta gyara zamanta kafin tace.
" Kamar yadda kika fad'a ne Harira,tabbas Malam yazo gidannan kuma Yayi min maganganu masu shiga jiki,ya tsoratar dani sosai wallahi,shiyasa kwana biyu bakwa ganina ina fitowa,sannan D'an lek'en da na saba ma duk na daina,duk da ina jina tamkar a kurkuku,kuma kamar wadda aka sawa mari aka d'aureta,amma ina ganin duk da hakan gara mu hak'ura da yawace yawacen gidajen juna,kowacce ta zauna a gidanta tayi zaman aure,mu gyara alak'armu da mazajenmu,a hankali zamu saba har ya zame mana jiki,idan ba haka......
"Dakata Saratu....
Habiba ta katseta tana d'aga mata Hannu,sannan ta cigaba da magana tana k'ank'ance idanu.
" D'an k'aramin wa'azin da Malam me almajirai Yayi miki shine ya karya miki zuciya haka?to bari kiji yanzu muka sa d'amba wallahi,duka shekarunmu nawane da za a kime mu a gida a hanamu rawar gaban hantsi,mu dai ba sata ko yawan iskanci muke zuwa ba,ba kuma wani layin ko gidajen muke tafiya yawan gulmace gulmace ba,abin mu iya imu imu ne,in zaki farka daga barci ki farka,in kuma wa'azin Malam ne yasa jikin tak'aura Yayi la'asar shikenan ,mu dai yau ma nan da kika ganmu Gidan Amarya zamu antaya,in kinga zaki bimu ki tashi kisa kayanki,in kuma ba zaki ba mu d'aware mu barki,mu dai yau a Gidan Amarya zamu wuni sai mun maida k'walamar mu"
Habiba na direwa Shafa'atu ta d'ora da cewa.
"K'warai kuwa Habiba,Dan wallahi yau bakina ba d'ad'anon da yake son ji sai na dankalin turawa,Allah dai yasa Angon ya siyo"
Zahra'u ta karb'e zancen da cewa
"ke kuwa Shafa me zai hana ya ajiyewa Amarya dankalin turawa,kinga kuwa nima ina marmarinsa yau idan nayi ido biyu da shi cin k'oshi zan masa billahillazi"
Harira ta kwashe da dariya ta na fad'in.
"Ku jini da Mayun yara,wato kun sa rai za ku ci dankali ko?
Ta k'ara juyawa ta kalli Habiba tana dariya ta cigaba da cewa.
" Ke Habiba shugabar mayu ta afrika ba zaki ci dankalin turawan ba?ko da yake kin fi kauri wajen maitar Diddigar k'uli k'uli ko?
Ta mak'e murya ta na tsokanar Habiba.
"Baba da Diddiga"?
Suka kwashe da dariya suna kallon Habiba,Habiba tayi tsaki tana kau da kai.
Nan suka maida hankali kan Saratu suna ta zuga ta akan ta watsar da wa'azin Malam kawai ta bisu,in yaso sai ta dawo da wuri kafin Salisu ya dawo daga kasuwa,Shafa'atu har da cewa.
" Ni nan da kika ganni ma bak'i zan yi,k'annen Kamilu ne su biyu za su zo yau,tun jiya yake jaddadamin ,amma wallahi ba zan zauna ba sabgar gabana zan tafi,idan sun zo su jirani a k'ofar gida in zasu jira"
Haka su kayi ta zuga ta,amma Saratu tsoro ya cika zuciyarta ta na jin tsoron binsu,gashi tana son aje gidan Amarya da ita a wargaje ,da suka ga tak'i amincewa sai suka k'yaleta suka mik'e Dan tafiya.
Shaed'an ya cigaba da tunzira zuciyarta yana yi mata sak'e sak'e,yana raya mata kar ta yarda a tauye mata hakki,ita Y'ar Adam ce mai cikakken iko da y'ancin yin abin da ta zab'awa rayuwarta,ga su Harira nan babu Wanda aka tauye sai ita?kawai ta tashi ta bisu idan yaso sai ta kiyaye ta iya takunta.
Har sun je Soro ta k'wala musu kira ta tsayar da su,da Hanzari ta zura kayanta tazo ta tarar dasu, suna tayi mata tsiya wai"waya gaya mata borno gabas take"
Saratu tayi dariya,suka fito ta kulle gidanta ,sannan suka nufi gidan Amarya.
***********
Suna ta bin falon da kallo har ta k'araso ta dire musu ruwa da lemon da ta d'akko musu a fridge d'in ta,sannan ta zauna kan kujera ta dubesu da k'ayataccen murmushi akan fuskarta ta gaishesu.
Har rawar baki suke wajen Amsa gaisuwar ta,suna washe baki,ta zuba musu lemon ta basu kowa a cup,babu alkunya suka karb'e kowacce ta kai bakinta ta shanye,suna tand'ar baki.
Wucewar minti d'aya Harira tayi gyaran murya ta gyara zama,sannan ta dubi Amarya tace.
"Bari na gabatar miki da kanmu tunda na san baki sanmu ba kuma baki ganemu ba,ni dai sunana Harira me kitso,wad'annan kuma ga Habiba,ga Shafa'atu,ga Saratu ,ga Zahra'u,dukkanin mu a wannan layin muke zaune kowacce da gidanta,kuma duk mun saba da juna ke ce sabuwar zuwa shiyasa muka ce zamu had'u mu shigo Dan mu gabatar miki da kan mu ki sanmu zumunci ya k'ullu tsakaninmu"
Amarya tayi murmushi kanta a k'asa saboda kunyar amarci,cikin sanyin murya ta fara magana.
"Amma nayi farinciki da zuwanku,daman nima ina da niyyar Shiga gidajenku idan an kwana biyu,to sai gashi kun rigani zuwa ma,to ni dai sunana Hauwa'u,kuma ina fatan zaku rik'eni Hannu bibiyu a matsayin ku na yayyena wad'anda suka girmeni ,sannan ina fatan zumuncin mu ya d'ore ku dinga saitani a hanya da zarar kunga zan kauce"
Habiba tayi dariya tace.
"Ashe ma sunan kakata ne dake,kulun majadan Y'ar tsohuwa me ran k'arfe,to ki shirya za ki bani kud'in shara kuwa,kuma kar ki damu da Hannu d'ari zamu rik'e ki ba hannu biyu ba,ke dai kawai ki saki jikinki damu rayuwa muke mai dad'i babu takura kai"
Ta jinjina kai tana murmushi a lokacin da suka ji sallamar Mijinta,ya shigo falon rik'i rik'i da ledoji,su Harira aka had'a baki ana gaisheshi,ya amsa yana murmushi duk da dai bai sansu ba,Amarya ta mik'e tana kwarkwasa da yanga ta nufeshi ta karb'i ledojin hannunsa,ya sakar mata murmushi yana d'aga mata gira,Su Habiba aka saki baki ana kallonsu ana k'iftawa juna idanu,Yana shirin wucewa d'aki Amarya ta fara magana cikin yanga ta na yi Masa bayanin su Harira,ya washe baki ya juyo yana yi musu godiya, ganin ya samu masu kula masa da matarsa da yake tsananin so da k'auna.su kam dad'i suka ji ganin yadda ya sakar musu fuska,Saratu kam kallo take ta bin su da shi bakinta a sake har suka shige d'akinsu suka barsu a falon.
Zahra'u ce ta lura da Saratu da hankalinta ya tafi wani wajen,ta d'aga hannunta ta zubawa Saratun d'ad'o a cinya,firgigit ta dawo hayyacinta tana sosa cinyar da sauke ajiyar zuciya,duk suka dubeta suna tambayarta da idanuwansu.
Tayi murmushi ta rage murya a hankali tace.
"Wallahi mutuwar ido biyu nayi fa!kunga mijinnata wani D'an sumulmuli da shi ,sai naji gabad'aya na k'ara raina Salisu wallahi,gaskiya wannan ta cab'a da yawa,sullutuwa kenan"
Zahra'u ta doke bakin Saratu tana harararta tace.
"Amma Saratu baki da hankali wallahi,da aurenki ki dinga yaba mijin wata?nifa duk iskancina Bana tab'a mijina ya kamata ki dinga lura,kullum cikin raina Salisu kike kuma ni banga aibunsa ba,nifa duk munin mijina ganinsa nake yafi kowane namiji kyau a idanuwana"
Duk suka yi dariya a hankali,Harira ta cafe zancen tana kallon Zahra'u.
"Kinga Zahra'u nifa banga laifin Saratu ba Dan ta fad'i ra'ayinta,gaskiya da nice Saratu ba zan tab'a bari malam me almajirai Yayi nasara a kaina wajen tursasani auren gardi irin Salisu ba,Nifa har bana k'aunar na had'a ido da shi sai na ganshi tamkar damisa a gabana,ai Saratu kam kina hak'urin zama da Salisu har ki kalleshi a matsayin miji,wai!ni da titib'iri..."
Suka kwashe da dariya,Saratu ta kalli Habiba tace.
"Habiba ba babban Mara mutunci irin Babalalo ,Dan Allah kice masa idan Salisu yazo aski wajensa ya daina yi Masa tal kwabo,billahillazi huwar rahmanu rannan da Yayi masa ya shigo min na zaci bayan k'warya ya kifa a kansa saboda yadda Yayi tol da shi,nayi mamaki nace masa" kai kuma ina ka samo k'warya ka kifa a kanka kamar wata hula"ya shafa kan yana dariya yace "Ke Hajiyata Aski na sha fa,malamina ne ya bani sa'ar wani magani yace idan nayi Aski na shafe kaina da maganin,idan na fita duk budurwar da naci karo da ita rud'ewa za tayi a kaina tamkar na kwanta taita lasar Tolin kaina,budurwa zan samu zakad'ed'iya wadda zata tarairayeni ta riritani" dariya ta kamani kamar me,nace masa"Amma duk budurwar da zata ganka da wannan tuk'ek'en kan yasha soli taji ta na sonka ta d'ibga asara wallahi.
Domin ni banga abin so da sha'awa a wannan k'walelen kan kamar duro ba"
Suka kwashe da dariya jin maganar Saratu,gaskiya ta na cin fuskar Salisu da yawa.
A dai dai lokacin Amarya da Ango suka fito,su Harira a kayi k'us ana sunkuyar da kai,Yayi musu sallama da shirin wucewa kasuwa,Harira ce kan gaba wajen yi masa fatan dawowa lafiya,abin da bata yiwa nata mijin.
Amarya ta dawo ta zauna bayan ta rakashi har bakin k'ofa,suka cigaba da hirar duniya da labarai kala kala,tun bata sake ba har ta sake ta fara kwasar dariya kamar cikinta zaiyi ciwo saboda hirar da suke,da alamun matan suna da abin dariya sosai,suna zaune har azahar tayi babu shirin tafiya,Amarya ba taji wani Abu a ranta ba ganin sun shantake babu wadda ta nemi komawa gidanta,ganin kar ta barsu da yunwa sai ta mik'e domin shiga kitchen ta d'ora girki,ta d'ebo kayan miya za ta gyara nan da nan uwar kankanba Harira ta mik'e ta amsa ta na cewa.
"Bari na gyara miki Amarya, mu na zaune ai ba ma bar Amarya da aiki ba"
Tayi murmushi ta mik'a mata ta na cewa.
"Ai da kin barshi na gyara,kar na saki aiki,gashi Hubby ma ya fita bai mik'a min markad'en ba,ba wuta balle na markad'a a blender"
"Har kin samu Almajiri D'an aike kenan?"
Habiba ta tambayeta.
Ta amsa ta na k'ok'arin d'akko tukunya a drawer d'in kitchen.
"Ah ah me kika gani?"
Habiba tayi Hamma saboda yadda cikinta ya fara kiran ciroma tace.
"Naji kince Hubby bai kai miki markad'e ba,na zaci Almajinki ne Hubby d'in"
Amarya tayi dariya sosai sannan ta dubi Habiba tace.
"Haba dai!Almajirin zan kira da Hubby?ina nufin mijina fa,Hubby ai sunan Soyayya ne"
Zahra'u ta shek'e da dariya ta na fad'in.
"To ke Amarya waye ya fad'a miki Habiba ta san wani sunan soyayya,yadda kowa yake ambatar mijinta Babalalo ita ma haka take ambatarsa,dukkansu nan babu wadda take b'oyewa mijinta suna sai ni kad'ai,domin ban raina mijina ba,shiyasa na mallakeshi a hannuna sai yadda nayi da shi "
Duk suka fara hararar Zahra'u,yayin da Amarya ta matso ta zauna kusa da ita ta na washe baki da fad'in.
"Gaskiya Anty Zahra'u tafiyarmu ta zo d'aya,Dan wallahi kinga dai ban dad'e ba amma ina masifar son mijina kuma ina son na mallakeshi sai yadda nayi da shi,duk fara'ar nan da kuka ga yana yi muku shi mutum ne mai baud'ad'd'en hali wani zubin,duk soyayyar da yake min zan iya yin laifi ya rufe idanu yaci zarafina,to ni kuma bana son ta kaimu ga haka gara ki d'orani a hanya yadda zan mallakeshi kamar yadda kika mallaki mijinki"
"Anzo gurin Hajiyata" Zahra'u ta fad'a ta na mik'a mata Hannu suka tafa, ta nuna sauran da bakinta ta na duban Amarya tace.
"Kin gansu nan babu yadda banyi na d'orasu a hanya ba amma sunk'i,sun riga sun sawa zuciyarsu cewar ba zasu tashi tsaye su mallaki mazajensu ba wai gara suci uwar juna,basu san y'an alallab'a bane,sai da siyasa ake kamasu,mazan yanzu ba k'ananan y'an iska bane sai da wuta"
Saratu ta tab'e baki tace.
"Ni dai da na tsaya mallake Salisu gara na siyo D'an bunsuru na ajiye shi na mallakeshi Yayi min biyayya wallahi,yo ni kam meye abin mallaka a Salisu banda d'ibga asara?
" Balle kuma Sunusi,ina ruwan tsami gaye"inji Harira ta na bushewa da dariya.
Habiba ta lashi baki ta na kanne idanu tace.
"Kina ambatar tsami gaye naji sha'awarsa wallahi,ina ma zan ganshi na sha"
"To k'walamammiya......
Shafa'atu ta katseta ta na dariya sannan ta cigaba da cewa.
" Zo in rakaki ki siyo,ana siyarwa a gidan Malam Arabi"
Habiba ta dalla mata harara ta na sakin tsaki,basu da buri illa su tsokaneta akan Malam Arabi.
Har wajen la'asar suna gidan bayan sun ci abinci sun yi sallah,Zahra'u ta na ta yiwa Amarya Hauwa lakca,nan take fad'a mata akwai wani maganin mallaka da ta tab'a amfani da shi kuma taji dad'insa,a wajen wata Y'ar sokoto ta siyeshi dubu biyar,amma zata yiwa matar waya a kawowa Amarya Hauwa'u.
Hauwa ta dinga murna sosai,har da shigewa d'aki ta Lalo dubu biyar ta dank'awa Zahra'u a hannunta,nan da nan Zahra'u kuwa ta lalubo wayarta ta dokawa Y'ar sokoto kira,ba a jima ba ta d'aga suka gaisa,Zahra'u ta fara bayani.
"Wata Amarya ce k'anwata take son kulle zuciyar mijinta,ina fatan akwai wannan maganin mallakar da kika tab'a bani nai nasarar kulle zuciyar K'asimu da shi ?"
Y'ar sokoto ta amsa da karad'inta duk suna jiyota saboda wayar na hands free ne.
"Zahra'u zareriyar mata aikuwa akwai wannan had'in,domin kuwa yanzu ma an k'ara da wasu sinadarai Wanda idan mace tayi amfani da shi ko wuta ta nunawa mijinta tace ya fad'a afkawa zaiyi kai tsaye.
Nan da nan Hauwa Amarya ta soma murna,duk da Y'ar sokoto tace kud'in ya ninka ya zama dubu goma amma Hauwa tace zata biya taji ta gani.
Aka gama magana akan washegari Y'ar sokoto zata kawo magani a bawa Amarya Hauwa domin ta mallaki Mijinta.
COMMENTS
SHARE
VOTE
PLS
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️
[8/7, 11:05] Hassana D'an Larabawaπ₯°: *TYPING*π²
π️ *BAHAGON LAYI* π️
(MAGANIN MALLAKA)
*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR*π
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
*DA KUMA*π
BAHAGON LAYI
*BABI NA SHA BAKWAI DA NA SHA TAKWAS*
*WATTPAD:Hassana3333*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
π *PEN WRITERS ASSOCIATION*π️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*GODIYA MARA YANKE WA GAREKU MASOYANA,HAK'IK'A DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA,MUSAMMAN GROUPS D'IN*π
AISHA BAGUDO FANS
TABITAL PULAKU
ZAUREN JIKAR NASHE
JIDDA REAL FANS
TASKAR FATI TEEJAY
Y'AR MUTAN DIKKAWA NOVELS
WAYE SILAR LALACEWATA FANS
BAHAGON LAYI FANS
DA SAURAN GROUPS D'IN DA BAN AMBATA BA DUK INA SONKU SOSAI,INA KUMA GODIYA GA MARUBUTAN DA SUKE BIBIYAR WANNAN LITTAFI DOMIN KARANTAWA,HAK'IK'A INA JIN DAD'I SOSAI,ALLAH YA BAR ZUMUNCIN MU π€πΉπ₯°πππ
Sai yamma lik'is mijinta ya kusa dawowa sannan suka yi shirin komawa gidajen su,kafin su tafi sai da suka fad'awa Hauwa yanayin tsarin zamantakewar da suke yi a tsakanin su,karb'a karb'a ne tamkar mulkin farar hula,kowacce akwai randa za a yini a gidanta a bararraje ayi girki da hira,hatta da cefane da Kansu suke zuwa basu da almajirai,saboda almajiran yanzu tak'adirai ne a cewar Habiba.
Nan Hauwa Amarya tace.
"Nima na bada goyan baya akan hakan,domin na kan samu kaina cikin kewa idan Hubby ya fita,bai wani d'au Hutu Dan tayani zama ba,gashi zuwan da akewa amare ni ba a yi min ba,sai naji Gidan yayi min ba dad'i,amma yau idan ya dawo zan masa bayanin abin da kuka ce min Dan ya zama ina fita da saninsa"
Har sunje bakin k'ofa Saratu ta waiwayo a zabure ta dubi Hauwa tace.
"Amma ke Y'ar fari ce a gidanku ko?"
Hauwa ta girgiza kai tace.
"Ah ah me kika gani,ina da yayye da yawa ma,ko yanzu tare da yayata akayi bikinmu"
Saratu ta tab'e baki tace.
"Ganinki nayi kamar wata gab'uwa sak'andama,yo in ba gab'unta ba ta ya ya za ki ce zaki sanar da mijinki wannan maganar?d'azu fa naji kince D'an tarangahuma ne yana da zafi,to akul kar ki masa maganar in ba so kike ya nane miki ido d'aya ba ,ki zama irin uwar Mijina Iya me ido d'aya"
Suka k'yalk'yale da dariya,Hauwa ji take kamar ta bisu domin ba ta gaji da jin shaftarsu ba,Shafa'tu ce ta fara gaba ta na cewa.
"Ni fa Saratu sai da kika ambaci Uwar mijinki na tuna yau k'annen Kamilu za su zo,gashi yamma tayi k'ila sun gaji da jira sun ware ma"
Amarya Hauwa da k'yar ta koma bayan ta rakasu soro,suka yi sallama da Zahra'u akan gobe zata kawo mata maganin har gida.
Suna fita suka hango k'annen kamilu su biyu a k'ofar Gidan Shafa'atu,d'aya siririya d'ayar kuma k'atuwa,me k'ibar ce fuskarta a had'e tasha kunu saboda sunfi awa uku tsaye suna jiran Shafa amma shiru duk da ta san da zuwansu.
Suka k'arasa gabansu, Shafa'atu ta d'an washe ba ki tana Sosa k'eya tace.
"Ah ah Amina Ashe har kun iso?nan mak'ota muka Shiga dubiya dafatan dai baku jima da zuwa ba?"
Amina tayi banza da ita tana huhhura hanci,sai Karima ce ta Amsa da cewa.
"Anty Shafa'atu wallahi wajen awanmu uku muna jiranki,da tafiya ma zamu yi sai kawai muka tsaya"
Kafin Shafa tayi magana har Harira ta rigata tankawa.
"Ku kuwa kuka yi ta zama a rana Dan naci sai kace wasu mayu,maimakon ku d'aware zuwa Inda kuka fito?jibi dai waccan Y'ar sukutar yadda rana ta k'ara hurata?wannan dai da Alkubus ce ke za a kwashi girki,ni da dindimi"
Amina ta waiwayo ta zabgawa Harira wata shegiyar Harara,sannan cikin k'atuwar murya tace.
"Ke Dan kutumar ubanki nice Y'ar Sukuta?da man baki San haushinki nake jiba kaf layin nan ke kika maidasu haka,wallahi kika sake cemin Y'ar sukuta sai nayi wa bakinki lukuni,wallahi zaneki zan yi na zauna a kanki"
Duk ragowar suka ja baya saboda tsoran Amina,Dan ba k'aramar k'atuwa bace,amma sai Harira ta fara fiffik'alewa tana nuna Amina da Hannu tana masifa duk da yadda Shafa take janye ta,domin ta san halin Amina,akwai sanda ta tab'a marinta sai da ta kusa suma,Harira kam tak'i ji ta fara zagin Amina.
"Lallai yarinyar nan ba ki da mutunci ni kike zagi?to bani kika zaga ba Zulailaya me kan tantabara kika zaga,an gaya miki ni tsoranki zan ji,bisimillah idan kin fasa dukana kin ci bantan ubanki....
Kan su Ankara suka ga Harira ta wuntsula ta baje saboda mangarin da Amina ta kai mata,ta haye ruwan cikin Harira ta fara sakar mata naushi a kumatu,ihu Harira ta fara da k'arfi jin Amina zata b'urma mata kumatun ta tsabar naushi,da sauri suka yi kan Amina zasu d'agota, tasa Hannu ta ingijesu gabad'aya suka tarwatse har goshin Saratu ya k'ara dukan bango,ai da sauri Saratu ta mik'e tana murza goshinta me kama da suwaita ta nufi k'ofar gidanta tana cewa.
" ina dalili haka kawai a sake rub'a min goshi,gashi ban ajiye wani a k'ark'ashin gado ba,shikenan dani babu spare "
Harira kam ranar tasha duka a hannun Amina ba kad'an ba,bakinta ya karkace kamar wadda ta kamu da paralyze, hak'ori biyu na gaba suka cire ba ki sai jini,idan ta bud'e baki zata yi kuka sai su ganta tamkar horuwa,Ashe dai hak'ori rufin asiri ne a jikin mutane.
Amina kam da k'yar ta d'aga Harira sai da taga Karima na kuka ganin zata yi kisa,sannan ta d'agata ta na ta d'ura mata ashar,Amina har da cewa.
"Kad'an kika gani yanzu,na rantse da Allah sai na auri mijinki na shigo gidanki na kafa sarauta,duk wani iskancinki yazo k'arshe,Tsinanniya me warin mushen jaki kawai"
Da k'yar Shafa'atu da Karima suka janye Amina suna bata hak'uri sai numfarfashi take,yayin da Habiba da Zahra'u suka janye Harira da kamanninta suka sauya saboda dukan da ta sha,suka nufi k'ofar gidanta Dan Shiga da ita gida,Habiba ta rage murya Dan kar Amina ta jiyo ta tace wa Harira.
"Gaskiya Harira kin daku,amma kin bani haushi da ba ki rama ba,maimakon kiyi aljanun k'arya irin nawa,yarda nonuwanta suke ruguza ruguza kamar jarka ki cafki kan d'aya ki cizgo tsinanne,amma shine kika kwanta duk ta zubda miki hak'ora bakinki duk gib'i kamar k'ofar wambai?"
Harira ta zabgawa Habiba Harara ganin basu taimaketa da komai ba an lallasata,said a suka je k'ofar Gidan Harira ta bud'e k'ofa zasu shiga sannan ta waiwayo fuska a kumbure,ta bud'e wargajejen bakinta ta d'aga murya ta na Nuna Amina tace.
"Allah ya isa tsinanniya,Y'ar daba me kama da buhun kwaki,ban yafe miki ba annamimiya matsiyaciya,Y'ar sukuta kawai"
Amina tayi kukan kura ta fizge daga hannun Shafa'atu ta nufi Harira,da sauri Harira ta shige soro ta banko k'ofarta tasa sakata,ta garawa Habiba da Zahra'u k'ofar a fuskarsu,suka koma da baya suka fad'i,a dai dai lokacin da Amina ta k'araso gabansu,Zahra'u ta mik'e da azama tana tatata ta afka gidanta,yayin da Habiba ta fara rarrafe ta kasa tashi,tuni fitsari ya kubce mata a wando don tsoron Amina ganin tayi mata sank'ank'an aka,ba ta san lokacin da ta fara murmushi ta na kad'a kai ba,ta na kallon Amina tanai mata wak'a wai duk don' ta k'yaleta.
"Amina Amina fanteka,Amina Amina Fanteka"
Dariya ta kama Amina ganin fitsarin da Habiba ta saki,ta juya ta na tuntsira dariya har da rik'e ciki,a hankali Habiba ta zame da rarrafe ta shige gidanta kan Amina ta sake waiwayowa,bata San abin da ya sanyayar da k'afafunta suka kasa mik'ewa ba.
*************
Allah ya taimaki Saratu ta tsallake wannan sirad'in,Domin Salisu bai Ankara da fitarta ba lokacin da ya dawo,kuma yadda yaga kwana biyu ta nutsu ta na yi Masa biyayya sai ya zaci ta gyara halinta.
Ita kam Harira ranar a kan Sunusi ta huce haushin dukan da tasha gun Amina,ta dinga surfa masa masifa da bala'i ta hanashi sakat,da ta addabeshi sai ya fice ma ya bar mata Gidan,bai dawo ba sai da tayi barci,da ya fita ne ma suka had'u da Kamilu yazo ya bashi hak'urin abin da Amina k'anwarsa tayi wa matarsa Harira,a nan yake jin dalilin da yasa yaga Harira da wawulo a bakinta,tunda dai ya san ta girma da famfara balle yace.
A gaban Kamilu ya dinga tuntsira dariya yana murna da abin da Amina tayi,daman ya gaji da halinta yana ta so ya samu Wanda zai masa maganinta,aikuwa sosai yaji dad'in hakan,shi Kansa Kamilu saida ya dinga mamakin dariyar da Sunusi yake shek'awa babu damuwa a ransa ko kad'an.
**************
Washegari da safe sai ga Y'ar sokoto ta bayyana a gidan Zahra'u,sai da Zahra'u taga rana ta take sannan suka kwashi jiki suka fad'a gidan Amarya,a lokacin sun san mijinta baya nan,ba k'ara min murna Hauwa tayi ba da ta gansu,ta kawo musu ruwa da lemo har da cincin sannan ta samu waje ta zauna suka gaisa.
Y'ar sokoto ta bud'e k'atuwar Jakarta ta na fito da magunguna iri iri,na Hausa da na turawa,ta kalli Hauwa tana dariya tace.
"Tunda ke Amarya ce bakya buk'atar maganin matsi,Dan na san a matse kike gam,kawai zan baki maganin da zaki k'ara ni'ima,da kuma uwa Uba na mallaka,abin da zan baki idan har kika yi amfani da shi a yau bisa k'a'ida to ina tabbatar miki mijinki ya shiga zuciyarki kin kulleshi ba shi ba fitowa sai yadda kika yi da shi "
Hauwa ta k'ara washe baki dad'i ya cikata sosai,ta dinga jijjiga kai ta na kallon Zahra'u ta na murmushi.
Y'ar sokoto ta zaro wata farar roba sannan tace da Hauwa.
"Kinada reza?Dan aikin na buk'atar reza da zare da allura,amma ni akwai zare da allura a jakata"
Da sauri Hauwa ta amsa.
"Eh akwai reza,in d'auko ne?"
"Eh d'auko,sannan ki had'o da matashin da kika san Mijinki yana d'ora kansa akai ya kwanta idan za ku yi bacci"
Hauwa ta mik'e da Hanzari ta nufi d'aki,Jim kad'an ta fito da matashi a hannunta da reza,Y'ar sokoto ta karb'i matashin ta cire rigar jikinsa,sannan tasa reza ta D'an farkashi kad'an,duk Hauwa da Zahra'u suna kallonta,ta bud'e wannan farar robar ta fito da abubuwan da ke ciki,Hauwa ta zaro idanuwa ganin layoyi da wani kwad'o da mukullaye,Y'ar sokoto tasa mukullin jikin kwad'on ta bud'e shi, ta kalli Hauwa tana murmushi tace.
"Kinga yadda na bud'e kwad'on nan ?to a yanzu haka mun bud'e zuciyar mijinki"
Sannan ta d'akko layar ta sak'ala a jikin kwad'on tasa D'an mukullin ta kulle tsaf,ta kuma kallon Hauwa da ta tsura mata idanu tace.
"Haka nan yadda na kulle kwad'on nan mun kulle zuciyar mijinki kenan,sai yadda kika yi da shi "
Ta jawo matashin inda ta b'ula ta zura kwad'on da layar da mukullayen nan a cikin matashin,sannan tasa allura da zare ta d'inke tsaf,ta maida matashin cikin rigarsa ta mik'awa Hauwa,Hauwa ta mik'o hannu ta karb'a tana sauraren bayanin Y'ar sokoto.
"Matuk'ar yau mijinki ya aza kansa kan matashin nan kin gama mallakarsa a tafin hannunki,ina tabbatar miki biyayyar da zai miki ko uwar da ta haifeshi ba zai mata ba"
Saboda jin dad'i dubu goma ne kud'in maganin,amma Hauwa dubu sha biyu ta bawa Y'ar sokoto har da turmin atamfarta gallele na cikin lefe,Y'ar sokoto ta dinga murna,da suka fita ta dinga yiwa Zahra'u godiya da ta had'ata da mutuniyar arzik'i.
Amarya Hauwa akayi kwalliyar tarbar miji aka yi girki mai dad'i yaji onga da tafarnuwa,Ango Idrees ya dawo ya kwashi girki kunnuwansa na motsi,ko irin hirar Daren nan Hauwa bata bari sunyi ba ta isheshi akan suje su kwanta bacci take ji,tana wani langab'ewa,shi kuwa ji yake ai gaba ta kaishi tunda ta nemi aje a kwanta da kan ta,suka sauya kayansu zuwa na bacci suka haye gado.
Tashin farko Idrees yana d'ora kansa kan matashi yaji Abu ya tsireshi,da sauri ya muskuta ya ajiye kumatunsa kan matashin,ba zato ba tsammani yaji tsinin Abu yana k'ok'arin b'urma masa kumatu,Ashe tsinin mukulline,da Hanzari ya mik'e yana zare idanu,ita kuwa Hauwa ta zaci maganin ne ya fara ci har ta fara murna a zuciyarta,sai gani tayi ya d'ago matashin yana kallo,sannan cikin b'acin rai yace.
"Wato masu saida matashi sun zama maha'inta mugwaye,a maimakon susa katifa mai laushi sai su dinga zuba yayi da tsummokarai,ina tunanin allurai ne a ciki bakiji yadda suke tsireni ba"
Hauwa ta zaro idanuwa k'irjinta na bugawa ta kasa magana,Idrees ya dinga tattab'a matashin yana girgizawa,kawai sai yaji kacar kacar kacacar a ciki,mamaki ya kuma kamashi,ya kalli Hauwa da gumi ya fara yanko mata yace.
"Jiddatu na wani motsi nake ji da k'ara a cikin matashin nan,d'akko min reza na farke naga abin da ke ciki mana"
Ta sauke gwauron numfashi tana zare ido ta fara in ina.
"Wal...wallahi....banga ..banga rezar ba,babu ..reza a gidannan...ma"
Ya D'an kalleta yaga yadda take a rud'e,kawai sai ya mik'e da azama ya nufi ktcheen ya d'akko wuk'a,yana shigowa d'akin Hauwa ta daka tsalle ta b'uya bayan gado saboda yadda taga wuk'ar na walwali kar taje ya Burma mata,domin yana da zafi bai iya fushi ba,ko kallonta bai yiba yasa wuk'ar ya farke matashin yana zazzago shi,kawai sai kwad'o da mukullaye suka fad'o har da layoyi a jiki,ya yarda matashin yasa Hannu ya d'auko mukullayen yana kallo zuciyarsa na bugawa,a zafafe ya kalli Hauwa da ke mak'ure yace.
"Fito nan"
Ta kasa fitowa jikinta na rawa har ta fara hawaye,ya daka matsa tsawar da ta sa hancin cikinta curewa guri guda jin ya danna mata ashar.
"Ba za ki fito ba sai nazo nan naci kutumar ubanki?
Ta jawo jiki ta fito tana kuka,ya d'aga abubuwan hannunsa ya nuna mata,cikin fushi yace.
" menene wannan?
Bakinta na rawa ta fara magana,a ganinta gara ta gaya masa gaskiya kurum,shiyasa cikin kuka tace.
"Maganin Mallaka ne"
Ya tsura mata idanu kamar ya gaura mata mari yace.
"Maganin mallaka?ni za ki wa Asiri Hauwa?wane D'an iskan ne ya baki maganin domin wayonki bai kai kiyi tunanin yi min asiri ba?
Ta rushe da kuka sosai ta na rantse rantse,sannan ta gaya masa duk abin da ya faru,nan da nan zuciyarsa ta k'ara k'uluwa sosai,ya fara yi mata tambayoyi akan matan bahagon layi ta na ba shi amsar abin da ta sani,so sai hankalinsa ya tashi ganin zasu lalata masa tarbiyyar matarsa,Ashe da gaskene abin da ake fad'a a Kansu?mutane da yawa sun sameshi akan ya kula da matarsa kar tayi huld'a da matan,ya zaci sharri ne Ashe gaske ne,aikuwa tilas ya d'auki mummunan mataki a Kansu ta yadda ko ance su k'ara shigowa gidansa sai sun zura da gudu.
Haka Hauwa ta dinga ba shi hak'uri da nadama,da k'yar ya hak'uri da niyyarsa ya korata gidan iyayenta a k'ara koyamata tarbiyya,tunda cikin kwanaki k'alilan shashashun mata sun fara fatali da tarbiyyarta,amma da ta rungumeshi cikin kuka ta kanainayeshi tilas ya hak'ura ya tarbeta,babu kuma abin da yake jira illa gari ya waye yaga wad'annan mata sun shigo,Lallai zasu ga tijara ganin idanuwansu.
Kamar kuwa ya san zasu shigo washegari yak'i fita kasuwa ya zauna zaman jiran shigowarsu,ya mak'ale a d'aki ya bawa Hauwa umarnin kar ta gaya musu yana nan,babu b'ata lokaci ya kira wani abokinsa D'an sanda yace yazo gidansa kuma ya tawo da tiyagas,cikin mintuna k'alilan ya iso ya fita ya shiga dashi har cikin d'aki.
Harira kam Dan masifa ta zauna ma tayi jinyar bakinta kasawa tayi,k'afarta na k'aik'ayin fita,gulma na cinta ta na son zuwa gidan Amarya aji yadda aka kaya da maganin mallaka ko yayi tasiri,aikuwa ta fito ta fad'a gidan Habiba,daga nan suka biyawa Zahra'u da Shafa'atu,suna zuwa gidan Saratu fir tak'i fitowa ta na ganin kamar Salisu zai gane ta fita,babu yadda basu yi ba tace gara tayi lek'en ta yafi mata sauk'i akan ta fita.
Sha d'ayan rana a gidan Amarya tayi musu,aka baje a falo ana kwasar hira ana darawa da tafawa,Hauwa ta biye musu suna tayi mata tambayoyi tana basu amsa.
Zahra'u ce me cewa.
"Ni kuwa kulun majadan ya maganin da aka baki jiya?kin yi amfani da shi ya d'ora Kansa a matashin?
Hauwa ta girgiza kai ta na dariya tace.
" Sosai ma,ai wannan maganin sha yanzu magani yanzu ne,yana sa kansa jikin matashin ya rikice,tsakanin jiya zuwa yau duk abun da na sashi yi min yake da Hanzari "
Harira ta kwashe da dariya wawulonta ya bayyana,tace.
"Shegen sama yana tafiya kamar na sammasa kwankwaso,ai wallahi Hauwa tunda kin mallakeshi karki raga masa,kici Uwatar kawai,in ya raina miki ajawali ki wawushi wannan kurtsitsin kwankwason nasa ki maka shi da k'asa"
Habiba da Shafa'atu suka kwashe da dariya,haka suka cigaba da aibata Idrees suna ci masa mutunci a gaban Hauwa,ita kuma tana ta biye musu,basu san ramin mugunta ta had'a musu ba,suna cikin shewa kawai sai ganin Idrees suka yi a gabansu fuskarsa murtuk,suka fara zare idanuwa suna gyara zama,Habiba ta jawo d'ankwalinta da garin hira ya zame ya fad'i,suka hau rige rigen gaisheshi muryarsu na rawa cike da tsoro.
Yayi wani miskilin murmushi na mugunta ya jinjina musu yace.
"Sannunku wakilan Shaid'an,barkanku da zuwa tatattun y'an iska,marhabun daku shakiyyai fitsararru tantirai,ina muku lale maraba da zuwa gidan da za ku sha tiyagas"
Wani d'imemen tashin hankali ya rufto musu a lokacin da suka ga D'an sanda ya bayyana a gabansu da k'aton kulki a hannunsa,k'ato dashi fuskarta bak'a k'irin babu alamun imani,babu wadda bata saki fitsari a wando ba tsabar tsoro,nan da nan suka fara kuka da Neman Afuwa,D'an sandan ya dubi Harira ya na Nuna ta da kulkin Hannunsa yace.
"Ke yanzu Dan ubanki tsofai tsofai dake bakinki duk ba hak'ora kike shuka iskanci?kina shiga cikin y'ay'an cikinki kuna tab'argaza?
Harira ta fashe da kuka tace.
" wallahi yallab'ai ofisa yarinyace ni shataf,mahangurb'a nasha jiya hak'orana suka zube ba tsohuwa bace"
Ya jijjiga kai ya na zagayesu yace.
"Jiya kin sha mahangurb'a yau kuma za ki ci na jaki kuma kisha tiyagas Dan ubanki,shegu daga yau idan an ce ku sake shiga gidan wani kuyi gulma ba zaku yi ba.
Ya kalli Idrees yace.
" ja matarka ku shige d'aki ka barni dasu "
Idrees ya ja hannun Hauwa suka fad'a d'aki suka rufo k'ofa,Hauwa ta na yi musu gwalo,su kuma suna kuka suna Neman ceto da danasanin shigowa,Allah ya taimaki Saratu bata biyo su ba da har da ita za a tarfa.
D'an sanda baiyi wata wata ba ya fara buga musu tiyagas yana lodarsu da kulkin hannunsa,ihu da kururuwa kawai suke yi suna jin tamkar su mutu saboda azabar,idan ya buga tiyagas sai ya daidaici gadon bayansu ya muk'a musu kulki,Harira kam har a baki ya dinga muk'a mata,wai gara ya zubda hak'oran gulma a huta.
Wani mugun ihu Habiba ta saki jin ya sauke mata kulki a agararta.
0 comments:
Post a Comment